Amfanin Ganyen Magarya a Jikin Dan’adam, Amfanin Ganyen Magarya a Gaban Mace, Amfanin Ganyen Magarya ga Budurwa, Amfanin Ganyen Magarya ga Mata
Amfanin Ganyen Magarya: Itaciyar magarya wadda aka fi sani da (Assidir) a larabce kuma (Lote) a turance, itaciya ce mai albarka da dadewa Annabi S.A.W ya tabbatar da amfaninta. Magarya na kunshe da magunguna masu matukar mahimmanci ga jikin dan Adam kuma ta na da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci.
Ita Magarya Antibiotic ce mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah ba ta da wani illa wato side effects na a zo a gani. Ga abinda mu ka dan Kalato muku dangane da amfaninta :
- Ta na maganin Ciwon daji (cancer) : Idan ana dafa garin magarya ana sha da zuma ya na kashe kwayar cutar daji ko da a cikin jini ne.
- Ta na da karfin yakar cutar fata kamar irinsu tautau, makero,Kazuwa da sauransu. A kwa6a wa da zuma a dunga sha ana shafawa a Wurin da abin ya shafa.
- Ta na tsaftace jini domin ta na dauke da sinadarin Saponin,alkaloid da triterpenoid wadannan Sinadarai ne masu tsaftace Jini.
- Sha Ganyenta da ruwan zafi ya na magance gajiya da ciwon Jiki.
- Ta na magance ulcer idan ana shanta da madara ko zuma.
- Ta na taimaka wa hanta ya hanata jin ciwo da cututtuka.
- Magarya na daidaita nauyin mutum.
- Ta na tsaida zawo cikin kankanin lokaci idan aka Sha Ganyen da ruwa ko a kunu.
- Ta na taimaka wa wajen mikar da kasusuwa musamman ga mai karaya.
- Ta na maganin rashin sha’awa ga mata idan su na tsarki da ita kuma su na sha da madara.
Amfanin Sabara ga Mata da Maza