Hausa Novels

Garkuwa Complete Hausa Novel

Garkuwa Hausa Novel Complete

Download Garkuwa Hausa Novel Complete anan dama sauran sabbi da tsofaffin hausa novels wattpad masu nishadantarwa da ilimantarwa audio da na karatu

Bismillahirahamanirahim
Ina mai farawa da sunan Allah mai rahama mai jinƙai mai komi mai komai.
Ina gode Allah daya bani aron rai da lafiya da nitsuwa da konciyar hankali ya bani damar fara wannan littafinawa mai suna GARKUWA. Ya Allah ina roƙonka ka tsare min tunanina da hannuna ka tsare min al’ƙalamina daga rubuta shari da duk wani abu da zai zamo guba ko masifa a rayuwar al’ummar Annabi, ya Allah ka bani ikon rubuta al’khairi da abinda zai zamewa al’ummar Annabi dan al’farma Annabi da Alqur’ani mai tsarki, ya Allah ka bani rai da lafiya dani da masu karatu ka nuna mana ƙarshen littafin nan lafiya kamar yadda ka nuna mana forkonsa lafiya, Amin ya rabbil izzati…

*LITTAFINA NA KUƊI NE, BIYA ƊARINKI UKU KACAL DOMIN SAMUN DAMAR KARANTASHI BA TARE DA HAƘƘIN KOWA A KANKIBA, AKWAI SP GROUP SHI KUWA 1K PASTING NASU YAFI NA ƳAN 300 YAWA, TURO ƊARI UKU TA ASUSUNA 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA, SAI KI TURO SHAIDAR BIYANKI DA WANNAN NUMBER TAWA 09097853276, ƳAN SPECIAL GROUP BANA SON KATI, GA POS BURJIK A GARI, KUMA YAN 300 IN DAI KINADA DAMA DAN ALLAH YIMIN TRANSFER TA AC YAFI, AMMAN IN YA ZAMA DOLE BA MATSALA TURO KATIN MTN NA ƊARI UKUN, KANA BA HOTON KATIN ZAKIYI KI TURO MINBA, A A NUMBERS ƊIN ZAKI RUBUCE KU TURO MIN*

Dan girman Allah da Manzonsa.
masu tambayata tsoffin littatafaina ku daina bana so.
Ku nema a cikin groups zaku samu, in dai ba Hukuncin Allah ko NAKASA BA KASAWA BACE, da GARKUWA kada ku tambayeni in kuna ƙaunar Allah, in kuwa bakya ƙaunar Allah to tambayeni.

*YAHUNDE! Babban birnin ƙasar Cameroon.*

Cikin wani kekyawan rugar FULANI mai tarin al’barkatun duniya.
Kota wani sashi Allah yayiwa Rugar Arɗo Babayo, ni’imomi na musamman, makiyaye ne cikakkun Fulanin ƙasar Cameroon.

Ranar wata jumma da yammaci la’asar sakaliya, makiyaya nata dawowa gida yayinda kota ina. Shanu tumaki raƙuma awaki zabbi keta kai komo ko wanne na nufar garken ma-mallakinshi domin ko dabba tasan uban gijiyinta,
Garken Arɗo Babayo yana ɗaya daga cikin garken da babu kamarsa a nahiyar Afirka baki ɗaya,
Yanada MAKIYAYA a ƙala mutun arba’in.

Garin ya fara duhuwar sanire alamun yanayin sanyin damina da ake ciki ko ina yayi kore shar ga tarin tsirrai kana ga igiyar ruwa da yayiwa rugar Babayo ƙawanya,

Wasu dattawane a zaune bisa ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake ƙofar gidan Arɗo babayo Farin dottijon ne mai cikar zarra da mutun taka ke zaune a tsakiyarsu, kana sai wasu manyan mutane dake zagaye dashi.
A gefen damanshi kuwa wani Babban mutun ne mai cikar zarra da wadatar zuciya ga tarin alamomin mutuntaka da cikar imani da haiba, bisa dukkan alamu tattaunawa sukeyi kan abinda ya shafi rayuwarsu.
Da sauri Arɗo Babayo ya ɗago kanshi ido ya zubawa sashin damanshi, inda ya hango wasu ƴan saffa-saffan samari guda huɗu suna biye da ƙatuwar suntsuwar Boleru babban cikinsu ne a gaba wanda zai kai shekaru 15 sa mai binsa wanda zai kai shekaru 13 sai mai bin masa da zai kai shekaru 11 kana sai ƙaramin cikinsu da bazai gaza shara 9 ba, gudu sukeyi sosai da iya ƙarfinsu sun tasa tsuntsuwar Boleru nan a gaba wacce ta kasa firewa sai gudu takeyi da sawunta biyu, bisa dukkan alamu tsuntsuwar tanada tsohon ciki mai girma.
Gudun da takeyi gudune na ceton rai.
Arɗon Babayo daya buɗe baki kenan da nufin zaiyi magana sai kuma ya juyo ya kalli kekyawar yarinya ƴar kimanin shekaru 8 a duniya wacce take kan cinyar mutumin nan dake gefen damanshi.
Ta miƙe da sauri cikin tsananin azama da harshen fillanci da ƙarfi tace.
(“Acce mo) Ku barta”. Sai kuma ta juyo ta fuskanci mutumin da take zaune kan cinyarshi cikin kaɗuwa da firgici da alamun tsananin tausayawa tace.
(“Appa a vi’a ɓe acca tokkugomo nɓe naunanmo) Appa kace su dena binta zasuji mata ciwofa”.
Murmushi Arɗo Babayo yayi tare da cewa.
“Kai Gainako ku barta zaku kamata a hankali ai”.
Da sauri wanda aka kira da Gainako yace.
“Baffa Giɗaɗo ne yace mu kama mishi ita mu yanka mishi”.
Da sauri suka juyo kan ƴarinyar jin wani irin ihu da tai tare da cewa.
“Ku yankata kuma, Appa kajifa wai zasu yankata, wayyo Appa kace musu kar su yankata, gashifa tanata kuka gashi sun sa taji ciwo a hannunta yanata zunda jini”.
Da mamaki suke kallon ƴarinyar sabida furucinta na wai hannunta yaji ciwo yana zubda jini, ina tsunstsuwar Boleru ina hannu?.
Wanda ta kira da Appa ne ya jawota gabanshi tare da cewa.
“Parvina tsuntsu kuma tanada hannune?.”
Da sauri ta miƙe tare da ɗaga murya tace.
“Ba tsuntsu bane Appa wlh mutunce gata nan da ciki gashi ma tana kuka tana-ta kare cikin jikinta”.
Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Boleru ido su dai Allah ya gani gaba ɗayansu tsuntsuwa suke gani tana guduwa da kyar wanda kuma kowa ya ganta yasan tanada tsohon cikine.
Giɗaɗo ne wanda shine ƙarami yaron ɗan shakara 9 kuka yasa tare da cewa.
“Wayyo ya Gainako kayi sauri ka kamo min ita karta gudu”.
jin haka yasa ƴarinyar nan da aka kira da Parvina ta miƙe da gudu tabi bayansu tana gudu tana kuka wanda har ga Allah daga cikin zuciyarta yake fitowa kuma ita ba tsunstsuwar Boleru take ganiba a zahiri a fili da kuma baɗinin Allah ya nuna mata mutum take gani kekyawar mace mai cikar sura da kamala kana ga ƙaton cikin dake jikinta wanda haihuwa yau ko gobe.
Ihu takeyi tana binsu tana cewa.
“Dan Allah ku barta zataji ciwo Wayyo Appa kazo mu ceceta zasu kasheta.”
Ihu tasa da dukkanin ƙarfinta tana yarfa hannu cikin gigita take kurma ihu lokacin da su Gainako suka isa kan tsuntsuwar Boleru suka danne fikafikinta suka kama suka medata baya.

Ihun da tayine yasa gaba ɗaya dattawan nan suka miƙe tsaye suka biyosu a guje dan ihun nata ya cika illahirin rugar babu wanda zaice baiji ƙaranta ba dan saida tsaunuka da kogin da suke gaɓarsu ya amsa da sautinda da take cewa.
“Wayyoooooooo! Appaaaaaa! zasu kasheta, sun karya mata hannu”.
A gigice suka ƙaraso wurin wanda ganin yadda take a gigice yasa Appa kamata da sauri, yayinda ita kuwa taketa son zillewa tana fiffizgewa daga hannunshi, Arɗo Babayo kuwa tsawa ya dannawa Gainako tare da cewa.
“Kai! Kai!! Kai!!! Gainako sake tsunstsuwar nan saketa”.
cikin sanyi Gainako ya sake tsunstsuwar, daga tsaye ta faɗi ƙasa hakan yasa,
Parvina sake saka ihu da ƙarfi ta fizge ta nufi kan tsuntsuwar da ita mace take gani kuma sanadin saketa da akayi daga sama ta faɗi ƙasa a kife yasa cikinta buguwa wanda yayi sanadin a take naƙuda ya fara murɗarta kana ga jini daya fara bin sawunta.
Tana isa gaban tsuntsuwar tasa hannunta ta kamo hannun baiwar Allah nan da ita kadai Allah ya bawa damar ganin a mutun ba tsunstsuwar Boleru ba, hannunta data riƙo su kuma kab mutanen wurin gani suke fiffigen tsunstsuwar ta riƙo.
Cikin kuka take shafa kan kurciya a ganinsu yayinda ita kuwa hawayen fuskar matar da take ganin take sharewa cikin muryar kuka tace.
“Sannu sunji miki ciwoko, kice musu ke ba tsunstsuwa bace ki gaya musu ke mutunce kamarsu ki gaya musu kema bani adam ce karsu yankaki”.
Kuka ta kuma fashewa dashi ganin matar nan bata magana sai dai hannunta data riƙo ɗin ta ganshi tamkar robo wato alamun hannun a karye yake, cikin sauri ta sake hannun tare da cewa.
“Appa mu tafi da ita mu kaita wurin masu gyaran ƙashi”.
To al’amarin parvina fa ya fara zarta zaton mai zato ya fara shallake tunanin mai tunani abin ya girmi shekarun Dattijannan.
Shi kuwa Giɗaɗo kuka ya fashe dashi tare da nufarta yana mai cewa.
“Ki bani tsunstsuwata ai tawace nine nayi ta renonta kullum tare muke cin abinci tare komai duk abinda naci sai na barmata dan tayi ƙatuwa, kuma yanzu kice baza a yanka min itaba”.
faɗawa tayi jikin matar wanda su a ganinsu ruggume tsuntsuwar tayi ita kuwa parvina cikin kuka ta juyo ta kalli Giɗaɗo tare da cewa.
“Kai mayene ko? To Wlh bazan baku itaba in dai ina raye a duniya bazan bari a cutar da itaba, babu wanda zai kasheta a gabana sai dai in bana raye ku bar ce mata tsuntsuwa wallahi tallahi mutunce kamar kowa”.
Kiran sallan magriba da akayine yasa ɗaya daga cikin dottijon mai suna Yayari yace.
“Arɗon Babayo lokacin salla yayi”.
Sai ya kuma kalli Giɗaɗo da Gainako da Seyoji da Ja’eh yace.
“Maza kuje kuyi al’wala kuzo muyi salla, kai Giɗaɗo ka bar mata tsuntsuwar kurciyar kaji ko gobe da safe zabbi za’a yanka muku ku gasa kuci”.
Cikin kuka Giɗaɗo yace.
“Wallahi Ni dai ta bani tsunstsuwata, bana son zabuwar ni ko ɗawisu zaku yanka min bana so kurciyata nake so a bani abuna”.
(Giɗaɗo sabo da kaza baya hana a yankata kenan)
Cikin tsawa Arɗo Babayo yace.
“Kai tafi daga nan ba kaine babba ba kaci girma ka bar mata tsuntsuwar kaji ko Giɗaɗona”.
Tura baki yayi yabi bayan yayun nashi yana cewa.
“Ni a dena cemin Giɗaɗo ai dani Giɗaɗone da komai nakeso zaku bani”.

Basubi ta kanshi ba duk suka meda hankalinsu kan Parvina da tsuntsuwar dan ganin ƙasan tsuntsuwar Bolerun yana zubda jini, wannan abun ya sasu cikin nazari to, amman sai mgnar Parvina ta katse musu nazarin da cewa.
“Allah sarki gashi sunji mata ciwo har sun fidda mata jini”.
Jin haka yasa suka sa a ransu yess jinin ne daya fita sanadin jin ciwo,
cikin kula Arɗo Babayo ya matso parvina da taketa shafa kan tsuntsuwar da suke gani a idanunsu a hankali ya kamo hannunta cikin lallashi yace.
“Parvina muje cikin gida ko, kinga dare yayi kiyi salla kici abinci, tsuntsuwar taki kuma ki saketa zata fire ta hau makwancinta”.
Da sauri ta fara jujjuya mishi kai hawaye na zuba tace.
“Baffa Arɗo ta fire kuma? Bata da fiffigefa mutunce fa,tare zamu kwana da ita wallahi ba tsunstsuwar bace, mutunce ku daina ce mata tsuntsuwa, karmu barta ta kwana a woje”.
Sai ta kuma kama fiffigen tsunstsuwar tace.
“Ga hannunta nan sun karya mata”.
Sai ta kuma kama ƙafafun tsuntsuwar tace.
“Baffa Arɗo kaga ga sawunta ga idonta tanata zubda hawaye ga cikinta ga kunnenta ga bakinta ga gashin kanta har bayanta”.
Kallon-kallon suka tsaya sunayiwa junansu,
domin kafiyar parvina kan cewa Wannan tsuntsuwar Boleru mutun ce bani Adam ce ya fara basu tsoro to ko dai ƴarinyar tayi gamone? Koko tsuntsuwar iskace?.
cikin tsoron daya fara rufe Appa baki na rawa ya kamo hannun ɗiyar tashi da yake masifar so tamkar ƙoƙon ranshi cikin kaɗuwa da muryar fillanci kasan cewar sam fulanin ƙasar Cameroon basa jin hausa koda kawo min wuƙa in kashekane shiyasa cikin fillanci yace.
“(Parvina tsonɗu on fa na ɗum innu adamajo, ko waɗi a vi’ata neɗɗo on) parvina tsuntsuwace fa ba mutun bace meyasa kicewa mutunce?”.
Kuka ta kuma fashewa dashi harda shessheƙan gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi ganin yadda jikin matar ke karkarwa. Ruggume tsuntsuwar kurciyar tayi a ganinsu yayinda ita kuwa cikekkiyar kamilar mace take gani hannunta matar ta kama ta juya ta nufi cikin gidansu dansu da Gainako suka shiga tana kukan shur-shur da hawayenta.

Zurui sukayi suka rakata da ido har ta ɓacewa ganinsu.

A mashigar gidan sukayi kiciɓis dasu Giɗaɗo da sauri ta koma gefe.
Shi kuwa Giɗaɗo wani irin dundu ya kima mata a tsakiyar bayanta tare watsa mata harare cikin fillanci yace.
“Hegiya muguwa wallahi sai na yanka tsuntsuwata muna fuka”. da sauri tasa jikinta ta kare tsuntsuwar, tare dayin sauri tayi cikin gida.
Seyoji ta samu tsaye gefen mamansu yana bata labarin tsuntsuwar da duk gidansu babu wanda bai san Giɗaɗo da itaba dan yanzu kimanin watanni takwas kenan kullum babu dare babu rana a nan gidan nasu tsuntsuwar take rayuwa kullum in Giɗaɗo yaci abinci ya rage inta kuma sai tazo tayi ta tsastsaga har sai tacinye duk abincin daya bari kana ya ajiye mata madarar shanu nanma tazo tasha,
idan tasha ta ƙoshine sai ta juya da tafiya take barin cikin gidan ta koma bakin kogi.

Da sauri Mamansu Giɗaɗo ta kalli Parvina tare da cewa.
“Parvina na zo nan zo keda tsuntsuwar ki kada ki damu babu mai yankata”.
Da sauri ta iso gaban matar tare da cewa.
“Inna ki hanasu yankata Allah kuwa ba tsunstsuwa bace mutunce”.
Cikin kula matar tace.
“To parvina kada ki damu babu mai yankata daga yau ta zama taki, yanzu ajiyeta kije kiyi al’wala kizo kiyi sallah”.
Da sauri tace.
“To”.
A jiye matar tayi bisa taburmar dake tsakiyar gidan, kana taje tayi al’wala tazo ta shimfiɗa sallaya a gefenta, itama Inna gefenta ta shimfiɗa suka sa baiwar Allah’n nan a tsakiya…

Kamar da wasa da abin ya girmama domin koda sukayi salla isha’i fir parvina taƙi ta rabu da tsuntsuwar nan.
Su kuwa su Arɗo Babayo sun mance batun tsuntsuwar ma, tunda sukayi sallan isha sukaci abinci.
Suketa lissafin kan dabobbinsu kama daga kan Raƙuma, Dawakai, shanu, tumaki, raguna, awaki, ɗawisu, tolo-tolo, zabbi, tattabaru, saida suka waresu baki ɗaya dan sanin adadin zakkar da zasu fitar sannan suka gama fayace na zakkar kowanne daga ciki da shariya ta umarci a bada zakkanshi.

Hira sukaci gaba dayi kan abinda ya shafi kiwon nasu.

A can cikin gida kuwa, tunda Inna ta gama yiwa su Arɗo Babayo gashin zabbi ta haɗa da madarar shanu aka kai musu taketa fama da Parvina kan yadda ta tasa tsuntsuwar nan a gaba tana mata magiya kan tasa hannunta taci abinci,
ganin bazata iya ci da hannun nata bane yasa iya tasa hannun tana bata abinci har baki tana amsa tanaci yayinda hawaye keta kwaranya a fuskarta babu ƙaƙƙautawa.

Koda taci ya isheta sai ta mirgina alamun zata konta.
Ganin hakan yasa parvina kallon inna cikin sanyinta da nitsuwarta tace.
“Inna tare zamu kwana da ita”.
Kai inna ta jinjina mata kana ta miƙe tace muje cikin ɗakin kinga gari yayi sanyi Giɗaɗo da kike tsoron kada kiyi bacci yazo ya ɗauke tsuntsuwar ma yayi bacci”.
Kai ta gyaɗa kana ta miƙe suka shiga cikin ɗakin,
bisa katifar gado huts ɗinnan ta zauna tare da tsuntsuwar a gefenta, yayinda ga hasken wutan da aka kunna janareta ya gauraye ko ina na gidan da kuma ɗakin.

Inna kuwa kan gadonta take,
suna ɗan hira,
yayinda sam hankali parvina kan tsuntsuwar nan yake.
Tashi zaune tayi lokacin da taga gaba ɗaya jikin matar nan yana ta karkarwan ga hannunta dasu Gainako suka karya ya kumbura simtin, hannunta mai lafiyan kuma ta ɗaurashi kan tirtsetsen cikinta, gaba ɗaya jikinta zufane keta tsastsafowa tako ina,
cikin tausayawa parvina tace.
“Sannu hannunkin ke ciwo ko? Kiyi haƙuri gobe da safe zamu kaiki gidan mai magani”.
Inna ce ta zubawa Parvina ido cikin yanayin tsoro tace.
“(Parvina ɗun sonɗufa) Parvina tsuntsuwace fa. ki dena magana da ita ba jinki takeyi ba”.
Da sauri ta jujjuya kanta hawaye na zubo mata tace.
“Inna Wallahi tallahi mutunce ku dena ce mata tsuntsuwa inna ki ganifa bata da lfy, jikinta duk rawa yakeyi”.
Kai Inna ta gyaɗa kana tace.
“To na yarda yanzu dai ki kwanta kiyi bacci sai gobe da safe zamu kaita gidan mai gyaran karaya da targade”.
Jin hakane yasa ta konta tare da lumshe idonta. Sai bacci ya fara saceta sai kuma tayi firgigit ta farka,
ta kuma tada Inna sabida, suntsuwar nan ta kasa nutsuwa, yayinda ita kuwa Parvina take ganin baiwar Allah’n cikin mawuyacin halinda ya rintane yasa bata gane cewa matarnan naƙuda takeyi ba.

A haka suka kwana, har garin Allah ya waye basuyi bacciba, sabida ita kanta inna yanzu tsoron tsuntsuwar ta fara haka kuma take tsoron parvina, ita kuwa baiwar Allah’n nan zafin ciwon naƙudane ya hanata bacci ita kuwa parvina tausayin matar da mutanen garin da gidan ke cewa tsuntsuwar Boleru ne ya hanata bacci.

Asuban fari suka tayi sukayi salla,
daga nan suka fito tsakiyar gida, kai tsaye sashin Arɗo Babayo suka nufa ita da Inna,
shiru sashin nashi alamun basu dawo masallaci ba, cikin alhini da tsoro Inna ta kalli Parvina cikin daburtacciyar murya tace.
“Ajiye tsuntsuwar nan haka kina rike da ita kamar kin samu uwarki maza ajiyeta”.
Cikin zubda hawaye ta tsuguna ta ajiye tsuntsuwar kan buzun Arɗo Babayo,
Wanda dai-dai lokacin ne kuma Arɗo Babayo da Appa, Gainako, Seyoji, Buba, Giɗaɗo, Ja’eh suka shigo kamar yadda suka saba.
Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Kurciyar nan ido ganin yadda taketa birgima a kan buzun tana wasu irin cure-cure tamkar ranta zai bar jikinta.
Ita kuwa Parvina kuka ta farayi bil haƙƙi da gskya tanayi tana yarfa hannu,
Buba ne yayi maza ya nufi kan tsuntsuwar kurciyar tare da cewa.
“Haukan banza a kan buzun salan Arɗo zaku ajiye tsuntsuwar.
Ihu mai ƙarfi parvina tasa ganin Buba ya ɗaga kafarshi da ƙarfin bala’i zai kaiwa tsuntsuwar harbi da naushin ƙafarsa,
Kamar a mafarki kamar gilmawar walƙiya tamkar daga sama.
Sukaga tsuntsuwar Kurciyar nan tayi wani irin ɗagowa ta karkaɗa fikafikinta cikin ƙudurar Ubangiji da hikimarsa da buwayarsa sai gata-ta d…!

Salon na dabanne labarine mai cike da sarƙaƙiya, biya 300 ko 1k ki karance badaƙalar cikin salama.

File Name: Garkuwa Hausa Novel
File Part: Complete
File Type: Text File
File Format: .txt
File Language: Hausa Language
Written By: Not Available
Uploaded By: Hausa Drama (https://arewangle.com.ng)

Download Here

Follow our youtube, telegram, facebook and whatsapp here

  • Hausa Novel Youtube Channel
  • Hausa Novel Facebook Group

Tsofaffin Hausa Novels Wattpad Complete

Ban Fi Karfinta Ba Complete Hausa Novel
Bibiyata Akeyi Complete Hausa Novel
Bakace Complete Hausa Novel

Leave a Comment