Health Care

Amfanin Namijin Goro ga Maza da Mata

Amfanin Namijin Goro ga Maza da Mata

Amfanin Namijin Goro

Amfanin namijin goro wurin ƙarfin maza, maganin sanyi nada yawa sosai, ga wasu kadan daga ciki.

  1. Namijin goro ya kunshi sunadaran quinones da kolaviron wanda ke warkar da zazzabin cizon sauro a wani bincike da aka gudanar a shekarar 2010, kuma aka buga a mujallar Medicinal Plants Research a Jamhuriyyar Kasar Congo.
  2. Bincike ya nuna cewa, sunadaran antioxidants dake cikin namijin goro suna inganta lafiyar Hunhu.
  3. A wani bincike da aka gudanar aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka ya bayyana cewa, yana kawarda cutar idon nan ta Glaucoma.
  4. Amfani da namijin goro yana hana teba da rage nauyin jiki, domin kuwa yana sanya shan ruwa matuka.
  5. Sunadarin saponin da antibiotic dake kunshe a namijin goro sukan taimaka wajen karfi da tasirin kwayoyin cutar kanjamau.

Illolin yawan cin namijin goro

  1. Namijin goro kan iya haddasa kansar baki (mouth cancer): Yawan cin namijin goro kan iya jawo ciwon dajin baki ko kuma uwar hanji. Namijin goro na dauke da sinadarin gahawa (caffeine) mai yawa, yawan gahawa a jiki kan iya kashe mutum ko ya jawo ma sa ciwon zuciya.
  2. Namijin goro yana taba ido/gani (glaucoma): Cin namijin gora kadan na taimakawa ido/gani, sai dai cinsa da yawa na iya haddasa matsalar idanu. Akwai bukatar ya kula da adadin namijin goro da ya ke ci a rana.
  3. Yana tunzura gudawa: Namijin goro na iya tunzura gudawa idan aka ci shi da yawa. Masana sun shawarci ma su fama da gudawa su guji cin namijin goro

Amfanin Citta ga Lafiyar Mata da Maza

Leave a Comment