[2/19, 5:28 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahrulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *1* Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi. Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min. Cike da takama da kasaita ta matso daf da ni janyo wuyana tayi tare da ɗauke ni da marin da sai da network din kaina ya dauke gaba daya. "Munafuka annamimiya irin mugun hali, wato ragowar tuwon da na bari zamu dumama da safe shi ne kika biyo dare zaki cinye shi ko? Dama na dade da fadawa Malam kin fara sata amma ya nuna min kamar nayi miki kaxafi" kafin kace wani abu tuni jama'ar gidan mu sun taru kasancewar gidanmu gidan yawa ne, shi yasa duk motsin da zaka yi a kunnen mutane zaka yi shi, tofa albarkacin bakinsu suka shiga yi dukkan su babu wanda ya tsawatar a kan abinda aka yi min sai ma zuga inna salamatu da suke yi, babu wata kalma da ke fitowa daga bakinsu banda ta aibatawa da muzantawa. Dakin babana inna salamatu ta shiga, tarar da shi tayi yana bacci abinsa, sababin da ta rika yi masa a kansa ne ya farkar da shi, tashi yayi ya biyota suka taho wajena, tsaye na ganshi a kaina, wani irin kallo yake min mai cike da tsana, babu abinda ya fito daga bakinsa sai "tabbas abinda ake zargin ki da shi ya tabbata Sa'adatu, wannan shi ne sakamakon tarbiyyar da nayi miki, sakayyar da xaki min kenan a ajiye abu ki sata ko? abin boye ya fito sarari abinda ake zargin ki da shi ya tabbata yau na gani da idona, da a zatona sharri ake miki amma yau naga zahiri" baƙin ciki ne ya tokare min xuciyata naji kukan ya tafi gaba ɗaya saboda ba wannan ne karo na farko da na fara gamuwa da irin wannan kalubalen ba idan da sabo na saba, indai wannan rayuwar ce mun saba da ita ni da mahaifiyata, an mayar da mu tamkar gumaka marasa amfani a cikin gidan. Maganar baba ce ta katse min tunanina "Sa'adatu ba ki da labarin na hana a rika baki abincina ne, ba ki da labari nace? amsa min!!! Kaina a kasa na amsa masa da "Eh" "To daga yau na haramta miki abincina ke da uwarki don baxan zauna ina ciyar da ƙatuwar banxa mara amfani ba, shekara sha tara babu abokin tashi duk yan uwanki an gabatar da su ke kadai kika rage, mugun halin uwarki ya hana ki samun miji, to ki sani baxan cigaba da ciyar da ke ba, saboda duk abinda ke faruwa uwarki tana sane ta kyaleki kara zube ta saka miki ido kiyi abinda kika ga dama to sai dai kuwa ta ɗauki nauyin ki, hidimar ma da nayi a baya ta isa Allah ya bada lada" Wucewa yayi dakinsa yana huci. Tuntsurewa Inna salamatu tayi da dariya. "Oh Allah ya taimake mu yayanmu suna da farin jini, tun suna yan sha shida ake kwashe mana su, to kin ji dai abinda tsohonki yace da kansa ba sako ba, sai a yi kokari a fito da miji ko kuma a tsufa a gida" Haka ragowar matan gidan da yayansu suka rika min dariya gami da goranta min a kan rashin samun mijin aure, jikina babu wani karfi kamar an xare min laka na kasa tashi daga wajen da nake sbd takaici nafi minti goma ina xubar da hawayen bakin ciki, yanxu idan Baba ya hana mu abinci wane hali yake so na tsinci kaina. Tabbas idan rayuwata ta cigaba da kasancewa a haka ban san ina xan sa kaina ba. Ya Salim na hango daga kofar ɓangaren su yana dago min hannu, alamar na biyo shi. salim dan kanin mahaifina ne kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda basa goyon bayan abinda ake yi mana ni da mahaifiyata, har wasu daga ya'yan gidanmu suna tunanin ko sona yake yi, wannan dalilin yasa mahaifiyarsa take ta fadi tashi dan ganin ta raba ni da shi. Bin bayan shi nayi muka fito soro, cikin nutsuwa ya kira sunana "Sa'ar mata!!" Da yake da wannan sunan yake kiran a. Dago fuskata nayi tare da share kwallar da ta cika idona na amsa masa da na'am ya salim. "Kiyi hakuri a kan abubuwan da suke faruwa a gidan nan, ina daki ina jin irin abinda suke miki kasa jurewa nayi na fita, saboda xuciyata baxa ta jure jin mugwayen kalaman da suke fada miki ba, ki daurewa zuciyarki ki rika kulawa da dukkan abinda xai sa a rika yi miki irin wannan cin mutuncin, indai matsalar abinci ce tasa aka yi miki insha Allah na ɗauki nauyi kullum zan rika kawo muku abincin da xaku ci ke da innah. Ki kara hakuri komai na Allah yana da iyaka kuma dukkan tsananin yana tare da sauki, wannan rashin auren ki ɗauke shi a matsayin jarrabawa, duk wadannan abubuwan da suke faruwa wata rana sai sun zama tarihi a gareku ke da innah, kiyi hakuri ki jure a kan dukkan kalubalen da xaki fuskanta a gidan nan, lokacin ki na yi xaki tashi, da aure da mutuwa duk lokaci ne da su kuma mijinki na nan xuwa ya ɗauke ki, ya samar miki kyakkyawar rayuwa. Wadannan kalaman na ya salim ba karamin kwantar min da hankali suka yi ba, sai naji dukkan damuwata tayi sauki, farin ciki ya saukar min. Leda ya miki min, karbi wannan sa'ar mata. Girgiza kai nayi ka bar shi yaya wannan kyautar sai ta jawo maka matsala. Bata rai yayi ki karba kowace irin matsala xata jawo ba ruwanki. Tsugunnawa nayi na karba tare da yi masa godiya, wucewa daki nayi na barshi tsaye yana min kallo mai cike da tausayawa. [2/19, 5:28 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @Jeeddahtou* *2* Ko da na shiga daki a zaune na tarar da innah mamaki tare da fargaba ne suka cika zuciyata saboda yadda na ganta a zaune ga kuma damuwa bayyane a fuskar ta, da sauri na ƙarasa wajenta, tsugunnawa nayi tare da dafa kafarta "lafiya na ganki a zaune innah?" Kawar da kanta gefe tayi da alama bata so na fahimci halin da take ciki ba, sake tambayarta nayi. "Dan Allah innah ki fada min damuwarki ni kadai na rage miki dan Allah ki fada min abinda ya sa ki kuka" share hawayen da ya cika idonta tayi "Babu komai Sa'adatu, amma tabbas ban ji dadin abinda kika janyo mana ba, da kin hakura Allah zai kawo mana hanyar da zamu samu abinci, bakin dan Allah ya tsaga baya hana shi abinci, da baki taɓa musu kayansu ba da duk haka bata faru ba, duk rashin mutuncin mutum bai isa ya keta alfarmarka ba matuƙar baka shiga gonarsa ba, haka zai ganka ya kyaleka, amma sanadin wannan kin janyo abinda za a yi ta goranta mana, shikenan sun samu topic din da zasu rika maimaita wa kullum, dan Allah ki xama mai gudun xuciya da yarda da ƙaddara Sa'adatu, duk halin da muke ciki Allah ya fi mu sani" Ji nayi kwalla na shirin fito min daga idona a takaice nace "Haka ne innah insha Allah xan kiyaye dukkan abinda zai kawo matsala a tsakanin mu" ledar da ya salim ya bani na miƙa mata, ga wannan ya salim ne ya bani, kuma yace zai riƙa kawo mana abinci kullum mu riƙa hakura da na gidan nan. Shiru innah tayi sannan tace "Ni fa bana son irin wannan Sa'adatu kin san halin uwar yaron nan sarai bata ƙi taci mana mutunci ba gaba ɗaya, ki dakatar da shi bana so ina zaman zamana a xo a daga min hankali" "Insha Allah babu abinda xai faru innah ai shi ba shi da matsala kuma tsakaninsa da Allah yake taimakon mu" bude ledar tayi gurasa ce da nama, godiya ta yiwa yaya salim tare da fatan Allah ya albarkaci rayuwarsa, sai da muka ci muka koshi sannan muka kwanta, amma abin mamaki sai bacci ya kauracewa idanuna maganganun da aka riƙa fada min ne suka rika dawo min cikin kunnuwana, tashi nayi na dauro alwala na fara jero nafilfili, bayan na idar na dauki Alkur'ani na karanta, sannan nayi addu'a Allah ya saukaka mana halin da muke ciki, daga lokacin naji nutsuwa ta lallube zuciyata bakina bai gushe da ambaton Allah ba, ban san lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba. Kiran sallar asuba ne ya tashe ni, da sauri na dauro alwala tashin innah nayi muka tada Sallah, azkhar muka rika yi har zuwa fitowar rana. Ina daki ina shara naji ana kwala min kira, jikina na rawa na leka ta window don ganin mai kirana, umma ce mahaifiyarsa salim, a ladabce na amsa mata da "na'am umma" Wani matsiyacin kallo ta bi ni da shi, "kada ki sake ce min umma domin ni ban haifi mai baƙin jini irinki ba, wato an rasa mai tayawa an ga dana kyakkyawa zaki makale masa ko to sam bazai yiwu ba, yanzu ma gargadi na karshe naxo yi miki babu ke babu salim, na yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninku, ki fita daga rayuwar dana idan ba haka ba kuma baxa tayi miki kyau ba, don baxa ki lalata min shi ba ki gurbata min rayuwarsa, kin shiga kin fita har sai da yaron nan ya nace miki, gashi yanxu har hidima yake miki, to baxan lamunta ba saboda shi ba ubanki bane ba a kansa nauyin ki yake ba, uban naki ma ya kasa saboda mugun halinki da na uwarki, tun wuri ki kyale shi kafin na fito bainar jama'a na yaye miki rigar arziki". Duk maganar nan da take kaina na ƙasa na kasa dagowa sbd bakin ciki, haka ta gama ban-bamin masifarta ta koma ɓangaren su, taimakon da Allah yayi min ragowar matan gidan basu fito sun tayata ba amma nasan duk abinda ya faru da sa hannunsu. A sanyaye na zame na xauna, cikin jimamin abinda ya faru dani naji innah na min magana "kiyi hakuri Sa'adatu ki daina damuwa Allah muke gayawa matsalolin mu shi muke fatan ya kawo mana dauki, tashi ki kintsa ki tafi makaranta Allah ya baki dukkan abinda kike nema" Maganganun innah suna ratsa ni kuma suna da matukar tasiri ga rayuwata, ko naji abinda ake min ya dameni idan na tuna da nasihohin da take min sai zuciyata tayi sanyi, sbd innah mace ce mai tawakkali da yarda da dukkan abinda ya sameta na rayuwa, sannan bata yarda taje ta fadawa yan uwanta halin da take ciki ba, wani lokacin ko tambayarta suka yi dangane da matsalolin gidanmu bata fada musu sai dai kawai tayi murmushi waɗannan dabi'un nata su suka sanya dukkan makota suke sonta. Kintsa kaina nayi na sanya kayana dai-dai na talaka Kasancewar duk kayan nawa sun mutu don rabon da baba yayi min dinki har na manta sai dai makota su tausaya min su bani kwance, allona na dauka na fita tare da yiwa innah sallama. A soro na ci karo da matan gidanmu sun saka faifan gulamata suna ta tattauna abinda ya faru jiya suna ganina suka kara bada himma wajen zagina kawai dan naji raina ya ɓaci, ban kula da su ba na ratsa ta cikinsu na wuce, daya daga cikinsu naji na cewa "aikin kenan kullum a ɗauki uban allo a tafi makaranta kamar gaske, Allah yasa dai ana ganewa" umma ce ta karbi zancen "ina fa ake ganewa a yi sha'ani dai wai na birni ya cuci na ƙauye, da ana ganewa a rika sata gashi ana so a lalata min yaro" Muryar A'isha kanwar salim naji "mu mun san inda ake xuwa ba wata makaranta ku ake rainawa hankali" Ba karamin zafin kalmar da A'isha ta jefe ni da shi naji ba, wato kallon ma yar iska suke yi min. Gidan su Rukayya na wuce don biya mata makaranta sbd na saba kullum tare da ita muke tafiya, dukkan mutane sun saba ganinmu tare idan ma ban biya mata ba duk wanda ya ganni sai ya tambayi inda take. Rukayya kawata ce tun muna kanana, duk da cewa ta dan girme ni amma mun yi matukar shakuwa da juna babu wanda yake jin tsakanin mu, babu wani abu da nake iya boye mata ita ma kuma haka, lokuta da dama idan aka bata min rai wajenta nake xuwa ta kwantar min da hankali, mutanen gidan mu sun yi iya bakin kokari wajen ganin sun zuga mahaifiyarta a kan ta raba mu, amma taki karbar kudirin su saboda ba yabon kai ba ina da nutsuwa da kamun kai kuma ba ni da yawan surutu sannan ban fiye shiga abinda bai shafe ni ba, wannan dalilin yasa mutane suke sona kuma suke son abota da ni. Saka kaina nayi cikin gidan tare da sallama ban tarar da kowa a tsakar gida ba don haka kai tsaye na wuce daki, a kan gado na tarar da Rukayya tana ƙarasa haddarta don haka ban yi mata magana ba har sai da ta kammala karatunta sannan ta kula ni. "Sa'adatu lafiya yau na ganki a haka da alama ma kamar kuka kika yi" yaƙe nayi kawai saboda bana son na sake maimaita maganar, kawar da tambayar da tayi min nayi da "ina umma ban ji motsin ta ba lafiya?" "Yau da sassafe ta fita an kwantar da yar kanwarta a asibiti shi yasa baki ganta ba" "Ayya Allah ya bata lafiya" amsa min tayi da "ameen" Sake jefo min tambayar dazu tayi "ki fada min abinda yake damunki Sa'adatu na sanki da zurfin ciki abu yana damunki baxa ki fada ba,kuma ga damuwa nan a idonki Ina gani, ki fada min komai kin san dai babu boye-boye a tsakanin mu" Sai da ta yi min magiya sosai na fada mata sbd ban fiye son bude cikina ba musamman ma idan mutum baxai iya yi min maganin abinda yake damuna ba. Kafin na fara faɗa mata har kwalla ta cika idona, rarrashina ta shiga yi har sai da hankalina ya kwanta na fada mata dukkan abinda ke faruwa da ni, tayi matuƙar tausaya min kasancewata yarinya mai kananun shekaru amma har na fara cin karo da matsalar masu yi min gorin aure, nasihohi tayi min tare da bani misalan da xasu kara min nutsuwa. Sai da ta gama shiryawa sannan muka tafi makaranta. 08094136204 Domin karin bayani A taimaka a rika comment a rika sharing [2/19, 5:28 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @Jeeddahtou* *3* A makaranta ma dai ban wani mayar da hankali nayi karatu ba saboda yawan tunane-tunanen da na riƙa yi har malam sai da ya fuskanci ina cikin damuwa. Tare da Rukayya muka dawo muna tafe muna hirar mu irin ta kawaye, gidanmu tace zata je saboda kawai tana so ta ɗebe min kewa na manta da dukkan damuwa ta, sannan kuma ummansu bata nan ko ta koma gidan babu abinda zata yi sai zaman kaɗaici. Sallama muka ji a bayanmu gaba ɗaya muka waiwaya ba tare da mun amsa sallamar ba, wani kyakkyawan saurayi ne mai cikakkiyar kamala sanye yake da shadda fara ƙall wacce aka yiwa aiki da brown din zare, takalminsa ma brown ne, kansa babu hula wanda Hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawan kwantaccen gashin sa, bai gajiya ba wajen sake yi mana sallama wucewa muka yi muka kyale shi ba tare da mun amsa masa ba, biyo bayan mu yayi. "Haba bayin Allah bai kamata ku ƙi amsa min sallama ba, ga alamu sun nuna min ku malamai ne baxa ku wulakanta ni ba wannan dalilin ne ma ya ja ni har nayi kwadayin yi muku sallama nasan baxan samu matsala ba ya kamata ku amsa min kada ku watsa min ƙasa a ido" kanmu a ƙasa muka amsa masa da "wa alaikumussalam" muna gama amsawa muka juya don cigaba da tafiya, saboda idan da abinda na tsana na tsaya ina magana a hanya ko da yar uwata mace ne ban so ballantana kuma da namiji. Ganin yadda muka wuce muka kyale shi bai sa yayi zuciya ba sake bin bayanmu yayi, ku yi hakuri na tsayar da ku a hanya ko, na san kuma hakan ba dai-dai bane amma na kasa hakuri ne sbd daya daga cikin ku ce tayi min sata" Gaba daya muka juya muna yi masa kallon mamaki Rukayya ce tayi ƙarfin halin yin magana sbd ta fi ni baki, gaba ɗaya na kasa cewa komai sbd mamakin jin fitowar kalmar sata daga bakinsa "sata fa kace bawan Allah?? Sake wani zancen dai ba wannan ba, mu bama sata kuma bamu taɓa satarwa wani dan adam komai ba, muna bakin kokari wajen dogaro da abinda Allah ya wadata mu da shi" Murmushi yayi wanda sai da fararen hakoransa suka bayyana sannan ya dan sha kunu "ba ke nace kin min sata ba kawarki ce, amma ita ma bata san ta min satar ba" A razane na dube shi kirjina na dukan uku-uku sbd bana so na sake dakkowa innah abinda xai xame mana abin gori da bak'ar Magana, cikin rawar murya na fara magana "ban taɓa yiwa wani sata ba tunda nake malam watakila mai kama da ni ka gani" ban jira amsar da zai bani ba na ja hannun Rukayya muka cigaba da tafiya. Sake shiga gabanmu yayi "ku tsaya mu warware matsalar mana ko su ku ke yi sai Maganar ta je gaba? Idan haka ku ka zaba shikenan, amma ni shi ne abinda bana so. Tsayawa muka yi cak muna sauraron shi, gyara tsayuwa yayi tare da tambayata kin san satar da kika yi min. Da sauri na amsa masa da ban sani ba, rausayar da kansa yayi. "To zuciyata kika sata" Gabana ne ya fadi mamaki ya mamaye ni wai yau ni wani da namiji yake cewa na sace masa zuciya abinda ban taɓa ji ba kenan, sbd tunda nake babu wanda ya taɓa tunkarata da sunan na burge shi ballantana har ya furta yana sona. Ganin dogon tunanin da na tafi ya sanya shi yi min magana "lafiya naji kin yi shiru ko ba gaskiya bane abinda na fada?" Ban bashi amsa ba na juya na tafi tare da Rukayya na bar shi suna Magana ban san me take fada masa ba. Sai da na shiga gida da kusan minti biyar sannan na ganta, sallama tayi na amsa mata duk jikina yayi sanyi. Masifa ta fara yi min "ke shikenan daga fara magana sai ki wani tafi ki kyale mutane sai ni nayi masa bayani, na fada masa sunanki da kwatancen gidan nan dan haka ki shirya yau kina da babban bako" Fito da ido nayi "Haba ya xaki min haka ban so kika bashi kwatancena ba" hararata tayi "ok so kike ki xauna a cigaba da miki gori ba mai tayawa ko, ai ko ba aurenki xai yi ba yana da kyau kema a ga kina xance kin huta gori" dakatar da ita nayi "Kinga ni duk wannan bai dame ni ba sama da yadda idan nayi aure xan tafi na bar innah a wannan gidan shi ne abinda ya fi tayar min da hankali" "Wannan duk na Allah ne Sa'adatu baki san alkhairin da ke tattare da wannan bawan Allahn ba, watakila ya zama silar farin cikinki ke da innah" a takaice na bata amsa da haka ne yar uwata. Aiki ta taya ni muka gyara ko ina sannan muka yi wanke-wanke muna aikin, mutanen gidanmu na hararmu duk wanda Rukayya ta gaisar babu wanda ya amsa mata, ita ma baƙin jinina ya shafeta. Har yamma muna tare da ita sai da aka kusa sallar magariba sannan na rakata hanya ta tafi gida. Ina dawowa bayan nayi sallah ban dade ba na dan ji hayaniya a tsakar gida, ban mayar da hankalin sauraren abinda ake yi ba sbd nasan alkhairi bai fiye fitowa daga bakinsu ba, muryar yan matan gidan mu naji suna cewa " sam baxai yiwu a ce da Sa'adatu ake sallama ba sbd tunda take ba a taba xuwa ana sallama da ita ba, me xa a yi da mummunar yarinyar nan ga baƙi ga baƙin hali ai farare irinmu ake yayi, kai koma ka sake tambayarsa ya faɗa maka wa ake nema" Ajiye littafin da nake karantawa nayi nasan mutumin da muka gamu da shi daxu ne yaxo, sallamar yaron ce ta katse min tunanina. "yace Sa'adatu yake nema wacce suka haɗu tare a hanyar makaranta" Jikinsu ne yayi sanyi saboda sun san duk cikin ya'yan gidanmu ni kadai nake xuwa makaranta ragowar basu san komai ba sai yawon gidajen makota. Umma ce tace da yaron "je ka fada masa bamu san da zaman wata Sa'adatu a gidan nan ba" Hawaye naji na ƙoƙarin fito min yanzu a ce na samu mai son nawa ma sai an yi min bakin ciki, ban samu ba kuma ana min gori. ni kuma baxan iya fita na fada musu Ni ake nema ba ballantana na cewa yaron ya faɗa wa mai nemana ina zuwa ba, saboda na san duk rintsi duk wuya rabona baxai taba wuce ni ba, mayar da idona nayi kan innah tana ta sharar bacci abinta, da nayi ƙoƙarin tashinta na fada mata sai kuma na fasa kasancewar yau bata jin daɗin jikinta. Ina cikin wannan halin naji sallamar ya salim ta window ya leko da kanshi "Sa'adatu kina ina, yi sauri ki leko xan yi magana da ke" Sauri nayi na janyo hijabi na saka, nima lekawa nayi ta window nayi masa magana sbd bana so Mahaifiyarsa ta san ina kula mata danta. "Ya salim gani" nace masa. Karasowa yayi wajena "Ba kece kika yi baƙo ba Sa'adatu kin barshi tsaye yana jiranki tun daxu, ga sanyi ana yi, baki kyauta ba wlh, abinda muke nema Allah ya kawo mana xaki mana asara" Ban fada masa abinda ya faru ba illa kawai murmushi da nayi "na zaci wajen su A'isha yaxo shi yasa ban fita ba" Hararata ya dan yi "menene alaƙa tsakanin sunan A'isha da Sa'adatu ke dai kawai kice kina jin kunya, tashi ki shirya yana can yana jiranki" Har ya juya ya tafi ya dawo "Au na manta ba ni tabarma na je na shimfida masa" Ɗan bata rai nayi "Haba ya salim daga xuwa sai a fara ba shi tabarma ka bari mu tsaya a tsaye, ni baxan dade ba minti biyu na dawo" Riƙe baki yayi yana kallona lallai Sa'adatu har yanzu ba ki san rayuwa ba, wanda yaxo wajenka abin girmamawa ne ya cancanci kayi masa dukkan abinda xai sa yayi farin ciki. Saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kansa ya fada mana cewa wanda ya bada gaskiya da Allah da ranar lahira ya girmama bakonsa, ke malama ce amma kuma kina mantawa, maza miko min na tafi" Ban tanka Masa ba na miƙa masa tabarmar, hijabin da naje makaranta da shi na sake sakawa na fita. A soro na biyu ya salim yayi mana shimfida, zaune na tarar da shi ya tankwashe ƙafarsa, kansa a sama kamar mai tunani har na iso gare shi bai san naxo ba sallamar da nayi masa ne ya dawo da shi hankalinsa, da fara'a ya amsa min tare da gyara xaman sa. A ladabce na gaishe shi tare da yi masa barka da zuwa, gefen tabarmar na samu na zauna, sai na samu kaina a jin kunya na kasa haɗa ido da shi tunda wannan shi ne karo na farko da na taɓa fitowa zance da saurayi. Gyara zama yayi yana kallona, wato Malama Sa'adatu sai an ja min rai za a fito ko, ko da yake ban ga laifinki ba ke din mai tsada ce don kin ja aji ba komai girmanki ne ranki ya dade. Murmushi akwai nayi ba tare da na bashi amsar maganar sa ba. Gabatar min da kansa ya shiga yi " nasan dai baki yi mamakin ganina ba, tunda kin san da xuwana kuma kawarki ta fada miki komai game da ni" girgiza kai nayi alamar bata fada min ba. Murmushi yayi tare da gyara zama "tunda bata wakilce ni ta fada miki ba to ni bari na fada miki da kaina don waka a bakin mai ita tafi dadi. Sunana Izuddeen Muhammad iyayena mu maxauna wannan unguwar ne gidan malam Muhammad mai yan makaranta , na san baxa ki kasa sanin gidanmu ba, sai a lokacin da yayi min wannan bayanin na gane a gidan da yake (mahaifinsa babban malamin addini ne, yana da rufin asiri sosai, sannan mafi yawan ya'yan gidan manyan ma'aikata ne) nayi karatuna a jami'ar Ahmadu Bello da ke zaria na karanci bangaren engineering, Amma ban samu aiki ba sai dai ina ragewa a wani Company kafin babban aiki ya samu. A gaskiya nayi matuƙar farin ciki da Allah ya bani damar yi miki magana, domin na dade ina sonki amma na kasa fitowa na furta miki, kullum sai na tsaya jiranki a hanyar zuwanki makaranta da dawowarki ko xan samu damar fada miki abinda ke raina sai yau Allah ya bani wannan dama kuma nayi farin ciki da yadda kika karɓe ni, Allah yasa na xama silar farin cikinki na har abada, ki miƙa min godiyar ki wajen kawarki domin da taimakonta na samu wannan damar mai tsada" Har yanzu kaina na ƙasa na kasa cewa komai "baki ce min komai ba Sa'adatu, ko dai ban yi miki bane?" A hankali na dago kaina "Na gode da kulawarka gare ni" ita ce kawai kalmar da na iya furtawa. Bamu fi minti sha biyar muna tattaunawa ba ya mike tsaye ya fara nade tabarmar da na shimfida masa. Da sauri nace "ka bari na nade da kaina" A'a ki bari ai baxan so na fara sa ki aiki ba. "to ni zan tafi Sa'adatu sai yaushe kenan?" Murmushi na dan yi "sai bayan sati daya" Da sauri ya dube ni "sai bayan sati daya fa kika ce, kema kin san baxan iya ba, ki bani dama gobe na dawo" "Gobe ina da unguwa ka bari ka dawo jibi" amsa min yayi da Allah ya kaimu. Sallama muka yi ya juya ya tafi, sai a lokacin na tsaya na kalle shi sosai, kyakkyawa ne mai matsakaicin tsawo baxa ka kira shi dogo ba haka kuma baxa ka kira shi gajere ba, wankan tarwada ne idanunansu masu kyawun gani Musamman idan ya daga ido xai yi kallo xamu iya kiransu da sexy eyes, bakinsa ma madai-daici ne ga kuma kyakkyawan saje da ya xayyana fuskarsa. Har ga Allah ban yi tsammanin wannan kyakkyawan saurayin zai furta yana sona ba, kasancewar ba wani kyau ne da ni ba, haka nake ba yabo ba fallasa. A tsoro na biyu na ci karo da A'isha da innah salamatu da da dukkan yan matan gidanmu, Maryam saliha da bilkisu sun kasa kunne suna sauraren tattaunawar da muka yi da Izuddeen abinda ya bani mamaki ganina bai sa sun ji kunya sun matsa ba, sai ma magana da naji suna yi "lallai abu ya ci-gaba ɗan iska har cikin soro Allah ya kawo Baba yau za a yita ta ƙare" Ji nayi kafafuna sun yi sanyi addu'a na fara yi Allah yasa kada su hada min tuggu a wajen Baba, don yanzu baya jin maganar kowa sai tasu, daki na wuce na bar su har yanzu dai innah bacci take bata farka ba don haka ban tashe ta ba na kyaleta. Maganar su na rika ji "Ai wlh baxa mu bari yarinyar nan tayi aure ba sai mun hada mata makircin da sai an koreta daga gidan nan sai yayanmu sun yi aure tsaf sannan xata yi, haka kawai ku fi ta komai sannan Izuddeen yaro nutsatstse yace yana sonta yaron da kowa ya san yayi fice a ilimin boko da dana addini, da ku ya dace ba ita don haka kamar mun sa an kore shi ne" 08094136204 A taimaka a rika comment kuma a rika sharing *Jeeddahtulkhair ce😘* [2/19, 5:29 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Gaisuwa mai tarin yawa gare ki yar tsohuwa mai ran ƙarfe kakata ta kaina abokiyar fadana, Zainab ummu Affan marubuciyar littafin MAJANEEN & SADEEQAT ina godiya da abin alheri Allah ya bar min ke ko ba kai ba kafa ko dan naci dariya🤣* *HALIMATU USMAN BAKORI naji sakonki na gode da kauna da kulawar da kike bawa wannan littafi kuma insha Allah zan riƙa kokarin yi muku page biyu a rana* *4* Washe gari da safe na tambayi innah ina son xuwa gidan kanwarta Adda saratu sbd a nan kusa da mu take kuma na dade ban ziyarce ta ba, kasancewar Baba baya barina na fita, maganganun su innah salamatu sun fara yi masa tasiri, wannan yasa yake saka min takunkumi sai wajen da ya yarda nake zuwa. Sai da na gama shiryawa tsaf na fito tsakar gida, tarar da innah nayi zaune a kofar daki tana gyara shinkafa, a ladabce nace "innah na fito ko kina da sakon da zaki bayar a kai mata?" Murmushi innah tayi. "Ba ni da wani sako Sa'adatu abinda zan ce miki kawai ki kula da kanki kuma kada kiyi dare, kinga dai irin rayuwar da muke yi ki gaishe min da ita da kyau, alewar kwakwa ta miko min, karbi wannan ki kaiwa yaran nawa. Sallama muka yi na fita a soro naci karo da zaliha wani kallon wulakanci tayi min a haka dai za a ƙare kullum a tafe an rasa mashinshini, ban saurareta ba sbd baxa tayi min haushi na rama ba. Cikin nutsuwa nake tafiyata, har na isa gidan Adda saratu sallama nayi na shiga gidan, yaran ta na tarar suna wasa a tsakar gida suna jin muryata suka taho da gudu suka rungume ni, "sannu da zuwa Aunty Sa'adatu, kin manta da mu" karɓar kayan da ke hannuna suka yi muka shiga cikin dakin Adda saratu, bamu tarar da ita a ciki ba kasancewar ta shiga wanka. Ruwa da lemo suka dakko min sannan muka fara hirar zumunci tare da su duk da cewa ƙanan yara ne amma suna da hankali da nutsuwa basu fiye shirme irin na yara ba, sbd Adda saratu mace ce mai nutsuwa da iya tarbiyya shi yasa ya'yanta suka fita daban a cikin yara. "Wata sabon gani yau kece a gidan namu" da sauri na waiwaya Adda saratu ce ta fito daga wanka, da sauri na ƙarasa muka rungume juna muna farin cikin haduwa da junanmu, waje ta samu ta zauna "yau kece a gidan namu, nayi mamakin ganinki don kin jima rabonki da mu, shi yasa nima nayi fushi na daina zuwa babu ke babu innah" Murmushi nayi wlh Adda makaranta ce ta boye ni, kin san na kusa haɗa haddata shi yasa bana samun lokacin ziyara" "Ayya shi yasa bana ganinki to Allah ya taimaka Allah yasa ta tsoron Allah ce, ai kuwa nima sai na hada miki walima 'ya guda ta haddace Alkur'ani ai dole mu nuna godiya ga Allah" tambaya ta jefo min. "Sa'adatu har Yanzu ba wani labari ne?" Murmushi nayi da akwai Adda amma Akwai yan matsalolin da ba a rasa ba, labarin Izuddeen na bata da irin matsalar da nake fuskanta a gidanmu addu'a ta yi min kan Allah ya kare ni daga sharrinsu. Haka muka cigaba da hira har zuwa yammaci sannan na tashi don tafiya gida, kayanta ta hado min kowanne da mayafinsa, saboda ta lura da irin kayan da suke jikina duk sun mutu, kusan kala goma ta bani, godiya nayi mata sannan na tashi na tafi. A kofar gida naci karo da Baba, wani kallo yake min wanda ya sanya gabana faduwa a cikin xuciyata na fada "Allah yasa dai ba wani laifin aka ce nayi ba" A sanyaye na tsugunna na gaishe shi amma sai naga ya kawar da kansa gefe, sake maimaita gaisuwar nayi a zatona ko ji ne bai yi ba, sai naga ya wuce ya barni a tsugunne. Jikina babu ƙarfi na tashi na shiga gida a tsakar gida na tarar da innah tana alwalar sallar magariba. A damuwar da ta ganni yasa ta saurin tambayata. "Lafiya Sa'adatu me ya same ki na ganki a haka" Ban fada mata ba Saboda bana so ta shiga damuwa ga shi ita kanta ba wani koshin lafiya gareta ba, "bana jin dadi ne innah ji nake kamar marata xata yi ciwo" cikin tausaya wa ta dube ni "Allah ya baki lafiya amma yana da kyau kije daki ki dauki maganinki sbd bana so ciwon nan ya tasar miki da ƙarfi" to nace na wuce daki. Shigowa tayi ta same ni, na hada kai da gwiwa "kin dai sha maganin ko, wai ni anya ma kuwa ciwon nan kike yi ba wani abu ne ya same ki ba?" amsa mata nayi da "shi ne innah babu wani abu da ke damuna" Kayan da aka bani na mika mata "innah kinga kayan da Adda saratu ta bani" cikin farin ciki ta fara bude kayan "kai madalla mun godewa sarai ita dai bata gajiya da yiwa zumunci hidima Allah ya saka mata da alheri" Cikin shagwaba nace "Kema ki duba ki zabi wanda xai miki dai-dai innah" "A'a Sa'adatu ki saka ai kece budurwa kin fini buƙatar kayan kwalliya, kuma ni wannan ɗinkin na yara ne ya xan yi da shi, ke dai ki saka ita kuma Allah ya biyata da aljannah" Muna cikin maganar naga Baba ya leko kwalawa innah kira ya fara yi, ita kanta tayi mamakin kiran da yake mata don rabon da ya kirata har ta manta, da sauri ta tashi ta fita. Ni kuwa xuciyata kamar ta tsaga kirjina ta fito saboda fargaba nasan da kyar ne idan kiran ba nawa bane. "Gani malam" A yatsine ya dube ta "ina Sa'adatu?" Ina ji kafin ta kirani naje tsugunna sbd bana so wani abin ya biyo baya "gani Baba" "Ina kika je yanxu don naga kwana biyu dabi'un ki sun fara canjawa ba irin yadda na sanki da kike ba" Kafin nayi magana har na fara kuka wannan yasa na kasa yin magana saboda baƙin ciki, wato dai ta tabbata zargina Baba yake yi. Kafin nayi magana ya wanke ni da mari "baxa ki fada min inda kika je ba sai na ci mutuncinki ko? Innah ce ta bashi amsa "Ba wani guri taje ba malam gidan sarai taje, sbd ta dade bata ziyarce ta ba" Dakatar da innah yayi "kada na sake jin kin min magana sbd kece munafukar da kike goya mata bayan duk abinda take yi, sbd ana shigo miki da leda ko, duk abinda yake faruwa ina ji kuma labari yana zuwar min, an fada min har yaron da yake lalata ta har gidan nan yake xuwa, to wlh duk randa na sake ganinsa sai ransa ya baci Allah yasa na sake ganin ƙafarsa a gidan nan" Dakawa innah tsawa yayi. "Maza dakko min ledar da ta shigo da ita haramiyarku" da sauri innah ta shiga daki ta kawo masa ledar kayan da Adda saratu ta bani, kiran innah salamatu yayi, cikin hanzari ta fito tana dariyar mugunta. "Gani malam" "Ina su zaliha" cikin kissa da makirci irin nata ta amsa da "suna daki" Kirasu su zo su kwashe kayan nan, da murnarta ta kwala musu kira kamar jiran a kirasu suke yi suka fito a guje, kayana baba ya miƙa musu ku karba ku je ku saka, ke kuma xaki gamu da ni. Ficewa yayi ya barmu a tsaye ni da innah, su innah salamatu da ƴaƴanta sai dariya suke mana tare da yi mana habaici. A salube muka shiga daki gaba ɗaya na kasa daina kuka, sbd na gaza gane irin wannan kiyayar da Baba yake mana, wani lokacin shi da kansa yake bada kofar da xa a ci min mutunci, nasihohi innah ta rika yi min tare da kwantar min da hankali cewa komai mai wucewa ne. Washe gari Baba bai fita ko ina ba sbd yana ta dakon xuwan Izuddeen, tunda dama sun riga da sun fada masa yau xai dawo, cikin ikon Allah sai kuma ranar bai zo ba, ban san uzurin da ya tsare shi ba kasancewar ba ni da waya, addu'a na riƙa yi Allah yasa dai ba su ne suka hargitsa min shirina ba don yanzu zuciyata ta fara kaunarsa Musamman da naga yadda yan gidanmu suka so su ya nema ba ni ba. Gaskiya rashin comment dinku Yana karya min gwiwa shi yake hana ni typing da yawa *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:29 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *NA* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ka ABDUL RAHMAN IBRAHIM admin Hafsat Hausa novels Facebook ina godiya da ƙoƙarin da kake yi wajen ganin littafin nan ya yadu ko'ina a duniya* *5* Washe gari ma shiru bai zo ba, tun daga lokacin hankalina ya tashi kewarshi nake yi sosai kamar mun dade da shi, tambayar kaina na shiga yi, anya ba baba ne yaje ya dakatar da shi ba kuwa, tunda mutanen gidan mu sun fada masa karya da gaskiya kuma sun san gidan da yake, ko kuma wani abu aka je aka fada masa a kaina, tambayoyin da na riƙa yi wa kaina kenan wanda na kasa samun amsar su, kasa hakuri nayi na tambayi innah ina son zuwa wajen Rukayya saboda nasan a wajenta ne kadai xan samu amsar tambayoyina. Gidansu Rukayya na nufa amma cikin rashin Sa'a sai na tarar da gidan a kulle basa nan. Raina bai min dad'i ba naso samunta mun tattauna a kan matsalar dawowa gida nayi da sauri kafin Baba ya fuskanci bana nan, addu'a na shiga yi Allah yasa alkhairi ne ya boye shi ba akasinsa ba. *WACECE SA'ADATU* Malam Salisu Abubakar shi ne sunan Mahaifina, muna zaune ne a garin kano cikin unguwa uku da ke kano, mahaifina ɗan kasuwa ne sai dai ba wani babban ɗan kasuwa ba, yana da rufin asiri dai-dai gwargwado, mun fi karfin ci da sha. Gidanmu irin babban gida ne family house kasancewar kakanmu malam Abubakar shi ne mai unguwar unguwa uku don haka duk yayansa shi yake yanka musu fili, wannan yasa muka kasance a dunkule a gida daya, mahaifina shi ne babban dansa, sai kannensa guda shida biyu maza huɗu mata dukkan matan suna aure a Kano, ragowar mazan ne muke gida ɗaya da su. Mahaifina yana da mata biyu, innah salamatu ita ce uwar gida tana da ya'ya tawas biyar maza uku mata, salisu, Hamza, Yusuf, Ibrahim, Musa, Aisha, zaliha, zainab. Ta aurar da ya'ya mazanta gaba daya sai kuma zainab wacce tun kafin mu yi wayo aka aurar da ita, wato A'isha da zaliha ne suka rage bata aurar da su ba wanda suka kasance kanne a gare ni. Innata Maryam ita ce amarya wacce na kasance yarta daya tilo kasancewar duk ya'yan da innah take haifa mutuwa suke yi ni kadaice na tsaya, shikenan kuma tun daga kaina bata sake haihuwa ba. Tare muke da kannen Babana da matayensu amma ɓangaren kowa daban, Baba Sani shi yake bin mahaifina wanda kuma shi ne mahaifin ya salim yana da ya'ya biyar biyu maxa uku mata an aurar da mata biyu saliha ce kaɗai ta rage ba a aurar da ita ba. Sai kuma Baba Umar wanda ya kasance dan autansu shi ma ya'yansa biyar shi kuma duka maza ne. A farkon zamantakewar gidanmu kan su innah da ragowar matan a haɗe yake babu wata matsala da ke tsakanin su, daga baya innah salamatu ta canja rayuwar gidan gaba daya da gulma da munafunci, aka hadewa innata kai muka zama abin tsangwama, babu laifin tsaye babu na zaune. Back to story A ɓangaren Izuddeen kuwa tunda ya koma gida yake fama da matsanancin ciwon kai, yayi ƙoƙarin zuwa yaga Sa'adatunsa amma hakan ya gagara sbd ko kofar gida baya iya fitowa sai dai abokansa su shigo su taya shi hira, ba karamin damuwa ya shiga na rashin ganin abin kaunarsa ba, ga shi ko waya bai bata ba ballantana ya kira yaji muryarta. Yau dai ya ɗan ji ƙarfi a jikinsa wanka yayi ya sanya farin yadinsa mai kyau, kayan ya karbi jikinsa kasancewar Izuddeen mutum ne ma'abocin son fararen kaya, cikin gidan su ya shiga don gaida mahaifansa, kai tsaye dakin Hajiya Amina (mama) ya shiga kishiyar mahaifiyarsa wadda ta kasance ita ce amarya kuma uwar dakinsa, tun lokacin da taxo gidan Izuddeen ya zamto dan dakinta, komai nasa a wajenta yake baxa ka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, Kasancewar kan iyayensu a haɗe yake komai tare suke yi baka gane tsakanin su. Da farin ciki ta karɓe shi "sannu da xuwa dana na kaina lallai jiki yayi sauki" guri ya nema ya zauna cikin ladabi ya gaisheta, amsa masa tayi tana mai tashi ta kawo masa kayan karin kumallo, bayan ya gama ci sun ɗan taɓa yar hira, sannan ya gyara zama "mama ina da magana da ke" da yake da sunan da yake kiranta kenan, hankalinta ta bashi ina "jinka dana na kaina" Sunkuyar da kansa yayi "Dama mama fada miki zan yi na samo miki suruka" farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta "Alhamdulillah Allah ya nufa nima xan ɗauki jikokina a hannu, ya sunan surukar tamu kuma a ina take" Kansa a sunkuye yake magana "sunanta Sa'adatu a nan kusa da mu take" Mamaki ne ya kamata "Izuddeen dama a nan kusa akwai yarinyar da zata burgeka gaskiya nayi matuƙar mamaki" Murmushi yayi "Dama lokacina ne bai yi ba mama shi yasa kika riƙa fama da ni a kan na samo mata to yanzu dai na samo na huta" murmushi suka yi gaba daya, fatan alkhairi tayi, "insha Allah yau xan gayawa malam, na san ba ƙaramin dadi xai ji ba" kujera ya nema ya kwanta. **************** Innah salamatu ce zaune a bakin Kofar dakinmu yau saboda tsabar raini da tsokana yau a Kofar dakinmu take bushe masara, tana busar tana habaici abinda na lura da shi a habaicin nata, da akwai abinda yake shirin faruwa da ni, ni dai addu'a nake Allah ya kare mu daga dukkan sharrinsu ni da innata. Sallamar Rukayya ce ta katse min tunanina da sauri na amsa mata lekowa nayi sbd baxan iya wucewa ba tunda innah salamatu ta tare bakin kofar da kayanta. gaisheta tayi amma bata amsa mata ba, sai ma bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo, bata kula da ita ba ta cigaba da magana da ni. "innah innarmu" amsa mata nayi tare da harararta "Ba a sani ba jiya ina ta nemanki kika kulle gida kika tafi" murmushi tayi "unguwa muka je ni da umma shi yasa baki ganni ba, ina innarmu nace miki?" "Bata nan taje unguwa" Hijabi na dakko tare da mika mata allona nace ta riƙe min kasancewar idan na fito da shi da kaina xan iya buge innah salamatu, ko samun kulle dakin ban yi ba sbd tare kofar da tayi. Wucewa muka yi muka makaranta. Muna barin kofar gidan mu abinda na fara tambayar Rukayya shi ne "ina Izuddeen kin ji wani labari daga gare shi" kallon saroro tayi min "ban gane ina Izuddeen ba ke da masoyinki ke xan tambaya inda yake" Rausayar da kaina nayi kamar xan yi kuka "tunda ya tafi bai sake dawowa ba dalilin da yasa naje gidanku nemanki kenan sbd hankalina ya tashi kwarai da gaske, kinga ranar da yaxo na tarar da su innah salamatu da yayanta har yayan wajensu ya salim sun kasa kunne suna jin tattaunawar da muka yi da shi, da Baba ya dawo sai suka juya min zance suka ce wai ɗan iskana na kawo shi ne Baba yace zai je ya dakatar da shi kada ya sake zuwar masa gida" Cikin tausayawa ta dube ni "kai amma mutanen nan an yi munafukai azzalumai, ta Allah ba tasu ba idan ina jin matsalolin gidanku sai na riƙa ji kamar a film, me yasa su innah salamatu suke haka na rasa dalilin wannan kiyayyar, ki kwantar da hankalin ki idan Izuddeen rabonki ne duk rintsi duk wuya sai ya aureki, matar Mutum kabarinsa wannan hassadar da suke miki baxa tasa kiyi ƙasa ba da yardar Allah sai kin fi ƴaƴansu komai" Har muka isa makaranta tattaunawar da muke yi kenan, don ko damar karatu bamu samu ba muna ta kullawa muna kwancewa, wani yaro na gani tsaye a kaina ɗaya daga cikin almajiran makarantar mu, "kixo inji malam jibo" kallon mamaki na hau yi masa a zuciyata na riƙa cewa kiran me malam jibo yake min, Rukayya ce tayi saurin cewa kace "Bata nan" dakatar da ita nayi "ki bari naje naji kiran kika sani ko maganar haddarta ce" har na miƙe ta zaunar da ni "wlh ba inda zaki je idan hadda ce ai da kansa yake xuwa, kika sani ko kararki Baba ya kawo, haka kawai ki kai kanki inda za a rika jibgarki kamar jaka" Komawa nayi na zauna 'Haka ne kuma Rukayya ni na manta da hakan ma sai da kika tuna min, ban san sharrin da aka kulla min ba" sake dawowa yaron yayi "Yace idan baki zo ba zai zo da kansa" Jikina na rawa na tashi na tafi, a cikin rumfar da yake karatu na tarar da shi zaune a kan buzunsa yana karanta Kur'ani, ga dogon carbi a gabansa, sallama nayi da fara'a ya amsa min, nayi mamakin karbar da yayi min kasancewar shi mutum ne ba mai yawan sakin fuska ba musamman ga dalibansa. Cikin ladabi nace "Gani malam" Murmushi yayi "Babanki bai fada miki komai ba?" kaina a sunkuye nace bai fada min ba, a xuciyata nace me Baba xai fada min haka? Katse min tunanina yayi da gyaran muryar da yayi, kallonsa nayi yana min murmushi tare da gyara hularsa. "to!! to!! to!! Tashi zai faɗa miki don jiya yazo nan ya same ni da wata magana ina fatan xaki bani hadin kai, amma nafi so dai kiji komai daga bakinsa" Jikina a sanyaye na tashi har na fita yana bi na da wani kallo da ni kaina ban san fassararsa ba. Wajen Rukayya na koma hankalina a tashe, tana ganina ta miƙe dafa kafadata tayi "lafiya naga walwalarki ta canja kawata faɗa min abinda ke damunki" Kwashe labarin yadda muka yi da malam Jibo nayi na fada mata, tunda Rukayya ta sunkuya bata dago ba ban san me ya hana ta dago bata kalleni ba. Jiya naji dadin comment dinku mutanena na group din DUKKAN TSANANI fans da JEEDDAH TIJJANI NOVEL mutanena na facebook ina gode muku ina jin dadin comment dinku Allah ya bar zumunci 08094136204 *Jeeddahtulkhair🥰* [2/19, 5:30 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gareka kanina sarkin fitina Buhari y ophicial (It'z B Y ebrerheem) Allah ya bar zumunci ina godiya da yadda kake taya ni sharing littafina* *6* Hawaye na gani ya cika idonta da sauri na fara tambayarta "menene ya sa ki kuka Rukayya? Kiyi hakuri insha Allah alkhairi ne xai same ni, ki daina damuwa da halin da na shiga a yanzu wata rana sai labari" ƙarfin halin mikewa tayi tare da riƙe hannuna "tashi mu je wajen innah hankalina baxai kwantar ba har sai mun samu amsar abinda malam ya fada miki, to ni me ma yake nufi da Maganar nan ni fa na fara tsoron al'amarin sa,, saboda tunda yake tare da mu bai taɓa kiranki ya faɗa miki wani abu makamancin wannan ba, gaskiya idan wani abu ya faru Baba ya cuce mu" tashi nayi ba tare da nayi mata gardama muka riƙe hannun juna muka tafi gida. Izuddeen muka hanga tun daga nesa yake mana murmushi babu wacce ta iya mayar masa da martanin murmushin da yake mana saboda dukkanmu muna cikin damuwa, ya lura da yanayin da muke ciki, sauri ya riƙa yi har yana tuntube don yazo ya tarar da mu. Sallama yayi mana gaba daya muka amsa Rukayya ce tayi ƙarfin halin yi masa magana "Izuddeen ya kake ya gida" amsa mata yayi da "lafiya" mayar da kallonsa yayi gare ni "nasan rashin ganina ne yasa kike fushi da ni to kiyi hakuri ba ni da lafiya ne shi yasa ban zo ba, sai yau na samu kaina" Kawar da damuwar da ke xuciyata nayi "Ai dole naji haushi kwana ɗai-ɗai har uku ban ganka ba kaima kasan dole na damu, kuma a ce kayi rashin lafiya baka faɗa min ba ai da naxo na duba ka, ko ban zo ba nasan Rukayya xata wakilce ni gaskiya kayi babban laifi kuma baxan hakura ba" Tsugunnawa yayi"ranki dade na san nayi laifi a yi hakuri kada a hukunta ni" murmushi nayi wanda bai kai zuci ba "baxan hakura ba har sai kayi min tsallen kwado" dariya muka saka gaba daya Rukayya ce tace "baza a yi haka ba tunda ya fadi uzurinsa shikenan" mun ɗan yi barkwanci sosai da shi kasancewar sa mutum mai saukin kai, kuma yana da nishadi da sakin fuska. Ya jiki muka yi masa, sannan na faɗa masa yadda nayi kewarsa amsa min yayi da "Na warware, nima nayi kewarki sosai ba don uzurin rashin lafiya ba da kullum sau biyu xaki ganni. Murmushi nayi "kada kasa a ce ka xama tun yanzu ka xama tace" rausayar da kansa yayi "Ai dama na xama ni kan kice ne ma ba tace ba, indai a wajen kyautata miki ne na yarda a kirani da kowane suna, idan kina da lokaci yau zan shigo" Gabana ne ya fadi saboda bana so yaxo Baba ya yanke mana hukunci karshe ya raba ni da shi ya janyo min asara, shirun da yaji nayi ne ya sanya jikinsa sanyi, cikin Siriya muryarsa yake min magana "ko dai bakya so naxo ne Sa'adatu, idan akwai wata matsalar ki fada min, don na san yadda zan yi na shawo kanta" Gargixa masa kai nayi alamar babu komai, sauke ajiyar xuciya yayi tare da furzar da numfashi mai zafi "shikenan Allah yasa abinda kika fada min haka ne" eh nace ai kasan baxan faɗa maka abinda yake ba dai-dai ba sallama muka yi da shi sai da ya rako mu daf da layinmu sannan ya juya. Ko da muka koma gida innah bata dawo ba, rashin dawowar innah ba ƙaramin damuwa ya jefa ni ba, muna cikin wannan halin naji maganar Baba sai a lokacin na san yana gidan, cike da fargaba da rashin sanin yadda xan tunkare shi da abinda malam Jibo ya fada min na tashi jikina babu ƙarfi, tunda na fito naga su A'isha da zaliha suna ta tuntsura dariya, wacce ni kaina na kasa gane fassararta wucewa nayi na kyale su suna ta haukansu. A dakinsa na tarar da shi yana cin abinci, da sallama na shiga ina ganin haka na juya saboda na san indai yana cin abinci baya saurarar duk wanda yazo wajensa. Juyawar da nayi ne yasa shi kwala min kira, jikina na rawa na koma "gani Baba" cikin ɓaci rai ya fara min magana "Lafiya naga kin zo kuma kin juya wane munafuncin ne kuma ya kawo ki da har yasa kika juya?" Kaina a ƙasa na fara magana "Dama malam Jibo ne ya kira ni daxu da naje makaranta yace idan naxo gida na tambaye ka maganar da ku ka yi" Ajiyar zuciya yayi "ina da dama da ikon da zan yi duk abinda naga dama a kanki, bana buƙatar shawara da ke ko wani abu da yayi kama da haka, kije idan da rai da lafiya zaki ga amsar tambayar ki a aikace" Ji nayi kafafuna sun kasa ɗaukana jiri na shirin dibana ya fadar da ni a kasa, don haka na nemi guri na tsaya. Tsawar da ya daka min ce ta dawo min da ni hankalina jikina "fice min daga daki munafukar banxa munafukar wofi kin tsaya kina sand'a kamar mutuniyar kirki" Da sauri na fita na bar masa dakin, abinda na kasa ganewa shi ne mai baba yake nufi da xan ga abinda yake nufi da idona idan muna da rai da lafiya?????? *Yau ba comment da yawa, idan ana comment pages uku xan dinga yi kullum matuƙar aka daina comment ni kuma xan daina typing gaba daya* Kada a manta a taya Ni sharing *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:29 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Wannan shafin sadaukarwa ne gareki DALA admin Dala novel Ina godia da gudunmawarki gareni* *7* Da kyar na ja kafa na shiga daki, ina zuwa na zube a ƙasa, mikewa Rukayya tayi tare da tambayata "ya faɗa miki abinda maganar malam ke nufi"? Cike da damuwa na yi mata bayanin yadda muka yi da shi, haɗa kai muka yi muna kuka mai cike da ban tausayi ni ina tausayawa kaina ban san ma'anar abinda Baba yake nufi ba, Rukayya na tausaya min halin da xan tsinci kaina a ciki. Har yamma innah bata dawo ba wannan dalilin ne ya ƙara saka ni a tashin hankali sbd tunda nake da ita ban taɓa ganin taje unguwar ta kai yammaci ba iyakar dadewarta la'asar, hankalina ne ya ƙara tashi ga damuwar Baba ga damuwar tafiyar innah, ga shi babu waya a hannuna ballantana na kira gidan da taje. Mayar da kallona nayi ga Rukayya "Ni fa na fara damuwa dadewar nan ta innah tayi yawa" cike da kulawa take min magana "Nima haka wlh magana ne kawai ban yi ba kada na sake ji miki wani ciwo a xuciyarki, amma tashi mu je gidanmu ki xauna zuwa anjima sai mu dawo mu duba ko ta dawo" tashi nayi na dakko hijabi na saka muka tafi. A cikin damuwa ummansu ta ganmu tambayar mu halin da muke ciki tayi, ban iya yi mata magana ba saboda na san ina farawa xan iya fashewa da kuka sai Rukayya ce ta faɗa mata abinda ke shirin faruwa da ni. Kwantar min da xuciya tayi da kalamai masu ratsa jiki da sanyaya ruhin ɗan Adam musamman idan yana cikin damuwa, abinci ta xuba mana bai fi cokali uku nayi ba na ajiye saboda damuwa ta cika cikina. Sai da muka yi sallar magariba sannan muka dawo gida, abin mamaki a kulle na sake ganin dakin innah tashin hankali ne ya bayyana a fuskata sai naji kamar na fashe da kuka amma sai na daure saboda bana so su A'isha su gane halin da nake ciki, jan hannun Rukayya nayi muka koma soro saboda baxan iya jure xama a dakin innah ba, ba tare da tana cikin dakin ba. Zama muka yi shiru babu mai cewa kowa komai sai dai tunani da kukan zuci da nake yi. Sallamar ya salim ce ta dawo da ni hayyacina, haska mu yayi da wayarsa "Au dama ku ne a zaune ai na zaci aljanu ne" dariya muka saka gaba daya nice nayi ƙarfin halin yin magana "Haba ya Salim aljanu xaka gani a haka" murmushi yayi "Eh mana idan ba aljani ba waye xai xauna a duhu shi kadai" "Akwai abinda muke jira shi yasa ka ganmu a nan" kallona yayi yana murmushi "ko dai mutumin ne zai dawo" girgiza kaina nayi "ba shi bane innah nake jira ta tafi unguwa tun safe bata dawo ba" ɗan hararata yayi " ka ji ta da wani zance wai innah kike jira banda abinki innah xata bata ne, xata dawo duk inda ta tafi bwatakila ma tana kan hanya, ke dai naga yadda xaki yi idan aurenki yaxo lokacin da xaki rabu da innah" Kwalla naji na ƙoƙarin fito min da sauri na mayar da ita "Ba don aure sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam bane da nace baxan yi ba saboda rabuwa da innah a rayuwata ba ƙaramin tashin hankali bane" ji nayi mahaifiyarsa ta kwala masa kira, bai amsa ba sai da muka gama magana sannan ya amsa mata da yana zuwa. Duk da cewa muna ɗan nesa da juna amma sai da na jiyo sautin muryarta tana yi masa faɗa "kai wane irin yaro ne mara jin magana, ba na raba ka da Sa'a ba, me kuma kaje kana ce mata? tun wuri ka daina kula yarinyar nan kafin nayi maka baki" shi dai shiru naji yayi mata bai ce komai ba ni kuwa a xuciyata nace "yau na janyowa ya salim faɗa" Ni kaina ina so na daina saurar shi idan ya kula ni, sai dai baxan iya yin hakan ba saboda yadda yake bani kulawa da yadda yake damuwa da dukkan abinda ya dame ni. Muna a wannan halin muka ji sallamar innah da sauri na tashi na rungume ta ina yi mata oyoyo ita ma Rukayya sannu da zuwa tayi mata, sai dai abinda ya bani mamaki tare da kakarta gwaggo Abu suke tafe, da alama ita ce ta rakota gaisheta muka yi da sakin fuska ta amsa mana, bin su muka yi gaba daya muka shiga ciki, ƙoƙarin bude dakin nake yi xamu shiga, muna gama buɗe musu dakin gwaggo Abu ta dakatar da mu "ku tsaya a nan na fito sai ku shiga" bin umarninta muka yi muka zauna a bakin kofa, abinda na fahimta akwai maganar da zasu yi wacce basa so mu ji. Cikin siririyar murya take yiwa innah magana "kiyi hakuri mero, wannan dakin shi ne sutturar ki duk abinda za a yi miki ki kawar da kai kiyi hakuri, idan kika ce kin yi fushi ki tafi kin bar gidan nan wane hali kike so 'yarki ta samu kanta, kin san dai halin malam Salisu sarai baxai bari ki tafar masa da 'ya ba, dan Allah kiyi hakuri da dukkan abinda zaki ji ko ki gani wata rana sai labari, basu isa su yi muku abinda Allah bai muku ba, komai kika ga ya samu bawa mukaddari ne sannan ki manta da Maganar mutumin nan zamu yi iya bakin kokarinmu wajen hana abin sai dai idan kuma ya fi karfinmu" Godiya innah tayi mata, sai da ta raka gwaggo Abu har bakin kofa sannan ta dawo, abinda na fahimta a Maganar da suke yi kamar yaji innah tayi aka dawo da ita. Daki muka shiga tambayarta na fara yi "Innah ina kika tafi kika barni ina ta tunani duk duniya tayi min zafi" ƙoƙarin mayar da damuwarta tayi don kada na gane halin da take ciki amma hakan ya gagara don kallo daya xaka yi mata ka gane akwai damuwa mai yawa a tattare da ita. "Yau na sha yawo ne a garin nan Sa'adatu shi yasa na dade ban dawo ba, kin san na dade ban fita ba to akwai gaishe-gaishen marasa lafiya da naje da gaisuwar mutuwa da yan barke-barke shi yasa na dade" Sannu da zuwa muka yi mata, har na bude baki xan tambayeta dalilin rakiyar da gwaggo Abu tayi mata sai kuma na fasa, saboda bana so na ƙara tayar mata da wani tabo a xuciyarta, sai bayan sallar isha'i Rukayya ta tafi gida yau da wuri muka kwanta bacci saboda mu yi yaƙi da damuwar da ta addabe mu. Yau ya kama Alhamis ba makaranta don haka ban tashi da wuri ba sai da rana ta ɗaga sosai kasancewar garin akwai dan sanyi, ita ma Innah baccinta take yi, daga gidansu Rukayya aka aiko mana da abin karin kumallo sai da muka watstsake sosai muka karya. Muna cikin cin abincin na jefawa innah tambaya "innah wai me Baba yake nufi dani? naje makaranta ne jiya sai malam jibo yace naxo na tambayi Baba a kan maganar da yaje masa da ita, da na dawo na tambaye shi ya nuna min cewa duk hukuncin da ya yanke a kaina ya yanku sai dai nayi hakuri dan Allah me yake nufi da hakan, na tambayi kaina na kasa gane amsar abinda suke nufi, na san duk abinda yake faruwa zaki iya sani kuma baxa ki boye min ba"? Ina kallon idanun innah kamar xasu xubar da hawaye, hadiye miyan takaici tayi gami da cewa "Babu komai Sa'adatu kawai xance ne irin nasa so yake ya tayar mana da hankali" Kuka na fara yi "Allah innah da gaske yake, lokacin da yake Maganar babu wasa a fuskar shi, shima malam din haka sannan malam Jibo yana magana yana murmushi, a jiyan kuma naji innah salamatu tana habaici maganganunta sun yi kama da abinda malam da Baba suka fada min kada fa a ce shi Baba xai aura min" Saurin dakatar da ni tayi " ya kike irin wannan maganar Sa'adatu bana so na sake jin irin wannan daga gare ki, kin san haka baxai faru ba insha Allah" Sosai nake kuka "wlh Innah indai shi aka ce za a aura min baxan xauna ba kuma sai yaga salo salo na rashin mutunci, saboda an raina mu duk ya'yan gidan nan ni kadai aka tsana wa aka taɓa yiwa irin abinda ake mana, wannan karon baxan iya yiwa Baba biyayya ba sai dai idan a kore mu" Shiru Innah tayi tana saurarona nasan bata taba tunanin fitowar wadannan xantukan daga gare ni ba. Rarrashina ta shiga yi har sai da xuciyata tayi sanyi. Yau muka yi da Izuddeen xai kawo min ziyara tun yamma na fara shiryawa saboda na kosa yazo a yi duk wacce za a yi yanxu tsoron kowa ya fita a xuciyata, Bayan sallar magariba na cigaba da jira shiru bai zo ba, sai daf da isha'i aka aiko yaro ana kirana, ban ja lokaci ba na fita shimfida nayi masa a inda ya xauna ran nan, gaisawa muka yi muka fara hirar mu ta masoya, cike da nishadi muke maganar mu kamar babu wata damuwa a raina, sai da hirar mu tayi nisa sannan ya miko min wata leda, "karbi wannan Sa'adatu" makale kafada nayi alamar baxan karba ba sake miko min yayi "ki karba kiga abinda ke ciki" ban yi masa gardama ba na karba ina budewa waya na gani sabuwa fil a kwalinta kirar infinex, da sauri na bude ido " wannan wayar ta min girma ka barta idan kana da karama ka bani" a xuciyata nace idan ka bani wannan ai sai a ce karuwancin nake yi da gaske, muna cikin duba wayar muka ji mutum a kanmu. Daga idon da zamu yi naga Baba yana mana wani kallo, cike da ladabi Izuddeen ya gaishe shi, harara ya kwada masa bai kuma amsa gaisuwar ba. Cikin fushi ya nuna Izuddeen da hannu "Dan ubanka dama kaina kake zuwa har gida kana lalata min yarinya" Kallon mamaki Izuddeen ya bi shi da shi saboda bai san me yake nufi da abinda yake fada ba, cikin ladabi ya sunkuya "wlh Baba ba da niyyar yaudarar Sa'adatu naxo ba naxo ne don na aureta" nuna shi yayi da hannu aurenta xaka yi amma kaxo kana lalata ta da Abin duniya salon ta bijirewa iyayenta ko? Irinku ne masu hurewa yaran Mutane kunne har gida, ashi ka fita ka bar min gida kafin ranka ya ɓaci kada na sake ganinka a nan, ke kuma xaki zo ki same ni" Wucewa yayi ya barni a tsugunne ina sharar hawaye har Izuddeen ya fita yana waiwaye na. Idan an yi comment na saki page 8 Idan ba a yi ba na rike kayana sai gobe Kada a manta a rika sharing don yan uwa su karanta *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:30 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *8* A bakin tebur ɗin mai shayin da ke saitin gidanmu ya tsaya yana hangena, kallo mai cike da soyayya da tausayawa yake min idanunsa sun yi jawur kamar zai fashe da kuka, sai da ya gama kallona tsaf sannan ya juya cikin tsananin ɓacin rai da damuwa. Bai wuce gida ba saboda zafin da yake ji a ransa kai tsaye wajen abokinsa Kabir ya wuce, a Kofar gida ya same shi yana yana karkade machine dinsa da alama shirin tafiya wani wajen yake yi, yana ganinsa ya saki fuska "mutumina yau kuma kaine a dai-dai wannan lokacin, ai kuwa kaxo a dai-dai sai kayi min rakiya wajen madam don yau zuwa na musamman zan yi mata" shirun da yaga Izuddeen yayi masa ne ya tabbatar masa da ba lafiya ce ta kawo shi ba yanayinsa ya canja lokaci daya idonsa ya faɗa gashi yayi ja. Matsawa yayi kusa da shi yana tambayarsa "lafiya kuwa mutumina na ganka a haka, Allah yasa dai ba mutuniyar ce ta haɗa maka xafi ba" ya karasa magana yana dariya tunda dama Kabir gwanin zaulaya ne sun saba tsokanarka juna ya tsokane shi, shima ya tsokane shi haka suke yi. Shiru yayi ya kasa magana saboda abinda ya cika masa zuciya. Ganin yadda yake ne yasa yayi saurin gane ba lafiya ba saboda babu yadda za a yi ya tsokani Izuddeen ba tare da ya rama ba, amma yau sai bin sa kawai yake yi da ido. Zaunar da shi yayi "me yake damunka Izuddeen ni fa ban saba ganinka a irin wannan yanayin ba faɗa min damuwarka mana" Wani daci yaji ya taso masa daga kasan makoshinsa a hankali ya hadiye miyan takaici, a gintse ya amsa da "ina cikin tashin hankali Kabir mu shiga daga ciki na faɗa maka" Tashi suka yi suka shiga soro wanda a nan dakin Kabir yake. Furzar da numfashi yayi mai cike da takaici "ka san yarinyar da nake baka labarin na haɗu da ita kwanaki?" Cikin kulawa Kabir ya amsa masa da "Eh" Shiru yayi na wasu yan mintuna sannan ya cigaba da magana. "Tun kafin na furta ina sonta nake ganinta a hanyar xuwanta makaranta, na yaba da hankali da nutsuwar yarinyar wannan dalilin yasa nake matukar sonta har na fara zuwa wajenta hira mun fara fahimtar juna, sai kuma babanta ya bijiro min da wasu abubuwa wanda na kasa gane inda ya dosa, yanzu ma kokarin da yake yi shi ne neman ya raba ni da ita, yanzu haka ma wajenta naje shi ne yayi min korar kare, ban sani ba ko bai shirya aurar da ita bane nayi masa katsalandan" Cikin nuna damuwa da halin da abokinsa yake ciki ya fara magana. "Subhanallahi to me yake nufi, Ni dai nasan gaba da baya ba kada wani abin kunya ko makusa abokina, kuma dai-dai gwargwado kana da rufin asirin da xaka iya riƙe yarinyar, sannan iyayenmu mutanen kirki ne ba su da wata matsala, ka cancanci a soka na san duk wani uban da kaje neman auren yarsa xai yi alfahari da hakan, amma bamu sani ba ko kuma miji yayi mata shi yasa ya dakatar da kai" Saurin girgiza kai Izuddeen yayi, "gaskiya bana zaton an yi mata miji don tun farkon haduwa ta da ita bata faɗa min cewa akwai wata magana a kanta ba, nafi tsammanin akwai abinda yarinyar take boye min" "Ok ba mamaki amma shawarar da zan baka, ka fadawa Baba kana sonta a aika a nemar maka izinin zuwa zance, ina ganin wannan rashin aikawar ne ya ɗan baka matsala" Girgiza masa kai kawai Izuddeen yayi sbd yanxu Maganar ma wahala take masa tunanin yadda za a ce an raba shi da Sa'adatu yake yi, ya san har abada baxai taɓa jurewa ba, Kabir ne yake ta yi masa hira don hankalinsa ya kwanta shi dai jin shi kawai yake amma zuciyar shi da hankalinsa yana wani wajen daban, har gida Kabir ya kai shi a machine sbd baxai iya tafiya da kanshi ba kasancewar baya jin karfin jikinshi. ************* Na fi rabin hour a zaune ina zulumi, ni ban shiga gida ba ni kuma ban tashi daga inda nake ba, tunanin inda zan ajiye wayar da ya bani nake yi saboda bana so a kwace masa wayarsa karshe nasan ba nice xan mora ba, a gabana xa a yi wa su A'isha kyautarta ni kuma a bar ni da kunar zuciya. A bayan kaure na ajiyeta da niyyar idan kowa ya shiga daki na dawo na ɗauka. Tunda na doso kai bakin kofa naji an cika tsakar gida ana ta maganganu da dukkan alamu zuwana ake jira, komawa soro nayi na zauna a raina nace "sai kun gaji da xama xan shigo dan baxan xo a kusan cinye namana danye ba" komawa nayi na xauna abuna, shirun da suka ji yayi yawa ne yasa Baba xuwa da kansa kirana. "Kina nufin baxa ki shigo bane Sa'a ko kuma binsa xaki yi ku tafi, ina nan ina jiranki kixo ko kuma ranki ya ɓaci" Daurewa nayi na miƙe idanuna suna ƙasa na kasa dagowa a hankali nake jan ƙafa har na shiga ciki, idanun kowa ne ya dawo kaina ana yi min wani kallo mai ɗauke da fassarori masu yawa, cikin kakkausar murya Baba ya fara yi min magana. "Tsugunna nan zan tsaga miki sharudda a gaban yan uwanki saboda ina so su zama shaida ko zuwa gaba" ban yi gardama ba na xauna tare da sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun kafata, addu'a na shiga yi Allah ya bani damar daurewa kada makiyana su ga kukana. "Wannan shi ne maganata ta ƙarshe da ke kada na sake ganin wannan yaron a gidan nan idan ba haka ba kuma zaki haɗu da fushina daga ke har mahaifiyar ki, kin ji abinda na fada miki ko" gyada kaina nayi alamar eh. Innah salamatu ce ta amsa da "kai kake bata bakinka malam amma ba saurara abinda take yi xata yi ba, sau nawa kasa doka aka karya maka, shawara daya xan baka kaje ka dakatar da yaron nan har gida, ko kuma ka bani dama ni naje da kaina tunda kai naga bori kake yi da sanyin jiki" Maganar innah ba ƙaramin tokare min xuciyata tayi ba, na san matuƙar taje gidan su Izuddeen Maganar aurenmu ta gama lalacewa har abada, har na gwammace zuwan Baba a kan nata saboda shi idan suka gyara zancen xai iya amincewa da aurenmu. Cikin gamsuwa da abinda ta faɗa ya jinjina kai "Kwarai kuwa xuwan naki ma ya fi muhimmanci tunda kin san gidan, kuma ke xaki samu mahaifiyarsa kai tsaye ki fada mata kudurinsa na son lalata mana yarmu. Ni kuwa ba lallai ne na samu babansa ba, don haka gobe da safe kije ki fada musu su katange dansu ni ma zan bawa yata kariya duk abinda ya biyo baya kuma kada su zarge ni su zargi kansu" Farin ciki ne ya bayyana a fuskarta taji dadin hukuncin da aka yanke min, cikin kissa take magana "Amma malam ina ganin har da rashin abincin nan da ba a bata, shi ne yasa take so ta jefa kanta a rayuwar da ba tata ba, ina roko a dawo musu da kwanon su ita da borar uwarta ko sa ji sassauci, idan aka tsare mata cikinta za a toshe wata kafar barnar tunda dama da yunwa ake fakewa ake wata lalatar" Shiru yayi na dan lokaci sannan yayi magana "to shikenan tunda kin amince ki cigaba da basu amma ki tabbatar sai kowa ya koshi" Amsa masa tayi da "To" har ya juya xai tafi ta kira shi. "Au malam baka ji ba" da rawar jiki ya dawo "Da akwai abinda kika manta ne baki fada ba?" Cike da makirci tace "Maganar bawan Allahn nan ya kamata a taso da ita tunda da kanka kaje ka same shi ka faɗa masa damuwarka, kuma ya yarda ya amince, amma kuma har yanzu baka sake cewa komai ba kamar wanda aka daurewa baki, kaga wannan ma wata hanya ce da xata sa a toshe kafar barna tunda dai ta nuna aure take so, kuma hakkinka ne dama ka aurar da ita don haka tunda akwai miji a kasa me ake jira sai magana kawai" Sauke ajiyar zuciya yayi "ina sane da wannan maganar akwai abinda nake jira ne shi yasa kika ji nayi shiru amma ba mantawa nayi ba" Juyowa yayi kaina "Au dama tun daxu kina nan munafuka, kin sa mutane a gaba kina zare mana ido wato duk maganar da za a yi sai kin ji ko, tashi maza ki bace min da gani kafin na karya munafukar kafar taki" Tashi nayi na shiga daki a xaune na tarar da innah tana karanta littafin addu'o'i babu wani alamar damuwa a tare da ita, duk da cewa na san duk abinda aka taji tattauna a kunnenta, sannan ta san da dukkan abinda ake kulla min, gefenta na samu na zauna nima ƙoƙarin kin nuna mata damuwata nayi, sai da naga alamar ba tada niyyar ce min komai sannan nayi magana. "Innah wai duk abin nan da ya faru baki ji bane naga kina ta karatu kamar baki san anyi wani abu ba, naga ma kamar baki damu ba". Fuskarta mai cike da kamala ta dago "to me zan ce Sa'adatu, wanda yake da Allah me xai dame shi, ina ganin addu'a ce kawai maganin abinda yake faruwa a gidan nan, ni da Allah na dogara kuma nasan xai isar min, duk abinda suke yi na barsu da Allah idan ba yau akwai gobe, kema abin ya daina damunki idan mijinki ne duk makircin da zasu shirya sai ya rushe kin aure shi, shi yasa abin nasu ma ya daina damuna" Tawakkali da nutsuwar innata da yadda take samun nutsuwa a duk lokacin da masifa ta same ta ba ƙaramin karfafa min gwiwa yake yi ba, wannan Dalilin ya sanya na daina saka kaina a damuwa, kallon duk abinda suke mana nake yi a matsayin film wata rana dole zai kare. Ban sake yin magana ba sai da naga ta idar da addu'ar da take yi saboda bana so na katse mata abinda take yi, cike da ladabi nace "innah waya fa ya bani shi ne abinda ya janyo wannan kace nace din, wai Baba da kansa yake cewa lalatani yayi sannan ya bani" Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, rarrashina innah take yi "Duk naji abinda suke faɗa Allah ya fi mu sanin halinmu, kuma zai mana hisabi a kan abinda suke fada shi yasa ban fito na kare ki ba, saboda nasan ko na faɗa a banxa ba yarda xasu yi ba, cewa zasu yi ni na yarda kiyi, don haka ki kyale su Allah baya bacci, yanzu ina wayar" Cikin kukan na amsa mata da tana bayan kyauren soro. Da sauri ta dube ni, "kika ajiye masa waya a soro salon a je a sace, yi maza kije ki dakko" tashi nayi na tafi naje na bude bayan kyauren abin mamaki banga waya ba, hankalina ne ya tashi na rika duba lungu da sako amma babu waya babu dalilinta. Da gudu na shigo gida na karbi touch light na haska ko idona ne bai ga dai-dai ba nan ma dai shiru babu waya, da kuka naxo nake sanarwa innah ban ga waya ba. Ita ma hankalinta ne ya tashi sosai saboda kada mu je Izuddeen yace bai san xance ba sai mun biya shi waya, ga shi ba wani na bawa ajiya ba ballantana na tunkare shi nace ya bani. Mun fi 2hours muna neman waya ba labarinta, mu ba abin mu yiwa jama'ar gida cigiya ba mu janyowa kanmu gori. Bayan Asubah ma sai da na sake dubawa ban ganta ba, kuka sosai na riƙa yi ina addu'ar Allah ya bayyana wanda ya sace ta, innah ma taya ni ta riƙa yi. Ina godiya gare ku mutanena na DUKKAN TSANANI FANS Ina godiya da comment dinku kuma kuna karfafa min gwiwa. Kada a manta da sharing *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:30 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *9* *Yau shafin gaba daya na baku shi kyauta ku yi yadda kuke so da shi saboda dadin comment dinku da naji Maryam Amatullah (maman kausar) da Ramcy k Aleeyu* Gari na wayewa na tafi gidan su Rukayya tunda ta ganni da sassafe haka ta san ba kalau ba, tana ganina ta miƙe tana tambayata "kada dai kice wani abin ne ya sake faruwa Sa'adatu" cikin kuka nake bata labarin zuwan Izuddeen da labarin batan wayar da ya bani, tayi bakin cikin batar wayar sosai, ummansu ce ta bani kudi muka siyo alewa tace mu kai makaranta a yi sadaka a roki Allah ya bayyanata, malamin ƙananan yara na samu na bawa na fada masa a kan bukatar da nake so a yi min addu'a Allah ya bayyana barawon da ya saci wayar, tun kafin na bar gurin aka sa yaran suka fara hasbunallahu abinka da yara sun ga alawa sai ƙara bada himma suke sosai. Mun juya xamu tafi kenan naji an kirani ban amsa ba sai da na juya don naga mai kirana, malam Jibo ne ya leko da kansa daga rumfar da yake karatu, nuni yayi min da hannu naxo, kallon Rukayya nayi tare da cewa "kixo ki raka ni" kafewa tayi a kan baxa tayi min rakiya ba, kuma nima baxan je ba, ganin yadda ya kafe ta da ido ne yasa ta sake ni naje kiran. Raina a haɗe naje yau ba irin tsugunnon da na saba nayi masa ba, a takaice nace ina "kwana" Yana murmushinsa mai cike da ban haushi ya amsa. Ina gama gaishe shi na miƙe na juya baya zan tafi ya kira sunana "sauri kike haka ne Sa'adatu daga gaisuwa sai tafiya, me yasa yau baku zo makaranta ba, naga kwana biyun nan kuna wasa da hadda bakwa bada himma irin da" a gintse nace "ina da abin yi ne shi yasa" Ina gama magana na fita ina ji yana kirana nayi banxa da shi na tafi. Ko da na dawo babu Rukayya babu dalilinta da alama fushi tayi shi yasa ta tafi ta kyale ni, a hanya naci karo da ita ta rabe jikin wani gini tana jirana, bi na tayi da harara duk maganar da nayi mata bata amsa ba sai can tayi min magana cikin fada "wlh duk kece kike bawa mutumin nan kofar da zai raina ki me xai hada ki magana da shi, kawai don ya kiraki sai ki bi shi kamar wata jela, idan bakya saurarsa ko shi ne shugaban marasa zuciya dole ya hakura ya kyale ki, wannan sanyin naki idan baki daina shi ba bazai haifar miki da ɗa mai ido ba, idan baki ɗauki mataki ba ke zai zo addaba ba ni ba, shawara nake baki tun wuri kiyi maganinsa don naga ke kamar ta ruwan sanyi kike binsa" Mayar da ajiyar zuciya nayi ina nazarin maganganunta wanda suke da tasiri a gare ni, shiru nayi har muka kusan zuwa gida tana min faɗa. komawa gidansu muka yi muka sanar da umma cewa mun bayar har an fara addu'a. ************** Yau Izuddeen a makare ya tashi tun bayan da yayi sallar asuba ya kwanta ba shi ya farka ba sai wajen sha biyu saura. Saboda jikinsa ba ƙarfi zafin abinda Baban Sa'adatu yayi masa ne yake taɓa xuciyarsa, shi yasa ya zabi yayi ta bacci ko xuciyarsa xata yi sanyi, a hankali ya mike daga shimfidarsa banɗaki ya shiga yayi brush ya dan watsa ruwa, bayan ya fito ya fesa turare kala-kala masu daɗin kamshi saboda shi ma'abocin tsafta ne da son kamshi shi yasa bai fiye fesa turare kala ɗaya ba, sanya farar jallabiya yayi, sai da ya kulle dakinsa sannan ya nufi hanyar shiga gida don ya gaisa da mahaifansa, tunda yau tun safe basu ji motsinsa ba zasu iya shiga damuwa idan basu ganshi ba musamman Mama da yake dan lelenta. A bakin kofa ya ci karo da wata mata wacce baxai iya tantance ko wace ce ita ba, sai dai abinda ya bashi mamaki ganin kwalin wayar da ya kaiwa Sa'adatu jiya a hannunta, tambayar kansa ya shiga yi "me kuma ya haɗa wannan matar da kwalin wayar Sa'adatu, ko dai ita ce mahaifiyarta, idan kuwa haka ne ya san duk shirinsa sai an tarwatsa masa, don ya fuskanci kamar iyayen Sa'adatun basa son alakar shi da ita" kai tsaye yaga ta shiga cikin gidansu wannan ya tabbatar masa da cewa tuntuni dama ta san gidan, don bata tsaya tambayarsa hanyar da xata sadata da wajen iyayensu ba, kasancewar gidan su Izuddeen babban gida ne ɓangaren kowa daban. Ɓangaren mama yaga ta nufa, dalilin da yaja hankalinsa kenan ya bi bayanta saboda ya san kowace ce daga gidan su Sa'adatu aka turo ta. Ganin ta shiga dakin mama ne yasa ya dawo da baya tunda ko menene indai maganar ta shafe shi sai yaji, dakinsa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarsa yana Game kamar yadda ya saba. Da sallama ta shiga dakin a zaune ta tarar da mama saboda a lokacin ta idar da sallar walha tana addu'a, sai da ta shafa sannan ta juyo gareta da karamci ta karɓe ta gami da yi mata sannu da zuwa, cikin farin ciki ta amsa. Bayan sun gama gaisawa mama ta mayar da kallonta gareta da cewa "kiyi hakuri Hajiya ban wanye da ke ba, da yake jama'ar tamu da yawa" Sunkuyar da kai kasa tayi sannan ta fara magana "La ba komai Hajiya ai komai sai da dalili, Ni sunana Hajiya salamatu a nan makotanku muke, nice matar malam Salisu" Murmushi Mama tayi "Ayya sai kuma da kika yi bayani na gane ki, kin san an dade ba a hadu ba" "Wlh kam haduwa tayi wuya kin san da yake komai sai Allah ya nufa" Bayan sun gama gaisuwar yaushe gamo ta kalli mama jin daɗin yadda tace ta gane ta ne yasa ta saki jikinta ta fara bayani. "Dama na zo ne a kan Maganar danku Izuddeen da yaje neman auran yarmu" cikin farin ciki tace "Oh Allah sarki kwarai kuwa ya faɗa min da har muna shirin aikowa ma kwanan nan tunda ya gama karatu me ake jira sai aure kawai" Rausayar da kai innah salamatu tayi "Hmm da kin san Abinda Ya kawo ni da baki fadi haka ba" Cikin rashin fahimtar abinda take faɗa ta dubeta, "Ban fahince ki ba Hajiya wani abin ne ya faru" jinjina kai tayi kwarai kuwa hakan ne ma yasa mahaifinta yace na taso da kaina na faɗa muku abinda ke faruwa don ku kula" Gyara xama mama tayi, a zuciyarta addu'a take Allah yasa dai ba wata maganar Izuddeen ya dakko musu ba, duk da cewa ta san ɗan nata kamili ne ba a taɓa kama shi da wani laifi ba, amma ta san sharrin zuciya ba tada Kashi ko ita ce, ta ja shi ya aikata laifi, jefa mata tambaya mama tayi "wani abin Izuddeen dina yayi" Jinjina kai innah salamatu tayi "A'a babu abinda yayi amma mun zo mu ankarar da ku ne, yarinyar da yake nema 'yata ce amma ba ni ce mahaifiyarta ba, amma ni nake rukonta duk halinta na sani yarinyar ba tada dabi'u masu kyau, an zubar mata da ciki ya kai sau biyar, jiya yaron yazo xance mahaifinta da kansa ya kamata tana ƙoƙarin lalata shi, kinga fitina tun tana karama ake maganinta shi yasa Babanta da kansa yace naxo na faɗa muku ku katange danku ku raba ta da shi tun kafin ta lalata masa kuruciya, saboda bai kamata a ce gida kamar wannan da ku ka yi shuhura a arxiki da ilimi a ce an auro muku mara tarbiyya ba, kinga abu bai yi kyau ba kenan" tunda ta fara fada mata wannan maganar mama ta kasa magana duk hankalinta ya tashi, yanxu a ce duk tarbiyyar da suka bawa Izuddeen sakayyar da xai musu kenan. Miƙa mata ledar wayar da ya bawa Sa'adatu jiya tayi " kinga Babbar shaida ko, don kada ma ki zaci ko sharri aka yi musu, jin dadin abinda tayi masa ne yasa yake bata kyautuka daban-daban, amma kada kiga laifin danki domin janye hankalinsa tayi har ya biye mata kuma kin san dai yadda mace take da tasiri ga da namiji, duk girmansa duk iliminsa duk abinda yake ji da shi cikin ƙananan mintuna zata gama da tunaninsa, shawara ki jawo danki a jiki ki nema masa yarinya ta mutunci ,ko mu a nan gidan namu idan yana so akwai yan mata kyawawa masu tarbiyya sai yaxo ya nemi wata" tana gama fadin Abinda Ya kawota ta mike. Duk gwiwoyin mama sun yi sanyi ta kasa magana ji take kamar ƙasa baxa ta dauke ta ba, tunda suke neman aure basu taɓa cin karo da matsala irin wannan ba sai a kan Izuddeen, sun aurar da yaya sama da sha Biyar amma babu wadda aka taɓa zuwa har gida aka fadi aibunta sai ta Izuddeen. Sallama innah salamatu tayi mata, cike da farin ciki ta bar gidan, har mama ta kama hanyar shiga dakin Izuddeen ta fasa saboda maganganun da aka faɗa mata suna buƙatar nazari dakinta ta koma ta kwanta rigingine idanunta sun yi ja saboda ɓacin rai, ta fahimci a maganganun innah salamatu akwai karya amma kuma wani abin gaskiya ta faɗa, tunda ga shaidar waya ta nuna, sai dai abinda ya bata tsoro a maganarta da tace idan yana bukatar aure yaje ya nema a gidan su, ta fuskanci kamar wata manakisar ake shirin kullawa yarinyar, sai dai har Yanzu ta kasa amincewa ɗari bisa ɗari cewa ba lalata suke da Izuddeen ba duk da cewa ta san halin danta amma ba a shedar dan yau. Tunani ta rika yi a kan ta samu mahaifinsa ta faɗa masa ko kuma ta fara tunkarar Izuddeen da maganar saboda bata so ta bata masa suna a idon yan uwansa. ******* A Hanyar mu ta komawa gida muka ci karo da innah Salamatu bin mu tayi da wani matsiyacin kallo, sannu da zuwa muka yi mata amma ko yan kallo bamu isheta ba, a soro suka ci karo da Baba shi ma sannu da zuwa yayi mata tare da cewa "Har kin dawo da wuri haka kin mayar musu da wayar su dai ko" kallon kallo muka rika yi ni da Rukayya dama su suka ɗauki wayar? Cikin kissa tace "naje mun gama magana da su sun yarda da dukkan abinda na fada musu kuma sun ce xasu katange dansu" tana gama faɗa ta juyo kaina tana bi na da kallo mai cike da tsana. Da gudu na shiga gida na fada dakin innah ina kuka "innah tashi kiji ashe innah salamatu ce ta sace min wayar nan mayar gidan su Izuddeen, sannan ta fadi karya da gaskiya a kaina, na shiga uku innah me matar nan take nufi da ni" A gigice innah ta tashi sai a lokacin na lura da bacci take, innalillahi wa inna ilaihi raji'un naji tana maimaitawa "ALLAH kayi mana maganin abinda ya fi karfinmu" kuka mai cin rai nake yi ita ma Rukayya haka, innah sai faman rarrashi take yi tana janyo mana hadisai da ayoyi masu magana a kan hakuri da yarda da kaddara da kyar ta samu kanmu muka yi shiru. Kada a manta a yi sharing yan uwa su karanta *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:30 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *10* Tun lokacin da innah salamatu ta je gidan su Izuddeen Mama bata ƙara samun kwanciyar hankali ba kullum a cikin tunanin yadda zata bullowa al'amarin take yi, ga shi ta kasa fadawa kowa kuma ta kasa tunkarar Izuddeen da maganar, ita kaɗai ta bar abin a ranta yana yi mata yawo, saboda har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya a kan gaskiya ta faɗa mata ko akasin haka. Yau dai ta yanke shawarar faɗa masa ko zata ji sanyi a ranta, tashi tayi da kanta ta nufi dakinsa, sai dai tayi rashin Sa'a baya nan dakin nasa a kulle, dawowa cikin gida tayi sannan ta ɗauki waya ta kira shi cewa tana kiransa da gaggawa. Yayi nisa da gida amma haka ya daure ya juyo saboda yadda mama ta jaddada masa cewa tana son ganinsa da gaggawa. Gabansa ne ya riƙa faduwa Allah yasa dai alkhairi ne yasa ta kira shi don tunda suke bata taɓa yi masa irin wannan kiran ba. A daki ya sameta tayi tagumi tana tunani, har yayi sallama bata san ya shigo ba sai a karo na biyu da ya sake yi sannan ta san da shigowarsa, cike da mamaki ya karasa wajenta tare da xama a ƙaramar kujerar da ke gefenta, fuskarsa bayyane da damuwa"mama lafiya yau na ganki a irin wannan halin me yake damunki? tunda nake ban taɓa ganin damuwa a bayyane a fuskar ki ba irin yau, ga shi kuma naga kina min kiran gaggawa Allah yasa dai lafiya" Mayar da ajiyar zuciya tayi. "Zan iya cewa lafiya amma ba lafiya ba, amma muna fatan Allah ya tabbatar da lafiyar zuwa nan gaba, Allah ya kawo mafita ya nuna mana gaskiya a kan tunanin da muke yi" Cikin kulawa ya amsa da "Ameen amma ban fahimci maganganun ki ba Mama". Murmushi tayi "zaka fahimta ne ɗana ka bari xan faɗa maka komai" Shiru suka yi na wani dan lokaci sannan tace. "Abinda yasa na kiraka matsala ce dangane da kai kuma ina so ta xama sirri tsakanina da kai, don bana so kowa yaji abinda ke tsakanin mu, amma kuma ina rokonka ka fada min gaskiyar abinda ka sani kada ka munafunce ni" Jikin Izuddeen ne ya dau rawa "wani abin aka ce nayi mama" jinjina kai tayi "Baka yi komai ba amma dai ana zargin ka aikata, don haka ka kwantar da hankalinka ba wani abin damuwa bane" Gabansa ne yake ta dukan uku-uku jira kawai yake ya ji abinda zata fada, "ina saurarenki mama wlh na kosa naji laifin da nayi miki" "Dama daga gidansu yarinyar da kake nema ne......." gabansa ne ya yanke ya fadi dama tunda yaga matar nan da wayar da ya bawa Sa'adatu a hannunta ya san wani abin ne ya kawo ta addu'a yake yi a zuciyarsa Allah yasa dai ba cewa aka yi an raba shi da ita ba, da sauri yace "wani abin aka ce nayi mama?" Dakatar da shi tayi "A'a ka tsaya ka saurare ni mana" hankalin shi ya bata gaba ɗaya yana saurarenta. "Ta zo ta faɗa min cewa yarinyar da kake nema ba yarinyar kirki bace, bin maxa take sanadiyyar hakan ta xubar da ciki ba adadi, Sannan kaima kuma tana ƙoƙarin janye hankalinka kuna lalata da juna saboda daɗin abinda take maka ne yasa ka bata kyautar waya ka ganta nan ma a hannuna" Miƙa masa wayar tayi ya gani sannan ta mayar da ita gefenta sannan ta cigaba da magana. "wannan dalilin yasa taxo da kanta ta sanar mana gudun kada mu yi kitso da kwarkwata" kafin ta kammala fada idanun Izuddeen yayi jawur kamar zai yi kuka, yanzu Sa'adatun tasa nutsatstsiyar yarinya kamila za a jefa da wannan kalmar, yarinyar da bata san komai ba sama da ibada da xuwa makaranta, bai san lokacin da ya sawa mama kuka ba. "wlh Mama duk abubuwan nan da ake fada sharri aka yi min, kuma ita ma yarinyar sharri aka yi mata, Sa'adatun da take kamila za a jefa da wannan kalmar sannan nima a yi min sharri, wlh ban yafewa matar nan ba Allah ya bi min hakkina, don ta zubar min da mutuncina a idonki" cike da kulawa ta fara yi masa magana "Ni fa dama ban yarda da abinda take fada ba kawai dai na ji ta ne, sbd har cewa tayi kaje ka nemi ɗaya daga cikin ƴaƴanta kaga ya tabbata auren yarinyar ne bata so shi yasa taxo ta kulla wannan sharrin, dalilin da yasa na same ka kenan na fada maka yadda muka yi da ita, don mu warware bakin xaren kaga bai kamata na yanke hukunci a bisa rashin sani ba, nice mahaifiyar ka Izuddeen nafi kowa sanin halinka, gaba daya ban yarda da abinda ta fada min ba, ka kwantar da hankalinka xan fadawa babanka a je a bincika a tabbatar da gaskiyar abinda take fada" Izuddeen ya dade a xaune bai tashi ba yana kukan takaicin jifansa da aka yi da zina, shi da ko hannun mace bai taɓa tabawa ba shi xa a yiwa kazafin zina, ya ji xafin abinda matar nan tayi masa kuma ya dauri aniyar duk lokacin da ya gano ko wace ce ita, sai ya ɗauki matakin Shari'a a kanta. Bayan ya tashi daga dakin Mama gidan su Rukayya ya wuce, yaro ya aika ya kirata a tsakar gida ya sameta tana tankade, cike da nutsuwa yaron ya fada mata cewa ana sallama da ita,tayi mamakin jin ana sallama da ita saboda ta san mai sonta baya nan da yake ba a gari yake aiki ba, kuma indai zai zo sai ya sanar mata. Hijabinta ta saka tare da leka kanta dakin umma "umma ana kirana a kofar gida zan leka naji mai kirana" amsa min tayi da to Leka kainta tayi kafin ta fita, hango Izuddeen tayi jingine da machine dinsa, yana ganinta ya taho da sauri da ganinsa yaƙe yake don ga damuwa nan bayyane a fuskarsa. Cikin sakin fuska ta karɓe shi tare da cewa. "yau kuma an tuna da ni kenan xiyara aka kawo min" a gintse ya amsa mata da "eh ai girmanki ne ranki ya dade" shigo da shi soro tayi tare da cewa "bari na samo maka abin zama" bai musa mata ba ta shiga gida ta dakko masa farar kujera ajiye masa tayi sannan ta nemi gefe ta zauna tana fuskantar sa. yadda taga fuskarsa ba walwala ne yasa ta fahimci yana cikin damuwa. Sun ɗauki lokaci mai dan tsawo kafin kowa yace da dan uwansa wani abu, ita ce tayi ƙarfin halin yin magana. "Daga wajen kawar tawa kake ne ka biyo ka gaishe ni" ta ƙarasa maganar tana ɗan murmushi. Ajiyar zuciya yayi tare da cewa "Daga gida nake na shigo wajenki ne don ki ɗan ƙara min haske game da abinda yake damuna" cikin mamaki tace "to!!! Me kuma ya faru da kai mijin kawata?" Kafin ya faɗa mata abinda ya faru idanunsa sun yi ja kamar zai yi hawaye, sai da zuciyarsa ta ɗan yi sanyi sannan ya kwashe dukkan abinda ya gudana tsakaninsa da Mama ya faɗa mata. Tunda ta ji inda maganar ta dosa ta gano makircin innah salamatu ne, don sun ji lokacin da take fadawa Baba dawowar ta daga gidan su Izuddeen. Girgiza kai kawai Rukayya take yi ta rasa bakin magana sai can tace "bazan boye maka dukkan irin rayuwar da Sa'adatu take yi a gidan su ba, xan iya cewa rayuwa ce irin ta tatsuniyar yar mowa da yar bora, tsananin tsana da kiyayya kishiyar mahaifiyarta da yayanta suke mata wacce ba tada asali ballantana toshe, kuma ita ce taje gidanku ta kulla wannan sharrin, hatta abinda Baban Sa'adatu yayi maka ranar da kaje wajenta duk da sa hannunta, na san ka fahimci abubuwa da yawa a ɗan xuwan da kake yi, xaka san cewa Sa'adatu da mahaifiyarta rayuwar hakuri suke yi, kada kayi mamakin dukkan abinda zasu faɗa a kanta zasu iya fadin abinda ya fi haka ma, tunda babu soyayyarta a zuciyarsu da suna da hali da tuni sun koreta daga gidan ita da mahaifiyarta, fatana a gare ka shi ne ka bincika komai kafin ka yanke hukunci, na san ba kai tsaye kaxo kace kana son Sa'adatu ba sai da ka binciki dabiunta kafin kace kana sonta, ka kwantar da hankalin ka a kan abinda aka faɗa maka, kayi naxari sosai kafin ka yanke hukunci" numfashi mai zafi Izuddeen ya fitar daga bakinsa "nima ba cewa nayi na yarda ba kawai naxo na tambaye ki ne sbd abin ya daure min kai na san wannan duk ba halinta bane, kuma ba Sa'adatu kadai abin ya taɓa ba har da ni, tunda gashi nima tace min lalata nake yi da ita, sauki ɗaya na samu da iyayena suka kasance mutane masu nazari da tunani, da wasu ne da tuni ba wannan zancen ake yi ba, amma xan bincika iyayena ma xasu taya ni mu gano bakin xaren, bana so bikinmu ya dauki wani lokaci saboda mu yi maganin makiyan mu" Rukayya taji dadin maganganun Izuddeen musamman da yace ya yarda da kawarta, kuma za su yi aure nan ba da jimawa ba, sun ɗan yi hira kadan sannan ya tashi ya tafi. bata iya shiga gida ba gidan su Sa'adatu ta zarce, a soro na biyu ta tarar da taron mutane kanta ta tambaya ko me yake faruwa a gidan haka, danna kanta tayi cikin gidan tare da cire takalminta kasancewar baxa ta iya wucewa da takalmi ba saboda shimfidar da aka yi. Wata magana ta ji ana yi wacce ta daki kunneta kamar saukar aradu taji an fadi wani abu, da sauri ta juyo ta tsaya gefe don sauraren abinda suke tattaunawa, kamar daga sama taji an ce................ Yawan comment yawan typing kada a manta da sharing *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:31 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *11* Magana ta ji ana yi ƙasa-ƙasa har bata iya jin abinda suke fada saboda ta fuskanci kamar tattaunawar sirri suke yi shi yasa basa so wani ya fahimci abinda suke cewa, ƙara bada hankalinta gare su tayi don a yadda taji salon zancen kamar maganar Sa'adatu ake yi, don ta ji kusan duk kalmar da xa a fada sai an ambaci sunan Sa'adatu, kuma dama tunda ta ga wannan tarin jama'ar ta san an taru ne saboda ita. Ji tayi an kwalawa Sa'adatun kira, cikin mintunan da basu wuce biyu ba ta gabata a gaban taron jama'ar da suka haɗu sbd ita. A ladabce ta gaishe su, amma ga mamakin Rukayya bata ji sun amsa ba, wani dattijo taji ya fara magana "yanzu dan Allah wannan hanyar da kika dakko mai bullewa ce kuwa, kina ganin hanya ce da zata sadaki da tafarkin tsira, kina yarinya yar asali mutuniyar kirki yar mutanen kirki xaki bata rawarki da tsalle, xaki daka ta yaro ɗan masu kuɗi ki lalace iskancin naki har ya kai ki fara kawo shi gida yana abin kunya da ke, naga alama so kike kiyi cikin shege ko? to mu hakan baxai faru da zuri'ar mu ba, yanxu xamu yi maganin abin, amma kai kayi ganganci tun farko malam yarinya kamar wannan shekara sha tara baka aurar da ita ba ai dole haka ta afku, idan ma miji ta rasa me xai hana mu baxa kayi mana magana mu kawo mata ba, sai ka kyale yan iska su lalata maka ita" Neman yawu nayi na rasa a bakina kululin baƙin ciki ya toshe min makoshina, duk da cewa ana dan sanyi amma haka naji xufa na yanko min, yanzu a ce duk jama'ar nan saboda ni suka taru? Kannen kakana ne da suke xaune a wani kauye da ake kira Bankaura, ina kyautata zaton jiya Baba ya je ya sanar da su Wannan sharrin da ake kulla min, shi ne yau suka zo ku san su goma duk a kan maganata Ita ma Rukayya da ke soro irin halin da ta tsinci kanta kenan, jiri ta ji na shirin dibanta don haka ta nemi waje ta tsugunna. Wajen ne yayi shiru kowa na sauraren bayanin Baba musa, sai da ya gama magana tsaf Baba ya karbe shi. "Ni fa dama Baba na dade ina xargin Sa'adatu da wannan aikin saboda a lokuta da dama ina ganinta da abubuwan da ba ni na siya mata ba, kuma mahaifiyarta ma ba tada kudin siya mata, amma ko menene ita uwar ke bata goyon baya salamatu na iya kokari wajen kula da tarbiyyar ta sai take ganin kamar takura mata take yi, ina rokonku dan Allah ku tafi da ita Bankauran ta xauna a can ko zata ƙara hankali, sannan kafin nan da sati biyu xan turo mijin da na bayar da ita sadaka a daura musu aure kowa ya huta" Hawaye masu xafi suka riƙa sauka a kan kuncina, wace irin rayuwa ake so nayi a kauye? Tunda nake ban taɓa sati guda a can ba sannan yanxu dare daya a ce can xan koma da rayuwa, wane hali innah xata shiga idan na tafi na barta, kawai niyyar kashe ni ake yi da raina. Da farin ciki ɗaya kanin kakan nawa ya amsa "kwarai kuwa kayi tunani malam Salisu can din ne gatanta kuma shi ne ya fi dacewa da ita, dama an ce duk wanda ya bar gida gida ya barshi, taje can ta shiga cikin yan uwanta tayi aiki, a haka ma xata koyi wasu sana'o'in tunda duk yan uwanta noma suke yi ita ma ya kamata ta shiga ciki tayi tarayya da su" Gaba daya suka amince da komawata Bankaura, cikin fushi Baba yace na tashi na hado kayana, da gudu na shiga daki ina kuka, tambayata innah take yi dalilin kukana amma na kasa bata amsa saboda takaicin shekara da shekaru da ya cika xuciyata, ita ma ganin halin da nake ciki ne ya sanya ta kuka, innah salamatu ce ta dage mana labule tare da cewa "tafiya dole a yi ta, baxa mu xauna da yar iska a cikin gidan mu ba" Sai a lokacin innah ta gano dalilin kukana tambayata ta shiga yi "Sa'adatu kokar ki malam yayi daga gidan nan ko kuma me"??? Hawayen da ya cika idona na share "cewa yayi sai na bi su Baba musa Bankaura wai baxan xauna masa a gida na lalace ba" Kwalla ce ta cika idon innah "Allah sarki rayuwa Allah kaine Allah, ka saka mana wannan cutar da ake mana" kafin innah ta rufe baki har Baba ya shigo dakin cike da fushi yake mata magana. "Munafuka wato kin sakata a gaba kina kitsa mata sharri ko, na lura da ke duk dokar da xan yi a cikin gidan nan sai kin rusata, ke dama kike goya mata baya har ta lalacewa, idan har kika bari ta dakko min abin kunya wlh kin gama xaman gidan nan, kuma xuwan Sa'adatu Bankaura ya xama dole saboda 'yata ce ba 'yarki ba ina da iko da ita, ki taka a hankali kafin na ci miki xarafi" Mayar da kallonsa yayi gare ni "ke tashi ki dakko kayanki kafin nayi ƙasa-kasa da ke" A sanyaye na tashi na nufi inda jakar kayana take, a hankali nake xakulo su kamar wacce kwai ya fashewa a ciki. Sake daka min tsawa yayi "za kiyi aiki da jikinki ko sai naxo nan" kayana kala uku na dauka na xuba a leda, tankada ni waje yayi tare da cewa "shege mu je ja'ira" har na bar daki innah na sunkuye tana kuka, nima kukan nake har na fita ina waiwayenta. A soro na biyu na tarar da su sun yi cirko-cirko suna jirana, idona a rufe na fita xuwa soron farko ji nayi an riko hannuna a hankali na bude idona, Rukayya na gani ta sha kuka har ta gaji, cikin kukan take min magana "wlh kada ki bi su Sa'adatu ki gudu, babu alheri a ransu neman ruguza miki rayuwa suke yi" Daga soron Baba ya jiyota, ita ma cin mutunci yayi mata ba shiri ta tafi gida tana ta rusa uban kuka. A dai-daita sahu aka kawo mana don xuwa tasha, ni na fara hawa sannan sauran kakannin nawa suka bi bayana, babu wanda ya rarrashe ni ballantana na sa ran za a bani hakuri ko za a ji tausayina zuwa gaba. Har muka isa tasha abinda nake yi kenan, sauke kayana nayi na samu gefe na tsaya, su kuwa sun kafa min ido kamar masu gadina, fakar idonsu nayi na ajiye kayan a kan wata mota, ina lura da basa kallona na gudu na bar musu kayan a wajen, gudu nake cin karfina ban san ina na nufa ba ni kaina. A yi hakuri da kadan ba ni da lafiya ina bukatar adduarku .kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:31 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *12* Gudu nake cin karfina kamar zan tashi sama burina kawai na bace daga inda suke, Mutane sai bi na da kallon mamaki suke sbd ganin budurwa kamata na gudu abin mamakin ne, har sai da naga nayi nisa da su sosai sannan na samu nutsuwa, tsayawa nayi don na huta, a bakin wata bishiya na zauna ina ta maida numfashi, sai da na dawo na huta sosai sannan na ci-gaba da tafiya, nayi tunanin na gudu gidan wata kakata kanwar Baba tunda tana sona sosai na san xata rufa min asiri, amma sai fasa sbd idan suka bincika zasu iya gano ni a can, yanke shawarar tafiya gidan kanwar innah nayi Adda saratu, ban bata lokaci ba na kama hanyar tafiya gidanta. *********** A ɓangaren kannen kakan Sa'adatu kuwa basu ankara bata nan ba sai da aka zo shiga mota, ɗaya daga cikin su ne ya lura da bacewar ta, a firgice ya dubi ragowar yan uwan tafiyar tasa "yarinyar nan fa bata nan kamar gudu tayi" Da sauri suka baxu a cikin tashar kowa yana duba inda Sa'adatu ta shiga, ga mamakinsu sam basu ganta ba hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, a tunaninsu ko gida ta koma abinka da mutanen karkara duk cikinsu babu mai waya ballantana su kira gidansu su ji ko nan ta dawo, haka suka hakura suka ƙara koma gidan su Sa'adatu ko xasu sameta. A Kofar gida suka ci karo da mahaifinta kallon mamaki ya bi su da shi gami da mikewa tsaye yana tambayarsu "Baba lafiya naga kun dawo?" Girgiza kai dattijon yayi "Hmmm Salisu yarinyar nan sai ta Allah kawai, don duk inda kake neman shu'uma ta kai, sai da ta san yadda tayi ta gudu sannan hankalinta ya kwanta, a gaskiya kayi sakaci da tarbiyyar yarka, tunda ta saba da yawo zai yi wuya ko aure tayi ta zauna" Dafe kai mahaifin Sa'adatu yayi wani gumin tashin hankali ne ya riƙa yanko masa, cikin sarkewar harshe yake magana "ko ma menene uwarta ce ta fara jawowa ita ce ta dorata a tafarkin da take yanxu, sannan wannan kawar tata ita ma ta taimaka wajen lalacewar ta shi ma saurayin haka" jajanta masa suka riƙa yi ko gidan basu sake shiga ba suka kama hanyar ƙauyen su. A fusace ya shiga gida tun daga soro yake kwalawa innar Sa'adatu kira mutanen gidan na jin irin kiran da yake yi mata suka fito saboda sun san ci mata mutunci zai yi, cikin kakkausar murya ya fara magana "Burinki na son lalacewar Sa'adatu ya cika kin hure mata kunne ta bi saurayi yawon iskanci, dokar da na saka kin karyata, duk shirina a kan yarinyar nan kin xuga min, tunda haka kika zaba mu zuba, a cikin minti biyu nake so ki tattara kayanki ki bar min gidana idan kinga kin xauna a gidan nan sai dai idan tare da Sa'a ku ka dawo" jikin innah a sanyaye ta miƙe ta shiga haɗa kayanta ita abin yayi mata dad'i dama ta gaji da wannan zaman kaskancin da take yi, kullum cikin xagi da cin zarafi, yanzu fargabarta ɗaya bata san inda yarta take ba, ta san Sa'adatu da kamun kai baxa tayi wani abu da zai xubar mata da mutuncinta ba amma duk da haka tana jin ba daɗi a ranta saboda sharrin xamani. Mutanen gidan sai murna suke suna ta habaici Sa'adatu ta tafi yawon iskanci. Innah salamatu ke cewa "Yadda kika fita kin fita kenan ba dawowa mun ci gida ni da yayana" ko kallonta innah bata yi ba ta fice ta kyale su. A soro taci karo da salim, har ƙasa ya tsugunna ya gaidata cikin farin ciki ta amsa, tambayarta ya hau yi "ina zuwa innah na ganki da kaya haka" labarin abinda ya faru da Sa'adatu ta bashi, ransa yayi matuƙar ɓaci, hakuri ya riƙa bawa innah kada ta saka damuwar hakan a ranta wata rana komai xai wuce, ɗari biyu ya bata yace ta hau mota. A fusace ya shiga cikin gidan, innah salamatu na ganinsa ta hau magana "yauwa Gara da Allah ya kawo ka, ana yi maka gata ana raba ka da yar iskar yarinyar nan kana nacewa to gashi nan dai yanzu ta gudu" Ba ƙaramin zafin maganar innah salamatu yaji ba, salim yaro ne mai tarbiyya baya yiwa manya rashin kunya amma yau tunda ta tsokano shi sai ya mayar mata da martani cikin fushi yake mata magana "ina ruwan ki dani indai kin san irin wannan maganar xaki rika fada kada ki sake yi min magana Sa'adatu yar uwata ce ta fi ki kusa da ni, duk rintsi duk wuya dole a ce kanwata ce, don haka sai na damu da dukkan halin da take ciki, duk ba ku kuka tunxarata ta aikata abinda ta aikata yanzu ba, kun hanata abinci kun hanata walwala kun hanata wanda take so, kun jefeta da zina wanda ina da yakinin duk tafi yayanku tarbiyya, sannan sbd zalunci yanxu kun dauke ta kun ce sai kun mayar da ita kauye, ya ku ke so tayi da rayuwarta, shi kenan so kuke yi ta zauna ku kasheta da baƙin ciki" Dakinsa ya wuce ya kyaleta ta saki baki tana mamakin maganganun salim, tanbayar kanta take yaushe yaron nan yayi baki haka?? Lallai idan ba su yi taka tsantsan ba wata rana zai kwance musu aiki. Dakinsa ya shiga yana xuwa ya faɗa kan ƙaramar katifarsa, kwanciyar rigingine yayi yana tunanin rayuwar Sa'adatu, yayi alkawarin indai yana doran ƙasa baxai bari ta tagayyara ba. Shi kuwa baban Sa'adatu tun bayan fitar innah daga gidan shima ya fita, bai xarce ko ina ba sai gidan su Izuddeen, a Kofar gida ya same shi tare da abokansa suna hira bai lura da xuwansa ba sai kawai ji yayi an shako shi ta baya, cike da mamaki ya juya don ganin wanda ya riƙe shi haka. Baban Sa'adatu ya gani yana yi masa kallo mai cike da tsana, a ladabce yace "lafiya Baba??" Wani kallo yayi masa tare da cewa "lafiyar kenan, ina ka boye min yata, ka fito min da Sa'adatu ?" A razane yace "ban gane Abinda kake nufi ba" "Zaka san baka gane abinda nake nufi ba idan ka ji ka a hannun hukuma" abokan Izuddeen ne suka fara tambayar baban Sa'adatu "malam mai ya faru haka kaxo ka shake shi, a matsayinka na babban mutum ai bai kamata ka kama shi da kokawa ba, tunda a haife ka haife shi" cika shi yayi yana haki "wannan yaron da ku ke gani azzalumi ne ya lalata min 'ya sannan yanzu ya hure mata kunne ta gudu watakila ma shi ne ya boye ta" kallon kallo suka hau yi kowa yana mamakin abinda yake faɗa, kasa magana suka yi sbd maganar ta daure musu kai, mayar da kallonsu ga Izuddeen suka yi. "Gaskiya ne abinda ya faɗa?" Shi kuma saboda takaici ya kasa magana sai dai ja da idanunsa suka yi, sai da ya gama tijara sannan ya tafi ya kyale su, binsa suka yi da kallo har ya kule. Komawa suka yi suka zauna suna tambayar Izuddeen "menene alaƙarka da wannan mutumin ɗan tijara , gashi ya xo har kofar gida xai zubar maka da mutunci" Labarin soyayyarsu da Sa'adatu ya hau basu dukkansu sun fahimci halin mahaifin nata, kuma sun gano cewa ba kaunar yar tasa yake yi ba, gaba daya suka shiga gida suka shaidawa Mama yadda suka yi da malam Salisu, ba ƙaramin takaici taji ba saboda abinda yayi masa, a wannan lokacin ta tashi ta shiga wajen mahaifin Izuddeen ta shaida masa abinda ke faruwa, tunda dama ya san Izuddeen na san yar aurensu da yarinyar, shi ma ransa ya ɓaci sosai, sa wa yayi aka kira shi ya tambaye shi yadda suka yi. Cike da tausasawa da kamala yake magana. "Faɗa min gaskiyar abinda ya haɗa ka da wannan mutumin, bana so ka rage min komai kuma bana so kayi min karya" kan Izuddeen a sunkuye ya fara magana. "Wlh Baba tun bayan korar da yayi min daga gidan sa ban sake komawa ba, kuma bana waya da yarsa hasali ma na cireta daga rayuwata, yanzu kuma kawai ina zaune sai yaxo ya shake ni wai na fito masa da yarsa da na boye, kuma ko abokaina za a tambaya babu macen da take shigo min dakina ku ma nasan zaku yi min wannan shaidar" Shiru mahaifinsa yayi yana nazarin maganganunsa, "tashi kaje xan sake neman ka" Cike da ladabi ya tashi fitarsa kofar gida kenan yaga Baban Sa'adatu tare da yan sanda, yana ganinsu ya tsaya don ya san bakinsa ne, suna karasowa ya nuna shi, tafiya suka yi da shi sauran abokansa ne suka je gida suka faɗa an tafi da Izuddeen, ana tafiya da shi suka bi bayansa su da ragowar yayan gidansu. Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:31 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *13* Bayan an kai Izuddeen police station tafiya Baban Sa'adatu yayi ya kyale shi, tare da alkawarin kada a sake shi har sai ya fito masa da yarsa, ko da yan uwan su Izuddeen suka je duk iya bakin ƙoƙarin da suka yi don ganin an bada belinsa hakan ya gagara sbd dole sai babanta yana nan xa a kashe case din, haka suka taho suka kyale shi ba da don ransu ya so ba. Tunda ya bar police station bai xame ko ina ba sai gidansu Rukayya a kulle ya tarar da kofar gidan, wani irin bugun rashin mutunci ya riƙa yi, ummansu ce ta fito da kanta ta bude don ganin mai bugun, bata yi mamakin ganinsa a wannan yanayin ba, don ta san ko wanene malam Salisu kuma ta san kalar tijararsa baya ragawa kowa wannan dalilin yasa da yawan makota basa shiga harkarsa duk abinda zai yi sai dai su zuba masa ido. Fuskarta a daure take tambayarsa "lafiya dai ko malam?" Shi ma a yatsine ya amsa mata "ina 'yata da ku ka boye min?" cikin rashin fahimtar abinda yake nufi ta sake tambayarsa "Ban gane abinda kake nufi ba yi min dalla dalla yadda zan fahimta" gyara tsayuwa yayi "ina yarki Rukayya ita ce ta xuga min yata ta gudu ta bar gida ki fada mata wlh ta fadi inda Sa'adatu take ko kuma hukuma ta raba mu" wani kallo umma ta jefa masa wanda sai da ya shiga hankalinsa "Rukayya ba tada hannu wajen batan Sa'adatu mugun halinka da masifarka ita ta tunxurata ta gudu, kaje ka fara tuhumar kanka da matarka kafin ka tuhumi wasu, duk halin da yarka ta samu kanta a ciki kai ka fara jefata don haka kanka zaka zarga ba wasu ba" tana gama faɗar haka ta mayar da kofarta ta kulle ta bar shi tsaye yana naxari. Gida ya koma yana ta masifa innah salamatu ce ta tarbe shi tana tambayarsa ko lafiya, faɗa mata yadda suka yi da Izuddeen da kuma mahaifiyar Rukayya yayi, zuga shi ta hau yi a kan kada ya yarda ya dauki mataki ta kuma bashi shawarar tafiya wajen Malam Jibo a kan yaxo a daura aure ko bata nan, in yaso idan ta dawo sai a kaita. Yaji dadin wannan zugar da tayi masa, a nan take ya tashi ya nufi wajensa. Tun a hanya yake ta tunanin Sa'adatu ya san dukkan halin da ya jefata a ciki shi ne sila amma ko kadan baya nadamar hakan sbd an riga an dasa masa tsanar yarinyar a xuciyarsa, kai tsaye makarantar sa ya wuce sai kuma bai same shi a can ba, don haka kai tsaye ya wuce gidansa, a soro ya same yana lazimi bari yayi ya ƙarasa sannan suka gaisa. Cikin karamci ya karɓe shi tare da shigar da shi shagon da ke soro sbd yadda ya ganshi ya san tattaunawar sirri ce ta kawo shi. Zaunawa suka yi suna fuskantar juna kafin Baban Sa'adatu yayi magana Malam Jibo yace "ina muka kwana a maganar mu?" Cikin nuna tsananin damuwa yace "wlh Malam ina shirye-shiryen zuwa na sameka a kan maganar kwatsam shekaran jiya ta gudu" dafe kirji yayi "Ta gudu fa kace subhanallahi ya aka yi haka ta faru" jinjina kai yayi "Hudubar saurayi ce ta hure mata kunne shi ya yaudareta ya tunxurata ta gudu" Shiru malam Jibo yayi yana tunani "To ai malam kai kayi sanya wajen tabbatuwar Maganar nan tun lokacin da ka same ni da maganar ya kamata a ce kayi wani abu amma kayi banxa da abin idan nayi maka magana sai kace zaka neme ni" Mayar da ajiyar zuciya yayi "akasi aka samu malam kamar dauke min hankalina aka yi a kan maganar, ka gyara inda zaka ajiyeta na baka ita sadaka kada kayi lefe kada kayi komai sadaki ma na yafe maka xan bata dan wani abin idan ka shirya kayi min magana, gobe ko jibi nake so a daura aure" yana gama maganar ya tashi. wani dadi ne ya sauka a zuciyar malam Jibo Allah ya bashi kifi daga sama gasashshe, yarinya kamar Sa'adatu ai abin alfaharinsa ne a ce ya aureta, godiya yayi masa har kofar gida ya rako shi suna ta tattauna maganar. Har ya juya xai tafi ya sake juyowa "Au malam na manta ban fada maka ba" mayar da kallonsa yayi gare shi tare da cewa "ina jinka" "Kada ka manta Sa'adatu ta ba yarinyar kirki bace ta riga ta saba da yawo banxa kana ganin xata iya xaman aure da kai?" Wani murmushi malam Jibo yayi "Ba matsala don ka samu mafita aka yi auren nan ko?? To Sa'adatu ta shigo hannun da babu rabuwa har abada sai dai mutuwa, ko nan da can bata isa ta je ba sai dai idan ni na bata izni xata xauna tayi ibada kamar yadda kowacce mace take yi ka kwantar da hankalin ka" Ba ƙaramin dadin maganar yaji ba yana farin ciki ya nufi gida don sanarwa innah salamatu. Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:31 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki yayata SUMAYYA MUKHTAR RABO (mrs Al-ameen) ina godiya da karfafa min gwiwa Allah ya bar zumunci* *14* Yau kusan satina ɗaya a gidan Adda saratu rayuwa nake mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali babu wani abu da ke damun xuciyata, sbd Adda saratu mace ce mai kirki babu wani abu mara daɗi da take min ta ɗauke ni tamkar yar da ta haifa a cikinta, sai dai abu ɗaya da ke damuna shi ne yawan tunanin innata da nake yi a halin yanzu, sbd ban san halin da take ciki ba, tunda Adda saratu da kanta taje gidan namu don shaida mata cewa ina wajenta, sai aka ce mata an koreta daga gidan, ga rashin masoyina da aminiyata wanda ban san halin da suka kasance ba bayan tafiyata, ban san lokacin da zan daina kewarsu ba. Tsaye nake a kitchen ina mayar da kwanukan da na wanke, Adda saratu ce ta shigo "Sa'adatu anya kina so mu yi tafiyar nan kuwa, ki kalli agogo har ƙarfe ɗaya saura tayi" da sauri na duba agogon da ke nanne a kitchen din "ayya ban kula lokaci ya tafi haka ba bari nayi sauri na ƙarasa abinda nake tunda nayi wanka baxa mu bata lokaci ba" sauri nayi kammala abinda nake yi, har ga xuciyata bana son tafiyar nan saboda kada wani daga cikin ahalin gidanmu ya ganni ya fadawa Babana inda nake, amma tunda ta nuna min muhimmancin tafiyar sai na yarda , saboda xamu je ne mu duba inda inna take da kuma yanayin da take ciki, na san duk inda take hankalin ta na kaina. Khadija da zainab muka bari a gidan kasancewar su yara masu nutsuwa, har mu dawo baxa a samu wata matsala ba. Kai tsaye gidan kanwar mahaifiyar su innah muka nufa gwaggo Balaraba amma da gwaggo suke kiranta, saboda mun san shi kaɗai ne gidan da xata iya zuwa ta xauna, kasancewar ita kadai ta rage musu duk iyayensu sun ƙare, kuma duk wata matsala ita ce take kashe musu ita. Da ƙarfin gwiwa nake tafiya na san yau xan ga innata farin cikin rayuwata, da sauri muka faɗa cikin gidan, gidan bangare-bangare ne, kusan duk ƴaƴanta idan sun tashi aure a gidan suke zama kaɗan ne suke fita waje su yi gini. bangaren gwaggo Balaraba muka nufa sai dai kash!!! Kofarta a kulle, don haka muka shiga wajen danta Abbas, tun daga nesa matarsa ta ganmu ta tarbe mu da farin cikinta, daki ta kaimu ta bamu lemo da abinci lemon kadai muka sha saboda mun ci abinci a gida, sai da muka ɗan taɓa hira take faɗa mana cewa gwaggo sun tafi kauye tare da innata, tambayarta Adda saratu tayi dalilin tafiyar tasu, a nan ta shaida mata cewa sun tafi ne a kan abinda yake faruwa da ni, kasancewar kusan kullum sai Babana ya zo yayi xage-xage a kan innah ta fito masa da ni ko kuma ya kaita ƙara, hakan yasa su tafiya don shaidawa magabatanta. Tunani da tausayin innah ne ya kamani duk wannan abin ana yi mata ne saboda ni, don haka ya dace na nemo hanyar da zata rabu da wannan baƙin cikin na har abada, sbd tunda innah take a gidanmu lokaci kaɗan take farin ciki ragowar duk bakin ciki take yi, jikinmu babu ƙarfi muka koma gida. Tunda na koma na shiga daki ina tunani da kuka, wane irin uba Allah ya bani da yake yi min wulakanci yake ƙoƙarin wulakanta mahaifiyata, yana iƙrarin yana sona amma ko kadan babu kaunata a xuciyarsa, tunda ga shi yana neman jefa rayuwata a halaka, gaba daya sha'awar zaman gidanmu ta fita a raina gara naje ko'ina nayi rayuwa a kan na xauna a gidanmu, amma kuma ina tunanin irin cin mutuncin da Babana xai yiwa innata a duk lokacin da ya duba yaga bana tare da shi, ko ina so ko bana so dole na koma indai ina son na samarwa mahaifiyata farin ciki. Ban san lokacin da hawaye suka riƙa gangarowa daga idanuna ba, ina a wannan halin Adda saratu taxo ta same ni, cikin kulawa take min magana tare da bani hakuri a kan irin jarrabawar da nake fuskanta, ta kuma yi min alkawarin duk rintsi duk wuya baxa ta bari na koma gidanmu ba sai dai duk abinda xai faru ya faru. ************* Baban Izuddeen ne a zaune gaban yan sanda suna tattaunawa dangane da abinda ake xargin Izuddeen din da shi, saboda yau har yayi sati daya babu wata kwakkwarar magana a kan xa a sake shi ko za a bada belinshi, shi yasa yau ya taso da kansa yaxo don jin inda aka kwana. Yana zaune Baban Sa'adatu yaxo, da izza da rashin mutunci ya shigo wajen bayan sun gaisa da yan sanda ya mayar da kallonsa ga mahaifin Izuddeen, wani kwarjini da kimarsa ne suka kama shi bai san lokacin da ya zube kasa yana gaishe shi ba, su kansu yan sandan sai da suka yi mamakin hakan, mutumin da ya dau xafi a kan abinda ya faru amma yau shi ne da xubewa kasa yana gaishe da mahaifin wanda ake zargi. Ba tare da bata lokaci ba aka fara magana daga ƙarshe aka cimma matsaya a kan xa a bada belin Izuddeen amma da sharadin nan da sati biyu idan ba a ga Sa'adatu ba za a sake cafke shi, fito da shi aka yi suka tafi gida tare da mahaifinsa. Yan uwa da abokan Izuddeen ne suka taru don tabarsa kowa na tofa albarkacin bakinsa wasu su ce ya rabu da Sa'adatu tunda ba yar gwal bace, wasu su ce ya cigaba da sonta tunda ita ma tana kaunarsa, sai da ya shiga wanka ya fito sannan ya ci abinci ya shiga wajen iyayensa don ganawa da su. A cike gidan su Sa'adatu yake da mutanen kauyen bankaura da kuma mutanen jarumawa, duk sun taho ne don jaje da kuma daura auren Sa'adatu wanda mahaifinta ya shaida musu za a daura shi da misalin karfe hudu na rana. Baka jin komai sai tofin ala tsine da yiwa Sa'adatu habaici, wasu su ce bakin mahaifinta ne ya kamata wasu kuma su ce yawon bariki ta tafi. Wasu daga cikin matan gidansu ne da waɗanda suka zo daga ƙauye, suka tafi gano dakin amarya don kai mata katifa da kuma shimfida mata leda. Gida ne karami mai ɗauke da dakuna guda hudu falle d'ai-d'ai ragowar dakuna uku na sauran matansa ne, sai kuma daki daya wanda ya barwa Sa'adatu, kyan gidan zaman mace daya a hakan ma zata takura musamman idan tana da ya'ya, amma mata uku ne da kusan yaya ashirin da biyar suke rayuwa a cikin gidan kowane yaro a dakin mahaifiyarsa yake kwana, shi hoton naka ma ba shi da daki sai rabe-rabe da yake a dakin matansa, duk matar da take da kwana sai dai yaranta su kwana a shago shi kuma ya kwana a dakin, gaba ɗaya gidan yayi musu kaɗan rayuwar takura kawai suke yi, shi yasa gidan ba tsafta duk a jike ga tarin tsummokaran yara. Sallama suka yi tare da tambayar matan gidan dakin amarya a yatsine suka amsa tare da mika musu mukullin dakin, daga gefe dakin Sa'adatu yake, sai kuma kitchen na langa-langa da yayi mata, shi kaɗai ne dakin da aka yiwa farar kasa sai faman jirwaye take alamar dakin ya dade bai ga fenti ba, kyauran dakin da tagar duk na katako ne, sai ka xura kafarka sosai sannan xaka iya shiga dakin idan baka yi da gaske ba xaka iya fasa baki, duk flastar da ke dakin ta cinye haka dai aka samu aka yi farar kasar ba tsiya ba arziki, ceiling din dakin ma na kwali ne banda uban duhu babu komai, kasancewar dakin tsohon daki ne ya dade a gine kuma daga lungu yake. A gaggauce suka shimfida ledar tare da jingine tsohuwar katifar da aka siya mata a gidan wata dillaliya, fitowa suka yi ko arxikin labule dakin bai samu ba. Sai rike baki suke suna mamakin irin wannan gida, duk macewar gidansu ya fi wannan kyau. Tunda suka dawo suke dariya an yi wa Sa'adatu auren mugunta, sai maganganu marasa dad'i suke fada. A fusace salim ya fito daga daki yana masifa, wajen yan uwan mahaifin nasu ya nufa "indai kuna ganin mugunta ku ka yiwa Sa'adatu insha Allah kanku xai koma, kuma ko ni kadai na ishi auren nan indai ina doron kasa Sa'adatu baxa ta auri almajiri ba" yana cikin wannan maganar malam Salisu ya fito daga dakinsa, dukansa ya fara yi kamar ya samu karamin yaro, hakan yasa salim ya bar cikin gidan tare da alƙawarin baxai sake dawowa ba indai wannan xaluncin za a cigaba da yi. Ƙarfe hudu dai-dai aka taru don daura auren Sa'adatu da malam Jibo ango ya sha tsohuwar farar shaddarsa wacce ta ji jiki kamar an kwatota daga bakin kura, sanye yake da jar Dara takalmin kafarsa baƙi ya saka, duk inda ya bi sai zundensa ake yi wai tsabar son xuciya shi xai auri Sa'adatu, mutane da yawa sun san auren cuta za a yi mata kuma laifin mahaifinta suke gani, a kan tabarmar da aka baxa a kofar gidan su ya xauna yana jiran fitowar sauran waliyyan Sa'adatu, don bashi aurenta. *Kada a manta da comment da sharing* *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:32 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *15* Su innah basu dawo daga ƙauyen da suka je a ranar ba, sai da suka yi kusan kwanaki uku a can, suna tattauna a kan yadda za a bullowa al'amarin Baban Sa'adatu, wasu daga cikin iyayenta har sun yanke shawarar a kashe auren tunda babu kwanciyar hankali a ciki ga zaluntarta da ake yi, wani kakan innar ne ya hana a kashe auren sbd shi mutum ne mai saukin kai da hangen nesa, yana duba yadda Sa'adatu zata kasance a bayan babu mahaifiyar ta a gidan, saboda a duk lokacin da suka kashe auren, tamkar sun kashe rayuwar Sa'adatun ne, a dalilin hakan xata iya fadawa cikin kunci da wahala saboda mahaifinta baxai taɓa bari ta zauna a hannun wani ba idan ba gidan shi ba, don haka dole a yi hakuri a zauna a haka don duba maslahar rayuwar yarinyar. ************ Zaune Malam Jibo yake ya zuba uban tagumi yana jiran dawowar Baban Sa'adatu, don tunda yace masa xai je ya dawo har yanzu shiru babu labarinsa, sai duba hanya yake ko zai ganshi ya bullo, yayi zama ya fi na awa biyu da rabi babu labarin malam Salisu, kuma babu labarin waliyyanta, hakan yasa ya fusata ya tashi ya bar kofar gidan yana tafe yana masifa kawai don yaga ba shi da kudi ne kuma bai bashi komai ba shi yasa yayi masa wannan wulakancin amma zai ganar da shi kuskurensa, bude shagon gidansa yayi ya shiga ya zauna yana cigaba da ban-bamin faɗa. Ko da Baban Sa'adatu yaxo bai ganshi ba hankalinsa ne ya tashi, ya san halin malam Jibo da fushi da zuciya watakila haushi yaji yayi tafiyarsa, a sanyaye ya zauna a kan tabarmar da ya shimfida yana jiran dawowarsa, har wajen sallar magariba bai dawo ba, wannan dalilin ya sanya shi nade tabarmar tare da xuwa gidan malam Jibo da kansa, a Kofar gida ya tsaya yana kwala masa kira, yana jinsa yayi banza da shi, yaro ya sake aikawa a fada masa cewa yazo yana kiransa, ko da yaron ya fada masa sai yace a koma a ce masa baxai samu fitowa ba, duk yadda ya so ya haɗu da shi yayi masa bayanin abinda ya tsare shi hakan ya garara don haka shi ma yayi fushi ya tafi gida. A fusace ya shiga gida yana masifa "shi wannan mutumin ya san bai shirya auren yarinyar nan ba yasa nayi asarar kudin katifata da ledata, haka na tatike aljihuna ban bar ko sisi ba, gaskiya malam Jibo ba mutum bane na bashi yar tawa kyauta ya wulakanta ni, nima kuwa sai na wukakanta shi duk da abinda yake takama sai nayi maganinsa" Da rawar jiki innah salamatu ta karaso wajen sa "me kuma ya faru malam naga kana fada haka kai kaɗai" dafe kanshi yayi tare da hadiye wani ɓacin rai da ya tare masa a makogoro "wane ne kuwa banda malam Jibo mun kulla magana za a daura aure ƙarfe hudu ga shi har magariba tayi Babu shi babu dalilinsa naje gida na kira shi yaƙi fitowa ya san bai shirya auren ba yasa na fadawa yan uwana" Jinjina kai innah salamatu tayi "Gaskiya malam kaine da laifi tun kafin lokacin malam jibo yazo kaine ka Kad'a kai kayi tafiyarka, neman duniyar nam an yi maka ba a samu inda kake ba" ajiyar zuciya yayi "to ai ba wani waje naje ba, naje ne na ƙarasa karbo gudunmawar da abokaina xasu bani sbd naga alama idan ban je da kaina ba, babu mai bani taimakon kwandala, don naga alama yarinyar nan ba tada goshi, ko sisi ban samu ba sai asara da nayi, gashi auren ma yana neman lalacewa" Tabe baki innah salamatu tayi "aure yana nan daram babu inda xa shi don baxa mu yi jeran mu a banxa ba, kaje ka samu malam Jibo ku sasanta a sake saka ranar daura auren, tunda yau dai ta wuce Allah bai yarda an daura ba, ta sai a sake lale, ni a ganina ma fa uwar yarinyar nan ita ke bata abin sbd ba so take ba shi yasa ta tsaya tsayin daka take bin abin ta ƙarƙashin kasa don haka ku dage sai an yi ko bata so, idan bata auri jibon ba uban wa xata aura? yarinya irin wannan mummuna kamar a yanka a boye wukar ga uwa uba bakin hali, jibon ne maganinta shi xai saita ta" Guri ya samu ya xauna ya haɗa kai da gwiwa duk wani shirinsa an rushe masa, amma xai yi kokari ya gyara komai, kafin sati mai kamawa. A ɓangaren malam jibo shi ma a damuwar yake bai ji daɗin abinda malam Salisu yayi masa ba, yau ya shirya tsaf don tarbar amaryarsa amma ya watsa masa ƙasa a ido, babban abinda ya fi damunsa habaicin da matansa ke yi masa a kan rashin daura auren, har dai yayi xuciya ya hakura da Sa'adatun gaba ɗaya, amma dole ya daure yaje ya bawa mahaifinta hakuri a kan a dawo a daura auren ko don ya huta da gori. Bayan dawowar su innah bai fi da kwana biyu ba aka aiko daga gidan gwaggo Balaraba ana nemana, jikina har rawa yake sbd shaukin son ganin innata, tare da yaron da aka aiko muka tafi, tun daga soro nake jin tashin muryar Babana da alama wata tijarar ya ƙara xuwa yayi musu, da sand'a na shiga cikin dakin a hankali cikin siririyar muryata da ta dashe sbd fargabar da ta cikata nayi sallama, gaba ɗaya kallo ya dawo kaina. Su ma a sanyaye suka amsa min ina ganin innata bata dago ta kalleni ba, wanda na kasa fahimtar dalilin hakan, gefenta na samu na zauna duk na takure kamar mai jin sanyi, bi nayi na gaida kowa har da Baba Amma bai amsa min ba. Dakin ne yayi shiru ana jiran a ji wanda zai fara magana amma babu wanda yace wani abu har sai da aka ɗauki wasu mintuna masu tsayi, gwaggo Balaraba ce ta fara bashi hakuri a kan abinda nayi masa tare da rokon ya mayar da innata dakinta kuma ya janye dukkan takurar da yayi mana. Na lura da fuskarsa yaji dadin kiran sulhun da aka yi masa, fuskarsa bayyane da murmushi ya fara magana. "Ba komai gwaggo komai ya wuce dama sharrin shaidan ne haka baxai sake faruwa ba, kuma a ja musu kunne duk su biyun sbd gaskiya basa jin maganata" Nasiha su gwaggo suka yi min tare da innah a kan yin biyayya a bisa dukkan abinda ya umarce mu, tunda gaba dayanmu a karkashin sa muke kuma yardarsa muke nema. Har aka yi maganar aka gama innah bata ce komai ba da alamu bata ji daɗin sulhun ba, kawai don an fi karfin ta ne shi yasa tayi shiru, don ta san ba canja xani xata yi ba ko ta koma ci-gaba xa a yi daga inda aka tsaya. A lokacin ya nemi mu tafi tare da shi, gaba daya muka nuna kin amincewa da hakan, kyale mu yayi ya tafi tare da faɗa mana cewa lallai gobe mu taho gida. Da farin ciki ya shiga gida a xuciyarsa yake fada duk burikan da yake son cika su a yanzu ne lokacin da zai cimma su tunda sun amince xasu dawo. Yana fita na faɗa jikin innah ina kuka "me yasa kika amince mu koma hannun shi innah wlh baxa su canja ba watakila ma yanxun wani tuggun aka hado mana...... Dan Allah kice baxa mu koma ba innah" Kuka nake mai cin rai ita ma innah haka, a ranar a can na kwana gaba ɗaya mun kasa gane kanmu banda kuka babu abinda muke yi kamar waɗanda zasu koma kurkuku haka muka ji. Kada a manta da sharing da comment *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:32 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *16* Tun safiyar ranar da zamu koma gida Baba yake ta aike mu taho ya aiko yara sun kai biyar, don mu bamu yi niyyar dawowa a kan lokaci ba, sai mun ƙara hutawa sosai takurar da yayi mana ne yasa ko karyawa bamu yi ba muka tafi, a kofar gida kan benci muka same shi sallama muka yi masa tare da gaishe shi a sanyaye ya amsa babu wani walwala ko farin cikin ganinmu a fuskar sa. Cikin gida muka shiga ya bi bayanmu, kamar jama'ar gidan sun san da zuwanmu duk suna tsakar gida sun jere suna kallon kofar da zamu shigo, da sallama muka shiga cikin gidan abinda ya bani mamaki yau sun ɗan canja kaɗan da fara'a suka tarbe mu, abinda na kasa ganewa shi ne anya ba wani tuggun ake shirin haɗa mana ba kuwa ni da innah. Don na lura da su suna cikin farin ciki sosai har wata yar dariya naga innah salamatu na yi min. Mukullin dakinmu muka karba a hannun Baba, ni na ajiye kayan da ke hannuna na shiga buɗe kofar, abin mamaki muna shiga muka tarar da komai namu na dakin an kwashe mana, sai yar katifar da muke kwana kawai aka bari hatta kayanmu na sawa da yan kwanukan da muke amfani da su duk babu. Kallon juna muka yi ni da innah, zan yi Magana kenan naga ta sa yatsanta a bakinta alamun nayi shiru. rausayar da kaina nayi xuciyata cike da damuwa kallonta na sake yi tare da son ta bani damar yin magana amma ta nuna kin amincewar hakan, wajen xama muka samu muka zauna, baka jin motsin komai a cikin gidan duk an yi shiru ana sauraren jin abinda xamu ce. Mu ma shirun muka yi kasancewar dukkanmu muna cikin damuwa, gaba ɗayan mu duniyar tunani muka tafi, sallamar Baba ce ta dawo da mu daga dogon tunanin da muka tafi. Gefen katifa ya samu ya zauna tare da yin gyaran murya "Abinda nake so da ku shi ne ku kasance masu bin doka da odar da na saka muku, sbd hakan ne kaɗai xai baku damar cigaba da xama a wannan gida da rayuwa a cikinsa kamar kowa" nuna innah yayi "ke kece sarkin bawa Sa'adatu goyon bayan yin duk wata lalatar da take yi a gidan nan, to ki shiga hanlinki ki, ki nisanci dukkan abinda xai kawo mana sabani saboda ke ba wajibi ne na cigaba da zama da ke ba, amma ita Sa'adatu dolena ce, don haka ki kula da kyau kuma na hana Sa'adatu fita daga rana irin ta yau, ta zauna ta jira ni har zuwa lokacin da zan yanke mata hukunci" Mayar da kallonsa gare ni yayi "kema ki gyara halinki ki zauna da yan uwanki lafiya duk abinda salamatu ta umarceki, kiyi kokari ki rika cikawa idan aka kawo min ƙararki kin yi wani abu da ya saɓa ka'ida ranki ne zai ɓaci sannan na hana ki fita, makarantar ma na soke ki bari kya ƙarasa a dakinki tunda dama gidan ilimi na kai ki, sannan kada na sake jin kin yi zancen saurayinki na raba ki da shi har abada saboda baxan bari ya gurɓata miki rayuwa ba" Juyawa yayi zai fita "Au na manta ban fada muku ba, kada ku ga babu kayanku na kwashe ne na siyar na siyawa Sa'adatu kayan aure, don yanzu haka ma an jera wasu daga ciki lokaci kawai muke jira". Shiru muka yi gaba ɗaya mun rasa bakin magana sai bin sa da ido kawai muke yi, nice nayi karfin halin yin magana "Yanzu innah haka xamu zuba ido ana yi mana cin kashi a gidan nan baxa mu yi magana ba, haka zamu rika rayuwar rashin yanci kamar wasu bayi?" Mayar da numfashi tayi "uhmm me kike so nace Sa'adatu so kike nayi magana mu riƙa tashin hankali ana jin kanmu da shi, duk abinda yake min da Allah na bar shi, sakayyar aure tun kafin a mutu Allah yake nuna ishara, to ni baxan daka ta tasa mu lalace ba" jin ana motsi a kofar dakinmu ne yasa muka yi shiru. Innah salamatu ce ta tsaya a bakin kofar tare da kirana naxo na karbar mana abin karyawa, cikin nutsuwa na karasa wajenta, murmushi take min mai cike da ayoyin tambaya tare da cewa "Sannu Amaryar malam har naga kin fara kyallin amarci, amarya kenan bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" kallon mamaki nake mata don ban fahimci abinda take nufi ba, ban amsa mata ba na karbi kwanon na koma wajen innah a gabanta na ajiye ina fuskantar ta "innah kin ji zaton da nake yi yana son zama gaskiya ko, dama nace miki ba a banxa suke wannan fara'ar ba, tabbas akwai abinda ake shirin kulla mana a gidan nan, tunda ga abinda innah salamatu ta faɗa shi ma kuma Baba ya bamu satar amsa, shi yasa nace miki kada mu dawo takurar da ake mana dai ita za a cigaba da yi, baxa su taɓa sonmu ba kuma baxa su daina musguna mana ba tunda dama ba burinsu mu yi farin ciki ba, sun fi son kullum mu dawwama a bakin ciki" murmushin takaici innah tayi "Har yanzu bakya fahimtar rayuwa Sa'adatu wani abin ko kana da ikon ramawa dole kayi hakuri saboda magabatanka sun shiga maganar, banda su gwaggo sun sa baki babu abinda xai dawo da ni, wallahi na fiki takaicin dawowata gidan nan, amma maslahar rayuwarki na duba, idan bana nan zaki shiga cikin matsala ne, wata rana ma zasu iya cewa baxa ki kwana a gidansu ba ko kuma duk wanda suka ga dama su aura miki duk munin halinsa, tun a gabana ana wulakanta ki ina kuma ga bana nan, duk abinda xan fuskanta nafi son mu yi rayuwa tare da ke, saboda na baki kariya irinta uwa" Har Cikin ƙwaƙwalwata nake jin kalaman innah tausayinta ne ya kama ni, gaskiya soyayyar uwa ta musamman ce ga ƴaƴanta babu wanda zaka samu a duniya yayi maka irin son da mahaifiyarka take maka, ta zaɓi mu sha wahala tare a kan ta tafi ta bar ni, Allah sarki innata, Allah ya bani abinda zan saka mata da shi. Da yamma nayi wanka na nemi iznin innah ina son zuwa wajen Rukayya saboda ina cike da kewarta, amma ta hanani saboda ta faɗa min hakan zai iya janyo mana wata matsalar, wannan dalilin yasa na hakura na zauna a cikin damuwa. Bayan sallar isha har mun yi shirin kwanciya bacci Baba ya shigo da kansa ya kira ni, a ladabce na tsugunna tare da cewa "gani Baba" fuskarsa a daure ya dube ni "Yi maza ki canja zani mijinki ya zo zaku yi magana ta fahimta da shi, idan naji kin faɗa masa wani abu wanda ya bata masa rai ni da ke ne" Zan bude baki na tambaye shi wanene mijina ya dakatar da ni "kada ki min wata tambaya ina da halin zaba miki duk mijin da naga dama saboda ni ne mahaifinki ina da ikon yi miki duk abinda naga dama matuƙar bai saɓa ka'idar Shari'a ba" Idanuna ne suka cika da hawaye "Baba wannan kayan ne kaɗai suka suka rage min ba ni da wasu" shiru yayi na wani ɗan lokaci "to naji kije a haka idan kika ci Sa'a ma kafin auren naku zai iya yi miki dinki, ni da nace na yafe masa saboda sadaka na bada ke" A sanye na dube shi "sadaka fa kace Baba" Idanunsa a zare yace "kwarai kuwa sadaka na bayar da ke ko ban isa bane?" Ban iya bashi amsa ba sai kuka da nake yi kawai, nuna min hanyar soro yayi alamar na fita. Idanuna a rufe na lalubi takalmi na saka sai da naje soron farko na ɗan goge hawayen da ke idona sai a lokacin na lura da takalmin da ke kafata wari da wari ne. Tarar wa nayi har an yi masa shimfida a xuciyata nace da alama an shirya cutata don naga wannan baƙo ne mai matukar muhimmanci ga Baba sallama nayi don ina son naji muryar bakon kafin na karasa inda yake, don nasan ko wanene kasancewar soron da ɗan duhu kuma babu hasken fitila. Bai amsa min ba sai da na matso daf da tabarmar da aka shimfida masa sannan ya zaro touch light ya kunna, haske soron da tayi ne yasa naga ashe malam Jibo ne ya sha uban rawani. Jajayen hakoransa wanda suka sha goro ya shiga buɗe min a yatsine na dube shi "lafiya malam na ganka a wannan lokacin, dama kaine kake kirana"? Murmushi yayi "nine Sa'adatu samu guri ki zauna xamu yi magana ne ta fahimtar juna ni da ke" ban yi masa musu ba na samu kan wani ɗan dutse na zauna "ina jinka kayi sauri ka faɗa min don bacci nake aka taso ni" Wani kallo yake bi na da shi kamar xai cinye ni "Ba ki da labarin xuwan bikinmu ne naga kamar baki san komai dangane da hakan ba" A firgice na dube shi "Bikinku da wa?? kai zan aura malam ni bana sonka kuma baxan aureka ba, domin a matsayin ubana kuma malamina na ɗauke ka baxan iya zaman aure da kai ba, kuma ni gaskiya bana sonka kayi min girma ina da wanda nake so kuma har an gama magana da shi" Murmushi yayi "Haba Sa'adatu kenan idan an gama magana da shi me yasa mahaifinki yaxo ya same ni yace ya bani ke, ki daina rudar rayuwarki da wannan shashan saurayinki naki mayaudari wanda ya lalata miki rayuwa, da kike ganin na tsufa, tsufan iya fuska ne kawai, amma duk namiji namiji ne babu yaro babu tsoho, abinda nake so ki gane yanxu shi ne, ki kwantar da hankalinki mu yi magana ta fahimta don wannan auren wallahi babu fashi sai an yi shi matuƙar muna numfashi ni da ke, idan kinga an fasa sai dai idan na mutu ko kin mutu, don haka ki bawa xuciyarki hakuri ki tsaya mu tsara bakinmu da yadda zai kasance. Kece baki san abinda ke faruwa ba har kike wannan maganar ba don tsutsayi ya gifta ba da tuni an daura auren nan, yanxu haka ma kina gidana, kuma ko jiya mun tattauna da mahaifinki a kan a sake daurawa nace a bari mu dai-daita junanmu, sbd bana son takura miki, amma naga har kina taurin kai kina wata fiffi'ka ko? To mahaifinki ma yaso bani ke, sbd ya faɗa min cewa ke bazawara ce a rigar yan mata tsohon saurayinki ya gama da ke, sbd na rufa miki asiri yasa xan miki lefe ko kala biyun ne saboda kada mutane su gane halin da ake ciki, amma tunda haka kika zaba bari na tashi na tafi, aure za a kaura ko ta halin kaka kuma gidana ya zama dole kixo" Yana gama magana ya miƙe ya tafi a fusace, dama malam Jibo mutum ne mai fushi da zuciya, a tsugunne ya barni ina kuka. Ni Sa'adatu naga ta kaina dama Baba yawo yake da ni yana kwance min zani, yanxu mutane duk kallon lalatacciya suke min, wayyo Allah ina xan sa rayuwata, yanxu ko Malam Jibon da nake rainawa na aura wane irin kallo zai rika min, a yanzu dai na zaɓi na mutu a kan na cigaba da wannan muguwar rayuwar da nake yi, baxan iya auren malam jibo ba wlh sosai nake faɗa. Kwanciyar nayi ina kuka mai cike da ban tausayi. Kwana biyu ban yi typing ba bana jin dadi a yi min uxuri Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:32 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *17* A hasale malam Jibo ya shiga shagon da ke cikin gidansa, zaunawa yayi ya haɗa kai da gwiwa yana tunanin kalaman Sa'adatu da irin yadda ta nuna bata kaunarsa, har ga Allah a yanxu xuciyarsa ba tada wani tunani wanda ya wuce ya mallaka ta, sbd ya san idan ya sameta ya gama samun farin cikin duniya, ko kaɗan kalamanta basu kashe masa gwiwa ba sai ma ƙarfi da suka ƙara masa, kuma ya yiwa kansa alƙawari duk wuya sai ya aureta ko tana so ko bata so, gobe da shirinsa xai je gidan su a daura auren don kada ma wani abin ya gifta a daga. Nafi minti goma kwance ina kukan baƙin ciki, banda zalunci an hana ni wanda nake so Yanzu kuma a haɗa ni da wannan tsohon wanda ko tsaftar kirki bata isheshi ba. Baba ne ya fito yana haska soron don ganawa da malam jibo tare da tambayarsa yadda suka yi da ni. A wannan halin ya same ni Ina ta rusa ihu dago kaina yayi tare da tambayata "ke lafiyanki ba ki da hankali ne kike faman kuka haka, wani abin yayi miki, ko kuma dai rashin kirki kika yi masa,menene dalilin da xai sa ki riƙa kuka a wannan lokacin da ya kamata na ganki cikin farin ciki, a wajen wannan mutumin farin cikin rayuwarki yake kada kiyi wasa da wannan damar taki domin taimaka miki xai yi, buɗe bakinki ki fada min gaskiyar abinda ya haɗa ku, kuma idan naje na tambaye shi naji akasin abinda kika fada min ni da ke ne" idona a rufe na bashi amsa da "wallahi bana son shi baba" . dauke ni yayi da mari Yana faɗin "haka kika fada masa ko Sa'adatu shi yasa ya fita a fusace mun yi da shi kafin ya tafi xai nemeni amma bakar maganar da kika fada masa ne yasa ya tafi to wlh xaki haɗu da ni ne" Takalmansa ya shura ya fita a hasale bai xame ko ina ba sai gidan malam Jibo kai tsaye ya shiga shagon gidan don ya san yana can, yana ganin Baban Sa'adatu ya miƙe yana cewa "yarka ta wulakanta ni ta tozarta ni, tace bata sona nayi mata tsufa, ta ci min mutunci da maganganun da bai kamata su fito daga bakinta ba, dama taimaka maka xan yi na aureta don haka na fasa kaje ka bata ɗan iskan da take so, dama jihadi xan yi tunda ta nuna bata so na kyaleta da tsiyarta, ka tashi ka fita ka bar min gida kafin na huce takaicina a kanka" jikinsa ne ya dau rawa bakinsa yana karkarwa yake magana "baxa a yi haka ba malam ka yiwa Sa'adatu uxuri har yanzu yarinya ce bata san rayuwa ba, baxa ta gane muhimmancin ka ba sai nan gaba, idan kace ka kyaleta akwai matsala kayi hakuri xata dai-daita halinta xuwa gaba" shiru yayi yana sauraren baban Sa'adatu, mayar da ajiyar zuciya yayi "shikenan nan naji kaje ka ja mata kunne idan ta cigaba da abinda take yi xata yi asarar aurenmu kuma kayi mata albishir lefen da nayi niyya na fasa, yanzu kuma shawara ya rage naka kayi kokarin da xaka yi a daura auren nan da wuri kada wani dan iskan ya sake hure mata kunne" Miƙa masa hannu Baban Sa'adatu yayi amma sai ya ƙi karba "insha Allah malam xan yi wannan kokarin na gode sosai Allah ya kara girma" fitowa yayi da sauri xuciyarsa tana ta sake saken irin cin mutuncin da zai yiwa Sa'adatu idan ya koma gida. A fusace ya nufi dakinsu cikin rashin Sa'a ya tarar sun kulle da alama yau da wuri suka kwanta. Tunda na shiga daki ban rintsa ba gaba daya na nemi bacci a idona na rasa kawai tunanin yadda xan tsara rayuwarta da malam Jibo nake yi, na san tunda Baba ya kafe xai yi wuya abin nan bai tabbata ba. Tashi nayi na bude kofa a hankali na daura alwala na koma daki sallah nake yi ina addu'a Allah ya nisanta ni da malam Jibo Allah ya kawo min sanadin da xa a fasa auren gaba ɗaya. *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:32 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *18* Tun bayan fitowar Izuddeen daga police station bai sake samun sukuni ba, kullum cikin damuwa da tunanin halin da Sa'adatunsa take ciki yake yi, yana ji a ransa baxai taɓa barinta ba har abada ko ana muzuru ana shaho, gaba ɗaya ya daina fita harkokinsa komai nasa ya tsaya cak saboda tunani, kullum cikin kuka yake duk ya rame yayi baƙi, ko abinci baya ci sai idan mama ta bashi shi ma sai ta rarrashe shi sannan zai ci. Yau ma kamar kullum kwanon abincin yasa a gabansa, hannunsa rike yake da wayarsa ya kurawa wayar ido yana hawaye, hoton Sa'adatu yake kallo zuciyarsa sai radadi take masa, ji yake kamar yaje ya shaqi Baban Sa'adatu ya fito masa da ita, saboda idan akwai abinda yake da muradin gani yanzu bai wuce Sa'adatunsa ba. Sallamar mama ce ta katse masa dogon tunanin da ya tafi, tare take da abokinsa Kabir karasowa daf da shi tayi fuskarta a bayyane da damuwa. "Wato har yanzu dai kana nan kana wannan tunanin naka ko Izuddeen, yaushe xaka cire yarinyar nan a ranka ne, tunda mahaifinta ya nuna baya sonka baya son tarayyarka da yarsa ya kamata indai da zuciya aka halicceka kayi hakuri ka kyale masa 'yarsa gudun kada a sake samun matsala, kana ganin dai irin cin mutuncin da yayi mana, aure indai yaxo da haka kamata yayi a hakura a canja she'ka sai Allah ya canja da mafi alkhairi. amma kai kaxo kana tunanin wacce bata damu da kai ba bata ma san kana yi ba, tana can tana rayuwarta cikin farin ciki" muryar Izuddeen a sha'ke ya fara magana "wlh mama ta damu da ni,duk inda Sa'adatu take yanxu ina cikin ranta ita ma ba a cikin nutsuwarta take ba, ki fahimci yarinyar nan mama tana matuƙar sona bakin ciki ake so a yi mana kawai a raba mu, dan Allah idan kina da hali ki taimake ni ki haɗa Ni da ita" ya karasa maganar yana kuka. Ba ƙaramin tausayawa ɗan nata tayi ba saboda ta san yadda zafin ciwon so yake da ciwon rabuwa da abinda mutum yake so, cikin nutsuwa suka samu guri suka zauna ita da kabir, dago fuskarsa tayi "kayi hakuri d'ana ka karbi kaddara ka sanya a ranka wannan ita ce kaddararka idan kayi hakuri Allah xai canja maka da mafi alkhairi, na san abin da ciwo amma kayi hakuri wata rana zai wuce ya xamto kamar bai faru ba" Shi ma kabir hakuri ya riƙa bashi a kan ya cire damuwa a ransa ya manta da komai kuma ya daure ya ci abincin da ke gabansa, kuka Izuddeen kawai yake sbd ko ya sa abincin a bakinsa baxai iya samun damar hadiye shi ba, duk magiyar da suka yi masa haka suka rabu da shi bai ci abincin ba. Duk ya xama wani iri ya fita a kamaninsa ba shi da aikin da ya wuce kuka kamar yaron da yayi rashin mahaifansa. Hankalin mama a tashe ta tashi ta shiga wajen Mahaifinsa da sallama ta shiga tare da karasawa inda yake, xaunawa tayi da niyyar ta faɗa masa abinda ke damun ɗan nasu, amma sai ta kasa sai hawaye da ke fita a idonta, tashi mahaifin Izuddeen yayi daga kishingidar da yayi cikin kulawa yake tambayarta "Lafiya Hajiya me ke faruwa naga kina kuka haka" gefen mayafinta tasa ta share hawayen da ya cika idonta "A kan maganar yaron nan ne Izuddeen wlh Alhaji yana cikin wani hali tun bayan rabuwarsu da yarinyar nan ya daina ci ya daina sha, kullum cikin kuka wai dan Allah baka lura da yadda ya koma ba ne, duk yayi baƙi ya lalace, dan Allah dan Annabi idan da ɗan kokarin da xaka yi masa, ka taimaka kayi masa ka shawo kan mahaifin yarinyar nan saboda mu ceto rayuwar ɗanmu" Da kuka ta ƙarasa maganar. Sauke ajiyar zuciya yayi "Hmmm Hajiya kenan dan Allah ki kyale maganar mutumin nan ki manta da su, mu taya shi da addu'a Allah ya canja masa da wacce ta fi ta, wai dan Allah duk kin manta da abubuwan da suka faru da mu ne? Kin manta irin cin mutuncin da mahaifin yarinyar nan yayi mana, ɗaukan ɗanmu yayi fa ya kulle sai da ya shafe wasu adadin kwanaki sannan ya fito, duk fa yayi haka ne da niyyar tozarta mu Allah ne ya kiyaye ya takaita abin, a tunaninki da Allah bai yayyafawa abin ruwa ba me kike tsammanin zai faru? Indai gidan wannan mutumin zan je nemar masa aure sai dai idan baxai yi ba gaba daya, saboda ni bana shiga harkar mutumin da baya ganin 'kima da mutuncin na gaba da shi, kije ki cigaba da bashi hakuri Allah ya canja masa da wacce ta fi ta alkhairi" komawa yayi ya kishingida yana sauraren amsar da xata faɗa masa. Magiya ta cigaba da yi masa "Ba halin mahaifinta xamu duba ba, nagartar yarinyar xamu duba da yadda mutane suke yabon kyawawan halayenta, idan ka lura da wani abu ita kanta yarinyar ba jin daɗin mahaifin nata take yi ba, kawai don ya zama dole a kira shi da mahaifinta ne amma da tuni ta canja wani uban, don Allah ka duba rokona ka taimaka ka samowa yaron nan mafita, ko baka je da kanka ba ka daure ka aika yayyensa tare da abokanka su nemar maka alfarma a bamu dama mu fito a yi biki" Har yanxu dai kalamanta ba wani ratsa shi suka yi ba kawai yana bin ta da kallo ne, ɗan murmushi yayi wanda ya ƙara bayyanar masa da kamalarsa. "Dadina da ke kafiya idan kina son abu, mutumin da bai duba mutuncin Musulunci da ma'kotaka ya ɗagawa ɗan da na haifa ƙafa ba, shi ne xan je wajensa na nemi alfarma yayi min? kawai wannan bata lokaci ne ki tashi kiyi hakuri" Magiya take yi masa sosai amma har yanxu yaƙi sauka, umarni ya bata taje ta kira Izuddeen yana son magana da shi, da sauri ta tashi ta nufi ɗakin nasa faɗa masa tayi cewa mahaifinsa na son magana da shi, jikinsa babu karfi ya tashi ya bi bayanta. Cike da ladabi ya shiga dakin tare da yi masa barka da rana, cikin sakin fuska mahaifin nasa ya amsa. "Yanzu duk a kan soyayya ka xama haka Izuddeen, ka manta da dukkan abinda suka faru a baya? Me yasa kake son jefa rayuwarka cikin wani hali, kaifa malami ne bai kamata ka manta da kaddara ba ka jefa kanka a damuwar da xata iya kai ka ga halaka, bana so na cigaba da ganinka a wannan halin kayi hakuri xan nemar maka wani auren da kaina, kuma baxa a ɗauki lokaci ba za a daura shi" Kan Izuddeen a sunkuye ya fara magana "Dan Allah Babana mai tausayina kayi hakuri ka taimaka min ka aika gidan su Sa'adatu ka nemar min aurenta wlh Baba ita nake so da ita na tsara rayuwata, baxan iya xaman aure da wata ba idan ba ita ba" da kyar ya iya ƙarasa Maganar sbd kukan da ya ci karfinsa. Cike da tausayawa mahaifinsa ya dube shi, "shikenan kaje magana ta ƙare xan aika gobe da kuɗin aure idan sun amince sati mai zuwa ma za a sa muku rana a daura aure tunda haka kake so amma duk abinda ya biyo baya babu ruwana" Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskar Izuddeen bai san lokacin da ya saki murmushi ba. "Na gode na gode Baba Allah ya kara girma Allah yasa kafi haka" Amsa masa yayi da ameen ya tashi ya tafi, a ranar da farin ciki ya wuni sbd dadin albishir din da aka yi masa, ita ma mama tayi farin ciki sosai sbd ɗanta zai samu abinda yake so. Kada a manta da comment da kuma share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:33 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @Jeeddahtou* *19* Yau tsayin wuni a daki nake ko tsakar gida ban leko ba, sbd ciwon kai mai tsanani da zazzaɓin da ke damuna, maganar da malam Jibo ya fada min ke min yawo a ƙwaƙwalwata duk da cewa ina addu'a amma ina tsoron sharrinsa, na lura da shi sosai akwai manufar da yake son cimmawa a kaina, ba alkhairi ne ya kawo shi wajena ba, duk kulle-kullen da ake yi a gidanmu ina ji, amma sai naki fitowa sbd kada na haɗu da Baba, sai da na tabbatar ya fita kasuwa Sannan na fito na ɗan yi abinda zan yi na koma. kwanciya nayi da niyyar na huta sallamar Rukayya ce ta katse min baccin da nake yi, da sauri na tashi na rungumeta fuskata cike da farin cikin ganinta, muryarta a ƙasa take min magana sbd bata son su innah salamatu su san da xuwanta su haɗa mana tuggu a wajen Baba, gurin zama ta samu ta xauna. Tambaya ta jefo min "Yaushe kika dawo Sa'adatu nayi kewarki sosai kuma na shiga tashin hankali da naji ance kin gudu tunanina kada ki faɗa hannun azzalumai kinga duniyar nan ba amana, tun lokacin ban sake samun nutsuwa ba sai da naji an ce kin dawo, naso naxo tun lokacin da kika dawo amma sbd matsalar gidan nan yasa nayi xamana kada na sa kiyi laifi" Murmushi nayi wanda ya tsaya a iya hakorana, takaici da baƙin cikin da ke tattare da ni baxai bari nayi murmushi sosai ba. "Ba fa guduwa nayi ba Rukayya ina gidan Adda saratu can na koma sbd naga cutata ake shirin yi, ya za a yi ina rayuwar birni na koma ƙauye ai ba a yi min adalci ba" "Ni kaina naji dadin gudun da kika yi, amma daga baya da nayi tunani sai naga rashin dacewar hakan, sbd kada makiya su samu kofar da xasu yi miki sharri, kinga dai irin rayuwar da kike yi, yau zaƙi gobe maɗaci" Rausayar da kaina nayi idanuna kamar zasu kawo hawaye "indai sharri ne ban ga ranar da xasu daina min ba har sai ranar da Allah ya raba ni da su, yanxu haka ma a tarkonsu nake suna son haɗa ni da malam Jibo kuma ina ganin alamun da wuya ne abin bai tabbata" A razane Rukayya ta miƙe "wannan wane irin zalunci ne da mugun hali, me yasa ake miki haka ne Sa'adatu?? Sai kace ba Baba ne ya haifeki ba innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah ya canja miki da mafi alkhairi Allah ya kawo miki mafita, shi ne kaɗai abinda xan iya cewa dan al'amarin ya wuce lissafina" komawa tayi ta xauna tana min kallo mai cike da tausayawa "wlh sosai nake jin tausayin ki Sa'adatu amma ba komai rayuwa ce duk abinda suka yi dan kansu, ke dai kiyi hakuri kuma ki riƙe Allah dukkan tsanani yana tare da sauki" mun ɗan taɓa hira sosai amma hankalina gaba ɗaya ba a kanta yake ba, yana wani wajen daban kawai tunanina ya zan yi da Malam Jibo, idan nayi tunanin na gudu sai naga hakan ba mafita bace saboda innah xan jefa a wani hali, sannan kuma har ga Allah bana son bijirewa umarni Baba, sbd bana so a zargi innata da laifin da ba nata ba, haka na kasance ina ta sakawa ina kwancewa har lokacin tafiyar Rukayya yayi, iya soro kaɗai na iya rakata sbd dokar da aka kafa min. Bayan na koma daki Baba ya dawo daga kasuwa ya neme ni xai min faɗa a kan abinda ya faru jiya, duk kiran da yayi min ban amsa ba sai na nuna bacci nake yi, hakan yasa bai samu ganina ba. Ya zauna zai ci abinci kenan naji an aiko wani yaro cewa ana kiransa a waje, ba tare da bata lokaci ba ya hau wanke hannu ya fita don ganin masu nemansa. A kofar gida ya tarar da mutanen da ke nemansa, mutane ne dattijai masu kamala da mutunci kowannen su sanye yake da Babbar riga da hula, cikin karamci suka yi masa sallama, fuskarsa a ɗan d'aure ya amsa musu tare da tambayar su dalilin zuwansu ɗaya daga cikinsu ne yayi magana. "Allah ya gafarta malam magana ce mai muhimmanci ta kawo mu, idan so samu ne mu shiga daga ciki xai ɗan fi sirri saboda idanun mutane" bai yi musu ba ya kwalawa A'isha kira ta kawo musu babbar tabarma ta baxa musu suka zauna. Bayan sun gama gaishe gaishen da xasu yi, wani dattijo ya fara masa bayani "mun zo wajenka ne neman wata alfarma dangane da ɗanmu da yaga yar wajenka Sa'adatu yana so, idan da hali muna so a bamu dama mu fito, yaron bai zo da wasa ba kuma mu ma haka, don da shirinmu muka zo" Kamar bai fahimci abinda suka faɗa masa ba yace "Ban gane Sa'adatun da kuke nufi ba, ni dai nasan ina da 'ya Sa'adatu amma kuma har aurenta an daura" kallon kallo suka shiga yi tare da mamakin jin abinda yake faɗa musu. "Ikon Allah amma nayi mamakin wannan maganar don mu gidan nan aka kwatanta mana kuma tare da yaron da yake neman auren ma muka zo shi yayi mana rakiya, kaga batun a ce ba nan bane bai taso b" Murmushin mugunta yayi "Na gane yaron da ku ke magana a kai na sanshi farin sani, na kuma san yana son 'yata Sa'adatu sai dai a gaskiya baxan iya bashi aurenta ba sbd na riga da nayi mata miji tun da dadewa, da tuni ma an daura auren yar matsala aka samu shi ne ya kawo jinkirin abin" Girgiza kai suka yi tare da mikewa "shikenan mun gode Allah ya sanya alheri shi kuma Allah ya bashi ta gari" Ameen yace tare da bin su da wani matsiyacin kallo. fita suka yi daga gidan suna ta tunanin abinda mahaifin Sa'adatu ya faɗa musu. Izudeen na tsaye a bakin kofar gidan yana jiran ganinsu da amsar da xasu ba shi, yana ganin fitowar su ya taho da sauri tare da tambayarsu "An dace kuwa?? Wani dattijo ne ya hau shi da faɗa "kai da kasan an bada ita har an kusa aure zaka sa mu nemi aure a kan aure, gaskiya baka kyauta mana ba da kimar mu da mutuncin mu" Yayan izuddeen ne ya dafa dattijon yana yi masa magana "wlh bai sani ba Alhaji kawai dai baxai bamu auren bane amma ko mutanen unguwa sun tabbatar babu wani aure a kanta" Mayar da kallonsa yayi ga izuddeen cike da tausasawa ya fara yi masa magana "kana so na baka shawarar da zata amfaneka?" da sauri ya amsa masa da "eh" "Tabbas zaka ji zafi idan ka rasa abinda kake so amma kuma xaka ji dadi idan ka tuna Allah zai canja maka da wanda ya fi shi alkhairi idan kayi hakuri, kowane dan adam da kake gani da irin ƙaddara ko jarrabawar da take samunsa sai dai na wani ya fi na wani, ka ɗauka wannan shi ne ƙaddararka kuma zaka yi hakuri don ganin ka cinye. Dan Allah dan kaunarka da Annabi ina yi maka magiya saboda Allah, ka kyale yarinyar nan ka cire soyayyarta a ranka, tunda iyayenta sun nuna basa sonka basa son kayi tarayya da yarsu kuma baxa su baka ba aurenta ba, ka bawa zuciyarka hakuri tun kafin ciwo ya kamaka, yanxu haka maganar da nake maka an kusa daura mata aure, dan haka ka rabu da ita Allah xai canja maka da wacce ta fita" Wani baƙin ciki ne ya kama izuddeen kamar ya fashe da kuka, amma sai ya nemi hawaye gaba ɗaya ya rasa a idonsa sbd bacin rai, bin bayansu yayi suka tafi, ji yayi kamar kafafunsa baxa su iya daukansa ba ga jiri da ciwon kai da zazzaɓi mai xafi da yake ƙoƙarin rufe shi, gaba ɗaya baya ganin hanya duhu kawai yake gani sbd bacin rai. ********** Da bacin rai Baban Sa'adatu ya shiga cikin gidan yaji ciwon maganar da dangin izuddeen suka xo masa da ita, kuma bai ga laifinsu ba illa laifin Sa'adatu da har ta basu damar xuwa su tunkare shi da maganar, don haka kai tsaye dakin su Sa'adatu ya nufa yana ta surfa mata kira da yaga ba tada niyyar fitowa zata bata masa lokaci, shiga dakin yayi a fusace yana fadin "Fito nan munafukar banxa ni xaki je ki haɗawa tuggu da munafunci, har wasu mutane su tutsiye ni a dole sai sun sa nayi abinda ban niyya ba, ke wai a dole sai na aura miki wanda kike so ko, kin kyauta kuma xaki ga sakamakon abinda kika yi nan bada dadewa ba, za kiyi nadamar tozartanin da kika yi" Cikin rashin fahimtar abinda yake faɗa min na dube shi "Baba me nayi wlh ban turo kowa ba, kuma ban sa wani mutum ya tozarta ka ba" Ture ni yayi yana nuna ni da ɗan yatsansq, wlh idan kika sake magana sai nayi ƙasa-kasa da ke a gidan nan karya xan miki? dole ne sai na aure miki wannan ɗan iskan yaron da kika kawo wanda bai san mutunci ba mai ƙoƙarin keta alfarmarki ta ya mace, to wlh ki sani a daren nan xan daura aurenki zan ga wanda ya isa ya hana ni, tunda kin nuna ke ba yar mutunci bace xan nuna miki ba kida wayo" Fita yayi ya bar ni ina ta sharar kuka ita kuwa innah bin shi tayi da kallo, bayan ya fita ta jawo ni jikinta tana rarrashina "kiyi hakuri Sa'adatu Allah baxai wulakanta mu ba, suna ganin sun yi mugunta sun hada ki da Malam Jibo ko, da yardar Allah karshe sai ya xama alkhairi a gareki, tunda muka riƙe Allah baxa mu yi da na sani ba, ki daina wannan kukan baxai mana maganin komai ba addu'a ita ta kamace mu" Yana fita bai zarce ko ina ba sai gidan malam Jibo, a zaure ya tarar da shi tare da wani abokinsa suna tattaunawa, yadda yaga Baban Sa'adatu a birkice ne yasa ya tambaye shi "lafiya malam Salisu me kuma ya faru haka Allah yasa dai kalau??" Cikin zafin rai ya fara magana "ka shirya yau xan daura maka aure da Sa'adatu da misalin ƙarfe bakwai na daren yau ka fadawa mutanen da zaka fadawa, ni na riga na gama yanke hukuncina yanxu xan kira abokina Alhaji Lamma yaxo shi ma ya shiga cikin shedu" Wani farin ciki gami da daɗi ne ya saukarwa malam jibo, ji yayi a ransa kamar yayi ihu dan dadi, cikin girmamawa yace "to shikenan Allah ya kaimu ni dama a shirye nake ko yanzu a kawo amarya" Wajen abokinsa ya wuce ya sanar da shi daurin auren Sa'adatu yau, duk wanda yaji labarin auren sai yayi Allah wadai, dukkan mutanen unguwar sun san auren mugunta aka shirya yi mata, babu wanda yake cewa Allah ya sanya alkhairi sai dai Allah ya sakawa Sa'adatu. Da misalin ƙarfe bakwai malam jibo da abokinsa suka hallara a Kofar gidansu su Sa'adatu dukkan mutanen da suka halarci daurin basu wuce mutum bakwai ba, ba tare da bata lokaci ba aka daura aure, dubu goma Malam Jibo ya biya na sadaki sun ɗan zo da goransu da alewa wanda bai taka kara ya karya ba, bayan an kammala aka gabatar da addu'a tare da fatan Allah ya bawa ma'auratan zaman lafiya. Cikin gida mahaifin Sa'adatu ya shiga hannunsa riƙe da kullin dabino da goro da alewa, dakin salamatu ya shiga tare da mika mata kayan, cikin kissa da makirci take tambayarsa "wannan kuma na menene malam?" kawar da kansa gefe yayi yana magana "Na daurin auren Sa'adatu ne da malam Jibo yanzun nan aka kammala shi" wani gud'a ta saki "Alhamdulillah yau dai Allah ya nuna min auren bazawarar yata mai baƙin jini ashe dama ina da rabon ganin aurenta, oh!!! ALLAH da iko yake" shewa tare da ihu suka rika yi ita da ƴaƴanta. Daga nesa na riƙa jiyo karad'insu, a xuciyata nace yau kuma me ke faruwa a gidan namu naji innah na murna Allah yasa dai ba ni abin ya shafa ba, kafin na rufe bakina har sun fado dakinmu jefo mana dabino Baba yayi gami da mayar da kallonsa gare ni. "Ki daina daukan dukkan abinda nake fada miki da wasa idan nace xan yi abu la shakka sai na aikata don haka ki kiyaye ni, aure an daura shi kuma ya dauru ga sadaki dubu goma ya bayar amma baxan baki ba sbd ni sadaka na bayar da ke, don haka xan mayar masa da kudinsa ke kuma idan na samu xan biyaki" yana gama faɗa ya juya, hawaye kawai na gani a idanuna na sauka, ji nake kamar xuciyata xata faso kirjina ta fito, na kasa cewa komai sbd bakin ciki. Innah salamatu ce ta karaso cikin dakin da mu ke zaune ni da innah "Sa'adatu ina taya ki murna yau dai nauyin 'kashi ya ƙare Allah yayi xaki tafi gidan aure kema ki samu irin falalar da ake samu, wannan ranar na dade ina jiran xuwanta ashe a kusa take, kuma wani ikon Allah ashe ma mijin anan kusa yake bai fito ba sai da lokaci yayi, gaskiya na yarda da karin maganar Bahaushe da yace komai da lokacinsa wai mahaukaci yayi girbi a watan bakwai, fatana a gare ki shi ne kiyi hakuri gidan mata uku Allah ya kai ki kece cikon ta huɗun, duk wani girman kai da jiji da sai kin cire su kin ajiye su gefe guda, wannan nu'kufurcin naki kiyi watsi da shi da wannan mugun halin don baxai kai ki ga tafarkin tsira ba, sannan ki kama ƴaƴan mijinki ki rike su tsakani da Allah banda rowa da sharri da makircin don nasan duk kin........." Kafin ta ƙarasa innah ta dakatar da ita "ya isa haka ya ishe ki salamatu, na gaji hakurina ya ƙare baxan juri wannan bakaken maganganun da kike fada mata ba da me xata ji, da bakin ciki da hassadar da kuke mata da sharrin da kike kulla mata ko kuma da maganar da kike mata yanxu, duk abinda ya faru da Sa'adatu wace ce sanadi idan ba ke ba, ina da labarin dukkan sharrin da kike kullawa Sa'adatu kawai shiru nayi na barki da Allah tunda ba a duniya za a dauwama ba, ke idan ana maganar bakin hali da mugun hali har kya yi magana da cin amana da ha'intar ya'yan miji har kya yi magana, wanda bai san halinki ba xaki fadawa wannan amma wane irin makirci ne baki iya ba, tun daga kan karfar baka har yawon malamai wanne ne a ciki bakya yi, ki je na barki da fitowar rana da faduwarta na san dukkan abinda kika shuka wata rana sai kin girbi irinsa, kema kina da ya'ya xaki gani a kansu, auren nan kuma insha Allah alkhairi xai xamewa Sa'adatu ba sharri ba, da yardar Allah abinda kike da burin ya same ta baxai sameta ba har abada muguwar banxa wahalalliya" Fashewa innah salamatu tayi da kuka wai innah ta xageta, aikawa tayi aka kira Baba shi ma yaxo ya riƙa faɗa da xage xage, a ranar dai gidanmu a rikice ya kasance sai can dare abin ya lafa, daga ni har innah bamu samu mun rintsa ba sbd tunani wannan dalilin ya bamu damar yin Sallah da fadawa Allah muguntar da ake shirin yi mana. Washe gari da yamma su Rukayya da ummansu suka zo don jajanta mana abinda ya same mu, don ko su Adda saratu basu san da daurin auren ba sai a yau din innah ta aika ta faɗa mata, sbd takaici cewa tayi baxata xo ba. Sallama mahaifiyar saleem tayi tare da shigowa dakinmu yau fuskarta a sake sbd tana farin ciki da abinda aka yi mana, gaisawa suka yi da innah tare da fada mata cewa Baba yace a fito da ni za a kaini dakina, ban san lokacin da na rusa wani ihu ba wanda sai da ya gigita mutanen gidanmu gaba daya, fitowa suka yi suna sallallami tare da tambayar abinda ya faru da ni, a lokacin ne Baba yaxo ya daka min wata tsawa yace na d'akko mayafina a kai ni, amarya babu kunshi ballantana fulawa, ba wani kamshi da nake yi a matsayina na amarya, duk wanda ya ganni ya san auren dole aka yi min, saukinta ɗaya nayi wanka amma ko mai ban shafa ba, sutturar jikina ma ba wata mai kyau ba ce, haka aka ɗauke ni muka tafi ina tafe ina kuka saukin da na ji ɗaya ne na samu rakiyar Rukayya da mahaifiyarta sai kuma ya'yan gidanmu da suke son xuwa su ga kwakwaf. Kada a manta da sharing da kuma comment 08094136204 *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:33 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *20* *Wannan shafin gaba ɗaya naki ne halak malak na bar miki shi kiyi yadda kike so da shi, kawata aminiyata maxumunciyata abokiyar shawara abokiyar faɗa AISHA SABO ABDULLAHI (mrs khamis) Allah ya bar min ke ko ba kai ba ƙafa ko dan naci dariya🤣🤣🤣* Muna isa bakin kofar gidan umman Rukayya ta umarce ni da yin Bismillah tare da shiga da kafar dama don neman sa'a, ban yi gardama ba nayi abinda ta umarce ni, daga saka kafata a soron gidan na fara cin karo duwatsu da kawazzabai saura kiris na fadi, haka na daure na buɗe idona don gudun kada na fada wani ramin sai da muka isa tsakar gida na rufe fuskata, hayaniyar da ake yi a gidan ne ya daki kunnena yara ne ƙanana waɗanda baxa su wuce shekara biyar ba xuwa shida suke ta wasanni da tsalle-tsalle, ilahirin tsakar gidan a jike yake baka jin komai na tashi banda warin banɗaki, gidan dai babu sha'awar gani saboda tsafta bata wadaci mazauna gidan ba, yaran gidan na ganinmu suka hau ihu suna ga amarya har da masu kokarin kama mayafin jikina sai da Rukayya ta kai musu duka sannan suka tarwatse. kai tsaye dakin uwar gida aka shigar da ni, tare suke a dakin ita da ragowar matan nasa biyu, gefen gadonta aka samu aka xaunar da ni ragowar yan rakiyata kuma suka tsaya daga waje, kasancewar dakin baxai dauke mu gaba ɗaya ba, gaisawa suka yi da su umma sama sama saboda uwar gidan ba sosai take da kirki ba, ragowar kishiyoyin nata sun ɗan fi ta sakin fuska, sun fi karɓar mu hannu biyu-biyi. umma ce ta fara magana "To ga kanwarku kuma amaryarku mun kawo dan Allah ku riketa amana, duk abinda ya dace na gyara ku rika yi mata, kuma ku riƙa hakuri da gazawarta" Duk bayanin da umma tayi basu ce komai ba ƙaramar cikinsu ce tayi ƙarfin halin yin magana "to xamu riketa amana Allah ya bamu ikon zama lafiya da junanmu" Gaba daya aka amsa mata da "ameen" Tashi muka yi muka nufi ɗakin da xan xauna tunda na hango kofar dakin wani baƙin ciki ya daki xuciyata, ilahirin bangon dakin duk yayi jirwaye, ita kanta farar ƙasar ba mai kyau ya siya ba, duk macewar gidan mu ya rufawa na Malam jibo asiri, mukulli Rukayya ta karba ta bude kofar dakin, a hankali na saka kafata na shiga babu komai a dakin sai uban duhu, wayar Rukayya aka kunna don ganin hanya, duba dakin na shiga yi naga bangon duk ya lalace, wani ƙarin abin takaici ko labule ba a saka min ba, ledar ma bata shimfidu dai-dai ba saboda ramukan da ke dakin, kukana ne ya tsananta yanzu nake kara tabbatar da irin cutar da aka yi min. Kama hannuna umma tayi ta zaunar da ni kan tamulalliyar katifar da aka shimfida min wacce ko arxikin zanin gado bata samu ba, kusa da ni ta xauna hannunta cikin nawa a hankali take min rada a cikin kunnena"kiyi hakuri Sa'adatu kinga dai yadda Allah yayi da mu, ba yadda xamu yi tsarin Allah shi ne tsari kuma duk yadda ya tsara haka xa a yi, a kullum addu'ar alkhairi muke yi kuma muna nan insha Allah xai tabbatar mana da alkhairin, kiyi hakuri ki daina kuka wata rana komai xai xamo tarihi, ki yiwa mijinki biyayya ki xauna da kowa da xuciya daya, insha Allah xaki cinye wannan jarrabawar cikin sauki kuma baxa ki tabe ba har abada fatana a gareki shi ne ki riƙa Allah tare da addu'a duk rintsi kada ki manta da karatun Alkur'ani da kiyamullaili ki kuma saka a ranki DUKKAN TSANANI yana tare da sauki" rungume ni tayi muna ta kuka tare, ita kuwa Rukayya tun shigowar mu take ta kuka kamar iya ce Amaryar babu abinda take iya faɗa banda Allah ya saka miki Sa'adatu. Sun ɗan yi zama na yan awowi don sai da aka kira sallar isha muka yi sallah tare da su sannan suka tashi don tafiya gida, kana kallon fuskokin ya'yan gidan mu xaka tabbatar da cewa suna cikin farin cikin abinda aka yi min banda fara'a babu abinda suke yi, ganin idon ummansu Rukayya ne ma ya hana su magana amma da babu ita da sai na gudu don habaicin da xasu yi min. Har bakin dakina na ɗan taka musu ina ta kuka "yanzu umma tafiya xaku yi ku bar ni a wannan gidan dan Allah kada ku tafi ku kyale ni ban san yadda xan yi rayuwa a cikin gidan nan ba, na rabu da ku na rabu da innata na shiga uku" Rungume ni Rukayya tayi tana kuka ita ma umma kukan take sosai aka rasa mai rarrashin wani a tsakaninmu, sai da muka yi kukan da ya ishe mu sannan muka saki junanmu, riko hannuna Rukayya tayi gaba ɗaya ta kasa sakina, kuma ta kasa magana ji take kamar ita aka saka a wannan kurkukun, cikin ƙarfin hali na fara yi mata magana. "Dan Allah Rukayya ki nemi izuddeen duk inda yake ki bashi hakuri ki fada masa dukkan abinda ya faru ba a son raina ya faru ba, kuma dan Allah idan da hali kice na bashi dama ya aureki ko xai samu sassaucin xafin da yake ji" ina karasa maganar na fashe da matsanancin kuka ban san lokacin da suka wuce suka barni ba, sbd idan suka daka ta tawa baxan bari su tafi ba gashi dare ya ɗan fara yi. Sai da nayi kukan da ya ishe ni sannan duba jakata na dakko wata tsohuwar touch light din innah da na sakata a jakata, haska dakin na fara yi ina ƙare masa kallo, baka ganin komai sai ramukan kiyashi da cinnaku, daki kamar ba na amarya ba a xahiri nake furta Allah ya isa Allah ya bi min hakkina, gyaran muryar da naji an yi ne ya dawo da ni cikin tunanina. Malam Jibo na gani hannun shi rike da touch light sallama yayi min tare da isowa wajen da nake, ko dagowa na kalle shi ban yi ba ballantana ya samu arxikin amsa masa sallamarsa. samun guri yayi ya xauna daf da ni da sauri na janye jikina na sauka daga kan katifar ma gaba ɗaya, ledar da ke hannun shi ya ajiye tare tare da budeta, murmushi yake yana min magana. "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida, ga Gurasa nan da balangu na siyo musamman sbd ke kizo mu ci, daga nan mu yi sallah mu godewa Allah a bisa baiwar samun juna da yayi mana" A fusace na dube shi Allah ya kiyaye na ci abinci da kaxamin Mutum irinka wanda bai san hakkin kowa a kansa ba sai kansa, azzalumi wanda ya raba ni da farin ciki a rayuwata, ka sani yadda ka zama sanadin sanya ni cikin baƙin ciki kaima baxa ka taɓa samun farin ciki Daga gare ni ba" gaba ɗaya na nemi tsoronsa da kimarsa da nake gani na rasa, ji nake kamar na tashi na xane shi komai nashi haushi yake bani. Murmushi yayi tare da shafa cukurkudadden gemunsa "Kanki kalau kike fadin haka Sa'adatu anya kina cikin hankalinki kuwa, ba wani abu kika sha ba Sa'adatu ni ne fa malam Jibo malaminku ko kin manta ne?, ki kwantar da hankalinki ki min biyayya duk abinda wata mace take samu a gidan mijinta kema xaki samu, ki sani duk cikin matana nafi sonki kuma sai kin fi samun soyayya fiye da kowace mace da ke gidan nan" Gefe na koma na sunkuyar da kaina nayi gami da toshe kunnena, ina ta sharar kuka baxan iya jure sauraren kalamansa ba idan na cigaba da ji xan iya faɗa masa abinda ya fi haka ma. Numfashinsa naji na dukan kunnena da sauri na miƙe, wani kallon ban haushi yake bina da shi, cikin fushi nace "Bana son rashin jan girma me kuma ya kawo ka nan, tun wuri kaja mutuncinka kafin nayi maka abinda xaka yi nadama, abinda ka siyo nace baxan ci ba kaci kai kaɗai talauci na bai kai naci abinda ya fito daga hannunka ba" Shafa kansa yayi "Tunda baxa ki ci abinda na siyo ba tashi mu je wajen yan uwanki na gabatar da ke na kuma faɗa miki dokokin gidana". Fita yayi na bi bayan shi a tsakar gida na tarar da su an yi shimfida ana jiran karasowar mu, wajen xama suka bani amma sai naki xama a kan shimfidar tasu, ajiye takalmina nayi na xauna a kansa ina sauraren abinda xai faɗa min. Gaishe shi naga matan nayi a yadda na fahimta suna matukar jin tsoron sa, a murtuke ya amsa musu kamar baya son yin maganar, gabatar da ni yayi a gurinsu ya kuma faɗa musu irin yadda yake ji na a ransa. Albarka suka shiga sakawa auren tare da yi mana fatan alkhairi, Ni kuwa duk abinda suka faɗa sai nace ba Amin ba don har sai da maganar tawa tayi kokarin fitowa. Mayar da kallonsa gare ni yayi yana murmushi "malama Sa'adatu kinga dai yanxu kin shigo cikin wata sabuwar rayuwa wacce baki saba da ita ba, kuma na san ko a mafarki baki taɓa tsammanin xaki yi ta ba, dan haka ki xamto mai hakuri da kawar da kai, kuma ki xama mai biyayya a gare ni, duk abinda na umarce ki ko yayyen nan naki suka ce kiyi, ki riƙa kokari kina yi, sbd ni gidana yana da tsari da kuma doka, dole ne karami ya yiwa babba biyayya ta haka ne xamu samu xaman lafiya da cigaba. Sannan kuma ina da sharadi ba a fita unguwa sai dai da kyakkyawan dalili kamar mutuwa ko rashin lafiya, shi ma sai dai idan a gidanku abin ya faru, sannan kuma ba a xuwa asibiti ina da kokarin da nake yiwa iyalina idan suna rashin lafiya, yayana ashirin da bakwai amma dukkansu babu wanda aka taba kaiwa asibiti, kuma babu wanda aka haifa a asibiti, sannan kuma magana ta biyu bana so baƙi su rika zuwa kowane lokaci, sai lokacin da ya dace za a rika zuwa xan fada miki lokacin idan buƙatar hakan ya taso" Mayar da kallonsa yayi ga ragowar matan "Rabon kwana fa ya canja kowace mace zan rika yin kwana biyu a dakinta sabanin kwana ukun da nake yi a da, amma yanzu tunda ga Sa'adatu amarya an kawo xan fara yi mata kwana bakwai kamar yadda Musulunci ya yarda a yiwa budurwa idan an aureta, daga nan kuma xamu koma kamar yadda muka tsara, tsarin girki zai zo daga baya idan Sa'adatu ta huta" Da sauri na tashi "Bana so ka rike kwananka bana buƙatar ganinka a dakina sbd ba sonka nake yi ba, kayi harkar gabanka nima nayi nawa kada kayi tsammanin xaka same ni a matsayin matarka ta aure, ka ƙaddara ajiya aka kawo ni gidan nan kuma yadda na shigo lafiya haka xan fita, sannan kana maganar girki babu ɗan matar da ya isa na dafa masa abinci idan xasu dafa da kansu su dafa idan ba haka ba kowa ya kwana da yunwa, kana da zabin sakina ko cigaba da xama da ni wannan duk matsalarka ce" Sakin baki matan suka yi suna kallona, mamakin yadda babu shakka nake fadar abinda na ga dama, ji nayi suna magana ƙasa- ƙasa "Dama ba sonsa take yi ba ya aurota, lallai ya siyo tsaye" A fusace ya mike yana nuna ni da hannu "Za kiyi nadamar abinda kika fada min, kada kiyi xaton ko sonki nake yi, nima ba kaunarki nake ba kamar yadda bakya kaunata taimakawa ubanki nayi na aureki, ganin kina kokarin lalacewa, ko kin manta sadakar ki ya bani, ina baki shawara ki taka a hankali indai ni ne da sannu xan yi maganinki" Kallon kallo matan ke yi suna mamakin jin wannan kalaman daga bakinsa ni kuwa ko a jikina ban damu ba, da zai sallame ni ma haka nafi so a fusace ya tashi ya bar wajen nima dakina na koma. Duba kyauran dakin na shiga yi ko xan ga sakata na saka amma ban ganta ba, tura kofar nayi na koma na kwanta. Can cikin dare naji an bude kofar dakin a razane na tashi don ganin ko wane ne, malam jibo na gani sanye da............ Ku biyo ni rashin comment da rashin yabawarku shi ke karya min gwiwar typing Jeeddahtulkhair novels, dukkansa tsanani fans 1-3 Ina jin dadin comment dinku a hankali insha Allah duk xan kira sunanku ina matukar godia *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:34 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @Jeeddahtou* *21* Sanye yake da wasu kaya marasa fasali, su dai baxa a kira su da manyan kaya ba haka ma baxa a kira su da ƙanana ba, amma kusan surar jikinsa a bayyane yake sbd kayan ba masu kauri bane, kuma da dukkan alamu sun dade basu ga ruwan wanki ba, babu abinda kayan suka yi masa sai ƙara bayyanar masa da asiritaccen muninsa, sai a lokacin na ƙare masa kallo naga ilahirin gashin sa babu baki sai kaɗan amma majority din gashin ya xama furfura. ina ganin shi nayi karfin miƙewa duk da cewa akwai bacci a idona amma hakan bai sa naji kasalar miƙewa ba, a fusace na dube shi. "lafiya ka shigo min daki a wannan daren, me ya kawo ka me kake nufi da xuwanka a dai-dai wannan lokacin, tun wuri ka fita kafin nayi maka abinda ranka xai ɓaci, na riga da na faɗa maka baxa ka taɓa samuna a matsayin matarka ba ka ƙaddara cewa rainona aka kawo maka, insha Allah sai na kai budurcina gidan izuddeen" Gyara wuyan rigarsa yayi tare da matsowa inda nake warin jikinsa ne ya daki hancina miƙa hannu yayi xai riko ni, da sauri na bar wajen sbd idan na tsaya xan iya yin amai, cikin tausasa murya ya fara min magana "ki tsaya ki saurare ni Sa'adatu na lura har yanxu kuruciya na damunki, wanda ya samu miji kamata me yasa xaki tafi hangen wani saurayi daban wanda ba shi da niyyar aurenki sai niyyar lalata miki rayuwa, abinda ya kawo ni yanxu naxo ne mu yi sulhu da junanmu, mu kuma bawa juna kulawa da haqqin auratayayya, ina ganin wannan hanyar da muka dakko baxa ta bulle da mu xuwa alkhairi ba, ni da ke ma'aurata ne masu fatan ganin sun zama ɗaya har abada ki bani dama na nuna miki irin yadda nake sonki, da yadda nake jinki a cikin xuciyata" Wani kallon raini na bi shi da shi "Allah ya kiyaye nayi rayuwar ma'aurata da mutum irinka ina neman tsarin Allah, ka manta irin maganganun da ka fada min a gaban matanka, kai fa ka kira ni da yar iska karuwa wacce aka baka sadakarta, me yasa kuma yanxu ka shigo dakin karuwa baka tsoron na shafa maka cutar HIV ne tunda duk kace na gama bin maxa kafin a haɗa ni da kai, wlh da xaka burge ni da ka sake ni yanxu, don xamana da kai ba mai dorewa bane, duk son da kake min haka wata rana zaka kyale ni na auri wanda nake so" Kafin na ankara ya dako tsalle ya dawo inda nake, ji nayi ya rungume ni yana sumbatata kokarin dauke numfashi nayi sbd muddin na shaki warin jikinsa xan iya amayar da abinda ke cikina, cikin kalmomi masu taushi ya fara min magana "ki tsaya ki fahimce ni Sa'adatu duk abubuwan da na faɗa miki na faɗa ne a cikin ɓacin rai amma ba don na wukakanta ki na fada ba, na san baxa ki gane girmanki da matsayinki gare ni ba sai a wannan lokacin da xan da dandana miki dadin soyayyata, ki bani haqqina kada ki shiga sahun matan da Mala'ikun Allah suke tsinewa" kokawa muka riƙa yi sosai yana kokarin sai ya zame mayafin da ke jikina da karfin hali na tunkude shi ya faɗa baya, na fita da gudu tsakar gida ina mayar da numfashi. A gigice ya biyo ni, kallo ɗaya xaka yi masa ka gane yana cikin matsananciyar jaraba komai nasa ya canja, hanyar kofar gida na kama ina ƙoƙarin zare sakata, biyo bayana yayi yana min magana. "Sa'adatu ina xaki je a wannan tsohon daren yanzu fa karfe biyu da rabi ina hankalinki yake tafiya ne, so kike ki fita kiyi gamo da aljanu" Kuka na fara yi "ka sake ni wlh bana sonka bana kaunarka ka kyale ni na tafi duk inda naga dama, hakan ne ya fi dacewa da rayuwata, a kan na xauna a wannan kurkukun wlh gara na fita ko duniyar aljanun ne na koma na xauna" Ina gama faɗa na juya baya ina ta rusa kuka, a yadda nake ji ban ki na fita ba duk abinda zai same ni ya sameni. Jin shi nayi ya jingina jikinshi a nawa ya hade ni da bangon soron yana sake sumbatata a fusace na juyo na ture shi na wuce dakina da gudu na turo kofa, a daren haka na sha gwagwarmaya da shi duk yadda ya so yaga ya keta alfarmarta ta "ya mace Allah bai bashi dama ba, haka muka sha kokawa a ranar gaba ɗaya ban samu na runtsa ba. Washe gari da safe da misalin ƙarfe goma sha daya Rukayya taxo min, yan kayan aiki da labule umma ta bata ta kawo min, ina ganinta na rungumeta ina rusa kuka abinda ta fara tambayata shi ne babu abinda malam Jibo yayi min ko da na fada mata yadda muka yi da shi ba ƙaramin dadi taji ba. Daya daga cikin yaran gidan ne ya shigo hannun shi rike da kwanon abinci sallama yayi tare da ajiye kwanon a gabanmu, abincin karyawa ya kawo min ko da na bude kwanon ido huɗu nayi da tuwon dawa miyar kuka, a take nace ya mayar musu da abincinsu bana ci. Ina jin matan na yan maganganu a kan rashin cin abincin da ban yi ba ni kuwa hakan bai dame ni ba don ni neman dukkan abinda xai raba ni da gidan nake yi a yanzu ko na huta da jarabawar wannan mugun tsohon. A yi hakuri da kaɗan abin ne sai a hankali yau da gobe sai Allah *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:34 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Wannan shafin gaba ɗaya sadaukarwa ne gare ki uwar dakina maganin kukana AUNTY AISHA A BAGUDO kiyi yadda kike so da shi na Mallaka miki shi halak malak* *22* Kai tsaye gidan innah Rukayya ta wuce, tun a hanya take ji a ranta kamar ta fashe da kuka saboda halin da ta bar kawarta a ciki, don ba tada ikon kashe auren Sa'adatu ne amma da tuni wani labarin ake yi ba wannan ba, da sallama ta shiga cikin gidan a tsakar gida ta tarar da Baba da innah salamatu suna hira yadda taji salon zancen nasu a kan Sa'adatu suke magana, a ladabce ta gaishe su haka dai suka amsa mata ba yabo ba fallasa, har ta kama hanyar shiga dakin innar Sa'adatu Baba ya kirata, cike da ladabi ta dawo tsugunnawa tayi a gabansa gami da cewa "gani Baba". Wani kallon tuhuma ya bi ta da shi "To an yi bikin Sa'adatu dai Allah ya nufa, yadda ku ka so ba haka Allah yayi ba, kuma an yi komai lafiya an gama lafiya, kada naji kada na gani, kuma kada ki kuskura na fara ganin kafarki a gidanta, don baxa ki je ki kashe mata aure ba, an samu tayi auren da kyar ki je ki xuge min yarinya ta bujirewa umarnina da na mijinta, dama duk sha'kiyancin da ta riƙa yi kwanakin baya ke kike sakata a hanya, ban hana ki xuwa nan gidan ba amma gidan Sa'adatu dai bana so na sake ganinki a can, xumuncin da aka yi a baya ya isa idan ita taxo kwa gaisa" Jikinta a sanyaye ta tashi ba tare da tace masa komai ba, dakin innah ta shiga, shigarta ke da wuya sai ta tarar da innar ba irin yadda ta saba ganinta ba, da dukkan alamu ita ma tana cikin kewar yarta da tausayin irin rayuwar da ta shiga, har tayi sallama bata san ta shigo ba sai da taje ta dafa kafadarta sannan ta dago tana murmushi. Jefa mata tambaya tayi. "Lafiya innah, Allah yasa dai ba wani abu ke damunki ba"? ƙoƙarin hadiye kwallar dake shirin zuba daga cikin idanunta tayi duk don kada Rukayyah ta fahimci halin da take ciki, gajeran murmushi ta saki gami da gyara zamanta. "Babu abinda yake damuna Rukayya illa dai kewar Sa'adatu amma tunda na ganki yanxu tamkar na ganta ne, har naji sanyi a raina kuma kewarta ta tafi a xuciyata ina fatan xaki riƙa xuwa sa'i da lokaci kina ɗebe min kewa" Murmushi Rukayya tayi tare da ajiye abinda ke hannunta "insha Allahu innah indai wannan ne ki daina saka damuwa a ranki, kullum xan zo na ganki mu yi hirar mu ta 'ya da uwa, nima bana so ki xauna ke kaɗai ba, kaɗaici xai iya cutar da ke" Abincin da ke gefenta ta jawo ajiye shi tayi a gaban Rukayya "buɗe kici abinci nan tun daxu aka gama amma na kasa ci" Girgiza kai Rukayya tayi "nima wlh a koshe nake innah na ci abinci amma ki daure ki ci zama da yunwa ba daɗi" sun ɗan yi hirar duniya kaɗan sannan Rukayya ta dubeta. "Inna naje gidan sa'adatu yanzu ma daga can nake" Cike da kulawa ta amsa da "ya kika barota da fatan dai babu abinda ke damunta" Idanun Rukayya ne suka ciko da kwalla a hankali tasa hannu ta share ba tare da innah ta gane ba "Lafiya lau take amma ta.........." shiru tayi ta ƙasa karasawa. "Me tace miki Rukayya kada kiyi shakkar faɗa min komai" Rausayar da kanta tayi sannan ta cigaba da magana "Ta bani labarin dukkan halin da take ciki da irin ka'idojin da Malam ya kafa mata bayan tafiyarmu" Cikin nutsuwa innah ta dubeta "Dokoki kuma Rukayya dokokin menene haka?" Girgiza kai Rukayya tayi "yace baya son a rika yawan zuwa kuma ita ma baxa ta riƙa fita ba sai da babban dalili, kuma dole ta fito ta girkawa matansa da ya'yansa abinci" Hawayen da innah ke boyewa ne suka yi nasarar zuba daga idanunta jin an fama mata tabon dake cikin zuciyarta, a ranta take faɗa dama ta san za a yi haka amma baxa ta gushe ba tana yi wa diyarta addu'a har sai Allah ya sassauta mata halin da take ciki. Hankalin Rukayya ne ya tashi ganin yadda kamar innah take xubar da hawaye, wanda tunda suke basu taɓa ganin ta bayyana damuwarta ba ballantana har tayi kuka, fuskarta bayyane da damuwa ta riƙe hannunta. "Haba innarmu bai kamata wannan maganar ta saki kuka ba na faɗa miki ne don ki xage damtse wajen taya Sa'adatu da addu'a, ki kuma yi kokarin jawota a jiki da kai mata ziyara don a wannan lokacin tana da tsananin buƙatarki, dan Allah ki daina kuka innah, kukanki zai zama ƙarin damuwa a gare mu, a yanzu tafi buƙatar addu'a da kwantar da hankali fiye da wannan kukan" Numfasawa Inna tayi tare da cewa "Shikenan na daina diyata" murmushi Rukayya tayi "Yauwa innata Allah ya ƙara miki hakuri da juriya" amsawa tayi da "ameen". Cigaba da magana Rukayya tayi "innah idan kina da zanin gado ko tsoho ne ki kawo a kaiwa Sa'adatu katifarta haka take tsura ba shimfida, daxu umma ta bani labule da yan kayan aiki na kai mata, amma baxa su isheta ba sbd ba masu yawa ba" "Kai!!! Amma mun gode Allah ya ƙara zumunci Allah ya saka mata da alkhairi kice ina godiya da kulawarta gare mu, Insha Allah ina kokari xan samo mata ko a wajen saratu ne, fita ne ban samu ba shi yasa, duk ranar da na fita xan je na karbo na baki ki kai mata" Har Rukayya ta tashi xata tafi ta juyo tana dubanta idanunta kamar zasu kawo hawaye "Akwai abinda nake son faɗa miki innah amma dan Allah kada ki sa damuwa a ranki, xan fada miki ne kawai idan kina da taimakon da xaki iya bawa Sa'adatu" Fuskarta a sake tace ina jinki 'yata. "Cikin irin dokokin da malam ya kafa mata har da na rashin zuwa asibiti duk irin tsananin cutar da ke damunta, yace shi gargajiya ake yi a gidansa baxai ta taɓa bari matarsa taje asibiti ba, dan Allah ki faɗawa Baba ko xai tsawatar masa a kan haka, duk cikin dokokin da ya saka mata babu wacce ta fi daga min hankali sama da wannan" Har ga Allah innah taji ciwo a ranta sbd babu uwar da xata so ta aurar da yarta ga irin wannan mijin, kuma ya kafa mata wadannan zafafan dokokin, kawai don ba tada yadda zata yi ne amma da sai ta rushe wannan dokar, cikin jarumta innah ta fara magana. "Haba Rukayya don wannan kika tashi hankalinki kowane ɗan Adam fa da irin ƙaddararsa, kika sani ko hakan ya zama silar samun aljannarta idan tayi hakuri ta jure tayi ibada ta yiwa mijinta biyayya, kije ki faɗawa sa'adatu ta karbi wannan kaddarar hannu biyu kuma ta godewa Allah,idan ta duba tata ma da kyau a kan ta wasu, kada ta manta komai yayi zafi maganinsa Allah, kuma DUKKAN TSANANI yana tare da sauki, kija hankalin ta a kan muhimmancin yiwa miji biyayya da hadarin saɓa umarninsa, ki faɗa mata yanzu Malam Jibo a matsayin mijinta yake ta danne zuciyarta tayi masa dukkan abinda ya umarceta kuma ta gujewa saɓa umarninsa domin aljannarta tana ƙarƙashin kafafunsa sai ya daga mata zata wuce, duk rintsi duk wuya kada ta yarda ta danne hakkinsa ko yaya yake sbd sakayyar aure tun a duniya Allah yake nuna ishara, kuma kice mata ta fito cikin matansa ta kama girki kamar yadda suke yi, kuma tayi ƙoƙarin taka rawar da matan aure ke yi a gidajen mazajensu, ina rokonki kema ki ƙara nusar da ita girman miji, kuma ki koma yanxu dan Allah ki faɗa mata sakona, nasan xai yi tasiri a zuciyarta kuma xata ji saukin damuwar da take ciki a yanxu" Jikin Rukayya ne yayi sanyi sbd jin nasihohin innah gaskiya innah uwace wacce ta amsa sunanta uwa, dukkan wanda ya samu kamarta a duniya ya dace tana da xurfin hankali da tawakkali gami da yarda da dukkan abinda Allah ya tsara mata a rayuwa. Ita kanta zuciyarta tayi sanyi da taji kalamanta tashi tayi tare da yi mata sallama ta nufi gidan sa'adatu kamar yadda Innah ta umarce ta. Fitar Rukayya ke da wuya ta kifa kanta ta cigaba da zubda hawaye masu zafi, tashi tayi ta dauro alwala ta ɗauki Kur'ani ta fara karantawa don ta san shi kaɗai ne abinda zai saukaka mata damuwarta. ********** A ƙarshen katifa nake zaune na haɗa kai da gwiwa, babu komai a raina banda kewar Rukayya da innah na riga na saba a dai-dai wannan lokacin muna tare muna hira, idan bana gidanmu ina wajen Rukayya, sallamarta ce ta dawo da ni hankalina ba ƙaramin farin cikin sake ganin Rukayya nayi ba a karo na biyu, fuskata bayyane da farin ciki nake mata magana "kamar kin san tunaninki nake yi babu komai a raina banda kewarki, daxu sai naji kamar na biyo ki mu tafi gida, da fatan dai kwana xa kiyi ko?" Cike da zaulaya Rukayya ta dube ni "ya za a yi na kwana so kike malam ya koro ni xan hana shi cin amarci" Duka na kai mata "Allah ki daina wannan maganar ko mu yi faɗa" Kama hannun juna muka yi muka ƙarasa wajen da xamu xauna. Kallona Rukayya tayi "yanzu fa daga wajen innarmu nake" cikin murna nake tambayarta lafiyar innata da halin da ta barta a ciki. "Lafiyar innah kalau tana cikin farin ciki amma dai tana ɗan kewarki kaɗan" harararta nayi "da yawa take kewata ai ni aminiyar innah ce ba tada kawar da ta wuce ni" ture ni tayi "Ni din kuma fa a ina kika ajiye ni?" Toshe baki nayi "Au na manta kiyi hakuri ban miki kara ba". Mayar da kallonta tayi gare ni "Inna ta bani sakonni masu yawa kuma masu muhimmanci, haka tace min lallai na isar da su gare ki a yau ba sai gobe ba, don har nayi niyyar wucewa gida ta sake jaddada min cewa lallai naxo na faɗa miki". Bata hankalina nayi sbd na san dukkan sakon da innah xata bayar mai muhimmanci ne gare ni, kuma mai tasiri ga xuciyata sannan kuma xai taimaka wajen sassauta damuwata cikin nutsuwa nace ina jinta Faɗa min nasihohin innah tayi, Sannan ita ma taja hankalina a kan na bi dukkan abinda ta faɗa min sbd innah ita ce wacce tafi sona a duniya baxa ta faɗa min abinda zai cutar da ni ba. Kafin ta tafi sai da ta sanyaya min xuciyata da kalmomi masu kwantar da hankali kasancewar Rukayya yarinya ce mai tunanin manya da xurfin ƙwaƙwalwa, sai na nemi dukkan damuwata na rasa, bata tafi ba sai da muka yi sallar magariba, ko da ta tafi ban yi sakaci ba tashi nayi na dauki Kur'ani na fara karatu ina addu'ar Allah ya bani ikon bin abinda Innata ta umarce ni, da kaucewa sabawa malam Jibo a haka na kasance har nayi sallar isha. Kada a manta da comment da sharing Ina Godiya gareki yayata SUMAYYA MUKHTAR RABO (mrs Al-ameen)ina godiya da yadda kike kara min haske da dawo da ni hanya idan xan karkace i really appreciate *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:34 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *23* Bayan na gama karatun Alkur'ani kishingida nayi sbd ina so na ɗan huta amma duk da haka bakina bai bar ambaton Allah ba, tashi nayi na karkade katifata na shimfida zanin gadon da innah ta aiko min da shi. Sallama malam Jibo yayi tare da dage labulen dakina, ina ganin shi na tashi zaune tare da amsa masa sallamar, tsaye yake a bakin kofa bai karaso inda nake ba ya fara min magana "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" haɗe fuska nayi ban amsa masa ba, murmushi yayi "wai sai yaushe xaki daina fushi da ni Sa'adatu na zaci komai ya wuce a tsakanin mu, dan Allah ki saki ranki ki min murmushi ko zan ji daɗi, wai kin ci abinci ma kuwa naga tsakanin jiya da yau kin ɗan rame, ko sai naxo na dura miki ne" duk maganar da yake min idanuna na ƙasa ban dago na kalle shi ba ballantana na bashi amsa. Sako kafarsa yayi cikin dakin ya cigaba da yi min magana. "Sa'adatu ina so ki dafa min ruwan wanka xan ɗan watsa a jikina ko xan ji dadi, yau kin san a dakinki xan kwana ina so na faranta miki ranki sosai, shi yasa zan yi wankan nan amma banda haka babu abinda zai sa na watsa ruwa a jikina da wannan uban sanyin, da fatan kema xaki tanadi abinda zai faranta min raina sosai don na san ke ɗin ba ta wasa bace" ya karasa maganar yana wata irin dariya. Kallon shi nayi tare da mayar da kaina gefe idan yana magana a wasu lokutan kamar ba babba ba, da farko naji kamar kada na dafa masa ruwan amma sai na tuna da nasihar innah hakan yasa na tashi, duba gefena nayi tare da miƙa hannu na dakko tukunyata yar madaidaiciya hanyar fita na nufa tare da cewa "Bani hanya na wuce" murmushi yayi "Haba Amaryar malam zaki iya wucewa ai babu wani abu don jikinki ya gogi na mijinki, ni da ke duk abu ɗaya ne don an riga da an bamu junanmu, zamu iya cin karenmu babu babbaka babu abinda zamu samu sai lada" komawa gefe nayi sbd bana son kusantar inda yake a lokacin da yake min magana kasancewar shi mutum ne da bai damu da tsaftar hakoransa ba, ganin na ja da baya ne ya bashi damar sake matsowa inda nake tare da cafkoni ya mannani a kirjinsa yana sumbatar goshina ƙoƙarin kwatar kaina na shiga yi ina faɗin ya sake ni, sai kace na ƙara masa kaimi ya cigaba da shafa gashin kaina da sumbatata, cikin wata irin murya yake min magana. "Me yasa kike min haka Sa'adatu ya kike so nayi da raina idan kina min rowar jikinki, ki faɗa min dukkan abinda kike so na canja wanda zai sa ki soni, ki kuma riƙa bani kulawarki sbd ni dai ina sonki kuma har abada baxan taɓa rabuwa da ke ba duk irin wulakancin da xaki yi min" Muryata na rawa na amsa masa "ka sake ni na dawo daga ɗora maka ruwan wankan sai mu yi magana" sai da ya gama mammatsani sannan ya sake ni, numfashi na shiga mayarwa ban san lokacin da hawayen takaici ke zuba daga idona ba, taɓa min jikin da yayi ba ƙaramin bata min rai yayi ba, takalmi na saka na fita wajen da matansa ke yin girki, ɗaya daga cikin matan na tambaya wajen da itacen girki yake, fuskarta a sake ta amsa min sannan ta miko min sai da ta taya ni kunna wuta sannan ta dawo wajena ta zauna, hira ta fara min tare da bani labarin halayen mijinsu da abubuwan da yake so da wanda baya so, kaɗan-kaɗan nake bata amsa sbd bana so ma na saba da kowa a gidan fatana kawai na fita na bar musu gidansu na huta. Sai da na tabbatar da ruwan ya tafasa na surka masa sannan na wuce daki, makalewa nayi a bakin kofa tare da cewa "na surka maka ruwan wankan kaje ka kai shi banɗaki kada ya huce" ina gama faɗa na koma bakin dakin na zauna. A tsaye yake a kaina da cewa "tashi mu shiga ciki akwai abinda nake son faɗa miki" dagowa nayi na kalle shi "ka fadi dukkan abinda xaka faɗa a nan ina saurarenka" Ganin ba nida niyyar tashi ne yasa ya ɗauke ni cak ya shigar dani cikin dakin, cike da mamaki na dube shi. "Bana son irin abin nan da kake min, na faɗa maka bana so nayi maka abinda zan shiga hakkinka, amma kai kullum kokarinka kayi min abinda zaka tunxurani, ka saka ni aiki yanzu nayi abinda ka umarce ni, menene dalilin da yasa yanxu kuma zaka dakkoni, na fada maka baxan iya tafiya da kaina bane??" Kallo ya bi ni da shi, sannan ya bude baki ya fara magana "naga ba ki da niyyar shigowa ne shi yasa na dakko ki kuma ai ba haramci na aikata ba tunda jikin matata na taɓa, kuma don naga yau kamar sarauta kike ji ne shi yasa na dakko ki, kuma ma dai bana so kiyi wahalar tafiya da kanki shi yasa na aikata hakan" Shiru nayi ban bashi amsa ba, gabana ya dawo yana fuskantata, "kince xaki fada min abinda kike so na gyara wanda zai sa ki daina guduna ko?" Gyada kai nayi alamar "eh" Gyaran murya yayi to faɗa min don ina so na faranta miki, kuma ina so na samu farin ciki daga gare ki, don ki daina guduna. Baƙin cikin jin kalamar samun farin ciki daga gare ni ne yasa naƙi faɗa masa abinda nake son ya gyara, don ni gyaransa da rashin gyaransa bai dameni ba, duk yadda yaso yaji daga gare ni bai samu ba. Ganin ruwansa na neman salamcewa ne yasa ya miƙe, tare da cire kayansa gefe nayi da kaina tare da ƙoƙarin kawar da numfashina sbd warin da ke tashi daga jikinsa, babbar riga ya mayar ya fita, bar min boxes dinsa yayi a cikin dakin wanda shi ne ya ƙara taimakawa wajen ƙaruwar wari a dakin, Allah Allah na riƙa yi ya dawo ya ɗauke kayansa don ni ko taɓa shi baxan iya yi ba. Bai fi minti biyar da tafiya ba ya dawo, wasu matattaun kaya ya sanya komawa kan katifata yayi ya kwanta, ni kuma kasa na samu can kusa da kofa na zauna sai da nayi sallar isha sannan na kwanta ban farka ba sai Asuba. Fita nayi na daura alwala na dawo daki na fara tashinsa, duk maganar da nayi masa sai ya nuna bai fahimci abinda nake nufi ba, har sai da na fita waje na samu ruwa na ɗan shafa masa sannan ya bude ido, cikin nutsuwa nace masa "lokacin sallah yayi" Amma ga mamakina sai naga ya mayar da kansa ya cigaba da bacci abinsa, duk ƙoƙarin da nayi wajen ganin ya farka yayi sallar Asuba bai tashi ba sai wajen bakwai na safe yayi sallar Asubah. 'Dansa ya aiko ya kawo min koko da kosai bayan yaron ya fita ya shigo, fuskarsa a d'aure yake min magana "kada ki kuskura ki sake yi min katsalandan a cikin lamarina, daga yau sai yau kada ki sake tashina idan ina bacci, kece xaki faɗa min abinda ya dace da ni, hankali kika fi ni ko girmata kika yi?? naga dai duk karatun da kike takama da shi a wajena kika same shi, to nayi miki kashedi na karshe idan kika sake min haka xaki ga ɓacin raina" yana gama faɗa ya fita don ko abincin karyawar sa bai tsaya ya karba ba. Ban yi mamakin jin hakan daga gare shi ba, don dama tun muna makaranta idan lokacin sallah yayi baya bata muhimmanci sai dai ragowar malamansa su yi shi kuwa ko a jikinsa. *************** Zaune Rukayya take tana nazarin irin rayuwar da kawarta ta tsinci kanta a ciki, tana cikin tunanin ta tuna alkawarin da ta yiwa Sa'adatu na samun izuddeen ta bashi hakuri dangane da abinda ya faru, wayarta ta ɗauka ta shiga neman numbersa ta fara kira. A xaune yake yana kallo yaji shigowar kiran Rukayya, yana dubawa yaga bakuwar number da har baxai ɗauka ba, sbd baya ɗaga number da bai sani ba, shahada yayi ya karata a kunnensa tare da yin sallama. Da farko bai gane ita bace sai da tayi masa bayani ita ce, kasancewar wayarsa ta fadi tun bayan fitowarsa daga police station, bayan sun gama gaisawa ne ta fara yi masa magana cikin murya mai taushi. "Sa'adatu ta bani sako na fada maka" Jin an ambaci Sa'adatu yasa ya gyara zama tare da bata hankalinsa dari bisa dari don jin sakon da ya fito daga wajen Sa'adatunsa. Fuskarsa a sake ya amsa mata da "ina saurarenki kawarmu" "Na san kai Musulmi ne izuddeen kuma ka yarda da ƙaddara ka yarda da cewa Allah shi ke bayarwa kuma shi ke hanawa, kuma dukkan abinda bai zo hannunka ba to ba naka bane, kuma dukkan abinda yaxo hannunka rabonka ne duk rintsi duk wuya babu dan Adam din da ya isa ya kwace maka" amsa mata yayi "da haka ne Rukayya ina jinki". Wani abu taji ya taso mata na baƙin ciki amma sai tayi ƙoƙarin mayar da shi sbd bata so ta fiye saka damuwa a ranta. "Na san ba lallai ne kana da labarin abinda ya faru ba ko?" Da sauri ya amsa mata da "Eh" yana da labarin dukkan abinda ya samu Sa'adatu sbd har gida aka xo aka faɗa masa labarin, ya nuna mata bai sani bane sbd bai sani ba ko wani sabon abin ne ya taso. A hankali ta cigaba da magana. "Bayan zuwan nan da yan uwanka suka yi a kan maganar aurenka da Sa'adatu, a ranar mahaifinta ya daura mata aure da Malam Jibo, don har an kaita ma yau kwananta biyu a gidan, shi ne tace na sameka na faɗa maka kayi hakuri ba da son ranta hakan ya faru ba, kuma idan ka samu mace kayi aure, tace ka kasance mai yawan yi mata addu'a kuma kada ka manta da ita da irin soyayyar da take maka" Numfashi mai xafi ya furzar muryarsa na rawa kamar xai yi kuka yake magana. "ki faɗa mata baxan manta da ita ba har abada, duk inda na kasance a rayuwata, ki mata albishir ina sonta kuma xan jirata baxan taɓa aure ba har sai ta fito ko 'ya'ya nawa ta aura, kuma ki faɗa mata ta kasance mai biyayya ga mijinta insha Allah sai mun mallaki junanmu" Kuka ya fara yi sosai, wani ciwo sabo Rukayya ta tabo masa, haka Rukayya ta kashe wayar ita ma xuciyarta cike da tausayin masoyan guda biyu. Kada a manta da comment da sharing *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:34 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *24* Yau kusan satina biyu a gidan malam Jibo har na fara canjawa daga kamannina na Sa'adatu xuwa wani sunan daban, saboda tsabar wahalar da nake girba na girki da aiyukan gida, kusan girkin mutum talatin nake yi a duk ranar girkina, sannan kuma babu mai taya ni ko iza wuta duk da cewa gidan akwai yan matan da xasu iya taimaka min da wani abun, gani ba gwanar iya tuka tuwo ba haka dai na daure na koya, wata rana yayi kyau wani kokacin kuma ba yabo ba fallasa, ko xan mutu da aiki babu mai taimaka min sai dai idan na gama a xo ci karshe ma yaran gidan su yi min rashin kunya haka nake kyale su ba tare da na tanka musu ba, abinda yasa bana damuwa da abinda suke min sbd nasan insha Allah xamana ba mai tabbata bane a gida. Taimako ɗaya Allah yayi min duk tsayin satukan da na shafe a gidan malam Jibo, Allah bai bashi damar cimma burinsa na sanina a 'ya mace ba, sai dai mu sha kokawa ya gaji ya kyale ni. Da yake yau ba a dakina yake ba shi yasa bani damar samun isasshen bacci, don matuƙar yana dakina ba ni da kwanciyar hankalin kwantawa nayi bacci kamar kowa, sbd fargabar kada ya min illa ina bacci, tun bayan da nayi sallar asuba ban farka ba sai wajen sha biyu don ko karyawa ban yi ba, tashi nayi a hankali na nufi banɗaki ina isa wajen naji wani wari na tasowa a daddafe na kwara ruwa na ɗan wanke shi sbd baxan iya amfani da shi a haka. Zan shiga kenan naji ana min magana waiwayar da xan yi naga uwar gidan Malam Jibo ce a tsaye tana ƙare min kallo, nima kallonta nayi tare da sauraren jin abinda xai fito daga bakinta, sai da ta gama ƙare min kallo tsaf sannan tayi magana. "Na fuskanci tunda kika shigo gidan nan kike mana gani-gani kin wi fitowa cikinmu ki sake tamkar wacce kike ƙyamar mu da yayanmu, yanxu kin xo shiga banɗaki kin hau toshe hanci kamar waɗanda xamu shafa miki cuta, alhalin mun san gidanku mun san tarihinki gaba ɗaya ke ba yar kowan kowa bace, kamar yadda labari ya tabbatar mana mannawa mijinmu aka yi, idan kinga baxa ki iya hakuri da yadda muke ba, xaki iya tafiya dama mu ba a son ranmu aka dakko mana ragowar karuwanci aka kawo mana gida ba" Kallonta nayi zuciyata cike da mamakin jin waɗannan kalaman daga gareta, har nayi niyyar mayar mata da martani sai kuma na fasa, sbd bai kamata karya tayi min haushi ba ni kuma rama, kuma ko ba komai akwai banbanci mai yawa tsakanina da ita, wannan yasa na kyaleta na cigaba da abinda nake yi. Daya daga cikin matan nasa ce ta taso tana mata magana. "Haba maman biyu wannan abinda kika yi bai kamata ba, kuma zubar da kima ne da mutunci, kuma ko yanxu kin xubar da girmanki a idonta wanda hakan bai dace da ke ba, tunda yarinyar nan ta shigo gidan nan bata yiwa kowa abinda xata bata masa rai ba kullum kokarin kyautata mana take yi, kuma tsakani da Allah ko mu idan xamu shiga banɗakin nan sai mun wanke sbd mutane ne daban daban suke shigarsa laifi ne don mutum ya tsaftace wajen da xai biya bukatarsa, gaskiya bai kamata ba kuma hakan da kika yi xai bawa yaran mu damar rainata, ko me tayi a baya bai kamata ki goranta mata ba tunda dai Allah ta yiwa ba ke ba kuma idan yaga dama dai yafe mata" jikinta ne yayi sanyi da jin kalaman yar uwar tata na lura duk kunya sai da ta kamata, shiga banɗakin nayi na kyale su tana ci-gaba da yi mata faɗa ni kuwa ko kadan abin bai bata min rai ba sbd na san ban aikata abinda ake zargina da shi ba. A tsantsame nayi wankan duk ina jin kyankyami, kasancewar masan gidan a cike yake fal da kashi gashi ko murfi basu saka masa ba, ga iyayen kyakyasai da suka mamaye shi abin dai sai wanda ya gani, don kawai bana son kazanta ne amma da baxan iya wanka a wannan banɗakin ba ko don kada na kwashi wata cutar. Ina gamawa na shiga daki na saka kayana har da hijab kamar dai mai shirin zuwa unguwa, fitowa nayi tsakar gida na shimfida sallayata na zauna kasancewar garin ana ɗan zafi. Daga soro na jiyo murya kamar ta ya salim, tsayar da hankalina nayi don sauraren muryar mai maganar, a karo na biyu kuwa naji ya ambaci sunana da sauri na tashi na nufi soron Ina ganin shi wasu hawaye masu xafi suka riƙa xubo min sai naga kamar innata na gani sbd ya salim yana cikin mutanen da suka gwada min so, sai na rasa kukan me nake yi kukan murna ne ko na baƙin cikin halin da nake ciki. Hankalin shi a tashe ya dube ni "ki daina kuka sa'ar mata kada kisa hankalina ya tashi ziyara na kawo miki domin kiyi farin ciki ba na xama silar sanyaki a damuwa ba, sai da nayi kukana sosai duk lallabanin da yayi bai sa nayi shiru ba sai da nayi mai isata sannan na hakura. Cikin gida na shiga na dakko masa tabarma kasancewar Malam Jibo baya bari namiji ya shigar masa gida duk kankantarsa, wannan yasa na dakko masa tabarma na shinfida masa. Waje ya samu zauna muna fuskantar junanmu, tambayar farko da ya fara min shi ne babu abinda yake damuna kuma babu abinda malam Jibo yake min wanda yake kuntata min.? Nan da nan naji idanuna xasu kawo hawaye amma sai nayi ƙoƙarin shanyewa sbd bana son na d'aga masa hankali girgixa kai nayi alamar babu komai. Tsare ni yayi da ido yana sake tambayata "ki fada min gaskiya sa'ar mata wane ne zai kalle ki yace babu abinda yake damunki, ko makaho idan ya dube ki zai fahimci akwai damuwa a tattare da ke, dubi fa yadda kika yi baƙi kika rame, sati biyu kacal da aurenki amma duk yanayinki ya canja, kin xama kalar tausayi" Share guntun hawayen da ke shirin fito min nayi "babu abinda yake damuna sai kewarka kai da innah, sai kuma aikin da nake yawan yi wanda ya fi karfina shi yasa kaga na rame" A xubure ya dube ni "aikin me kike yi da har yake shirin yi miki illa haka?" Rausayar da kaina nayi "aikin girki ne na kusan mutum talatin shi yasa kaga na rame" Kallon tausayawa yake bi na da shi "kiyi hakuri Sa'adatu komai mai wucewa ne wata rana xaki ji dadi har ki bada labarin irin wannan halin da kika shiga" Sake jefo min tambaya yayi "amma kina samun abinda kike so kina ci ko? dan na sanki sari ba gwanar cin abinci bace kin fi son kiyi ta xama da yunwa, wai ke kada kiyi kiba" Har sai da ya bani yar dariya. A takaice na bashi amsa da "bana iya ci" kallon mamaki yake bi na da shi "bakya iya ci kuma to sbd me, kinga irin halin naki ko" Kaina a sunkuye nace "Abincin da aka dafa da daddare shi ake ci safe da rana sai wani daren ake sake yin sabon girki shi yasa bana iya ci" Na lura da ya salim kamar kuka yake son yi amma ya daure, a hankali ya fara min magana "Allah sarki sa'ar mata Allah yana tare da ke kuma zai kawo miki mafita" Hannu yasa a aljihu ya miko min "karbi wannan duk lokacin da aka yi abinda bakya so ki siya abinci ki ci wannan zaman baxai yiwu a haka ba, sbd Allah ne kaɗai yasan ranar fitar ki daga gidan nan tunda aure rai ne da shi, sai lokacin da Allah ya ƙare shi xai mutu, ki cigaba da hakuri da kuma jajircewa da ibada da addu'a nima xan taya ki" Gabana ne ya fadi jin yana kiran Allah ne ya san ranar fitata daga gidan Malam Jibo, sai da na ɗan yi nazarin maganar na wasu lokaci sannan naga gaskiya ya faɗa min. Cike da ladabi nasa hannu na karbi kuɗin tare da cewa "na gode ya salim Allah saka da alkhairi Allah ya bude maka hanyoyin samu, amma fa kaima ba kudi ne da kai ba me yasa ka bani kuɗi masu yawa haka, kada ka karar da yan canjin naka" Cike da kulawa yake min magana "duk abinda nayi miki wajibina ne kuma ban yi asara ba Sa'adatu fatana dai Allah ya kawo miki ƙarshen wannan matsalar da kike ciki, insha Allah kuma sai kin ji dadi a rayuwarki, kuma ki kwantar da hankalinki da yardar Allah kin kusa fita daga wannan kurkukun da aka kawo ki" Wannan kalmar da ya faɗa karaf ta shiga kunnen malam jibo ashe ya dawo ma basu sani ba sai kawai ganinsa suka yi a kansu yana musu masifa. "Dama kaine munafukin da kake xuwa har gida kana hure mata kunne kada tayi zaman aure da ni ko, shi yasa na rasa duk wani farin ciki daga gareta, take wulakanta ni tare da tozartar da son da nake mata duk gwanintar da xan yiwa yarinyar nan baxan taɓa burgeta ba, to wallahi yau Allah ne kaɗai xai raba ni da kai, har gidanku xan kai ka naji idan kwangila ma ka karbo daga hannun wannan ɗan iskan yaron don kayi sanadin raba aurena da Sa'adatu" Kafin ya salim yayi magana har ya sheke shi ya fara ƙoƙarin dukansa, Kokawa suka shiga yi da ya salim, wuyan rigarsa ya kama yana xaginsa shi dai ya salim bai tanka Masa ba sbd yasan mutuncin na gaba da shi, duk abinda ya faɗa masa sai dai ya bi shi da kallo kawai. Gidan su Sa'adatu suka nufa don gayawa mahaifinta abinda salim din yayi masa. A yi hakuri ba kullum xaku rika ganin post dina ba sbd wasu dalilai Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:34 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *25* A soron nake tsaye kamar wacce aka kafe na kasa komawa cikin gida, duk fargaba da tsoro sun mamaye zuciyata addu'a ɗaya nake yi Allah yasa kada malam Jibo yaje ya fadi karya da gaskiya ya kunno min wani shirrin a wajen Baba, ban iya komawa cikin gida ba a soron na tsaya don jin abinda zai dawo min da shi, fatan da nake yi Allah yasa wannan zargin da yayi mana ya zama silar rabuwar auren gaba ɗaya. Jan salim ya riƙa yi tamkar ya kamo barawo shi kuwa bin sa kawai yake kamar raƙumi da akala. Cikin soron gidan su suka shiga, sallama malam jibo ya shiga yi, jin muryarsa da Baban Sa'adatu yayi shi ne dalilin da yasa ya fito da sauri don duk lokacin da yaji malam Jibo yana irin wannan sallamar yasan ba lafiya. Ganin shi riƙe da kwalar rigar salim ne ya bashi mamaki gami da tambayarsa ko lafiya, yana huci ya fara bashi amsa. "Wlh yaron nan naku ɗan kwangilar kwartanci ne, masifa yake ƙoƙarin kunna min a gidana, shi ne yake ƙoƙarin kashe min aure, yanzun nan daga wajen Sa'adatu yake yaje yana xugata, a kan ta rabu da ni ban dace da rayuwarta ba, har faɗa yake idan tana son guduwa xai bata mafakar inda zata buya, kuma zai bata kuɗin motar da zata tafi" Wani kallo Baban Sa'adatu ya bi salim da shi tare da girgiza kai. "tabbas duk abinda aka zargi yaron nan da shi baxan yi musu ba Malam, sbd tun tana gida shi ne mai shige mata gaba ta rika yin shashanci" Cikin fushi ya shiga nuna Salim da yatsa "Wannan ita ce tarbiyyar da muka baka ko salim? dama duk abinda Sa'adatu take yi kaine kake goya mata baya ko, cin amanar da xaka yi min kenan me nayi maka kake bina da sharri haka? Allah ya isa tsakanina da kai" yana ƙarasa fadar haka ya shige cikin gida. Bangaren su salim ya shiga inda ya kira mahaifinsa, ganinsa a gigice ne yasa ya fara tambayarsa amma bai saurare shi ba ballantana ya bashi amsa. Hankalinsa a tashe ya sake dubansa "lafiya yaya na ganka a hargitse haka Allah yasa dai ba wani abin ne ya taso ba, don naga kamar baka cikin nutsuwarka" Kofar fita ya shiga nuna masa "mu je soro kaga irin maganar da salim yake shirin dakko mana muna zaman mu lafiya" jin ya ambaci salim ne ya sa ya fita da sauri hankalinsa a tashe ko takalmi bai saka ba ya fita. Har yanxu dai malam Jibo rike yake da wuyan salim yaƙi sakinsa, ba don bazai iya kwacewa bane yasa ya kyale shi kawai don yana gani mutuncin wanda ya girme shi ne. Cike da mamaki mahaifinsa yake magana "Lafiya malam Jibo wani abu salim yayi maka haka naga ka riƙe masa wuyan riga, Allah yasa dai ba aika-aika yayi maka ba" Gyara tsayuwa yayi fuskarsa a murtuke ya fara magana "Na Kama su suna lalata shi da Sa'adatu, kaga abinda yayi yafi ƙarfin mu kira shi da aika-aika sai dai lalata" Cike da tashin hankali salim ya dubi malam Jibo "ka rantse da Allah abinda ka kama mu muna yi kenan, da girmanka ka rika karya kaji tsoron Allah duk abinda ka faɗa yana kallonka kuma Mala'iku suna rubutawa, kuma zaka tsaya ranar shaida" Daka masa tsawa mahaifinsa yayi "yi min shiru mutumin kawai kada na sake jin bakinka, na shiga ban dauka ba ai bata fidda barawo, me yasa kaje masa gida? da baka je ba zai ce kayi masa haka ne, ko kai kaɗai ne ɗa a cikin gidan nan, duk abinda ya faɗa dole mu yarda tunda daga gidansa ya kamo ka" Sauke ajiyar zuciya Baban Sa'adatu yayi "gaskiya yarinyar nan ta cika lalatacciya, dama abinda take yi kafin aure shi ne bayan tayi auren ma baxa ta sallata ba sai ta ɗora daga inda ta tsaya, amma kuwa yarinyar nan bata ji daɗin halinta ba, malam Jibo kada kaga laifin salim ka fara ganin laifin Sa'adatu sbd ita ce ta gayyato shi yazo mata, da bata kira shi ba baxai zo ba, idan kayi aiki da hankali xaka ga cewa sai da ta lura baka nan sannan ta kira shi, ya zama dole na ɗauki mummunan mataki a kan yarinyar nan sbd idan nayi sake ƙarshe ni xata jawowa abin kunya" Cikin nutsuwa mahaifin salim ya dube shi "A'a yaya ba haka za a yi ba a bi abin nan a hankali, sbd abu ne da yake buƙatar bincike ka bar min komai a hannuna zan san yadda za a yi" kallon salim yayi tare da cewa "tashi ka shiga ciki ka jira mu da irin hukuncin da zamu yanke maka" Waje suka samu suka tsugunna gaba ko nutsuwar dakko tabarma basu samu ba, a hankali mahaifin salim ya fara tambayar malam Jibo "Naji dukkan abinda ka faɗa kuma bana goyon bayan yayana a kan abin nan da ya faru, tabbas basu kyauta maka ba, kuma ya keta maka haddi duk da kasancewarsa ɗan uwanta, bai kamata ya shigar maka gida kai tsaye ba tare da ya nemi izninka ba, tunda dai ba muharraminta bane, Amma ina mai baka hakuri zamu ɗauki matakin da ya dace a kansu" Girgiza kai malam Jibo ya shiga yi "Babu wani mataki da zaka ɗauka ni xan ɗauki mataki da kaina sbd ni aka ciwa zarafin kuma ni aka zalunta" A tsorace mahaifin Sa'adatu ya kalle shi "Dan Allah kayi hakuri malam kada ka sakar min 'yata, idan ta dawo gida abinda zata yi sai ya fi haka, duk matakin da ka ɗauka a kanta xan amince kuma xamu yi biyayya, amma dan Allah banda na saki kayi mata hakuri tunda wannan shi ne karo na farko" A wulakance ya dube su "shikenan naji amma abinda yake tayar min hankali shi ne, kada ta riƙa fita yawon banxarta ƙarshe ta kawo min cikin da ba nawa ba gida, tunda dai ni tunda nake da ita ko hannunta bata taɓa bari na taba ba, ballantana a kai ga auratayya" Kallon kallo suka shiga yi shi da mahaifin salim, a sanyaye mahaifin nata yace "ya aka yi ka kyaleta tana wannan shashancin, dama akwai abinda take nufi dole ta hanaka hakkinka, yau din nan xan je har gidan na bata kashi sbd naga kamar akwai abinda yake mata yawo a hankalinta" Sai da suka gama tsara yadda za a yi wa Sa'adatu hukunci, sannan suka rankaya gidan tare da shi da malam Jibo shi kuma Baban salim ya shiga gida. Yadda nake a soron dai ban matsa ba ina nan ina tunanin irin yadda salim zai fuskanci matsala daga wajen iyayenmu, ganin basu juyo bane yasa hankalina kwanciya tare da komawa daki, ina mai addu'ar Allah ya kare salim daga sharrin malam jibo. Komawa ta daki ke da wuya naji sallamar malam mutan gidan ne suka riƙa xubewa suna gaishe shi, tare da yi masa sannu da dawowa, daga can kuma naji murya kamar ta Babana kafin na tashi na fito naga ko waye har sun iso cikin dakina. Ina ganin shi na zube kasa ina masa sannu da zuwa, kallon da yake bi na da shi ne ya tabbatar min da cewa ba lafiya ce ta kawo shi ba, tashi nayi na koma gefe cikina duk ya ɗuri ruwa sbd ban san da abinda suka xo min ba. Malam Jibo ne ya dubi Baba "To kaga dai abinda nake fada maka malam Salisu haka take shigo min da karti kala-kala cikin gida idan taga bana nan na fita harkokina, ko 'ya'yana ka tambaya abinda xasu faɗa maka kenan, yau ma Allah ne ya toni asirinsu ta ajiye kwarton nata a soro" A tsorace na dube shi xan fadi gaskiyar abinda ya faru har na bude baki xan yi magana Baba ya dakatar da ni alamar nayi shiru, haka naja bakina na kulle sai da ya gama jero masa karya da gaskiya sannan ya mayar da kallonsa gare ni. "Wannan ita ce sakayyar da xaki min Sa'adatu, dama ashe na kashe miciji ne ban sare kansa ba ina ganin na aurar da ke xan samu kwanciyar ashe tsuguni bata ƙare ba, ke a duniya ba ki da wani buri wanda ya wuce ki dakko min magana, yau xaki gane kuskuren abinda kika yi min, indai ni na haifeki yau sai ranki ya ɓaci" Kafin na ankara ya dakko sabuwar bulala ya hau dukana da ita, malam Jibo na ganin haka ya fita yana murmushi, dukana yake ko ta ina iya karfinsa, duk kukan da nake yi bai saurare ni ba sai da yayi min laga-laga kamar baxai bar ni da rai ba, sai da yaga komai na jikina ya daku har Ina kokarin suma sannan ya kyale ni" Hango kishiyoyina nayi su da ƴaƴansu cike a kofar dakina, duk sun zo kallon abinda ke faruwa, duk wanda yaji ance Babana ne yaxo hukunta ni sai dai kaga ana kama baki ana mamaki, kowa tunanin girman laifin da nayi masa yake da har yaxo gidana cikin kishiyoyina yake dukana a gabansu. Kiran malam Jibo cikin rawar jiki ya shigo yayi fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonsa, da alama yaji daɗin hukuncin da aka yi min. Fuskar Baba a daure ya dube ni "wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe a gare ki, idan na sake jin wani abu ya bullo tsakaninki da wannan bawan Allahn ni da ke ne, kuma ki saka a ranki matuƙar kika kashe wannan auren babu ni babu ke, kada ma ki nuna kin sanni ballantana har ki kirani da mahaifinki" Mayar da kallonsa yayi ga malam Jibo "Gata nan ka kula da ita ka saka mata takunkumi kada ka sake bari ko soro ta leka kuma duk wanda yaxo wajenta na baka damar ka koreshi tunda ta nuna ita ba yar mutunci bace" Jinjina kai ya shiga "madalla na gode malam Allah ya kara girma" sake kallona Baba yayi "mijinki ya bani labarin har yanxu baki bashi hadin kai ba to wlh gobe nake so yaxo min da labari mai kyau, idan naji sabanin abinda nake tunanin xan sake dawowa na ƙara baki kashi, tunda naga alama kunnen kashi gare ki" Duk maganar nan da suke ina sunkuye ina ta gunjin kuka hawayen ma sun ƙafe saboda tsabar xafi da axabar da nake ji, ilahirin jikina duk a fashe yake na rasa gane kan irin wannan rayuwar da nake yi, kamar Babana baya sona haka nake gani don babu uban da xai iya yiwa yarsa wannan toxarcin da yayi min a gaban Ya'yan miji da kishiyoyi. Fita suka yi tare suka barni cikin yanayi mara dadi Masoya kada ku damu da halin da Sa'adatunku take ciki ku yi hakuri haka tsarin labarin yake shi yasa ma na kira shi da Dukkan tsanani insha Allah saukin na nan xuwa na tabbatar da cewa xaku yi farin ciki nan gaba. Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:34 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *26* Bayan tafiyar su Baba da kaɗan, 'ya'yan Malam Jibo suka riƙa shigowa dakina sahu-sahu suna tsokanata, haka na kasance a daki babu damar na fita tsakar gida sai uwar gidan ta riƙa yada min da magana, ko nayi niyyar ramawa sai na fasa sbd duk abinda aka min mahaifina ne ya fara zubar min da mutunci don haka ko me suka faɗa bana ganin laifinsu. Bayan na dawo ɗaki komawa nayi na kwanta sbd jirin da ke dibana, ina kwanciya na tashi sbd kwanciyar naji ba daɗi, duk na takura ina ta fama ciwon da ke jikina, don haka na fara ƙoƙarin tashi zaune amma na kasa, duba jikina na shiga yi sai naga duk jini ya bata min kayana, ina so na tashi na canja wani amma na kasa, kukana ne ya ƙara tsananta, addu'ar Allah ya duba halin da nake ciki ya kawo min mafita na riƙa yi. A ranar wuni nayi ban fito ba ko alwala a daki na riƙa yi sbd bana son na fita a faɗa min abinda zai sosa min raina, a zaune na riƙa sallah sbd zazzaɓi mai tsanani da ya kamani, shi kuwa malam Jibo tunda ya fita ban sake ganinsa ba, har zuwa wayewar gari kasancewar ba a dakina yake ba, ko shigowa ya duba halin da nake ciki bai yi ba, sai dai naji muryarsa a tsakar gida yana wasa da dariya da matansa. Haka na kasance cikin kunci da damuwa musamman idan na tuna innata da yadda aka raba ni da ita, aka kawo ni wannan kurkukun, ga rashin abinci mai kyau uwa uba kuma ba kulawa, kullum ƙoƙarinsa ya za a yi ya sanya ni cikin halin baƙin ciki da damuwa. ************ Ko da Baban Sa'adatu ya koma gida bai samu ganin Salim ba, kafin ya koma ya tarar da shi har ya gudu sbd yana jin tsoron karansu da malam Salisu, duk jiransa da yayi don ganin ya same shi ya ci masa mutunci Allah bai yarda ba. Salim bai sake dawowa ba sai washe gari, cikin sand'a yake shiga cikin gidansu, kai tsaye bangaren su ya nufa, a tsakar gida ya ci karo da mahaifinsa yana alwala, Sallama yayi tare da tsugunnawa ya gaida shi, wani kallo ya bi shi da shi tare da kiran sunansa. "Salim jiya a ana ka kwana don na duba dakinka jiya, ban ganka a cikin yan uwanka ba, faɗa min inda kaje ka kwana" Motsa baki ya shiga yi kamar yana son yin magana amma ya kasa sbd bai san abinda xai ce da mahaifin nasa ba. Tsare shi yayi da ido ya sake tambayarsa "Ba magana nake maka ba, ka faɗa min inda kaje don baxan amince ka riƙa kwana a wani waje daban ba?" Kansa a sunkuye ya amsa "A gida na kwana Baba amma ban shigo da wuri bane shi yasa baka ganni ba" a fusace yace "Ni xaka rainawa hankali, ka riga ka sani bana son karya, ya zaka ce a gida ka kwana alhalin na leka dakin da kike kwana ba adadi naga baka nan, ka faɗa min gaskiya tun kafin na saukar maka da fushina" Shafa fuskarsa yayi "A dakin abokina na kwana" Ajiye butar da ke hannun shi yayi ya matso kusa da shi "yanzu kuma irin lalacewar da kake son yi kenan, banda laifin da kayi jiya yanxu kuma kana ƙoƙarin sake yin wani, me kake son xama ne Salim ka tuna kai fa ba ƙaramin yaro bane da za a ce kullum sai an fada maka abinda ya dace a kayi, ya kamata ka shiga hankalinka wannan ba rayuwa bace" Kansa na ƙasa ya fara magana "kayi hakuri Baba insha Allah baxan sake yi maka irin wannan ba" Girgiza kai yayi "zancen kenan kullum baxa ka ƙara ba amma gobe ma sai ka sake yi Allah yasa dai ka gyara halinka don bana so ka riƙa dakko min magana kullum" Tashi yayi zai shiga daki ya gaida mahaifiyarsa kafin ya shiga har ta fito tana faɗin "Hmm sannu Salim sannu da aika-aikar da kayi, ka janyo min xagi da abin faɗa a tsakar gida, yanxu abinda kayi ya dace kenan ka daka ta wannan yar iskar yarinyar xata lalataka, tunda ita ta kwashe kayanta daga gaban Annabi menene na zuwa inda take.." Saurin dakatar da ita Baban salim yayi "ke me yasa kullum bakinki baya son furta alheri ne, Sa'adatu 'yata ce duniya da lahira kamar yadda salim yake ɗana don haka ki guji furta munanan kalamai a kanta" Shiru tayi ta kasa cewa komai sbd tana tsoron mijin nata duk gutsuri tsomar da suke yi ita da innah salamatu bai sani ba, amma da ya sani da tuni ya dade da taka mata burki. Nuna salim yayi "tashi kaje wajen yaya yana son yi magana da kai, kuma ka bashi hakuri don ka fusata shi sosai" Tashi yayi ya fita bai bi ta kan kiran da Baban Sa'adatu yake yi masa ba ya wuce wajen harkokinsa. ************ Kwance nake ina ta juyi yau da wani matsanancin ciwon ciki na tashi ga zazzaɓi da ke damuna, tun bayan da Baba ya dake ni ban ƙara samun sauki ba kullum ciwon gaba-gaba yake yi gashi ban sha magani ba ballantana nasa ran warkewa, shi kansa malam jibon tun daga wannan lokacin ban ƙara sa shi a idona ba, yau kusan kwana uku kenan, sautin nishin da nake yi ne ya fita har tsakar gida, shi ne dalilin da yasa ɗaya daga cikin matan nasa ta shigo dakina don ganewa idonta halin da nake ciki. cike da tashin hankali ta dube ni "lafiya Amaryarmu?" da yake da wannan sunan take kirana, ban iya buɗe baki na faɗa mata abinda yake damuna ba sbd ni kaɗai na san irin radadin da nake ji, nuna mata cikina na shiga yi. Cike da kulawa tace min "Sannu Allah ya baki lafiya watakila karuwa muka samu, Allah ya inganta" Ganin yadda nake ƙoƙarin fita daga hayyacina ne yasa ta fita a gigice, kai tsaye soro ta nufa tare da shiga cikin shagon da yake zama, lekawa tayi tare da faɗa masa cewa ba ni d lafiya, kuma ina cikin mawuyacin hali, rokonsa tayi ya bata dama zata kaini asibiti. A kaikaice ya dubeta "me yasa wani lokacin ba ki da lissafi ne Talatu? Kina so ki riƙa yi min shishshigi a harkar gidana, sai kace kin fi ni sanin dai-dai, shekarar ki nawa a gidan nan baki taɓa ganin an kai wani asibiti ba, kin san dai halina kin san tsarina ba zuwa wajen likita duk ciwon da xai kama mutum, tunda ina da maganina a gida babu wanda ya isa ya canja min tsari, amma ke kullum ƙoƙarinki shi ne kiyi min gyara a al'amurana sai kace ke kike aurena, ita yar gwal ce da baxa ta sha irin abinda nake haɗa muku ba, ko kuma zane ta fi ku a fuska, kije ki ƙara jaddada mata ba a taɓa zuwa asibiti a gidana ba kuma baxa a fara ta kanta ba". Wani kofi ya dakko ya barbaɗa garin magani sannan ya kafa kansa a bakin kofin, babu wani abu da yake karantawa banda tofa uban miyau da yake yi, miƙa mata yayi cike da ladabi tasa hannu ta karba tare da cewa "mun gode malam Allah ya ƙara hasken makaranta" cike da ƙasaita ya amsa da "Ameen" Jikinta na rawa ta shigo dakina kafin tazo har na suma, da gudu ta sake fita ta kira ragowar matan gidan, ruwa suka shiga yayyafa min tare da jijjigani amma kamar dutse na kasa farfaɗo wa, sake komawa wajen Malam Jibo tayi ta sanar da shi cewa na suma a yatsine ya kalleta. "Wai ke me yayi miki zafi da yarinyar nan ne, ke kika kawota gidan nan ko ni na kawota, naga kina xakewa da yawa a kan al'amuranta ko kina so ki nuna min cewa kema halinku ɗaya da ita?? Tun wuri ki fita daga idona ni na kawota kuma ni na san irin hukuncin da zan mata" Hawaye ne suka fara xuba a idanunta cikin kuka take masa magana "ba ina nufin na fika sonta bane sai dai hakkinmu ne mu kula da ita da dukkan abinda ya sameta, sbd kaine a haqqu da ka kula da lafiyarta tunda har ka barota da wajen iyayenta" Tsawa ya daka mata "ki kama bakinki ki kuma san me xaki riƙa faɗa min idan ba haka ba kema xaki shiga irin tarkon da ta shiga" jikinta a sanyaye ta kyale shi ta shiga cikin gida, tambayarta suka shiga yi ina malam, labarin yadda suka yi da shi ta kwashe ta faɗa musu. Uwar gidan ce ta fita da kanta ta masa magana, sai da yaja lokaci sannan ya shigo, yana tafe yana baza babbar riga buɗe labulen ɗakin yayi ya shiga. Xama yayi a ƙasa yana tofa mata miyau duk dakin ya rikice da warin bakinsa, babu abinda yake karantawa sai tofa miyau. A yi hakuri da kaɗan Kada a manta da comment share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:35 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Yan uwa na gode da addu'o'inku Allah ya bar xumunci* *27* Yau tunda innah ta tashi taji jikinta babu daɗi babu komai a zuciyarta sai tunanin Sa'adatu, ji take kamar ta tashi ta tafi gidan nata don taga halin da take ciki, amma kuma sai taji bata son xuwa sbd kada ta janyowa kanta abinda za a zo ana maganganu a kansa, har ta daure ta hakura sai taji baxa ta iya ba, tashi tayi ta nufi ɗakin mahaifin Sa'adatu don ta faɗa masa abinda take ji a ranta, har tasa Ƙafa ta shiga ciki ta juyo sbd ta ganshi tare da innah salamatu suna magana, don haka ta juya don bata son tayi magana a gabanta, juyawarta ke da wuya ya kirata a sanyaye ta dawo ta tsaya tana dubansa, fuskarsa a d'aure yace "Ya naga kin shigo kuma kin juya lafiya dai ko?" A takaice ta bashi amsa "Dama magana nake so mu yi kuma naga ba kai kaɗai bane shi yasa na koma" Bin ta yayi da wani irin kallo "Ban gane ba ni kaɗai bane kina nufin ita Salamatu wata ce daban??" Kanta a sunkuye tace "Ba haka nake nufi ba, naga ita ma tana magana da kai ne, kaga bai dace na katse muku hirarku ba" Wani kallo innah salamatu ta watsa mata, mayar da kallonsa yayi ga innah "Ba wani nan ke dai kawai akwai abinda kike son kullawa don kin ganta ne xaki canja magana, ke dai ki riƙa jin tsoron Allah wlh wannan halin da kika dakko ba halin kirki bane, gashi nan kin koyawa yarki baƙin hali bata kaunar yan uwanta gaba ɗaya, to ni baxan juri wannan abin ba ni bana son gulma da munafunci da raba ɗaya biyu, abinda ya yi ni shi yayi Salamatu duk abinda xaki fada min xaki iya faɗa a gabanta, ke ko baki faɗa ba ma sai na faɗa mata don tana da hakkin da xata san halin da kike ciki ke da yarki, tunda ita ce gaba da ke" Mayar da ajiyar zuciya innah tayi tare da kallonsu gaba ɗaya, ba tare da tace wani abu ba ta juya ta kyale su suna mayar da maganar, tana fita aka saka faifan gulamarta cike da makirci innah salamatu ta dube shi kamar xata yi kuka. "Na rasa me na yiwa matar nan ta tsane ni, kullum burinta taga bayana ni kuwa xama a gidan nan daram don ni taxo ta tarar, mugun halin da yake kunshe a ranta ya fi karfin cikinta, Allah ne yaga niyyarta ya barta a haka, yanxu banda tsabar masifa maganar ce baxa ta faɗa a gabana ba sbd ga munafuka ko, kada na kwasa na gayawa duniya, tunda bata son naji ni kuma wlh sai na san halin da ake ciki, tashi ka bi ta daki kaji me ke tafe da ita" Da sauri ya miƙe ya shiga dakin innah , yadda taga ya shigo yana tambayarta abinda ya kawota ne ya bata mamaki, hakan ne ya nuna mata cewa ba yin kansa bane aiko shi aka yi, don haka ita ma a takaice take bashi amsar duk abinda ya tambayeta ba tare da ta wani sakar masa fuska sosai ba. A hankali ta fara yi masa magana "Dama a kan maganar Sa'adatu ne yau na tashi duk jikina ba daɗi banda tunaninta babu abinda nake yi ko aiki na kasa yi, shi ne naga ya dace na tambayeka ina so xan je na ganta, kaga tunda aka yi aurenta ban taɓa zuwa naga muhallin ta ba ballantana na san halin da take ciki" wani kallo ya bi ta da shi gami da gyara tsayuwa "kinga dakata bana son kinibibi da son iyawa, sai kace a kanki aka fara aurar da 'ya xa kice xaki je ki ganta, duk yan uwanta da suke xuwa su ganta basu wadatar ba sai kin je da kanki dole kin ganta, wato salon kiga wani abin da bai miki ba ki kashe mata aure ko?? To ban yarda ba, kuma idan har kika je ban yafe miki ba, duk abinda kike so a yi mata ki faɗawa Salamatu xata yi miki, don ta fi ki kyakkyawar zuciya kece ma kike nuna mata baƙin hali amma duk abinda kake so xata yi miki" Sai da ta bari ya kammala magana, cikin nutsuwa ta dube shi "Haba dan Allah malam idan aka yi min haka sam ba a yi min adalci ba, ya zaka yi min Allah ya isa a kan xanje naga halin 'yata ɗaya tilo da na mallaka a duniya, duk abinda Salamatu xata yi min ai ba kamar wanda xan yi da kaina ba, gaskiya ka janye maganar Allah ya isan nan sbd idan aka yi min haka an shiga hakkina tunda kowace mace a gidan nan kana bari tana xuwa gidan yarta ni me yasa zaka yi min haka?" Yana gyara Babbar riga yake mata magana "sbd ke kin nuna kina 'kin auren tun farko, shi yasa baxa ki taɓa zuwa gidan ba sai dai idan ita taxo miki, wannan dalilin ne yasa na saka miki wannan dokar kuma dole ki bi ta, matuƙar kika fara xuwa gidan Sa'adatu nasan xaman lafiya ya ƙare, kuma baxa ki bari yarinya tayi xaman aure ta xauna lafiya da mijinta ba" yana gama faɗa ya fita, duk abin duniya ne ya damu innah ta rasa abinda yake mata daɗi, wannan karfa karfar da ake mata ba ƙaramin mamaki take bata ba. Tana cikin wannan halin ne taji sallamar Adda saratu, wani sanyi taji a zuciyarta taji kamar an yi mata gafara da murna ta fita tsakar gida tana yi mata sannu da zuwa kama hannunta tayi suka shiga daki tare da yi mata shimfida. Tambayar farko da tayi mata shi ne ina Sa'adatu?? nan da nan fuskar innah ta canja daga farin ciki zuwa akasin haka, cikin rawar murya ta amsa mata da "tana gidanta" girgixa kai Adda saratu tayi "wallahi ina jin xafi a raina duk lokacin da na tuna Sa'adatu malam Jibo ta aura, wannan auren cuta har ina, shi yasa ma kika ga wlh ban taɓa karambanin xuwa gidanta ba, sbd bana son naje naga abinda xai bata min raina" Murmushin takaici innah tayi "Ganin abinda zai bata miki rai ai ya zama dole saratu, don yadda naji labarin gidan abin ba dadi, nayi ƙoƙarin zuwa amma malam ya hana wai baxan bari ta xauna lafiya da mijinta ba, ko yanxu ma kafin kixo sai da nayi masa maganar yace Allah ya isa idan naje wai kashe mata aure xan yi" A firgice Adda saratu ta dubeta "kan malam kalau kuwa? Ya za a yi ke da gidan yarki yayi miki Allah ya isa don kin je, gaskiya rayuwar gidan nan naku ba adalci, to ke yanxu kin hakura da xuwa kenan?" Dagowa tayi "to ya xan yi saratu, na kyale shi tunda ina da ke na san ba nida matsala, idan kin je duk abinda xan yi kema xaki iya yi" girgixa kai tayi "Haka ne yaya insha Allah duk abinda ya kama xan yi miki" Bayan sun ɗan yi hira sai ta kwatanta mata gidan Sa'adatu don xuwa ta ganta, ba tare da bata lokaci ba ta tashi ta nufi gidan, da farko da taje bata gane kwatancen ba sai da ta sake tambaya aka nuna mata, tun daga kofar gidan take jinjina irin wannan gida da ya kawo Sa'adatu gida kamar a ƙauye, ko fulasta babu a kofar gidan, ko'ina na cikin gidan ƙasa ne ga uwar kazanta, a soro taci karo da malam jibo ya sa benci yana zaune yana jan carbi, ya kasa ya tsare kamar mai gadi, sallama tayi masa, fuskarsa babu walwala ya amsa, neman hanyar wucewa ta shiga yi. Tsareta yayi da ido yana tambayarta, "Baiwar Allah ba a shiga gidan nan sai da izni, naga kina kokarin wucewa ciki ba tare da kin tambaya ba da alama dai baki san dokar gidan ba ko" Mamaki ne ya kama Adda saratu yanxu a wannan mataccen gidan za a ce sai an tambaya idan za a shiga, kallon mamaki ta bi shi da shi sannan ta fara magana. "Au Yi hakuri malam ban sani ba ai" Kallonta ya cigaba da yi "to ba matsala wajen wa xaki je" Cike da nutsuwa ta bashi amsa da cewa. "wajen Sa'adatu naxo" kamar ta yafa masa ruwan xafi yaji, don haka a fusace ya amsa da "Bata nan taje ganin gida, sbd tunda aka yi aurenta bata fita ba sai yau ta fara fita" A kaikaice ta dube shi. "Haba malam da girmanka bai kamata ka riƙa karya ba, yanxu haka daga gidan nasu nake ban ganta a can ba" Fuskarsa a daure ya dubeta "Nace miki tana can kije ki duba mana ya xaki saka ni a gaba ki riƙa tuhumata kamar wani yaron gidanki, matarki ce ko tawa?" Ita ma gyara fuskarta tayi tare da haɗe rai "Yau naga ikon Allah, me kuma yayi zafi haka daga tambaya sai faɗa, kai dai kace kawai baka son naje wajen Sa'adatu amma tabbas tana nan" Ɗaya daga cikin ya'yansa ne yayi sauri yace da malam Jibo " Baba Aunty amarya tana nan, ka manta tana can a kwance ba lafiya" A firgice ta dubu yaron "Ba tada lafiya kuma??" Cikin zuciyarta ta rika addu'a Allah yasa dai ba ciki ne da ita ba. Duka ya kaiwa yaron "ban hana ka wannan shegiyar maganar taka ta banxa ba nasa da kai ne, da xaka sa min baki, wlh idan kana mun haka ranka xai riƙa ɓaci" Yana Cikin wannan maganar ta kewaye ta bayan shi ta wuce, bai lura ba sai da ta kusa kaiwa cikin gidan, da sauri ya bita bayanta yana masifa, shan gabanta yayi "Ba ki da hankali ne,ban baki dama ba zaki shigo min gida, idan bakya so na xubar miki da mutunci tun wuri ki fita ki bar min gida tun kafin ranki ya ɓaci" Mamaki ne ya kamata "me kuma ya kawo maganar xubar da mutunci wajen yata naxo ina da hakkin da xan ganta don haka baka isa ka hana ni ba" A fusace ta wuce da sauri ya sake bin ta tare da tare kofar shiga bangaren Sa'adatu. Gardama ce ta tufke a tsakaninsu yana cewa baxa ta shiga ba, ita kuma tana cewa sai ta shiga, a fusace ya sake dubanta, "ke wace irin mace ce da bata san mutuncin aure ba tun farko na fada miki cewa bana bari a ga Sa'adatu ko mahaifinta ne yaxo a wannan halin bai isa ya ganta ba don haka ki kama hanya ki bar min gida tun kafin kiga abinda xai faru" Kallon shi kawai take yi, don ita yanxu a shirye take duk abinda xai faru ya faru indai a kan Sa'adatu ne. *Comments and share pls* *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *28* Musu ne ya kaure tsakanin su, baka jin komai sai tashin hayaniya, gaba ɗaya matan nasa sun bi gefe suna ganin rashin dacewar hakan da yake yi, amma kuma ba su da ikon yin magana sbd gudun kada ya huce a kansu, haka suka koma dakunan su suka barta da shi suna bugawa, yana cews baxa ta shiga ba ita, kuma tana sai ta shiga ko ta halin ƙaƙa, ganin ba tada niyyar fita daga gidan ne yasa ya fita wani kallo mai cike da tsana yake bin ta da shi yana tafe yana jan wani tsaki, babu wanda ya san inda ya tafi da abinda yake shirin yi, ganin hakan ne yasa matan suka taho da sauri wajenta suna mata magana, "ke kuwa baiwar Allah ki rufawa kanki asiri ki wuce ki bar gidan nan don ba a jayayya da malam, idan yace baza a yi abu ba ta xauna, sai dai kowa yayi hakuri, mu ma nan da kike ganinmu biyayya muke yi amma kaf cikinmu babu wacce ta isa tayi jayayya da shi" Murmushi Adda saratu tayi "To ai gara da ku ka ce ku, ni ai ba a cikinku nake ba, kuma ni ba yarinyarsa bace da zan ji tsoronsa ko na bi umarninsa hakkina ne naxo naga 'yata kuma dole ya kyale ni na shiga, banda ya san akwai abinda yake boyewa menene na hana ni ganinta" tana gama faɗa ta wuce ta kyale su a tsaye. Saka kanta tayi tare da bude kofar ɓangaren Sa'adatu, tarar kofar dakin tayi an turo kamar bata nan, don haka tasa kafa ta tura kofar ta buɗe, a kwance ta tarar da ita cikin mawuyacin hali banda numfarfashi babu abinda take yi duk ta galabaita ta fita daga cikin hankalinta, cike da gigita ta ƙarasa wajenta tare da dago kanta tana kuka, kiran sunanta ta shiga yi amma ga mamakinta sai taga ko ɗan yatsanta baya motsawa, sai ta sarrafata sannan take sarrafuwa. A gigice ta fara jijjiga jikinta amma sai taji shiru duk iya kiran da tayi mata bata amsa ba, ihu ta fara yi tana neman taimakon matan gidan, da sauri suka taho suna tambayarta ko lafiya cikin kuka take ce musu "Yanxu kuna ganin halin da Sa'adatu take ciki amma ku ka kyaleta a wannan yanayin, kuma naxo wajenta tsabar wulakanci mijinku yana ƙoƙarin hana ni ganinta, ashe ya san zaluntarta yake yi shi yasa xai hana naga halin da take ciki, sbd kada na tona masa asiri" Dafa kafadarta daya daga cikin matan tayi "wlh ba laifinmu bane baiwar Allah mu ma hakuri muke yi da shi, haka tsarinsa yake duk tsananin ciwon da mutum zai yi, da halin da xaka shiga baxai bari a kai shi asibiti ba, sai dai a rika yi masa yan jike-jike, ita ma Sa'adatun tana da laifi duk abinda ya bata bata sha sai sai ta xubar shi yasa kika ganta a wannan yanayin da tana sha da tuni ta warke" Wani kallo Adda saratu ta bi ta da shi "ya za a yi a ce mara lafiya da iya jikon magani kaɗai xai warke, ai ko ana shan jiko dole sai an kai mutum asibiti an san me yake damunsa, amma yanxu don wulakanci ya jibgeta a daki dubi yanxu ko hannunta bata motsawa bata cikin hayyacinta gaba ɗaya, kuma alamu sun nuna yunwa ta shigeta dubi hannunta a bushe ba jini, to wlh ko xai mutu yau sai na kai Sa'adatu asibiti, sai dai idan tsafi ne da shi ya karye" Da sauri ta fita ta kira mai a dai-daita sahu, taimako ta nema daga wajen matan a kan su taimaka mata a saka Sa'adatu a dai-daita sahun, amma gaba ɗaya sai suka riƙa komawa gefe suka ki taya ta, cike da ƙarfin hali ta dube su kamar xata yi kuka sbd takaici. "Haba bayin Allah ina neman taimako amma gaba dayanku sai dai ku bi ni da ido, babu mai taimaka min na sakata a mota, ko baku san yarinyar nan ba ai ya kamata ku tausaya mata, ballantana kuma yar uwa ce a gare ku" A sanyaye suka dubeta "kiyi hakuri baiwar Allah, ba kin taimaka miki muka yi ba, akwai abinda muke gudu ne shi yasa indai yaji da hannunmu wajen taimakawa a kaita asibiti mu kaɗai muka san irin tashin hankalin da xamu fuskanta, dan Allah kiyi hakuri da fatan kuma baxa ki damu ba kin ji uzurinmu" Girgiza kai tayi kawai ba tare da tace wani abu ba. Cike da jarumta tayi kokari ta daga Sa'adatu ta ɗora ta a dai-daita suka nufi asibiti, tun a hanya Adda saratu take ta kuka tana tausayawa halin da yarta ke ciki, kai tsaye privet hospital tace ya kaita sbd idan suka je na gwamnati sai an kai ruwa rana kafin a karɓe ta. Suna zuwa aka fara bata taimakon gaggawa, daga baya likita yaxo yayi mata bayanin cewa, tsananin yunwa ke damunta don tana da barazanar kamuwa da cutar olsar sannan kuma malaria na damunta, lissafin kudade masu yawa aka yi mata har wanda xata siya magani, ganin kudin hannunta baxai isheta bane yasa ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki, yayi ƙoƙarin kiran innah ya sanar da ita amma ta dakatar da shi, sbd bata san kowa ya san abinda ake ciki har sai Sa'adatu ta samu kanta. ******************* Shi kuwa malam Jibo yana fita bai xame ko ina ba sai gidan su Sa'adatu yau ko bari a kira Babanta bai yi ba da kansa ya danna kai cikin gidan, Inna Salamatu ce sunkuye tana shara, tana ganinshi ta xube a ƙasa da sauri tana yi masa sannu da xuwa. "Malam yau ya na ganka a wannan halin ban saba ganinka a haka ba, kamar dai ba a hayyacinka kake ba, lafiya dai ko, ko yar tamu ce tayi laifi na santa da taurin kai da rashin jin magana?" Yana huci ya fara magana "ina malam din yake wajensa naxo, shi ne yace wata mata taxo ta shigar min gida bada ixnina ba, idan shi ya turota yaxo yayi min bayani don baxan yarda da irin wannan abin ba, a rika keta min alfarma na saka doka a karya, idan kuma aurena ne da yarsa baya so sai na saketa ta cigaba da yawon iskancin tunda haka ya zaɓa" Cikin rashin fahimtar abinda yake faɗa ta dube shi "wani abin aka yi maka ne malam ban gane abinda kake nufi ba? Mu dai daga nan babu wanda yaje gidanka da niyyar kashe maka aure, don malam baya barin kowa yaje sbd gudun fitina, sai dai kuma idan ita ta tura yan iskanta su yi maka haka, amma dai bari naje na sanar da shi halin da ake ciki, dan yayi maka bayanin yadda aka yi aka haihu a ragaya" Da sauri ta yar da tsintsiyar da ke hannunta ta faɗa dakinsa, ganin yadda ya ganta ba nutsuwa ne yasa yayi saurin mikewa tare da tambayarta "lafiya na ganki a haka salamatu wani abin ne ya biyo ki?" Jikinta har rawa yake sbd ita a duniya tana farin ciki taji an fadi aibun Sa'adatu ko kuma wani abin sharrin ya sameta, cikin rawar murya tace "kaxo an kunno maka wuta daga wajen Malam Jibo, waccan munafukar ta daki ta kunna maka masifa, sai kayi ƙoƙarin zuwa ka kasheta da kanka tunda xamanka take yi a gidan" tana gama faɗa ta fita, kiran sunanta ya shiga yi a hankali ta waigo. "Malam ɗin yana ina??" Hanya ta nuna masa "Kaje yana soro yana jiranka amma dai tabbas kayi kokarin yin maganin abin, ka yiwa tufkar nan hanci idan ba haka ba kuma za a bata tsakaninku da shi" Jikinsa har rawa yake, ji yake kamar yayi fiffike yaje ya tarar da malam Jibo ko takalmi bai samu damar sakawa ba ya fita, a tsaye ya tarar da shi ya goya hannunsa a bayansa, miƙa masa hannu yayi suka gaisa sannan daga bisani ya tambaye shi abinda ke tafe da shi, bayanin xuwan Adda saratu yayi masa, da dukkan abinda ya shiga tsakanin su da ita. Wani bakin ciki ne ya tokare wuyan baban Sa'adatu don haka ko komawa gida ya saka takalmi bai yi ba suka rankaya suka tafi gidan malam jibo don ganewa idonsa abinda ke faruwa. Kai tsaye dakin Sa'adatu suka nufa duk a tunaninsu xasu ganta a ciki amma abin mamaki babu komai sai filin wajen, ba ƙaramin tashin hankali malam Jibo da mahaifin Sa'adatu suka shiga ba, a gigice ya fito daga dakin yana tambayar matansa ko sun ga Sa'adatu da matar da taxo. Jikinsu na tsuma suka bashi labarin tafiyarsu asibiti, nan fa hankalinsa ya tashi ya san matukar aka kai Sa'adatu asibiti xai yi wuya likitoci su bari ta dawo gidansa. Juyawa yayi ya dubi mahaifinta. "Kaga irin abinda matar nan tayi min ko? masifa take shirin jawo min, dama tunda na ganta na san ba alheri ne ya kawota ba, watakila ma yar yankan kai ce ba a sani ba, amma kuma tace min wai ita yar uwar mahaifiyar Sa'adatu ce wanda ni hankalina sam bai kwanta da hakan ba, shi ne dalilin ma da ya hana na bari ta ganta" Girgiza kai baban Sa'adatu yayi tare da cewa malam Jibo ya kwatanta masa kamannin matar, yana gama faɗa masa ya dube shi. "tabbas ba karya take yi ba kanwar mahaifiyar ta ce, don yanxun ma daga gidana ta fita, da hadin bakin mahaifiyar Sa'a aka yi komai duk wannan tsiyar ita ta kulla, ai kuwa sai ta gane kurenta sai ta faɗa min inda ta kai min 'yata idan bata yi wasa ba a bakin igiyar aurenta, shi yasa ai tun farko na faɗa maka na haramtawa kowa zuwa gidan nan har mahaifiyar tata amma baka ji ba ka kyaleta ta shigar maka gida, gashi nan ai ta samu damar karya maka doka, watakila ma tayi kutungwilar da auren zai lalace" Shiru malam Jibo yayi yana naxarin maganar sa sannan ya bashi amsa "wlh xaka yi mamakin gwagwarmayar da muka yi a kan baxa ta shiga ba amma ta kafe, gudun kada a yi abin kunya ne yasa na tafi na kyaleta" Cikin fushi baban Sa'adatu ya dube shi "Kai da gidanka xata zo tayi maka gadara me yasa baka sheme ta ba" Malam Jibo ne ya dafa shi "a'a dakata malam ai ba a yi haka ba, gara dai da na kyaleta din taci arzikin igiyar aurenta, yanxu abinda za a yi mu fara xuwa gidan matar ko sun dawo daga asibitin, kuma mu faɗawa mijinta irin aika-aikar da tayi mana, shikenan xai fi sauki sai ya san irin matakin da xai ɗauka a kan matarsa" Fita suka yi gaba ɗaya suna huci, bin su matan gidan suka yi da ido don kuwa su kansu idan ya dawo sai ya sauke musu kwandon tijara, gidan Adda saratu suka nufa a kulle suka tarar da kofar gidan don haka suka xauna don jiran ganin dawowarsu. Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:35 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *29* Sun ɗauki lokaci mai tsawo suna jiran dawowarsu Adda saratu amma shiru babu su babu dalilin su, sun yi jira ya kai na awa biyu har sai da suka fara gajiya, ganin ba su da niyyar dawowa ne yasa suka ɗauki hanyar xuwa wajen innar Sa'adatu don jin wajen da suka tafi da kuma inda aka boye Sa'adatu. Zaune take a daki ta idar da sallar la'asar tana ta jero addu'o'i a kan Allah ya kawo musu mafita ita da Sa'adatu, bayan ta kammala ne ta janyo Kur'ani ta fara karantawa. Hayaniyar jama'a ta ji a tsakar gidan a yadda alama ta nuna dukkan matan gidan ne suka hallara a tsakar gidan suna jin abinda Baban Sa'adatu yake faɗa musu, gaba ɗaya sun bashi hankalinsu suna sauraren abinda yake faɗa, ganin ba a kirata ba kuma ba a sa da ita bane yasa tayi xamanta a daki ta cigaba da karatunta, daga can taji kamar har da Malam Jibo ake maganar don taji irin muryarsa duk da dai bai fi gani ɗaya ta taɓa yi masa a rayuwarta ba, amma kuma magana ɗaya biyu sai taji an kira sunan Sa'adatu, wannan dalilin ne yasa ta ƙara bada hankalinta don jin abinda suke faɗa tare da addu'ar Allah ya kareta daga sharrinsu da dukkan abinda suke kullawa. Tashi tayi ta fara ninke kayan wankin da tayi, juyowar da xata yi tayi ido huɗu da Baban Sa'adatu a bayanta yana bin ta da wani irin kallo mai cike da alamomin tambaya. A hankali ta ɗaga baki xata tambaye shi, ganin tana da niyyar yin magana ne yasa ya dakatar da ita "Ba ki da wani abinda xaki faɗa min na yarda da ke, sbd duk sharri da bita da ƙullin da ake yi kece kika shirya shi, ke kika tura kanwarki saratu gidan Sa'a ta kashe mata aure, sbd har yanzu kuna da burin aura mata wancan shashashan yaron" Cike da gigita ta dube shi tana motsa baki sai taji maganar ta kasa fita sbd ɓacin rai, kafin tayi ƙoƙarin cigaba da magana ya hau kanta da masifa "wannan wane irin wulakanci da cin amana kike son shirya min, me nayi miki da xaki saka min da wannan abin, tunda ban cuceki ba kema baki isa ki cuce ni ba, ina baki shawara tun wuri kafin lokaci ya ƙuri miki, kiyi ƙoƙarin bayyanar min da inda 'yata take kafin na wulakanta ki nayi miki tozarcin da baki taɓa tsammani ba,wai ke mutuniyar kirki ko da an fara magana sai ki mayar da fuskarki ta muminai bayan ke cikakkiyar munafuka ce, to wlh kiyi gaggawar cika umarnina kafin ranki ya ɓaci" Yana gama faɗa ya fice ya bar ɗakin bin sa tayi tsakar gida tana tambayarsa. "Malam ka bani magana a dunkule ban fahimci abinda kake nufi ba?" A fusace ya juyo yana nuna ta da ɗan yatsa "Ai baxa ki fahimta ba sbd kin san abinda kika shirya, ni dai na baki lokaci kafin nan da faduwar rana ki san abin yi idan ba haka ba kuma kiga wulakanci" gaba ɗaya idon matan gidan yana kan innah, shi ma malam Jibo bin ta yake da kallo mai cike da tsana kamar xai kwada mata mari. Har ta juya xata shiga daki Innah Salamatu da jama'arta suka biyo bayanta suna mata magana. "Ke kuwa baiwar Allah lalacewar da ta same ki kenan kawai sbd kwadayin abin duniya, kina matsayin uwa kina bawa 'yarki goyan bayan tayi iskanci kowace uwa ta gari tana so 'yarta tayi xaman aure, ke kuma kina ƙoƙarin wargaza mata rayuwa wlh kin ji kunya ki gyara halinki sbd kwanciyar kabari" Girgiza kai tayi kawai ba tare da tace komai ba tayi shigarta daki, don bata san amsar da xata basu ba tunda bata ma san a kan me suke magana ba. Bayan fitar su malam jibo daga gidan su Sa'adatu kai tsaye sake komawa gidan Adda saratu suka yi don ganin ko sun dawo, bai fi xaman mintina biyar suka yi ba sai ga mijinta tare da ƴaƴanta sun dawo daga islamiyya. Yana ganin su ya miƙa musu hannu da girmamawa don su gaisa, amma abin mamaki sai suka ki miƙa masa, cikin fushi mahaifin Sa'adatu ya dube shi. "Ba gaisuwa ce ta kawo mu ba don haka ka riƙe gaisuwarka ba ma buƙata, kawai abinda ya kawo mu shi muka zo yi" Cike da mamaki ya dube su "me kuma yayi zafi haka malam me ya faru me nayi maka da har xaka ki gaisawa da ni?" Gyara tsayuwa suka yi gaba ɗaya suna ta faman huci shi kuwa malam Jibo can yayi da kansa yana ta kunbure-kunbure kamar zai kai masa duka, sake jefa musu tambaya yayi "me nayi muku haka ne naga bamu taɓa samun sabani da ku ba, yau kuma kun xo min da wani bakon al'amari wanda ban saba ganinsa ba" Cikin fushi Baban Sa'adatu ya dube shi "ina 'yata da aka hada baki da kai aka je har gidan mijinta aka ɗauke ta ba tare da iznina ba ko na mijinta?? Amsa kawai muke bukata" A hankali ya dube su "Ba nida hannu ko masaniya a kan abinda kake tuhumata da shi sai dai kawai na san mai dakina taje gidan ka" ya nuna malam Jibo "ta tarar da yarinyarka cikin hali na rashin lafiya, ganin halin da take ciki ne yasa ta taimaka ta kaita asibiti tunda kun gaza, kuma ita ma tana da hakki a kan yarinyar shi yasa ma tayi ƙoƙarin ceto rayuwarta" A fusace mahaifin Sa'adatu ya dube shi "hakkin menene da ita a kan 'yata, ita ta haifeta ko kuma dawarta taci ta girma, menene dalilinta nayi min katsalandan a cikin rayuwar iyalina, to wlh tun wuri a dawo min da 'yata kafin hankalin kowa ya tashi" Cike da nutsuwa mijin Adda saratu ya fara yi masa magana "wannan duk ba wani abu ne na tada hankali ba malam, taimako mai dakina tayi mata, kuma don Allah tayi ba don wani a cikinku ya yaba mata ba, tunda kun nuna bakwa so shikenan yanxu xamu tafi tare da ku asibitin ku ɗauke ta ku tafi da ita gida kamar yadda ku ka buƙata" Sauke ajiyar zuciya suka yi gaba ɗayansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba da yace zai kai su inda suke, buɗe gidan yayi yasa yaran suka shiga sannan ya taho suka tafi Asibitin, suna tafe suna faɗawa Adda saratu munanan maganganu shi dai bai tanka musu ba, sbd idan ya daka ta tasu sai a yi batacciya. Suna isowa bakin gate suka tambayi mai gadi don ya nuna musu dakin da Sa'adatu take kwance, ba tare da bata lokaci ba ya nuna musu suka shiga. Tararwa suka yi ana ƙara mata ruwa, don haka suka nemi waje suka zauna, juyowa likitan yayi ya faɗa musu cewa bata san hayaniya don haka su kula, cikin fushi mahaifinta ya dubi likitan. "Mu ba ruwanmu da bata san hayaniya domin mu hayaniyar ce ta kawo mu, a bamu yarmu mu tafi da ita ko kuma hankalin kowa ya tashi" cike da nutsuwa likitan ya dubi Adda saratu "wadannan mutanen kuma daga ina suke me kuma suke so a wajen yarinyar nan" kafin ya gama magana Malam Jibo har ya buɗe baki ya fara magana "Au tambayar matsayinmu ma kake yi, to ni mijinta ne wannan kuma babanta ne, wannan matar kuma yar shiga abinda ba ruwanta ce, domin ita ta karya min dokata ta kawo min matata asibiti ba tare da amincewata ba, kuma yanzu dole ne a tsinke ruwan nan a bamu ita mu tafi gida" A hankali likitan ya xare farin gilashin da ke idonsa ya dube su "to ai ba haka ka'idar aiki take ba malamai dole sai ta samu sauki ko da xamu yi wata magana da ku, yanzu dai kun ga halin da take ciki ya kamata a tausaya mata" Cikin fushi mahaifin Sa'adatu ya mayar masa da amsa "kai malam dakata kada ka raina mana wayo kai ka haifar mana 'yar da xaka fada mana abinda ya dace da mu" Sai a lokacin Adda saratu ta kalle su tare da mikewa tsaye tana musu magana "Duk da kasancewar Sa'adatu 'yarka kai kuma matarka, a wannan lokacin babu wanda yake da iko da ita a cikin ku, sbd baku bata kulawar da Allah yace a bata ba, kuma baku yi abinda ya dace a gareta ba, don haka a yanxu ni nake da iko da Sa'adatu kuma babu wanda ya isa ya rabata da asibitin nan sai dai idan warkewa tayi sbd Sa'adatu ba 'yar da aka ciyo ganima a wajen yaƙi bace da kowa zai riƙa sauke masifarsa a kanta, idan ku bakwa so mu muna sonta kuma xamu kula da ita, idan mahaifiyarta tana jin tsoron ku taki tayi magana a kan zaluncin da ake yi mata, to ni lokaci yayi da xan kwatar mata yancinta" Hannu malam jibo yasa xai mari Adda saratu da sauri mijinta ya riƙe hannunshi "kada ku kuskura hannunka ya taɓa matata, xan iya hakuri a kan komai amma banda iyalina idan ka sake hannunka ya taɓa ta hukuma ce xata raba ni da kai" Cikin zafin rai malam Jibo ya fara magana "Ni ba a ga abinda aka yi min ba har xaka ce xaka kaini kotu, idan ka kaini nima Ina da abin faɗa a kanku sbd an keta min haddina" Murmushi mijin Adda saratu yayi "To ai ko kotu aka je kaine a hannu, kana da abubuwan da za a tuhumeka da su, domin ka tozarta hakkin 'ya mace ka wulakanta amanar da ka ɗauka, ka hana ta dukkan kulawar da ta kamaceta, ka hanata abinci da suttura sannan ka sa mahaifinta ya aura maka ita a dole kaga kuwa ko anje kotu kaine a hannu" Jikin mahaifin Sa'adatu ne ya hau rawa "kaga malam baxa ka kashe mun auren 'ya ba babu ruwanka da abinda nayi mata tunda ba kai ka haifar min ita ba" Jan hannun malam Jibo yayi suka fita, kara kanshi yayi a kunnesa yana yi masa rada wanda babu wanda ya san abinda suke tattaunawa. *Kada a manta da comment da kuma share* *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:35 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Masu karatu sai kun yi hakuri da ni, baxan rika samun damar typing kullum ba sbd ina xuwa makaranta, na gode da yadda ku ke nuna kaunarku ga wannan littafi* *30* Sun yi tsayuwar sama da minti talatin suna tattaunawar sirri, amma babu mai iya jin abinda suke faɗa, sai da suka gama suka shigo dakin da Sa'adatu take, ko sallama basu yi ba suka samu wajen xama suka zauna suna fuskantar likitan, Malam Jibo ne ya fara yin magana "Yanxu dai ina ganin sulhu ya kamata a yi likita bai kamata a ce matata ta samu matsala kuma an barta a nan wajen ba, ina ganin hakan babu maganin da xai yi sai dai ma ya ƙara mata wata cutar, duba da asibiti matattara ce ta shaidanu, kuma ciwon Sa'adatu ba na Asibiti bane maganin gida za a yi mata, don a ganina tana fama da shaidanun da suke hanata jin maganar mijinta, tunda mun gano hakan, to a bani sallama mu tafi gida tunda ina da taimakon da nake bayarwa, kaga ya kamata a bani ita mu tafi kasancewar matar nan mallakina ce, ko musulunci ya yarda na kafa mata doka ta bi, ga kuma mahaifinta ya bani damar yin dukkan abinda naso a kanta kaga kuwa babu Maganar ta sake xama a nan" Cikin nutsuwa likatan ya dube shi gami da sakin wani ɗan siririn murmushi "Dadina da kai dawo da hannun agogo baya Malam, yanzu fa aka gama maganar cewa baxa a sallame ta ba har sai ta warke, me yasa kake son tada mana da hankali, idan har da gaske kake kana son matarka ya kamata ka kula da duk wani abu da xai taɓa lafiyarta, dan Allah ku gaggauta fita daga nan sbd bana so ta farka taji hayaniya jikinta ya sake dawowa sabo, tana buƙatar hutu sosai" Mijin Adda saratu ne ya dubi likitan "ka ma daina haɗa su da Allah tunda sun nuna basa jin kunyar yin abin kunya, mu ma mun shirya yaƙi da su, xamu yi iya bakin kokari wajen ganin basu samu nasara a kanmu ba" nuna malam Jibo da Baban Sa'adatu yayi "ku fita ku bar Wajen nan na riga da na fada muku yanxu Sa'adatu ba taku ba ce har sai ta warke xata dawo hannunku, idan kuma ba haka ba yanxu ku ga hukuma a nan" Wani kallo malam jibo ya bi shi da shi, xai buɗe baki yayi magana Baban Sa'adatu ya tari numfashinsa "kada ka fara cewa komai idan ka duba xaka ga mutanen nan ba da alheri suke nufin mu ba, tunda kaga muna sa'insa da su akwai abinda suke shirin kulla mana tashi mu tafi, idan sun san wata ai basu san wata ba" fita suka yi suka bar asibitin zuciyar su cike da baƙin ciki, suna tafe suna tattauna yadda zasu kwato Sa'adatu daga asibitin. Sai washe gari Sa'adatu ta farfaɗo a hankali ta fara buɗe idanunta tana ambaton Allah, shafa fuskarta Adda saratu tayi tare da yi mata sannu, a hankali ta bude baki tana mata magana "yaushe kika xo Adda saratu, dama ina ta kewarki malam ya hana naje na ganki" murmushi tayi "Da bai bari kinxo wajena ba ai gashi ni naxo ko?" Yunkurin tashi daga kwanciyar da tayi ta fara yi amma sai ta kasa, a hankali Adda saratu ta dagota tare da jinginata a jikin gadon, a hankali ta sake buɗe ido "Nan kuma ina muka xo Adda"? Cike da kulawa ta bata amsa "Asibiti aka kawo ki" Zaro ido tayi tare da gyara zaman da tayi "Asibiti kuma Adda ya aka yi malam ya bari aka kawo ni amma nayi mamaki sosai" Rausayar da kai tayi"ai dole kiyi mamaki idan kinga tagagarin da muka yi kafin ma ya bar ni na shiga gidanki xaki yi mamaki, ke dai labari sai kin warke kawai" Suna cikin hirar likitan ya shigo hannunshi riƙe da magunguna, guri ya samu ya xauna yana duban Sa'adatu "lallai jiki yayi kyau matar malam Allah ya ƙara lafiya" "A hankali ta amsa da "ameen" Mayar da kallonsa yayi xuwa ga Adda saratu "Hajiya akwai maganganun da nake so mu yi da ke, Hakan yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar yarinyar nan, idan babu damuwa ki same Ni a waje" Cike da nutsuwa ta dube shi tare da cewa, "to ba matsala" Tashi tayi ta bi bayansa. Waje suka samu suka tsaya, kallonta yayi tare da neman izinin fara magana, cike da kulawa tace masa "Ina saurarenka" "Kiyi hakuri da tambayar da xan miki yanxu, abin ne ya d'aure min kai ina bukatar na san amsar tambayar da xan miki" Dago fuskarta tayi tare da cewa"ina saurarenka" Sauke ajiyar zuciya yayi "Dan Allah da gaske wannan shi ne mahaifin wannan mara lafiyar, ko kuma dai riketa yake yi?" A sanyaye ta amsa masa da "shi ne mahaifinta, shi ya haifeta amma me yasa ka tambaye ni?" Gyara tsayuwa yayi "Abinda yasa nayi miki wannan tambayar naga kamar bai damu da halin da take ciki bane, duk da cewa tana cikin halin rashin lafiya amma banga ya nuna damuwa a kan hakan ba, sai ma kokari da yake wajen ganin ya tayar mata da hankali kuma ya rabata da asibitin" Gajeran murmushi tayi "Hmmm likita kenan idan ana sallah ba a magana Allah dai ya rufa mana asiri kawai" "Ameen" yace Cike da nutsuwa ya sake kallonta "Sai kuma magana ta biyu ita kuma shawara ce ba tambaya ba" Hankalinta ta bashi tare da saurarensa. "Rokonki xan yi a kan duk rintsi duk wuya kada ki bari yarinyar nan ta koma hannun mutumin nan naga alama kamar bai san darajarta ba, ko da xata koma kiyi iya bakin kokarin wajen ganin kin kwatar mata hakkinta na ya mace, sbd auren nan akwai cutarwa a cikinsa" Sauke ajiyar zuciya Adda saratu tayi "nima tunanin da nake yi kenan amma ina ganin hakan baxai yiwu ba sbd mahaifinta mutum ne mai taurin kai, kuma ba shi da kirki ko kaɗan" Girgiza kai yayi "kada ki damu kiyi iya bakin kokari Allah xai taimake ki" Sun jima suna tattaunawa sannan ta koma wajen Sa'adatu tarar da ita tayi tana bacci don haka ta kyaleta bata tashe ta ba. ******** Yau na ɗauki tsawon kwanaki biyar a asibiti, jikina yayi kyau na dawo cikin hayyacina babu abinda yake damuna sai ɗan abinda ba a rasa ba, tun bayan xuwan da Baba da malam Jibo suka yi basu sake dawowa sun duba ni ba, wannan dalilin yasa xuciyata tayi sanyi don alamu sun nuna cewa malam Jibo ya fara fita daga cikin harkata. Adda saratu ce ta fita ta kira likita inda ya bamu sallama tare da bani shawarwari a kan na rage damuwa, kuma na daina xama da yunwa, godiya muka yi sannan muka kira mai a dai-daita sahu ya kwashe kayanmu muka shiga. A hankali Adda saratu take min magana "ina kike ganin xamu je Sa'adatu gidana ko na gidan malam Jibo ko gidan Innah" A xabure na dubeta "Haba dai Adda me xan koma wannan gidan nayi idan kinga na koma sai dai ko gawata aka kai, wannan gidan da ba shi da maraba da kabari, bana so mu je gidan Innah sbd idan naje kamar na koma gidan Malam Jibo ne" Murmushi tayi tare da dafa kafadata "Nima tsokanar ki nake yi, ai baxan bari ki koma ba sai kin warke sosai kuma sai yaxo mun yi da wajewa cewa baxai cigaba da azabtar da ke ba sannan xaki koma" Hawaye naji suna shirin gangarowa daga idanuna "Dama kina tunanin komawa ta wannan gidan Adda dan Allah ki daina, ina ji a raina ƙarshen aurena yaxo da malam Jibo" Dafa kaina tayi "Bana so kina wannan tunanin Sa'adatu, kinga dai yadda muka yi da mahaifinki da irin cin mutuncin da yake mana bana so na shiga hakkinsa na raba shi da ke, tunda kinga ya fi ni iko da ke" Kafin nayi Magana har kwalla ta cika idanuna, "kada kice haka Adda, idan da sabo kin saba da halin Baba bai kamata wannan abinda yake yi ya sanyaya miki gwiwarki ba, kiyi min gata ki kwato ni daga wannan tsaka mai wuyar da nake ciki, idan ku ka kyale ni ban san inda rayuwata xata kasance ba nan gaba, kinga fa malami ne xai iya yi min asirin da ko ku baxan sake kulawa ba, ballantana har nayi tunanin barin gidansa tunda dai ya iya asirin sana'arsa kenan" A firgice ta dube ni "Haka ne Sa'adatu insha Allah baxa ki koma hannun wannan azzalumin ba" Sai a lokacin muka lura da har an wuce layin gidanta, fadawa mai a dai-daita sahun muka yi ya dawo da mu baya, a kofar gidan aka sauke mu. Da gudu yaranta suka taho suna murna da ganinmu. "Yau kuma kece a gidan mu Aunty Sa'adatu yaushe rabon da mu ganki har mun manta" Takaitaccen murmushi nayi tare da rike hannayensu "To ai gani naxo yanxu kuma kwana xan yi a nan yau ba tafiya" Tsalle suka riƙa yi tare da karɓar kayan da ke hannunmu muka shiga cikin gidan tare, kai tsaye daki muka wuce don mu huta. Hirar su Malam Jibo da Baba muke tayi, da hanyar da xamu bi wajen ganin na tsere daga hannun malam Jibo, shi ma mijin Adda saratu tare da shi muke ta hirar. ƙara jaddada min yayi cewa baxan koma ba, ba ƙaramin daɗi xuciyata tayi ba na jin kalamansa, ji nake kamar an gafarta min xunubaina. A ranar da aka sallami Sa'adatu daga asibiti mahaifinta da malam Jibo suka koma, duba dakin da take kwance suka yi basu ganta ba, wannan dalilin yasa suka je har office din likitan don jin inda ya boyeta, ko sallama basu yi masa ba suka afka office din, sai dai ganinsu yayi kawai a gabansa. Ajiye takardar da ke hannunsa yayi yana dubansu. "Lafiya ku ka shigo min office babu sallama ba neman izini??" Binsa suka yi da kallon raini "Baka biyo ta hanyar da xamu yi maka sallama ba katon banza munafuki mai cin amanar bayin Allah" Cikin rashin fahimtar sakon da suke son isar masa ya miƙe tare da cewa "Har cikin office dina xaku shigo ku xageni ba tare da hakkina ba me nayi muku?" Malam Jibo ne ya nuna shi da hannu "ai baxa ka san abinda kayi ba sbd ana so a hada baki da kai a ci amanata, to wallahi ka fito min da matata kafin mu bawa hammata iska ni da kai" Murmushi likitan yayi "Allah ya sawwake da mutuncina na hada jiki da kai, umarni nake baku ku fita ku bar min office kafin na nuna muku fushina na nuna muku gaba dayanku baku isa ba" A fusace baban Sa'adatu ya dube shi "kai har kana da abin da xaka yi mana kuri da shi, mara kunyar karya, shege ka fasa tsakaninmu da kai, sai ka fito min da 'yata xan fita na bar nan" Bai tanka musu ba ya fita ya bar office din, kafin su ankara tuni ya kulle su a ciki ya tafi. Sai da ya ɗan yi mintuna da fita sannan suka lura da ya kulle su. Xaginsa suka riƙa yi tare da jijjiga kofar ya buɗe musu amma yayi banza da su. Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:35 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *31* Hannu yasa a aljihu ya dakko wayarsa, laluben number ya shiga yi cikin sa'a kuwa ya samu number wanda yake nema, kara wayar yayi a kunnesa tare da yin sallama, cike da ƙasaita mutumin ya amsa tare da yi masa barka da aiki. Tambayar shi dalilin kiran da yake masa yayi, cikin siririyar muryarsa ya amsa masa da "wallahi wasu ta'kadaran mutane ne na hadu da su, yanxu suka shigo office dina suna ƙoƙarin ci min zarafi a kan abinda ba nida masaniya a kansa" Gyara xama mutumin yayi tare da ajiye biron da ke hannunsa "Su wane ne su kuma daga ina suke? sannan wanene ya turo su wajenka" Ƙara saita wayar yayi a kunnesa tare da cewa "ban san su ba ranka ya dade, kawai dai an kawo min mara lafiya ne ta kwanta a asibitina, sai suka nuna kin amincewa a kan kwantar da ita da aka yi, wai su a tsarinsu ba xuwa asibiti sai dai a yi maganin gargajiya, shi ne suka zo xasu tayar min da hankali" Sake jefa masa tambaya yayi "yanxu ina mutanen suke? Ina fatan dai kun rike su baku bari sun gudu ba" Da sauri ya amsa masa "Eh suna office dina na kulle su, ban bari sun gudu ba" Murmushi mutumin yayi. "Yauwa alhamdulillah naji dadin hakan, yanxu xan turo yara su tafi da su" Godiya yayi masa sannan ya kashe wayar, ta window Baban Sa'adatu ya leko yana yi masa magiya ya buɗe su, shi kuwa malam Jibo sai masifa yake masa xuciyarsa ta kasa yin laushi. A hankali ya ƙarasa wajen su yana taku cikin nutsuwa " Ba dai ba ku da mutunci ba kuma baku san darajar mutane ba, kuma baku san irin wajen da xaku rika rashin mutuncinku ba to yau xan koya muku darasi, ko wani aka ce ku sake ci wa mutunci a duniya baxa ku ƙara ba" Yana gama faɗa ya bar gurin, cikin mintinan da basu wuce biyar ba har yan sandan sun iso, mikawa likitan hannu suka yi suka gaisa sannan ya nuna musu office din da su malam Jibo suke ciki a kulle, mukulli ya mika musu tare da bin bayansu. Ba tare da bata lokaci ba suka shiga buɗe gurin, su Malam Jibo na ganin yan sanda ido ya raina fata, nan fa suka fara magiya a kan a taimaka a rufa musu asiri a bar maganar, yan sandan basu sauraren su ba suka sanya musu ankwa suka yi gaba da su. ************* Innah Salamatu ce zaune a kofar dakinta tayi tagumi, tun bayan isha'i ta gama abinci amma ta kasa ci, sai tunani da take yi kwallawa innar Sa'adatu kira ta shiga yi. "Bak'ar daga iyayen baƙin hali a fito na kammala tuwon tun daxu a zo a ɗauka, tunda dama haka aka saba abinda aka fi iyawa kenan, a ci a ƙarshe a yiwa miji rashin mutunci a kuma taimaka wajen kakata masa yarsa an yi asara" innah na jinta bata tanka mata ba kuma bata fito ta dauki abincin ba sbd takaicin abinda ta faɗa mata, don ita tuni ta sallama abincin gidan ta hakura da karɓarsa, kasancewar kullum idan za a bata sai an gaya mata magana ko kuma an yada mata da habaici, shi kansa mai gidan bai raga mata ba, wannan dalilin yasa a kullum take jan mutuncinta kuma bata yarda wani abu ya haɗa su da ita ballantana har a faɗa mata abinda xai sosa mata rai. Ganin shiru bata fito bane yasa ta ɗauki kwanon abincin ta bawa almajiri sadaka, daga bisani kuma ta nufi ɓangaren su salim. Dakin mahaifiyarsa ta faɗa tare da yin sallama, a kwance ta sameta don har tayi shirin kwanciya bacci, tana ganinta ta tashi xaune tana mata sannu. Ganinta tayi fuskarta bayyane da damuwa, cike da kulawa ta dubeta "lafiya innar A'isha na ganki haka kamar mara lafiya, Allah yasa dai ba wani abin ne ya faru ba" Rausayar da kai tayi "Dole ki ganni a haka mama, tun azahar da malam ya fita neman Sa'adatu da jin wajen da aka boyeta har yanxu bai dawo ba, kuma shi ba waya ba ballantana mu kira shi, tunda muke tare da shi bai taɓa tafiya irin wannan ya dade ba, ni tunani nake anya ba haɗa baki aka yi da munafukar nan ta daki ake shirin salwantar mana da rayuwarsa ba kuwa, abin ya bani mamaki, kuma ya d'aure min kai don matar nan ba abar a yarda da ita bace" Gyara xama tayi "To fa!!! Ni har na rasa bakin magana ma, na rasa ta ina xan fara ni dai nasan malam ba gwanin yawo bane ina zai je haka, shi dai ba karamin yaro ba ballantana a ce ko wajen budurwa ya tafi, kuma kin ce ya faɗa miki inda zai je ko? A hankali ta dago kai "ya faɗa min xasu fita da malam Jibo su je neman Sa'adatu, kin san ai uwarta ita ta tura kanwarta gidan ta gudu da ita" Jinjina kai ta shiga yi "kwarai kuwa an yi haka, tabbas waccen munafukar ta daki tana da masaniyar inda malam yake, amma dai kafin mu yanke hukunci bari na dakko hijabina mu je gidan malam jibo mu tambaya ko shi ya dawo, ko Allah xai sa ya faɗa mana inda yake" Hijabi ta janyo suka fita, kallo daya xaka yi musu kasan ba a cikin hayyacinsu suke ba don tafiya suke gaba daya ba nutsuwa kamar xasu tashi sama, da sallama suka shiga gidan malam jibo, cike da mutuntawa matansa suka karɓe su gami da yi musu shimfida a tsakar gida, bayan sun gaisa innah salamatu ta fara tambayarta su. "Dama xuwa muka yi mu tambaye ku dan Allah ko malam yana nan"? Cike da kulawa uwar gidan ta basu amsa "Ai tun rana da ya fita bai dawo ba" Sake jefa mata tambaya tayi "Dan Allah ko ya faɗa muku inda ya tafi??" "A'a gaskiya bai faɗa ba, muna tunanin dai ko gonarsa yaje" Gyara xama innah salamatu tayi "Hmm Idan kuna wannan tunanin to ku daina ba gona yaje ba, tare da maigidana ya fita, kuma ni maigidana ya faɗa min xasu fita da mijinku ne wajen neman Sa'adatu kinga kuma har yanxu gashi karfe tara da kusan rabi basu dawo ba, a ganina anya ba salwantar musu da rayuwa ake shirin yi ba" Da sauri matan suka dubeta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un to ai mu bamu san haka ba, bai kuma faɗa mana ba sbd kwana biyun nan yana fushi da mu a kan mun bari an kai Sa'adatu asibiti yau ku san sati guda baya yi mana magana" Girgiza kai Innah Salamatu "Ai tun usuli ku kuka yi wa kanku shirme da ku ka bari aka fita da ita, duk wannan rashin lafiyar da take yi na karya ne tana so ne ta kashe aurenta taje ta cigaba da sheke ayarta kamar yadda ya saba yi a baya, shi ne aka hado baki da kanwar babarta aka zo aka ɗauke ta, sbd wanda suke yin abin da shi mai kuɗi ne ya sakar musu kudi shi yasa suka gigice a kan abin duniya" Salati matan suka fara yi "Dama haka Amarya take ni duk a tunanina yarinyar mutunci ce ashe dai kura ce da fatar akuya, oh ni wannan xamani" Da sauri innah salamatu ta dakatar da me maganar "kada ki sake wannan tunani ke dai kawai a bar kaxa cikin gashinta amma idan aka figeta abin baxai yi kyau ba" Mikewa tayi tare da cewa "yanzu menene abin yi?? xaku tashi mu tafi inda muka san za a fito mana da maxan mu ko kuma xaku xauna a nan ne ku jira har ya dawo?" Tashi suka yi suna cewa "ina muka ga ta xama ai dole mu taso mu tafi idan ba malam ai ba gida" Kai tsaye gidan su Sa'adatu suka nufa, tare da tafiya dakin innah, tarar da Kofar dakin suka yi a kulle, don har ta kwanta kasancewar bata ma son wainar da ake soyawa a gidan ba. Cike da gadara innah salamatu ta fara buga kofar, "fito munafuka ki kwance kullin da kika yi" Cikin bacci taji ana buga mata kofa a hankali ta fara buɗe ido tare da ambaton Allah, cikin nutsuwa tashi don xuwa ta buɗe musu kofar da kuma jin abinda ke tafe da su. Kada a manta da comment da share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:35 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *follow me on Wattpad @Jeeddahtou* *32* A hankali ta xare sakatar kafin ta bude har sun 'kagu sun hankado kyauran saura kaɗan ta fadi a kasa, cikin kasalalliyar murya take tambayar innah salamatu "Haba Hajiya ya xaki turo min kofa da karfi haka, idan kin yi hakuri xan bude miki, yanxu da ina da rabon wahala karya ni xa kiyi saura kiris na fadi" Wani kallon wulakanci ta watsa mata "to menene dan kin karye, ai da xaki karye din ma haka nafi so, da xamu fi samun sassauci a kan masifar da kike kokarin jefa mu a ciki" Cike da mamaki ta dube su "Ban fahimci abinda kike son faɗa ba wani abin ne ya faru, ni dai na san ban yiwa kowa komai ba?" Matsowa tayi kusa da ita "Au tambayata ma kike?? Ki fada mana inda malam yake kafin mu fara canja miki halittarki, don na fahimci sai mun fara gyara miki xama a gidan nan xaki daga mana kafa" Da jin wannan kalaman nata sai taji ta warware daga dukkan kasalar da take ji, murmushi tayi gami da kallonta ido cikin ido. "wannan ne kuma baki isa ba, ba ki da wannan ikon, dakata kiji salamatu shiru fa ba wasa bane gudun magana ne, kada kiyi tsammanin dukkan abinda kike yi ina kyale ki tsoronki nake ji, ina kyale ki kawai ba don komai ba sai don gudun tashin hankali, amma ba wai don ina tsoronki ba ko dan kin fi karfina, magana ta fatar baki don kin yi min bai zama lallai na tanka miki ba, sbd karya baxa tayi min haushi na rama ba, amma matuƙar kika yi kuskuren taɓa jikina da sunan duka a ranar xaki gane halina da yadda nake, ko an fada miki hakuri hauka ne? To ki shiga hankalinki kin san idan 'kura ta kai bango dan adam baya iya jurewa" Jin kalaman Innah da tayi da yadda ta ɗau zafi ne ya sanyaya jikin Innah Salamatu amma sai ta daure, bata nuna cewa taji tsoro ba, ita ma zazzaga mata masifar ta shiga yi. "Dama ai ban ce kiji tsorona ba, amma dai tabbas dole kiyi abinda muke so ki fada mana inda kika boye mana mijinmu, tunda dama ke ya sallama ki ba ki daga cikin matansa sbd halinki na tsiya" Murmushin takaici innah tayi "Banda abinki daga sallamar sai me na mutu ne ko kuma kinga na ragu?? Ina nan yadda nake sai ma cigaba da yake ta xuwar min" Kwashewa tayi da dariya "Tabbas haka ne cigaba yaxo tunda gashi nan an dakko 'ya daga gidan mijinta an kai ta bariki karuwanci, tabbas cigaban mai hakan rijiya yazo" Wannan maganar ba ƙaramin sosawa Innah rai tayi ba sai dai kawai ta share ta kyaleta sbd idan ta tanka mata abinda xata fada mata sai ya fi haka" Matan Malam Jibo ne suka mayar da kallonsu ga Innah "Dan Allah Hajiya ki faɗa mana inda maxajen mu suke, kinga tun safe da suka fita basu dawo ba kuma uwar gidanki ta faɗa mana cewa kece kika boye su" Rausayar da kai Innah tayi "wlh ban sani ba, sannan kuma ban san dalilin da ya hana su dawowa gida ba, amma idan baku yarda ba shikenan baxan rantse muku a kan hakan ba" Tana gama faɗa ta mayar da kallonta ga Innah Salamatu "matsa na kulle kofata malama" Kafin tace mata wani abu tuni ta tunkud'eta ta kulle kofarta, haka ta bar su cikin mamaki, musamman Innah Salamatu da bata taɓa tsammanin innar Sa'adatu xata rama cin zarafin da take mata ba. Jikinsu a sanyaye suka kama hanya suka bar kofar dakin, soro suka koma suka fara tattauna yadda xasu samowa kansu mafita. Haka suka riƙa tattaunawa ƙarshe dai suka yanke shawarar washe gari xasu fita nemansu, tare da bada cigiya gidajen radiyo. ********* Zaune nake bayan na idar da sallar walha ina addu'a, Adda saratu ce ta shigo hannunta rike da flask din abincin karin kumallo, gefena ta samu ta xauna tare da ajiye flask din abincin a gabana, sai da na shafa addu'a sannan ta juyo da kallonta gare ni "ga abincinki nan kiyi maza ki ci ga maganinki nan kuma ki sha saura kuma ki bar min ragowa, yanxu nan Baban su ihsan ma xai koma asibiti ya sake karbo miki wani maganin" Murmushi nayi tare da cewa "Ai baxan bar ragowa ba yau na ƙara jin ƙarfin jikina sosai" A hankali na ja kwanon abincin na fara tsakuwarar doyar da ta soya min, bai fi guda biyu naci ba na ajiye kasancewar bakina babu dandano ko kaɗan, da kyar nake iya cin abincin, haka dai ta takura min sai da naci da yawa. Hira muka fara yi da Adda saratu tare da taya ni murnar yadda na samu kaina daga hannun malam Jibo, muna cikin maganar ne mijin Adda saratu ya shigo, ƙoƙarin tashi nayi xan fita na bar ɗakin sbd su samu damar yin maganarsu. Har na mike yayi min magana "kiyi xamanki mana Sa'adatu ba xama xan yi ba" Mayar da kallonsa yayi ga Adda saratu "ina takardar nan da aka rubuta mana magani bani na tafi yanxu na siyo" Cike da nutsuwa ta tashi ta mika masa sallama yayi mana ya fita. Dawowa tayi kusa da ni ta xauna tana fuskantata "Oh Allah mai iko Sa'adatu kin yar da kwallon mangwaro kin huta da kuda, da tuni yanxu kina gidan malam jibo kina fama da warin hammata" Kwashewa muka yi da dariya a tare "wato abin ma har da cin fuska Adda sweetyn nawa kike fadawa haka" Murmushi tayi "tunda sweetynki ne ai sai mu mayar da ke, ku cigaba da shan soyayya" Da sauri na dakatar da ita ina murmushi "Ina baxa ai ba a yi haka ba Adda, wato baxan iya mislata miki irin daɗin da nake ji ba a xamana a gidan nan, ji nake kamar an saka ni a aljanna, tunani ɗaya nake yi kawai ya xan yi da Baba" Cike da kulawa ta dube ni. "ki daina wannan tunanin ko yace baza ki koma masa gida ba a kan Malam Jibo xan riƙe ki har lokacin da Allah xai baki miji kiyi aure, dama ai zaman kuncin kike yi a gidan banda wahala babu abinda kike sha" Wani sanyi naji a raina "to amma kuma Adda Inna fa?" Dan tabe baki tayi "Innah ba matsala bace ita ma xata samu mafita insha Allah" Hirarmu muka cigaba da yi cike da farin ciki da annashuwa babu abinda yake damunmu, don ni tuni na cire tunanin Malam Jibo a raina. Bayan fitar mijin Adda saratu daga gida kai tsaye asibiti ya wuce, office din likita ya shiga don ya gaishe shi ya kuma faɗa masa yadda jikin Sa'adatu ya kasance. A hankali ya bude kofar office din ya shiga tare da sallama, yana ganinshi ya fara murmushi tare da yi masa sannu da xuwa, kujerar da ke gefensa ya samu ya xauna, hannu ya mika masa suka gaisa sannan ya xauna, ya mai jiki yayi masa. Fuskarsa a sake ya amsa masa da. "Jiki alhamdulillah yayi kyau sosai, don har ta kusa shanye maganinta yanxu wannan da ba a siya ba naxo na siya mata shi ne nace bari na shigo mu gaisa" Cike da farin ciki ya amsa masa "Ai kuwa ka kyauta kuma naji dadin xuwan da kayi, dama ina ta tunanin ina xan sake ganinka na baka labarin matsalar da ta taso" Gyara xama yayi tare da bashi hankalinsa "me kuma ya taso doctor" Sauke gilashin da ke idonsa yayi "kada ka damu ba wani abu ne mai xafi ba naga kamar hankalinka ya ɗan tashi" A tare suka murmusa "to ai dole ya tashi ni da nake da mara lafiya ai sai na xaci ko wani ciwon ne ya samu" Girgiza kai likitan yayi "ba ma a kan wannan matsalar bane a kan wadannan mutanen ne da ka fada min cewa ɗayan mahaifin mara lafiyar ne dayan kuma mijinta ne, to su ne suka dawo nan suka min ba dai-dai ba" Da sauri ya dube shi "me suka yi maka doctor?" A nan ya kwashe ya bashi labarin yadda suka yi da su malam Jibo, da irin cin mutuncin da suka yi masa, da kuma matakin da ya ɗauka a kansu. Ba ƙaramin dadin hakan mijin Adda saratu yaji ba sbd shi ma ya samu damar da xai kwatarwa Sa'adatu hakkinta, sbd idan kai tsaye ya kai su ƙara sai abin ya xama abin magana, a ce ya shigar da mijin yayar matarsa ƙara. A lokacin ya nuna damuwarsa, ya kuma nuna bai ji daɗin abin ba sbd kada likita ya gane akwai rashin jituwa a tsakanin su. "Da ka sani ba baka kai su ba doctor ka kyale su da halinsu" Cike da nutsuwa likitan ya sake dubansa. "To ai kyale su da ake yi ne yasa suke yin haka, ɗaukan matakin shi ne abinda ya fi dacewa sbd su kiyayi gaba, kuma su san bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane, kuma kaga ko ku kun samu hanyar da xaku warware matsalar da ta taso muku a kan auren yarinyar". Sauke ajiyar zuciya yayi "Haka ne kuma to ba komai xan koma gida na sanarwa da iyalansa halin da ake ciki" Number wayar mijin Adda saratu ya karba shi ma ya karbi tasa sannan suka yi Sallama. Tunda ya koma gida yake ta tunanin ta wace hanya xai bi ya fadawa Sa'adatu cewa an kama Babanta, yayi ƙoƙarin danne zuciyarsa ya fada mata amma sai ya kasa, sbd baxa ta so a ce mahaifinta yana hannun hukuma ba, duk da cewa ita kanta yana kuntata mata. Fita yayi ya nufi gidan malam Salisu dan ya fadawa Inna Salamatu inda mijinta ya makale. Kada a manta da comment share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:35 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *Masoyana masu bibiyar rubutuna ku yi hakuri baxa ku riƙa samun posting kullum ba sbd ina xuwa makaranta, sai dai a ranakun Litinin da talata da laraba da juma'a, na gode* *33* Ko da yaje bai samu ganin innah salamatu ba kasancewar bata nan, sai ɗaya daga cikin yaranta ya bawa sakon, tare da cewa ya faɗawa innarsa yadda suka yi, shi kuma ya kama hanyar tafiya gida. Yana zuwa ya sanarwa Adda saratu inda Baban Sa'adatu yake, ya kuma roketa da kada ta faɗawa Sa'adatu don kada hankalinta ya tashi, tunda har yanxu bata gama warkewa ba. *********** Washe gari ma yawon neman Baban Sa'adatu innah salamatu ta fita yi, ita da matan malam Jibo duk inda suka tsugunna sai sun bada labarin cewa da Innar Sa'adatu aka haɗa baki aka sace su, duk sun bi sun gama yaɗawa a unguwa. Babu inda basu je suna cigiyar shi ba amma babu shi ba labarinsa, hakan ba ƙaramin tada musu hankali yayi ba, don har ya'yansa na ma'aura duk sun xo daga gidan maxajensu tare da su ake yawon nemansa, gidan a cike yake da ya'ya ana ta jimami kamar gidan makoki, yau tun safe da suka fita basu dawo ba sai yamma. Dawowarta ke da wuya ɗaya daga cikin ƴaƴanta wanda mijin Adda saratu ya bawa sako ya shigo a firgice, don ko sallama bai samu damar yi ba sbd halin rudani da ya tsinci kansa a ciki, tunani kawai yake yanxu a ce kamar Babansa bai wuce kamun yan sanda ba, Babban abinda ya dame shi bai wuce rashin sanin abinda mahaifin nasa ya aikata ba, addu'a yake Allah yasa ƙaramin laifi ne ba babba ba, tana ganinsa ta miƙe tare da cewa. "Kaji wani labari ne dangane da mahaifinka?" Jikinsa sanyaye ya nemi guri ya xauna. "Eh naji innah amma ba labari ne mai daɗi ba" Gaba daya hankalin mutanen dakin ya dawo kansa kowa yana jiran abinda xai fito daga bakinsa. Cike da kosawa Innah Salamatu ta kara tambayarsa "Me ya faru da Baban naku, kuma yana ina yanxu"? Kansa a sunkuye ya amsa mata da "yana hannun sanda su suka kama shi" Dakin ne ya rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa, tare da mamakin jin yan sanda sun kama Mahaifinsu. Dafe kirji tayi tana salati "yan sanda kuma me ya haɗa malam da yan sanda shi da baya rigima da kowa kuma bai ci bashin kowa ba, don da akwai wata matsala tun a ranar da ya fita xai faɗa min tunda baya biye min komai, mun shiga uku na salame" Cikin nutsuwa yace "ba tada hankalin ki za kiyi ba innah, komai xai zo da sauki ke dai kiyi addua idan mun je a bamu belinsa" Kuka take yi kamar wacce ake ce ya mutu, cikin kukan take cewa. "me yayi aka kama shi kuma wanene ya faɗa maka ma an kama shi, dan ni har yanxu ban gama yarda ba" Nan yake bata labarin cewa mijin Adda saratu ne ya bashi sako ya faɗa mata, tana ji an ambaci cewa mijin kanwar babar Sa'adatu ne ta fita a fusace, ƴaƴan ne suka fara kiranta tare da tambayar inda zata je amma bata saurare su ba, kai tsaye kofar dakin innah ta nufa hannunta riƙe da muciya, sai dai tana xuwa kofar dakin ta tarar bata nan. Tsayawa tayi a bakin kofar tana xagi hade da cin mutuncin innah, jin abinda take yi ne yasa ya'yan suka fito suna tambayarta dalilin xagin da take yi. Cikin sarkewar harshe ta fara magana. "Wannan munafukar da ku ke gani ita ce ummul abasin shigar malam wannan masifar, da ita aka kulla komai, baku ga bata nan ba ta fita, yanxu haka mijin kanwarta ne yaxo ya fadi cewa an kama malam, sun yi haka ne don su kashe auren Sa'adatu ta samu lasisin yawon karuwanci, sun san idan basu bullo ta haka babu yadda za a yi ya bari auren ya mutu, tunda shi mutum ne mai taurin kai" Rike baki ya'yan suka yi, da yake duk tunaninsu iri daya ne sai suka hau xagin innah da Sa'adatu suna tsine musu, namijin ne kawai bai goyi bayansu ba. Gaba daya suka fita dan zuwa police station din, sai da suka biya ta gidan malam jibo suka sanarwa matansa sannan suka tafi tare. Da farko sun yanke shawarar xuwa gidan Adda saratu don ci mata mutunci, sai kuma suka canja shawara don kada su bata goma ɗaya bata gyaru ba. Tafiya suke ba nutsuwa kamar an koro su, kai tsaye suka kama hanyar shiga cikin police station din, daga can nesa aka daka musu tsawa, nan da nan jikinsu ya hau rawa, wani police ne ya karaso tare da tambayarsu. "Me yasa kuna xuwa xaku shige ba tare da kun neman izini ba, kuna tafe kamar an koro ku, mama son rashin da'a a nan, nan waje ne na ladabtarwa ba wajen rashin da'a bane, me ke tafe da ku"?? Bakin innah na rawa ta amsa da "maxajen mu aka kama shi ne muka xo mu gansu mu ji me suka yi aka kama su" Girgiza kai yayi tare da cewa. "Shi ne kuma ku ka saɓo gayya haka kamar masu zuwa gidan biki, ku zabi mutum uku waɗanda zasu shiga su ji abinda ya faru, amma baxa ku shiga gaba daya ba, ragowar su nemi guri nan su tsugunna" Innah Salamatu da danta da matar malam Jibo guda daya ne suka shiga wajen, police din ne yayi musu rakiya suka shiga har cikin office din da ya kamata su je. Gabatar da su yayi a wajen D.P.O tare da fadin abinda ke tafe da su. Umarni ya bayar da a shigar da su wajen wanda case din ke hannunsa, sai dai cikin rashin sa'a wanda case din ke hannunsa baya nan ya tashi daga aiki, don haka aka basu umarni da su tafi gida gobe su dawo. Cikin ladabi suka tsugunna suka yi masa godia, Inna salamatu ce ta dubi police din "dan Allah yallabai ko xamu samu ganin maxajen namu" Fuskar shi a d'aure ya amsa mata "baxa ku gansu yanxu ba sai gobe aka ce, ko bakya ganewa da Hausa da nayi magana" Jikinta a sanyaye ta amsa da "Na fahimta Allah ya kaimu goben" Cike da bakin ciki suka fito, ragowar waɗanda suka taho tare suna ganinsu suka fara tambayar su yadda suka yi, fada musu innah tayi bata samu ganin su ba ance sai gobe. Gaba daya bakin ciki da ɓacin rai ya bayyana a fuskarsu, daya daga cikin su ce tace "ya zama dole mu dauki mummunan mataki a kan wannan shegiyar matar duk wannan masifar ita ta janyo mana, ko hakan zai zama sanadiyyar mutuwata wlh yau sai naga bayanta sai dai a hada mu a kulle ni da su Baban" Goyon baya suka bata tare da cewa xasu taya ta a daki innar Sa'adatu. Comments and share *Jeeddahtulkhair😘* [2/19, 5:36 PM] Aunty Hibba: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Wannan shafin gaba ɗaya sadaukarwa ne gare ki HIBBATULLAHI ABUBAKAR (real hibbah) admin QUEEN'S OF HEART* *34* A fusace suka shiga cikin gidan tare da kiran sunan innah suna cewa kwananta ya kare idan ta isa ta fito wajensu, ji suka yi shiru bata amsa ba don haka cikin fushi, suka hankada kofar dakin har sai da ta karye sbd dukan da suka yi mata, cikin xafin rai suka shiga ciki suka hau duddubawa ko xasu ganta, ganin basu sameta a dakin ba ya sanya su fitowa tare da tunanin ko tana banɗaki ne, leka banɗakunan gida suka shiga yi suna ambatar sunanta suna xagi, duk yadda dan uwansu ya kai ga yi musu nasiha a kan su hakura da dukanta basu ji ba, don haka ya fita ya kyale su, tafiya yayi gidan da aka ce innah taje don shaida mata cewa kada ta dawo gidan tare da faɗa mata abinda suke shirin aikata mata. Dukkan Mutanen gidan ne suka fito kowace mace hannuna riƙe da abin duka. A hanya suka ci karo da juna cike da kulawa ta kira sunan shi tare da tambayarsa inda zai je, damuwa ce ta bayyana a fuskar sa a nan yake faɗa mata abinda ake shirin yi mata tare da bata shawarar kada ta koma gidan ta nemi wani wajen daban ta kwana har zuwa lokacin da fitinar xata lafa, komawa gidan yayi ya tarar duk sun fito da kayan dakinta suna watso shi waje, sbd takaici ma bai iya yi musu magana ba sai ya fita ya kyale su. Tunda ya fadawa Innah wannan maganar sai ta nemi dukkan wani ƙarfi ta rasa a jikinta, komai nata yayi sanyi, da har tayi niyyar komawa gidan amma kuma sai ta fasa, sbd bata shakkar dukkan abinda aka ce su innah salamatu za su yi mata, baxa ta taɓa musawa ba sbd dama basa kaunarta. Juyawa tayi ta nufi hanyar gidan Adda saratu, tun daga nesa Sa'adatu ta ji Muryar Innah da gudu ta karaso tare da rungumeta kasancewar tunda aka yi mata aure aka kaita gidan malam jibo bata sake tozali da innarta ba, kwantar da kanta tayi a kirjinta tana zubda hawayen takaici. Ita ma innar kukan take yi sai da suka yi mai isarsu sannan suka saki junansu, kama hannunta tayi suka shiga daki, sai da suka gaisa da Adda saratu sannan suka fara magana Wani farin ciki da walwala naji ya ziyarci zuciyata, naga innata wacce na kusan shafe watanni biyar ba tare da nayi tozali da ita ba, ji na nake tamkar a aljanna, mayar da kallona nayi ga innata sai naga kamar ba a cikin farin ciki take ba, wannan dalilin yasa na ƙara bada hankali wajen nazarin abinda ke damunta, ban iya cewa komai ba a lokacin, kasancewar suna magana da Adda saratu sai a nan nake jin abinda su Innah salamatu suke shirin yi mata. Cikin firgici na dubeta, kwalla naji na ƙoƙarin fito min a hankali na sa gefen mayafina na goge, muryata na sarkewa na fara tambayarta "me kika yi musu innah da har suke shirin yi miki wannan muguntar" Cikin ƙarfin hali ta buɗe baki ta fara zayyano mana abinda ya haɗa su, sai a nan nake ji an kama su Baba, ban ji daɗin kamun da aka yiwa Babana ba duk kuwa da irin tsanar da yayi min, shi ma Malam jibo ban so aka kama shi ba tunda yana da iyali, amma na san duk yadda aka yi wannan mummunan aikin suka aikata don ruwa baya tsami banxa. Mayar da hankalina nayi ga Innah tare da cewa "yanxu Innah wane hali suke ciki, ni baba ma nafi tausayawa wlh, ga shekaru ga kuma zaman kurkuku" Sauke ajiyar zuciya tayi "wlh ban sani ba Sa'adatu basu fada min komai ba, sbd sun ce ni sa aka kama su don na kashe miki aurenki ban san a inda aka tsaya ba har yanzu, sai dai muna sauraro Allah yasa mu ji alheri" Gaba daya muka amsa da "ameen" Tausayi tare da jimamin halin rudani da innah ta samu kanta a ciki, ba ƙaramin daga min hankali yayi ba ina tausaya mana sbd irin rayuwar da muke yi, tunda na taso nayi wayo ban san wani abu mai suna farin ciki ba ,kullum da irin matsalar da xata kunno kai, har abin ma ya fara xamar mana jiki. A ranar a gidan Adda saratu ta kwana tare da mu. ************ Washe gari bayan mun karya mijin Adda saratu ya kirata a waya tare da shaida mata cewa ana son ganinmu a police station ya kuma faɗa mata zai aiko mana da daidaita sahun da zai dauke mu ya kaimu, jikina ne ya dau rawa sbd ban taba shiga police station ba kuma bana fatan wani abu ya shigar da ni, sai gashi yau ta sanadin malam jibo da Baba xan shige shi. Rudewa nayi gaba datya na kasa yin komai, tsoro ɗaya nake ji kada su je su shirya mana sharri karshe mu koma hannu, har sai da Innah ta lura da irin halin rudani da nake ciki, kwantar min da hankali ta shiga yi muna wannan halin mai daidaita ya iso. Jikinmu a sanyaye muka shiga muka tafi, cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba muka isa wajen. A cike muka tarar da office din, innah salamatu da ƴaƴanta gaba ɗaya sun halarci gurin sai bin mu suke yi da kallon wulakanci, matan malam Jibo ba ma duk sun zo, su ma harara suka bi ni da shi gani suke kamar nice nasa aka kama mijin su. Su Baba da malam Jibo suna tsakiyar kanta a tsaye, ga kuma likitan da ya duba ni xaune a kan kujera, sai kuma yan sanda guda hudu da ke tsaye biyu a bayan su Baba, daya riƙe da littafi da biro, dayan kuma hannunsa riƙe da kulki da bindiga, gaishe su nayi gaba daya amma mutane kadan ne suka amsa. wajen xama aka nuna mana, jikina na rawa na xauna sbd ban saba ganin irin wannan ba, muna xama mijin Adda saratu ya shigo. Gyaran murya wanda case din ke hannunsa yayi tare da mayar da kallonsa ga likitan, "Doctor ga ka ga kuma masu laifi, ga kuma iyalansu don haka sai ka maimaita abinda suka yi maka kowa ya ji da kunnen sa" Gyara xama yayi ya fara zayyano abinda suka yi masa daya bayan daya. Daya police din yana rubuta dukkan abinda ya faɗa sai da ya gama tsaf. Police din ya mayar da kallonsa ga su Baba, fuskarsa a daure ya tambaye su. "Kun ji dai abinda yace kun yi masa ko, kun tabbatar da abinda ake xargin ku a kansa? Ko kuma kuna da ja" Cike da ladabi suka dago, ban taba zaton malam Jibo da Baba xasu yi laushi haka ba, har da sunkuyawa. Baba ne ya yi magana a madadinsu "Tabbas dukkan abinda ya faɗa haka yake babu karya a ciki, mun yi kuskure sai dai muna fatan a yi mana sassauci" Daka masa tsawa yayi "kana so a yi maka sassauci kaje ka aikata, babu makawa sai mun kai ku kotu kun girbe abinda ku ka shuka gobe ma kwa sake cin mutuncin wasu" Jikin su ne ya hau rawa, suna rokon a yi masu sassauci ni kuwa ban san lokacin da na fara kuka ba, ina taya su rokon likita ya yafe musu. Tsawa ya daka wacce sai da kowa ya shiga hankalinsa "ku saurara ba ku da hurumin da xaku tursasa wanda aka yiwa laifi a kan cewa dole ya yafe, sai abinda yake so shi xamu yi tunda mu aikin al'umma muke yi, ba son xuciyar wani xamu bi ba" Dukkan yayan gidanmu kowa kuka yake yi sbd matuƙar aka kulle Baba tamkar mu aka kulle. A hankali likitan ya dubi police din yace "Albarkacin iyalansu na yafe musu, amma da tasu ne sai kowannensu ya ja sarka tunda ba su da mutunci kuma basu san shi ba. Da har ɗan sandan ya nunawa likitan kada ya hakura, ya kai maganar gaba amma sai yace ya yafe, haka dai aka turza ƙarshe aka bada belin su a kan dubu ashrin, nan fa ake yinta malam Jibo ba dubu ashirin baba ma haka, haka dai aka yi karo karo tsakanin ya'yan gidanmu da matan Malam Jibo aka biya musu.. Sai da aka gama case din likita tsaf, sannan mijin Adda saratu ya miƙe tare da yin magana. "Nima Ina da nawa case din da su yallabai" Cike da kulawa ya bashi amsa da "ina saurarenka" Gyara tsayuwa yayi tare da nuna Malam Jibo. "Wannan shi ne mijin Sa'adatu yar wannan bawan Allahn da aka gama magana a kansa yanxu" ya nuna ni tare da nuna Baba Sannan ya cigaba da magana. "Ya aura mata wannan mutumin a don bata so, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar yake musguna mata, bayan haka baya bata abinci baya kula da ita, bai san wani hakki nata ba, satinta kusan biyu tana cuta kaita asibiti ba, a dalilin hakan ne yasa ya ci wa doctor Mutunci, kullum kokarinsa ya xai yaga ya cutar da ita, banda Sa'adatu yarinya ce mai tarbiyya da tuni abinda muke ji a radio ya faru da ita, amma sai ta danne zuciyarta ta hakura ta zauna, amma duk da haka bai saurara mata ba, kullum sai ya haɗa mata sharri a wajen babanta, har cikin gida mahaifinta yaje ya daketa ya ci zarafin ta, duk a kan wannan mutumin idan ba so suke su tunxurata ta zama mara kirki ba me suke so da ita" Sai da ya karanto dukkan abinda malam Jibo yayi min da abinda Baba yake mana ni da innah tun daga farko har ƙarshe sannan yayi shiru, girgiza kai kawai ɗan sandan yake yi shi kansa abin ya d'aure masa kai, dama kuma doctor ya fara bashi labarin halin da nake ciki. Mayar da kallonsa yayi gare ni "ke baiwar Allah kin ji dukkan abinda aka fada shin da gaske me duk wadannan abubuwan da ya fada sun faru?" da sauri na girgixa kai nace "haka ne abinda ya fada" Sake mayar da kallonsa yayi ga malam Jibo "kai ma kaji abinda ya faɗa a kanka gaskiya ne" Bakinsa na rawa yace "Ba haka bane dukkan abinda ya faɗa karya yake min kawai yana so ya kashe min aure ne" Kallonsa police din yayi kawai ba tare da yace komai ba, sannan ya sake mayar da kallonsa ga mijin Adda saratu. "Ina ganin wannan matsalar kotu ce kawai xata iya rabata, xamu rubuta takarda mu mika ga kotu a saka ranar da za a saurari ƙarar, ina ganin komai zai fi zuwa da sauki, yanxu xan bada belin mutum ɗaya ku tafi, shi kuma wannan malamin xamu rike shi tunda bamu gama da shi ba, ana tuhumarsa da cin zarafin 'ya mace, dole sai an warware xai koma gida" Cike da girmamawa yace "hakan ma yayi yallabai Allah ya wuce mana gaba" Jin an ambaci baxa a sake shi bane yasa malam Jibo yayi saurin cewa "Dan Allah a taimaka a kashe maganar nan yau, wlh ina cikin damuwa na baro yayana da iyalina ban san halin da suke ciki ba" Wani kallo dan sandan ya bi shi da shi " kana so a kashe magana amma kake yi mana musu a maganar mu, ka fada mana gaskiyar abinda ke faruwa, idan ba haka ba kuma kotu ta raba ku" Jikinsa na rawa ya fara cewa "Abinda ya faɗa wani haka yake wani kuma sharri yayi min, amma tunda har yayi magana, ina so ku fadi abinda ku ke so a yi a wuce wurin kawai, xan gyara dukkan halina baxan sake kuntata mata ba, kuma xan kula da ita" Kallon mijin Adda saratu police din yayi "to kaji abinda ya faɗa me ku ke so a yi, kuna so ya gyara halinsa ne ko kuwa??" Mayar da ajiyar zuciya yayi "Ni yanxu yallabai ba ni da wani zaɓi tunda ga yarinya nan a zaune ita xata fadi yadda take so a yi" Kiran sunana yayi a hankali na dago na dube shi. "Fada min yadda kike so a yi" Kaina a sunkuye na amsa da "Ina so ya sauwake min" Kamar na sokawa Baba da Malam Jibo kibiya haka na gani, nan da nan gumi ya fara yanko musu kallona Baba yake yi yana min alamar na janye maganar, ni kuwa na nuna kamar ban ganshi ba. Bakin malam jibo na rawa yace "Gaskiya baxan iya rabuwa da ke ba Sa'adatu idan kuma xan rabu da ke sai an biya ni dukkan abinda na kashe a wajen aurenki" Fuskar ɗan sandan a d'aure ya dube shi "kai kada ka kuskura ka sake magana idan ba ni nace kayi ba nan ba wajen hayaniya bane wajen sulhu ne da maganin matsala" Sake nuna shi da hannu yayi "kaji dai abinda yarinya ta faɗa bata sonka tana so ka sauwake mata, a yanzu kana da zaɓi ko dai ka sake ta ko kuma mu mika ku kotu tayi muku Shari'a" Wani gumi ne yake ta yanko masa cikin dusashewar murya yace "Na sake ki saki biyu......." Innah Salamatu ce ta xaro idanu tare da cewa "malam kana ganin ana barna a gabanka baxa ka hana ba" Sai da police din ya dakatar da ita sannan tayi shiru. *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *35* Bayan wajen yayi shiru ana jiran umarnin police ya bada damar tafiya ko tsayawa, mikewa Adda saratu tayi tare da cewa ina da magana, damar yin magana ya bata. Gyara tsayuwa tayi tana mai fuskantar mutanen da ke wajen. "Ina ganin yallabai kamar mun yi suya mun manta da albasa, domin kuwa akwai wani abu guda daya da muka manta ba mu yi magana a kansa ba wanda barin nasa ba karamin illa bane ga rayuwar waɗannan bayin Allah, yallabai ina so a shiga tsananin yayata da wannan matar" nuna innah salamatu tayi tare da kafeta da ido, dafa kirji Innah Salamatu tayi, xata yi magana kenan Adda saratu ta katseta ta cigaba da bayani. "Da kuma mijinta sannan da ragowar ƴaƴansu, abinda nake so shi ne yallabai ka jawo hankalin mijinta ya dinga sauke hakkin da ya rataya a wuyansa, sannan ya saurara da cikin zarfinta, ya kamata kuma ya kafawa matarsa da ya'yansa dokoki domin suna take hakkin wadannan bayin Allah ba tare da sun yi musu komai ba, kullum burinsu su zage su sannan su ci musu zarafi, cin kashin da suke yi mata ita da ƴaƴanta yayi yawa yanzu haka kafin mu taho nan sun yi yunkurin dukanta, Allah ne bai sa sun samu damar hakan ba, sannan labari ya iske mu cewa ilahirin kayan dakinta duk sun fito da shi waje sun lalata mata, wannan Dalilin yasa nayi maka magana, don haka a shiga tsakanin su da ita, idan mutunci baxai hada su ba kada su kuskura su shiga gonarta ballantana har su yi tunanin dukanta" Tana gama magana ta koma ta xauna. A hankali ya juya ya kalli Baba nasiha mai ratsa jiki yayi musa, kasancewar police din mutum mai addini, ya kawo masa hadisai da ayoyi waɗanda suke magana a kan sauke hakkin aure. Mayar da kallonsa yayi ga su Innah Salamatu da tawagarta. "Naji dukkan abinda ake xargin ku da shi, don haka wannan ya xama karo na farko kuma na karshe idan muka sake jin wani labari makamancin wannan,to wlh gaba daya sai hukuma ta dauki mataki a kanku, duk abinda ya biyo baya kada ku zargi kowa sai kan ku" Umarni yayi da a rubuta takarda dukkansu su saka hannu a kan baxa su sake cin zarafin mu ba, haka kuwa aka yi kowa ya saka hannu sannan aka bada su Baba muka tafi gaba ɗaya. Kallo daya xaka yi musu ka san abinda ya faru bai musu dad'i ba shi kuwa malam Jibo da iyalansa basu biyo mu ba, sai da muka yi nisa sosai sannan suka biyo bayan mu, wani irin kallo Innah Salamatu take mana tana so tayi magana amma ba dama, sbd dokar da aka saka kafa mata. gidan Adda saratu muka wuce su kuma suka tafi gida. Zuciyar mu cike take da farin ciki, na dade ban ji dadi irin na yau ba Allah ya kwato ni daga hannun azzalumi Jibo. shigar mu gidan ke da wuya naji sallamar Baba, don su innah ma basu san yaxo ba gabana ne ya yanke ya fadi, cikin xuciyata na fada "me kuma ya dawo da Baba wajenmu" sai da ya sake yin sallama ta biyu sannan na amsa. A sanyaye na sanya hijabi na fita, tsugunnawa nayi har kasa tare da cewa "sannu da xuwa Baba ashe kaine kaxo ya hanya?" shiru yayi min ba amsa, jin bai amsa min bane yasa na dago ido don ganin yanayin da fuskarsa ke ciki. Idanunsa na gani sun yi ja da dukkan alamu yana cikin damuwa, a hankali ya daga baki yace. "Kira min babarki xan yi magana da ita, sannan ina so kuma ku taho tare da kanwar uwar taki duk ina son ganin ku a nan" A sanyaye na tashi na shiga ciki, abinci na tarar suna ci don haka na nemi guri na tsaya sbd bana so na katse musu abinda suke yi, gaba ɗaya na kasa zama sbd ban san da sabon abinda yaxo mana da shi ba, maganar Innah ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na tsunduma a ciki. "Tunanin me kike yi haka Sa'adatu kika yi shiru ke kadai, ni fa bana so kike yawaita wannan tunanin kada ki je ki cutar da kanki" A hankali na dago "ba tunani nake yi ba Innah Baba ne yaxo yace yana so xai yi magana da ku, shi ne ban fada muku ba na bari ku gama cin abinci" Xare hannunta tayi daga kwanon da dukkan alamu ita ma jikinta yayi sanyi "Me kuma ya dawo yayi ba yanxu muka rabu da shi ba?" Ita ma Adda saratu tayi mamakin dawowarsa, ajiye abincin suka yi suka saka hijabansu muka fita. Sallama muka yi masa amma babu wacce ya kalla a cikinmu ballantana har mu sa ran zai amsa mana, waje muka samu, su Innah tsayawa suka yi, ni kuma na samu gefe na tsugunna. Innah ce tayi ƙarfin halin cewa "Malam lafiya naga ka sake dawowa naga yanxu muka rabu ko wani abin ne ya sake tasowa?" A yatsine ya dago Yana bin mu da wani irin kallo. "ko ban ce komai ba kema kin san abubuwa sun dade da tasowa, kuma burinki na son toxarta ni ya cika, kin wulakanta ni kin tozarta amanar da Allah ya baki, kin yi sanadiyyar girgizar al'arshin Allah a yau, da sannu xaki girbe abinda kika shuka, ba wani abu ne ya kawo ni ba illa dai na fada miki cewa tunda kika yi kokarin da har auren Sa'adatu ya mutu, to sai ki nema mata wajen da xata koma ta cigaba da rayuwa don ni dai baxan iya rike karuwa a gidana ba, taje duk inda zata je amma ko a hanyar gidana na ganta duk abinda nayi mata ita ta siya. Sannan abu na biyu kina da xabin da xaki dawo ki ci-gaba da xaman aure da ni, idan kema kin xabi zawarcin ne sai ki faɗa na sawwake miki, kinga yarki ta samu yar uwa kenan, na bar ku lafiya" A fusace ya fice ya bar mu, bin sa muka yi da kallon mamaki, a cikin mu babu wanda ya iya yin magana sbd mamakin jin waɗannan kalaman nasa. Murmushin takaici innah tayi tare da kallon Adda saratu "ko kaɗan waɗannan kalaman nasa basu tayar min da hankali ba, sbd idan da sabo na saba jin su, kuma batun komawa gidan sa nima na gama baxan koma ba, Gara na koma ƙauye nayi xamana ina jin xan fi samun kwanciyar hankali a can, amma wannan masifa har ina" Girgiza kai kawai Adda saratu take yi, cikin nutsuwa ta dube ni "Sa'adatu kada ki damu da wannan abin da yake faruwa jarrabawar rayuwa ce kowa da irin yadda take xuwar masa, ni nayi alkawari xan cigaba da riƙe ki baxa kiyi kuka ba matuƙar kina tare da ni, ke kuma yaya kada kice baxa ki koma, tunda aure ya xama ibada dole kici karo da abinda zai sosa miki ranki, sbd ita aljanna ba a samunta da sauki, kiyi hakuri ki koma sbd rashin komawarki ba shi ne xai warware waɗannan matsalolin ba, kuma idan kika ƙi komawa kamar kin bawa salamatu wata kofa ne na cin karenta babu babbaka, amma xamanki a gidan shi kansa nasara ne tunda baxa ta sake tayi yadd take so ba, tunda dai yanxu an shiga tsakanin ku da ita, nafi tunanin duk wannan abin ita ce ta shirya masa yaxo ya faɗa, don haka ki koma xaman gidan ya xama dole ko tana so ko bata so" Ni kaina nafi so Innah ta koma sbd baxan so a ce ni ina gida ita ma tana gida ba, abin xai iya zama abin magana, tunda mutane basa raina abinda za a yi ta xance a kansa. Jikinmu ba ƙarfi muka koma daki, rarrashin mu Adda saratu take yi da kalamai masu dadi sai da Innah ta huce sannan tafi gida. Comments nd share *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *36* Bayan komawar Innah gida sai da muka kirata a waya muka ji yadda xaman nasu ya kasance tsakanin ta da su innah salamatu, faɗa mana tayi babu wani matsala da take fuskanta sai dai kawai yanxu basa ko kallonta ko magana tayi musu basa amsawa sai dai su bi ta da harara, amma dai ta samu sauƙin cin zarafin da suke mata, wannan maganar ba ƙaramin faranta mana tayi ba, domin kuwa zuciyata cike take da tunanin yadda rayuwarta xata cigaba da kasancewa ita kaɗai a gidan ba tare da ni ba, sai dai har yanzu ina kewar innata kuma ina kewar wajen da nake kwana domin na kwashe kwanaki da dama ba tare da nayi tozali da shi ba sai dai kuma an haramtawa min shiga gidan hakan yasa na ƙara bawa xuciyata hakuri, na fara cire tunanin gidan daga zuciyata. Rayuwa nake yi mai tsananin dadi a gidan Adda saratu, mijinta ba mai kudi bane sai dai yana da rufin asiri sosai, iya xamana a gidan ban nemi komai na rasa ba, yanzu babban tunanin da yake yi shi ne mayar da ni makaranta, ba ƙaramin farin ciki na shiga ba sbd na dade ina son yin karatu amma Baba ya hana ni. Sakkowa nayi daga gadon da nake kwance kasancewar tun bayan da na farka da asuba nayi sallah ban rintsa ba, sai da na gyara gida nayi abincin karyawa sannan na koma bacci, a hankali na janyo jiki na sakko daga kan gadon tare da duba agogon da ke manne a bangon dakin 12:30 na rana, da sauri na ƙara mutstsike idona gami da yin miƙa, toilet din da ke cikin dakin na shiga na kunna fanfo na hada ruwan dumi nayi wanka, bayan na kammala na shirya cikin wata atamfa ja (red) wacce Aunty saratu ta bani, nayi matuƙar yin kyau Kuma kayan sun karbi jikina sosai, har sake kallon kaina nake yi a mudubi kamar ba ni ba, na fara dawowa cikin nutsuwata amma lokacin da nake gidan Malam Jibo ficika baxa ka siye ni ba sbd yadda na fita a hayyacina duk nayi baƙi na rame. Jan mayafi na yafa tare da kullo kofar dakin na fita, dakin Adda saratu na shiga tare da yin sallama kwance take a kan doguwar kujera ta tsurawa screen din waya ido tana ta faman karatu, a hankali na ƙarasa wajenta ina mai murmushi "Dadina da ke Adda saratu bakya gajiya da karatun littafi" Murmushi tayi tare da tashi daga kwanciyar da tayi "Hmm tunda bakya yi baxa ki gane dadin karatun littafi ba da kuma muhimmancinsa, akwai abubuwa da yawa na karuwa da xaki gani kuma xaki koyi xaman duniya da iya zama da mutane" Gyara xama nayi ina mai fuskantar ta "Nima dai xan fara Adda ko don na san yadda xan kama izuddeen dina" Murmushi tayi tare da dafa kafadata "ban san lokacin da kika zama mara ta ido ba Sa'adatu ko xaman gidan malam jibo ne yasa kika xama haka?" Sunkuyar da kai nayi tare da rufe idona "Ba haka bane Adda kawai ke kadai nake iya faɗawa haka, kuma don ma izuddeen din ya shiga raina ne shi yasa" Cikin nutsuwa ta dube ni "A shawarce ki manta da maganar izuddeen Sa'adatu kiyi addu'a Allah ya kawo miki wani don a ganina izuddeen kamar yayi miki nisa yanxu" Cikin ɓacin rai na tsinci kaina idanuna kamar zasu zubar da hawaye amma sai na daure "Me yasa kika ce haka Adda" Hannuna ta riƙe "Ni fa ban ce ki tada hankalin ki ba, na fada miki haka ne sbd ina ganin hakan shi ne xai fi sauki a gare ki, kin manta irin abinda Babanki yayi masa da irin cin kashin da ya yi wa iyayensa, a ganina ko izuddeen ya yarda zai aure ki iyayensa baxa su bari ba, sbd xasu tuna abinda aka yi musu sannan xasu dakatar da shi su ce ɗansu baxai auri baxawara ba" Ihu ne kawai ban yi ba sbd takaici tabbas abinda ta fada gaskiya ne, amma har yanxu zuciyata bata yarda cewa izuddeen baxai aure ni ba sbd na san irin mugun son da yake min. Shirun da nayi ne yasa ta gane ina cikin damuwa "Addu'a ita ce mafita Sa'adatu kada ki damu kowace mace mijinta take aure, idan har izuddeen rabonki ne babu wanda ya isa ya hanaki auren shi, idan kuma ba rabonki bane duk son da kike masa haka xaki ganshi ki kyale, to babu damuwa a cikin lamarin aure Allah ya dade da tsara komai" Naji daɗin maganganunta kuma sun kwantar min da hankali, mikewa nayi ina gyara mayafi "Dan Allah Adda ina neman alfarma xan je wajen Rukayya na ganta kin ga na dade rabona da ita" Tsura min ido tayi ba tare da tace komai ba "Ni fa bana son fitar nan Sa'adatu idan kina yawan fita munafukai xasu samu damar cewa wani abu, amma tunda wajen Rukayya ne don Allah kiyi sauri kada ki dade" Naji dadin barina da tayi, sbd a wajen Rukayya ne kaɗai xan samu labarin inda izuddeen yake da matsayin da soyayyata take a wajensa Jikina na rawa na nufi gidan *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *37* Cike da nutsuwa nake taku a hankali kaina a ƙasa har na isa kofar gidan su Rukayya, da sallama na shiga cikin gidan, tun daga uwar daki ta jiyo muryata da gudu ta taso muka rungume juna muna murna, hannun mu riƙe da na junanmu muka shiga dakin tare da samun guri mu zauna. Ina umma na tambayeta, faɗa min tayi tana banɗaki tana wanka, Sannu da xuwa tayi min tare da jawo min flask din abinci gami da cewa. "Ga abinci ki ci Amaryar malam don na san kin yi kewar girkin umma" Murmushi nayi "Ai kuwa dai kamar kin sani" Plate ta janyo ta fara xuba min abincin, kallonta nayi ina murmushi "kada ki zuba abincin nan Rukayya wlh a koshe nake sai da na ci abinci na fito" Tsayawa tayi da zuba abincin tana hararata "Tunda malam ya shagwaba ki ai dole kice baxa ki ci irin girkin mu ba, lallai Sa'adatu amarci yayi daɗi, to ko bakya so sai kin ci abincin nan" Cigaba da xuba abincin tayi, sai da ta haɗa komai sannan ta turo min shi gabana. Cike da kulawa ta dube ni "Sannu da zuwa Amaryar malam kin yi kyau sosai kin canja, kin fi komai a kan xuwan da nayi kwanaki, yaushe rabon da na ganki aminiyata, yau dai wato yaga dama ya bar ki xaki yi zumunci" Ɗan murmushi nayi wanda sai da hakorana suka bayyana " Hmm ashe fa baki san wainar da ake soyawa ba ko?" Kallo ta bi ni da shi "Kamar yaya, yi min bayani kawata" Rausayar da kai nayi "mun rabu da Malam Jibo fa nayi zaton ma kin ji labari don duk xancen ya baxa gari" "Ban ji ba wlh, ai kin san baxan ji ba tunda bana shiga harkar yan unguwar nan sbd munafuncinsu" Nayi tsammanin xan ga ɓacin rai a fuskarta sbd aurena ya mutu sai naga ta daka tsalle tana murna " Alhamdulillah Allah ya taimake ki kin yar da kwallon mangwaro kin huta da kuda, wannan masifaffen aure ina ranarsa, ai da naga kin yi kyau kin canja na xaci kyallin amarci ne, ashe kyallin yan matanci ne" Dariya muka sa gaba dayan mu, a dai-dai lokacin ummansu ta shigo, tun daga nesa take ta buɗe ido, da alama tana son tabbatar da gaskiyar abinda idanunta ke nuna mata ne, da ƙarfi tayi magana tare da ajiye abin wankan da ke hannunta. "Wa nake gani haka kamar Sa'adatu?" Murmushi nayi "nice umma ba idonki bane" Da sauri ta karaso "Sannu da xuwa amarya yau an tuna da mu kenan" Rukayyah ce tayi saurin cewa "ki daina cewa amarya umma Sa'adatu sun rabu da Malam Jibo Allah ya taimake mu" Dafe kirji tayi tana salati "Oh amma ban ji daɗi ba mutuwar aure ba tada daɗi ko kadan Allah yasa haka ne yafi alkhairi" Amsawa muka yi da ameen. Sai a lokacin nake labartawa Rukayya sanadin rabuwata da shi da irin azabobin da na sha bayan ziyarar da ta kai min, ba ƙaramin farin cikin rabuwa da shi tayi ba, sbd dama tana cikin mutanen da gaba ɗaya basa son tarayyata da shi. Tambaya na jefa mata. "wai kuwa ina izuddeen ne?" Shiru tayi min tare da tafiya dogon tunani sannan ta dago ta dube ni "Tun bayan rabuwar ku da shi sau biyu kawai muka taɓa yin waya, sai a wajen abokinsa nake jin labarin cewa ya samu aikin custom yanzu haka yana can yana training" Ji nayi gaba ɗaya jikina ya mutu, tabbas abinda Adda saratu ta faɗa min na cewa izuddeen yayi min nisa gaskiya ne, ban iya cewa komai ba sbd halin da na tsinci kaina. A hankali ta dago da kaina tana dubana "ya naga kamar kin damu Sa'adatu? Na san dole xaki ji ba daɗi na rashin izuddeen, sbd shi ne mutum na farko da ya fara koya miki SO, amma hakan kada ya sanyaya gwiwarki idan har izuddeen rabonki ne xai dawo gare ki, fatana dai ki cigaba da addu'a sai kiga komai ya zo da sauki" Sauke ajiyar zuciya nayi tare da cewa"Haka ne insha Allah xan cigaba da yi" Nayi zaman sama da awa biyar a gidan muna ta hirar yaushe gamo da kuma labarin izuddeen, ban tafi ba har sai da nayi magariba, har gida Rukayya ta raka ni. ********* Malam Jibo ne zaune ya haɗa kai da gwiwa ya rasa me yake masa daɗi a ransa, tun bayan rabuwar su da Sa'adatu bai sake jin wani abu mai suna farin ciki ba, ko abinci ya daina ci kullum tunaninsa ya zai yi ya dawo da ita gidansa, burinsa yana cika zai ɗauke ta ya mayar da ita kauyensu ta cigaba da rayuwa a can. Ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya kira tare da umartarsa ya kira masa ɗaya daga cikin almajiransa, da sauri yaron ya fita ya sanar da shi ya shigo. Da Sallama ya shiga shagon da malam Jibo ke xaune, tsugunnawa yayi tare da gaida malam din. Sakin labulen shagon malam Jibo yayi Sannan ya dawo ya xauna yana mai fuskantar sa "wani aiki nake so ka taya ni" A ladabce ya amsa da "to malam" Wata farar takarda ya xaro tare da mika masa. "Ina so kayi min sirrin da Sa'adatu Amaryar da na aura kwanaki, xata dawo wajena da kafafunta, kayi iya bakin kokarinka wajen ganin ka mallake min ita ta dawo gidan nan ko tana so ko bata so, nima ina nan xan bada himma wajen yin wani, na raba aikin ne sbd abin namu yayi sauri" Tashi kaje, daga yanxu nake so ka fara aiki, nan da jibi kuma nake son ganin sakamako. Jikin sa na rawa ya tashi yana fita malam Jibo ya bushe da wata dariya yana mai cewa "Da kafarki xaki zo kina neman gafara Sa'adatu indai ni ne na isheki riga da wando har da yar ciki" Comment nd share *Jeeddahtulkhair😘* [3/2, 3:04 PM] Jeeddahtulkhair Tijjani😘: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *38* Sake bushewa yayi da wata irin dariya wadda har sai da ya tuntsura, Allah ne kaɗai ya san irin muguntar da yake shirin kullawa Sa'adatu wani abu zuciyarsa ke hasaso masa matuƙar ya samu Sa'adatu a yanxu shi kaɗai ya san irin garar da xai kwasa, domin ya dade da sanin Sa'adatu tana dauke da baiwa mai yawa, ƙoƙari ɗaya zai yi shi ne yayi duk mai yiwuwa ta dawo cikin rayuwarsa, tunanin irin lugwigwitar da zai yi mata yake yi, saboda ya san dole yanzu yarintar ta taqara fitowa tunda ta samu huta tare da nutsuwa. Kamar wanda aka zabura ya tashi ya janyo wata adaka da ke ajiye a gefensa, ya fara fito da wasu irin takardu yana ware wanda zai yi amfani da su fuskarsa na ɗauke da murmushin mugunta. Bincike yake yi sosai sai dai har yanxu ya kasa gano wacce xai yi amfani da ita, wacce da ya xuba aiki xai kama Sa'adatu. Rigingine ya kwanta yana cigaba da dogon tunanin da ya saba. ★★★★★ Salamu alaikum nace sannan na sanya kaina cikin gida. Da murna "Adda saratu ta karɓe nii Sa'adatu har kin dawo amma kin yi sauri sosai" Zubewa nayi a ƙasa ina share gumin da ya ɗan taru a fuskata gami da cire hijabin da ke jikina. "wash Allah wlh na gaji addah ko don na kwana biyu ban yi tafiya ba, ga shi kuma a qafa na taho ban samu abin hawa ba, shi yasa fa bana son fita sbd a gajiye nake dawowa" Riƙe haba tayi tana kallona "oh!! ni saratu Yanzu yar tafiyar nan har kin gaji Sa'adatu, gaskiya ki rage lalaci abinda gidan ba wani nisa ne da shi ba, a ƙafa ma xaki iya zuwa, lallai yaran zamanin nan, idan bakwa motsa jiki wlh xaku tsufa da wuri" Murmushi nayi ina gyara xama, mikewa nayi xan karbi wukar da take yanka salad na Taya ta aiki dakatar da ni tayi. "A'a ki bar shi na kusa karasawa, shiga ki samu ruwa a fridge ki sha, baki dade da fita ba suka dawo da wuta" Amsawa nayi da to Adda, dakko ruwan nayi na dawo muka cigaba da hira. "Ya kika baro innar Ruqayyah da fatan dai kowa lafiya" "Suna nan lafiya duk suna gaishe ki sosai ashe wai basu samu labarin abinda ya faru ba, sai da naje nake fada musu, abinda yake bani mamaki Adda babu wanda yake baƙin cikin rabuwata da Malam Jibo kowa murna yake min" "Ai dole a yi miki murna Sa'adatu Allah ya raba ki da ƙaddara Allah dai ya kyauta ya kare ki daga sharrinsa, abinda nake so da ke yanzu Sa'adatu, ba zama za kiyi ki ta bacci ba, dole mu dage da addu'a don kin san wanan algungumin mutumin ba rabuwa damu zai yi ba, sbd ki san zuciyarsa babu alkhairi Allah ya shige mana gaba ya raba mu da sharrin masu sharri." Jikina a sanyaye na amsa da "Ameen" tashi nayi na shiga kitchen na kama mata girki, har na fara haɗa miya naji kamar an tsikare ni na fito, daga gefenta na tsaya yana dubanta "Adda kin ji izuddeen ya tafi training din custom dan Allah Adda ki taimake ni kije gidan su izuddeen ki jiyo min labarinsa" Sakin wukar da ke hannunta tayi "Ke Sa'adatu ina raba ki da izuddeen din nan har yanxu kin ki karbar shawarata ko, wannan ai Bara a kufai kike yi, tunda kina son mutumin da ya manta da ke a rayuwarsa ya fita daga shirginki, dan Allah ke a tunaninki yanxu me izuddeen xai yi da ke, ai ya wuce ajinki kiyi addu'a Allah ya haɗa ki da wanda ya fi shi, amma kwallafa rai a kanshi ba naki bane" Hawaye ne suka kwace min baxan iya cire son izuddeen daga raina ba har abada sbd shi ne mutum daya tilo da ya fara koya min soyayya, kuma duk duniya ina ji da shi kadai xan iya rayuwar aure, amma xan yi kokarin bawa xuciyata hakuri kamar yadda tace, kitchen din na koma na cigaba da aikin gabana. Tun daga wannan ranar na dage da addu'a tare da kiyamullaili ina gayawa Allah ya kare ni daga sharrin malam jibo ya haɗa ni da dukkan alkhairi idan kuma izuddeen alkhairi ne a gare ni Allah ya tabbatar min, ita kanta Adda saratu tana taya ni wannan dalilin ne ya ƙara min nutsuwa na daina shakkar komai tunda ina gayawa Allah kuma na san xai min maganin matsalata. Ranar wata Lahadi ina zaune a dakina ina tsifa, Ihsan yar Adda saratu ta shigo da gudunta ta faɗa jikina, rungumeta nayi ina kallon kyakkyawar fuskarta. Cikin siririyar muryata ta fara min magana. "Aunty saadatu kizo inji Abban mu yana kiranki" Sauke ta nayi daga jikina na mike "Kice ina zuwa Ihsan" Hijabina na saka na tafi amsa kiran mijin Addah Cikin nutsuwa na janye labulen dakin tare da cewa "Salamu alaikum" Fuskarsa a sake ya amsa min "wa alaikumussalm" Jikin kofar dakin na damu na tsugunna kasancewar dakin Karami ne kuma Adda da sauran yaranta duk suna ciki shi yasa dakin cunkushewa har na rasa wajen da xan xauna. Cike da kulawa ya dube ni "Shigo mana Sa'adatu" A ladabce na shiga na samu kusa da Ihsan na xauna, kaina a sunkuye nace "Barka da dawo wa Abbah ya kasuwa" "Alhamdulillah Sa'adatu ya zaman hakuri Allah yayi mana jagora, dama wata shawara muka yi da Auntynki naga yana da kyau ki koma skull saboda zaman a haka ba dadi, kinga yanzu rayuwa ta canza sai kana da ilimi za'a tafi da kai, na samo miki wata makaranta a nan kasan layin mu ta manya ce akwai fannin ilimin boko dana islamiyyah kinga riba biyu kenan, tunda kina da haddar Alkur'ani babu wani abu da xai miki wahala, ina fatan zaki mayar da hankalin ki har muga abinda Allah zai yi a nan gaba" Wani irin hawayen farin ciki ke bin fuskata tare da wani dadi mara misaltuwa daya mamaye ni, ban taɓa xaton wannan ranar xata riske ni da wuri haka ba, ashe burina zai cika Allah kenan mai yadda yaso, wanda yayi hakuri zai ga ribar hakan, wanda yayi gaggawa kuma xai yi nadama" Ban san lokacin da na xube ina godiya ba tare da yi masa addu'a, tabbas mijin Adda saratu mutum ne mai karamci da kirki, na dade ban ga mutum irinsa ba, iya xamana a gidan bai taɓa banbanta ni da ya'yansa ba, kuma ko a fuska bai taba nuna min bai son na xauna a gidansa ba, wannan dalilin yasa nima nake girmama shi don yayi min rikon da ko mahaifinta bai min irinsa na. "Na gode sosai Allah ya kara girma insha Allah bazan baka kunya ba" Yaji dadin godiyar da nayi masa, cikin sakin fuska yace "Tashi kije kinji insha Allah gobe zaki fara zuwa Allah yayi miki albarka" Amsawa nayi da Ameen na fita. Alhamdulillah Allah kalmar da nayi ta maimaitawa kenan bayan na dawo dakina, ina san karatun sosai musamman na boko amma sbd an fi karfin mu aka danne hakkina ko primary ban yi ba, banda arzikin Alkur'ani da ko Hausa baxan iya karantawa ba, sai ga shi cikin falalar Ubangiji, Allah ya dube ni zan yi karatu kamar kowace diya mace. Kasa cigaba da tsifar nayi sbd farin ciki, fita nayi naje na dauro alwala nazo na fara jero nafil filun godia ga Allah da ya nuna min wannan rana. *Jeeddahtulkhair😘* [3/3, 8:23 PM] Jeeddahtulkhair Tijjani😘: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @Jeeddahtou* *39* Washe gari misalin karfe tara na safe naji muryar mijin Addah yana kirana, fitowa nayi cikin shiga ta kamala sanye nake da atamfa na rufe jikina da dogon hijabi wanda sai da ya kawo min idon sahu, cike da nutsuwa na tsugunna na gaida shi tare da cewa "Abba na shirya" Addah ce ta fito daga daki tana yi mana fatan alkhairi da dawowa lafiya Makaranta ce mai girma tare da wadatattun ajujuwa, cike take da dalibai manya da ƙanana, tsarin makaranta yana da kyau sannan akwai cikakkiyar tarbiyya uwa uba kuma ga karatu, makaranta ce da ta haɗa bangarori biyu boko da islamiyya, wannan dalilin ya sanya mutane tururuwar sanya ƴaƴansu a ciki, muna shiga office din shugaban makaranta muka nufa, a hankali mijin Adda yasa hannu ya tura kofar office din tare da yin sallama, da girmamawa aka karɓe mu tare da bamu gurin zama, form din da muka zo da shi ya miƙawa shugaban makarantar, duba form din ya shiga yi tare da kiran wani malami ya bashi umarnin ya tafi da ni ya gwada ni, a nan na bar mijin Adda saratu suna magana, ni kuma na bi bayan malamin ina taku cikin nutsuwa. Bakin wani aji muka je zaunawa yayi a kan wani benci ya bude file din ya fara tambayata, izifi nawa na haddace yayi mamaki kwarai da nace na haddace Alkur'anin gaba ɗaya, gwada ni ya fara yi duk inda ya janyo min sai yaga na karanta shi dai-dai babu wani kuskure, Kasancewar mun yi karatu mai kyau a makarantar malam Jibo, bangaren littafai muka dawo a nan ne kaɗai na samu matsala, kasancewar makarantar da nayi Kur'ani kadai ake koya mana, don haka ya yanke shawarar sanya ni cikin wani aji da suka bude kwanan nan don na samu karatu tun daga farko. Raka ni yayi tare da nuna min ajin da xan shiga, a ladabce na saka kai cikin ajin, tarar da su nayi suna ta tilawa ban yi wa kowa magana ba sbd bana so na katse musu abinda suke yi, guri na samu na xauna sai da suka kammala na miƙa musu hannu muka gaisa, wadda nake kusa da ita ne ta juyo ta dube ni fuskarta dauke da murmushi. "Sannu da xuwa bakuwa, ya sunanki? Ni sunana Khadijah" Nima murmushin nayi mata tare da bata amsa "Yauwa na gode Ni sunana Sa'adatu" A hankali muka fara yar hira kafin malam ya shigo, a ɗan hirar da nayi da ita na fahimci Khadijah tana da kirki da san mutane, kwatanta min gidansu ta shiga yi, ashe ma makociyar mu ce gidansu yana kusa da gidan Adda saratu, naji dadin hakan sbd xan samu abokiyar tafiya kasancewar makarantar tana da dan nisa da gidan da nake. Muna cikin maganar malam ya shigo. Gyara xama muka yi muka bada hankalin mu gare shi, yana shigowa, Ajin yayi shiru kamar ruwa ya cinye kowa da alama dai ana jin tsoron malamin yadda ya kamata, duk da kasancewar sa saurayi hakan bai sa dalibansa sun raina shi ba, kallo daya xaka yi masa ka fahimci mutum ne da baxai karbi raini ba, fari ne sosai yana da manyan idanuwa da dogon hanci fuskarsa kewaye take da saje wanda ya sha gyara, a hankali ya buɗe ɗan karamin bakinsa yayi sallama, cike da ladabi muka amsa gaba ɗaya. Ji nayi yan ajin suna gaishe shi tare da kiran sunan shi da mu'allim Ahmad, a nan na san sunansa Ahmad. Dora idonsa yayi a kaina da sauri na sunkuyar da kaina, tambaya yayi yaushe aka kawo ni gaba ɗaya yan ajin suka amsa masa da yau naxo, girgiza kai yayi ya samu guri ya xauna. Ƙarin Bulugul maram yayi mana biyawa biyu naji na iya, don haka da aka xo biyawa gaba ɗaya muryata kadai kake ji a ajin, malamin yayi mamakin kokarina da yadda na mayar da hankali kan karatuna kamar dama can a cikin ajin nake, duk abinda aka biya mana cikin kankanin lokaci na haddace shi, mamakin ƙoƙarina yan ajin ke yi a ranar mutane da dama sun so kulla alaƙar ƙawance da ni, amma ban saki jiki da su ba sbd ina so na fahimci halin kowa, dama ni a halittata ban fiye sakin jiki da jama'a ba, sai na san halin kowa nake sakin jikina. Da aka tashi tare muka taho da khadeejah muna tafe muna hira har muka xo kofar gidan Adda saratu, sbd gidan su yana ɗan gaban gidan mu, a nutse na saka kai na shiga soron gidan, me xan gani??? Malam Jibo ne jingine da bango ya tsura min ido yana kallona, ban bari mun haɗa ido da shi ba na sunkuyar da kaina sbd na san sharrinsa xai iya saka wani abin a idonsa don na rikice nace sai shi, shan gabana yayi ya tare min hanya, ki tsaya ki saurare ni Sa'adatu nayi nadamar abinda nayi miki a baya yanxu nazo gare ki na gyara kuskure na, ki daure ki kalle ni da wannan kyakkyawar fuskar taki, ina so kiyi min murmushinki mai kwantar min da xuciya, wlh na dade a cikin baƙin ciki da damuwa tun bayan da kika tafi kika barni, wani kululin bakin ciki ne ya tokare min kirjina, ban san lokacin da nayi kukan kura ba na hankade shi da karfina, da sauri yayi kokarin fixgo ni Allah ya bani sa'a na shige gida a guje ina haki. A firgice na faɗa dakin Adda ina kuka, na shiga ukuna Adda wannan mutumin neman ganin bayana yake ban san wanda ya nuna masa gidan nan ba, kinga yanxu yaxo yana magiya wai sai na koma gidansa, na shiga uku ki taimake ni ki shiga tsakanina da wannan azzalumin kada ya salwantar min da rayuwa. A birkice Adda ta tashi tana dubana, me kike son fada min haka sa'adatu? kada dai kice wannan masifaffen mijin naki ne ya sake biyo ki. Girgiza kai nayi alamar shi ne, hijabinta ta dakko ta saka, tare muka fita da ita, duba soron ta shiga yi ko xata ganshi amma babu shi babu dalilinsa don haka muka dawo cikin gida. Dakina na shiga na faɗa kan gado na fara aikin kuka, na tsani malam jibo ko sunansa bana so a ambata sbd muddin na kasance a ƙarƙashin sa, rusa min farin cikina xai yi na har abada, da na koma gidansa gara na mutu na gwammace mutuwa ba aure a kan dai na aure shi, ganin tunani na ƙoƙarin illatani ne yasa na tashi na dauro alwala na shiga jero nafila tare da karatun Alqur'ani, a ranar daga ni har Adda kasa cin abinci muka yi sbd tunani Allah Allah muka rika yi mijinta ya dawo mu sanar da shi halin da ake ciki. Mun kasa aikata komai sai aikin tunani, bayan isha'i ya shigo ganin halin da muke ciki ne yasa ya tambaye mu Adda ce ta bayyana masa komai, yaji haushi kwarai sbd shi ma ya tsani malam Jibo, ba ƙaramin bata masa rai yayi ba da har yaxo gidansa. A lokacin ya fita yaje har gida ya same shi, yau ma a kofar gida ya tarar da shi ya riƙe zungureren carbi yana ta faman muzurai, yana ganin shi ya san ba kalau ba don haka ya mike yana ƙoƙarin mika masa hannu su gaisa, bai karba ba ya bishi da wani kallo yana huci ji yake kamar ya rufe shi da duka, buɗe baki ya hau yi wato sakona ya isa gareka kenan, ai dama Sa'adatu tana sona shiga tsakaninmu aka yi, nayi farin cikin ganinka, na san ko ta qini kai mai tursasata ne ta so ni dole. A fusace ya kalle shi bana son maganar banxa me kake so kace min wannan ya xama na farko kuma na karshe da xan kara ganinka a gidana, idan kuma ba haka ba wlh wlh sai na daureka. Matsawa kusa da mijin Adda yayi yana masa wani kallo, kai ka isa kaxo har kofar gidana ka fada min magana a kan matar da nake so, duk baƙin cikin ka sai Sa'adatu ta dawo hannuna idan kuma kace baxa ta aure ni ba ,ina mai tabbatar maka cewa ita ma har abada baxa tayi aure ba ko kare bai isa yaxo wajenta ba shashashan banxa da wofi. Murmushin takaici yayi tare da furzar da numfashi mai xafi, sai me don ka hana Sa'adatu aure ka sani baka isa ka cutar da ita ba sai da yardar Allah, kaine jahili dakiki da har kake ganin xaka iya yin wani abu a kanta, amma babu wanda ya isa ya hana wani aure sai da yardar Allah, yana gama faɗa masa ya wuce ya kyale shi. Wani tsaki malam Jibo ya buga, dole na dauki mummunan mataki a kanku, a sati biyu nake so yarinyar nan ta dawo hannuna, kafin shekara nayi mata ciki makiya su mutu da bakin ciki Sa'adatu ta zama ta malam jibo har abada, tattara babbar rigarsa yayi ya koma ya xauna.. A fusace muka ji ya shigo don ko sallama bai samu yi ba sai da ya ɗan nutsu, ya zama dole mu yi wa tufkar nan hanci saratu wannan mutumin son ganin bayan yarinyar nan yake yi, a firgice Adda ta dube shi me kake fada min haka Abba, da yake da sunan da take kiranshi kenan Gyara tsayuwa yayi yanxu daga wajen wannan mugun nake, shi ne yake faɗa min wai idan Sa'adatu bata koma hannunsa ba ko kare baxai zo wajenta da niyyar aure ba, maimakon naga ta bata rai sai naga tayi murmushi. Lallai sai yanxu na tabbatar da cewa malam Jibo jahili ne da rigar malamai, shi har ya isa yace wani baxai yi aure ba, insha Allah yana ganin Sa'adatu xata yi aure ta haihu kuma ta bar hannunsa da yardar Allah. Nima ko kadan maganar bata taɓa min zuciyata ba, sbd na san Allah shi ke bayarwa kuma shi ke hanawa, a ranar kwana nayi ina salloli gami da neman sauki a wajen Allah, *Jeeddahtulkhair😘* [3/4, 10:03 PM] Jeeddahtulkhair Tijjani😘: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *40* Washe gari da wuri na tashi na gama aikace-aikacen da zan yi wa Addah sai da na karya sannan na fito daga dakina, a bakin kofar dakin su na tsaya na gaida su tare da yi musu sallama, nace xan tafi makaranta addu'a suka yi min, kafin na fita naji sallamar Khadijah ta biyo min makaranta. Fuskarta ɗauke da murmushi take min magana kiyi sauri Sa'adatu mu tafi, nasan da kyar ne idan mu'allim Ahmad bai shiga aji ba, kin san dai halinsa sarai baya son makara, ko da yake dai baxa ki fahimci wane ne shi ba tunda jiya kika shigo ajin namu amma sannu a hankali xaki fahimci halinsa, ni har Allah Allah nake yi a canja min aji na huta da takurarsa, yana matsa mana da yawa ragowar ajujuwan makarantar duk ba haka ake musu ba. Jikina na rawa na dubeta wayyo Allah ban sani ba wlh ai da ko karyawa baxan yi ba xan tafi, amma dai baya duka ko? Dariya tayi baya duka amma abinda xai miki sai ya fi dukan ban haushi ke dai ki taho mu tafi kya ji labari idan mun je aji. Da sauri da sauri muke tafiya kamar xamu tashi sama, bana so daga fara karatuna mu fara samun matsala da malami shi yasa duk na shiga damuwa. Bayan mun shiga makarantar kuwa shi muka fara hangowa a bakin ajin mu yana janyo kofar ajin, gabana ne ya fadi tare da nunawa khadeejah abinda ke faruwa ku san da gudu muka ƙarasa bakin ajin, tararwa muka yi har ya fara karin Alkur'ani, ja da baya muka riƙa yi aka rasa wanda xai buɗe kofar ya shiga, ni nayi shahada na fara yin gaba ita kuma tana makale a bayana, a hankali ta min rada a kunnnena ke Sa'adatu ba a shiga fa kai tsaye sai an nemi izni, ko saurarenta ban tsaya yi ba na saka kai cikin ajin tare da yin sallama a takaice, babu wanda ya amsa min kasancewar suna karatu, dakatar da abinda yake yi yayi yana bina da wani kallo na tuhuma. A ladabce na tsugunna tare da cewa mu'allim ina kwana. A hankali ya dago dara-daran idanuwansa fuskarsa a murtuke ya sake dagowa don ganin wacce zata karya masa dokar aji, ya dade yana nazari kafin yace min wani abu sauke ajiyar zuciya yayi sbd ganin yarinyar da jiya tunaninta ya hana shi bacci, ya dade yana mamakin kansa tare da tambayar zuciyarsa ko menene dalilin da yasa ya tsinci kansa a irin wannan yanayin, shi dai ya san a tsayin lokacin da ya ɗauka a rayuwarsa yau yana da shekara 33, babu wata diya mace da ta taɓa burge shi ballantana har ta hana shi bacci, amma kuma menene dalilin da yasa wannan ƙaramar yarinyar ke san haifar amsa da wani abu dai bai saba da shi a rayuwarsa ba, dakewa yayi ya sake kallona bai ce min komai ba ya mayar da hankali kan Alkur'anin da yake karantawa ni kuma ya barni a tsugunne, sai da ya gama karatun sa tsaf sannan ya waiwayo ya kalle ni. Kece bakuwar da aka kawo jiya ko? Kaina a sunkuye na amsa masa da eh, murtuke fuska ya sake yi sannan ya cigaba da magana, wannan ajin namu yana da ka'idoji da sharudda wanda na san baki sani ba ko? Cikin nutsuwa na girgixa masa kai, gaba daya idanun yan ajin yana kanmu suna son ganin yadda xata kaya a tsakanin mu. yadda yake min magana ne ya basu mamaki, sbd shi baya yi wa dalibansa magana a hankali ko kadan, hakan yasa daliban ke ɗari-dari da shi, sbd baya sakar musu fuska komai da xafi yake musu. Cigaba yayi da magana, daga yanzu idan kin xo kin tarar na riga ki shigowa aji to kada ki shigo ki tsaya a bakin kofa har sai na gama na baki izinin shigowa, sannan wannan ya xama karo na karshe da xan sake ganinki da kayan gida kafin wani satin ya kewayo kiyi kokari ki dinka kayan makaranta, duk maganar da yake yi kaina na sunkuye sai da ya sallame ni naje na xauna sannan na dube shi. Cikin siririyar muryata mara karfi nace "mu'allim da......" Kwarjinin da yayi min ne yasa na kasa ƙarasa maganar da xan yi sbd yadda ya tsare ni da manyan idanuwansa, kamar baya son yin magana yace min, me kike son faɗa min. Sunkuyar da kai nayi "Akwai abokiyar karatuna a waje tare muka xo" Kallona yayi ba tare da yace komai ba, bude kofar ajin yayi ya kira khadeejah jikinta na kyarma ta shigo bai ce mata komai ba ya nuna mata guri ta xauna, har muka yi karatu muka gama gaba ɗaya bai juyo ya tuhumi khadeejah ba, yau ma ku san na riga kowa iya karatu don waɗanda basu gama iyawa ba ma ni na cigaba da koya musu. Mutane da dama sun yi mamakin yadda malam ya ɗagawa khadeejah kafa bai ce mata komai ba, wasu har suna xargin ko akwai wani abu a tsakanina da shi, shi yasa har ya kyaleta sbd ni. Yau ma mu biyu muka dawo daga makaranta muna tafe muna hirar mu, ina shiga gida naji muryar innah, da gudu na ƙarasa na faɗa jikinta ina murna da ganinta, a hankali tasa hannunta ta ɗan ture ni tare da kallon fuskata, ke dai bakya girma Sa'adatu, murmushi nima nayi ya za a yi na girma da hawa cinyarki innata, yadda na dade ban ganki ba ai dole xuciyata ta cika da kewar ki. Tambayarta lafiyar Babana nayi da sauran yan gidanmu, duka ta faɗa min suna cikin koshin lafiya, kuma ta fada min yanzu tana zaune lafiya babu mai keta mata alfarmarta. Tashi nayi na shiga dakina don na bar su innah su yi hirarsu ta xumunci, dama irin tarbiyyar da tayi min kenan, matuƙar tana da bako bana saka ta a gaba naji me xasu fada, fita nake yi naje nayi harkokina. Cire hijab dina nayi sannan na shiga kitchen don xubo abinci. Daga can nesa naji innah na faɗawa Adda saratu wata magana wacce tasa na xubar da abincin da ke hannuna sbd yadda maganar ta daki kunnena. Ku biyo ni rashin comment shi ke hana ni typing *Jeeddahtulkhair😘* [3/7, 6:26 PM] Jeeddahtulkhair Tijjani😘: 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *41* Karaf naji a kunnena Innah na bawa Adda labarin zuwan doctor wajenta wai yana neman aurena, ba ƙaramin dukan zuciyata maganar tayi ba, zuciyata ce ta fara tafasa naji kamar na fashe da kuka, mamaki ne ya kamani ko ya aka yi ma ya gano gidanmu har ya samu ganin Innah, tambayar kaina na shiga yi, anya Baba ya san abinda ya kawo doctor gidanmu kuwa? Na san ko ya faɗa masa ma baxai amince da aurenmu ba, tunda abubuwa marasa dad'i sun faru tsakaninsu. tsayar da abinda nake nayi na cigaba da sauraren abinda suke fada, shawarar Adda saratu ta nema a kan ta bashi izni yaxo wajena ko kuma a dakatar da shi zuwa wani lokaci? Wani radadi da zafi zuciyata ta hau yi min, a gaskiya yanxu babu niyya ko shirin aure a tare da ni, hasalima ni tsoron maxan nake ji gani nake yi kamar irin halinsu daya da malam Jibo, yaushe har na fito daga tarkon malam jibo da har za a sake kokarin tura ni a wani, a yanxu dai bana burin auren kowane namiji idan ba izuddeen ba, na san shi kaɗai xai iya rike ni amana ba tare da ya cutar da ni ba, ji nayi hawaye na ƙoƙarin fito min, a hankali nasa gefan mayafina na share, har cikin zuciyata ban jin don doctor ballantana har na aure shi, sbd babu wanda na yiwa tanadin soyayyata sama da izuddeen, da wannan tunanin nawa naji innah ta sake cewa, zata sa yaxo wajen mijin Addata su tattauna yadda abin namu xai kasance, amma a yadda na lura ita innar tawa taji dadin xuwansa kuma tana so mu kasance tare, don a maganarta na gane tana cikin farin ciki sosai. Tambayarta Adda saratu tayi ko yaya aka yi ya gano gidanmu, sai da ta mayar da ajiyar zuciya sannan ta karanta mata yadda aka yi ya san inda nake, faɗa mata tayi cewa. Tare suka yi karatu da makocin mu Dr mukhtar, don haka yaxo wajensa don ya kawo masa ziyara, sai yaga mahaifina zaune a kofar gida, shi ne yake tambayarsa dama makocinsa ne, nan yake bashi labarin babana da irin halinsa, don shi kansa a lokuta da dama yana taimaka mana da abinci da kudi don ya san irin rayuwar da muke yi ni da innata, doctor bai yi mamakin jin halin mahaifina ba sbd shi ma ya gwada masa irin halin nasa ya gani, a nan yake faɗa masa cewa yana sona da aure, amma bai san inda xai ganni ba kuma baya tunanin cewa Babana xai bari alaƙarmu ta kullu ballantana har ya aure ni, karfafa masa gwiwa yayi a kan ya aure ni, sbd kyawun halin da muke da shi ni da innata, ya kuma labarta masa wuyar da muka sha a hannunsa Baba da innah salamatu, washe gari da ya dawo shi ne ya raka shi wajen kanin mahaifina baban su salim yayi masa bayanin abinda ke tafe da shi, yayi farin ciki sosai da jin xancen kuma shi ne yake labartawa innah ya kuma gargadeta da taja bakinta tayi shiru kada ta ɗaga Maganar kowa yaji, shi ne yau taxo wajen Adda saratu take bata labarin abinda ya faru. Jikina a sanyaye na fito ina jan ƙafa duk jijiyoyin jikina sun yi sanyi, yadda naji Innah ta karbi xancen ne ya daga min hankali sbd bana so hakan ya zama sanadiyyar rabuwata da izuddeen, wannan yar maganar ba ƙaramin tada min hankalina tayi ba, sbd bana son abinda xai katse min karatuna duk da dai na san cewa doctor mahmud mutum ne mai fahimta kuma ya san halin da nake ciki, baxai katse min ilimina ba. Kama hanyar shiga daki nayi, Adda ce ta kwala min kira a hankali na waiwayo ta lura da yanayina sosai kamar ina cikin damuwa, jikinta ne ya bata cewa naji dukkan abinda suke tattaunawa shi yasa yanayina ya canja, zuba min ido tayi tana girgixa kai tare da cewa ba ki da lafiya ne Sa'adatu naga yanayinki ya canja. Girgiza mata kai nayi almar eh ban koma wajensu ba, na shiga daki na faɗa kan madaidaiciyar katifata na kifa kaina Ina tunani. Tabbas halin da na samu kaina a ciki yanzu babbar ni'ima ce, domin a da irin wannan baiwar muke nema amma Allah bai bamu ba, sanadin hakan ne yasa har aka aura min malam jibo, godiya nayi ga Allah da ya fara share min hawayena ya azurtani da wanda yace yana sona, tambayar xuciyata nayi me yasa xan shiga damuwa don Allah ya haɗa ni da miji irin doctor mahmud na san matukar na same shi na gama dacewa, dukkan abinda nake tunanin samu a wajen izuddeen xan same shi a wajen doctor, to me yasa xan damu kaina da tunani? Babban abinda ya fi a gare ni shi ne nayi addu'a na nemi zabin Allah, tashi nayi xan fita na dauro alwala sai kuma na yi tunanin ashe ba ni da tsarki, don haka na koma na kwanta kan katifata ina cigaba da tunani ban san lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba, ko tafiyar innah ban sani ba sai da na tashi aka fada min ta tafi gida. Ko da na tashi Adda bata yi min xancen ba nayi tunanin sai ta fara faɗawa mijinta, abinda suka yanke na shawara sannan sai ta fada min. Yau na samu kusan sati biyu ina xuwa makaranta kullum cigaba ake samu a harkar karatuna, ku san xan iya cewa duk ajinmu babu daliba kamata, wannan dalilin yasa sunana ya fara zagaye sassan makarantar babu wanda bai san Sa'adatu Salisu ba, don wannan karon musabakar da makarantar zata je ina cikin daliban da xasu wakilceta. Kamar kullum yau ma kawata khadeejah ce ta biyo min makaranta, ciwon kai mai tsanani da nake fama da shi ne ya hana ni zuwa nayi ƙoƙarin na daure naje amma hakan baxai yiwu ba, don haka Adda ta bata sako ta fadawa mu'allim kafin mijinta yaje ya fadi uzurina. Na ɗauki tsawon kwanaki uku ko tsakar gida bana fitowa, sai a kwana na hudu na samu na ɗan fito, sallamar Rukayya naji da sauri muka rungume juna muna murna, dakin Adda ta shiga ta gaisheta sannan muka shiga dakina. Tare muka xauna na dakko mata ruwa, tayi min ya jiki sannan na koma gefe na haɗa kai da gwiwa, dafa kafadata tayi wai har yanzu jikin ne Sa'adatu. Girgiza kai nayi ba iya ciwon kai nake fama da shi ba har da ciwon zuciya, a firgice ta dubeni, me ye Haka Sa'adatu, wannan wane irin abu ne xaki sa kanki a matsala. Tsare ni tayi tana tambayata a kan abinda ke damuna. Nan na kwashe labarin doctor na bata. Murmushi tayi wlh kin bani kunya kawata sbd wannan xaki sa kanki a damuwa to albishinki. Bude baki nayi nace mata goro, abinda ya kawo ni gidan nan kenan na fada miki cewa izuddeen ya kusa dawowa jiya abokinsa yake bani labari, kuma ko da suka yi waya ya fada masa kina ina kinga kuwa kina xuciyarsa bai manta da ke ba Wani farin ciki ne ya lullube xuciyata naji kamar an yi min kyautar hajji da umara ban san lokacin da na rungume Rukayya ba ina kukan farin ciki idan akwai abinda nafi bukata a rayuwata bai wuce izuddeen ba, na san shi ne waraka daga dukkan matsaloli na... Ganin yadda nake farin ciki ne yasa Adda ta tambaye ni, Sa'adatu lafiya tun daxu kike murmushi kamar wacce aka yiwa kyauta da aljanna. Labarin abinda Rukayya ta faɗa min na bata amma ga mamakina sai naga ta tabe baki ta tafi ta barni ba tare da tace komai ba. Jikina ne yayi sanyi xuciyata ta kasa bani amsar abinda take nufi. *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *42* Samun guri nayi na xauna a tsakar gida ita kuma ta wuce dakinta, kallon mamaki kawai take yi min wanda ni kaina ban san fassararsa ba, nayi jira sosai ko xata dawo na sake tambayarta dalilin rashin saurarar abinda na faɗa mata, amma bata dawo har na gaji na tashi, shiga dakinta nayi tarar da ita nayi tana ninke kayan su husna, karba na fara taya ta, ina mata aikin ina ɗan jefo mata maganar izuddeen ko Allah xai sa ta tanka min, amma sai naga ta share ni ba tare da ta bani amsa ba, da naga bata son zancen sai kawai na kyaleta na shiga harkokina, ina gamawa na koma dakina na kwanta. Shigata ke da wuya naji sallamar yaro a tsakar gida, wai yana nemana da sauri na fito don jin abinda ke tafe da shi, takarda ya miƙo min rufe take da envelope da dukkan alamu wasika ce aka aiko shi ya kawo, mamaki ne ya kama ni, cikin nutsuwa na tambaye shi ko wanene ya aiko shi? Cike da ladabi ya bani amsa da cewa wani mutum ne shi ma bai gane ko wanene ba, umartar yaron nayi da ya biyo ni naje naga ko wanene, dakin Adda na fara shiga na fada mata abinda yaron ya faɗa min, hijabinta na sanya muka fita tare amma abin mamaki bamu samu wanda ya aiko shi ba har ya tafi, don haka na kyale shi ya tafi ba tare da na cigaba da tambayarsa ba, sbd ko wanene xan gane shi ta hanyar wasikar da ya aiko da ita. A sanyaye na shiga dakin Adda, tsaye na tarar da ita hannunta rike da takarda bata buda ba tana jiran dawowata, tambayata tayi ko naga wanda ya bani sakon, a hankali nace banga kowa ba. Miko min tayi, "karbi ki bude Sa'adatu" girgiza kai nayi "a'a ki bude ki gani Adda" hannu tasa ta fara buɗe wasikar, ga mamakin mu sai muka ga rubutun ajami ne da shi aka rubuta wasikar, miko min tayi tare da cewa, "karbi Sa'adatu kece yar makarantar allo ke xaki iya karantawa" Karba nayi na fara budewa. Ina ganin yanayin yadda aka rubuta wasikar da irin takardar da aka yi rubutun da ita na san sakon malam Jibo ne, jikina a sanyaye na fara karantawa. _sallama gare ki hasken idaniyata, wacce ta guje ni a lokacin da nake da bukatar kulawarta_ _gaisuwa mai yawa da fatan alkhairi a gare ki amaryata mai share min hawayena Sa'adatu, da fatan kina cikin koshin lafiya,na rubuto miki wannan wasikar ne domin na kara jaddada miki soyayyata da kaunata a gareki,ki sani duk inda kika shiga a fadin duniya kina cikin raina har abada baxan taɓa mantawa da ke ba. Ina dada tunasar da ke cewa kiyi gaggawa ki amince da komowa gidana idan ba haka ba kuma xaki dawo ba tsiya ba arxiki ,don nayi alwashin muddin ina doran kasa babu wani da namiji da ya isa yayi tarayya da ke idan ba ni ba, ina fatan baza kiyi taurin kai wajen bin umarnin mijinki ba,sannan xaki sanar da masu hure miki kunne dangane da kudurina a gare ki_ _Ki huta lafiya daga mijinki mai kishinki mai kaunarki Sheikh Jibo_ Ina gama karanta wasikar na kalli Adda, kallon kallo muka riƙa yi da ita, gaba ɗaya mun kasa magana, kallona tayi kamar xata xubar da hawaye "Ina so ki tattara nutsuwar ki Sa'adatu kiyi watsi da dukkan abinda yake faɗa a kanki, ki sani babu wanda ya isa ya amfanar da ke ko ya cutar da ke sai da iznin Allah, don haka ki ɗauki wannan maganar tasa a matsayin tatsuniya, ke dai ki kama Allah kuma ki dage da addu'a babu abinda xai miki da yardar Allah" Ban iya cewa komai ba sai girgixa mata kai kawai da nayi, tashi nayi na faɗa dakina na fara kuka, tabbas na yarda da maganganun Adda, amma ina kara jin takaicin abinda ya faɗa min, idan da wanda ya jefa ni a wannan halin bai wuce Mahaifina ba, da bai hadani da malam Jibo ba da baxai yi tunanin yi min wani sharri ba, na san bai isa ya cutar da ni ba sai abinda Allah ya rubuta min amma duk da haka ina jin ciwon abinda yake furtawa zai aikata a kaina don na dade da sanin ba imani gare shi ba, tashi nayi na fara addu'a ina kai kukana wajen Allah tare da neman tsari ga sharrin da ake shirin kunno min. A ranar cikin baƙin ciki na kwana ban yi cikakken bacci ba sbd damuwa, yau ma da wuri na tashi na shirya don tafiya makaranta, kamar kullum sai da na gama aikin gida na tabbatar Adda baxa ta bukaci komai ba idan ta tashi daga bacci sannan na tafi, ina fitowa kofar gida naci karo da kawata khadeejah. tare muka rankaya makaranta, muna tafe tana min hira sbd damuwar da nake ciki bana samun damar amsa mata, har sai da ta fahimci akwai abinda ke damuna, tambayata ta shiga yi tana min naci na faɗa mata damuwata amma sam naki amincewa na buda mata cikina, haka dai ta gaji ta kyale ni. Ku san yau mun riga kowa zuwa aji har shi kanshi malamin, don haka muka fara muraja'ar karatun mu, rufe fuskata nayi da Alkur'ani ina ta faman kuka yau ko kadan ban ji xan iya karatu, sbd tunani da damuwar da suka cika xuciyata ina a nan halin mu'allim yaxo, ba tare da bata lokaci ba ya fara yi mana kari, shi kansa ya lura da yanayina ba irin yadda ya saba ganina bane. Sai da aka kammala karatu yake min ya jiki sbd fashin kwanki uku da nayi ban zo makaranta ba, a hankali na amsa da na warke, shi kansa bai iya jin me nace ba sbd kukan da ya ci karfina ya hana ni bude baki nayi magana, har aka gama ƙarin sauran littafai ban dago ba idona rufe yake da littafi ina ta faman kukan da na kasa tsayar da shi, kiran sunana yayi tare da cewa na buɗe fuskata duk a tunaninsa ko surutu nake yi. Muna hada ido da shi yaga idanuna sun yi jawur fuskata har ta kumbura sbd kuka, a razane ya dube ni. "Lafiya me ya same ki Sa'adatu, ko wani abin ku ka yi mata kafin naxo" yana Maganar yana kallon yan ajin Da sauri suka bashi amsa "wlh bamu sani ba mu'allim tunda tazo da safe take kuka" Mayar da kallon shi yayi ga khadeejah wacce take a gefena, ita ma tambayarta yayi ko ta san abinda ya same ni, ita ma irin amsar da yan aji suka bashi ta faɗa masa. Cike da tausayawa ya dubeni tare da cewa na biyo bayansa, cikin nutsuwa na tashi na bi shi. office din malamai muka shiga, kujera ya samu ya xauna sannan ya umarce ni da na xauna a ta kusa da shi. Cike da girmamawa na xauna, tsura min manyan idanunsa yayi yana naxarina sannan ya bude baki a hankali yace. "Fada min abinda yake damunki Sa'adatu tunda kike ban taɓa ganin ki a irin wannan yanayin ba, ki fada min ko me ke damunki nayi alkawarin xan taimaka miki matukar ina da iko a kan haka" A hankali na dago idona bude baki nayi xan yi magana kuka mai tsanani ya kama ni, maganar gaba daya ta makale na kasa fitar da ita, rarrashina ya shiga yi da kalamai masu sanyaya xuciya. Lallabani yayi sosai har sai da hankalina ya kwanta na fara dawowa cikin nutsuwata, labarin aurena da malam Jibo na fara bashi da kuma wasikar da ya rubuto min yau da abinda aka rubuta a jikin wasikar. Cike da mamaki yake kallona tare da tambayata "dama kin taɓa aure Sa'adatu?" A sanyaye na daga masa kai alamar eh. Cike da tausayawa ya Girgiza kai. Cigaba yayi da tambayata dalilin da yasa malam Jibo ya sake ni da abinda yasa yake min haka, ban rufe masa komai ba na bashi labarin dukkan abinda ya faru tsakanin mu, ba ƙaramin tausaya min yayi ba, sannan ya bani addu'o'i yace na dage da karanta LAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH indai ina yinta ko asiri ko wani abu bai isa yayi tasiri a kaina ba, ko da kuwa da aljanu aka haɗa ni, sbd LAHAULA taska ce daga taskokin gidan aljanna, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya faɗa mana, ya kara min da addu'o'i masu yawa yace na dage da yinsu. Nasihohin da yayi min sai suka zama tamkar waraka a gare ni na daina jin tsoron komai na miki al'amurana ga Allah *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *43* Cikin nutsuwa na tashi ina tafiya a hankali kamar wacce kwai ya fashe wa a ciki, kallo daya xaka yi min ka san ina Cikin matsananciyar damuwa, don ma nasihohin mu'allim sun fara tasiri a gare ni ne shi yasa na dakata da kukan da nake yi, bi na yayi da kallo mai cike tausaya wa, ina kaiwa bakin kofa naji ya saki wata ajiyar zuciya, tare da kiran sunana, waiwaya nayi muna haɗa ido na sunkuyar da kaina, bai iya ce min komai ba sai nuni da yayi da hannunshi alamar na tafi, kifa kanshi yayi a kan table din har nayi nisa bai dago ba, ko tunanin me yake yi ban sani ba, amma dai yadda na lura maganata ce ta girgiza shi Musamman da nace na taɓa aure. Ina shiga aji aka bi ni da kallo, da yawan mutanen da ke ajin na son tambayata abinda muka tattauna da shi amma babu dama, kasancewar bani da sakin fuskar da xasu samu damar tambayata. Mu'allim bai samu dawo wa ajin ba har aka tashi sai wani malamin ne yaxo yayi mana addu'a. mamakin ne ya kama ni tare da tambayar kaina ko menene dalilin da ya hana shi dawowa? Rashin samun amsar ne ya dagula min lissafina nima sai na tsinci kaina a cikin damuwa mai yawa, yanxu ma haka muka dawo tare da khadeejah taso ta bugi cikina taji abinda muka yi da mu'allim amma ban saurareta ba, hirar ma jefi-jefi nake sanya bakina a ciki. Ko da na dawo Adda saratu ta gama komai, don haka dakina na wuce na tube kayana na shiga wanka ko xan ci sassauci a xuciyata. ★★★★★★★ A ɓangaren mu'allim kuwa tunda Sa'adatu ta bar office dinsa ya faɗa dogon tunani tausayi da soyyyarta ne suka mamaye masa zuciya, mamaki ne ya cika ransa yanzu a ce yarinya kamar wannan ita ce ta haɗu da kalubale kala-kala a rayuwarta, yana ji a ransa xai iya sadaukar da rayuwarsa kawai don ya faranta mata, ji yayi kaunarta ta kama shi, da xata amince ta bashi zuciyar ta da sai ya aureta, duk da cewa ta taɓa aure shi kuma yana saurayi, amma a hakan zai iya rayuwa da ita, tsanar malam Jibo ce ta kama shi, ji yake kamar ya same shi ya hau shi da duka, sbd irin wulakancin da ya yiwa Sa'adatu, addu'a ya riƙa yi a ransa Allah yasa dai bai mayar masa da mata bazawara ba, da wannan tunanin ya tashi xai tafi gida. Bai iya yin sallama da kowa ba a salube ya tafi gida yana ta tunanin rayuwar Sa'adatu, ko da ya koma gidan bai kula kowa ba ya faɗa dakinsa, kwantawa yayi rigingine ya cigaba da aikin tunani, wanda a yanzu yake son xama cinikinsa. Sai lokacin sallar magariba ya fito ya nufi masallaci yayi sallah sannan ya sake komawa gida yayi wanka ya shirya cikin wata brown shadda, wacce aka yi wa aiki da brown din xare, hular da ke kansa ma brown ce haka ma takalmin da ya sanya, kasancewar mu'allim mutum ne ɗan gayu mai tsafta ga kamun kai, wannan dalilin yasa yan mata da yawa ke kawo tallan kansu wajensa amma bai taɓa saurarsu ba sbd shi mutum ne mai tsari da tsaurin akida, a kofar gida ya tsaya yana nazari shib yaje wajen Sa'adatu ya faɗa mata abinda ke ransa ko kuwa kawai ya kyaleta, sbd baya so yayi mata katsalandan cikin al'amarin rayuwar ta, duk a yau ta bashi kwatancen gidan su sbd yace xai zo ya bata wasu addu'o'i. Ya dauki ku san rabin hour yna wannan nazarin kafin daga bisani ya yanke shawarar zuwa wajenta. Wuta ya bawa machine dinsa ya saita kansa ya nufi hanyar gidan su Sa'adatu, ya dade a tsaye yana tunanin ta ina xai fara gabatar mata da kansa, tambaya ya jefawa kansa wacce ya gaxa samun mai amsa masa, da wane ido ma xai dubeta yace yana sonta, shi dai tunda yake a tarihin rayuwar sa bai taɓa xuwa kofar gidan su wata yarinya da sunan soyayya ba, amma ga shi yau yaxo wajen Sa'adatu, shi dai bai san me xai ce ba. Ba shi da tabbacin ma xata karbi soyayyar tasa ko kuma xata yi watsi da ita, wannan ita ce fargabar da ta cika xuciyarsa. Ta maza yayi ya kira wani yaro ya aika shi gidan. Muna tsakar gida muna shan iska ni da Adda sbd zafi ya fara xuwa, labarin yadda muka yi da mu'allim nake bata da yadda ya nuna damuwa a kan abinda ya same ni, ba ƙaramin burgeta yayi ba sbd ita kanta tana son mutum mai irin halayensa, zaulayata tayi da cewa ko shi ɗin ma yana ciki ne, sunkuyar da kaina nayi tare da bata amsa da cewa shi baya wasa da ɗalibai ma ballantana har na samu dama yace yana sona, kawai dai ya tausaya min ne a matsayinsa na malamina, muna a wannan halin muka ga yaro tsaye a kanmu. Adda ce tayi masa magana me yasa ya shigo mana gida ba tare da sallama ba, a ladabce ya amsa da cewa ya dade yana mana magana bamu ji ba, tambayar shi ta shiga yi ko me ke tafe da shi, a nan yake faɗa mata cewa wai ana sallama da ni ne. Cike da mamaki ta juyo ta kalle ni "Kin bawa wani kwancen gidan nan ne Sa'adatu" a sanyaye na amsa mata da a'a, mamaki ne ya cika zuciyata tare da farin ciki, wannan farin jinin da ya fashe min ba ƙaramin mamaki yake bani ba, yanxu nake kara tabbatar da ribar hakuri, a xuciyata nace Allah na gode maka, mayar da kallonta tayi ga yaron "je ka tambaya kace wanene yake kiranta" Cikin mintinan da basu wuce biyu ba ya dawo yace "mu'allim Mahmud ne yake kiranta" Gabana ne ya fadi, kallon Adda nayi ina mamaki, ko me yasa yazo wajena a dai-dai wannan lokacin. Amsa ta bawa yaron da cewa yace masa ina xuwa. Cike da kulawa ta dube ni "tashi ki kintsa Sa'adatu kije kiran nasa, ashe dai hasashen da nake yi ya zama gaskiya, tunda naji abinda kika fada min dangane da mu'allim din nan na san yana ciki akwai magana a bakinsa" Murmushi nayi tare da mikewa, daki na shiga na canja kaya na shafa yar powder na fesa turare sannan na sanya hijabina na fito, ni kaina nasan nayi kyau duk da cewa ba wani kaya masu kyau na saka ba. Kujeru guda biyu na ɗauka na fita da su na ajiye a soro, lekawa nayi don yi masa iso cewa ya shigo ciki, a bakin machine dinsa na hange shi yayi matuƙar yin kyau, kana ganin shigar ka san waje na musamman xai je da ita. Muna hada ido ya sakar min kyakkyawan murmushinsa, a hankali ya tako ya shigo kirjina sai dukan uku-uku yake yi sbd ban san me ya kawo shi wajena ba. *Jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *44* 'Daya daga cikin kujerun da na ajiye masa ya samu ya xauna yana fuskanta ta, tsananin kunyarsa da kwarjinin sa ne suka kamani, cikin kasalalliyar murya nace "mu'allim barka da dare" kafin ya amsa sai da ya bi ni da wani mayataccen kallo wanda yasa nayi saurin sunkuyar da kaina sannan ya daga baki yace "lafiya lau Sa'adatu" tun daga wannan maganar da nayi ban ƙara cewa komai ba, gyaran murya yayi min har yanzu idanunsa na kaina ya kasa ɗauke idonsa daga kallona, jikina har rawa yake yi ni ban saba da irin wannan kallon ba. A hankali ya daga bakinsa yace "Na san dole za kiyi mamakin ganina a wajenki kuma a dai-dai wannan lokacin, sbd baki taɓa tsammanin hakan daga gare ni ba" kaina a sunkuye na amsa masa da "eh" Gyara xama yayi cikin siririyar muryar shi ya cigaba da cewa "Tun bayan lokacin da kika bani labarin irin halin da kika tsinci kanki na kasa samun nutsuwa, hankalina ya tashi naji idan har ban kasance cikin rayuwarki na tallafa miki ba nima baxan iya cigaba da rayuwa mai daɗi ba, da fatan dai dukkan damuwa da fargabar da tsohon mijinki ya sanya ki a ciki kin manta da ita, ina fatan kuma xaki karkade xuciyarki ki manta da labarinsa da dukkan abinda ya shafe shi, ina so ki saki jiki da ni nayi miki sabon dashen farin ciki a rayuwarki, ina fatan dai ban miki shishshigi ba" Duk maganar da yake yi kaina na sunkuye na kasa magana, kunyar shi ce ta mamaye ni, sake tsare ni yayi da manyan idanunsa yana tambaya ta, "baki ce komai ba Sa'adatu" A takaice na amsa masa da na amince. Sake kwantar da muryarsa yayi yace min dago ki kalle ni kiga sakon da ke cikin idanuna, na san shi kaɗai xai baku amsar abinda ke kunshe a cikin zuciyata. A hankali na dago na kalle shi, Muna haɗa ido ya kashe min kyakkyawan idanunsa gami da sakar min kyakkyawan murmushi, da sauri na sunkuyar da kaina, sbd idanunsa baxa su jure kallon kwayar idanunsa ba, soyayyarsu na gani sosai a cikin su. Murmushi yayi "me yasa kika yi saurin ɗauke idonki?" Ban bashi amsa ba sai wasa kawai da nake yi da yatsun hannuna. Na lura da shi sosai farin ciki ne ya mamaye shi, fuskarsa a sake ya kuma cewa. "Me yasa kika yi saurin amincewa da ni Sa'adatu don a kallon da kika min nima naga soyayyata a idonki?" Sadda kaina nayi ina cigaba wasa da yan yatsuna "na tabbatar da cewa a wajenka ne kaɗai xan samu dukkan abinda na rasa a rayuwata, kana da kyawawan halayen da duk mace da kace kana so dole ne ta karbi soyayyarka, ga ka malami ga ka mai addini uwa uba kuma kai me kyau ne" ina gama fada na sa hannuwa na na rufe idanuna. Murmushi naji yayi wanda sai da naji sautinsa a kunnena " yanxu wannan duk ni kaɗai Sa'adatu anya baki yi son kai ba kuwa"? Murmushi nayi tare da girgixa kaina alamar eh, haka muka kasance cikin farin ciki da nishadi sai naji na manta da komai a rayuwata, sbd na shiga wani sabon darasin rayuwa, wanda malaminsa ya kasance kwararre kuma masani a kan aikinsa. Bai wani dade sosai ba ya tashi xai tafi, sai naji kamar nace ya dawo mu xauna mu cigaba da hira, sbd yadda kalamansa ke bin dukkan wani jini da sassan jikina, amma kuma kunya da nauyinsa da nake ji baxa su bari na fada masa ba, tabbas na san idan na roki wannan alfarmar xai min amma ni din ce baxan iya ba. Hannu yasa a aljihu ya miko min yar ƙaramar waya kirar Nokia, karbi wannan idan naje gida ina so xa mu yi magana, don ni gaskiya ban gaji da sauraren zazzakar muryarki ba. Makale kafada nayi alamar ya baxan karba ba, tsare ni yayi da ido ranshi a haɗe yace "Bana so idan na baki abu ki ƙi karba, da ni da ke mun xama abu daya" Rausayar da kai nayi kamar xan yi kuka "Kada ka bani waya Game ta shagaltar da ni naƙi yi maka hadda ka dake ni" murmushi yayi wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana. "Ki karba ko ana dukan kowa kin san baxan daki gimbiyata ba, kuma ma ai wannan karama ce babu game din da xata ɗauke hankalin ki a ciki, ina so mu rika magana ne na rika jin lafiyar jikin ki" har ga Allah ban so karɓar wayar ba sbd yana amfani da abarsa amma ya ɗauka ya bani, sallama muka yi ya tafi. Kwasar kujerun nayi na shigar da su gida, a inda na bar Adda a nan wajen na sameta, da gudu na ƙarasa wajenta na faɗa jikinta ina murna. Kallona tayi tana mamakin yadda na shigo da farin ciki "lallai mu'allim yayi kamu, amma da doctor ne yace zai xo, da baxa a bashi dama ba" Murmushi nayi kawai ba tare da na bata amsa ba, miƙa mata wayar da ya bani nayi, cikin farin ciki ta karba tana dubawa. "Wato mu'allim da karfinsa ya faso baxai iya jure rashin jin muryarki ba shi ne har da baki waya to Allah ya riƙe miki Allah ya sanya alkhairi" amsawa nayi da ameen mun dade muna hira sannan kowa ya tafi dakinsa. Wanka nayi na dauro alwala na saka kayan bacci, mamaki ne ya cika zuciyata ta yaya mutane hadaddu masu kyau da ilimi, suke rikicewa a kan soyayyata, na san banda ikon Allah babu yadda za a yi mu'allim ya so ni, ya fi ni komai na rayuwa, tunda ni ba wani kyau gare ni ba ya ninka kyauna sau ɗari, amma yanzu ya rikice a kaina da ni kadai yake so yayi rayuwa, gaskiya dole na godewa Allah don ba kowa Allah ya yi wa baiwar da yayi min ba, sai da nayi Sallah raka'a biyu nayi addu'a, ina shirin kwanciya naga kiransa, a hankali na kara wayar a kunnena tare da yin sallama, cikin kasalalliyar murya ya amsa min yana tambaya ta me yasa har yanzu ban yi bacci ba, amsa masa nayi da yanzu nake shirin kwanciya. Kwantar da muryarsa yayi yana cewa "Ni kuwa kinga tunaninki ya hana ni bacci sai juyi nake yi ni kadai na rasa me ke damuna" rufe fuskata nayi kamar yana ganina ban bashi amsar maganar shi ba, na kawar da tunaninsa muka shiga wata hirar. Mun ɗauki lokaci muna hira sannan muka yi sallama. Juyi mu'allim yake yi yana jin wani sanyi da daɗi a ranshi, idan da abinda ya fi so a yanxu bai wuce farin cikin Sa'adatu ba, yarinyar ta riga da ta gama yi masa, yana ji a ransa baxa su ɗauki lokaci mai tsawo suna soyayya ba za a yi maganar auren su. ★★★★★★ Da gari ya waye ma da text message dinsa naci karo, kalamansa na musamman ne, kamar yadda komai nasa yake abin burgewa, sai da na gama komai na tafi makaranta, da naje aji sai na nuna kamar ba shi ne yazo wajena ba jiya, shi ma bai nuna ya sanni ba, yadda yake min a baya haka muka kasance har aka tashi. Rashin comment dinku da rashin nuna kuna jin daɗin labarin shi ke hana ni yin typing da hana ni yi da yawa, Sannan ina kira ga wadanda suke cikin groups dina dan Allah idan ke ba masoyiyar wannan littafin bace dan Allah ki fita. *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *45* Innah ce xaune a tsakar gida tana 'yan aikace-aikacen gida, yanzu rayuwar gidan tana yi mata dad'i sosai don ta samu sassaucin cin kashin da Innah Salamatu da ƴaƴanta suka yi mata shi kansa baban Sa'adatu ya gyara halinsa, don yanzu har girkin gidan tana yi. Yaro ne yayi sallama tare da karaso wa inda take cikin ladabi yace wai ana sallama da innar Sa'adatu, kallon mamaki ta bi shi da shi tare da xare hannunta daga robar da take tsintar shinkafa. Wane ne yake kirana? amsa mata yayi da wani Mutum ne a waje, cikin mamaki ta sake cewa anya nan aka aiko ka kuwa ba can dakin aka ce maka ba. Sake maimaita mata yayi da cewa wajenta aka aiko shi, cewa tayi ya faɗawa mai kiran nata ya shigo daga soro tana zuwa. 'Daki ta shiga ta sako hijabinta tare da dakko tabarma ta fita, tana xuwa soron taga ashe makocin su ne Dr mukhtar. Da fara'arta ta ƙarasa wajensa tare da baxa masa tabarmar da taho da ita. Lalale marhabun Dr ashe kaine a gidan namu, cikin sakin fuska ya amsa tare da xama a kan tabarmar, gaisawa suka yi sannan ya fara magana. Dama doctor ne ya turo ni a kan Maganar nan da muka yi kwanaki da ke, to ya ji shiru ne har yanxu ba a sake cewa da shi komai ba, shi ne yace na sake dawowa naji a ina aka kwana, don shi a yadda yaso ma a yi magana da wuri sbd baya so abin ya dauki lokaci mai tsawo, kin san abokin nawa yanxu gauro ne sun rabu da matar shi ya karasa maganar yana murmushi. Murmushi Innah tayi, to ai ba komai mu taimakon da Dr yayi mana baxa mu taɓa mantawa da shi ba, don haka ka faɗa masa na bashi dama yaje wajenta su daidaita kansu, amma yaje a ranakun asabar ko lahadi sbd yanxu tana zuwa makarantar islamiyya. Doctor mukhtar yaji dadin jin labarin Sa'adatu tana xuwa makaranta, mun gode sosai da wannan damar da aka bamu Allah ya shige mana gaba. Suna cikin maganar suka ji tafiya a bayan su da sauri suka waiwaya, ido biyu suka yi da baban Sa'adatu yana ta faman muzurai, ashe duk maganar da suke yi a kunnesa. Fuskarsa a daure ya fara tambayar Innah Naji dukkan abinda kike shirin yi Kuma na gode, kin kyauta mero, abinda kika yi kin yi dai-dai. Yanzu har isarki ta kai ki bayar min da auren 'yata ba tare da iznina ba, sai dai kawai naji ana magana har kina cewa kin bada dama kamar ke kaɗai kika haifeta sbd kin raina ajawalina, wai ma wane doctor kike magana? Fada min naji wane ne da wannan ƙarfin halin. D'aure fuska tayi sbd yanxu ita ma ta daina sakin fuska kamar da, kuma ta ɗan rage tsoro. "Doctor din da Sa'adatu ta kwanta a asibitin sa ne shi ne yanzu yazo yana sonta" Wani kallo ya bi ta da shi me kike faɗa min haka mero, kina nufin mutumin da ya ci mutuncina ya tozarta ni ya d'aure ne har adadin kwanaki uku a kurkuku, Sannan yayi silar kashe aure yata shi ne yanxu zai lallabo yace yana sonta da aure, tabbas maganar malam Jibo ta zama gaskiya da yace dama so yake ya kashe masa aure ya aureta, to wlh tun wuri kiyi gaggawar kwance wannan mugun kullin da kika yi, don baxan taɓa amincewa da wannan maganar ba, ko da hakan zai yi silar ajalina. Mayar da kallonsa yayi ga Dr mukhtar, kai kuma doctor Ina ganin mutuncin ka tun wuri ka fita daga wannan Maganar idan ba haka ba kaima xata kwabe da kai. Kallon mamaki kawai doctor mukhtar yake binsa da shi yana mamakin tijara irin ta malam Salisu. A nutse Innah ta dube shi. Nayi mamaki da ka shiga abinda ya shafi rayuwar Sa'adatu kaifa kace babu kai babu ita, kuma kada ta sake nuna ka a matsayin mahaifinta, to menene na damuwa don xata auri Wani mutum daban. Wani abu yaji ya saukar masa a cikin jikinsa ya ji duk wani karfi da ke jikinsa ya neme shi ya rasa, mamakin kalaman Innah yake yi yaushe ta waye har ta koyi mayar masa da martani, bai taba tsammanin jin hakan daga gareta ba. A sanyaye yace "Dama dole ki fadi haka mana tunda son xuciya da kwadayi sun rufe miki ido, shikenan yanxu ƙoƙarin fin karfina kike yi babu damar na saka doka a gidana sai kin karya min sbd kun raina min arxikina, kin samu masu xuga ki kina raina ni, to wlh baki isa ba indai ina doran kasa baxa a yi abin nan ba, kuma da kike cewa bana kaunar Sa'adatu na tabbatar da cewa na fi ki kaunarta, don ni duk abinda xai tseratar da ita daga halaka shi nake yi, amma ke kulllum burin ki ya za a yi ki jefata a hanyar shaidan don kawai ki samu kuɗi". Murmushi Innah tayi tare da bin sa da kallo yana ta kumfar baki, a fusace ya shiga cikin gida ya barta tare da doctor suna magana, sai da suka gama magana sannan ta shiga ciki tare da faɗa masa cewa ya faɗawa doctor duk lokacin da ya samu dama ya je ya ga Sa'adatu Nade tabarmar da ta shimfida tayi, Sannan ta shiga cikin gida, dakinta ta shige jiyo Baban Sa'adatu tayi a dakin Innah Salamatu suna Magana. A fusace ya shiga dakin tana ganin shi ta san ba lafiya ba, da sauri ta tashi ta tarbe shi tana tambayarsa. Lafiya naga fuskarka a haka malam, me kuma ya sake faruwa sauke ajiyar zuciya yayi tare da cewa "waccen matar ce ta haɗa min takaici, wlh na rasa yadda xan yi da ita ƙoƙarin xame min masifar take yi a rayuwata, duk abinda ta san zai jefa ni a matsala shi take yi, gaba daya bata tausayinta, wlh ba don dokar da aka saka min a wajen hukuma ba da tuni na dade da sakinta" Bayar da hankalinta tayi gare shi tare da gyara xama, Wani abin ta sake yi maka ne malam? labarin zuwan doctor mukhtar ya bata da abinda suka tattauna da innah. Maimakon ranta ya ɓaci sai kawai ta saki wani murmushi cikin kissa ta fara Magana. Haba Malam menene na damuwa don anxo maka da wannan maganar ai kai abin alfaharin ka ne, Allah ya kawo mana nama har gida, yanzu abinda ya rage mana shi ne mu bi duk hanyar da xamu bi don ganin damar ta dawo hannun mu. Cikin rashin fahimtar abinda take nufi ya dubeta Ban gane nufin ki ba salamatu, kuma gyara xama tayi "abinda za a yi kaje ka samu doctor din kayi masa magana kace kaji dukkan kudurinsa da alfarmar da yake nema a wajenka, kace xaka yi masa ka nuna komai ya wuce a wajenka, kayi ƙoƙari ya xama amininka ya xamto baya jin maganar kowa sai taka har ita uwar yarinyar, ta haka xaka shigar da bukatar ka, sai kace yazo yaga A'isha ko zaliha ka nuna masa sun fi Sa'adatu kyau da komai, tunda dai kaga mutumin nan mai kuɗi ne sosai xamu samu abubuwa da yawa a hannunsa, tunda yanxu ya'yan namu babu wanda yake zuwa wajensu, A'isha saurayinta tunda yace xai kawo kuɗi har yanzu shiru ko xance ya daina xuwa, ita kuwa zaliha kofarta ma a kulle take babu wanda yake ganinta yace yana sonta, kuma na san ba sharrin kowa ba ne illa wannan munafukar ta daki ita ce ta kulla asirin da babu wanda zai gansu yace yana so, ta ƙarasa maganar tana share hawaye, ka taimake ni malam kayi min wannan ƙoƙarin wlh ji nake yaran nan kamar a kaina suke na kosa na aurar da su, bana so wannan shegiyar mummunar yarinyar ta riga su aure sai su yi mana dariya ita da uwarta. Shi kuwa duk abinda take faɗa masa jinta kawai yake yi, yaushe xai yi gangancin xama aminin doctor har abada baxai taɓa iyawa ba, sbd tsanar da yayi masa ba 'yar karama bace. A xuciyarsa yace duk ba irin mugun halinki bane ya faɗa a kan ya'yan naki shikenan ba ki da aiki sai jafa'i, shi yasa duk ƴaƴan ba su da albarka, shi kansa ya san halin Innah Salamatu amma tsoronta baxai bari ya faɗa mata gaskiya ba. Haka ya xauna ta riƙa yi masa Huduba amma shi ko a gefen silifas dinsa jinta kawai yake yana yi mata kallon mahaukaciya. ★★★★★★★ Yau mun samu ku san watanni biyu muna soyayya da mu'allim, kullum kaunarsa kara xurfi take yi a xuciyata, sbd a kullum kyawawan halayensa dada bayyana suke yi, duk wanda aka tambaya dangane da halinsa da mu'amalarsa alkhairi ake faɗa a kansa, yanzu har innah ta san da zamansa, abu ɗaya ke sanyaya min gwiwa idan na tuna da izuddeen dina, har yanzu na kasa cire soyayyarsa a xuciyata. A kitchen nake tsaye ina yanka salad Kasancewar yau ba makaranta, Adda ce ta shigo ta tsaya bakin kofa tana kallona, da sauri na juyo don har na dan tsorata ma, murmushi tayi min tare da cewa amaryar doctor. Dan turo baki nayi, haba Adda Amaryar mu'allim dai xaki ce ko ta izuddeen, ɗan murmushi tayi ke da baki ganshi ba kika sani ma ko duk ya fi su haduwa, ɗan juyar da kaina nayi haba dai Adda ki daina faɗa kada jinina ya hau. Murmushi tayi nima da wasa nake yi Allah ya zaba mafi alkhairi, amsawa nayi da ameen. Cigaba nayi da aikina, sake mayar da kallonta tayi gare ni. Sa'adatu idan kin gama ki shirya yau doctor xai xo ku gaisa Yanzu ya kira abban su husna ya faɗa masa, a sanyaye na juyo na dubeta Kamar idona xasu kawo hawaye, ji nayi kamar nace mata ta faɗa masa kada yazo ina da wanda nake so, amma baxan iya yin hakan ba sbd ina ganin kimar Adda A cikin zuciyata na amsa mata da to, girgixa kai tayi "naga alama kamar zuciyarki bata gama amincewa da doctor ba, alhalin kin san shi kin san wanene shi da dukkan halayensa, kada ki manta da karamcin da yayi mana, kada ki manta shi ne yayi mana sanadin fitar ki daga hannun tsohon mijinki" Jikina ne yayi sanyi da kalamanta "haka ne Adda amma ni xuciyata gaba ɗaya tana wajen izuddeen ne da mu'allim idan ban auri ɗaya daga cikin su ba, baxan ji daɗin rayuwata ba, murmushi tayi shikenan ni dai ki fara shiri bana so ya zo ya jira ki. Jikana ne duk yayi sanyi bana so na sake shigo da wani mutum cikin rayuwata ya tarwatsa min farin cikina, barin kitchen din nayi na shiga dakina. *Jeeddahtulkhair😘* 💋💋💋💋💋💋 *DUKKAN TSANANI* 💋💋💋💋💋💋 *Na* *Jeeddah Tijjani* *Adam* *(Jeeddahtulkhair)* *Follow me on Wattpad @jeeddahtou* *46* Ban wani yi kwalliya ba don raina a bace yake hijabina na xurma, fuskata sai faman maiko take yi, xama nayi ina jiran xuwansa, mijin Adda ne da kan sa yaxo ya kira ni yace min doctor ya xo, a salube na shiga daki na dakko masa sallaya na fita wajensa, shimfida masa nayi ina jiran shigowar sa, bin hanyar da xai shigo na riƙa yi da kallo, don ganin ta inda xai shigo. Wata hadaddiyar mota kirar Mercedes Benz yazo da ita mai launin baƙi, a hankali ya bude murfin motar ya fito fuskarsa dauke da murmushi, manyan kaya ne ɗinkin kufta mai launin blue a jikinsa yayi matuƙar kyau, kasancewar doctor kyakkyawan mutum ne sai dai ya ɗan fara manyanta dan xai kai shekara arba'in da biyar, sosai kamalarsa ta bayyana musamman da ya sanya manyan kaya, a hankali ya yake takowa har ya shigo soron, yana bi na da kallonsa mai matuƙar burgewa. Shimfidar da nayi masa ya samu ya xauna ni kuma na xauna daga gefensa muna fuskantar junanmu, kamshin hadadden turarensa na dukan hancina, a ladabce na gaida shi, sunkuyar da kai nayi cike da jin kunya yayin da wani sashi na xuciyata ke cike da farin ciki da godewa Allah da yayi min baiwa mai yawa, banda ikon Allah na san babu abinda xai kawo doctor wajena, duk inda ake neman cikakken mutum mai kyau ilimi da addini tare da abin hannu ya kai wajen, tabbas babban abin alfahari ne a gare ni namijin kamar doctor faruq a ce shi yake so ya aure ni, idan aka ce na fitar da mace mafi sa'a a cikin dangin mu babu abinda zai hana na fitar da kaina. Cikin kyakkyawar muryar sa ya amsa min da "lafiya lau sa'ar mata" wani daɗi ne ya daki kunnuwana ina jin dadi sosai idan aka kira ni da wannan sunan, sai ya tuna min da yayana salim don shi kadai ke kirana da wannan sunan. Cigaba da magana yayi "Tabbas ina cikin farin ciki a wannan lokaci kuma na tabbatar da cewa na xo wajen da idan na miƙa kokon barata baxa a yi watsi da shi ba, yanayin karɓar da aka yi min shi ya tabbatar min da nafi kowane namijin sa'ar zaɓen abokiyar zama, ina fatan baza a ƙi karbar buƙatata ba" Har yanxu kaina a sunkuye yake ban dago ba kuma ban bashi amsa ba, katse shirun da nayi yayi da cewa. "Me yasa kika yi shiru Sa'adatu, ko dai docton naki bai miki bane?" Ya katse min ɗan gajeran tunanin da nake yi. Ɗan takaitaccen murmushi nayi "Ba tunani nake yi ba kawai dai nayi shiru ne sbd ban san me zan ce ba" Murmushi ya ɗan yi gami da sukuyowa saitin kunnena, naga kamar kunyar mijinki kike ji sa'ar mata, ki saki ranki da mijinki kike magana don yanxu a raina ji nake har an bani ke. Saurin dagowa nayi ina kallonsa wannan yar maganar tasa ta ɗan sosa min raina amma sai na kawar da wannan tunanin na dan yi murmushi wanda bai kai cikin zuciyata ba. Cigaba yayi da magana, ki ajiye duk wani tunani sa'ar mata ban zo da niyyar yaudarar ki ba, aurenki naxo yi da gaske, duk da dai na san cewa baxa ki rasa masu sonki ba amma ina so duk kiyi watsi da su ki bani kyautar zuciyarki, na kasance mamallakin ta mai sanyata farin ciki a ko da yaushe, tsakani da Allah nake son auren ki kuma bana so na ɗauki lokaci mai tsawo ba tare da ke a cikin gidana ba, na san duk wadannan bayanan doctor mukhtar yayi miki, idan da so samu ne ma bana so ya wuce nan da sati biyu ko uku" "Da sauri haka?" Na faɗa cikin muryata wacce kalaman doctor suka sanyayata. Sake mayar da kallon shi yayi gare ni. "to menene a ciki indai kina sona hakan nake buƙata, sbd a yanxu ba ni da aure zaman hakuri kawai nake yi, kuma ina bukatar na karbo yarana su dawo wajena sbd ban yarda da tarbiyyar gurin da suke ba" Da sauri na dago Ina kallon shi tare da tambayar shi "Dama ka taɓa aure?" Cikin rawar murya ya amsa min "Na taɓa aure sa'ar mata shekarar mu biyar da matar muka rabu muna da ya'ya biyu mata, sbd wani dalili wanda xan faɗa miki shi nan gaba idan kika zama mallakina, yanxu ku san watana tara babu mace, kinga ni abin tausayi ne namiji kamata lafiyayye babu matar aure, shi yasa na lallabo wajenki na san xaki share min hawaye na, kuma xaki riƙe min yayana amana shi yasa ma na zaɓeki ki xama abokiyar rayuwata" Sunkuyar da kaina nayi cike da tausayin shi a sanyaye na amsa masa da "insha Allah zaka same ni mai bin dukkan umarnin ka, amma me yasa baxa ka faɗa min dalilin rabuwar ku da matarka ba, don na san irin shirin da xan yi wanda zai sanya ka farin ciki na har abada" A jiyar zuciya yayi tare da cewa. "Ban yi niyyar bankada asirin iyalina ba, amma tunda kin bukaci jin abinda ya raba mu dole na faɗa miki, Sa'adatu tunda na auri matata ban san menene dadin aure ba, kullum cikin tashin hankali da bata min rai take, ban isa na sakata ko na hanata ba, bata san tayi min dukkan abinda xai faranta min raina ba, wannan dalilin ya tarwatsa tunanina har ya kai ga rabuwar mu, dan Allah ki yarda mu yi aure cikin sati biyu ki share min hawayena ki bani farin cikin shekaru biyar da na rasa a rayuwata" Cikin tausayawa na dube shi. "Kayi hakuri insha Allah xan xamo mai share hawayenka mai sanyaka dariya, zan riƙe ƴaƴan ka tamkar ni na haife su, baxa kayi kuka da ni ba ko kaɗan" Dan murmushi yayi. "Naji dadin kalamanki sa'ar mata, tabbas na san na dace da mace ta gari, kin fi matata komai, kyau ilimi uwa uba kuma ga tarbiyya, wannan ya sa zuciyata ta kwadaitu da son rayuwa da ke" Da sauri na dube shi, kawai dai xuga ni kake yi doctor amma ni ai bani daga cikin sahun mata masu kyau, kawai dai soyayya ce tasa kake min kallon mai kyau" Yar dariya yayi gami da shafa dan kwantaccen sajen da ke fuskar sa "da gaske nake kin fita komai, ke yar baiwa ce kina da baiwoyi masu tarin yawa, amma ke baki san da su ba ni kaɗai nake iya ganin su" Murmushi nayi gami da rufe idanuna da tafukan hannuna, a xuciyata nace na san kawai faɗa yake yi don yaji dadin bakinsa. Murmushi yayi gami da lumshe idanun shi. "Bari na tashi na gudu matar doctor yau ina da aiki mai yawa a asibiti ki kula min da kanki, kina da mijinki mai sonki da kaunar ki" Gefen sa ya duba ya janyo wata ledar da ya taho da ita. "Ga wannan naki ne kiyi amfani da shi" Kaina a sunkuye nace "ka bar shi na gode" tsare ni yayi da ido "ki karba ke tawa ce komai na baki ban yi asara ba" Karba nayi tare da yi masa godiya. tashi tsaye yayi yana min sallama, murmushi yayi min "gobe ma sai na dawo don baxan iya hakuri ban yi tozali da kyakkyawar matata ba, da ina da hali ma yau za a daura mana aure na tafi da abata" Kallon shi nayi kawai ban bashi amsa ba sai ɗan murmushi da nayi, har fita daga soron ya kama. Yana tafe yana waigena, ban shiga gida ba har sai da naga ya hau motarsa ya tafi. Da gudu na shiga gida tarar da Adda nayi a kitchen tana aiki, tana ganina ta hau murmushi, xube kayan da ya bani nayi a gabanta. "Adda kin ji yadda doctor ya iya kalami kuwa, ya iya soyayya sosai amma Adda ya dyan fara manyata xai kai shekara arba'in da biyar" na karasa Maganar ina dan turo baki. Murmushi tayi "lallai Sa'adatu har yanzu Akwai kuruciya a kanki, auren mai hankalin bai fi na wadannan kananan samarin ba, manyan maxa fa sun fi iya rike mace, kuma sun fi bata kulawa, ki tsaya kiyi karatun ta nutsu kafa kije ki cuci kanki" Rausayar da kaina nayi "Ni ba wannan ne yake damuna ba Adda ya taɓa aure fa har da ya'ya biyu amma sun rabu da matar, Allah bana son auren bazawari" Saurin rufe idona nayi sbd nasan dole tayi min raddi. "Inye lallai kin samu lafiya Sa'adatu, ke da kika auri kaxamin tsoho ko brush baya yi ga kazanta kin samu wannan kice bakya so, to xauna kallon ruwa kwado yayi miki kafa" Kayan da ya bani ta shiga fito da shi lesina ne da atamfofi da takalma masu kyau, sai da ya kawo min kaya kala goma takalmi kala uku, gaskiya ya kashe min kuɗaɗen masu yawa, gefe guda kuma kwalin hadaddiyar waya ne kirar Samsung, har da sim card ya hado min, farin ciki ne ya bayyana a fuskata ganin yadda doctor yake son mayar da ni yar gayu dare daya, kamar ya san ba ni da wata sutturar kirki, wata envelope muka gani, da sauri Adda ta kai hannu ta shiga budewa, sababbin kuɗaɗe ne yan dari biyar zasu kai Kimanin dubu talatin, gefe guda kuma wata takarda ce yayi rubuta a ciki *_wannan kuɗin ɗinki ne sa'ar Mata ki karba ba yawa_* Rungume takardar nayi ina murmushi, abinda ya bani mamaki shi ne yadda son doctor ke ƙoƙarin shiga zuciyata da wuri, tambayar kaina nayi ko dai so yake ya siye ni da kudinsa? Idan kuwa haka ne baxan bashi damar ya zamo abokin rayuwata ba. addu'ar fatan alkhairi Adda tayi min sannan ta ajiye don nunawa mijinta abin arzikin da aka yi min, daki na tashi na shiga na fada kan gado ina godewa Allah, xuciyata cike take da farin ciki ban taba xaton xan samu irin wannan mijin ba a rayuwata, gefe guda kuma tunanin mu'allim da izuddeen na fara yi, ko yaya xan yi da soyayyar da suke min?? Wane hali xasu shiga idan na auri doctor na kyale su?? Wannan ita ce tambayar da na riƙa jefawa kaina wanda na rasa mai bani amsarta. Sai aikin typing amma comment na yi muku wahala😭😭😭😭 *Jeeddahtulkhair😘*