Health Care

Amfanin Kankana ga Lafiya Dan’adam

Amfanin Kankana ga Lafiya Dan'adam

Amfanin Kankana: Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuka ga jikin bil’adama. Masana sun bayyana Kankana da ƴaƴan itaciyar mai matukar amfani ga rayuwar bil’adama, don sindarai da ke cikinta na Vitamins da Minerals da Antioxidants da kuma Calories.

Kankana na da nau’ika biyar: akwai mai ƴaƴa da mara ƴaƴa, akwai mai kalar ruwan dorawa da dan karami kore da mai kama da lemun zaƙi. Sai dai a galibin kasashen Afirka irin Najeriya koriyar kankana mai ƴaƴan itatuwa aka fi sani.

Kashi 92 cikin 100 na kankana ruwa ne zalla, don haka mai yawaita shanta ba shi da matsalar ƙarancin ruwa a jiki, musamman lokacin zafi, in ji Maijidda Badamasi Burji da ke da ƙwarewa a ilimin abinci mai gina jiki. Ga wasu abubuwa 9 da ƙwararru ke cewa kankana na iya a jikin dan Adam:

Kara ruwan jiki

Rashin shan ruwa na illa sosai ga jikin dan adam, hakan yasa ake yawaita jan hankali mutane kan alfannu shan ruwa domin inganta lafiyar jiki. Sai dai shan ƴaƴan itatuwa irin kankana wanda kashi 92 cikin 100 ruwa ne zalla zai maye gurbi bukatar da ake da ita na yawaita shan ruwa. Sannan kankana baya ga ruwa akwai sinadarin Fiber a jikinta, don haka shan ta tamkar anci abinci ne mai matukar inganci wanda ke kunshe da galibin sinadarin da jiki ke bukata.

Sinadarin Vitamins da Minerals

A cikin jeren kayan marmari ko itatuwa, Kankana ita ce wacce ke da karanci sinadarin calories. Calories din da ke jikinta bai kai na ƴaƴan itatuwa da ake ganin kwata-kwata basu da zaki ba, danginsu inibi. Kofi guda na ruwan kankana na kunshe da sinadaran Vitamin C da A da Potassium da Magnesium da Vitamis B1 da B5 da B6.

Kariya daga daji ko Cancer

Daga cikin sindaran da ake samu a jikin kankana akwai masu bada kariya daga wasu nau’ikan ciwon daji ko cancer. Bincike ya nuna cewa masu yawaita shan kankana masu fiye kamuwa da cancer ciki ba.

Kariya daga ciwon zuciya

Ƙwararu sun sha cewa ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen hallaka mutane a duniya baki ɗaya. Sai dai an lura akwai nau’in cimakar da ke taƙaita bugun zuciya da shanyewar barin jiki ta hanyar rage kamuwa da hawan-jini da rage kitse a jiki. Sinadarai da dama a jikin kankana na iya samar da waraka da taimaka wajen yaƙi da wadanan cututtuka.

Garkuwa da kuzari

Kankana na bai wa jiki garkuwa, sannan yana taimakawa da sinadarin da ke taimawa halittar da suke yaki da cututtuka da kuma samun wakara daga ciwo ko rauni, sannan tana maganin kasala da sa kuzari.

Ƙwarin Ido

Shan kankana na kara ƙwarin ido da kariya daga kamuwa daga wasu cutuka ido masu lahani ko kai wa ga makanta. Mutanen da ke yawaita shan kankana ko ɗiga ruwanta a ido kan tsufa da idanunsu a cewar ƙwararu

Maganin kumburin gabobi

Sinadarin citrulline, da ke jikin kankana, na rage kumburin gabobi. Sannan ana amfani da shi a hada magunguna kara ƙwarin gabobi da cutukan da ake samu saboda yawaita zama ko kin motsa jiki. Hakazalika yawaita shan kankana da bada kariya daga kamuwa da Basir.

Gyaran fata da gashi

Vitamins A da C na cikin kankana na da muhimmanci sosai wajen baiwa jiki sinadarin collagen da ke sa fata laushi da kyau da gyara gashi da kwari.

Taimaka wa wajen narkewar abinci

Kankana da kunshe da ruwa sosai don haka shanta na taimaka wajen narkewar abinci. Yawaita shanta na hana cushewar ciki da bai wa jiki dama sarafa abinci da narkewarta cikin dan kankanin lokaci.

Ko ku san sirrin ƴaƴan kankana ?

Watakil kana/kina cikin mutanen da ke zub da ƴaƴan kankana wajen shanta – ko tsameta kafin ayi amfani ko sarafa kankana. To ga wasu bayanai masu muhimmanci da muka tattara da ka iya taimaka mu ku wajen sauya ra’ayi kan ƴaƴan kankana a tattaunawarmu da Maijidda Yahaya.

Ƴaƴan kankana na da sirika sosai da ba kowa ya san da su ba, suna kunshe da sinadarin Zinc da Magnesium da Potassium da Iron da dai sauransu. Ƴaƴan kankana na bai wa jiki garkuwa da matsalar ciwon zuciya da hana ko warkar da ciwon suga da inganta jima’i. Ga karin alfannunsa ga jikin dan adam.

  1. Yana sa kuzari
  2. Inganta jima’i ko saduwa
  3. Gyara maniyin maza musamman masu matsalar haihuwa
  4. Inganta lafiyar kwakwalwa
  5. Kwarin kashi
  6. Garkuwar jiki
  7. Warkar da Ciwon suga nau’i na biyu ko Diabtes type 2 a Turance
  8. Ƴaƴan kankana na gyara gashi ga mace
  9. Gyara fatar jiki
  10. Lafiyar zuciya

Minene Amfanin Jima’i ga Mata da Maza

Amfanin Kankana ga Mace, Amfanin Kankana da Madara ga Mace, Amfanin Kankana da Dabino, Amfanin Kankana

Leave a Comment