Amfanin Zobo Ga Mai Ciki
Amfanin Zobo ga Mai Ciki: Ba shakka da zarar an ambaci zobo, farkon abin da zai zo zuciyar mafiya yawan ma su karatu shine, wani abin sha mai dadi da ake sarrafa wa a gidajenmu cikin sauki, mu sha don nishadantuwa. Sai dai, baya ga sarrafa shi wajen sha don jin dadi, zobo na da matukar amfani ga lafiyar dan adam. Saboda haka ne a wannan makala za mu duba irin amfanin da zobo ke da shi ga lafiyar dan adam.
Ba shakka, ana samun zobo cikin sauki, musamman a yankin Arewacin kasar nan, saboda haka ne mu ke ganin idan mu ka bayyana amfaninsa za a iya jarraba wa, kuma mu na fatan Allah Ya sa mu dace. Kafin tsunduma cikin wannan aiki, zai yi kyau mai karatu ya san wasu daga cikin sanadaran da wannan tsiro ke kunshe da su. Binciken masana ya nuna cewa, Zobo ya na kunshe da wasu muhimman sanadarai da ke da amfani ga lafiyar dan-adam, kamar su ‘citric acid, Malevich acid da kuma tartaric acid, Bitanmin A, Bitamin C, Bitamin B2, Bitamin B3, sodium da sauran su.
Wani masani, mai suna, Dakta Ochuko Erukainure a jihar Ikko ya gudanar da bincike kan amfanin zobo ga lafiyar dan-adam, kuma ya gano cewa, za a iya amfani da Zobo wajen rage hadarin kamuwa da hawan jini. Dakta Erukaimure, ya bayyana sakamakon bincikensa ne, yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, inda ya ce, amfanin zobo ga lafiyar dan-adam ba shi misaltiwa, saboda yadda ya ke taimaka wa wajen maganin wasu cututtuka tare da rigakafin kamuwa da wasu.
Masanin ya kara da cewa, yana da kyau mu rika shan ruwan Zobo a duk lokacin da mu ka kammala cin abinci, amma ba tare da sanya sikari cikinsa ba, saboda gudun gurbata sanadaran da zobon ke kunshe da su. Yanzu ba tare da bata lokaci ba, ga amfanin zobo guda 11 ga lafiyar dan-adam, da fatan Allah Ya sa mu dace, amin.
- Daga cikin amfanin zobo ga lafiyar dan adam akwai rigakafin kamuwa daga hawan jini. Kamar yadda mu ka ambata a sama cewa, sakamakon binciken kwararren nan, Dakta Erukaimure, ya nuna cewa, yawan shan ruwan zobo wanda ba a zuba sikari ba, bayan cin abinci ya na taimaka wa wajen kare mutum daga kamuwa da ciwon hawan jini.
- Zobo na taimaka wa ma su hawan jini. Baya ga rigakafin kamuwa daga ciwon hawan jini, hakanan, zobo ya na taimakawa ma su hawan jini ta hanyar saukar da shi. Saboda haka Idan mutum yana fama da ciwon hawan jini sai ya samu zobo ya Jika da ruwan sanyi, ya tabbatar ya juku sosai, sannan ya ke shan ruwan, da yardar Allah hawan jinin zai sauka . Masana sun ce, zobo na saukar da hawan jini sakamakon yadda ya ke taimaka wa wajen bude hanyoyin jini ta yadda jinin zai rinka gudanuwa yadda ake bukatarsa.
- Hakanan, ana amfani da zobo wajen maganin gyambon ciki. Yadda mutum zai yi amfani da zobo wajen maganin gyambon ciki shine, mutum ya samu zobo ya dafa shi, idan ya huce sai ya zuba zuma da man habbatus-sauda, ya ke sha akalla sau uku a kullum.
- Ana amfani da zobo wajen maganin ciwon ciki da mara ga mata lokacin jinin al’ada. Idan ana son samun wannan fa’ida ta zobo sai a jika shi a hada da garin citta a sha, in sha Allahu za a samu afuwa.
- Shan zobo na taimaka wa wajen saurin narkar da abinci. Bincike ya nuna yadda zobo ke kunshe da wasu sandarai da ke taimaka wa wajen saurin narkar da abinci, haka ya sa idan mutum ya ci wani nau’in abinci mai nauyi, kuma ya na son narkewarsa kan lokaci to sai ya jika zobo ya sha ruwan.
- Kamar yadda mai fama da hawan jini zai iya amfani da zobo don samun sauki, hakanan wanda jininsa ya sauka zai iya amfani da zobo don samun sauki. Ko mai karatu ya san cewa, kamar yadda jinin mutum kan hau, hakanan kuma ya kan sauka ? Kwarai haka al’amarin ya ke don haka duk mai fama da wannan matsala zai iya amfani da zobo, don kuwa zai taimaka ma sa sosai. Ya samu zobo ya dafa ya ke shan ruwan bayan ya huce, ma’ana zai ke shan ruwan zobo da duminsa, da yardar Allah zai samu afuwa.
- Ana amfani da zobo wajen rage kiba ga mutanen da ke fama da wannan matsala. Masana sun bayyana haka ne, sakamakon yadda su ka ce yana kunshe da wasu sanadarai da ke rage maikon cikin jini marar amfani. Shan kofi daya na zobo bayan cin abinci ya na taimakawa wajen rage kiba.
- Harila yau, daga cikin amfanin zobo ga lafiyar dan adam akwai, taimakawa wajan karin jini ajikin mutum. Haka ya nuna yawan shan ruwan zobo zai taimaka wajen samun karuwar jini a jikinmu. Shan kofi daya na zobo bayan cin abinci ya na taimakawa wajen samun karuwar jini a jikin dan adam.
- Wani bincike ya nuna cewa, shan ruwan zobo ya na taimaka wa wajen inganta maniyyin dan-adam, musamman ma ga da namiji. Kamar yadda masanan su ka bayyana ingancin maniyyi na da dangantaka da iya yiwa mace ciki, saboda haka idan ingancin maniyyin mutum ya ragu, zai iya samun matsala wajen yi wa matarsa ciki.
- Zobo na taimaka wa wajen bunkasa garkuwar jikin dan-adam. Sakamakon binciken da masana su ka gudanar kan zobo, sun gano daga cikin sanadaran da ya kunsa akwai wadanda za su iya taimakawa wajen bunkasa garkuwar jikin dan-adam.
- Ana sarrafa zobo a sha don jin dadi da kuma nishadi, ta yadda za ka ga har a guraren shagulgulan biki ake amfani da zobo domin karrama mutanen da aka gayyata wajen bikin.