Amfanin Citta Ga Jiki Dan’adam
Sakamakon tambaya da wani bawan Allah yayi min cewar wai don Allah “meye amfanin CITTA ga jikin ɗan Adam?” Dukda cewa Ni ba masanin kimiyyar abinci bane amma muna da alaƙa wajen sanin amfanin wasu cimaka dake alaka da kiwon lafiya. Amfanin CITTA ya haɗa da;
- Maganin Tashin zuciya. kamar masu samun tashin zuciya lokacin hawa mota ko ga mata masu juna biyu.
- Maganin rashin narkewar abinci da wuri ( Indigestion ), kumburin ciki ko rashin jin dadi a ciki bayan anci abinci.
- Taurin Bahaya (Constipation) Basir.
- Rage ciwon mara ga mata lokacin al’ada.
- Maganin ciwon jiki da gabobi. kamar wanda yayi wani aikin karfi, ko yake da (osteoarthritis).
- Maganin ciwon makogaro , Mura ko Tari.
- Bada Ɗandano a girka.
- Tana rage kitsen dake cikin jini. musanman ga masu hawan jini.
Amfanin ta na da yawa amma na ɗauki masu mahimmanci ne kawai. Citta na kunshe da wani sinadari da ake ce masa ” Gingerol ” wanda shi yake bata damar amfanar da jiki. Bayanan sa na da yawa sai dai mu barshi haka.
Yadda ake amfani da citta
- Ga masu fama da tashin zuciya, mutum zai iya samun bushashshiyar CITTA yar kaɗan ya dan dinga tsotsa har iya yadda ya daina jin tashin zuciyar.
- Ga masu matsalar narkewar abinci, kumburin ciki da sauran matsalolin ciki da na ambata a baya, mutum zai iya haɗa ruwan shayin CITTA bushashshiya ko ɗanya, amma fa kar tayi yawa, sai yasha. Anan ma mata masu fama da ciwon mara( riƙewar mara)lokacin al’ada suma su hada shayi mai zafi sai su sa CITTA a ciki ɗanya ko bushashshiya. Amma wajen haɗa shayi ɗanya tafi daɗi. Masu ciwon jiki ma duk haka za suyi.
- Ga masu fama da ciwon makogaro da tari, suma su haɗa shayin da CITTA sannan sai su sa lemon 🍋 tsami a ciki.
Mutanen da baza suyi amfani da citta ba
- Masu Ulcer saboda CITTA na da zafi
- Wanda yake kan magunguna kamar misalin, Aspirin, Ibuprofen, Naproxen, wafarin da sauransu. saboda tana tsinka jini, sannan suma magungun haka.
- Wanda yake da wata matsalar fitar jini daga cikin sa. musanman in yayi Bahaya yana ganin jini, to shima karya dinga amfani da CITTA.
Abubuwan da citta ke haifarwa
- Gudawa, In mutum ya sha da yawa ko kuma jikin shi bazai iya jura ba zai iya gudawa.
- Kunar cuziya ( Heart burn).
- Matsananciyar tashin zuciya; saboda ka sha da yawa.
Wannan shine iya abun da zan iya karar da ku ilimi. Bayananta na da yawan gaske wasu abubuwan bayanin zaiyi wuyar fassara da Hausa.