Health Care

Sirri da Amfanin Cin Yayan Kankana ga Mata da Maza

Sirri da Amfanin Cin Yayan Kankana ga Mata da Maza

Yadda ake Amfani da ƴaƴan kankana

Amfanin Yayan Kankana: Kana iya taunewa hade da kankana, ko a shanyata ta bushe ko a soyata sama sama. Duk yada mutum ya sarafata zai ji dadinta.

Amfanin Ɓawon kankana

Na san galibin mutane idan ana shan kankana zub da ɓawonta ake yi ko a shanye jiki a ɓare bayan a zubar. To kamar dai ƴar’uwarta gurji, ita ma kankana kyanta a shanye komai har da ɓawonta da galibin lokuta ake ganin an watsar a cikin shara, a cewar ƙwararu.

Ga wasu dalilai da ka iya sa ki/ka gamsu da waɗanan bayanan.

  1. Tana kara gamsuwa wajen kwanciya

    To amma fa kankana ba maganin karin kuzari ba ce, sai dai wani bincike ya nuna cewa za ta iya taimakawa maza wajen magance matsalar saurin kawowa. Tasirinta wajen kara karfin maza yana zuwa ne daga sinadarin amino da ke jikin ɓawonta. Wani binciken ya nuna cewa sinadarin L-citrulline da ke cikin kankana zai iya taimakawa wajen inganta yanayin karfin maza ba tare da wasu illoli da ake samu a magungunan karfin maza ba. Hazalika ga mata ɓawan kankana na taimaka musu wajen karin ni’ima musamman idan aka markadata cikin madara, in ji Maijidda Yahaya kwarariya kan abinci masu gina jiki.

  2. Inganta maka kuzari

    Za kuma ta iya inganta maka kuzari bayan kara nishadi a gado, domin sinadarin ruwan citrulline zai iya taimakawa wajen kara kuzari yayin motsa jiki.

  3. Maganin hawan jini

    Idan likita ya ce akwai bukatar jininki ya yi kasa, to gwada cin kankana baki dayanta – har da ɓawonta. Binciken masana ya nuna cewa shan kankana na taimakawa manya da tsoffi musamman masu ƙiba yin maganin hawan jini. Wata dabarar jin dadin kankana kamar yadda ƙwararru a fanin abinci mai gina jiki ke cewa, shi ne a sanyata a firij don ta yi sanyi a yankata sala-sala a shanye baki daya.

  4. Tana kunshe da Sinadarin Fiber

    Wani alfannun kankana ga jiki shi ne tana ƙunshe da sinadarin Fiber sosai da ke taimakawa matuka wajen kariya daga cututuka, rage kitsen jiki ko suga, da kuma cimma buri ga masu son rage kiba.

Wani karin haske da shawarwarin ƙwararru kan shan kankana shi ne mutum na iya bare ɓawonta ya yanka sala-sala sannan ya barbade da yaji, ma’ana a yi kwadonta ga wadanda cin ɓawon zai yi wa wahala.

Sirrin Yayan Kankana, Amfanin Yayan Kankana, Amfanin cin Yayan Kankana

Amfanin Kankana ga Lafiya Dan’adam

Leave a Comment