Yadda Ake Rarrashin Miji ko Saurayi Idan Ransa Ya Baci
Rarrashin Miji ko Saurayi: Bacin rai dai dabi’a ne da duk wani mutum yake da shi. Sai dai abubuwan dake batawa mutane rai sun bambamta. Bacin ran ma’aurata abune da ba aso, amma dole ake samun hakan. Sai dai kuma rashin sanin yadda ma’aurata zasu kwantarwa juna hankali a lokacin bacin rai yayi karanci. Musamman mata. Ga wasu hanyoyin da zaki kwantarwa mijinki rai.
- Kada ki rika cewa mijinki yana cewa a lokacinda ransa yake bace. Bashi hankalinki kuma ki saurare shi yadda zai fahimci bacin ran nasa ya dameki.
- Duk irin gaskiyar da kike da shi kada ki nunawa mijinki kice mai gaskiya a lokacinda ransa yake bace. Nuna masa yafiki gaskiya idan bacin ran dake yake yi. Idan wani ko wasu ne suka bata masa rai goyi bayansa. Nuna masa basu yi daidai ba. Kada ki bata rai a lokacin da mijinki ya bata nasa rai. Saki fuskarki ba ki nuna masa kema ranki yana bace ba saboda ya miki mita.
- Rike hannunwansa kina wasa da tafin hannunsa kina mai nuna masa baki son ganinsa a irin wannan yanayin bare kuma yara. Nuna masa yayi hakuri ko domin kada yara su ganshi ransa a bace.
- Idan mijinki yana fushi ne a tsaye jawo shi ki zaunar dashi. Idan yana zaune jawo shi jikinki. Yadda zai ji musamman nonuwanki yana sukansa cikin hikima.
- Tabbatar masa ba za a sake aikata wannan abun da ya jawo masa bacin rai ba. Kuma yaga hakan a fuskarki.
- Kirashi da suna mafi soyuwa a wajensa a lokacin da ran mijinki yake bace. Cikin tattausar murya zaki furta kalmai da sunansa da yake so a fadamasa ko yake fata da buri kamar His Excellency idan Dan siyasa ne. Allah Ya Maka rawa rai idan masarake ne, Allah Ya huci zuciyar Shike idan Malami ne.
- Kada ki shigo da wani na ku a lokacin da mijinki yake cikin bacin rai. Idan da wasu a wajen jawoshi cikin daki ko inda zaku kadaita.
- Samu ruwa mai sanyi ko Lipton mai zafi, idan abocin son cafe ne mika masa a lokacin da ransa yake bace. Lallabeshi ya Sha, yana sakawa a baki ki kula zaki ga fuskarsa ya saisaita.
- Ki dan bashi waje shi kadai ya kasance. Kamin ki barshi shi kadai ki tabbatar kin taba jikinsa, kin yi masa wasa da hannayensa, kin sumbaci kumatunsa, kin goga masa nonuwanki sunada tasiri wajen jawo maigida ya wuce da wuri.
Yadda Ake Samun Lambar Wayar Budurwa