Amfanin Tumfafiya
Maganin Ciwon Gabobi
Za’a samu ganyen Tunfafiya sai sanya shi a garwashin wuta a dinga fifita garwashin har ganyen ya ɗauki zafi sai dinga dannawa a wurin dake da cewa Kamar: Ciwon Gaɓoɓi, ciwon tafin Ƙafa, ciwon sanyin ƙashi da sauran duk wani nau’i na ciwon ƙashi.
KURMAN TAKA TA DALILIN WATA CUTA.
Ana samun ganyen Tunfafiya wanda ya fara canza kalar rawaya ( Yellow ), sai a tafasabshi sosai idan yayi sanyi sai a dinga wanke kunne dashi, yana maganin Kurman taka ta dalilin wata cuta.
CIWON BASIR MAI TSIRO
Za’a samu ganyen Tumfafiy said a konashi sama sama sai a sanya man basilim akan ganyen sai a danga danawa akan inda Basir din ya fito insha allahu zai koma kuma ya warke sarai.
Amfani Ƙwallon Tunfafiya
Maganin Mayu
Ana cin ƙwallon tunfafiya don maganin Mayu ko sihiri. Zaku samu furen Tunfafiya saiku bude cikin sa akwai kwallaye a ciki to.
Maganin Daukar Cuta Yayin Saduwa
Ana shanya furen Tunfafiya indan ya bushe sai a da kashi yayi laushi sai a dinga ɗiban girgije ɗaya na cokali a dinga sha a Nono; shi kuma yana maganin rashin ɗaukar duk wata cuta da ake ɗauka a wurin saduwa mace ko namiji.
Maganin Tsutsar Ciki
Haka kuma ana samo furen Tunfafiya a markaɗashi a tafasa a tace shi a samu kofi a zuba shi a zuba zuma a sha, yana kashe Tsutsar ciki.
Amfanin Madarar Tunfafiya
Maganin Cututtukan Fata
Ana matse madarar Tunfafiya sai a haɗa da man Kade a juye su a yar ƙaramar roba a dinga shafa wa bayan anyi wanka yana maganin Cututtukan fata kamar kurajen Jiki, ƙaiƙayin Jiki, da sauran cututtukan fata.
Maganin Makero
Shi kuma za’a kankare makeron idan ya fara jini sai a ɗiga madarar ruwan tunfafiya a kai duk bayan kwan biyu, zai warke Insha Allahu.
Amfanin Dan Tunfafiya
Matsalar Kwakwalwa Ko Ciwon Kai
Ana cire barkonan tsohuwa dake cikin ɗan tunfafiya a zubar dashi sai a shanya dan idan ya bushe sai a daka shi yayi laushi ba’a shansa saidai ayi shaƙe ta hanci idan an shaƙa ɗin yana magani kamar: mai fama da matsanancin ciwon kai, mai ciwon hauka da duk wata matsala dake cikin ƙwaƙwalwa.
Amfanin Icen Ko Bawon Tunfafiya
Maganin Ciwon Hakori
Ana samo icen ko kuma ɓawon Tunfafiya sai a ɗora shi a garwashin wuta hayaƙin dake fita sai a dinga shaƙar hayaƙin. Shi kuma yana maganin ciwon Haƙori da kuma tarin fuka.
Maganin Cutar Kuturta
Sannan ana samun ɓawon Tunfafiya a dake ya daku sai a hadeshi da man kaɗe a dinga shafa wa a inda cutar Kuturta ta bayyana.