Hausa Novels

Ban Fi Karfinta Ba Complete Hausa Novel

Banfi Karfinta Ba Hausa Novel Complete

Download Banfi Karfinta Ba Hausa Novel Complete anan dama sauran sabbi da tsofaffin hausa novels wattpad masu nishadantarwa da ilimantarwa audio da na karatu

Tsoro na Allah tsoro na muhadu dashi ahanya saboda ko ba komai dai ni nasan bana iya kallon cikin kwayar idanunshi,wani mugun kwarjini yakeman ta bangare guda kuma tsareni da idanunshi masu rikitar dani dayakeyi aduk lokacinda zamu hada hanya.

dukda an bashi shedar tinda ake dashi ba’a taba ganin miskili ta bangare guda kuma kamilin saurayi aduk fadin unguwar ba irin shi.

Unguwar da take cikeda ‘ya’yan masu kudi ‘yan gata, ‘ya’yan masu fad’a aji a fad’in Nigeria, da yawa yawansu ma ba a qasar sukeyin karatu ba ta wani bangare kuma sha’aninsu sukeyi da ‘yan matansu ‘ya’yan k’usoshin gwamnati irinsu amman duk da haka acikinsu Ya Ameen daban yake.

mata dayawa suna sonshi amman shi Sam basa gabanshi Aikinshi da kasuwancinshi kadai yasanya gaba, acewarshi har yanzu ba’ayi yarinyar dazai tsaya b’ata ma kanshi lokaci akanta ba, kai shi soyayyar ma gabaki dayanta bai yarda da itaba.

Menene abunso a jikin mace? Kullum tambayar da ya keyi ma kanshi kenan.

(Nidai nace bakaje hannu baneba lol🤣)

“”””””***************”””””

Ahankali nake takawa cikin natsuwata da tafiya ta mai ban sha’awa da burgewa, ni ahakan ma gani nakeyi sauri nakeyi saboda aiken da ummata tayiman kasuwa banaso na rasa adaidaita din da zai kaini duba da yanayin unguwar tamu, akwai drebobi har guda uku acikin tanqamemen gidan namu ko nace nasu amman dukda haka ummana ta haneni da shiga motocin domin kaini inda zani, a cewarta in tsaya matsayina na diyar mai aikin gidan mara galihu saboda gudun wulaqanci dukda cewa su drebobin ba zasu wulaqantani ba kasancewar mu dasu duk matsalar mu daya na wulaqanci da muke fuskanta daga matar gidan,

A wajen mai gidan da babban yaron gidan ne kawai muke samun sassauci amman ba daga su ba mudin da dabbobin dake gidan gonar bangare daya daga cikin gidan duk daya muke awajen iyalan gidan in kacire mutum uku rak cikin mutum bakwai daga cikin gidan watau Ya ameen Babban Dandan Gidan a maza, afnan watau autar gidan dashi kanshi kuma uban gayyar watau mai gidan Alhj Mustapha Dambulan

Ban aune ba naji nayi karo da mutum kasancewar saurin da nakeyi kuma da son kaucewa idanun drebobin saboda banaso su yiman tayin kaini din, lokaci guda kuma nayi baya zan fadi bankai ga kaiwa qasa ba naji an janyoni dakarfi har na fada faffadan kirjinshi da yake cike da haiba, lokaci guda dad’edd’en kamshin turarenshi da ke kara taimakawa wajen rikitar dani ya yiman sallama a hancina.

“Subhanalla” nace ina mai ja baya dasauri amman dukda haka damtsen hannuna na cikin nashi ba tareda ya sakeni ba,

“yi hakuri don Allah yaya…”

“Shiiii🤫” ya katseman hanzarin bashi hakuri da nakeyi, cikin isa da rashin son magana dinnan nashi ya bude baki dakyar yaceman “is ok ya wuce amman nan gaba ki dinga kula, bakyau ana tafiya ana tinani”

ya fada ahankali yanda nikadai zan iyaji dukda dai cewa dama haka yanayin maganar tashi take don in ba saninshi kayiba saima ka dauka maganar zuci yakeyi labb’anshi ke motsawa

Sakina yayi tareda zagayeni ya wuce kaman ma ba shine ya gama magana ba yanzu

Girgiza kaina nayi yayinda har yanzu ban koma normal ba bugun zuciyata ya qara gudu lokaci daya kuma ina kokarin daidaita numfashina domin ji nayi kaman ya wuce tare da numfashin nawa,

juyawa nayi nabishi da kallo har ya shige dan madaidaicin apartment din nashi da yake cike da kyau da qayatuwa a bangare guda na gidan.

File Name: Banfi Karfinta Ba Hausa Novel
File Part: Complete
File Type: Text File
File Format: .txt
File Language: Hausa Language
Written By: Not Available
Uploaded By: Hausa Drama (https://arewangle.com.ng)

Download Here

Follow our youtube, telegram, facebook and whatsapp here

  • Hausa Novel Youtube Channel
  • Hausa Novel Facebook Group

Tsofaffin Hausa Novels Wattpad Complete

Bibiyata Akeyi Complete Hausa Novel
Bakace Complete Hausa Novel
Girma Ya Fadi 3 Complete Hausa Novel

Leave a Comment