Hausa Novels

Girma Ya Fadi 2 Hausa Novel Complete

Halima Atete Biography, Films and Net Worth

Girma Ya Fadi 2 Hausa Novel Complete

Download Girma Ya Fadi 2 Hausa Novel Complete anan dama sauran sabbi da tsofaffin hausa novels wattpad masu nishadantarwa da ilimantarwa audio da na karatu

Cikin su ya duri ruwa, idanunsu ya raina fata suka yi jigum-jigum. Ba sai ga Imran da kan wayoyi har uku ba? Har cikin dakin barcinmu ya shigo yake tambayar ina Zaynab? Da fari sun tsorata sun dauka zancen jiya ne ya kawo shi, don haka a tsorace suka ce tana toilet tana brush. Ya ce, “To madallah, ga tsarabar ku, saura in ji ana kiran ‘ya’yan banza”. Ni dai sai ihun su Azizah na jiyo don wayoyi ne ya kawo mana ‘yan uban su duk iri daya (Nokia), sai dai duka ba layi nawa ne kadai ya sanya layin ‘glo’. Ni dai tunda na karba na jefa kasan filona ban kara tunawa da ita ba, don ba ita ce a gabana ba jarabawar da nake yi ne.
Yau da muka fito paper din ‘geography’ Mr. Segun ya biyo mu, tun farkon zuwan su yake min nacin na tsaya na saurare shi na ki, an turo shi invigilating ne daga Minna jami’in NECO ne, ga tsagun nan na Nufawa rankacau cike da fuskar shi, amma shi tsakanin shi da Allah sona yake yi da aure kuwa ba da wasa ba.
Su Iftihal dariya yake basu, idan kuma ya rubuto masu amsa su karbe su kwafe babu ko tsoron Allah, su koma bayan idon shi suna dariyar shi. Ga mamakin su yau tsayawa na yi da Mr. Segun ina jin wadda ya zo da ita, wato yana so in kwatanta mishi gidanmu ya zo, yana so in mun kare jarabawa zai aure ni, kar in damu da matarshi da ‘ya’yansa ba zai hada mu gida daya ba.
Na ce masa, “To”. Ya ce, “Wane gari nake son zama? Minna ko Sokoto?” Na ce, “Duk inda ya fi maka sauki”. Dadi ya kama shi sai washe baki yake. Daga can gefe kuma GG ne zaune a benci yana kallon mu fuskarsa a hade. Mr. Segun ya tambayi nambar wayata na ce da shi ban rike ba tukunna yau aka bani wayar, amma gobe zan kawo mishi. Ya rasa inda zai sa kanshi don dadi, muka yi sallama kamar ya goye ni ya gudu dani.
Ina yin taku biyar don cimma su Azizah sai ganin GG na yi a gabana kamar an jefo shi, tsulum! Ya ce, “Wato don wulakanci Zaynab don kin ga na damu dake kike yi min duk abin da kike yi min?” Na ce, “Ba wulakanci bane GG na ga irinmu fitina ne a bayan kasa, shine nake jiye maka haduwa da fitinar mai narka-narkan mazauna”.
Ya fashe da dariya, daga nan inda nake ina iya jiyo mugun doyin da bakin shi ke yi. Ya ce, “Don Allah don Annabi Zaynab ki yafe min ki bar TUNA BAYA….., wallahi tun a lokacin son ki ne ya yi min yawa nake kuma neman hanyar da za ki kula ni na rasa……”
Na dan juya don gano su Azizah, na hango su duk a nutse cikin motar Ya Im suna ta jirana, shi kuma yana jingine jikin kofar motar wadda take a bude, ya dage kafarsa ta hagu ya jingineta jikin motar ya harde hannuwanshi a kirji, manyan idanun shi fes a kanmu. Ban bari ya fahimci na san da tsayuwar shi ba, da na kakaro wani lallausar murmushi na kwarawa GG bai san sanda ya sanya hannu a aljihunsa ya rarako duk abin da ke ciki ya miko min ba, ni ko sai na ce, “Mai da abinka muje ku gaisa da Yayana ga shi can, dama ya ce yana son yin abota da kai tun sanda ka sani wankin toilet, shine waliyi na a wajen shi za ka karbi aure”.
Da GG ya hanga ya dubi Ya Im, kayan jikinshi da irin motar da yake tsaye a jiki, duk da ba a gano kwayar idanunshi ya saya ta da bakin gilashi (blackmail) sai ya rikice, ya ce, “A’a, ayi haka Zaynab? In ce ko ba gatsen da na yi miki a kan a koreni daga aiki kika dauka da gaske ba? Ki yi hakuri don Allah ki yi mun arziki, wannan aikin da shi nake ci, nake sha ni da iyalina da gyatumata. Kuma wallahi karya nake bani da wata gonar gado wani busasshen kango ne kawai a kauyen mu”.
Na yi mai murmushin kwantar da hankali na ce, “Kai dai tunda na ce ka zo muje, to ka zo muje, baka san alheri irin na Yayana ba, cewa fa ya yi zai sa a mai da kai principal dinmu”.
Ai jin haka GG ya gyara hula tare da gyara zaman kwalar rigar shi, ina tafe yana biye dani kamar wani mai take min baya. Shi kuma Ya Im ganin mun nufo shi sai ya shiga mazaunin shi ya zauna, garam ya rufe kofa ya danna wani abu a jikin hannun motar tintics suka rufe mana ido rufe bakake sidik, kan in ce me! Ya ja motarshi aguje ya bude mu da kura muka yi futuk ni da GG, amma GG bai damu da kansa ba sai sannu yake min, na tabbata da da hali ma da ya karkade min kurar da ta bata fararen uniform dina.
Wata matsiyaciyar kunya ce ta kama ni, domin bayan GG akwai sauran malamai da dalibai da dama da suka ga faruwar al’amarin da basu ga dalilin shi ba. Ban ko bi ta kan GG ba na yi gate ina share hawayen wannan wulakancin da Imran ya yi mani a bainar jama’a, wata zuciyar kuwa sai ta ce dani baya da laifi, ai ba ubanki ne ya saya masa motar ba.
Achaba na tara ya dawo dani gida har cikin gate, lokacin Imran na tsaye tare da wani abokin shi Jabir suna magana. Gaba daya suka juyo suka zubo min ido ina lalubo kudi a jakata don bai wa mai babur, ya kara kuluwa iyaka da ya ganni na dare a bayan mai mashin, ya kuta ya kada kai ya mai da hankalin shi ga Jabir yana ta yi masa magana amma shi hankalinshi da attention din shi duk yana kaina. Sai da na wuce cikin gida sannan Jabir ya ce (yana nuna hanyar da na bi na kule) da dan alinsa, “Wannan (fresh baben) fa Imran? Yanzu dama kuna da irin wadannan a gida ka barni ina bin kadangarun bariki karmasassu?”
Imran ya wani irin juyo ya lafta mishi harara, kamar ya yi aman zuciyarshi don takaici, ya ce, “Idan za ka yi iskancinka ka san a inda za ka yi shi, me kake nufi? Kannen nawa ma basu tsira ba? To ahir dinka, kuma in gaya maka ba a nan gidan ba, kuma wallahi ka yi kadan ka lalata min kanne J.B, su basu san irin wannan rayuwar ba yara ne, kada ka sake ko da wasa ka kula su, ka ga hanya sai mun hadu…..”
Yadda ya fitittike yana ta fada ko idanunshi baya iya budewa, duk sai ya ba Jabir dariya, ya kara kular da shi da cewa, “Kanwar ka? Ta ina kuma? Wannan Balarabiyar haka? Na san Iftihal da Azizah amma wannan kam ba ‘yar gidan nan ba ce, don haka ina kamu babban Yaya, kuma ka yi hakuri ni ba da manufar da ka fassarani ba nake son ta, ina nufin…. da aure!”
Wayyo Allah! Karshen ta dai Imran sai shigewa ya yi gida ya barshi a nan don ya san muddin ya ci gaba da sauraron shi, za ayi batacciya, amintar shekara da shekaru ta zama tarihi.
Su Azizah me za su yi da gani na ba dariya ba. Nima dariyar ce kuma ta kama ni na taya su muka yi ta yi sai da muka yi mai isar mu. Na ce, “Ni yau na ga abin da ya fi karfina, kunyar duniya yau kam na gama jin ta, kin ganni kuwa goye a bayan acaba? Sai ka ce wata karuwa, kai Allah ka yafe mini”.
Mama ta shigo tun daga falo take cewa, “Meye dalilin tahowa a bar Zaynab ta hawo acaba? Kuna tunanin in Abba ya ji daga ku har Yayan ku za ku iya kwanan dadi a gidan nan?” Suka yi tsit, na yi saurin cewa, “A’a, Mama wallahi ba laifin su bane, na bi wata kawata ne cikin kwatas din malamai zan amso (past question pepers) sai basu ganni ba suka taho”. Ta ce, “Rufe min baki, ai dama kullum ke a wurin ki basa laifi, in ban da iskanci a jira ki man ko a nemo ki, sai a taho a rabu dake? Ni kam ba da ni ba, Allah wannan Abba zai yi hukuncin sa, don Zaynab ‘yar aman ce a hannu na. in kuma da wani mugun abu ne ya same ki fa a cikin makarantar shima haka za a taho a rabu dake?”
Ganin ranta ya baci ba da wasa ba, gaba daya muka shiga ba ta hakuri kar ta gayawa Abba har da hawayena, ta ce, “To gaya min gaskiyar dalilin tahowar a barta, in ba haka ba, ba makawa wallahi sai na gayawa Abba”. Na ce, “Wallahi laifi na yi masa”. Ta ce, “Shi waye?” a sanyaye na ce, “Ya Im”. Ta zaro mana ido ta ce, “Laifin me?” Hantar cikina ta kada, wani fitsari ya kulle min mara ban san takamaiman abin da zan ce ba.
“……. Ai laifin da Zaynab ta yi mun Mama kema in kika ji sai kin hukuntata”. Gaba daya muka juya muka dube shi, yana bakin kofar bai shigo ba, hannunsa na dama dafe da kofar fuskarshi babu alamun wasa. Ya ce, “Mama Zaynab ce mai rubuta jarrabawa su Iftihal su kwafa, da na yi magana suka mai dani shashasha, har wata gadara suke wai ai malaman duka samarin ta ne ba abin da za su yi masu. Yanzu kamar ‘ya’yan V.C a ce suna aikata examination malpractice, wai kuma har suna gaya mun har bencinsu malaman suke rubuto musu su kawo musu. Shine yau na ce bari dai in je in genewa ido na me ake a makarantar nan?
Wallahi Mama a kan ido na Zaynab zance da maza har layi ake a kanta, in wannan malami ya wuce sai wannan malamin ya zo. Wani kuma har da kwaso kudi a aljihu wai zai ba ta. Sun fi rabin awa a tsaye duk ina tsaye ina kallon ikon Allah, can kuma ba sai na ga an nufo ni ba, ko me za a ce min oho, na ga wannan rainin hankali da ake min ya yi yawa, ko ba ta sanni ba ai gaba nake da ita, ya dace ta nuna ta san girmana amma wallahi yarinyar nan kamar wani direban ta ne ya zo, kamar ba ta san da tsayuwata a wurin ba, kawai sai na ja mota na barta a nan, don wallahi da na biyewa zuciyata a lokacin dukan ta zan yi”.
Mama ta samu kujera ta zauna tana kallon mu tana gyada kai cikin mamaki, duk muka yi tsuru-tsuru, ba ya ni da cikina ke ta kartawa, na soma kukan da nasani da haushin Imran. Mama ta ce, “Da gaske ne Zaynab abin da nake ji? Ke da nake yabon ki sallah za ki biye ma wadannan shashahun ki kasa alwala”.

File Name: Girma Ya Fadi 2 Hausa Novel
File Part: Complete
File Type: Text File
File Format: .txt
File Language: Hausa Language
Written By: Not Available
Uploaded By: Hausa Drama (https://arewangle.com.ng)

Download Here

Follow our youtube, telegram, facebook and whatsapp here

  • Hausa Novel Youtube Channel
  • Hausa Novel Facebook Group

Tsofaffin Hausa Novels Wattpad Complete

Girma Ya Fadi 1 Complete Hausa Novel
Mai Sona Complete Hausa Novel
Babban Sirri Complete Hausa Novel

Leave a Comment