[11/08 à 00:10] Shalelen Mamata🥳🥳: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Wannan labarin da gaske ya faru ban yarda achanjamin shi da wata siga ba domin sai da yarjawar wadda hakan ya faru da ita nake rubutawa_ ```Barka da sallah masoyana,,,🥰fatan kunyi sallah lafiya,,,wannan shafin sadaukarwa ne gareki auntynah Shaxee kiyi yadda kikeso da shi Xayyeesher ta ki ce😍😍``` _*PAGE 1*_ ____________________________________________________________________________ "Wallahi sai ka saketa yanzun nan bazan yarda na fadama ni dai bana son yarinyar nan" cewar Wata Dattijo kennan tana ta kumfar baki. Mutanen ciki agidan Fam anata shagalin biki Amman tun daga shigowar matar nan komai ya watse, Amaryar ma da suke daukan hotuna da ango sunyi sumar tsaye. Kuka kawai Faruq ya ke domin bakin ciki ya rasa abin yi bare kuma abin fada. Cigaba da jawabi wannan Tsohuwar tayi tana, "Na fadama wallahi sai ka saketa ko na tsine ma, haba ni na taba ganin naci irin wannan kuwa?" Dukusawa kasa Faruq ya yi yana fadin, "Dan Allah hajiya kimin rai Wallahi ina son Sakina bazan iya rayuwa ba in babu ita, ki taimaka ki barni da ita." Tsawa ta daka ma sa tare da fadin, "Wallahi Wallahi ba fashi sai ka saketa ai ga matar ka chan agida,wato kai bakason zabina sai zabin kanka to wallahi daga kai har wa inda suka asirce kan sunyi kadan." Tuni gida yakaure da kuke kuke, yan uwa da abokan arziki, tun ba kanwar Sakina ba da tafi kowa zubda kwalla. Sakina kuwa bin yan uwanta take tana basu hakuri ita da za abawa amman ita ke basu domin kuwa ita kam zuciyarta akune take kukan zuci da kuncin zuci kawai ta ke. Yayunta maza ne suka shigo domin jin hayaniyar da suke tundaga waje. Yah Usman na zuwa yace, "Ance ka saketa ana dolene?, mu ma fa muna sonta wannan wulakancin naku ya zo karshe ka saketa kawai kowa ya huta." "Yaya dan Allah kuyi hakuri ina son Sakina kar ku rabani da ita." Hajiya dai ta dage sai faruq ya saki, Sakina awannan lokacin anfi awa biyu ana abu daya har sai da Baban Sakina ya shigo. "Haba nagaji da wannan masifa indai ina raye daga yau ba kai ba Sakina kuma kabi umarnin mahaifiyarka kowa ma ya huta."Cewar Baba. "Faruq na fadama kasaketa ko na tsine ma."Hajiya ta fada tana karkada kai. Faruq na kuka yana fadin, "SAKINA NA SAKEKI NA SAKEKI SAKI DAYA." Gida ya kara kaurewa banda tashin aljanu da sume sume ba abinda ake amman abu mafi mamaki shine Sakina ko ajikinta ba ko alamar hawaye bin yan uwanta take tana basu hakuri tare da fadin Wannan Shine _Azzawajul-Mukaddar dina (Auren kaddara)_ Ku dai na kuka kunji." Hajiya na ganin danta ya cika aikin da take bukata fuuu tabar gidan ita da yan koranta. Faruq kuwa sai da Yayun Sakina suka fita dashi ta karfi domin ya ki barin gidan. Gaba daya yan anguwa duk an fito. Abangaren Sakina kuwa zaune ta ke banda tunanin duniyar nan ba abinda take, batasan me tayiwa mahaifiyar Faruq ba ta tsaneta haka. *zan cigaba amman nuna sonku ga labarin shi zai ban karfin gwiwar cigaba ,,comments nd share pls* *_Urs Xayyeesherth_* [11/08 à 00:10] Shalelen Mamata🥳🥳: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Wannan labarin gaskiya ne mai cike da tausayi tare da sarkakiya,ban yarda achanjamin shi ta ko wace siga ba, domin kuwa da yarda wadda hakan ya faru da ita nake rubutun_ _*PAGE 2-3*_ __________________________________________________________________________ *Gaskiya naji dadin yadda littafin nan ya samu karfuwa gareku ina yin ku irin sose dinnan 😘😘* Nasan cewa ma su karatu zasu so suji shin wacece Sakina sannan wanene Faruq Dafarko dai Faruq 'Da ne ga Marigayi Alhaji Yusuf tare da Mahaifiyar sa Hajiya Amina wadda ta ke yar asalin Niger ce Almajiranci yakai Alhaji Yusuf Ya Auro ta sannan suka dawo mahaifarsa Bauchi inda har su ka haifi Faruq tare kannan sa guda biyu Zainab da Hamza, Azahirin Gaskiya Faruq saurayi ne kyakkyawa mai ji da kan sa domin kamanin Dangin Mamansa ya yo fari gal ga hanci, sannan yagama karatun sa yanzu yana kasuwanci ne. Abangaren Sakina kuwa 'Ya ce ga Alhaji Sulaiman tare da Mahaifiyar ta Hajiya Maryam Tana da Yayu maza guda biyu, Auwal, Da Aliyu Sannan kannanta Mata Maryam da Khadija, Sakina kyakkyawa ce ajin farko ba wanda zai ganta bai kyasa ba, zan iya cewa tsabar soyayya tsakaninta da Faruq har kama suke abun ka da fararen mutane. _Soyayyace mai karfi tsakanin Faruq da Sakina dan zan iya danganasu da Majnon nd Laila, soyayyarsu ta mussamance kamar yadda suma suke na mussaman_ Abu daya ke wahalar da Faruq da Sakina , Mahaifiyar Faruq wadda batason Sa da Sakina. *WAIWAYE______________* Yar Budurwa na Hango tare da wani saurayi tun daga nesa zaka fahimci cewa suna cikin nishadi irin ta masoya. Faruq ne ya ce da Sakina, "Ni fa Agaskiya bazan iya jiran har sai kin kammala karatun nan naki ba kawai ki bani dama in fito ayi Auren mun nan kowa ma ya huta." Murmushi sakina tayi tare da fadin, "Haba Dan Allah Hubby yaushe ma na fara makarantar da har zan ce da su na zan ajiye." Tuni Faruq ya murtuke fuska tare da fadin, "Kennan karatu ya fi mi ki ni ko sakina? Daman ni ba kowa ba ne gareki? yanzu kinfi son karatu akai na." Tambayoyi Faruq ya cigaba da jerowa Sakina, duk hanyoyin da zai bi dan ganin ya watsar da maganar makarantar ta kawai ya ke. Tun Sakina na basa hakuri har sai da yasa ta aminta taji maganar makaranta ta fita mata akai. "Shikennan Hubby zan sanar da Baba yau inna koma gida insha Allah sannan ka turo." Cewar Sakina kennan. Da Sauri Faruq ya ce, "Yauwa Hubbyna shi yasa kullum na ke kara son ki, domin ke tadabance cikin mata,in ana maganar mace ta gari aka sameki an gama." Mumrmushi kawai Sakin tayi tare da da fadin, "Byee byeee, zan shiga gida kaga dare ya fara yi, zanyi kewarka,kasani cewa ina son ka kuma zan cigaba da son ka har bayan raina." Faruq ya ce, "Fatana da burina a kullum bai huce ace naga ranar da zan mallakeki matsayin mata ba, nima ina son ki Hubbyna mukwana lafiya." Tafiya yayi tare da juyowa yana ma ta byeebyee ita ma tana ma sa har sai da ya shiga motarsa sannan ta shige gida. Sakina na shiga gida kuwa ta tarar da kowa na falo ana kallo. Durkusawa tai akasa kowa ya ganta dai yasan da magana abakin ta. Mama ce ta ce, "Sakina kalau dai." wasa da hanunta tafara sannan ta fara da cewa, "Daman, daman ina so ne na ajiye karatun Diploma ma ne?" Dasauri yayan ta ya tashi tsaye tare da fadin, ",Whatt! ki na da lafiya kuwa Sakina? . Araunanane ta ce, "Daman Faruq ne ya ce wai zai turo." Tsabar takaici sai da Yaya Haidar ya kusa dukan Sakina Babane ya dakatar da shi. Baba ya ce, "Sakina kennan Dai Maganar kawai Aure ki ke so?" kai asunkuye dai bata amsa ba amman alama ta nuna hakan. Baba yakara da cewa, "Shikennan Allah ya kawo su, daman tun farko ai bani na nace kiyi karatun ba raa'ayin ki ne." Yaya Haidar ya ce, "Haba Baba ya za ace wai ana biyewa yaran nan ne suna abinda suke so." Baba ya dakatar dashi tare da fadin, "Bakomai ai Auren na ta shine ma fi alkairy." Dakyar dai Baba ya samu damar dakatar da Yaya Haidar Amman duk da haka bai aminta da mgnr Auren ba dai. Tun daga ranar Sakina tabar zuwa makaranta a ka koma ta hidimar biki duk da cewa dangin Faruq din ma ba su zo ba. Acikin kwanakin nan Faruq yaje garin su Niger gun dangin Maman sa, domin Aure ne yakawo Mamarsa Nigeria. Shirye-shiryen biki kawai ake ba wasa domin kuwa yau take ranar Auren Sakina da Faruq... An gama shirya komai tsaf mutane sun taru amasallaci domin daurin Aure,, Alokacin da aka gama jawabi tare da shirin daura Aure ,,, wakilan Sakina na shirin Amsa kennan ihun wata ma ta ya rikitasu wanda hakan yasa komai ya tsaya chak cewa ta ke, "Wallahi baza adaura auren nan ba, in kun ga andaura to bani aduni........ *Nasan cewa kwakwalwar mutane da yawa za ta juya amman kubini asannu za ku fahimci komai anitse🥰lamarin ne asarkakye* ✍️Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:11] Shalelen Mamata🥳🥳: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-4* ____________________________________________________________________________ Aduniya,, Hajiyan Faruq ce me wannan kunfar bakin tare da fadin baza adaura ba..... Faruq ya yi kokarin shawo kan mahaifiyarsa amman ina ba dama domin kuwa kamar kara zuga ta ake. Ba ta bar wajen ba sai da ta tabbatar komai ya watse anfasa Auren sannan taja danta su kai gida. Baban Sakina ne ya shiga gida jiki asanyaye yana shiga bai kulawa kowa ba ya nufa dakinsa domin su kan su mutanan gidan suji abinda ya faru wanda kusan ma a idon su akai. Sakina kuwa zaune ta ke ta rasa meke mata dadi ace wai yau daurin Aurenta amman an fasa. banda hawaye ba abin da ke futa daga idon kanwar Sakina wadda duk ta fita ahayyacin ta wanda bai sani ba ma zai ce Maryam ce Sakina domin Sakina ta zauna ne kawai wanda azahiri ta nuna ba abinda ke damunta amman cikin zuciyarta kuwa bakin ciki ne aciki fal. Haka taro ya watse,,, Sakina da Faruq kullum suna cikin waya banda kuka ba abinda faruq kewa Sakina, maimakon shi ya bata hakuri ita ce ta daure tare da basa hakuri tana lallabasa... Misalin karfe hudu na yamma Faruq ya zo kofar gate din gidan su Sakina kiranta ya yi awaya asabule ta fito ba tare da ta bari kowa ya gannta ba,, tana fita kennan sai ga ya haidar yayi kicibis da ita da kuma Faruq da gudu Sakina ta shige gida domin tasan halin Yayan na ta daman chan ba son auren ya ke ba, bare kuma an sami matsala, Yaya Haidar fin Faruq ya yi kawai da wani mummnan kallo sannan ya bi Sakina suka shige gida. Duk da wulakancin da ake ma Faruq amman hakan bai sa ya daina zuwa gidan su Sakina ba, domin kuwa kullum yana gidan tare da roko akan akara basa damar auren Sakina Insha Allah ba matsala. Yaya Haidar ya ki yarda fur tare da fadin, "Wannan ai rainin hankali tun yanzu uwarsa na wulakanta mu inaga anyi Auren? ni fa ban san wace irin zuciyace da Sakina ba, Shikennan Baba ayi Auren nan amman duk abinda ya biyo baya ita ta jawa kanta." Haka dai aka cigaba da shirye-shiryen baki batare da Hajiyan Faruq ta sani ba.. Faruq ya shirya tsaf domin zuwa garin su dan ya sanar da dangin Mamansa maganar Auren sa, yana zuwa kan ma ya sanar da su aranar su ka Aura ma sa yar uwarsa domin su daman asali aka'i'dar su sai ka Aure yar kabilar su da fari koda kuwa za ka kara Aure, Haka aka ma Faruq Aure da yar uwarsa SUBAI'ATU, haka ya shirya domin dawowa gida asanyaye akan zai zo yasanar da Mahaifiyarsa kan ya zo ya tafi da amaryar sa. Haka itama Hajiyan Faruq ta na nan tana shirin Aura ma sa yar kawarsa shirye shiryen biki kawai ta ke tana jiran Dan ta yadawo ta Aura ma sa wadda ta ke so, haka kuma dangin Baban Faruq ma suna na nan ana shirin Biki da Sakina. *karku man ta an ma Faruq aure agarin su sannan anan Nigeria Maman sa na nan ta na shirin Aura ma sa yar kawarta haka kuma shima da dangin Babansa suna nan suna shirin Auren Sakina kuma duk arana daya za'a daura* *KARKU BARI KWAKWALWARKU TA RIKICE DOMIN BINA ASANNU SHI ZAI SA KU FAHIMTA ASAUKAKE...* *YAWAN CMMTS YAWAN TYPING😍* Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:11] Shalelen Mamata🥳🥳: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-5* ____________________________________________________________________________ *A min afwan muna fama da rashin wuta ne 🙏* _*Wannan shafin sadaukarwa ne ga yar uwata gudan jinina SUBAI'ATU SANI MUNKAILA (suby) ki yi yadda kikeso dashi😘ina kewarki a kulamin da die heart dina🤣*_ a ko wani bangare Shiryen baki suke ba na wasa ba, mussaman gidan Su Sakina dan zan iyacewa ba abinda ba suyi ba nakayan fulawa,robobi,buga stikas,kalan,sobeniyas dai nagani afada. karfe 11:00 na safiyar asabar A ka daura Auren Sakina da Faruq kennan mahaifiyarsa labari ya zo ma ta ita tana nan ta na shirin karfe 2:00 za daura da yar kawarta Safiya. Tana jin labarin nan bata sarara ba dibi yan koranta harda Maman Safiya suka nufi gidan su Sakina..... *a pejin farko na sanar da ku abinda yawakana wanda sai da hajiyan faruq tasa aka saki Sakina kan taji dadi yanzu zamu cigaba da tsunduma cikin labarin ku biyoni asannu karku gaza😘😘* *CIGABAN LABARI.......* ba fashi kuwa karfe 2 dai-dai aka daura Auren Faruq da Safiya amman ba Ango domin tsabar zazzabi da ya addabi faruq ko daurin auren ma bai iya hallarta ba duk da cewa koda yana da lafiyar ma bai da niyyar zuwa a cewar sa *Ni na ga kaddarar aure* A haka dai a ka gama shagalin biki adaddafe domin kuwa Ango baya ta amarya. Ankai amarya Safiya Gidan Faruq wanda daman gidan mace biyu ya gida. Dakyar Hajiyarsa ta tirsasa shi aka rakasa. Sakina na zaune ta rikye wayarsa tare da kallon hotunan da sukai na pre-weeding da Faruq din ta azahiri murmushi ta ke amman cikin zuciyarta banda kuna ba abinda ta ke ji. Misalin sha biyu na dare tana ta fama ta kalla ta kara kalla sai ga kiran Faruq ya shigo, shi kan shi kiran da taga ya shigo murmushi tayi kaman zata kama amman kuma sai ta katse tare ajiye wayar ta juya ma ta baya. Faruq bai gaji ba yacigaba da kira kusan sau biyar bata dauka ba sai tunani ya zo ma sa ta hanyar yi ma ta text msg.. " _Sakina ta kinsan dai halin da na ke ciki ko? ko da ace kalau na ke bana iya rintsawa batare da naji muryarki ba, bare ace yau da na ke cikin tashin hankali, Sakina ina son ki ina son ki dan Allah karkicemin kin dai na so na ki dau wayata naji muryarki ko zuciyata zata bar kuna."_ kuka Faruq ya ke yana wannan rabutun. Sakina na jin karar mssg ta mikye tare da janyo wayar ta, duban da zatayi ne yasa jikinta ya yi sanyi domin kuwa ita kan ta tana ma Faruq so ba na wasa ba, hakan yasa bata jira ya kara kira ba tuni ta kirasa tare da fadin, "Hubbynah ka yi hakuri karkasa damuwa aranka kaji wannan itace kaddarar auren mu kuma komai mai hucewa ne, ba na so kana sa damuwa aranka kaji please." murya araunane. Tuni Faruq ya ji Zuciyarsa tai fari ya ce, "Maddalla da samun mace ta gari kamarki, insha Allah sai na mallake ki mallaka ta har abada, ina son ki Sakina, ina son kyawawan dabi'un ki, kin cika jarumar ma ta da kowani irin namiji zai yi alfahari da ita." Murmushi Sakina tayi tare da fadin, "Nima ina son ka, byebyee aje gun Amarya." Kan Faruq ya kara magana tuni ta katse wayar tare da rufe idanunta. Safiya kuwa taga abin ba yi Faruq na falo kwance akan kujera tunda suka gama waya da Sakina ya zubawa fuskar wayar ido domin hoton Sakina ne akai.. Safiya na zuwa ta fusge wayar tare da fadin, "Wai wannan wani irin iskanci ne? wa ce Amarya aka tabama haka, ka bar ni kamar wata gunki ina ta zaman jiran shigowarka." Faruq ya ce, "Ya isa haka Safiya ke kan ki kin san ba son ki nake aka aura min ke ba, ki barni naji da damuwata Aure dai gashi anyi kuma kin shigo gidana burinki da na mahaifiyarki ya cika dan haka ki bar ni please." Mika hannu ya yi zai karbi wayarsa ta bige ma sa hannu tare da fadin, "Wai akan waccer karuwar ka ke wulakantani? da me ta fini." Kalmar karuwar da Safiya ta kira Sakina da shi ne ya girgiza Faruq bai san lokacin da yadauketa da mari ba fusge wayarsa ya yi tare da shigewa cikin dakin ya rufo kofar. Tsaye ya bar Safiya jim domin tayi biyu ba bu ya mareta sannan ya shige cikin daki tare da rufo kofa. Haka kuwa ta kwana a kan kujerar falo tun tana kuka harta gaji tai shiru. Da asuba Faruq ya fito da alwalarsa tare da nufar massallaci domin salla, Ko kallon inda ta ke bai yi ba bare magana. Daga masallacin nan ba inda Faruq ya nufa sai kofar gidan su Sakina, tun gari bai yi haske ba har yayi haske yana cikin motarsa banda kallon kofar gidan tare da tunani kala-kala ba abinda ya ke. Daukan wayarsa yayi tare da kiran Sakina A waya ai ko tana gani ta daga ya ce ma ta yana kofar gate. Da sauri ta zura hijabi zata fita Maryam ta ce, "Aunty Sakina ina zaki da sassafen nan?" Sakina ta ce, "Abu zan karba agidan su Hafsa." Da sauri ta fice tun kan wata tambayar ta biyo baya. Tana fita ta hango motar Faruq. Karasawa tayi da murmushin ta. Tana zuwa Faruq ya fara...... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:11] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-6* ____________________________________________________________________________ *SADAUKARWA GAREKI AMINIYA MOM ANNUR😘INA YIN KI IRIN SOSE DINNAN🥰* ****** Kuka Murmushin da ba ataba rasashi afuskar Sakina shine dai ya bayyana tare da fadin, "Haba Hubby na sai ka ce ba namiji ba karka ba ni kunya ma na." Faruq ya ce, "Haba Sakina ya bazan yi kuka ba? kina gani fa Hajiya ta dage sai ta rabani da farincikina, na farko ta sa anfasa daurawa wannan kuma andauran ma ba ta barni ba ta sa na sakeki, ga shi ta Aurar min wadda ta ke so, haka ma yan uwanta sun aura min wadda suke so wai duk hakan bai isa ace anbar ni nima nabi zabina ba?" da kuke ya ke maganar tsabar takaici da bacin rai ne zance ko bakin ciki. Sakina ta ce, " _Hmmm ba mu da wata manufa da ya fi mu bi umarnin iyayen mu bin na gaba bin Allah, indai Allah ya kaddara ni matar ka ce to ba makawa sai munyi aure ko da kuwa za acigaba da rusawa ne dole su gaji su barmu."_ Goge hawayen sa yayi da hankichif din da ke hannunsa tare da fadin, "Nagode Sakina, ki kulamin da kan ki, kinji kishiga gida kar azo agan mu asami matsala." _"To hubby byebyee miss u."cewar Sakina kan ta shige gida_ Tuni ta shige da saurin ta, shi ko bai tafi alokacin ba sai da ya dan jima yana tunani. Daga nan ba inda ya huce sai gun aikin Baban su Sakina, bai ma iso ba har sai da ya tsaya ya iso sannan ya gesheshi ba mu su ba bata rai Baba ya amsa. Faruq na ta kame-kame ya na son yin magana amman ya rasa ta ina zai fara domin ba yau yasaba neman wannan alfarma. Baba ya fahimta hakan ya sa shi fadin, "FARUQ ka saurareni nasan me ya kawo ka nasan bai huce maganarka da Sakina ba Wadda kuma tun jiya na fadama babu ita, kasa aranka cewa indai kaga kun yi rayuwa da Sakina to Allah ne ya kaddara amman abu mafi mahimmanci shine kawai ka sa aranka ka hakuri kaje ka bi umarnin mahaifiyarka, indai Mata ce ai gashi kana da su har biyu ma ina mai ba ka shawara da ka koyawa kan ka sansu tun kan lokaci ya kurema, ni dai ina son abin da 'ya ta ke so, amman indai ya kai ga wulakanci dole na hakura sannan ita ma na tirsasa ta, ta hakura, daga kai har Sakinan 'ya 'ya ne a guna dan Haka ina mu ku fatan alkairi." Gaba daya jikin Faruq ya yi sanyi hakan ya Sa shi godiya ga Baba sannan ya tashi da nufin tafiya. Tun daga ranar Faruq bai kara zuwa gidan su Sakina ba, kasancewa ba jin dadin jikin sa ya ke ba, gaba daya ma ya fita ahaiyyacin sa. Safiya kuwa ta na nan ban da zubar masifa ba abin da ta ke ma sa duk da kasancewar bai da lafiya amman hakan bai dameta... Sakina kuwa hakurin ta ya fara gazawa kana ganinta ka ga wadda take cikin wani hali domin duk yanayin ta ya chanja. Mama na ta kiran ta tazo taci abinci kennan tasowar da zatayi sai ga ta akasa warwas ko motsi batayi numfashin ta ya tsaya. Gaba daya Mama da Maryam sun rikice kasancewar Baba da Yayunta maza duk ba sa nan, Maryam ce tai saurin kiran Yaya Haidar awaya, ba adau mintina goma ba kuwa sai gashi yadau Sakina suka nufa asibiti. A na zuwa a ka fara ma ta taimakon gaggawa, Faruq kuwa ya jin Sakina ba lafiya tuni ya ji ciwon shi ya warke kamar bai taba ciwo ba, shiryawa ya yi ya fita domin bin su asibitin, tun da ya je yaga Yaya Haidar ya ka sa karasa domin yasan za a iya samun matsala Zagayawa ya yi ta windon dakin da take yana tsaye kamar wani mai gadi, ba kowa adakin sai ita kadai tana farfadowa kuwa yana ankare da ita ya ce, "Sakina." Taji muryar Faruq amman ba ta ga kowa adakin ba. Azuciyar ta take fadin, "kar fa ace son Faruq har ya fara haukatani." Kara kiran ta yayi tare da fadin, "Gani nan ta windo." juyowar da zatai kawai ai ko sai suka hada ido da ita ga kuma Yaya Haidar da su Mama sun shigo. *Anya kuwa ku na jin dadin labarin nan?😘 gsky ban ga alamar hakan ba* Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:13] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-7* ________________________________________________________ *Am back🥰ayi min afwan duk kasancewar nasanar tun kan nadakata amman wa su ba su sani ba suna ta tmby, ngd sose da nuna kulawarku gareni❤️* Faruq na ganin su yalabe agefe ya na jin maganar su har Mama ta ce wa Yaya Haidar suje pamasi ga maganin da a ka rubuto, ai kuwa Faruq na jin fitar su ya zaga ya shige dakin. Sakina ta ce, "Kar su Mama su shigo fa Hubby in suka gan mu za asami matsala. Faruq ya ce, "Tun da dai naganki ai ba na gudun duk wani abun da zai faru Ynzu ko anjima. " Murmushi Sakina tayi tare da fadin, "Ya naga kaman ba ka da lafiyane. " Janyo kujerar robar da ke gefen sa ya yi tare fadin, "Ki na ganin zan sami lafiya ne bayan an rabani da farincikina?, Sakina ina sonki ina so na rayu da ke rayuwa ta har abada. " Magana ya ke hawaye na zuba daga idanunsa. Dafa karfen gadon Sakina ta yi ta dan zauna tare mikawa Faruq hanki tana, "Kai ne farincikin rayuwata a kullum ina fada ko da ba ka gareni, ka goge hawayenka masoyina ina so kasa aranka cewa indai rayuwarmu tare alkairi ne to ba makawa zan kasance mata agareka, ka sawa zuciyarka ruwan sanyi tare da neman mafita ma fi alkairi daga wajen Allah. " Goge hawayensa ya yi shima ya na murmushi kamar yadda sahibarsa ke yi, "Maddalla da samun Mace ta gari, in na rasaki na yi babbar asara, zan cigaba da hakuri tare da mi ka komai ga Mahallincin mu, ina son ki Sakina ina Alfahari da ke. "Cewar Faruq. Sakina ta ce, "yauwa jarumina nima ina alfahari da kai kuma ina son ka byee, byee ka tashi ka tafi kar su Mama su dawo. " Faruq ya tashi yana, "Owk Byee, byee zan dawo amman fa. " Murmushi kawai Sakina ta bi sa da shi. Ai kuwa Faruq na fita sai ga Mama da Yaya Haidar. Faruq ya gaida Mama ta amsa shiko Yaya Haidar kallon da ya ma sa ma ya hanasa iya ka ra magana bare ya geshesa wucewa kawai ya yi. Sai da Sakina ta yi sati daya asibiti kuma a kullum sai Faruq ya je ko da bai sami shiga ba sai ya tsaya a jikin window. Rayuwa ta cigaba Sose dai tsakanin Faruq da Sakina karuwa ta ke a kullum, duk da kasance ma su neman Aurenta kara zuwa su ke amman fir ta ki amincewa da su ita dai sai Faruq. Kullum sai dai suyi waya ko kuma in ta fita ta kirasa su hadu. Yau ma kamar kullum Sakina ta shirya tsaf domin tafiya shagon ta *(ta na da shagon sai da dogayen riguna na ma ta, gyalulluka hadda ma kananun kaya kasancewar fasa auren da akayi ga shi tavar skul y sa kawai a ka bude ma ta da ta zauna ba abin yi.)* Tun safe ta fita har lokacin dawowarta ya fara kurewa ba Sakina ba labarin ta, tun yan gida ba su damu hardai a kaga dare ya yi fa shiru. *Ko me ya faru da Sakina? Ku biyoni a shafi na gaba* Xayyeesherthul-Humaeran ku ce😘 [11/08 à 00:13] Shalelen Mamata🥳🥳: https://chat.whatsapp.com/CqOjIFZU0AGLrgtAWmOAVb *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-8* ________________________________________________________ *HAPPY BIRTHDAY AUNTYNA SHAXEE ALLAH YAKARA TSAWON KWANA DA BASIRAR SUBURBUDO MA NA DAD'ADAN NOVELS🥰INA YIN KI INA ALFAHARI DA KE MY MENTOR🎂🎂🎂🎂* *WANNAN SHAFIN SADAUKARWANE GAREKI SARAUNIYAR COMMETS DIN XAYYEESHERTH FAN GROUP MAMAN USMAN KI YI YADDA KIKESO DA SHI INA YIN KI IRIN SOSE DINNAN🥰🥰* Su Mama, Maryam, Yaya Haidar da Baba duk hankalin su y tashi hakan ya sa Yaya Haidar nufan shagon Sakina domin wayarta ma akashe ba ta shiga, ya na zuwa kuwa ya sa'a shagon abude, hakan ya sa shi karasa da sauri. Abun mamaki Sakina gani zaune Faruq na gefenta su na ta hirarsu ban da dariya ba abinda Faruq ke yi, da ka gansu za ka fahimci cewa masoyane wanda su ke cikin shaukin So. Wa ta tsawa da Yaya Haidar ya yi ne ya fargar da su domin ba su ma lura da zuwan sa ba. Tuni Sakina ta mikye. Daga hannun da Yaya Haidar zai yi aiko sai ya dallawa Faruq mari tare da fadin, "Wai kai wani irin mayye ne? Iye? Mahaifiyarka ta nuna ma ta kiyayya a fili amman ka ki rabuwa da ita? Kai ka na ganin wai akwai wani aurene tsakanin ku nan gaba? To wallahi tun huri kasan inda dare ya ma, ficemin daga shagon nan. "Ya fada tare nuna ma sa kwofa. Ya dawo kan Sakina, "Ke kuma muje gidan za kiyi bayani, daga yau ma an rufe shagon zan ga ta inda zai na bin ki. " Ko uffan Faruq bai iya cewa ba ya fice. Domin yasan ko miye ma ya faru Hajiyarsa ce ta ja ma sa. Yaya Haidar daukan key yayi y rufe shagon sannan y rikye hannun Sakina su ka shiga mota, tun da su ka shiga Yaya Haidar bai kara ce ma ta komai ba har su ka isa. Suna shiga su Mama su ka fito su na Alhamdullillahi ta rongume Sakina tare da fadin, "Haba Sakina ina ki ka je haka? Duk kin ba mu tsoro mun zata wani abu ne ya faru da ke. " Jan ta tayi suka shige daki. Bayan kowa ya zauna ne Yaya Haidar ya ce, "Baba ka ga dai wannan yarinyar ta karbi kaddarar auren ta hannu bibbiyu amman yanzu Faruq na neman hure ma ta kunne kuma ba za mu yarda ba dan haka ni na yanke hukunci kawai in Khadija *(Khadija Yayarsu Sakina ce da ke Aure a Abuja, daga ita sai Sakina tukun na Maryam)* ta zo zata bi ta suje chan abuja domin in ba haka ba akwai matsala." Baba da Mama sun karbi shawarar Faruq domin kuwa sun san ba wata manufa da ta huce wannan, mussaman Baba da kullum sai Faruq ya je shago ya gallabesa kan abashi dama ta karshe. Washe gari kuwa sai ga Aunty Khadija ta zo bayan sun gama magana da Baba ne. Ta ce to insha Allah gobe zasu huce domin tana makaranta. **** Da Sassafi Sakina da Aunty khadija su ka fara shirin tafiya. Misalin karfe goma dai-dai sun gama shiri tsaf. Gaba daya jikin Sakina ya mutu domin ita kwata-kwata ba sa son tafiyar nan. Suna fita ba jimawa suka sami mota. Bayan sun shiga mota ta tashi daga idon da Sakina za taga Faruq a gaban mot.......... *Cmmts din ku shi ke karawa hannun mu gardin rubutu🥰* Xayyeeshern ku ce🥰 [11/08 à 00:14] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-9* ________________________________________________________ *WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA YAN GROUP DI NA XAYYEESHERTH FANS GROUP😘😘😘 INA YIN KU IRIN SOSAI DINNAN ACIGABA DA SHARHI MUTANENA* Mota wani matsakaicin murmushi ta yi tare da kawar da kan ta gefe. Har su ka isa garin Abuja Aunty ba ta gane Faruq na cikin motar su ba har sai da su ka sauka rikye baki kawai Aunty ta yi ganin Faruq agaban ta ya na gesheta, murmushi kawai ya yi dan ya ga mamaki tsarara afuskar Aunty kara fadi ya yi, "Ina hini Aunty? " Murmushi ta yi tare da fadin, "Lafiya Romio dan kai kam kaci ace ma Romio ko ince Yayan sa ma. " Murmushi kawai Faruq ya yi tare da karban jakar hannun su Anty driver ya zo ya dauke so. Bayan sun shiga gida sun yi sallah an kawo ma Faruq abinci ya ci suma sunci sannan Anty ta ce, "Daman na so na nemaka kan mutawo dan mu yi magana amman ba lokaci to yanzu tun da dai Allah ya kawoka shikennan, Faruq ina so na nemi wannan alfarmar ce daga gareka dan Allah dan Annabi ka rabu da Sakina. " Daga Faruq har Sakina sai da gaban su ya fadi da jin wannan kalmar da ta fito daga bakin Aunty. Tuni Sakina ta sunkuyar da kan ta kasa shi ko Faruq ya ka sa cire idon sa daga duban na Aunty. Ita kuwa cigaba da magana ta yi tana, "Wannan itace mafita agaremu da mu da kai, ba sai an fada ba mun san kana son sakina so kuma na gaskiya amman azahiri auren ku ba mai yuhuwa ba ne ko da anyi ma ba amfani tun da dangin ka ba son ta su ke ba, karka manta fa sau biyu kennan na farkon anzo za adaura aka fasa na biyun kuwa an daura mahaifiyarka ta sa kasake ta. To miye amfanin hakan, dan haka ina rokon ka da ka fita arayuwar Sakina kasan cewa ba dan kowa naje na dauko Sakina ba sai dan kai domin bibbiyartan ma da kake zaka iya ja mana babbar matsala. Hawayene kawai ke zuba a idanun Faruq, ya ce, "Anty yanzu shikennan kina nufin b ni ba Sakina? Za ta je ta Auri wani ba ni ba?, ni kuma kaddarar Aure na kennan Mata biyu ba wadda nakeso aciki?, Aunty na fahimce kuma na gode, insha Allah zan fita arayuwar Sakina amman hakan ba wai yana nufin nadaina son ta bane, ina son ta kuma zan cigaba da son ta har karshen rayuwata, in dai ina nigeria ba zan iya juran rashin Sakina ba zan bar kasar nan kodan na var sakina tai rayuwa cikin walwala, amman ku sani Sakina ita ce rayuwata. " Ta shi ya yi yaje gaban Sakina ya durkusa yana, "Ina son ki Sakina duk wanda ya sameki matsayin mata ya dace, ina alfahari da ke, karki manta dani ko da ace kinji mutuwata karkiyi kuka kimin addu'ah. " Sakina ta kasa dagowa sun hada ido kawai wasa ta ke da yatsun hannunta. Ta shi Faruq ya yi tare da goge hawayen da ke fuskarsa. Sannan ya fita XAYYEESHERTH [11/08 à 00:14] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-11* ________________________________________________________ *AFWAN PLS BIKI MU KE WLH KUKAJINI SHIRU AMMAN YANZU TUNDA AN KAMMALA KOMAI ZAI YI DAI DAI INSHA ALLAH😘😘😘* Suna gama wayar nan ba inda Faruq ya nufa sai gidan babban malamin da ke anguwar su Sakina. Ita kuwa Sakina kiran Ibrahim ta yi tare da ma sa albishir cewa ta amince ya turo. Ba karamin Farinciki Ibrahim ya yi ba da jin hakan, acikin daren kuwa ya sanar da mahaifiyar sa ita ma tai murna sose kasancewar ta san Sakina sose kuma ta na son ta itama. Ya na zuwa ya sanarwa da malamin duk abin ke faruwa daga farko har karshe. Faruq ya bukaci da malamin ya shiga maganar domin ma Baban Sakina magana. Malamin kuwa ya aminshi lamarin hannu bibbiyu hakan ya sa shi kiran sauran malaman da ke anguwar su ka tattauna akan lamari sannan su ka nufi gidan su Sakina har da Faruq din. Suna zuwa kuwa sun ci sa'a Baba ya fito kennan za shi masallaci,kasancewar lokacin sallah ya ku sa kurewa ya sa su yin maganar atsatsaye. Baba ya ji batun su kasancewar ya na ganin darajar su amatsayin su na malamai ya sa shi fadin cewa zai yi tunani su duba su gani. Ba ason Ran Faruq ba ya bar gurin domin acewarsa ma shi bai ki adaura auren yanzu ba. Washe gari************ Da Asuba Baba yatafi masallaci chan kawai sai ga kiran Baba nan awaya kan cewar abawa Yaya Haidar goron Auren Sakina. *kasancewar wancen goron na nan ajiye da a ka fasa auren*. Mama ta ce, "Oh ina ga Sadaka zai bayar kuma da asubar nan." kiran Haidar tayi ya dauuka sannan ya nufa masallacin. Chan sai ga wani kiran ma Mama na amsawa Baba ya ce ma ta Auren Sakina fa za adaura. "Iyeee auren Sakina kuma?."Abin da Mama ta iya furtawa kennan sai ta ajiye wayar ta nufa dakin su Sakina da Maryam. "Sakina,Sakina,Maryam ba za ku tashi ba ne?" Kin motsawa su kai domin barci na kan su. Mama ta kara cewa, "Ba za Ku tashi ba? to auren Sakina za adaura." Ai tuni Maryam ta bude kofa. Mama ta ce, "Jeki masallacin ki jiyo ma na." Ai ko ba takalmi Maryam ta nufa masallaci da ga zuwan ta kuwa karaf akunnan ta andaura auren Sakina Da Faruq. Ai da gudu Maryam ta kara komawa gida. Tana zuwa ta sanar da Mama duk da cewa suma sunajin daurin Aure daga gidan. Sakina kuwa tayi mutuwar tsaye ban da hawaye ba abin da ke fita daga idonta. Baba na shigowa ta durkuusa gare sa ta na kuka, "Baba ba na son Auren nan, ni nadaina son sa,dan Allah ka ce min ba adaura ba." Kawai ta fashe da kuka. Gaba daya Sakina ta rikice ita fa adole ba ta son Faruq. Baba ya ce, "Sakina ai sai dai ki yi hakuri kawai aikin gama ya riga ya gama,ban yi tsammamin zakice Aa ba,ki yi hakuri ki karbi wannan kaddarar ma kamar yadda ki ka karba ta farko." Ina ai Sakina ba ta san wannan zancen ba ta dage alan fur ba ta son Faruq. Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:14] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-12* ________________________________________________________ *WANNAN SHAFIN SADAUKARWANE GAREKI FIRDAUSI NA BAKI SHI KACOKAN KIYI YADDA KIKE SO DA SHI XAYEESHER TA KI CE,,INA YIN KI IRIN SOSE DINNAN😘* Azahiri dai Sakina ta nu na ba ta son Faruq Amman cikin zuciyar ta kam har yanzu ta na son abun ta. Shagalin bikin da ba shiri kawai aka fara agidan, ma su zuwa kasuwa nazuwa,ma su gyara kaya na gyarawa,kasancewar duk kayan ta da man su na nan a ajiye sai yan was su kananan abun da ba arasa nema ba. Sakina kuwa da ka ganta zakasan cewa amaryace domin kuwa ta sha lalle da gyaran jiki na bikin aminiyarta Wanda ba ta San Ashe harda na ta ba. Sakina ta yi hakuri Amman gaba daya arikice ta ke ta rasa ma me zata fara gani ta ke kaman wasa ne ba auren ta ake ba, ko ince gani ta ke wani Abu na shirin afkuwa kamar yadda aka saba abaya. Faruq kuwa ya na chan ban da washe baki ba abin da ya ke,Safiya kuwa ta kama karamar hauka da jin wai Faruq ya yi Aure. Ba shiri ta kira Maman ta awaya ta sanar da ita sukayi gidan su Hajiyan Faruq. Ba sallama suka shige gidan suna huci kamar sabon biredi. Hajiya ta ce, "Ah Aminiya ke da sirikar ta wa ce?" Mummunan kallo Mama ta bita da shi Sannan Safiya ta ce, "To munafuka daman yadda mu kai da ke Kennan? Wa to kin yarjewa Dan ki akan ya je ya auro wannan mayyar yarinyar? To wallahi ba Ku isa ba daga ke har Dan na ki." Hajiya ta rikye baki tana, "Safiya ni kika fadawa magana haka? Aminiya kina jin ta?" Mama ta CE, "Ai wannan ma kadan ta mi ki dalla chan karamar munafuka kawai ashe daman da abin kika shirya to na fadamiki in sake Fada miki daga ke har Ita Sakinan zaku gayawa aya zaki." Hajiya kuwa mutuwar tsaye ta yi domin itama yanzu taji labarin auren Faruq Abu mafi mahimmanci da ya ba ta mamaki shine yadda aminiyarta ta juya ma ta baya gashi komai da ya faru duk akam ta ne Dan kawai ta faranta ma ta Faruq ya auri yarta. Amman yanzu ta nuna ba ta san komai ba. Maman Safiya kuwa ba inda suka nufa sai wajen BOKA *A na wata ga wata an gama wani case din fa ga wani sabo fil aleda.* Hajiya kiran Faruq tai awaya kawai sai ga shi ya zo ba mu su. Ya na zuwa Hajiya ta ce, "Faruq ka kyauta ka auri Sakina ka bi son ran ka, wannan karam dai banda bakin magana domin kuwa nagano wani babban lamari, ba abinda zan ce ma sai dai Allah ya ma albarka Allah ya sa anyi wannan aure asa'a,kamin alfarma daya a kan Safiya ka yi hakuri nasan kana da hakuurin amman ka kara hakuri nasan halin Safiya da mahaifiyarta, nayi dana sanin hadin auren kuu da tun farko na barka ka bi zabin ka Sakina na chan tana ta neme nemen kayayyakin ta. Karfe biyar dai-dai aka zo daukan amarya. Sakina tayi kukan rabuwa da iyayen ta ba kadan dan da kyar ma aka fitar da ita daga gidan. Anje kai amarya dai dai lokacin da Safiya ta koma gida. Zama tai atsarkar gidan tanai wa mutane kallon hadarin kaji. Su kuwa yan uwan Sakina ba mai kallonta bare shiga harkarta. Ana kai amarya aka watse kasancewar ba kwana. Faruq ya shiga gida ya na washe baki kawai sai ga Safiya abakin kofar Sakina. "Miye ha ka Safiya? bani waje na huce ma na." cewar Faruq. Safiya kowa cin cingom din ta take tana girgiza kai. Faruq ya ga abin bq yi tuni ya fige ta ya shige abin sa. Safiya ta tafi tana masifa domin ba yadda ta iya ya riga ya shige ya kulle kofar. Da sallama Faruuq ya shiga dakin Sakina. Kan Sakina durkushe agaban gado. Ta amsa sallamar asanyaye. Zai kara magana kennan sai sukaji bugun kofa kamar za acire. Da huci Faruq ke fadin," wai wacece ne?" Safiya ta ce, "Ni ce nan wallahi ka zo ka bude ko in balla kofar nan. Rai abace Faruq ya nufa kofa Yana zuwa..... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-13* ________________________________________________________ *WANNAN FEJIN NA KU NE MASOYAN KWARAI,MMN KHAIRAT,RAHIMA ADAMU,FIRDAUSI,MAMAN USMAN,RUKAYYA FULANI,KUYI YADDA KUKESO DA SHI INA YIN KU OLL❤️* Safiya ta fara kukan munafurci, Kawai bin ta da kallo Faruq yA yi dan ya ma kasa magana. A shagwabe ta ce, "Sweet ni wallahi tsoro nakeji bazan iya kwana ni daya adakin ba,ko na zo nan mu kwana please." harda durkusawartA kasa ta na kuka. Faruq ya riko ma ta hannun ta na murna za su shige ciki sai ko ya yi dakin ta da ita. Ban san me ya ce ma ta ba kawai dai naga fitowarsa ya na murmushi. Washe gari Da sassafe Safiya ta tashi ta dafawa su Faruq ruwan wanka tare da yi mu su breakfast. Abin na ta ya ba Faruq mamaki sosai amman kawai ya basar. Hajiyan Faruq kuwa da sassaafen nan ta shirya domin zuwa gidan aminiyarta. Ta na zuwa Maman Safiya ta juya ma ta baya tare da fadin, "Wani munafurcin ne ya kawoki gida? Murmushi Hajiya tayi tana fadin, "Aminiya ke ma dai kin san ba mai iya rabamu,Ba ma wannan ba kawo kunnanki kiji batun da na ke tafe da shi." Ji na yi kawai suna shewa Mama na fadin, "Kai Aminiya amman kin san salon mugunta kala-kala wallahi." Hajiya ta ce, "Ah to in anki abin da mu ke so ai ba a ki ga ni a aikace ba." Mama ta mik'a ma ta hannu su ka tafa sannan ta ce, "Ina alfahari da ke Aminiya, yanzu zan kira Safiya in laburta ma ta komai,Kin san jiya da na fusata har na fara aikin da kai na." Hajiya ta ce, "uumm ai kawai nai shiru ne sabida nasan baku fahimci kan lamarin ba." ****************Rayuwar jin dadi mai cike da farinciki ta cigaba da wanzuwa tsakanin Faruq da Sakina sai dai kash bi ta da kullen da ake mu su na bibiyarsu ba tare da sun fahimta ba,domin kuwa Safiya faran faran ta ke da Sakina in ta gan ta kaman za ta durkusa ma ta, ta hau bayanta. Maman Safiya da Hajiyan Faruq su na nan su na shiga da fita,su na kashe kudede amman ba chanji. Hakan ya sa Hajiya yan ke shawarar da suje chan garin su Niger domin anan ne ta ke da tabbacin samun nasara. Haka kuwa akayi Niger ta nufa ita da Maman Safiya. Sai da sukai Sati fir sannan su ka dawo gida nigeria. **********Sakina ta tashi safiyar yau jiki ba kwari gaba daya jiri ta ke ji hakan ya sa ta kiran Faruq awaya ta sanar ma sa,ya na zuwa kuwa ya dauke ta suka nufa asibiti. Bayan likita ya yi yan gwaje-gwaje ne ya ke yi ma Faruq albishir da cewa Sakina na tare da juna biyu na wata guda. Ba karamin farinciki Faruq yA yi ba wanda bai san lokacin da ya rungume matarsa ba. Safiya kuwa takaici kaman ta yi, ya ya kawai dariyar yak'e ta ke, ba ta iya hakuri ba kuwa ta kira Mama ta sanar ma ta, Mama ta ce, "Karkiji komai Safiya komai da shirin maganar ciki kam kamar anyi an gama,anjima ina so kije gidan Aminiyata za mu hadu achan. Da haka su kai sallama Shi ko Faruq ya na nan ya na lallaba abarsa kamar k'wai abin natabawa Safiya zuciya amman ta danne ba ta nunawa gudun kar shirin su ya baci. Suna komawa kuwa Safiya tai gidan Hajiya anan ta tarar Da Mama, ba karamin bayani su Kai ma ta ba ta yadda abin na su zai tafi atsari. Wani irin bakin abu ta bata mai sifar kunama ita kan ta sai da ta tsorata. Mama ta ce, "ke dalla ana nema mi ki hakkin ki da mafita ke ku ma kina kawo shiririta." Haka dai Safiya ta karba ta sa ajaka duk a tsorace. Hajiya ta ce, "Yauwa kina ganin abun nan karkiyi wasa da shi domin bakisan mak'udan kudin da na kashe a kansa,da farko dai ki tabbatar ta yi barci sai kije dai dai kasan inda ta kwanta sai tin filon na karkashin gadon kisa Safiya karkiyi wasa in kikayi wasa wannan abn kamar rayuwarki ya ke." Daga karshe dai atsorace Safiya ta bar gidannan. Tana zuwa gida kuwa Faruq ya ce, "Yauwa Safiya damam kin san tun jiya ya kamata na tafi niger wajen SUBAI'ATU amman ban samuu dama ba naga jikin Sakina da sauki zan tafi Akira kanwarta ne ko ke zaki taimaka ma ta." Da sauri Safiya ta ce, "A a ai ba komai ka bar mu kawai." Kwata-kwata Sakina ba ta son tafiyar Faruq domin jikinta ya bata akwai abin da ke shirin Faruwa. Ita kuuwa Safiya murna ta ke domin zatai aikin ta cikin nutsuwa. Faruq ya ta fi. Karfe takwas dai dai Safiya na Dakin Sakina da alama dai Sakina tai barci domin da suna yar hira ne jifa jifa. Safiya ta tashi domin aiwatar da aikin ta. Motsawan za tai sai ga Sakina ta...... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-14* ________________________________________________________ *WANNAN SHAFIN NAKINE MARYAM ABDULLAHI KANWA A GUN ANTY SAKINA🥰 KI YI YADDA KIKESO DA SHI DOMIN DA TALLAFIN KI LABARIN NAN KE TAFIYA A TSARI* Motsa. Tsayawa tai chak da alama barcin bai bar jikin Sakina ba hakan ya sa ta cigaba da barcinta cikin nishadi. Safiya kuwa tu ni ta durkusa kasan Sakina ta aiwatar da aikinta. Ta ajiye kennan kaman an mintsini Sakina ta farka ta na, "Safiya ina jin yunwa." Ba mu su kuwa da rawar jiki Safiya ta je kicin ta dibowa Sakina abinci. Sai da Sakina tai nak sannan Safiya ta ce, "To Sai da Safe Sakina in kina bukatar wani abu ki kirani awaya." Sakina ta ce, "To bakomai ma zan iya insha Allah." Safiya ta tafi dakin ta tare da farinciki fal cikin zuciya. Washe Gari*** Tun Asuba Sakina ta fara murkususu ciwon ciki ta rasa ma ina za ta sa kan ta, ta dau waya domin kiran Safiya amman Safiya ta ki daukam wayar kuma ta na gani, chan sai ga jini ya ballewa Sakina, tun tana iya motsi har ta fita hayyacinta, kiran Safiya ta ke amman Safiya kam ko ajikinta karshen magana ma wayar na hannuun ta daga karshe ma kiran Hajiya tai ta sanar da ita da alama aikin su fa ya yi kyau. Sakina ta rasa ina za ta sa ranta tun ta na iya daga wayar ta kira Safiya har karfin ta ya kare ba ta iya komai. Tun Asuba a ke abu daya har karfe sha biyu na rana, Sakina ta kasa motsi ma . Chan karfe daya saura sai ga Maryam kanwar Sakina kamar anhankadota, ta na shiga ba ta ga Sakina ba ku ma ba ta ji motsinta ba. , "Anty Sakina ina ki ke, wai ina ki ka shiga ne." cewar Maryam Da ta ga alamar ba mai amsa ma ta ne ta fara dube-dube tA shige cikin Dakina, abin da Maryam ta ganine ya sa ta suman tsaye. Sakina ce kwance cikin jini ba alamar motsi ko kadan da ka gan ta kasan ta fita a haiyyacin ta. *Rayuwa kennan ban san yaushe Sakina za ta tsallake kaddarar rayuwarta ba😭* Da gudu Maryam ta yi dakin Safiya tana, "Anty Safiya ki zo ki taimakeni dan Allah Anty Sakina ta mutu." Kuka kawai Maryam ta ke yi ita kuwa Safiya ta rikyeta tana muje mu gani ki bar kuka. Azahiri ta nuna tausayinta ga halin da ta tsinci Sakina amman azuciyarta farinciki ta ke fal harda fadin, "Allah ya sa ma mutuwar tai kowa ya huta." Da gudu Maryam ta je ta kira mai Nafe ya zo domin kai Sakina asibiti. Safiya ta na abu kamar ba zatai ba atunanin ta Sakina in ma ba ta karasa ba gwanda ta karasa kan su isa asibiti, hakan ya sa Maryam kiran mai nafe din ya taimaka su dau Sakina. ban da kuka ba abin da maryam ke yi har su ka isa special hospital d Ke garin bauchi. Su na isa aka farawa Sakina taimakon gaggawa amman ina likitoci sun rasa gane kan Sakina. Hakan ya sa Maryam ta kira su Mama da Faruq awaya domin likitocin sun bukaci ganin su. Tuni Faruq ya hawo jirgi domin ya na ji gaba daya ya rikice ya fita hayyacin sa burin sa kawai ya gan sa gaban sahibarsa. Mama da Baba da su Yaya Haidar kuwa tuni sun hallara a asibiti. Faruq na isowa ba wanda ya kula illa nufar da kin likitin in da Sakina ta ke. Ya na shiga....... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-15* ________________________________________________________ *SADAUKARWA GA YAN KUNGIYATA ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *INA KI KE AMINIYA🤣 HAJIYAR MU FATIMA ZAHRA EYMAN NAGODE DA KATI AJO A KARAMIN WANI🤗🤗* Sai misalin karfe 11:00 na dare Sakina ta fara dawowa hayyacinta. Faruq, Mama da su Maryam ba karamin farinciki su ka yi ba. Safiya kuwa tun da taji Sakina ta farfado kamar an watsa ma ta tafashasshen ruwa gabadaya taji ba dadi. Hakan ya sa ta kiran Mamanta A waya ta sanar ma ta da komai *ma su jiran jin mutuwa sun ji ta shi* Maman Sakina ta ce, "Kar ki ji komai mun shiryawa komai daki-daki in wannan bai yi ba ai wani zai yi balle kuma ma ya ma na abin da mu ka fi bukata a yan zu, ki bari sai ta koma gida zamu cigaba daga in da mu ka tsaya." Murmushin mugunta Safiya tai tare da fadin, "Shiyasa na ke son ki uwa ta gari, ni yanzu ma babbar matsalata hankalin Faruq na ke so yadawo gareni." Mama ta ce, "Haba sai ka ce ba ki sanni ba wannan ai da kan mu zamuyi ko Mahaifiyarsa ma ba za ta sani ba domin za ta hana bazata bari a illata d'an ta ba. Sai misalin karfe 11:00 na dare Sakina ta fara dawowa hayyacinta. Faruq, Mama da su Maryam ba karamin farinciki su ka yi ba. Safiya kuwa tun da taji Sakina ta farfado kamar an watsa ma ta tafashasshen ruwa gabadaya taji ba dadi. Hakan ya sa ta kiran Mamanta A waya ta sanar ma ta da komai *ma su jiran jin mutuwa sun ji ta shi* Maman Sakina ta ce, "Kar ki ji komai mun shiryawa komai daki-daki in wannan bai yi ba ai wani zai yi balle kuma ma ya ma na abin da mu ka fi bukata a yan zu, ki bari sai ta koma gida zamu cigaba daga in da mu ka tsaya." Murmushin mugunta Safiya tai tare da fadin, "Shiyasa na ke son ki uwa ta gari, ni yanzu ma babbar matsalata hankalin Faruq na ke so yadawo gareni." Mama ta ce, "Haba sai ka ce ba ki sanni ba wannan ai da kan mu zamuyi ko Mahaifiyarsa ma ba za ta sani ba domin za ta hana bazata bari a illata d'an ta ba, Dan ha ka karkiji komai kaman Faruq ya dawo tafin hannunki ne, ita kan ta mahaifiyar ta sa sai ta sha mamaki in fada miki, yanzu dai kinga dare ya yi bara na kwanta ku kuga ta kwannan zaune." ta karasa maganar ta na dariya. Safiya ta ce, "Hhhh Mama kennan ai Gwanda kar nai barcin a yi komai a idona." Mama ta ce, "Oh hakane fa ashe ki na daukan darasi, yan zu dai insha Allah gobe zan bazama inna dawo zan kira ki naji kuna asibitin ne ko gida sai inzo kinga daga nan na geshe da Yar Shila." Safiya tA kyalkyale da dariya tare da fadin, "Mamana kennan wai Yar Shila, tam byee byee ki kwanta da safen ma yi magana." Mama ta ce, "Owk byee ki kula da kan ki fa ana kaaf kaf kin san suma ba zama zasuyi ba dan ba a ban Faruq ya na ce mu su ba." Da ha ka su kai sallama. Faruq ya zo kennan ta na katse wayar ya ce, "... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:16] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-16* ________________________________________________________ *SADAUKARWA GA MY GRP XAYYEESHERTH FANS GRP🥰* *YANZU BAKWA SON SHARHI, KUMA NI NAFARA GAJIYA GASKIYA DAGA WANNAN PAGE DIN IN BAKUYI BA NI ZAN AJIYE NOVEL DIN KAWAI TUNDA BAKWA SO🤷‍♀️* Faruq ya ce, "Safiya ki zo mu je na maidaki gida kinga dare ya yi." Marairaicewa tai tare da fadin, "Haba Honey ka na ganin yar uwata kwance ba lafiya ni Ina naga ta tafiya." Faruq ya ce, "Eh Amman kin ga, ga Maman ta da Kanwarta su ne ma sukace in kaiki gida Dan yau anan ki ka hini." Safiya za ta kara marairaicewa Faruq ya ce, "Mu he please Safiya ban son gardama na lura ki na matukar ji da yar uwar nan ta ki." Wa ni Dadi Safiya ta ji aranta, ta tashi ta na fadin, "Tam Honey mu je Amman tare za mu kwana ko? Dan kasan ni dai bazan Iya kwana ni daya ba." Magana ta ke yi cike da kissa da kisisina wan da duk sai da ta sanyayarwa da Faruq jiki. A kasale ya ke fadin, "Bakomai mu je ta ya ma zan bar My Princess ita daya." Tun Safiya ta ga ta fara samun shiga ta tun ga kara shigewa Faruq da salo da ban da ban Wanda ya kara karkato da hankalinsa kan ta, har su ka isa gida. A ranar Dai kam Faruq ya nunawa Safiya Soyayyar da bai taba nunawa gare ta ba, ya yin da ta dun ga kashe shi da Shagwaba. Tuni ya manta da cewa wai fa Sakina na gadon asibiti, sai chan da Asuba ya farka afirgice tare da fadin, "Subhannallah! Na bar Sakina na jira na fa oh' oh kai Safiya ba ki kyauta min ba gaskiya. Safiya ta fara kukan munafurci ta na fadin, "Ni ni me kuma nayi? Bayan kai ne.... Kawai sai ta kara fashewa da kuka. Faruq bai San lokacin Da ya janyota jikin Sa ba tare da Fadin, " Am Sorry My Dear ki dai na kuka please bana so." Araunane Safiya ta ce, "Umm to ba ka ce ban kyauya ma ba?" Faruq ya yi murmushi tare da fadin, "Aa Farinciki na, bazan kara Fada ba ko in kama kunne na ne?" Murmushi itama sannan ta ce, "A ko da na yi niyar hukunta Honeyna sunan ma da ya kirani da shi kadai ya isa ya kwace Sa." Faruq ya ce, "Godiya na ke Farincikina yanzu dai muje mu yi sallah." Bayan sun idar da Sallah ne Safiya ta shiga kicin domin yi ma su kayan karyawa. Sai da ta gama tsaf Faruq ya ce, "To mu je a kaiwa su Sakina na su ko?" Safiya ta shagwabe fuska sannan ta ce, "Ni sai na ciyar da mijina tukunna." Ba gardama kuwa Faruq ya zauna sukai break shi da Safiya cikin nishadi ba tare da ya kara tunin Sakina ba. A haka lokaci ya dunga ja sai kusan 9 kan su ka nufa asibiti domin kai wa Sakina Break. Suna shiga tun da Sakina ta gan su tare kuma cikin nishadi jikinta ya yi sanyi gaba daya ta kasa kara kallon su illa sunkuyar da kan ta ds tai. Faruq ne ya karasa gaban ta tare da rikwo hannun ta, "Am Sorry Matata abar so na, na yi lattin zuwa, mun tsaya ma ki girki ne." Murmushi Sakina tai tare da fadin, "Bakomai mijina, ina kwana antashi lafiya?" Faruq ya ce, "Matar so, matar kirki ke ta daban ce a kullum kara son ki na ke acikin rai na, ina lafiya fatan rabin rai na ma haka." Sakina ta na gafe gabadaya ran ta ya yi baki ta kumburo baki tare da fadin, "Ni kan ina waje." Ta tashi fuuuu ta fita. Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:16] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-17* ________________________________________________________ *KUNA MATUKAR BANI MAMAKI🤔BAKU IYA SHARHI BA AMMAN KUN IYA FADIN A KARA YAWAN PAGE MUSSAMAN GRP DIN KHALEESAT HAIYDAR HAUSA NOVEL TO YSN YAWAN SHARHI YAWAN TYPING DI NA🥰* Oh typing Erorr ne a karshe fejin ba ya i mean Safiya not Sakina. Safiya ta tashi fuuu ta fita. Sakina ta kalli Faruq tare da fadin, "Ka je ka ba ta hakuri Honey."t Faruq ya ce , "Me a ka ma ta da zan ba ta hakuri na ga ai ke ma matatace ko?" Sakina tai murmushi tare da fadin, "Honey kennan ni dai je ka bata hakuri ban son damuwa wallahi." Faruq ya yi murmushi sannan ya ce, "As you Wish Madam." wa ni kyataccen murmushi kawai Sakina ta bi sa da shi. Faruq na fita kuwa ya tarar da Safiya ta fara kukan munafurci. "Haba Sofy na mi ye na kuka am so so sorry please." Cewar Faruq kennan. Safiya ta shagwabe sannan ta ce, "umm umm ba yan ka manta da ni dan ka ga Sakina." Faruq ya tallafota tare da fadin, "ni na isa in manta da my princess ke kin san na yi kewarta ne." Murmushi Safiya tai ganin ta cimma burin ta ta ce, "Umm umm to ni Sakeni in je mu gaisa ni ma kar azo a gan mu haka." Dariya Faruq ya yi sannan ya ce, "Yoo ai na ga dai matata ce ko?" Safiya ta ce, "Sosai ma kuwa amman ana ragewa, ka ga nikam na tafi gun Sakina byeebyee." gwalo Safiya Ta ke wa Faruq tare da dariya har ta shige d'akin sannan shima ya bita. Su na shiga Sakina tai murmushi tare da fadin, "Kun shigo? sannunku, Mama ta tafi gun likitan wai zai yi sallama ka je kai ma." Tuni Safiya taji RAS aranta domin ita ba haka ta so ba, ta so ace sai Sakina ta kwashi kwanaki kan nan ta gama more soyayyar Faruq amman wai a ce daga kwana daya har za ta koma gida. cije baki tai tare da fadin, "Ni na san me zanyi". a zuciya ta dunga sake-sake. Ba ta zauna a asibitin ba ta ce da su za ta je gidan Maman ta sanar ma ta kar tazo anyi sallama. Ai kuwa haka ta nufa gida, ta na zuwa ta sami mamanta ta shirya domin zuwa asibiti. Mama ta ce, "Ah ni da na ke shirin zuwa gunku ku ma." Safiya zauna ta na nishi tare da fadin, "Hmm Mama abin bai min dadi ba nafara kafa tarkona amman yau zai watse domin an sallameta ku ma kin san sa da nici akan wannan mayyar." Mama ta dafa kafadar Safiya tare da fadin, "Haba Safiya sai ka ce ba 'YA ta ba ke kin san ai bazan barki haka ba ko kin manta ne?" Safiya ta ce, "Hakane Mamana Shiyasa na zo ai kawai." Mama ta ce, "Yauwa yanzu kinga daman ina so daga asibiti mu huce ne dan haka muje kawai." Ta shi su kai suka nufa wajen wa ni BOKA dan ba na ce Malami ba. Suna zuwa ya fara birgar karyasa ya na fadin ai yasan komai. A ta ke malamin nan ya ba su wani magani tare da fadin a birne akofar gidan dai-dai inda ya saba bi in zai shiga. *"DAGA RANA MAI KAMA TA YAU INAI MI KI ALKAWARIN SAI ABIN DA KI KA CE FARUQ ZAI YI,KIN ZAME MA SA HASKE SAI YA GAN KI ZAI NA IYA MOTSI."* cewar malamin kennan ya na ihun haukarsa. sun karba Cike da farinciki da murna. Suna fita Safiya ta kira Faruq ko sun koma gida, ta ci sa'a kuwa ya ce aa yanzu su ke shiri dai. Da Sauri su Safiya su ka nufi gidan Mama ce ta fara tayata tona gurin domin birne a layar. Ai kuwa haka a kayi sun tona sannan suka birne da shike wajen da Karamin carpet sai su ka mayar su ka rufe ruf ta yarda ba wan da zai gane. Sun gama kennan sai ga Su Faruq din kuwa. Safiya da Mama sun tsaya ta cike sai murmushi su ke. Sakina da kanwarta Maryam ne su ka fara shiga. Faruq ya daga kafarsa......... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:16] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-18* ________________________________________________________ *TO MASOYAN FARUQ ALLAH YA YI DAI ADDU"AR KU TA KARBU BA MU SAN KO NAN GABA BA...* *Xayyeesherth Fans Grp ina nan a kan ba ka ta ko ku gyara ko in kulle grp din last warning ⚠ ⚠ ⚠* Kafarasa sai Sakina juyo ta nufesa tare da fadin, "Laaa Honey na, na manta ba mu shigo tare da addu'ah ba." Murmushi Faruq ya yi tare janyota shi kuma ya koma gefe. Addu'ar shiga gida suke tare ya rikye ma ta hannu kan suka shiga da bismillan su. Daga Safiya har Mama abin ya mutukar bata mu su rai domin kuwa Sakina ta bata ma su aiki. Mama kawai jan yarta ta yi fuu su ka nufi daki. Sakina ta ce, "Honeey ya na sun ta fi ko gesawa da Mama ba mu yi ba fa." Faruq ya ce, "Ohoo ni ina nasani muje ciki ai ta na nan inkinyi wanka k'e je ku gesa." Murmushi Sakina kawai ta yi domin ranta ya ba ta akwai wa ni abu. Maryam ce ta taimaka ma ta tai wanka, ta sa kaya sannan ta yi sallah. Ta na idarwa ta ce, "Maryam zo mu je mu gaida Mama." Maryam ta taso suka nufi dakin Safiya. Safiya na nan Mamanta na ma ta wa'azin agwagwa dan ba na ce na mutum ba tun da shedananci a ke koya ma ta. Da Sallama Sakina da Maryam su ka shiga ai ko suna shigA MAMAN safiya ta ba ta rai, Sai Safiya ce ta fara yakyen dole ta amsa da hike makirace, *Ma ko yi ya fi mai koyarwa* Dan yanzu kam Safiya ta ninka Mamanta a makirci,kisisina tare da kissa. Jikin Sakina ya yi sanyi kai a kasa take fadin, "Ina Hini Mama". Mama tai kaman bazata amsa ba sai da Safiya ta dan tabata. Jim sai ta ce, "Lafiya ya jikin na ki." magana ta ke kaman ta ga wani muchachcan bera na wari. Sakina ta ce, "Da Sauki." Safiya ta ce, "Ai jiki ma ya yi kyau sose ga shi har shek'i ki ke yar uwa." Murmushi kawai sakina ta yi tare da ta shi suka fita ita da Maryam, domin ita maryam tafara gane take-taken su hakan yasa ta ko geshesu ma ba tai ba. Su na fita Mama ta ce, "Ahir din ki Sakina kar in karaji kin kira wannan makiyiyar ta mu da Yar uwa, abin da har yanzu mun kasa kwasan rabon mu ta dalilinta kawai." Safiya ta ce, "Comman Mama calm dwon please, ta ya za ta saki jiki da ni in ban na nuna ma ta soyayya ba, ke kinsan shi kan shi Faruq din zuwanta ne fa yafara kulani, SO dole ne in ma ta biyayya in nuna ma ta so, Mama ni da kika ganni fa nasan abin da na ke sarai ki barnj da su kawai zan na chusa ma ta bakin ciki ne batare da ta gane ni ce ba, ni dai yanzu damuwata Faruq ya ta ka wajen nan ko ya ya ne." Mama ta ce, "Woo diyar kirki sai yanzu na fahimci cewa har kin kusa kereni, kar ki damu zai ta ka insha Allah." *********** Sakina kuwa suna zuwa daki ta ce wa Maryam, "Meyasa ba ki geshe su ba? haba Maryam." Maryam ta ce, "Anty Sakina kina ganin abin da su ke mana fa, ni wallahi da ni ce ke ma bazan shiga harkar ta ba dan makirace wallahi." Sakina ta janyo kanwata kusa da ita tare da fadin, "Ke yarinyace Maryam ba zaki gane ba, ni daj Nasan da zuciya daya na ke zaune da ita in ma ta chutar da ni Tawa kan ta,ita da Allah." Maryam za ta kara magana kennan Sakina dakatar da ita. Karfe Biyar Faruq ya mai da Maryam gida ita kuwa Mama na nan har karfe takwas su na ta kintsa tsiya ita da yar ta, sai kusan tara ta bar gida. Faruq har ya je ya ma Safiya sallama akan zai tafi dakin Sakina. Ta fara marairaice ma sa da makircin ta shi ko ya nuna ko ajikinsa Ya yi fitowar sa. Cije baki tai tare da binsa a baya har sun rufe kwofa ta buga ma su. Faruq ya ki budewa Sakina ce ta tashita bude. Tana budewa kuwa taga Safiya na kuka. Tuni Sakina ta rikice tare da fadin, "Me ya Faru Safiya shigo ciki." Shiga tai tana rikye cikin ta tare da fadin, "Cikina ke ciwo ku ma bazan iya barci ni daya ba, Faruq kar in matsa mu ku ko zaka kai ni gidan mu in kwana." Sakina ta ce, "Aa ba ayi haka ba, Honeey ka je ku kwana kawai." Faruq ya ce, "To ke zski iya kwana ke daya ne ko dai kawai duka mu kwana anan?" Tuni Safiya ta ji ras kar fa Sakina ta aminci. Ta ce,"Aa nikam kawai a kai ni gida." Sakina ta ce, "Bakomai fa ni naji sauki kuje kawai ba komai." Faruq ya yi murmushi tare da damko kumatun Sakina ya ce , " Matar kirki nagode ki kulamin da kan ki kinji." Safiya an sami abin so tuni ta damko Faruq irin a dole ita bazata iya tafiya ba sai an rikyeta. Daukan ta kawai ya yi tare da fadin, "Ni karki wahalar da ni da Tafiya muje ki sha magani." SAKINA ba ta san lokacin da hawaye Su ka fara zubo ma ta ba. Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:18] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-19/20* ________________________________________________________ *MY NEW GRP Xayyeesherth Fana Grp1 yau inga ruwan sharhi🥰* Safiya kuwa su na shiga ta rungume Faruq tare da fadin, "Umm Masoyina Har na ji cikin ya fara sauki, ina ga daman rashin ka ne." Faruq ya juyo da ita tare da zaunar da ita agefen gadon shima ya zauna sannan ya ce, "Dakyau My Princess daman ai haka na ke so." Tuni Safiya ta fara nunawa Faruq tsantsar soyayya wanda ya kai ga ya manta da Sakina. Sakina ta na daki har barci ya dauketa kawai sai ta juyo dariyar Safiya wanda da ka ji zakasan cewa suna cikin nishadi. Wani azazzaban kishine ya lullube Sakina wanda ya kai ga tafara hawaye, murmushi tai tare da share hawayen sannan ta tashi ta yo alwala sai da ta yi Sallah raka'a biyu sannan ta dauki littafi mai tsarki wato AL-QUR'ANI ta karan ta iya ka yin ta wanda sai da taji ranta ya yi fari tas ta manta da damuwa da ke ran ta, tuni barci ya dauketa awajen mai cike da nishadi. WASHE GARI""""""""""" Sakina na tashi da asuba ta ji jikinta ras kamar ba tai wani ciwo ba, hakan ya sa ta fara gyare-gyaren gida, sai da gama gyara dakinta tsaf sannan ta gyara tsakar gidan ma, ba ta huta ba ta shiga kicin domin hada mu su kayan karyawa. *DOYA ta fara ferewa sannan ta wanke ta tsaf ta fara suya, bayan ta gama suyan ta dibo kwai guda biyar tai greating attaruhu da albasa ta sa abin suyan ahuta da mangyada da kayan miyan sai da suka fara soyuwa sannan ta zuba kwan ciki, ta na zuba kwan ta fara jujjuya shi sannan tasa kayan dan dano tuni gida ya kaure da kamshi miya ta yi kyau sose a ido ma bare a abaki,,,,,ta gamawa ta sa aflas sannan ta koma ga yi musu tean waken suya, waken ta ta fara tsincewa kusan ba arasa kasa ko wani datti aciki, sannan ta wanke shi tsaf bayan ta wanke ta dauko blandar ta tai brandin, ta tace shi tsaf ta cire dusar tukun ta daura ahuta, ta sa gishiri dan kadan tare da yar cittar ta,,,,in kina da bukata za ki iya sa ma sa lipton,,,,Ashawarce tean waken suya ya na da matukar amfani garemu yan uwa kamar yadda Sakina tai mu ma muna kokari wajen yi domin gina jikin mu da na yaran mu.* Ta na kammala kayan karyawan ta shirya su tsaf a kan dainin gwani sha'awa, sannan ta nufi toilet tai wanka ta na fitowa kennan sai ga Faruq ya shigo ya na fadin, "Matar Aljannah me a ka girka mana ne gidan ya cika da kamshine?" Murmushi Sakina tai tare da wuce sa ta na fadin, "Za ka gani ai." Faruq ya janyota cikin sa ya na fadin, "To baza afadamin ba kennan sai na gani." Girgiza kai kawai Sakina tai tare da fadin, "Morning Honey." Sai da ya ma ta wani k'ayataccen kiss sannan ya ce, "Morning Darling mie fatan kin tashi lafiya." "Ni ban tashi Lafiya ba domin na kwana cike da kewar mijina."cewar Sakina. Faruq ya tallafo fuskarta garesa tare da fadin, "Ni ma nasan da hakan amman yau kam ai sai kin gaji da ni dan ba inda zani domin nima nayi kewarki sosai." Sakina ta ce, "Uhumm uumm Ni fa yau ina so inje in bude shagona ka ga fa nafi wata banje ba tunda dai abin da ya hanani zuwan ya tafi ai sai inkoma." Faruq ya ce, "To a ka ce Miki wani Babyn ba zai zo bane? to ki ma sani ya hanya ehee, yau dai a min alfarma sai gobe ma fita gaba daya." Sakina ta ce, "Uhimm to nikam kira Safiya muci abincin bara nasa kaya." Faruq ya tafi ya na murmushi. Safiya kuwa kaman jiran kiris take tuni ta fito tana wani rangwada. rikye ma Faruq hannu tai suna tafiya har dakin Sakina. shigar Kananun kaya Sakina tai wanda inka ganta zakace dan ita akayi ko, ko ajikinta aka dinka domin kuwa sun matukar ma ta kyau. Safiya na ganinta jikinta ya yi sanyi Faruq kuwa bai san lokacin da ya bige hannun Safiya a na shi ba ya nufi.......... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:18] Shalelen Mamata🥳🥳: https://chat.whatsapp.com/CKMOcEDk0a6AqOB4Y2k4Jm *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-21/22* ________________________________________________________ *CIKIYA🗣️🗣️DAN ALLAH MUNA NEMAN SHAFUKAN LITTAFIN MAI SUNA YAYA IMRAN WANDA MU KA FARA NIDA FATIMA ZAHRA EYMAN MUN RASA WAYOYIN KUMA MUN RASA FEJIS DIN INDA MAI SHI PLS TA TURO MANA MUNA SO MUKARASA INAGA DAGA 1 ZUWA 12KO 13 MU KA TSAYA👏👏* *WANNAN SHAFIN NAKINE KE DAYA JIDDATYY TA GRP DIN IMAAN CASTLE KI YI YADDA KI KESO DASHI SHARHIN NA SANI NISHADI* Nufi inda Sakina take janyota ya yi jikinsa tare da fadin, "Sweetheart kin san yadda ki ka yi kyau kuwa." Murmushi Sakina ta yi tare da fadin, "Ban sani ba kuma bana fatan sani indai nama wanda na yi dan shi." Faruq ya ce, "Madalla da mace ta gari yanzu dai azubamin abincin nan na ci domin hanjin jikina sunfara motsi." Dariya Sakina tai tare da fadin, "Ai kuwa naga alama tunda ga Safiya ma ta kasa magana." Wani mummunan kallo Safiya tai ma ta,,ita kuwa Sakina Murmushi ta sake ma ta mai nunin cewa ba ta ga komai ba. Ababban faranti Sakina ta zuba mu su doyar dukan su sannan ta sa miyar a karamin boll,, tean kuwa ta zubawa kowa nasa. Faruq ya fara shafa ciki tare da fadin, "Ni har kamshin ma ya fara kosar da ni, gwanda muyi muci kar ciki ya koshi baki bai koshi." Dariya sukai su biyun ban da Safiya wadda tuni ta hasala da kaganta zaka fahimci akwai wa ni abu aranta. Faruq ya lura da hakan amman ya basar. Faracin abincin ya yi tare da fadin to , "Duk wadda ta riga bude baki ita zan bawa." Da gangan Sakina ta yi jinkirin budewa domin ya ba Safiya ai kuwa take Safiya ta washe ya ba ta. "Umm umm to nima ka tsaya in ba ka mana." cewar Safiya. Murmushi Faruq ya yi tare da bude bakin sa, Ta ba sa. Faruq ya ce, "Yauwa matar kirki ke da bakya son cin abinci ma dole yau inyi feeding din ki da kai na." Sakina ta ce, "umm Honey zanci kabarni kawai." Faruq ya ce, "Aa."tare da kara janyota jikin sa, ya rada ma ta magana akunne, wanda ni kai na banji ba sai dariyar su da ke tashi. Tuni Safiya ta tashi tare da fadin, "Nikam na koshi inka gama ina so zamuyi magana." sai da tama Sakina wani irin kallo sannan ta fice. Faruq ko, ko ajikinsa dan ko amsa ma bai bata ba ya ce, "Darling kinga bude bakin ko sai na bude miki da kai na ne?" Sakina ta bige ma sa hannu tare da fadin, "umm ni na bude." Ya ba ta ta ci chokaki 3sannan ta ce, "umm nikam nakoshi tsaya mu yi magana." Faruq ya ce, "ba wani magana sai kinci kin koshi." Sakina ta shagwabe tare da fadin, "umm umm Allah amai zanyi kabari zan sha tean kawai." Ya ce, "Owk Madam to yanzu wace maganace." Sakina tai murmushi sannan ta ce, "Ka yi hakuri da duk abinda zance karage zakyewarka akaj na indai Safiya na guri kaga bata jin dadi kuma hakan bai kamata ba." Faruq ya ce, "Amman dai kin san ina iyaka bakin kokari na ko kuma naga ai dukanku din matanane jiya ma fa...... Sakina ta rufe ma sa baki tare da fadin, "Umm ni karka fadamin komai nidai kawai ka yi kokarin kiyaye abinda na ce." Murmushi Faruq ya yi tare da fadin,"Matar kirki matar aljanna ina sonki Sakina ta ina alfahari da ke dabi'unki suna birgeni, Ki yafemin pls." Sakina ta sauke ma sa hannunsa kasa tare da fadin, "Ni bakamin komai ba, ina sonka mijina." Faruq ya ce, "To yanzu mekikeso in miki?" Sakina ta shagwabe ta ce, "Umm ni ka goyani to." Faruq ya ce, "Laa ashema so kike in balle." Sakina ta kara shagwabewa kamar zatai kuka. Faruq ya ce, "Haba gimbiyata miye na kuka ku ma wasa na ke miki fa ai yau har abin da ya fi goyama zan miki." Sakina ta ce, "To muje." Daukan ta ya yi chak sunata dariya .... Safiya kuwa tunda taje daki ta kasa tsaye ta kasa zaune Zuciyarta kamar zata fashe dan takaici daga karshe dai ta kira maman ta awaya. , "Mama ni wallahi na gaji haba dan Allah wai inyana gaban waccer munafukar sai ya manta dani kamar an ajiye dusa ni wallahi bazsn iya ba nagaji duk abin da namai da yaganta sai ya manta."cewar Safiya Mama ta ce, "Da Sauranki Safiya kin manta abinda kika fadamin jiyane wai? ai dole sai kinyi hakuri kin nuna ma su soyayya dukan su hakan ne kawai mafita, wai ma bai taka alayar nan ba ne?" Safiya ta ce, "Ina fa tunda ta makyalesa adaki ai inaga ko kofar gidan ma ba ya je ba." Mama ta ce, "Oh nikam ko ya zanyi da wannan mayyar ne oho kuma fa kinsan ya ce inya kwana biyu ko antaka ba zsi yi aiki ba, amman karki damu anjima zanzo miki da wani sirrin." Safiya ta ce, "Owk ni ina son zuws kasuwa ma dole zsn yi siyayyan kanun kaya dan naga alamar so ta ke ta kereni da yawa." Mama ta ce, "ki bar wannan ma aguna zan siyo mi ki fitattiu ban so kije ko ina gwanda ki zauna agidan. Safiya ta ce, "Yauwa Mamana byebye sai kinzo." ****Afannin su Sakina kuwa.. *Yawan comments yawan typing🤷‍♀️* Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:18] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-23/24* ________________________________________________________ *SADAUKARWA GAREKI MY FIRDAUSI KI YI YADDA KI KESO DA SHI I REALLY LYK UR LVLY CMMTS🥰🥰* Ta na nan tana farantawa mijinta rai. A na cikin haka sai ga SUBAI'ATU ta kirasa awaya *Matar sa da ke niger* Kallo daya ya ma wayar ya kauda kai,, Sakina kuwa ta janyo wayar tare da mik'a ma sa ta na, "Suby ce fa ka dauka kasan bazataji dadi ba in ba ka dauka ba.' Murmushi Ya yi ya amsa tare da sa ta Free. Sallama Subai"atu tai ma sa tare geshesa. Ya Amsa tare da fadin, "Fatan ki na lafiya?" Ta ce, "Lafiya lau ya jikin Anty Sakinan?" Faruq ya kalli Sakina tare da fadin, "Ga ta nan ta ware." Sakina ta ce, "Subyna na ware fatan kema kina lafiya." SUBAI"ATU ta ce, "Lafiya lau Anty yaushe za ki biyo Yaya ku zo?" Sakina tai Murmushi sannan ta ce, "Na kusa insha Allah subyna." Da haka sukai sallama. Sakina ta ce wa Faruq, "Gaskiya Suby na birgeni Wallahi kwata-kwata ba ta da damuwa." Faruq ya ce, "Sose ma Wallahi ai yarinyar ta huta a bin ta." ***** Maman Safiya na zuwa fuuu ta huce dakin yar ta, ta na zuwa kuwa Safiya ta taso da gudu ta rungumeta sannan su ka baje kolin su. Maganin Mama ta fara cirowa tare da fadin, "Fatan dai yau a dakin ki ya ke?" Safiya ta ce, "Eh." Mama ta ce, "Yauwa wannan a cikin abinci za ki sa ma sa,, ga kuma ka yayyakin nan kala biyar ne ki zabi wanda za ki sa yau, ko ma in zaba mi ki wannan." ta dago wa ta yar shafa-shafa riga iya gwiwa da wani dogon wando. Safiya ta ce, "Yesss Uwar kirki haka za ayi to amman maganin nan kennan a abincin sa shi kadai zan sa ko?" Mama ta ce, "Eh shi kadai ma na, wai ma ya naji gidan tsit ne ina su ke da munafukar matarsa." Safiya ta ce, "Hmm ai yau Su na d'aki tun safe ko kofa ba su fito ba." ta karasa maganar ta na tabe baki." Mama ta ce, "Ke kuma ki ka bar su? to ma za ta shi muje sai ka ce ba ma ce ba, bazaki fita ki shiga da makirci ba." Tare su ka fita, dai-dai kofar d'akin Sakina su ka tsaya Mama ta ce, "Yauwa bari kiga." Kwankwasa kofar ta fara da karfi. Faruq ya ce, "Wa ye." Mama ta ce, "Ni ce." Ya zo yana budewa ya ga Safiya da Maman ta. Mama ta ce, "Umm daman na ga nazo ne ba mu gaisa ba na ce bara in ma magana, Faruq ya durkusa ya gesheta tare da fadin , "To ku shigo mana." Safiya na ja da baya Mama ko na jan ta. Sakina na ganin su gabanta ya fadi, ka sa hada ido tai da Mama kan ta a kasa ta gesheta. Dan gulma da Murmushin ta, ta amsa tare da fadin, " 'Ya ta ya jikin na ki dai." Sakina ta ce, "Da Sauki Sose Mama ." "Alhamdullillah." cewar Mama. Faruq kuwa ya shige ciki kawai ba dan zuciyarsa ta so ba, Mama da Safiyane kadai su ke ta hira Sakina kuwa ta kasa sakewa sai wasa take da yan yatsunta kawai, Su na ta gulmarta da ido. Sakina ta tashi zata dauko mu su sallaya su yi sallah Mama ta tashi ta shiga kicin ta dibo mangyada ta zubo a kofar dakin. Safiya za tai magana Mama ta ma ta alamar tai shiru. Sakina kuwa da saurin ta za ta ba su ai sai jinta tai tim a kasa ta sule. Mama ta kasa rikye muguntarta sai da tai dariya sannan ta zo suka dagata. Da Sauri Faruq ya fito ya karbi abarsa tare da fadin, "Sannu Sakina mi ye ya yarda ke haka? fatan dai ba kiji ciwo ba ko?." Murmushi tai tare da fadin, "Ina ga mangyada ban san ta ya yazo kofar dakin ba wallahi,, Smile banji ciwon komai ba." Ta tashi ta na Mama ga sallayar bara nayi mopin din wajen. Faruq ya koma domin shima ya dauro alwala, su Mama da Safiya kuwa su kai Adakin. Mama ta na kintsawa Safiya, "Amman gaskiya Yaron nan bai da kunya agabana zai dauki matar tasa." Faruq ya fito za shi massallaci ya ce da Mama, "Zani masallaci na ce ko zaki zo in karasa da ke gida." Mama ta ce, "Aa nagode jeka abin ka kawai." Faruq ya ce, "Da dai kinzo na Kai ki dan yanzu anguwar nan in yamma ta yi ba aciki fita ba domin yan daba sunyi yawa." Ba abinda Mama ta ke tsoro kamar yan daba dan haka tuni ta ce, "Ah mu je kawai banci ta zama ba, Safiya ma yi waya ko?" Su ka fita tare da Faruq. Mama na tafiya Safiya ta tafi bangarenta domin yin girkin dare kamar yadda mamanta ta bukata. Ta gama tsaf sannan tayi wanka tasa kanun kaya. Da kaganta zakasan ba sabanba domin rawa ma take acikin kayan ya tafi ma ta wani zulum ba kyan ga ni, bai bi jikinta ba ko kadan bare ma ko ya bi bazai ma ta kyau ba domin single ta ke. Tana jin shigowar Faruq ta kara kintswa domin ita gani take yau tayi wankan kece raini. Sai da Faruq ya shiga dakin Sakina ya kirata sannan su ka nufi bangaren Safiya. Ta na jin su ta tawo da rangwada tare da shagwabe fuska. Suman tsaye Sakina tai shiko Faruq bai san lokacin da dariya ta subuce ma sa ba. Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:19] Shalelen Mamata🥳🥳: https://chat.whatsapp.com/CKMOcEDk0a6AqOB4Y2k4Jm *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ FOLLOW ME ON WATTPAD AishaMuhammad958 *PAGE-25/26* ________________________________________________________ _~SADAUKARWA GAREKU YAN GROUP DINA XAYYEESHERTH FANS GROUP INA YIN KU IRIN SOSE DINNAN🥰🥰🥰~_ Safiya ta tsaya jim ta kasa ma motsi gannin dariyar da Faruq ya ke hadda faduwa kasa. Sakina ta karaso gareta tare da fadin, "Safiya ai da kin ba da anrage mi ki kayan." Safiya ta galla ma ta harara tare da fadin, "Ni haka nakeso naga kema ai haka kikesa naki." Ta karasa gaban Faruq tare da fadin, "Sweety banyi kyauu ba ne naga kana dariya?" Faruq ya kara kyalkalewa da dariya ai tuni Safiya ta shige cikin daki ta na kuka. Sakina ta ce, "Haba Honey wannan bai kamata, kamata yayi ace ka gyara ma ta ba wai kafara dariya ba ka ga fa ta tafi tana kuka." Faruq na dariya ya ce, "To ni ina ma dariya za ta barni ne ina ganin abu kamar silindar gas." Sakina ta ce, "Ya isa yanzu dai jeka fito da ita muci abinci danni yunwa na ke ji wallahi." Faruq ya ce, "Owk ki zauna ina zuwa." Ya na shiga ya ga Safiya ta kafa kai banda kuka ba abinda ta ke. Faruq ya ce, "Ah my slinda baby mi ye na kuka kuma kyan da ki kayi ne fa yasani dariya bana so sakina ta gane ne." Da Sauri Safiya ta dago tare da fadin, "Da gaske?" Faruq dai ya yi kokari wajen kintse dariyar sa tare da fadin, "Eh Sosai ma ki zo muci abincin ko?" Safiya ta tashi hadda kara gyarawa kayan zama ajikinta ta fara wata sabuwar rangwadar tare da rikyewa Faruq hannu Su ka fito. Sakina ta na ganin su ta kawar da kai domin inta cigaba da kallo itama zata iya kwashewa da dariyar da ta fi wadda Faruq ya yi ma. Faruq kuwa murmushin dole ya ke wanda dariyar ke shirin kara subuce ma sa. Suna zama safiya ta ce, "Eheen yau plate din ka daban namu daban." Faruq ya yi murmushi tare da fadin, "An wareni kennan wariyar launin fata to shikennan azubamin nawa na ci ni daya tunda an maidani marayan dole." Sakina tai murmushi tare da murguda ma sa baki sannan ta ce, "E in ba zai dai kaci da mu ba." Faruq ya ce, "Hhhhhh yarinya zan kamaki ne." Safiya ta ce, "Oyaa ga naka muma ga namu. " Faruq zai fara ci kennan a ka kirasa awaya ya tashi ya na fadin, "Ina zuwa bara na amsa waya saura kuma ku cinyemin nama na." Dukan su su ka masa dariya kawai. Ran Safiya dai bai so ba domin burinta kawai ace Faruq ya ci maganin nan.. Sakina da Safiya kuwa suka fara cin na mu, abincin dai ba dadi kamar anwanke kan mahauukaci taliyace da tea tare farfesun kan rago, taliyar gabadaya ta jagwale, farfesun ku wa banda karni ba abinda ya ke. Dakyar Sakina ta ke cin abincin nan wandA ta ci ma shirin dawowa ya ke amman ta na ta karawa kardai Safiya ta ji ba da di. Ita kuwa sai rawar kai ta ke adole tayi girki mai dadi. "Sakina ai in fada ma ki nasha wahala a kan girkin nan shiyasa ya yi dadi har fa vedio na sa ina yi ina gani, hmmm Ashe daman ana wanke nama? ai ni ban ma sani ba sai yau shine fa na wanke sa ya fita kall." Sakina dai ta kasa magana kawai sai bin ta da Eh Eh ta ke. Faruq ya shigo da Murmushin ya na fadin, "Yauwa afara bani farfesuna in farfesa shi a ciki." Sakina ta ce, "Aa abincin dai ko oga?" Safiya ta ce, "Eh ma na adai fara cin abinci danni harma na koshi Sakina ko in kara mi ki ne?" Sakina ta ce, "Aa ni kam". Faruq ya zauna zai ci yana...... Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:19] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-27* ________________________________________________________ 🥰🥰```SADAUKARWA GAREKU YAN UWA GUDAN JINI 5STARS INDEED, FARIDA SWEERY,REAL NANA AISHA,HAUWA'U HAUPHA,MANAB YAR BABA TARE DA NI KAI NA XAYYEESHERTH WANNAN FEJIN NAMU NE MU YI YADDA MU KE SO DA SHI INA SON KU SO DOMIN ALLAH🥰🥰🥰INA ALFAHARHI DA KU❤️❤️❤️``` Sawa abaki ya tofar, suna hada Ido da Sakina ta girgiza ma Sa kai alamar yadaure ya ci. Ha ka kuwa Faruq ya ta turawa kamar zai yi amai bai fi chokali biyar ba ya fara shafa ciki yana, "Wallahi na koshi Safiya Amman fa girkin nan na ki ya yi dadi domin ya Sa cikina cika Amman ba ki na bai koshi ba." Wani dadi Safiya ta ji aranta domin ya ci kuma ya yaban ma ta girki ta ce, "Kar da mu ai gobw ni zan ma na kayan break." Sakina tai murmushi tare da duba agogo ta ce, "Nikam ma kunga barci ina ji sai da safen ku." ta karasa maganar ayayin da ta ke tashi. Faruq ya kalleta tare da fadin, "Ha ba dai tun yanzu Darling?" "Wallahi kuwa gudnyt oll".Cewar Sakina. Faruq ya taso tare da rikye ma ta hannu ya na "Oya muje in raka gimbiyata D'aki dan ko sauro ban so yatabamin ke." Murmushi kawai Sakina tai su ka fita tare. Suna fita Safiya tadau tsalle tare da kiran Mamarta ta sanar ma ta cewA Faruq ya ci abincin. Ba karamar Murna Maman Safiya tai ba domin burinta na tatile arzikin Faruq ya ku sa ciki. Sai da Faruq ya raka Sakina har da ki sannan su kai sallama yadawo dakin Safiya. Ashe wannan ranarce rana ta karshe da Faruq zai nunawa Sakina tsantar So Domin kuwa tun daga ranar rayuwar gidan Faruq ta sauya. Bai dai na son Sakina ba amman bai damu da ita ba kamar da Safiya kuwa ta fara samun abinda ta keso duk da dai ba hakan akaso ba domin Faruq ya kasa mallakuwa gabadaya. Maman Safiya ta kara komawa wajen malamai da dama amman kowa ce ma ta yake hakan ma da akayi ta gode domin Faruq tsayayen mutum ne ba kowa zai iya da shi ba. It kuwa Sakina komai zasuyi gabanta bata taba nuna damuwarta domin ta fahimci cewa da gaiya Safiya ke ma ta hakan. Ya kasance zaman gidan ma ba so SAKINA ta ke ba inta tafi shagonta tun safe sai biyar ta ke dawowa,,, Sakina ta fito za ta tafi Shago kasancewar Faruq A dakin Safiya ya ke ta je tai Nocking Da kyar Safiya ta fi to ta na wani gyatsine. Sakin Ta ce, "Morning Safiya da man ina so zan tafi shagone ina Ogan ya ke." Safiya ta ma ta wani kallon sama da kasa sannan ta ce, "Ya na barci inya tashi zan fada ma sa." ba ta bari Sakina ta ba ta amsa ba ta kulle kofar ta harda dan guntun tsaki. Sakina ta tsaya kusan na minti biyar Sannan ta nufi hanyar shagonta. Safiya kuwa ta na shiga ta fara kuka tare da tashin Faruq ta na,"..... Urs Xayyeesherth [11/08 à 06:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-28/29* ________________________________________________________ "Ka tashi wallahi ni bazan yarda ba kullum shiga da fitan kayan da matar nan ta ke daban kuma ma su tsada da angani za'a fahimci hakan,sannan nasan ba wanda zai siya ma ta face kai, to wai ni ma ba mace ba ce ko ya wallahi bazan yarda ba." Ta kara fashewa da . Faruq ya ce, "Safiya ke kan ki kinsan dai Sakina tanada shagonta wanda shi kan sa shagon ba ko biyar di ta aciki bare kuma kayan sawan ta." "Karya ka ke wallahi abin da sun riga sun gama mallakeka ai dole ka ce min haka kuma wallahi bazata sabu ba ni dai." cewar Safiya kennan tare da guntun hawayenta na munafurci. Faruq ya ce, "Shikennan dai bari Sakinan ta dawo kin san ba na son tashin hankalin nan na ki." Safiya tai dariya tare da fadin, "Ummm wai ma kasan da tazo tafiya fa nace ma ta, ta tsaya in tasheka ta ma sallama ta wani gwalalo ido tare da fadin ina ai ni sauri na ke inya tashi kya fada ma sa." Faruq da mamaki ya ce, "Sakinar?" Safiya ta ce, "kwarai ma kuwa nayi-nayi ta zauna ta jiraka amman ta ki fir daga karshema tsaki ta min ta fice abin ta." Faruq na tantamar hakan azuciyarsa amman wani gefen kuma natabbatar ma sa da maganar Safiya. Daga nan Faruq ya shirya ya yi wanka sannan shima ya tafi aiki. ******Kamar yadda su ka saba Misalin Karfe biyar Faruq ke zuwa dauko Sakina ashago yayin shima ya tashi a aiki domin su koma tare, Sakina ta na ankare da lokacin da taga lokacin zuwansa ya yi kara gyara kwalliyarta tai tare da feshe jikin da turare. Yau ba kamar kullum domin kuwa duk tsiya ya kan zo da fara'a amman yau fuskarsa a murtike ba alamar walwala. Tun daga nan jikin Sakina ya yi Sanyi tare da fadin, "Ina hini." Ya amsa ya na fadin, "Ki kulle mutafi ,batare da ya kalli inda ta ke ba ma bare ya ma ta kyakkyawan kallO. To kawai Sakina ta ce jiki asanyaye ta rufe shagon ban da Addu'ah ba abin da ta ke cikin zuciyarta. Ya kan bude ma ta kofa da kansa amman yau kam ko ajikinsa ya je ya zauna kawai. Ta na zuwa ta bude ta shige Ciki. Haka akai tafiyar nan batare da kowa ya ce kalla ba. Ita dai Sakina Addu'ar ta tacigaba da yi domin za ta iya cewa bata taba ganin Faruq a irin yanayi na fushi kamar yau ba. A haka har su ka isa gida, Ya na gama Fakin ya ce, "Ki zo dakin Safiya ina nemanki." Sai da gaban Sakina ya fadi, ta na shiga dakinta ta ajiye jakarta sannan ta nufi dakin Safiya. Ta na shiga taga Safiya tsamo tsamo a kan cinyar Faruq suna ta washe baki. Faruq na ganinta ya murtike fuska Safiya kuwa kara jan sa da wasa ma ta ke. Faruq ya ce, "Safiya Stop it tsaya mu yi magana incire abin da ke rai na." Sakina dai ta zauna shiru kanta a kasa. Faruq ya ce, "Sakina! abin nan na ki ya isheni haka wato kin bijiro da sa kayayyaka kala daban-daban domin ki sa Safiya zargin ni ke siya mi ki? nagaji na fada mi ki nagaji ki kiyayeni wallahi daga yau indai kaya ba ni nasiyo mu ku kalla daya ba ko na akwatin ki to karki kuskura ki kara sa wani daban sannan kuma wa to da safe yanZu kin fi karfin kizo ki gaidani mu yi sallama ko? ana ki Zo ki na Aa shago ya fini mahimmanci." Girgiza kai kawai Sakina ke yi domin ta ma rasa ta cewa. Safiya ta ce, "Ni fa ban yarda ba in ma drama ku ka shirya ni dai kawai asiyamin irin rigar jikin tan nan ehee." Faruq ya ce, "Haba My dear karki damu wadda ta fita ma gobe zan siya mi ki." Safiya tai wani murmushi wanda ba wanda yasan fassararshi illa ita da Ubangiji. Faruq ya kara da cewa, "Ki tafi kawai ki kulle kofa danni ba zuwa dakin ki zanyi ba tunda ban da amfani." Safiya ta ma Sakina gwalo. Sakina ta tashi za ta tafi sai ta dawo tare da fadin, "......... Urs Xayyeesherth [11/08 à 06:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-30* ________________________________________________________ _*SLINDA BABY🤣INJI YAN GRP DINA,,TO NIMA NA DANA SAURA KUMA AFADAWA SAFIYA😅*_ Faruq, "Ina ga dai ko me zan ma bai ci ace zaka gujeni ba, bayan kasan cewa yau a d'akina ka ke." Tsawa ya ma ta tare da fadin, "Na ce mi ki bazan zo ba din ko kin isa kimin dole ne? Iye? Sai ka CE wata mayya to na ki zuwan." Haka Sakina tafita jiki asanyaya zuciya na kuna, Safiya Ku wa Dadi ya mamaye ma ta zuciya da sauri ta riko hannun Faruq tare da fadin, "Haba darling Mie kabar damuwa ka rabu ita taje chan da rashin kunyarta ni zan faranta ma ai." Faruq ya yi murmushi tare da fadin, "Gaskiya ban kyauta bara naje na bata hakuri kar hukuncin ya ma ta yawa." Tuni Safiya ta fara kukan munafurci tare da fadin, "Haba Dan Allah ni ni fa? Ka tsaya nidai kuma ma fa yanzu inkaje za ta iyama komai tinda ran ta ya baci, ni karka je a kara bata min ranka." Faruq ya ce, "Ku ma fa hakan Safiya kin yi tinani mai kyau barta kawai muje muyi sallah mu sha tea kawai." ****Sakina kuwa ta na komawa daki tai alwala tai sallah ta yi karatun littafi mai girma kamar yadda ta saba, nan da nan ta ji ya kore ma ta damuwar da ke ranta, kasancewar ta na jin jikinta wani iri ga yar yunwar da takeji hakan ya Sa itama ta sha tea. Sai da ta kara gyara dakin ta tsaf sannan ta kwanta domin barci. Addu'a tai tashafe dukkan jikinta da ita sannan ta fara barcin ta cikin nishadi,Misalin karfe 1nadare kamar amafarki ta ji wani abu na taso Ma ta da sauri ta farka taji wani irin Amai. Dagudu tanufi toilet tin da taje ta ke kwarara Amai gabadaya jikin ta ya mutu ba kwari domin tin tana amaryar da abin da ta ci har ya kai ga tafara A man zallan ruwa. Jan jiki ta yi dakyar ta karasa kofar d'akin ta bude sannan ta je saitin na Safiya tana bugawa, Faruq ya yi Nisan barci sose ita kuwa Safiya na jin Maganar Sakina akasale ko ajikin ta. Tun tana da karfin bugawa har ta gaji ta daina alokacin Allah ya kawo ma ta wani irin barci ya yi gaba da ita. Da asuba Faruq ya fito za shi masjininsa. kawai me zai gani banda Sakina kwance barci take Amman da kaganta zakasan cewa ba ta cikin koshin lafiya. Dago ta yayi yana. 'Sakina me ke faruwa tashi ki fadamin kar dai abin da na mi ki jiya ne." Bude idon da Sakina zatayi sai ta ganta ahanun Faruq , "Magana kasa-kasa ta ke fadin banda lafiya tun jiya da daddare na ke tashin Ku Amman ba Ku tashi ba." Faruq ya ma kasa kara magana kawai daukan ta yayi ya kai ta dakin ta sannan ya kira likita. Ita kuwa Safiya ta na daki tana jin duk abin da ke faruwa tai tsit. Likita naxuwa ya duba Sakina tare da ma Faruq albishir cewa wani cikin gareta. Ba karamin farinciki Faruq ya yi ba domin bai da burin da ya huce ya ga jininsa. Safiya na labe tana jin hakan ta cije baki tare da komawa daki da sauri, Maman ta takira awaya tana fadin, "Mama wallahi bazan Yarda ba sai anzub da wannan ma kamar dayan indai INA gidannan ba Sakina ba haihuwa in ba wai ninafara ba." Mama ta ce, "Kai Safiya ni Wallahi ma har kin bani tsoro dai a kan wannan karamin case din za ki na tada jijiyoyin wuyan ki? To ma za Ina so kizo gida yanzu ki sameni." Ko wanka Safiya ba tai ba taje dakin Sakina tana, "Faruq Mamana ta na kirana bara naje." Faruq ya ce, "Haba Safiya bakiga wai Sakina ba lafiya ba ne ke da yakamata ki zauna da ita." Hararsa ta yi tare da fadin, "Yo to tafi uwata CE? Ni fa kagani na tafi." Fita tai batare da ta bari ya bata amsa ba. Faruq ya CE.... Urs Xayyeesherth [11/08 à 06:16] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-31/32* ________________________________________________________ *_Daga yau zan ajiye typing sai Allah ya kai mu bayan sallah,kar amanta dani arabon Neman hilis🤣amman fa ni naman saniya Ina so_* _wannan fejin na Ku ne,,Yan GRP dina Rukkayya Fulani,Ummu Nana, Aysher shu'aibu,Ummu khairat,,Ummukausar,,Er Hajja,Waya, Hauwa Alhaji Muhammad,,Rabaha,Maman Shukhra,Nafy mudangi,Rahima Adam,da ma sauran oll INA son Ku INA jin dadin sharhin Ku a ajiyemin naman Sallah na😘😘😘_ "Hmm Allah dai yakyauta." Sakina tai Mumurshi tare da fadin, "Ai da gaskiyarta kuma ma ni naji karfi zan Iya komai." Faruq ya CE, "Allah ya Sa nidai yanzu babban burina bai huce ace Kin Sauka lafiya ba." Sakina ta CE, "Karka da mu bakomai insha Allah." Nan Faruq ya hini agida ya na jinyar matarsa ya kira Maryam ta Dan tayasa wasu abubuwan. **Safiya na zuwa ta farama mamanta kuka tana, "Mama anya ni INA haihuwar nan kuwa? Ki ga Sakina fa ciki na biyu Kennan to ni wai me ke faruwa da ni ne?" Mama ta janyo yarta ta zaunar da ita gefenta sannan ta ce, "Haba Safiya ta me ya kawo wannan tunanin? To ma tsaya wai kin manta da ajiyar mu na karkashin gadonta ne? Ai indai abin nan ya na gun to Sakina ba ta isa ta dau ciki har ya zauna ba ko ya fara zama muna nan da ke jikin nan zai zube kamar na farkon." "Oh natuna Ai ni da hankalina ya tashine Wallahi, to Mama a yi tawa maganar wai ba Yarda xa ayi in sami cikin nan ne?" Cewar Safiya. Mama tai murmushi tana, "Wannan kam ba abin da muka isa mu yi illa Addu'ah Allahn da ya ba ta shi zai baki." Safiya ta ce, "Umm to ni kam Gaskiya Adage da Addu'ar nan Dan na matsu." Mama ta ce, "Iyeee Safiya ni kike fadawa hakan ko kunya." Safiya ta rufe fuska tare da fadin, "Umm to ni kam Ai Mama na matsu ne." "Umm to karkiji komai diyar kirki nakusa samu yar jika." Cewar Mama. Safiya ta ce, "Mama to bara nakoma gidan mukwashi kallo zan kiraki duk yadda akai ma." Mama ta ce, "Owk ki kula ma yi wayar." Safiya ta koma gida ta tarar da Faruq sai nan-nan yake da Sakina. Abin ba karamin takaici ya ba ta ba Amman ta barsar domin tasan abin da ta kulla. A kwana atashi cikin Sakina ya na cikin wata na uku. Kullum acikin tashin hankali Safiya ta ke da Mamanta domin sun koma wajen boka yatabbatar mu su cewa wannan abun fa ya na nan kuma ba by shakka ko da cikin Sakina ya kai wata Tara sai ya zube muddin abun bai bar mazaunin Sa ba. Duk da bayanin da bakon na su ya mu su bai ishesu ba domin sai da su ka cigaba da bin wasu bokayen Wanda duk sukance ai abin ya fi karfin su ba abin da suka isa suma Sakina. Hakan ya Sa Safiya kudiri niyar zubda ma ta cikin da kanta. Ta yi girkin dare miyar Ayayo sai da ta bari kowa ya shige daki kan taje dai-dai kofar dakin Sakina ta zuba bayan ta gama zubawa ta na sauri za ta koma kar a gan ta kawai sai gashi ta sule. Da Sauri Faruq da Sakina su ka fito su ka dagata ban da kuka ba abin da Safiya ke yi tana fadin, "Nazo zan duba jikin Safiyane sannan in huce in zubar shine ya zube santsin ya yardani." Sai da ya kai ga Safiya ta yi targade akafarta da kyar ta ke Iya tafiya hakan yasa ta hakuri da duk wata mugunta ta zubawa sarautar Allah ido. Wa ta ranar jumma'ah Faruq da Sakina sun fito za ta tafi shago shi kuma xa shi gun aiki. Zuwanta kofar gida ke wuya ta fadi kasa....... Urs Xayyeeesherth [11/08 à 06:17] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-32* ________________________________________________________ _*Appy sallah my piple INA jiran nama dai har yanzu shiru inji slinda baby*😋😋_ Jinine kawai ya bara zubowa da ga jikin Sakina. Faruq ya gigice ya rasa inda zai Sa ransa tuni ya dauketa su ka koma cikin gida Sannan ya kira likitansu. Kamar yadda akai abaya dai cikin Sakina ya zube, ban da kuka ba abin da ta ke yi haka ma Faruq Wanda ya ka Sa jurewa,, Safiya kuwa na daki ban da murna ba abin da take ta kira mahaifiyarta sai shewa su ke. Ha ka Sakina ta cigaba da fuskantar kaddarar Aurenta domin kuwa ta na yin ciki ba ya zama ya ke ficewa. Safiya kuwa ansami abin yi ta fadawa Faruq cewa ai Sakina CE ke zub da cikin da kan ta domin ta ce ita bazata taba hada zuri'ah da dangin da ba Sa kaunarta ba. Ba karamin bacin rai Faruq ya yi ba da jin wannan kalaman. Atakai ya je ya cima Sakina mutumci zagi ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba. Sakina kuwa ta kasa magana ban da hawaye ba abin da ke fitowa Daga idanunta Dan takaici. "Ki yi ta hawayen munafurci daman ai kin saba kije chan nikam dai Daga yanzu in kin kara ganina dakin ki ma to wani babban dalili ya janyo hakan kije ki ta tsiyarki ni kam na fi karfin ki zanje gun wadda za ta so hada zuri'ah da ni." Cewar Faruq Ficewar Sa ya yi batare da ya kara kallonta ba ma bare ya saurareta. Tin daga Ranar Faruq ya bar shiga harkar Sakina gabadaya ko kofar dakin ta ba ya zuwa bare ya shiga ko abinci ne sai dai ta girka na ta ita daya ta ce inko cefane yakare sai dai Shida Safiya suje suyi a ajiye ma ta abakin kofa inta fito ta gani sai ta dauka. Ya kasancewa Sakina in ba Shagon ta za ta ba to fa indai ta na gida ban da kuka ba abin da ta ke yi shiyasa ta fi jin dadin tafiyanta ma yadda zata shiga mutane su Dan kawar ma ta da damuwarta. Duk wannan abin da ke faruwa Sakina ba ta taba fadawa kowa ba ko gida ta je aka ce me ke damunta ta kan yi murmushi ta ce bakomai, ta bar abin azuciyarta Wanda ya Sa banda zabga rama ba abin da ta ke Kullum cikin kunci ya kasance ma d gayya Safiya ke abu in ta ga Sakina. Har ta kai ga Safiya ta hana Faruq zuwa Niger wajen subai'atu. Hajiyan Faruq kuwa Abu yafara damunta domin kuwa Safiya ba sarara ma ta ta ke ba agaban ta take mulkinta son ranta a kan Faruq ko ta bukaci da ya ma ta Abu in Safiya ba ta Sa baki ba to fa bazai taba yi ba. *****Sakina ta fito tana sauri za ta tafi shago shi ga Faruq nan da Safiya, Faruq ya ce, "Ki ma koma ki zauna agida Dan baza a barmin gida ba kowa ba yanzu barayi sunyi yawa Dan haka indai zamu fita bazakina zuwa shago ba." Har Sakina ta koma daki sai ta fito. Ta ce, "Faruq ." Ya juyo ya kalleta . Ta kara da fadin, "A ganina duk irin wulakancin da Ku ke min ya isa ba sai kahanani sana'a ta ba Dan haka nikam na gaji kawai ka sawakemin na koma gida." Wani irin da di Safiya ta ji aranta. Faruq kuwa sai da zuciyarsa ta fara bugun Tara ya ma kasa magana. Safiya ta ce, "Sweetie ka ma ta abin da take so ma na nikam mu tafi." Faruq ya ce, "Ai in kinga kin fita agidannan to na mutu ne Amman ba wai na sakeki ba.' Ya ja Safiya suka fita wanda Safiya ko kadan ba ta ji dadin hakan ba. Agurin Sakina ta durkusa ban da kuka ba abin da takeyi. Daga karshe dai ta yanke shawarar tafiya gidan su.... Urs Xayyeesherth❤️ [11/08 à 06:17] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-34* *_jiya na yi mistake page 33 ne na sa 32 duk da feddyna dai ta ce nama naci yamin yawa🤣* ________________________________________________________ _*Fejin nan sadaukarwa gareku en GRP dina Xayyeesherth fans GRP mussaman kawayen SLINDA BABY🤣Ina jin dadin Sharhin Ku acigaba da gashi,,CNT love u less😘*_ Tattara kayanta ta ke tana kuka, kayan sawanta kadai ta diba ta kulle kofar dakin ta sannan ta janyo kofar gidan ma. Ta ci sa'ar samun napep kuwa ta Dane sai gida. Ta na isa gida da kuka ta shige a bin da ya bawa Mama tsoro Kennan,,,, Maryam ma ko, ko tsayawa bai tai ba ganin yayarta na kuka tuni itama ta fara. Mama ta ce, "Me zan gani haka Sakina me ke faruwa ne wai? Sakinki Faruq din ya yi?" Sakina ta girgiza kai alamar Aa. Mama ta ce, "To Shikennan Ku shiga ciki." Aiko kamar yaya haiydar ya sani sai gashi ya zo. Mama ta ce, "jeka daki ka ga ikon Allah." Ba musu kuwa Haiydar ya yi dakin Mama inda ya tarar da Sakina ban da zubda kwalla ba abin da ta ke sai Maryam da ke ba ta hakurin itama tana kuka. Tsawa Ya yi Musu tare da fadin, "Dalla kuma mutane shiru kunbi kun cika ma na gida da ihu." Zama Ya yi tare da fadin, "Sakina! Kin fara fuskantar kalubali ko? Ba wai komai ya Sa na ki Auren nan na ki illa ina guje mi ki wulakanci da tozartar da za ki fuskanta, yanzu me ya hadaki da shi." Kan Sakina a kasa ta ce, "Yaya ni wallahi bana sonsa kawai ya sakeni ni na hakura da auren." Murmushi haiydar ya yi sannan ya ce, "Yau Ku ma Sakina ke kike bukatan Saki da kan ki! Ba ri Baba dai yadawo sai ki yi ma na bayanin komai." Daddare bayan Baba ya dawo kowa na falo Yaya Haiydar ya bukaci da Sakina ta yi mu su bayani kamar yadda tai ma Sa tare da dalilinta na fadin hakan. Magana ta ke ta na shshshekar Kuka irin wulakanci, tozarci da halin ko in kulan da Faruq ke nuna ma ta. A wajen ba Wanda bai tausaya ma ta ba, barin ma Mama da ta ke Uwa, abin ya fi taba ma ta zuciyata Wanda har sai da tai kwalla ga irin azabar da yar ta ke fuskanta agidan Aurenta. Yaya Haiydar ne ya fara fadin, "Yanzu duk wannan abun da ke faruwa ki ka Sa fadawa kowa kamar ba ki da gata? In Faruq na da laifi 70% to 30% na ki ne wallahi domin da kin fada, da tuni andauki matakin da yakamata Amman kin bijire ke an fada mi ki ana zaman Auren dole ne ma wai?" Girgiza kai kawai Sakina ta yi. Baba ya ce, "Ba ma wannan ba shin yanzun ya sakekine ko kuwa cewa ya yi ki dawo gidan?" Sakina ta ce, "Aa ni na tawo." Baba ya ce, "Owk Shikennan ai Haiydar Ku barsa in ba wai shi yanememu ba kar wani ya kara tada maganar ." Haiydar ya ce, "Insha Allah Baba Amman ni fa inma ya zo kawai takardarta zai ba ta domin ita ma ta na da gata ba zai yu ya maidata baiwarsa ba." Mama dai tana ji ta ma kasa magana kawai tausayama yarta ta ke ga irin yanayin da ta koma. Faruq kuwa suna dawowa gidan su ka tarar ba kowa ga dakin Sakina arufe bai San lokacin da ya fara zufa ba ya na fadin, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'u kar dai Sakina ta tafi gida, Safiya wallahi bazan iya rayuwa ba tare da Ina ganin Sakina ba, ki je ki dawo min da matata Dan Allah, Safiya ke muguwa CE ke ki ka rabani da Sakinata safi... Bai karasa maganar ba ya fadi a kasa warwar. Urs Xayyeesherth [11/08 à 06:17] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-35* ________________________________________________________ 💃🏻💃🏻💃🏻 *Xayyeesherth Fans GRP Ina matukar kaunarku yan GRP dina ma su sani farinciki da nishadi❤️❤️Mussamman masoyan slinda baby🤣kun ga dai tabarar da ta aikata awanga feji* Harara safiya ta bisa da ita taja dogon tsaki sannan ta dau waya ta kira likitansu. Dasauri kuwa likinta ya zo domin duba ubangidansa Faruq. Yana zuwa ya dubasa sannan ya ma sa allura kan ya tafi. Safiya ko, ko ajikinta sabgar gabanta tafara tare da kiran tsohon saurayinta gidan. Tabar Faruq dakinsa kwance ita ko tana nan adakinta tare da tsohon saurayinta. "Kai Baby ba karamin kewarki nai ba fa, yau jina nake cikin wani farinciki Mara misaltuwa domin na farinciki ya dade Da fita arayuwata Ashe akwai ranar har zaki tuna da ni har ki kirani? Humm." Cewar Adam Kennan saurayin Safiya da su ke cin duniyarsu. Safiya ta ce, "Hmm ni fa daurewa kawai na ke da wancen gajan ni wallahi son sa ma yafara fita akaina kwata-kwata bai iya soyayya ba bai ma San hanyar da zaibi ba." Dariya Adam ya yi tare da fadin, "Ki CE min da bagidaje ki ke tare yasin na tausayamiki No wonder ma na naga kin kara ramewa kamar bulugari." Safiya ta daka ma sa duka tare da fadin, "Banason iskanci Adam ni ce bulugarin ko?" Murmushi ya yi tare da fadin "Aa sorry babyna". Sakina ta ce, " Kasan miye?" Adam ya kara matsowa gareta tare da fadin, "Aa sai kin Fada." "Ni wallahi gabadaya yafara fitamin arai shiyasa na matsu matar nan ta sa tabar gidan Dan kana zuwa muna shanawa ka ga in ta na nan ba damar harka, Dan ba wai ma ni inason cin dukiyar ba ai da tuni na gaba indawo gareka, shi abin da nafi bukatan yaki zuwa (ciki) da nasan daga nan ne zan cigaba da mulkarsa son raina." Adam ya ce, "Aikin banza indai cikine ba sai kiyi na karya ba daga karshe muje gidan marayu arakito." Dariya Safiya ta yi tare da fadin, "Wannan ai ba mai yuhuwa ba ne kasan Waye Faruq kuwa? Da ya ma nayi hankalinsa ya fara karkatowa gareni, hmm ayi shiru kawai ni barci ma nakeji ." Hamma Adam ya fara yi tare da fadin, "Yau wani zai yi kwannan zaune." Dariya kawai Safiya tai. ********** Sakina na kwance banda tunina farko ba abin da ta ke ta kasa barci kwata-kwata, haka ta kwana cikin sake-sake. Washe gari da safe Faruq ya farka jiki dai kwari yana ta kwalla safiya kira ya ji shiru. Daga karshe dai ya rarrfa domin zuwa dakin. Kan ya isa yana ta jin dariyarta . Yana zuwa ya fara kwankwasa kofar Safiya na jinsa ta rikice Adam ko tuni ya kulle karkashin gado. Faruq ya ce, "Safiya ki budemjn mana." Safiya ta ce, "Kaje dakin ka Ina zuwa ma na." Da karfi kawai Faruq ya hankada kofar.... Yana shiga..... *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-36-37* ________________________________________________________ _*My Group Members Ina Matukar Alfahari da Ku Addu'o'in Ku gareni babban makamine a duk in da na ke🥰Allah yabarmin Ku masoyan Asali Son so na ke mu Ku fisabilillah Xayyeesherth ta Ku ce❤️❤️*_ Yana shiga yaga Safiya sai waige-waige ta ke yi. Faruq ya ce, "Dawa ki ke wayane naji kinata dariya?" Sosa kai Safiya ta fara tana fadin, "Wallahi Wallahi Mama CE Au Kawata Zainab zan ce." Faruq ya ce, "Anya akwai kamshin Gaskiya kuwa duk kin wani dibibice kin rikice to ni bama wannan ba wanka nakeso nayi kinga jikina ba kwari." Karasa maganar ya yi tare da nufar bakin gado domin ya zauna. Da Sauri Safiya ta taresa tana fadin, "Aa muje dakin ka in hadama ruwan ka yi ni hitata ta samu matsala ai dazu." Faruq ya ce, "Kai Safiya Amman baki kyautamin ba da kin fada ai naturo a gyara Amman muje chan din to." Safiya ta bi bayansa ta na ma sa gwalo tare da fadin, "Ai ma naga jikin na ka ya yi kyau muje." Tana raka Faruq ta hada ma sa ruwan wanka sannan ta yi sanda ta dawo dakinta domin fitar da Adam. Ta na zuwa kuwa ta tarar Zai fitan ma Kennan. "Yauwa munsha dakyar wancen gajan bai ganmu ba."cewar Safiya. Shi ko Adam Kiss kawai ya ma ta sannan ya ce, " Byee byee ni da fatan gobe ma akuma." Maganar ya ke ya yin da ya fita yana ma ta bankwana da hannu. Safiya ta ce, "Karkaji komai ai yanzu aka fara wasan." Dariya kawai ya bita da shi yayin da ta komo gida shi kuma ya tafi. Tana komawa ta tarar Faruq ya fito shagwabe Fuska tai tare da fadin, "Sweety kasan mi ye?" Girgiza kai kawai Faruq ya yi. Ta ce, "Ni Wallahi har ka fara bani tausayi ace wai kana son wadda ba ta damu da kai ba kwata-kwata ai ko da ace kullum Jajjagenta mu ke indai tana sonka to ba inda zata ka ga fa kahanata fita Amman da yake tana ji da girman kai shine ta fita inaga yanzu sun rasa abin yi ne anje gun bokayen an kasa mallakeka shine a ka tsiri barin gidan kuma." Faruq dai ya kasa magana sake-sake kawai ya ke yi wata zuciyar na tabbatar ma sa da cewa maganar Safiya gaskiyace wani bangaren kuma na fadin cewa Sakina ba za ta taba ma sa haka a son ranta ba. Safiya dai taga alamar har yanzu bai gama gamsuwa ba . Hakan yasa ta fara kukan munafurci tana fadin, "Ni da nake sonka na ke binka kamar mayya Amman kana wulakantani ita ko kana binta tana kinka ai Shikennan kata son na ta ni dama mutuwa na yi na huta nagaji ita da kakeso ai gashi kana ta ma ta ciki tana zubarwa ni kuwa kaki ko sau daya ma." Kara feshewa da kuka tayi tare da fadawa jikinsa. Tuni ta jagwal-gwala ma sa tunaninsa hankalinsa ya dawo gareta kawai. ***Misalin karfe 2 dai-dai Hajiyan Faruq ta nufo gidan domin likita yasanar da ita cewa Faruq ba lafiya. Afalon Safiya ta tsincesu Faruq na zaune safiya kuwa ta kwanta ajikinsa. Tana jin sallamar Hajiya ta kara k'ank'ame Faruq ba ta da alamar tashi bare ta amsa sallamarma. Hajiya na shigowa tai saroro ganin Faruq da Safiya ahaka. Faruq ne ya amsa tare da fadin" Ina kwana Hajiya." Ka sa amsawa tai tana fadin, "Me zan gani haka Faruq ko da anganni ba a tashi haka ba? Safiya ko gesuwa ma ban isheki ba ko?" Wata irin masifaffiyar harara Safiya ta gallawa Hajiya yayin da ta tashi ta yi wani hamshakin Tsaki sannan ta nufi daki tana fadin, "In ni ban hau jikinsa ba inaga ke kikeso ki hau jikin na sa ko ince ki auresa ma."ta shige daki abinta. Hawaye kawai ke zuba daga idanun Hajiya ta na fadin, " Lallai wannan shine halaccin da zaku min ke da mahaifiyarki ba laifinki ba ne nawa ne nagode." Ta dubi Faruq sannan ta kara fadin, "Ina Sakinar ta ke?" Faruq ya fara Sosa k'eya yana fadin, "Jiya ta tafi gidansu." Hajiya ta kasa fadin komai fita kawai tayi agidan tana kuka. Sakina..... Urs Xayyeesherth *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-38* ________________________________________________________ *_Xayyeesherth fans group Ku ji dadin Ku da wannan fejin na gode da addu'o'in Ku gareni🙏domin ku kadai nai wannan kuntun typing din❤️_* Sakina na zaune ta yi jigum ban da tunanin Faruq ba abin da ta ke aiyanawa aranta, Mama ce ta karaso garete ganin shirun ya ki ci ya ki cinyewa, "Haba Sakina me ya sa ki ke so ki kara jefa rayuwarki cikin wata ukubar? Na lura tin da ki ka zo gidan nan kin kasa sake ranki, to in baki sake anan ba ina zaki sake?" Murmushi Sakina tai tare da fadin, "A yi hakuri Mama insha Allah zan kiyaye." Mama ta ce, "Yauwa diyar kirki Dan nasan tunanin ki bai huce a kan Faruq, abin da ciwo ace kiri-kiri gidanka ya fi karfinka Amman karki damu Addu'ar nan dai da mu ke itace mafita sannan zan ba da sadaka ma domin a kara tayamu da Addu'Ah Dan ina da wata tantama akan Safiya Amman bakomai Allah ya fita kuma ya na gani." Murmushi ne kawai ya fara bayyana afuskar Sakina ta ce, "Nagode sosai Mama ke ce uwa ta gari wadda ko wa miji ke bukatar samun uwar 'ya'ya kamar ki, ina Alfahari da ke Mamana duk da irin son da ki ke mana hakan bai hanaki tsawatarwa garemu ba tare da nuna ma na hanya madai-daiciya, Allah ya bar min ke Mamana." Karasa maganar tai tare da kwanciya ajikin mahaifiyarta ta. *Wannan ita ce Uwa ta gari, mace tagari sannan kuma tauraruwar al'umma Allah ya ba mu ikon aikata alkairy tare nuna hanya ma fi kyau ga 'ya'yan mu har ma da na wasu....* *****Shigewa daki Faruq ya yi, Safiya ya tarar ta na kwalliya gaban mirror, Faruq ya ce, "Safiya ina za ki kuma bayan kin San ba isasshiyar Lafiya gareni ba, ba ma wannan ba yanzu abin da ki ka ma Hajiya ya kamata kennan?" Juyowa tai ta ma sa wani matsiyacin kallo tare da fadin, "Anguwa za Ni kuma baka isa ka hanani ba, sannan maganar Hajiya kuma ai Gaskiya na fada in son ka ta ke sai inbar ma ta kai ka Aura." Abin ya matukar batawa Faruq rai Amman ya ka sa magana ko miye dalilin hakan oho,, ji ya yi kawai ya fara jin haushin kan sa. Safiya kuwa ko ajikin ta kwalliyarta ta karasa sannan ta dauko wa Ni karamin mayafinta tana, "To malam ko saj na yi maganane za ka matsamin ahanyar?" Faruq kawai tsintar kan sa ya yi da matsa ma ta Amman ba Dan zuciyarsa na so ba. Kara ma sa kallon banza tai tare da fadin, "Sak'ago kawai." Ta yi ficewarta ba tare da ta kara waiwayarsa ba. A gurin kawai ya durkusa ya na kukan miye dalilin da ya sa Safiya za ta bakanta ma sa son ranta Amman ba zai iya budan baki ya yi magana ba. Gaba daya ji ya yi ya tsani kan sa domin kuwa ya rasa me ke damunsa ma. Safiya na fita kuwa tai wajen Adam su ka cigaba da sharholiyarsu, sai Misalin karfe Tara n dare ta dawo, Faruq na ganin ta maimakon ya fara ma ta fada Amman sai ya tsinci kan sa da ma ta barka da dawowa. To kallonsa ba tai ba ta nufi dakin ta ta kulle kofar. Washe gari, da sassafe Maman Sakina ta Tara malamai domin Sauka Wanda babama ya na chan ya Tara nasa ba tare da sanin ta ba. Sakina ta sake sose da jin irin nasihar da mahaifiyarta ta ma ta Amman abun da ya fi ba ta Mamaki shine wai Tun da ta dawo gida ko lek'ota ma Faruq ya kasa. Abangaren Faruq da Safiya kuwa... Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-39/40* ________________________________________________________ *Baby love tnx for d song😘😘i really like ita* *Ina ki ke Mrs Habeeb marubuciyar lauratu wannan fejin kacokan sadaukarwane agareki ki ba wa Wanda ki keso ya karanta Amman ban da Kawu atk😉* Ba magana harkarta ta ke yi domin kuwa ko abinci na ta daina girkawa kullum sai dai ya fita waje ya ne ma. Safiya sharholiyarta ta ke son ranta ba mai tanka ma ta. Hajiyan Faruq ta yi matukar nadama da danasani akan lamarin aminiyarta da diyarta , hakan ya sa fara bin malamai domin nemawa kan ta da 'Dan ta mafita. Rokon Allah ya ta shi gadan-gadan ko wa ni bangare kawai yi a ke. Safiya da uwarta kuwa sun cigaba da ma ka tsiyarsu da makircin su ba tsagaitawa kamar zigasu a ke. Washe gari Da sassafe Hajiyan Faruq ta nufo gidan, ta na zuwa kuwa ta tarar da Faruq tsaye atsakar gida ban da sake-sake ba abin da ya ke aransa. Hajiya ta ce, "Yauwa Faruq zo muje." Rik'o hannunsa tai ta na murmushi ba mu su ko Faruq ya bita. Ba inda su ka nufa sai gidansu Sakina. Jiki Asanyaye Hajiya ta shiga, shi ko Faruq tin da su ka je k'ofar gidan gabansa ban da faduwa ba abin da ya ke. Fitowa Sakina daga daki Kennan sai ga shigowarsu, saroro kawai Sakina ta yi ganin abin da ba tai tsammani ba, Faruq kuwa ya ma kasa magana ban da hawaye ba abin da ke zubowa daga idanunsa. Murmushi Mama tai tare da fadin, "Sannu dai Sakina ina Mama ta ki ta ke?" Sakina ta durkusa ta ce, "Ina kwana Hajiya, Ku shiga Suna ciki." Ta ma su alamar shiga falon da hannu. Ba karamin Mamaki Mama tai ba ganin Hajiyan Faruq da faruq murmushi tai tare ba su wajen zama Sannan ta sa Maryam ta kirawo Babansu. Bayan sun gama gaisawa ne Hajiya Faruq ta fara jawabi. "Dafarko dai ina mai ba Ku hakuri da dukkan lamarukan da su ka faru daga gareni da ma d'ana faruq, na gane kuskureni kuma na yi nadama ko ince wa inda na ke ta tsiyar Dan su, sun nunamin halarci na fahimci inda na dosa ba hanya ba" ce me fillewa, nuna faruq tai tacigaba da fadin, "Shi da na ke gadarar da shi anfara rabani da shi kamar yadda a ka rabasa da matarsa, Ku yafemu Ku gafarce ma na domin yanzu ma daga nan gida zan kai sa anata faman ma sa Sauka." Babane ya yi gyaran murya ta re da fadin, "To Alhamdulillah dai zan ce tin da yanzu kin gane kuskurenki kuma kin fahimta, Faruq kuwa shi ma sai dai mu CE Allah ya kara kiyayewa, Amman fa zan iya cewa da lafinsa adukkan abin da ke faruwa domin kuwa ya na wasa da ibada, Sannan kuma ya na biyewa makircin mace Wanda inkace za ka bi to bazaka taba ganin dai-dai ba arayuwarka domin makirar mace babbar illa ce ga al'umma, kin gan mu nan tin da Sakina ta dawo gida ba mu zauna ba kara dagewa mu ka wajen Addu'o'i da rokon Allah, Sauka kuwa ba fashi kullum sai anyita. Faruq dai na zaune kasak'e ban da hawaye ba abin da ke fita daga idanunsa ya na jin duka abin ake fada Amman ya ka sa koda magana daya ce. Hajiya ta ce, "Godiya na ke da fahimtar da Ku kai min Amman na ce Dan Allah ko Sakina zata koma gidan Faruq ba yan komai ya dai-daita? A taimaka Dan Allah, Dan yanzu ma nasan innace ya saki Safiya ba abin zai taburane na bari yadawo haiyacinsa." Baba ya ce, "To Maganar Gaskiya dai ban jin cewa Sakina za ta kara komawa gidan Faruq , Sannan kuma maganar ya saki matarsa ba ta ki bace, Fatan mu anan shine Allah ya yaye ma sa ita kuma Allah ya ganar da ita zuwa hanya madai-daiciya Maganar Sakina kam abarta Dan yanzu ma anfara maganar komawarta makaranta ne." Ba dai haka Hajiya ta so ba Amman haka tai godiya Sannan su ka tashi ita da Faruq, Sakina na daki ta na jin duk abin da ke faruwa kamar yadda Faruq ke zubda kwalla haka ita ma ta fara zubarwa. Mama ce ta raka Hajiya da Faruq har bakin gate sannan su kai sallama ta dawo gida. Hajiya kuwa gida su ka nufa ita da faruq inda malama su ka cigaba da karatu da Addu'o'i, tuni kwakwalwar Faruq ta fara jagwal-gwale ta rikice gabadaya Wanda hakan ya sa shi yin wani barci da bai taba yin irin sa ba. Safiya kuwa na gadj rashin ganin Faruq da ba tai ba ko ajikin ta sabgoginta ma ta ke sai kiran Adam da tai cikin gidan. Tare su ka kwana suna sharholiyarsu... Washe gari Tin jiya karfe 2da Faruq ya fara barci a dakin hajiya bai farka ba sai Sa karfe biyar na yammacin yau, ya na farkawa ya fara fadin, "Mama ina Sakina ta ya jikinta, Ina ta ke Safiya ba tai....... Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-41-42* ________________________________________________________ *_GROUP MEMBERS😘YAU ZAN YI WALIYAR LAUNIN FATA WA IN DA KADAI BASA GAZAWA WAJEN MIN SHARHI ZANWA KYAUTAR FEJIN NAN DOMIN NASAN XASU FI KOWA JIN DADI GAREKU MASOYAN ASALI⬇️_* _*RUKKAYYA FULANI,BABY LOVE,FIRDAUSI,RAHIMA ADAM,UKTY UMMI,WALIDA,MAMAN SHUKRA,MAMAN KHAIRAT,MOMYN IHSAN,HAWWA MUKTAR,HAUWA ABUBAKAR,UMMI JAMILAT,FATIMA ZAHRA, HAFSAT,MAMAN RUKKY, MARRIYA DAUDA,AISHA SHU'AIB, JIDDATY,SISTER,NAFY MUDANGI, PRINCESS OF LIGHT, MAMAN RUMASA"U, MAMAN USMAN,RAHABA🥰🥰I HEART U OLL MASOYAN ASALI SON SO SABIDA ALLAH*❤️❤️_ ******* ******* ******* Ma ta komai ba ko?" Murmushi Hajiya tai tare da fadin, "Alhamdulillah yanzu dai kaje kai sallolin da ake bin ka tin na jiya kan sai ka zo mu yi magana." Bai karacewa komai ba Ya tashi ya dauro alwala sannan ya yi sallolinsa ya na idarwa kuwa bai ko karasa wajen Hajiya ba ya yi saurin ficewa domin komawa gidan sa. Tuki ya ke yi cikin sauri Amman duk da hakan ya Gaza gani ya ke kamar motar ba ta tafiya. Ya na zuwa kofar gidan ya jefar da motar ba tare da yayi kwakkwaran Pakin ba . Da sauri ya shige gidan ba inda ya nufa sai dakin Safiya ya yi sa'a kuwa tabar kofar abude, ya na bugawa ta bude kuwa ya yin da ya ga abin da ya sa shi suman tsaye, Safiya ce kwance da Adam suna lalalata ba su ma lura da shigowarsa ba kasancewar sunyi nisa a iskanci. Da Faruq ya mu su wata gigitacciyar tsawa sai da Adam ya ji sa a kasa, Safiya kuwa kallo kawai ta kura ma sa tare da fadin, "Miye ha ka zaka shigomin daki ba sallama?" Faruq ya ce, "Au tambayata ma ki ke? OK bara nafara gama da wancen karamin Dan iskan kan nadawo gareki." Cire bel din sa ya yi ya fara zabgawa Adam ba ji ba gani tin Adam na ihu har ya ga ji ya yi shiru, sai da Faruq ya fara nishin wahala kan ya kyale Adam. Tin ni kuwa Adam ya ja jiki wando ahannu ya fice. Kukan munafurci Safiya ta fara tana fadin, "Faruq Dan Allah ka yi hakuri wallahi shine ya sa ni dole." Karasowa Faruq ya yi yana numfasa ya ce, "Ina ni ki ke Tambaya na shigo mi ki daki ba sallama ko?" Tuni ya fara dukanta sai da ya ma ta jaga-jaga jini ta baki ta hanci. Sambatu kawai ya ke, "Wa to ni kin maidani boyi-boyi ko? Kin je kinyi tsubbunki kin rabani da farinciki kina snnan Ku ma ki zo ki na cin amanata? Kin maidani Dan iska Kennan ko?" Sai da ya jibgeta son ransa sannan ya fige zuwa kofar gida ya ce, "Wallahi ki barmin gida ba na bukatar kara ganin kazantaccen jikin nan na ki, ki je chan ki karasa iskancinki. Ba komai a jikin Safiya sai wa ni da mayafi Wanda shima din akanta ya ke ta zaro ta daura ga Faruq ya kulle gidansa bare ta shiga ta sa kaya haka ta fara tafiya da kafafunta domin zuwa gida. Ahanyar komawarta gida ban da ihu ba abin da yara su ke ma ta suna mahaukaciya gabadaya ta rikice ban da kuka ba abin da ta ke yi har ta isa gida. Ta na shiga Mama na ganinta ta sume ta ke awajen. ****A bangaren Faruq kuwa Ya kulle gidan ba inda ya nufa sai gidan su Sakina,,, Ya na zuwa ya tarar da Yaya Haiydar tsaye ajikin gate wani mummunan kallo yaya Haiydar ya ma Faruq, Wanda shi ko kawai durkusar da kai ya yi azuciyarsa ya na fadin ," *ba a ma yi ba ya a ka kare bare anyi kuma ai sai ta Allah*." A zahiri kuwa gaida Yaya Haiydar ya yi. Murmushi yaya Haiydar ya fi sannan ya amsa. A bin da ya bawa Faruq Mamaki Kennan Wanda ya kai ga ya kusa summan tsaye. *A jiya bayan tafiyan Mama da Faruq ne yaya Haiydar ya zo a ka ma sa bayanin komai ba karamin tausayawa Faruq ya yi, sannan kuma ya ji dadin gane kuskuren da hajiya ta yi ta kuma gano hanya madai-daiciya, duk da kasancewar hakan ya faru Amman baya fatan komawar Sakina gidan Faruq kamar yadda Baba ma haka*. Bayan sun gama gaisawa ne Haiydar ya ja Faruq su ka shiga gidan domin ga dukkan alamu Haiydar ya fahimci cewa Faruq ya sami sauki ya dawo dai-dai. Sakina na jin Muryar Faruq ta ji wani irin farinciki aranta da sauri ta koma daki, kasancewa ta gansa cikin kwanciyar hankali ba kamar jiya ba ta yi hamdala ta godema Allah, Amman alokaci daya ta chanja yanayi ta fara kuka. Faruq bayan sun gama gaisawa da su mama sannan su ka masa murnar samin mafita Baba kuwa fada ya ma sa sose akan yadaina wasa da ibada ya rikye Addu'o'i dare da rana. Bayan Baba ya kammala ne Faruq ya nemi alfarmar da Sakina ta koma dakin ta,, anan ne fa Baba da Yaya Haiydar su ka ki Yarda fur Wanda ita dai kam Mama tanason hakan har cikin ranta domin farincikin 'yarta. Jiki a sanyaye ya fito zai tafi kawai sai ya hange sakina ta window..... Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association___ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-42/43* ________________________________________________________ *_Ina ganin sharhin Ku yan group dina Xayyeesherth fans Group Ku min afwan rashin reply network ne ke wahalar dani wallahi🤦‍♀️amman duk INA gani kuma INA sane da ma su yi da yan labe ma🙁🙁 sannan INA jin dadi❤️_* ******* Ban da zubda kwalla ba abin da ta ke, suna hada ido ta kakalo murmushi sannan ta daga ma sa hannu. Wani irin yanayi Faruq ya kara tsintar kan sa aciki kawai daurewa ya yi shima ya kakalo murmushin sannan ya fita. Maganar zuci ya ke, "Allah sarki, Sakina baiwar Allah ita yakamata ta fara fushi da ni Amman ba tai ba, Allah ya sa ka mi ki da alkairansa matar Aljanna." Ya na gama fadin hakan azuciyarwa kawai hawaye ya fara fita daga idanunsa da sauri ya shige Mota ya kwashi wajen minti talatin kan ya fara diraibin. ****A bangaren Safiya kuwa sauri tai tasa kaya sannan ta kira mutane a ka taimaka ma ta su ka kai Mama asibiti, gado a ka ba su domin tashin ba na yanzu ba ne. ************* Annemwa Sakina Admission za ta cigaba da karatunta a polytechnic da ke cikin garin Bauchi. Faruq ya na nan lamarin duniya ya ishe sa kullum sai ya bi Sakina Makaranta tun safe sai yamma, Sakina ta kan tsaya sudan yi hira domin itama ta na cike kewarsa. Yau ma kamar kullum Faruq da Sakina zaune ta fito sallah daga lectures, Faruq ya ce, "Sakina ni kam dai Ina ganin mutuwa zanyi wallahi domin rayuwata ba ta da amfani, su Baba da Yaya sun kasa fahimtar me na ke ji a cikin zuciyata wallahi, Wallahi ciwon zuciya nadab da kamani Sakina." Sakina tai murmushi tare da fadin, "Ko mai ya yi zafi maganinsa Allah, irin wannan maganar ba ta kamaceka ba sam, ko dai ba Faruq dina ba ne?" Murmushi ya yi ya ce, "Faruq din Sakina ne a gaban Sakina ba wani bayan ni, Amman kinsan cewa abun ne ya min yawa narasa Ina zan sa raina ko Niger ma na kasa zuwa domin so na ke muje da ke sai indauko subai'atu ko zauna tare ko?" Sakina ta ce, "A ba ya ma anrabamu fiye da hakan kar ka manta ka sakeni aranar aurenmu sannan an hargitsa aurenmu tin kan adaura to Dan kuma yanzu munyi auren mun rabu batare da ka sakeni ba to miye abun damuwa anan? Kar ka manta fa har yanzu ni matarka ce, ko da a ce bazan koma gidanka ba ina ba ka shawarar da ka je ka dauko subai'atu domin nasan ita kam ba ta matsala kuma baza asamu ba insha Allah." Durkusawa Faruq ya yi tare da rikwo hannun Sakina ya na fadin, "Sakina Dan Allah ki min rai ki fadawa su baba zaki dawo gidana, ni na amince na Yarda zaki cigaba da karatun acikin gida, ina sonki Sakina ina so na rayu da ke." Kara damkye hannun Faruq sakina tai ta na, "Na karbi kaddarar rayuwar Aurenane kawai Dan nasan ba abin da zan iya duk da kasancewar Allah ya Riga ya tsara dole hakan zai faru da ni Amman kasan miye musabbabin hakan? Kin biyayyawa wa iyaye ta bangarena da na ka dafarko mahaifina ya yi burin na yi karatu tin ina da karancin shekaru Amman fir na ki bin umarninsa na nunacewa ni fa Aure na ke so, a lokacin da na fadi hakan nasan cewa bai ji dadi ba Amman ko kadan bai nunamin ba kasan miye dalilin? Sabida yafifita farincikina fiye da Nasa alokacin ya manta da duk kudin da ya kashe akaina ya koma kan burina da na sa gaba alokacin, ka ga wannan fannina kenan, a na ka fannin kuwa dafarko mahaifiyarka ta ki Yarda akan ka aureni ta nuna cewa ba ta so na ba ta son tahada jini da ni, to a lokacin da ace duk munyi Hakuri munyiwa iyayen mu biyayya da hakan bai faru ba, ka ga dani da kai da Mama dukkan mu munyi kuskure awannan lamarin Amman sai dai mugodewa Allah tin ya na son mu kuma har ya nuna mana laifin mu tin kan muje ko ina, yanzu Abu mafi mahimmanci agaremu shine mu ma su biyayya sannan mu barwa Allah zabi." Faruq da tin da Sakina ta fara magana ya yi shiru kawai ya zubawa sarautar Allah ido. Ko da tai shiru sai da ya yi jim kan ya ce, "Maddala da samun mace ta gari, tauraruwar al'umma ke din Haske CE ga duk wa ni Wanda ke tare da ke, ina Alfahari fa ke kuma nagane kuskure domin ni musababbabin komai da na rufe mi ki ido da soyayya ta ki ya femin Sakina." Saukar ma sa da hannunsa tai tana fadin" Allah ya yafe mana." Da sauri Sakina ta kalli Agogonta ta ce, "Laaa kai Sweetyn ka sa har an koma ban sa ni ba." Murmushi Faruq ya yi ya ya ce, "Ayya Sorry Matar kirki mu je in rakaki ma yi waya ko?" Daga ma sa kai kawai Sakina ta yi sannan ya rakata har bakin lecture room ya koma. *** Safiya na nan kudi ya kare na maganin mama sun gama sai da kayayyaki Amman kullum abin da ake bukata daban.... Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-44/45* ________________________________________________________ Faruq na nan kullum cikin tunanin danuya ya rayuwarsa za ta kare babu sakina aciki? Maganganun Sakina ne kadai ma su kwantar ma sa da hankali a yayin da ya tuna sai ya ji bakinciki ya nisanceshi sai farinciki. Sai da aka diba wajan watanni biyar Sakina na zuwa makaranta abin ta Faruq ma ya cigaba da rayuwarsa kamar da Amman fa kullum ya na tare da Sakina kan ya tafi gun aiki da kuma inyadawo sai ya biya ta skul ko shago yadubata. Duk da kasancewar Mama da Baba har ma da Yaya Haiydar sun fahimci cewa Sakina na tare da Faruq Amman ba su nuna ma ta ba sannan ma ba su nuna damuwar su akai ba. Ranar Asabar kwatsam Baba ya dawo daga wajen aiki ya ce akira ma sa Sakina. Kowa na zaune ana jiran jawabin Baba ai ko ya fara da, "To Masha Allah na ji dadin ganinku du ka awannan lokaci daman dai magana ce a kan yar uwarku ." ya nuna Sakina ya yin da idda maganar. Ya cigaba da fadin, "Kin ga dai zama agida ba na ki ba ne a matsayinki na 'ya mace gidan mijinki shine darajarki Dan haka na yanke shawarar nema mi ki mijin Aure." Tuni Sakina ta ji gabanta ya fara faduwa azahiri kuwa wa ni irin murmushi dole ta kakalo. "Nasan za ki yi Tunanin cewa Ai Faruq bai sa ke ki ba na ke fadin ki yi Aure ko? To Albishirinki diyar kwarai yar albarka ina mai farincikin sanar da ke cewa za ki koma gidan ki gidan mijinki, domin abin da ya sa mu ka jinkirta kuma mu ka ki neman Saki munaso mu ga iyaka yadda lamarin zai kasance ne domin ina gudun ka da a kara wani kuskuren kamar yadda aka yi a baya, munyi magana da Yayanki Haiydar ya ba ni goyon baya Dari bisa Dari domin na fahimci cewa hadinki keda Faruq sai Allah ba Wanda ya isa ya raba, da wannan na ke fada mi ki cewa ki sanar da Faruq ya zo yadaukeki ki koma dakinki Dan duk nan munsan kuna tare kawai zuba mu Ku ido mu kai." Tuni Sakina ta ji wa ni irin sanyi aranta, "Murmushi ta ke Amman hawayen farinciki bayyana afuskarta, tuni ta tashi da gudu ta nufi daki. Dariya CE kawai ke tashi a falon ganin yadda Sakina tai, Yaya Haiydar ne ya katse su da fadin, " Ni fa ina da magana Gaskiya ban Yarda ba." Kowa ya tsura ma sa ido. Murmushi ya yi sannan ya ce, "Bazan Yarda da komawar kanwata ba indai ba za a chanja ma ta komai na daki ba sannan akara sabon taro domin tayata murna ta manta da baya ta sa gaba aranta da shine farincikin da mu ke ma ta fata." Dukkan su murmushi su ka yi Mama ta ce, "Wannan ai na ka komai na hannun babban yaya." Hira suka cigaba da yi cikin farinciki da walwala. Sakina kuwa na shiga daki ta kira Faruq awaya. "Albishir zan ma Amman sai ka fada min wace irin kyauta zaka min?" Cewar Sakina. "Ummm Auntyna ni Sakina. ban da lafiya ina wata kyauta ni indai ba ke zakimin kyautar kan ki ba ai ni bana bukatar komai, Sakina wallahi ni kam nagaji nakasa jurewa ina jin kamar zan bar duniya ayau dinnan." Sakina ta ce, "To na ji nikam yi shiru ka ji, ina dai Sakina ka ke so? Baba ya ce ka zo ka daukeni mu koma gida." Wani irin ihu faruq ya yi tare da fadin, "Gani nan zuwa yanzu, Dan Allah dai da gaske ki ke ko Sakina? Ko da mafarki na ke,indai mafarkine Dan Allah karki tasheni in farka." Dariya kawai sakina ta fara tana, "Allah am serious natabaa wasa irin wannan?" Tuni Faruq ya fara hamdala ya na fadin, "ganinan zuwa yanzu zan zo mu tafi, ki jirani please." Sakina ta ce, "Kai dauki to ba yau ba ai sai anshirya biki tukunna kuma ma naji kaman Yaya Haiydar na fadin za azo akwashe kayan akawo wasu." Faruq ya ce, "Alhamdulillah duk da haka dai gani nan zanzo na ganki wallahi har na warke karki damu ki Bini bashin kyauta inna dawo seti kin San yanzu giyar son ki na kai na." Katse wayar ya yi kawai ya nufo hanyar gidan su Sakina. ya na isa ya kira Sakina Awaya kan cewar ta fito, ta ce Aa ya shigo kawai. Kana ganin Faruq za ka ga farinciki ya bayyana a fuskarsa. Ya na shiga.... Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر* _(Auren kaddara)_ _A True Life Story_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________ _*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_ _Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_ *Instagram page* _@zamani_writers_association_ *Youtube channel* _Zamani_writers_association_ *PAGE-46* 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 ________________________________________________________ Ba inda ya nufa sai dakin Mama, da fara'a kuwa Mama da Baba su ka amshe sa. Waige-waige kawai ya ke yi Dan ganin ta ina Safiya za ta fito? Yaya Haiydar ne ya lura da hakan ya ce, "Kar ka ji komai nan da jibi za ka tafi da abarka Dan angama komai, ko dai zaka Dan bar ma na ta kara sati ne Dan ba mu gaji da ganin ta ba." Murmushi kawai Faruq ya yi, ya fara Sosa kyeya sannan ya ce, "ai ba komai in dai za ta koma din an gama min komai." Dariya kawai su ka yi daganan kowa ya fita ya bar Faruq Sakina ta shigo su ka fara shan love, Faruq ji ya ke kamar kar ya rabu da sakina aranar domin wani tsantsan sonta ne ke kara shiga zuciyarsa. *Yan Group din Xayyeesherth Fans Group kuwa sai murna su ke yiwa Sakina ban da kayan tsimi na 'ya mace ba abin da su ke kawowa mussaman Admin Ambeby,Tare da Maman Shukra sun dage sai sun maida Sakina Amarya* ***Daga ranar zuwa washe gari a ka kammala komai ya yin da akaje kwashe kayan danki Sakina kuwa anci karo da loyoyi na karkashin gado Dana kasan kujeru har ma da kicin, ba Wanda ya yi mamakin ganin hakan domin kuwa Safiya ta yi a kan faruq ma bare Sakina, sai da a ka chanja komai na dakin tsaf aka saka sabbabi, Faruq kuwa sai da ya karama Sakina setin akwati na tukwicin albishir din komawa. Walima a ka hada akayi saukan Al'Qur'ani sannan a ka ci a ka sha . Washe gari ma komawar Sakina sai da akaje gidan akai Sauka sannan kowa ya watse. Sakina da Faruq jin su suke kamar amare Wanda zance ba su yi irin wannan farincikin ba ko a darensu na farko. Faruq ne ya shigo dauke da gatuwar bakar leda ban da kamshi ba abin da ke tashi a dakin. Zaune Sakina ta ke akan kujera chatting ta ke da yan Xayyeesherth fans group da ke WhatsApp ban da murmushi ba abin da ke bayyana afuskarta domin kowa murna ya ke tayata gashi sai tsokanarta su ke ma su korarta ta Sauka na yi ma su cewa ta zauna na yi. Tin da Faruq ya shigo ya kasa karasowa gareta murmushi kawai ya ke ya yin da ita ma ta dago ta kallesa ta mai da ma sa da wani murmushi mai sanyaya zuciya. "Ba za ki ajiye wayar nan ki min oyoyo ba." Cewar Faruq. Shagwabe fuska Sakina ta yi tare da girgiza kai ta na, "Umm umm ni bazan iya tashi ba." Da murmushi Faruq ya karaso gareta, "Ai ni ko zan karaso na mi ki abin da ya fi wannan." Amsar wayar ya yi ya na, "To A ajiye wannan tin kan fara kishi da ita." Daukatanta ya yi chanchank ya na, "Oyaa mu je ko?." Dukan sa da hannu sakina ta ke tana kara shagwabe ma sa Wanda ke kara ingiza shi. **Kwanan farinciki, cike da nishadine ya kasance acikin gidan Faruq da Sakina. Bayan Sati daya da dawowar Sakina Faruq ya je yadauko Subai'atu. Ba karamin jin dadi Sakina tai ba domin da ka ga subai'atu za ka San cewa ba ta da matsala, zama suke cikin nishadi da walwala. Hajiyan Faruq ban da soyayyar da nuna kulawa ba abin da ke tsakanin ta da surukanta. **Safiya kuwa Mama ta yi mutuwar wulakanci domin korarsu a kai a asibiti sun ka sa biya gashi ba Wanda su ke ragawa a family din su bare wani yayi tinanin taimaka ma su, Mama na mutuwa rayuwar Safiya ta kara rikicewa ta koma bara daga karshe ma dai ta haukaci. Sakina kuwa ta koma makaranta, Subai'atu ma Faruq ya nema ma ta duk randa ba su da makaranta sai su je shagon Sakina tare, in Faruq ya dawo ya biya ya dauko su. **Zaune su ke suna cin abinci ban da shewa ba abin da ke tashi a gidan da gudu Sakina ta, tashi ta shige toilet ban da Amai ba abin Da ta ke yi, tuni Faruq ya kai ta asibiti ai ko aka tabbatar da cewa tana da ciki wa ta biyu, ba karamin farinciki Faruq ya yi da jin hakan da ga hajiya har Subai'atu kowa murna. Watan cikin Sakina tara dai dai ta haifo yan uku, maza biyu ma ce daya *Fadil,fahdil,nd little fadila* Anyi shagali an karshe kudi kamar ba asan yadda a ke samowa ba Dan tsantsan farinciki. ........ Bayan shekara biyu Subai'atu CE zaune da tsohon ciki sai ga Sakina ta fito ta na fadin, "Mai tumbi sannunki da zama." Subai'atu ta CE, "Aunty Allah ni kidaina cemin mai tumbi ai ke ma kina da shi." Dariya Sakina ta fara, "A'a wlh kar kimin sharri ai Fadila CE Auta." Faruq ne ya shigo ya na fadin, "Wa ya fada mi ki? A I kina shirya sai kin Ajiyemin dozin." Murmushi Sakina tai tana fadin, "In dai wannan ne kaddarar Aurena na karba ko da dozin biyune za su zo su huce kamar yadda azzawajul-mukaddar ya zo karshe." Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah *_Yau dai Allah ya yi , Ina godiya da Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai dumbin masoya cikin koshin lafiya, ya ubangiji ya Allah ina rokonka da ka yafemin duk kurakuren da aikata acikin wannan littafi, ka sa Sakona ya isa ga al'umma sannan kuma ya amfanar da su_* *_Godiya ta mussaman gareki Antyna Real Shaxee ke din yar uwace a gareni ta mussaman, tare da illahirin yan kungiyar zamani writers Association ina Alfahari da Ku oll._* Ban manta da Ku ba yan group dina Mussaman ku _*RUKKAYYA FULANI,BABY LOVE,FIRDAUSI,RAHIMA ADAM,UKTY UMMI,WALIDA,MAMAN SHUKRA,MAMAN KHAIRAT,MOMYN IHSAN,HAWWA MUKTAR,HAUWA ABUBAKAR,UMMI JAMILAT,FATIMA ZAHRA, HAFSAT,MAMAN RUKKY, MARRIYA DAUDA,AISHA SHU'AIB, JIDDATY,SISTER,NAFY MUDANGI, PRINCESS OF LIGHT, MAMAN RUMASA"U, MAMAN USMAN,RAHABA🥰🥰I HEART U OLL MASOYAN ASALI SON SO SABIDA ALLAH*❤️❤️_ Dama wa'inda ban sami damar lissafawa ba inayinku duka. _*Fatan zaku kara nunamin tsantsar soyayyar gareni ta hanyar siyan sabon novel di na JAMEEL (Nafseen) wan da na ke shirin fitarwa nan da sati daya karku bari a ba Ku labari, ta nan ne zan tabbatar da cewa ni tauraruwar kun CE da gaske ko ko dad in baki ne?_ *Domin sharhi, shawara ko gyara game da littafin Azzawajul-Mukaddar Ku tuntubeni ta wannan number 08103080717* _*Urs Xayyeesherth*_😍