Health Care

Amfanin Sabara ga Mata da Maza

Amfanin Sabara ga Mata da Maza

Amfanin Sabara ga Lafiyar Jiki

Amfanin Sabara: Ganyen sabara nataka muhimmanchi sosai arayuwar dan adan kawai rashin sanine da mafi yawanchin mutanenmu basuyiba domin hausawa nacewa magani agonar yaro amma ga kadan daga cikin amfanin sabara ga dan adam.

A kasar Hausa, mata su kan yi amfani da ganyen sabara a sanda suka haihu, inda suke dake ganyen ta su yi kunun gero suna sha dan kara yawan ruwan nono da kuma inganta lafiyar ciki.

Ana amfani da garin ganyen sabara dan warkarda ciwon daji waton cancer a Turance.

Ganyen sabara na maganin kumburin jiki da kaikayin jiki.

Ganyen sabara na maganin kurajen kazzuwa da kurajen fiska masu kaikayi da kuma zafin jiki dama na ciki.

Ganyen sabara na magance tarin asima da kuma tarin tibi.

A kan gauraya garin ganyen sabara da garin bawon bagaruwa dan a yi maganin kuna a jiki.

A kan hada wasu ganyayyakin itatuwa da ganyen sabara a tafasa ko a dake a maida su gari dan a iya warkar da basir, gudawa, cututtukan ciki, farfadiya, ciwon gabobin jiki, hawan jini, kuturta da dai sauransu.

A kan yi amfani da danyen ganyen sabara dana nunu sai a tafasa macen dake jego sai ta rinka surace da ruwan hakan zai ba ta lafiya da karfin kassan jiki da kuma rage kumburin jiki ko na kafafuwa dama jin ciwo a bayan haifuwa.

Macen dake shayarwa za ta iya fake shan kunun sabara dan ta tsabtace nononta dama kara yawan ruwan mamma.

A kan tafasa saiwar sabara sai a tace ruwan a sha da safe kamin a ci abinci dan kashe tsutsar ciki.

Ana tafasa saiwar sabara da kuma kirya sai a rinka zama a cikin ruwan dan magance basir maisa kaikayin dubura da kuraje ga dubura kai har da basir mai tsiro.

Ana amfani da sabara dan magance kurajen da suka yi lailayi a cikin baki ko harshe.

Ana shan cokali daya karami misalin 5ml na garin sabara a cikin nono sai a sha a sanda ake fama da dan kanoma.

A nasu tsarin maganin gargajiyan, Sudan su kan yi amfani da ganyen sabara su yi maganin ciwon suga.

Sabara na maganin amosanin kai da kuma iskan dake ma yawo a cikin jiki kamar tana.

Amfanin Gishiri a Gaban Mace

Leave a Comment