Hausa Novels

Mai Sona Complete Hausa Novel

Hanyoyin Sace Zuciyar Budurwa

Mai Sona Hausa Novel Complete

Download Mai Sona Hausa Novel Complete anan dama sauran sabbi da tsofaffin hausa novels wattpad masu nishadantarwa da ilimantarwa audio da na karatu

Zaune take tana kallon farin watan da ya haskaka ko ina…yanayin sararin samaniya take kallo yana matukar debe mata kewa ga wani iskan dake kadawa a hnkli ta lumshe ido tana jin wani nishadi amma kash!! Rashin masoyin nata kusa da ita shine babban matsalarta a wannan lokacin a hnkli ta furta “Allah sarki *mai sona* yana raye ne oho? Idan yana raye kuma nasan dole yayi auri yana can tare da matarsa ya manta dani a rayuwarsa” wani sirirn hawayene ya fito a idanunta dai dai lokacin aka dafa kafadarta ckn firgita ta juya a hnkli tsohuwar ta xauna a gefe fuskarta dauke da murmushi “jikata kiyi hakuri ki cigaba da adua wata ran Allah xai bayyana masoyin naki idan da rabon xaku sake haduwa”ta kwantar da kanta ajikin tsohuwar tana hawaye dakyar ta rarrasheta ta daina kukan da take tana bata tarihin xamaninsu haka nan ta mance da duk wani damuwar da take cki…
Da safe ta tashi ta share gidan nasu fes tayi wanke2* bayan ta gama ta fada wanka tana fitowa a falon tsohuwar ta hadu da mahaifinta har kasa ta xauna Suka gaisa ya amsa ckn faraa da sakin fuska “er Abba yaushe zaki koma makarantar taku? “Abba IT xamuyi ba skul xamu koma bah” “toh yayi kyau Allah ya taimaka ya bada saa” “ameen nagode” daga nan tayi shigewarta daki ta shirya ckn atamfa mai kyau ta fesa turare a nan na tsaya na kare mata kallo…doguwace ba har can bah, tsayinta dai2* da jikn da take dashi wankan tarwadace tana da shape iya gwargwado ga dogon hanci se dan karamin baki , gashin idonta xara2* se kuma dimple da take dashi ga kuma wushirya masha Allah kyakkyawace ba karya ta hadu sosai.hijabi ta dora sannan ta fito har ynxu mahaifin nata yana nan hira suke da tsohuwar ta wucesu wani bangare ta shiga wata mata kyakkyawa tana rike da tea flask ta fito daga kitchen.”ina kwana umma ” “lfy ya kuka tashi ya kakan naki” “lfy alhmdllh” daga nan matar tayi shigewarta falo nan tabi bayanta tace “umma akwai aikin da xan tayaki dashi ne” “babu na rigada na gama” tayi shiru wata budurwace ta fito daga ckn dakin bacci hannunta dauke da cup da ruwa a cki se kuma brush da toothpaste “ina kwana anti maryam” ko uffan bata ce mata bah tayi ficewarta waje tayi brush se da ta gama ta dawo falon ta galla mata harara tace “nikam bansan ke wace irin halitta bace..a ckn gidan ma yawo xaki dinga mana da hijab, wllhi umma da islamiya kawai kuka turata Abba ya daina bata kudinsa a banxa don wannan batayi kama da en boko bah” “uhmm Abban naku shiyake biye mata ai nikam na rasa gane kan ruhaimat wllhi..kin fita daban ckn ya’yana ” wacce aka kira Ruhaimat ta sunkuyar da kanta kasa tana sauraronsu idan da sabone ta saba muryar maryam naji tana cewa “in banda kauyanci ya xakima mutum magana ko brush beyi bah”😳🙊 hmmm….muryar Abba Suka ji yana cewa “sannu Ya’r birni ..wllhi maryama ki kiyayeni fah,kullum ina gaya muku Ku daina sangwamarta amma Baku jin magana , kuji tsoron Allah Ku canza hali ” ya juya gun umma yace “me kuma Allah yaganar dake ..ban taba ganin wacce take sangwamar Ya’r cknta ba sai ke ,ki dai bi a hnkli ita wacce kike rainawa…
“Dakata Alhaji..nifa ba tsanarta nayi bah, ina Neman wayar da kantane sabida naga tana ckn duhu.da kke xancen na tsaneta kuma wannan kai ka janyo saboda anki a rada sunan mahaifiyata don son kai ka sanyawa taka mahaifiyar ” murmushi yayi tare da cewa “Allah ya ganar dake Halima, er Abba taho muje mu ci abinci koh” sumui2* ta tashi tabi bayan mahaifin nata umma da maryam sukabi bayanta da harara.

😘😘 *Reefat CE*
[1:52PM, 11/12/2016] ‪+234 703 007 7024‬: 💞💞 *MAI SONA*💞💞
*2*
BY *Reefat Yahya*

*Asalin labarin*
Alhaji Abubakar Hammawa shine asalin sunansa..su 3 iyayensu Suka haifa , Alhaji Ahamdu shine babba yana aikin gwamnati a garin kano yana da mata 2 da yara 8. Sai Hajiya maryam wacce take aure a yola ma’aikaciyar asibiti senior nurse ce *FMC*yola yaranta 4, se Alhaji Abubakar shine auta.asalinsu mutanen garin jada ne na jahar Adamawa a can aka haifesu har suka girma.mahaifinsu Allah yayi masa rasuwa se mahaifiyarsu Hajia Aishatu wacce suke kira da Hajja Dada , Alhaji Abubakar yayi karatun primary da secondary daga nan ya fada kasuwanci har Allah ya buda masa yayi aure ya auri Halimatu er garinsu.ya’ya 6 Allah ya basu Mohammed ( Hamma).. Ahmadu..Zainab..Yusuf..maryam..Aisha ( Ruhaimat) daga nan haihuwan ya tsaya musu cak..halima taso a sanyawa Ruhaimat sunan mahaifiyarta Amma Alh Abkr ya sakawa tasa mahaifiyar sunan yarinyar daga wannan lokacin umma take jin haushin surukar tata harda ita jaririyar. Mohammed wato Hamma yayi karatunsa yana aikin banki a can kano ya auri Ya’r baffansa Ahmadu, Ahmad Wanda ake kiran tijjani yayi karatunsa shima da ya kammala degree ya fada kasuwanci yana aiki tare da mahifin nasu duk fadin garin jada ansan shagunansu ya auri wata Ya’r jada suna xaune yaransu 2,se zainab wacce take yola da aure bata aikin kome mijinta barrister ne suna da yara 2,se Yusuf ya kammala karatunsa yana bautar kasa a nan garin jada Maryam wacce take aji 4 a jamiar modibbo Adama uni of tech yola.sannan auta Ruhaimat wacce take Adamawa state uni tana aji 3 a bangaren biochemistry ynxu xasu fita IT wannan kenan.
*Cigabn labari*
Bayan sun kammala kari ita da mahaifin nata ta gyara masa falon daga nan ta wuce bangaren Hajja Dada.. tana xaune a falonta “jikalle kin dawone” “nadawo takwarata” “kin ci abinci kuwa..gashi na ajiye miki , wannan Mara kunyar yayar taki ta kawo ina tambayanta kina ina bata amsa min bah” “hmm anti maryam se a hnkli” “ko ina xata samu mijin aure da wannan rashin kunyar tata oho” dariya sosai Ruhaimat take tana ckn haka wayRta ya hau ruri “masoyiyata” sunan da tagani kenan ta daga tana murmushi “Allah sarki tawan nayi missing naki” “haba ruhi Nah shine kwana 2 ko flashing babu” “yi hakuri kinsan idan ina kusa da Hajja Dada baa cewa komai” “uhmm..wato xaki manta da kowa kenan harda *mai sona*” ckn sauri tace “a’a rufamin asiri, idan na manta da *mai sona*ai ban numfashi a duniya kenan” “uhmm..ruhi kenan har ynxu de kina nan kina fama da son mutumin da baki San ko ya mutu ko yana Raye bah” “insha Allah yana nan da ransa don ina jin ajikina na kusan haduwa dashi” “toh malama Juliet Allah ya bayyana shi” “ameen nagode” haka Suka cigaba da waya daga bisani sukayi sallama.

File Name: Mai Sona Hausa Novel
File Part: Complete
File Type: Text File
File Format: .txt
File Language: Hausa Language
Written By: Not Available
Uploaded By: Hausa Drama (https://arewangle.com.ng)


Download Here

Follow our youtube, telegram, facebook and whatsapp here

  • Hausa Novel Youtube Channel
  • Hausa Novel Facebook Group

Tsofaffin Hausa Novels Wattpad Complete

Babban Sirri Complete Hausa Novel
Kuruciya Complete Hausa Novel
Yarima Ashman Hausa Novel Complete

Leave a Comment