Entertainment

Yadda Ake Samun Lambar Wayar Budurwa

Yadda Ake Samun Lambar Wayar Budurwa

Yadda Ake Amsar Lambar Wayar Budurwa

Baiwa namiji lambar waya alamune na mace tana da ra’ayin Namiji. Hakan yasa da wuya cikin sauki namiji ya samu lambar wayar mace musamman a farkon haduwarsu. Sai dai akwai wasu dabaru da maza suke dasu domin samun lambar wayar mace cikin sauki kamar haka:

  • Da farko dai ka saka a ranka tana iya hanaka, kuma zata iya baka. Don kada kaje da tunanin dole sai ta baka.
  • Don haka ba kai tsaye daga zuwa zaka bukaci lambar wayan nata musamman idan a ranar kuka soma haduwa.
  • Don haka a mataki na farko ka saka a ranka babu dole na sai ta baka.
  • Mataki na biyu na karbar lambar wayar mace kada ka je mata da tsoro. Ka tinkareta da saurin idanu a matsayinka namiji.
  • Mata suna son ganin namiji mai kwarjini ba wanda zai rika sanyi ba ko tsoro.
  • Don haka kaje mata a matsayin namiji wajen neman lambar wayan nata ciki karfin hali shine mataki na biyu.
  • Dole ne ka tabbatar ka tanadi amsar da zaka bata idan ta nemi sanin mai yasa kakeson lambar wayar nata, wanda kuma zai yi wuya ka nema bata tambaya ba.
  • Amfar da zaka bata na dalilin dayasa kake son lambar wayarta shine mataki na 3.
  • Kada kai tsaye ka soma tambayar ta lambar waya bayan ka tsaida ita ko ka mata magana. Shigo da hira ko zancen da zai dauke hankalinta ya kuma sa ta saki jiki da kai shine abu na 4 da zaka yiwa macen da kake bukatar karban lambar wayarta.
  • A mataki na biyar idan har ka nemi lambar ta soma ja maka aji, kada ka takurata rabu da ita, a kalla yanzu ta fahimci kana bukatar lambar wayarta koda nan gaba zaku sake haduwa ka tambayeta.
  • Idan tana tare da kawayenta ko kannenta ne kada ka waresu daga hiran taku. Shigo dasu cikin maganar zai sa a samu wata daga cikinsu da zata iya daka baki domin ta baka lambar wayar. Hakan kuma zai rage zafin adawa ko kishin da zasu ji na kebe su daga abunda kuke zantawa.
  • Mataki na karshe kada ka dauki lokaci mai tsawo wajen neman sai ta baka lambar wayarta. Ka mutunta lokacinda ta baka. Kuma ka fahimci ba wajenka tazo ba tanada wani uzuri ka tsaidata.

Sakonnin Soyayya Na Barka Da Shan Ruwa

Leave a Comment