Health Care

Amfanin Man Almond a Jikin Dan’adam

Amfanin Man Almond a Jikin Dan'adam

Amfanin Man Almond A Jikin Dan’adam

Amfanin Man Almond: Almond wasu tsirran wata bishiya ce masu siffar diyan dabino alhali ba dabinon ba ne. Da larabci ana kiran ta suna zaitul Lauz. Ya samo asali ne a yankin gabas ta tsakiya da kuma gabacin Asia. A wajajen karni na goma sha tara(19th century) Jihar California da ke a kasar Amurka, ta bi sahun jerin wasu kasashe masu samarda wadanannan tsirran itatuwan na almond, bayan da wasu masanan kimiyyar hada magani suka bankado wasu muhimman magungunnan da almond ke yi a doron kasa wadanda duka an jarraba kuma an samu galaba. Ga abin da binciken kwararrun masana kimiya da harhada magani suka gano a kan man Almond.

  • Fatar jiki na da bukata da man almond : A hakika man almond yana lausasa fata koda ta kasance a bushe, zai darje garjinta ya fitar d kaushinta ya ingantata ya kuma maida ta fata mai laushi da kyalkyali musamman ga mata ‘yan kwalliya.
  • Zuciya na da bukata da man almond, domin kuwa yana inganta aikinta. Mun dai san muhimmancin lafiyar zuciya, don haka sai mu kula da ita zaman ta ginshiki.
  • Babbar hanzanya waton (colon) na matukar bukata da man almond, domin saukin fitar da kasha, musamman bayan-gari mai karfi. A nan, man almond kan zamo tamkar mai da zai rinka jike colon din don sauwake wahalar fitar bayan-gari ko yawan yin yunkuri ko jin zafi a lokacin bayan-gari.
  • Yana narkar da kitsen tumbi musamman ga masu jiki ko kiba wanda yawan kitsen kansa ya daskare hanji, ya zamo wani abu mai haifar da illa ga lafiya, illa ga zuciya da kuma hanyoyin jinni su kansu.
  • Mai fama da yawan bugawar zuciya zai iya amfani da almond oil.
  • Mai cin abinci nan take sai cikinsa ya kumbure ya rinka jin kamar zai yi amai ko tashin zuciya ya dame shi, inda zai rinka zubar da yawu sai ka ce mace mai juna biyu, sai ya fake amfani da man almond.
  • Wanda ya san yana jinya ko yana fuskantar barazanar kamuwa da ciwon daji waton (cancer) sai ya rinka shan man almond.
  • Mai ramewa yana tsotsewa kan wata rashin lafiya na nan da ake kira da suna anorodia nebosa waton cuta da ke hana cin abinci, to sai ya yi amfani da man almond da kuma man tafarnuwa mai kyau.
  • Mai ciwon suga sai ya fake amfani da man almond.
  • Masu nauyin jiki ko kiba a jiki, to za su iya rage nauyi sosai ta hanyar yin amfani da man almond. Kowani giram 100 na man almond yana dauke da kaso 60 na sinadirin Bitamin E. Wanda yana da muhimmanci sosai ga lafiyar fata da kuma karfin maniyin namiji.
  • Akwai almond mai daci da ake kira bitter almond, domin wannan da muke magana shi ake kira sweet almond oil. Shi bitter din yana dauke da anti biral, anti bactetial da kuma anti fungal. Ka ga kenan maganin wasu dimbin kwayoyin cuta ne.
  • Man almond na sassauta kumburin hanji na ciki da kuma kumburin jiki.
  • Allurar man almond (almond injection) ta kasance abu ta farko da aka fara amfani da ita a matsayin hanyar warkar da cututtukan nan da ke rike dubura ga kananin yara. A wani bincike da tsangayar nazarin magani waton ‘Faculty of Meficine’ da ke a Jami’ar Cairo, na kasar Egypt ta gudanar, binciken ya tabbatar da cewa kashi 93 a cikin dari na majinyatan da ke fama da rashin lafiyar nan ta kakayin dubura, sun warke duka bayan an yi masu ita wannan annura ta man almond. (almond oil injection). Sai dai mu a nan kasashen bakaken fata ba kowane ilimi muke das hi ba, haka koma akwai ilmin to hanyoyin aiwatar da shi wani kalu bale ne.
  • Man almond na maganin ciwon kunne ga yara, sai a diga shi a cikin kunnen da ke ciwo.

Amfanin Citta ga Lafiyar Mata da Maza

Leave a Comment