Girma Ya Fadi 3 Hausa Novel Complete
Download Girma Ya Fadi 3 Hausa Novel Complete anan dama sauran sabbi da tsofaffin hausa novels wattpad masu nishadantarwa da ilimantarwa audio da na karatu
Na zauna dum, naki ko motsi, har ya gama fiddo jakunkunan da yazo da su a but din motarsa, ya zagayo ya bude min kofa ya ce “you are welcome to gwauro’s house…” na hadiyi miyau da kyar nace “zai fi kyautuw ka fara shiga, ka yiwa mutanen gidan bayani na, ba wai kawai su ganni a kansu ba, idan sun yarda da bakuntana falillahil hamdu, idan basu yarda bama babu damuwa, sai muje ka kama mun (Guest House) wannan ma ba karamin taimaka ne kayi mun ba and I really appreciate”. Ya sarke ‘yan yatsun shi cikin na juna,yayi baya dasu suka bada kara, kas. Yana murmushi yace “you seem lacking confidence in everyone’ kina da gaskiya, Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro ne. Allah ya kiyayeki da kwana a (Guest House), domin da jin muryarki an ji ‘yar mutunci, wanda ta san ciwon kanta. Ki yarda da ni, bani da niyyar cutarki, hanyace ta hadamu kuma Allah ya kulla zumuncin mu.
Yadda kowanne dan uwa na jinni, ba zai ci amanar ‘yar uwarsa da suka fito ciki daya ba, haka ba zanci amanar ki ba. Feel free with me, am not that type of person, don haka fito ki biyo ni, nayi miki alkawarin ba zaki yi nadamar bina ba”. Sai kawai nayi kundumbala na bude motar na fito, muka jera zuwa ciki, yayin da maigadi ya biyo mu da kayan sa.
Tun daga falo ya daga murya yana cewa (Manma na dawo), daga can kuryar daki ta amsa “mon fils tu ed rtour (sannu da zuwa dana)” kafin ta dogaro sandarta ta fito tana laluben bango. Idanuwanta a bude farare tar-tar amma na fahimci bata gani. Da sauri ya karasa ta lalubi kanshi ta rungume suna magana cikin harshen su. Na yi tsaye tamkar an kafeni, ina kallon dattijuwar da nan take wani abu ya tsirga min a cikin kirji, a dalilin kamanninta da Innata.
Ya ce “bani kadai bane Manma, ina tare da bakuwa ne, har da ita ‘yan fashin suka tare mu, gashi bakuwa ce a Nijar shi yasa na taho da ita, ta sauka a wajen mu kada ta fada mugun hannu” tace “ina fata kasa an kamesu duka? Tunda ka tafi nake maka addu’ar Allah ya kara daukakaka akan aikinka” da alama bai ji dadin hakan da tace a kunnena ba, ya basar ta hanyar kamo hannunta zuwa kujerar da nake. Tasa hannu tana lalubani sai kyalle take ji. Na zare niqabin ta shafa fuskata sosai, sai kuma tayi murmushi tace “budurwa ce ko? Da alama zatayi kyau, tunda ga dogon hanci ina ji, gashi kace ba daga alkaryarmu take ba”.
Na daga ido na dubeshi yana kallona, da baki a bude, amma ya kasa magana. Ta ce “kawo mata ruwa mana? Ko sai na buge maka kai da sandata?” Ya hadiye mayataccen kallon mamaki da tsoron da yake mani, ya nufi kofar da jikina ya bani kitchen ne, ya dawo da gorar ruwan (Ragolis) da lemon (Don Simon) masu sanyi, sai raba suke, yake ya ja tebur ya aje mani har yanzu idonsa akaina, ya ce “Laliya bata zo ta dafa miki abinci bane Manma?” Ta lalubi kujera ta koma ta zauna ta ce “bar Laliya da son kudI, yanzu haka wai ta tafi karBo zakkane gidan KANGIWA, bayan albashinda ka bari na bata jiya-jiyannan”. Ya hade rai sosai yana cewa “ni kam zan sallameta, ya zan dauko yarinya ina biyanta, domin ta kula da cikin uwata amma ta fita ta bar min uwa da yunwa, Allah bata isa ba tayi kadan, ko ita ‘yar Uban wane ne” daga ni har gyatumar dariya muka yi, ya soma tattare hannun rigarsa da alama kitchen din zai shiga da kansa, ta ce “dadi na dakai kenan Mon Amour (masoyina), babu hakuri.
Mutumin dake yi maka hidima kullum ranar Allah, rana daya da bai samu yayi ba sai ka yi masa uzuri”. Ya ce “nayi uzurin Manma, me kike so na dafa miki cikin mintuna goma sha biyar?” Ta ce “dafa mun kabeji, bakuwarka kuma ka tambayeta abinda take so” ya juyo gareni “bakuwata ke kuma mai kike so?” Tsohuwar tace “au ko sunanta baka sani ba?” Kunya ta kamani, domin ban kyauta ba, na ce “sunana Zaynab, shine bai fada min sunan sa ba Mama, shi yasa nima ban fada masa ba”.
Yayi murmushi, amma bai dago daga abinda yake yi ba, wato zuba lemu a tambulan ya kai bakinsa, ta soma laluben sa wai zata dake shi, ta ci karo da bango kamin ta kai kas yayi maza ya cafo ta, ya kwantar da ita akan doguwar kujera, ya ce “dukkan ku kuyi hakuri, sunana mai tsada ne. Ina fadarsa ne kawai ga matar da nake matukar so, don haka Manma ki tambayamin bakuwata, shin ta shirya amsa na a matsayin mijin aurenta, in gaya mata sunana?” Kafin gyatumar ta amsa na yi hanzarin tarar numfashinta da cewa “ban shirya ba, ba kuma zan amsa ba, don haka ka rike sunanka mai tsada, bana son ji”.
Ya russuna ya kwantara da kansa a cinyar gyatumarsa, cikin matsananciyar nadama yace “ina fatan ba fushi kikayi da tsokanata ba?” Nace “ta yaya zanyi fushi da mutumin da ya karBi bakuncina, alhalin bai san ko ni wace ce ba, bai ji tsoron kada in cutar da gyatumarsa dake da lalaru ba? Bai sani ba mutum ce ni koko ina daga jinsin jinnu? Bana daga cikin mutanen dake yin fushi da wanda yayi musu alheri, komai kankantarsa. Daga baya kuma ya bata musu, sai iny masa uzuri. Jeka dafowa Mamarmu abincinta, mon amour, ko ba haka ne sunan da na ji Mama na kiranka ba?” Ya mike yana dariya yace “inda kinsan menene ma’anar Mon-amour, da baki kirani da shi ba”.
Daga kwance tace “rabu dashi diyata, ko kin rasa masoyi me zakiyi da wannan tsololon?” Daga can (kitchin) ya amsa “lala Manma, amman kin yanke ni. Na rantse, duk fadin garinnan, kafin a samu saurayi mai kiba ta aiki ne ja” ta ce “a inda babu masu kibar ba”. Haka sukayi tayi tana tana yankansa yana kare kansa, kamar wasu kaka da jika. Akwai alamun shakuwa da matsananciyar kaunar juna a tsakaninsu. Yana ji da ita, tana ji da shi, sun fahimci juna, don haka ne bata wani tsaurara magana a kaina ba, don tasan ba zai kawo mai cutar ta ba.
Cikin mintuna goma sha biyar din da ya ambata, sai wani irin kamshi ya game gidan gabadaya. Ya iso rike da kwanon silver mai fadi, dafadukan kabeji ne da aka dafa ruwa-ruwa, an kuma yanka kabejin manya-manya. Ban taBa ganin irin wannan abincin ba, kamar in tambaya amma ina tsoron gwasalen da ya yi min dana nuna ina son jin sunan sa. Don haka naja bakina na yi tsit.
Ya koma ya shiryo min farin kuskus da aka dafa da koren wake da karas sunyi shar a ciki da miyar hanta, da aka yanka hantar kanana-kanana, a gefe kuma soyayyen nama ne irin wanda ake soyawa a ajiye, domin bukatar gaggawa da lemun (7-alive) ya ce “to Zaynabu, aci da hakuri kinsan girkin gwauro ne” Maman ta ce “gwauro, ko tuzuru?” Ya koma gabanta yana bata kabejin a baki da cokali, yace “duk wanda kuka ga ya dace da ni, dai-dai ne.”
Maman ta ture lomar da zai sanya mata a baki, ta ce “nidai don Allah ka daure kayi aure Babana, na gaji da wannan wahalar da kake da ni bata dace da kai ba, da wane zaka ji? Da wannan aikin mai hatsari koda kula da gyatumarka, alhalin kai baka da mai kula da kai?” Ya sunkuyar da kai kasa bai ce mata komi ba. Da lama bai so tayi maganar a gabana ba.
Na sauko daga kujera na dawo gabanta na karbi silvern a hannunsa, nace “ni idan na baki zaki ci? Ki yi masa hakuri Mama aure ai lokaci ne” na cigaba da bata tana karba tana ci bata ce komai ba. Ban juya na kalle shi ba amma jikina ya bani kallona kawai yake yi.
Sai data koshi na bata ruwa tasha, sannan na karasa cin nawa, na lura har zuwa lokacin zaune yake a inda yake, bai tashi ba. Na daga ido na dubeshi, don ganin abinda ya hana shi Magana, fararen idanunsa har yanzun akaina suke, cikin kollon da ba yau na fara ganinsa a idanun maza ba.
Na ce cikin basarwa “kai baka ci abincin ba” ya lumshe ido a hankali, maimakon ya masa min abinda na tambaye shi, sai ya mike yana cewa “idan kin gama kiyi amfani da wannan dakin, (ya nuna dakin da dan-alinsa) duk abinda zaki bukata akwai a ciki, domin kanwata ke yin hutu a dakin idan tazo daga makaranta, duk abinda babu kiyiwa Mamana Magana, zata fada miki inda yake”.
Ya fita daga falon ba tare da ya waiwayo ba tace “yarinya jeki kiyi sallar azuhur, ki kwanta ki huta zuwa la’asur, ai kinga duniya nidai wannan aiki bana sonshi, to ya kafe ne, amma wannan sai da rai dame yai kama?” Na so in tambayeta kowa ne irin aiki yake wanda bata so? Naga wannan ba damuwa na ba ne. Damuwa na shine in samu masauki, in gabatar da abinda ya kawo ni, sannan in nemi dangin Innata. Kenan abinda ya kawoni daban, suma rayuwarsu daban. Saidai babu shakka tsarin rayuwar su shi da mahaifiyarshi ya burgeni. Cikin ‘yan awannin da nayi tare dashi, na fahimci abubuwa da dama game da shi. Duk matar da tayi sa’ar aurensa ta yi babbar sa’a, domin zata zauna lafiya. Kasancewarsa mutum mai saukin kai da duk wasu qualities da ake nema daga da namiji, uwa-uba irin mazannan ne da albarkar Uwa ke bibiyarsu, saboda tsananin biyayyar da suke mata da nuna jin kai a gareta, tamkar zasu kwanta mata.
File Name: | Girma Ya Fadi 3 Hausa Novel |
File Part: | Complete |
File Type: | Text File |
File Format: | .txt |
File Language: | Hausa Language |
Written By: | Not Available |
Uploaded By: | Hausa Drama (https://arewangle.com.ng) |
Follow our youtube, telegram, facebook and whatsapp here
Tsofaffin Hausa Novels Wattpad Complete
Girma Ya Fadi 1 Complete Hausa Novel
Girma Ya Fadi 2 Hausa Novel Complete
Mai Sona Complete Hausa Novel