Hausa Novels

Sanadin Accident Complete Hausa Novel

Demi Moore Biography, Career, Awards and Net Worth

Sanadin Accident Hausa Novel Complete

Download Sanadin Accident Hausa Novel Complete anan dama sauran sabbi da tsofaffin hausa novels wattpad masu nishadantarwa da ilimantarwa audio da na karatu

Tafe take tana rusa kuka kamar wanda aka ce parent d’inta sun rasu ..hannunta d’aya ta kare fuskarta da shi d’ayan hannun kuwa tana rike da wani fashen2 tulu koda na matso kusa da ita na k’are mata kallo senaga yarinyace qarama fara wacce baza tafi 11ans(11years)duda karanci shekarunta aman bai hana kyan ta fitowa ba tanada hancinta zarot ..bakinta dan madedeci pink ga magana masha Allah amma fa kayan jikintaa dakon2 dasu bakyan gani duk sun kod’e sun cicire …riga da zanen da d’an kwalin duk daban2 tayi daurin nan irin namu na yan kauye wato ta zaro jelar dan kwalin ta gaban rigarta …..ganin irin shigar yasa nayi zaton tallaka wane amma me..😳 ganin gidan data take shirin shiga yasa nayi mamaki dan kaf kauyen manga gidan daya kaishi ba dan shafe da sumunti gidan yake kuma an kewayeshi da katanga sab’anin sauran gidajen da kusan duka buka ne…

Ta jima tsaye baki kofar gidan ta kasa shiga se tayi kamar zata shiga se kuma ta dawo baya tayi haka yafi sau ukku daga karshe tayi shahada ta shige ganin haka nima na mara mata baya ..

Wata bakar mata nagani zaune bisa kujerar nan tayani tsegumi se girgiza kafa take tayi d’aurin d’an kwali ture kaga tsiyar nan ..

D’an nesa da ita yarinyar nan naga ta durkusa se kame2 take ta kasa magana ga hawaye na tsiyaya bisa ”joue”(cheek) d’inta …

Matar ta kalleta tace wai miyene kin wanizo kin sani gaba kamar ni d’in bakuwar ganin kice…..ina kuma ruwa dakikaje d’iba ne eee ta fad’i cikin tsawa..

Seda ta firgita yarinyar har tayi baya ta fad’i ragwaf baki na karkarwa tace kiyi hakuri Inna Murza wly mun d’ebo ruwan nida su Ma’u kawai sega su Murtala sunzo fice wa gani suna gigin tseda mu ne . da muka ki tsayawa se kawai suka biyo a guje ina cikin gudu nayi tuntub’e nafad’i tulun ya fashe kuma ma harda ciwo naji ta bud’e gwiwarta idan taji ciwon..tana nuna mata

A maimakon taji tausayi yarinyar se wani uban ashar ta abka tace yoni ina ruwana dajin ciwonki .kuma kice de kin tafi wajen karuwan cin ki da samarinki de.. walahi baki isa tulun nawa zafi fasa sanan wani bani hakuri … to walahi se kin biyani ko jikin ki ya fanshe ki yanzu nan dan bazan dauki asara ba….

Cigaba da kukan take tana bata hakuri amma ina Murza ita neman ma bugi take ..muciya naga ta d’auko tayi kanta .nanfa ta dinga jibgar yarinyar tun kana jin ihun ta har muryar ta dishe bata barta ba seda ta sumar da ita tayi jifa da muciyar taja kafafun yarintar takaita tsakiyar rana tayi shigewarta daki se mita da zagin yarinyar take …

Ba’ita ta farka ba se wajejan karfe biyu na rana shima sakamakon ruwan da Inna Murza ta sheka mata…firgit ta tashi se wuki2 da ido take ….

Murza tace shegiya mai kama da aljana tashi ki fice kiwo sauran inkin tafi ki tsaya yawon karuwancin naki dakika saba …

sum2 ta d’au buta ta nufi rijiyar cikin gidan da niyar yin alwala tayi sallah ..ashe ma akwai rijiya cikin gidan dan tsabar mugunta irin na Inna Murza tace baza’a ja ruwan ba sede taje can cikin rijiyar garin ta d’auko mata..

Wata tsawa ta daka mata tace ke kina hauka ne uwar mi zakiyi min da butana iye..

Cike da tsoro tace Inna alwala zanyi inyi salla..

Shewa tayi tace gaji ladaniya to kokece tabarmar massalaci wacce kullum acikin mosque d’in take baza kiyi sallar ba kamar wacce tafi kowa addini …..maza aje ki fice..

Tace inna to bari nayi fitsari sena tafi …

Shiga kiyishi hakanan base kin kama ruwan ban …shasha kawai ..

Fitsarin da batayiba tace Inna abincina fa yunwa ake ji…

Iye i lalle wuyanki yayi kwari kai tsaye tace to ban dafa dake ba

Zata yi magana Murza tace.MAYSAM MAYSAM dige ki fita a idona in rufe tau..tayi shigewarta d’aki

Bayanda MAYSAM d’in ta’iya dole ta d’au sandar kiwon ta kora shanun ta fice….Allah yaso ta cikin shanun akwai masu shayar wa bayan taje idan take kiwon se ta tatsi nonon tasha ta gama.cikin ta dan dama kullum hakace take faruwa idan anbata abincin safe tofa da ranan batada kwanon tuwo idan kuwa bata bata na safe ba to zata bata d’an tsakure da rana…
Bayan tagama sha tayi alwala tayi sallah
Wanan kenan…

File Name: Sanadin Accident Hausa Novel
File Part: Complete
File Type: Text File
File Format: .txt
File Language: Hausa Language
Written By: Not Available
Uploaded By: Hausa Drama (https://arewangle.com.ng)

Download Here

Follow our youtube, telegram, facebook and whatsapp here

  • Hausa Novel Youtube Channel
  • Hausa Novel Facebook Group

Tsofaffin Hausa Novels Wattpad Complete

Yar Bincike (C I D) Complete Hausa Novel
Garkuwa Complete Hausa Novel
Ban Fi Karfinta Ba Complete Hausa Novel

Leave a Comment