Entertainment

Yadda ake Fara Soyayya da Mace ko Namiji

Sakonnin Masoya Na Dare Masu Dadi

Yadda Ake Fara Soyayya

Yadda ake Fara Soyayya: Amma fa duk wanda yai yaudara to bada yawu na ba. Ga abunda zakai don sato zuciyar ta:

  1. KA rinka bata labarai masu dadi da tsuma zuciya musamman ma labarin daya shafi soyayya.
  2. Duk lokacin da kuka haɗa ido ka sakar mata tattausan murmushi na musamman.
  3. Ƙannenta su zama abokanka, kake kyautata musu fiye da zatonsu ta yadda zasu dami kowa da zancenka a gidansu.
  4. Ka rinƙa girmama iyayenta da yan gidansu.
  5. Ka rinka yaba mata koda batai abin yabon ba. Misali; in kun kiciɓis kace gaskiya kin haɗu, nutsuwarki ta birgeni, gaskiya duk wanda ya aureki yayi sa’ar Mace ta gari.
  6. Ka rinka girmamata, banda janta da musu, amma kake sawo labarai na nishaɗi.
  7. Ka yawaita kwalliya kaima musamman duk sanda kasan zaku iya haɗuwa da ita ko ƙawayenta, domin Mata sunfi son ɗan gaye gsky.
  8. Ka rinka tanadar kalmomi na musamman don ita.
  9. Ka zama mayen saka tirare yadda koda yaushe zata rika son zama tare da jimawa tare dakai.
  10. Ka guji hantararta da kusheta koda da wasa. Haka ka guji zaginta, yi mata ƙarya ko kula ƴan mata agabanta.
  11. Ka riƙa sirkawa da kyauta koda bazata karɓa ba ka riƙa Mata.
  12. Karka kuskura ka rika mata hirar kai ƴan Mata da yawa na sonka.

Sakonnin Soyayya Na Barka Da Shan Ruwa

2 Comments

  • Kalaman soyayya domin masoya

    hakika kina da kyau ga iya kwalli lalai nayi sa’ar samunki a matsayin masoyita, a kowane yanayi duk tsanani duk wahala ina son kisan da cewa bazan taba barin sonki ba har abada ina sonki masoyiyar raina.

    amin cin Allah ya tabbata a gareki yake kyakkyawar da babu kamarta a fadin duniyar masoya!! a duk lokacin da nake kallonki sai naga tamkar babu kyakkawar mace saike tabbas kinyi kama da kanki.

    zaku iya samun wadannan dama wasu dadama a website dinmu mai suna lafazitv.blogspot.com

Leave a Comment