Girke Girke

Yadda ake Sarrafa Fulawa a Saukake

Yadda ake Sarrafa Fulawa a Saukake

Yadda ake sarrafa fulawa cikin sauki

Sarrafa Fulawa: Yadda ake sarrafa fulawa acikin sauki kamar yadda muka sani fulawa ana iya sarrafa ta abubuwa da yawan gaske Wanda yanzu yakasance kusan zamu iya cewa kaso saba’in da cikin abincin da mukeci duk fulawa ne musamman a arewacin kasarmu ta nigeria. Sabida haka mukaga yadace mu kawo muku hanyoyi kala-kala na yadda zaku sarrafa taku fulawar wata kila kunayin wani Abu daban Kuma ya isheku Kuna bukatar ku sauya want kunga wannan zai matukar taimaka muku.

Abunda yake yanzu ya kamata muyi zamu lissafo muku abubuwan da akeyi da fulawa cikin sauki dukda dai wasu anayinsu da oven abin gasawa wasu Kuma akan soyasu a Mai Amma sai zaku duba kuga Wanda zaku iyayi sannan bayn mun lissafu zamuyi cikakken bayani akan guda daya Wanda daga baya zamuci gaba.

Abubuwan da ake yi da fulawa

  1. Concot
  2. Cin-cin
  3. Gurasa
  4. Doughnut
  5. Taliya
  6. Dubulan
  7. Bredi
  8. Cake
  9. Meat/fish pie
  10. Fanke
  11. Biskit
  12. Dan-wake
  13. Wainar fulawa
  14. Alkubus
  15. Funkasau

Ga kadan nan na lissafo daga cikin abubuwan da akeyi da fulawa dukda nasan ko rabi ban fado bah amma nasan wadannan ma zaku karu dasu sosai idan Allah ya yarda Kuma zamu dauki daya aciki muyishi ta yadda kowa zai fahimta. Zamu dauki na farko wato (concot) Wanda gaskiya kamar zai Zama bako sabo daga cikin abubuwan Dana lissafo shiyasa na dauko Shi domin nayi Mana bayaninsa Kuma bawai you agida kawai ba zaku iyayi domin sana’a ce sosai Kuma yanada matukar riba Mai yawa.

Yadda Ake Concot

Abubuwan da zaka nema kafin ka kwaba Shi saika tabbatar suna gefenka sabida gudun kar afara azo arasa wani abun kunga shiri ba baci kenan sedai ayi wani abun ko afasayi gaba daya.

  1. Fulawa
  2. Sugar
  3. Yeast
  4. Baking powder
  5. Gishiri
  6. Manja
  7. Man gyada

Wadannan sune jerin abubuwan da zamuyi amfani dasu wajen Yin wannan concot din saiku natsu ku karanta dakyau sabida gudun kuskure.

Amfanin Namijin Goro ga Maza da Mata

Leave a Comment