*_Typing📲_*[9/6, 6:54am]Aysha Galadima: 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) *_Ina mai farin cikin sake had'uwa daku a CIKI DA GASKIYA.....kashi na biyu, ALLAH ya amfanar damu abinda ke cikinsa, kuskurena kuwa ku watsar dashi gefe, dannima mutumce kamar kowa ajiza, ALLAH ya mana jagora, yajikan mahaifanmu dadukkan musulmai baki d'aya._* Ina godiya agareku sosai😘😘😘. ➡1⃣ Fadeela dake bayan Aysha tace, "gwaggo! Dama kece babu lafiya?, ina mama taganoki?. Duk atare tajero tambayar. Da k'yar Gwaggo bintu take fidda numfashi, da yak'en dole wa Fadeelah, Aysha kam takasa cewa komai, jitake tamkar takashe gwaggo bintu kawai kowa yahuta. Wani mugun plashing yashigo wayarta, saikuma sak'o yashigo, samun kanta tayi da ciro wayar daga post d'in hannunta taduba. _karki yarda kiyi wani abunda zai nuna gwaggonki tayi wani mugun Abu akanki, hakan tamkar wargaza aikinmune, ki kiyaye, so kisan yanda zaki nuna komai normal tsakaninki da ita saboda sister d'inki, karki 6atamin aiki._ Abinda aka rubuta kenan kuma an 6oye number, Aysha takuma maimaita sak'on a karo Na biyu, cikin mamaki tace wanene wannan?...... Muryar gwaggo bintu ta tsinkayo tana fad'in Aysha da gaske kece? Kece kika dawo garemu? Tayi maganar tana rushewa da kuka. Da sauri Aysha taje ta rungumeta, ta fakaici idanun su fadeelah tafad'a ma gwaggo bintu magana a kunne, _gwaggo kada kiyarda ki nuna wata alamar dazata gane kin saka rayuwata agarari, wlhy inba hakaba sai an kasheki, kinuna murnar dawowata daga karatu, Dan ALLAH ya juya zalincinku agareni yazama alkairi nayi karatun._. Su fadeelah dabasu San abinda ke faruwaba suka Shiga lallashinsu, fadeelah ta janye Aysha daga jikin gwaggo bintu tana bata hak'uri. Bak'aramin mutuwa jikin gwaggo bintu yayiba, tabbas maganar Aysha ta shigeta, _(nace karan bana aishi ke maganin zomon bana gwaggo bintu😂)._ Aysha takoma kusada gwaggo bintu ta zauna, bishirah jitake tamkar cinye Aysha dan murna, suna rik'eda hannun juna, kai Aysha wlhy kin canja, ilimi dad'ine dashi, kamar bakeba wlhy😁. Dariya Aysha tayi, wlhy nima duk kin canja mini bishirah, kinzama babbar budurwa, halan kinkusa aure ma?. Hhh saura wata 2 ma. Eyeee Ashe zamusha biki, ALLAH yasanya alkairi. Ameen fadeelah ta amsa. Sund'an dad'e a sibitin, amma gwaggo bintu takasa sakin jikinta, sai yanzu nadama da Dana Sani ke k'ara yawa a zuciyarta, taci amanar d'iyar zumunta, gashi wadda tasata aikata hakan y'arta ta azabtar da ita, tunda ta kwanta asibitinnan babu jinin hajia babba ko d'aya daya lek'o dubata, bare ita hajia babban, lallai tayi kuskuren dabatasan tushen gyarashiba, afakaice taketa share hawaye, Wanda Aysha Ce kawai talura dasu. Aysha taja bishirah gefe suka zauna. Bishirah nikam bayan barina gidannan miya farune?. Humm abubuwa dayawa sun faru Aysha, ciki harda Auren da alhaji ya k'ara, tas bishirah takwashe komai tafad'ama Aysha, har zuwan gwaggo bintu Lagos da dawowarta, harda sanadin kwanciyarta a asibitin. Aysha tace ALLAH ya kyauta. Itama bata 6oyema bishirah komaiba, tabata labarin komai akan abinda yafaru da'ita, kuka sosai bishirah takeyi harda majina, tad'ora mata bayani akan amaryar alhaji mahaifiyartace. Bishirah kinsan miyasa na baki labarin sirrina kuwa?. A'a saikin fad'a Aysha. Saboda ki taimakeni, kuma Dan ALLAH ki rik'emin sirrina, zan d'auki fansa akan hajia babba da sauran mutanen k'ungiyarsu, amma hakan bazai faruwa saina samu wasu sirrika atareda ita. To Aysha wane taimaki kikson namikine?. Kawo kunnenki. Aysha tagama fad'ama bishirah abinda nikam banjiba🤷🏽‍♀. Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan al'amuran rayuwa dakuma yanda zasu 6ullowa komai kafin auren bishirah. Hango fadeelah dake nufosune yasakasu mik'ewa suna dariya. Aysha tace yi hak'uri yaya fadeela munbarki ke kad'ai, kinsan andad'e ba'a had'u baneba. Batace komaiba sai juyawa tayi sukabi bayanta. Koda suka koma basu dad'eba sukamusu sallama, Dan itama gwaggo bintu suna saran sallama yau da daddare. _____________________________ K'arar dasukajine tasakasu farga da abinda ke faruwa, da sauri babban yaron Barau modibbo yalek'o, ganin jami'an tsaro yasakashi rikicewa, yunk'urawa yayi danufin guduwa amma sai hakan ya gagareshi, sakamakon harbinsa da Joseph yayi a k'afa. Da sauri ya khaleel dake la6e kusadasu yafito shima, saukar harbi yaji a hannunsa Na haggu. Da sauri yadafe wajen tareda kallon saitin da'akayo Harbin, barau modibbone, yakuma Harbin ya khaleel a ciki, amma bata shigaba, saboda rigar dake jikinsa mai kare shigar bullet. Ganin haka barau modibbo yajuya da sauri zuwa wani d'aki. Cikin sassarfa ya khaleel dawasu ma'aikata suka take masa baya, dukda d'an Karen azabar da hannunsa ke masa, ga jini tuni yafara jik'a yellow d'in rigarsa. Neman duniya sunrasa inda barau modibbo yake, babu binciken dabasuyiba agidan, amma babu ko alamarsa. Basusan ya silale tawata k'ofaba yabar gidan tabaya, dama antanaji k'ofarne saboda irin wannan ranar. Saidaga baya ya khaleel yafarga da k'ofar, cikin cije le6ensa yatura Waldrop dake wajen gefe, cikin nazarin k'ofar yace, Taheer inaga yagudu ta Nan..... Awahalce yake magana saboda jiri daya fara gani, sakamakon jinin dake zuba a hannunsa. Suduka suka k'araso wajen da sauri, wasu fita sukayi, inda k'ofar ta kaisu harcan baya, alamar tashin motarsa suka gani, wannan ya tabbatar musu cewa yagudu. Dawowa sukayi inda ya khaleel yake dafeda hannunsa, sai faman lumshe idanu yakeyi. Da sauri Adams yak'araso wajensa, sunma manta boss yasamu harbi, youseef ne ya yago bedsheet d'in gadon da hanzari Adams yakar6a ya d'aure hannun ya khaleel Dan tsaida zubar jinin. Basu wani 6ata lokaciba sukabar gidan da gawar wad'anda ya khaleel ya kashe, saikuma yaraonsa dasuka kama. Dr Abraham sukakira, yace yana General hospital, suyi hak'uri su sameshi a can, Dan sun fad'a masa boss ne yasami harbi. Da sari Adams ya amsa da to, Emmanuel muje general hospital. motar Ramadan na niyyar fita daga Asibitin tasu ya khaleel tashigo, Ramadan yace ai wannan motar ya khaleel ce, yay maganar yana taka birki. Wani irin fad'uwar gaba Aysha taji, tuna a yanayin daya fita d'azun, fitowa sukayi sudukansu. Ramadan yanufi motar da Sauri. Da kansa yafito, saida kana ganinsa kasan babu lfy, Dan dak'yar yake d'aga ido ya kalli hanya, wannane ya haddasama tafiyarsa d'an rangaji. Da sauri Ramadan yak'arasa ya rik'eshi yana fad'in ya khaleel lfy?. Cikin jarunta irin tasa yace, shiga dani ciki, mubi ta baya. Banason su tada hankalinsu, harbine kawai. Ta baya sukabi, Aysha da Fadeela suka nufi cikin asibitin hankalinsu a tashe. Kai tsaye office d'in sa suka nufa, Bahama a ciki. Babu dad'ewa Saiga Dr Abraham, tareda Adams suka shigo suma. Duk fita sukayi, suka bashi damar aikinsa, ya khaleel nazaune akan kujera yajingina da bayansa idonsa a lumshe. Cikin hanzari Dr Abraham yake gudanar da aikinsa. Ya khaleel akwai jarunta, inbanda matse ido dad'an cije baki babu abinda yakeyi, har Dr Abraham yagama cire bullet d'in, sai zufa ya khaleel keyi saikace ana kwara masa ruwa, dukda kuma ac dake aiki a office d'in, duk wani abinda yadace anmasa, harda allurar barci, dak'yar Dr Abraham ya lalla6ashi ya kwanta a gadon dayake duba marasa lfy, amma da yadage akan gida zaije, Dr Abraham yace yayi hak'uri allurar da akayi masa ta sakesa first, saiya tafi. Su Aysha Na waje sai safa da marwa sukeyi, ahaka baffah da Ramadan yakira yak'araso. Cikin tashin hankali yake tambayarsu miya faruda Mu'azzam d'in?. Adams ne yamasa bayanin harbine, baikai k'arshen zancenba Dr Abraham yafito. Ya tabbatar musu ancire, kuma ya khaleel yana barci, zaid'an huta danya saka masa k'arin ruwane. Damuwar tad'an ragu agaresu yanzu. Amma banda Aysha, daketa share hawaye tun d'azun, idon baffah na kanta, duk abinda takeyi yana kallonta, ganin kukan datakeyi yak'i ya karene yasaka baffah matsawa kusada ita yana lallashinta, da nuna mata tamasa addu'a ba kukaba. *_hours ago_* Bayan awoyi kusan 5 ya khaleel ya farka, dama tuni ruwan ya k'are, saboda tashin hankalin da 'yan gida suka shiga yasakasu tafiya gida, lokacin anata sallar isha'i. Su Aysha tuni baffah yasaka ya Ramadan ya maidasu gida dama. Duk suna falo kowa jigum-jigim, hajia babba ce kawai babu da y'ay'anta, itama tana 6angarenta jigum, Dan labari yazo mata akan abinda yafaru da ya khaleel d'in. Shigiwarsu tasaka kowa mik'ewa, kowa yayo Kansu, Dan dukkan mazan gidan suna asibitin, a babban falo yazauna sunata masa sannu. Ganin yanda suke arud'e yasakashi sakin murmushi, yace kufa kwantar da hankalinku, ni Na warke. Jiki a sanyaye suketa d'aga kai. Anty Mamie takawo masa tea, kar6a yayi yana fad'in thanks you Mamie na. Murmushi tamasa tana jinjina kai. Ahankali yake sha idonsa Na kallon familien nasa, daduk suke zaune afalon, harsu hajia babba dasuka fito, saidai yanayinta yabama kowa mamaki yau, Dan babu masifa, saidai tanata kaffa-kaffa da ya khaleel d'in. Ahankali yad'ago idonsa ya sauke akanta, tanacan raku6e bayan Umme amarya, daka ganta kasan a hargitse take. Guntun murmushi yayi, aransa yace, trouble marker d'ina yau kuma miya maidata haka?. Aysha dabatasan ita yake kallonba tad'ago ido danufin satar kallonsa, amma sai karaf suka had'a ido, da sauri ta janye nata tana d'an tura baki gaba. Shima ya kauda kai gefe, ahankali yace anan da hali. Hajia babba dake gefensa duk hankalinta atashe tace mikace?. No momy bance komaiba, baradai naje nad'an watsa ruwa, Na rama sallolin dake kaina. Ok. Mik'ewa yayi sunata masa sannu. Hajia babba tabi bayansa, dakanta tahad'a masa ruwan wankan, sai wani dama-dama takeyi dashi, danso take taji idan sun kama barau modibbo. Abin Na momy mamaki yake bama ya khaleel, Dan bayaune karon farko da'aka ta6a harbinsa ba, amma momy bata masa irin wad'annan abubuwan, hasalima saidai Anty Mamie tamasa. Baikawo komai aransaba yashiga wankan, itakuma tafita tabashi waje. *bayan 2days* Ya khaleel yaji sauk'i sosai, ga kulawa ta musamman dayake samu daga momy da Anty mamie, harma da mama dadukkan sauran 'yan uwansa. Aysha bata ta6a zuwa gaidashiba a kwana biyunnan. Daga wajen aikinsa kam lamarin ba'a cewa komai, manyansa dayawa sunzo, hakama wad'anda suke k'asa dashi. Gwaggo bintu ma an sallamota jiya. Mama da kanta tayima baffah bayanin dangan takarta da gwaggo bintu. Baffah yasha mamaki, danbai ta6a zaton hakaba. Yacema mama to yakamata gwaggo bintu takoma hannunta, baikamata tacigaba da zama mai aikiba, ya y'antata. Mama taji dad'in haka sosai, Dan dama haka take so. Wani sepia d'aki aka gyara mata a 6angaren mama. 🤣saidai abinda nalura dashi, gwaggo bintu bata murna da hakan, idan San samune ita kawai ta fece Kano abinta. Amma tana nuna hakan mama zata gane wani Abu, shiyyasa tayi gum da bakinta😂. Hajia babba duk batasan hidimar da'akeba sai ayau. Wannan lamari yatada hankalinta, da gaggawa ta aika aka kira mata gwaggo bintu kuwa. Bintu! Wane labari nikeji agidanan? Kina nufin k! Y'ar uwar fad'ima ce? Idan hakane ina yarinyar damuka tura karatu?. Ganin yanda tarikice sai abin yabama gwaggo bintu dariya, amma batayiba, mamaki takeyi dama akwai abinda zai tsorata hajia babba haka?. Bintu dake nakefa, kikamin shiru. Gwaggo bintu tanisa, tareda fad'in hajia ni k'anwar mijin fad'ima ce uban Aysha dakika kai karatu, amma ki kwantar da hankalinki batasan komaiba, har anzu azatonta d'iyarta tana makarantane, kuma ni bazan ta6a fad'a mata komaiba kinji. Ajiyar zuciya hajia babba ta sauke, tadafa kafad'ar gwaggo bintu tana fad'in yauwa bintu ngd sosai, shiyyasa kike birgeni, ga wannan kud'in dubu100 ne, kiyi amfani dashi. Sosai gwaggo bintu ta nuna murnarta, hajia babba ta sallameta tana zabga mata godia. Fitowa tayi tana mai daria a zuciyarta, tace hajia laurah kenan, aii bazaki ta6a fitaba daga wannan tarkon, Shiga ukuma yanzu kika fara Shiga cikinta wlhy, masu iya magana kance *CIKI DA GASKIYA...* wuk'a bata hudashi aii🤷🏽‍♀ aii. Nace na hajia babba kam babu *GASKIYAR NAN* nasan 6us!!!!! zamu hudashi🔪🤰🏻aradu😆😆😆🤣. ________________ Da daddare baffah yatara dukkan families d'in nasa, harda Ammah data dawo aranar saga Jigawa............✍ Komi baffah zai fad'a??🤔. Kumuje zuwa my guys, inaji ajikina alkairine fa😁. Bara nafara kwaso shoky💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻tun yanzun, kumafa kuyi aradu🤣 🤣🤣inda nace yau zanyi posting bazaku barni Na hutaba😂😂😂😜 😍😍😍😍😍❤❤❤❤❤💋💋💋💋💋 [9/6, 5:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) _gaisuwa da fatan alkairi *Ayusha Ilyasu & Aysha Galadima*😍😍😍😍😘😘💋_ 2⃣ Falon yayi shiru, kowa ya maida hankalinsa ga baffah, dukda ba wannan ne karon farko da aka ta6a irin wannan taronba agidan kuwa. Amma a wannan karon sai taron yafirgita zuciyar wasu daga cikin al'ummar gidan, musamman ma hajia babba da gwaggo bintu, Dan taron harda su Aysha aciki, da ita kanta gwaggo bintun. Bayan an bud'e taro da addu'oi Ammah tafara magana. Nasan zakuyi mamakin wannan taro, to kudaina mamaki, nice nasaka babanku yayishi, maganar gsky taron yashafi wasunku, kuma ina fata yazama alkairi agaremu baki d'aya. Ta maida kallonta ga baffah, tareda jinjina masa kai, alamar tabar wuk'a da nama a hannunsa. Baffah yafara da sallama da nasiha, sannan yad'ora da fad'in wannan zama yashafi 6angarorine guda biyu zuwa uku. Na farko shine bintu wadda kuke kira Maman yara tanada alak'a ga fad'ima, nasan kuma duk kunsan haka. Duk suka amsa da eh. To alhmdllh, daga yanzun tafita daga jerin masu aikin gidannan, itama tadawo cikinmu, zata cigaba da zama wajen fad'ima insha ALLAH. Kowa ya nuna farincikinsa, Dan bazasu iya manta alkairin gwaggo bintu ba akan d'awauniyar yaran gidan, tundaga kan Amatullah taketa d'awainiya dasu, wannan yasaka taci suna Maman yara. Ayanda nakula hajia babba ce kawai batayi na'am da batunba, amma batace uffanba. Baffah yaciga da fad'in, akwai yarinyar Hama maisuna bishirah, zatayi aure nanda 2 month's idan ALLAH ya kaimu, to tunda bikinta yataho, itama mun dakatar da ita ta huta, ALLAH ya Sanya alkairi. Nanma akace amin. 6angare na biyu kuma shine, za'a kawo sabbin masu aiki su hud'u insha ALLAH, dansu zama canji gasu bintu d'in. Kashi Na uku kuma shine maganar auren Mu'azzam!...... Kowa Afalon saida yad'ago ya kalli baffah, musamman ya khaleel da k'irjinsa yay tsawar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta🤣. Hajia babba ma ta kafe baffah da kallon kid'ima. Ammah kam murmushi takeyi. Aysha kuwa aii atare k'irjinsu yabuga itada ya khaleel😆.lol Baffah yacigaba da maganarsa yana nazarin kowannensu, dariya taso kubce masa lokacin da idonsa ya sauka kan ya khaleel d'in, amma saiya danne ya kauda kai yana murmushi. Zaman khaleel ya isheni hakanan, Dan haka Na yanke hukuncin masa aure da mace tagari, wadda Na yarda da ingancin tarbiyyarta, ban hanaka anangaba idan kasami wadda kakesoba ka k'ara. Bawata baceba illah Aysha y'ar uwarka, yay maganar yana nuna Ayshar. Mutum hud'une suka zabura alokaci d'aya. Ya khaleel, Aysha, mama, hajia babba.😂 Ya khaleel yay k'arfin halin fad'in baffah wannan y'ar yarinyar?. Kaci gidanku iro, dan k'aniyarka bakaine kata6a fad'amin kafison auren k'aramar yarinya ba? Shiyyasa ina dawowa jiya naga wannan y'ar albarka Na sanarma babanka matar aurenka tazo, haka kakeso muzuba maka ido muzama sakarkaru irinka?, ta maida kallonta ga sauran yaran, kutashi kujeku angama daku, inma da sauran bayani a nemoku daga baya. Kowa mik'ewa yayi yabar wajen, saidai Aysha kuka takeyi Wanda batasan dalilinsaba, Na dad'ine kokuwa Na bak'in cikine?.🤷🏽‍♀ Tambayar dayakamata musani kenan masu karatu😂. Daga Baffah sai matansa da ya khaleel da Ammah aka bari awajen. Hajia babba tafara magana cikin 6acin rai. Gaskiya Alhaji wannan had'in bazai yuwuba, kuma shima aisai atsaya aji za6insa, yanada wadda yakeso aiiko. Baffah ya dubeta rai 6ace, to aii ban hanashi fad'ar za6in nasaba, shekaru nawa na6ata ina magana d'aya akan mu'azzam? Kinta6a tayani masa magana? Idan namiki maganar bacakike aure lokaci gareshiba?, to aii yanzu lokacin yazo. Kai mu'azzam wacece za6in taka? Kata6a sanar dani kanada wadda kakesone nahanaka?. Kan ya khaleel a k'asa yana sauke numfashi da k'yar, saboda damuwar dayake ciki, gawani Abu dayazo ya tokare masa mak'oshi saboda tashin hankalin had'ashi aure da waccan yarinyar da'ake shirinyi. Ya girgiza kansa ahankali saboda tambayoyin da baffah yay masa. Shiru yayi baice komaiba. Wannan ya k'ara hasala hajia babba, tace Ibraheem kabud'e baki kayi magana Dan ubanka, Dan bazan ta6a amincewa jinina yara6uda jinin Fad'ima ba, bazai yuwuba kuwa. Ya d'ago idanunsa jajur yazubasu kan hajia babba, please momy kiyi hak'uri, banida hujjar bijirema mahaifina, Dan yabani dama tuni, amma nayi sakaki da'ita......... Rufemin baki mara kunyar banza, ka isa kafad'amin mahaifinka? Nima aii mahaifiyarkace, wahalar ma danaci akanka ko Quarter d'inta baiciba, Dan Ubanka bakai kacemin kanason *_Aleeya d'iyar Alhaji Mudansir Na goma ba?._* Shine yanzu zaka canja magana anan? Kai sarkin biyayya? To magana d'aya nakeyi banyarda ka auri jinin fad'ima ba, inhar nice *Uwarka!.* Da Sauri mama ta nuna hajia babba zatayi magana baffah ya girgiza mata kansa, alamar kartace komai. Shiru tayi ta had'iye maganar ranta Na k'una. Anty Mamie da umme amarya dai basuce komaiba, amma k'asan ran Anty Mamie tanata farinciki da wannan had'in, Dan tana tausayama khaleel sosai, fatanta a kullum ALLAH yabasa mace tagari, to tana ganin ALLAH ya kar6i addu'arta kuwa. Ammah tace lallai Laure kin Isa, to bara kiji Na sanar miki, inhar ni d'innan Na haifi Abdullahi, shikuma ya haifi Ibrahim, to tabbas aurensa da d'iyar Fad'ima babu fashi, dagake har fad'ima babu Wanda ya Isa hanawa. Wlhy koda Ibrahim da Ai'shane kuwa, kingadai su za'ama auren ko? To koda zasu kashe kansune saina saka an d'aura auren, sannan arufesu aka bari d'aya, idan ana amarci alahira suje can suyi, Ibrahim kafara shiri, danna gama magana da k'anin mahaifin yarinyar, gobe idan ALLAH ya kaimu babanka Ma'aruff zasuje a tsaida magana, Aleya kuma take ko wacece? Idan kana buk'ata za'a iya had'a maka, babu ruwana dashiga hurumin ubangiji, wannan yarage ruwanka . Ammah tayi ficewarta. Baffah ma tashi yayi yafita, aikam hajia babba tafara zabga masifa, kowa na gidan yanajinta, ya khaleel yamik'e yabar musu falon, Dan shikad'ai yasan cikin masifar tashin hankalin dayake. Baita6a zaton baffah zai d'auki mataki akan rashin auren nasaba haka. d'akinsa yashige ya kulle kansa, yafad'a saman gado yana dafeda kansa dake masifar sara masa🤦‍♀, jiyake tamkar zai rabe biyu Dan ciwo. Aysha ma nacan tana 6arzar kuka a d'akin mama, ahaka mama tashigo ta isketa. Da sauri tak'arasa gareta tajawota jikinta ta rungume, tana mai lallashinta. Kiyi hak'uri Aysha, nima bazan yarda a cutarmin dakeba, amma miyasa kawu bilya zaimin hakane? Miyasa bai fara sanarminba kafin ya yanke wannan hukuncin?, shin ya mance wacece Laurah?. Indan ta Ibrahim ne bazan ta6a damuwa da aurennanba, Dan yanada nagartattun halayen dadukkan macen kwarai zata sosu, amma mahaifiyarsa bazata kasance surukar arzikiba, bakuma zata ta6a barinku kuyi farincikiba. Gaskiya bazan amince a cutar da marainiyar ALLAH ba, Ammah kada kimin haka, ki sassauta Dan ALLAH, wlhy nice zan cutu Ammah, Dan ayshace zata shiga k'angin wahala. Kalaman mama sunkuma narkar da zuciyar Aysha, takuma rushewa da kuka tareda k'ank'ame mamar. Har washe gari gidan tsit, kowa yashigo saiya San babu lafiya ga mutanen gidan, Dan raunin farincikin gidan yayi matuk'ar saukar farashin mizani, haka sukayi break fast sukuku, wanda babu Aysha aciki babu ya khaleel, hakama hajia babba da zuri'arta. Babu Wanda yatakura akirasu, Dan kowa yasan halin dasuke aciki. ______________________________ Komai yinsa yakeyi cikin wani yanayi, kokad'an babu alamar d'igon walwala tattare dashi, ga d'unbin kasala daya tashi da ita ayau, hakan tafarune saboda k'arancin barci dabai samuba a daren jiya, saboda maganar auren nasa, yaja siririn tsaki tareda yaye towel d'in dake kugunsa bayan yasaka boxer, yad'an Mirza mai kad'an ajikinsa tareda feshe ko ina Na jikinsa da body spry d'insa mai dad'in k'amshi, yasaka farar vest sannan yasaka Uniform d'in aikinsa, yayi k'yau sosai, musamman dayagama tsuke kugunsa da belt. Wani turaren yakuma d'an fesawa kad'an, sannan yajawo takalmansa da safa yazauna kan sofa yana k'ok'arin sakawa. Knocking d'in k'ofarsa da akeyi yasakashi jan tsaki, da k'yar yabud'e baki yace ashigo. Shahuda ce d'aukeda tire Wanda aka shirya masa break d'insa. Cigaba yayi da saka takalmansa batareda yad'ago ya kalletaba. Taja table ta ajiye sannan tace ya khaleel ina kwana?. Yanzunma bai d'agoba ya amsa da lfy. Duk atsorace take da yanayinsa, dukda baya sakar musu fuska sukan gane yanayin farin cikinsa Dana damuwarsa. jin alamar tana tsaye akansa yasakashi d'ago jajayen idanunsa yazuba mata, cikin daburcewa tace dama um..um....Anty Mamie ce tace akawo maka break fast naka, ta..tace kaci please. Baice komaiba yamaida kansa yana k'ara gyara igiyar takalminsa. Da sauri Shahudah tabar d'akin, tanamai godiya ga ALLAH data fito lfy. Koda yagama bai kalli abincinba, yak'arasa gaban madubi yad'auki agogonsa yasaka, ya d'auki gun nasa yasaka a gefen k'ugu, sannan yad'auki jakkar lap-top nasa yanufi k'ofa. Harya kama handle d'in k'ofar saikuma yatsaya cak, tamkar Wanda aka kirawoshi. Gani yayi baidace yawatsama wadda tadamu dashi k'asa a idoba, yadawo baya tareda jawo table d'in da Shahuda ta ajiye break fast d'in gaban sofa. Tea kawai yahad'a kad'an yasha, Dan bayajin cin komai ayanzun. Yana gamawa yamik'e yafice. Babu kowa afalon, wannan yasakashi shiga 6angaren umme Amarya dake kusadashi, a ahanya sukaci karo zata fita aiki, ya risina ya gaidata kamar yanda yasaba. Daganan 6angaren Anty Mamie yashiga, itama sun gaisa a tsaitsaye saboda yana sauri kada ya makara. Anty Mamie tace aff babana naga kana sauri yanzu, amma idan kadawo inason magana dakai kaji. Kansa ya jinjina mata, yana had'iye wani mugun yawu yafice da sauri. Itama binsa da kallo tayi, zuciyarta cikeda tausayinsa. Daga nan 6angaren mama yashiga, bata a falo. Jiyo hayaniyar 'yan uku a bedroom d'insu yasakashi nufar can, saida yay sallama tabashi izinin shiga sannan yashigo. Cikin girmamawa ya gaisheta kamar yanda ya saba. Yasaci kallon mutuniyar tasa Aysha dake zaune a gado, mama ta tasata gaba, da alama ansakata cin abincin dolene. Dan turawa takeyi tana hawaye, dagani kasan Dan dole takecinsa. Sai da yamik'e sannan yace mama lfy takene? Ita wannan?, tanacin abinci tana kuka. Lafiyarta k'alau babana, iskancintane kawai, tunjiya darana tak'incin abinci, tazauna tanama mutane kukan isakanci, saikace wata yarinyar goye, tak'are maganar da Harar Aysha. Shima Harar Aysha yayi, batareda yace komaiba yajuya zai fita, mama saina dawo. To babana ALLAH ya tsare. Ameen mama yafita zuciyarsa Na k'una, Dan kukan Aysha da ranshincin abincinta yanada nasaba da aurensa da aka sakatayi dole. Ya cije le6ensa yayinda yake kutsa kansa 6angaren momynsa. Su Hasnah kawai ya Tatar afalo, suka gaidashi. Batareda ya amsa ba yace ina momy?. Husnah tace tafita tun d'azun. Fita kuma? Wajen aiki?. A'a gaskiya, koma wanka batayiba, kuma ita ta tuk'a kanta. Shiru yayi yana nazarin inataje da sassafen nan?. Yajuya yafita dad'an hanzarinsa..............✍ 💋💋💋💋💋💋💋💋😍 [9/6, 5:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 3⃣ 6angaren baffah yaje suka gaisa, saidai baiji dad'in yanda baffan yamasaba, Dan baisakar masa fuskaba kamar yanda yasaba masa. Kasa tashi yayi daga gaban baffah, yay shiru kansa ak'asa ya tsurama carpet ido. Baffah dake kallonsa a sace yace bawajen aiki zakaje baneba?. Eh can zanje baffah. To katashi karka makara. Shiru ya khaleel yayi, yakasa tashi, wannan yakuma tabbatar masa baffah fushi yakeyi, inba hakanba daya hanashi fitar, zaice hannunsa bai gama warkewaba aii. Muryarsa cikeda d'aci yace kayi hak'uri baffah, inhar abinda yafaru jiyane ya6ata maka rai, ni bazan bijirema umarninkaba. Sanyi baffah yaji azuciyarsa, ya sauke ajiyar zuciya tareda guntun murmushi, shikenan mu'azzam, ALLAH yayi maka albarka, naji dad'in kasancewarka d'a nagari, amma wacece Aleeya?. K'asa yakumayi dakansa, muryarsa a sark'e yace baffah ban santaba. Bangane Baka santaba? Ba itace momynka tace kanasoba?. Humm baffah maganar gaskiya itace dama tace Na aureta, to nafad'a mata zanyi bincike akan yarinyar tukkunna, to bammayiba wannan al'amarin yafaru. Kai laurah kenan, to shikenan, kabincika d'in, inhar kaga itama tamaka saika fad'a mana, insha ALLAH zan had'a makasu Dan farincikinka. Zuciyarsa kamar zata faso k'irjimsa ta fito, yace to baffah, bara naje akwai aikin dazanyi. Shikenan, ammafa Kasan hannun nan naka da sauransa, saika kula, idankuma kadawo inaso ganinka. To, Insha ALLAH baffah. Yafita baffah nabinsa da k'yak'yk'yawar addu'a, tareda tausayinsa, yaron yanada halayya mai k'yau, ko kad'an bai biyo halin laurah ba, wannan yasaka yake matak'ar tausaya masa, saboda shikad'aine a samarin y'ay'an nasa bai more uwaba, damma Bilkeesu Na jansa ajikintane, shiyyasa yak'e k'ara k'aunar matar sosai. Koda yashiga wajen Ammah saiya taras bata tashiba. Fitowa yayi indasu Adams ke jiransa. Da sauri sukayi salute nasa atare, tareda tambayarsa hannunsa. Ya amsa musu murya a cinkushe, hakan ya tabbatar musu yau ogansu yana tareda damuwa. Da sauri Adams yabud'e masa motar tsakkiya yashiga. Yazauna yanamai lumshe idanunsa daduk suka canja kala zuwa jaa tun jiya. Motar tayi tsit, bakajin komai sai k'arar AC. Idanunsa a lumshe yace, "Adams wad'anda sukabi bayan Barau sun dawone?". Eh sir!, sundawo jiya da daddare, ammafa basu sameshiba, saidai sunkuma kamo yaronsa 1. Shiru yayi baice komaiba, har Adams yad'an kalleshi ta madubi, ganin idonsa a lumshe saiya d'auka ko barci ya d'aukeshine. Saida suka shigo katafaren Setesion d'in Nasu, Wanda yagama had'uwa, Dan yanada banbanci Dana ainahin police, Ahankali ya bud'e baki yace Adams muje d'akin bincike. Kakiramin juned da Faruk, Solomon, sai Taheer. OK sir!, Adams yafad'a yana fita amotar da sauri. Emmanuel yafito yabud'e masa motar, suma sauran securities d'in dake sauran motocin suka fito. Tafiya yakeyi cikin kasaitarsa da jarumta, saidai yanayinsa ya nuna baida k'arfin zuciya a yau. Sai gaisuwa k'ananun Securitys keyi tareda salutes nasa, hannu kawai yake d'aga musu, amma ko kallonsu bayayi. d'akin dasuka shiga ya tabbatarmin lallai d'akin bincikenne, ko ina Na d'akin zagaye yake da computers, d'akin kansa da zallar glass akayishi, akwai mutane aciki sunata danne-dannen computers, wasu kuma rubuce-rubuce, kowa dai da uzirinsa, duk sanye suke cikin Uniform d'in police masu tambarin interpol abaya. Shigowar ya khaleel tasakasu mik'ewa gaba d'aya, suka k'ame tareda salutea nasa atare. Wasu kujeru dake gefe a shirye yaje ya zauna, duk wani ma'aikaci dake awajen yadawo gabansa ya tsaya, sunyi tsit suna sauraren abinda zai fad'a. Saida yagama k'are musu kallo tareda nazarinsu su duka, bai yarda yayi aiki da kowanne acikinsuba, Dan yanada tabbacin akwai munafukai acikinsu, ya sauke numfashi alokaci d'aya da furzar da huci. Sannan yagyara zamansa, yakuma kafesu da idanu, suma kowannensu idonsa Na Kansu, wani Na hango acikinsu sai ta6e baki yakeyi da hararar ya khaleel a fakaice, (araina nace gaskiyar ya khaleel fa, akwai muna fukai acikinsu)..... Maganar ya khaleel ce takatsemin tunanina namaida hankalina akansa, jinayi yana fad'in, kuje duk d'inku nabaku hutun kwanaki 5, yau tsawon watanni 4 kenan dabaku aikin bincike akan Godwin amma babu wani kwakwkwarar magana, idan naso yin aikin da kaina zanyi nagano acikin kwana 1 kacal, amma ku sai yawo da hankali kukemin ko? Saboda anbaku aikin dayafi nawa muhimmanci, OK banida matsala daku, kuje Ku huta, amma Ku tabbatar idan har nagano saka hannun waninku wajen 6atamin aiki da akayi 3weeks daya wuce wlhy saiya raina kansa, kunsan halina basai wani yabaku labariba, zaku iya tafiya. Jikinsu duk asanyaye suka fara had'a kayansu suna ficewa, wasunsu basuda laifi, sakasu akayi akan dole, Wanda yake Harar ya khaleel kuwa sai jinjina kai yakeyi da cije le6e. Adams nakula dashi, yay dariya azuciyarsa, yana fad'in zakayi mai daliline alokacin da boss yakamaka dumu-dumu a hannunsa. Bayan duk sun fice ya khaleel yamaida kallonsa kan su Adams. Solomon & Juned kuyimin bincike akan dawa-dawaye a contact d'in barau modibbo, sannan da mutum nawa yake hud'a arana. Kai kuma Taheer kaida Faruk kumin binciken asusun bankin barau modibbo, da adadin kud'ad'en dake cikinsu, Kausar da Mahmud kuma inaso duk wani airport dake Nigeria ahana barau modibbo jirgi yatashi dashi, dadukkan wani abinsa mai muhimmanci kada yayi aiki, irinsu I'd cart dadai sauransu. Banason kuskure, Ku kula sosai akan abinda zakuyi, danshi tsuntsune mai wayo, *Tsuntsu mai wayo kuma, tabaki ake kamashi*. OK Sir!. Suka fad'a atare gaba d'aya. Wani 6angare daban Na d'akin suka shiga, Adams ya kunna dukkan computers d'ikin, dandanan komai yakawo wuta, kowa yazauna gaban computer d'aya, shiru kakeji babu wani mai motsi, saina k'arar danne-danne, ya khaleel natsaye akansu saikace malami da d'alibai a d'akin exam. Faruk yad'ago yana fad'in lallai wannan mutumin d'an cakwakiyane, asusun bankinsafa kusan 16 ne, aciki da wajen k'asarnan, kai d'an bala'ine wannan wlhy sir. d'aure fuska ya khaleel yayi, yace Faruk ka kula, bawasane yataramu ananba, banason shashanci. Da sauri Faruk yace sorry sir. Kausar tace, "sir! Gashifa yana shirin barin k'asar ta Kano state, jirginsa zai d'aga zuwa k'asar Germany da k'arfe 5pm. K'arasowa ya khaleel yayi inda suke, yaja kujera ya zauna kusadasu, computer tamatso masa da ita, yasaka siririn farin glass a idonsa yafara dubawa anutse. Le6ensa ya cije sannan yafara danne-danne, zuwacan yace Adams?. Da sauri Adams ya amsa da yes sir!. Kiramin number d'in Captain Salis muzambil. OK Sir!. Da sauri yafara laluben number a contact d'in ya khaleel, babu dad'ewa yasameshi, saidai bai d'agaba, yakuma kira a alokaci nabiyu, saida takusa tsinkewa yad'aga, da sauri Adams ya karama ya khaleel a kunne, muryar Captain salis yajiyo yana fad'in sorry j! Wlhy ina wani aikine kana lfy?. Lfy lau Captain, ya aikinka?. Alhmdllh, kaima yanaka?. Munata fama fa. Captain please akwai jirgin dazai tashi yau zuwa Germany?. Yes, Of course j!, akwai 5pm, zakayi tafiyane?. A'a, INA wani bincikene, ngd sosai OK thanks you j!. Karka damu. Cire wayar yayi daga kunnensa tareda turama kausar computer d'in gabanta. Yamik'e tsaye yana fad'in Adams inaso atura security report zuwa Immigration office yanzu da hanzari, dansuyi seizing d'in passport d'in barau modibbo, adakatar dashi daga barin k'asar. Ok sir!. cigaba da musu bayani da dabarun dazasubi wajen tafiyar aikinsu, duk kuwa da dukansu gwarazane akan sanin sirrin computer... _____________________________ Saida mama tayima Aysha tsiya sannan tad'an saki jikinta, ita mamakima abin kebata, to kodama can hasashenta baiyi daidaiba akan ko Aysha nasan khaleel d'in?. Duk Wanda yaga halin da ayshar take ciki tun ajiya zai tabbatar batason aurenne?. Amma tasan yanda zata 6ulloma lamarin kodan ta ku6tar da marainiyar y'arta. Aysha kam bayan tayi wanka saita d'auki wayarta takoma can bayan d'akunan gidan, Number d'in Anty meerah takira, babu dad'ewa tad'aga. Tana d'agawa tasaki kuka, cikin mamaki meerah tace k! Lfyarki kuwa? Ko wanine yarasu?. A'a, Aysha tafad'a cikin shashshekar kuka. Tomiya faru?. Aysha Na kuka ta zayyanema meerah komai, a mamakin aysha saitaji meerah ta daddage ta rangad'a gud'a. Da sauri Aysha ta janye wayar daga kunnenta, saida ta tabbatar Anty meerah tagama sannan tamaida wayar tana kuma rushewa da kukan. Kai kujimin sakara, tomiye abin kukan kuma, ALLAH ya cika miki burinki, baki ta6a zaton zaki samu khaleel a matsayin mijin aureba, amma cikin sauk'i ALLAH yabakishi, ko yanzu kin daina sonsane?. Nifa Anty meerah bawai Na daina sonsa bane, amma naso ace koda zan sameshi sai burinmu yacika akansu hajia babba tukunna, yanzu yaza'ayi ina auremsa nasamu damar d'aukar fansa akan abinda mahaifiyarsa tamin?. Yo aii wannan shinema mai sauk'i Aysha, kada ki 6ata abin farincikin d'aya samemu da bak'incikin mak'iyanmu, yanzudai kibari gobe idan ALLAH ya kaimu zamu dawo Abuja, idan nazo zamu tattauna, harda batun message da aka miki akan gwaggo bintu, danni abin yafa d'auremin kai, nayi iya hasashena nagaza binciko ko wanene?. Wlhy bake kad'aiba Anty meerah, ina cikin son gano wanene, aka kuma hargitsamin kwakwalwa da maganarnan, yanzudai saikin dawo d'in sannan, agaidamin mom da Raudat dasu Safwan. OK saimun dawo, zasuji. ___________________________ Hajia babba kam gidan hajia khaltum taje da sanyin safiyarnan. Koma barci basu tashiba, itace ta tashesu, Aminiya lfy kuwa da farra safiyarnan?. Inafa lfy aminiya, inacikin tashin hankali wlhy, wai Alhaji yarasa da wadda zai had'a Ibraheem aure sai jinin fad'ima makiyyata. 😳bangane mikike nufiba. Mtsowww wataran kemafa sai ahankali, to Alhaji ne jiya da daddare yataramu shida munafukar tsohuwarnan, wlhy dabadan yayar mahaifiyata baceba dasaina saka an6atar min da ita............takwashe duk abinda yafaru tasanar mata. Humm lallaima Alhaji Abdallah, mijinnan nakifa shima akwai taurinkan tsiya, to inbanda abinsa yama za'ayi yahad'a jinin kura da kare a rami d'aya? Ke baki fad'a masaba Ibraheem d'in yanada wadda zai aura. Na nawa kuma?, nafad'a shegiyar tsohuwarnan tace aure babu fashi, yakikeso nayi? Wlhy kullum addu'a nakeyi ALLAH ya kashe jemammar tsohuwarnan muhuta, danni itace kawai matsalata agidan, tashigemin hanci, narasa yanda zan fyatota tafito wlhy. K'yakkkkh aii insun San wata basu san wataba, kibarsu suyi auren kawai. Kamarya nabarsu aminiya? Kinsan kuwa mikike fad'a?. Hhhh nikuwa nasani aminiya, kawo kunnenki kiji. Da sauri hajia babba tamik'a kunnenta, hajia khaltum ta gwargwad'a mata maganar, dariya suka kwashe da ita harda tafawa, hajia babba tace wannan shawara tayi aminiya, kinga daga baya sai ayi bikinsu da Aleeya. Yauwa kokefa, dad'ina dake akwai fahimta wlhy, da duk kinbi kin tashi hankalinki abanza. Hummm kibari kawai, wlhy jiya ko barcima banyiba, yanda naga rana haka naga dare, amma yanzu zuciyata sakayau wlhy. Hhhhhhh to mud'in Na wasane aminiya.....suka kwashe da dariya suna tafawa😂🖐🏽🖐😂. saikace wasu k'ananun yara😏. ___________________ Gwaggo bintu nad'akinta Na 6angaren mama, zaune take abakin gado ta rabga uban tagumi, abin duniya dukya isheta, mamaki takeyi duk yanda ta k'untata rayuwar Aysha abaya amma yanzu taketa Neman hanyar kubtar da ita, anya kuwa bawani abu Aysha ke shiryama rayuwartaba? Kai Lamarin da mamaki gaskiya.....da sauri tad'ago kanta danjin alamar shigowar mutum. Mamace tashigo d'akin NATA. A'a bintu lfy kuwa?. Cikin kame-kame tace babu komai fad'ima, amma Dan girman ALLAH kiyafemin abubuwan danamiki lokacin kina gidan Yaya, wlhy sharrin shaid'anne, tabbas ke mutuniyar kirkice, tunda baki dubi halayena Na bayaba kika taimakamin, ngd sosai. Murmushi mama tayi tareda zama bakin gadon itama, babu komai bintu, aii yarigaya yawuce, nayafe miki, kowa yana kuskure arayuwarsa aii. Gwaggo bintu ta jinjinakai tana share hawaye, dasake jinjina k'yak'yk'yawar zuciya irin ta mama, dukda tanada fad'a amma mutumce mai matuk'ar sauk'inkai idan ka iya zama da ita. Nikam bintu wai Dan ALLAH waye yakai Aysha karatu k'asar waje agidanan?...............✍🏿 One Love my Fan's😍😍😍😍😍💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤❤ [9/6, 5:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 4⃣ Bak'aramar fad'uwa gaban gwaggo bintu yayiba, tuni har zufa tafara ketowa a sassan jikinta, tuna gargad'in daya matane yasakata saita kanta da sauri, murya adake tace fad'ima Wanda ya kai Aysha karatu yace karna fad'a. Bara namiki dallah-dallah yanda zaki fahimceni, lokacin danazo da Aysha gidannan kowa ya tausaya mata, sannan kuma Aysha tacigaba da tayani y'an ayyukan gida nakeyi, wannan yasakashi kirana gefe yamin tanbayoyi akan Aysha, ban 6oye masa komaiba Na sanar masa, shine yace zai taimaka mata taje makaranta, abinda yasa aka danganta tafiyar tata da taimakon mai ciki danku barine, nasan kai tsaye Yaya bilyamin bazai yarda Aysha tatafi karatu wata k'asaba. Amma Dan ALLAH ki fahimceni, shi yace domin ALLAH yayi, shiyyasa bayason kowa yasani. Ajiyar zuciya mama ta sauke, danta yarda da zancen Na gwaggo bintu. Tace, "to amma miyasa tunda Aysha tatafi karatu bakizo kano ba? Har bikinsu Hafsat amma babuke?. Hakane, hakan tafaru sakamakon Lagos danaje kulada zuwairah d'iyar hajia babba, tasamu ciki yana bata matsalane daga Bayama ta haifu d'an babu rai, wlhy fad'ima nasha wahala awajenta itada y'ay'anta, wannan dalilinne yasaka harnayi jiyyarnan a asibiti. To bintu rayuwa sai hak'uri aii, gashi yawuce kamar ma ba'ayiba. Aysha dake jikin k'ofa la6e tasaki ajiyar zuciya tareda fad'in Alhamdllh. Da sauri tabar jikin k'ofar danjin alamun mama zata fito... _____________________ Hankalin barau modibbo atashe yake sosai, Dan antabatar masa jirgi bazai tashi dashiba, hukumar shigi da fici ta k'asa tayi seizing d'in passport d'insa. Baigama fita daga wannan rikitarba yaga alamun rufe asusun bankunansa da akayi gaba d'aya, zuface tafa keto mata addukan sassan jikinsa, cikin sassarfa yake fitowa daga airport d'in tamkar zai kifa k'asa, yaransa biyu nabinsa abaya, sukansu akid'imen suke🤣. _______________________ Muna saurarenka j, tund'azun ka kiramu amma kayi shiru ka kasa magana, shin meke damunkane haka? Nifa tunda safe nafuskanci bakada walwala gaskiya. Ajiyar zuciya ya khaleel ya sauke, cikin cije le6ensa yace hakane Taheer, inacikin matsala gaskiya. Joseph yace matsalarmi j!?, idan akan kama barau modibbo ne aimun d'akko hanya, ko yanzu mukaso kamashi zamu kamashi. Ba wannanne matsalarba Joseph. To miye? Cewar youseef?. Aure!. Aure!! Kuma? Kakeson yi?. d'an Harar Taheer d'in yayi, ya gyara zamansa sosai, muryarsa cinkushe da d'aci yabasu labarin komai daya faru, dan ya yarda dasu, bashida abokan dasuka San sirrinsa sama dasu d'in, suma duk kukansu shi suke fad'amawa. Gaba d'aya suka kwashe da dariya, sai faman ta6awa sukeyi, tsantsar farinciki ta bayyana a fuskar kowannensu, Youseef yace alhmdllh j!, gaskiya mundad'e bamuyi makamancin farincikin nanba, dama kullum damuwarmu zamuyi aure mu barka, abin Na matuk'ar cin zuciyarmu, lallai Ubangijinmu ya kar6i addu'oinmu, ALLAH nun gode maka. K'aramin tsaki yayi yana Harar youseef d'in, kai Malam bamaganar wasa nakeyibafa, ya ina fad'a muku damuwata zaku maidani wani shakatafi?. Nifa banason aurennan, kuma bansan hanyar dazanbi Na yakiceshiba saboda baffah, please kubani shawara mana. Amma miyasa baka son auren j!?. Saboda bana sonta Joseph. Tab, nifa kana bani mamaki wlhy, tokai wa kakeso kuwa arayuwarka? Banta6a ganin kayi budurwaba tunda nake, shin bazakayi aure baneba arayuwarka, kome? Katuna addininkufa yabaku damar auren har mata hud'u, kaiko ko d'ayarma ka kasa kayi, badole baffah yaza6a maka da kansaba. Kunga duk wannan cecekucen baima tasoba, j! Kafad'a manane danmubaka shawara?. Khaleel ya jinjina kansa. To inhar shawararmu kake nema, kama iyayenka biyayya, tunda kagadai bawata kakesoba barema kace saboda soyayyartane, insha ALLAH darajar biyayyar dazakaimusu nangaba saika sota fiyema da tunanin mai hankali. Kaga saura 4weeks kawai bikin Joseph, daga nan saina youseef, nima Dady yasanarmin zuwa jibi za'a saka ranar aurena, kai kad'aine dama damuwarmu, to ALLAH ya yaye mana, kawai kayi hak'uri musha biki please, dukda bansan yarinyarba, nasan baffah bazai maka za6in banzaba wlhy, eyeeee angonba, harfa kafara k'yallin goshi Na angwanci.😜😆. Taheer yak'are maganar da tsokana. Gaba d'aya suka kwashe dadriya, amma banda khaleel Wanda yaja tsaki yana fad'in d'an iska kawai, aikai matsalarka kenan mtsoww!. Hhhhhhhh karka wani doje wlhy, nasan muna funcika j!, akwaika da taku akan Abu, saikayi kamar baka damuba, amma k'asan ranka kana son abin.🤨 Azumin dakakeyi wani lokaci namiye?. Na k'aniyarkane mara mutunci, tashi kabarmin office d'an iska kawai. Hhh ai wlhy babu inda zanje sai ankai k'arshen maganar nan dani, dolene shirin yazama Na musamman, dukfa d'aurewar nan taka ranar saikayi shaku-shaku da babbar riga Alhaji. 😂dariya suka kwashe da'ita suduka, harda khaleel, zan iya cewa yaune karan farko danaga yayi dariyar da har hakwaransa suka fito fili. Wlhy yaronnan bakada kirki, cewar ya khaleel yana nuna Taheer. Bayan sun tsagaita da dariyar khaleel yace kud'in abokaine Na gari, wad'anda suke taka rawar gani a sashen tarihin gwagwar mayar rayuwar Ibraheem Abdallah, babu abinda zan cemuku saidai naita mana addu'ar cin ribar abota har a aljanna. Ameen suka amsa gaba d'aya. Joseph yace, "ansaka rana kenan?". Kwanciya khaleel yayi jikin kujera, muryarsa a sanyaye yace basu sakaba, amma yau uncle ma'aruff nacan Kano zasu tattauna da iyayenta. To ALLAH ya sanya alkairi. Yasa ayi damu kuma, wlhy harna k'agara naga mai sa'ar data samu wannan jarumin jarumai, mai k'yak'yk'yawar zuciya da rik'on gaskiya, mai martaba k'asarsa da kare mutuncin al'ummar cikinta, koda basusan dashiba. Wlhy zancenka gaskiyane youseef, boss nadabanne acikin mutane, samun irinsa saida kwakkwaran bincike irinna masu hikima, da'ana samun ma'aikata jarumai marasa tsoro da kwad'ayi irinka da kasarmu bata lalace hakaba, saidai kash ru6a66un dasuke saida mutuncin k'asar tamu saboda kud'u sunfi nagartattun masu gaskiya irinka yawa, gashi kuma har yanzu al'ummar dake cikin k'asar basu fargaba, saboda *_KABILANCI DA 6ANGARANCI_* n dayayi tasiri aruhinsu, ga saka mana k'yamatar addinin juna da'akeyi, koda yake ba laifinmu baneba, laifin manyanmune, suna haddasa mana fad'ace-fad'acen addini saboda cikar gur6ataccen burinsu akan siyasa, mafi yawan fad'a da'akeyi ak'asarnan y'an siyaysane ke shiryashi, amma da tafiya tafara nisa saiya zama fad'an yazama na addini, wannan wace iriyar masiface, mund'auki amanar kanmu mun dank'a ga siyasa, wadda dama an kawo mana itane danta wargaza kanmu,, sai d'an siyasa ya d'auki mak'udan kud'i yabama Malamai da pastors, kaga sunata 6a6atu da cusawa jama'arsu mummunar ak'ida azukata, amma da tashin hankali zaizo duk kwashe y'ay'ansu da matansu zasuyi da kud'inmu subar k'asar, wad'anda suka kasance malaman kwarai acikinsu sai adinga binsu d'ai-d'ai ana kashe manasu, shin jama'armu bazasu farka daga nannauyan barcin daya d'aukesu baneba? Su nutsu wajen gano nagartattu irinsu khaleel a k'asarmu? Duk mutum mai gaskiyade zakaga bashida Pawer d'in hidimtawa al'ummar kasarmu, saboda mak'iya masu gur6atattun halayen dasuka raba hanya da halayensa na warai sune zagaye dashi. Hakane Taheer, amma aii mungodema ALLAH, tunda Anfara walk'iya munkuma fara tsinto k'asurguman munafukai, kuma tabbas y'ar manuniya zata cigaba da nuna manasu insha ALLAH, talakawanmu kuma dasuka kasa gano gaskiya haryanzu saboda rashin sanin ciwonkai ALLAH ya farkar dasu kafin lokaci ya k'ure musu. Ya khaleel dabaice komaiba Tun d'azun yace amin Joseph, saidai akullum ina tuna muku duk abinda zanyi da taimakonkune, kuma bazan ta6a amsa sunan waneba saida sunanku aciki, wannan zancen naku saiya tunamin dawani Abu mai muhimmanci dayake araina tuntuni. Atare sukace wane Abu kenan?. Saida yad'ago daga kwancen dayake akujera sannan yace yakamata mu kafa kungiyar taimakon matasa, wasu sun kammala karatu babu aikinyi, mukar6i takardunsu mu nema musu guraban aiiki, wasu rashin gata yasaka ko karatunma basuyiba, mu koya musu Sana'a dabasu jari, wasu kuwa karatunne ya yanke saboda babu kud'in k'arasashi, mu taimaka musu su gama, yakamata mu juya akalar zukatan matasanmu su farka daga ra'ayin karatu nayi danhaka sai aikin gwamnati, gwamnatin k'asarmu batada k'arfin d'aukar dukkan matasanmu suzama a k'ark'ashinta, amma idan ana jansu ajiki, danuna musu basaita silar gwamnati asiri ke rufuwaba, k'asar zata zauna lafiya, ataimakesu wajen ciremusu burin sainayi kud'i nima kamar wane, wannan zairagema k'asarmu cin hanci da rashawa, ta'addanci da k'abilanci harma da fad'an addini, za'a daina wawaso akan dukiyar y'an k'asa, wadda zakaga mutum shikad'ai yatara biliyoyin kud'i, kama rasa mizaiyi dasune? Ga gidaje da hannayen jari, jikokin jikokinsama bazasuyi talauciba, kaga mutum d'aya da mota ashirin shikad'ai, sannan duk y'angidansu kowa nada sama da biyu, kai wlhy idan kaje wani gidan saika d'auka anan ake k'era motoci saboda tsabar fariyya, to ba kud'insa baneba, hak'in al'ummar k'asane, shiyyasa baisan ciwonsuba, yawancin zakaga y'ay'ansune y'an cocaine, kuma sune ke shigomana daduk wani kayan maye ak'asarmu, saboda inama talaka yasamu abinda zaici? Bare yazama d'an safarar miyagun kwayoyi?. Abinda ke matuk'ar tada hankalina shine, bayan satar kud'inmu dasukayi, sukabama y'ay'ansu sukaje suka siyo kayan maye da kud'in, saikuma adawo dashi cikin y'ay'an talakawa ana saida musu domin gu6ata tarbiyarsu, baza'a barmu muji da zafin talaucin daya ishemubama. Sometimes idan kaga d'an talaka yazama d'an ta'adda wlhy zafin talaucine da bak'incikin zalincin da manyan k'asarmu keyi akanmu, ko shaye-shayen nan da y'anmata sukeyi duk silar masifar da'aka jefamune, kuma wlhy wasu sunkoyone wajen y'ay'an manyan, k'awaye ko samari, saboda shegen kwad'ayinsu, Dan muma talakawan wani lokacin bamusan darajar kanmuba wlhy, bamusan ciwon kanmuba, kowa burinsa ace dashi wane. Why!!!!?. My friends why!!?. Wace iriyar rayuwa mukeyi aduniyarmu? Miyasa muke mantawa da mutuwane? Miyasa muke mantawa akwai ranar hisabi? Ranar da kowa zai baje kolin ayyukansa a kasuwar daba'a ta6a Tara irintaba?. Wlhy muji tsoron ALLAH, mukiyayi ranar da ALLAH zai kamamu, Duk shagalar dazakayi duniya karunga tuna watarana zaka *MUTU*, ko shekaru millions aka Baka saisun k'are, kafinkai anyi manyan tantirai aduniya wad'anda suka fika shara aduniyarma amma sunzama labari, tofa kaima watarana saidai labarin, kuma bayankama za'ayi wad'anda suka fika, ammafa muringa tunawa akwai *WUTA DA ALJANNAH* kuma kowacce zata samu jama'a. Suduka jikinsu yayi sanyi da jawabin nasa. Murya a sanyaye sukace sun bada goyen baya, Dan haka saisu fara shirin yanda zasu kafa k'ungiyar. Alhmdllh naji dad'in amincewarku y'an uwana, nayi wannan tunanin saboda dubi da albashinmu alhamdllh. Ko aure mukayi zai ishemu rik'e iyalanmu harma da saura, gakuma y'an kasuwancin damukeyi a bayan fage, to damu tarasu abanza alhalin gamasu buk'ata nan aii gara muyi abinda ko bayan ranmu baza'a manta damuba, nifa banida burin barma y'ay'ana d'unbin dukiya dansu gada, Nafi burin natsaya tsayin daka akansu dansu sami ilimin addini dana zamani watarana suma sunema da Kansu, dansusan wahalar nema, mizaisa Natara musu dukiya sudunga k'agarama Na mutu dansu gada, bayan mutuwar tawa suje suyita iskanci anamin azaba akabarina, _(da abaka gasashshen kifi, gara akoya maka yanda ake kamunsa a rafi)._ Gaskiyane wannan, kuma duk munyi mubayi'a, ALLAH yamana jagora. Haka sukaita tattaunawa har zuwa dare, sanan kowa yanufi gidansa. ____________________ Khaleel zaune agaban baffah da uncle ma'aruff dayazo yau, sai Ammah, kansa ak'asa yana sauraren iyayen nasa. Uncle ma'aruff yay garan murya irintasu ta manya, idonsa akan khaleel d'in, cikin murmushi yace khaleel anzama manya kenan? ALLAH ya sanya alkairi. Ammah ta amsa da ameen. Alhmdllh munje anyi maganar aurenka da sirikanka mutanan kirki, komai nasu cikin turban addini da yanda ALLAH yace muyi. Sun yanke mana ranar d'aurin aure nanda watanni 6, saboda sunce ansaka bikin y'an uwanta dama su hud'u, to an daidaita danasu d'in, kaga yakama cikin sabuwar shekara watan biyu. Sun yanke sadaki naira dubu 50k kacal, dan albarka ake nema acikin auren. Ya khaleel yakuma yin k'asa da kansa, dama can shi mutumne mai kunya, shiyyas kaf yaran gidan babu Wanda zaice gashi yata6a ganin ya khaleel da ko sitirar dazata fidda masa jiki. Baffah yakatse tunaninsa dafad'in yauwa mu'azzam saika za6i 6angaren dayay maka a filayenku dake baya Dan afara ginawa, kakuma za6i kalar dakake buk'ata kamar yanda sauran y'an uwanka sukayi su Sultan. To baffah ngd sosai ALLAH yak'ara bud'i. Gaba d'aya suka amsa da ameen, sund'an cigaba da tattaunawa akan bikin, amma khaleel yayi d'if, baya cewa uffan. Hardai uncle ma'aruff ya fuskanci kunya yakeji, Dan haka yace yatashi yaje ya kwanta ya huta. Godiya yamusu tareda sallama yafice. Yana shiga falon Aysha Na fitowa da gudu daga d'akinsu, rik'e take da wayar fadeelah tana danna wani Abu, fadeelah kuma nabinta tana rok'onta da Aysha karki tura masa, ALLAH banason haka, Aysha karfa kitura. Hhh wlhy Yaya fadeelah dama kin hak'ura, yo haka akeyi baza'a turama bawan ALLAH kalaman soyayyaba, bayan yayi hak'uri kusan wata uku kinwani mak'ale wankan jego......... Maganar ta mak'ale mata amak'oshi saboda shigowarsa. Atare suka kalli juna, ya harareta ta murgid'a baki. Mamakin rashin kunyar yarinyarnan yakeyi, ko kad'an batajin tsoronsa, yarasa miyasa haka?, shiba rayuwa yayi a waje d'aya da itaba, ko k'annensa basu masa haka, ko mufeeda datake sakonsa sotsonsa takeji, haka duk jarabar Anty Zuwairah yayarsu shakkarsa takeji, amma wannan y'ar ficiciyar yarinyar take masa yanda ta gadama. Kwafa yayi yashige 6angaren momynsa. Aysha takuma murgud'a baki da harar bayansa tana k'unk'unai. Ahaka fadeelah tazo ta kwace wayarta tana fad'in mara kunya, watarana koda kud'i akace kimasa bazakiyiba wlhy, Arana d'aya kacal zai koyamiki hankali. Bata jira cewar ayshar ba tabar wajen. Itama bin bayanta tayi tana k'unk'uni. Nace hummm su Aysha ammata😂, zaki magantune indai ya khaleel ne😜. Afalo ya iske Momy, kallon datake masa kawai yasaka jikinsa sanyi.. Ita kad'aice afalon, guywa a sa6ule yak'arasa cikin falon..................✍🏿 😍😍😍😍😍😘 [9/6, 5:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 5⃣ Zama yayi kujerar dake kallonta, momy barka da dare. Adak'ile tace barka. Shiru babu Wanda yasake cewa uffan, hajia babba sai cika takeyi tana batsewa, Dan jitake tamkar karta amince da shawarar hajia khaltume, amma kuma wani 6angare Na zuciyarta Na nunamata hakan shine dai-dai. Ta saci kallon khaleel d'in Wanda idonsa ke kan TV, amma azahirin gaskiya yana nazarin momyne..... Ibraheem!!. Na'am momy! Ya amsa yana maido kallonsa akanta. Na amince da aurenka, amma da sharad'i. Shiru yayi yana saurarenta, gakuma maganar tata ta dakesa, Dan baiyi tunanin yardarta da wuri hakaba. Amma momy miyasa kika amice? Miye kuma sharad'in?. Karka damu da dalilin amincewata, wannan sirri nane, sharad'in kuma shine nangaba zaka auri Aleeya itama. Wani guntun murmushi yayi, Wanda yafi kuka ciwo, ya kauda kai daga kallonta yana cije le6ensa Na k'asa, babu damuwa momy ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi. Tsura masa idanu tayi cikeda mamakinsa, ko kad'an batayi zaton taurin kansa zai saka ya aminceba cikin sauk'i, anya kuwa bawani Abu yaronnan yake shiryawaba? Koda yake ance basu kama barau modibbo ba. Yana kallon, kallon da momy kemasa da gefen idonsa, aransa yay k'aramar dariya, yana fad'in momy kenan, *'DAN HAKKIN DAKA RAINAFA....* shike tsone maka ido watarana. Afili kuma yace momy kokinada damuwane?. A'a Ibraheem babu komai, amma yanzu ina zaka zauna?. Zan zauna inda gidana Na Asokoro. A'a kazauna anan gidan, kaima indasu mujahedeen sukayi gini. Miyasa momy? Kefa kikace bakiso Na zauna agidannan da matana idan nayi aure, miyasa kuma yanzu zaki canja?. Haka kawai. Ananma dariya yayi azuciyarsa, afili kuma yace shikenan momy duk yanda kikeso haka za'ayi to. Farin cikine ya lullu6e kasan ranta, Dan ganin duk abinda tace baya mata musu. Daga nan tasaki fuska sukad'an ta6a hira, cikin hikima irinnansu Na manya take sako masa tambayoyi akan aikinsa. Amsa yake bata kai tsaye batareda tunanin miye manufartaba. Itakam dad'i takeji yau tasami Ibraheem yanda takeso. ___________________________ Washe gari girkin mama, bayan tagama had'ama baffah breakfast agabansa tace Alhaji su Aysha zasu koma gida zuwa jibe idan ALLAH ya kaimu, Dan fadeelah zata koma d'akinta mijinta NATA waya. d'ago idanunsa yayi yana kallon mama, baice komaiba yacigaba dacin abincinsa, saida ya mammala tsaf sannan ya fuskanceta sosai, fad'ima fadila ce kawai zata koma, amma Aysha tazo kenan, Dan bilyamin yabani, ita kanta fadeelah badan aure takeba da babu inda zataje, akoda yaushe inaso ki gane sud'in y'ay'a nane koda banine mahaifinsuba, inajinsu azuciyata tamkar su Mu'azzam wlhy. Yanzu haka zancennan danake miki angama komai akan bautar k'asar Aysha (NYSCE) insha ALLAH k'arshen watannan zata fara, anan kusadamu. Dan munyi sa'a abin yazo daidai daza'a d'auki sababbi. Hawayene suka cika idonmama saikuma taji kunyar abinda tayi, cikin hikima tabama baffah hak'uri. Murmushi yayi tareda jawota jikinsa ya rungume yana fad'in babu komai first love d'ina, Dan bakisan irin matsayin dakike dashiba azuciyar Abdallah bane shiyyasa kike Raba d'aya biyu, amma namiki uzuri, daga yau karki sake. Dad'ine ya lullu6e mama, Dan itama tana k'aunar mijin NATA, tak'ara k'ank'ameshi da k'yau kamar mai gudun kar'a kwace matashi. 🏃‍♀a 100 nafito, Dan lamarin yafi k'arfina, wannan fagen Na manyane😂 irinsu baffah😉. _____________ Akwana atashi babu wuya wajen ubangiji, rayuwa tanata tafiya, yau kusan watanni uku kenan da saka bikin ya khaleel da Aysha. Saidai babu mai shiga harkar wani shida Aysha, ita bautar k'asar datakeyi ya d'aukema hankalinta gaba d'aya. Shikam yawon k'asashensa yahanashi zama waje d'ayama. Yanzu haka yana Mexico kusan kwanaki 13 kenan, daga nanma France zai sauka a gaba d'aya headquarters d'insu dake Lyon city, sosai aiki ya d'auke hankalinsa a y'an kwankinnan, shiyyasama yakan manta dawata aba Aysha, dama ko number d'inta bashida ita, koyayi waya dasu mama kuma baita6a cewa abataba. Ya gyara kwanciyarsa yana mai tunanin yanda rayuwar aure zata d'ore babu soyayyar juna. K'aramin tsaki yayi, lokacin daya tuno rashin kunyar yarinyar, yatuna bakinnan nata maikama Dana tsuntsu dake masa murgud'e, kwafa yayi tareda fad'in zan kama kine aii afili. Araina nace batama San kanayiba😂. Aysha kam soyayyar ya khaleel Na nan mak'ale aranta, amma tana danne abinta, tareda nuna halin ko inkula akansa, ga cin kashin da y'ay'an hajia babba kemata da habaici akan auren, ita kanta hajia babba ba d'aga mata k'afa takeyiba. Hakan baya damunta Dan aganinta kad'an yarage tayi maganin uwarsuma ba suba. Anty zuwairah ma tazo ta tata tsiya agidan dantaga baffah bayanan, babu cin mutunci dabatayima mama da Aysha ba, saida Ammah tamata tas sannan tabar gidan, tabi jirgi zuwa Lagos Dan tasan gidan bazai kwanu agaretaba, saboda ranar Baffah zai dawo daga Turkey. Sauran yaran kuwa kowa murna yakeyi ya khaleel zaiyi aure, zaikuma auri wacce suka Sani, amma ak'asan ran Zunnurain da musleem sunji babu dad'i, dansun k'yasa Aysha gaskiya😉. 🤣nace boss yamusu wawaso😜 *_2weeks ago_* Misalin 5pm Aysha tafe a hanya, sanye take cikin wando da riga Na Nysce, bak'armin k'yau kayan sukai mataba, tasak'a k'aramin jijjab fari daya k'awata k'yawun haibarta, ta d'aure rigar saman kayan a k'ugunta, tafe take cikin nutsuwarta bayanta rataye da schoolbag, dolene ka kalleta kasake kallo, dukda yanayinta ya nuna a tsorace take. Kad'an kad'an takan kalli sararin samaniyar dayay murutuk alamun hadari ya had'u bana wasaba, kuma ruwa zai iya sauka akowane lokaci, kullum driver ke kawota, idan lokacin tashinsu yayi takirasa ya d'auketa, amma yau takirasa wayarsa arufe, itakuma batason yin dare awaje Dan baffah bayaso, wannan dalilin yasakata hawan napep, saidai sunkusa shigiwa layinsu napep d'in yasamu matsala, ganin zata 6ata lokaci tace bara ta k'arasa kawai ak'afa Dan babu nisa, tama d'an tada jininta. Tafiya tafara dad'an sassarfa saboda iska tafara kad'awa alamun hadarin yafara tasowa, kuka da Neman taimako tafaraji ad'an nesa da ita kad'an, tafara waige-waige damson ganin mai Neman taimakon?. Saitin inda takejin kukan sosai matso, garadan samari biyu tagani suna k'ok'arin tura wata budurwa a mota. Inadanu tazaro waje, tuni wata jarumta tazo mata Dan ganin harsun gama turata mota, d'aya nashirin cire wando, da alama ma amotar suke shirin keta mata haddi, Aysha ta waiga ko ina babu alamar mutum, kowa yashige gida, Dana birnin Abuja dawuya kaga mutane nayawo ak'afa hakanan, ga anguwar dama babu yawan gidaje sai kamfanonu, zuwa yanzu kuma antashi aiki, wani k'arfe ta d'auka a gefen titin, cikin sand'a tak'arasa wajen motar, mai cire wando dahar ya danne d'iyar mutane yana shirin afka mata ta kwalama k'arfen a k'afarsa data fito waje. Azabace tasakashi sakin gigitacciyar k'ara, adaidai nan kuma ruwa ya sakko. d'an daya toshe bakin yarinyar Dan hanata ihu yay saurin sakinta yana fad'in Arfan miya farune? Da sauri yazagayo garesa, ganin Aysha da k'arfe a hannu tana k'ok'arin jawo yarinyar dazasuma fyad'en yace kutumelesi, mikika masa? Wlhy yau sainayi kaca-kaca dake, yay maganar yana damk'e hannun Aysha. Ihu Aysha tafarayi, Wanda takwalama k'arfen shima yataso yana d'ingishi, aii wlhy yau yarinya sai munmiki abinda bazaki sake moruwaba aduniya, ki yankemin jin dad'i sannan ki kwalamin Abu, aii saina fanshe ajikinki Dan ubanki. Suka fara k'ok'arin cire hijjab d'in Aysha. Hankalin budurwarnan yatashi, ganin Aysha ta taimaketa kuma abin ya juya kanta, rasa mizatayi musu tayi, sai kawai takwasa aguje babbar hanya tana kuka dafad'in a taimaketa.... Emanuel! Kamar yarinya nake hange agabanmu tana kuka?.... Eh sir, ammafa Baka tunanin ko wasune suka d'ana mama tarko.... Ya khaleel dake zaune abaya yanata danna lap-top nashi yace mike faruwane Adams?. Babu komai sir, dama wata yarinyace gatacan mund'an wuceta take kuka, shine nace koza'a taimaketa, Emanuel yakecewa k'ila tarkon mak'iyane. Da Sauri ya khaleel yajuya yana kallon bayansu, hango yarinyar yayi tana kuka da gudu tana tsaida motoci, amma babu mai k'ok'arin tsayawa. Emanuel!!! Mujiya, ya khaleel yay maganar cikin matuk'ar tsawa. Aii babu shiru Ema yajuya kan motarsa, sauran motocin suka biyo bayansa. Agabanta suka taka birki, tana ganin haka tabud'e k'ofar baya dasauri tana fad'in Ku taimaka zasu keta mutuncinta, please yayana kataimakeni karsu cutar da ita. Ya khaleel yatsura mata idanu yanason gano ainahin gaskiyarta, ganin yanda take yasakashi gaskatata, da Sauri yafito amotar batareda ya kula umbrella d'in da Adams yasaka masaba saboda ruwan yafara k'arfi. Ita kanta batasan tarik'e hannunsaba tana jansa saboda kid'imewar datayi. Sun k'araso lokacin da samarin ke kokawar cirema Aysha dogon wandonta, amma tarik'e kam tahana, d'ayan sai marinta yakeyi amma tak'i saki, mamakin taurin kanta sukeyi da k'arfi, farar fuskarnan tayi jajur saboda mari, garuwan sama ya jik'asu. Bai tsaya bin ba'asiba yahau jibgarsu. Aysha tamik'e da Sauri tana kuka, ganin ya khaleel yasakata zuwa da sauri Inda yake ta k'ank'amesa tana kuka da fad'in ka taimakeni ya khaleel zasu cutar dani, karka barsu, azzalumaine su..... Gaba d'aya arikice take, sai yanzu ya khaleel yaga Aysha, hankalinsane Yakuma tashi, danhaka ya tureta daga jikinsa tareda damk'osu ya gwara kansu, dukansu yakeyi afusace, dak'yar securitys d'insa suka kwacesu, dansunga zaiyi kisankai. Abirkice yajuyo kan Aysha dake gefe tana mak'yar k'yar sanyi, Dan ruwa aketa tsulawa kamar da bakin kwarya, mari ya falla mata, yana fad'in ubanmi yakawoki nan wajen?!!, nace miya kawoki?!!!!!!!. Cikin matuk'ar tsawa yayi maganar, Dan harsu Adams saida suka zabura Dan tsoro. Aysha tarik'e kumatunta tana matsawa baya saboda tsawar daya daka mata, wani Marin Yakuma kai mata Adams yatareshi yana fad'in please sir cool dawn. Ya cije le6ensa tareda kuma kaimata duka saikuma yafasa ya rumtse hannun yana ciza la66ansa da k'arfi, jiyake tamkar ya had'iye zuciya awajen, ransa amatuk'ar 6ace yake, ya tura hannunsa d'aya a aljihun wandon oxblood d'in suit nasa, dasuka gama jik'ewa da ruwa, idanunsa sunyi jajur, ya watsama Aysha harara yana fad'in Adams kallafa kaga wajennan?, shin miya kawo yarinyarnan har suke shirin k'etaramin gonata? batareda ni Nayi koda gewayentaba?. Yanzu dabamuzoba mikake tunanin zai farune? Mutuncinafa zasu Shiga saboda Mara hankalin yarinyarnan, Na mauje tama nahuta da ganinta. Yay maganar yana ture Adams gefe tareda kaima Aysha wawura. Yanzunma Adams kuma tareshi yayi, dukda bai fahimci zancen ogan nasaba, Dan baisan alak'arsama da yarinyarba. Budurwannan ne tak'araso tana kuka dabama ya khaleel d'in hak'uri, tamasa bayani akan balaifin ayshar baneba, taimakonta tazoyi, itama a d'aya daga kamfanin take aiki, motartace tasamu matsala, daga Neman taimakonsu shine suke shirin mata fyad'e, Aysha ce ta taimaketa. Zuciyarsa tad'anyi sanyi, amma bai huceba, Dan saiyaji ubanwa yasakata biyo hanyarnanma mai had'ari?, ina drivers d'in dake gidansu? Dahar ta taho ak'asa. Ya watsa mata harara dayin kwafa, rigar suit d'insa yazare ya jefa mata, saboda farar rigarta ruwa yajik'ata dukta nuna jikinta, har kalar bra d'inta ana gani. Jikin Aysha Na rawa tad'auka tasaka, dama Duk kunya tagama isarta. Dariya nayi azuciyata, Dan hannun rigar yamata tsawo, gata tayi tsumu arigar kamar antsamo zomo aruwa🤣🤣. Da kansa ya tattara kayanta, bag d'inta da hijjab, sai lemon green d'in rigarta data d'aure k'ugu, ijjab d'in yakuma jefa mata tasaka, dukda gyararren gashinta data d'aure a tsakkiya yagama jik'ewa jalab da ruwa bar d'iga yakeyi. Yadaka mata tsawa, bazaki shige mujeba saina 6alla kasuuswanki anan...... Bata bari yak'arasa ta zuba dagudu, saida batasan motar dazata shigaba, dolene tajira ya k'araso. Samuel karaka wannan yarinyar, kukuma Auwal ajeda yarannan kucimin ubansu dai-dai gwargwado, Adams kumuje. Atare suka amsa,, aka kwashi samarinan dasuka gama fita hayyacinsu saboda duka. Yana hararta yabud'e mata mota tashiga, sannan yazagaya Inda Adams yabud'e MASA shima yashiga shima.........✍🏿 💋💋💋💋💋 [9/6, 9:21 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) _Na gaisheki first lady, ALLAH yabar zuminci_. 😍😍😍💋 6⃣ Aysha ta k'ank'ame jikinta tareda takurewa amurfin mortar, sai rawar sanyi takeyi, saboda bak'aramin ruwane yadakesuba awajen. Ya khaleel ya gallamata harara yana d'auke lap-top d'insa dake tsakiyarsu, takuma k'ank'ame jikinta, harda rumtse ido, dan azatonda dukanta zaiyi. Tsaki yasaki mai k'arfi, dububeki, dawani kanki kamar curin dankalin Hausa, afuska kamar kinada wayo amma wawuyace ashe, atunaninki ko ina ake nuna jarumta? Amatsayinki Na mace bak'ya tunanin had'ari fiyema da wannan? To dabamu zoba mikike tunani zai faru?!!!!, yay maganar a tsawace. Aysha takuma k'ank'ame jikinta tana hawaye, wlhy ya khalee...... Ki rufemin wannan d'an banzan bakin naki kafin nazubar da hakwaran cikinsa amotarnan, aii sai kin fad'amin ubanda yasakayi biyo hanyarnan ak'afa Stupid girl kawai. Acikin ranta tace idan kazubar da hakwaran kaika huta aii, nibanga dalilin wannan bala'iba haka, bakaji tausayinaba ka isheni da jarabarka. Adai-dai nan suka iso k'ofar gate d'in gidan, Emanuel yay horn d'an gwari yabud'e. Motar bata gama tsayawa da k'yauba Aysha tafita da gudu tayi cikin gida. Kwafa ya khaleel yay shima yafito bayan Adams ya bud'e masa k'ofar. Drivers d'in gidan yashiga kwalama kira, sunata hada-hadar tafiya masallaci saboda magrib data kawo jiki. Ahanzarce suka k'araso gareshi, Dan sunsan shid'in zumane, ga zak'i ga harbi, gashi yanayinsa ya nuna a harzuk'e yake. Gaidashi suka shigayi, batareda ya amsasuba yace wanene yake kai yarinyarcan Aee'sha wajen aiki?. Jikin lawwali Na rawa yace nine wlhy yalla6ai. Wani kallo ya watsa masa, idan an idar da sallar isha'i ina nemanka. Maganar daya fad'a kenan yajuya zuwa cikin gida. Adams ya kalli su lawwali daduk hankalinsa yake atashe, wainikam wacece yarinyarnan awajen boss? Duk nasan k'annensa, amma ban santaba. Itace zai aura, cewar sadisu murya a sanyaye. Ido sosai Adams yazaro, aransa yace kutttt shiyyasa Oga yarikice, ashe antynmuce? Lallai kingama morewa y'an mata wlhy. Kayansa ya kwaso yamik'ama sadisu danya shiga dasu ciki. Afalo ta Tatar damafi yawan mutanene gidan, jikin Anty Mamie data fito daga kitchen tafad'a tana kuka, a'a Aysha lfy kuwa? Ina kikaje hankalinmu dukya tashi, lawwali yace yaje d'aukarki baigankiba?..... Anty Mamie nafa kirashi wayarsa akashe, shinefa...... Shigowar ya khaleel takatse mata maganartata. Yaran gidan sai sannu da zuwa suke masa Dan tsawon wata 1 baya k'asar. Adak'ile ya amsa musu, saboda ransa a6ace yake. Anty Mamie tace a'a babana ko tare kukene?. Kansa ya jinjinama Anty Mamie. To lfy duk naganku ajik'e haka? Mike faruwane? Mu kun sakamu aduhu aii, ita tashigo tana kuka, kaikuma rai a 6ace?. Muryarsa cikeda d'aci yayma Anty Mamie bayanin komai, kowa afalon ya tausayama Aysha, amma yanda ran ya khaleel d'in ya6aci sai abin yabasu mamaki. Aysha tace ALLAH Anty Mamie tausayi tabani shiyyasa Na taimaketa, kumafa badan niba dazasu keta mutuncin tan........ Idan bakima mutane shiruba ALLAH saina zaneki yanzunnan, ke mara hankalin inace? Miyasa bazakiyi kamar yanda tayiba? Zaki wuce ki canja kaya kosaina k'ara kummura wannan janaren fuskar takine?, yay maganar yana matsowa kamar zai mazgeta, Ta k'ank'ame Anty Mamie kuwa. Baffah dake tsaye yafito dashirin zuwa masallaci tareda y'an uku da Nuriddin yayi murmushi, Dan yaji dad'in yanda khaleel d'in yanuna kishinsa. Maganarsace tasaka kowa juyowa gareshi, yace to ya Isa haka, mu'azzam amata hak'uri tayi kuskure, kuje kucire kayan jikinku kar mura takamaku. Aii baffah fiyema damura saita kamamu, duk ruwannan nayau akanmu yak'are saboda sakarar yarinyarnan, yay kwafa tareda shigewa 6angarensu. Girgiza kai baffah yayi yana murmushi. Yaja hannun k'ananun y'ay'ansa suka nufi massalaci. Suma sauran kowa d'akinsa yanufa, Anty Mamie kuma tatafi da Aysha d'akinta itama. Duk abinnan dake faruwa mama nad'aki kuma tanajiyo komai, ita sotayima khaleel d'in yazane ayshar wlhy. Anty Mamie tahad'ama Aysha ruwa mai zafi sosai, kije kiyi wanka Aysha, kid'an shiga ruwan kona minti gomane. Tana hawaye tajinjinama Anty Mamie kanta. Shima yana shiga d'akinsa yafara cire jik'ak'k'un kayan jikinsa, sai tsaki yaketa zubawa, sosai yakejin sanyi, dakewa kawai yakeyi, shidamacan koyaya ruwa yata6ashi saiyayi mura, ko wanka yacikayi da ruwan sanyi tosai yayi mura bare wannan dakusan durom goma yak'are akansa. Gashi anfara kiraye-kirayen sallar magriba, da hanzari yashiga bathroom yahad'a ruwa mai zafi sosai yashiga ciki, baiwani 6ata lokaciba yafito saboda za'a shiga sallah, jallabiya yasaka da hanzari yafice. Sakamakon anad'an yayyafi har yanzun aka had'a sallar har isha'i. Gabad'ayan mazan gidan suka shigo, sun sako baffansu tsakkiya abin sha'awa, a babban falo aka yada zango. Harya zauna yamik'e, kai bara nasaka rigar sanyi, wlhy sanyi nakeji. Idan kasako rigar sanyin kuzo ga shayi nadafa muku mai kayan kamshi, Dan ita ayshama fuskar dukta kumbura, harma zazza6i yarufeta. Anty Mamie ce mai maganar. Baffah yace subahanallah, ina ayshar?. Tana d'akina k'udundune abargo baffansu. Ya salam, yakamata akira doctor kuwa, Sultan kira Dr Kabeer abokinka. To baffah Khaleel najinsu amma yay shigewarsa 6angarensu batareda ya nuna alamar yamaji zancen nasuba, d'akinsa yashiga, yacire jallabiyar jikinsa yasaka k'ananun kaya, dogon wando amma, yakawo rigarsanyi yasa, hular yaja har samankansa sannan yadawo falon. Hamdiyya takawo masa tea d'in da Anty Mamie tadafa musu, yanasha suna hira da baffah da y'an uwansa. Ana haka Dr Kabeer yakira sultan akan yak'arso. Bismillah Doctor shigo kawai ciki. Cikin girmamawa Dr Kabeer ya gaisa da baffah, yabi dukkan samarin yabasu hannu sukayi musabaha🤝🏻. Baffah kaine babu lafiya?. A'a Kabeer, d'iyatace, mu'azzam kuje yadubata ko. To baffah. Yana gaba Dr Kabeer Na binsa abaya har d'akin Anty Mamie. Dr Kabeer yatsa a k'ofar d'akin Dan amasa iso. Shikuma khaleel yashiga. Tana kwance bisa gadon Mamie, gaba d'aya tarufe jikinta har kanta, saida yamata kallon minti d'aya, sannan yatako a hankali har gaban gadon, hannu yakai ya yaye bargon, Aysha dake k'ank'ame da filo tanata rawar sanyi, dukda sanye take da jibgegiyar rigar sanyi kuwa, kanta kuma nad'e da towel. Jin anyaye mata bargo tad'ago kanta da k'yar, ganinsa tsaye akanta yasakata tashi zaune da hanzari, wani mugun tsoronsa takeji aranta, yanzunma fuskarsa a d'aure take babu alamun wasa, wannan yasaka Aysha takasa koda satar kallonsa, dama ga idanunta sunyi nauyi saboda marukan datasha. Baice komaiba yabama Dr Kabeer damar shigowa, tunda yaga kayan mutuncine ajikinta. Dr Kabeer yashigo da sallam, khaleel yanuna masa sofa ya zauna, shikuma ya jingina da madubin tareda zaro wayarsa a aljihu yafara danne-danne, saika rantse dukkan hankalinsa akan wayar yake, amma bahaka baneba, hankalinsa natareda su Aysha da Dr Kabeer kema tanbayoyi tana bashi amsa murya a sanyaye. Aransa yace trouble marker anyi laushi yau, fukarta tad'an tasa, takumayi jajur abinka da fara, tad'an bashi tausayi kad'an, amma haryanzu halayenta mamaki suke bashi, dan kullum da sabon salo take zuwa masa, amma wasu abubuwan nata nasakashi nishad'i kad'an...... Maganar Dr Kabeer takatse masa tunanisa, ya Khaleel kozamu samu tea tad'ansha saboda za'a mata allura, kuma zai taimaka mata tarage jin sanyin. OK. Harya yunk'ura zai fita saikuma yafasa, bazai iya barinta itada Dr kad'aiba. Wayar Muhseen yakira, yana d'agawa yace ka kar6o mata tea wajen Mamie. Baijira amsarsaba ya yanke wayar. Babu dad'ewa saiga Anty Mamie da Muhseen sun shigo, lokacin Dr Kabeer yagama ware mata magani, harya fara had'a allura. Aysha sai hawaye takeyi Dan batason allura dama can. A'a Aysha kukan kuma namiyene?. Anty Mamie wlhy banason allurar. Dr Kabeer yatsaya da had'a allurar yana fad'in to kiyi amfani da maganin kawai... No, cigaba da had'a allurarka Kabeer. Jinjina kai Dr Kabeer yayi, yayinda Aysha ta rushe da kuka. Ko kallo bata isheshiba, Anty Mamie Ce kawai ke lallashinta, muhseen kuwa dariyama yake mata, khaleel yad'ago ido ya kallesa. Zoka fice. Fitayay yana kunshe dariyar karta fito. Anty Mamie tarik'ekata Dr Kabeer yamatsa zai mata allurar, takware baki zatayi kuka ya khaleel yadawo kusadasu batareda yayi maganaba. Kallonsa kawai tayi tsoronsa yakamata, damacan tana tsoronsan, rashin kunyar datake masa ita kanta batasan sanda hakan ke faruwaba, amma tana danganta hakan da son danne soyayyarsa dake nuk'urkusar zuciyarta.. Har aka gama allurar batace uhumba. Saidai hawaye ke zurara. Murmushi Anty Mamie tayi kawai, tasan baban nata ba namijin wasan kowa baneba. Tasha tea d'in, saitasha maganin ta kwanta Mamie. To Kabeer sannu, kaima babana Aida ka kar6i maganin mura ko?. To Anty Mamie, amma ni normal ma nakejina, dukda dai nasan dolene sainayi murar. Shima magunguna Dr Kabeer yahad'a masa, sannan yamusu sallama yafita. Kan sofa Yakoma ya zauna, Anty Mamie tabama Aysha shayin. Tanasha tana satar kallonsa, tak'oshi amma tana tsoron fad'a yahau kanta da masifa, haka tadaure ta shanye tas, Anty Mamie tabata maganin tasha. Saida yaga ta kwanta, har barci ya sureta sannan yafito, kowa yashige d'aki, saboda sanyi, 6angaren Momy yashiga suka gaisa a tsaitsaye yafito. Shima d'akinsa yakoma yay shirin barci ya kwanta abinsa. _____________________________ Kwanaki biyu Aysha Na jinyar kanta, amma alhmddlh da sauki, dantana samun kulawa gun Anty Mamie, yanzu tama koma can gaba d'aya, ko fita batayi, ya khaleel ma sai idan yashigo gaida Anty Mamie take ganinsa. Dukda talura shima kwanki biyun baya zuwa ko ina agida yake yini, Dan shima Murar ta tasoshi gaba. Yau kuma tunda safe sunata shirin zuwa zariya d'aurin auren bishirah, Dan and'agane dama. Kowa yafito fes dashi, duka gidan kowa zaije amma banda hajia babba da umme amarya. Su Aysha sunci gayu cikin wani material mai k'yau Orange color, ammasa d'igon milk, danhaka d'ankwalin suma ya kasance milk da sark'a dadai sauransu. Baffah da mama da Anty Mamie motarsu d'aya, baffah da driver Na gaba, mama da Anty Mamie Na baya, sai ammah motarta ita d'aya da gwaggo bintu, y'an uku, nuriddin da Ummunoor. Su hamdiyya, shukurah, Amal, Hasnah, Husnah, Naseeba, Mufeeda wad'anda ya khaleel yasakasu dole zuwa motarsu d'aya. Sai Aysha, maleeka, Tasleem Ummu aymana (matar ya sultan) da Abashiyya (matar ya mujahedeen). Sai samarin gidan suma, sun kasu biyu. Duk hangen Aysha bataga ya khaleel a tafiyarba, haka sukatafi kowa zuciyarsa cikeda farinciki, amma banda hasnah da husna mufeedah, dansu tafiyar dolece agaresu. Da wuri suka isa zariya, anmusu tarbar mutunci, tamkar sune sarakunan zariya.😜lol. Bishirah kam tayi murnar zuwansu Aysha, Dan sune suka Zame mata abokai Aysha, tasleem, maleeka, tunda sanda girma yazo mata tana gidansu, anan batada k'awaye. Bayan an d'aura aure su Aysha dake makwaftan su bishirah sukad'an fito wai zasu zagaya gari. Gaban ayshane yafad'i lokacin da idonta ya sauka akan ya khaleel dake jingine jikin mota, sanye yake da dakakkiyar shadda Ash color, yasaka hulama ash, yayi masifar k'yau, tunda take yaune karon farko data gansa da manyan kaya, jitai inama zata iya tamasa pic, inda zata fad'a yaji databashi sahawara akan yamaida manyan kaya suturar sakawarsa...... Ihunsu Tasleem ne yadawo da ita duniyar mutane, maleeka tace woow wlhy ya khaleel yahad'u yau, kamar ranar aurensa. Tasleem tace ALLAH saina masa pic....tayi maganar tana zaro wayarta ajaka, hotuna suka shiga yimasa batareda yasanibashi, Dan waya yakeyi dawani abokinsa daga Canada, kokad'an hankalinsa baikaima kansuba. Tasleem tace kai Aysha Dan ALLAH kije wajensa mu d'aukeku. 😳kuttt, amma tasleem bakida hankali wlhy, to badaniba. Dariya sukayi, suna fad'in matsoraciya kawai, kwana nawane zakuyi barci a gado d'aya... gaban Aysha ne yafad'i, tadubi ya khaleel d'in da k'yau tadubi kanta, aranta saitaji tausayin kanta. Afili kuma tace ALLAH ya shiryeku wlhy. Kamar wasa yaga haske nata haska glass d'in motar dayake a jingine, mamaki yakamashi Dan hasken kamar Na camera. d'ago azababbun idanunsa yayi ya saukeau Kansu tasleem, kai, kajimin yara da iskanci, waidama nisuketama photo?. Yakai kallonsa akan Aysha data koma gefe tana waya, aransa yace kodawa take waya?. Ganin ank'ara haskashi yace k! Tasleem kuzonan?. Atare suka zabura, suka juya zasu gudu, muryarsa mai tsoratar da marajin magana tasauka akan kunnensu, kugudud'in naci ubanku agarin mutane. Dole suka tsaya, kowa guywa a sanyaye suka nufoshi. Dankun rainani shine kuketa wani min hoto ko?. Wlhy ya khaleel k'yau kamana ne, please kayi hak'uri, tasleem tafad'a kamar zatayi kuka . Ita waccan dawa take waya?. Wlhy yaya bamu saniba muma. Jeki kiramin ita. Dasauri maleeka taje takira Aysha. Gaban Aysha sai fad'uwa yakeyi tak'araso wajen, a d'arare ta gaidashi. Batareda ya amsaba yace shiga mota kirakani wani waje. Kukuma kujirata yanzu zata dawo. Suka amsa dato, Dan babu damar musu. Idon Aysha cikeda da kwallah tace ya khaleel please, wlhy........ Ruf tarufe bakinta saboda azababbiyar Harar daya zuba mata, yanuna mata k'ofa alamar tashiga. Harta fara matsar kwallah tabud'e motar tashiga, yarufe sannan yazagaya shima yashiga yabar anguwar... Motar nabarin wajen su maleeka suka shek'e da dariya suna fad'in soyayya ruwan Zuma.........😂✍🏿 One luv my sweet Fan's💋💋💋💋❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤. [9/6, 2:40 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 7⃣ Tunda suka tafi babu maima wani magana, duk tsoro yacika Aysha, tunani takeyi ina zai kaita. Yamik'a mata hijjab Fari tas, sai k'amshi yakeyi. Kar6a tayi tana dubawa, yadin yamata k'yau sosai, batace dashi komaiba tazame gyalenta tasaka, tana k'unk'uni k'asa-kasa akan INA zai kaitane?, batayi zaton yajitaba. Saidaki zanyi bak'auya kawai, muryar ya khaleel taji batareda tayi zatoba. ALLAH yabaka hak'uri, tayi maganar a sanyaye, Dan ita wlhy tsoronsa k'aruwa yake aranta, tunda taga yajibgi guys d'innan, dakuma Marin daya mata. Bai tanka mataba. Gani tayi sun shiga cikin makarantar A.B.U. zariya, mamaki takeyi mizasuyi anan kuma?. Guri yasamu agefe yayi parking, d'alibai nata hada-hada, dukda yaud'in ba ranar karatu baceba. Harya fita Aysha bata motsaba, yalek'o yana hararta, kosaina fiddokine?. Jiki a sanyaye tabud'e motar tafito, nanfa idon d'alibai Yakoma kansu, y'an mata anga had'ad'd'en gaye duksun rikece, su kallonma ayshar sukeyi amatsayin k'anwarsa, k'ilan yazo nema mata addimetion a school d'inne. Cikin takunnan nasa Na jarumta yake tafiya, dolene duk mace mai lfy ta k'yasa.😉.lol. Dukda cikin nutsuwarsa datazama tamkar halittarsa yake tafiya hakan baihana ya zarta Aysha ba, ita tanama had'awa da y'an sassarfa atata tafiyar. K'ofar wani office sukaje da aka rubuta professor Al-hassan ibn Mahmud, Knocking yayi aka bashi izinin shiga. Dattijone maicikeda kwarjinin kamalar addini, zasuyi sa'anni da baffah. Cikeda fara'a yake fad'in lale marhababinka Ibraheem bin Abdallah. Ya khaleel yak'arasa suka rungume juna kamar yanda larabawa keyi, sanan ya durk'usa har k'asa ya gaidashi, ganin haka itama Aysha tadurk'usa ta gaidashi cikin girmamawa. Cikeda fara'a ya amsa yana fad'in masha ALLAH sannunku dazuwa d'iyata, bismillah kuzauna kuzauna. Ya khaleel da Aysha suka zauna a kujerun dake gaban babban tebir nasa, Aysha tayi k'asa da kanta saboda kunya. Mamaki yayi mugun kama Aysha lokacin dataji ya khaleel yajuya harshe suna larabci shida dattijon, dole tad'ago manyan idanunta masu yalwar gashi ta kallesa, suka had'a ido Dan lokacin yajuyo yana gabatar da ita wajen dattijon amatsayin matarsa dazai aura. Janye idanunsa yayi yamaida kan sheaik Al-hassan. Masha ALLAH Ibraheem khaleel, masha ALLAH, cikin harshen larabcin yayma Aysha barka dazuwa akaro nabiyu. A mugun mamakin ya khaleel d'in shima saiyaji Aysha ta amsa da larabcin, daganan tacigaba da amsa tanbayoyin sheaik Al-hasan da larabcin. Shagala yayi yana kallon bakinta dake sarrafa larabcin cikin kwarewa danuna tabbas ta ilimantu a 6angaren addini, bak'aramin birgeshi tayiba, Dan baiyi zaton hakaba tunda baffah yasanar masa daga k'asar waje tadawo karatu. Sheaik Al-hassan ibn Mahmud malamin ya khaleel ne, ahannunsa yay karatun addini a Abuja, aikine yadawo dashi A,b,u zariya. Sundad'e basu had'uba saboda yanauin aikin ya khaleel d'in, shiyyasa dayazo d'aurin aurennan yaga yadace yazo ya gaidashi, shine daya kirashi yasanar masa yasameshi acikin makaranta. Yakawo Aysharne Dan malaminsa yaganta tunda baida tabbacin zasu sake had'uwa dukda yanada burin malamin NASA yay Iuctures alokacin aurennasa. Sheaik Al-hasan yaji dad'in wannan ziyara sosai, yayimasu nasiha akan aure da muhimmancin auren kansa, da girmama juna, yanda zasuyi zamantakewar dazasu amfanar dajunansu batareda samun sa6aniba ko k'osawa da junaba, sund'an dad'e sosai a makarantar Dan har saida baffah yakirasa, yasanarma baffah Inda sukaje. Baffah yace shikenan mukam zamu wuce saikun taho, ka gaidamin da Malam sosai, kace insha ALLAH nima inan zanzo wajensa zuwa Na musaman. Zaiji baffah, saimun taho, to kutahodai dawuri, karkuyi dare kajiko, Kasan hanya babu k'yau. Insha ALLAH yanzu ZAMU taho baffah. Bayan sun Yanke wayar ya isar da sak'on baffah wajen Malam, yaji dad'i sosai kuma ya amsa. Littatafan addini masu muhimmanci akan rayuwar aure dawasu fannonin yahad'ama kowannensu, sai godiya suke masa. Ya khaleel ya ajiye masa alkairi mai tsoka sannan sukafito. Har k'ofar mota Malam yamusi rakiya, saida yaga fitarsu sanan yakoma office yanamai jin dad'in ziyarar, Dan har ransa yana k'aunar khaleel d'in, yarone mai kwazon gaske alokacin daya koyar dashi, ga gaskiya da suffar kamala Na mutanen kwarai batareda yaron, yaga kuma haryanzu halayyar Na taredashi. ________________ Tunda suka d'auki hanya babu Wanda yace uffan, har sunshiga cikin kaduna. Shi yanata tuk'insa dajin wa'azin sheaik Jafar Mahmud Adam, itama Aysha wa'azin take saurare, yayinda wani 6angaren zuciyarta yatafi wajen tunanin ya khaleel d'in, komai nasa na burgeta, tako ina ya khaleel cikakken mutumne, saidai abinda ba'a rasaba, Dan d'an adama Tara yake bai cika gomaba, babu yanda za'ayi kace wane yakai 100%, dolene saika samu wani d'an taumashe koyaya ataredashi. Awajenwa kika iya larabci haka?. Maganarsa ta sauka a kunnenta. Batareda ta kalleshiba tace a islamiyyar abbanmu, shima yana koya mana. Alkur'ani fa?. Nayi sauka, ina izufi 37 a hadda. Yanzunkam saida yajuyo ya kalleta, banason k'aryafa. ALLAH ka tanbayi mama. Kansa ya jinjina, yacigaba da jeho mata tambayoyi akan sauran littatafan addini, sosai take bashi amsa daki-daki, saidai abinda ba'a rasaba, Wanda tasamu rauni akansa saboda rashin tunatarwa, tunda ba islamiyyar take zuwaba yanzun, jiyayi k'aunar iyayenta da kimarsu tak'aru azuciyarsa, dama haka yake burin samun matarsa mai ilimin addini, dukda har yanzu baita6ajin son yarinyar aransaba. Daganan baikuma cewa komaiba. Sunkusa fita Kaduna yatsaya wani wajen saida snacks agefen hanya, baicema Aysha komaiba yafita tareda saka mata luck. Baidad'eba sosai saigashi yafito da leda guda biyu a hannunsa. Yabud'e motar yashigo yana fad'in Alhmdllh. Kamar yanda yanuna ya manta da ita a motar haka itama ta shareshi har suka fice daga cikin Kd. meatpie dake nad'e cikin tessu yafaraci tareda fad'in bismillah. Aysha tasaci kallonsa ta gefen ido sannan tace a'a ngd. d'an juyowa yayi ya kalleta sannan yamaida hankalinsa ga tuk'insa, baisake cewa uffanba har suka shiga tsakkiyar dajin tsakanin Abuja da Kaduna. Wayarsa tayi wringing, saida ta tsinke aka sake kira sannan yad'aga. Ango kasha k'amshi, har yamzu baku shirya dawowa wajen aiki baneba kaida youseef? Kunbarmu aiki yamana yawa nida taheer wlhy. Joseph yayi dariya, karka damu my guy, end of this week zanshigo Abuja tareda madam. OK saikun isoto, agaidasu papa da joy. Zasujika da k'au, ina amaryarmu?. Waye amaryarku?. Hhhh madan Aysha mana. Aini bamma Santana, kaga sai munyi waya ina kan titine, yay maganar yana yanke wayar batareda ya saurari mi Joseph zai fad'aba. Abin yak'ule Aysha. Dan taji dukkan wayar tasu, amma tana mamakin dama yana wasa da mutane haka?. Sun isa jere aka fara kiran sallar magriba, tacikin jere yabi saboda gudun go slow d'in dazai samu idan yabi ta babbar hanya, musamman awajen dei-dei d'innan. Ganin lokacin sallah zai kwace masa yatsaya a bwari wani masallaci zaibi jam'i. Harya taka zai fita wayar Aysha tayi wringing, dakatawa yayi yafasa fitar, atare suka kai hannu kan wayar, shiyayi nasarar d'auka yayinda Aysha tayi saurin janye hannunta saboda d'orawa datayi akan nasa. Ya d'auke wayar daga cinyarta yaduba, Anty meerah yagani a screen d'in, saiya mik'a mata yafita. Baki ta murgad'awa bayansa sannan tad'aga wayar, harta tsinke ansake kira. Anty meerah Na I missing you wlhy, kin manta dani kusan 1week bamuyi wayabafa. Sorry lil sholyna, babynki ce batada lfy, amma tasamu sauk'i. Wayyo my Raudat shiyyasa nayita mafarkinta, yajikinta?. Kwantar da hankalinki da sauk'ifa, hak'orane. To duk kuna lfy? Ya Canada?. Gatanan k'alau, saidai muna kewarki wlhy, tunda muka dawo kullum sai munyi hirarki agidanan. Wlhy nima ina kewarku Anty meerah, wani lokacin jinake kamar nayi tsuntsuwa nazo gareku, karki damu, aimun kusa zuwa tunda ga bikinnan nata zuwa ko. Uhhm, ni Anty meerah kibari kawai, ALLAH yanzun banason aurennan, ya khaleel lamarinsa tsoro yake bani, saboda halin ko inkula dayake nunamin, yanda kikasan ba aurensa zanyibafa. Karki damu daduk wata shariyarsa, kowane namiji danasa salon, wani bazai ta6a nuna miki color d'insaba saikunyi aure, wasu kuma sununa miki soyayya awaje, idan kunyi aure kiga bahaka baneba. Shikenan Anty meerah. Yauwa sweet lil d'ina, yanzu ya'ake cikine?. Humm abubuwa kam sunata faruwa, kuma Alhmdllh ina k'ara samun bayanai akan su hajia babba, kinsanma wani Abu?. A'a saikin fad'a. Hhhhh wlhy mufeedah nakama shekaranjiya around 1:30am Na dare zata fita, batasan nagantaba, nafito d'aukar ruwa nasha, har tsakar gida nabita, naga tanatama d'an gwari maigadi jaraba, yabud'e mata gate kuwa tafita, rok'onsa nayi akan yabarni naga inda zataje. Kinsan minagani kuwa? Tana fita tacire hijjab d'in jikinta, wlhy daga ita sai bra da pant, saiwata shegiyar riga wadda da'ita da babu duk d'aya. Motar wani guy tashiga, inanan zan kafa mata wani tarko, ALLAH sanadin haka sai hawan jini yakama uwarta..... Hango ya khaleel natahowa yasaka Aysha fad'in kibari nakoma gida zamuyi waya, tayanke da sauri. Motar yashigo suka cigaba da tafiya. *_2month's ago_* Kwanaki nata shurawa, bikinsu ya khaleel yamatso gab. Aysha tanashan gyara wajen Ammah da Anty Mamie, harma da gwaggo bintu ( nace wannan bazai hana ya khaleel dakakiba😂 gwaggo bintu😜). Ga Anty Mamie tatsaya akanta wajen koyamata girke-girke dazama da miji, abinda ya khaleel keso da Wanda bayaso danta kiyaye kuma taci ribar zama dashi. Tayi k'yau harta gaji, Ammah ma Na koya mata dabarun zama da miji irinna zamaninsu, sosai Aysha take fahimtar komai daki-daki. A6angaren hajia babba kam batawani d'auki bikin da muhimmanciba, ko kayan lefe da Shukurah tace zataje Dubai tahad'o hajia babba cewatayi uban Dubai d'in, y'ar talakawar za'a had'ama kaya asu tsada?. Bazai yuwuba. Kai Momy, itamafa tazama d'iyarki, yakamatafa kugane khaleel shikad'aine namiji acikinmu, yakamata kuma a auransa mu nuna masa gata, kodan d'awainiyar dayakeyi damu, hakama Anty zuwairah nace nawa zamu had'a masa gudunmawa tace ko sisi bazata badaba, Momy kimata magana Dan ALLAH. yo maganar ubanmi zan mata, wlhy ina bayanta gara tasiyama y'ay'anta kayan sakawa, idan zaiyi auren gaskiya saita masa, Dan wannan auren rusashshene, kwanakin Dana bashi nacika zan wargazashi. Inzaki Adana kud'inkima sai aurensa da Aleeya ki Adana, inkuma zaki bashi kekika Sani, dama aii kema salla mammiyarce tamkar shi, karkuma kisake kirana akan bikinnan, dama zakiyi zamanki wajen y'ay'anki yafi miki alkairi basai kinsaka mijinki kashe kud'in jirgi abanzaba, ato kindaiji nafad'a miki. Hummm amma Momy....... Ya isheni haka Dan ubanki. Shiru Anty shukurah tayi, tace shikenan Momy sai anjima, insha ALLAH ana saura sati 1 zantaho. Kekika Sani kuma. Ya khaleel dake tsaye abakin k'ofa yanajin wayartasu yajuya dabaya, Dan baya buk'atar momyn tasan yashigoma, wajen aiki zaije shine yashigo gaidata, maybi da yama zaije Gabon, amma dasafe yake sakaran dawowa. Ko amma bai gaidaba yafice, saboda wayar Momy ta Sosa ransa, su Kansu su Adams sunlura ransa a6ace yake, yarasa miyasa Momy take masa hakane?, yakanji alabarin mutane idan mutum yanada y'ay'a maza dayawa, ya haifi mace 1 tak acikinsu takan samu gata fiye da kowa, hakama idan ya haifi mata da yawa, namiji yazama shikad'ai yakan samu gata fiyeda sauran y'ay'an, amma shi agaresa ba haka baneba, Momy tafi nuna soyayyarta kan y'an uwansa mata, mawuyacine suyi rayuwar sati d'aya Momy batayi abinda zai Sosa zuciyarsaba agidannan, Anty Mamie daba ita ta haifeshiba, nononta kawai yasha, amma yafi samun kulawa da kwanciyar hankali agareta. Yanzu kokan aurenan itace ta zaunar dashi tamasa nasiha da Nuna masa muhimmancin biyayya ga iyaye, da alkairin datake hango masa a auren, kullum tsaye take Kansu wajen kwantar da hankalinsa itada Amman akan auren, amma ga Momy bahaka baneba. Wanan wace iriyar rayuwace, shidai basain dad'in uwaba wlhy, gata da ranta amma maraya yafishi jindad'i...... Adams yak'ara magana akaro Na hud'u, sir! Munzofa. Firgigita yabud'e idonsa, tareda yin k'aramin tsaki, Natafi wata duniyarne Adams, bara naje wajen Oga nafito, kafin nafito kasanarma su fharuk ina nemansu a office d'ina. OK sir! Adams yafad'a yana masa salute. Yad'an dad'e a office d'in ogan nasa, suna tattaunawa akan abinda zai kaishi Gabon, dakuma mutuwar David Wanda khaleel d'in ya tabbatar da anbasa gubane aruwa yasha, kuma anhad'a kaine dawani makusancinsa, tunda bakowane ke shiga inda David yakeba, ya khaleel yace sir!. Inazargin wasunmu Na taredasu David, Dan a shekaran jiya nafara tatsar wasu bayanai agaresa, Yakuma tabbatarmin zai fad'amin jami'an tsaron dake basu taimako akan harkokinsu, shine jiya muka wayi gari an kashesa, nasaka anrufemin masu tsaron k'ofar, har sai sun sanarmin Wanda yayi aika-aikar, dansunsanshi, amma sunk'i fad'a saboda wani dalilinsu nadaban. Ha...ha..hakane, yakamata mu tsananta bincike akan kisan nashi, dan.... Dan babu wani bare dazai shigo yayi wanan aika-aikar. Wani murmushin kasaita ya khaleel yayi, cikin izzarsa yace karka damu sir, y'ar manuniya zata nuna, kuma wlhy kosu wanene saisunyi Dana sanin 6atamin aiki, sannan mutuwar David bashine zaisa su ku6ta daga farautata ba, saima hanya dasuka nuna mini, alk'awarine saina gurfanar dasu bisa guywoyinsu agabana!!. Y'ar zabura Oga yayi, Dan maganar khaleel d'in tashigeshi. Batareda sauraren komaiba ya khaleel yay salute nashi yafice daga office. Ajiyar zuciya Oga yayi (babu zancen fad'in matsayinsa, saboda tsaro😂👍🏻), gaba d'aya ya tsorata da j! d'in, yasan yaron gwarzone, kuma tabbas saiya bankad'osu, zuface tashiga keto masa, dolene su sake taku, kuma sud'au mataki wajen ragema Ibraheem Abdallah j kaifi, amma tayaya?, Dan sunan yaron yarigaya yayi tsawa a hukumarsu, manyan k'asashen duniya sun sanshi, kuma sunayi dashi. Miye mafita yanzu??.... A office d'insa yatarar dasu Solomon, atare sukayi salutes nashi, yazauna akujera yana binsu da kallo. Mahmud ya'ake cikine?. Yes sir, mun kammala komai, kamar yanda kabuk'ata mun tankad'e da rairaye wad'anda sukeda kusanci sosai da barau modibbo, so aranarma da kukaso kamashi akwai wata number da'aka masa massege da ita, cewar gakunan zuwa garesa. Inaga wananne yakawo matsala harya farga yagudu bayan yaga messenge d'in. OK wanene mai number?. Macece gaskiya, yasaka mata hajjaju kawai. OK. Yanzu mutane nawane kuka tace acikinsu?. Faruk yace su 37 ne sir. OK. Yakamata abisu d'aya bayan d'aya amin bincike akan sana'oinsu, da address nasu, har ita macen da tamasa massage d'in. OK sir. Solomon yace amma sir kana ganin lokaci baiyiba dazaku kama barau modibbo?. Hakane Solomon, zamu kamashi, amma inason kama Alhaji Aliyu bushasha ne first, danshine ogansa nalura, kokuma nace babban dila d'insa, to kafin kuma nakamashi dolene mucigaba da bibiyar barau modibbo dansamun wasu bayanan sirri daga garesa batareda shima yasaniba. Muna kamashi barau modibbo yanzu, Alhaji Aliyu zai gudu wlhy, kumashi mutumne mai wayon tsiya, baya hud'd'a da wayar tafi da gidanka, saidai yaransa.. Lallai yanada wayo, cewar kausar. Sun tattauna sosai gameda wasu ayyukan sannan ya sallameshi suka tafi. Shikuma yacigaba da 'yan ayyukansa, yana son kammala komai akan lokaci, saboda nanda 2weeks binkin taheer, tsakaninsu sati uku ne acal. Ga aiki yamusu yawa, ad'an tsakaninnan, hankalinsa yarabu biyu. Ga shirin bikinsa shi kansa, damma k'annensa suna tsaye akan komai da baffansa. Shi satin bikinma yana Saudia, sai ana 3days d'aurin aure zai dawo Nigeria. Akwana atashi, babu wuya wajen ALLAH, biki saura kwanaki 10 kacal..............✍🏿 😍😍😍😍😍😍💋💋💋💋❤❤❤❤❤ [9/6, 8:54 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) *_wannan page nawani duk masoyin ciki da gaskiya ne aduk inda kuke, ngd sosai da k'yauna, ALLAH yabar zuminci, inayinku irin million's d'innan wlhy._* 😍😍😍😍❤❤❤❤💋💋💋💋💋 8⃣ Alhamdulillahi shirin biki ya kankama, anatama Inda zasu zauna fenti, can baya kusadasu ya Sultan, tunda aka saka ranar auren baffah yasakashi za6en yanda yakeso agina masa nasa wajen, yakuwa za6a. Tun sannan aketa ginin, hargashi ankammala cikin nasara. Kaf gidan kowa yanata shiryama wannan biki, dukda uban tafiya yace babu wani shagali daza ayi, acewarsa da kud'in daza 6arnatar wajen wani dinner, lunch, mother day.....etc, gamma ataimakama marasa k'arfi dashi. Baffa yaji dad'in hakan sosai, kuma yasaka masa albarka. Hajia babba kam ko a jikinta, da ayi dakar ayi duk uwar ubansu d'aya, yarantama basa wani nuna murnar Auren, saboda anhad'a yayansu da Aysha, amma sunata burin sai lokacin bikinsa da Aleeya, sukad'ai sukasan misuka shirya. Nidai nace uhhhhmmm.😏 ______________________ Aysha kishirya gobe idan ALLAH yakaimu zaku wuce Kano keda gwagggonki. Lah mama da gaske?. Eh mana, can zaki koma, nasanarma baffanku ma, nima insha ALLAH ranar laraba zantaho gaba d'aya, kokinje Kano karkiyarda wani yabaki wani abin cushe-cushe ko wani ganyen magani kisha, banason shaye-shayen maganin matannan wlhy, Dan abubuwane masu illah, mutanene kawai suka Gaza gane haka, kingadai anan mamien ku tabaki tsaftatatttu itada Ammah, tunda nonon rak'umine Dana shanu sai kayan marmari dasu aya Zuma kanimfari mazarkwaila dafanfar gyad'a dadai sauransu, wad'annan basa cutarwa tunda damacan ALLAH ya halatta mana shansu koda badan wannan manufarba, shiyyasama nahanaki shan nawajen bintu gaskiya. Nasan Yaya bazata bakiba itama, tunda bataso, kannena kawai nakeji da asma'u sai matar Ahmad, amma Na gargad'i Hafsat da fadeelah, tunda suma sunsan bamumusu wannan shashancin ba. Damu zauna 6ata lokaci wajan baku wannan shirmen da 6ata kud'inmu gamma mu nutsu wajen koya muku zaman auren da biyayya, maganin mata baya hana d'a namiji ya wulak'antaki idan yaso, idanda matanmu nada hankali dasun gane hakan, (wlhy naga matarda tahad'a kayan mata ta kwankwad'arma cikinta da yamma da daddare mijin yaji dad'insa, washe gari da safe sa6ani yashiga tsakaninsu ya sheshshek'ama fuskarta marika), shin Dan ALLAH maganin mata yayi riba kenan?, alokacinfa dasuke tareda sune kawai sukejin dad'in har miji yamiki wani sambatun banza, dazarar buk'atarsa tabiya shikenan anwuce wajen, wannan bazai hana yaci ubankiba, bazai hanashi cin zarafinkiba, bazai hanshi ya sakekiba, bazai hanashi yimiki kishiyaba, shin mata nawane suke amfani da kayan d'a'a amma basu fita daga cin kashin d'a namijiba, ga cututtuka dakiketa tanadama kanki wanda bazasu bayyana agarekiba sai lokacin da tsufa yazo miki, shin Dan ALLAH miye abin birgewa duk inda kika zauna kika tashi aganshi jik'e da ruwa, wannan wace iriyar masiface?, mutanan da maganin mata sukesha?, bama su sanshiba, amma suna zaune lafiya da mazajensu, wani aurenma sai anyi mace zata San mijinta, miji yasan matarsa, amma saikiga aurensu ana kiran shekararsa 80-70-60, kuma suna zaune lfy, ko sa6ani zakiga baya yawan shiga tsakaninsu. tsakaninku da ALLAH awannan zamanin aure nawane kekai shekara 10 kacal babu tashin hankali da masifu acikinsa, awannan zamanin inhar mace sukai zaman lfy Na kwana uku da mijinta acikin sati, to wlhy kwana hud'u cikin fad'ane, mafi yawancin abinda ke faruwa kenan, kuma koda yaushe kud'inki nagidan dillaliyar kayan mata, bakiciba, bakiba y'ay'anki sunciba, bakiba iyayenki sun sakamiki albarkaba, baki taimakawa marasashiba, saikije kisha abinda zai ruguza rayuwarki batareda kinsan hakanba, kedai kawai mijinki yaji dad'i, yaringa zunduma ihu lokacin dayake taredake, indan anhad'u gidan suna ko biki kiringa bama sauran mata labarin sambatun dayake miki da ihu, mata suna dariya ana cafkewa da miki jinjina kinci gari. Haba mata, wannan wace iriyar asarace haka, sirrin aurenkine agidan biki? Kaiconmu wlhy, ALLAH kuma ya tsinema duk ma'auratan dake fallasa sirrin aurensu, wlhy mugyara, keba karuwaba amma rayuwar aurenki tafi ta karuwai fita fili, wa'iyazubillah, Dan ALLAH mu kiyaye mata. Aysha karki yarda koda da kuskure hakan takasance dake, kada naji kada nagani. Kuka sosai Aysha keyi, tana jinjinama mama kai, kidaina kuka dan bama ayi komaiba, abinda yasa nabarki saboda kina kusadanine, akoda yaushe zan ringa nuna miki kuskuren abinda ke hana rayuwar aurenmu k'arko awannan zamanin. Tashikije ki kimtsa komanki, Dan duk za'a maidasu 6angarenku kafin natafi. To mama, ngd, tafita tana cigaba da kuka. Mama tabita da kallon tausayi, tana tausayama d'iyar tata da dududu bata wuce shekaru 18 ba, gata da k'aramin jiki, bandama karatun kasashen waje ba irin namu baneba da saifama yanzu ayshar zata kammala Secondary nata, amma gata ayanzu hartana bautar k'asa (NYSC) d'inta ____________________ Yauwa Amatullah, kune y'an zamani, dama zuwanki nake jira, bud'e d'akincan Na bak'i muje kiduba kayancan idan sunyi, idan kuma akwai abinda za'a k'ara ko za'a sake kinga zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu saimu shiga kasuwa, Dan yakamata akaisu ranar alhamis ko. To Anty Mamie kayan miye haka?. Mujedai kigani mana. Woow Anty mamie! Kayan auren ya khaleel ne?. Sune Ama... Masha ALLAH, akwati shidda, wlhy sunyi k'yau akwatinan, zama sukayi bakin gado, anty Ama.... tamasu fillah-fillah, kai wlhy komai yayi Anty, komai dama ayishi dai-dai misali yafi, amma nuna fariyarnan bata birgeni nidai. Aii Ama...ita rayuwa basai ka nuna kaid'in maishi baneba, koda kanada kud'inda zakayi abinda fiyeda nak'asa dakai yayi, karkace saikayi Wanda ya ninninka nasa, wannan shike saka Wanda k'arfinsa bai kaiba burin yin kamar nakan, wannan fariyarce tasaka zaman y'anmata da zawarawa yawa, kowa burinta sai anyi mata abinda akama k'awarta lokacin aurenta, hakama iyayenmu burinsu Aueen y'ay'ansu yafi nakowa, Idan ankawo lefen auran d'iyar makwafta sudinga hura hanci aina d'iyansu yafi, sukansu samarin burinsu suyi bajinta tamkar ta auren wane, shiyyasa saikiga fitintinu sunyi yawa acikin bikin auren, da rayuwar auren kanta bayan anyishi, zakiga ma'aurata burinsu ayi events kala-kala Na k'awa da birgiyewa awajen shagalin aurensu, ad'akko mawak'a masu zamani da tashe su wak'esu, alik'a y'an dubu-dubu bugun Abuja ana takasu, amarya da Ango su d'au k'yalk'yali cikin kayan kece raini Na alfarma, wuyan amarya da hannunta kaga ruwan gwal k'irar Dubai nata k'yal-k'yal, k'awayen amarya da abokan ango da dangi ank'ure wanka cikin kayan birgewa, ga camera man agefe yanata k'yastu, washe gari dukwata kafar media tad'auka anyi auren wance da wane, abinda ke 6atamin raima wai kayan lefen aurenki dazarar ankawo zakifara ganin ana yawo da hotunansu a social media, y'an group ga kayan auren🤣. Sukuma saisu d'auki shewa, kai amma wance kingama morewa, ALLAH dai ya maidamu danshinki, kai wacece addu'a gareki haka, muma abamu Dan ALLAH😂😂😂, kujifa wawanci. Kekam anfasa miki kai, kinacan dad'i kamar yakasheki kayan aurenki sun birge mutane😏. Sai ank'are biki kaf ango yayta sace kayan da d'aid'aya yana maidawa shagon daya aro🤣. Inkuwa siya yayi dagaske ma da sauk'i, amma dasun k'are kikace wane kayana sun tsufa zaice duk kayan Dana saka miki alefe kice sun kare, kinsan wahalar danaci natarasune? K'ilama y'an uwankine suka kwashe anga banza, to banidashi nikam😜. Wlhy tundaga k'aryar biki ake fara samo matsaloli a aure, please mukula Dan ALLAH. Hakane wlhy Mamie, ALLAH dai yasa mudace, amma yanzu wannan baffah ne yasa ahad'a ko ya khaleel. A'a Ama... Gudunmawa tace, babana yamin magana akan lefen, amma nace masa yad'an saurareni, shima baffan naku dayay maganar haka Na sanar masa. Yanzu saiki nemo su Amal Ku kwasa kukai wa Ammah kawai tunda komai yayi. Kai amma kinsha kud'i Anty Mamie, ALLAH yak'ara bud'i Na alkairi, lallai ya khaleel d'an gatan Anty Mamie. Fita Anty Mamie tayi tana murmushi batace komaiba. ............................................. Ohni Halima, yanzunan duk bilkisunce ta had'a wad'annan kaya haka? Ya ALLAH ka albarkaci wannan yarinya da zuri'arta, ALLAH yakareta daga dukkan wani sharri itada zuri'arta. Su Amal sunata amsawa da ameen cikin jin dad'i. Bayan baffah yadawo Ammah tasaka aka kaimasa kayan, dakanta taje tamasa bayani, shima yaji dad'i sosai, sai albarka yake sakama matar tasa. Yace amma gawata shawara. To inajinka. Mu 6oye kayannan, akuma gargad'i yarannan suyi shiru dabakinsu, inason naga lefen da laura tace zata had'o itakuma, hartake masifa kar wanda yamata shishshigi. Ah wannan shawara taka tayi d'annan, aii babu matsala, amaidasu 6angarena to. *_Washe gari._* Hajia babba zaune da bataliyarta, dansu Anty zuwairah ma duk an iso, harda y'ay'anta, hakama Anty shukurah, akwatunane guda 3 agabansu, said'an kit karami, daga ganin akwatunan kasan irin wad'anda sukayi muguwar dad'ewar nance ashago ba'a samu masu siye da wuriba, Dan harsun fara tsufa. Shukurah tayi tagumi tareda zubawa momynsu ido da y'an uwanta, ganin yanda suketa d'aga kayan suna shewa da dariyar mugunta, gaba d'aya kayan ciki babu ko fasali, duk irin atanfofinnane leda aka zuba, saiwani shegen leshi da kalarsa kamar kagudu Dan muni kala uku, sai shadda d'aya dadai sauransu, ko'a k'auye baza'a had'a wad'annan kayanba. Komaidai babu tsari da mutunci aciki. Hajia babba ta ta6e baki, yo dakuke dariya badan gidannan banebama zata samu kamar wad'annan d'inne? Kuhad'asu akaima babanku da kakarku su gani. Shukurah batace komaiba, amma saida tayi kuka dan bak'in ciki. _____________,,, Baffah yagama ganin kaya tsaf yace ALLAH ya sanya alkairi, hakama Ammah abinda tace kenan. Su Anty Mamie ma duk sun gani, umme amarya data kasa shiru saida tace amma alhaji ba kayannan za aikaba dai?. To basu uwarsa tahad'aba Saudah?, suza'akai kuwa. A'a Dan ALLAH alhaji, wlhy bai daceba, gsky acanja shawara, nidai gatamu gufunmawar nida yaran d'akina, ayi hak'uridai babu yawa, 1.5million ne. Aii sune masu yawan saudah, ALLAH yasaka da alkairi kinji, amma tashiga saka mata albarka itada baffah, hakama Anty Mamie tanata godiya. Baffah yakira ya khaleel dake tsaka da aiki a office. Bayan sun gaisa yace dasafe naga baka shigo baneba lfy dai ko?. Wlhy lfy lau baffah, muna dawowa sallar asuhi nafita saboda akwai aikin danakeson kammalawa, yau da daddare jirgina zaitashi zuwa saudia kuma inagama sai ana jibi d'aurin aure zan dawo, shiyyasa nake had'a ayyukan dasukad'an cushemin. OK, tom zaka shigo gida dai ko?. Eh insha ALLAH, yanzuma Dana gama wannan aikin zan taho. To saikazo. Bayan la'asar yashigo gidan, saida yashiga ya gaisa da dakowa, sanan yaje wajen baffah, bayan sund'an tattauna akan bikin yanuna masa kayan auren, Na Anty Mamie Dana momynsa. Baidaice komaiba gameda kayan Momy amma fuskarta tanuna alamun 6acin rai, yakumayi godiya sosai akan Na Anty Mamie da umme amarya. Baffah ma baice dashi komai akan kayan momynba. 4days ago. Bayan tafiyar mama da kwana d'aya aka kai lefen Aysha Kano. Anmusu tarba ta mutunci da girmamawa, a 6angaren haiya babba Anty shukurah Ce kawai taje, saida sukaje Kano taga bakayan da Momy tahad'a baneba, tayi farinciki sosai Dan dama Abin nata damunta azuciya. Sunso ganin Aysha amma tak'i yarda, Dan bamata gidan, suna gidan Anty zainaba d'iyar kawu bilya itadasu Sadiya sauran amaren. Aranar suka juyo da shatara ta arzik'i, kowa yanata yaba lefen Na Aysha, suma sauran duk ankawo nasu Dama. Abinda kecin zuciyar Aysha baiwuce ya khaleel ba, musamman intaga yanda sauran y'an uwanta keta shirye-shirye da angunansu, amma ita banda ita, indama tad'anji sauk'i d'ayane Taheer yakirata akan zaizo kanon gobe danyaji abinda suke buk'ata Na y'anmata shidasu Joseph. Wannan ne yad'an rage damuwar tata kad'an.............✍🏿 💋💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤😍😍😍😍 [9/7, 1:21 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 9⃣ Washe gari da yamma saiga Taheer da Joseph, dukda babu angon nata taji dad'i sosai, batada wasu k'awaye dasuka wuce y'an uwanta, sai maleeka da Tasleem, komai a hannunta suka damk'a, dukda tasanar dasu babu wani Abu dasuka shirya. Kafin tafiyar nasune ya khaleel yakira wayar Taheer, bayan sun gaisa da maganganinsu yasanarmasa suna Kano. "Kano kuma? Mikukajeyi a kano?". Taheer yace, "Munje wajan amarya mana, kaibaka cemana komaiba gameda shirin biki, shiyyasa mukaga yadace muje". "Uhmm OK, to yanzu yakukayi?". "No babu komai, Gatama muna atare". "Bata wayar". Aysha dake magana da Joseph Taheer yamik'ama waya, ta amsa batareda sanin dawa zatayi maganarba Dan sanda aka kira Taheer matsawa yayi daga wajensu. Asanyaye tace, " Assalamu alaikum". "Wa'alaikissalam!, muryarsa tadaki dodon kunnenta, maganarsa takatse tunaninta"... "Kinajina? Banason wani shirmen day day d'inan, karnaji ance kunhad'a wani events na banza da wofi, dan bana buk'ata, nabama Amatullah sak'o tabaki, tundasu ranar Friday zasu zo nan kano, ni saima ranar zan dawo dasafe". Muryar Aysha a sanyaye tace, " ALLAH yatsare hanya". "Ameen ya amsa" yana yanke wayar. Su Taheer sukamata sallama suka tafi. _________________________,_ Ranar Alhamis aka sakasu Aysha a lalle, bawani taro akayiba, irin al'adar Malam bahaushe tada akamusu, matar yayansu Qaseem ta feshesu da turare da fauda, aka rangad'a gud'a akansu, shikenan. Sukad'an cigaba da sabgoginsu Na a are da k'awayensu. Aranar su Ameerah suka sauka daga Canada, Aysha tayi murna sosai tamkar anyi mata bishara, baby Raudat tayi girma sosai, yarinyar abin sha'awa wlhy, ifteehal tashige cikin k'awayen amarya anata abubuwan arzik'i, meerah kam tanataredasu Hafsat fadeeala dasu amal. Washe gari su Anty Ama... Suka iso suma, harda Anty Mamie da Ammah, su inna ma y'an Jigawa sun iso. Gidafa yayi dank'am dajama'a, abin ba'a cewa komai. Ranar juma'a aka d'and'asama amare k'unshi, gaskiya sunsha k'yau abin har ba'a cewa komai, sunje wankin kai da yamma, sanda suka dawo gidan ko'ina bak'ine, anata aikin gyaran kayan miya dadai sauransu. Aysha tafad'a jikin Anty Mamie tana murnar ganinsu. "Eyee kaga d'iyata amaryar kamshi, k'unshin yayi k'yau sosai wlhy, waye yamukune?". "Anty Mamie wata k'awar Anty Nasara ce". "Wacece Anty Nasara?". "Matar ya Qaseem. Kai gaskiya ta'iya sosai, kunsha k'yau kuduka". "A'a amaryar Yaya babu magana?".. "Hannu Aysha tasa tarufe fuskarta, kai Anty Ama....ALLAH ban gankiba, dama kinzo?". "Wai Aysha babumu abikin babban Yaya aii gayya ta 6aci, kintaho da kwana biyu Na iso, randa muka kawo kaya kuma kika 6uya mana, ya hidima?". Y'ar dariya Aysha tayi kawai batace komaiba. Nan dai abokan wasa suka cigaba da tsokanarsu. _____________________________ 10:23am jirginsa ya sauka Nigeria, su Adams sukaje suka d'akkosa, yana bayan mota zaune, sai amsa calls na jama'a yakeyi, musamman abokansa dasukasan da dawowar tasa. Bayan ya cire wayar akunnensa Adams yace, "aii Oga bak'ifa suncika tab wlhy, bakaga jama'aba, abin ba'a cewa komai, saidai ALLAH ya kaimu gobe a d'aura aurennan lafiya kawai". "To ameen Adams, yanzuma youseef ke sanarmin su Sameer sunkusa sauka suma, yazata bamubar airport d'inba mutsaya mutafi dasu, nacemasa mun baro". "Ai wlhy oga tunjiya babu abinda mukeyi sai kwaso jama'a kawai, a ciki da wajen Nigeria, aii mutum mai jama'a yamore arayuwa". Murmushi kawai ya khaleel yayi, amma baice komaiba. "Oga Asokoro zamuje kokuwa mai tama?". "Adams muje mai tama tukun, zanyi magana da baffah, kuma zand'an k'imtsa ko, saiku barni a can kukoma d'aukar su Sameer d'in, zuwa dare zan k'arasa can gidan". "OK sir, hakan yayi aii". 'Dan gwari yabud'e musu gate suka shiga, nanma gidan akwai jama'a sosai, y'an uwan mahaifin hajia babba sunzo sosai, hakama 6angaren mahaifiyarta Wanda sukazama dangin gidan, tunda da Ammah da mamanta uwarsu d'aya uba d'aya, danhaka sai dangin sukazama d'aya, wasukuma suna kano sai an d'aura aure gobe su k'araso abujar. Najwa d'iyar Anty zuwaira tazo da gudu kamar zata rungumeshi, amma saitaja birki, Dan wargima waje yaka samu, "uncle oyoyo". Murmushi yamata tareda fad'in "dota ank'araso kenan?". "Lah uncle yau kwananmu 6 fa a Abuja". "Eye kunsha Abuja abinku, muje ciki to". Kar6ar jakarsa tayi suka k'arasa ciki, tun afalo suka fara gaisawa da jama'a, wasu nad'an tsokanarsa da ango kasha k'amshi, amsarsa d'ayace murmishi. Saida yashiga 6angaren Momy suka gaggaisa da jama'a sosai, itama momyn sun gaisa a tsaitsaye saboda bak'i, yafito zuwa 6angarensu. Duk samarin gidan sunan hardama k'arin bak'i, sunbaje afalo kowa na harkar gabansa, wasu kallo wasu gugar kayansu na kwalliyar biki, masu danna waya nayi, masu hira nayi. Duk suka Shiga masa sannu da zuwa da gaisheshi. Ya amsa fusakarsa d'aukeda murmushi. Saida yashige sannan "Hafiz yace a lallai Yaya nason aurenan, irin wannan fara'a haka". Ramadan yace, "dagedai yajika, dawani kankan like kwakwa". Dariya sukayi gaba d'aya. So rayuwar families d'in tana burgeni gaskiya, komai nasu cikin mutunta juna. Bayan kamar awanni biyu yafito, ya tambayi su Musleem Anty Mamie fa? Yaga baigantaba da sauran yaran?. "Ya khaleel ai wad'annan sun tsufa a kano, tuda asuba suka tafi, dagamu sai baffa da umme amaryar saikuma Momy dasu Anty zuwairah aka bari".. Jinjina kansa yayi sannan yafita, yana nazarin hidimar bikin nasa. Yaje sun gaisa da baffa, Wanda shima yana tareda bak'i abokansa dasukazo daga Turkey, dakuma dad d'insu ya Naufal. Baffa yajashi gefe suka tattauna sosai, akan d'aurin auren na gobe, dakuma walima da aka shirya bayan d'aurin aure, wadda aka gayyaci manyan malamai dazasuyi lectures awajen, sannan baffah yabashi akwati guda na d'unkunan biki dayamasa. Godiya sosai yayma mahaifin nasa sannan ya sallamesu yatafi inda bokansa suke. bayan Momy takar6i kud'ad'e masu yawa a hannunsa. Acewarta sisinta bazaiyi kuka a bikinba, shida ya yarda sai dai ayi da gumimsa. Bai nemi ba'asiba yamata transfer yatafi. Yana shigowa abokansa suka saka ihun ganinsa, shima yayi farincikin ganinsu sosai, wasu andad'e ba'a had'uba, tun'a schools, harda wad'anda sukayi Secondary dakuma University, abokan aiki dakuma na kasuwa, y'an uwa da abokan arzik'i, nanfa akashiga hirar yaushe gamo da firar abokan ango dakowa yasani. Abdul'azeez yace, "wlhy mamaki nakeyi wai J! Da mata?". "Aii bakai kad'aiba cewar Nawaff, kasanfa wasanmu na k'arshe a k'asar Argentina damuka had'u nake masa maganar aure, cemin yayi babu rana". Mahmud yace, "aii mutumin namu akwai taku, amma dai bahaka zakajema yarinyar mutane kana mazuraiba?". Hararsa j yayi, "kai banason iskancinkufa, kai ince mazuran karingama Noor da billy, kaikuma Nawaff saboda jarabarka dafad'a kuka fara da Yasmeen ahad'uwar farko, su mai mata uku Abdul'azeez (Dady) kam aiba'a magana". Harara Dady ya wullah masa, "kai Malam yanzu matata d'aya my Munnerah kaji". Dariya suka shek'e da ita, Sultan yace, "wlhy auren mata biyu da dad'i, Juwairiyya takula dani, itada ikram d'ina haka, uncle G dake gefe yace kai malam my sopy ma ba bayaba, auredai dacene kawai". Mus'aff yace, "wannan gaskiyane, idan INA gaban My Nazeefa tamkar kwai a cokali nake". "Muzzaffar ya kar6e dafad'in wlhy haka Ameedah na take, tauraruwata kenan". Isma'il yace, "kukefad'a anaji, aii soyayya sai Iman d'ita wlhy". hummm kowa nasa yasani, kuje gidana kuga yanda Rahma ke riritani Cewar Abdulmaleek bobo. Umar Fharuk yashek'e da dariya, "amma sanda aka aura maka ita kanata wani dojewa kai na Ni'ima, hakanayi a lokacin aurena da Asma'u, amma yanzu kam babu kamarta". "kana nufin har Uwargida Lubna?". "Daga baya kenan malam". Shureim ya shek'e da dariya, "aiini nida my badar sai mutuwa". Khaleel da sauran abokan daketa binsu da kallo suka shek'e da dariya, "to iyayen soyayya, sannunku da k'ok'ari". "Yauwa Wanda bai iya soyayyaba, kaima aii zaka shiga layinmune, daga gobenefa". Sameer yace, "ALLAH kasadamu da matan kwarai, bilyn Abdull nimafa yakamata labarina yashigo layi gaskiya".😂👍🏻. Babu damu Sameer, kaine next insha ALLAH😂😉🤝🏻. Haka sukaita shafta d'insu, ranardai k'alilanne acikinsu sukayi barci, washe gari tunda 7:30 suka d'auki hanyar kano a motoci. Sun Isa lafiya, yayinda suka sauka a hotel, annan suka cigaba da shagalinsu har zuwa 12, daganan akafara shirin tafiya d'aurin aure. Gidansu Aysha. Cike gidan yake, da k'yar nake kutsawa cikin mutane, har Na isa inda su Aysha suke, a d'akin abbansu marigayi, y'anmatan da amare sunata kwalliya dacin gayu, amma banda Aysha, kwance take kangado tanata kallonsu, dukda d'unbin son datakema ya khaleel sai jikinta yay sanyi k'alau yau, tun d'azun takeson tayi kuka takasa, sunata rk'onta tatashi tayi wanka amma tak'i k'oda motsawa daga inda take kwance, hak'ura sukayi suka barta. *_RANA BATA K'ARYA...._* K'ofar gidansu Aysha dank'am yake da al'ummar annabi, kasancewar d'aurin aure biyar za'ayi, y'ay'an kawu bilyamin biyu. Sai Rufaida da Sadiya, sai Aysha. Dole kasancewata mace natsaya daga gefe har liman yafara sanar da d'aurin auren Rufaida, kasancewar itace babba, sai Aysha, etc...., gaba d'ayansu sadakinsu dubu 30 30 ne kacal. Ana gama d'aurin aure police Interpol da ainahin police, da sauran masu d'ammara daban-daban dasuka halarci d'aurin Auren, suka d'ana kunamun bindugunsu atare, kamar yanda suka shirya aka saki harbi lokaci d'aya, gabad'aya wajen ya hargitse, saboda abin yazoma jama'a babu zato, 🤣🤣zokaga gudu wajan jama'a🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃🏻‍♂🏃🏻‍♂🏃🏻‍♂🏃🏻‍♂🏃🏻‍♂🏃🏻‍♂🏃🏻‍♂🏃🏻‍♂, Dan harbinne na bindingu kusan 50+, kuttt idan bakayi bani guru, k'afa minaci banbakiba. Kanawafa sunzata bomb ne zai tarwatse dasu🤣🤣🤣🤣🤣😆😆. Aradu harsu baffah sun tsorata😂. Saida kowa yafuskanci wasan manyane domin girmama Ango sannan aka koma cin dariya datuna gudun da'akasha🤣🤣🤣. Canna hango muku xoxo da buje a hannu, mom of 12 kam filet d'in shinkafa tasaki ak'asa, su Aysha Umar anacan mamuke da Manshat data kusan sakin Zunnurain a k'asa. Hadiza muktar harda fitsari a kayan ankonta, tab danbakuga halinda Maman Khaleed da Zarah maigari sukashigaba da kdeey😂, jamila zozo da mamybmj ana can bayan durom, kuttt kunga nasiba a bokitin ruwan datti kuwa,🤣, Uwargida can Na hangota tasaka kai a drom d'in ruwa, y'an group d'in cikin da gaskiya kam ba'a magana, duk zumud'in tafiya bikin ya khaleel da ankon dasukeyi baihanasu kwasa agujeba, wasu takalma ahannu wasu d'ankwali, harda masu zani a hannu🤣, kuttmelesi kunga y'an taskar littafan Hausa kuwa, tashin hankali😌🤣🤣🤣, wasu harsunkai k'arshen layi, anasu dawo ga kaji suna fad'in sun yafe wlhy🤣🤣🤣, radu sunga mutuwa yau babu kwad'ayi. Falfala kenan wai Malam bud'e mana littafi, yaukam naga gudun gayu aradu, abin ba'a cewa komai, Na hauwa'un Janu yafi nakowa, idan nafad'a saikun toshe kunnuwa🤣, su d'an mom kuwa tuni aka baza babbar riga aka ranta cikin Na kare,. Hakama abokan Ango su Nawaff dabasusan da shirinba kowa yanemi ma6oya🤣🤣🤣. Abin yabirge ya khaleel, Dan baisan da wannan shirinba, aikam saigashi yana tuntsura uwar dariya😆, ya khaleel an iya dariyar mugunta😏. Damma baiga mata acikin gida baneba, dayayi wadda tafi wannan😜. Fans d'in ciki da gaskiya wlhy kun iya gudu zazuuuuuu🤣🤣🤣🤣👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻kenan. Lokacin da zance yashigo cikin gida and'aura aure sai Aysha ta rushe da kuka, Dan sai yanzu tasamu damar yin kukan datakesonyi tun d'azun. Nanfa dangi suka rufu akanta dasonjin ba'asi, kasa cewa komai tayi tacigaba da kukanta, (dolene duk macen da akace and'aura aurenta saitaji wani iri tareda ita😥, bawai Aysha kawaiba). Ganin tak'i yin shiru ifteehal takira Anty meerah. Babu dad'ewa tashigo d'akin, ita ta lallashi ayshar har tasakata tayi wanka, dak'yar tayarda aka mata simple makeup, tasaka doguwar rigar farar shadda kamar yanda sauran y'an uwanta suka saka. Bayan d'aurin aure aka zauna yin saukar alkur'ani, domin nemawa amare tabarraki, bayan ankammala saukane su Anty Mamie suka shirya tafiya, Dan tarbar amaryarsu gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai lokacin nagano muku ya khaleel dayaci kwalliya cikin farar shadda d'inkin babbar riga, Wanda yasha adon golden d'in surfani, hular kansa golden, hakama agogo da takalmansa sau ciki, fuskarnan washar da annurin angwaci, said baza kamshi yakeyi, Dan kusan kwalbar turare Taheer ya zazzage masa ajiki Dan shak'iyanci.😂 kwarjininsa da sihirtaccen k'yawu sunk'ara fitowa, babudai dariya, amma anama jama'a murmushi😊. Yanata gaisawa da abokansa, dakuma manyansa a wajen aiki dasuka halarci d'aurin auren. Saida komai yanatsa sannan suka tafi wajen waleemar da aka shirya, manyan malami sunyi lectures mai ratsa jiki, anci ansha kam alhmdllh. Bayan antashi baffah da gayayyarsa suka tafi, su ya khaleel kam sai washe gari zasu tafi da amarya Aysha. Dan haka da daddare suka shirya d'an biki a hotel d'in dasuke iyasu kad'ai abinsu, wajen ya k'ayatar sosai, sunyi nishad'i Alhamdllh. Adaren akakai su Rufaida, Aysha duk saida taje gidan kowa batareda ansan tabi y'ankai amarya ba😀. Bayan dawowarsu kam mama takirata, itama dangi suka sakata tsakkiya anata mata nasiha, tasha kuka kam, ranar tareda mama takwana. Washe gari...........✍ *_kowa ya shirya, yau sai abuja😜_* 🚗🚕🚙🚌🚎🚘🚓🚔🚖 😍😍😍😍😍😍😍😍😍 [9/8, 1:56 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣0⃣ Jama'a sunata shirye-shiryen tafiya Abuja, domin rakkiya ga Aysha. Itakam tanacan k'uryar d'aki sai zuba kuka takeyi, gabad'a tausayin kanta takeyi, tasan tana son ya khaleel, amma shi takula baidamu da itaba ko kad'an, jibafa tunda aka d'aura aurennan bataga idanunsaba, ahaka za'ayi rayuwar aure kenan?. Hayaniyar jama tafara jiyowa suna fad'in mitocin d'aukar amarya sunzo, gabantane yacigaba da fad'uwa, kukanta yak'aru, har rawa jikinta keyi saboda tashin hankali. Ahaka gwaggo Asma'u tashigo ta sameta, "haba Aysha, kekuwa bazaki daina kukannan bane hakanan? Kowafa dahaka yafara, yanzu y'an uwanki basun kwana gidan nasu mazajen ba, kinsandai tafiya babu fashi aii, kikamaje wata k'asar kikayi hak'uri zama babu mu bare nan gaki ga Yaya fad'ima, kinga tashi ki saka wannan hijjab d'in da nik'af kinji, yihak'uri bar kukan hakanan?". Haka taita lallashin Aysha harta kuma sakata ta k'imtsa, ankai Aysha tayi sallama da dangin mahaifinta tsofaffi maza da mata, aka kaita wajen Umma wadda takasa magana sai kuka itama, dak'yar aka 6an6are Aysha daga jikin Ummah, mama ankaita tayi sallama da ita, (ita sai zuwa jibi zata koma abujan). Haka akafita da Aysha tana 6arzar kuka, sanye take cikin atanfa ruwan zuma mai duhu da ratsin ruwan shanshanbale mai haske, hijjab d'intama ruwan Zuma, sai bak'in nik'af, tana kallon kowa tacikin nik'af d'inta, dukda har yanzun tanata kwarar da hawaye kuwa. Gabanta yafad'i lokacinda idonta ya sauna akan ya khaleel dake jingine da wata farar mota, rabonda taganshi harta mantama ita, sanye yake cikin shadda galila ruwan sararin samaniya, (sky blue) ya murza hula kalarta, hakama takalmansa, agogonsane kawai bak'i, yayi masifar yin k'yau, mayun idonsa k'yam akan Aysha da fuskarta ke lillu6e da Nik'af, dukda baya ganin fuskartata hakan baihanashi cigaba da kallontaba, baka Isa gane wane yanayi yake cikiba. Gwaggo Asma'u tace, "wainikam ko wancanne angon? Naga yakafe d'iyar tawa da idanu?". Dariya meerah tayi, tace, "gwaggo shine kuwa wlhy". Kai masha ALLAH, "ALLAH yabada zaman lfy dai". "Ameen ya rabbi gwaggo". Duk Aysha najinsu. Zungurinsa Sameer yayi, da sauri yamaido kallonsa ga Sameer d'in, yad'an sauke siririyar ajiyar zuciya. Sameer yace, " haba alhaji, gidankafa zataje, irin wannan kallo haka?". Baki ya khaleel yad'an ta6e, "kai nifa karkamin Sheri, ba kallonta nakeba, kawai tunanin yatafi wani wajene daban". "Hhhh j!, J! Ikon ALLAH, Na Aysha bada kanka asare kajegida kace yafad'i, d'ad'ina dakai komai naka akwai tsari, kana tunanin shan angwancine kenan?". "Hhmm wlhy Sameer kaima ka canja, yakamata Papa yamaka aure gaskiya". Dariya Sameer yasaka, hakan yayi dai-dai da isowar Joseph wajen, j! Zaka shiga motar amaryane? Kozaka tafi daban?. "Haba saikace wani kai, mubaha akeyiba, bakagama da y'an uwanta suka shigaba?". "Aii nazata zaka zauna agabane?". "A'a". Tom saiku tafi kaida su Sameer ko?. "Nifa karka had'ani da wad'annan, kasan zasu takuramin da surunsune wlhy". Dariya sukayi, Sameer yace, ''aikam zamu barka a kano wlhy". ___________ Kowa yagama shiga, motocin sun wadata alhamdllh, y'an anguwa anata d'agama amarya Aysha hannu, wadda tacusa kanta akan cinyoyinta tana kuka. To Aysha ALLAH yabada sa'ar zaman aure. Kunsan miya faru?. Harmun fara tafiya saiga gayyar motocin y'an CIKI DA GASKIYA...FANS, group 1,2,3,4, wai daga baya zasu tsaya kada abokan ya khaleel suk'ara irin najiya🤣🤣. Ammafa antara matsota😂. *_Abuja_* Sun Isa Abuja 2:pm dai-dai, saboda babu laifi sund'anyi gudu, kasancewar harabar gidan akwai mutane motocin suka tsaya ak'ofar gida, ta amaryace kawai tashiga cikin gida. Anty Mamie dakanta tazo tafiddo Aysha, Wanda ganin Anty Mamie yasakata kuma rushewa da kuka, lalashinta tashigayi. Anma bak'i tarbar mutunci, amma hajia babba da Anty zuwairah ko lek'owa basuyiba, Anty shikurah komai itakam tana aciki, ankai amarya Aysha d'akin Anty Mamie, kafin da daddare amaidata 6angarenta. Daga ita sai ifteehal a d'akin, saikuma wasu y'an uwansu su uku, zee da Saleema da Mimi. Hirarsu sukeyi cikin nutsuwa, amma Aysha batacewa uffan, tana kwance kangado tana saurarensu dabinsu da ido. Amal takawo musu abinci. Sukad'ai sukaci, amma Aysha ko saukama tak'iyi daga gadon Anty Mamie. Gayyar ciki da gaskiya fans kuwa aii dole aka bud'e musu d'aki guda agidan, dukda hakama yamusu kad'an, sundaiyi manege ne kawai, Dan kowa yasan hidimar biki yanda take, Baka Neman komai kasamu yanda kakeso. Haka akaciga da y'an hidimomi har zuwa 8 Na dare. Kowa yafara shirin dinner da abokan ango suka shirya, wadda shima baisan da itaba saida suka dawo daga Kano, babu yanda zaiyi tunda sunriga sungama komai, amma baiso hakanba gsky. _________________ Amarya Aysha ansha kwalliya, Hamdiyya tamata danta iya sosai, tasaka popul d'in doguwar riga, aka nad'a mata farin ashoke, tayi k'yau harta gaji, kowa fad'i yakeyi masha ALLAH, itakam gabanta sai fad'uwa yakeyi, tana tunani had'uwarta da ya khaleel, tunda tasan dolene amota d'aya zasu tafi. Isowar Anty shikurah ce ta katse tunaninta, ''Aysha tashi muje Yaya Na jiranki". Cikin marairaicewar murya Aysha tace, "wlhy Anty Ama kamarma afasa". Dariya Anty Ama tayi, " kiyi hak'uri kinji Aysha, shima ya khaleel d'in bada son ransa baneba, abokansa Na wajen aikine suka shirya batareda saninsaba, kinga kuma babu damar yace bazakujeba yasakasu asara". Kinga tashi muje karsuyita jira. Dole Aysha tamik'e, Anty Ama tarik'e hannunta, saima yanzu talura duk mutane sungama tafiya, gidan yayi shiru, Dan harsu hajia babba duk anacan😂. Anty Ama tabud'ema Aysha motar dake gabansu, zuciyar Aysha sai harbawa takeyi, ahaka tarumtse idanu tashiga tana karanta addu'a aranta. Kamshin turarensane yadaki hancinta, ta sauke numfashi da k'yar tareda had'iyar yawu. Lafewa tayi ajikin murfin motar bayan Anty Ama tarufesu. Ema...dake gaba zaya tuk'asu yace, "antynmu barka da dare". Yanda hausar tasa take gura-gura yaso bama Aysha dariya, amma saita dake tad'an murmusa tareda amsawa, takula ya khaleel ya yarda ta tuk'in EMA gaskiya, indai bashi zai tuk'a kansaba to zakaga Emanuel ne driver d'insa. Ta gefen ido tasaci kallon boss d'in, Wanda yayi tsit tamkar babushi a motar ma, sanye yake da popul d'in shadda irin ruwan kayan jikinta, d'inkin babbar Riga, sai farar hula akansa, yanata zabga k'amshi. Muryarta can k'asan mak'oshi tace, "ina yini?". Idanunsa dake a lumshe yabud'e ahankali, ya saukesu akanta, kwalliyar Tamata k'yau yafad'a aransa. Jin bai amsa mataba yasaka Aysha d'ago idanunta masu yalwar gashi ta sauke akansa, azatonta baijitabama. Da sauri ta janye idanunta saboda kallon ido cikin ido dasukaima juna, wani kwarjini Na musamman yak'ara mata, kanta tamaida taduk'ar tana kallon zanen material d'in jikinta. Babu wanda yasake cewa komai har suka Isa wajen dinner d'in. Abokan ango suka fito domin yimusu rakkiya, sunfara tafiya Taheer ya gwargwad'a masa wani Abu a kunne. Saida ya hararesa sannan. Taheer yamatsa baya yana dariya. Batareda Aysha tayi zatoba taji yarik'o hannunta ya rumtse anashi, atare sukaji shock, ya khaleel ya sauke sassanyar ajiyar zuciya, yayinda Aysha taji wata kasala tadaban, wadda ta k'ara haddasama tafiyarta sanyi ainun. Wajen atsare kuma cikeda jama'a, suna shigowa aka saki tafi, su Ammah ana gaba-gaba itada inna da baba jummai Maman hajia babba, Ammah sai baza hakwara takeyi Dan dad'i😁. Saida Aysha ta zauna sannan shima yazauna kusada ita, Dan kujera d'aya aka ajiye musu, amma basu matsuba saboda tanada d'an fad'i. Anfara gudanar da abinda yatara mutane batareda bata lokaciba, ayshadai tayi tsit tamkar ruwa ya cinyeta, tamkar ance tad'ago idonta yasauka akan Anty kubrah da glory, bak'aramin tashin hankali Aysha tashigaba, takai dubanta kan Anty meerah wadda tahango itama hankalin nata atashe yake. Innalillahi kawai Aysha take ambata azuciyarta, tsabar rikicewar datayi batasan ta d'ora hannunta kanna ya khaleel ba, jin tana Neman jimasa ciwo a bayan hannu yasashi juya hannunta yasak'ala nasa aciki, yatsunsu suka sark'e cikin najuna, tamatse kammm kuwa batareda tasan mitake aikatawaba, kallonsa yamaida direction d'in datake kallo saiyaga momynsace awajen da wasu mata biyu da kubra, yamaido kallonsa ga Aysha da idanunta ke zubar da siraran hawaye. Matso da bakinsa yayi saitin kunnanta, batareda tayi zaton maganar tashiba taji saukarta cikin kunnenta. Bashiri tadawo cikin hankalinta, tafara k'ok'arin zame hannunta, bai hanataba yasaki hannun nata, tareda mik'a mata hanky d'insa alamar tagoge hawayenta. K'ar6a tayi, tanamai satar kallonsa, Yakuma maimaita tambayar tasa. Suwanene su?. Gaban Aysha Yakuma tsananta bugawa, muryarta Na rawa tace, "suwaye?". Kafeta yayi da idanunsa, tayi saurin janye nata. Yace, " ya ina tambayarki? Kuma kina tanbayata?, banason shirme suwanene sud'in?, miyasaki kuka akansu kuma?. "Basu nakema kukakaba, nibanma sansuba, natuna Abbah ne kawai". Bai gamsu da zancentaba, amma ya shareta baisake cewa komaiba. Haka biki yacigaba da gudana, duk motsin Anty Kubrah da Anty glory akan idon ya khaleel da Aysha yake faruwa, kowa kuma da abinda yake kitsama zuciyarsa akansu. Meerah kam tuni tabar wajen dinner d'in, saboda bata buk'atar su Anty glo su ganta. Aysha da ya khaleel suka mik'e a k'ark'ashin jagorancin mc sukabi dukkan manyan iyayennan suna godiya agaresu, (Dan kowa zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kama gabansa). Lokacin dasuka Isa wajensu Ammah sai Ammah tajawo Aysha ta d'ora akan cinyarta, tana kukan farincikin ganin wannan rana ta auren a khaleel. Shikam yazauna kusada ita yana share mata hawayen da hannunsa yana murmushi, nanfa camera tafara aikinta, masu d'auka a waya nayi masu camera d'in da aka d'akko nayi. Konifa abin ya birgeni. Momy kam dasukaje gabanta saita dafa kan ya khaleel kawai, taki kallon ko Aysha. Ganin haka ya khaleel yakamo hannunta itada Ayshar yahad'e waje d'aya yarumtse, cikin sanyin murya yace, "ga momyna farincikina, ga matana amanata, namik'a muku amanar kaina, banida abokai mafi kusanci dani samadaku Momy & Aee'sha!". Hakan ya Sosa ran Momy, wai miyasa zai had'a matsayinta dana Aysha?, tazare hannunta batareda ta tankaba. Aysha kam taji dad'i harcikin ranta, sai damuwarta tad'an ragu, ganin kodai Yaya, ya khaleel d'in yadamu da ita. Idanun Anty glo nakan Aysha, sotake tatuna Inda tasan mai irin yanayinnan amma takasa tunawa. Kubrah kam wani d'acine aranta da kishi, tadad'e tana nunama ya khaleel d'in k'auna amma yana shareta, sai yanzu Dan abin kunya zai kwaso y'ar cikinsa amatsayin matarsa, ita kanta hasashen inda tasan matar tasa takeyi amma takasa tunanowa. Dasukaje wajen Anty Mamie kam tamkar ta cinyesu, itama rungume ayshar tayi tana kukan dabatasan dalilinsaba, tashafa kan ya khaleel tana saka musu albarka, da fatan nasara a Auren nasu. Komai ya gudana cikin nutsuwa da tsafta, zuwa 10:30mp aka tashi. Yanzukam Aysha batareda ya khaleel suka tafiba, mota d'aya suka tafi da Ammah. Shikuma yatsaya sallama da abokan arzik'i wad'anda zasuyi asibancin tafiya gida. Koda suka dawo gidan babu 6ata lokaci aka shirya Aysha akamata rakkiya 6angarenta. Tana kuka darok'on ifteehal takwana dan ALLAH nan suka barota suna dariyar shak'iyanci.😂 Bayan tafiyarsu saita kifa kanta akan filo tana kuka mai tsuma zuciya da tausayin kanta, kowane irin zama kuma zasuyi da mijin nata? Ya rayuwa zata kasance da surukarta? Makiyarta, wadda taso ruguza rayuwarta tun tana y'ar k'arama, ga k'annen miji da yayyensa marasa mutunci Acan kuma hankalin hajia babba tashe, Dan Anty glo da kubrah sungano ayshace amaryar bayan dogon nazari, dasake ganinta dasukayi lokacin da'aka dawo dinner ta wanke kwalliyar fuskarta, aka rakota wajen hajia babba amatsayin surukarta. Hankalin hajia babba amatuk'ar tashe yake, su Kansu su Anty glo hankalinsu atashe yake, haryanzu suna zaton Aysha da meerah suna cikin islands UK Ashe bahaka baneba, ya akayi suka dawo gida Nigeria? Lallai kam lik'o Na Neman 6alle musu kuwa. Hajia babba sai safa da marwa takeyi, gawata uwar zufa dake keto mata, shin ya'akayima takasa gane Aysha?, bazai yiwu d'anta yazauna da KARUWA ba. Aysha ba karuwa baceba☹😏. Ya khaleel dabaisan hidimar da akeyiba yashigo gidan kusan 12pm, tawaccan k'ofar yabi 6angarensu kenan, gaba d'aya jikinsa a sanyaye yake, waishine da mata yau, yanzu bashida hujjar k'in zuwa gareta sai ALLAH ya rubuta masa zunubi, tundaga lokacin da'aka d'aura auren dukkan hak'k'inta yadawo kansa, guda d'aya yatake sai ALLAH ya kamashi da laifi. Shikad'ai ya iso gidan, babu rakkiyar kowanne aboki. Da addu'a yatura k'ofar falon yashiga.............✍🏿 Yasin yatsuna zafi, zand'an huta gaskiya😿🤕🤧. 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘*_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣1⃣ A tsakkiyar falon yatsaya, yanamai binsa da kallo daki-daki, komai ya birgesa da k'ayatar dashi, gawani sassanyan k'amshi Na tashi, Wanda akasan duk gidan amarya dashi, yadire ledojin hannunsa Wanda shima baisan miye acikinsuba, Dan youseef ne yabashi. Rasa d'akin dazai dosa yayi, baisan ainahin d'akin da matar tasa takeba, yay shiru yana nazarin d'akuna ukku dake cikin corridor d'in, zuciyarsace tafi karkata dana k'arshe, cigaba yayi datakawa ahankali, kaikace yana tsoron Isa ga d'akinne. Harya k'arasa jikin k'ofar. Zuciyarsa tashiga harbawa da sauri-da sauri, shikam ba jarumi baneba awannan ga6ar, zai iya rantsuwa baita6a kasancewa dawata mace daba muharramar saba Na tsawon minti talatin, dagashi sai ita, saidai abokan aiki, suma basukad'aiba gaskiya, dolene kasamu akwai wani taredasu. Cikin rinmtse ido yamurd'a handle d'in k'ofar yashiga, bashida za6in daya wuce hakan, musamman idan yatuna da lectures d'in malamai data gudana a wajen waleemar auren nasa. Sallama yayi amma babu amsa. Jikin Aysha ne yafara rawa, danjin muryar Wanda batayi zaton ganiba a wannan lokacin, takuma cusa kanta acikin filillukan da aka k'awata kwalliyar gadon dasu, gaba d'aya jitai yau soyayyar datake masa tagudu, sai d'unbin tsoro da firgici dasuka maye gurbinsa. Cikin takun nutsuwarsa da jarumtar data zame masa halittar jininsa yak'araso gaban gadon. suduka zuciyoyinsune suka k'ara karfin gudun harbawa, saboda kusanci dasuka samu dajuna. Ya d'an lumshe idanunsa, tareda kauda kai daga kallonta, yama rasa ta'ina zai fara?. Jinsa tsaye akanta yakuma karyar da jarumtarsa, rauni da d'unbin fargabane kawai keta gudu da bugawar zuciyarta, tsoronta yakuma hauhawar farashi lokacin dataji ya khaleel yazauna abakin gadon, kusa gab da k'afafunta, da'ace zata motsama dolene koyaya ta ta6ashi. Wata jarumtace tazo masa alokacin daya tuna da wadda yake tare. Cikin muryarnan tasa, maikad'a hanjin marajjin magana yace, "k! tashi mana". Shiru Aysha batako motsaba. Yakuma fad'in "bak'ya jinane!!". Yanda yay maganar ad'an tsawace, amma cikin sanyin murya yasa Ayshan tashi zaune, idanunta nacigaba da zubar da hawaye, tagefen ido tasaci kallonsa, tsoro yasake kamata saboda cin karo da fuskarsa a d'inke, kamar yanda tasanta. Shima satar kallon nata yakeyi, yabi zara-zaran yatsun hannunta da kallo, lallen yamata k'yau sosai, daga bak'in har jan, yanda take hawaye saita bashi dariya, yau kam babu bakin rashin kunya, tausayinta yad'anji aransa, dan masu iya magana kance *aure yak'in mata*, amma yasan halin kayarsa, zumace saida wuta. Mik'ewa yayi tsaye yana fad'in tashi muje. Saida yakai bakin k'ofar sannan Aysha tamik'e da k'yar, bata sameshi a falonba, saikawai tasamu kujera ta zauna, jitake gabad'aya auren yafita aranta. Fitowarsace takatse mata tunaninta, saiyanzu tama kwalliyar tasa kallon tsaf, kayan d'azunne ajikinsa, amma yanzu yaje yacire babbar rigar, sai wando da riga y'ar ciki wadda dakad'an tawuce d'uwawunsa, yakuma cire hularma, sai kwantaccen gashinsa, Wanda baicika yawaba saboda askewa dayakeyi, hakama sajensa kwance yake luf, da'alama yad'an kwana biyu bai aske sajen nashiba, yasha gyaran fuska, wadda tafito da ainahin chocolate color d'insa, ya khaleel k'yak'yk'yawane, amma bazaka cedashi k'yawu ajin k'arsheba, komai nasa yana tsaka tsaki, idonsanefa dai ALLAH yabashi masha ALLAH, Dan manyane tubarkallah, ko mace sai haka wajen k'yawun idanu da girma, gasu farare tas, idan ransa ya6acine kawai zakaga sunyi jaa da k'ara fitowa, yanada k'yawun mai k'ayatarwa, Wanda zamu iya cewa kwarjininsane ya kuma fiddo taswurar k'yawun haibar tasa. Batasan yak'araso falonba, saimaganarsa taji yana fad'in "k tashi ki d'auka min filet da cup". Jikin Aysha amace tamik'e, saidai batasan inane kichin d'inba, amma tayi tsaye takasa tanbamayarsa. Tsaf yalura da nufinta, amma saiya shareta yad'auki remote yana k'ok'arin kunna TV. ‘‘ya khaleel inane kichin d'in?”. Shiru yamata, saida yamula Dan kansa sannan yanuna mata da hannu. Kichin d'in yayima Aysha k'yau sosai, komai atsare gwanin sha'awa, kala biyune kawai a kichin d'in, jaa dakuma Fari, kamar yanda falonta yake, ta d'auki filet da cup tad'ora bisa wani madaidaicin tire tafita. Yana zaune inda tabarsa, gabansa taje ta ajiye, ya nuna mata ledojin batareda yayi maganaba. Itama bata tankaba tasakko, harzata fara bud'e ledojin yasaka hannu yazare gyalen dake lulu6e da jikinta, saboda kid'ima saida Aysha tajuyo ta kallesa, harara ya sakar mata, tayi azamar janye idanunta da kwallah suka fara taruwa aciki. Ta d'auka tabud'e, ledar farko kayan fruit ne aciki, d'ayar kuma gasassun kaji guda hud'u, saikuma d'ayar ledar fresh milk ne aciki. Kaza d'aya tasaka a filet d'in tanata tashin k'amshi, tabud'e fresh milk tazuba a cup d'in. Tad'ago ido ta kalleshi, ganin idonshi akanta, ta janye nata, tanaso tacemasa tazuba amma takasa magana. “Shin waike kinzama kurmane yau?”. Kanta ta girgiza masa. Yace, "dabakinki nakeson ki amsa mini, dama Ashe ked'in mara kunyar k'aryace?". Itadai bata kulashiba tace, " nazuba maka". “kin zuba mana dai, ko kina nufin wad'annan kwala-kwalan idanun naki ba yunwa baceba?”. Shiru tayi bata tanka masaba, aranta tace, “dayakema talle bazatama Audi goriba, kaima kanada kwala-kwalan idanun, komawa tayi jikin kujera tayi shiru. Shima baisake cewa komaiba yasakko k'asan yazauna kusada ita, yunwa yakeji, rabonsa da abinci tun breakfast dayayi a Kano, fresh milk yad'auka yafarasha da bismillah. Saida yasha kusan rabin kofin sannan yacire tareda d'ora kofin kan bakin Aysha, d'ago idanu tayi suka had'a ido, takuma marairaice fuska ALLAH ya khaleel nak'oshi. Eh nasan kin k'oshi, nima aibance baki k'oshinba, ina jaddada sunnar manzon ALLAH ne (SAW), Dan haka bismillah. Akunyace Aysha tabud'e baki ta kar6a, baicire kofinba daga baki ta saida yaga ta shanye. Namanma koda yaci saiya kai baki ta, danma karta masa gardama saiya kuma had'e fuska, duk kunya ta dabaibaye Aysha, amma babu yanda zatayi, dole taita kar6a, ganin zaisata amai tace wlhy nak'oshi ya khaleel. Daina bata yayi yana fad'in gulmammiya, dama kinaso kiketa wani dojewa, amare natsoron cin kazar amarci amma ke kincinye guda d'aya sukutum, ammadai kinji kunya gaskiya. Aysha batasan sanda murmushi ya su6uce mataba, can k'asan ranta kuma tanajin nishad'i, ya khaleel ya ciyar da ita da hannunsa, batayi zaton samunsa da sauk'i hakaba, ganin halin ko'in kula dayake nuna mata kafin auren Nasu, azatonta kafin auren zata had'a watama bata ganshiba wlhy. Wringing d'in wayarsane takatse tunanin Aysha, shima cikin matuk'ar mamaki yace, "wanene a darennan haka? Yay maganar yana ciro wayar daga aljihun rigarsa, Momy kuma? to ALLAH yasa dai lafiya? Ya kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan yad'aga wayar. Maimakon muryar Momy saiyaji ta Anty Zuwairah. ‘Khaleel kana gida kuwa?’ tafad'a akid'ime. “eh ina gida, amma lfy a darennan?”. Babu lafiya khaleel, momyce keta murkususu harda suma cikinta Na ciwo....... Da sauri yamik'e yana fad'in, "subahanallah, ganina zuwa", baijira amsartaba ya yanke wayar. Amma zuciyarsa Na mamaki, ganin babu dad'ewa da dawowarau wajen dinner. koda yake ba'a mamaki da ikon ALLAH, saima ta iya mutuwa, wannan kad'an daga ikonsane. Aysha tace, “lafiya kuwa?”. “momyce babu lafiya, bara nadubo jikin Nata ”. To kawai Aysha tace, tareda fad'in, “ALLAH yabata lafiya”. Yana tafiya yana amsawa. Kokad'an batun baikama hankalin Ayshaba, tabbas tasan makircine, saidai tana tsoron kullin nasu. Da sauri tamik'e tashiga bedroom d'inta, wayarta tad'auka takira Anty meerah. "Lil sholy lfy kuwa da daddarennan? Ina kikabar mijin naki?". Yafita wajen Momy. Kamarya sholy?. Aysha ta zayyane mata komai tana hawaye, tak'are maganar da fad'in Anty meerah wlhy inajin tsoro". 'Dolene Aysha, Dan tabbas akwai abinda suka shirya, su Anty glo shaid'anune, nasan sun sanarma surukarki komai, yanzu ki kulle ko ina, kuma ki ajiye waya a hannunki, dakinji abinda bai gamshekiba ki kira ya khaleel ki sanar masa'. " Anty meerah banida number sa". 'Babu damuwa, bara nad'auka a wayar dadyn Raudat Na turo miki, ALLAH yasa da ita yake aiki, dannaga waya d'ayace a hannunsa k'aramar Nokia'. To amin, baradai Na turo miki. Babu dad'ewa Anty meerah taturo mata number ya khaleel, gaba d'aya a tsorace take, duk motsin dataji saita k'ara k'ank'ame jikinta tana addu'ar daduk tazo bakinta, tun tana saran shigowarsa harta fara fidda rai, har karfe hud'un asuba tayi, iskar asuba datake busowa ta taimaka barci 6arawo ya sace Aysha batareda ta shiryaba. Ya khaleel kam tunda yafita da sassarfe ya isa 6angaren hajia babba, cikin halin ciwo sosai ya isketa, yazauna abakin gadon kusada Anty Shukurah, suna d'akin itada Anty zuwairah da Anty glo da kubrah. Hajia babba tarik'e hannun ya khaleel tana fad'in zan mutu Ibraheem. "Ba zaki mutuba Momy". 'Anty zuwairah why not asanarma Dady mutafi asibiti'. 'A'a Ibraheem karku sanar masa, yana tareda bak'i'. Hajiya babbace mai maganar tana murk'ususn ciwo. Badan yasoba ya hak'ura, haka sukaita zama jigum-jigum, da barci yad'an figeta, sunfara yunk'urin tashi saita farka tana ihu. Glory da kubrah saisu kalli juna a sace suna y'ar dariya. haka suka kwana zubur batareda sun runtsaba. Saida sanyin asuba yafara busawa, ALLAH yaymusu maganinta barcin gaskiya ya saceta. Daga Anty Zuwairah har Anty shukurah sun galabaita da barci, glory da kubrah kam dake sunsaka kansune basu damuba, ya khaleel madai da sauk'in damuwar, Dan yarigaya yasaba, tunda wani lokacin aikin dare yakan kamasu. Ganin barci ya d'auketa yazare hannunsa dake rik'eda nashi ahankali, kuje kud'an kwanta tunda barci yad'auketa, zuwa Safiya idan ALLAH ya kaimu saimu tafi asibiti. anty zuwairah tace, “to khaleel sannu da k'ok'ari, anbar Aysha dai ita kad'ai”. “ALLAH yasa bata kwanta cikin tsorob”. ‘cewar anty shikurah’. "Yazatayi Anty Shukurah,? Inma tanajin tsoron aii dolene ta dainashi, tunda nid'in ba mazauni baneba”. Hakane "Amma Dukda hakadai akwai tausayi, amarya guda adaren farko babu ango". Kubrace da wannan maganar. Batareda ya tanka mataba yafice abinsa. Anty zuwairah ta ta6e Baki, yayinda kubrah taraka bayansa da harara tana maganar k'asa-k'asa, (wadda nima banajinta). Koda tashiga saiya fara cin karo da kayan dasukaci abinci. Tattaresu yayi da sauran naman duk ya kaisu kichin, ya ajiye komai Inda yadace, sannan yad'auki gyalenta yanufi d'akinta dashi. Akan gado ya hangota k'udundune da bargo, dagani kasan tayi barcin cikin tsorone, girgiza kansa kawai yayi yafice bayan ya ajiye gyalenta kan sofa.. d'akinsa yashiga komai tsaf, sai babbar rigarsa da hula d'aya cire ya ajiye bakin gadon, jin Anfara kiraye-kirayen sallar farko yacire kayansa yashiga wanka yad'auro har alwala, koda yafito jallabiyya kawai yazira bayan ya tsane ruwan jikinsa, ya shinfid'a sallaya ya kabbara sallah, raka'atainul fijir yayi, sannan yafita masallaci. Saida yafara shiga d'akin Aysha, tana nan yanda yabarta kwance, tunanin yanda zai tada ita yatsaya yi, ganin lokacin sallah zai kwace masa yad'an duk'o Kansa saitin Inda take kwance ya yaye bargo data lullu6a, yanda Kasan idonta biyu, tamik'e azabure tareda kwallah k'ara!!. Da sauri ya ruk'ota, "k Aee'sha nutsu mana nine, yay maganar tareda rungumeta ajikinsa". Jin muryarsa yasakata sakin kuka tana sauke ajiyar zuciya. Baice komaiba, saidai buga bayanta dayakeyi ahankali alamar lallashi. Aikam sai sabuwar shagwa6a tatashi ga Aysha, tacigaba da raira masa kukan, jin ana shirin Shiga masallaci ya janyeta daga jikinsa, kinga bara natafi masallaci, kema kitashi kiyi sallah, da hanzari yafice batareda ya kalli fuskartaba. Wani kukan Aysha tasaki, saida tayi mai isarta sannan tatashi ta d'auro alwala tayi sallah, tana idarwa takoma gado, Dan wani azababben barci takeji. Shima koda yadawo masallacin saiya shige d'akinsa ya kwanta, babu dad'ewa barci ya kwasheshi, dama ga gajiyar biki Na nukurkusarsa. ___________________________. Ya khaleel yariga Aysha tashi, saboda kiran da Taheer yamasa akan bak'ifa zasu tafi, yakamata yazo akawosu su gaisa da amarya amusu rakkiya. A hanzarce yay wankan ya shirya cikin farin boyal mai shara-shara, Dan har best d'insa ana gani, babudai hula amma yayi k'yau, turare yafesa kad'an sannan yafito yana saka ma6allin link d'in hannun rigarsa. d'akin Aysha yashigo da sallama, tana tsaye jikin madubi fitowarta kenan daga wanka, daga ita sai guntun towel. Batayi zatoba taji dallamarsa kuma harya shigo, cikin rikita tafara neman abinda zata rufe jikinta. Shima kallo d'aya yamata yakauda kansa tareda juya bayansa. Bayan kamar Monti biyu yajuyo Dan yanada tabbacin ta kimtsa, hijjab d'in datayi sallah tasaka, yakaimata har k'asa, taduk'ar da kanta k'asa saboda kunyar ganinta dayayi ahaka. Shima kanshi yaji wani iri, Dan hakan baita6a faruwa dashiba, ganin mace ahaka, bashiga d'akin k'annensa yakeba, bakumashi dalokacin kallace-kallecen films d'in banza, shi indai film baishafi bincike-bincikeba baya kallonsa. "Ehhm, bara naje zamuzo dabak'i, dan zasu wuce yau". Aysha tace, ''to, tana d'an satar kallonsa, kwalliyar tasa tamata k'yau, saidai fuskarsa babu walwala, itakam batasan randa zata fara ganin dariyarsaba". Juyawa yayi zaifita, tace, " ALLAH ya tsare". Ya amsa da amin ciki-ciki. Harya kama k'ofar zai fita tace, "umh....". Saikuma tayi shiru. Juyowa yayi yana kallonta, alamun yana saurarenta, ganin tayi shiru yace, " kinsanfa ana jiranane". Cikin jinjina kai tana had'iye yawu tace, "dama zancene bazaka karyaba?". 'murya a sanyaye tayi maganar'. "Saina dawo zan karya", 'yayi maganar yana fita'. A gaggauce yashiga ya duba Momy, amamkinsa saiya isketa ragal, tanata dannama cikinta breakfast. " A lallai Momy sauk'i yasamu? harkinsamu kina cin abinci?". d'an murmushi tayi tana gyara zamanta, "da sauki kam Ibraheem, jiki Alhmdllh, amma inazakaje haka kaci gayu?". " Zanje nazo da abokainane zakuyi sallama, duk yau zasu wuce". "To masha ALLAH, ya Aysha?". "Lfy lau take, bara naje Momy. koma wajen baffah bazan shigaba saina dawo". Sallama yamata yafita ad'an hanzarce. Itakuma tasaka dariya tana fad'in Ibraheem kenan, inhar ina raye bazaka ta6a had'a shinfid'a da y'ar isakar yarinyarnanba, lafiyata k'alau, nasan bazaka ta6a biyuwa ta sauk'iba shiyyasa na 6ullo maka tahaka, damacan natsani uwarta bare ita...............✍ Nace hummm, hajia babba sai ku zuba migani keda Aysha.🤝🏻😂 Wlhy banajin dad'i, ALLAH yasama Na iya typing gobe idan ALLAH ya kaimu😥, INA buk'atar addu'arku🙏🏻. 💋💋💋💋💋💋💋💋💋😍😍😍 [9/12, 6:48 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣2⃣ Yana fita Aysha tasauke ajiyar zuciya, hijjabin jikinta tacire tayi simple kwalliya, tasaka siket da riga Na atanfa, kayan sunmata k'yau sosai, amma ita kokad'an bawani tadamu da sawar baneba, saboda gargad'in da mama tamatane kawai take kiyayewa. d'akinta tagyara tsaf, tasaka turare sannan tanufi falo shimadai gyaran kad'an tamasa tasaka turaren, tayi mamakin rashin ganin kayan abincin jiya, aranta tace, "k'ila ya khaleel ne yad'auke". Harta nufi hanyar kicin taji ana Knock d'in k'ofa, tajuyo dabaya danufin dubawa ya khaleel yashigo da sallama, Aysha ta amsa kanta ak'asa. d'an nesa da ita yatsaya, idonsa kyam akanta, saidai fuskar haryanzu babu walwala. yace, "tarenake da bak'i, kinzo kin tsayamin akai, kije kisaka hijjab zasu shigo". Haushine ya kama Aysha, batasan ta murgud'a masa bakibama, tawuce tana k'unk'uni batareda yaji mitake cewaba, ransane yad'an sosu, amma saiya danne yayimusu iso zuwa ciki, Dama suna bakin k'ofane tsaye. Masifa natacin Aysha a zuciya tana d'akko hijjab a wardrob tana tsogumin yanda halayen ya khaleel yake, shidai bazai ta6a kuyi magana mai dad'iba dashi, to yaushema yasakema mutane fuska, itafa gaskiya bazata iya wannan rayuwarba..... Tajiyo bayan tad'akko hijjab d'in danufin rufe wardrobe d'in taji tabuge Abu, ad'an figice tawaigo dansan ganin minene?. Bak'aramar fad'uwa gabanta yayiba ganin ya khaleel tsaye abayanta, kokad'an bataji alamar shigowarsaba. "Zan.....zan wu wuce". Tayi maganar cikin in ina da rawar baki, jikinta sai tsuma yakeyi. Bai motsaba, kuma bai tanka mataba, fuskarnan babu alamar sauk'i. Hakan yak'ara saka Aysha cikin tsoro, tatura murfin wardrobe d'in tareda jingina ajiki, idanunta Na kallon k'asa tana k'arema yatsun k'afafunsa kallo. Yayinda shikuma itad'in yake k'arema kallo, baita6a damuwa da kallon ya Aysha takeba a can baya, amma ayanzu saiya samu kansa dabin halittar jikinta da kallo daki-daki. Kad'an tad'ago ido ta kalleshi, ganin kallon k'urillar dayake matane tayi saurin saka hijjab d'inta. Yalumshe manyan idanunsa yana kauda kansa, Aysha tara6a ta gefensa zata wuce cikin d'ari-d'ari. Da sauri yaruk'o hannunta, cikin Aysha yabada k'ululu!.. "dawo magana zamuyi". Jiki a sanyaye tadawo baya, kafin yace wani Abu wayarsa tafara ring. Cirota yayi yaduba, taheer ne, batareda yad'agaba yasaki hannun Aysha yanufi k'ofa, saida yabud'e sannan yace, "kizo Ku gaisa, zasu tafine, sannan kitanaji bayanin dazaki Kare kanki akan murgud'amin Baki dakikayi". 'Baijira cewartaba yafice abinsa'. Bak'aramin rud'u Aysha tashigaba, itama tasan hakan ba daidai baneba, amma wlhy rantane bayason dizgin dayake mata. Jiki a sanyaye tabi bayansa, gudun karta k'ara wani laifin. Sannu da zuwa tamusu tanufi kichin, sukuma suna tsokanar ya khaleel d'in, wai daga kira yayi bulum ad'aki, miyakeyi?. Tsaki yayi yana hararsu, yaxauna a kujera yana ''fad'in duk abinda zuciyarku tabaku shi Ibraheem khaleel yakeyi". Dariya sosai suka Sanya masa da shak'iyanci irinnan abokai. Ayaha tafito daga kichin d'aukeda babban tire dake cikeda drinks, ta ajiye a tsakkiyar falon takoma, babu dad'ewa tadawo da snacks, ta ajiye takoma tad'akko glass cups, duk suka mata sannu. Cikin kunya take amsawa, anutse tagaishesu, duk sun yaba da ayshan, harsuna taya abokinsu burna azukatansu, sunta tsokanarta irinnan abokan miji, bata iya cewa komai saidai murmushi. Ya khaleel kam saima karantse baya falon, waya yaketa dannawa batareda saka bakinsa a zancensuba. Aysha tamik'e tabar musu falon dansu d'an ci abinda ta ajiye musu. Shigarta d'akinta da y'an mintuna saiga anty glo...da kubrah, saida suka gaisa dasu ya khaleel afalo sannan suka shigo, bisa umarnin ya khaleel d'in. Zumbur Aysha tamik'e daga bakin gadon, Dan batayi zaton ganinsuba. Anty glo tashek'e da dariya tana "fad'in sholy amarsun ango, Ashe dama tsoron john Na k'aryane kikeyi, koda yake naga kinzama y'ammata, ina Antyan taki meerah?". Amamakinsu sai sukaga Aysha tayi murmushi, takoma bakin gadon ta zauna tana musu wani kallon rainin hankali, "mtsowww! Wlhy ku kama kanku, kenaga kanki rawa yakeyi glory!, inaga dai k'awar taki bata sanar dake wanene mijin nawaba ko? Karfa wajen tone tonen kaza, tatono wuk'ar yanka kanta". Kubra tabud'e baki zatayi magana kenan ya khaleel yaturo k'ofar ya shigo, kallo yabisu dashi su duka, glory da kubrah sund'anji shock da shigowar tasa, Aysha kam ko'a kwalar rigarta, Dan zuwa yanzu batak'i komai ya 6aciba. Ko kallo su kubra basu isheshiba, yace, ''taso kuyi sallama zasu tafi". Aysha tamik'e itama batareda ta kalli su kubra d'inba tanufi k'ofa. Ganin haka suma dole sukabi bayanta, bak'aramin Sosa ransu lamarin yayiba, suna mamkin yaushe Ayshan tawaye har haka? Lallai hajia laura kallon baibai takema Aysha, kuma dolene sud'auki mataki akan Aysha da meerah, Dan zasu 6allo musu ruwane. Bayan tafiyarsu glory da abokan ya khaleel, mutanen Kano sukazo mata sallama, kowa dai yak'ara mata nasiha, gayyar ciki da gaskiya fans ma sunzo sallama, cikin mutunci Aysha ta kar6esu, ko'ina sun zagaya a gidanna Aysha, sannan suka mata sallama suka tafi, harda 'yan kwallanta kuwa, acikin fans d'in ciki da gaskiya kuwa wasu basuso tafiyaba😂🤧😜. Amma na tusa k'eyarsu gudun samun matsala,🤣, karsu ragema ya khaleel jin dad'i💺😏🤧kundai gane😉. To Alhmdllh bak'i sunyi halin ruwa, gida yayi tsit, saisu Anty zuwairah da y'ay'ansu kawai. ______________________________ Har 4 ya khaleel bai shigoba, Aysha tad'an damu, ko breakfast baiyiba, Na ranama da Anty Mamie ta aiko itakad'ai taci. Yanzu haka saboda bak'in daketa kara kaina shiyyasa yak'i shigowa. Bayan tayi sallar la'asar takuma gyara ko ina da'aka 6ata, gidan yad'auki k'amshi, babu wuta gakuma babu Wanda yashigo, ta zauna shiru tana tunanin ina ya khaleel yashiga? Tundaga rakkiyar 6ak'ifa. Jitayi ana Knocking d'in k'ofa, tamik'e a d'arare taje tabud'e, su Tasleem ne d'aukeda abinci, rungume juna sukayi Dan duk yau bata gansuba. Suka shiga tsokanarta matar yaya matar Yaya. Nandai suka zauna sunata hirarsu, ananma suke bata labarin soyayyar tasleem da maheer, maleeka da shakur, sosai Aysha tayi farinciki. Suna cikin hirar ya khaleel yashigo. Kowa yay tsit, suka shiga gaisheshi da sannu da zuwa. Bayabo babu fallasa ya amsa tareda nufar d'akinsa. Su Tasleem suka mik'e, rok'onsu Aysha tashigayi akan su zauna, basu sauraretaba suka gudu. Tarasa miya dace tayi?, tana nan zaune inda suka barta ya khaleel yafito, ya sauya kayansa zuwa jallabiya blue black, ya zauna afalon bisa 2sita, tareda ajiye system d'insa dake hannunsa da wayoyi. Mik'ewa Aysha tayi tashiga kichin, yabita da kallo a munafunce. Bata dad'eba tafito d'aukeda k'aramin tire, tad'oro ruwa da cup, sai drink. Harya kunna system d'insa yafara aiki, da'alama aikin mai muhimmancine, kuma yazo masa a gaggaucene, ruwa Aysha tafara zuba masa, ya kar6a hankalinsa nakan aikinsa, saida yasha ya ajiye cup d'in sannan yad'an d'ago ido yakalli Ayshan, kallon dabaifi second4 ba yamata yajanye idonsa, "wazai gyaramin d'aki?", 'Yay maganar murya adake'. Kunyace takama Aysha, Dan yakamata ace tunda safe tashiga ta gyara, to amma tsoron dizginsa takeyi, murya a sanyaye tace, ''kayi hak'uri, wlhy bak'ine sukamin yawa, amma zan gyara yanzu, sannan ga abinci, naga ko break fast bakayiba kafita". Baice da ita uffanba, saima k'ok'arin amsa call yakeyi, "hello Joseph!, yawwa nagani, amma yakamata kunema mana bayanai akan Ak'ilu Abbas d'innan, Dan banyarda dashiba, idan kanutsu akan zancensa akwai kalamai masu kama da rashin gaskiya, ina Hutu amma tilas gobe idan ALLAH ya kaimu nafito aiiki, Dan zankama Lazarus da kainane". "OK babu damuwa, kausar da fharuk sumin binciken asusun bankinsa, inason bayanai kuma akan hajiar data tura massege wa Barau modibbo, awaccan ranar". Bayan ya sauke wayar yakalli Aysha dake tsaye tana saurarensa, yace, " waye barau modibbo? ". maganarsa takusan sakata fitsari atsaye, tawaro idanu akansa batareda ta shiryaba, tace, "ya khaleel kamarya? Wanene barau modibbo?". Kafeta yayi da mayun idanun nan nasa, masu hana Mara gaskiya zaman lfy, soyake yagano ainahin gaskiyarta, muryarsa adake yace, "idan ban mantaba, aranar na rutsaki kina waya a garden, sannanma kena aika kika d'akkomin guns ad'akina, kifad'amin gaskiya, kece kika turamasa massage akan yagudu?". Innalillahi wa'inna ilairirraji'un, "wlhy ya khaleel bansan komai gameda hakanba". Ahankali ya lumshe idanunsa sannan yabud'e akanta, "shikenan jeki kiyi aikinki". Innalillahi kawai Aysha take ambata azuciyarta, tana mamakin miyasa tun awancan lokacin baimata maganarba sai yau?, tabbas bata shakku akan zarginta hajia babbace, Dan tata6ajin sunan barau modibbo abakin Anty kubra lokacin suna UK, ayanzune yakamata tayi aikin sirri da ya khaleel batareda yasaniba", tasaki murmushin mugunta. d'akin nasa yabirgeta sosai, komai farine tamkar tsohon d'akinsa, cikin nishad'in samun bakin zaren tona asirin su hajia babba tafara aikinta. Ya khaleel kam koda tabar wajen saiya bita da kallo, wasu al'amura Na yarinyar suna bashi mamaki, tundaga randa abinnan yafaru yad'ora zarginsa akanta, amma zuciyarsa tak'i amince masa, tana nuna masa hatsabibancin yarinyar baikai nanba, to amma wacece? Yasha bibiyar Ayshar amma baiga wani abun rashin gaskiya tattare da itaba, yafurzo zazzafar iska daga bakinsa, Kokuwa badaga 6angarensa mai tura massage d'in takeba?, yakamata yabinciki Joseph Taheer youseef, alokacin dazasuje kama barau modibbo awaccan ranar suna inane?. Da wannan tunanin yacigaba da aikinsa. Aysha tagama gyara komai tsaf tafito, dama babu wani datti. A inda tabarsa anan ta iskesa, yakuma maida hankalimsa gaba d'aya akan aikinsa, itama saikawai tamaida hankalinta ga TV. Lokaci-lokaci yakan d'ago ya kalleta, yamaida kansa, ahaka har aka kira sallar magriba, yarufe lap-top d'insa yamik'e danyin alwala yana "fad'in kidafamin shayi kafin nadawo". Aysha ta amsa da ''to tana mik'ewa itama". ______________________________ Yauma abinda yafaru adaren jiya shiyya faru, bayan dawowar ya khaleel daga sallar isha'i kaitsaye d'akin Aysha yashiga, gama wayarta da Anty meerah kenan tafad'a mata komai akan zuwansu kubrah da tuhumar da ya khaleel yamata, sunk'ullah hanyar dazasuyi aikin sirri da ya khaleel batareda ya fahimci suneba. Khamshin turarensane yasaka Aysha d'agowa, Dan ciki-ciki yay sallama, cikin hanzari tafara Neman hijjab d'inta ta sanya, Dan k'ananun kayane ajikinta, sunkuma kama jikinta sosai amma sunmata k'yau. Jiyayi wani Abu yadaki zuciyarsa yay azamar kauda kai daga kallonta, itama cikin in ina take masa sannu da zuwa. Kansa kawai ya gyad'a mata yajuya zai fita yana fad'in zoki bani tea. Aysha batajin dad'in yanda yake mata wlhy, amma yazatayi, insha ALLAH zata canjashi kamar yanda Anty Mamie tasanar da ita, (mace takan canja namiji duk a yanayin datakeso, cikin hikima da ilimin da ALLAH ya bata irinna y'a mace mai daraja), ajiyar zuciya tasauke, afili tace hakane Anty Mamie, insha ALLAH nima zan gwada. Saida ta zumbula hijjab sannan tafito, zaune ta iskeshi da remote ahannu yana Neman tasha, tabi tabayan kujerar dayake zaune tanufi kicin, babu dad'ewa tafito d'aukeda tire k'arami Wanda tad'ora k'aramin filas da mug, taja table gabansa ta d'ora, tana k'ok'arin fara zubawa yace, "cire wannan hijjabin". Da sauri Aysha tad'ago ta kalleshi. Ya harareta, ''miye kikawani tsareni da wannan kwala-kwalan idanun? karfa zuciyarki tafad'a miki shirme, danbakida abinda zan kallah ajikinki, mtsoww". Maganarsa ta 6ata mata rai, ta janye idanunta daga kansa tana murgud'a baki. Ganinta kawai tayi a cinyarsa, amma batasan tayaya ta hauba.........✍ Kuyi manage da wannan jikin babu kwari😟. *_ina tayamu murnar shiga sabuwar shekarar musulinci, alkairin dake cikinsa ALLAH ya sadamu dashi, shirrinkuwa ALLAH ya nisantamu dashi, ALLAH ka gafartama mahaifanmu dadukkan y'an uwa musulmai baki d'aya, muma ALLAH ka gafarta mana, kacika zuciyarmu da tsoronka da soyayyar ANNABINMU (SAW), ameen._*🙏🏻 _ngd da addu'oinku gareni, masu kirana daturomin sak'o dukna gode, ALLAH yak'ara mana lfy baki d'aya ameen._🙏🏻🤝🏻💋💋 ❤❤❤❤❤💋💋💋💋💋💋💋💋💋. [9/13, 7:32 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣3⃣ Yayi mugun had'e fuska, tsoro da fargaba suka mamye zuciyar Aysha, yasaka yatsunsa biyu yamatse bakinta, hawaye kawai tafara zirararwa amma babu damar kuka. Jin yana Neman tsinke mata la66a takama tsintsiyar hannunsa tarik'e kam, yay tsaki tareda watsa mata wani mugun kallo, "ni sa'ankine ko? Miyasa raini keneman shiga tsakanina dakene?", yakuma matse bakin "zaki kuma murgud'amin wannan bakin naki maikama dana tsuntsu?". Aysha Na kuka da k'ok'arin janye hannunsa tashiga girgiza masa kai. Saida ya tabbatar taji ajikinta sannan yasaki bakin yana fad'in " fitsararriya kawai". Aikam saita fashe da kuka tana k'okarin tashi daga jikinsa, maidata yayi ya kwantar bisa k'irjinsa yana jan k'aramin tsaki, “ki tsaidamin wannan kukan kafin nakuma hukuntaki”. Da k'yar ta had'iye kukan, shikuma yatsura mata idanu yana dariya a cank'asan ransa, yajanye hannunta data dafe bakinta dashi yana fad'in, “o, sholyn Anty meerah naga le6en baicireba dai ko?”. Sosai Aysha tarazana da sunan daya kirata dashi. Shikam baima nuna yasan miya fad'a d'inba, saima zagaya yatsansa dayakeyi bisa la66anta, Aysha tabud'e baki danufin tambayarsa ina yasan wannan sunan?. Saikawai taji bakinsa cikin nata. Ya salam tafad'a acikin ranta, jikinta yafara rawar mazari, yaune rana ta farko da'aka ta6a kissing nata, shikansa jikinsa tsuma yakeyi, danbai ta6a tsintar kansa a wannan yanayinba, tuni zuciyoyinsu suka k'ara k'arfin gudu, wannan yak'arama khaleel k'aimi a sabuwar duniyar daya tsinci Kansa. Aysha kam hawaye sunjik'e fuskarta, tsoro kuwa yazama shike tafiya da gudun jininta, sai k'ok'arin tureshi rakeyi amma takasa, mamaki yacika zuciyarta, dama haka ya khaleel yake shima?, shi baima San tanayiba, danya tsinci kansa aduniyar dabaisan haka takeba, saida ya dirji bakin Aysha San ransa sannan yacire bakinsa yana sauke numfashi, rungumeta yayi tsam ajikinsa yana shafa bayanta alamar lallashi, saboda kukan datake rera masa. Bayan shid'ewar wasu y'an mintuna yad'agota, tadaina kukan saidai shashsheka, kunya dukta lullu6eta, jitake kamar ta tsaga k'asa tashige, ta rumtse idanunta GAM danta kasa kallonsa.. Murmushi yayi, yasunkuya ya sumbaci la66anta dasukayi jajur saboda punishment dasuka fuskanta a hannun boss, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, “bud'e idonki kona k'ara........". Baima rufe bakiba Aysha tabud'e idonta da Sauri suka had'a ido, tayi saurin janye nata, Dan ganin yanda nashi suka canja kala, lallausan hannunsa yasaka ya tallafo fuskarta data maida gefe. Zata rufe ido yace, “bud'esu ki kalleni!”. Da sairi tabud'e danjin yanda yay magana adake. Jikin Aysha yafara rawa, harga ALLAH bazata jure kallon kwayar idanun ya khaleel ba, shima lura dahakan yasakashi sakin guntun murmushi, yajanye idanunsa daga cikin natan, “daga yau zaki kuma murgud'amin baki?”. Da Sauri ta girgiza kanta tana matso kwalla, gaba d'aya tsoronsa Yakuma kamata, tundaga john take tsoron maza arayuwarta. “dabakinki zakimin magana, banason raini”. Kafinma yak'arasa tace, “kayi hak'uri ya khaleel wlhy bazan sakeba, wancanma kuskurene”. Yanda ta marairaice fuska tana masa magana saita bashi dariya, amma ya gimtse fuska yace, “idan kika sakefa?”. "Wlhy ka d'auki kowane mataki". “kowanne matakifa kikace?”. “eh, wlhy Na amince”. "OK to shikenan, tashi ki had'amin shayin". Dasauri tamik'e tafara cika umarnin Oga, saidai duk kunya ta isheta saboda kayan jikinta. Shikam Yakuma jikin kujera ya lafe yana kallonta k'asa-k'asa, saika d'auka idanunsa arufe suke, amma duk wani motsinta akan idonsa yake, tagama tamik'a MASA mug d'in tea d'in. Raba hankalinsa yayi gida biyu, rabi a kallon labarai, rabi akan Aysha, yana shan shayi yayinda k'asan zuciyarsa ke shirya masa wani Abu daban. Aysha dai Baki yamutu, tanacan lafe cikin kujera 1seat abin duniya dukya isheta, dama duk maza haka suke da halinnan?, tana kallon ya khaleel kamar babu ruwansa Ashe Bahaka baneba, shi ko kunyama bayaji Yakama tsotse bakinta, tashafa la66anta da har yanzu suke mata zogi, hawayene Yakuma cika idonta, amma tahanasu zubowa. Ring d'in wayarsace tasakata juyawa ta kalleshi, wayar na aljihunsa yana k'ok'arin cirowa, ahankali yafurta "Momy kuma? Badai jikinba?" Dan da yamma daya shiga ya tarar da ita tanama Anty zuwairah complen cikinta da k'irjinta sun fara ciwo, saida yace, "suje asibiti" amma tace, "ad'an bari zuwa anjima tunda tasha magani, idana baidenaba saisu jed'in". Cikin damuwa yad'aga wayar, "ya khaleel jikin momyfa yayi tsanani", 'cewar mufeeda datayi kiran wayar'. Yanke wayar yayi batareda yace komaiba zai fice, Dan hankalinsa a tashe yake. Aysha kamar zatayi kuka tace, " jikin momynne?". Baiyi maganaba, amma ya jinjina mata kai yafita da hanzari.. Kuka Aysha tafashe dashi, Dan wlhy tsoro takeji, tasan kuma tashiga cikin gida yanzu fad'a za'a mata miyasa zata baro d'akinta, batada damar shiga 6angarensu Anty Aymana kuma, dan duk mazajensu nanan, tana mamakin mugun k'udiri irinnan Momy, tarasa mita tsare mata aduniyarnan, tasan tanayin hakane Dan k'untata rayuwarsu, amma babu komai ALLAH nanan. Tashi tayi ta kulle k'ofar falon, tadawo ta kwanta saman doguwar kujera, kallo takeyi a tsorace dajiran dawowar ya khaleel, amma har 2pm babu alamarsa, kashe TVn tayi dama bata fahimtar komai, takwashi wayoyinsa da lap-top tanufi d'akinta, bata yarda yau tayi zaman wahala da tsoro irinna jiyaba, saita d'auro alwala tazo taita sallah da karatun alkur'ani, wannan yad'auke hankalinta har tayi sallar asubahi sannan tazame a wajen ta kwanta. Su ya khaleel yauma kwana sukayi akan Momy, Dan jikinma yafi jiya tsanani, dukkan y'ay'anta Na gewaye da ita, harsu hasnah sunanan, Tanana a kira kowa, har baffah, haka suka kwana azaune zubur. Ya khaleel baidawoba saida gari yayi haske bayan yayi sallar asubahi, saida yalek'a d'akin Aysha sannan, akan abin sallah yaganta kudundune cikin hijjabinta, ga alk'ur'ani a gefenta, tabashi tausayi, ya d'auketa tamkar wata babe ya kwantar a kan gadon, cikin dabara yazame mata hijjab d'in ya lullu6eta da bargo, sannan yamik'e yafice daga d'akin. Bai kwantaba yau, Dan akwai aikin dayakeson yi ayaud'in, dukda yana cikin hutun angwanci, shirinsa yayi cikin uniform d'in aiki, masu k'ara masa kwarjini da cikar haiba, yashiga d'akin Aysha yana d'aura agogo, haryanzu tanata barcinta, yad'auki lap-top d'insa da wayoyinsa yazuba a jaka, sannan yad'anyi short not ya ajiye mata kan madubi yafice su Adams na jiransa awaje. Ta gate d'insu yafita, Dan haka babu Wanda yasan fitarsa acikin gidan. Atare sukayi salute nashi, yad'aga musu hannu damusu godiya akan hidimar bikinsa dasuka tsaya tsayin daka aka kammala lfy. Adams yabud'e masa motar yashiga, sannan suma duk suka shiga. ___________________________ Aysha bata farkaba sai around 10, ta tashi d'aukeda addu'ar barci abakinta, tayi mamakin Wanda ya maidota saman gadon, aranta tace, "k'ila ya khaleel ne". A gaggauce ta k'imtsa kanta, saida tazo gyaran d'akin sannan talura babu wayoyinsa da laptop, d'aukar y'ar takardar daya ajiye tayi, written d'in yamata k'yau. _“Nad'an fita wani aiki, amma insha ALLAH bazan dad'eba zan dawo.”_ _“ki kula da kanki.”_ Aysha tayi murmushi, tareda maimaita _ki kula da kanki_ sau babu adadi, kalmar Tamata dad'i sosai, aganinta wannan kalmace dake nuna kulawa akan abinda kadamu dashi, "kenan ya khaleel yadamu da ita?", takai hannunta tana shafa la66anta datuna abinda yamata jiya da daddare, ta sumbaci takardar tanamai lumshe idanunta, ahankali tafurta ina k'aunarka sosai ya khaleel, Dan ALLAH Nima kasoni fiyeda yanda nake sonka, (Dan bazaka ta6a Sanin inasonkaba harsai kafuta soyayyata da bakinka), zan rayu dakai, zankuma mutu da sonka, Abadan inafatan mukasance tare har mutuwa, dukda mugayen dake zagaye da rayuwar aurenmu, amma ALLAH zaimana maganinsu da k'arfin ikonsa. Haka taita sambatun begensa ita kad'ai, tanayi tana aikinta, tsaf tagyara gidan, ko ina yad'auki k'amshi, har d'akinsa saida takuma gyarawa, dukda babu wani datti, tunda baikwana acikiba. ____________________________ Su ya khaleel kam suna can sunyi fakon Lazarus, babban yaron Ahaji bishasha, Wanda suka sami damar kamashi a babban shagon saida kayan masarufi dake kasuwar suleja, yazo sayen kayan abinci dasukan saya duk k'arshen watanni uku zaikai mafakarsu, ankamashi bisa had'inkai damai shagon yabasu, saboda shima yagaji da cutar dasuke masa, sometimes sukan d'ibi kayan masarufi amma basa biyanshi, idan yay magana sumasa barazana da mutuwa, yanason Barin kasuwar kuma sun hanashi saboda zalunci, since yana Barin wajen zasu kasheshi shida iyalansa. Abinciken su ya khaleel ne suka gano nanne shagon dash Lazarus kezuwa siyen kaya aduk bayan watanni uku, shiyyasa suka nemi had'inkan mai shagon, dukda daga farko yaso musu k'arya saboda tsoron abinda zaije yadawo, saida ya khaleel ya tabbatar masa zai sassa6a masa kamanni sannan yabada bayanan gaskiya. Aysha nacikin aiki saiga tasleem dakayan break fast, ita ta taimaka mata suka kammala komai, sannan tagudu, Dan azatonta ya khaleel nanan, dukda kuwa Aysha ta tabbatar mata dabaya gidan, amma tak'i tsayawa. Aysha tazauna tayi break d'inta, bayan ta kammala takira Ummah suka gaisa, tak'ara mata nasiha. sannan takira mama, tana mata shagwa6ar yaushe zata dawo? Itafa Tayi missing na sosai. Mama tace, "to daba'a gidan kuka zaunabafa? Kijimin yarinya da iyayi, INA mijin naki kike addabata da safiyarnan?". " kai mama, wannanne Safiya, 11 fa tawuce". "Eh duk da hakan, ainasan mijinki nagidan ba aiki yake fitaba shiyyasa". " to aii mama barci yakeyi bai tashiba, mama kamarma kin daina sonafa?". Dariya Maman tayi tace, "keni bazan iya da fitinarkiba Aysha, kinga sai anjima, ki gaida mutan gidan". Kafin Aysha tayi magana mama ta Yanke wayar. Dira k'afafu tafarayi irinnan shagwa6a tana fad'in kai mama! kai mama!, saikace tana gabanta, a haka mufeedah tashigo tasameta, ta ta6e Baki da sakin tsak'i, tawuce d'akin ya khaleel batareda tayima Aysha maganaba. Itama ayshan ko kallo mufeeda bata ishetaba, saima fad'i take aranta, "" inama yananan yacimin uwarki, shegiya karuwar gida, lokaci kad'an yaragemin namiki tonon silili, tsohuwar guzuma kawai, badolema kiyi karuwanciba shekara kusan 28 babu mijin aure". Tana cikin gulma da zuciyarta mufeedah tafito tana cikada batsewa, "k! INA ya khaleel?". Yatsina fuska ayshan tayi tana kauda fuska, tamkarma batasan dawata halitta awajenba. Hakan Yakuma tunzura mufeeda kuwa tace, "k! Dan uwarki bak'ya jinane? ALLAH saina lakad'a miki dukan tsiya". Idanu Aysha tazaro tana fad'in "Kuttt dukafa? Ina matsayin matar yayan taki? Lallai Ashe kuwa zaimiki dukan mutuwa agidannan, aiko Momy tadakeni banyi tunanin zai d'aga mata k'afaba bare ked'in, idankuma zaki gwada bismillah". Duk maganarnan da Aysha keyi a tsorace take, dantasan mufeeda zata ita zaneta d'in, gashi gida babu kowa, amma Dan k'arfin hali irinnan Aysha saita dake, harda wani girgiza jiki. Bak'inciki yakume mufeeda takasa magana, sai zuwacan tayi kwafa tareda Nuna Aysha da yatsa, ai wlhy sainaci ubanki agidannan naga mai d'aure miki gindi, dagake har uwarki sai zaman gidannan ya gagareku. Aysha tarik'e k'ugu tana fad'in tofa babbar magana, wai d'ansanda yaga gawar soja, zaman gida bai gagari karuwar dareba, dakuma dillaliyar kai yara karuwanci k'asashen duniya saimu?, a dai kula kar'a kwaso mana ciwon sida, a6ata sunan gidan dattijo mai mutunci irin baffah. Shiru mufeeda tayi, Dan maganar Aysha ta birkita kwalwarta, sai kawai ta6ige da borin kunya tana zagin Aysha, saita fad'ama Momy tazo taji dasu ubanda take, a can k'asan zuciyarta kuwa sai luguden Daka yakeyi, tana mamakin a INA Aysha tasan tana fitar dare? Saidai idan d'an gwari mai gadi yafad'a mata, aiko aikinsa yak'are agidannan, gwamma tamai kutu-kutun daza'a koresa kafin ya tona mata asiri, sosai maganar ta daketa, dukkan ga66an jikinta rawa sukeyi. Tana fita Aysha ta ta6e baki tareda Jan tsaki, tafara laluben number yaya fadeela dansu gaisa. Mufeeda kam k'arya da gaskiya taje ta zayyanema Momy, amma ita babu zancen ance mata karuwar gida, saidai tafad'i na Momy dillaliyar kai yara karuwanci kasashen duniya. Anty shukurah tace, "k! Mufeeda kiji tsoron ALLAH, y'ar yarinyarnance zata fad'i haka? Wlhy babu k'yau tada musifa, keda aka aikekima kiran khaleel miye ya had'aki da ita?. Mufeeda ta turo baki gaba, "kai kajimin Anty shukarah d'innan, bata fad'aba zance tafad'a". Momy kam takasa cewa k'ala, danba k'aramin dukan zuciyarta Aiken na Aysha yayiba, Anty zuwairah tamik'e tana hucin bala'i, " bara naje naci uban yarinyarnan da kaina, saita fad'i waye dillalin kai yara karuwancin?. Momy tanason dakatar da Anty zuwairah amma bakinta yamata nauyi. Anty shukrah ta harari mufeeda tana fad'in "hankalinki ya kwanta kin had'a saikijira kuma sakamako daga khaleel, dannasan ba k'yaleki zaiyiba wlhy. Mufeeda ta tunzuro baki gaba tana k'unk'unin fad'in "yo basai Momy tabarsaba sannan zai dakeni". Aysha nacikin yin waya da Anty Hafsat Anty zuwairah tafad'o, sallama Aysha taima Anty Hafsat a hanzarce, danbata buk'atar kowanta yasan matsalar gidanta har kuwa da mama dazata dawo, ina arzik'i daga kai amarya kwana 2 aji tana fad'a da dangin miji. "K! Dan ubanki wakike cema dillaliyar karuwai?". Aysha tazaro ido waje tana fad'in "kai Anty zuwairah yaushe nafad'a? A ina kuma?". "bara na lakad'a miki dukan mutuwa saiki tuna to". "Wlhy Anty zuwairah karki tsananta bincike, Dan ALLAH ma yamana hani da hakan, inkuma kink'i Allura zata tono garmane kawai fa, dan babu ruwana A to Z zan rattafo zance, tawatsema kowa wlhy". "Barito na nad'eki saiki rattafo zancen dan uwarki", 'tayo kan Aysha'. Aii da gudu Aysha tashige d'akin ya khaleel da hanyarsa ke kusada ita, takuwa danna makulli a k'ofar. Ahaka su mufeeda dasu hasna suka shigo, dawowarsu kenan daga school mufeeda tabasu labari, shine sukayo gayyar dukan Aysha, saikace wata uwar mata🤣, (bayan duksun girmeta) Kosu hasnah sunbama Aysha wajen shekara 7-7 ma, bare anty zuwaira data haifeta, dan dakad'an Aysha tagirmi Najwarta. Sai buga k'ofar suke suna zagin Aysha dacin mutuncin iyayenta, abinda yasaka Aysha kuka shine saka Abbanta dasukeyi, yana kabarinsa kwance, bata jamasa addu'aba sai zagi. Takuma rushewa da kuka. Ana cikin wannan balahira ya khaleel yashigo gidan, duk agajiye yake, abakin k'ofa Adams yamik'a masa jakkar laptop d'insa da hularsa, yay salute nasa. Ya khaleel ya jinjina masa kai yana fad'in "Adams kukula fa sosai, koyaya kukaga abinda baimukuba Ku kirani, hutunnan yazama dolene kawai amma daban zaunashiba, saboda d'an tsakaninnan ayyuka garemu sosai a k'asa, amma dukda haka zan ringa lek'owa saboda gudun samun matsala". "OK sir, agaida Anty". Zataji Adams, inaso kumaida hankalinku akan Ak'ilu Abbas, dan da gaggawa nakeson sanin masu hannu akan kisan David". Insha ALLAH Sir, karka damu, ALLAH yana tare damu, zaikuma cigaba dabamu nasara kamar yanda yake bamu akan mak'iya". " to ALLAH ya tabbatar, kukula sosai". Tunda yadoso 6angaren nasu yakejin hayaniya, mankine yakamashi, dan yasan duk bak'i sungama tafiya, yabud'e k'ofar falon yashiga, turus yayi yanabin y'an uwan nasa da daketa zage-zage da kallon mamakin............✍ 🤧maga Wanda ya khaleel zai goyama baya. _Ngd sosai da addu'oinku, kuyi hak'uri darashin amsa muku a groups, wlhy messages d'in sunmin yawa, Na PC ma har yanzu bangama amsawaba, ALLAH yabar zuminci, inayinku irin millions d'innan wlhy💋💋💋💋💋._ .💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋 [9/14, 7:25 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) _gaisuwa da fatan alkairi Maryam wasagu, Bebe'arth, mummeetie, mzzdaddy, alkairin ALLAH ya iso agareku._ 💋💋💋💋💋 1⃣4⃣ .......Anty zuwairah ce tafara ganinsa tace, "yauwa khaleel aigara dakazo, yau saina zane mara kunyar matarka a gidannan, ita hartayi balagar aikama da momy zagi?". Shiru yayi yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya, Anty zuwairah tace, "wai bakajin minace? naji kayi shiru". "Naji". 'Yafad'a yana cigaba da tafiya hanyar d'akinsa'. Sudai su mufeeda baki yamutu, sunyi tsit. K'ofar d'akin nasa yamurd'a zai shiga yajita 6am. Mufeeda tace, " ya khaleel tana cikifa ta kulle kanta saboda tasan batada gaskiya". K'ala baiceba, sai harara daya bankama mufeedar, tayi k'asa da kanta tana k'unk'uni. Yafara kiran " Aee'sha! Zoki bud'e k'ofar nan". Dukda tagane muryarsace saida tace, "wanene?". "k'aniyarkice, kibud'emin k'ofa nace!!". 'Yay maganar a tsawace'. Batareda tabud'e k'ofarba ta jingina ajiki ta fashe da kuka, ''ALLAH ya khaleel nabud'e dukana zasuyi, nikuma tsoro nakeji, kace sutafi sannan saina bud'e". Huci yafurzar daga bakinsa. yace, "Aee'sha karki bari raina ya6aci, kibud'emin k'ofa, babu wanda zaimiki wani Abu acikinsu ina nan". " har Anty zuwairah? ". 'Aysha tayi maganar tana kuka'. Cikin tsawa yace, "k! Wlhy zan sa6a miki idan baki bud'emin nan da 3minutes ba!!". Su Anty zuwairah kam duk dad'i yakamasu, sunsan saiya yima Aysha dukan mutuwa. k'ilama ya saketa saboda zagin momy datayi, kai da sunji dad'i kuwa.😂 Aysha kam saida taga minti ukun daya bata sunkusa cika sannan tabud'e k'ofar. Yana niyyar Shiga su Anty zuwairah suka tashi suma, hannu yad'aga musu alamar su dakata, sannan yashige, yamaida k'ofar yarufe harda Murza key. Aysha tak'ara k'arfin kukanta, tana ja da baya dafad'in wlhy ya khaleel ni ban zagesuba, sunema suketa zagin Abbana, ALLAH Anty mufeeda Ce tahad'a". Ko kallon Inda take baiyiba, ya ajiye jakkar laptop d'insa da hula akan gado, fuskarnan a murtike, babu alamun wasa, yafara cire ma6allan rigar Uniform d'insa, saida ya 6alle tas sannan yafara k'ok'arin zare belt d'insa. Aysha tanacan jikin Bango tana kuka, duk zatonta dukanta zaiyi da belt d'in. Ganin yacire komai, dagashi sai vest da boxer ta rintse idanunta, ya zauna akan sofa yana kwance igiyar takalminsa, sannan yazare har sock's d'in, yana mik'ewa Aysha tak'ara k'ank'ame jikinta, azatonta kanta yayo, saitaga yashige toilet. Ajiyar zuciya tasauke da baza idanu kozataga key d'in, bataso yafito ya sameta a d'akin, kuma tana tsoron fita sabodasu Anty zuwairah. Suna falo kuwa sai cika da batsewa sukeyi, suna jiran jin hukuncin da ya khaleel d'in zai yankema Aysha, amma sai sukajiyo tsit, sunsan wani lokacin idan yanacin uban mutum baya barinsa yayi kuka, shiyyasa sukad'an k'ara jira. Inda yabarta anan yafito ya sameta, sanye yake da lemon green d'in rigar wanka, hannunsa rik'eda k'aramin towul yana goge Kansa zuwa fuska, da'alama wanka yayo. Aysha tana ganin Yakama igiyar rigar zai kwance tazame k'asa, tareda cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana rera kuka a hankali. Kallo d'aya yamata ya d'auke kansa, cigaba yayi da shafa mai, yasaka k'ananun kaya marsa nauyi dabazasu takura masaba, yad'an yafesa turare. Inda Aysha take zaune yanufa, yad'auketa cak, aikam tafasa masa k'ara, tsawa yadaka mata, tayi saurin to she bakinta da hannu. Su Anty zuwairah dake falo suka fashe da dariya, harda tafawa, su duk zatonsu ya khaleel Na punishing d'in Ayshane. Ya d'orata visa gadonsa, ya haye shima tareda rungume kayarsa, ya lumshe manyan idanunsa dake cikeda barci, mutsu-mutsu Ayshan tafara, yabud'e ido dak'yar Dan barci harya fara figarsa, "k wlhy inbaki nutsuminba zan dakaki ad'akinnan, sannan Na turaki waje su Anty zuwairan suyi duk yanda sukaso dake, stupid girl kawai". Tsit Aysha tayi, takoma ta lafe a k'irjinsa, Yakuma rungumeta da k'yau, yamaida idanunsa ya lumshe, cikin lokaci k'ank'ani barci ya d'aukesa. Aysha tabud'e idanunta dasukasha kuka, duksun mata nauyi, fuskarsa take k'arema kallo, yanda yake barci cikin nutsuwa, numfashinsa nafita ahankali, fuskarsa tayi fayau ko'a fili bata zama haka Dan tamkar yana murmushi, wani dad'i ya mamaye zuciyar Aysha, wai itace kwance visa k'irjin ya khaleel yau? abinda ko'a mafarkinta bata ta6a zaton faruwarsaba, "ya ALLAH Na gode maka da wannan k'yauta, shima ALLAH kasaka MASA sona, fiyeda yanda nake sonsa". Haka taita tunane-tunane itama har barci 6arawo ya saceta. Afalo kuwa bayansu Anty zuwairah sunji ihun Aysha da tsawar da ya khaleel yaymata sai Anty zuwairah tace sutashi suje, tasan khaleel zai tunkud'o k'eyar Aysha har gaban momy, bayan yagama kir6arta, da wannan shawarar suka koma cikin gida, tareda kaima momy dadd'an labari, wai khaleel nacan na zane Aysha, harda kulle k'ofa. Momy taji dad'i sosai, har zuciyarta tad'an huce, amma dolene tad'auki matakin gaggawa, inba hakaba Aysha zata musu 6arin makauniya agidannan. Anty shukura kam hankalinta yatashi, batareda sanin kowaba tanufo gidansu Aysha, tsit taji falon, harta juya amma hankalinta yakasa kwanciya, komawa tayi tacan bayan d'akunansu, talek'a window d'in ya khaleel, kwance ta hangosu manne da juna suna barcinsu hankali akwance, murmushi tayi dafad'in Alhmdllh. Cikin nishad'i takoma tacigaba da harkar gabanta, tana mai k'arajin k'aunar khaleel d'in aranta, da halayensa masu matuk'ar birgeta. ___________________,,, Kiran sallar la'asarne ya farkar da khaleel, ya bud'e idonsa akan Aysha dake kwance bisa jikinsa, dagani kasan tanajin dad'in barci, aransan yace, "masha ALLAH, balaifi yarinyarnan k'yak'yk'yawace, komai nata yana tsaka tsaki wajen k'yawun, babu abinda yafi d'aukar hankalinsa sai kwantacce gashin gaban goshinta, Wanda yakusa had'ewa da gira, ga zara-zaran gashin idanu, zaka iya d'aukama ta k'arane amma natane, samun kansa yayi da Sosa saman idonta da d'anyatsansa, yanayi yana murmushi". Acikin barci Aysha taji kamar ana mata tafiyar tsutsa akan idanu, tabud'e idonta ahankali, yayinda ya khaleel yajanye hannunsa yana wani k'ara had'e fuska, shi a dole kar a kawo masa raini. Tsaf Aysha tagane shine ke ta6a mata saman ido, dariya abin yabata, amma batayiba ta gimtse, tana kallonsa yasauka daga gadon yashige toilet, itama sauka tayi tana mamakin barcin dasukayi. Tana nan zaune yafito da alama alwala yayo, yanata shan k'amshinsa yace, ''kitashi lokacin sallah yayi". Kanta tad'aga masa batareda ta tankaba, itafa yana bata dariya, duk dan kar arainasa yake wannan cika da batsewar. ____________________________ "Aminiya kece agidan namu?". "Wlhy kuwa nice aminiya, canayi bara nazo namiki barka da tashin bak'i ko". Baki hajia babba ta ta6e, "kinada abin haushi wataran hajia khaltum, ni namaji dad'in zuwanki, koda bakizoba nidama zanzo". "Tofa miya farune". " aminiya yarinyarnan zata zamemana matsalafa, nifa bazan 6oye mikiba inacikin matuk'ar tashin hankali tunda su kubra suka sanar mana yarinyarnance". "Bake kad'aiba wlhy Aminiya, ingaya miki nakasa zaune nakasa tsaye, akwana biyunnan tufk'awa da warwara kawai nakeyi, dama jira nakeyi bak'i sugama tafiya Nazo muyi magana, matsala biyuce ta tasomu gaba, d'anki da matarsa, Dan kinsanfa duk wani asusun banki na Oga barau yadaina aiki, gashi hukumar shigi da fici sunyi seizing d'in passport nasa, yau yau d'innan aka kama Lazarus". "Kai haba! Aminiya munshiga uku, waye yakamashi?". "d'anki Ibraheem". "Ibraheem fa!?, yaushe yafitama daga gidan? Shida yake hutu". "Aikamdai yau d'innan da safe, dan gwaska ya tabbatarmin dayaga Ibrahim da idonsa, kinsan kuma yasanshi dai". Zuface tafara ketoma hajia babba, tace, "shikenan munshiga tara". "Nifa mamaki kike bani, miyasa kike tsoronsane? ina ganin akwai mafuta". "Hummm kaltum haryanzu bakisan wanene Ibrahim ba nakula, amma miye mafitar?". "Kawo kunnenki". Hajia khaltum tafad'a ma hajia babba abinda nima banjiba. Tad'anji sauk'in damuwarta, harta zayyanema hajia khaltum abinda Aysha tamusu yau. "Ammafa yabirgeni daya zaneta, kuma tabbas ayau d'inan zamu kawo k'arshen iskancinta, Dan sha yanzu magani yanzu yafi dad'i, dama binda tayima su kubrah ya 6atamin rai, nakula itafa jin kanta takeyi on top saboda ta auri Ibrahim, shiyyasama takemana barazana, tana wasa damune, duka-duka shekarunta nawa?". "Ca zakiyi shekarun uwarta nawama bare ita". "Wlhy kuwa. Kedai yau ki birkice musu kawai, Dan bazasu ta6a kasancewa a inuwa d'ayaba, nasan duk Girman kan namiji saukeshi yakeyi akan mace, duk wannan mazuran dakikaga yanayi tsaf zai iya kwanciya da ita, tom inhar kikayi k'ok'ari yauma yakwana awajenki zamuci nasarar aikinmu, Dan adaran yau su gwaska zasu gama aikinsu akanta". "Shikuma sai Aleeya tashigo rayuwarsa, Dan yakamata ki tada maganar bikinsa da ita da gaggawa". "Kinsani farinciki aminiya, amma da zuciyata tamin k'unci, yanzu kam nasamu nutsuwa, shiyyasa banida kamarki duk duniyarnan, ngd ngd". "Kibarmin godiya, munrigada munzama d'aya aii, kedai kawai kiyi k'ok'ari yauma, Dan wannan ciwon nakine kawai zai hanashi kwana agidansa". "Gaskiyane, nima aii nasan taurin kansa, Ibrahim murd'ad'd'en mutumne, juyasa saimai basira, tun yana k'araminsa mutumne mai masifar taurinkai, balle yanzu da aikinnan nasa ke k'ara masa masifa da bushewar zuciya". "Aii bak'aramin kuskure kikayiba dakika amince masa shiga aikinnan". "Inbanda abinki wayasan mi gobe zata haifar, kumafa alhajine ya d'aure masa gindi". Hummm like Father like son. "Aigashinan yazame mana masifa kuwa, amma zamu nuna masa mun rigasa zuwa duniya aii''. Haka sukaita tattauna batun, da yanda zasu 6ullo masa. _____________________________ Aysha na zaune gefen ya khaleel dakecin abinci, itama ya tsareta saitaci, turawa kawai takeyi, Dan ko kad'an batason cin Abu mai nauyi tunda tadawo daga turai d'innan. Tsaf shima ya fahimceta, Dan haka yad'aura d'ammarar dawo da ita kan turbar al'adarta, tanaci tana tunzura baki gaba. Yi yayi tamkar baisan da zamanta awajenba, cin abincisa yakeyi yana kallon labarai a aljazeerah. Kamar zatayi kuka, sai Harar gefen ido take masa, wadda tasan inhar yagani sai kashinta ya bushe. Ahakadai suka gama, ammafa saida ya tsare Aysha taci sosai, da kuka kuwa tacid'in, tana bashi mamaki yanda kuka baya mata wahala ko kad'an. Suna kammalawa ta tartare wajen, shikuma Yakoma saman kujera ya zauna, k'afafinsa nakan k'aramin table na glass, ya canja tashar zuwa sunnah TV, wa'azin sheaik Kabeer gwambe aka saka, kuma akan aure ake wa'azin. Aysha tafito data kichin, ya khaleel yana burgeta, zata iya cewa bata ta6a ganinsa yana kallon wak'ok'i ko wani film d'in dabai daceba, kai ko wak'a bata tunanin yanajima, dukda kasancewarsa matashi, koda yaushe saidai kaga yana kallon labari ko wa'azi, Indai kaga yazauna kallon film to tabbas zai k'arune dawani Abu aciki. Shiru babu mai cema wani uffan, amma suna sauraren wa'azin, saidai kunya takama Aysha sosai, daurewa kawai takeyi. Wa'azin kam sosai yay tasiri ga ya khaleel, harma yake sak'ama ransa wani Abu daban.... __________________________ Bayan yadawo daga sallar isha'i ya iske babu kowa afalon, Aysha na d'akinta tana sallah. Kusan minti talatin da zamansa tafito, saidai sanye take da hijjab, sannu tamasa da tambayarsa akan abinci?. Idonsa nakan waya Yace, "a'a dafamin tea kawai". Ta amsa da to, aranta tana jinjina masa akan k'aunarsa da shayi, cikin mintuna kad'an tagama dafawa, tajuye cikin flask, sannan tad'ora saman k'aramin tire tareda mug. Ta taras yatashi, ta ajiye a inda yake zaune, babu dad'ewa saigashi yafito d'aukeda system d'insa. Yakoma inda yatashi ya zauna, tea d'in Aysha ta had'a masa, yayinda shikuma yamaida hankalinsa wajen jona system d'in a charge. Yana danne-dannensa yana shan tea, yayinda Aysha tamaida hankalinta akan kallon film a tashar Action. Sallamar husnah ce tasaka Aysha d'agowa tana amsawa, hararta husnar tayi, itama tarama, ta kauda kanta, ya khaleel baisan hidimar dasukeyiba, amma yaji sallamar husnah. "Ya khaleel barka da dare". Batareda yad'agoba yace, " yauwa, lfy dai?". ''Yaya wlhy jikin momyne, kuma tahana akiraka, wai abarka kawai, yanzu hakama basusan nasilaloba nazo fad'a maka". 'Dago ido yayi yana kallonta, yace, "yanzu yajikin nata?". " wlhy Yaya tanacan sai murk'ususu takeyi, tunfa wajen 5pm". Mik'ewa yayi da sauri, ko kashe laptop d'in baiyiba, yana fad'in "muje naga jikin nata". Husnah ta ballama Aysha harara tareda mata gwallo. Hawayene suka cikama Aysha idanu, ta kauda kanta daga kallon husnar. Suna fita tamik'e ta kulle k'ofar falon, tasandai saikuma gobe itada ganinsa. Wannan wace iriyar rayuwace, kodai takira mama ta sanar matane?, kai a'a mizama tace mata?, mijinta baya kwana gida?, kai za'a fassarata dawani Abu daban, itakuma wlhy badan hakanba, koda yana d'akinsane tana nata tasandai gidan aure take, amma ace wai tunda aka kawota amatsayin amarya yau kwana 2 kacal, za'a Shiga na uku bata ta6a zaman awa 10 ba da mijinta, ta fashe da kuka maiban tausayi. Nikaina kuka nakeyi😿. Dana sani nabar y'an ciki da gaskiya fans, ko hira sa tayatama☹. ______________________________ Hajia babba nata juye-juye, hannun ya khaleel cikin nata, yace, " gaskiya momy kibari yau muje asibiti, yaza'ayi kullum ciwo na addabarki amma kin hana a nema miki lafiya". To Ibrahim muje d'in, mom tayi maganar cikin matse baki, ita adole ciwo yahana sakat. Suna shirin tafiya asibiti su kad'ai, Dan tahana afad'ama baffah, sai kawai sukaga Ammah tafad'o falon. A'a lfy dai naga kun zagaye uwar taku?". "Batada lfy Ammah, kusan kwana uku kenan kullum bama barci wlhy", cewar Anty shukrah. "Kenan tun randa aka kawo Aysha?". "Eh wlhy Ammah tun ranarne". Anty shukrah ce kawai ke magana, amma Anty zuwairah dasu mufeedah sunmata shiru, ya khaleel kam hankalinsa nakan momy wadda taji wani k'arin tsanar Ammah, fad'i take azuciyarta "miya kawo fitinanniyar tsohuwarnan?". Ammah ta jinjina kai tana fad'in "to lallai sanu Laure, amma shine ko mijinki zaki hana afad'amawa, to kujirani, aibasai anje ssibitiba, ina zuwa". "Kajimin tsohuwarnan, kaga khaleel kutashi mutafi". "A'a Anty zuwairah, yakamata mujirata d'in, cewar ya khaleel". Dole Anty zuwairah ta hak'ura suka jira dawowar Amman. Babu dad'ewa saiga baffah da Ammah harda Anty Mamie da Ramadan. Bak'inciki kamar yakashe momy da Anty zuwairah, duk sannu sukai mata, baffah yace, " Ramadan kakirashi?". "Eh baffah, yana zuwa yace". " aidama kunbarshi, tunda asibiti zamuje", 'momyce kemagana da k'yar wai ita ciwo'. "A'a aibai kamata sai an kinkimekiba, bara kawai yazo d'in". Babu dad'ewa saiga family doctor d'insu yazo, ammah tajashi gefe, babu Wanda yasan mita fad'a masa. (ho Ammarmu🤪👍🏻). Doctor yak'araso gaban momy yamata tambayoyi, cikin bak'in ciki take bashi amsa. Yagama jinta sannan yahad'a allurai, momy ta tubure baza'a mataba, Cikin kaushin murya baffah yace, "kamarya baza'a mikiba, su yarannaki basuda y'ancin dazasu sami barcine? Kusan kwanaki uku basa samun barci bazaki tausaya musuba, doctor yimata kaji, banason shirme, keba k'aramar yarinyaba kidinga Abun yara". Doctor bai saurari masifar momy ba ya zurkud'a mata allura🤣. Cikin mintuna 5 barci ya d'auketa. Baffah yace, "duk kutashi kuje Ku kwanta tunda tasamu barci, mu'azzam tashi, kullum kana barar min yarinya ita kad'ai, ko tausayinta bakayi, basai karinga tahowa da itaba". Kansa ak'asa yace, " amin afuwa baffah". Anmaka tashi kawuce, aini nasan maganin kowanne shege aduniya, Amman ce da wannan zance😂. Kowa kuwa makwanci yanema, su Anty zuwairah bak'inciki kamar zai kashesu, dansu ciwon momy dad'i yake musu, tunda yana ma ya khaleel Katanga da kwana da Aysha. Haka Ammah tatafi tana mita, sama-sama momy kejin abinda ake fad'a, hankalinta atashe yake, amma batada k'arfin d'aukar mataki, Dan allurar barci Amman tasaka akama momy🤣. Tanaji tana gani ya khaleel yatafi wajen amaryarsa💋. ___________________________ Saida yay Knocking d'in k'ofar saboda Aysha ta kulle. Tsoron da Aysha takeji yak'aru, tasandai ba ya khaleel baneba, k'ilama su Anty zuwairah ne sukazo casata adarennan, tunda sunga yanacan, kuka takuma fashewa dashi, jikinta sai rawa yakeyi. ya khaleel kuwa Yakuma kwankwasawa, nanma yaji tsit. Zagayawa yayi tajikin window d'in d'akinta, can ya hangota k'arshen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta tana kuka, tabashi tausayi, cikin taushin murya yace, "taso kubud'e min k'ofar nadawo, daina kukan". Da Sauri tad'ago kanta, ganin ya khaleel ajikin window sai kunya takamata, ta goge hawayenta tafito ta bud'e masa, k'asan zuciyarta kam tanajin dad'in ganinsa. Tana bud'e masa yashigo sai kawai yad'auketa cak. Zaro ido Aysha tayi waje Dan mamaki. Bai kalletaba yanufi d'akinsa da ita. Ya khaleel please kabarni barci zanyi, zanje na kwantanefa. Oh kina kukan bana nand'inne zakiyi barci?, Saikin fad'amin miya sakaki kuka?, yau ba ranar barci baceba, ranar biyan kazace. Bata fahimci zancen nasaba ko kad'an, harya direta bisa sofa. Yashige toilet, bin bayansa tayi da kallo, tana juya maganar biyan kaza aranta, kowacce kazar?............✍🏿 Hhhhhh, zaki tuna wacce kazar? da k'yau sholy🤣🤣🤣🤣. 🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀muhad'u tomorrow, Dan muji kazar da Aysha zata biy boss💪🏻😂😜 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋 [9/15, 3:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣5⃣ ......Tana nan zaune wajen tunanin kazar dazata biya yafito, da Alana alwala yayi, ya kalli Ayshan fake satar kallonsa ta gefen ido. “tashi kije kiyi alwala”. "Nafayi sallar isha'i har shafa'i da wutirima". 'Aysha tayi maganar a shagwa6e'. Batareda ya kalletaba yace, "umarinine ba shawaraba". Yanda yay magana cikin d'aure fuska sai tsoro Yakama Aysha, jiki a sanyaye tatshi zataje d'akinta, ak'asan ranta tana mamakin halayen ya khaleel masu rikid'a kamar hawainiya, yanzu zaimaka maganar arzik'i, yanzu kuma zai juya ta tsiya......... "Ina kuma zakije?". Maganarsa ta katse mata tunani, harta kama k'ofar tasaki, juyowa tayi garesa, amma kanta ak'asa takasa kallonsa. Ya fesar da zazzafan huci daga bakinsa, a zuciyarsa yana fad'in matsalar auren k'ananun yaran kuma kenan, komai saika koya musu, ansaka surutu da ciwon kai, yaja guntun tsaki afili. Aysha dai tana bakin k'ofa tsaye saikace dogariya. " idan bazakiyi alwalarba kiwuce ki tafi". Muryarta Na rawa tace, "kayi hak'uri, aii alwalar zanje nayi, daganan nad'akko hijjab. Banza yamata Yakoma kan sofa ya zauna, tareda d'aukar wayarsa yahau danne-dannen k'addara. Ganin ta 6ata masa rai, sai kawai tayi tunanin bara tayi a toilet d'insa, a d'arare tawuce tashiga toilet d'in, babu dad'ewa saigata tafito, shareta yayi, saida tace, " nayi alwalar". Nanma ya6ata wasu mintuna sannan yamik'e, ya mik'a mata hijjab, kar6a tayi tana mamakin a ina yasamo?. Jam'i yajasu raka'a biyu, sannan yadafa kanta yay addu'ar da addini ya umarcesa dayi, daga nan yazarce kwararo addu'oi akan musulmi baki d'aya, masu rai da matattu, marasa lafiya da fannin aiiki!. Aysha dai y'ar amince, nima daga gefe ina amin, amma ahankali.😂.lol Batayi mamakiba, danta gama yarda da mijin nata a fannin ilimin addini, yayi zurfi bana wasaba, bayan shafa addu'ar yajuyo gareta suna fuskantar juna, yatsareta da wad'annan mayun idanun nasa, masu kwarjini da hasken aminci, cikin taushin murya dabatasan yanada itaba yafara mata tambayoyi akan addini, cikin harshen larabci. Itama cikin harshen larabcin take amsawa, inda takeda rauni yakan tunatar da ita, daga k'arshe suka kuma rufewa da addu'a. Ya Sanar da'ita zai samo mata islamiyya tacigaba, tunda yaga tayi nisa sosai a ilimin addini, aganinsa baikamata a dakushetaba. Tamasa godiya cikin raunin murya, wadda tak'ara tsundumasa cikin wani yanayin shauk'i Na musamman. *_Hattara samari_* _yakamata idan kayi sabuwar amarya, adaren farkonku, bayan kun gudanar da sallah domin Neman tabarraki, kad'an kwankwasa amarya dankaji ya kwarinta a fannin addini, tanan zakasan wane mataki zaka d'auka domin gyara fagen tarbiyyar y'ay'anka tunkan suzo, kaga idan akwai rauni ta fannin addininta saika maidata islamiyya, kokuma idan kai kanada lokaci karinga d'ora mata agida, inaga hakan zai kawo gyararraki a gidajen ma'auratan da suke cikeda hargitsi a halin yanzu, Dan wlhy k'arancin ilimin addini Na taka rawar gain wajen ruguza tubalin ginin rayuwarmu baki d'aya, ko k'arancin tarbiyyarnan daya addabi al'ummarmu harda jahilcin ilimin addini, Dan munfi bama boko amanar kanmu da y'ay'anmu, ALLAH yasa mun fahimci sak'on._ Da kansa yazarema Aysha hijjab d'in, itadai duk kunya da mamakin sun cikata, wannan sabon salon Na ya khaleel yad'aure mata kai. Yaymata umarni akan tatashi takoma kan sofa, babu musu ta tashi, Dan babu wasa acikin al'amuran nasa, shikam yana d'aurewa ne dankar Aysha ta kawo masa raini. Nace.hummmm.🤪👍🏻sai babana. Ficewa yayi, babu dad'ewa saigashi yadawo d'aukeda fresh milk da glass cup, kusada ita yazauna, kan Aysha na k'asa tana wasa da yatsun hannunta da har yanzu lalle yake rad'am bai fitaba, hakama na k'afafunta. Fresh milk d'in yazuba yasha kusan rabi, sannan ya d'ora cup d'in abakin Aysha, d'ago idanu tayi ta kallesa, ganin fuskarnan babu alamun wasa ta lumshe idanunta tareda bud'e baki tana sha, saida ta shanye tas sannan ya janye cup d'in, tashi yay dasu a hannu yad'ora bisa dirowar gefen gado, yashiga bayi, kusan mintuna 20 saigashi yafito d'aure da towul. Aysha tai saurin rintse idonta, danta tsorata da ganinsa haka, shikam baimasan tanayiba, yace, "tashi kije kiyi wanka mu kwanta, koba kince barci kikejiba?". Jinjina masa kai tayi, Dan babu bakin magana, miyyasa zaice wankanma ad'akinsa zatayi? Yana nufin barcinma tare zasuyi? Itakam yau taga takanta, mi ya khaleel ke nufi da itane?, da wannan tunanin tashiga bayinsa tayi wankan, tayi brosh, duk wani abin k'amshi datayi karo dashi a bayin saida tayi amfani dashi, tasaka farar rigar wankasa, tsaye tayi takasa fita saboda kunya. Muryarsa tajiyo yana fad'in " kifito kiyi shirinki, ni Na fita falo", baijira cewartaba yafice abinsa, yasan inhar yana nan bazata fitoba d'in. Tanajin alamar fitarsa tafito, cikin mamakin take kallon kwalliyar furanni da akama gadon, harta Shiga wanka dai babusu, kuma blue d'in bedsheets nema agadon d'azun, amma yanzu an lailayeahi da Fari tas, sannan aka k'awata tsakkiyarsa da furanni ja da farare, anyi love k'ato💝. Nace Aysha tunda rana mai d'akin yayi abunsa, ya lulu6a wani bedsheets d'in Asama Dan karki gani, 😏to ammafa batajiniba, Dan ina la6e a bayan labuloli, gudun kar ya khaleel ya ganni, ya koroni rahoto ya wuce daku🤥🤧. Mansa tad'auka ta shafa, mai sanyin k'amshi, ta faffesa turarurrukansa, tunanin yanda zata d'aukar kayan barci d'akinta tatsaya yi, idontane ya sauka akan rigar dake gefen gadon, fara mai adon firanni jajaye, d'aukar rigar daketa wani bala'in k'amshi tayi tabud'e, kutt tafad'a tana zaro ido waje da bud'e baki😨, mi ya khaleel yake nufi? Ni shatu d'iyar Abubakar, waini zan saka wannan rigar natsaya agabansa?, kai impossible wlhy bazan iyaba, aii wannan rigar da ita da babu duk d'ayane, shiko kunyama bayaji?. To amma kuma idan ban sakaba akwai matsalafa, bara kawai nasaka kafin ya shigo, saina saka hijjab, kinga Na rufama kaina asiri kenan. Cikin hanzari tasaka rigar, cif taimata tamkar an gwadata, gashi Tamata bala'in k'yau, ta haska farar fatarta, tajuya tana fad'in woow! Ammafa Na had'u wlhy, ko a ina ya khaleel yasiyo rigar barcinnan? Nibamma ta6a ganin kayan barcin dasukamin k'yauba irin yau, da Sauri ta tufk'e gashinta (Dan Aysha dama can batason kitso, kullum kai atsefe, sai mama Tamata tsiya takeyi ko gudun dukan makaranta, tokuma zamanta a turai d'innan Yakuma lalatata akan k'in kitso). Hijjab d'in datayi sallah tad'auka ta zumbula, tana gama sakawa kuwa ya khaleel yashigo d'akin, tsaye tayi jikin madubi tayi k'asa da kanta, takasa d'agowa ta kalleshi saboda kunya, gani takeyi kamar yana kallon rigar tata. Cikin takunsa Na nutsuwa da k'asaita yak'araso Inda take, zuciyar Aysha tak'ara k'arfin gudu da sauri-sauri, saida ya kalli gadon yaga babu rigar sannan yamatso kusada ita, kumayin k'asa tayi da kanta. Guntun murmushi yasaki, sannan ahankali yakai hannu kanta yana k'ok'arin cire hijjabin. Da sauri tadafe tana fad'in "please ya khaleel kabarmin". 'Tayi maganarnr kamar zata masa kuka'. Harara yasakar mata, wadda tasakata cire hannunta dole, shikuma yacire hijjabin, da k'arfi Aysha ta rintse idanunta, siraran hawaye nabin kumatunta, yanzukam tadaina mamaki saidai tsoronsa daya fara shigarta, tarasa dalilin ya khaleel nayimata hakan. Ya khaleel kam yagama mutuwa atsaye, saboda k'arema halittar Aysha kallo dayakeyi daki-daki, rigar tayi masifar yimata k'yau fiyema da zatonsa, tamkar an halicci rigar ajikintane, baisan sanda ya furzar da sassanyan huciba, yasaka hannunsa yana sharema Aysha hawayen dake zirara a kumatunta, har yanzu idanunta arufe suke, yad'an lumshe idonsa yana sakin guntun murmushi, tad'an bashi dariya, Ashe duk tsiwar tata matsoraciyace haka?". Jitayi kawai ya mannata da jikinsa, atare suka saki sassanyar ajiyar zuciya, cikin wata irin muryan da Aysha bata ta6a zaton ya khaleel Nada makamanciyarta bama bare itad'in yake mata magana acikin kunne, " Ashe duk tsiwarkinnan ked'in matsoraciyace sholy?". Gaban Aysha yafad'i, danjin sunannan akaro Na biyu daga bakinsa, yacigaba dafad'in ked'infa jarumace mai kare mijinta daga harbin bullet, matar police aii police ce inji masu iya magana. Gaba d'aya kalamansa sun dulmiya kwalwarta a awata duniyar tunani tadaban, kafin tadawo hayyacinta yacirota daga jikinsa, yakamo hannunta da'aka k'awata da zanene lallale ya sumbata, sannan yace, "bud'e idonki". Babu yanda zatayi, dole tabud'e idon nata, amma takasa kallon inda yake, shiyamata jagora har gaban gado, danta kasa bud'e idonta da k'yau saboda kunya da tsoro. Yace, " bud'e idonki ki kalli gadonnan". Bud'e idonta tayi sosai bisa gadon, an lailayeshi da da farin bedsheets, Flowers d'in sunyi k'yau sosai agadon, sai k'amshi furannin sukeyi, anyi wani rubutu da flowers d'in a tsakkiya, Wanda ayshan takasa ganewa, amma saitaga kamar tata6a ganin rubutun, to amma a ina?, wannan shine abin tambayar. Batakai k'arshen tunanintaba taji an sureta andire bisa gadon, kafin tayi wani yunk'uri taji bakinsa cikin nata🤫. Abubuwa masu wuyar fassara ga Aysha suka cigaba dagudana, tuni tsoro da firgici sun gama cikata, jikinta sai 6ari yakeyi, shikansa boss d'in jikinsa tsuma yakeyi, abinka da sabun shiga🤭. Da zafi-zafi yake sarrafata, (hummm auren tuzuruma aii had'arine alkur'an🤣). Yaukam Aysha tagane batada wayo, yayinda ya khaleel yanufi yin mai gaba d'aya sai Aysha ta rikice masa da kuka da magiya, abinda yaso faruwa tsakaninta da john yafad'o mata rai, tatuna yanda ya kacaccala Ngozi ranar a maimakonta, tuni k'arfin kukanta yak'aru, ganin zata masa tonon silili yarufe mata baki danasa🙊. Anzo wajenda alk'alamin bilynku bazai iya aikiba😒, dan haka nakwaso akorikurar k'afafuna da d'an littafina da alk'alami nayo waje, inama Aysha addu'ar fitowa lfy,🚶🏻‍♀, Dan irinsu ya khaleel tuzurai sai anhad'a da addu'ar🤐😫😝. Cikin sand'a da dabara suka hauro katangar, sukusan 6 ne, kuma duk garada majiya k'arfi da k'uruciya. Ahakankali suke zagaye 6angaren nasu ya khaleel, wanda yajia khaltum tamusu kwatancensa. Gwaska yace, "mufayi komai da lura, kunsandai mijinta kowanene, amma haija ta tabbatarmin baya cikin gidan, ita kad'aice, Dan haka mu kwamusota cikin taka tsantsan mu fice kawai............✍ Hummmm, su gwaska sai abada himma🤣👍🏻. Please kuyi manage da wannan, yau inada bak'i, idankuma sun wuce da wuri, k'ila Na k'ara muku, inatafa godiya da k'auna, kuma kuna zuciyar bilyn Abdul💖. ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤👍🏻. [9/16, 4:13 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) _Gaisuwa agareku Hauwa'u (kululuwa uwar gidan janu😉) & fateema (Maman Rufaida) & Maman Huzaifa, kuna ran bilyn Abdull irin sosai sosai d'innan😍😍😍😍_. 1⃣6⃣ Tsorone yafara kamani danjin kamar takun mutane, hhhh yaukam tak'arema bilynku, karfa su kwamishine su zata Ayshan ce😿. Addu'a nafara da fatan ALLAH ya fiddo ya khaleel nikam😩. _______________________________ Su gwaska suka gama zagaye gidan, kowa yatsaya inda yadace, suna hasashen yanda za'ayi sushiga ainahin cikin gidan. Ya khaleel kam yanacan rungume da Aysha daketa kukan da muryartama bata fita, wani irin tausayinta da k'aunarta Na ratsa dukkan wata ga6a da magudanar jini ta jikinsa, yana godiya ga ALLAH daya masa k'yautar samun mace tagari, wadda tarik'e mutuncinta, takuma kawoshi inda yadace, sosai kukanta ke sukar zuciyarsa, amma yakasa hanata, Dan shima bashida wani k'arfi, ga wani zazza6i dake Neman rufesa. Dukda ba lokacin sanyi baneba, amma rawar sanyi yakeyi, yanaso yaja bargo yarufesu amma yakasa hakan, kuma matse Aysha yayi ajikinsa daboda taimako da d'umin jikinta ke bashi. Aysha tafara tsagaitawa da kukan datakeyi, saboda jin ya khaleel na rawar sanyi, gawata matsa dayamata ko numfashin kirki batayi, dukda d'akin akwai duhu hakan bai hanata bud'e idanuntaba da k'yar, dansun mata jingim saboda kukan data 6arza, bata ganinsa sosai, d'akin babu fitila dukya kashe, sai hasken fitulun waje dana farin wata dasukad'an hasko glass d'in windows d'in. Tana k'ok'arin mik'a hannu ta kunna fitilar gefen gadon kuma aka d'auke wutarma gaba d'aya, yarage asken farin watane kawai. Hakan yayma su gwaska dad'i sosai, zasu gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali kenan. Dukda tayi bala'in wahaltuwa hakan baihanata son tashi danta taimaki ya khaleel d'inba, rawar sanyi yakeyi sosai, har hakwaransa Na had'uwa waje d'aya. Kuma matseta yayi, Dan bayason tabar jikinsa. Muryarta a dakushe cikin wahaltuwar tace, "ya khaleel kabari natashi, ko fitila Na kunna". " karkibar jikina A'eesha, sanyi nakeji, kedai lullu6emu". 'Yaya maganar cikin dauriya'. Bata iya cewa komaiba, Dan itama bawai lafiyar garetaba, da k'yar ta yunk'ura tajawo jargon takuma kullu6esu da k'yau. Kamar wasa ya khaleel ya rikice mata sosai, ga jikinsa yayi masifar zafi, sai rawar sanyi kuma yakeyi, ita kanta kamar zazza6in keson kamata, ga azabar zugi da k'asanta keyi, gakuma ya khaleel yahanata koda motsin kirki yamanneta tsam da jikinsa, sai hawayen wahala da tausayin ya khaleel d'in takeyi, tarasa yazatayi. Kamar wasa tafara jiyo motsin takun mutum ta bayan windows d'insu, tad'aga ido da k'yar saita hango inuwar mutum. Wata irin fad'uwar gaba tasameta, itama sai jikin NATA yafara rawa, ahankali cikin rad'a tace, "ya khaleel kalla mutum jikin window d'inmu". Baijitaba saboda muryarta a dasashe take, bata fita da k'yau, takuma matsar da bakinta saitin kunnesa tafad'a masa. Dukda halin dayake ciki bai hanashi d'ago kai cikin hanzariba ya kalli window d'in shima, shiru yayi yana nazarin inuwar mutum d'in. Aysha zata k'ara magana yay saurin rufe bakinta alamar tayi shiru. Shirin kuwa tayi, saidai Duk tsoro ya dabaibayeta. Dak'yar ya iya mik'a hannu yad'auki wayarsa dake gefen gadon, komai yanayinsane cikin dabara da taka tsantsan, Yakuma Jan bargon ya lullu6esu sosai sannan yakira number Adams. Atak'aice yamasa bayani yakashe wayar. Itadai Aysha dukta Shiga damuwa, gani takeyi kafin su Adams d'in suzoma mutanene sunyi yanda zasuyi dasu. Su gwaska kam nacan suna nazarin yanda zasu Shiga gidan, d'aya daga cikinsu yana gwada wani d'an k'arfe a k'ofar falonsu kozai bud'e, cikin ikon ALLAH kuwa k'arfen yabud'e k'ofar falon su Aysha. Dad'ine yacikashi, ya dunk'ule hannu yana fad'in yeees!. Jin haka Wanda ke a kusadashi yamatso yana tambayarsa tabud'e?, yace Masa eh tabud'e. Zagayawa yayi domin sanar dasu gwaska, shikuma d'ayan yashiga cikin falon. Hankalin Aysha yayi masifar tashi, Dan batasan dami mutanene sukazoba, amma amamakinta saitaga ya khaleel ta Kansa kawai yakeyi bawai damuwa da mutanenba, Dan haryanzu yana manne da jikinta, data yunk'ura danta tashi zaice please karki barni, sanyi nakeji, Abu goma da ashirin inji Aysha. Motsi sukafaraji alamun ana ta6a k'ofar d'akin, amma anjita GAM a kulle, sunata k'ok'arin sakab. k'arfennan dansu bud'e amma sun kasa, saboda key d'in yana ajiki ya khaleel bai zareba. A tsorace Aysha tace, "ya khaleel zasu shigofa, Dan ALLAH katashi, wlhy k'ila kashemu zasuyi". Tabashi tausayi, amma bashida k'arfin tunkarar kowa awannan yanayin dayake ciki, shikad'ai yasan halin dayake ciki, baita6a tsintar kansa acikin wannan halin ciwonba tunda yay wayo, yasandai yana ciwo, tunda yasha kwanciyama a asibiti, amma baita6a jin mai azaba irin wannanba, gabad'aya ga6o6in jikinsa kwankwatsa sukeyi, ga bala'in sanyin dayakeji. Ahankali yace, "ki kwantar da hankalinki gasu Adams nan zuwa, bazasu iya bud'e k'ofarnanba saboda akwai key aciki, kibar kuka". ''Ya khaleel idan suka 6allafa?". Shiru yayi yakasa bata amsa, ana cikin haka sukajiyo alamar ana dukan Abu, ya khaleel ya sauke ajiyar zuciya, Dan yasan su Adams sun iso, magana suke jiyowa sama-sama. Su Adams ne suke dakama su gwaska tsawa, bayan sun tattaresu waje d'aya, katafila ne zaimusu gaddama Samuel ya dakesa, shine su Aysha sukajiyo. Su Samuel suka tasa k'eyar su gwaska zuwa waje, mamaki yakama Adams ina ogan nasu yashiga haka? Har wawayennan suka shigarmasa gida?, gashi yaji maganarsa kamar a mawuyacin hali d'azun daya kirasa, tomeke faruwane?. wayarsa yad'auka yakirashi. Ya khaleel yad'auka murya a dakushe yace, " Adams kunzone?". "Ye sir, harma mun kamasu, amma kana inane?". Da k'yar yace, " inan ad'aki kwance banida lfy, kuje dasu kawai, saida safe idan naga yanda natashi zan shigo". "Oga kodai akira doctor k muje asibiti?, nake ganin baikamata kazauna cikin ciwoba". " karka damu kuje, da safe zan kira Dr Abraham". Badan Adams yasoba yace, "to shikenan Oga, ALLAH yak'ara afuwa". "Ameen". ya khaleel ya amsa yana yanke wayar. _______________________________ Haka suka kwana suduka babu mai isashshiyar lfy, duk agalabaice suka wayi gari, da k'yar ya khaleel ya iya raba jikinsa dana Aysha dake barci a wahalce itama, yana layi ahanya ya Isa toilet d'in, cikin dauriya yahad'a ruwa maid'an zafi yayi wanka tareda wankan tsarki, wani ruwan yakuma had'awa sannan yafito, yad'anji k'arfi ajikinsa, amma haryanzu zazza6in yana nan, kuma yanajin sanyi sosai, jallabiya yasaka da rigar sanyi mai kauri, ya dogara yay sallar Asubahi a d'akin, Dan bazai iya fita konan da tsakar gidaba. Bakin gadon ya zauna yana cije la66a, idonsa nakan k'yak'yawan face d'in Aysha dake barci, dagani batajin dad'in barcin, yasan dukda wahalarnan dayake aciki tafisa, Dan bak'aramin wahalar da ita yayiba, kasa control d'in kansa yayima shi gabad'aya wlhy. Ya lumshe idanunsa dake jajur sannan yabud'e akan Aysha, hannu yakai ya yaye bargon, Aysha tabud'e ido, kallo d'aya tamasa tamaida ta rufe saboda kunya. Huci ya furzo a bakinsa, yad'an huro hancinsa alamun baya jin dad'in jikinsa, yace, "zaki iya tashine A'eesha?". Shiru Aysha tayi masa, amma tad'aga kanta. "Daure to kitashi kiyi wanka, kar lokacin sallah yashige", dagaji kasan a wahalce yake maganar. Cikin zubda kwallah tace, " to kabani hijjab d'in nasaka". Hijjab d'in yatashi da k'yar ya d'akko akan sofa, yamik'a mata, tana a kwancen tasaka, ta yink'ura zata tashi, amma azabar zafin dataji yasakata fad'in ya sallamm!!. Tausayi tabashi, dukda jikinsa babu k'arfi haka yad'auketa cak yanufi bayin da ita, Aysha kasa bud'e ido tayi ta kallesa, ya direta, karki cutar da kanki, kishiga ruwan zafi sosai, zakiji sauk'in zafin kafin doctor yazo. Kanta ta iya gyad'a masa kawai, amma takasa amasawa da baki. Fitowa yayi, yacire bargon saman gadon, sannan ya cire bedsheets d'in gaba d'aya, ya nannad'eshi waje d'aya ya ajiye, wani bedsheets d'in yad'ako ya shimfid'a, batareda tsayawa wani gyarawaba ya haye yakwanta, ya k'udundune cikin bargo. Aysha kam tanacan tashiga ruwan zafi, jin zafi yaratsata tamik'e zaram, kuma d'ibar ruwan sanyi tayi ta surka ruwan, zafin ya salamce, ahaka tashiga, shima batawani dad'eba tafita tayi wankan tsarki. Fitowa tayi tana tafiya kamar wata y'ar kac.....🤭. Saboda bata gasa jikin da k'yauba. Ganinsa kwance yasakata ficewa daga d'akin, tanufi d'akinta, a can ta sauya kaya sannan tayi sallah a daddafe takoma kan gado ta kwanta. Ya khaleel yanajin fitar Aysha, tun yana sauraren dawowarta harya fidda rai, yanda tafito daga bayin dawuri ya tabbatar masa batawani tsaya Gasa jikinta da k'yauba, yasan zata sha wahalane, saboda jikinta zai k'ara tsami, amma bashida wani k'arfin taimakonta. Waya ya d'auka yakira doctor Abraham, dukda likitansune ta fannin aiki ya yarda dashi, duk wata Matsala ta ciwo Indai zata taso masa shi yake nema. Babu dad'ewa kuwa saiga Dr Abraham d'in, ashema Adams ya Sanar masa yazo tunda Asubahi, Dan haka ya khaleel yay mamakin zuwan nasa da wuri. Kwatancen d'akin yamasa yashigo, ya khaleel Na kwance suka gaisa, yace, "ashema kana kusa Na kiraka?". " yes sir!, dama Adams ya sanarmin tun d'azun, nad'an dakatane gari Yakuma haske nazo, INA kan hanyar zuwama kakirani". Ya khaleel ya jinjina kai yana lumshe idanu. Bai 6oyema Dr Abraham ba, yasanar masa abinda yakawo ciwon. Sorry sir, inaga ka Tara sha'awane shiyyasa, kadad'e kana buk'atar mace amma Baka d'auki wani matakiba akai, shiyyasa yau daka fidda (S) Ya haddasa maka da zazza6i da jin sanyi, sometimes irin hakan yana faruwa, idan mutum yakai age d'in buk'atar mace amma baiyi hakanba, sai (s) yarink'a taruwa amararsa, yakan haddasa masa yawan mantuwa, 6acin rai, ciwonkai, so duk randa yasamu damar fitarwar saikaga kuma ciwo mai tsanani ya sameshi, kamardai yanda katsinci kanka aciki, please Oga akiyaye gaskiya, Dan hakan had'arine ga lafiyar Dan adam". Jin Nina kai ya khaleel yayi yana fad'in "OK doctor insha ALLAH". Allura yamasa, sannan yabashi magunguna. Ya khaleel yace, "itama yakamata kad'an bata magani, dannanga kamar zazza6inne ajikinta". "OK sir! Amma ita NATA ba damuwa baneba sosai, gajiyace darashin sabo, tasha wannan maganin insha ALLAH zatajita normal". "Amma yakamata kusha koda tea ne yanzu kafin kusha maganin, musamman kai da akama allura, Dan tanada k'arfi". "Babu damuwa doctor, ngd sosai". Sallama Dr Abraham yayi masa yatafi. Tunani yafarayi akan waya kamata yakira danya taimaka masa akan Aysha, yakamata yasamu mai tsayawa akanta danta Gasa jikinta, Inda Anty zuwairah mutuniyar kirkice ai saiya kirasa, tunda dai y'ar uwarsace, kuma yayarsa, yaja guntun tsaki, garama yakira anty shukrah ko Amatullah. Amatullah k'anwarsace, bara kawai yakira Anty shukurah d'in, tunda yaga ita halinta ya banbanta da su Anty zuwairah. Harya fara nemanta saikuma yadakata, wani tunanine yazo masa, kodai yakira Ammah, Dan ita kakarsuce, akwai d'an k'arancin jin nauyinta tartare dasu, yanda zai iya fad'a mata damuwarsa itada Anty Mamie ko momy bazai iya fad'awaba. Gaskiya kuma yanajin kunyar Anty Mamie matuk'a, Anty shukurah d'inma saiyaji kamar da kunya, garadai Ammah, dukda itama yanajin kunyar tata Amman dad'an sauk'i akan sauran. Wayar Ammah yakira, bugu d'aya kuwa ta d'auka. "Iro! Injidai lfy?". Bayason iro d'inan, amma babu yanda zaiyi da Ammah, murya a tausashe yace please Ammah kid'anzo mana". ''Kaini kamin magana da yaren dazan gane, miye wani falis koma uwarmi kace?". Dukda halin dayake ciki saida ya murmusa, aransa yace, " Ammah jaraba kenan, afili kuma yace, "to yi hak'uri, kizo bamuda lfy muduka". Subahanalilahi, to ganin zuwa, aidama inada shirin lek'oku yau, amma dakam sai anjima, to amma ganina yanzu. To saikinzo. ___________________________ Hhhhhh🤣, momy dai har Around 7am bata farkaba, tanata kwasar barci, babu Wanda yatada ita, su azatonsuma tatshi tayi sallar Asubahi takoma barcinne, basusan hajia momy ko motsima batayiba😆. (Aikin amma yayi k'yau😂👍🏻). __________________________ Har barci yafara figar ya khaleel yajiyo Ammah Na kwad'a sallama daga falo, bai iya amsa mataba, Dan bashida k'arfin hakan. Jiyota yayi tana fad'in "yoni halima ina kuke y'ay'annan?, yad'an murmusa yana gyara kwanciyarsa, can saiya jiyo ta turo k'ofar d'akinsa, talek'o kanta, saida ta hangoshi sannan ta ida shigowa, "o, kajimin d'an nema, iro dama kanajina inata kwad'a sallama amma kamin banza?". Yi hak'uri Ammah, banida k'arfin amsa mikine". ''Wayyo, to sannu, ina ita Aysha d'in?, tun d'azun tafita, inaga tana d'akinta kwance". ''To ALLAH ya sauwak'a", tad'auki maganin tana dubawa, kaikace tasan mi'aka rubuta, cikin tsokana ya khaleel yace, " Ammah kina karantawane?". Ta ta6e baki, "yoni iro minasani a wannan shirmen?, to wayazo yabaku magani kuma? Kotun jiyane ciwon?". " A'a Ammah, yanzu doctor yatafi, yamin allura, yacene nasha tea da Sauri saboda allurar tanada k'arfi, ita kuma tasha wannan maganin". ''To bara na had'a maka shayin, amma ni halima nata6a ganin ciwo da salo, kakama mata kakama miji, iro wai miyema yasamekune haka?". Yawu ya khaleel yahad'iye da k'yar, yad'an sosai saman girarsa yana fad'in "um, um, Ammah kedai dakin bani tea d'in k'awai, kingafa rawar sanyi nakeyi, ga zazza6i mai zafi ajikina. Tofa, ninaga wannan aiki, wai kishiya tara rana d'aya, tafice tana tsogumi akan momy, kai laure ko y'ar banzar yarinya, dasotayi tasaka yara cikin tsaka mai wuya, kullum tahana yaro samun ladan aure, aikinga danayi maganin tsagerancinta yanema ma kansa mafita, shima da munafiki yana min mazurai bayason auren, to yanzu ubanwa ya aikeshi gunta hardasu ciwo, mtsoww yaran zamani aii akwai iyayi da firfirta, yo inba firfirtaba miye nakirana wai basuda lfy?. Koda dayake daya fad'ama tsagerar uwarsa d'incan aii gwamma nid'in, Dan nasandai Bilkisu bazai iyaba, bare waccan shema'un da bata shiga sabgar kowa (umme amarya🤣). Tana had'a shayi akicin d'insu take wannan tsogunguman nata, (nace kai Ammah ikon ALLAH😀). __________ Dakanta tabashi tea d'in, danta lura da gaske bashida lfyar, dauriyace kawai da jarumta irin tasa, saida ya shanye tas sannan yanuna mata yanda zata bashi maganin yasha, tace, "to kwanta kahuta, itama Ayshan bara naje kanta, ALLAH yak'ara afuwa". Cikin gyad'a kai yace, " Ameen ammah". Bargon ta gyara masa, ta lullu6eshi da k'yar sannan tafice. Barci mai nauyi ya figesa, tunaninsa nakan Aysha, duk tausayinta yacika zuciyarsa, shi ga halin dayake ciki bare ita kuma daya wahalar. ************** Akan gado amma ta iske Aysha kwance, itama ta k'udun dune cikin bargo, tazauna kusada ita tana sakamata albarka, tabama jikanta farinciki, jikanta datafi k'auna aduk cikin jikokinta, jitai k'aunar Ayshan takuma yawaita azuciyarta, tanason jarumin mutum, sosai mama takuma kima a zuciyar Ammah. Ammah ta yaye bargon da ayshan take k'udundune ciki, dakar Aysha ta'iya bud'e baki tace, "wayyo ya khaleel please kayi hak'uri, wlhy sanyi nakeji, kuma nayi sallan aii". Idonta arufe take maganar, duk zatonta ya khaleel ne yabiyota d'akin. Murmushi Ammah tayi, tace, " kwantar da hankalinki, ba iron baneba, nicenan". Zunbur Aysha tatashi zaune, ganin Ammah sai kunya ta kamata, tace, "Ammah ina kwana". Lfy lay d'iyar albarka, yajikin?. Kan Aysha ak'asa tad'an motsa bakinta, amma takasa cewa komai, wata kunyar Amman takeji sosai, gani takeyi kamar ya khaleel d'in yafad'i komai. Dariya Ammah tayi tareda mik'ewa tashiga toilet d'in Aysha, babu dad'ewa saigata tafito, tacema Aysha taso. Babu musu Aysha ta sakko, saida tana tafiya tana hard'e k'afafu, batason Ammah tafahimci halin datake ciki, dukda azabar datakeji wajen tafiyar. Batasan Amman kar take kallontaba, kafinma tazo wajenta tuni ta gane komai😂. Ammah taji tausayin Aysha, Dan bak'aramar 6arna khaleel yayiba, sosai ta taimaka mata da dabarunsu irin Na tsoffi, tayima Aysha gashi Na musamman Na y'an gata, ita kanta Aysha taji sauyi sosai ajikinta, Har tana iya tafiya babu laifi, bakamar d'azunba dasai ta ware k'afafu. Itama tea mai kauri Ammah tahad'a mata, itakam ba gwanar shan shayin baceba, saida Ammah ta lalla6ata sannan tashanye, tabata maganin da ya khaleel yace abata tasha, itama ta kwanta. Saida Ammah taga barci ya d'auke Aysha sannan tafito daga d'akin takoma Na ya khaleel. Zanin gadon datagani a k'udundune saman sofa yad'auka tabud'e, flowers d'in dake ciki suka zubo, wasu duksun d'an 6aci, cikin ta6e baki amma tace kajimin iyayi irinna yarannan, sunwani zuba filawa agado saikace wasu kafirai, mtsowww wlhy bokon nan ta6ata mana yara dai, aiimu a al'adar Malam bahaushe farin k'yalle muka Sani bawata filawar banzaba, dukda zanin gadon farine inma al'adar zasuyi saisuyi irin tamu. Hakadai tayita jaraba tana zazzagewa, Leda tasamo tazuba flowers d'in aciki taje tasaka abola tana tsaki. (Ho Amman ho Amman!, maganin kowane shege🤣🤣🤧). A wishing matching tasaka bedsheets d'in, tawanke fes tazagaya zan bayan d'akunansu ta Shanya inda aka d'aura igiyar, sannan takomo falo tazauna tana gadin tashinsu. Muna godiya Ammarmu, ciki da gaskiya fans suna mik'o gaisuwar ban girma, suna nan suna had'a miki k'yaututtuka Na musamman danjin dad'i👍🏻👍🏻, xoxo tace, "tabaki k'yauta homajeep, amma sai Aysha ta haihu za'a kawo miki.🤭😆👍🏻. ______________,,___,__________ Wajajen 8:36am momy tafarka afirgice, sunan khaleel tafara kira da k'arfi. "Ibraheem! Ina Ibraheem!? Badai yatafi can d'inba? Ibraheem! Kana inane?". Anty zuwairah ce tajiyo sambatun momy, dasauri tashigo d'akin tana fad'in "momy kintashi?". " eh zuwairah, ina Ibraheem yakene?". "Yo momy k'yaga khaleel nankuwa, yana 6angarensu mana". "kambu, kina nufin a can ya kwana? Amma kuka gaza hanashi?". " to momy waya isa hanashi tafiya, waccan fitinanniyar tsohuwar Na kammu, gakuma baffah da waccan munafukar". Shikenan Ibraheem kagama dani, inhar ka kusanci shegiyar yarinyarnan karuwa, zuwairah muje 6angaren nasa, muje muje da sauri. Momy yakamata kufara yin sallah ko, dan nazata kinyi sallah, amma tunda naji kina Neman khaleel nagane baki farkama". Danma dai kawai, "to amma bara nayi sallar, amma anyi munafukar tsohuwa, kenan allurar barci tasaka akaminfa zuwairah?". "Wlhy kuwa momy, aini nak'agara tsohuwarnan tamutu, dukda kasancewarta uwar ubana, amma nagama tsanarta tuni wlhy". Gaba d'aya momy lissafinta a jagule yake, ahaka tashiga tayi alwala. Sallarma dai tayitane kawai, amma babu wata nutsuwa aciki, Anty shukurah Na falo suka fito, tace, "lah momy kintashi?, bata kulataba suka fice itada Anty zuwairah, ganin haka tamik'e da sauri danson ganin inda zasuje. Suna huci suka nufi 6angarensu ya khaleel........... 😄momy afito lfy🤭 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋 [9/17, 8:59 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣7⃣ Ammah Na kacire saman kujera doguwa ta kurama TV data kunna idanu, kaikace tanajin yaren da'akeyi, tanason canzawa amma tarasa yanda zatayi, kunnan tvn dai ta iya. Daga momy har Anty zuwairah babu Wanda yalura da Ammah, itakam tun shigowarsu idanunta Na Kansu, k'iyarsata yanda zataci mutuncin momy azuciyarta kawai takeyi. Momy daketa harare-harare da hura hanci tafara kwalama ya khaleel kira. "Ibrahim! Ibrahim!! Kobaka jinane?". "yaza'ayi yajiki? Bayan yanacikin halin ciwo Laure!". Afirgice suka juyo suduka suna kallon Ammah, Anty shukurah dake k'ofar d'aki tsaye tayi murmushin jin dad'in ganin Ammah, shiru momy tayi takauda kanta daga kallon Ammah, zuciyarta sai suya da zugi takeyi. Anty zuwaitah ce tasamu k'arfin halin Jan k'aramin tsaki, tana ta6e fuska. Ammah tace, "kinyiwa Abdillahi da Laure, mara mutunci fitsararriya, mai girman kwabo kawai, 'Yar banza magajiyar uwarta". "nidai badai uwataba ehe". Tassssss!! Kakeji afuskar Anty zuwairah, gaba d'ayansu suka waigo dansan ganin Wanda yay marin, bakowa baneba face baffah da Anty shukurah takira awaya tasanar masa gasu momy can suntafi 6angaren khaleel. Dafe kunci Anty zuwairah tayi, tunda ta girma tayi hankali baffah baita6a ko dungurintaba, amma yau harda mari? Da girmanta, ga zagada-zagadan 'ya'ya. Momy kam baki bud'e take kallon baffah, tama rasa abin fad'a. Ammah tataso tana tafa hannaye, ''kayimin dai-dai, kuma tabbas nahaifi d'an halak, kekuma kince badai uwarkiba?, to saitawa kenan?". Cikin zubda hawaye Anty zuwairah tace, "nidai aii ban fad'aba ko". Ammah zata sake magana baffah yace, ''kiyi hak'uri Ammah Dan girman ALLAH, basai kincigaba da 6ata rankiba akan rashin tarbiyya irin ta wannan mara mutuncin da uwarta ba, namuku biyayya Na auri Laure badan inason halayentaba, ayanzukam ina rok'on alfarma agareki, abisa madadin baba zan saki Laure yanzunnan, saboda halayenta sun isheni, banajin dad'inta, banajin dad'in 'ya'yanta sai shukurah da mu'azzam kawai, dan ALLAH Ammah kibari nasaketa kawai". " humm bazaka saketaba Abdullahi, saboda wasu dalilaina, munhad'a aurenka da ita saboda darajar zumincin dake tsakanina da jummai mahaifiyarta, sannan kuma akwai 'ya'ya tsakaninku yanzu, to taci darajar y'ay'an dakuka haifa, d'ayan sirrin kuma nabarma zuciyata, dan haka kabarta duniyace zata koyar da ita hankali kwanannan". Wani irin kallon momy take bin Ammah dashi, maid'aukeda abubuwa da dama, tsoro, tsana, k'iyayya, k'yama, hasala, bak'inciki, wai agaban 'ya'yanta wannan tsohuwar take cin zarafinta itada d'anta, lokaci yayi dazata d'auki mataki akan baffah da uwarsa, batareda tace komaiba tajuya afusace tabar falon. Anty zuwairah ma baya ta take mata. Baffah ya dakatar da ita, "kije yanzun ki tattara kayan 'ya'yanki da naki kibarmin gida Dan ubanki, kuma wlhy karna sake ganin k'afarki agidannan Harnan da shekaru biyu, inkuwa bahakaba saina sa6a miki kamanni Mara mutunci kawai, karna fito Na iskeki cikin gidana wlhy kinji Na fad'a miki shashasha". Wannan hukuncin yamin dai-dai, Dan in ba hakaba wannan makirar saita kashema iro aurensa, Dan itace ke zuga uwarsu, Na tabbata ko wannan ciwon k'aryar da Laure taitayi harda bakin 'yar banzar can". Anty shukurah tamatso jiki a sanyaye tana Bama baffah da Ammah hak'uri. Albarka sukaita saka mata, sannan Ammah Tamusu bayanin ya khaleel d'inma bashida lfy. Har d'akin ya khaleel baffah yashiga, khaleel Na kwance idonsa biyu, tun fara maganar Ammah dasu Anty zuwairah ya farka, komai akan kunnensa yafaru, bak'inciki da k'yamar halin mahaifiyarsa da 'Yar uwarsa yahanashi fitowa, dukda abin yahad'ama darashin jin k'arfin jikinsa. Su Ammah na shigowa ya lumshe idanunsa, baya buk'atar Susan idonsa biyune, Anty shukurah tajawo stool d'in madubi ta ajiyema baffah gaban gadon, kusada ya khaleel, zama yayi yanamai tausayin d'an nasa, saboda halin mahaifiyarsa, yasan kokad'an khaleel bayajin dad'in mahaifiyarsa, hak'uri kawai yakeyi kasancewarsa mutum mai kawaici da had'iye damuwa, kokai waye Baka isa tantance damuwar khaleel ba, mutumneshi mai taka tsantsan da iya zaman duniya, komansa namasu nazari da dattakone, gashidai yaro amma akwai halayen manyan mutane tattare dashi, wannan baiwace da ALLAH yamasa tun yana k'araminsa. Ahankali baffah yakai hannu yana shafa kan ya khaleel d'in, cikin taushin murya yace, "ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, ALLAH yabaka lfy". Ammah da Anty shukurah sukace ameen. Ammah tace, " aii zazza6in ya sauka ko? Dan sanda yakirani yanajin jiki sosai, amma dayake iro jarumine baka gane hakan". Murmushi baffah yayi, "Ammah da d'an sauran zafi kam ajikinsa, amma ba sosaiba". "To Alhmdllh, aidayake likita ya dubasu". Baffah ya jinjina kansa yana kuma fad'in " ALLAH dai yak'ara sauk'i, ina ita matar tasa?". "Itama tana d'akinta babu lafiyar, Shukurah duba ita kiga tashi". " to Ammah". Addu'a ya khaleel yakeyi azuciyarsa ALLAH yasa kar Ammah tamasa 6arin makauniya a gaban baffah, kaidata gama kasheshi wlhy....... Tunaninsa yakatse lokacin da Anty shukurah tadawo tana fad'a musu haryanzu Aysha barci takeyi. d'akin Ayshama saida baffah yashiga, sun isketa tanata barcinta itakam hankalli kwance, itama baffah yamata addu'a sannan suka fito. Suna fita Aysha tabud'e idonta, Ashe itama idonta biyu, duk badak'alar da akeyi acikin kunnenta, jin motsin tahowarsu yasakata rufe ido harda d'an munsharin k'arya. Jitai wata k'aunar surikin nata kuma mijin mahaifiyarta na ratsata, tareda kakar mijinta, surukar mamarta, dakuma d'iyar mijin mamarta kuma yayar mijinta, ta share hawayen dasuke kwarara bisa kumatunta, zuciyarta Na mamakin hajia babba wace irin mutumce?, akoda yaushe tana mamakin taurin zuciya irinta hajia babba, ga maigadonta nan kuma sak tasamu Anty zuwairah. Ta sauke ajiyar zuciya, yayinda tunaninta ya iso kan mijinta, shikuma halayensa sunyi mugun samun tazarar nisa tsakaninsa dana mahaifiyarsa, kokad'an ko alama babu kamanceceniya yanayin halitta ta halaye da jini da yakamanta hajia babba da ya khaleel, tomiyasa haka?, wannan ikone kuma Na ALLAH mad'aukakin Sarki, mai fidda rayayye daga jikin matacce, zuciyar Aysha tafad'a yayinda tunaninta ke k'ok'arin tasirantuwa da shakku, "hakane kuma" tafad'a tana gyara kwanciyar, tareda dawo da tunaninta akan mutanene jiya dasuka shigo musu gida. Tabbas yakamata tayi tunani akan waya turosu? Shin ta 6angarenta sukazo? Kokuwa ta 6angaren mijinta?, tasan zuciyar su hajia babba a bushe take, bushewa kuma irinta kututturen marke daya mutu a shekarun tashen k'uruciyarsa, tacije le6enta Na k'asa da k'arfin masifa, kaikace zata hudashine da hakwaranta, lokacifa yayi dazatayi aiki ba saka lokaciba, inkuwa bahakaba lokaci zaita gudun zomo da tunaninta, zata kira Anty meerah dansu mik'e tsaye, wannan lokacin bana tsare-tsare baneba na gudanarwa ne da zartar da hukunci ga masu laifi irinsu hajia babba, zasu farane da k'ananun kwari irinsu glory domin dakushe kaifin su hajia babba, tasaki murmushin gamsuwa akan tunaninta. Shima ya khaleel suna fita yacije le6ensa, zuciyarsa namasa zafi da k'una, musamman daya tuna da gardawan jiya, zai d'auki mataki kam sosai, shi tunaninsama baikawo Kansu hajia babba, azatonsa daga wajen aikine aka masa turre. Cikin k'arfin zarrar jarumtakarsa yature wannan tunani danasu momy, bayason 6ata wannan ranar farincikin nasa da 6acinrai, danhaka yamaye gurbinsa da tuna farinciki da baiwar da ALLAH yamasa adaren jiya, daga tagomashin alkairi na matarsa Aysha.😘👍🏻 ____________________________ Babu inda zakije, saidai mutafi kamar yanda yayniyya tun farko, aini banso munafukarcan tahanashi ya sakeninba, saimima danya sakeni, bajira nakeyi agurinsaba, idan dukiya yake tak'ama da ita wlhy ayanzu ni Laurah na ninninkashi, idan k'arfin iko yake tak'ama dashi nafishi, idan k'yaune yanzunkam babushi Dan tsufa yacinye masashi, to saime? nace saime? Saime kegareshi dayakeda zarrar wulak'antani? Wlhy Abdallah kayi k'arya ka kwana da yunwar wulak'anta laurah dagakai har uwarka, dolene nad'auki mataki, dolene kasan laurah tawuce dasaninku da tunaninku tuniii!!!". Yanda tak'are maganar a tsawace saida yasaka Anty zuwairah zabura, saikuma ta sauke ajiyar zuciya ganin momy na hawaye, "nayi kuskure tun farko a rayuwata, tabbas danasan ALLAH zai d'aukakeni zuwa yanzun dababu abinda zaisakani aikata hakan, Abdallah abinda yasani auranka danshi yanzu nafika, nace nafika abinda kesakaka tak'amar dahar nawahalar dakaina dominshi abaya!!, Abdallah zan d'auki mataki akanka cikin ruwansanyi, matakin dazai ta6a zuciyarka da rayuwarka, matakin dabazaka ta6a mantawa da lauraba, abinda kafiso da tak'amar dashi zan salwantar, wlhy nad'auki alk'awarin salwantar da ruhinsa domin haddasa bak'inciki dawwamamme azuciyarka na har Abadan". Tsoro da mamakin maganganun momy suka rikita Anty zuwairah, kallon momy takeyi cikin matuk'ar tashin hankali da tunanin kodai tazarene?. Atsorace tace, " momy wai mikike fad'ane haka? Nagaza fassara wad'annan kalaman naki". Idon momy jajur tajuyo tana kallon Anty zuwairah, tayi wani murmushin takaici, "zuwairah bazaki ta6a ganewaba, Dan banama buk'atar ki ganed'in, kishirya keda yaranki kutafi kamar yanda ya buk'ata, kuma karki sake waiwayar gidannan harsai adadin abinda ya yanke miki yacika, nikuma zuwa sannan inamai tabbatar miki alk'awarin Dana d'auka yacika ko yana gab da cika". " Amma momy.........". "Karkice komai zuwairah, kedai kiyi yanda nace". Jinjina kai Anty zuwairah tayi tana had'iye yawu mai kaurin tsiya, itafa lamarin momy yafara bata tsoro, wlhy tun kwanaki tafara tsarguwa dawasu lamura nata, takuma dulmiya zuciyarta cikin tunani lokacin data saka gwaggo bintu zama awajenta, anya kuwa momy bata aikata wani 6oyayyen Abu kuwa a 6oyewa?, to amma miyasa zatayi hakan?, kai zato zunubine aii". Haka Anty zuwairah taita tunani tana had'a musu kaya. Aranar sukaje airport itada mufeeda suka nemi jirgi, sunsami maizuwa Lagos, zaitashi 6:15pm, saida suka gama komai sannan suka dawo gida dansu ida shiryawa. Momy tace, " Anty shikurah ma tasanarma mijinta yashirya musu jirgi nanda kwanaki uku sutafi. "Momy mufa munzone danmu dad'e, inagama ni bazan komaba, dan wlhy nagaji dazaman wata k'asa, nafison zama a k'asata". " Baku isaba shukurah, dolene Ku koma, bana buk'atar zamanki a k'asarnan, danhaka kishirya". Uffan Anty shukurah batacema momyba. ___________________________ Ammah fa yau gaba d'aya takoma 6angaren su ya khaleel, har break fast d'intama can aka kaimata, zuwa sannan kuma ciwon ya khaleel ya karad'e gidan, tuni k'annensa suka fara turuwar zuwa dubashi, wannane yasaka Aysha watstsekwar dole, dan batason asakata a lissafin masu rashin lfyar. Shimadai yaji d'an dama-dama Dan harya fito falo, inda Amman da Aysha da k'annensa ke zaune. Sannu suka shiga yimasa da tambayar jikinsa, amsa musu yaytayi cikin yanayin rashin jin dad'in jiki, tsakaninsa da Aysha kam sai 'Yar satar kallon juna, dukda shid'in yakan kalleta kai tsayene wani lokacin, Amma itadai takasa kallonsa. Anty Mamie dakanta tabashi abinci abaki, yana matuk'ar k'aunar matar, musamman yanda take tattalinsa da nuna masa k'auna irinta mahaifiya, wadda mahaifiyar tasama tagaza nuna masa koda mafi k'ank'antane, sarai taji bashida lfy, Amman tagaza koda lek'oshi sau d'ayane, hakama k'annensa da Anty zuwairah, sai Anty shukurah kawaice keta zarya, Amman momy tun zuwan safennan datayi bata kuma lek'owaba barema kiran wayarsa tasamu tabbacin bashida lfyar. Anty Mamie kam da Ammah tun d'azun suke tsaye akansa, harda matarsa da Ammah kebama kulawa cikin hikima, Dan bata bada k'ofar da kowa zai fahimci ainahin abinda ya haddasa ciwon na khaleel ba, hakan yamasa dad'i, dan kobabu komai Ammah Tarufe sirrin aurensa da matarsa. Kiran sallah yasaka Ammah da Anty Mamie mik'ewa, sai Anty Ama..., sauran yarankam yawanci duksun fita wajen aiki da school, Ummunoor, Nuriddin, da 'yan uku suna Kano tareda mama, kasancewar yara suna hutun makaranta, su tasleem ne kawai agida da maleeka, kasancewar bana suka kammala secondary d'insu. Anty Mamie takalli Aysha dake kwance cikin kujera 1seat, tayi shiru, ko baki bata sakawa a firar tasu Ammah, ''Aysha tashi ki had'ama mijinki ruwa maid'an zafi yayi wanka, danya kuma samun k'arfin jikinsa kinjiko". ''To Mamie", 'Aysha tafad'a cikin jin kunya'. Bayan fitarsu Anty Mamie falon yay tsit, saisu biyu kad'ai, kan Aysha ak'asa tamik'e tanufi d'akinsa dan cika umarnin Anty Mamie, binta yayi da kallo kawai harta shige d'akin, ya lumshe manyan idanunsa yana fesar da huci ta bakinsa. Kunsan mintuna uku da shigarta shima yabi bayanta, tana cikin toilet, kayansa yafara cirewa, ya d'aura towul, tana shirin fitowa shikuma yashiga, karo sukayi ak'ofa, Aysha tayi saurin jada baya tana fad'in "sorry, wlhy bansan katahoba". Idonta ak'asa take wannan maganar, dan wata matsananciyar kunyarsa takeji sosai ayau, shikam hard'e hannayensa yayi ak'irji yakafeta da mayun idanunsa masu tsoratar da mara gaskiya, fuskardai ba'a d'aure takeba, sannan ba murmushi yakeyiba, tana asakedai yanda mutum bazai tsorata dashiba🙂. Ganin yak'i bata hanya tawuce tace, " ga ruwan nahad'a". Bakinsa yad'an ta6e sannan ya warware hannunsa yana cije le6ensa na k'asa, k'ara matsowa yayi gab da ita ya tsaya, yasaka hannun damarsa yad'ago fuskarta, lumshe idanunta tayi, yasaki guntun murmushi yana k'arema zara-zaran gashin idonta kallo, suna matuk'ar d'aukar hankalinsa dasakashi a shauk'i suda kwantaccen gashin dake goshinta. Ahankali yashiga hura mata iskar bakinsa saman idonta, far-far tafarayi da ido, dole tabud'esu batareda ta shiryaba, amma suncika da kwallah, ruwan hawayen saiya k'ara musu wani k'yalli mai d'aukar hankali, daga ita harshi anrasa mai tankawa. Sakin fuskar tata yayi yajawota ya manna da jikinsa, ajiyar zuciya suka saki atare, yasaka hannu agadon bayanta yazuge zip d'in rigarta doguwa. Cikin sauri tayi k'ok'arin raba jikinta da nasa, amma saiya kuma k'ank'ameta, saida yakai k'arshen zip d'in sannan yacirota dakansa, hannu yasaka akafad'unta zai zame hannuwan rigar tayi saurin dafe hannayensa. Muryarta na rawa, dan tuni hawayen sun fara zuba, tace, ''please sallah zanje nayi fa". "Uhhhhmm!" Kawai yafad'a ya ture hannunta ya ida zare rigar gaba d'ayama, Aysha ta matse idanunta, hawayen masu d'umi suka zubo, baibi takantaba yacira bra d'inma, sannan yad'auketa cak yadire a kwamin wanka, shima yashige. Haka akayi wannan wanka idon Aysha arufe, shiyayi kid'ansa yay rawarsa, harya gama yanad'ota a towul bayan yasakata yin alwala. Mai yashafama kansa, sannan yajuyo ga Aysha dake zaune kamar gunki ido arufe, dariya tabashi amma baiyiba, yamatso kusada ita bayan yasaka k'ananun kaya ajikinsa, man yafara shafa mata, tana kakkaucewa har aka gama. Yabud'e wadrob nashi ya d'akko doguwar riga Arabian gown, ita mamakin wad'annan kaya dayake fiddowa d'ai-d'ai takeyi, dakansa yasaka mata, takuwa yimata azabar k'yau, ta haskaka farar fatarta, sannan tamata cif tamkar an gwadata, ita kanta Aysha rigar ta birgeta sosai. Nidai 'Yar rahotonku haushi yafara kamani😠, sai wani Abu sukeyi kamar kurame😏. Sallar Azhur yajasu, bayan sun idar yajuyo yana kallonta, yajikinki? Yafad'a ahankali". Cikin turo baki tace, "nidai lfyata lau, kainedai za'ace yajikinka?". Baisan sanda yasaka guntun murmushi ba, yasa yatsansa ya d'alli bakinta data turo gaba. Da sauri tasaka hannu tadafe bakin, saiga hawaye. Jikinsa yajawota ya rungume, " kewai baki gajiya da shagwa6ane? Laififa kikayi na hukuntaki, to miye nakuma asarar hawayen? Ke kullum babu Abu mafi arha agareki irin hawaye?, waishi saunawa kikeyin kuka arana?". Yay maganar yana d'ago fuskarta tareda zuba mata idanu. Shiru tamasa tana kuma kwa6e fuska zatayi wani sabon kukan, "a'a nikarkimin kuka, tashi muje kibani abinci nasha magani, inga zuwa la'asar zan iya fita, inason naje office akan maganar yaran jiya dasuka shigo gidanan. Kanta ta jinjina masa tana yunk'urin mik'ewa, da sauri yajawota tadawo saman cinyarsa, " magana zakimin dabaki, kinsan banason shariya". Kallonsa tayi damamki, shi babu dad'i yakema mutane shariyar?, amma afili saitace to". 'Cikin sanyin murya'. "Hummmm abin mamaki, waini yau kinzama ustaziyane?, kokuma wani salihancine yazo bayan biyan kaza?". Kunyace takama Aysha, tacusa fuskarta a k'irjinsa tana dariya k'asa-k'asa. Shima rungumeta yayi tsam yana sakin tattausan murmushi. Daka gansu kasan suna matuk'ar farinciki da nishad'i na musamman................😂✍ *_inayinkufa wlhy🙋🏻‍, acigaba da gashi, suya sai anacin uban hajia babba♀😜_* 🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀babu ruwana karta kaini karuwanci turai, masoyan hajia babba amin afuwa😆🤭. ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤💋💋💋💋 [9/18, 3:59 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣8⃣ Zazza6i dai yak'i sakin ya khaleel, yana kwance a d'akinsa cikin bargo, Ammah da Anty Mamie duk suna d'akin, kowa jigum-jigum, Aysha ma tana gefe ta zabga tagumi, tunani a zuciyarta barkatai, dama haka mazan keshan wahala idan hakan tafaru? yawanci alabarai saidai kaji ance matace tasha wahala a daren farko, to amma ita nasu sai yazo da ban, dukda tasan tasha wahala, har yanzuma zata iya cewa bata gama dawowa dai-daiba, ammah ya khaleel yafi bata tausayi, danya fita wahaltuwa, jiyamafa haka suka kwana yana rawar sanyi, wannan wane irin ciwone haka?...... Shigowar baffah da doctor ne yakatsema Aysha tunani, yau Dr Faisal ne zai dubashi, Wanda yakasance family doctor nasu. Anty Mamie tajanye bargon da ya khaleel yarufe har fuskarsa,, yad'ago idon yana kallon Anty Mamie, sunyi jajur dagani kasan bayajin dad'i kam. "Sannu babana kaji". Cikin murmushin k'arfin hali yad'agama Anty Mamie kansa, baffah yamatso ya taimaka masa yatashi zaune ya jigina da fuskar gadon, yakai dubansa ga Aysha dakecan zaune ta zabga tagumi, kasancewar itama shitake kallo suka had'a ido, ita tafara janye nata, sannan shima ya d'auke nasa yamaida kan Dr Faisal dake masa tambayoyi. Ganin kamar yanajin nauyin amsawa Dr Faisal yace, "please Alhaji kozaku d'an bamu wajene?". Baffah yace, "OK babu damuwa doctor, bismillah kayi aikinka". Har Aysha tamik'e zata fita Ammah race, "a'a kekam yi zamanki". Babu yanda zatayi, dole takoma tazauna, sukuma suka fice. Ya khaleel yayma Dr Faisal bayani kamar yanda yayma Dr Abraham jiya, Yakuma Sanar masa Dr Abraham yabashi magani harda allura. Dr Faisal yakar6i magungunan yaduba, "kwarai yabaka magani mai k'yau, zazza6inne kawai yamaka naci, kuma inaga hakan yahad'a da buk'atar Hutu da jikinka keso". Guntun murmushi ya khaleel yayi, "Dr aii Hutu bai ganniba nikam, kasan yanayin aikin namu". "Hakane Ibraheem, amma gaskiya kad'an dinga dubawa, kana ayyukan dasukafi k'arfin jikinka sosai, garashin isashshen barci, amma tushen matsalar gaba d'aya shine tuzuranci". ' yay maganar cikin zolaya'. Murmushi ya khaleel yayi, "Dr kaima zaka ta6ani kenan". "Hhhh aikai d'innefa, shekaru kusa 37 babu mata? Amaryama tayi k'ok'ari data iya kar6arka". "Hummm Dr kenan, bazaka ganeba ne kawai". 'Ya khaleel yay maganar idonsa nakan Aysha, datum d'azun take cikin matsananciyar kunya, saboda bayanin da ya khaleel kema Dr ko kunya babu, bawai fallasa sirrinsu yakeyiba, a'a musabbabin ciwon nasa yafad'amasa. "yanzu dai bara ak'ara maka magunguna, saikuma nasaka maka k'arin ruwa". Ya khaleel ya amsa da to yana janye idonsa daga kan Aysha. Dr Faisal yasakama ya khaleel k'arin ruwa, sannan yace a samu towel k'arami a d'an jik'a da ruwa ana dannama ya khaleel d'in goshinsa, saboda yaji kansa yayi matuk'ar zafi. Godiya baffah yamasa sannan yatafi, Anty Mamie tace, " Aysha tashi ki d'akko towel, saiki zubo ruwa ak'amin roba". "To". Aysha ta amsa tana mik'ewa. Koda tadawo saita Taras su Anty Mamie duksun fice, wannan ya tabbatar mata cewa aikin natane, ganin idonsa alumshe tad'auka barci yakeyi, saman gadon tahau ta zauna kusada Kansa, tamatse towel d'in dagan ruwan ahankali tad'ora bisa goshinsa. Ajiyar zuciya ya saki tareda bud'e lumsassun idanunsa yasauke kan Aysha saboda sanyin ruwan. "sorry ruwan da sanyi ko?", 'tafad'a kamar zatayi kuka'. Guntun murmushi yasaki, sannan yamaida idonsa yalumshe, k'in cigaba dayi tayi, saima ta6ige da kallon fuskarsa, jin shiru bata cigababa Yakuma bud'e idanun nasa akanta yace, "miya faru?". Daburcewa Aysha tayi, bataso yakamata tana kallonsaba, shikuma saiyayi tamkarma baisan mitakeyiba, "cigaba Dayimin mana, kobakiso nasamu sauk'i?". Girgiza masa kai kawai tayi, amma takasa magana, cigaba tayi da saka masa towel d'in tayi, ahankali kan yafara hucewa. Kamar daga sama Momy tafad'o d'akin ko sallama babu, kunyace tad'an kamata, dataga ansakama ya khaleel k'arin ruwa, amatsayinta Na mahaifiyarsa bashida lafiya har haka amma batazo ta dubashiba, alhalin kuma tasani sarai, ko yanzun zuwa tayi tamasa fad'a akan wai yak'i yaje inda take saboda yayi aure, saikuma tazo ta taras Ashe jikin nasane. Batareda Aysha ta kalletaba tace, "Momy ina kwana". Harar Aysha Momy tayi, batareda ta amsaba tamatso kusada khaleel, cikin d'an rikicewa tace, " Ibrahim! Dama bakada lfy amma aka gaza sanarmin? Tunkafin ayi nisa son rabani dakai akeyi kenan?". Aysha data fahimci zancen Momy tsaf da ita take, saitayi murmushi, tana cigaba da goga towel a goshin ya khaleel tace, "uhmm to k'ila laifin Anty shukurah ne, Dan itakam jiyama kusan anan tawuni tareda kowa na gidannan, Momy inagama dai kekad'aice bakizoba sai Anty zuwairah dasu mufeedah". Ya khaleel najinsu, amma kokad'an bai fahimci bak'ar magana sukema junaba, musamman yanda yaji Aysha nama Momy magana cikin girmamawa. Magana Momy zatayi ya khaleel yabud'e idonsa, shiru Momy tayi tadawo da hankalinta kansa, saitakama borin kunya wai ank'i sanar mata. Murmushi kawai yamata, amma baice komaiba. _____________________________ Anty zuwairah dai tun jiya tawuce, Anty shukurah kam baffah yahana, yace tayi zamanta har mijinta yazo. Hakan da baffah yayi yakuma hasala Momy, amma bata nunaba. Wajen 3pm saiga hajia khaltum a rikice tazo gidan, ko gaisuwa basuyi da momyba tace, " Aminiya yanzunan ankamasu gwaska shine baki sanarminba". Wata zabura Momy tayi tareda fiddo ido waje, tace, "kamarya? Ban ganeba?". "Hummm kina bani mamaki wlhy wani lokacin, abinda yasa tun jiya banzoba wasu yarane muka tura k'asar Dubai amma aka kamasu suda Ruth d'in, gabad'aya hankalina atashe yake, shiyyasa ban maida hankali akan su gwaska ba, ni duk azatona yarinyar tana hannunsu, sai yau naje gidan gwaska wani yaronsa ke sanarmin ankamasu agidannan daren jiya, shima abinda yasa yatsira ba'aje dashi baneba, sunbarsa tsaron gida". Sosai naga tashin hankali da rud'ewa tattare da Momy, tama rasa abin fad'a, komai ya kwace mata, suna cikin wannan tararrabi aka kira number hajia khaltum, wai ankama Alhaji bishasha. 😆 kuttt saida hajia khaltum tashiga bayin Momy, dama ita akwai tsoro, sai tsageranci fal cikinta kuma😄. Momy kamar zatayi kuka tace, " hajia khaltum nafara jin tsoro gaskiya, yanzu kuma suwaye suka kama Alhaji bishasha?". "Wai sss tareda police Interpol ". "to ammah Ibraheem yana gida kwance babu lfy aii". " da gaske". "ALLAH kuwa, tun jiyama bashida lfy, kama su gwaska ma saidai idan wasu yasaka".. ......jinjina kai hajia khaltum tayi tana fad'in "dolene k'ungiya tahad'a taron gaggawa kuwa, bara naje, zamuyi waya".... Momy dai takasa cewa uffan, ita gani takeyi haryanzu tanada mafitar kare kanta wajen ku6uta. Nace hummm. ____________________________ Aysha zaune kusada ya khaleel tana had'a masa shayi, shikuma ya tsareta da idanu ko k'yaftawa bayayi. Tad'ago danufin bashi tea d'in saitaga ita yake kallo, kunyace takamata, asanyaye tace, "ga tea d'in". Kar6a yayi batareda yace komaiba, wayarsa tafara ring. "hello Taheer! Ya garin?". "Alhmdllh sir". Yanda yaji taheer yanutsu saiya gane kiran bana fannin abokantaka baneba, Na aikine. Shima saiya nutsu yaci serous. Taheer yace, " sir idan babu damuwa zanzo gida saboda namaka bayanin wani aiiki". "OK babu damuwa, saina ganka", ya yanke wayar. Aysha najinsa, bayan ya ajiye wayar yace, "jeki saka hijjab taheer zai shigo". Ta amsa da "to", sannan tamik'e tanufi d'akinta, shikuma yabita da kallo. Babu dad'ewa saiga taheer ya iso, yau Aysha taga ikon ALLAH, yanda taheer yawani k'ame tareda salute d'i ya khaleel d'in, shikuma yaci serious, babu ko magana, hannu kawai yad'agama taheer d'in, Aysha a zuciyarta tace Sabon salo, saikace ba abokinsaba? Kai wannan hali Na ya khaleel baiyiba. Itadai ta ajiye k'aramin tire data d'ora ruwa da lemo agaban taheer, yanda taheer yace mata ya gode cikin nuna girmamawa sai kunya takama ta, takoma gefe ta zauna tana kallon ikon ALLAH. taheer yamik'ama khaleel laptop dake hannunsa, "sir! Ga jerin wad'anda muka kama tareda Alhaji bishasha, aciki mutum 4 sun rasa ransu, 1 sss ne, 3 kuma yaran Alhaji bishasha, wasu kuma sun sami rauni ta silar harbi da yankan wuk'a, gsky Alhaji bishasha yanada had'ari sosai". Jin jina kai khaleel yayi, maimakon yabama taheer amsa da turanci kamar yanda yamasa magana, saiya juya da French. Taheer daya fahimci yayi kuskure yace, "sorry sir". Dan acikinsu nasan sirri, kuma ga Aysha awajen, baikata kuma tasan wani Abu dangane da aikinsuba, dukda kasancewarta matarsa, saidai baisan Ayshan kuma tanajin French d'inba. Jin jina kai kawai ya khaleel yayi, yacigaba da magana yayinda yake duba hotunan mutanen, da French yace, "amma taheer wannan guy d'in kamar Wanda muka ta6a kaima hari a Nouakchott ta k'asar Mauritania, shekaru kusan 5 kenan, amma yagudu". "Yes sir!, nima nayi wannan tunanin wlhy, Wanda muka kama makamai a hannun budurwarsa ko?". "kwarai kuwa, amma miya kawoshi Nigeria? ". " yakamata a bincika kam sir". Ya khaleel ya furzar da huci mai zafi daga bakinsa tareda shafa gemunsa, yamaida yatsansa kan bakinsa yanad'an bugawa a hankali, idonsa nakan laptop d'in yana dannawa da hannunsa d'aya, saida yagama kallonsu tsaf sannan ya kalli taheer, dashima idonsa ke kan laptop d'in, "ummm amma ita wannanfa?". 'Yay maganar yana nuna masa pic d'in wata dattijuwa dake cikin hotunan su Alhaji bishasha'. "Itama acikinsu take, saidai abinda Na lura dashi, kamar tana zamane dole dasu, bada son rantaba, tama samu harbi a k'afarta, Dr Abraham yayi treatment d'in, yanzu tana nan a clinic d'in setetion kwance, nake ganin zamu samu wasu bayanai agurinta". "OK, yayi k'yau, amma mi IG yace gameda kamasu?". "Yanuna jin dad'insa sosai, shinema yace namaido aikin wajenka dukda kana hutu, tunda dama kaika fara". Nanma ya jinjina kansa. Cigaba yayi da danne-danne, shikuma taheer yazuba lemo a cup yana sha, shima ya khaleel d'in yanayi yanashan tea d'insa. Zuwa can yad'ago ido yana kallon taheer, "miye labari gameda mutane 37 damuka tace a contact d'in barau modibbo?". "Suma Alhmdllh aikin yana tafiya, taheer yad'akko wani files yamik'a masa, ga wannan, bayanaine akan mutane 9 damuka tantance acikinsu, matar data kirashi a waccan ranarma munfara aiki akanta, Dan munkama wata mata dake aiki a k'ark'ashinta zatakai yara 6 k'asar Dubai jiya, nakira phone naka danna sanar maka amma bansamekaba, naturo sak'o kuma baka bada amsaba". "ban kulaba, Dan jiya ina kwance babu lfy, amma yakamatafa kurufe asusun bankinta, miyasa Solomon baiyi wannan aikinba? Dolenefa kadinga zaburar dasu kamar yanda nakeyi, dukda inagama dole nayanke yawan hutunnan nadawo office, naga aiki yana neman cakud'ewa". "Wlhy yama cakud'e, Kasan kuma yanda suke shakkarka suna aiki da kwazo idan kana nan, basayi idan baka nan, saikaga suna janjani akan aiki, kaga ko sanda aka kashe david kana Mexico ne, sunyi amfani da wannan damar suka kasheshi, kwafa ya khaleel yayi, amma baice komaiba, yacigaba da duba files d'in, saida yagama tas sannan yamik'ama taheer. Taheer yace, "yakamata kasaka hannu sir". "OK, amma ya akayi kuka samu bayanai dangane da fita da yara zuwa k'asar Dubai?". Da sauri taheer yace, "sorry sir, kaga ina neman mantawa, munsami bayanai tawani email ne, amma an6oye kai wajen bayyana sak'on, ma'ana mai email d'in ya 6oyemana kansa, sannan kaga jerin sunayen mutum 5 daya bamu, yakumace muyi bincike akansu, mai email d'in yabamu tabbacin shiba komai baneba, yaza6i bamu bayanaine saboda cutar dashi da mutanen sukayi yunk'urin yi, bazai yuwu ya bayyana kansaba saboda tsaro". Ya khaleel yajawo laptop d'in, cikin d'aurewar kai yake binciken email d'in, amma taheer kana ganin bawanine yake mana k'ofar ragoba kuwa?, kasanfa bancika son bayanan sirrin nanba, inhar ba irinku Dana yarda bazasu cutar daniba". "Hakane sir, amma wlhy nayi k'yak'kyawan nazari nidasu Joseph, saimuke ganin kamar gaskiya mai email d'in yake fad'a, musamman idan mukayi la'akari dakama Ruth". "To shikenan, zanshiga tunanin mai email d'in nima, saiku fara bincike akan mutane 5 d'innan daya turo mana numbers nasu, kasanarma fharuk sukula sosai, idankuma sukaimin wasa nadawo office tabbas zand'auki mataki akan kowa". " tom shikenan, ALLAH yasa mudace". "Ameen, yamaganar yaran da aka kama agidannan?". " yes sir! Suma muna bincike akansu, amma bamu matsantaba sosai, muna jira saika dawo kan aiiki, mun dai kaisu d'akin duhu". "Ok, kubarsu saina dawo d'in". Sund'an k'ara tattunawa akan aikin. Daga baya kuma suka koma tsokanar juna irinna abokai, abinma dariya yabama Aysha, wato idan ana fagen aiki babu wasa tsakaninsu, saidai girmamawa juna, idan kuma aka dawo fannin abota saikaga an canja, afirar tasune ya khaleel yake sanarmasa bashida lfy, nandai taheer ya jajanta masa, harya juyo yana tsokanar Aysha, wai kodai ciwon angon NATA Na wayaune dan a k'ara masa Hutu yasha amarcine?, batadaice komaiba sai murmushi Dan kunyar taheer d'in takeji. Yace, "su shirya weekend d'innan insha ALLAH zasu kawo musu ziyara suda matansu, dama sund'an basu iskane susha amarci. Ya khaleel yace, " ALLAH yakawoku to, muna zuba idanu". ''Insha ALLAH zamuzo". Taheer yad'an dad'e agidan kafin yamusu sallama yatafi. Cikin matuk'ar farinciki Aysha ta turama Anty meerah sak'o, wai sunci nasara, aikinsu yayi, harma su ya khaleel sun kama k'awar Anty glory Ruth. Meerah tayi farinciki sosai, Dan kullum burinta dama bai wuce ta rusa k'ungiyar su glory ba.. Meerah ta tabbatar ma Aysha tashirya gobe idan ALLAH ya kaimu zasuzo musu sallam, Dan jibi jirginsu zai d'aga zuwa Canada, dama Dady da maheer tun washe garin d'aurin aure suka koma, maheer zai fara exam ne a school, dady kuma saboda aiki. Ya naufal kam akwai aikin daya rik'esa anan Nigeria, shiyyasa su meerah suka tsaya jiransa. Cikin d'oki Aysha tace, "ALLAH ya kaimu lfy Anty meerah na". Meerah tayi dariya, "oh ke lil sholyna, har yau dai ba'a canjaba, k'uruciya fal ciki, ya khaleel na hak'uri dai". "Kai Anty meerah, saikace wata jinjira?". 'Tayi maganar a shagwa6e'. Cikin dariya meerah tace, "sai anjima, kigaida boss". Bata jira cewar Aysha bata ta yanke wayar. 'Yar dariya Aysha tayi itama kawai, tana fad'in " I love you Anty meerah na, kina sakani farinciki wlhy, ked'in tadabance atarihina😍. ___________________________ Alhmdllh ya khaleel sauk'i yasamu, harma yad'an fita iya nan tsakar gidansu yanashan iska, Aysha data kammala gyara ko ina na gidan nasu, tasaka turaren wuta ko ina yad'auki k'amshi, komai tanayinsa cikin nishad'ine, saboda d'okin zuwansu meerah gidan, ga mama zata dawo yau. d'akinta tashige domin yin wanka tacire kayanta, tad'aura guntun towel, tana tsaye gaban madubi tana tura sak'o ta email d'insu na sirri gasu ya khaleel, sai zabga murmushi takeyi. d'agowarnan dazatayi suka had'a ido da ya khaleel ta madubi, yana tsaye a bayanta. Kawai saita fasa k'ara saboda tsoratar datayi. Cikin sauri ya tallafota tafad'o jikinsa, wani mugun bugu zuciyar Aysha keyi, babu abinda take ambata sai innalillahi wa'inna'ilairraji'un, shikenan k'aryarta ta k'are, inhar ya khaleel yaga email d'innan nasune, cikin dabara tasaki wayar ak'asa, tasaka k'afarta ta shureta kamar bata ganiba, wayar tashige k'ark'ashin gadonta. Shikam tana rungume ajikinsa, idonsa kan bak'inta daketa motsi babu magana. Batareda sanin miyake k'ullawaba taji bakinsa kawai cikin na🤫..........✍ Nace, "Hummmm🤭. *_jiya wutarmuce tasamu matsala, har dare banyi posting ba, gashi angyara takuma gocewa, kumana addu'a agyara yau, inbahakaba typing zai gagareni kam_*.😄 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋😍😍😍😍😍😍😍😍❤❤❤❤❤ [9/20, 3:26 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 1⃣9⃣ Tsorone yakuma kama Aysha, dan ganin ya khaleel na Neman kauce hanya, tarik'e hannunsa dake yawo ajikinta, tsayawa yayi cak yadaina kissing d'inta, jin yadaina tafara k'ok'arin zame jikinta daga nasa. Bai hanataba yabata dama tatashi zaune. Kwanciyarsa ya gyara zuwa rigingine, yay filo da hannunsa yana kallonta ta k'asan ido, sotake tatafi wanka amma tanajin tsoron tafiya yad'auki wayar, ita duk zatonta yagantane. Hijjab tad'auka tasaka, yad'an ta6e baki yana tashi daga kwancen dayake. Gyara zamansa yayi sosai yana kallonta, itakam kanta Na k'asa takasa kallonsa. "Ukkhhmm! Yay gyaran murya". d'ago idanu Aysha tayi tana kallonsa, yad'age girarsa d'aya yana wani yatsina fuska. Dariya yabama Aysha, Dan haka ta murmusa, shikuma yata6e baki yana jingina da gadon sosai. "zoki zauna muyi mugana". 'Yay maganar batareda ya kalletaba'. Bak'aramin fad'uwa gaban Aysha yayiba, tunaninta akan wayarne, haka tatafi jiki a sanyaye tazauna bakin gadon nesa dashi. Jawota yayi tadawo saman gadon sosai, yad'ora kanta bisa cinyarsa, "miyasa kika kasa sakin jikine dani har yanzun?, nifa sonake mu shinfid'a k'yak'yk'yawar rayuwar aure, A'eesha aure hak'urine kawai acikinsa, bakomaine ake nema asamuba, duk abinda akace masa ibadane to tabbas yanada wahala, banmiki alk'awarin farinciki 100% ba a aurenmu, Dan zomu zauna zomu sa6a, ballantana mutum Irina da ayyuka sukama yawa, inafata zakiyi hak'uri dani lokacin sa6ani da lokacin farinciki, insha ALLAH zan kula dake iya iyawata, nima nabaki dukkan amanata, kirik'emin, Dan kece sirrina ayanzun". Dad'i, farinciki, murna, duksun taru sun dabaibaye zuciyar Aysha, tarasa yanda zata musalta mitakeji, saidai Abu d'ayane ke ta6a zuciyar Aysha tawani 6angaren, har yanzu ya khaleel bai furata kalmar yana sontaba, shin kodai baya sontane? Itace keta shirmentane?". Ganin tayi shiru yad'an girgiza k'afarsa, da sauri ta kalleshi, saikuma ta kauda kanta ganin yakafeta da idanu. Lallausan hannunsa yasaka yamaido fuskarta, saita lumshe ido. "Bud'e ido ki kallenimana, nifa sonake kisaki jiki dani, banason wannan nuk'u-nuk'u d'in, saikace wata matar k'auye, banson shariya, kice wani Abu". Hannu tadaka tarufe fuskarta, "ALLAH inajin kunya". bakinsa ya ta6e, yace, "kunya kuma aii tak'are A'eesha, tunda kinbiya kazar dakikaci bashi, kinzama Ibraheem, Ibraheem yazama A'eesha", yay maganar yana janye hannunta, tareda sunkuyowa ya sumbaci goshinta. Dad'i Yakama Aysha, amma tanason ya khaleel yafurata mata kalmarso da bakinsa, dukda tagani a aikace bata gamsuba gaskiya, amma abinda talura dashi jin Kansa bazai bari yace yana sontaba, zatabishi su tafi ahaka itama. K'ok'arin cire hijjab d'inta yafarayi, ta kallesa da dasauri zatayi magana, amma saitaga ya had'e fuska, dole tahak'ura yacire, hannunsa yad'ora saman cikinta, d'ayan kuma yana shafa kwantaccen gashin goshinta, muryarsa a tausashe yace, ''ina binki bashin maganar danayi, Duke kin wani maidani aku, kekuma kinyi tsit, nifa ustazancinki mamaki yake bani". Ganin kamar da damuwa yake magana saita daure tace, "insha ALLAH zaka sameni mai biyayya agareka, saidai kayi hak'uri da dukkan kurakuraina idan nayi, koda kuskure, ko akan Sani saboda ajizancin Dan adam". "Hummm". kawai yace, yasauka daga gadon yafita. Da kallo tabisa haryakai k'ofa yajuyo yana kallonta, kiyi wankan zanje cikin gida Na gaisa dasu momy.. Kanta ta jinjina masa, ya ida ficewa. Da Sauri taduk'a k'asan gadonta tad'auki wayar harta d'an tsage, kashewa tayi tatura can k'asan kayanta acikin wadrobe, sannan tashiga wanka. _____________________________ Saida yafara shiga 6angaren baffah suka gaisa, sund'an dad'e suna tattaunawa, baffah yace, "yaushe matarka zata koma wajen aikintane? Banason asamu matsala, kagadai kusan watanni 6 kenan tana k'ok'ari, watanni 6 kawai yarage mata ta mammala NYSC d'inta, baikamata aimata wasa da damartaba". "Insha ALLAH baffah zata koma ranar Monday insha ALLAH, nima ranar zan koma aiiki". " to shikenan ALLAH ya kaimu lfy". "Ameen". ****** Da sallama yashiga falon Momy, tana zaune ta rabga tagumi, itakad'ai tasan mike damunta, mufeedah Na wajen aiki, hakama hasnah da husnah sunje makaranta, Anty shukurah kam tana gidan surukanta, harya zauna kusada ita batasan ya shigoba, kansa ya d'ora saman kafad'arta, sai lokacin tayi firgigit tadawo hayyinta. Ganin khaleel yasakata sakin ajiyar zuciya, " Ibraheem yaushe kashigo?", 'tayi maganar zuciyarta cikeda d'aci'. d'agowa yayi yana kallonta, yamaida dukkan hankalinsa kanta, hannunsa rik'eda nata, "haba momyna miye damuwarkine? Kwana biyunnan bana ganin walwala taredake, shin miyyake faruwane?". d'an murmushi tayi maikamada yafi kuka ciwo, tashafa fuskarsa tana had'iye yawu maikamada tafasashshem ruwa a mak'oshi". Ganin tak'i cewa komai saiyaji babu dad'i, yazame ya kwantar da kansa bisa cinyarta, itadai Momy kallonsa kawai takeyi, hannayensa ya hard'e bisa k'irjinsa, yakafe Momy da kallo, gabad'aya hankalinsa ya tattara kanta, cikin muryar kwantar da hankali yace, " momyna damuwarki damuwar ibraheem khaleel ce, please & please my dear maah-maah, kifad'amin damuwarki, insha ALLAH zanmiki maganinta, inhar batafi k'arfinaba". Wata ajiyar zuciya Momy tasaki, akankali takai hannu tana shafa sumar kansa, "Ibraheem konafad'a maka damuwata bazaka iya maganintaba". " Momy miyasa zaki yanke hukuncin bazan iyaba da Sauri haka?, inason farincikinki Mamana, banta6a k'aunar wani mahalukiba fiyeda son danake miki.". Sosai Momy taji dad'in kalamansa, Dan haka tad'an sake fuska kad'an, ''Ibraheem inason maganar aurenka tatashi kaida Aleeya". Bak'aramin fad'uwa gaban ya khaleel yayiba, amma saiya dake, cikin taushin mirya yace, "to Momy, amma baiyi kusaba? koda yake yakikeson ayi?". Dad'i Yakama Momy, takuma fad'ad'a fuskarta danganin alamomin nasara, ''kaima baffanku magana da kanka". " OK karki damu Momy, zanmasa, ammafa ina Neman wata alfarma". ''Wace alfarma kenan?". Muyi hak'uri nanda kamar wata shidda, sai ayi maganar, kinga inhar mukaima baffah maganar auren yanzun dawuya ya amince, zaice bandad'e dayin aureba, koya kika gani?". "Na fahimceka yarona, amma kasamu lokaci kuyi maganar dashi, Aleeya zata shigo Nigeria next week, akwai wani aiki dazai kawota, kuma nan gidan zata sauka". "Hummmm nifa Momy mamaki kike bani, wai ina kika sansu haka?". " labarin mai tsawone, amma wataran zan baka". Jinjina mata kai yayi yana lumshe idanu, daganan tasaki jiki sukahau hira. Harsu hasnah suka dawo daga school, kallo suka rink'abin yayan Nasu dashi, aransu, suna fad'in yaukuma ta6arar ta tashi?. Basuda damar zaman falon, Dan haka suna gaidasu suka shige d'akinsu. ____________________________ Aysha tagama komai tsaf, dukda bata girki har yanzu amma yaudai tad'anyi Abu mai sauk'i, Wanda mutanen gidan bazasuga tayi ba daidaiba, tunda sun bartane tayi hutun amarci. Tana zaune afalo ya khaleel yadawo, sannu tamasa ya amsa babu yabo babu fallasa, maganar dasukayi da momyce take cizon zuciyarsa. Batareda ya kalli Ayshanba yace, "zanyi wanka". Tasan miyake nufi, danhaka ta amsa da to, tamik'e tabi bayansa. Kanta ak'asa tashige bathroom d'in, dan harya fara cire kayansa. Abakin gado ta iskeshi zaune shiru, da'alama yana duniyar tunanine. Tace, " nahad'a ruwan". Kansa ya jinjina mata sannan yamik'e yashige abinsa. Aysha tabisa da kallo zuciyarta Na k'una, wai yazatayi ta canja ya khaleel ne?, idonta cikeda hawaye tabar d'akin. Babu dad'ewa dafitowarta tajiyo ihun ifteehal, da gudu itama tafita suka rungume juna, kowa yana murnar ganin d'an uwansa. Yana cikin wanka yajiyo ihunsu, Kansa kawai ya girgiza yamaida idonsa ya lumshe, yanamai jin dad'in yanda ruwan d'umin ke ratsa kowacce ga6a ta jikinsa. Su Aysha kam sunacan sun kaure da murnar ganin junansu, Raudat Na hannunta tana cillata sama tana cafewa, itakam sai wangale baki takeyi. Yadad'e a bayin kwance cikin ruwan, zuciyarsa amatuk'ar cinkushe, yarasa wane tunani zaiyi dankamo zaren lamuran Momy, badan yagaji da tunaninba ya d'auraye jikinsa yafito, shiri yayi cikin k'ananun kaya, bak'in wando da farar riga mai dogon hannu, yad'an fesa turare kad'an, yad'auki wayoyinsa da key d'in mota yafito. Afalo yatsaya suka gaisa dasu Anty meerah, harya d'auki Raudat yamata wasa (nakula ya khaleel nason yara, tun akansu 'yan uku), mik'ama Aysha Raudat yayi, yana fad'in ''bara nad'an fita, zuwa yamma zan dawo". Suduka suka had'a baki wajen yimasa adawo lafiya. Kansa ya jinjina musu yajuya zai fita, da Sauri meerah ta zunguri Aysha, ta nuna mata tatashi tamasa rakiya, saida ta zum6ura baki sannan ta ajiye Raudat tatashi tabi bayansa. Shi harma yafita, saida ta had'a da sauri sannan tacimmasa, kasancewar ahankali yake tafiya, tun maganar dasukayi da Momy d'azun ta haddasama dukkan jikinsa sanyi, jin kamar ana binsa abaya yasakashi juyowa. Tsayawa yayi yana kallon yanda take tafiya cikin sassarfa harta k'araso inda yake. "Lafiya dai ko?". 'Yay maganar cikin d'age gira sama'. Kad'an ta turo bakinta tace, " rakkiyafa namaka". "Uyimmm". 'Yafad'a yana ta6e baki da lumshe idanu'. Haushine Yakama Aysha, dan ganin kamar da rainin wayo yay abin, sosai ta tunziro baki yanzu, shikuma ya hard'e hannayensa ak'irji yana kallonta. Juyawa tayi zatabar wajen yarik'o hannunta, batareda yayi maganaba yajata har zuwa inda motarsa ke ajiye kusadata ya sultan, bud'ewa yayi da key d'in yashiga, har sannan yana rik'eda hannun Aysha, itadai kallon ikon ALLAH takeyi, saida ya zauna sosai sannan yajawota saman cinyarsa, idanu tazaro waje, " kai ya khaleel idan wani yagammufa?". "shiyaso". 'Yafad'a yana d'aga kafad'a sama da ta6e baki'. Yunk'urawa Aysha yayi zata tashi yay saurin maidota jikinsa, " jimana madam!, haka akema miji rakkiya a garinku?". Yanda yay maganar saiya bama Aysha dariya, tasaki dariya har hakwaranta suka bayyana, shidai kallonta kawai yakeyi, amma bak'aramin tafiya dashi dariyar tayiba, ya tattara hankalinsa wajen kallonta yaji tace, "wai ya khaleel anya kuwa kana dariya?". Asama kawai yaji tambayar tata, wadda baita6a zatoba, saikawai yasamu Kansa dasakin k'aramar dariya, Dan wlhy tambayar tata dariya tabashi, ya rungumeta sosai tareda manna mata kiss agoshita, sannan yad'agota yana kallon fuskarta, haryanzu fuskarsa d'aukeda ragowar dariyar, " miyasa kikamin wannan tambayar?". Cikin shagwa6a tace, "yoni banta6a ganin dariyarkaba, murmushima zan iya irga adadin Wanda naga kayi". "umyimm, kinason naringa dariya kenan?". Yakai hannu zai d'alli bakinta, da sauri tasaka hannu tatare dantasan muguntar dayake shirinyi mata. Nanma guntun murmushi yayi. Itakuma tace, "inason naga kana dariya mana, Dan wlhy tana maka k'yau sosau". Yad'an ta6e baki yana sosa girarsa da d'anyatsa d'aya, idonsa kyam akanta, " hummm nikuma kinga yawan dariya baya birgeni, hasalima ni bancika son mutum mai yawan dariya koyausheba, saikace wani mahaukaci". Aysha ta jinjina kanta sannan tayunk'ura tatashi zaune sosai tace, "banga laifinkaba ya khaleel, domin kaid'in _Sadaukine_". Tana gama fad'a tafice da sauri. Kafin yayi yunk'urin rik'ota tabar jikin motar tana masa bey bey. Da kallo yabita, yana wani sassanyan murmushi, jiyayi dukwata damuwar daya kwaso daga 6angaren Momy ta kwaranye, Aysha ta gogeta da shirmenta, ahankali ya maimaita sunan data kirashi dashi *_" Sadauki!"_*, yalumshe idanunsa ahankali, tareda kwantar da bayansa ajikin kujerar, kasala dajin k'yuyar fitar duksun saukar masa, (dama soyake yad'anje yasha iska, kozai samu nauyin zuciyarsa yaragu), saiga matarsama ta wanke 6acin ran nasa cikin sauk'i, saida yagaji dasak'awa da kwancewa sannan yatada motar yafice daga gidan zuciyarsa fes. Yau yini guda su Aysha suka kwashe suna kwasar hira, sallace kawai ke tashinsu, abincima daga cikin gida aka kawo musu. Sai bayan sallar azhur Anty Mamie tarako mom 6angarensu Aysha, Dan ita tunda sukazo tanacan cikingida wajen Anty Mamie. Aysha tarungume mom tana murnar ganinta, itama mom sosai yaji dad'in ganin Aysha, daka ganta kad'an tasamu kwanciyar hankali agidan mijinta, sund'an ta6a hira sannan suka rungud'a suduka zuwa cikin gidan, saboda dawowar su mama daga Kano, Aysha ma binsu tayi. Ta rungume mama harda kuka, "oh ni Fatima wanne shashancine kuma haka?, Ku ganemin Dan ALLAH, dariya akayi, mama tacire Aysha daga cinyarta tana fad'in " ni d'agani kinji, badaniba wannan sakarcin". Haka Aysha taita lik'ema mama tana korarta ita kuma. Har akayi magrib tanacan cikin gida d'akinsu maleeka, sunata hira cikin nishad'i. Bayan sallar magrib ya khaleel yadawo gidan, saidai k'ofa arufe, yaji mamakin rife k'ofar,, inakuma taje? Yay tambayar yana waige-waige. Ya mujahedeen da shigowarsa kenan daga cikin gidan yak'araso suka gaisa, ya tambayi ya k'arin k'arfin jikinsa?. "Alhmdllh mujahedeen, daga cikin gida kake?". "Eh, dagacan nake". " OK kokaga A'eesha a can?". "Bandai gantaba gaskiya, amma zata iya yuwuwa tanacan d'in, Dan mama tadawo, itama naje gaidawa". " barato naje mu gaisa, saina duba daga nan". "To shikenan saika fito" Ledojin hannunsa ya ajiye bisa kujeru biyu dake kan barandar 6angaren Nasu, sannan yanufi cikin gidan. Afalo ya iske su 'yan uku da yaran Anty Amatullah, saisu ummunoor, suduka dagudu sukazo suka rungumesa, suna murnar ganinsa, shima yayi kewarsu, haka yayta d'agasu d'ai-d'ai. Duk suka bishi har d'akin mama, samun Kansa yayi da jin matsananciyar kunyar mama, ita kanta talura da hakan, (dariya abin yaso bata), sun gaisa cikin mutunci, kamar yanda suka saba, saidai d'an sauyi daga ya khaleel d'in, Dan yau yakasa sakin jiki suyi hira kamar da, kusan mintuna 15 sannan yamik'e, akunyace yace, "Ashe batazo nanaba?". Mama tace, " wai Aysha?". "Eh mama". A kana nufin bata koma canba tun d'azun? inko hakane tana d'akin mamien Ku kokuma wajensu Tasleem, kajimin ja'irar yarinya kai". " babu damuwa mama, bara nadubata a can, saida safe, ALLAH ya huta gajiya". "Amin baba saida safe to". Saida yashiga d'akin gwaggo bintu itama suka gaisa, sannan yashiga d'akin Anty Mamie, bata nan saisu mom dake shirin tafiya gida, ya gaida mom Dan baima San da ita akazoba. Saida suka fito rakkiya sannan yaga Aysha tafito daga d'akinsu Tasleem suna dariya. Da ya khaleel tafara cin karo, mukut ta had'iye dariyarta saboda Harar dayeke jifanta dashi. Hakadai suka rungud'a wajen mota aka rakasu mom dazasu tafi, Muslim ne zai kaisu gida. Ya khaleel yamatsa jikin motar yanama mom godiya, yace, ''mom saina shigo gobe in ALLAH ya kaimu sallama ko". "To khaleel saikazo". Bayan tafiyarsu yakad'a kan Aysha suka koma Nasu 6angaren, su maleeka namata dariya afakaice😄🤭........✍ 💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤😕😍😍😍 [9/21, 3:49 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣0⃣ Aysha tabud'e k'ofar shikuma yakwaso ledojin daya ajiye suka shiga, afalo suka yada zango, yana ajiye ledojin yajuya zuwa masallaci, Aysha kuma tatafi d'akinta itama tayi sallar. Bai shigoba har Aysha tadawo falon, tazauna akan doguwar kujera tana danne-danne awaya dan babu wuta and'auke. Kusan mintuna 10 da zamanta aka kunna Gen...., haske ya gauraye ko ina, saiga ya khaleel shima yashigo, sannu da zuwa tamasa. Ya amsa babu yabo babu fallasa, d'akinsa yashiga, kusan mintuna 15 yafito d'aukeda laptop ahannu, yacire kayansa, yacanja zuwa 3quarter da best. Ya ajiye kayan hannunsa sannan ya zauna, Aysha tamik'e tad'akko masa ruwa. Zubawa tayi tabasa yasha, yamik'a mata kofin yana fad'in thanks. Jinjina kai kawai tayi batace komaiba. Ya kalli ledojin daya ajiye suna nan inda yabarsu, d'ago manyan idanunsa yayi yazubasu kan Aysha, fuskarsa ahad'e yace, "su wad'annan ledojin misukeyi anan?". "um..um....kayi hak'uri Dan ALLAH, Na mantane wlhy". Baice komaiba yaja k'aramin table Na glass yad'ora k'afafunsa akai, sannan yad'ora laptop d'insa daya d'akko bisa cinyarsa yasaka siririn farin glass. Laptop d'in ya kunna, yashiga aikinsa. Aysha tana kichin tana bud'e ledojin, kayan fruits ne sai gasassun kaji guda biyu da robar ice-cream guda biyu, saikuma fura guda uku. Komai d'aya tad'auka, tazuba sauran a fright tafito, tana ayyanawa azuciyarta yau komai zai faru bazataci kazar nanba, haka kawai yadawo yace tabiyashi kuma, har yanzun bata manta da wahalar data shaba adaren ranar, koda yake shima aiya gane kuransa tunda harya fita jigatama, kusan kwanaki 2 yana shan ciwo harda k'arin ruwa.. Sosai hankalinsa nakan aikin dayakeyi, ta ajiye tiren kusadashi, ahankali tace, "bismillah". Batareda ya kalletaba yace, "zauna anan ki d'ora bisa cinyarki, yay maganar yana nuna mata gefensa, dayake akan doguwar kujera yake zaune. Bayanda zatayi dole ta zauna kamar yanda yace, yanzuma bai kalletaba yace, ''saiki ciyar dani, Aramawa kura aniyarta". Idanu Aysha tazaro waje, sannan tace, ''wayyo ya khaleel, nifa....nifa wlhy".... Juyowa yayi yana kallonta, saita kasa cigaba da maganar, yajanye idonsa yamaida kan laptop d'in, "ashe babu dad'i ke nake baki kici, oya maza kan aikinki, kuma banda k'atuwar lauma". "Nifa na k'oshi, tayi maganar a shagwa6e". Yata6e bakinsa, "hummm, kuma bazai hanani abinda nayi niyyaba ba, gwamma kicima kisan cikikayi kika biya". Dama abinda take gudu kenan, taci Kazan yace kuma saita biyashi kamar ranar. Jin tayi shiru yajuyo ya kalleta, dariya tabashi yanda tayi wani kwale-kwale da idanu, aransa yace, " sai tsiwa ga tsoro". Afili kuma yace, ''infa tahuce yazama sau biyu kenan, kuma babu k'oraf.......". ......aibama tabari yakai k'arshen maganarba, tad'ibo Takawo bakinsa..... "Hhm, d'uran k'arfi zakimin?". "wlhy kaifa ya khaleel d'inan........ Tayi shiru takasa k'arasawa. "Nifa ya khaleel me?, dukdai yanda kikai dani, haka zanyi dake agado, garama kibini a sannu ehe, kuma kidaina cemin wani ya khaleel, daga yau *_Sadauki!_* nakeso. Idon aysha yacika da kwallah, danjin wannan k'arfa-k'arfa, itadai addu'arta ALLAH yasa wasa yakeyi, ba irin abun shekaran jiya yake nufin mataba". Haka tacigaba dabashi naman abaki ahankali, shikuma yanata aikinsa a laptop hankali kwance, yayinda ak'asan zuciyarsa yakejin wani nishad'i da sarauta, yana lura da Aysha ko sau d'aya bataci namanba. Dariya yayi a zuciyarsa, yana tunanin dama akwai abinda zai tsoratar da Aysha haka harta iya danne kwad'ayinta? Dan yaga ko ice-cream bata kallaba, baice da ita k'alaba, har saida ya tabbatar ya k'oshi sannan yace, "Alhmdllh dainamin d'ura hakanan, karna kasa sunnah anjima". Ita bamata fahimci Inda zancensa ya dosaba, tamik'e zata maida kayan kichin yace, "dawo aii ba'a gamaba". Dawowatayi tazauna, duk tsoronsa ya gama kamata, mamakinma wad'annan abubuwan dayakeyi take ita. Kunsan Mintina 3 sannan ya ajiye laptop d'in gefe yajuyo sosai yana fuskantarta, tiren yakar6a yamaida kan cinyarsa fuskarsa k'unshe da murmushin mugunta yad'ebo naman yakai bakinta. ''ALLAH Na k'oshi ya k...... Amin Sadauki....ta canja maganar tata saboda uwar harara daya balla mata". "Kinga gwamma ma kici, Dan babu d'aga k'afa babu alfarma, Niba cazanyi kibiyaniba aii, da zuciya d'aya nabaki". d'ago idanunta tayi takallesa Dan tabbatar da gaskiyar maganarsa, ya jinjina mata kai yana lumshe idanu, dukda ba yandda tayi dashiba dai tabud'e bakinta ya bata, haka yayta bata naman saida yaga taci da yawa sannan ya k'yaleta. Ruwan data kawo ya wanke hannunsa aciki, yad'auki cup yazuba fura, ita kuma yamik'a mata ice-cream yana fad'in nasan anan kikafi kauri". Da mamakin furicinsa tace, " kamar ya?". "Kamar yanda kika Sani, yay maganar batareda ya kalletaba, saima k'ok'arin canja tasha dayakeyi a TV, yamaida NTA domin kallon labarai. Tunanin Aysha yafara canjawa akan ya khaleel, tafara Zargin anya kuwa baisan Wani abuba Dangane da ita?. Ganin kallon datake masa yad'an juyo ya kalleta sannan yamaida hankalinsa kan TV, "yayadai kike kallona?, konayi wani abun mamakine?". "A'a Aysha tafad'a tana girgiza kanta a sanyaye, daga nan babu Wanda yasake tankawa, kowa da abinda yakeyi, yanashan fura yana kallon labarai, itama tanashan ice-ceam tana kallon labaran. Harsuka gama kallon labarai babu wata hira data kuma Shiga tsakaninsu, ya khaleel ya tattare kayansa waje d'aya, azatonta zai tashine yashiga d'aki, saitaga yazame ya kwantar da Kansa saman cinyarta. Aysha tazaro idanu waje, amma takasa yin magana. Shima bai tankaba, dukda yana kallon mamakinta ta gefen ido. Canja tashar yayi yamaida wisal Hausa TV , Tafseer akeyi, hankalinsa yamaida kan tvn. Itama Aysha saita maida hankalinta akan wa'azin. Sai kusan 11:30pm aka kammala tafseer d'in, ya khaleel yamik'e yana fad'in Alhmdllh, Malam mungode, ALLAH yabiyaku. Itadai Aysha batace komaiba, yakwashi kayansa yashige d'akinsa. Itama d'an kaye-kaye tayi tashige nata d'akin. Kowannensu yay shirin barci, hankalin Aysha kwance ta kwanta, tunda tasan ta kulle d'akinta, ko ya khaleel yayi yunk'urin shigowa babu dama. Takuma tura key d'in k'ark'ashin filo, sannan ta gyara kwanciya tanamai jin dad'in yima ya khaleel wayo. Nace, "hummm, aysha kenan.🤣.lol. ______________________________ Abin duniya ya ishi momy, ko barcin kirki bata iyayi, yanzuma tana zaunene shiru, gama wayarsu kenan da hajia khaltum, take sanar mata anrufe mata account d'inta, yanzunnan sak'o yashigo mata. Momy tace, "Aminiya garin Yaya hakan tafaru kuma?". "Wlhy bansaniba aminiya, amma insha ALLAH da safe zanje na bincika, inaga bawata matsala baceba mai yawa". "To shikenan ALLAH ya kaimu, saidai ina miki albishir Ibrahim ya amince da auren Aleeya, nama sanar masa zuwanta k'asar". "Alhmdllh, kinga munsami bakin zaren, yanzu saimuyima tufk'ar hanci". "Gaskiyane aminiya". Sunyi sallama kenan Momy tajiyo kamar motsi. Da sauri tamik'e ta lek'a window d'inta, mufeedah ta hango sanye cikin dogon hijjabi, tana tafiya cikin sand'a a tsakanin motoci. Gaban Momy yafad'i, dasauri tafita zuwa tsakar gidan, lokacin data fito har mufida taje k'ofar gate tana tashin d'an gwari dake gyangyad'i yabud'e mata gate. " Dan ubanki INA zakije a darennan?". Maganar Momy tasaka mufeedah juyowa arikice, tuni jikinta yafara 6ari, wlh...wlh....wlhy momy credit zanje Na sayo, shine nazo tashin d'an gwari yasayimin....... Tsawa Momy tadaka mata, "kimin shiru 'Yar iskar yarinya, yanzunan mufeeda nizaki tonama asiri agidannan?, da mutuncina dakomai". "Momy Dan ALLAH karkice haka wlhy gaskiya nafad'a mik....." Bata k'arasaba taji saukar mari a face d'inta, da Sauri tadafe kunci Dan Marin kan yashigeta, Momy tanuna mata hanya. Suna shiga falo ta fisge hijjabin jikin mufeeda. Sallalallami Momy takamayi, Dan ganin tambad'ad'd'iyar shigar dake jikin mufeedah, tuni jikin Momy yafara rawa, tadafe k'irji tana layi zata fad'i, mufeeda Ce tayi azamar tarota suka fad'a saman kujera, tana kwala kiran Momy! Momy!!.... Ina Momy ta suma aii. Ihuntane ya farkar da Anty shukurah, tafito falon cikin yanayin barci. Idanu tazaro, tak'araso dasauri inda suke, "k mufeeda lfy? Miya faru da momyn?". "Wlhy Anty shukurah fad'uwa tayi, dankawai taga zan fita siyen credit, tazata wani gurin zanje.. Wani kallon Anty shukurah Tamata, ahakan zakije siyen credit mufeedah? Da wannan shigar mufeedah? Kekuma wannan rayuwar kika za6ama kanki?". "Wlhy Anty shukurah gaskiya nafad'a miki, kiyarda dani"... "Banida wannan lokacin, kinga tashi ki tado su husnah mu kamata akaita d'aki, mu biyu bazamu iyaba''. "Anty shukurah ko ya khaleel za'a kirane?". "A'a bazamu tadoshiba yana cikin iyalinsa, mudai kaita d'akinta". Mufeedah tasaka hijjab d'inta ta tado su hasnah. Da k'yar suka d'auki Momy suka kai d'akinta, Anty shukurah ta shafa mata ruwa takawo numfashi, saidai da k'yar numfashin ke fita, sai huttai takeyi, fanka suka kunne, aka kashe ac d'in, duk suka zagayeta suna mata addu'a. Anty shukurah dai Tahana atado ya khaleel dukda Kiran sunansa da Momy keyi ahankali. __________________________ Cikin barci Aysha taji ana shafata, abirkice tafarka, tazabura zata tashi ya maidata, cikin kunnenta yace, "k nutsu mana nine". Jikinta Na rawa tace, "amma ya akayi kashigo bayan Na kulle k'ofar?". Murmushi yayi, yakuma rungumeta da k'yau, cikin kunnenta yace, " haba 'yammata, zakici kazane a banza baki biyaba?". "Aii wlhy banciba, kaine kasakani dole naci aii, kuma ALLAH shine shaidata, cikin kuka tayi maganar". Yanda take magana tana kuka saita bashi dariya, cikin salonsa na jarumta yadara yana mata abinda ke k'ara firgitata. Tarik'e hannunsa tana fad'in, " naji kabari da safe zan biyaka kazarka danaci". "Tab kinma rainani kenan, banason wata kaza, sunnah zanyi yarinya". Yink'urin tashi tayi yamaidata da sauri yakuma matseta. 🚶🏻‍♀Sum-sum nafito dannagafa ya khaleel da gaske yakeyi, yauma kazarsa Aysha zata biyashi.😆.lol. *_washe gari_* Daga masallaci ya khaleel yawuce cikin gidan, Dan tunda asuba Anty shukurah takirasa tasanar dashi momy babu lafiya, idan yayi sallah yazo suje asibiti. Ana idar da sallar kuwa suka iso shida baffah da sauran samarin gidan. Ba'awani 6ata lokaciba aka d'auki momy zuwa asibiti. Suna Isa aka kar6eta da gaggawa zuwa Emergency, duk suna k'ofar d'akin da aka kwantar da ita, kowa kagani hankalinsa ba'a kwanceba, mazan kad'aine sukazo, koda Anty shukurah ba'azo asibitinba. ************* Da k'yar Aysha tatashi tai sallah, tun dare ya khaleel ya taimaka mata ta gasa jikinta da kansa, Dan wlhy yauma tasha bak'ar wahala, azuciyarta tana mamakin masucewa aure da dad'i, ina wani dad'i anan ana azabtar damutum😢😜. Tana idar da sallah takulle d'akinta takoma ta kwanta, batawani dad'eba barci ya d'auketa, Dan barcin bai ishetaba. Sai around 9am tafarka, cikin hanzari ta dirgo daga gadon saboda ganin time. Agurguje tashiga toilet tayi wanka, bata tsaya wata kwalliyaba, dama can Aysha kwalliyar tsiyarnan badamunta tayiba, doguwar riga 'Yar kanti roba-roba orange tasaka, tamata k'yau sosau, Dan duk wani Shep nata saida rigar ta fiddo, gashi kuma ta fidda ainahin colour d'inta, tasaka hula black sannan tafito falon. Amamakinta babu kowa, d'akin ya khaleel tanufa, azatonta bai tashiba shima, saitaga wayam, tamatsa jikin toilet shiru, ''kodai yafitane inata barci?, maiybi kam yafita, ko yaje cikin gida gaidasu baffah". Hakan Aysha ta ayyana aranta tacigaba da ikin gyaran gidan. Tsaf ta gyara ko ina kamar yanda ta saba, saiga maleeka takawo musu breakfast, alokacinne Aysha taji momy ce babu lafiya, tanuna jimaminta agaban maleekah, gudun karta zargi wani abu. Amma azuciya catake ALLAH yak'ara ma momy zafin dayafi wannanma🤭. Maleekah na tafiya tazauna tayi break d'inta hankali kwance, kamarma babu wani abinda ke faruwa agidan. Ho sholyn sadaukinta, kina aljannah ina binki da addu'ar fatan alkairi nida fans🤣👍🏻. Har wajen 12 su baffah duk suna asibiti, amma jikin momy da sauk'i, barcima takeyi an saka mata k'arin ruwa. Baffah yace, "duk suje gida su karya, idan sukaje saisu Shukurah su taho shima yaje gida ya shirya". Suduka suka amsa da to. Ya khaleel yace, " baffah kabisu kuje, idan su Anty shukurah sukazo nisana tafi". "A'a mu'azzam kuje kawai, karka damu". Badan yasoba ya amsa dato. Aysha na kwance afalo saman doguwar kujera, hankalinta a kwance take buga game a waya, k'arar bud'e k'ofane yasakata saurin kashewa ta gyara fuskarta takoma kalar damuwa, sannu dazuwa tamasa, murya a sanyaye tace, ''yajikin momyn? Nida harzamu taho aii". Huci ya furzar yana sauke numfashi, "da sauk'i tana barcine". " amma to wakuka baro a wajenta?". "Baffah nacan, zanyi wankane saina koma, gasu Anty shukurah can zasuje su kar6esa shima yazo ya karya". " ALLAH yabata lafiya to". "Ameen, had'amin ruwan wanka". Dad'an d'umi tahad'a masa ruwan, tana niyyar fitowa yashigo toilet d'in, harda saka key a k'ofar. Aysha ta marairaice fuska tana rok'onsa akan yabud'e mata. Kauda kansa yayi, fuskarnan babu walwala yace, "wanka zakimin". "eyeee! Tafad'a da zaro ido waje😨". Baice da ita komaiba, yad'auki shawa🚿 yakunna, kafin Aysha tayi yunk'urin guduwa yafara zuba mata ruwan ajiki. Tsalle-tsalle tafarayi dan gujema ruwan, wayyo ya khaleel, please kabari, ALLAH nayi wankafa. Uffan baice da itaba, saida yaga tayi sharkaf da ruwan yanda dole tasake wanka sannan yak'yaleta. Babu yanda ta iya, haka tabiye masa suka sake wanka, awajen shafa maima haka ta shafa masa dole, Dan yayi kicin-kicin da fuska babu damar turjewa. Tsaf suka fito falo, tahad'a masa abinci, baiwanima ci sosaiba yamik'e, hankalinsa ta lura yana asibitin gaba d'aya. Duk 'yan gidan suka shirya suka tafi asibiti, harsu Aysha, masu aiki kawai aka bari..............✍ *_Nagafa kamar kuna neman rikicewa, kutuna ba hajia babba takira barau modibbo ba aranar, hajia babba takira hajia khaltum ne tasanar mata taji ya khaleel zaije kama barau modibbo, itakuma hajia khaltum takira barau modibbo bata bai d'agaba, shine ta tura masa message. Wanda bai ganeba yakoma page 40 k'arshen part 1 yaduba kuma._* Ngd sosai da k'aunar dakuke nunama buk d'inan, Nina wlhy ina k'aunarku irin Trillions d'innan, ga diamond k'yauta💎💎💎💎💎💎💎💎💎😂👍🏻👍🏻 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋😍😍😍😍😍😍 [9/22, 3:10 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣1⃣ Wajajen 1 Momy tafarka, duk suka shiga suka dubata, kanta kawai take iya d'aga musu amma babu magana, ya khaleel dakansa yabata abinci abaki, Aysha Na mamakin irinson da ya khaleel kema mahaifiyarsa. Baffah yace, duk sutashi su koma gida, itamad'in an sallamesu. Kaya suka shiga harhad'awa, sai gida. Tunda suka dawo ya khaleel Na 6angaren Momy, yana zaune kusada ita yanzuma a bedroom d'inta, itakuma tana kwance, tarik'o hannunsa tana magana ahankali, "Ibraheem inaso aiima mufeedah aure, kazaunar da ita tafad'ama Wanda takeso kaimasa magana yafito, saika sanarma baffanku". " amma Momy miya faru haka? Lokaci d'aya ace ta fidda miji?". "Ninasan minagani Ibraheem, mufeedah Neman zubar mana da mutunci takeyi agidannan, gaban kishiyoyi da 'yan uba, mufeedah sotake amin dariya da eho agidannan", nan Momy takwashe duk abinda yafaru jiya tasanar masa. Sosai ransa ya6aci, amma Momy tace yay shiru Dan ALLAH, fitowar maganar tamkar tonon asirinsune, kawai yasaka mufeedah ta fidda mijin aure, su aurar da ita kawai ahuta. " shikenan Momy zan mata magana, Dan ALLAH kema kicire komai aranki, kingafa jiya ALLAH ne ya kiyaye fad'uwar dakikayi, bawuya saikiga ansamu matsalar ciwon 6arin jiki, kisama zuciyarki hak'uri". ''To ibaraheem ngd". Ya jinjina mata kai, cikin hikimar iya zance yayta bata labari mai dad'i da kwantar da hankali, itama saitaita sakin jikinta, saida yaga tasamu 'Yar nutsuwa sannan yabarta. _______________________________ Kusan kwanaki biyu Momy Na jiyya, Alhmdllh sauk'i yasamu. Kulawa dai sosai tana samu wajen 'ya'yanta, musamman Anty shukurah da ya khaleel. Anty zuwairah dai babu damar zuwa, saidai waya takira Tamata sannu. Ayau kuma Aleeya zata iso daga England. Sosai Momy tasaka akema zuwan NATA shiri Na musamman, d'aki guda tasa aka gyarama Aleeya a 6angarenta, komai Na buk'ata aka tanada mata aciki, kaikace wata sarauniyar bak'uwa zasuyi, (lallai Momy nason Aleeya kam). ************ "Nikam dakinbar shayinnan natafi kawai, inada aiki sosai a office wlhy". " please yafa huce, wlhy nasan katafi zaka mance da yunwar cikinka ne kawai, gashima ya huce aii". Kar6an mug d'in yayi yana girgiza kai kawai, yay bismillah yafara sha, "rigimarki yawane da ita Sholy". " nidai kadaina cemin wata sholy, wai a inama kasan sunan?". "Bakinsa yata6e, yana shan tea d'in da dankali ad'an hanzarce, saboda saurin dayakeyi yafita, yajuyo yana kallonta, kinsan a ina asan sunan?". Girgiza masa kai tayi, batareda tayi maganaba. Ya maida kansa kan abincin, ''wajen meerah naji, nikuma sunan yamin dad'i, Dan haka dole abarni nake kira". "uhm, Aysha tafad'a tana tunzuro baki". Mik'ewa yayi yana gyara belt d'in wandonsa, danharya shirya cikin uniform d'insa masu k'ara masa kwarjini da cikar haiba, "idan Baki maida wannan bakinba yanzu zanyi maganinsa". Da Sauri Aysha ta gyara bakinta, danta San sauran sarai. Yad'auki jakkar laptop d'insa da wayoyi da hula zai fita, ya kalli Aysha "bazaki rakaniba?". Da sauri tamik'e dantaji kunya, takar6i jakar suka fito, babu mai magana harsuka fito tsakar gidan, tom bani kayana ki koma ciki, su Adams najirana awaje. Mik'a masa tayi, tanamasa addu'a. Saida ya kar6a sannan ya sunkuyo ya sumbaci goshinta da la66anta. Kunya yabata, tasaka hannunta tarufe fuskarta, kai Yaya, ko kunya bakaji?". " Yaya ko?". Da Sauri tamatsa bays o sorry sadauki, tayi maganar a shagwa6e". Lallausan murmushi yasaki, sannan yajuya yatafi. Saida yaje k'ofar gate dannan yajuyo ya kashe mata ido d'aya tareda d'aga mata hannu yafice gaba d'aya. Dariya abin yabama Aysha, ta juya cikin gida tana mamakin ya khaleel da halayensa, yanzu takuma tabbatarwa ya khaleel murd'ad'd'en mutumne, Dan har yanzu yana nan yanda tasanshi, kwanakinta Tara kenan taredashi, amma kaf halayrnsa suna nan Tatare dashi, babu wani canji, wani lokacin kigansa mutum mai sauk'i, wani lokacin kuma amurd'e, dariya abuce mai tsada awajensa, hakama bashida yawan surutu, Alhmdllh tana samun kulawa bakin gwargwado daga wajensa, dukda har yanzu bai furta yana sontaba, bata damuba, aganinta watarana shima zai fad'ane, Abu mafi burgeta agareshi shine tsafta, ya khaleel akwai tsafta da gwalli tamkar mace, yamafi wata macen. Komai nasa k'al-k'al yake sonshi, shiyyasa tadage da bada himma wajen gyara kanta da muhallinsu, bata yarda tabar wata 6araka dazaiga gazawartaba, iya k'ok'arinta tanayi Dan ganin tak'ara daraja da kima a idonsa, halayensa kuma basu dametaba, insha ALLAH zata iya zama dashi a aduk yanda yake, kuma su zauna lfy. Agurguje itama ta shirya driver yad'auketa zuwa Inda take aiiki. Yana fita Adams yak'araso da hanzari yakar6i kayan hannunsa, atare sukayi salute nashi, ya maida musu da murtani cikin sanin darajar d'an Adam. Adams yabud'e masa Mora yashiga, Ema... sarkin mota yafara aikinsa Na tuk'i, yayinda sauran mota biyu ta securitys nashi kebinsu abaya. Shiru ya kwanta jikin kujera, tunaninsa gaba d'aya yatafi akan aysha da shirmrnta, yana mamakin yanda take komanta cikeda k'uruciya, saidai kasancewarta mai tsafta da yanda take girmamashi yakan sakashi cikin farinciki da annashuwa, yarinyar tanada mafi yawan halayen dayake buk'atar matarsa dasu, Abu da kedamun zuciyarsa shine aurennan da Momy tatasoshi gaba akansa, yanzu haka yauma saida tace yaje ya d'akko Aleeya idan ta sauka a airport, da to kawai ya amsa mata, amma bayajin akwai yarinyar data Isa ya6ata lokacinsa wajen wani tarbarta, yaja siririn tsaki Wanda har saida Adams yajuyo ya kalleshi, yana mamakin miya saka boss tsaki haka?. Babu dad'ewa suka iso setetion d'in nasu, nanfa aka Shiga gaisheshi damasa murnar aure, shikuma yana musu godiya da halartar dasukayi. Duk saida yashiga office's d'in oganninsa yakai gaisuwa, sannan yadawo nashi, shima wad'anda suke k'asa dashi suka shiga zaryar zuwa gaidashi, dakawo masa aiyukan dasukayi bayan baya nan. Aiki kam ya iskeshi jingim, damma su youseef nayin wad'ansu. Su Joseph ma sunshigo sunyi gaisuwa amatsayinsa Na ogansu. Kowanne yakawo masa aikin dayayi dawanda suke kai, sosai yau aiki ya rinca6e masa, gaba d'aya yagaza samun kansa. Wajen 12:30mp yaji shigowar sak'o a familie phone nasa, baibi takan massage d'inba, saboda aikin dake gabansa. Zuwacan kuma sai kira yashigo, nanma bai d'agaba, saida aka kira kusan 3times bai d'aukaba, daganan aka daina kira. Nock d'in k'ofar office d'in akayi. Yabada izinin shigowa, Basheer ne wani ma'aikacinsu, ya k'ame tareda salute Na khaleel. Kansa ya jinjina masa sannan yanuna masa kujera alamun ya zauna. Basheer ya zauna a kujerar dake kallon ya khaleel, sannan yamik'a masa wasu files dake hannunsa. "Sir ga bayanan damuka samu akansu, wannan kuma sunayen mutane 17 ne damuka kama acikinsu, akwai 13 anan setetion d'in, saikuma 3 a hannun police, 1 yana hannun hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi". "OK, yakar6i files d'in yana dubawa, saida yagama tsaf yad'ago yana kallon basheer, "wanene Dr Sageer!?". "shine likitan da aka kama Na Osun d'innan, Wanda ake zarginsa da saida kwayoyi ta asibintinsa, amma ya tabbatar mana bashi kad'ai baneba a bayanansa, hukuma sha da fataucin miyagun kwayoyi tana bincike akan sauran mutanensa". "Kukuma kuna aikinmi? Kuna zaune kawai kuna jiran su kawo muku bayanai kenan?". " a...a'a sir, Bahaka baneba". "To yayane? Bansan miyasa kuke sakaci akan aikinkuba, kunada damar kwatar cases a hannun kowace hukuma idan kukaga tanada rauni wajen hukunta mai laifi, amma saiku zuba idanu yayinda aikin had'aka yashiga hannunku, ni narasa mike damun tunaninku?, shin kunada tabbacin za'a hukuntasu yanda yakamata acand'in? Shiyyasa kullum muna aiki amma bamu samun alk'aluman cigaban wahalarmu, idan muka toshe can saikaga can ya 6alle, sakacinkune kuma kejamana wannan fad'uwar tasar". Sorry sir, insha ALLAH za'a gyara". " zancen kenan kullum, za'a gyara za'a gyara, amma haryanzun gyaran baizoba, haka za'a gama yayinmu bamukawo wani sauyiba a k'asarmu kan 'yan ta'adda, muwuce wasuma suzo Suyi tsarinsu suwuce, haka-hakadai kullum k'asa nak'ara ta6ar6arewa da lalacewa, mtsoowww aikin banza kawai". "Basheer dai yanata bada hak'uri". files biyu ya khaleel yamik'a masa bayan yasaka hannun, kakai wad'annan office d'in Taheer, wad'annan kuma yasaka hannu kakaima Mahfouz su". " OK sir, thanks you sir". Kansa kawai ya jinjina masa, yajanyolaptop d'insa yacigaba da aiki, shikuma basheer yafice, yanamai jin k'auna da sha'awar halayen Ibraheem Abdallah j!, yana addu'ar ALLAH yabashi ikon yin koyi dashi.. Dan bakowa keda makamancin k'yak'k'yawan hali irin nasaba, nason a gyara k'asa, musamman masu girman matsayi irin nasa, da Wanda suka fishi, harma da wad'anda basu kaishiba. ******* Kiran wayarsa da'aka k'arayine yasakashi yin k'aramin tsaki, batareda yaduba mai kiranba ya d'auka yasaka a kunne yanayin sallama, yayinda hankalinsa kenan aiki a laptop. "Ibraheem Aleeya ta saukafa, tace tanata kiran wayarka Baka amsaba". " wlhy Momy aiki yamin yawa a office, please ki aika driver ya d'akkota mana, kokuma cikinsu Muhseen idan wani yana gida yaje ya d'akkota". ''ni babu wasu su muhseen dazan saka, dadai zaka daure saikaje ka d'akkota minti nawane kwata-kwata". "Hummm Momy bazaki baneba wlhy, kinganni kuwa a office?, yanzu haka sallah nakeson natashi nayi nadawo kan aikina, kisankusa kwanaki goma bana office, please amin afuwa Dan ALLAH driver ya d'akkota". Shikenan bara nama driver magana, sai suje da 'yan biyu". OK saina shigoto, baijira cewartaba ya yanke wayar yana mita. "kajiminfa Momy dawani zance, ita hartakai Isar dazanje airport d'aukarta, haba saikace wani lusari, mtsoww, wlhy kemafa Momy kinada matsala, haba kullum zance d'aya, yay maganar yana mik'ewa saboda Kiran sallah da akayi Na azhur. Wayar yad'auka yaduba number data kirasan, saiyaga harda miss call d'in Aysha, itacema tafara kira, saikuma Na Aleeya guda biyu. Kansa yadafe, Dan baiyi tunanin kiran nataba, yama manta yanada number ta, yakar6ane wajen mama tun lokacin gabatowar bikinsu data tafi Kano, tunda yakar6i number ma baita6a kirantaba, ita kanta ayshan batasan yanada number d'intaba. Massage d'in da'aka turo yaduba Dan ganin number ayshane. _"Sadaukina ya aikin?, kakasance cikin farinciki da kwazon aiki irinnan gwarazan sadaukai mijina"._ *_Sholynka Ce_*😘 Murmushin dabai niyyaba ya su6uce masa, yakuma maimaita massege d'in, aransa yana jinjina baiwar Aysha, gata 'Yar k'arama sai wayon tsiya. Masallaci yafice Dan gabatar da sallah. Bayan idar da sallah suka had'u dasu taheer. Cikin tsokana Taheer yace, "kai alhaji kaga kuwa k'yawun daka k'ara? Lallai ango kana kwasar amarci yasin". " mtsooww! ALLAH ya shiryeka Taheer, kaidai bazaka ta6a canjawaba ko? To dan k'aniyarka muni kakeso Na k'ara saboda nayi aure?". Cikin dariyar shak'iyanci youseef yace, "A'a bak'inciki yakeson maka, k'ilan soyay kadawo aiki wujiga-wujiga ko? Katina lokacin daya dawo hutun angwanci, ALLAH Taheer harwani yallew-yallew yakeyi saboda gara daya kwas.........." .......Bai k'arasaba taheer yakai masa rankwanshi....... Youseef yamatsa yana dariya. "Kai Malam ALLAH ka rankwasheni ramawa zanyi, koka manta Na girmeka tunda narigaka aure?". "To uban 'yansan girma, munji karigamu aure saime to? abinda kake tak'amar kasani mumadai yanzu mun sanshi koko Taheer?". " A'a j bakada bakin maganama kaikam, tunda kaine auta acikinmu". "Kuttt ammafa ka sameni, d'an iska zan ramane, nakula tonon silili zakamin cikin yara, bara nawuce office aiki nacan jingim yana jirana, ni dama banje wannan hutuba". " hhhh tab wlhy ganganne, muzaka saka a kwali, kagama dirzar amarci da young girl d'inka kazo kanawani daddojewa🤣". "Banza d'an iska banida lokacinka, kagama tafiyata", 'ya khaleel yay maganar yana barin wajen, fuskarsa d'aukeda murmushin iskancin da youseef kemasa'. Suma dariya sukayi, youseef ya kalli taheer, "d'an uwa Alhmdllh, kagafa j yasamu kwanciyar hankali wlhy, gaskiya Na yarda aure na k'arama mutum daraja arayuwa". "Hakane youseef, kagadai kamar wasa duk munzama masu iyali, ga matarka harda ciki, kai Alhaji kaimafa shegen samane, kafayi aiki alkur'an". "A, yoni Na wasane aka gaya maka?, inagamafa matar Joseph itama takamu, dan jiya nakirasa yakecemin sunje Asibiti madam babu lfy, nikuma d'an mutuncin bansake kiraba, gashi yau tun safe sukatafi Zamfara shidasu Zakariyya". "ALLAH ya inganta mana to, baka saniba, dolece tasaka Joseph zuwa Zamfara d'innan wlhy, dan babu yanda zai kaucene". "aini tunda naji jiya j yayi maganar naketa addu'a kar sunana yafito amasu zuwannan wlhy, haka kawai, bakagama amarciba asambad'aka daji". "Hhhhh wlhy kaji haushi taheer, aikam saina zugashi ansaka sunanka a masu zuwa Lagos insha ALLAH". " munafiki basai kabadaba". Cikin dariya youseef yabar wajen, dan yasan Taheer ya shak'a.😆.lol. Sai kusan 6 ya khaleel yadawo gidan, yaukam motocin har cikin gida suka shigo, saboda sun saka mai gadi suma. Kamar yanda aka saba Adams yarakoshi da kayansa har barandar 6angarensu. Anan ya kar6a, "uhmm Adams inagafa yau munada fitar dare gaskiya, dan d'an iskannan Moxies ancemin yana 9ja, nagane club d'in dayake zuwa, tom inaga dolene daren yau mu ziyarci club d'in, ni da kai kawai zamuje, saimunga yanda wajen yake sannan inma muna buk'atar wasu saisuzo, tunda bamusan yawan yaransaba da mabiya, so ka sanarma su Samuel, suzama cikin shiri". "OK sir ALLAH ya kaimu daren, amik'amin gaisuwa wajen antynmu". " Zataji tunda dai kak'i zuwa ka gaidata". " ayi hak'uri boss insha ALLAH Wannan weekend d'in zan shigo". " ALLAH yasa to". Sukayi sallam ya khaleel yashiga ciki. Babu kowa a falon. Saidai yanata tashin k'amshi, ko INA k'al-k'al yake, yayinda karatun alkur'ani ke tashi cikin sifikun, wata nutsuwa yaji ta saukar masa, dukkan gajiyarsa tatafima baki d'aya. d'akin Aysha yalek'a, saiyajiyo motsinta ruwa a toilet tana wanka, "badai sai yanzu yarinyarnan tadawo aiikiba?", 'yay maganar yana kallon agogon hannunsa'. Babu mai bashi amsa, danhaka yajuya zuwa nasa d'akin danya d'an watsa ruwa............✍ Wayyo kaza zanci😩🤧👻 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍 [9/23, 8:35 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣2⃣ Babu dad'ewa Aysha tafito daga wankan, simple makeup tayi tasaka wandon jins blue dawata lemon green d'in riga wadda Tamata masifar k'yau, ta gyara kanta ta d'aure, bawai Aysha Nada wani uban gashi baneba, amma daidai gwargwado yanada tsayi. Kasancewar ba sallah zatayiba tafito falo, kwanciyarta tayi saman doguwar kujera tana sauraren karatun alkur'anin data saka, kokad'an tunaninta bai kawo ya khaleel yadawo gidanba. Shima a d'akinsa wanka yashiga, ya d'auro alwala yafito, jikinsa kawai ya goge da k'aramin towel ya zira jallabiya blue black ajikinsa, turare yafesa kad'an sannan yafito zuwa masallaci. Ganin Aysha a kwance idonta kuma alumshe saiyayi nufin tsokanarta, cikin sand'a yak'araso kusada inda take, k'afarta datad'an lek'o Yakama babban yatsanta yaja, da sauri yaduk'e bayan kujera. Kawai Aysha jitayi an matsa mata yatsan k'afa, aiko tamik'e a firgice tareda kwallah k'ara, sosai ta firgita, ta wawwayga kuma bataga komaiba, hakan yakuma tsoratata, sai tasaka kuka da kiran mama ta shiga uku, anturo abu zai kasheta. Yanda take dire-diren k'afafu da kuka tamkar taga dodo ido da idone abin yabama ya khaleel dariya, duk k'ok'arin rik'ewa dayakeyi Baisan dariyar ta kwace masaba. Aysha takuma tsorata, saida taji muryarsace sannan tagane shine. Yafito daga wajen 6uyarsa yana cigaba da dariya sosai. Tunda Aysha take bata ta6a ganin dariyar ya khaleel irin hakaba, saita samu kanta da shagala kallonsa. Shikam baimasan tanayiba, yaga mugunta dariya ta tik'eshi, ya zauna kan kujera yana dariya. Saida yayi mai isarsa sannan yad'ago yana kallon Aysha wadda ta cuno baki gaba saboda jin haushin dariyar dayake mata. "Wai dama haka kike da tsoro? Hhhhhhh, wlhy kinbani dariya, to dakika tashi ina zakije ne?". "Cikin shagwa6a Aysha tace, " yoni wlhy nama rikice, narasa INA zan dosa, d'aki ko waje, towai yaushe kadawo ban sanibane?". "Kina wankafa nashigo, harnayi wankama, masallaci zanje kawai naganki kwance ido arufe, shine naji sha'awar tsokanarki, kinzata miye to?". " yo aljani mana". "kinajin karatu wane aljani ya Isa zuwa kusadake, kedai shegen tsorone dake, saikuma tsiwar tsiya fal kanki". "Wlhy bazaka ganeba ya khaleel, natsorata wlhy, kaikuma kanatamin dariya, dama haka ka iya dariyar mugunta?". Bai bata amsaba yamik'e, ''kinga bara naje massalaci karna lalace anan ashiga sallah". Binsa kawai Aysha tayi da kallo tana murmushi dajin dad'in ganin dariyar mijin NATA murd'ad'd'e, dama yana dariya har haka? Oni shatun mama, su ya khaleel an iya mugunta. Saina rama aii Nima". Lallai yarinya zaki rame dai, naje madallaci". To adawo lfy. Saida akayi sallar isha'i yadawo gidan aysha takawo masa ruwa ya kar6a yana fad'in "thanks", yana gama sha ya ajiye cup d'in yana satar kallon Aysha k'asa-k'asa, kwalliyar tata tamasa k'yau, amma dayake ya khaleel akwai iya shariya, bazaka ta6a zaton yama damu da itaba. Danne-danne kawai yakeyi a waya. Aysha tace aranta aljanun miskilancin sun motso kenan?...... Maganarsace takatse tunaninta, tad'ago tana kallonsa, Dan bataji miyaceba sosai. "Kin tsareni da idanun kinnan, canayi ki dafamin shayi". Kad'an Aysha ta murgud'a Baki, azatonta baya kallonta, Dan haryanzu waya yake dannawa, tanufi kichin tana 'yan k'unk'uni. Yana kallom murgud'a bakin data masa, dakuma k'unk'uni datakeyi, saidai bayajin mitake fad'a, ransane ya6aci, "shin mi yarinyarnan ke nufi? Kodan taga Na sake mata ina wasa da ita?", kwafa yayi yacigaba da danna wayarsa. Kusan mintuna 10 Aysha takawo masa shayin, tasha jinin jikinta dan ganin fuskarsa cid'in-cid'in ad'aure, duk kuma saitaji babu dad'i, koba komai tana shiga farinciki idan taga ya khaleel Na walwala. Kofin tea d'in ta mik'a masa, batareda ya kalletaba ya kar6a, baisake bi ta kantaba, yacigaba da shan tea d'insa yana danna waya. Itama Aysha tayi shiru cikin kujera tana kallo, amma duk Rabin hankalinta Na Kansa, sai satar kallonsa takeyi. Ahaka hasnah tayi sallama tashigo ta samesu. Aysha ce kawai ta amsa mata, amma Oga ko ido baid'ago ya kallesuba. Hasna sai Harar Aysha takeyi, yitai tamkar batasan tanayiba, Dan bata gabanta, arantama sai ayyanawa takeyi, yarinriya da uwarki laura zanyi badakeba, danke kinmin kad'an a filin daga. Kusada ya khaleel hasnah ta k'arasa, ta rissina tana fad'in "'ya khaleel Momy tace kazo tana kiranka". Saida ya6ata mintuna biyu sannan yad'ago ido ya kalleta, "naji to, inazuwa, kinzo kinmin tsaye akai". 'Yak'are maganar da hararta'. Fita tayi tana tutura Baki wai ya dizgata gaban Aysha. Bai fitaba saida yagama shan shayinsa. Fita yayi batareda ya kalli ko inda Aysha takeba. Aysha ta ta6e baki cikin hanlin ko inkula, yana fita takira Rufaida da Sadiya a waya, tahad'asu waje d'aya suna hira, dayake shashashune kowacce k'uruciya Na d'ibarta, sai sukaita bama juna labarin first night d'insu. Nace, "ALLAH ya shiryaku".😏 ****** Afalo ya iske k'annen nasa duk, har samarin suna kallon kwallo, 'yan matan kuma suna d'ayan group d'in kujerun kowacce da waya a hannu, masu charts nayi, masu karatun novels nayi, k'annensa ne 'ya'yan Momy kawai babu, damasu basa shiga cikin yaran gidan.. Gaidashi suka shigayi yana amsawa da k'yar, dan abinda Aysha tamasa ya 6ata masa rai. Musleem ya k'unshe baki da hannu, cikin magana k'asa-k'asa yacema zunnurain, ''ya zunnurain bakaga ya khaleel yak'ara kaurin wuyaba da haske?". Zunnurain ma dariyar yayi yace, "gulmamme ALLAH yasa yajika, kaikam aure aiba wasaba, Nima kwannan zan shigo da maganata gida, tuzurancin nan ya isheni, bazanso nayi tuzuranci irin Na ya khaleel ba gaskiya, yanda yanzun ake yayin mutuwarnan farat d'aya". Dariya duk sukayi, dansinji mi zunnurain d'in yace. A 6angaren momy ma kowanne da hidimar dayakeyi, wasu waya wasu laptop, gaisheshi suka shigayi, yakuma kicin-kicin da rai, Dan ganin bak'uwar fuska cikin k'annen nasa, wadda ya tabbatar itace Aleeya. Aleeya kam dukta rikice, ashema guy d'in yafi had'uwa a fili fiyeda hoto, ita saitagama picture d'insa data gani kamar anrage masa k'yawune, tama kasa cewa uffan, saibinsa take da kallo kawai. Yazauna kusada Momy da itama idonta ke kansa, ita batasan irin wannan hali Na Ibraheem ba....... Maganarsa ta katse mata tunani. "Momy gani, ance kina kirana". ''To ba doleba na kiraka Ibraheem, koka mance munada bak'uwane?". " hummm, kusan haka d'in momy, kinsan aiki yasha kaina ga iyali, amma amin afuwa. Ita bak'uwar bata iya gaisuwa bane?". Murmushi momy yayi, tasan d'an nata dason girma, "ta iya mana Ibraheem, Aleeya ga Ibraheem nan". Da k'yar Aleeya ta iya saita kanta, gaba d'aya tagama raina ajinta agabansa, amma abinka da wayayyiya girman turai, ido yarigaya ya bud'e, saita wayance, "o!, sorry my boo.., ya aikin naka? Ina fata komai normal?". Bai amsaba, hakama bai kalletaba, sai harara daya makama k'annensa, aii da sauri kowacce tatashi tabar falon, momy ma saita mik'e, tasan Ibraheem akwai kunya, bazai ta6a amsawa Aleeya magana tana wajenba, " bara Na watsa ruwa nima". Aleeya Ce kad'ai tace, "to momcy afito lfy". Ya khaleel kam bai tankaba, Dan haushine yakuma kamashi akan rashin kunyar yarinyar, Dan rashin mutunci agaban mahaifiyarsa zatawani kirashi da boo!, "mtsoow" yaja siririn tsaki. Wanda yasaka Aleeya kafeshi da idanu, 100% ya khaleel yamata, tanason namiji mai aji da mulki, duk kuma tagansu agunsa. "Bakida abincewane? Natashi natafi, nabar matata ita kad'ai". Murmushi Aleeya yayi, dukda maganarsa ta k'arshe tamata zafi saita danne, cikin salon wayayyun mata tace, " my boo, ajinkafa yafi tsada, tsada, nazacima fiye dahaka agareka, domin irinka ko'a masarautun duniya kad'anne, saidai nalura kaiba Prince baneba, king ne da kansa gabad'aya, ina alfahari da samunka amatsayin miji, Wanda nadad'e ina bulayin nema, dukda zuciyata nayawan gargad'ata akan azar6a6i, harda tsoratar dani akan nacika kaud'i, bana bama karatunta muhimmanci, Dan ina alfari banta6a neman Abu narasaba". Tayi crossing k'afarta, tana kad'ai idanunta manya, "hummm kasan wani Abu kuwa?", batajira amsarsaba tacigaba.. " Aleeya nada tarin masoya, turawa da bak'ak'e, kuma duk sun zauce akan sonta, duk burinsu shine su mallaki Aleeya, idan zan kafa za6en mijin aure, to tabbas sama da mutum babu adadi zasu jefa k'uri'ar Neman za6in aurena, amma abin al'ajab. Kallo d'aya tak namaka ajikin hoto sai zuciya da kwanji suka fara azar6a6in gogayyar kar6arka amatsayin mijin aure, Dan zuciyata tayi dai-dai da samun irin tsarin da kullum take zana taswurarsa, aganina babu Wanda ya cancanci samun k'uri'ar aurena sai babban gwarzon jarumi irinka, so Aleeya tabaka makullin zuciyata kawai, basai kasha wahala wajen lalubeba". Tunda tafara magana yake danna wayarsa, ko kallo bata isheshibama, wannan surutunma datake zubawa, kallon mai kwantaccen notikan kai yake mata, (lallai Aysha ta cancanci zama matarsa 100%, dukda kasancewarta k'aramar yarinya akwai aji da sanin darajar kai, wani lokacin yakanyi zargin Aysha Na sonsa, amma iya kamun kanta da jan ajinta yakan ruguza hasashensa), abin mamaki yau saiga ballagazar mace agabansa, dukda yasha gamo da irinsu Aleeya, amma yakula farashinta yafi nakowa sauka acikinsu, ahaka kuma momy take fata tazama uwar 'ya'yansa, lallai akwai babban aiki agabansa, gatadai afuska kamar mai aji, amma a zance wawuyace..... "My boo!.. Naji kayi shiru, kobaka gamsu da bayanina baneba?". "Naji, zan duba", yamik'e yana kallon agogon hannunsa, "uhm kinga bara naje, kina neman Shiga time d'in matata". Mamaki da tsoro suka lullu6e Aleeya, yandafa take tunanin guy d'innan yawuce nan, irin wannan rainin haka, ta sauka k'asarnan takirashi a waya bai d'aukaba, yadawo aiki bai nemi inda takeba saida aka kirashi, tsabar ya maidata 'Yar iska, tasaki baki tana masa magana Yakama danna waya batareda ya kulataba, shine dankuma cin fuska zai mik'e yace wani tashiga time d'in matarsa, hummm". Harya kama handle d'in k'ofa zai fice momy ta katseshi, " a'a Ibraheem harkun gama gaisawar?". Juyowa yayi yana k'ara d'aure face, cikin dakiyar murya yace, "eh momy bara naje muyi magana da baffah". Momy ta washe Baki, "to maddalah yayi k'yau". Ita azatonta zaije akan maganar aleeyane, tace, " zaka dawo tanan kenan?". "A'a momy, zanje Na kwanta danna gaji" "To shikenan, ainaga da sauran dare, dadai yadawo kunsake gaisawa, da safe saikuyi maganar da baffan naku". Aransa yace, " jifa momy dawani zance, itakuma matatafa?", amma afili saiyace "a'a momy gwammadai naje d'in, ita saitayi hak'urin goben". "Babu damuwa ALLAH ya kaimu goven, daughter tashi kimasa rakkiya ko". "OK momcy". Shikam baima jira k'arshen zancenba yafice. Afalo duk k'annensa suka zubo musu ido, babu mai damar cewa wani Abu, amma kowanne mamaki da tambayoyi fal ransa, ita kanta Aleeya tasha jinin jikinta, Dan sanda ta iso gidan d'azun babu kowa, batayi zaton ganin familie d'in dayawa hakaba. Tunda suka fita ko juyowa baiyiba barema yanuna yasan tana binsa, saida yakusa k'ofar dazata sadashi da 6angarensu sannan yatsaya, batareda ya juyoba yace, ''har wajen baffan zaki binine?". Yanzunkam abinda yata6a mata zuciya, da ajinta da komai, itada mazan tuturawa da bak'ak'en fata ke gurfana agabanta suna rok'on tasosu, tana wulak'antasu, amma itace abin yazo kanta?, Dan kawai tace tana son wannan man d'in yake dizgata. Kasa daurewa tayi tace, ''haba alhaji, dannazo gidanku kake wulak'antani?". " idan haka tunaninki yabaki, hakane", yacigaba da tafiyarsa, harya shige yamaida k'ofar yarufe tana kallonsa kamar tasamu magiji. Murmushi tasaki, tajuya takoma tana ayyanawa azuciyarta, komi zaiyi bazatayi fushiba, saita mallakeshi zata rama dukkan abinda yamata. Yanzunma a fallo haka su amal sukai mata ratai da idanu, kamar zasu cinyeta d'anya harta shige 6angaren momy. Suka fara 'Yar gulmarsu k'usk'us.😂.lol Ya iske Aysha afalo tana kallo, itama bai tanka mataba yashige d'akinsa, kusan mintuna 30 saigashi yafito, yaci kwalliya cikin k'ananun kaya sai bulala k'amshi yakeyi. Murya a cunkushe yad'an dubi ayshan yace, "zan fita". "Fita kuma? A wannan Daren ya khaleel? ". Idonta yacika da kwallah, yana kallonta, amma bai bata amsaba yafice abinsa. Sai kwallah shar-shar sukafara bin kumatun Aysha, tazauna jagwab a kujera tana cigaba da kukanta, zuciyata Na zafi, waishin tayaya zata maido da hankalin ya khaleel kantane? Bazata 6oyeba tana k'aunar mijinta sosai, tanakuma fatar yakasance da ita, tasamu kulawarsa 100% har Abadan, gaskiya bazata iya jurewaba, to wai inama zaije adarennan? Takuma rushewa da kuka😭. Sallamar datajine tasakata saurin goge hawayenta, zeenatu Ce d'aya daga cikin masu aikin gidan. Ta rissina tana gaida Aysha, dukda ta girmrta sosai. Aysha ta jinjina mata kai, "lafiya dai zeenatu?". "Eh, Anty, dama ya khaleel ne yace Nazo natayaki kwana zaije wani wajene". Jimm Aysha tayi, sai zuwa can,tace, " to zoki xauna, ngd".. Zeenatu tak'araso cikin falon, zata zauna k'asa Aysha tace, ''a zauna saman kujera mana". " a'a Anty nanma yayi wlhy". Haka suka zauna shiru saboda rashin sabo, kowacce idonta a tv, sai wajen 11 Aysha taga zinatu tafara gyangyad'i, tace, "tashi muje Na nuna miki d'aki ki kwanta". "To Anty ngd". Bayan Aysha taraka zinatu saita dawo falon ta zauna Dan ita damuwa ta busar Mata da idon Nata, ko barcin bataji ma....................✍ ❤❤❤❤❤❤😍😍😍😍😍😍👍🏻 [9/24, 3:26 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) _'Dungurun gum yau shafin nakine *Ummulkhairi Shehu sardauna* ina godiya da soyayya ALLAH yabarmu tare, bilyn Abdull na k'aunarki irin Trillions d'innan💓💓💓💓😄👍🏻_ 2⃣3⃣ Ya khaleel yana fita suka had'u da Adams, Adams yabud'e masa baya da sauri, dakatar dashi yayi. Yabud'e gaban motar yazauna, Adams yadawo mazaunin driver yaja motar sukabar anguwar, suna tafiya sunad'an tattaunawa akan aikin dazasuje, har suka iso wani katafaren club Tun a k'ofar club d'in suka fara gamo da 'yan mata da samari, duk cikin shigar rashin mutunci, saika rantse a turai suke ba 9ja ba, kuma harda cikakkun 'ya'yan hausawa awajen😢. Duk da aikin ya khaleel yasha kaishi irin wad'annan wajajen, harma da inda yafishi fitsararru, Hakan bai hanashi jan tagwayen tsakiba, da Neman kariya wajen ubangiji gudun fad'awa tarkon shaid'an, babu abinda zai hana sha'awa bijiro maka a irin wad'annan wajajen inhar Kannada lafiya, dakuma raunin imani. Shikansa Adams tsigar jikinsa sai tashi takeyi, addu'a kawai yakeyi ALLAH yasa sugama abinda yakawosu dawuri subar wajen kafin shaid'an yayi tasiri akansa. Jikin beer parlor suka k'arasa, irin kantarnan da ake zuba kayan shaye-shaye aciki, sai a gewaye inda mutane kan tsaya su jingina. Ya khaleel ya zauna a kujerar nan maid'an tsayi tajikin table d'in. Shima Adams zaman yayi. Wata budurwa dake tsaye jingine da table d'in sai hambud'ar giya takeyi da'aka zuba cikin irin k'ananun glass cups d'innan, ta shanye Na hannunta idonta akan ya khaleel. Wanda shima satar kallonta yakeyi da takaici. "Hii", 'tafad'a tana d'aga masa hannu🙋🏻‍♀'. d'an murmushin yak'e😁 yayi shima yace mata, "hii". Saves ta kallah tamasa sigina da ido, da nuna yatsun hannunta uku. Kansa ya jinjina mata, sannan yajuya ya d'akko kwalaben guilder guda uku acikin Kantar glass d'in wajen, ya goge kofuna biyu yazuba k'ank'ara yakawo gabansu ya khaleel dake kallon Shiga da fitar mutane cikin kwarewar aiki. Ajiye kofunan dayayi yasaka ya khaleel juyowa ya kalleshi, Save's yanuna masa budurwarnan data saka aka kawo musu, ta kannema ya khaleel ido d'aya tareda lashe la66anta da harshe. Guntun murmushi yasaki tareda kauda kansa, matsowa tayi kusadashi ta d'ora hannayenta saman cinyarsa, a'uziyya yayi azuciyarsa cikin dabara yaxame jikinsa, rankwafowa yayi saitin kunnrnta yace, " kozamu zaunane?". Jajayen idanunta tad'ago ta kalleshi, cikin salon barikanci ta kanne masa ido d'aya tana mayaudarin murmushi. Awasukujeru sukaje suka zauna. Giyan datayi Order aka biyosu da ita wajen, har saves yajuya zai koma yamasa sigina, siiii!! Jimana my man. Saves yadawo yana sauraren ya khaleel. "Kawo mana sorpt drinks". "O, my friend!, why? bazakasha wannanba danasaka akawo?". Guntun murmushi yayi, yasaka yatsansa yana Sosa girarsa, cikin basarwa yace, ''no, banashan giya". " why?". Tasake tambayarsa. Bakinsa yad'an ta6e tareda d'age kafad'a yace, "haka kawai".🤷🏻‍♂ " woow, amma ka birgeni, rayuwarka abin sha'awa, handsome irinka baya shaye-shaye, akwai k'ayatarwa a tsarinka". Adams yay guntun dariya, yana fad'in ''kad'anma kenan daga abubuwan dake tattare dashi". Jinjina tama khaleel dukda bata fahimci maganar Adams d'inba sosai, saboda ba bahaushiya baceba, tamik'ama ya khaleel hannu alamun su gaisa "am blessing". Amma saiya basar bai bataba, saiya wayance dafad'in, "Nice name, Ibraheem Abdallah, ko kice j!". " woow komai naka daban Dana kowa". Murmushi yasake yi, amma Baice komaiba. Tayima saves alamun yazo, da Sauri saigashi, giya takuma buk'ata kwalba biyu, amma sai ya khaleel ya dakatar da saves d'in akan karya kawo, ya kalleta cikin nuna kulawa yace, "please ki huta mana". Batace komaiba sai guntuwar dariya Datayi. Suduka kowa ya maida hankalinsa wajen waige-waige, da Alama kowannensu da abinda yake nema, shiru nawani lokaci sannan ya khaleel ya jefeta da tambayar data sakata maido hankalinta Kansa. Ahankali hira tacigaba da gudana atsakaninsu, yayinda Rabin hankalin ya khaleel yake wajen nazarin jama'ar club d'in, shikam Adams gaba d'aya yamaida hankalinsa ga mutane. Itama ya khaleel yalura baduk hankalinta ke kansaba, kamar kuwa an tsikareta saiyaga tamik'e, da Sauri yace, " lafiya kuwa". Cikin rabuwar hankalinta biyu tace, "please 2minutes". Tana d'aga k'afa zata bar wajen wani cart yafad'o daga aljihun wandonta. Kiranta ya khaleel yashigayi danta d'auka, amma INA bata jishiba ma, ganin harta fice ya sunkuya ya d'auka, bin bayanta yayi da Sauri domin kaimata batareda ya dubaba. Waige-waige yafara a waje amma bai gantaba, 🤦🏻‍♂Omg saikace aljana, haryayi shirin juyawa ciki saiya duba cart d'in, yazaro ido waje dan ganin kowacece ita ajikin ID cart d'in. A hanzarce yafara bincikenta cikin mutanen dake tsaye a wajen, cikin dabara yake dubata, cikin sa'a kuwa yasamota tsakanin wasu motoci tana kici-kicin kama wani guy, daka ganta kasan tasamu kyakykyawan training, saidai giyar datasha ta haddasama k'arfinta rauni, duk da shima guy d'in abuge yake, amma bai kaita shawuwaba, hasalima shi kusan normal yake, giyan bata fara tasiri ajikinsaba. K'arasowa yayi wajen da Sauri, da taimakonsa suka kamashi, cikin motarta suka sakashi suka kulle. Sai a sannan ta kalli ya khaleel, yatsun hannunta biyu ta d'aga masa tace, "thanks". "amma miyasa ka taimakeni? Bayan kuma bakasan alak'ata da guy d'inba, kasani ko zan cutar dashine?". Hannunsa duk biyu yatura cikin aljihun wandonsa, tareda gyara tsayuwa yasaki guntun murmushi, ID cart d'inta yaciro daga aljihunsa ya mik'a mata. Cikin mamaki ta kar6a, saikuma tafara laluben aljihun wandonta itama, tabbas ID cart d'intane, yaushe yafad'i bata saniba, tad'ago danufin tambayarsa saiya nuna mata nasa ID cart d'in, d'an zabura tayi taja baya, saikuma tak'ame tareda salute d'insa. Kansa ya jinjina mata. Tamatso kusadashi tace, " thanks you so much sir, amma kana neman wanine? Dan bakayi kama damasu zuwa club ba". Saida yad'an wawwaiga yaga babu mai kallonsu, kowa harkar gabansa yakeyi sannan yace mukoma ciki, amma yaza'ayi da sannan Na mortar?". "OK INA zuwa, tayi maganar tana zaro k'aramar wayarta acikin bra d'inta, baidamuba Dan yasan dun cikin salon aikine,, su jami'an tsaro sunada salo iri-iri saboda tsaro, kira tayi, babu dad'ewa saiga mutane hud'u, tamusu bayani akan ya khaleel. Nan take suka fara salute nashi Dan d'ammararsa tafi tasu. Key d'in motarta ta mik'a musu, tace suje dashi, amma d'aya ya jirata, zata koma ciki ta k'arasa wani aiki, duk suka amsa mata da girmamawa tareda salute nata, suka cika umarni. Itada ya khaleel kuma suka koma cikin club d'in, kujerar dasuka tashi suka koma, zaune suka tadda Adams wata budurwa a cinyarsa, sai shafashi takeyi, shikuma yana lumshe idanu tareda maida murtani, da d'an k'arfi ya khaleel ya buga table d'in cikin Jan tsaki. Da sauri Adams yadawo hayyacinsa, yature yarinyar daga jikinsa yana soshe-soshen jin kunya. Itakam blessing dariya tayi kawai. Ya khaleel baisake cewa komaiba yacigaba da dube-dubensa, can kuwa idonsa yafad'a kan Moxies dake zaune kan wata kushin, haggu da damarsa 'yanmata biyune suna rungume ajikinsa, kowacce cikin shigar rashin mutunci, gabansu kwalaben giyane birjit. Sai garadan samari majiya k'arfi dake tsaitsaye alamun yaransane, Duk saida ya khaleel yagama nazarinsu kaf. Sannan ya waigo da kallonsa wajensu Adams, da har yanzun kunya bata sakeshiba. Murya k'asa-k'asa yace, "ga Moxies can". daga Adams har blessing kallonsa sukayi, har Adams zai tashi blessing ta dakatar dashi, ta kalli ya khaleel dashima ita yake kallo, ''sir! Bara Na gwada sa'ata. Jinjina mata kai ya khaleel yayi. Tana barin wajen yamaida kallonsa ga Adams, ka sanarma su Samuel su taho, naga alamun Moxies bazai kamu cikin sauk'iba, dolene saimun d'an tada jini". " OK sir!". Can ya khaleel ya hango blessing kan cinyar Moxies suna kissing d'in juna, (sosai ya khaleel ya jinjina hatsabibancin blessing) kusan mintuna 10 yaga Moxies ya d'auki blessing zuwa wani d'aki, juyowa tayi ta kalli ya khaleel tamasa sigina da idanu, jinjina mata kai yayi cikin lumshe ido, daidai da isowar su Samuel wajen. Ya khaleel yamik'e, "Adams kuji da yaransa, INA zuwa. Adams ya amsa da OK sir. Saidai su ya khaleel basusan suna shuka bane a idon makwarwa, Duk abinda ke faruwa idon yaran Moxies biyu yana Kansu, duk wani motsinsu ya khaleel akan idonsune, yana tashi sukabi bayansa, bayan sun sanarma sauran 'yan uwansu abinda ke faruwa. Yakusa d'akinda Moxies yashiga da blessing yajiyo k'arar harbi, yaran Moxies sun kaima su Adams hari, dandanan club d'in ya hargitse, aka fara gudun tsira, yayinda sukuma suke musayar wuta, kowa takansa yakeyi. Ya khaleel zai Shiga d'akin wad'anda suka biyo bayanshi suma suka fara harbinsa, kaucewa yakeyi cikin kwarewar samun cikakken training, d'akin ya k'arasa da hanzari bayan ya harbi d'aya kafad'a, jin k'arar harbi da bud'e k'ofa moxies yatsaya da romancyn d'in blessing. Da sauri yad'aga hannunsa sama saboda nunasan da ya khaleel yayi da gun, juyawa yayi yana kallon blessing dake dariya, gira ta d'aga masa tareda kama hannayensa tamaida baya tasaka hand cop, sorry dear you are onder arrest🤨 ". Bak'in ciki tamkar zai kashe Moxies, wai anyi amfani da mace ankamashi, tsawon shekaru yana harkokinsa, ya gagari mazanma, amma yau da mace aka masa tarko. Suna fitowa da harbi suka fara cin karo, ya khaleel yay saurin komawa baya, yala6e jikin bango, saida yad'an lek'a sannan yay harbi, Yakuma komawa baya da Sauri yana rimtse ido, wancanma harbin yayo Yakoma ya la6e, haka sukaita Harbin juna har bullet d'in wancan yak'are. Amma babu Wanda aka sama. Ya khaleel ya fito, Ashe wancan Yakuma samun gun, yana fitowa yaron Moxies yafara ruwan harbi, wata sufa ya khaleel yayi akwance harya k'arasa Inda wancan yake ya tad'eshi da k'afa ya fad'i. Yay saurin harbinsa a cinya, shikuma yasaki k'ara. Blessing tayi masa wani duka ya durk'ushe k'asa. Cikin club d'in suka fito, ko INA a harmutse, kwalaben da kofuna duksun fashe, kowane table da kujera akwai Inda sukayi, babu kowa sai wad'anda suka samu raunikane kawai kwance, suma Duk yaran Moxies ne, sai kad'an da tsautsayi ya afkamawa. Kwashesu aketayi ana kaiwa mota. Ya khaleel yabi club d'in da kallo yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa. Ahankali saves dake 6oye yad'an lek'o da Kansa, yana ganin su ya khaleel Yakoma ya durk'ushe, dariya abin yabama khaleel amma baiyiba, yak'arasa Inda yake yasaka hannu ya jawosa, jikinsa sai 6ari yakeyi, ya had'e hannayensa alamar rok'o. Sakinsa khaleel yayi tareda jinjina masa👍🏻, yace, ''kayi k'ok'ari, thanks daka bamu had'inkai". Sai yanzu saves yad'anji sanyi, ya jinjinama khaleel kai, haryanzu dai a d'arare yake, dukda ya amince babu abinda zasu masa, Dan shine yabada dukkan bayanai akan Moxies, kwana uku kenan dasuka wuce ya khaleel yazo club d'in yay bincike. Bayan sun gama kwashesu suka fice, lokacin har garin yafara haske, harma an idar da sallar asuba. Kai tsaye setesion d'insu suka wuce dasu, duk aka zubasu inda yadace. Ma'aikatan daba nan suke kwanaba harsun fara isowa. Ya khaleel ya kalli agogonsa yana fad'in bara naje gida nayi wanka nai sallah asuba, bazan iya sallah da kayan nanba. Adams ya yunk'uro zaibi su rakashi kamar yanda suka saba, ya dakatar dashi. kai Adams idan akace kabini saika bini?, koka manta da nauyin dake kanmu wanda yafi komai muhimmanci, kaje tunda akwai mota hannunka, nima dagani sai ema zamu tafi, daya ajiyeni zaitafi gida. Idan nagama kwaje ku d'akkoni. Baijira cewar adams d'inba yashiga mota da ema ya bud'e masa. Yayinda adams ke binsa da kallo, wata k'aunar ogan nasa dakuma ganin kimarsa na k'aruwa a idonsa, tunda yake dashi baita6a ganinsa yana aikata wani abun asha ba arayuwarsa, mutumne mai tsananin rik'o da addininsa, baya wasa da dokar ALLAH, inhar kaga sallah takwacema ya khaleel to tabbas dolene, babu yanda zaiyine, kodai jikinsa babu tsarkin gabatar da sallar, kokuma bai yarda da tsarkin wajen daya tsinci kansaba. Ya ALLAH kabani ikon yin koyi da k'yawawan halin bawan ALLAHn nan, ALLAH ka kare manashi dadukkan wani sharri. Nace, "amin Adams". ********** Aysha Na tsaka da gyaran gidan, zeenatu Na tayata ya khaleel yashigo da sallama, har k'asa zeenatu ta tsugunna ta gaisheshi, ya amsa yana nufar d'akinsa, Aysha ma sannu da zuwa tamasa tana ajiye moper d'in hannunta tabi bayansa, zeenatu kuma tacigaba da aikin. Ad'aki ta iskeshi yana 6alle ma6allin rigarsa, warin giya da Aysha taji yanayi bak'aramin tada hankalinta yayiba, cikin kare hancinta da hannunta tace, " sadauki warin giyafa kakeyi? Dama kana shan giya?, atsorace take maganar, dan muryarta har rawa takeyi". Amatuk'ar d'aurewar fuska yajuyo yana kallonta, yazame rigar daga jikinsa yana fad'in bakisan inashan giyaba? Barama Na tabbatar miki!!", cikin tsawa yayi maganar. Har saida Aysha ta zabura baya. Shikuma yatako inda take, ya matseta ajikin bango, da hannu d'aya ya damk'o ha6arta yamatse da k'arfin tsiya, d'ayan hannun kuma yadafe bango. Saboda matsotan dayayi saitaji warin giyar Na hawa kanta, kamar zatayi amai, ga jikinta sai rawa yakeyi saboda yanda yazo gabanta a fusace, bakinsa yad'ora kan nata ya had'e da k'arfi saboda mugunta😏..............✍ 💓💓💓💓💓😍😍😍😍😍😍😍😍❤❤❤❤❤❤❤❤❤ *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) *_hummm bazaku ganeba, typing akwai wahala wlhy, wani lokacin kuma mutum yanada uzuri, muma mutanene kamar kowa, munada gida, munada yara, muna zuwa zuminci, munada miji, amma ahaka muke cire lokaci muyi typing d'in, duk da hakadai gazawarmu ake gani, ba'a ganin k'ok'arinmu, saikaji wasu nacewa ana musu Jan ajiaji ko wulak'anci ko yanga, humm kumana adalci mana, tun farkofa mu muka saka kammu, babu Wanda yasamu, wataranfa idan mutum yaga yana free har 2pages yi yakeyi arana, amma dukda haka inbakayi washe gariba sai anmaka maganar dazata sosa ranka, dukda dai nasan soyayyar dakuke manace take sakaku zumud'in son posting d'inmu._* _To ALLAH yabar k'auna, muna godiya. Amma please & please aringa amana uzuri_.💓💓💓💓💓❤❤❤🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀. 2⃣4⃣ Iya dai gurzuwa bakin Aysha ya gurzu wajen ya khaleel, Dan harda bak'ar mugunta yahad'a wajen kissing nata, saida ya tabbatar ta jigatu sannan yasaketa, cikin balla mata harara yabar wajen. Kuka Aysha tafashe dashi, "ALLAH saina had'aka da baffa nace giya kakesha, wataranama Baka kwana agida". Wandonsa ya ida cirewa, sannan yad'ago idanu ya kalleta, "k! Bakinki baya mutuwa ko?, aikam yau zaki tabbatar giyar nakesha d'in", zuwa yayi yasakama k'ofar key, baibi takantaba yashige toilet. Aysha tak'arasa jikin k'ofar tana jijjigawa, wai nufinta tagudu kafin yafito, amma ina ya kulle k'ofar ya cire key d'in, dawowatayi tana Neman key d'in, bata ganiba. Rasa yanda zatayi tai, sai kwarar da hawaye takeyi, tasan inhar yafito kashinta yabushe, dukda akan gaskiyarta take, aiba k'arya tayiba, warin giyar yakeyi. Tana nan tsaye tana sak'a wasik'ar jakai yafito sanye da rigar wanka, kallo d'aya yamata tana tsaye ya d'auke kai, babu ko kunya yacire rigar wankan yazauna zir dashi. Da sauri Aysha tasaka hannu tarufe fuskarta gaba d'aya, bakinsa yata6e, yad'auki body spry ya fesa yasaka doguwar farar riga, sallar asuba yarama. Saida Aysha taji alamun ya kabbara sallah tabud'e idonta, idanu tazaro waje, batareda tasan maganar ta su6uce mataba take, la'ila, harma sallah bakayiba?, tab lallai giya takai maka, hu'im, aikam tamkar agaban baffah akayi, saina fad'i komai👯‍♀. Atsanake yay sallarsa, yay addu'oi da azkar kamar yanda yasaba, tareda rok'on ubangiji gafara akan taushe hak'in lokacin sallah dayayi, bayan ya shafa yamik'e yanad'e abin sallar. Itadai Aysha tana tsaye kanta ak'asa, la66anta sai uban zugin azabar zafi sukeyi mata. Tana cikin tunaninta taji kawai anyi sama da ita, wutsil-wutsil tafara da k'afafu tana fad'in "wlhy nidai ka saukeni, ni ka saukine nace". Bai kulataba yajefata agado, shima ya haye, nauyin rabin jikinsa yasaki ajikinta, 🤣dak'yar Aysha ke numfashi, cikin huttai tace, " please ya khaleel wlhy kanada nauyi, karka fasamin ciki ALLAH kuwa". "Uhhm, mikike fad'a ina sallah d'azun". 'Yay maganar cikin d'aure face'. "nifa ALLAH bance komaiba, please wlhy zaka fasamin ciki". "yafashe mana ina ruwana, kedai bakinki bazebar rashin kunyaba ko? Wai miyasa bak'yajin maganane?". Tunzuro baki tayi gaba, " yo aidai kaima kasan gaskiya nafad'a, wlhy sanda kashigo warin giya kakeyi, kuma ba jiya kwalliya kaci kafitaba? ina kaje to?". "Kishinsa yagani k'uru-k'uru a cikin idanun Aysha, tana bashi mamaki yarinyarnan, ko kad'an bata tsoronsa, baisan miyasaba?". Ya dungure goshinta, tareda saka yatsansa ya d'alli bakinta, da sauri tadafe bakin tana zubar da kwallah. " shikenan, bakince zaki fad'ama baffah ba?, bara nahad'a da punishing d'inki saiki had'a duk kifad'a masa yamin hukunci". Kafin Aysha tayi wani yunk'uri ya janye hannunta...........🤫kundai san sauran basai an fad'aba. (Wlhy ya khaleel yacika wayo, shidai kawai yace yakwaso damuwarsa a club zai sauke kan Aysha, amma yake dojewa😂). ______________________________ *_Islands uk_* Hankali tashe Anty glory keta safa da marwa da waya a hannu, su Lola sunyi cirko-cirko kowanne fuska da damuwa, Lyn tayi k'arfin halin cewa, "shin wai Anty glo..... Mima yakai Moxies 9ja yanzu?, bayan kuma anfad'a masa anakama Anty Ruth a 9ja cikin wannan week d'in". " hum Lyn bakisan taurin kai da izza irinna moxies ba, shi yad'auki kowa wawa, ranar Saturday fa saida nasanar masa yahak'ura da zuwa 9ja, saboda jami'an tsaro suna farautarmu, ankama Alhaji bishasha da yaransa, hardama Lazarus, yanzu hakama Neman alhaji barau modibbo sukeyi, amma sai cemin yayi su sukaso, shifa birthday d'in joy k'awarsa zaije, nabashi shawara yabi mata kud'in jirgi tazo nan saimuyi amma dayake munafukine saiya zare jiki yatafi bansaniba, yamin k'aryan zaije America ". " yanzu haka cocaine yasiya yatafi da ita a6oye dankar musani, mai kwakwalwar kifi kawai". "Happy tace, " ALLAH ya k'ara masa, ni dama su tarwatsa Kansa da bullet jaki kawai". "Besi tayi dariya tana fad'in amma happy ked'in muguwace". Serah da Queen dai basuce komaiba. Anty glo ta zabga tsaki, " nifa Inda zasu kasheshin daidai kenan, kunsan bakin Moxies tamkar bututun mai yake, dayaji wahala wlhy tonamana asiri zaiyi". Sudukansu kallonta sukeyi a tsorace, Lola tace Mo.....ka cucemu wlhy, Anty yakamata kikira ko Anty kubra kisanarma, kokuma Anty Grass". "Hakane Lola kema kinzo da shawara". Grass tafara kira amma baijeba, tamaida akalar kiran kan kubra, bugu biyu tad'aga, bayan sun gaisa ta kwashe komai ta sanarma kubra. Hankalin kubra yayi masifar tashi, Dan itama jiya dak'yar tasha, wata mota taita binta abaya, shin wanene kemusu tsinci d'ai-d'aine haka?, kiran hajia khaltum tayi itama ta fad'a mata". ''Duk hatsabibancin hajia khaltum matsoraciyace, dandanan tagama rikicewa, tasaka driver yakaita gidansu ya khaleel, Dan aganinta zancen yawuce Na wayama.... 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀muje zuwa guys🤧. ___________________________ Ido sha6e-sha6e da hawaye Aysha tashiga wanka, bak'aramar mugunta ya khaleel yamataba wajen kusantarta, saida tayi nadamar yimasa maganar shan giyarnan, (tasan baikamata ta tambayeshi ta wannan sigarba, amma tanada dalilinta itama nayimasa wad'annan abubuwan), haka tahad'a ruwa a toilet d'insa tagasa jikinta, Dan yahanata key d'in bare taje d'akinta ta kimtsa. Shikam yana kwance akan gado idonsa a lumshe, zuciyarsa fal da tunanin Aysha da k'uruciyarta, akwai rashin kunya kuma akwai tsoro, saidai dauriyarta wajen k'ar6arsa yana sakashi jin tana burgeshi, sosai yake jinjinama k'ok'arinta wajen kar6ar uzurinsa aduk yanda yazo mata, yakanji tausayinta over, saboda tayi k'arama dayawa, shigarta bayi yasakashi bud'e lumsassun idanunsa. Ya furzar da iska abakinsa sannan yasakko daga gadon shima, toilet d'in yashiga, tana kwance cikin ruwa ta rufe idanunta, kallonta kawai yatsayayi, tabashi tausayi yanda take zubar da hawaye har yanzun, yasaki guntun murmushi sannan yashiga cikin ruwa. Da sauri tabud'e idanu tareda zabura zata tashi, yamaidata cikin ruwan, amma baice komaiba, itama shiru tayi takasa fitar, takoma ta lafe a k'irjinsa saboda rungumota dayayi, ahankali yake shafa gashin kanta idonsa a lumshe, duk suna cikin ruwan, d'uminsa na ratsa dukkan wata ga6a ta jikinsu. Kusan mimtuna 40 suka d'auka cikin ruwan, sanan sukayi wanka da taimakon ya khaleel, yanad'o Aysha a towel yafito, itadai tama kasa kallonsa saboda kunyakunya. (Nima nakasa kallonku saboda kunya gaskiya🙈). Dakansa ya shiryata cikin wata doguwar riga brown, mai kwalliyar fari d'ishi-d'ishi, tamata k'yau, har yanzun tana mamakin yanda yake zak'ulo kaya iri-iri yana bata tana sakawa, badai tayi maganaba saboda tsaro ba tsoroba😎. Bayan sungama kimtsawa yabud'e k'ofar, aii Aysha tarigashi fitowama, ta tarar zeenatu tafita, amma ankawo break fast an jera a dinning table. Tana cikin bud'e abincin yafito, dining d'in yak'araso, yaja kujera ya zauna, batareda ya kalletaba yace, "had'amin abinci yunwa nakeji". Yanda yay maganar yana wani cin d'aci sai abin yabama Aysha dariya, tasaki murmushin daya bayyana jerarrun hakwaranta farare tas, batace dashi komaiba tanufi kichin. Bin bayanta yayi da kallo shima yana murmushi, yana kallon sanda tasaki murmushin d'azun, bayansa ya jingina da kujerar yajawo wayarsa yakira Taheer. Babu dad'ewa yad'aga, suka gaisa. " hummm sannufa da k'ok'ari j!, kace jiya operation d'in dare kafita?, nakulafa mai email d'in sirrin nan dagaske yake taimakonmu zaiyi". "Hakane taheer, dama nace inhar muka kama mutum uku acikin sunayen biyar daya jero, tom tabbas da gaske yakeyi, amma ina mamakin waneneshi? Miyasa kuma ya 6oye mana kansa?". " hakane j, wlhy nima tambayar dakemin yawo kenan kullum arai, amma ko wayema insha ALLAH zai bayyana mana kansa k'ila anan gaba kad'an". "To ALLAH yasa". " Ameen to, kana inane?". "Ina gida wlhy, sallar asubahice ta kwacemin shine nakoma gida nayi wanka nayi, amma zuwa kamar 1 zanzo office, akwai wasu files dana sakama hannu please kad'auka ka kaima Oga, kaima Na ajiye wasu takaddu kad'aga k'ark'ashin files d'in da youseef yakawomin ranar Friday Na d'ora kwalin pen akansu, saika d'auka kadubasu, idan kagama kabama Solomon". "Ok, shikena saika shigo". "Ok". Duk agaban Aysha yayi wayar, jitake wani uban dad'i Na ratsata, tamkar ta taka rawa Dan murnar ganin aikinsu Na tafiya dai-dai, lallai bud'e email d'in sirrinnan bak'aramin sauk'ak'a musu aiki yayiba, ALLAH mungode maka, kubrah kece next😆, insha ALLAH". 'Tayi maganar tana dariya a zuciyarta'. Abincin tahad'a masa, yanda take komanta cikin nutsuwa da Jan aji sai ta burge ya khaleel, harya shagala da kallonta tun yana waya da taheer, harga ALLAH yanson mace mai nutsuwa, kai shi harma namijin, yanason mu'amulla da nutsatstsun mutane....... Sai magana take masa, tagama, amma yana wata duniyar, cikin mamaki Aysha tace, "naga ta kaina, mikuma ya khaleel yake tunani? Ko har yanzun giyar bata gama sakinsa bane?". Karaf sai a kunnensa, ya fesar da iskar bakinsa, sannan yakamo hannunta ya zaunar kan kujerar dake kusadashi, "A'eesha! Kalleni nan". Babu musu Aysha ta kallesa, amma bazata iya jure kallon tsakkiyar idonsaba, saboda kwarjinin dake cikinsu Na kamala da nutsuwa, tajanye idanunta akansa, amma dukkan hankalinta na kansa. " miyasa kika rainani wai?". "Lah nifa ba rainaka nayiba". " uyim to miye? Inba rainiba". "Shikenan to, kayi hak'uri bazan sakeba". Idanunsa ya lumshe, batareda da sake tankawaba yagyara zamansa, abincin yad'iba yakai bakinsa, lumshe ido yayi Dan dad'i, yasandai wannan girkin kodai mama kokuma Anty Mamie, Dan sune keciyar dasu bbinci mai dad'i da gamsarwa. Yad'iba yakai bakin Aysha, bata bud'e bakinba, saidai d'ago ido tayi ta kallesa, ya harareta, babu shiri tabud'e bakin azuba mata. Sallamar su mufeeda ne yasakasu d'ago ido suka kallesu, Aleeya da mufeedah ne, wadda Aleeya tamatsa sai an rakota wajen ya khaleel d'in sun gaisa, shine momy tasaka mufeeda ta rakota. Ya khaleel kallo d'aya yamusu ya d'auke kansa, yad'ibi abinci Yakai bakin Aysha, itako Dan kawai ta k'ulal da mufeeda takar6a a yangance. Aikam ba mufeeda kawaiba har Aleeya sak'on Aysha ya iso gareta, mufeeda falo taje ta zauna, bayan ta gaida ya khaleel da ko kallonta baiyiba, itakam Aleeya dining d'in tak'araso, taja kujera tazauna. Da mamaki Aysha take kallonta, ya khaleel baima nuna yasan da zamantaba. "my boo... Good morning". Maimakon shi ya amsa sai Aysha ce tace, " tofa, kajimin wani sabon salo, boo...kuma? Babbar magana, su gwaggo daga ina? Dan nikam kin wucemin Anty saidai gwaggo, Dan nakula kinkai haihuwar kamata". Bak'aramar dariya Aysha tabama ya khaleel ba, amma yadake bai yiba, sai guntun murmushi, yakula yarinyarna akwai rainin wayon tsiya, Ashe rainashin datayima k'aramin alhakine, inbanda wulak'anci dai yaza'ayi takalli Aleeya tace mata wau tama haifeta, kajifa iskanci, hardama kiranta gwaggo...... Tea d'in da Aleeya tad'auka agabansa tana sha wanda Aysha ta had'a masa yasakashi juyowa ya kalleta, tamasa fari da idanu. Janye idanunsa yayi yamaida kan Aysha, wadda tacika tayi fam daboda rainin wayon Aleeya, gashi Aleeya tak'i tanka maganar da Aysha tamata. Amma itama sai cakud'a maganar ayshan takeyi cikin zuciya, tarasa abin da zata cema Aysha ne shiyyasa taza6i yin shiru tashare maganar, batareda ta maida murtaniba, saidai tunani takeyi akan badai Aysha bace matar khaleel?. Wani tea d'in Aysha tahad'ama ya khaleel, batareda takuma kallon ko Aleeyar ba, yauce rana ta farko da Aysha tamasa Abu mafi mamaki, Wanda baita6a zaton tsaurin idonta yakai nanba, dukda hakan yasaka takuma birgeshi da k'ara kima a idonsa, domin ta nuna martabarta ta d'iya mace mai aure. Humm. Koda Aysha tagama had'a tea saita kar6i cokalin hannunsa, bai hanataba, yabata yanamai kallonta da mamaki fes a fuskarsa, soyake yaga mizatayi.... Baikai k'arshen tunaninsaba yaji lallausan tafin hannunta a face d'insa, kuma fuskarta d'aukeda murmushi, tad'age gira d'aya sama kamar yanda yakeyi sannan tazuba masa abinci abaki. Shikansa batareda yasaniba yabud'e bakin😂, Dan salon Aysha yagama kashe masa jiki murus. Aleeya dai da mufeeda kallonsu sukeyi cikeda bak'in ciki, har Aysha tagama ciyar da ya khaleel abinci, shima kuma yaciyar da ita dariya kuwa nata cinsa azuciya, wai wannan 'yar yarinyar tasan kishi. Kamar wasa aleeya takamo hannun ya khaleel, cikin shagwa6a tace, "haba my boo...wajenkafa Nazo mu gaisa, tunda kagama break fast d'in saika juyo aii muyi hira". "Kambu tak'ashin ubankiiii Aysha tafad'a azuciya, tayi kwafa aziciyarta tana fad'in yau zan nuna miki Na haddace karatun Anty glory Ashe, sannan inasamun ilimi wajansu Lola da Lyn. Kawai ya khaleel nashirin juyawa yama Aleeya tatas saikawai yaga Aysha bisa cinyarsa, kutttt🤥, baikai k'arshen mamakinsaba tafara shafa fuskarsa tana fad'in cool dawn Sadauki na, kasanfa 'ya'yan tasha ako ina sai sun nuna hali, naga ranka zai 6aci abanza akan shakatafin gwaggon nan, kwantarmin da hankalinka mana sadauki na", 'tayi maganar tana shafa k'irjinsa'. 🤣su ya khaleel an suma alkur'an. Lallausan murmushi yasakar mata Wanda bai shirya yinsaba, saidai kawai birgeshi datayi, ita kuwa Aysha ganin tasamu goyon bayansa saita kashe masa ido d'aya, zuciyarta Na dukan uku-ukun tsoron tahad'e bakinsa danata".🙀 Sassanyar Ajiyar zuciya kawai ya khaleel yasaki, aransa yace ya salam zata kasheni🤣. Kawai saiya bada kai bori yahau, yakuma tallafota da k'yau jikinsa suka cigaba da faranta ran juna😝. Mamaki yakama mufeeda dakecan falo tana hangosu, dama yarinyarnan haka take?. Aleeya kam aii mutuwar zaune tayi, tuni zuciyarta tafara tafarfasa kamar talgen tuwon dawa, dak'arfi tabuga table d'in dining waidan su tuna akwaifa mutane a falon, amma ina ko gezau basuyiba, su ya khaleel anyi nisan kiwo.🤭 Da sauri mufeeda tataso tazo takama hannun aleeya dake hawaye sukabar falon🤣🤣🤣. (ho Aleeya kinyi gamo da sholyn sadauki😹) Suna fita Aysha tacire bakinta dagana ya khaleel tana sauke numfashi, yunk'urin tashi tayi daga jikinsa, yay saurin janyota yamatse, murya awahalce yace, "aibaki isaba yarinya, zaki tadamin hanakiline abanza kigudu, kinci bulus kenan?". Hawaye Aysha tafarayi, "please ya khaleel wlhy bakina yakusa daina aiki, kaji kuwa zugin dayakemin, kaima baka iya con kwan makauniyaba, daga tayi saika nemi zarmewa acinye dakai". " koma miye kekika Sani, wayace ki kawo kanki". 'Yay maganar yana d'aukarta cak yanufi d'akinta'. Wutsil-wutsul taketayi da k'afafu da kukan bashi hak'uri, amma ko'a kwalar rigarsa. (Nikam bilynku dariya kamar ta karni🤣🤣🤣🤣, maganin sholy kenan aii, waya gaya mata barno gabas takene?, ta6o su ya khaleel aiba wasan yara baneba🤣🤣🤣, gashinan wajen maganin aleeya, ita ya khaleel zaiyi maganinta😆. gobema tak'ara aii.🤣 su ya khaleel ba'a gayyacesu bama sunzo🤧, bare ankawo musu goro🤐. ______________________________ Da kuka aleeya tashiga 6angaren Momy, babu kowa saisu kad'ai, Dan su husna suntafi makaranta, Momy kuma tatafi aiki bayan fitarsu. Lallashin Aleeya mufeeda taitayi. "Humm bazaki ganeba mufeey, waini yau wannan 'Yar yarinyar zatama bariki?, tasan koni wacece kuwa mufeey?, shi yarasa wadda zai aura sai wannan tatsitsiyar abar, miyagani to ajikinta? Ko farar fatar da wad'an nan kwala-kwalan idanun nata uwa Na mujiya?".🦉 " wlhy Anty aleeya muma ba k'aunarta mukeba, shima bawani sonta yakeba baffah ne yahad'a auren". "Baya sonta ya biye mata?". " lallai Anty aleeya, bakisan shaid'aniyar yarinyarcan baneba kawai, shiyyasa nak'agara ayi bikinku da ya khaleel kije ki gayarama shegiya zama, wlhy natsaneta itada uwarta, jinake kamar Na cinna musu wuta su k'one k'urmus wlhy". "Wayyo, dad'ina da gobe aii saurin zuwa, kubarni da ita, tunkan nashiga gidanma zan fara saitata narantse". " Yauwa auntynmu kina wuta wlhy hajiyata🔥🔥". Aleeya akayi wani far da ido ita an fasa mata kai. Hummm🐺 ____________________________ 🤣🤣🤣 Aysha ido yayi gwale-gwale, a hannunsa ya khaleel, yasha ALLAH ya Isa tafi cikin drom.🤣 Suna zaune afalo kowa yacanja shiga, kan Aysha abud'e tabarsa yasha iska, saiwata roba da k'aramin hanky a cinyarta tana d'ebo ruwan zafi aroba tamatse saita gasa bakinta, bak'aramin ciwo da rad'ad'i yake mataba, sai k'un k'uni takeyi kuwa, ya khaleel yana kwance a doguwar kujera yana kallonta, dariya sai cinsa takeyi arai yana dannewa. Zuwa can yatashi zaune yana fad'in, "zona taimaka miki Na gasa miki bakin". Harara ta balla masa,🙄 amma batace komaiba, tacigaba da gasawa tana hawayenta. Yataso yadawo kujerar datake zaune yana dariya k'asa-k'asa, wayyo harfa ya kumbura sholyna, kai sadauki baka k'yautaba, irin wannan aika-aika daka tafka". Ture hannunsa dake shafa la66anta tayi, takuma tunzuro bakin gaba, aii wlhy sai ALLAH ya sakamin, kaima za'ama 'yarkane". 'Tak'are da ziraro da hawaye'. Yanzukam sosai yake tuntsura dariya, aiko Aysha takuma k'ulewa tafashe da kuka🤣...........✍🏿 Wayace kikawo masa kanki sholy?.😆😆😆😂🤪 💓💓💓💓💓💓❤❤❤❤❤❤❤❤❤🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀. *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣5⃣ Dariya yakeyi sosai harda kwanciya, saida yayi mai isarsa sannan yad'ago yana kallon yanda take kuka tana cigaba da gasa bakinta. "Hhhhh wato nima za aima d'iyata?, kuttt aini 'yatama bazata biyo halinkiba yarinya, ita bazatama mijinta rashin kunyaba". " aikoda batayiba sai mijin yamata, Dan abinda babanta yamin ALLAH zai sakamin akanta". Wlhy yakula yarinyarnan kokad'an batada hankali, k'uruci dangin hauka kenan, kar6ar handky d'in yayi daga hannunta yana fad'in "to yanzu yaza'ayi nagoge laifina dankar nima ama d'iyata". Hararsa Aysha tayi, tace, " saika bani hak'uri alku'an, sannan kadainamin mugunta, kakuma fad'amin inda ka kwana jiya, saikuma waccan gwaggon tad'azun datajamin wahala wacece ita?". "Lallaima yarinya, wato jaridancinki akaina zai fara aiki kenan?, irin wad'annan tambayoyi haka? Wanne kikeso Na amsa aciki to?". Kuma turo bakin tayi, " tab duka mana, inkaki amsawa duka babu makawa sai anma 'Yar baba". "Tofa, wace 'Yar baba". "'Yarka mana, tunda bansan sunan dazaka saka mataba, saikawai nace 'Yar baba kafin lokacin". " uhhm hakane kumafa, to amma wazai haifamin 'yarne?". "Yo oho maka🙈". " a'a, miye najin kunyar to? Kefa kika fara maganar da kanki". "Nidai Dan ALLAH mubar wannan zance, kabani amsata". "Zanbaki amsarki aii, amma shima zancennan dolene muyishi, Dan nimafa baby's nakeso dawuri, amma ninaga kamar jiya bakiyi sallar magriba ba? Saikuma yau naganki normal, miya faru?". Fuskarta arufe har yanzu tace, " jiya d'innefa naji marata tafara ciwo, kuma duk lokacin dazayi Period inayi dama, nazata yazone shine nad'an dakata saboda yanamin wasa damacan, tom bayan fitarka kuma Dana duba sainaga normal nake, shine nacigaba da sallah na". "Amma yakama kije wajen doctor, Dan idan period yanama mace wasa wani lokacin infection ne, kokuma wata matsalar". Cikin zare ido Aysha tace, " a INA kasani?🤥. "Guntuwar dariya yayi, yace, ''INA ruwanki". Shiru Aysha tayi, Dan ita wlhy wani abun Na ya khaleel mamaki yake bata. Robar cinyarta ya sauke k'asa, yazame ya kwanta yad'ora kansa bisa cinyarta, dukda kujerar 2seat ce, amma haka yay manège. "Kinsan ina naje jiya?". " a'a, 'Aysha tafad'a da girgiza kai'. "Humm club Na kwana". Wata zabura tayi, had'eda ture kansa daga cinyarta, rankwashi yasakar mata akai, " kinutsu mana". Yay maganar yana hararta tareda maida kansa. Itakuma tadafe kai saboda zafi, mugu kawai, tafad'a zuciyarta. Amma afili batace komaiba. "Aikinefa yakaini, saboda abubuwan dasuka faruwa awajen yasakani warin giyarnan, amma mijinki baita6a jin koda d'and'anon giyaba aharshensa, ke ko Na sigari ma". _"A'eesha! Mutanene kawai basu fahimtaba, amma babu Abu mai saurin rusa rayuwa da ruguzata irin shaye-shaye, shaye-shaye na tarwatsa rayuwar mutum, zakiga inhar mutum yana shaye-shaye komai Na rayuwarsa ya durk'ushe, barakiji, shaye-shaye 6arna d'ayace dake jagorancin dukkan wata asara. Inhar mutum yana shaye-shaye zai iya aikata *zina* da uwarsa, k'anwarsa, yayarsa, surukarsa, k'anwar matarsa, yayarta. Zai iya fyad'e wa 'Yar wani, yarinya ko babba, domin baya tareda tunaninsa. Shaye-shaye yana saka mutum *sata*, zakiga inbasu samu kud'in dazasu shaba sunama iyayensu satar kud'i, kokuma sud'auki nawani, Dan burinsu bai wuce susami abinda zasu shaba yasakasu a wannan mayen. *Addinin* masu shaye-shaye yanada rauni, Dan wani lokacin za'ayi sallah suna cikin maye, basuda nutsuwar dazasuyi karatun Alkur'ani, basuda hankalin yin azkar Dan kariyar jikinsu, basuda lokacin yin azumin nafila Dan Neman lada, basuda nutsuwar tuna ubangijinma gaba d'aya, sai inbasa cikin maye, zakiga wasunsu akwai k'ok'arin sallah, amma inda ake samun matsalar wani lokacinma acikin mayen suke ibadar. mai shaye-shaye zai iya yin *shirka* yana cikin maye, awannan surutan nasu Na banza yayinda suke abuge zasu iya fad'ar duk abinda yazo bakinsu. Mai shaye-shaye, baisan darajar kowaba aduniya, harta da *iyayensa* dasukayi sanadin zuwansa duniya, Dan zai iya cin zarafinsu komai girman tsufansu kuwa, bazai ta6a tausaya musuba, Dan bashida cikakken tunanin tausayinsu, saidai idan sun ajiye yasace, gashi kullum yana cikin saka zukatansu bak'inciki da 6acin rai, alhalin fushin iyaye akan 'ya'ya bala'ine, amma shi baimasan yana kuskurenba ballantana yanemi gafararsu. Mai shaye-shaye zaki sameshi baisan ciwon kansaba, Dan bazai iya Neman nakansaba ballantana al'umma suyi tunanin amfana dashi watarana. Mai shaye-shaye koyayi ilimi saikinga ilimin yazama Na banza domin babu mai amfanuwa da iliminsa takowanne fanni. Mai shaye-shaye zakiga duk Inda yashiga ana tsangwamarsa, ba'ason zama dashima, babu maison abota fashi sai irinsa, babu mai wata k'yak'yk'yawar alak'a dashi koda acikin gidansune, babu mai damuwa dasakashi cikin al'amarin familie saboda bashida nutsuwar da za'a a samu k'aruwa dashi koda a shawarane. Mai shaye-shaye zakiga ko iyalinsa k'yamarsa sukeji, kokuma mijinta baya sonta, ke idanma macece da mijinta yasani zai iya sakinta nan take, idan budurwace tarasa mijin aure, namijinma akan raba aure, idan kuma saurayine babu mai bashi 'yarsa, saidai k'addara, zakiga 'ya'yan irin wad'annan suna girma cikin bak'inciki da tsanar iyayensu azukatansu, Dan basu barmusu wani tarihin dazasuyi alfahari dashiba harsu bigi k'irji wajen kwarmanta ahalinsu acikin k'awaye ko abokai. Mai shaye-shaye zakiga k'arshensa mutuwace abola, bayan mutuwar tasa kuma babu Wanda zai damu da tattauna wani abun alkairi NASA da mala'iku zasuyi guzurin tafiya dashi yayinda ruhinsa ya Isa wajen ubangiji, babu mai bak'incikin mutuwarsa Dan bai amfanama al'umma komaiba, baima amfani rayuwarsaba ballantana tawaninsa. Mai shaye-shaye kulum lafiyarsa raunine da ita, gashi cikin k'angin rayuwa Na k'ila wak'ala, Dan ciwuwukane zasuma dukkan illahirin jikinsa dafifi takowacce ga6a, ciwon huhu. Hanta, kansa, olsa, dadai sauransu. ga d'umbin zunubi wajen ubangiji, Dan wlhy bazai k'yalekaba, tunda bai halliceka dankazo kayi shaye-shaye ba, ya haliccekane danka bauta masa, yamaka dukkan Ni'ima amma kagaza gode masa, duk duniya babu Addinin dayake goyon bayan shaye-shaye, saidai son zuciya yasakamu aikatawa"._ ''To kinga Dan ALLAH miye ribar shaye-shaye gamai hankali?". Gashi idan suka fara dawuya kiga sun bari, sai k'alilan wad'anda ALLAH ya tsame, zakiga mai shaye-shaye yanata cewa gobe, jibi, gata, duk zai bari, amma saiya kasa iya Barin saboda kururuwar shaid'an dake jagorancin rayuwarsa. Kinga maganin ayi aikarma afara kenan, ALLAH dai ka shirirya mana zuri'a, ka tsaremu daga rikicin duniya da k'yale-kyalen cikinta. Aysha tashare hawayenta, tace, "ameen sadaukina, wlhy maganarka gaskiyace, kuma tanakan turba, nagodema ALLAH dazan kasance ak'ark'ashin jagorancinka, 'ya'yana su kasance bisa Jan zaren tarbiyyar mahaifi mai kamala da mutunci irinka, kayi hak'uri da zargin Dana maka, wlhy hankalinane yatashi ajiyan kawai, Dan nima banason shaye-shaye ko kad'an wlhy😭🙏🏻". Mirmushi yayi yana lumshe idanu, aransa yace, " wataran tayi abun hankali, wataran namasu k'uruciya", Yakama hannayenta ya sumbata, ''karki damu kinji sholyna, Na fahimceki nima, kuma haka yakamata mace takasance akoda yaushe, tazama mai tuhumar mijinta intaga wani Abu dabai gamshetaba, Dan miji yana taka matsayi iri dayawane, miji ubane tawani fannin, miji yayane tawani fannin, miji abokine tawani fannin, miji d'an uwane tawani fannin, miji aminine tawani fannin, miji surukine tawani fannin". " zaki iya tsoronsa (kamar yanda ake tsoron iyaye), zaki iya abota dashi (domin shawara da koyin halayensa Na kirki, Dan yawanci mutane sukan koyi abun kirki kona banzane daga abokansu), zaki iya kallonsa amatsayin yayanki (idan yamiki fad'a ko hukunci kiyi hak'uri kamar yanda yayanki zaimiki kiyi hak'uri), zaki iya kallonsa amatsayin amini (domin bashi sirrinki saboda yarda dashi), zaki iya kallonsa amatsayin suruki (domin jin kunyar yin wani Abu agabansa, kojin nauyin yasan kina aikata wani mummunar halayya), zaki iya kallonsa amatsayin d'an uwanki (domin yad'ebe miki kewar ahalinki yayinda sukayi nisa dake, ko mutuwa tarabaku, kowata k'addara tarayuwa datakan riski bawansa) kuma ki kallesa amatsayin miji, (abokin jin dad'inki, da kauda k'ishirwarki, mai yalwata farincikinki. Mai sakaki kuka, mai sakaki dariya, wataranama harya sakaki bak'inciki, tunda zaman tare yawuce wasa, musammanma Na aure dayafi komai dad'ewa aduniya)". "Inhar mace zata kalli miji tawannan fannonin daban-daban, shima miji ya kalli matarsa ta irin wannan fannonin, to tabbasa zaku gina rayuwar aure mai inganci da k'arko, harma wasu suringa alfahari daku dason koyi da zamanku kuwa". "Sadauki na kai d'infa nadabanne wlhy, kamata yayi abaka shugabancin k'asa gaba d'aya wlhy". Harara ya zabga mata, "amma nakula yarinyarnan bakida kai, aii ko'a mafarki bana fatan kasancewa awannan matsayinma, sarautar gidana ta isheni". Dariya Aysha tayi, tace, " matsoraci, kaidai kanamin bak'incikin zama first lady kawai". Tashi yayi zaune, yad'auki filo ya kwala mata akai, "kinamin rashin kunyar zanwani zama shigaban k'asa, angaya miki haka first lady sukene?". Dariya Aysha tashigayi tana karewa, ganin yak'i bari itama tajawo filon tana dukansa, haka sukaita wurgama juna filulluka, duk suka hargitse falon, daga k'arshe Aysha tagudu d'aki ta kulle kanta, dariya sosai ya khaleel yayi, sannan yay alwala yafice sallah saboda kiran azhur da'akayi. _____________________________ Akid'ime hajia khaltum tashigo 6angaren momy, bayan driver ya ajiyeta, ALLAH yasotama babu kowa agidan, masu aiki sun fita, yara suntafi makaranta, Ammah ce kawai sai su mufeedah, Anty Mamie da mama sunje wani gidan abokin baffah da akayi haihu. Ammah kuma ma barcinta takesha. Masu aiki kuwa suna 6angarensu. Gwaggo bintu kawai tawuce afalo tana kallo, itakam batada Matsala dan ita tasuce. Yanda tashigo arikice yasaka mufeedah da Aleeya tsorata, saida sukaga itace suka sauke ajiyar zuciya. Gaidata sukayi, mufeedah Na k'ok'arin kawo mata ruwa ta dakatar da ita. ''Ina aminiya mufeedah?". "Lah Ammi, kinmanta yau akwai aiki?, tafita wajen aiki aii tunda safe". Dafe kai hajia khaletum tayi, Dan bataso hakaba. " lafiya kuwa dai Ammi?, a'a babu damuwa, bara naje zan dawo anjima". "To ki gaida mana su Salma". Ko amsa bata bama mufeedah ba tafice abinta. Gaba d'aya arikice take, amotama sai zabga tsaki takeyi, shi driver ma har abin ya ishesa, amma babu yanda zaiyi. ______________________________ Ya kahleel yana dawowa sallah bai nemi ayshaba yashiga d'akinsa yashirya cikin k'ananun kaya, amma bak'ar rigarsa ansaka police abaya da gaba, yayi k'yau sosai, yad'an saka turare yafito. Aysha natsaye jikin wardrobe yashigo, daina abinda takeyi tayi tajuyo tana kallonsa da mamakin ina zaije da ranarnan?. " bara naje office, saina dawo". "Amma office yanzu da rana?". ''To yaza'ayi, yazama tilas aii, badanma naje aikin dareba aida tuni ina office, ina 6ata lokacin saina dawo, yafita da Sauri". " hummm kajimin ya khaleel d'inan, kaika tafi aiki, nikuma ka kashemin zuwa nawa, sai k'arya nakira Na zabga banida lafiya, Afrah harda cewa zatazo dubani, ALLAH ya shiryeka to". 'Tafad'a tana cigaba da aikinta'. ******** Ashe su Ema.. Suna jiransa awaje, yana fita sukayi salute nashi tamkar yanda suka saba, aka bud'e masa mota yashiga. Ema da Adams sunata hira k'asa-k'asa dan sunsan boss bayason surutu, har suka Isa kuwa idonsa a lumshe, babu abinda yake tunanin sai matarsa, da yanda take kwantar masa da hankali, dukda wani lokacin yakan kalli al'amuranta amatsayin k'uruciya hakan baihanashi ganin kimarta da k'arin darajar datake samu a zuciyarsaba, wani sashe na zuciyarsa yakan k'awata girman nata har dak'arin wani matsayi daharyau baigama amincewa zuciyarsaba akan zamansa gaskiya. Koda suka isa saida Adams yasanar masa anzo sannan yadawo duniyar mutane, amma da tunanin yad'aukesa zuwa wata duniya tadaban. Kai tsaye office d'insa yashiga, Adams yatake masa baya da tarkacensa. Har Adams zai fita bayan ya ajiye kayan yace yadawo suyi magana. Zama Adams yayi zuciyarsa Na d'ar-d'ar, dan baisan mi ogan zaice dashiba, tunda yasan yanada laifi jiya, kuma boss bawai yak'yaleshi baneba. Saida ya khaleel yagama abubuwan dayakeyi, irinsu kunna laptop da d'an bincika wasu files da aka ajiye masa baisan dasuba, bayan yagama yad'ago ya kalli Adams d'in dayay shiru. "Adams kasan miyasa nace katsaya?". " a'a sir". "Hummm kuskuren dakaso tafkawa adaren jiya, inamaka kallone amatsayin su Ramadan, yanda bazanso k'annena su lalaceba haka bazanso rugujewar taka rayuwarba, karka yarda rud'un duniya yasakaka Neman mata ko shaye-shaye, dukda na yarda dakai nikam, tunda ban ta6a kamaka da wani abun ashaba, amma nasan halin rayuwa, wani abun kan canja rayuwar wani, musamman ma wannan aikin namu dakan kaimu wajaje daban-daban acikin duniya, kuma cikin k'azaman mutane masu aikata duk laifin da ake gudu, ajiya kad'an yarage a afkaka nasani, ALLAH ne yatak'aita abun ina kusa". " shawarar dazan baka shine, inkasan bazaka iya jurewaba kayi aure, kanada shekaru kusa 28 yanzu aduniya, kayi aure kawai kaji, karka bari rayuwarka taruguje abanza, bana fatan haka, idan bakada lokacin za6ar matarne, kokuma baka samu wacce tamakaba kashirya kaje gidanmu, inada k'anne 'yammata, kaza6i wacce Tamaka aciki, idan babu wacce tamaka kasanarmin karka cuci kanka, zan sake sakawa alalubamaka wasu". "Ba nemankai nake da k'annenaba, bakuma dansun rasa mazajen aureba, a'a Nafi sanin nagartarsune fiyeda wadda zan samo maka awaje, dansu nasan tarbiyyar iyayenmuce dani nan, idankuma kanada wadda kakeso fine, zanyi farin ciki dahakan, danka samo za6inka". Hawaye suka cika idon Adams, yanzu nan har k'aunar da oga kemasa yakai yaso had'a jini dashi? Yabasa damar zuwa yaza6i matar aure cikin k'annensa jininsa, hawayen suka zubo akumatunsa, yad'ago yana kallon khaleel, bansan mizance makaba Oga, kalaman bakina sunyi k'aranci fad'e agareka, yanzu nan har can cantata takai kabani damar za6en abokiyar rayuwa cikin jininka?, Oga wace k'auna kakemin haka aduniyarnan?, ni Adams mizan biya wannan bawa dashine?, bayan jana dayayi ajiki, ya fifitani sama dakowa cikin nak'asa dashi, sannan kullum yake controling d'in zaran tarbiyyata danna zama nagartacce, yabani Dana wajen koyan k'yawawan halayensa, sannan yanzu yamin k'auta da abu mafi mutunci da nagarta, Oga ALLAH yabiyaka kawai, bazan gusheba ina maka add'ua har k'arshen numfashina nag......... "A'a Adams bana buk'atar godiya, kacancanci fiyema dahaka daga gareni, inason nutsatsten mutum mai tarbiyyar arayuwata, wannan yasa k'aunarka ta tasirantu azuciyar Ibraheem Abdallah, k'yawun tarbiyyarka yasakani yima d'aya daga cikin k'annena sha'awar zamowa mata agareka, danhaka kayi shiru kawai, kafara zuwa gidan Kaduba tukunna, inhar babu wadda Tamaka karka tauye kanka saboda kunyata, dan nafad'a maka yanda bazan cutar dasu musleem ba, haka kaima bazan cutar dakaiba". ALLAH ya za6a abinda yafi alkairi, tashi kaje kawai, banaso kasake cemin komai amaganar". " shikenan ago, amma akwai yaranfa da'aka kama d'innan agidanka, naga tsawon sati biyu kenan amma bakace komaiba". "O shit, wlhy kagafa namanta Adams, kasan bubuwan sunma kaina yawa, kaikuma saibaka tunaminba". " sorry sir!, wlhy nazata kana sanene, tunda naga kadawo aiki jingim akanka shiyyasa nayi shiru, tonaji ko magarsu bakaminba shiyyasama namaka yanzu". "ALLAH ya k'yauta, muje yanzu nagansu kona mintuna 15 ne". "OK sir!". "'Dakin da aka kaisu Adams yabud'e suka shiga"................✍ ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤💓💓💓💓💓💓💓💓🤸🏻‍♀ina yinkufa.😂 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣6⃣ Duk sun fita hayyacinsu, dukda bawanima wahala aka basuba, saboda ya khaleel baice komai akansuba tunda aka kawosu wajen. Fitulun da aka kunna yasakasu kare idanunsu da hannu, kunsan idan mutum yadad'e acikin duhu yaga haske aii. 'Daya bayan d'aya ya khaleel kebinsu da kallo, saida yagama nazarinsu baki d'aya sannan yaxauna bisa kujerar da Adams ya ajiye masa, crossing k'afafunsa yayi, tareda hard'e hannayensa a k'irji, fuskarnan d'am-d'am take babu alamar yasan miye dariya. Ya d'auke idonsa akansu, cikin murya mai tsoratarwa yace, "wanenen oganku?!". Cikin rawar jiki d'aya ya nuna gwaska. d'age gira ya khaleel yayi yana kallon gwaska sama da k'asa, " wanene kai? Waya turoka gidana?". "Babu". 'Gwaska yafad'a yana wani ciccijewa'. "hum d'an samari kafad'a cikin sauk'i kawai, inba hakaba zakayi nadamar yima Ibraheem Abdallah taurinkai, zan maimaita maka sau uku tak, wanene ya turoka gidana?!!". Shiru gwaska bai amsaba. Ya khaleel yakuma maimaitawa, nanma yay shiru, kafin ya khaleel yafad'i Na ukun Adams yace, ''karufama kanka asiri kafad'a, karka bari yafad'i na uku wlhy, zakayi nadamar dabaka ta6a yin irinsab....... Hannu ya khaleel yad'aga ma Adams alamar yayi shiru..... Shiru kuwa Adams yayi, ya khaleel yamik'e tsaye yana takawa ahankali, takalmansa na k'ara, saida yagama zagayesu sannan cikin k'araji Yace, "wanene yaturoku gidana nace?!!!!!!!". Duk saida suka razana saboda azababbiyar k'arar da khaleel yayi, har bangon d'akin Na amsawa kuwa. Har wani acikinsu yad'aga hannu zaiyi magana gwaska ya tsaidashi, cikin sauri yace, "matar babankace". Shiru khaleel yayi yana kallonsa, kamar bazaiyi maganaba, saikuma yace, "wace acikinsu?". " hajia Bilkeesu ". Wani kallon bakada hankali amma ya khaleel yamasa, iska yafurzar daga bakinsa, ya taka k'afar gwaska da k'arfi, har saida tayi k'ara alamar yasamu targad'e ko tsagewar kashi, " inhar baka fad'aminba, haka zantabin ga6o6in jikinka ina karyasu d'aya bayan d'aya, kwanaki ✌🏻 nabaka kacal". Yakuma taka k'afar yafice abinsa, gwaska kuma yasaki k'ara yana rik'eda k'afarsa ta dama da ya khaleel yataka. Duk tsoro kama sauran yaransa yayi, lallai yau sunga maza ba mazare ba. Kashe fitulun Adams yayi yafice shima da sauri. _______________________________ Aysha Na idar da sallar azhur tafito falo, Dan tun tana sallah takejin ana kwad'a sallama. Idanu tazaro waje, tareda daka tsalle ta rungume Afrah, ''ALLAH nazata dawasa kikeyifa". Dariya Afrah tayi tana rik'e ha6a, "oke Aysha Dama k'alau kike kika zabga k'arya?". Kichin Aysha tanufa tana dariya, " kinga ajiye zancen nadawo tukunna". "Tom jeki dawo".. Ahankali afrah takebin hotunan Aysha Dana ya khaleel dake falon da kallo. Aranta tana jinjina dacewar da ma'auratan biyu sukayi. Mintuna k'alilan saiga Ayshan tadawo, ta ajiye tiren hannunta gaban Afrah. " humm k'awata bismillah, towai harma kintashi aikine? Naganki yanzu". "Inafa, hankalinane yatashi nace baradai nafara ganinki sannan, da k'yarma nasamu Oga yabarni wlhy. Ina angon namu to?". "Wlhy yanzunnan yafita, shinema yahanani zuwa aiki saboda yana gida, shiyyasa nayi k'aryar banida lfy fa". Dariya Afrah tayi, " a lallai. Soyayya ruwan Zuma, mumafa baradai muyi aurennan". "ALLAH ya shiryaki, aigara kuyi musha biki to". Nan suka zauna sukasha hirarsu, har bayan la'asar sannan Afrah tatafi. Alkairi mai yawa Aysha tamata kuwa. ___________________________ Da yamma lik'is hajia babba tadawo gidan, yawancin yaran duk suna babban falo, kowa da uzurin dayakeyi, kamar yanda suka saba suka gaidata. Ad'age ta amsa musu da nuna halin ko inkula agaresu. Sinrigada sun saba da hakan, shiyyasa babu Wanda yadamu, suka cigaba da harkar gabansu. A 6angarenta kuwa Aleeya tazo ta rungumeta, tana mata oyoyo, cikin washe baki hajia babba ke amsawa. 'Dakinta tanufa danta watsa ruwa, Aleeya kuma takoma ta zauna tsakiyarsu hasnah dake tura mata pictures d'in ya khaleel a system d'inta. ******** Ana tsaka da sallar magriba saiga hajia khaltum, ta Tara's hajia babba Na sallah, dan haka ta zauna abakin gadonta tana jira ta idar. Tanayin sallama kuwa babu zancen addu'a tace, "aminiya lfy kuwa yanzu da magriba?". " inafa lfy, tunda safe nake Neman wayarki switch up, nazo gidannan ance kinje aiiki, Na aiko Baby tace baki dawoba". "Kinsan idan ina wajen aiki bana kunna waya wani lokacin. Amma dukma miye makasudin neman?". " takusa tatashi damune, Dan jiya ankama Moxies a club, kuma yanzunnan ake tabbatarmin Oga barau yana hannu". "Innalillahi, aminiya Dan ALLAH karki saka hawan jinina tashi, Dan ALLAH wasa ko gaske?". "Dan ALLAH karki bani haushi mana, mizaisa nayi wasa dake akan wannan maganar, Hajia laura maganar gaskiya nakai mak'urar rud'ewa, barin k'asarnan zanyi nikam". " kamarya zaki bar k'asa? Kina tunanin hakan zaisa ki tsira?, aminiya zokiji miye mafita kawai". Da sauri hajia khaltum tamik'a kunnenta, hajia babba ta fad'a mata, gumi hajia khaltum ta yarfe, yauwa aminiya kokefa, tuntuni nike baki shawararnan kink'i yarda, kina Neman biyema tausayi waidan kinsha wahala kansa, idan kinbiyema wannan wlhy saiya k'arar damu mud'in". Aiyanzu Na amince, ki saurareni zan shirya komai a Daren yau. Shikenan, da safe zan aiko baby da sak'on". "OK shikenan". ____________________________ Yau ya khaleel bai dawo gidanba sai bayan sallar isha'i, bai tadda Aysha a faloba, danhaka yawuce d'akinsa, kayansa ya cire ya canja da jallabiya, sannan yadawo falon, kusan tare suka fito da Aysha. " Ashe kadawo?". Kansa kawai ya jinjina mata amma baiyi maganaba. Bata damuba, Dan yanzu tagama fahimyar wasu daga cikin halayensa, bako yaushe yakeson wasaba, komai yana basa lokacinsane. Afalo ya zauna, itakuma tawuce kichin, fruits ta had'o masa da ruwa, harta ajiye bai kalletaba, idonsa nakan TV yana kallon wani labari da akeyi a ait, labarin yad'auki hankalinsa matuk'a, wasu mutanene aka kama a Lagos bayan gari da k'ananun yara, amma sunce 'ya'yansune, shine mutane suketa fad'ar albarkatun bakinsu. Ganin hankalinsa a TV sai itama Aysha tanutsu tana kallo, batasan tafurta kuttt melesi Talatuwa!. Da sauri ya khaleel yadawo da kallonsa kanta, " kin santane?", gaban Aysha ne yafad'i datagano 6arin bakin datayi. Tsawa yadaka mata, "wai badake nakebane?". " da k'yar ta had'iye yawu tana jinjina masa kai". Tsura mata idanu yayi yana nazarinta, shifa lamarin yarinyarnan yana birkita tunaninsa watarana wlhy, tamaka abun marasa gaskiya, tamaka namai k'uruciya, tamaka Namai hankali, why?". Kamo hannunta yayi ya zaunar gefensa, "A'eesha kinga fad'amin a ina kika santa?". ''Aii itad'in mai aikin hajia khaltum ce, matar dake zuwa gidannan wajen momy". " wajen momy?!". 'Yafad'a da mamaki a maganar tasa'. Aysha ta jinjina kai batareda ta tankaba. "Shikenan.... shikenan..... Yanzu kiyi shiru da bakinki, amma inason kimin wani aiiki gobe idan ALLAH ya kaimu". "aikinmi". "Ki shirya bayan kin taso aiki, Zeenatu zata rakaki kuje gidan hajia khaltum, kiyi komai cikin nazari, kije mata amatsayin kinzo gaisheta saboda amintarsu da momy, daganan kiyi k'ok'arin aiken mai akinta d'aya siyen kati, nikuma zan k'arasa sauran aiki". "OK ALLAH ya kaimu, amma baka tunanin zasuyi zargin wani Abu". "A'a karki damu, nasan kinada wayo A'eesha zaki iya bin komai cikin tsari. Karki damu zeenatu tana tare dake". Kai Aysha ta jinjina masa. " Yamik'e da sari, ina zuwa, bara naga baffah". "To saika dawo". ____________________________ Afalo ya khaleel ya iske baffah da mujahedeen suna lissafi, Dan shima yana aikine a company d'in baffah Na center rog. Gefe ya zauna suka mammala, sannan suka gaisa da mujahedeen, yafice. Ya khaleel yadawo kusada baffah suka gaisa, suka d'an tattauna akan aikinsa dakuma rayuwa. " baffah mizai hana kasaka Ramadan da Zunnurain da mufeedah harma dasu Amal su fidda mazajen aure da matan aure?". Murmushinsu Na manya baffa yayi, zuciyarsa fari tas daganin d'annasa ya girma, tunda har yake tunanin gina rayuwar k'annensa. Hannu yasa ya shafa kansa, yana fad'in "ALLAH Na gode maka, mu'azzam yazama babban mutum, wannan shawarar taka tasakani farinciki, kuma Na gamsu da ita, inason gobe idan ALLAH ya kaimu katara taron familie sai a tattauna akan hakan, mukumaji ra'ayinsu". "To baffah ngd sosai". "Bakomai mu'azzam". Sund'an ta6a hira sannan ya khaleel yataho saboda zuwan mama, Dan yau itace da baffan. Saida suka gaisa da ita sannan yafito. 6angaren Ammah yaje itama suka gaisa, sun tattauna akan shawarar auren k'annen nasa da ita, taji dad'i kuwa sosai, taita saka masa albarka. ****** Harya doshi 6angaren momy saikuma yafasa, zai juya saikuma yaga bai dace saboda wataba yahana kansa neman lada, juyawa yayi yashiga. Duk suna falo, amma babu momy, Aleeya tamkar taita rawa haka taji, Dan jin dad'in ganinsa, k'annensa duk suka gaidashi, batareda ya amsaba yace, " momyfa?". "Tana d'akinta cewar husnah". Aleeya Na zumud'in ganinsa amma ko kallo bata isheshiba yashiga d'akin momy, yanda yatarar da ita sai abin yabasa mamaki. Ita bama tasan yashigoba, saboda tayi nisa a duniyar tunani. Saida ya girgiza hannunta sannan tadawo hayyacinta, "ibra....I...Ibrahim! Kaine?". " eh momy nine, lfy kuwa? Mike damunkine?". Murmushin yak'e tayi, tace, "babu komai khaleel". Mamaki takuma bashi, Dan baita6a jin takirasa da khaleel ba. " momy please, kifad'amin mana, koban cancanci sanin damuwarki bane". "A'a Ibrahim, dama akan auren mufeedah ne, naji haryanzu alhaji baice komaiba, kodai Baka masa maganarbane?". ''Yanzunnanma muka gama maganar dashi, amma momy har yanzu tana fitar darenne?". " batayi, amma hankalina bai kwantaba, tunda kaga tana zuwa aiki aii". ''Hakane, ki kwantar da hankalinki kawai, insha ALLAH kwanannan za'a aurar dasu, sainake ganinma kamar ahad'a dasu hasnah, sa k'arasa karatun kawai a gidajensu". "Hakane, amma agama nasu mufeedar tukunna kaji". "Shikenan momy, duk yanda kikeso haka za'ayi, Dan ALLAH Ki kwantarmin da hankalinki, banason ganin damuwarki kokad'an wlhy". ''Kafad'arsa tadafa tana murmushin dayafi kuka ciwo, karka damu farinciki na bari kaji, ya matar taka?". " cikin mamaki ya amsa da lafiyarta lau momy". ''To ka gaidamin ita, tashi kaje kartaga kadad'e". ''Amma momy hirafa nazo gun Aleeyarki". "A'a barta kawai, kaje gun matarka". Kansa kawai ya jinjina yatashi, k'asan zuciyarsa tana mamakin wanann salo Na momy yau. Batareda ya kula Aleeya dake tsaye tana jiransa a wajeba yashige 6angarensu. Haushi Yakama Aleeya, tana kuma tsoron binsa yaje ya dizgata gaban waccan mara kunyar matar tasa, kosu kamayin abinda zai tsaga💔 zuciyarta abanza. ******* Iskewa yayi har Aysha tayi barci, shima shirin barcin yayi yakwanta tareda rungume matarsa, suka Lula duniyar barci.💞💞💞. *_Bayan kwanaki uku_* Aysha taje gidan hajia khaltum, tama iske bata nan, Alhmdllh sun gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali kamar yanda ya khaleel ya tsara mata. Bayan ta aiki mai aikinsu siyen credit, tana fitowa Samuel ya satota kamar yanda ya khaleel yasakashi. Su Aysha suka gaji dajiranta sukamusu sallama suka taho, har baby da Salma suna bama Aysha hak'uri, dacewa dama halintane, idan aka aiketa saita gama iskancinta take dawowa. Aysha tace babu komai wlhy, dama zata saka katinne takira hajia khaltum, amma idan takawo su saisu amsa suyi amfani dashi. Har harabar gidan suka rakota itada zeenatu, (nafa nakulafa kamar itama da wani bayani tartare da ita🤭). ****** Hakama an gudanar da taron familie kamar yanda baffah yafad'a, duk antanbayi kowanne za6insa, wasu daga cikinsu sunkawo za6in nasu, kamar mufeedah, Zunnurain, Ramadan, Hamdiyya, Shahudah, amma Naseeba da Amal basu kawoba, anan take ya khaleel ya yanke hukuncin Amal yabama Adams, Naseeba kuma ta yarda da Jabeer d'an wan mamansu, kamar yanda Maman nasu tabuk'ata tuntuni, amma Naseebar ta tirje saboda soyayyar ya khaleel data sakama ranta. Amma yanzu kam babu yanda zatayi ta amince, tunda taga mafarkinta bazai kasance gaskiyaba. Saidai tasha kuka itada Amal, amma su shahudah sukaita lallashinsu. Mufeedah kam sai rawarkai akeyi za'a auri muradin rai, Ameenuddin, Wanda suka dad'e suna soyayya, amma yanzu yana Sudan ne yana karatunsa, shima d'annan anguwarsune, mutumin kirki nutsatstse ma kuwa. Baffah yabama dukkan samarin damar turo magabatansu, sannan su Ramadan ma ankai gaisuwarsu gidan 'yan matansu. ***** A kwanaki ukunnan komai yagama kammala, aka tsaida biki watanni uku da sati biyu kacal😄. Saimuce ALLAH ya kaimu lfy to. _____________ Kasancewar yau Saturday babu aiki, kowa yana gida, wajen 9am ya khaleel yashiga gaida momy, Momy kad'ai da husnah yatarar afalon yazauna yana gaida momy cikin girmamawa, husnah ma ta gaidashi. Momy ta kalli ya khaleel tace, "aikam kazo a dai-dai, ALLAH yasadai baka karyaba?". " tofa momyna uwa mai dad'i, miya farune? ban karyaba kuwa, tashina kenan daga barcima nayi brosh nafito gaidaku". Momy tayi masifar washe baki kuwa, Alhmdllh, yau saboda kai nashiga kichin da kaina, mutuminka nayi Alkubus, Mashi'a!!. takwalama mai aikinta kira, wadda taware cikin 'yan aikin gidan. Murmushi ya khaleel yayi, "wayyo momyna ALLAH yak'ara yawancin kwana, yanzunan saboda ni kika wahalar da kanki?". Dariya kawai momy tayi amma batace komaiba, saboda zuwan Mashi'ah. ''Yauwa mashi'ah, ina abincin khaleel danace ki ajiye min?". "Yana kicin hajia". " to d'akko masa". Babu dad'ewa mashi'ah tazo ta shirya abinci gaban ya khaleel, takoma kichin, tana shiga ta rushe da kuka, nashiga uku ni mashi'ah, yanzunan ina kallo za'ayi kisan kai?". "Kai. Bazai yuwuba, dolene Na ku6tar da bawan ALLAH nan, mutumin kirki dashi, kodai nafad'ama momy maganin kashe d'anta hajia khaltum tabata, kai fad'ar hakan matsalane". Gabanta yay mummunar fad'uwa data tuna zaifa iya faracin abincin yanzunnan, da sauri tafito daga kichin d'in zuwa falo................✍ *_tofa masu karatu, yaya zata kasance idan ya khaleel yaci abincinnan?, miyasa hajia khaltum tabama momy guba amatsayin maganin gusarma ya khaleel hankali akansu? Shin momy tasan gubace kokuwa?._* Kucigaba da kasancewa da d'iyar baba iro danjin cakwakiyar dazata cigaba da faruwa, Dan alamomin tonuwar asirifa sun fara bayyana🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀. 💓💓💓💓💓💓💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣7⃣ Da gudu mashi'ah tafito daga kichin d'in, hakan yayi dai-dai da k'ok'arin saka laumar alkubus da ya khaleel keyi cikin bakinsa, gaba d'aya suka mik'e suna tambayar ta miya faru?, ina mashi'ah bata saurari kowaba, burinta ta isa inda ya khaleel yake, Dan d'ago ido kawai yayi ya kalleta yacigaba da k'ok'arin saka abincin abakinsa, tirjewa tayi tafad'i, k'afarta ta bigi table d'in gabansa yakife, komai yazube k'asa har laumar hannunsa daya jefar yay saurin tashi saboda yanda ta hankad'o abincin jikinsa. Bak'aramin 6acin raine yaziyarci momy da ya khaleel ba, yadaka mata tsawar data tadasu Aleeya daga barci. "K wacce iriyar dabbar yarinyacene? Shin wani Abu yashiga kwakwalwarkine Dan ubanki?". Kanta yayo zai daka momy tarik'eshi, "barni da ita Ibraheem, karma ka 6ata ranka abanza"..... Husnah dake kusada ita tayi wani uban ball da mashi'ah tafara dukanta, daga ya khaleel har momy babu wanda yahana husnah, harsu Mufeedah suka fito suma, da k'yar mashi'ah ta kwaci kanta, zata gudu 6angaren masu aiki Aleeya tadaka mata tsawa, ''k ubankine zai gyara wajennan?". Dawowa mashi'ah tayi, jikinta sai rawa yakeyi, kokad'an bataji zafin dukan da husnah tamataba, hakama zagin dasuke mata bai 6ata rantaba, saima godiya takema ALLAH azuciyarta data samu damar hanashi cin abincin, gyaran wajen tashigayi. Ya khaleel kuma yafice ransa a6ace, jallabiyarsa dukta 6aci da miya. *********** Aysha Na shirya abinci a tsakkiyar falo yashigo, cikin mamaki take kallinsa, shikam ko kallonta baiyiba yashige d'akinsa. bin bayansa tayi da sauri, gaban madubi ta iskeshi yana cire rigar yana Jan tagwayen tsaki. Taimaka masa tayi yacire rigar, tana rik'e ahannunta sai duba miyar takeyi, tace, " sadauki miya 6ata maka jiki hakane?". "Mtsoww wlhy wawuyar mai aikincan Ce ta momy mana, tawani fito daga kichin kamar mahaukaciya kawai ta6aramin abincin da momy tamin". "wai kana nufin mashi'ah?". K'in tanka mata yayi, sai tsaki dayaja yashige toilet, tabishi da kallo itama, aranta tana raya miyakai mashi'ah aikata hakan?, tasan halinta, yarinyar batada damuwa, tabbas akwaidai dalilin yin hakan, shin miyema yasaka momy girkama ya khaleel abinci? alhalin ita bata ta6a ganin hakanba?. Bakinta tata6e tana d'age kafad'a, "🤷🏽‍♀komadai miye susuka Sani, d'antane dai". 'Aysha tafad'a tana ficewa d'akinta darigar a hannu'. Jik'ata tayi a boket sannan tadawo d'akinsa, bai fitoba, kaya marasa nauyi ta fiddo masa, ta fesa turare ta ajiye a bakin gado, tadawo falo tazauna tana jiran fitowarsa. Kusan mintuna 25 saigashi tafito sanye cikin kayan data fiddo masa, saidai fuskarnan babu walwala ko kad'an. Bata damuba ta sauka k'asa ta zuba musu abincin, saida tamasa magana kusan sau biyu sannan ya sauka k'asa. Hakadai sukaci abincin kamar wasu kurame, babu mai cewa uffan, garama Aysha tana kallo tanacin abincin. Hardai suka kammala. Wajen ta gyara tsaf. Batareda ya kalletaba yace, "yau su Joseph zasuzo da matansu, saikima su Amal magana da zeenatu su tayaki had'a musu abinci", baijira cewartaba yamik'e yafice. Kanta kawai ta girgiza, ahankali tace, " ALLAH ya canjaka ya khaleel". Koda tafito domin zuwa cikin gida saita taraddashi a barandarsu zaune bisa kujerun wajen, yanata danne-danne awaya. Batace komaiba tawuceshi, shima ko d'ago kai baiyiba ya kalleta, amma yaji alamun wucewarta. Maimakon tashiga 6angaren masu gidan kai tsaye, saita wuce 6angaren 'yan aiki, cikin sa'a ta taras babu kowa afalon nasu, tasan suna cikin gida, saboda yau weekend kowa zaici abinci agida. saida ta lallek'a sauran d'akunan taga babu kowa aciki sannan talek'a d'akinsu mashi'ah, akwance ta hangota tana kuka, ta k'arasa da sairi inda take, "mashi'ah tashi". Da sauri mashi'ah tamik'e zaune danjin muryar Aysha, saikawai tafashe da kuka, "Anty wlhy zasu kasheshi?". "Mashi'ah waye zasu kash?". 'Aysha tayi maganar ahankali'. "Anty ya khaleel mana". " ya khaleel kuma?, mashi'ah miyasa kikace haka?". "Anty shekaran jiyane hajia khaltum takawo wani magani wai abama ya khaleel yaci acikin abinci, abinda yasa nima nasani naje kaima momy fura da yamma d'akinta, harzan shiga sainaji magana k'asa-k'asa, hajia khaltum nafad'a mata cewar maganin inhar ya khaleel yacishi zai manta da komai, wannan ne zaisa su zauna lfy karya kamasu wai, cikin farinciki momy takar6a, tace insha ALLAH yau da safe zata yimasa alkubus da kanta, saboda yana masifar sonshi". "Inajin haka saina koma baya, saida hajia khaltum suka gama sanan nakaima momy furar, nadawo tsakar gida zan komo nan saiga hajia khaltum tafito itama tana surutai cikin harshen futanci, nikuma batasan inajintaba, hummm wai zatayi maganin ya khaleel, Dan babu wani maganin manta komai data bashi, gubace tabashi, zatayi awa 48ne ajikinsa kafin tafara aiki, kinga kwanki biyu kenan, batareda an zargesuba saidai ya mutu, kuma gubar bata nuna wata alamar daza'a gane guba yaci, saidai idan binciken likitoci". "Wlhy jiya banyi barciba Anty, sau kusan uku ina zuwa 6angarenki saina samu ya khaleel na nan, shiyyasa Na hak'ura, yau da safe bayan nagama taya momy yin alkubus shine ta aikeni babban kichin d'aukar Abu, harna fita namak'e ina lek'enta ta kafar makulli Dan nasan maganin jiya zata zuba, shiyyasa ta aikeni, ilai kuwa Na hangota tafiddo kullun maganin cikin zaninta ta barbad'a amiyar ya khaleel". "Bayan yazo gaidata aka sakani kawo masa abincin, to banida mafitar dazan hanashi cin abincin, shine nayi pretending harna samu nasarrar zubarwa, shinefa Anty husnah ta dakeni, bayan tafiyar ya khaleel sai momy ma ta mammareni😭". Lallashinta Aysha tashigayi, tabata hak'uri sosai, saida taga tayi dariya sanan tafito. ____________________ Girki sukeyi amma hankalin Aysha nakan juya zancen guba da akaso bama ya khaleel d'azun da safe, wanan lamarin yana buk'atar k'yak'yk'yawan nazari, haka kawai Aysha taji tana zargin wani Abu, musamman da zuciyarta ta waiwayi tarinhin baya akan lamarin gidan, kafin samuwar yara da bayan samuwarsu, har zuwa yanzun, amma tabarma zuciyarta, kuma lokaci yayi dazata fara bincike awannan fannin kam... Hummm saidai kuma ta ina zata fara?, tana buk'atar shawarar wani kenan? To kuma wannan sirrintane all, ko Anty meerah batason tasan dashi, wacce mafitace da ita kenan?......... Girgizatan da Shahudah tayi yasakata juyowa da sauri, antynmu miya faru haka? Kiketa tunani?". Ajiyar zuciya Aysha tayi, ''kibari Anty shahudah, wlhy ina tunanin zuwan bak'innan ne kawai". Dariya sukayi su duka, harsu Amal, daganan kuma akacigaba da hira. Cikin awanni 2 suka gama kammala girgi masu dad'i da d'and'ano, aka zuba a sabbin kuloli, Dan yaune rana ta farko da aka fara girka abinci a kichin d'in ayshar, shayine kawai take dafama boss. Saida suka taimaka mata ta mammala komai tsaf, sanan suka koma cikin gida, har lokacin ya khaleel yana baranda zaune. Saida su Amal suka fita sannan yashigo shima, Aysha nacikin wanka taji ambud'eta, juyowa tayi saitaga ya khaleel, maida kanta tayi k'asa, Dan har yanzun kunyarshi takeji, batawani gama sakin jikinta dashiba gaba d'aya (aganina ko shekaru ashin kukayi da mijinki yakamata kiringa irin wannan 'Yar kunyar, Dan tana saka miji nishad'i dajinshi sabo awajenki). "Wayyo sadauki, zanmaka ihufa inbaka rufeniba". Yanda tayi maganar a shagwa6e tana kuma k'ank'ame jiki Dan karya ganta, said abin yabashi dariya, baiyiba amma yayi murmushi yamaida k'ofar yarufe. gadonta yadawo ya kwanta, yana jiran fitowarta. Ita a zatonta tama yafito, danhaka ta d'auro guntun towel tafito kanta tsaye, saida tafito tsakkiyar falon sosai sannan taganshi kwance yana danna wayarta. Da Sauri taja baya zata koma yace, " kina komawa saina hukuntaki, garama kizo ki shirya". Babu yanda ta iya tak'araso, sai k'unk'uni takeyi, yanajinta amma ya shareta, yacigaba da buga game d'insa a wayarta. Atakure dai tayi shirin, tasaka atanfa d'inkin zani da Riga, kayan sun mata k'yau, ta gyara gashinta, tana cikin d'aurewa maganar ya khaleel tasaka juyowa ta kalleshi". "Kishirya gobe idan ALLAH ya kaimu nakaiki kitso, nakula in barinki za'ayi wannan kan naki saiya shekara a haka babu kitso". Baki ta tunzuro gaba, ''nidai banason kitso ALLAH sadauki, bakasan akwai zafi baneba?". Wayar hannunsa ya ajiye ya maida hankalinsa gaba d'aya kanta, "rantse kitso yanada zafi?". Saida ta kammala d'aurin d'an kwalinta, da yay mugun zama yay k'yau sannan tataso gaba d'aya tadawo bakin gadon, " ALLAH sadauki kitso akwai zafi, nifa Na manta tsawon lokacin Dana zauna amin kitso wlhy". "Miyasa to?". " haka kawai nidai damacan banason kitso ALLAH kuwa". Girarsa d'aya yad'age sama, yana kallonta, kinga nikuma inason kiyi kitso, harda wannan lallin da'aka miki irin Na biki, ko kad'an banso ya gogeba ni". Nima inason lalli, ammafa banda kitso, tayi maganar da turo baki. Jawota yayi saman gadon sosai, sadauki bak'ifa na hanya, please kabari kada kayana suyi S.....bai bari takai karshen zancenba ya 🤫. ALLAH ya k'yauta nafad'a ina d'akko d'an alk'alamina da takarda nayo waje🧞‍♀. ___________________________ Wajajen 12:30pm saiga su Youseef, kowanne yakawo matarsa. Tarba ta mutunci Aysha tamusu, dukda duk sun girmeta gaskiya sosaima kuwa, dandanan Aysha tacika gabansu da kayan ciye-ciye, duk saida sukayi mamakin ganin k'aramar yarinyar da ya khaleel ya aura, dukda sun ganta a wajen dinner, amma lokacin tasaka hill, kuma gown d'in data saka bubu Ce, amma babu Wanda yace komai, garama matar Joseph tama mijinta gulma ahankali, my sweet! Dama j! K'aramar yarinyar nan ya aura haka? Amma awajen dinner kamar ba itabafa?". Mintsininta Joseph yayi, taja bakinta tayi shiru kuwa. Bayan an gaggaisa Aysha taja Matan suka koma wani k'aramin falo da akayishi Dan hutawa kawai. Ananne sukai mata introduces d'in kansu. "Amaryarmu Aysha ko?". Aysha ta gyad'a kai cikin jin kunyarsu, dan tana ganin dunsun girmeta, dariya mai tambayar tayi, takama hannun Aysha tana fad'in "kisaki jikin damu, munzama k'awaye yanzun aii, ni sunana Haneefa, nice matar taheer". Kai Aysha ta gyad'a, tace, " ngd Anty haneefa". Dariya duk sukayi, "nikuma sunana Joy, matar Joseph". "Thanks you Anty joy". "Nikuma Hafeezah, matar Youseef". "Anty Hafeezah thanks". "Hhhhh duk kin maidamu Anty, haba Aysha mud'in friends nakine aii". " dukda hakadai Anty joy ". Tun Aysha na d'ari-d'ari dasu harta saki jiki, sukasha hira, dandanan sabo yashiga tsakaninsu kuwa, saika rantse sun dad'e da sanin juna, musamman ma joy datakeda yawan tsokana. Afaloma abokan hud'u sun had'e kai suna tattauna zance bud'e k'ungiyarsu ta taimakon matasa, kowa yana kawo shawararsa. Kiran sallar azhur ne ya tashesu, hakama matan, akabar Joseph da joy kawai. Duk sai sukaji babu dad'i, abin yata6a zuciyarsu, joy tace, "Sweet! dan ALLAH basu birgeka ba?". Murmushi yamata, amma baice komaiba, tun tuni idan suna zaune da abokan nasa aka kira sallah suka tashi, saiyaji wani iri babu dad'i, abin na cizon zuciyarsa sosai. Itama joy shiru tayi. Saitayi tagumi. Suna nan zaune shiru, har duk suka dawo, Aysha tanufi kichin domin shirya abinci, su Hafeezah duk sai suka bita suka taimaka mata, a falon aka shinfid'a ledar cin abinci, suka shirya abincin akai. Kowa yana kusada matarsa, sukaci abincinsu, itadai Aysha takasa sakewa taci, dan kunyarsu Taheer takeji. Ya khaleel na lura da ita sosai, saida yagama cin nasa sannan yamaida hankalinsa kanta, kar6a cokalin yayi ahannunta, Babu musu tabashi, dan batasan mizaiyi dashiba. Sai kawai taga yad'ebo yanufi bakinta dashi, idanu tazaro waje, "na k'oshi ALLAH sadauki, tayi maganar a hankali". "Naji kin k'oshi, amma kar6a dai". rok'onshi zata farayi yadakar da ita, "infa baki kar6aba, ninasan mizan miki yanzu awajennan, dan saina sakaki jin kunyarsu fiye da wadda kikeji yanz.... Bata bari ya k'arasaba tabud'e bakin da sauri ya zuba mata. Gaba d'aya suka kwashe da dariya, ashe duk suna kallo dajin abinda ke faruwa. Sinne kai aysha tayi jikin ya khaleel, yayinda shikuma yake murmushi. Haka sukaci sukasha cikin nishad'i, bayan sun kammala suka taimaka mata wajen gyara wajen tsaf. Saida akayi sallar la'asar sannan aysha tamusu rakkiya cikin gida, suk saida sukaje suka gaida kowa agidan, saboda aysha ta k'ular da momy saita bar 6angarenta yazama k'arshe. Aikam sak'on aysha ya isa ga momy. Dan zuciyarta tayi k'unci sosai, aganinta ita ya cancanta sufara zuwa su gaida. Su Mufeeda sai antayama aysha harara sukeyi, itako ko'a jikinta, su sukaga zasu iya wai sautin mahaukaciya. Basu wani dad'eba aysha tace sutafi. Momy kasa hak'uri tayi, tace, ''to isashshiya bazasu tafi d'inba, kedai tafi ga hanya nan, ko akwai Wanda ya rik'ekin........ Shigowar su ya khaleel ya katsema momy bayaninta, sarai kuma ya khaleel yaji da Aysha momy take, amma koda suka had'a ido da ayshar saita sakar masa murmushi mai kashe zuciya. Shima baisan sanda ya maida mata murtaniba. Duk hakan nafaruwane akan idon momy da Aleeya. Aikam bak'inciki tamkar zai karsu awajen. Har suka tafi momy na antayama Aysha harara. Itakam Aysha na sakarma momy murmushin k'ular da zuciya🤣🤣🤣🙀🙀. Sai bayan sallar isha'i wannan suka tafi, sukabar Aysha da kewa, ita dama akwai saurin Sabon tsiya da mutane, shiyyasa 'yan ciki da gaskiya fans suka maidata k'awarsu😜😜😜. *_Monday morning_* Around 11am ya khaleel yasaka aka kawo masa mai aikin hajia khaltum har office. Daka ganta kasan a tsorace take, ya khaleel na zaune saman kujerarsa yana duba wasu files, Mahfouz yashigo da yarinyar, matsashiyar budurwace, bazata wuce shekaru 19 ba a duniya. Cikin daka tsawa Mahfouz yanuna mata kujerar gaban table d'in ya khaleel, bai d'ago ya kallesuba, yana cigaba da aikinsa, Mahfouz yace, ''sir! Ga yarinyar". Batareda yad'agoba yace, ''ok, zaka iya tafiya". Saida yayi, salute nashi sannan yafita. Kusan mintuna 10 yanata aikinsa, baisake bin takan yarinyarba daketa zare idanu, sosai tsoronsa ya shigeta, dan tsaf tagane ya khaleel d'in, tunda tana zuwa gidansu idan hajia khaltum ta aiketa, taga kuma hotunansa a jikin abubuwan bikinsa da hajia khaltum tabuga, suma har aka babbasu. Fuskarsa a d'aure yad'ago yana kallonta, bayan yahad'a files d'in gabansa waje d'aya ya ajiye. Bindiga ya nuna mata, kinsan wannan komiye aii🔫?". Atsorace ta gyad'a kanta. "Baki zaki bud'e kimin magana". "Im.....Im..bindiga Ce". "Minene aikinta?". " harbi". "Idan aka harbi mutum da ita a ciki ko kansa, ko k'ijinsa, mike faruwa?". " idonta cikeda kwallah tace, "zai mutu yalla6ai". " thanks god dakikasan aikinta, to inhar baki bani amsar tambayar dazan mikiba, saina tarwatsa kwalwar kanki da ita". "Wlhy insha ALLAH zan fad'a maka komi kake buk'ata, inhar nasani". "da k'yau 'yar gari". "Miye sunanki?". " sunana Sakina................✍ *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣8⃣ "Sakina kinsan miyasa aka d'akkoki aka ajiye anan harna tsawon kwanaki hud'u?". "a'a yalla6ai". "Inason wasu bayanai awajenkine, miye alak'arki da gidan Alhaji mustapha Adamawa?". "ni mai aikice agidan yalla6ai". "Aikinmi kikeyi?". " sharan d'akunan masu gidan, saikuma falo dadai sauransu". "Uhm, atunanina Wanda ka yarda dashi kake sakarwa shiga lungu da sak'o Na gidanka, danya gudanar da irin aikinki, da alama kema masu gidan sun amince dake kenan?". Cikin in ina tace, "ha...hakane yalla6ai, amma nima duk sanda zanyi wannan aikin, musamman Na bedrooms nasu saiwani d'an gidan yatsaya akaina harna gama, sannan mu fito tare". Shiru ya khaleel yayi yana kallonta, yakoma jikin kujera yana lilawa ahankali, hannunsa rik'eda bindiga yana sosata akan kwantaccen sajensa zuwa baki. Sakina dai atsorace take sosai, tunda take bata ta6a ganin bindiga ido da ido hakaba, saidai ta 'yan sanda, itama daga nesane. Kusan mintuna biyu baisake cewa komaiba, sai zuwa can yajeho mata tambayar data gama rikita dukkan illahirin halittar jikinta. "Hakan yana nufin basu yarda dakeba kenan kema? Dukda tsawon shekaru Biyar dakika d'auka kina aiki agidan? Shin wacecema talatuwa agidan?". Tsoro, razana, kad'awar ciki data zuciya duk suka riski sakina lokaci d'aya, takasa cewa komai, sai zufa dake keto mata takowacce ga6ar jikinta. Cikin daka tsawa yace, "nace wacece talatuwa agidan dakike aiki?!!". "yalla6ai fad'ata tamkar salwantar rayuwatane narantse maka, sannan bansan miyasa basu yarda dani d'inba". Wani murmushin k'asaita yayi, tareda fad'in ''dak'yau yarinya, anzo wajen". "Ki fad'amin, kokuma kafin ki koma wajensu su kasheki, ni zansaka alburushin bindigata acikin kanki, saidai akai musu gawarki su tambayeta". Hawaye masu zafi suka fara zarya akumatun sakina, tace, " yalla6ai zan fad'a maka, amma Dan ALLAH karufamin asiri karkace nina fad'a". Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanu, amma baice komaiba. Tace, "shekaruna kusan biyar ina aiki agidan, lokacin da'aka kawoni banwuci 14 ba, kuma talatuwace ta d'akkoni daga k'auyenmu Na boza a fika Local Government, jihar yobe, mahaifina da hannunsa yabadani wajenta, bayan tabashi mak'udan kud'ad'e, ina kuka mahaifiyata Na kuka aka taho dani. Koda aka kawoni Abuja wani gida aka kaini, agidan akwai 'yan mata dayawa, k'anana da manya, kuma kowanne irin yare dake Nigerian zaka samu, hardama 'yan Niger dawasu k'asashe makwaftan Nigeria, banfahimci abinda yatara wad'annan mata agidanba aka d'akkoni aka dawo dani gidan Alhaji mustapha, nikaina bansan dalilin yin hakanba, amma daga nanne nacigaba da aiki agidan, Alhaji mustapha ba mazauni baneba, shiyyasa gidansa yazama k'ark'ashin mulkin matarsa, dukda dai nakanji masu gidan sukan tattauna akan hajia khaltum tanada kishiya, kuma alhaji mustapha yafi zama a can, yalla6ai satar amsa 1 zan baka, nasan kaid'in kwararrene Dan nakanji firarka awajen yaran gidan, suna yawan yabama kwazonka saboda soyayyar da baby take maka". Da Sauri ya khaleel yataso daga jikin kujerar, ''kinga fad'amin wace satar amsace?, bar batun wancan shirmen". Sakina ta jinjina kanta tace, " yalla6ai mafi yawancin masu zuwa gidan wajen hajia khaltum, namiji ko mace zaka samesu dawani tambarin hoton tarttu na 🦂kunama a damtsen hannunsu Na haggu, tabbas wannan shine tambarinsu, wannan kawai Na iya fahimta tartare dasu yalla6ai, wlhy iya gaskiyata nafad'a maka, Dan ALLAH karka kasheni, kuma karkace Nina fad'a". Kwantar da hankalinki, zansa a maidaki yanda bazasu fahimci komaiba, da sauri yad'auki ☎waya yayi kiran office d'in Mahfouz da Basheer. Babu dad'ewa saigasu sunzo kusan atare, saida suka k'ame, tareda salute nashi, sannan ya khaleel yace, "Mahfouz! Amaida yarinyarnan, amma yanda za'a iya fahimtar saceta akayi". "OK sir" "Kibishi kuje, inhar ina buk'atar k'arin bayani zansa akuma d'akkomin ke". ''To yalla6ai ngd, tayi maganar tana hawaye, Dan bata fatan akuma kawota wannan wajen". Saida aka d'aure idonta kamar yanda aka kawota sannan aka fita da ita. Ya khaleel yamaida hankalinsa akan Basheer dake zaune, ''Basheer ina buk'atar hotunan gawar David". " OK sir!, bara na kawo, amma akwai Na binciken k'arshe da akayi suna hannun Oga Joseph ". Jin jina kai khaleel yayi, yakira Joseph akan yakawo masa file d'in binciken mutuwar David. Babu dad'ewa saiga Joseph ya iso, kar6a khaleel yayi yafara bincike, zuwa can yad'auki wani hoto da David ke shinfid'e a table doctors nata aikinsu akan gawar, damtsen 💪🏻hannunsa ya khaleel ya kalla, cikin zare ido yace, "Joseph hoton miye wannan?". Kar6ar picture d'in yayi yana kallo, sir! Inhar hasashena yayi dai-dai wannan kunama ce🦂, dukada ba'a gani dak'yau". Da sauri ya khaleel yamik'e yana fad'in Joseph inason ganin gawar David yanzunnan. " OK sir!, idan ka shirya saimuje". Cikin takunsa Na jarumta da isa yake tafiya, yanayinshi kawai zaka kalla kagane ransa a 6ace yake, sunshiga inda akan ajiye gawawwakin wad'anda wahala tasakasu mutuwa, ko aka kashesu, kokumadai Abu mai muhimmanci yasaka aka ajiye gawar tasu, Dan ayi bincike akanta. Ma aikatan wajen sai k'amewa sukeyi, kasancewar suma police ne, amma likitoci. Bakai tsaye su ya khaleel suka shiga wajenba, saida aka basu wata Riga suka saka, suka rufe dukkan jikinsu👨🏻‍🚀, har hannayensu da hanci sannan suka shiga, doctor Sadam mai bincike akan gawar David yabud'e abinda aka lullu6eshi, bayan anjawo gawar daga cikin wani glass, fitulu aka kunna saitin gawar David. Doctor Sadam yabama khaleel wata fitila mai haske🔦, suna haska damtsen hannun David Na haggu saiga hoton kunama🦂. Hoton wajen Joseph ya d'auka har sau biyu sannan suka fito. Ahanya khaleel kecema Joseph, ''wato da muna aikine a birkice, ko kad'an mun Gaza samun bakin zaren matsalarmu sai a yau, tabbas akwai masu laifin dake da alak'a da juna a setetion d'innan, amma wad'anda suka kashe David basusan wannan sirrinba, mu kanmu bamusan da hakanba, wannan tambarin kunamar yana nufin tambarin wata k'ungiyane kenan?". Maganarka gaskiyace sir, amma ya akayi kagane wannan tambarin kunamar?". Ya khaleel bai bashi amsaba har suka k'arasa office d'insa, yacema Joseph kiramin Taheer, youseef. Adams, & Solomon". ☎duk yagama kiransu cikin mintuna k'alilan. Babu dad'ewa saigasu sunzo. Yana shan shayin daya had'a suka shigo, kowa yazo saiyayi gaisuwa sannan ya zauna, kowa yayi shiru yana sauraren boss. Khaleel yamik'e hannunsa d'aukeda mug d'in tea yanasha a hankali, idonsa a kansu, "kunsan dalilin kiranku?". Atare sukace a'a sir!. Remote yad'auka, ya danna TV d'in office d'in, saiga hoton kunamar dasuka d'akko ajikin gawar David, "wannan kunamarce, ita wannan kunamar takasance tambarin nawata k'ungiya, kuma nasameta ajikin David, ranar Taheer kasanarmin kana zargin alak'a tsakanin David da barau modibbo ko?, to yanzu inason abinciki wannan kunamar ajikinsa, bama shi kad'aiba, harda duk wasu criminal's da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi kamar David, sannan David yana safarar yara shima, kenan dukmai alak'a dashi akan bigire d'aya suke?". "Zamu gudanar da aikinmu da lura, shiyyasa Na taraku kud'in amintattuna, bana buk'atar asaka wasu yara a aikin, dakanmu zamuyi, saboda akwai magoya bayan su David acikinmu, wannan ne yasakasu kasheshi dankar yafad'a mana komai". Gaba d'ayansu suka jinjina kai. Adams yace, " sir!, aikuwa akwai wannan hoton kunamar a hannun Moxies". "Da gaske"?. " am telling you sir". "Kenan Moxies yanada alak'a da David?". " zamu iya cewa hakan". To inkuwa hakane, Ku bincikamin Ruth da aka kama da yara a air port zataje Dubai, sannan Solomon miye labari gameda bincike Dana sakaku akan email d'in sirri da'aka turo sunayen su Ruth aciki?". Sorry sir, munata k'ok'ari, amma gaskiya mai email d'in mutumne mai wayo, Dan saida yabi matakan Kare kai daga binciken kwankwanto kafin yafara aikinsa, kuma tabbas yasan computer sosai, inhar ba k'arya zan makaba zan iya cewa bamu samo komai game dashiba, saidai kuma yin maganar kunama mai tambarin k'ungiya yatunamin dawani Abu, tabbas mai email d'in yasan wani Abu dangane da wannan k'ungiyar, domin duk sak'on dazai turo akwai hoton k'aramar kunama da bindiga kusada ita, bara kaganai". 'Solomon yay maganar yana bud'e laptop d'insa, mik'ewa yayi yay connecting da TV d'in office d'in, tana gama searching saiga jerin sakwannin mai email d'in sirri, acan gefe mak'ale kunamar take, 🦂🔫, sannan an nuna kunamar da bindiga. Huci mai zafi ya khaleel ya furzar daga bakinsa, ya ajiye kofin hannunsa tareda matsawa jikin tvn, nazarin komai yakeyi cikin kwarewar aiki, saikuma ya jinjina kansa, yajuyo yana kallonsu youseef, ajerin sunayen damai email d'in yaturo guda biyar, macece ta uku, kuma yabamu tabbacin zata sauka Nigeria aranar 17-ga watan 4, watan dazamu Shiga kenan, zata tasone daga k'asar Malawi, ta sauka Dar es salaam, babban birnin Tanzania, washe garine zata k'araso Nigeria. Jirginta zai sauka a Kano state ne, daganan yabamu za6in kamata a Kano, kokuma a Abuja, acewarsa wannan yarage namu, shi yagama nasa". Gaba d'ayansu sunyi shiru, kowa da abinda yake tunani, ya khaleel yakatse shirunsu dafad'i "so ina jinjina kwakwalwar mai email d'innan, koda criminal ne shi tabbas yanada kwakwalwa, kamar yanda yabamu satar amsa akan kama Moxies haka yabamu akan wannan matar, saidai bazamu saki jiki kai tsaye da bayaninsaba, saboda tsaro". Youseef, kaida taheer Ku tattaramin bayanin David, da Moxies awaje d'aya, tunda sunada alak'a da juna, Joseph kaida Faruk da Mahfouz kucigaba da bincikamin Duk wani mai wannan tambarin dake a setesion d'innan, Solomon kanemi su Kausar acigaba da bibiyar mai email d'in sirrinnan, nasan dolene watarana yayi kuskuren dazamu samu wani bayani akansa". "Nida Adams da Samuel Zamu cigaba da farauta". " komai yazama da kula, banason kuskure kuma kunsani, duk Wanda yamin wasa da hankali acikinku koyaci amanata wlhy dakaina zan fasa kwakwalwarsa da bullet, koda kuwa cikinsu youseef". Ku kula da k'yau, Adams ina buk'atar Ak'ilu Abbas agabana yanzunnan, kukuma zaku iya tafiya". Atare suka mik'e baki d'aya, duk sukayi salutes d'insa, murtani ya maida musu, sannan yakoma kujerarsa ya zauna, sukuma duk suka fice. ___________________________ "Aminiya agarin Yaya kikayi sakaci baici maganinnanba?, anya kuwa kinsan bala'in dake tinkaromu?, kekankifa kinama cikin saka idanun k'ungiya, dansu gano cewa Ibraheem d'ankine, kuma shine yake mana tsinci d'ai-d'ai, k'ungiya ta bada date d'in daza'ayi zama Na musamman domin Ibrahim kai tsaye, Alhmdllh munsami damar ku6tar da talatuwa daga hannun police, Dan munyi gamo da d,p,o kwad'ayayye, yanzu haka talatuwa Na gida". "Alhmdllh, naji dad'in hakan, sannan karki damu aminiya rashin cinsa bashi yake nuna ya tsiraba, Dan nakafa masa wani tarkon ma, k'ungiya kuma zan fahimtar dakowa komai kai tsaye, Dan banason d'ana yafuskanci wani Abu daban, inasonsa fiyeda tunanin mai hakali". " tsaki kawai hajia khaltum tayi, amma batace komaiba". Hajia babba tace, "aminiya zan kashe matar Ibrahim". " miyasa? aminiya, ita mitamiki?". "Kinsani aii". Dariya hajia khaltum tayi, tace, " bazan hanakiba aminiya, dama a k'ungiyance kisa yarinyar ya cancanta agareta, saboda gudun tonuwar asirinmu, dannasan wani daga cikin sirrinmu. Damacan ina shirya abubuwa akanta tuni, sonake sai mungano Inda meerah take, kisan Aysha tamkar munkashe macijine bamu sare kansaba, inhar meerah Na numfashi a duniya, wannan ne dalilin dayasa nabar Aysha bansake waiwayartaba". "Shikenan aminiya nabar komai a hannunki". Aysha dake bayan windown hajia babba tazaro ido, danjin maganar su momy, dasauri tabar wajan tana sauke numfashi, tabbas maganar su tadaki zuciyarta, amma bata tsorataba, haka takoma 6angarensu tana juya maganganunsu, takira Anty meerah ta zayyane mata komai. " lil sholy kibani kwanaki biyu zanyi tunani, kema kiyi tunanin mafita saimu had'a tunaninmu waje d'aya muga miya dace muyi". "Shikenan Anty meerah babu damuwa". Yauwa ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH babu abinda zai cutar damu, kisa aranki *_CIKI DA GASKIYA..._* wuk'a bata hudashi da yardar ALLAH". " To Anty meerah ngd". "Aha saimunyi waya". Bayan Aysha ta yanke wayar takwanta taci kukanta, da mamakin hatsabibanci irinna momy da hajia khaltum, lallai tasan zukatansu sun gama bushewa. Dama dawowarta daga aiki kenan, driver ya ajiyeta saiga hajia khaltum, shinefa tabi bayanta ta mak'ale ta window hartajiyo abinda suke tattaunawa. Saida tagaji da tunane-tunane sannan tatshi tayi wanka, kichin tashiga ta tanadarma ya khaleel abinci kafin yadawo, dukda batada tabbacin zai shigo gidan dawuri, tunda wani lokacin yakan kai 10 Na dare a office ma. _______________________ A d'arare Ak'ilu Abbas yashigo office d'in, shima sanye yake da uniform na police Interpol, saida ya k'ame tareda salute d'in khaleel sannan yabashi izinin zama. Ya khaleel yad'ago manyan idanunsa ya sauke akan Ak'ilu Abbas, shikuma saiyayi k'asa da nasa idon, Dan mara gaskiya baya iya kallon ya khaleel ido cikin ido. Murmushi ya khaleel yayi, yajawo iPad d'insa yamik'ama Ak'ilu Abbas. Kar6a yayi cikeda mamakin mizaiyi da itane?. "Nasan kana mamakin mizakayi da ita ko?, akwai game aciki, kuma shikad'aine, inaso kaje kayishi, iya inda kasamu game over kakawo min, idankuma kawuce abinda kasamu har sau uku to zan gane zaka iya tafiya". Cikin rawar murya Ak'ilu Abbas yace, " sir? Nikuma miye had'ina da game?". ''Basai kasaniba, banason yawan surutu jeka". Duk Ak'ilu Abbas ya rikice, baisan dalilin yin hakanba gareshi, tabbas yasan wanene j!, kuma baya Abu saida manufa. Koda yak'arasa office d'insu su kusan 20 aciki, sai yake gayama abokinsa wanda sukafi shak'uwa. "Tab wlhy Ak'ilu kashiga tarkon Oga kawai, shiyyasa naita kwa6arka al0kacin amma kak'i, yanzu wa gari ya waya". " please Sha'aibu kabani shawara mana". "Yoni shawarar mizan Baka?, kayi abinda yace kawai". Shiru Ak'ilu Abbas yayi, Dan yasan shi'aibu ma mutumne mai gaskiya, aransa yace shikenan nashiga uku nikuma, anbani kud'i Na aikata abinda zaiyi sanadin k'ask'antuwata, gashima kud'in harsun zama labari, tunda naje karuwai sun cinye .............✍🏿 Nidai nace, " hummm". *_Ayya my sweet Xoxo, ALLAH yabaki lafiya, yasa kaffarane, yatashi kafad'a, fan's Ku had'o kayan dubiya tawan babu lafiya😞._* *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _~Home of experts and perfect writers~_ *_part 2_* (littafi na biyu📕) 2⃣9⃣ Akwana atashi babu wahala awajen ALLAH, kwanaki nata gudu lamarin tamkar k'yaftawar idanu, kamar wasa saikaga seconds sunkoma minutes, minutes sunkoma hours, hours sunkoma day's, days sunkoma weeks, weeks sunkoma months, months sunkoma years, baka fargaba saikaga kanka amatsayin gawa😭. Da d'an Adam yana tunawa akwai k'alubalen mutuwa agabansa dabai aikata wata 6arnarba, hummm kunsan wani abu kuwa?, (wlhy dayawanmu gani muke bazamu mut yanzuba, dukda munsan tabbas mutuwa gaskiyace, Dan inba'a d'auki mamankaba, and'auki babanka, ko yayanka, ko k'anwarka, ko mijinki, ko mataraka, ko k'awarki, ko makwafciyarki, amma lokacin da'akayi mutuwarne kawai zakiga hankalinmu yatashi, kwanaki k'alilan zamu koma dukkan ayyukanmu, wani gani yakeyi shifa k'aramine mutuwa bazata d'aukeshiba yanzu), kai👉🏻🧕🏻👳🏻‍♀d'an adamu wanene kai?, mikake tak'ama dashi?, karinga tunawa mutuwa tana d'aukar d'a acikin uwarsa👉🏻🤰🏻, tana d'aukar jariri a hannun uwarsa👉🏻🤱🏻, tana d'aukar yaro d'an shekara 1👉🏻🙇‍♀tana d'aukar masu shekaru biyu👉🏻👫, tana d'aukar budurwa ko saurayi masuji da tashen lokacin k'uruciya👉🏻🙎🏻‍♂🙍🏻‍♀, tana d'aukar magidanci. Mai fafutukar Kare martabar iyalinsa wajen cigar dasu da tufatar dasu👉🏻👨🏻, tad'auki miji gaban matarsa, 'Yaya gaban iyayensu, uba gaban 'ya'yansa, bazatabar tsohoba komin tsufarsa👉🏻🧔🏼, Duk k'arfin mulkin mai sarauta saita d'auka👉🏻🤴🏻, duk yawan dukiyar attajiri da alfarmarsa saiya tafi, Duk iskancin d'an iska koyakai shaid'an 👹tantiranci wajen bijirema ALLAH sai anshafe tarihinsa watarana. Shin miyakaika shagala yakai bawa?, miyasaka mantawa da k'alubalen mutuwa?, miyasa? duniya da kayan cikinta sukafi tasirantuwa azuciyarka fiyeda tunawa kwanciyar kabari daranar hisabi, ranarda kowa aikinsane makaminsa, wane rud'in shaid'anne ke d'awainiya dakai har kakasa jin kunyar ubangijinka daya halicceka danka bauta masa kake aikata zina agabansa, kake shaye-shaye agabansa, kake luwad'i agabansa, kake mad'igo agabansa, kake sata agabansa, kake bin bokaye agabansa, kake cutar da d'an uwanka saboda ALLAH yabaka wata dama ta mulki ko k'arfin iko, miyasa yakai bawa?, shin baka tsoron randa za'a shiryo rundunar mala'iku domin kar6ar ranka?, aranarfa aikinkane kawai guzurinka?, anya kuwa bawa yana k'iyasta kansa amatsayin gawa idan yanutsu, kokayi wannan tunanin, kobakayiba wlhy billahi saika mutu👉🏻😭😭😭. ________________________________ Bikinsu Amal nata matsowa, gaba d'aya yau saura kwanaki 6 kacal d'aurin aure, kusan zan iya cewa duk masu aikin gidan da 'yammata harda matansu sultan dasu mama duk suna kichin, chin-chin d'in gara dakuma rabo akeyi. Aysha ce kawai babu awajen, tana d'akin Anty Mamie kwance, yau kusan satinta d'aya kenan, Dan ya khaleel yayi tafiya zuwa France tun last week, shine yace tadawo d'akin Anty Mamie harsai yadawo. Kusan kwanakinta uku kenan batajin dad'i, k'irjinta namata ciwo, dauriya kawai takeyi bataso kowa yagane. Wajen aikin chin-chin d'inma hartaje takasa zama saboda jiri datake gani kad'an-kad'an. Batacewa kowa komaiba tazaro jiki tadawo d'aki, kwance take shiru tana tunanin ya khaleel, tunda yatafi sau hud'u kacal sukayi waya, ko kiransa tayi saiyace aiki yakeyi, lamarin ya khaleel Na damunta wlhy, ita yanda take karanta novels taga mazan ciki Na tattalin matansu, harma sukan manta da ayyukansu, duk motsinsu yana gidansu, soyayya kaga harta fitar hankali, catake haka zata dinga gani ga ya khaleel, amma yayinda ta auresa saitaga sa6anin hakan, dai-dai gwargwado yana nuna mata kulawa da soyayya, saidai batakai ko rabin wadda ake nunama matan novels ba, shin ko ita bata iya tattalin miji baneba kamarsu? To amma ai matan novels ma girki, iya kwalliya, tsafta, kusan shine sukema mazajen, itama duk tanama mijintashi, hardama biyayya, wadda take ganin mafi yawan matan novels basuda ita, (hummm indai hasashenta gaskiya ne to tabbas zata iya cewa irin wannan mahaukaciyar soyayyar da miji kan nuna ga matarsa, harkiga yana mata kuka to sai'a novels, saboda k'arancin samun irin wannan soyayyar a gidajenmu yasaka mata raja'a wajen karanta hikayoyin marubuta, musamman ma buk na batsa, Dan suna kallon hakan amatsayin soyayya, mukuma yawanci bama samun irin wannan soyayya agidajenmu) "ya ALLAH ka gyara gidajen auranmu", Aysha tafad'a tana share hawaye. Wayarta tajawo ta dialing d'in number ya khaleel ta France, harta tsinke bai d'agaba, saida takira sau biyu. Ana uku harta kusa katsewa sannan yad'auka. Cikin dauriya tace, "Assalamu alaika". Ya amsa yana fad'in "o, nayi laifi fa, jiya nace zan kiraki ban kiraba, amin afuwa aikine wlhy A'eesha". Danne zuciyarta tayi tace, " babu komai sadauki, Na fahimceka, ya aikin?". Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, yakuma jingina sosai da kujerar motar tareda lumshe ido, yace, "Alhmdllh, ngd sosai dakike fahimtata akowane lokaci, haka akeson mace tazama maima mijinta uzuri, Dan itadama rayuwar aure tagaji hak'urine kawai, bakomai ake nema asamu 100% ba". Aysha tace, " hakane". "Yauwa ya shirin biki?". ''Gashinan anatayi, duk sunacanma suna chin-chin". "Tofa, kekuma kina ina". " ina d'aki kwance, wlhy haka kawai naji inajin d'an jiri, bansan daliliba, amma yanzu yadaina". "Sholyna kodai asibiti zakije?". " lah karfa ka damu, wlhy da sauk'i, yanzuma zan koma wajen aiki, yaushe zaka dawo". "Tom ALLAH yak'ara afuwa, Indai kinji bai tafiba karkiyi shiru, kifad'ama Anty Mamie kuje asibiti, Nima insha ALLAH zuwa nanda 4days zandawo k'asar". "anafa jibi d'aurin aure kenan?". "Eh, insha ALLAH, ko kina kewatane?". Cikin shagwa6a tace, " wlhy sosaima kuwa". "Humyim, karfa nadawo kice kuma Na gundureki". "ni wlhy babu waninan, kadawo please ". Guntun murmushi yasaki, yayinda shagwa6arta ke rura masa wata kasala mai kashe jiki da sanya jini gudu da sauri, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, " my sholy karki kasheni da salonkifa, kinga bana kusadake, please karki saka sadaukinki cikin wani hali kinji". Dad'ine Yakama Aysha, tasaki siririyar dariyar data kuma narkar dashi, aii babu shiri ya Yanke wayar gaba d'aya, yay saurin kifa kansa jikin sitiyari yana sauke numfashi a hankali, tabbas Aysha dabance wlhy, yafad'a cikin furzar da iska daga bakinsa, kashe AC d'in mortar yayi, danshima k'ara sakashi kasala yakeyi, dajin buk'atuwar kasancewa da matarsa. Aysha ko yana kashe wayar ta tuntsure da dariya, dama da gayya tayi, wai itama sotake tagwada Na matan novels tagani zaiyi tasiri, dad'i kamar zai kasheta, sai juye-juye takeyi agadon ("kai dagaskefa marubutannan suna fad'akar damu wlhy, infa zaka d'auki Abu mai k'yau kagwada ga mijinka zakaga kana canjashi kamar mijinki novels, Kodai bazai lalace akankaba kamar mazan novels to zaka samu farinciki kaima) aii idan akace matar novels tayi wanka sau uku Arana, kekuma saiki kamanta yin biyu, (suma marubutan suna saka hakane Dan ka kamanta ba dole sai d'in kayi kamar ta novel ba, idan sunce 1 akayi, kekuma wataran bazakiyi d'ayan bama, abunda yasa bama amfanuwa da abinda marubuta suka rubuta, saboda muna karanta books d'inne dan kawai nishad'i, burinmu muji soyayya ruwa-ruwa, matsa can kamacan, badukanmune Muke maida hankali wajen fahimtar wane sak'o writer suke son isarwa a buks d'insuba, soyayyarce kawai damuwarmu, amma bamabin matakan mizamuyi musami soyayyar muma agidajenmu, wata Indai ta karanta labarinki yasakata dariya ko haushi anan zata kakka6ar miki da kayanki, bazata amfanu da komaiba, kota gwada danta samu mafita agidanta ko cikin al'ummar datatsinci kantaba, nikam danayi wannan asarar 6ata lokacin, aigarama ace ban karantaba wlhy). (Yakamata dai reader's sudinga fahimtar writers bamuyita wahalar banza da asarar data ba, ALLAH yasa nun fahimta). ____________________________ Momy madai tanata shirya d'iyarta mufeedah, daka shiga 6angarenta kasan ana bikin 'Yar gata, danma babu Anty zuwairah, Dan baffah yahanata zuwa gidan kusan harna tsawon shekara biyu. Sosai momy takema mufeedah komai na 'yan gata. Babu Abu mafi d'auremin kai sai zaman Aleeya agidan, narasa mitakeyi har tsawon watanni biyu da rabi?, kuma babu Wanda yamata maganar barin gidan, gashi bama ta ishi ya khaleel kalloba, amma ko yaushe tana nane dashi. Komai Na bikinnan da Aleeya akeyinsa. Momy dai an ajiye girman kai taje ta rok'i Ammah akan tabama baffah hak'uri yabar zuwairah tazo, da farko Amman shareta tayi, saida tayita mata magiya sannan Ammah tace taje zata masa magana. Ilai kuwa dasafe yazo gaisheta tarok'eshi akan yabar zuwairah tazo, tunda komai ya wuce, da angama biki saita tattara tatafi. Badan baffah yasoba ya amince, sosai Anty zuwairah tayi murna kuwa. Taitama Ammah da baffah godiya acikin waya, harda kukanta akan baffah ya yafe mata, hakan bazai sake faruwaba. Amma dukda haka bawai tanason Aysha baneba, haka kawaidai batason mahaifinta tayi fushi da itane. __________________________ Biki bidiri bired'e, gidafa Alhmdllh yacika da al'ummar Annabi, dangi tako ina sun cika gida, yo kikam harfa 'ya'yan mutum hud'u, momy zata aurar da mufeedah, Anty Mamie, Ramadan, zunnuarain, Amal. Ummie amarya, Shahudah, sai matar uncle ma'aruff k'anin baffah, Naseeba da Hamdiyya, (Dan itama nangidan tadawo za'a had'u waje d'aya ayi kawai. Aikam gida dai ba'a magana, mama ma dabazata aurar dakowaba danginta dank'am da gida, su Yaya fadeelah, hafsat, Ummah, Anty nasarah matar ya Qaseem duk suna nan, harda matan kawu bilyamin, da babbar 'yarsa, saikuma Rufaidah da Safiya amare, kowacce da cikinta, su Rufaidah anata zubar da yayu. Aiko Aysha tatasosu gaba da dariyar mugunta, wai daga yin aure harsun sami ciki. Yaya Hafsat tayi dariya tana kallon ayshan, tace, "hummm Aysha kema wannan k'yawun naki aii inkaji gangami da labari, kinga yanda kika k'ara 'Yar k'iba kuwa, harda wasu hips na musamman, gawani bala'in k'yau dakikayi, anya ya khaleel Na kallonki kuwa?. Kwa6e fuska Aysha tayi, tatashi daga d'akin mama tafice, dama anan suke hirar, tun isowar mutanen kanon da safe Aysha tadawo tsakkiyarsu anatashan hira, tayi kewarsu sosai. Maganar Yaya Hafsat tasakata fita, danta Sosa mata inda yake mata k'aik'ayi, tun jiya yakamata ya khaleel yadawo gidan, amma shiru, har tayata su maleeka sukayi tagyara 6angarenta, suna shirya masa abinci. Amma har dare babu labarinsa, tasha kuka kuwa da daddare, da safennanma haka tatashi cikin bak'in rai, zuwansu yaya fadeelah nema yasakata d'an sakin jikinta. Tunani yatafi da hankalinta wata duniyar baki d'aya, jitayi anyi sama da ita kawai. Zaro idanu tayi waje, cikin matuk'ar firgita, wanene ya d'auketa, jikinta sai 6ari yakeyi takai dubanta kansa. Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki, ''sadauki! Yaushe kadawo?". Kashe mata ido d'aya tayi, yana wani k'asaitaccen murmushi, saida yatura k'ofar 6angarensu yashiga sannan yabata amsa. "Yanzunnan nadawo". Shiru tayi bata tankaba, saima hawaye data kamayi. Harsuka isa 6angarensu tana kuka, shikuma baice mata komaiba, tana rik'e a hannunsa yasaka key d'in yabud'e k'ofar falonsu. Bai ajiyeta a faloba yanufi d'akinsa kai tsaye da ita, yasan yayi laifi dolene yayi lallashi. Ko ina tsaf yanata tashin k'amshi, saboda gyaran dasukayi masa jiya, kuma yauma batareda sanin Aysha ba Anty Mamie ta turo tasleem takuma gyara Inda k'ura ta sauka. Saman gadonsa kawai ya d'ireta, takara k'arfin kukanta tana bubuga k'afafu yanda yara sukeyi Idan ansakasu kuka. Bai kulataba nanma, yaje ya kulle k'ofar yahau cire kaya, Aysha kam bata gajiba tacigaba da ta6ararta😜. Toilet yashiga, kusan 20minute yafito d'aure da towel, alamar wanka yayi, jikinsa kawai ya goge yad'an fesa turare yasaka boxer ya haye gadon. Jawo Aysha mai kukan shagwa6a yayi jikinsa, tanata tureshi itakuma alamar karya ta6ata. Cikin sigar tsokana yace, "o, Sholyn sadaukinta bagani nadawoba to, kema kinsan aikina aii, sai kinamin uzuri, haka Nike kullum tamkar kud'i, koda yaushe acikin yawo nake". " amma inda bakada mata kake wannan yawon, aii yanzun saika tuna Kannada ita ko...... "Umh hakane kuma, yakatseta da Sauri, zata k'ara magana ya d'ora bakinsa akan nata🤫... 🏃‍♀🏃‍♀. __________________________ Biki kam dai ba'a cewa komai, gida yagama. rikicewa, baka ganin kowa ba'a ganinka, duk son d'aukar rahotona Na tsiya dole Na hak'ura, nakoma gefe nazuba idanu. Karfe 10am aka d'auro auren Zunnurain da Amaryarsa Maryam, sannan aka d'unguma misali 11am aka d'auro Na zunnurain da amaryarsa Samha. Tom angwaye saimuce ALLAH ya sanya alkairi😂😂😂. Misalin 1:30pm bayan idar sallar Azhur aka d'aura auren mufeedah & Ameenudden, sai Hamdiyya & Abdul-Hakem, Amal & Adams, Shahudah & Anwar, Naseeba & Najeeb, ubangiji ALLAH ya sanya alkairi amare da angwaye, su babban Yaya ya khaleel sai baza babbar Riga akeyi, angwaye kam aii ba'a cewa komai, su Adams da ya Ramadan baki kamar ya yage😂, hakama amare sunsha k'yau acikin gida, kamar zasuje gasar sarauniya k'yau.lol. komai yana cigaba da gudana cikin tsari, acikin gidama mata nata shigi da fici da shagalinsu. Amma banda Aysha da zazza6i yarufe, su Rufaidah na 6angarenta tun jiya, a can suka kwana, hirar family d'insu sukeyi, dauriya kawai Aysha dake kwance a 2seat takeyi tana jefa magana a first tasu, Sadiya ce ta fahimci kamar ayshan batada lfy. Tace, "Aysha lfy kike kuwa?". " eh mana sadiya mikika ganine?". "Naga sai hura hanci kikeyi, kamar kuma a wahalce kike magana?". ''A'a wlhy, kawai gajiyar aikice". Hararta Sadiya tayi, tace, " aikinmi kikayi agidannan Aysha?, tun d'azun kina like da ya khaleel a d'aki, sai 9 kuka fito, kijimin 'Yar rainin senses ". Dariya duk sukayi. Amma banda Aysha data harareta itama, to gwaggo mai tsari, sokike nabarsa shikad'ine? Ke haka kikema mijinki da har kika k'unso ciki?". Hhhhhh mi kowa zaiyi ba dariyaba, dama Aysha da sadiya inhar suka had'u sai anyi tsiya, kamar sakone da sako aii (like nida Anty Ruk'ayya maikan goruba😜😂🤭). Abinci suketaci, Aysha na kwance tana kallonsu, babu abinda ke bata sha'awa a abincin, sai wani kallonsu takeyi a yatsine kamar taga gotta. "K dallah malama kidaina mana wannan yatsine-yatsinen, idan bazakici bane babu dole, ki d'auke kanki mana". 'Rufaidah tayi maganar tana harar Aysha'. Baki Aysha ta ta6e, ta kauda kanta daga kallonsu, tajuya kwanciyarta tama basu baya. Babu Wanda yasakebi takan Aysha, sukaita shagalinsu da abinci. Ita daga nanma barcine ya kwasheta. An idar da sallar la'asar ya khaleel yashigo gidan, bayan yasamu mutane sund'an lafa musu, saidai cikin gidan dank'am yake da mata, har 6angarensu dayake anan 'yammatan amare suke, 6angaren ya sultan, danshi yad'anfi sauk'in kai, mujahedeen ma halinsa d'aya da ya khaleel, shiyyasa basu cika sakewa a wajensaba, balle yau yana gida. Babu wacce ta isheshi kallo yashige 6angarensa, su Rufaidah suna bedroom d'in Aysha, wasu na sallah wasu na gyara kwalliyarsu. Aysha na falo tana barci, Dan basu tada itaba, tunda sunga tanajin dad'in barcin. Harya wuce zai shiga d'akinsa ya hango Aysha na Neman fad'owa daga kujera. Da sauri yak'araso cikin falon, ahankali ya d'auketa gudun karya tada ita, yana jiyo hayaniyarsu maleekah ad'akin Aysha, saikawai yawuce d'akinsa da ita, ya shinfid'e agado yana mai kallon face nata, mamakin irin kyawu da farin da ayshan tak'ara yakeyi, yakai hannu yana shafa sumar kanta ahankali, gashin gaban goshinta kwance luf-luf, cikin tsanaki yakebin dukkan illahirin jikinta da kallo, shi saiyagama kamar tad'an k'ara k'iba, ga fatarta harwani k'yalli takeyi, gashi gazar-gazar duksun fito taciki k'ofofi dasuka k'awata shek'in fatarta. "Sholyna wane irin k'yawune haka?, ga jikinki akwai d'umi kamar bakida lafiya". 'yay maganar yana sumbatar goshinta'. Kusan mintuna 12 ya lalata wajen k'arema Aysha kallo, sannan yamik'e ya canja kayansa zuwa k'ananun kaya, wani d'an aiki yakeson fita shi kad'ai. Harya gama kimtsawa yafice tanata barcinta. Sai wajen 5 Aysha ta farka, sai zubama su Rufaidah masifa takeyi wai basu tasheta tayi sallah ba. " yo aii bamu kad'ai zakiyima jarabarba, saiki bari ya khaleel ma yadawo ki had'a dashi, tunda shiyya d'aukeki daga falon yamaida bedroom, amma bai tadakiba, kujimin yarinya kai, kodanmu kin gama rainamune?". Banza Aysha tama sadiyan, tasan inta biye mata bazata huta da surutuba. ____ Zuwa 9pm duk angama kai amare d'akunansu, ankawo nasu Ramadan 6angarenda su ya khaleel suke, suma anan aka musu gininsu. Babu inda Aysha taje, Dan ya khaleel yahana, yana gida yakasa ya tsare, dole ta hak'ura, Dan itama batajinma dad'in jikinta sosai. *_ABINDA KA SHUKA........._* (sabon buk d'ina mai zuwa insha ALLAH)😉. Masu iya magana kance abinda ka shuka shizaka girba. (Wannan batu haka yake) Asafiyar litinin misalin 11:30am bak'i wasu duksun tafima, wasu kuma na haramar tafiya kamardai mutanen Kano, dake shirin tafiya amma amai da Aysha tawayi gari tana shek'awa yasakasu dakatawa. Ana tararrabin ciwon na Aysha wadda yasaka ya khaleel rikicewa saiga mufeedah da 'yan rakkiya har mutum uku, tana rusarkuka. Cirko-cirko kowa yayi, a tsakar gidan, Dan ya khaleel ne d'aukeda Aysha zai saka amota zasu tafi asibiti, yunk'urin amai datakeyine yasakashi sauketa k'asa, yana rik'e da ita tana tsaka da kwara a man m ne motar 'yan rakiyar mufeedah tashigo gidan, ananne wasu suka raba hankalinsu biyu lokacinda akaga mufeedah tafito a motar tana sharar kwalla🤐...................✍ *_"yaro bari murnar karenka Yakama zaki"._*👉🏻🐅😱 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ _hummm kunata yad'a jita-jita feedohm tarasu, inaga wataran sai wata tace agabanta aka saka gawar wata writer a kabari, to da ranta, haka kawai kudinga jamata bala'i, wai tayi had'arin mota, please mana, haka babu k'yau, duk masoyinka Na kwarai bazai gizganya masifa a kankaba, mutuwa dolece, kokun fad'a kobaku fad'aba zamu mutu aii, amma adaina jamana masifa please._ *duk wadda ta rubuta kuma ALLAH ya shiryeta, ammafa jakace wlhy tunda ta d'auki alhakin mutane, mtsoow.* 3⃣0⃣ Ya khaleel baisan hidimar da akeyiba, shi gaba d'aya hankalinsa nakan Aysha, ya kar6i ruwan da Anty Amatullah ke basa ya wankema Aysha baki, duk jikinta ya saki, sai langa6e masa ajiki takeyi, (kunsan dai yanda amai ke saurin galabaitar da mutum), bare Aysha datakeyi tunda daddare. Anty Mamie ce tayi azamar k'arasawa garesu, ''hajia Atine lfy dai ko? Naga d'iyata Na kuka?". "Hajia Bilkisu mudai shiga daga ciki wajen Alhaji Abdallah, lfy naganku waje tsaitsaye?". " wlhy Aysha ce matar babana khaleel babu lfy, shine zamuje asibiti, amma kumuje ciki, alhajin yana nan aii". Wajen Ammah datun d'azun itama idonta nakan mufeedar Anty Mamie ta k'arasa, saida ta rissina sannan tasanar mata sunzo wajen baffane. Ammah ta ta6e baki, ''to Bilkeesu, kiyi musu iso, nasandai lalatacciyar nan ta tafka halin uwartane gidan mutane". Anty Mamie dai batace komaiba, tamusu jagoranci zuwa 6angaren baffah. Saida tafara Shiga ta sanar masa sannan tabasu izini suma. Dukda daga baya ya khaleel yaga mufeedah amma bai maida hankalinsa kantaba, yashige mota da matarsa Na jikinsa, Hafez nagaba zai tuk'asu. Harya tada motar mama tak'araso wajen. "Babanmu inaga kabar su Amatullah saisuje da Ayshan asibiti, kaga ga mufeedah dabak'i, ba'asan mike faruwaba, nasan kuma dolene anemeka amatsayinka Na babba". Marairaicema mama fuska yayi, please mama kibarmu mutafi, wlhy Aysha ta galabaita, aii su Sultan suna nan, kuma uncle ma'aruff ma yana nan, mama Dan ALLAH jikinta k'ara zafi yakeyi". Tamkar mama tayi dariya, amma saita danne, tace, " shikenan, kuje, amma idan kaga da sauk'i kudawo gida". "To mama". Hafiz yaja mota suka fice, Amatullah na agaba, shikuma yana baya rungume da Aysha. Anty shukurah ma batabi takan abinda yadawo da mufeedah ba tashiga mota itada Ramadan sukabi bayansu. Duk rugund'imin da akeyi agidan akan ciwon Aysha hajia babba naji amma kota kula, sunatama shan hirarsu da sauran bak'inta, hakama Anty zuwairah tanaji amma tayi kunnen uwar shegu, saima k'ok'arin had'a sauran kayan mufeedah takeyi wai su najwa suje su kaimata. Fitowar su Najwa zasuje gidan mufeedah ne sukaji k'ananun magana Na tashi akan dawowar mufeedar, dasauri suka koma suka gayarama hajia babba. Da Sauri tamik'e tana fad'in, " ke shashasha mikike fad'ane?". Baki najwa ta zun6uro gaba, "Niba shashasha baceba, kajimin momynnan, bajinayi ana gulmaba awaje, wai tana 6angaren baffah Anty mufeeyn". Da sauri Momy da zuwairah suka nufi 6angaren baffa, kotakan jama'ar tsakar gidan basubiba. Mufeedah Na k'asa, 'yan rakiyarta da baffa da ammah Na zaune. Wayace a hannun baffa yana kiran Ameenudden, Dan yafison ayi komai a gabanshi. Babu dad'ewa ameenudden yad'aga, cikin ladabi ya gaida baffa. Baffah ma ya amsa cikin kulawa, yace, " yarona Ameenu kana inane?". "Baffah ina gida". ''gidanka konan gidanku?". " a'a gidana". "Idan ban takurakaba kazo INA nemanka". " to baffah inazuwa". Dama ashirye Ameenu yake, yasan dolenen anemeshi, tunda mahaifiyarsa da yayyensa biyu kawai sukasan miya faru, wad'anda suka raka Mufeedah kuwa Yayar babansace da k'anwar mamansa. Babu dad'ewa saiga aminudden. Cikin girmamawa ya gaida kowa dake falon, Yakoma kusada mufeeda k'ad'an ya zauna. Baffah ya kalli Anty Mamie, "Bilkeesu ina Mu'azzam da Sultan?". " babana yatafi kai Aysha asibiti, saboda tanata amai, saidai akira Sultan d'in". ''Ya salam, shine ba'a sanar daniba, yaushe abin yafaru". "Kayi hak'uri baffansu, wlhy dukmun rud'ene". ''To ALLAH yabata lfy, bara agama da wannan matsalar saimu bisu, kiramin sultan da Mujahedeen awaya........ Shigowar hajia babbane yasaka kowa waigawa ya kalleta, mufeeda tatafi da gudu tafad'a jikinta tana kuka. Tsawa baffa yadakama mufeedah, ''Dan ubanki dawo ki zauna, kafin Na sassa6a miki kamanni". " tofa zaka raba 'ya da uwane?". Banza baffah yayma Momy, kuma babu Wanda yasake tankawa, dukda surutai da Momy ke saki marasa dad'i, wai ba'a kirataba, amma ancika mak'iyanta da falo sun saka mata 'ya tsakkiya. Cik'in 'yan rakkiyar mufeeda hajia Altine tace a lallai, Ashe da dalili shiyyasa matarka babu tarbiyya Aminu?". Kowa dai yay shiru ba'ace komaiba, harsu ya Sultan suka shigo. Ananne baffah yay gyaran murya, tareda sallama, yace, "aminuddin mike faruwane?". Kafin yayi magana hajia babba ta kar6e, wlhy bazai yuwuba, saidai kowa yafice yafad'a dagani saikai da mufeeda, amma baza'a fad'i komai gaban kishiyoyinaba". Tsaki baffa yayi, yad'auki waya yakira mama da umme amarya, yace suzo yana nemansu. Cikin k'uluwa hajia babba tafara zuba jaraba. Amman Ce ta taka mata birki, Laure wlhy inbakiyi shiruba yanzu zakibar falonnan, kokuma nasaki nadama. Saida Momy ta gatsina baki sannan tayi shiru, tasandai wacece ammah, bata d'aukar raini. Su mama suna isowa kowa ya zauna, sannan baffah yasake maimaitawa Aminu tambayar. Kan aminuddin ak'asa yace, "baffa ka gafarceni da abinda zan fad'a, nasan wannan ba tarbiyyar gidanka baceba, Dan kamalarka data yaran gidannan yasakani kwad'ayin auren mufeeda, wlhy koda hakan ya bayyana ban zargekaba, shiyyasama namik'a zancen ga magabatana". "Tunda aka kai mufeeda gidana ranar asabar da zazza6i taje jikinta, ni duk Na d'auka gajiyar bikice tasakata zazza6in, haka muka kwana babu dad'i dai har safiyar jiya lahadi, shine nakira family doctor namu ya dubata, yay mata text yace zaije ya bincika yau zai kawo mana sakamako, ganin yanda takejin jiki sosai ajiyan, kuma maganin da doctor yabata zazza6in yak'i sauka, harma tana ganin jiri, gashi tak'i cin abinci har 4 Na yamma, shine nasake kiransa, hak'uri yabani akan bara ya bincika text d'in daya mata, saiyazo da sakamakon, dakuma maganin daya dace tasha. Nacemasa shikenan ngd. Wajen misalin 8:30 saigashi yazo, saidai duk yanayinsa ya nuna a sanyaye jikinsa yake, kirana gefe yayi yabani result d'in. wlhy baffa Dana bud'e saida juwa ta kwasheni, saida doctor Ameer yarik'eni saboda tashin hankalin abinda ke ciki. Dana dawo dai-dai nahaushi da masifa akan baisan aikinsaba, yanata bani hak'uri dason fahimtar dani amma nak'i saurarensa, saina d'auketa mukaje Rahma especial hospital, amma bayan gama dubata result d'in duk d'ayane dana doctor ameer, saidai saboda bushewar zuciya irinna mufeeda ta dage akan k'aryane wlhy, tun a asibiti muka fara fad'a, ganin abin zaiyi tsamari karnaje Na daketa Na illatata nakira ummi Na Na sanarmata komai, tun a Daren sukaje suka taho da mufeeda nan maitama, anan gidanmu takwana". "Humm mi result d'in ya nunane Aminu?". Farar takarda Aminu yamik'ama baffah kansa ak'asa. Baffah ya kar6a zuciyarsa Na harbawa, jikinsa a sanyaye yamik'ama Ya sultan, Dan bazaiso yafara ganiba, gudun karyaga abinda zai saka zuciyarsa bugawa. Ya Sultan yabud'e takardar yafara dubawa, saida yamik'e tsaye Dan tashin hankali, har zufa saida tafito kan goshinsa, murya Na rawa yace, " mufeeda kin 6ata sunan gidanmu, da girmanki kije wani yamiki cikin shege harna tsawon watanni uku, kuma kinssan da hakan amma kika bari aka d'aura miki aure dawani?". Duk falon kowa sallallami ya d'auka, baffah kam yakasa koda motsi, hajia babba kanta ture mufeeda tayi daga jikinta, ta fisge takardar daga hannun ya Sultan tana dubawa, jikinta sai 6ari yakeyi kuwa, aii batakai k'arsheba tazube awajen. Zuwaira da ya sultan dasu mama duk sukai kanta, ya mujahedeen kam sarkin zuciya aii kan mufeedah kawai yayi yahau duka kamar ALLAH ya aikoshi. Da k'yar Aminuddin ya kwaceta a hannunsa, please ya mujahedeen kayi hak'uri kasan ba ita kad'ai baceba, kar dukan yajawo wata matsalar". "Kabarni Ameenu, sainama yarinyarnan dukan mutuwa tafad'i yanda akayi, munafuka afuska kamar bazata iyaba, idanma ka hanani dukanta wlhy ya khaleel yadawo saiya kusan kasheta agidannan". Duk da hakadai kayi hak'uri Dan ALLAH, nima danya zama dolene asani shiyyasa nafad'a wlhy". Ammah da hankalinta nakan d'anta baffah tace Ameenu kabarsa yadaka fitsararriyarnan, Mujahed kiramin Babanku Ma'aruff awaya. Ya mujahedeen yana huci yakira uncle Ma'aruff dayaje gidan wani abokinsa. ____________________________ Lokacin da ake bak'incikin cikin dake jikin Mufeey baby🤣, ya khaleel nacan Na farincikin result d'in kazarsa da Aysha taci tabiya a asibiti. Gwajin farko doctor Faisal ya tabbatar musu Aysha ta harbu, cikin watanni biyu da sati 👆🏻😀. Wayyo zokaga bidiri wajensu anty Shukurah da Ama... Oga kwata-kwata kam rungume Aysha yayi dukda tana barci ansaka mata k'arin ruwa, hawayen farincikine ke zirara a kumatunsa, wai yau shine za'a haifama d'a, gudan jininsa, wanda dole akakira sunan d'an ahad'a da nasa sunan, duk inda 'yar ko d'an yaje za'ace d'an/'yar Ibraheem khaleel ce, wayyo ya ubangijina, kaike bada k'yautar da kud'i ko mulki bazasu sayaba, kaike bada abinda babu wani mahaluki aduniya dake ikon bama mutum ko hanashi sai kai kad'ai ubangijin talikai, ngd maka godiya mara adadin k'ididdiga, godiya irin wadda tafi k'arfin harshe, saidai zuciya taita ayyanawa. Duk su Hafiz cirko-cirko sukayi suna kallonsa, kowa fuska d'aukeda murmushi, yau sunga farincikin d'an uwansu. Cikin tsokana hafiz ya kirashi, "ya khaleel tunda nina kawota asibiti idan ta haifi namiji sunana za'a samasa". Dariya duk sukayi, harda ya khaleel da idanunsa ke a lumshe, ya kwantar Aysha ahankali yana kallon Hafiz, " Hafiz ko sunan 'yan gidanmune duka zan iya sanya masa ko mata kaji". Nanma duk dariya sukayi, Hafiz yaciro waya zai kira gida yayi kwarmato Anty shikurah ta dakatar dashi, "A'a Hafiz dakata, dolenefa mufad'a yanda za'a bamu goron Albishir, wayakamata afara kira?". "Anty!, baffah ko Ammah". " yes akirah Ammah, tunda itace tushen kowa". Hafiz ne yakira Ammah, dukda yanda ta amsa sallamarsa bai damuba, Dan zumud'i baisa yagane muryar tata da damuwaba, "Ammah Albishirinki". Cikin dakewa amma ta amsa da goro, Dan batason katsema Hafiz farincikinsa, dantaga azumud'i yakirata". " mizaki bani to?". "Duk abinda kakeso bayan kafad'amin kaza6a". " anzo wajen, Anty Ayshan ya khaleel tanada ciki". Da sauri Ammah tamik'e tsaye tana fad'in Alhmdllh, yanzu kuna inane?". "Muna asibitin doctor Faisal, ansaka mata k'arin ruwa tana barci". Duk jama'ar falon suna kallon Ammah ne, jira kawai suke tagama wayar ta sanar dasu abinda yasakata farinciki, dukda suna cikin bak'inciki. Tana yanke wayar kuwa tayi gud'a, dafad'in "Alhmdllh. Dama wani Na haddasa maka damuwa wani yana yaye maka, matar iroce da ciki". kowa saida yafurta Alhamdllh, banda hajia babba data farfad'o yanzu, hakama Anty zuwairah bak'inciki kamar zai karta. Tuni kowa yadaina damuwa da cikin mufeedah yakoma murnar Na Aysha, mama dai batace komaiba itama, saboda kara. Bayan uncle ma'aruff ya iso akabama dangin Aminu hak'uri, aka kuma sanar dasu za'azo har gida ak'ara bada hak'urin. Annakuma take Aminuddin cikin jin kunya yabama mufeedah saki d'aya. Babu Wanda yaji haushi, saidai mufeedarce ta rushe da kuka, momyma kukan zuci takeyi. Sudai su Aminu sukayi sallama suka tafi, bayan sunmusu murnar cikin Aysha. Babu wanda yasake bi takan mufeedah, Dan hukunci kuma sai'an zauna, baffah ya sallami kowa, suka d'unguma zuwa asibiti. Momy dai da Anty zuwaira basubiba.🤣.lol. ******** Labarin cikin Aysha dana mufeeda yakarad'e gida, harda result d'in saki d'aya. Kowa saidai yace ALLAH ya k'yauta, Na Aysha kam sai murna sukeyi, musammanma 'yan Kano. Amma da baffah dawasu cikin 'yan Kano da uncle ma'aruff dasu Sultan, Anty Mamie duk suka d'unguma zuwa asibitin. Har lokacin dai Aysha bata farkaba, ya khaleel yana manne kusada ita yak'i ya matsa konan dacan, jiyake yana matsawa wani Abu zai iya samun matarsa da cikinsa. Su Anty Ama....... Sai dariya suke masa kuwa, INA ko'a jikinsa, dama ya khaleel da son yaran tsiya, barekuma yau ganashi😁. Su baffah sun iso anatama juna barka da addu'ar ALLAH ya sauketa lfy, ya khaleel kuma duk sai kunya tad'an kamashi, sai sinne kai yakeyi kuwa. Harma abin yabasu dariya, Ammah ta tasashi gaba da tsiya kuwa, shiru yayi yakasa maida mata, saidai su ya Sultan ke karemishi da uncle Ma'aruff. ____________________________ Sai kusan 1 Aysha ta farka, lokacin su ya khaleel sun fita sallah, Anty Mamie Ce kawai da Ammah, saisu Anty Shukurah dawasu daga bak'in Kano da gwaggo bintu, duk suma sallar sukeyi.. Aysha tabud'e idanu da kyar, ledan ruwan tabi da kallo har k'arshe, ta lumshe ido tareda maida kallonta Kansu Anty Mamie dake sallah, aranta tace ni Aysha nice da kwoncia asibiti? Banta6a ciwon daya kwantar dani asibitiba, ta yunk'ura danta tashi amma saida kasa, saboda jikinta babu kwari, kusan tun shekaran jiya rabon Aysha dacin abinci, saidai taci wannan taci wancan, shima 'yan yame-yamene, bawai abincin kirkiba. Komawa tayi takwanta tana sauke numfashi da k'yar, Anty Mamie ce tafara hangota, da Sauri tamik'e ta k'arasa gareta, ''Aysha kin tashi?". Kanta ta iya d'agama Anty Mamie da k'yar, sannu kinji, mike miki ciwo yanzun?". "Anty Mamie yunwa nakeji wlhy". " ok... To mizakici?". Shigowarsu ya khaleel yakatsema Aysha bada amsa, duk suka k'araso gaban gadon da sauri, suma su Ammah sun idar. Sannu duk suketa mata, ya khaleel kam yakasa cewa komai, sai kafe Aysha yayi da idanu, jiyake kamar ya tsaga jikinsa yasakata. Itadai sau d'aya ta saci kallonsa. Anty Mamie takuma cewa ''fad'i mikikeson ci a nemomiki?". Saida tad'an yatsine fuska sannan tace, "Anty Mamie kaza gasashshe, da papcorn, da waina masa, sai kuma ice-Cream da shinkafa da wake, garau-garaufa irin adafata daga attarugu sai manja kad'an da daddawa". Kutttt miza'ayi inba dariyaba🤣🤣🤣, har baffah dariya yake mata. Ya khaleel kansa harda jingina da bango saboda dariya. Itako ta turo baki, danmi za'a mata dariya, itafa da gaske yakeyi duk zata iya cinyewa🤣🤣🤣🤣. Ho sholyn sadauki, nimafa kinbani dariya, nasan dolene fans ma su dara🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣. Saida suka gama cin dariyarsu sannan uncle ma'aruff yace, '" karki damu d'iyata, yanzunnan zaki samu duk abinda kikeso, amma bara afara siyo miki abinda ke kusa ko?". Kanta ta gyad'a masa tana murmushi. Ya khaleel aransa yace lallai ba'a biyani kazata abanzaba ashe.😉😂 Babu dad'ewa saiga ya Mujahedeen yadawo da kaza, harma dawasu abubuwan. Sanda yadawo nurse tashigo tacirema Aysha k'arin ruwan, aka kawo mata wata tasa ta wanke bakinta, sannan Anty Mamie dakanta tadinga bata kazar, saidai kuma bataci ta kirkiba labarin ya canja, tafara yunk'urin amai, kafin abata wani taimako tafara kwarashi. Duk kuma sai tausayita yakamasu, kowa fuskarsa ta canja, saida tagama sannan nurse suka shigo suka gyara wajen, ya khaleel kamar zaiyi kuka. Doctor Faisal dakansa yashigo yakuma dubata. Cikin damuwa ya khaleel yace, "yanzu nan doctor haka zatayita amayar dad'an abinda tasamu taci?". " saidai hak'uri j!, amma inaganin kawai mutafi gida da ita saina saka mata wani k'arin ruwan a can, zaima taimaka mata akan cin abincin, koya kukagani?". "Hakan yayi doctor". 'cewar baffah'. Kowa yayi na'am da zancen. Saida doctor yayma Aysha Allurar barci sannan suka tattara suka fito, ya khaleel ya d'auketa kamar wata 'Yar babie, to dama tsawonne kawai, garama cikinnan yasakata 'Yar k'iba. Koda suka Isa gida sai Ammah tadage akan 6angarenta za'akai Aysha, dole aka yarda a hakan saboda jarabar Ammah, inba hakaba kuma ta buwayi kowa😂. 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀sai Ammarmu ko k'asar ba kowa wlhy🤣🐀. Ya khaleel kam baiso wannan tsari Na Ammah ba, yaso yabama matarsa kulawa da kansa, dukda dai yasan dawuya aikinsa yabarsa, ballema yanzu da aiki yagama rinca6e musu, cases sunyi yawa a hannunsa, wasu ana kan shari'a a Cote, wasu kuma anakan bincike, wasuma basu kamasuba. Hakadai yadire Aysha a doguwar kujerar falon Ammah mai taushin tsiya, 😉komaifa Na Ammah Na musamman ne😜. Saida doctor Faisal yagama d'aura mata ruwa yatafi sannan 'yan uwa sukaita shigowa dubiya, 'yan Kano dai tafiyarsu saikuma gobe. Mamaki yacika zuciyar ya khaleel danbaiga giccin Momy da sauran k'annensaba, Anty shukirah ce kawa. Ficewa yayi yanufi 6angarenta dam duba ko lafiya?................✍🏻 *_kuzo mu yanka cake tawan (Xoxo) tasamu lafiya,😀👯‍♀🔪🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂, kowa dai yamaida kwad'ayinsa saita faraci😉🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀_* *_ina Reefat yahaya 'Yar team d'in Hajia babba? Yakamata kimatso kusafa, takusa 6arewa daku🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀😂_* Koya kukace fans?🤷🏽‍♀🤣. *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ _Gaisuwa da fatan alkairi agareki takwarata, Bilkisu, *(Ummie Garkuwa writer d'in JENNIFER)* ALLAH yabar zuminci, ina godiya agareki har babu adadi, I love you so much wlhy my Sister._ ❤❤❤❤💃🏻 3⃣2⃣ Da dariya ya isa 6angarensu, yacire kaya yashiga wanka, can k'asan zuciyarsa kuwa tana cikin nishad'i, yayinda gefe guda kuma yake tunani akan matar da taheer ya tabbatar masa tana cikin gidansu, dadai Aleeya zuciyarsa ke zargi, amma idan yatuna da cewar ance kwannanta uku agidan saiyaja tsaki, afili yace, "to wacece wannan?". Haka yayta sak'awa da kwancewa harya kammala wankan yafito, gaba d'aya kwakwalwarsa a dagule take, abubuwa biyu sun gitta masa a ranar farin cikinsa, ranar data kasance yadace yayta murmushi har washe garinta. K'aramin tsaki yaja, sannan yahaye gado yakwanta danya d'an huta. ____________________ Farkawar Aysha tasaka ammah saurin isowa gareta, sai sannu take mata, Aysha kuma tana d'aga kai da k'yar, ta yunk'ura zata tashi taji hannunta yamata nauyi, dakatawa tayi tabi hannun da kallo. Ammah tace, "karki tashi. Bara nakira iro yazo yacire miki, shima nazata bama zaiyi nisaba aii". Aysha dai batacewa Amman komaiba. Kiran ya khaleel Ammah tayi, bayan tagano Alamar data sakama number sa da k'yar, harta yanke bai d'aukaba, kunsan dai Ammah babu sauk'i, tacigaba da doka masa kira babuji babu gani. Tun yanajan k'aramin tsaki cikin yanayin barci, harya bud'e idonsa ahankali, sosai kirannan yatakurasa, batareda yaduba wake kiransaba yad'aga yakara akkune, a muryar barci yace, "hallo! Please wanene". ''Iro nice, kazo kacirema Jikata wannan ruwan ta farka". Da sauri yatashi zaune, ''Ammah kina nufin A'eesha ta farka?". "Eh, kana inane?". " ganinan zuwa". Bai jira cewartaba ya yanke wayar, sakkowa yayi daga gadon yashiga bathroom, mintuna kusan 5 yafito. ******* Da sallama yashigo, haryanzu Aysha Na kwance Ammah ta hanata tatshi, yak'araso da saurinsa, gaban kujerar ya durkusa saitin fuskar Aysha, idonta Na a lumshe yasaka hannu yana shafa kwantaccen gashin goshinta, ahankali ta bud'e shanyayyun idanunta, wad'anda ciwo yasakasu komawa k'ananu kuma sunyi d'anja. Sassanyan murmushi yasakar mata, sannan ya sumbaci goshinta, ta kuma lumshe idanunta tabud'e ahankali bisa fuskarsa. "Babiena ya jikin?". Cikin mamakin sunan daya kirata dashi, muryarta can k'asa tace, "Alhmdllh." " masha ALLAH, bara kiga acire ruwan tunda yak'are" kanta ta jinjina masa kwai. Yacire ruwan sannan ya taimaka mata tatashi zaune, daidainan Ammah tafito daga kichin d'aukeda kula k'arama. Sannu itama tama Aysha, sannan tazauna gefenta tana tambayarta ina kemata ciwo yanzu?. Aysha tace babu komai, saidai bakinta d'aci. "Karki damu shima zai daina watarana?". Nanma kanta kawai ta d'agama Ammah. Ya khaleel yad'an murza hannunta dake cikin nasa, tajuyo ta kallesa. Gira d'aya yad'age mata, yace, " mizakici yanzu to?". Janye idanunta tayi daga kansa, tad'an jingina kanta da gefen hannunsa, Dan zaman yafara gundurarta, cikin dadishewar murya tace, "dama zan samu dafaffen gyad'a". Murmushi yayi yace, " saikuma mi?". "Shikad'ai ya isheni ya Sadauki". Yashafe fuskarta da hannunsa Na haggu, " haba my Sholy kidai fad'i wani abun bayan gyad'an, kinsan bakici komaiba". Ta d'ago idanunta tana kallonsa, fuskarta a yamutse tace, nidai gyad'an is OK, idan kuma za'a samu zogale ahad'amin dashi to". Ammah dake kallonsu cikeda sha'awa dajin dad'i tace, "Abu mai sauk'ima kuwa, bara ajenan gidansu Ameenu arok'o zogalan tunda sunadashi, barama dakaina zanje aii". "Yauwa Ammah jar wuya, shiyyasafa nake yinki akoda yaushe, dolene nasiya miki motafa". Baki ammah tawashe. "Lah iro gaske ko wasa?". " ahaf aii dagaske nakeyi ammah, amma sai nanda k'arshen shekara idan ALLAH ya kaimu, yanzu abubuwa sunmin yawa". "Yo konanda shekara biyune aii zanhak'ura iro, kaidai kawai kacika alk'awari idan munkai daranmu". "Insha ALLAH zancika ammah". Ammah tafita anata washe hakwara ya khaleel zai saya mata mota. Tana fita ya khaleel yamaida kallonsa ga Aysha yana murmushi, A'eesha kinfaji Ammah tsohuwa, ko INA ita INA mota?". Murmushi Ayshan tayimasa, tace, " Yaya kacika alk'awari kawai". Harar yazuba mata. tace, "o, sorry sadauki, tayi maganar tana rufe bakinta da hannu. guntun murmushi yayi, sanna yamik'e da Aysha ajikinsa yana fad'in muje kiyi wanka, kafin Ammah takawo zogalan ko, tunda kinsan saita dafa tukunna. Cikin 6ata fuska Aysha tace, "to gyad'anfa kuma?". Yatsansa guda d'aya yasaka ya d'alli bakinta. Zafi yasakata dafe bakin da sauri. Shikuma yay murmushi yakaita toilet d'in Ammah. Dak'yar ya yarda yafito tayi wankan da kanta bayan yahad'a mata ruwa maid'an zafi, amma da ya dage saiya mata wankan dakansa. Ganin shagwa6ar datake zuba masa zata sakashi ya narke, yasakashi hak'ura yafita. Tanayi tana hutawa, haka tagama wankan, saboda jikinta duk babu k'wari, ga ko INA ciwo yake mata, musammanma mararta wlhy. Koda tafito abakin gadon Amman ta iskeshi zaune, yabud'emata hannayensa alamar tazo gareshi. Akunyace tak'arasa tashige kuwa, ya rungumeta tareda gyara mata zama acinyarsa, ahankali ya sumbaci goshinta, murya k'asa-k'asa cikin kunne yace, " nizan shiryaki ko? Tunda kin hana namiki wanka". "kai ya khaleel wai bakajin kunya? Ammah fa zata iya shigowa ta ganmu". Hannu biyu yasaka ya tallafe kumatunta, sai raba idanu yakeyi a fuskarta, itakam takasa kallon cikin idonsa, saikawai ta lumshe idanu, ganin haka yayi murmushi tareda d'ora bakinsa akan NATA yashiga abubuwa. Tun tana k'ok'arin kwace kanta harta hak'ura ta mik'a wuya. Saida ya sumbaceta San ransa sannan yacire bakinsa suna sauke numfashi. Kunya ta lullu6e Aysha, tayunk'ura ahankali zata tashi Yakuma rik'eta da k'yau, "kinga Izamanki, bara Na shafa miki man, nasan jikinki babu kwari sosai". Dole Aysha tahak'ura ya shafa mata man, amma idonta arufe akayi komai. Kwantar da ita yayi agadon Ammah yace, " kwanta kihuta inazuwa". Ta gyad'a masa kai tana wani lumshe idanu, jinta takeyi wani fayau da ita yau d'inan wlhy. Fitar ya khaleel babu dad'ewa saiga Anty Ama.. Tashigo, k'arasowa tayi Indaa Aysha take tana mata sannu, Aysha ta amsa kanta tsaye, harda cema Anty Ama wai mi doctor yace yana damunta?". 'Yar dariya Anty Ama tayi, tace, "ya khaleel nasan aii zai fad'a miki, yasan kin tashine?". Aysha ta gyad'a kanta ahankali, kamar wata k'adan garuwa.. Babu dad'ewa ya khaleel yakawoma Aysha da doguwar riga Arabian gown, Anty Ama tatashi tafita. Yanzuma dakansa yasakama Aysha kayan, duk kuwa kunyarsa ta gallabeta, harzai d'auketa tace, "please Anty Ama batatafiba fa". Yad'an d'age gira yana ta6e baki, harya mik'o hannu zai d'auketa yajiyo sallamar Anty mamie a falo. Dole ya dakata, yadai taimaka mata tamik'e zaune, dad'an rangajin rashin kwarin jiki ta isa falon, Anty Mamie tayi saurin tararta tana mata sannu, a kujera doguwa ta zaunar da ita ta jinginata da jikinta, yanzu ina ke miki ciwo?". "Wlhy Anty Mamie dukdai banajin dad'in jikina, gakuma bakina d'aci". "Sannu, Duk zasu daina kinji." Ya khaleel kallonsu yakeyi cikeda sha'awa, saiyaji inama momyce kebama matarsa kulawa haka? kwallah suka cika idanunsa, karo Na farko dayafajin d'acin rashin kulawar Momy akansa, da k'yar ya maida kwallan, saidai tuni Anty Mamie tagani, ita kanta saida ranta ya sosu, Dan koba'a fad'aba tasan mi khaleel keyima kewa, (kulawar mahaifiya), amma yaza'ayi, haka ALLAH ya tsara masa. Sallamar da Ammah ta doka yasakasu duk maida hankalinsu kanta, Anty Ama...tamik'e ta kar6i kayan hannunta tana mata sannu, "a'a Ammah mi'aka samomana kuma?". " uhm mizan samo nikuwa, zogalene da gyad'a, wai Indo kesonci". "Kai Ammah waye indo kuma?". Da hannu Ammah ta nuna Aysha, "matar iro mana". Mi Anty Mamie kuwa zatayi inba dariyaba, ya khaleel kam 6ata fuska yayi, Amma baice komaiba. Zogalan Aysha tafaraci, babu laifi ansamu ya zauna, harma tad'anci gyad'ar. Daganan akaita shigowa dubata, mama ma tazo, hakama bak'in 6angaren Momy da Anty shukurah tamusu jagora, Amma banda Aleeya da Anty zuwairah da kubrah, dama mufeedah ba'a sakata a lissafi, su Hasnah kuwa suna makaranta. ***** Momy kuwa sai bayan magriba ta farka, bayan k'arin ruwan yak'are Aleeya ta cire mata. Ya khaleel baije wajenba saida yadawo sallar isha'i, yatarar Momy zaune akan gadonta ta jingina da fuskar gadon, shayi takesha Wanda Hasnah ta had'a mata. Yazauna kusada ita gefen k'afafunta, " momyna ya jikin?". Ahankali tace, "da sauk'i Ibraheem, kana ina nafarka tun d'azun ban gankaba?". " naje sallah ne, kinsan kuma itama Aysha babu lafiya, nad'an lek'ane naganta shine nawuto nan, bammasan kin farkaba." Batace komaiba dangane da Aysha, Dan bak'aramin sosuwa zuciyarta keyiba idan tatuna da cikin jikin Aysha, gakuma babban bak'incikinta Na mufeedah, babu abu mafi hassala ranta sai idan tatuno wai Habeeb ne ya lalata mata rayuwar yarinya, yaron datasanshi afagen iskanci, babu nau'in zina wadda za'ace habeeb baiyitaba, wai shin yama akayi yashiga rayuwar mufeedah?, bayan kobarinsu zuwa gidan hajia khaltum batayi, saboda tasan gidan tamkar rezane da katifa awajen had'ari, wasu zafafan kwallan suka gangaro bisa kumatunta, ita kanta batasan kuka takeyiba. Ya khaleel yasaka hannayensa yana goge mata cikin tausayawa, muryarsa a raunane yace, "haba Momy, Dan girman ALLAH ki kwantar da hankalinki, kinsandai bakida isashshiyar kafiya, yaufa bak'aramin hawa jininki yayiba, ALLAH ne kawai ya taimakemu Doctor Faisal yazo kawo magungunan A'eesha, Amma da kafin mukaiki asibiti ansamu matsala, kicire batun mufeedah aranki, kid'auki hakan amatsayin k'addara, kuma bawai na k'yale baneba, dolene nad'auki mataki akansa". Jin jina masa kai kawai Momy ta iya, Amma itakad'ai tasan irin tafarfasarda zuciyarta keyi, aii wannan yak'in natane, dolene tad'auki mataki da hannunta, Dan habeeb bai Shata abanzaba, tsorontama ALLAH yasa baida wata cutar dazai zubama mufeedah batajiba bata ganiba, saikawai tarushe da kuka data tuno lalacewar rayuwa irinta Habeeb. Ba ya khaleel ba, hatta inna jummai mahaifiyarta kukan d'iyarta yad'aga hankalinta, sukai cirko-cirko suna kallon yanda ya khaleel ke lallashinta, dak'yar yasamu tayi shiru. Bayan tagama shan shayin da ya khaleel ya lalla6ata, ya 6alle magungunanta yabata tasha, baffahma yashigo yadubata, kusan mintinsa 30 sannan yafita, hakama su mama duksun shigo sun dubata, dukda dai k'in amsamusu tayi, danji take kamar takashesu tahuta Dan bak'in cikin sanin sirrinta dasukayi, saidai babu damar hakan kuma.🤪 *********** Kusan 10pm ya khaleel Yakoma 6angaren Ammah, ya tarar Aysha hartayi barci, Ammah ma zaune take tana kallo da gyangyad'i, Amma dan k'unata tak'i taje ta kwanta, wai film take kallo, gashima ba Hausa akeyiba bare ace tanajin misuke fad'a, kamarma yaren Germany akeyi. Cikin sand'a yawuce tabayanta yashiga bedroom d'inta, Aysha Na kwance a gadon ta k'udundune da k'aton bargon Ammah, barci takeyi, saidai dagani kamar batajin dad'in barcin, yakwanta ahankali ta bayanta, mannata da jikinsa yayi, yasaki sassanyar ajiyar zuciya, idonsa alumshe ya sumbaci wuyanta yana shinshinar k'amshinta, yasan Aysha dabance a fagen tsafta, ko 'Yar ahekara 100 taganta tabari, gabanta yadawo, yasumbaci goshinta da la66anta data ta6e kamar zatayi kuka, murmushi yayi yana zagaya la66an da d'an yatsansa, kamar tasan miyakeyi tagyara bakinta yakoma normal, wani murmushin yasaki, sannan ahankali yad'ora bakinsa, kad'an yay kissing d'inta yajanye bakinsa, saboda motsi data fara. Maganar Ammah yajiyo sama-sama, dasauri yatashi Yakoma bakin gadon ya zauna, addu'oi yayma Aysha ya tofeta dasu, jiyake kamar karya barta wlhy, Dan yana buk'atar jinta ajikinsa, amma yasan jarabar Ammah bazata yardaba, gwara yabarta nanda kwana biyu saiya lalla6ata tabashi ita. Ammah data shigo tarik'e kunkumi👯‍♀, "kaikuma yaushe kashigo saikace wani Aljani?". " kinacan kina gyangad'i yazakisan Na shigo". "Kajimin d'an jakar uba, yo bakaida matarka bane kuka jamin, tunda safe bakubar uban kowa yayi barciba, nitashi katafi saida safe". " ko bakicebama zantafi aii Ammah, saidaifa ga amanata nan, nabaki kirik'e gam-gam, karki saki baki kita barci taita shan wahalar ciwo cikin dare". "Ank'i kar6ar Amanar taka, tashi kafita kafin nakira ubanka nasanarmasa". "A'a aiba'azo nanba Jar wuya, kinga saida safe, nasanki jar wuyace, dolene nayi shakkarki".. ''Kaidai kasani fitsararre dogon banza". Haka taita mitarta ita kad'ai, saida tayi mai isarta sannan ta kwanta tayi musu addu'a, Dan Ammah akwai kulada addini, shiyyasa ta tsaya tsayin daka jikokinta suka samu ilimin addini, gashinankuwa kowa yanacin ribarsa. Damma zakkar mufeedah dasuka fitar. Nace, " itama Jamata akayi aii🤷🏽‍♀". _____________________________ *_Washe gari_* Dak'yar ya khaleel ya iya tashi, Dan baisamu barciba sai gab da asubahi, bayan yagama nafilfilinsa kamar yanda yasaba, yay addu'oi da mik'a godiya ga ubangijin talikai, dayay masa gagarumar k'yauta, yayta jero kirari wa ALLAH, harda kukansa. Around 2 yakwanta, Amma sai barcin ya gagaresa, jiyayi yana kewar matarsa, gashi dama tunda yadawo daga tafiyarnan basu sakeba, saboda bak'in Kano dasuka sauka 6angarensu, gakuma hidimomin biki da rashin lafiyar Aysha,, har kusan 3:19am yanata juye-juye, iskar asubace data kad'a barcin ya kwashesa, shinefa haryatashi duk babu dad'i. Alwala yayi yafita masallaci, bai dawo gidanba saida gari yay shaaa. 6angaren Ammah yashiga, yatarar tana lalla6a Aysha tayi sallah, itakuma tana complain d'in jiri take gani. Yamatsa yarik'e Ayshan, yace, "Ammah jekiyi azkar d'inki, bara Na taimaka mata tayi sallan". ''To iro", 'Ammah Tafad'a tana sakar masa hannunta Aysha. Da taimakonsa tayi sallan, tana idarwa tazame ta kwanta awajen, d'aukarta yayi yamaida bisa gadon sannan yafice. Itama Momy yaje yadubata, sannan Yakoma 6angarensa yay shirin office. Cikin Suit blue black yafito, yayi k'yau sosai, sai baza k'amshi yakeyi, (duk bin kwankwantonka Baka Isa banbance turaren ya khaleel ba), kullum dakalar k'amshin dazakaji yanayi, saida yashiga suka gaisa da baffah, hakama uncle ma'aruff, yashiga kowanne 6angare Na Matan gidan suka gaisa, sunyi sallama da 'yan Kano yamusu alkairi, Dan yau zasu wuce, kai dukma wani bak'o da biki ya kawoshi yaune zai wuce, harda Na 6angaren Momy, dama kusan dangin babantane dakuma k'awayenta, saikuma innah jummai, Amma yaga alamar itad'in ba yauba, kakarsace Amma babu wata shak'uwa tsakaninsu, Dan bata sakewa dashi ko jansa a jiki, shima shiyyasa ya watsar da lamarinta, saiyaje Jigawa sau uku bai lek'a Inda takeba, gwamma yaje gidan inna mahaifiyar Anty Mamie susha hirarsu, taita masa gata kamar itace kakar tasama ta gaskiya, shiyyasa shima yakeji da ita kuwa. Yashiga 6angaren Ammah ya tarar har yanzun Aysha barci takeyi, Ammah tamatsa masa yasha tea a tsaitsaye yafice, bayan ya ajiye mata kud'i wai ko Aysha tana buk'atar wani Abu. Godiya Ammah tamasa tarakashi da addu'a, shikuma yafita yana amsawa cikin jin dad'in addu'ar kakar tasa mai sonsu da k'aunarsu. Yana fitowa suka had'u da Ema... sai Samuel, yaukam babu Adams, yanacan yanashan amarci.🤪.lol Samuel ne yau amazaunin Adams, bayan sun gaisheshi da salute nashi Sam...yabud'e masa mota yashiga sannan yamaida yarufe. Sauran securitys nashi suma duk suka shiga mota sannan suka tafi. ___________* Yakamata kibar kukannan haka mufeedah, ninama rasa miya kaiki aikata hakan batareda d'aukar wani matakin kare kaiba, haba mufeedah, ba'a bama namiji kai hakanan babu tsaro aii". Cikin share kwallan mufeedah tace, "wlhy Anty kubrah bansan hakan tafaruba, dan saida nad'auki kowanne mataki, nibanma San miyaja ra'ayinaba wajen aikata zina?, dukda nasan buk'atar aure da yaudarar beeb guy ta tataka rawar gani wajen zirmani, bawai abinda Na aikata bane yasakani kuka, asarar miji mai k'yak'yk'yawan hali irin Ameenuddin danayine yake ta6a zuciyata, wlhy inasonsa Anty Kubrah, Amma kowa yakasa fahimtar hakan". Rungumeta kubrah tayi tana lallashi, saida mufeedah ta tsagaita da kuka sannan tace, ''ki kwantar da hankalinki, da yau zanbar k'asarnan, amma saboda matsalarki Na dakata, yanzu zanje Lagos insha ALLAH agobe zan dawo miki da maganin dazaisa wannan cikin yabi rariya, karki damu dabatun Ameenu, dakansa zai dawo gareki kinji". " amma Anty tayaya kenan?". Cikin murmushi kubrah tace, "karki damu ki zuba ido kedai". " shikenan Anty ngd sosai da kulawarki gareni, ALLAH ya dawo fake lfy". "Ameen". Duk hirar da kubrah da mufeedah keyi a kunnen Aleeya ne, amma batace uffanba, tadayi shiru tana kallonsu, har Kubrah tabar d'akin. Kobayan fitar kubrah Aleeyan batacema mufeedah wani abuba, saima harkokinta datakeyi...............✍ *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu ameen_*🙏🏻🙏🏻😭😭 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ _bilyn Abdull bata manta dakuba 'yan *BBC HAUSA NOVELS* wlhy ina k'aunarku kamar yanda kuke k'aunata, ngd sosai da comments d'inku, ALLAH yabar zuminci, I love you wijiga-wijiga Alkur'an sisters._ 😂❤❤❤❤❤❤🤸🏻‍♀. 3⃣3⃣ Su ya khaleel Na isa office aiki kawai yafarayi, yakwana biyu baizo office ba, saboda tafiyar dayayi, dukda dai akan aikine shima, amma baihana yatadda jibgin aikiba dake jiransa a office. Zamansa dakusan mintuna 40 kiran Taaheer yashigo wayarsa, harta kusan tsinkewa yad'aga. Bayan sun gaisa taheer ya tabbatar masa da wadda zasu kama tafito. "A'a mikuke jira, Ku kamata mana, damani banaso akamata cikin gidanmune kawai ne". "OK sir". Duk suka yanke wayar suduka. Aiki ya khaleel yakeyi amma zuciyarsa tarabu gida biyu, rabi akan Aysha rabi wajen matar dasu taheer zasu kama. Yana tsaka da tunaninnan akayi knocking d'in k'ofar office d'in, umarnin shigowa yabada, youseef yashigo hannunsa d'aukeda takardu, saida yayi salute nashi, ya khaleel yanuna masa kujerar zama sannan yazauna, hannu yabashi sukayi musabaha. Yauseef yace, "sir, gashi munsami mutum kusan 16 masu tambarin kunamarnan". Da sauri ya khaleel yakar6i takardun yashigo dubawa. Saida yagama tsaf sannan youseef yacigaba da maganarsa. " tabbas barau modibbo yana ciki, sannan akwai yaron Alhaji bishasha Lazarus shima yanada ita, akwai yara da'aka kama agidanka suma duk sunada ita. Cikin mamaki ya khaleel yake kallonsa, kallo irin Na tabbatarwa. Youseef ya jinjina masa kai alamar gaskiyane. Huci mai zafi ya khaleel yafurzo daga bakinsa, gaskiya wannan lamarin yafara d'aure kansa, shin miyasa hakan kuma?, kenan da gaske akwai mai alak'a da wannan k'ungiyar acikin gidansu?, (zuciyarsa tana karkata ga zargin Aysha ne, musamman idan yatuna da lokacin da'aka sanarma barau modibbo zuwansu, ya tabbatar Aysha ce kawai taji hakan, amma to mizai sakata tiromusu 'yan Daba kuma? Bayan harda ita zasu cutar?, tokuma ya'akayi tasan talatuwa mai aikin Hajia khaltum ce?, kenan tanada alak'a dasu?, musamman idan Yakuma tattara bayanan matashiyar budurwa sakeena. Kai, bai yarda da zuciyarsaba, yabibiyi Aysha amma haryanzun bai kamata dawani Abu dayashafi wannan k'ungiyarba, yakamata gakuma sato masa Sakina, zaimata wasu tambayoyi....... Youseef ne yad'an buga table yace, "sir!, lfy kuwa?." Da Sauri ya khaleel yakawo numfashi, kuma furzar da hucin yayi sannan yace, "babu komaiba youseef, cigaba ina saurarenka". Ajiyar zuciya youseef ya sauke shima, yacigaba dafad'in sannan akwai wasu 'yammata biyu damuka kama kusan 3years kenan da cocaine a airport d'in Lagos, suma sunada wannan tambarin kunamar." Cikin jinjina kai ya khaleel yace, ''kunyi k'ok'ari youseef, kuma kucigaba da aikinku cikin kulawa, ina alfahari daku sosai". Murmishin jin dad'in yabon da ogansu yayimusu youseef yayi, yace, "duk wani kwazonmu yanadaga cikin tarbiyarka Sir". Murmushi kawai ya khaleel yayi, yace, "babu damuwa kaje, zuwa anjima zan nemeku kaidasu Joseph". "Ok, thanks sir". Ya khaleel ya jinjina Kansa yacigaba da aikinsa. __________________________ Cikin nasarar aiki su Taheer suka sami damar cafke kubrah, a babban filin jirgin sauka da tashi Na Abuja, ankamatane tana k'ok'arin tafiya Lagos. mamaki yayi matuk'ar kama Taheer, Dan yasan kubrah sosai, tadad'e tana kamun k'afa dashi akan yashawo mata kan khaleel yasota. Yamzu har yarinyarnan zata iya ta'addanci haka?. Kai yanzukam ya gama yadda ba'a shedar mutum. Kallon-kallo kubrah da Taheer sukayi, sai gumi takeyi da rawar jiki. pretending tafara musu, akan mitayi daza'a kamata?, tanayin hakanne kuma saboda taga Taheer, atunaninta zata samu sassauci daga gareshi. Amma abin mamaki saiya nuna halin ko inkula da ita, saima ka rantse baisantaba. Cikin yaran taheer wani yadaka mata tsawa da zabga mata lafiyayyen maruka, tuni tadafe kunci tana hawaye, bakinta kuma yayi gum, danta gane rijiya bawajen wasan makaho baneba. kad'an daga aikin masu bak'ar fuskarnan su suburbud'a mata alburushi atsakkiya kwalwarta yanzunan. Hankalinta baigama tashiba gaba d'aya, ta tabbata inhar ya khaleel nawajen zai kubtar da ita, tunda baita6a kamata dawata 6arnaba, koma hajia babba tasaka ya fiddota aii. Nidai nace hummm. ******** Ya khaleel Na tsaka da aiki su Taheer suka dawo, ko d'agowama baiyi ya kalli taheer ba, yadai amsa gaisuwar da Taheer d'in kemasa tareda jinjina masa kai. "Sir! Munsami yarinyarnanfa, amma abun mamaki da d'aure kai kubrah ce fa". Babu shiri ya khaleel yad'ago kansa, yace, " kubrah kuma? Wace kubrah?. " "Kubrah dai daka sani, mai zuwa gidanku, Dan haryanzun bansan dangar takar zumincinkuba". Azabure ya khaleel yamik'e, lokaci d'aya kansa ya sara masa, yay saurin dafe kansa, yama rasa wane tunani zaiyi. Miyasa zuciyarsa ke alak'anta mutanan nan da matarsane?. ranar dinner d'insuce tafad'o masa arai, tabbas aranar hankalin Aysha da meerah yatashi saboda ganin kubrah dawasu mata biyu, idanma bai mantaba meerah barin wajen tayi baki d'aya, kuma Aysha batada wata aminiya sama da meerah. Sannan washe garin ranar lokacin su Sameer sunje musu sallama kubrah da wata mata sunshigo yima Aysha sallama, harya basu damar shiga inda take a bedroom, kuma yashiga d'akin kiranta saboda tazo suyi sallama dasu Nawaff, saiya taddasu cirko-cirko, tabbas akwai alamar tambaya akan matarsa. To amma idan yace haka kuma, miye alak'ar Momy da kubrah, sannan hajia khaltum kuma?. ''Ya salam!! yafad'a da k'arfi yana dafe kai". Da sauri Taheer yamatso kusadashi, "j! Miyake faruwane haka?". Kansa ya girgizama Taheer, cikin k'unar zuciya yace, " Taheer ina zargin wasu abubuwa biyu, kuma akan mutum biyu, amma bana fatan hakan ta kasance, domin duksun shafi katanguna, ya ALLAH!". kamashi yayi ya zaunar, yaringa kwantar masa da hankali, saida yaga yad'an nutsu sannan ya idamasa bayanin yafice. Gaba d'aya yau ya khaleel yakasa ta6ukama kansa komai, tunani yafaracin k'arfinsa, yanaso yakira gida yaji yajikin Momy da Aysha amma haushinsu yahanashi, kuma yayi alk'awarin inhar suka kasance cikin abinda yake zarginsu wlhy billahi bazai d'aga musu k'afaba, saiya hukuntasu, kuma da hannunsa zai kamasu. Wannan alk'awarine, bazai ta6a barin mai laifi a k'ark'ashin inuwarsaba. Idonsa yayi jajur saboda 6acinrai, zuwa can maganar yarannan tadawo masa arai itama, lokacin dayake tambayarsu waye ya turosu, (sunce matar babansa hajia Bilkeesu) kai jama'a miyasa zuciyarsa take karkata dukkan zarginsa akan wad'anda ya yadda dasu? Mafiya kusancu agareshi kuma?, zai sakama dukkan wani dake gidansu ido kawai, Dan yanzu ba Aysha kad'aice abin zarginsaba, harda Momy da Anty Mamie.🤥 ____________________ Yauma dai haka Aysha tayini duk babu dad'i, komai taci kamar jira saita amayar dashi, zogalene kawai dataci ya zauna, haka 'yan Kano suka tafi suna tausaya mata. Bak'in 6angaren Momy ma duksun wuce, inna jummai Ce kawai tarage. Misalin 10 Na safe baffah yashiga duba hajia babba, bayan sun gaisa da inna jummai yashiga d'akin. Duk 'ya'yanta suna zagaye da ita, har mufeedah dake raku6e gefe d'aya. Ganin baffah suka fara yunk'urin fita amma saiya dakatar dasu, kujerar madubi husnah tabashi yazauna, Momy Na kwance dukta kuma janga6ewa saboda dagaske batada lafiyar, k'arfin haline kawai, da k'yarma tasha tea da magungunanta takwanta yanzu. Sannu yamata cikin tausayawa, da tambayar k'arfin jikinta, tace, k'irjintane kemata ciwo yanzun, amma tasanarma doctor dasukazo yanzun shida sultan, yace zai kawo mata magani. "To shikenan ALLAH yak'ara afuwa, sannan kuma ki kwantar da hankalinki, Dan kinsandai kinada hawanjini. Idankuma hankalinki ba'a kwanceba ciwon bazai barkiba". Kanta ta jinjina masa, wasu siraran hawaye suka zirara a idonta na dama, suka gangara har cikin kunnenta, Anty shukurah ce ta goge mata. Baffah ya maida kallonsa ga mufeeda, "k kuma kishirya kayanki, 6angaren Ammah zaki koma harki haihu, rashin ganinki zai sassautama mahaifiyarki rad'ad'in datakeji". Mufeedah kuka tafashe dashi, Dan tasan inhar takoma 6angaren Ammah bata Isa zubar da cikinnanba, tasan jarabar Ammah da k'unatar tsiya. Cikin daka tsawa yace, " kobak'ya jinane?". Azabure tace, "to baffah". Yayi tsaki yana maida kallonsa ga Momy dake yunk'urin tashi zaune, Anty zuwairah da Shukurah suka taimaka mata tatashi. Muryarnan ta Momy duktayi low, tace, " Alhaji kana ganin ita Ammah baza'a takurataba?, nida canayi tabi inna Jigawa kawai, idan ta haihu saita dawo, koya kagani?". "Eto kema kinzo da shawara mai k'yau, amma abani nanda kwana uku nagani". Murmushin samun nasara Momy tayi, tacigaba dafad'in " to ALLAH ya kaimu, sannan sai kayanta, yakamata akwasosu aii". "A'a baza'a kwasosuba, Dan zamu maida auren kan Nafisa d'iyar k'anen Bilkisu Hameesu, tunda ta isa aure, dadai tasleem ko maleeka zan bashi, tokuma duk sunada manema ashe, Dan haka baza'a kwaso kayanba, mungama magana da innah za'a d'aura auren k'arshen satinnan, shukurah keda Amatullah kuje Ku d'akko kayan sawar Mufeeda kawai, sannan karku d'akko akwatinan lefen, kubarshi can, sadakintama za'a maidashi Na Nafisane". Tunda baffah yafara magana Momy take zabura, haryakai k'arshe, " Alhaji ban gane wannan zancen nakaba?, daga INA kuma wannan annamimancin yafito?, asaki 'yata agida, bayan kwana biyu rak da kaita gidan, sannan amaye gurbin gidan da jinin Bilkeesu, wlhy impossible, wannan wane irin rikitaccen tunanine?, ko ance muku idan mufeedah ta haihu bazata koma d'akinta baneba?". Mik'ewa tsaye baffah yayi yana guntun murmushi, yace, "Laurah Baku Isa hanani abinda nayi niyyaba, Ammah datai sanadin kawoni duniyama ta amince, hakama d'an uwana ya amince, Ameenudden ya amince, ahakama iyayen yarinyar, banida abinda zan sakama Ameenudden dashi saboda zalincin da ballagar 'yarki tamasa, adalilin sakacinki, babu abinda zai saka aurennan fasuwa saidai mutuwa, idanma zaku kwantar da hankalinki Ku kwantar, idan bazaku kwantarba kune awahale, narigada Na zartar da hukunci babu mai canjashi, wlhy da'ace akwai budurwar danake da ita bayansu Tasleem saina aura masa, bazankuma aura masa Hasnah ko Husnah ba, saboda suma hankalina bai kwanta dasuba, ki kiyayeni kuma". Yajuya zai fice abinsa......... Cikin k'araji hajia babba tace, kayan kicin aida kud'ina nasiya, Dan haka sai an kwasomin kayana, kuma zargin dakama sauran 'ya'yana ban yafeba, dama cin zarafina kazoyi gaban 'ya'yana ba dubaniba, dama aii tuni nagama sanin Bilkisu ta shanyeka, kayi nisa bakajin kira, ALLAH saiya mana hisabi tsakanina daku". Juyowa baffah yayi yana kallonta. Yasaki guntun murmushi, kiyima kayan kichin d'in kud'i konawane zan biya, sauran maganarki kuma kisameni zan baki amsarsu, amma ba'a nanba, yanagama fad'a ya ficewarsa abinsa. Kuka rurus momy takeyi, sai zage-zage da zabgama mufeedah ALLAH ya isa takeyi, wai itace taja ake cin zarafinta. Inna jummai tashigo tana mata fad'a. Dak'yar suka samu yayi shuru kuwa. ___________________ Har bayan isha'i ya khaleel bai dawo gidanba, Aysha Na kwance bisa doguwar kujerar ammah, lullu6e take cikin bargo saboda sanyi datakeji, ga zazza6i mai zafi ajikinta, tun d'azun tunanine da damuwa suka to she kwalwar kanta, duk yau bataga ya khaleel ba, dukda tana zargin yatafi aiikine, amma yakamata yakirata yaji yajikinta, ganin bai kira d'inba takirashi har kusan 4times amma bai d'agaba, hawaye masu zafi suka zubo akan kumatunta, tun d'azun take kukannan, saboda lullu6a datayi da bargo har fuskarta yasa ba'a ganin. Ammah dabatasan abinda ke faruwaba, suna zaune da inna jummai suna hirarsu irinta zuminci, sai Tasleem da maleekah dake can gefe zaune kowacce suna chatting, inbakama saniba zaka zata suna falonba. Sallamar ya khaleel tasakasu d'agowa suduka, amma da inna jummai suka masa sannu da zuwa, suma su Tasleem suka gaidashi. Ya amsa awani yanayi, Ammah sai binsa da kallo takeyi, Dan taga Alamar yana tareda damuwa. Inna jummai tamik'e tafita, waizata duba jikin Momy tadawo. Ko kallo bata ishi ya khaleel ba, danshi bayason wanda bai sonsa, tana fitama k'amin tsaki yaja, ammah datajisa batace dashi komaiba, Dan tuni take fuskantar 'Yar tsamar dake tsakanin Khaleel da kakarsa tawajen uwa, kuma k'anwar kakarsa ciki d'aya. Zama yayi saman hannun kujerar da Aysha ke kwance, wadda tunda taji sallamarsa tashare hawayenta. Hannu yakai ya yaye bargon, hucin zafin zazza6in yasakashi fad'in ''ya salam, wannan zazza6in har yanzu bai saukabane Ammah?". "Yana sauka yadawone iro, aii saidai hak'uri kuma, idan ba kwari yayiba haka za'aita fama". " ALLAH ya k'ara lfy, yay maganar yana lek'a face d'in Aysha data lumshe ido, saika d'auka da gaske barci takeyi, ammashi tuni yagano idonta biyu. K'aramin hannun rigarta ya janye, babu komai a damtsen hannunta, aransa yace k'ila d'ayan hannun tane kunamar take?, saikuma yace amma banta6a ganiba?". Aysha dai batako motsaba, yamaida bargon ya lullu6eta yana mak'ewa, ammah bara nad'an watsa ruwa, shigowata kenan gidan. ". A to yakamata aje a kimtsa, kazo ga abincinka Bilkeesu ta aiko dashi". Kansa kawai ya iya jinjina mata yafice, Aysha tabishi da kallo asace, tabbas akwai abinda ke damun mijin nata gaskiya, to minene?". Batada amsa, babu kuma mai bata, wannan yasakata tsuke bakinta tayi shiru. Tana binsa da addu'a a zuciyarta................✍🏿 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻🙏🏻🙏🏻😭 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of expert & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ 3⃣4⃣ Bai shiga 6angaren Momy ba, kai tsaye 6angarensu yawuce, yad'an watsa ruwa sannan yadawo falo yazauna, komai akashe yake, babu haske Afalon, yana zaune cikin duhune. Sai tunani yakeyi, yarasa yanda zai fassara abubuwan dake tunkaro rayuwarsa, kallon komai yakeyi abaibai, miyasa abubuwa suketa rikid'ar hawainiyane acikin gidansu?, muyasa baita6a kawo tunanin komaiba dangane da wasu abubuwa sai yanzu?. Guntun tsaki yaja, yazame ya kwanta a doguwar kujerar, hakai yayta tunane-tunane har kusan 10, ring d'in wayarsane yadawo dashi hayyacinsa, yad'auki wayar yana kallon mai kiran, baffah ne, harta katse bai d'agaba, kamar bazai kiraba saikuma yay k'ok'arin dailing d'in number, gamo yayi da miss call d'in mimy har uku, ya furzar da huci, Dan kokad'an baiji kiranba, baikai karshen tunaninsaba kiran baffah yasake shigowa. 'Dagawa yayi, cikin ladabi yagaida baffah tamkar yana gabansa. "Mu'azzama kana inane?". ''Ina gida baffah". " kazo to ina nemanka, amma yanaji muryarka haka?". "Babu komai baffah, barcine yad'an figeni, ganinan zuwa dai". *********** Baffah kad'ai ya tarar zaune afalo yana kallom labarai a NTA, harma sunkusa gabawa, zama yayi yagaidashi. Baffah ya amsa idonsa akansa, danya hango damuwa tartare da d'an nasa, baidai cemasa komaiba dangane da damuwar tasa, Dan yasan bazai wuce awajen aikibane. baffah yafara magana " dama nakirakane akan shawarar damuka yanke nidasu Ammah, saboda kafita tunda safe yau, akan maganar Ameenudden ne, da cikinsu tasleem zance yaza6a, amma sai Ammah takecemin Tasleem tana tareda k'anin Naufal ne, Maleeka kuma yaron Alhaji musa batsari, kuma duk takula mu'amullar tasu tayi k'arfi, wannan yasa na janye batun akansu, saida bazan bashi Hasnah ko husnah ba, saboda mahaifiyarku bazata barsu su zauna lafiyaba, akwai yarinyar Hameesu, k'anin Bilkeesu, Nafisa, tazo bikinnan, Tanama gidannan bata tafiba, kawai mun yanke shawarar maidama Ameenu ita a madadin mufeedah." Jin baffah yayi shiru, ya khaleel yagane yagama, zamansa yagyara shima. "Baffah shawararku tayi dai-dai, kuma ALLAH yasanya alkairi aciki". "To ameen, saikuma batun mufeeda, da nace takoma 6angaren Ammah, Dan asamu jinin ita momyn taku yasauka, tokuma saitace tafison tabi innah jigawa, idan tahaihu wai saita dawo". " karka yarda da wannan batun baffah, kasandai halin inna jummai, wlhy dakanta zata 6arar dacikin jikin mufeedar". Hakama Ammah tacemin d'azun. "Tokagani baffah, kawaima tatattara adarennan takoma 6angaren Ammah, barama dakaina zanje". " shikenan Mu'azzam, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, yajikin matar taka?". "Ameen baffah, jiki Alhmdllh". " ALLAH yak'ara afuwa to, tashi kawai kaje". Sallama ya khaleel yayma baffah yafice. 6angaren Momy yanufa. Afalo ya iske su suna hira, inna jummai Na tsakkiyarsu, Duk suka gaidashi, sama-sama ya amsa yashige, innah jummai tarakashi da harara. dariya Anty Zuwairah tayi, tace, "nifa 'Yar tsamar innah da khaleel tana bani dariya, waimi kika masane haka innah?". Kunyace takama innah jummai, saita fara 'yan kame-kame, tarasa abinda zata fad'a domin Kate kanta. Daga Momy har ya khaleel da Anty shukurah suna jiyosu daga d'aki, saidai hankalin Momy nakan khaleel, sosai taga damuwa afuskarsa. "Ibraheem mike damunkane?". " murmushin yak'e yayi, babu komai Momy, ciwonkune mana keda A'eesha, waini momya bammaji kinmin maganar A'eesha ba, kobakisan batada lfy ba?, kinsamu jika Momy, amma banga kin nunamin farincikiba ko sau d'aya". Cikin daburcewa Momy tace, "ba....bahaka baneba Ibrahim, in...I..ina farin ciki mana sosai, Kasan tashin hankalin mufeedar nanne yadanne komai azuciyata. Amma yanzu ya jikin nata?". " Alhmdllh, saidai tana shan wahala". Baki hajia babba tad'an ta6e, amma khaleel bai ganiba, afili kuma tace, "ayya Allah Yakawo afuwa, dama ciki saida hak'uri, barema cikin fari". "Hakane Momy". " naga kema aii jikin naki Alhmdllh". "Uhm da sauk'i kam sosai, saidai abinda ba'a rasaba, kaji wai mi baffanku suke son k'ullawa?". " naji, Indai akan Auren Nafisa da Ameenu ne". "To mikace musu?". " mizance Momy, Addu'ar fatan alkairi namusu mana, ai hakan shine dai-dai kodan halaccin da Ameenu sukamana shida iyayrnsa". Fuska Momy tahad'e, "wai Ibraheem nikam mikakeson maida kankane?, Kaine babba acikin yara mazan gidannan, amma kokad'an bakada wata jarumtar kwato mana 'yancinmu nida 'yan uwanka, katunafa kaikad'ai ALLAH yabani namiji". ''Hakane Momy. Amma inason kiringa fahimta abinda yazo akan turbar gaskiya. Kasan cewata wakilinku agidan nan, bashine zaisa nayita danne gaskiyaba saboda farincikin Ku, itafa gaskiya D'ayace, daga k'inta sai 6ata, shin bakiji masu iya magana nacewa *_CIKI DA GASKIYA WUK'A BATA HUDASHI BA_*, wannanfa zancen gaskiyane wlhy, idan zaka kasance mai gaskiya abuga-abuga, dole abarka momy, Idan Abu yazo a turbar gaskiya yakamata kudinga kar6arsafa". " naji shashasha, tashi ka6acemin anan, sallamamme kawai, basaikaje kaita goyon bayansunba". Khaleel baice komaiba yatashi yafice, afalo yace INA mufeedah?. Hasnah tace, "tana d'akinta ya khaleel". Baice komaiba yashiga d'akin muferdah, tararwa yayi tana 6alle magunguna zatasha, jikinta sai rawa yakeyi bataso kowa ya ganta, shiyyasa taketa waige-waige. Shigowarsa yasaka jikimta k'ara k'arfin rawa, tasaki magungunan hannunta a k'asa yanayinta kawai ya tabbatar masa batada gaskiya, cikin takunsa Na jarumta yak'arasa gareta, tsugunawa yayi yad'ibi kwalayen maganin yana dubawa. Fuskarsa amatuk'ar d'aure yad'ago manyan idanunsa da suka koma jajaye gabad'aya yinin yau yad'orasu akanta, (humm todama Yaya lafiyar giwa) idon ya khaleel Na a daidaima ya'aka k'are ballantana yau dayake cikin 6acin rai, fitsari kawai mufeeda tasaki atsaye, jikake tsululululu!!😂. Lafiyayyun Marika hud'u yasakar mata, cikin daka tsawa mai firgitarwa yace, " ubanwa yabaki maganin zubar da ciki?!!! Nace ubanwaye yabakishi agidannan?!! Wlhy koki fad'amin koma 6a66allaki, dagake har cikin kutafi barzahun 'Yar iska maikama da dabba. Wlhy bak'aramin asarar kud'in Tara akayiba wajen biya miki kud'in makaranta, mai kwakwalwar kifi kawai, bazaki fad'amin Wanda yabakibane saina miki dukan mutuwa?". "Wlhy ya khaleel innah Ce, narantse bani nasiyaba..." Bata rude bakiba innah jummai tafad'o d'akin, saiwani cika da batsewa takeyi, Dan duk abinda ke faruwa sunaji afalo. Cikin masifa tace, "kai wallhi kafita idona in rufe, kafara shigarmin hancifa, yanzunnan saina fyatoka". kallon samada k'asa yamata, kamar ba kakarsaba, Dan Ransa amatuk'ar 6ace yake, idonsa yarufe baima tantance wadda yake agabansa, yace. "Dan ALLAH karki fasa fyatonin, ya da girmanki da shekarunki zaki d'auki abinda zai cutar da yarinya kibata?, anya kuwa ked'in kakarmuce? Nifa INA kokwanto wlhy, dan tuni nakula da rashin k'auna dakike nunamin tun INA k'aramina, yanzu kuma shine zakibama yarinya magani wai danta Barar da ciki?, shiyyasa kika nemi abaki ita kutafi Jigawa?, shin idan ita batada hankali kema bakida shine?, wlhy tuni dama nakula ked'in tsohuwar...... Bai k'arasheba yaji saukar mari akumatunsa, shiru yayi yaduk'ar da kansa, Dan yaga k'afafun Momy, karo Na farko data mareshi dawayonsa, bama itaba, zai iya rantsuwa da hankalinsa wani baita6a marinsaba sai yau. "Ibraheem bakada hankaline?, uwar tawa katasa gaba kakema fitsara? Shin INA hankalinka yatafine?, koka fara shan giyane wai?". Shiru yayi bai tankaba. Cikin daka tsawa Momy tace, "ibraheem kobaka jinane!!!!?". Nanma shiru yamata, har yanzu kuma hannunsa Na dafe da kuncinsa, idanunnan sunkuma rinewa jajur. " yaza'ayi yabaki amsa, dukdai kece kika jamana bala'innan, tunda kece kika dage wajen....... "Haba innah mikikeson fad'ane haka?"...... Adai-dai nan baffah da Ammah suka shigo. Anty Zuwairah Na kuka tasanar musu abinda ke faruwa, Dan yau tausayin d'an uwan nata yashigeta, tadad'e da fahimtar tsangwama da k'yara da innah jummai ke nunama khaleel, ita kanta tana mamakin hakan, amma bata ta6a kawo komai arantaba, Dan innah nacewa saboda miskilancin sane da taurin zuciya, itakuma batason mai wannan halayyar, dukda dai wannan bai Isa abin gamsarwa ba haka Anty zuwairah tashare bata maida hankaliba..... Baffah baice komaiba, sai Jan khaleel yayi ajikinsa, yana buga bayansa ahankali, wannan ne ya karya zuciyar ya khaleel, dama ga damuwar dake cunkushe da zuciyarsa tunda safe, saikawai hawaye suka fara zirara a kumatunsa. Karo Na farko danaga ya khaleel yana kuka😳. " Jummai iro yanada hujjar fad'a miki duk kalamin dayazo bakinsa, shin amatsayinki Na babba yadace kifita kinema maganin zubar da ciki kibama mufeedah?, shiyyasa kai tsaye nace banyarda kitafi Jigawa da itaba, saboda nasan halinki, nasan mizaki iyayi, wato hanawata tasakaki canja salo?, kika bata maganin dantasha yazube ayanzu? Wlhy jummai kinji kunya, tunda ke bazaki ta6a zama mai hankaliba, da ALLAH bai kawoshi d'akinba dashikenan ........ Haba yaya, wai yazaki tasani gaba kina gayamin maganganu agaban yara? Naga yanda kikeda iko da mufeeda nima inada iko da ita aii. Tabbas kinada iko da ita jummai, amma ikon bashi zaisa abarki ki cutar da itaba..... "Ammah kiyi shirunki kawai, kidaina 6ata ranki, aiiduk abinda kashuka saika girbeshi watarana". Hannu Innah jummai tad'aga zata mari ya khaleel dake magana, da sauri yarik'e hannun, ido cikin ido suka kalli juna, (wani irin tsoron khaleel ne yashigi inna jummai, mugun kwarjininsa da baiwar rikita Mara gaskiya da ALLAH yayma kwayar idonsa yasaka dukkan sassan jikin inna jummai fidda zufa) yace, "daga yau banida kaka ta 6angaren uwa, nashafeki acikin tarihina, danhaka jummai, wlhy kikayi kuskuren marina saikinyi nadamar haiguwata dakika bari akayi, Dan saikinji inama Momy kika bama maganinnan tasha lokacin tanada cikina, Na radaddage aciki kuka watsani a gotta......" Baffah ne yazo ya janyeshi yana masa fad'a, Momy kuwa da innah jummai kuka suka Sanya, itakam Ammah ko'a kwalar rigarta, dantaji dad'in abinda ironta yayma k'anwar tata, taja hannun khaleel da mufeedah tafice. Baffah ma bayanta yabi. Anty zuwairah madai yau bataji dad'in lamarinnanba, kuma zuciyarta tafi karkata ga khaleel, Dan ganin gaba d'aya yanda aka tozartashi, tamkar ba jinin momyba, tomi khaleel ya tsarema innah haka? Miyay mata dazafi haka? Kowa yasan tun suna yara batajan khaleel ajikinta, "why?". ___________________________ Tunda suka shigo idon Aysha nakan ya khaleel, tun d'azun itama take rabzar kuka, Dan komai akan idonta yafaru, tunda Hasnah tazo arikice tafad'ama Ammah abinda ke faruwa itama ta tak'ark'ara tabi bayan Ammah batareda ta saniba, la6ewa tayi tajikin window, komai akan idonta yafaru, (Mashi'a kuma tafad'a mata sauran) tausayin ya khaleel d'inta Yakuma kamata, tabbas zarginta yana Neman zama gaskiya. Shima hankalinsa Na kanta, kunyar baffah kawai tahanashi matsawa kusada ita. Baffah ya masa fad'a akan abinda yayma inna jummai yamusu sallama yafita, saboda dare yayi, 11 yawuce sosai. Baffah Na fita ya khaleel yakoma inda Aysha take zaune, muryarsa a sanyaye yace, "mike faruwa? Ko wani guri kemiki ciwo?". Girgiza masa kai tayi, tana share kwallah. Shima baice komaiba yajawota jikinsa ya rungume, yamaida kansa yajingina da kujera ya lumshe idanu. Tausayinsu yakama Ammah, ita kanta mufeedah taji tausayin yayan nata, yaune rana ta farko data farajin nadamar abinda ta aikata, gashi ta silarta sa6ani Na k'ok'arin shiga familie d'insu, tashare hawayen fuskarta tana satar kallon miji datar cikeda sha'awa. Saida Ammah taga barci ya suri ya khaleel ahaka, itama Aysha barcin ya d'auketa, tadashi tayi, " iro tashi katafi ka kwanta, kaga dare tayi, gashi zakaje aiki gobe idan ALLAH ya kaimu". Kansa ya jinjinama Ammah, ahankali yad'auki Aysha dankar ta tashi, yakaita bedroom d'in Ammah, ya kwantar agado, zama yayi kusada ita yamata addu'oi ya tofeta, yaja bargo ya lullu6eta saboda yaga tanata takurewa waje d'aya alamun sanyi takeji, jikinta ringim yake da zazza6i, yariga yazame mata jiki, haka take wuni dashi takwana dashi. Idonsa akanta yasunkuya ya sumbaci goshinta da la66anta, sannan yagyara mata bargon sosai yajuya yafice. Ko sallama baima Ammah ba yafice, bata damuba, dantasan zuciyar 'yan mazan tana kusa yau. Itama Tisa k'eyar mufeedah tayi suka shiga bedroom d'in, suduka a gadon suka kwanta, Dan gadon Ammah babbane, zaima iya cin mutum 6. Yauma haka ya khaleel ya kwana babu dad'i, da k'yar barci yad'aukesa wajen 2:30, bayan yayi nafilfilinsa yamik'a kukansa wajen ubangiji. ********** A 6angaren Momy kam, tunda Ammah tafita da ya khaleel da mufeedah hankalinta yakuma tashi, inna jummai kuwa Dan munafunci kuka tasanya, wai za'a rabata da jikokinta. Babu Wanda yabi takanta, Dan kowa damuwarsa ta isheshi🤕. *_Bayan kwana uku_*. Kowa ka kalla agidan kasan akwai damuwa, Dan kowa sukuku yake, duk abinda yafaru adaren ranar yagama karad'e gidan, harara da tsaki da habaicin yaran gidan yasaka inna jummai tattara inata-inata dole tabar gidan, dansu Tasleem sungama tasota gaba, dasu Nureedin Ummu noor babu mai raga mata agidan, musammanma matansu ya Sultan, basa yimata agaban mutane, saisun ganta itakad'ai. Ita kanta Anty Zuwairah da Anty Shikurah bawani shiga sabgarta sukeyiba, Aleeya kam kwana biyu ma bata gidan, waitaje aiki wani asibiti Na sati 1, dama haka takeyi, takanje tayi kwanaki saikuma yadawo, babu Wanda yata6a damuwa dahakan, Dan a zatonsu aikin daya kawota take zuwayi. Nidai nace hummm. Akwanaki ukunnan kuwa ya khaleel ba'a magana, dukya wani birkita kansa, duk binciken daya dace akan Aysha yayishi, amma baikamata dawani kuskureba, saidai hakan baisa yagama yarda da itaba, hakama Anty Mamie yasaka mata idanu itada Momy. Shida Momy yanzu kam gaisuwace kawai, itama sama-sama take amsashi, baidamuba, baikuma ta6a nuna mata yadamunba. Aysha kam sosai takeshan wahalar cikinnan, gadamuwar rage kulawar da ya khaleel ke nuna mata, ita harma mamakin mufeedah takeyi, kokad'an nata cikin baya bata wahala, amma ita kullum tamkar kurar wasa haka take yini agidannan. Mama nazuwa da safe da dare kawai dubata,, Anty Mamie kuwa aii koda yaushe tana zaryar tambayar mi Aysha zataci adafa mata ko a siyi mata?. Data fad'ane zataje ta dafo matashi, kokuma tabada asiyo, Ummie Amaryama tana bakin k'ok'arinta, kafin tatafi aiki satazo dubata, idan tadawoma haka, kuma zakiga tasayo mata 'yan abubuwan kwalama namasu ciki. Yaran gidanma kwai da kwarkwata dasafe saisunzo gaisheta, masu schools sutafi masu aiki su tafi, Anty zuwairah madai anad'an lek'owa sau 1 saboda gori da Ammah tamata, to gobema suke shirin komawa Lagos, dama yaran tuni sun koma saboda makaranta, Anty Amatullah kuwa tatafi jiya, Anty shikurah dai tana nan tukkuna, mijin take jira, Dan INA k'yautata zaton sundawo Baki d'aya, yanzu hakama gyaran gidansu akeyi. Matansu Sultan kam yanzu sunmaida 6angaren Ammah wajen hirarsu, harda amare suma, duksun saki jikinsu anata harkokin arzik'i dasu. Gwaggo bintu itama kulawa ta musamman Aysha kesamu saga gareta, ita har mamaki abin kebatama ********** Ya khaleel dasu Joseph zaune ad'akin bincike, su Solomon duksun duk'ufa akan computers, har shima ya khaleel d'in, suna bincikene akan wani dasuke harin kamawa, kusan awanni biyu suka d'auka, bayan sun kammala suka fito. Ya khaleel yakalli Taheer dake gefen haggunsa. " Tafeer inason ganawa da kubrah". "OK sir, babu damuwa, idan ka shirya saimuje". "Eh, muyi sallah first amma, tunda naga time yayi", yay naganar yana kallon bak'in agogon hannunsa". "Atare sukace to". Wad'anda zabasuyi sallan ba suka koma office, sukuma suka nufi massalacin dake cikin setetion d'in. Suna idar da sallar la'asar suka fito, ak'ofar massalacin suka iske Joseph, basabon abu bane hakan awajensu, Indai zasu shiga sallah yakan tsaya yajirasu awaje. Musabuha🤝🏻duk sukayi da juna, annanema ya khaleel yake sanar musu Ayshafa nada ciki, gaba d'aya duk suka rungumeshi cikin Nuna farinciki da tayashi murna, dama matar Youseef da Joseph duk sunkusa haihuwa, matar Taheer ma tanata Jan nata. Sund'an ta6a hira akan abinda ya shafesu, akuma k'arshen watannan zasu bud'e k'ungiyar matasansu dasuka kafa. Daganan su youseef suka tafi office, taheer kuma shida ya khaleel suka tafi Inda kubrah take a gark'ame. ....... ✍🏿 Kubra one Luv🤣🤸🏻‍♀ *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ 3⃣5⃣ Dogon d'akine, saidai anyi kananun d'akuna aciki tamkar na prison, yawancin d'akunnan dukda mutane aciki, matane kuma zallah awajen. d'akin dake can k'arshe suka k'arasa, kubrah Na zaune tacusa kanta tsakanin cinyoyinta, sai kuka takeyi, bata ta6a tunanin shiga wanga haliba, musamman yanda ta'iya takunta. K'arar bud'e k'ofarce tasanyata d'agowa da sauri dukta fita hayyacinta, kamar wata sabuwar kamu a hauka. Ganin khaleel yasakata mik'ewa zumbur zata nufosa, wata uwar tsawa Taheer yadaka mata, babu shiri tayi baya ta zauna da6ar. Lumshe ido khaleel yayi yana girgiza kansa, Samuel dake binsu abaya ya ajiyema ya khaleel kujera, zama yayi idonsa akan kubrah data koma jikin bango ta raku6e. Saida yamata kallon minti 2 sannan yajuyo yakalli Sam... Da Taheer batareda yayi maganaba. Ficewa sukayi, Dan sungane miyake nufi. Suna fita yadawo da kallonsa kanta, itama dataga daga ita saishi saita fashe da kuka, tana fad'in "Dan ALLAH khaleel kafitar dani, wlhy bammusu komaiba, zalincine yasakasu kamani". K'asaitaccen murmushi ya khaleel yayi, Wanda yadad'e baiyi irinsaba saboda damuwa, cikin turo iska daga hancinsa yace, " nima abinda yakawoni kenan kubrah, nasan ked'in mutuniyar kirkice, banta6a ganinki kina aikata Abu mara k'yauba, zan ku6tar dake ammafa saikin bani had'inkai". Har taune harshe takeyi wajen fad'in "wane irin had'inkai?". Nanma murmushin yasaki, muryarsa can k'asa yace, "kwantar min da hankalinki mana my Sweet". Wani dad'i yaratsa kubrah, khaleel yacemata Sweet. Shima murmushin yayi danya hango matakan nasara. " kubrah wanne kasuwanci kikeyi ak'asashe daban-daban Na duniya?, dannaga bak'ya kulla watanni biyu a Nigeria ". Tashin hankali, jikin kubrah ne yafara 6ari. Khaleel yace, " yahaka kuma da rawar jiki? Tambayacefa bawani abuba, saikace wata mara gaskiya?". "A...a'a wlhy, inada gaskiya khaleel, dama dai tambayarce tazomin a bazata, shi....shin...shinefa kawai". "Uhyimm, Sorry fa kinji".🤨 Khaleel yay maganar yana d'age gira d'aya sama. " ina jiran amsarki". "To khaleel mizance maka, kasan ina business ne aii". " Nasan business kikeyi, amma wane iri nufina?". Gumin da keta tsatstsafo mata ajiki tashare da hannun doguwar rigar atanfarta, amma takasa furta komai. Shikam khaleel yayi masifar tsura mata idanu, zuwacan yace "shikenan, shikenan, barma waccan tambayar Nagano amsarta, miye alak'arki da hajia khaltum?". "Kamar Yaya take a wajena". "OK". " akwai wadda kuka ta6a zuwa gidanmu da ita, lokacin bikina, itakuma wacece? A INA kuma take?". "Kamar zata fasa kuka tace k'awatace". "Tana ina yanzun?". " kwanaki tayi had'arin mota tama rasu". "Ayya, lalai ta iya mutuwa, amma nikuma naganta kwanakin baya a Lagos, zataje America". Afirgice kubrah tace, "glory d'in?, itafa a Islands UK takema". K'aramar dariya ya khaleel yasaki, danya samo amsar tambayarsa, yace, "kwarai kuwa, saidai inaga bayan dawowarta tamutu ko?, waccan dai kamar sunanta glory Zamani, koba ita baceba?". Kubrah tasaki ajiyar zuciya, "A'a ba ita baceba, k'awata sunanta glory maba". " dak'yau 'Yar gari, kin gamamin komai, tabbas ba ita baceba, amma ina jajanta miki mutuwar k'awarki, zanje muyi magana da habeeb dan yazo ya kar6eki, idan ni nanemi haka baza'a baniba, za'aga kamar munhad'a bakine". Godiya kubrah tamasa, dad'i yakamata baigano komaiba, gashima har yana shirin k'ubtar da ita. Harya mik'e Yakoma ya zauna, af kinga kuma Na manta, a INA zan samu habeeb?, Dan inaso yazo gobe, jibi inada tafiya zuwa London ". "Ito habeeb d'inne sai a slow, amma hanya mafi sauk'i kaje Cinema, yau za'a haska film, Na tabbatar zaije". "OK thanks, angama, gobe ki saurari sakamako, bye my Sweet😉". Dad'i kamar yakashe kubrah, haka Sam...yashigo ya d'auki kujera yafice, aransa yace banza, bakisan halin boss bane, dagani wayo yamiki. ______________________________ Tunda ya khaleel yadawo office yaketa tunane-tunane, ta hanyar dazaibi yaje Cinema yau, ga tunanin binciken glory, ta inama zai fara?, kiran wayarsa da'akayi yakatse masa tunani. Wayar ya d'auka yaga Aysha Ce. Guntun murmushin yayi, danya kula kwana biyunnan tashiga damuwa da sharetan dayakeyi, saida takatse yakirata, bugu biyu kuwa ta d'aga. Muryarta can k'asa akuma galabaice tayi sallama, komawa yayi yajingina da kujera, shima murya can k'asa ya amsa mata, yace, " gimbiya yajikinne?". "Ga shinandai, ya aikin?". 'Duk a shagwa6e take maganar'. Saida ya furzar da huci sannan ya amsa mata da Alhmdllh, yaudai babu zazza6in ko?". " akwai mana, yanzuma nagama amai". "Wannan amai bazai tausayaminba, yabarki kid'anyi k'ibama, mikikaci to?". "Kunun gyad'ane". " sannu kinji sholyna, babies suna wahalarmin dake, dolene idan sunzo duniya namusu bulala, Saboda wahalarmin dake dasukayi, kona dawo gidane?". 'Yar dariya tayi, wadda tadad'e batayiba, tace, _''A'a Sadauki, gara kazauna a office, kullum burina bai wuce kakawo k'arshen azalumaiba, idan kayi hak'an 'ya'yankama zasuyi alfahari dakai, hakan zaikuma tabbatar musu mahaifinsu jarumin jarumaine, 100% nimai k'arfafakace, bamai raunanakaba, koda yaushe addu'ata nanan biye dakai, nidai Burina kada kabar Azzalumai suyi barci mai dad'i, kahanasu dariya da farinciki, ALLAH ya dafa maka mijina abin alfaharina nida al'umma💋💋._ d'ifff takashe wayar. Zabura ya khaleel yayi daga kwancen dayake yana saurarenta, "please karki kash......" Ina harta kashe, cikin hanzari yake dialing d'in number, amma ance switch up, yagwada yakai sau hud'u amma maganar d'ayace akashe take. Maida akalar Kiran yayi kan Ammah, cikin kwakwazonta ta amsa, dama Amman bata iya waya ahankaliba🤣. Kowacce Lamba da alamar datama mutum yanda zata gane, Dan haka khaleel Na kira taganeshi, iro!! Kaine da rana tsakarnan? toya ofishin nakune?". Dafe Kansa yayi, afili yace, ''wayyo nafa kira uwar kwarmato, yanzun saita had'amin mutanene gidan duka". "Wai iro Baka jinane?! Allo iro!, nifa banajinka, inaga natuwok ne, kasake kirana kawai ta ajiye batareada ta Yanke wayarba. tsaki yaja ya Yanke wayar, afili yace, " kai tsohuwarnan akwai kwakwazo, zubaina kenan, tuni Ammah zata saka kwalwar mutum harmutsewa, shi kawai inda yake sonta akwai tsage gaskiya". Komawa yayi Yakuma lafewa jikin kujerar, kalaman Aysha sai kai kawo suke a zuciyarsa, yarasa mitake nufi? Yakuma kasa fassarasu? Amma tabbas kalaman NATA sunfi kama dana mai gugar zana. "O my god, waimike faruwane?".🤦🏻‍♂ ********* Gaba d'aya yau haka yaraba hankalinsa biyu a office, rabi kan aiki rabi wajen FASA kalaman Aysha Dason fassarasu, amma har kusan 11 Na dare dayakai baisamu fashin bak'i ko d'ayaba. ____________________________ Wajen k'arfe d'aya Na rana saiga hajia khaltum tazo yima Momy barka da tashin bak'i, batasan abinda yafaruba ita, saboda tayi tafiya zuwa Benue state tun washe garin bikinsu mufeedah, wani aikin k'ungiyane yakaita. Tunda tashigo falon taga sauyin fuska ga aminiyar tata, bata damuba tazauna suka gaisa, Momy tajata suka tafi k'uryar d'aki kamar yanda suka saba, saboda bataso yaranta su fahimci komai, babuma kowa daga ita sai zuwairah da mashi'a mai aiki, ganinma tayi bak'uwa Anty zuwairah tad'auki gyalenta tafita nan makwaftansu gidan wata k'awarta Tamata sallama. Mashi'a ce kawai a kichin, itama ganin Anty zuwairah tafita sukuma shunshige bedroom saita turama Aysha message akan tazo. Aysha nakwance ciwon ciki ya isheta taga message d'in mashi'a, amma dan k'arfin hali haka tasato jiki tafito. Hajia babba da hajia khaltum na shiga d'aki suka zauna a bakin gado, hajia khaltum ta kalleta, "umm aminiya barka da tashin bak'i fa, Ashe 'yan biki duksun kama gabansu?, kai Alhmdllh, daganan kuma sainasu babie na, kisan kuwa yanda aiki yayi k'yau a Benue? Yara kusan 13 nasamo mana, kuma zagad'a-zagad'a, wannan karon kubrah ce zata tafi dashu UK, munsami sabon dila ma bayan john, hhhhh aikifa na k'yau aminiya, kud'i sai k'ara zama sukeyi, shiyyasa ban damu da account d'ina da Ibrahim yarufeba, saboda k'aramine, nidama bana zuba zunzurutun kud'i a banki aii." Itadai Momy batace k'alaba, duk uban surutunnan da hajia khaltum kezubawa, bata kula Momy tayi kicin-kicin da fuskaba, saida takusa kai k'arshen aya sannan talura. " a'a aminiya waishin lafiya kuwa?". "Da sauk'i dai khaltum". "Mike faruwa to?". " mufeeda tadawo gida tun kwana biyar dasuka wuce". Wata zabura hajia khaltum tayi, tagyara zamanta sosai tana fuskantar hajiya babba, "ki min dallah-dallah mana yanda zan fahimta". Afad'ace hajia babba tace, " aii dolene namiki dallah-dallah kuwa khaltum, domin tasilar habibu aka sakkomin d'iya, habibu ya yaudare Mufeedah ya d'irka mata ciki, wannan ne dalilin dawowarta gida harda saki". "Habibu kuma? Habibuna daine ya yaudari mufeeda da girmanta? Shekarun mufeeda nawa aduniya hajia laurah? Ince 27? Yanzu mai shekaru 27 ne aduniya za'ace an yaudareshi?, please babu wannan tsakaninmu, idan har cikin ya bayyana jikin mufeeda, kuma yakasance Na habibune to tabbas da had'in kanta, amma babu batun ya yaudareta anan, idanma gaskiya kikeso kawai mu jingina laifin Kansu su duka, amma bawai shikad'aiba......." "K!!! Hajia khaltum!, wlhy ki iya bakinki, zan d'auki komai arayuwa amma banda wulak'anta rayuwar 'ya'yana, ya ina gaya miki magana zakina gayamin babu dad'i? Kema kinsan wanene bunsurun k'aninki aii........ " laurah!! Maza sakama bakinki linzami wlhy, inhar habibu bunsurune aii mufeeda ma akuyace, tunda ba har ciki gida yazo yamata fyad'eba, kum......... Aysha data shigo d'akin da sauri tace, "kai Sirikata kuyi ahabkali, kuna d'aga murya dayawafa, gashi ya khaleel yana gida, kuyi maganar k'asa-k'asa surukata🤭. Saikuma Aysha ta shek'e da dariya.🤣 Daga hajia khaltum har hajia babba mutuwar tsaye sukayi, suma kasa cema Aysha uffan Dan mamakinta. Hajia babba ce ta harzuk'o zata shak'e Aysha, da sauri Aysha tad'aga mata hannu tanaja da baya, " A'a fa Surukata, karkiyi wannan kuskuren, akwai jikanki anan", tanuna cikinta, "sannan ta6ani babban kuskurene dazai iya 6allo ruwafa, nidama shawara nazo Baku, aganina daku zauna tada jijiyoyin wuya kan k'yautar jika da ALLAH yabaku, gamma kulura da abinda ke tunkaroku fa, kuyi azamar bincika ina Kubrah? yau tsawon kwanaki 3, itada tace zataje Lagos tayi kwana 1". " sannan kekuma k'awar surukata kibar tada jijiyar wuya akan beeb guy, 🤣🤣kema yasama miki jika kuma d'a ajikin 'yarki babie🤪". "Please & please aminan juna, abar fad'a fa, kusan masu iya magana nacewa *_SHARRI 'DAN AIKENE, DUK KUMA INDA KA AIKASHI SAIYA DAWO YASANAR MAKA YAJE😉_*. Bye, har Aysha tafita tadawo, "o, wlhy Na manta suruka, dama inason fad'a mikine idan za'a siyama mufeeda kayan haihuwa atuna da d'an jikalle🤨, tayi maganar tana nuna cikinta🤣🤣, tafice tana 'Yar dariyar mugunta. Rasa wanda zai iya motsawa acikinsu akayi, maganganun Aysha sungama dukan zukatansu, kowanne arikice yake, hajia khaltum ta kalli hajia babba, itama kallonta takeyi, " Aminiya da gaske yarinyarnan keyi? Habibu yayima babie ciki, kuma ankama kubrah?". Cikin marairaicewa hajia babba tace aminiya ban saniba, amma ina mamakin rashin dawowar kubrah dama, Dan kwana d'aya tace zatayi, gashi tunda tatafi bata kiraniba", hajia babba tayi maganar tana zama agado ja6ar'. Itama hajia khaltum zubewa tayi, sai zufa sukeyi kamar babu fanka ad'akin, jiki Na rawa haji khaltum ke Neman number Kubrah, amma switch up, tagwada yafi sau 30, maida akalar kiran tayi kan wata mata, ko gaisawa basuyiba tace kubrah tazo?". Daga can aka sanar mata batazoba, amma tabbas sunji k'ishin-k'ishin cewar an kamata.... Aii zabura hajia khaltum tayi itada hajia babba, kowacce tarasa inda kemata dad'i, sai faman zagaye d'aki sukeyi suduka, sun rasama wane tunani zasuyine, zuwacan hajia babba tace, "Aminiya miye mafita?". Wlhy aminiya kaina ya toshe, kibani nanada gobe, inaso naje Na binciki babie yanzunnan". "OK saikin dawo". ___________________________ Tunda Aysha takoma 6angaren Amman yanayinta ya canja, daka ganta zakasan tana cikin farin ciki, hardai Ammah takasa hak'uri ta tambayeta. Murmushi Aysha tayi, "tace babufa komai Ammah". Ammah bata sake cewa komaiba. ********** Tunda ya khaleel yabar office baizame ko inaba sai Cinema, abakin k'ofa yatsaya, duk wani mai shiga da fita akan idonsane shida Taheer da youseef da Joseph, suna nan tsaye kuwa saiga beeb guy da 'yanmata biyu, saikuma abokansa, cikin nishad'i suka kar6i ticket suka shiga, suma su ya khaleel suka kar6a a sannan, su habeeb na gaba su ya khaleel Na bayansu, can kallo yay nisa habeeb yamik'e zaije fitsari, asace Youseef yabi bayanshi har toilet d'in. Habeeb nacikin fitsari youseef yashigo, juyawa yayi yad'an kallesa ya janye idonsa, youseef yad'anyi kamar shima fitsarin yakeyi, Habib nagama youseef yayo kansa, yaje yatare k'ofa. Cikin kallon sama da k'asa habeeb yace, " Malam lafiya kuwa?". "Dadai sauk'i, dama zan fad'a makane kasan an kama kubrah kuwa?". " kubrah fa kace?, wasa ko gaske?". "Mizaisa namaka k'arya, idan kanason tabbatarwa zomije kagani". " a tunaninka kai tsaye zan yarda dakai?". 'Cewar Habib'. Murmushi youseef yayi, yazaro waya a aljihunsa yanuna masa k'aramin video lokacin da'ake kama kubrah, yace budurwatace, dakanta taturomin video d'in nan kafin su kwace wayar, kaga sak'on data turomin akan Na nemeka mu tatatuna yanda za'a ku6tar da ita". Kar6a Habib yayi, yaduba sak'on, tabbas no d'in kubrah ce, babu musu yabi bayan youseef har waje, suna zuwa jikin mota yafaki idon mutane ya shak'a masa abunda ke cikin hanky d'insa, tuni jikin Habib yasaki, yasulale zai fad'i, youseef yay saurin turashi mota yarufe, sannan yakira number khaleel yace aiki ya kamalla, sufito kawai. 'Dai-d'ai suka ringa fitowa, sabida tsaro ba tsoroba, daganan ya khaleel gida yawuce. Youseef da Joseph kuma suka wuce setetion dansu kai Habib. Sanda yashigo gidanma su Ammah harsun rufe k'ofa alamar sunyi barci kenan. 6angarensu yawuce kawai, shima yayi duk abinda yadace yakwanta. Har yau maganganun Aysha suna masa yawo a kwalwar kai. ___________________ Hajia khaltum kuwa tana zuwa gida tatasa babie gaba sukaje asibiti, gwajin farko yanuna babie batada ciki, ajiyar zuciya hajia khaltum tayi, hankalinta yad'an kwanta, suka dawo gida, mamakinta babie taitayi, dan batasan ma'anar gwajin ciki da ammi takaita aka mataba. 🤣hajia khaltum batasan cikin yana jikin salima baneba, Aysha tayi yawo da hankalinta ne kawai..........✍🏿 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀ *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of expert & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ 3⃣6⃣ Yau dai babu laifi Aysha antashi dad'an k'arfi-k'arfi, saidai tunda farar Safiya tatashi da jarabar son rake, Ammah na zaune afalo tana shan kunun tsamiya, k'a'idane kullum Safiya saita shashi, idan 'yan tsiyarma Na kanta saida k'osai, haka takecewa tagaji dawad'an nan maik'on banzan😂. Aysha tafito daga d'akin Ammah, dakaganta dukta rame, sai uban haske data k'ara, har wani yellow-yellow takeyi, kusada Ammah ta zauna tana sauke numfashi. Amma tabita da kallo, sannu indo, kai wannan ciki nabaki wahala, gashi ALLAH ya had'aki da birkitaccen miji, ni tsoroma nakeyi karki haifo irinsa". Murmushi Aysha tayi. Tace, ''kai Ammah, kedai kullum kintaso ya khaleel gaba, kemafa doguwarce, awajenkima yakwaso tsawon, nibama wannanba, ina zan samu rake dan ALLAH Ammah?". Ammah ta kur6i kununta tana ta6e baki, kai wannan ciki naki yacika shegen hange-hange, shiyyasa nacemiki ina tsoratar miki haihuwar irin iro, Dan yahalin cikinki ya halin dogon banzarcan". Baki Aysha taturo gaba, "duk kigama fad'a saina sanar masa gulmarsa dakikeyi". " yo kifad'a mana, angaya miki tsoronsa nakeji, dagake harshi saina had'aku nayi k'uli-k'ulin kubrah daku". Dariya sosai Aysha keyi, hakama Musleem daya shigo kusan mintuna hud'u, maganganun Ammah akan kunnensa suka faru. Hararsa Ammah tayi, "to kaikuma d'n kwairo wakakema dariya?". Had'e fuska musleem yayi, " waike Ammah kowama agidannan saikin saka masa sunan banzane? Nifa shiyyasama Mafison kitafi jigawa". "Yo basai ka kainiba d'an banza bakwai, aii dai gidan d'anane, babukuma mai iko dashi sama dani, faratun banza kawai". "oho dai, farin aka gani aka rud'e". Yamik'e yana hararta, "nikingama tafiyata, Anty Aysha bara nasa akawo miki raken". " yauwa ya musleem, ngd sosai, Ammah kinji dad'inki, kedai dakowama karawa kikeyi, ya Sultan ne kawai bakwa fad'a". "Aishi Sultan mutumin arzik'ine, ba irinkuba, amma d'aya bayan d'aya zanyi maganinku, d'an banzancan zigawa zanyi amasa auren dole kwannan, kekuma aure zansa iro yak'ara, kuma 'Yar k'auye zan za6o masa wadda haushi zaiyi kamar ya karsa.... Tsayawa Aysha tayi da dariyarta, ta had'e fuska tamau, mi Ammah zatayi ba dariyaba, afili tace, " ja'ira, ashedai kinason dogon banzan can mai zuciyar tsiya, amma lokacin auren hardasu kuka". Shiru Aysha tama Ammah, daga waje akayi sallama. Ammah tace, "kowaye shigo kaji, d'akin tsohuwa aina kowane". d'aya daga cikin drivers d'in gidanne, har k'asa ya durk'usa ya gaida Ammah, yamik'o leda viva, gashi inji musleem yace akawo". Aysha najin haka takar6e da sauri, yauwa sannunka. Rakene mai yawan tsiya aciki, irin wanda aka yanka k'ananunnan aka d'aura afarar Leda, Ammah tayi dariya, ''yoshi wannan duk raken yasiyema mai tallan ko?, saikiyata sha har kigaji". "Wlhy kuwa Ammah, dama mafarkinsa nayi a barcin asuba d'innan Dana koma, bara kiga nayo brosh nadawo". ''Dama bakiyi burushi ba kikazo kika zauna kinata had'iyar k'azamin yawu?, ke indo kirage k'azantafa". " k'yadai jidashi Ammah, aikinsan idan nayi brosh babu abinda zanci amai nakeyi dai", batareda tatsaya jin mi Ammah zataceba tashige bedroom, Mufeedah Na kwance d'ai-d'ai tana shak'ar barcinta, dama ita cikin nata sai saka barci. Brosh Aysha tayo tadawo falon, tatarar Ammah tazuba mata raken cikin fleet bayan ta wanko matashi, ankuma ajiye roba na zuba datti. "Yauwa Ammarmu, shiyyasa nake yinki sosai-sosai". "Kedai kika Sani" cewar Ammah tana shigewa kichin d'inta. Aysha tama bayanta gwalo, tafara shan rakenta, harda mik'e k'afafu kamar tasamu gasashshen kifi🤪. Tayi nisa sosai da shan rakenta, harwani lumshe idanu takeyi Dan dad'insa datakeji, ya khaleel yashigo da sallama, sanye yake cikin k'ananun kaya, blue dogon wando da oxblood d'in sheart, sunmasa k'yau sosai, kwarjini da cikar kamalarsa ta k'awata k'yawun haibarsa, yad'an rame kad'an saboda yawan tunani da cud'ewar aiki dasuka tasoshi gaba. Kokad'an Aysha bataji sallamarsaba, idonta alumshe tanata shan rakenta, dariya tabashi, Dan haka yajin gina da bango yana kallonta, sai murmushi yakeyi, ganin abun bana k'are baneba yafiddo wayarsa a aljihu yashiga mata video. Oho Aysha batasan yana yibama, Ammah Ce tafito daga kicin taga abinda ke faruwa. "Iro mikakeyi haka?". Harara yazuba mata, "waya sanya dakene jar wuya?, kinzo kin 6atamin show", 'yay maganar yana save d'in video dayayma Aysha'. Itama idanu tabud'e da dauri, kokad'an batayi zatonsa yanzunba, danta manta yau Saturday, babu aiki. " kai iro ka kiyayeni wlhy, naga kwana biyunnan jaraba kakeji, nimafa Na iyata mota-mota, bar ganinka sangamemen k'ato batsoronka zanjiba ehe😏". Yanda tayi maganar da murgud'a baki, saita bama ya khaleel dariya, yasanta da nacin tsiya, idan tafara nacin maganarnan yinin yau babu sauk'i. Yace, "hakanefa jar wuya, ni nama manta kece, kinga zauna muyi hirar arzik'i". " ato inda arzik'in kazo basai ayiba, nidama nemanka nakeyi". "To gani Ammah ta". Aysha dai dariya kawai take musu, Dan ita lamarin nasu dariya yabata, Ammah da ya khaleel tamkar tom & jerry haka suke. Khaleel kam dukkan hankalinsa nakan Aysha, sauraren Ammah kawai yakeyi, sosai dariyarta take narkar dashi, dama kwana biyunnan hak'uri kawai yakeyi, yamatso kusada ita yana fad'in " a lallai kinji sauk'i, hardasu dariya?". Murmushi Aysha tamasa mai kashe zuciya, tace, ''Alhmdllh, yau natashi babu laifi, harma inajin zan koma aiki ranar Monday". Girarsa d'aya yad'e yace, "da gaske?". Jinjina masa kai kawai tayi. " to ALLAH yak'ara lfy". 'Yay maganar yana kuma shigewa jikinta, Dan Ammah tashiga bedroom yin wanka. Murya can k'asa yake mata magana, "waya siya miki rake da safiyarnan". Kuma narke masa tayi ajiki tace, " ya Musleem mana, wai ina kashigene jiya, har nayi barci baka dawoba, bayan wahalar danasha tun wajen 6pm Nake amai, saida doctor yazo yasaka min k'arin ruwama". Da sauri ya kalleta, "da gaske kikeyi". " ALLAH kuwa". Tausayinta ne yakuma kamashi, azuciyarsa yace kai uwa dabance, (ALLAH ne kawai zai biya mahaifiya gaskiya), Ahankali ya sumbaci goshinta, "sorry kinji my pretty na, yanzu inane kemiki ciwo?". " babu ko ina, yau dad'an sauk'i aii". "To Alhmdllh, kinga yau agida zan yini, yakamata mud'anje 6angarenmu muyi hira ko? Naduba babyna mu gaisa dashi". Aysha bata gane nufinshiba, tace, " idan Ammah tayi fad'a fa?". "Babu wani fad'a dazatayi, tashi mujema kafin tafito". Kamardai Aysha bazatajeba amma yamata wayo tabishi, shiya d'auka mata raken fleet d'in dana ledan, tacan baya sukabi dankar agansu, sai 6angarensu. Komai fes Aysha ta iskeshi, Dan kullum sai Maleeka da Tasleem sunje sun gyarashi, afalo suka yada zango, suka zube bisa doguwar kujera, ya khaleel ya kwantar da Aysha bisa cinyarsa tana shak'ar daddad'an turarensa, sai lumshe idanu takeyi, Dan wani barcine taji yana fisgarta. Idonsa akan fuskarta yana shafa kwantaccen gashinta da hannunsa Na dama, Na haggun kuma yana kan shafaffen cikinta maikama da babu komai aciki, " my pretty badai barciba?". Bud'e lumsassun idanunta tayi akansa, saikuma tamaida tad'an lumshe takuma bud'ewa, muryarta harta fara sark'ewa tace, "ALLAH barci kawai naji nafaraji". " lallai 'yar gata, rakenfa to?". "Nakuma k'oshi". Guntun murmushi yayi yana kauda kai daga kallonta, itakuma tamaida idonta talumshe. ______________________________ Adaren jiya gaba d'aya Momy takuma fita hayyacinta, zuwa yau kam jininta yagama kai k'ololuwar hawa, gaba d'aya daren jiya bata rintsaba, tunani dai babu kalar dabatayiba a daren jiya, amma har yanzu tarasa matsaya, dama d'ayace tarage mata ayanzun, kuma zuciyarta tafi karkata awajen, tana tsaka da tunanin ne aka kira wayarta, cikinta har rawa yakeyi tad'aga saboda ganin number hajia khaltum, babu batun gaisuwa hajia khaltum tafara shaida mata cewar ankama habibu, cikin kuka hajia khaltum keyin maganar, kasa cewa komai hajia babba tayi, saima wayarce ta sulale tafad'i k'asa, aikam tayi kwatsa-kwatsa, abinka da tayis, abin mamaki saiga hawaye a kumatun hajia babba, sai gudu sukeyi kuwa, wasu Na korar wasu, kusan mintuna 20 tad'auka awajen, sannan saigata ja6ar ak'asa tayi zaman 'yan bori🤣🤣🤣🤣. 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀Reefat amin afuwa🤪. _________________________ Ammah na fitowa taga babu khaleel babu Aysha, babukuma ledar rakensu, "amma dai ALLAH ya shiryeka iro, dama satarta kazoyi kenan?, zan kamakane aii, INA zaune shararren wajena zakazo ka iskeni, tayi kwafa". ************ Ya khaleel kam tunda yaga Aysha tayi barci ajikinsa saiya d'auketa zuwa d'akinsa, saman gado ya shinfid'ar da ita, shima yakoma gefenta ya kwanta, dama bawani isashen barci yasamuba, babu dad'ewa shima barcin ya sureshi. Basu farkaba har 12:56pm afirgice ya khaleel yafarka, saboda mafarki yayi anata sallah amma shi yana zaune, kansa yadafe yana addu'ar tashi abarci, saiyaji ana sallamar idar da sallah, waigawa yayi yana kallon Aysha dake barcinta har yanzun lafe ajikinsa, ahankali ya zameta yasakko daga gadon, alwala yashiga toilet yad'auro a hanzarce, ganin koma yatafi masallacin anrigada an idar, saikawai yashinfid'a sallaya yayi ad'aki. Tun yana raka'a ta biyu Aysha tafarka itama, cikeda sha'awa take binsa da kallo, bak'aramin burgeta yayiba yanda yake sallah a tsanake, kuma komai cikin k'a'ida, tana nan tashagala da kallonsa harya idar. Bayan yayi sallama yajuyo ya kalleta, danyaji ajikinsa ana kallonsa, d'an murmushi yamata, " my pretty kintashi?". Kanta ta girgiza masa batareda tayi maganaba. "To sakko kiyi wanka ki sallah, time yana k'urewa". Sai yamutse fuska takeyi haka ta sakko, ganin yanda take tafiya kamar wadda batada laka ajiki yasaka ya khaleel shafa addu'ar yabita toilet d'in. Taddata yayi zaune wai tana hutawa, yay murmushi tareda girgiza kai, dakansa yahad'a mata ruwan wankan maid'an zafi, ya taimaka mata tacire kayan, dukda tanata wani nok'e-nok'e, dakansa yamata wankan, amma da manufa biyu, taimako da bincike, (ko d'igon zanene tattu bai gani ajikin Aysha ba, barema wata kunama🦂, hakan bak'aramin d'aure kansa yayiba. Bayan sun fito ta tak'ark'ara tayi sallar Azhur. Tana idarwa yay sama da ita zuwa gado, Dan dukta birkita masa tunanin sanda yake mata wanka. ganin lamarin nasu yafi k'arfin alk'alamina, Dan tamkar mayunwata haka suke kissing d'in juna, dagani Kasan sunyi missing d'in junansu. 🚴‍♀🚴‍♀dolene nakama gabana, kafin su koyamin fitsararsu😏. ____________________ Momy dai tayanke d'aukar matakin k'arshe, kamar yanda suka yanke shawara itada Aminiyar tata, dakanta tashiga kichin, ta kori mashi'a, filawa naga ta kwa6a kala biyu, babu dad'ewa tagama had'a meat pie d'inta, kowanne tagasa a oven, abinda yabani mamaki shine rarrabashi datayi. Gaba d'aya yanayinta kuma yakoma Na farinciki, bakamar d'azuba datake cikin tashin hankali. Ita kanta Anty Zuwairah taga wannan sauyin Na Momy, bata zargi komai arantaba, Dan tunanunta sauk'in data samune. Wajen around 2 tafito zuwa 6angaren Ammah, afalo ta iske Ammah da Mufeedah, saisu Abashiyya matasu ya sultan, harda su maleeka, hira suketa sha, Amma nabasu labarin zamanin da, kowa yayi mamakin ganin Momy, duk suka gaidata, wani k'arin mamakin ta amsa da sakin fuska, aladabce kuma ta gaida Ammah. Sai binsu takeyi da kallo Ammah bataga Aysha ba. "Ammah badai jikin Aysha ya matsanta mataba ko? Naga dukga yaran amma ita babu ita?".. Cikin shan k'amshi Ammah Tace, " a'a jikinta da sauk'i, tanacan tareda mijinta a 6angarensu, da safennan yazo ya saceta". Duk falon saida akayi dariya, amma banda Momy dataji kamar Ammah ta soka mata mashi. Tayi dariyar yak'e "ayya amma, dama meatpia ne namata datacemin tanasonci, kuma ganaku, bara aina aiki hasnah Takai musu". ''A to kin k'yauta gaskiya, sunacan". Ajiye musu Nasu tayi tafice, babu Wanda yazargi komai suka faraci, sai Santi sukeyi, yayi dad'i, dama Momy ta iya kayan snacks d'innan muguntace kawai Dason jiki ke hanatayi. Bata zame ko inaba sai 6angarensu ya khaleel. ******* Sun fito wanka kenan Aysha tace masa yunwa takeji wlhy, Dan harta fara ganin jiri, k'arasawa yayi kusada ita ajikin madubi, ya rungumota tabaya, hannayensa duka nakan cikinta, kansa yad'ora gefen kafad'arta suna kallon juna ta madubi, my sholy kinfa zama consumer, kad'an-kad'an saici". "Kai sadauki, duk yaufa banci komaiba sai rake, nidai kaje kasamomin abinci acikin gida, ALLAH harna farajin tashin zuciya". Sumbatar gefen wuyanta yayi, cikin kunnenta yace, " idan naje aikennan nikuma miye tukuycina?, hannu tasaka ta shafo kumatunsa, sannan tad'aga masa gira🤨, saika dawo zaka gani". "Wata sassanyar dariya yasaki acikin kunnenta, yana shinshinar wuyanta yace, ''yanzu kuwa zan samo abinci, kuma duk kukanki saina kar6i tukuycina". Baijira cewarta ba yasaketa yafice. Murmushi Aysha tayi tana binsa da kallo ta madubi, akan la66anta tafirta I love you so much sadaukina, kabani farinci yau d'innan, bakuma zanta6a mantawa da hakanba😊". Shima abinda yake ayyanawa aransa kenan, fuskarsa d'aukeda murmushi sukayi karo da Momy afalo zaune. " Momy kece?". Juyowa tayi ta kalleshi, bak'incikin ganin fusakarsa a farinciki yadaki zuciyarta, amma saita dake, "nine my lovely son, zonan mana, kwana biyu ana fushi da Momy ko?". Murmushi yayi, yak'arasa gefenta ya zauna tareda d'ora kansa a kafad'arta, yace, ''I miss you momyna". " miss you 2 my dealing, ykk?". "Alhmdllh momyn, saidai missing naki danayi, kiyi hak'uri kidaina fushi dani, ranarma sharrin shaid'anne, kinsan banida kamarki duk duniyarnan". "Karka damu kaji Ibrahim, komai ya wuce, ina d'iyata d'in Aysha". Kunyace takamashi, yad'an Sosa kansa yana murmushi, da hannu yanuna mata d'aki. Murmushin yak'e Momy tayi. Khaleel yace, ''dama zanje cikin gidane samo mata abinci, wai yunwa takeji". " ayya gama meat pia na kawo muku, dama itace tacemin tanaso jiya, shine nayishi yau, kamaji da zafinsa saika kaimata taci, ni bara naje, Dan zuwairah na shirin tafiya". Dad'ine ya lullu6e khaleel Dan ganin momy tafara basu kulawa shida matarsa, yamata godiya tafice, shikuma yanufi d'akinsa, tararwa yayi Aysha kwance bakin gado, yunwa tahanata ta6uka komai. Kwanon tangaran d'in kawai yamika mata, jikinta har rawa yakeyi tatshi zaune, kusan tare suka d'auka, amma tarigashi gutsura, harta fara taunawa tatsaya, waini Sadauki inama kasamo meat pia ne haka? da zafinsa. Harzai gutsura yatsaya bata amsa, momyce takawoshi yanzu, tace dama jiya kikace mata tamiki". (Acikin d'oki yake gaya mata). Da sauri Aysha ta furzar dana bakinta, shima tayi saurin ka6e na hannunsa daya gutsura, bayi dasauri, fuskarsa a murtike yace, "k miye haka?". Hankad'a kwanon Aysha tayi yafad'o k'asa ya tarwatse, Aysha tayi azamar tura hannu cikin bakin khaleel tana kwakulo Wanda ya 6allah, dama ko taunawa bayyiba. Hankad'ata yayi tabigi gado, bata damuba, tunda tasami nasarar Ciro na bakin nasa. " waike wane irin iskancine sannan? Uwatafa nace takawo ba uban waniba!!!". Itama Aysha a tsawace tace, "ko itad'ince takawo bazakacishiba, kasan miye cikinsa?!!! To gubace ta kasheka inbaka sanib........... Bai bari ta k'arasaba ya d'auketa da mari, ''k!!! Karfa kiga ina wasa dake kiringa kawomin iskanci, kina nufin uwata data tsugunna ta haifenice zata kawo guba tabani naci na mutu!!!!!?". Hannun Aysha dafe da kuncinta tana kuka tace, " wlhy koda zaka kasheni saina fad'a, nace gubace aciki, bai dameni da matsayin Momy agarekaba, inma bakai tayi nufin kashewaba nitazo kashew........ Da sauri yamatsota, itakuma tamatsa baya, duka takuma kaimata ta kauce, ya wawurita tafice da gudu, shima binta yayi har cikin gida. Basu zame ko inaba sai 6angaren Ammah, yanda Aysha tashigo aguje yasaka kowa mik'ewa, saiga ya khaleel shima, Ammah ce tayi jarumtar tareshi, sai huci yakeyi tamkar kurar daji. Aysha da bakinta bai mutuba, saboda rud'ewar datayi, cikin kuka takuma fad'in wlhy koda zaka kasheni yau agidannan saina fad'a, gubace Momy tabamu muci a meat pia muci mu mutu, idankuma bahaka baneba tazo ta gardama mana....... Kuma yunk'urowa yayi kanta, baffah daya shigo yanzu yay saurin rik'eshi, dandanan 6angaren Ammah yacika daduk Ahalin gidan. Daga Aysha har ya khaleel sunkasa nutsuwar da za'a tambayesu, sai Aysha daketa fad'in ko khaleel zai kasheta saita fad'a guba Momy tabasu suci su mutu, kuma inba haka bane tazo ta Musa zancen. Shikuma ya khaleel sai fisgewa yakeyi daga rik'on baffah, burinsa kawai Yakama Aysha yamata dukan mutuwa, tunda har tsaurin idonta yakai taringa yima mahaifiyarsa sharri haka. "Tsawa baffah yadakamusu, yace, " kai duk banason rashin hankali, minene yahad'aku?". Aysha zatayi magana ya khaleel yay saurin tareta ta hanyar fara fad'e.............✍ Hummm sannu-sannu bata *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ 3⃣7⃣ Tunda ya khaleel yafara bayani kowa yay tsirmai-tsirmai da idanu, dankuwa duk Wanda yake a 6angaren Ammah yaci meatpia d'in, Dan Tasleem ma sarkin tsoro hawaye takeyi, tasandai sungama aiki sukam, yau sai mutuwa🤣. Mama ce tadakama Aysha tsawa, tayo kanta zata daka, Ammah ta dakatar da ita. "Fad'ima kema bakida hankalin kamar iro, waishin kun mantane yarinyarnan k'aramin cikine da ita?, sokuke cikin yazube saboda rashin hankalinku..........? Maganar Ammah takatse yayinda sukaga Aysha nalayi, tamkar wadda tasha giya, dak'yar numfashinta ke fita, duk kanta sukayi suna kiran sunanta. Yarab Aysha tazube ak'asa asume, sallalami kowa yafara, Muhseen yafita da Sauri d'akko key d'in mota. Jikin ya khaleel ne yayi sanyi, dukda bai k'arasa inda Aysha takeba, amma idonsa Na kanta, gashi gaba d'aya mutan gidan sun rud'e, mamace kawai take tsaye agefe kamar ya khaleel, saidai itama hankalin nata amatuk'ar tashe yake. Baffah ya dakama ya khaleel tsawa akan yazo yad'auki Aysha yakaita mota. K'arasawa yayi ya d'auketa, koda yasakata mota bai shigaba, sai Anty Mamie ce tashiga tarik'e Aysha, babu Wanda yadamu dashi motocin biyu suka fice aguje. 🤔wai inama momyne?. Tunda hajia babba tabama khaleel meatpia tabar gidan, sai gidan Aminiyarta, cikin farinciki take sanar mata komai ya kammala, yau damuwarsu tak'are. Atare suka shak'e da dariya, suka tafa, hajia khaltum tace aminiya nasan dolene k'ungiya tabaki k'arin girma wlhy, dama abin yazo a dai-dai, jibine za'ayi gagarimin taron k'ungiya. K'yak'yal suka saka dariya. "Amma aminiya wani hanzari ba guduba, shin kinsaka Wanda zai kwashe meat pia d'in idan sunci?". "A, Aminiya daguduma kuwa, nasaka yarinyarnan Dije mai aiki, babu Wanda yasan yarinyar tanamin aiki ta k'ark'ashin k'asa aii, barama nakirata naji mike wakana agidan?". Kiran Dije momy tayi, babu dad'ewa dije ta d'auka, jikin dije har rawa yakeyi tace, " hajia akwaifa Matsala". Zumbur hajia babba tamik'e tsaye, ke banason mummunan labari kinfa sani". "Hakane hajia amma dolene nafad'a miki, ................kaf dije ta sanarma hajia abinda yafaru, tad'ora dafad'in amma hajia ki kwantar da hankalinki, yanzu haka naje nakwashe meatpia d'in dakika basu, Na canja dawani mai k'yau, koda d'auka akayi danyin bincike bazasuga komaiba, itakuma matarsa dazasu sami bayanai tasuma, bansan miya sametaba, yanzu haka suntafi asibiti. Kinga sauran aiki nakine, saikiyi azamar samun Wanda zai ida miki ita a asibitin". Ajiyar zuciya Momy tasaki, tace, " shikenan dije, ki kula da komai, yanzunnan zanzo gidan nima". A gaggauce Momy tayima hajia khaltum bayani, dukda a rud'e suke hakan baihanasu Neman yanda zasu salwantar da rayuwar Ayshaba, sungama shirya hajia khaltum zataje asibiti, Momy kuma tanufo gida. *********** Suna tafiya asibiti ya khaleel yanufi 6angarensu, meatpia d'in nanan inda suka barsa, tattarashi yayi yazuba aleda, yad'auki key d'in mota da sauri yafito. Aharabar gidan sukaci karo da Momy, kallon-kallo aka tsaya yi, amma dayake Momy A ce, saita wayance, tak'araso gun ya khaleel tana fad'in Ibraheem! Lafiyarka Kuwa? Naganka wani iri?". Hawayen dasuka mak'ale a idonsa suka ziraro, Momy tak'araso kusadashi sosai tana share masa, 'yan gidan wad'anda basubiba asibitin duk suna tsaye suna kallon ikon ALLAH. kad'an ya khaleel yazame jikinsa daga kusada Momy, yabi sauran 'yan gidan da kallo, yace, "duk Wanda yasan yaci meatpia d'in yashiga mota muje asibiti". Cikin dukan k'irji da zare ido Momy tace, " meatpia kuma? miyafaru dashi?". Bai bata amsartaba, sai cewa yayi "kedai Momy Shiga mota kawai muje asibiti". "Wane irin nashiga mota muje asibiti? Waimike faruwane? Ninasan ninayi meatpia agidannan yau, kuma anacewa duk Wanda yaci yashiga mota aje asibiti, Ibraheem banason kwana-kwana fad'amin miya faru!?". Tayi maganar ad'an tsawace. Rintse idanu ya khaleel yayi, bai cema Momy uffanba yara6a ta gefenta zai wuce, wata razananniyar tsawa ta Dana masa, "kai!!! Ibrahim, banason iskancifa, Dan ubanka inamaka magana amatsayina Na mahaifiyarka shine kake shareni?". Ransa amatuk'ar 6ace yake, amma cikin sanyin murya yace, " Momy mikeso nace mikine, kefa kika bada meatpia d'innan, kuma kinfi kowa sanin mikika zuba acik........ Baikai k'arsheba ta tari numfashinsa, " minazuba Dan ubanka?". "Momy A'eesha tace kinzuba guba aciki, kuma dabata ganiba bazata fad'aba, dukda zuciyata bawai ta amince baneba, amma inason Sanin mike tsakaninki da matar d'anki? tabbas akwai wani Abu 6oyayye tsakaninki da A'eesha, yazamemin dolene naje abincika duk Wanda yaci meatpia d'in agidannan". " yanzu nan Ibrahim harni kake zargi akwai wani Abu tsakanina da matarka??, harma zargina kakeyi nazuba wani Abu aciki nabaku kuci Ku mutu ko? To aii Alhmdllh tunda Baku kad'aine kukaciba, su Ammah ma sunci. shikenan naji, muje asibitin abincikasu". Babu Wanda yace komai duk suka Shiga mota, harda ita momyn. ________________ A asibiti kar6ar gaggawa akaima Aysha, harsu khaleel sukaje doctors basu fitoba daga kan Aysha. Cirko-cirko suka iske su baffa, kowa da sak'e-sak'en dake ransa, musammanma baffah daya rasa wane kalar tunani zaiyi, koda Momy sukazo itadasu khaleel bai kalli inda takeba, tabbas zuciyarsa Na raya masa akwaidai abinda basu saniba, Dan haka kawai Aysha bazatace Momy tabasu guba suciba, ya salam, wannan wane irin lamarine haka? idan zancen Aysha gaskiyane miye ribar hajia laura Na kashesu?, Mu'azzamfa d'antane nacikinta, Wanda tafiso duk cikin 'ya'yanta, dan tasha fad'a masa hakan, ya ALLAH ka warwaremana wannan lamari cikin sauk'i". Nace amin baffah. Ya khaleel office d'in babban likitan yaje gaba d'aya, yafad'a masa aikin dayakeso amasa yanzun cikin gaggawa, Dan gudun kar gubar tafara aiki ajikin wad'anda sukaci, inhar gaskiya Ayshan takeyi. Babu kuwa 6ata lokaci aka kira duk Wanda yaci meatpia d'in, likitoci dayawane suka maida hankali Kansu, harda meat pia d'in da ya khaleel yad'akko a Leda. Yini guda zubur a asibitin sukayishi, Dan har zuwa bayan isha'i anata bincike, Aysha kuma ta farka, amma sun mata allurar barci. Ganin dare yayi aka sallamesu akan sukoma gida, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu komai zai kammala, amma dukkan wanda yaci meatpia d'in anmasa allurar rigakafi, dukda dai doctors d'in sunga alamun babu guba ajikinsu. Ya khaleel da baffah sai anty mamie gwaggo bintu kawai aka bari a asibitin, sauran duk baffa yace su koma gida, tuni ya khaleel yabaza ma'aikata a asibitin. Dukda hakan bai hanasu hajia babba k'ule-k'ullensuba akan Aysha, saidai har yanzun basu sami nasarar aiwatarwa bane. *****"***** Daren ranar gaba d'aya hajia babba bata rintsaba, tasan wanene khaleel akan bin k'wak'wk'wafi, dukda babu wata hanyar daza'a gane tabasu meatpia mai guba, tunda sauran 'yan gidan Wanda babu gubane tabasu, kuma dije tayi saurin canja Wanda tabama Ayshar. Haka taita safa da marwa a d'akinta, takasa zaune takasa tsaye. ****** Kusan dukkan ahalin gidan atsorace suka kwana jiya, musamman ma yara😉. *WASHE GARI* Washe gari takama lahadi, salla ce kawai ta fidda ya khaleel daga jikin d'akin da aka kwantar da Aysha, garama baffah bayan sallar asuba yaje gida ya kimtsa yadawo. Aysha har sannan barci takeyi sosai, tafiyar baffah babu dad'ewa saiga Momy. Ya khaleel ya gaidata, ta tambayi jikin Aysha yace da sauk'i badai ta farkaba har yanzun. Dad'i sosai Momy taji. Tace, "to aii dakunje gida kaidasu Bilkeesu, nisaina tsaya wajenta kafin kudawo". " A'a Momy, saidai su Anty Mamie suje su, amma ni barin asibitinnan bai kama niba yanzun". Shiru Momy tamasa bata tankaba, Dan yazama dole tayi yanda zatayi subar asibitin, dansu sami damar aiwatar da shirinsu, zuwacan wani tunani yafad'o mata, tabbas baikamata ta matsa akan saisun tafinba, Dan zai iya zargar wani abun. Suna nan zaune awaje su duka Dan ba'a buk'atar yima Aysha hayaniya, wata nurse ce tazo tashiga d'akin da Aysha take kwance, kusan mintuna 30 tafice, fitarta dakamar minti 10 saiga watama, kamar ya khaleel zaiyi magana amma saiyayi shiru, yakoma yasake jingina da bango. Kusan mintuna 20 nurse d'in ta d'auka ad'akin Aysha, sannan tafito ad'an hanzarce, harta gotasu ya khaleel ya tsaidata dafad'in jimana". Idanu tarintse, gabanta Na fad'uwa tadawo baya. Ya khaleel yace, "mike faruwane sai shigi da fici kukeyi?, kunk'i kuce mana komai, tafarkane naga kin fito jikinki Na rawa?". Gabantane yakuma fad'uwa, muryarta Na rawa tace, " sorry Alhaji, zankira doctor, naga kamar tana motsawa". Ajiyar zuciya ya khaleel ya sauke, da hannu yamata alamar taje to. Da saurinta kuwa tayi gaba. Saida ta6acema ganinsa kuma saiyaji zuciyarsa takasa nutsuwa, da sauri yatura k'ofar d'akin da Aysha ke kwance yashiga, idanu yazaro waje😳, Dan ganin halin da Aysha take ciki, sai juye-juye takeyi kumfa Na fita ta bakinta. Aguje yafito, su baffah Na tambayarsa lfy, INA bai sauraresuba yashige sashin offices d'in doctors d'in asibitin. Ganin haka suma suka afaka d'akin da gusu. Sallallami kowa yakamayi, Anty Mamie da Momy suka fashe da kuka, gwaggo bintu ce tayi k'arfin halin rik'e Aysha daketa fisge-fisge, harta fincike k'arin ruwan da aka saka mata. Da doctors uku ya khaleel yashigo, cikin hanzari suka kori su baffah waje, sukuma suka duk'ufa kan aikinsu, duk yanda sukaso ya khaleel yafita yak'i fita, yanzukan hankalinsa atashe yake, yadafe kai yana jujjuyawa, waimike faruwane haka a gudundune? Wlhy kwalwar kansafa Na neman tarwatsewa daga jiya zuwa yau. Ganin halin dayake ciki doctor Faisal ya lalla6ashi da k'yar yakaishi waje. Yana zama kiran youseef yashigo wayarsa, tamkar zai fasa kuka yad'aga wayar. Daga can youseef ya sanar masa cewar sunfa sauka Nigeria dasu glory, babu wani Neman bayani yace, sukaisu su ajiye. Cikin mamaki youseef yace, "j! Kana lfy kuwa?". Huci ya khaleel ya furzo kawai, amma yakasa cema youseef komai. " j! Kayi shiru, kana inane wai?". "Asibiti". Abinda ya iya fad'a kenan ya yanke wayar. Youseef ya sanarma su Samuel da Taheer, gaba d'ayansu suka furta asibiti kuma? Atare. ''Haka kawai yace ya yanke wayar". Taheer yace, " tabbas babu lafiya, nidama tun a jiya dana kirashi yak'i d'aga waya kusan 18 call nacemuku badai lfy ba, tunda yasan irin aikin damukaje yi mai had'arine". Gaskiyane, yanzu dai kawai munemi asibitin dayake, wani yakira mana Emanuel. OK. Bayan sun kira Emanuel yamusu bayanin abinda yasani shima, yace suna babban asibiti. Cikin mintuna 40 saigasu kuwa. Bak'aramin tashin hankali suka shigaba daganin abokin nasu, kuma ogansu ta fannin aiki, gaba d'aya yafita hayyacinsa, gawata uwar rama ta kwana biyu dayayi. Basu nemi ba'asi awajensaba, sai baffah ne yamusi bayanin komai, babu abinda sukace sai ALLAH ya k'yauta. Babu Wanda yay tunanin tafiya gida yahuta acikinsu, Dan isowarsu kenan daga islands uk, sunsami nasarar kamo glory da yaranta su Lola, amma john basu sameshiba. Kusan awanni biyu likitocin suka d'auka aciki, sannan ne suka fito kowanne yana yarce gumi, ya khaleel ya taresu da tambayoyi. "Cool down mana j! Zomuje office zanmaka bayani". 'Cewar Dr Faisal'. Yajuya yakalli sauran doctors d'in, inason a ajiye security a k'ofar d'akinnan yanzunnan Doctor Ahmad". "OK sir". Ya khaleel yajuya yana kallonsu Taheer, wannan aikinmu ne bana doctors ba. Atare suka jinjina masa kai. Tsurewa Momy tayi, dandanan tafara k'yak'yk'yafta idanu. Saurin bin bayan khaleel tayi office d'in doctor Faisal. Amma tana shiga doctor Faisal yanemi alfarmar tafita, da khaleel kawai yakeson ganawa, sai baffah. Kamar hajia babba tashak'e doctor Faisal haka taji, tafice tana dalla masa harara, aranta tana fad'in zanyi maganinka ne aii. Tana fita doctor Faisal yakira baffah awaya. Baffah yashigo yazauna akujerar dake kusada ta ya khaleel. Kusan mintuna 3 doctor Faisal Na 'yan rubuce-rubucensa, saida yagama yad'ago yana kallonsu baffah, ''maganar gaskiya Alhaji akwai wani 6oyayyen Al'amari dake faruwa, ajiya duk na duba mutanen gidanka babu wanda yaci guba, munkuma bincika meatpia d'in da Ibraheem yabamu, shima babu komai acikinsa, to amma ita matar khaleel tabbas inhar taci wani Abu ko yayane to shine aka sakama gubar, shinema yafara aiki ajikinta jiya, Dan tabbas ta had'iya, kodai abisa kuskurene kokuma bayan zubar da meatpia d'in bakinta bata wanke bakinba ta had'iya yawu, dan gubar tanada k'arfi sosai, cikin mintuna 20 kacal take fara aiki ajikin mutum, Alhmdllh kunyi azamar kawota asibiti jiya, muka samu nasarar ceto rayuwarta, saboda gubar batada tasirin dazata hallakata, dama cikin jikintane abin damuwa, amma Alhmdllh yanacikin k'oshin lafiya". "Abinda kuma yafaru yau, tabbas akwai Wanda yashiga d'akin datake kwance yabata wata gubar.......". Zabura ya khaleel yayi daga zaune, jikinsa har rawa yakeyi yace, "nurse d'inku biyu sunshiga d'akin, kuma ina zargin ta k'arshe, dan alamun rashin gaskiya sun bayyana tartare da ita, harna tsaidata amma tacemin zataje kirankane A'eesha ta farka". "Ni!, no nurse d'aya natura d'akin da take kwance, kuma bana zarginta, sister Ruk'ayya ce, kuma tasanarmin taje tadubata tana barci har lokacin, bayan ita ban tura kowaba, babu kuma wata nurse datazo wajena saikai Daka kiramu, Amma ina zuwa, waya ya d'auka yakira wani doctor, yana d'auka yace, "doctor Hambali inason a tattara dukkan nurses d'in asibitinnan". " no dukansu, harda masu aikin safe dasukazo yanzun". Yana ajiye wayar ya khaleel yace wannan ba aikinku baneba, namune. Waya ya d'akko shima yakira Joseph, "hello Joseph, kunemi Dr Hambali inason a atattara min dukkan doctors da nurses dake cikin Hospital d'inan, harda ma'aikata cleaners". "OK sir". Baffah dai yayi shiru Danshi gaba d'aya ma tunaninsa ya kulle. Ya khaleel Na ajiye wayar yace, "yanzu ya jikin matata doctor?". "Alhmdlh, mun sami nasara, yanzu hakama barci takeyi, amma cikin jikintane dai kamar......... " kamarme? Doctor karkacemin dai ya salwanta please...... " Yanda yay maganar sai tausayinsa yakamasu, doctor ya girgiza masa kai, ''bahaka nake nufiba j, ka kwantar da hankalinka, cikin yana nan lfy, saidai muyita addu'a ALLAH yasa gubar karta shafi wani sashe Na lafiyar yaron/ko yarinyar kawai". Huci mai azabar zafi ya khaleel yafuzar daga bakinsa, yarintse idanu da k'arfi yana dukan tebir d'in gaban doctor. . Please j ka kwantar da hankalinka, bawai inada tabbacin za'a haifi babien da dawata nakasabane, kawai hasashene". "Haba doctor yazakace haka? Karkayi k'ok'arin yimini yawo da hanakali akan abinda kakeda tabbas akansa, wlhy ko wanene wannan mai aika-aikar saiyayi nadamar shiga gonata........ Ganin yanda ya birkice sai baffah yajawoshi jikinsa, rungumesa yayi, jinsa ajikin mahaifinsa sai kawai yasaki kuka mai tsanani. Bubbuga bayansa baffah yashigayi, shikansa jiyake tamkar yay kukan saboda tausayin d'an nasa, amma saiya dake, yashiga k'arfafashi. " haba Mu'azzam kaifa namijine, kuma ma'aikaci mai kare rayukan al'umma, mizaisa ka karaya hakane?, karka bari abinda yafaru da matarka ya raunanaka, kamata yayi yak'ara maka karfin guywa, kowaye ya aikata wannan abun tabbas sanadin tonuwar asirinsane, kuma hakan yana nuna yadad'e yana cutar damu, yanzune ALLAH ya nuna mana hakan, banaso ka zargi mahaifiyarka, dan batada dalilin kasheku, sannan mutane dayawa sunci meatpia d'in, amma baimusu komaiba, wandama mamanka tabaku an bincikashi babu komai acikinsa, amma miyasa aka samu gubar ajikin Aysha?, kuma shine last Abu dataci ajiya?........" Zumbur ya khaleel yatashi daga jikin baffah, danya tuna masa abinda yamanta, kuma yakamata kowa yayi nazarin hakan awannan ga6ar, shikansa shaidane Aysha bataci komaiba jiya, daga rake sai wannan meatpia d'in, amma miyasa babu gubar acikinsa?, wannan lamari da d'aure kai gaskiya. Wayarsa yazaro, kiran wasu doctors yayi cikin ma'aikatansu, yasanar musu yana buk'ar ganinsu a General hospital yanzunan. Cikin girmamawa duk suka amsa, bai kuma sauraren bayanin doctor faisalba yatashi yafice. Daga doctor har baffah da kallo kawai suka bishi..... Harya kama handle d'in k'ofar zai fita doctor yace, "j!". Cak ya khaleel yatsaya amma bai juyoba, Dan allurar 'yan mazan tamotso. Doctor Faisal bai damuba yace, " please bamuson kowa yasan matarka nacikin k'oshin lfy, anunama kowa tana cikin halin k'ila wakala, inaga hakanne zai dakatar da masu harinta, kuma zai bamu damar aikinmu atsanake". Jinjina kansa kawai yayi batareda yace uffanba yafice. Baffah ya sauke ajiyar zuciya yana kallon doctor, "doctor ngd sosai, amma Dan ALLAH ak'ara bama yarinyar nan kulawa sosai". "Insha ALLAH alhaji, Na yanzunma kuskurene, bakuma zamu bari yasake faruwaba, kuma babu Wanda zai sake shiga d'akin datake kwance, dagani sai kai da Ibraheem". " masha ALLAH, hakan yayi". Baffah yabashi hannu sukayi musabaha yafito...........✍ *_wasu sun zata yau asiri zai Tonu kai tsaye ko?, ai idan hakan tafaru labari yasamu rauni kenan, kuma kanku saikunji babu dad'i, amma Ku k'ara hak'uri kam, Dan dolenen komai yafito fili awannan ga6ar, tunda Aysha tabasu bakin zaren, yanzunkam fad'an Na manyane🤣🤣._* *_masu had'a fitina tsakanin writers kuji tsoron ALLAH wlhy, karku d'auka hakan kamar k'aramin abune, kuji tsoron addu'ar Wanda aka zalinta, shin miye ribarku wajen cewa wasu na amfani da fasahar wasu?, wlhy idan kin had'a kinci riba yau, aranar gobe kiyama zakiyi Dana Sani, Dan ALLAH baya barin hak'in wani akan wani, kudaiji tsoron ALLAH, akwai mutuwa, akwai hisabi, duk Wanda yake k'irk'irar irin wad'annan fituntunun ya ALLAH kayi gaggawar tarwatsa al'amarinsa, kahanashi barci mai dad'i, kasaka bak'inciki da k'unci a zuciyarsa, ALLAH kamana maganin munafukain fili dana 6oye dake la6ewa abayan writers suna kunna musu wuta ameen._*😭🙏🏻 *_ALLAH ka gafarma mahaifina, da dukkan sauran musulmai baki d'aya.😭🙏🏻_* *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ *_Na gaisheki k'yauta Anty Ruk'ayya maikan doya🤭😉, saura kicigaba da gulmata nahanaki page🤫🤣😜_* 3⃣8⃣ Yana fita a can baya wani d'aki da doctors kanyi meeting yanufa bisa jagorancin Taheer, dukkan nurse's d'in da doctors anhad'asu awajen, shigarsu babu dad'ewa doctor Faisal ma yashigo. "Amma zaka ganeta j!?". "Zan iya ganeta insha ALLAH, saidai inbata nan". " d'aya bayan d'aya nurse ke tasowa mazansu da matansu, ya khaleel Na kallonsu, amma harsuka k'are babu komai kama da ita, sai wadda tashiga Na farko kawai, danhaka aka tsaidata ita. Bayan kammala dubawa babu ita aciki ya khaleel yamaida hankalinsa kan d'ayar nurse d'in, yayi masifar had'e fuska. yace, "k wace nurse ce tashiga bayanke? Nasan kin santa?". " wlhy yalla6ai ban Santaba, danni inagama dubata nafita kuma duk kuna tsaye, saida nasanarma doctor cewa barci takeyi, amma wlhy bansan wacece takoma d'akinba bayan fitata". Ran ya khaleel bak'aramin 6ace yakeba, ya maida hankalinsa akan doctor Faisal. "Doctor tabbas kowacce wadda ta aikata tana cikin ma'aikatan asibitinnan, dan haka nikoma wacece nabada awa 50 kacal anemomin ita". Yajuya yafice daga d'akin. Kowa da kallo yabishi, tabbas kowa yasan yau ma'aikatan asibitinnan sunshiga tarkon khaleel saidai ALLAH. Dayake su Anty Mamie ma duksun ganta, dole saidaisu aka cigaba da duba har masu shara da goge-goge, tunda abune Na laifi, cikinsuma za'a iya samu. Khaleel kam yama bar asibitin shida doctors d'insu nawajen aiki, su doctor Abraham, amma saida yakuma saka tsaro mai tsauri azagayen d'akin da Aysha ke kwance sannan suka tafi. Gidansu sukaje, su Ammah duk suna harabar gidan, shirin tafiya asibitin sukeyi saiga motarsu khaleel, dakatawa sukayi harya fito. Suduka babu wanda bai tsorata da yanayin khaleel ba, har Ammah, Dan sunsan idan yana cikin irin wannan Fushin komaima zai iya faruwa, sannan komin kusancinka dashi bazai d'aga maka k'afaba, kuskure k'ad'an wani zaimasa yaci dukan banza. Babu Wanda ya isheshi kallo acikinsu yaja zugarsa suka wuce 6angarensa. Afili Ammah tace, " lallai gidannan gab yake da kamawa da wuta, tabbas inaji ajikina akwai gagarumin Abu dazai faru". Kowa kallonsa ya maida kanta, amma batasake furta komaiba, kujera tanema ta zauna. Suma duk sai suka nemi wajen zaman. Su khaleel suna shiga yace, bincike mai k'yau nakeso, Dan tabbas akwai abinda bamu saniba, ajiya A'eesha bataci wani abuba agidannan, kowa ya shaida haka, amma dai ina zuwa. Waya yaciro yakira Ammah, babu dad'ewa saigata tazo. Suna zazzaune, itama saita nemi waje ta zauna. khaleel yace, "Ammah kamar yanda bincike ya nuna a 6angarenki Aysha take kwana, kuma kinfi kowa Sanin dukkan wani motsi akanta, shin jiya ko taci wani abinci kafin meatpia?". Ganin yanda khaleel keyin magana ya tabbatarma Ammah ba fagen wasa ko sanayya akeba, yana fagen aikinsane, danhaka itama taci Serious. " tabbas yalla6ai a 6angarena Aysha take, kuma saboda juna biyu datake dashi bakomaine takeciba, wanima idan taci amai takeyi, ajiya bataci wani abuba, idanma ban mantaba da rake ta karya, kuma har kaje kataho da ita bataci wani abuba a 6angarena, ban saniba ko zuwanku anan d'in taci". "Anan ma bataci komaiba, koda mukazoma barci tayi, sai around 1 tatashi, meat pia ne kawai nasan ankawo taci, shima gutsura d'aya kacal tamasa, bama ta had'iyaba, ta furzar dashi. Kamar yanda doctor Faisal yace k'arfin gubar yana fara aikine cikin mintuna 20 kacal ajikin Wanda yaci, daga barinmu nan zuwa 6angarenki zaikai minti ashirin kafin A'eesha ta suma. Abinda Yakuma d'aure kammu shine, babu wata guba ajikin meatpia d'in Dana kwashe atsakar d'akinnan, Wanda A'eesha tazubar, kuma acikinsane taci. Wannan shine yarud'ar damu, akan son Sanin mi A'eesha taci?". Dr Abraham yace, " sir, inabuk'ar ganin raken datasha". Da hannu khaleel ya nunu masa ledar rake da fleet dasuke a falon, Wanda suna nan Inda suka barsu tun a jiya. ''Yauwa, kozamu iya ganin inda aka 6arar da meatpia d'in?". Nanma Kansa ya jinjina musu, yamik'e suka bishi baya, harda Ammah. 'Dakimsa da abin yafaru sukaje. Tangaran d'in d'aya fashe yana nan, Dan khaleel meatpia d'in kawai yatsince yabar fasashshen kwanon. Wata Na'ura suka saka, wasu Na haskawa, Dr Abraham kuma nasaka wani d'an tsinke, kusan mintuna 7 Dr Abraham yace kozamu sami ruwa?". Ammah Ce tafita da Sauri, babu dad'ewa saigata tadawo da ruwa. K'ar6a Dr Abraham yayi ya yayyafa awajen daduk suke zaton meatpia d'in yazuba, sannan yasaka wani Abu kamar sirinji yazuk'e ruwan, aka tattara fasashen kwaonon aka zuba a Leda, d'an lallek'awa sukayi kozasuga koda wani guntun meatpia ne ad'akin, amma basu ganiba kuwa, sai can wani acikinsu yatsinto wani d'an mitsit a akusada wardrobe, shima da Alama dije bata Ganshi baneba, dukda dai k'ank'antarsa takai akasa ganinsa musamman idan mutum ba'a cikin nutsuwa yakeba. 'Daukarsa sukayi suka saka awata Leda aka d'aure.. Yo bandama dai binciken tsiya irinna ma'aikaci mizasuyi da wannan 6allin abun, saikacefa yaro mai k'yuya yabaka Abu da k'yar😂, gaba d'ayafa baifi Girman wannan gyad'arba👉🏻 (🥔). Amma haka suka d'auka Dan zai iya Zame musu wani madubin dubawa. Daga Nan fitowa sukayi, raken fleet Dana ledama Duk suka d'auka aka tafi dashi. Asibiti suka koma, suma su Ammah asibitin suka tafi. Sai lokacin Ammah taji cewar ankuma zuwa har Inda Aysha take kwance anbata gubane. Kutt Amman iya bala'i kuma, aikam tashiga zazzaga masifa asibitinnan, catake ALLAH ka tona asirin kowanne tsinanne ke keson kashemin jikata, ALLAH katona asirin matsiyaci. Bak'aramar sukan zuciyar Momy adu'ar ammah keyiba, jin Adu'arnan take tamkar tana k'onata da garwashin wutane, Dana tun d'azun arikice take, tarasa hanyar dazata bar asibitin, Dan tafa kula kwa6arsu zatayi ruwa, sotake taje su tattauna plan F, kafin agano yanda Aysha taci guba dakuma wadda aka bata, dije takirata tasanar mata su khaleel sunje gida dawasu doctors kuma taga bincikene Na bin kwakwkwafin tsiya sukeyi, ALLAH ma yasota sanda dije takira wayar tata tasami k'arfin dakewa kamar babu komai ta amsa mata, bama zaka ta6a zargin dawani take wayaba, saboda iyafis dake kunnenta, sauraren dije kawai tayi, amma batace uffanba. ********* Su doctor Abraham sun kar6i dukkan bayanan hannun su doctor Faisal, suka tattara suka koma setetion d'insu, harda ita Ayshan, wadda aka d'auka kashir6an tamkar mara rai, babu Wanda baimata kukaba a 'yan gidan kuwa, duk da basusan barcine takeba, dansu anfad'a musu har yanzu tana cikin damuwa. Khaleel yace, "baffa yakamata duk Ku koma gida, yanzun mundawo da case d'in hannunmu, sannan kukula sosai, Dan yanzun koma wanene zai iya d'aukar kowanne irin mataki". Jinjina kai baffah yayi yana murmishi, yadafa kafad'ar khaleel yana fad'in " haka nakeso kadawo jaruminka, banason karikice kazama mai rauni, dan sun cutar da itane dama dansu raunana zuciyarka, ka karaya gaba d'aya, nikuma sonake hakan yazama allurar k'arin k'aimi suka maka yarona, ALLAH yabada nasara, ya kareminku baki d'aya, kaje, karkayi sanya, ka tabbatar kakama azzalumai Ibraheem!!! ". Karo Na farko dakowa yaji wannan sunan abakin baffah, kuma yanda yay maganar saida kowa ya tsorata, Dan cikin daka tsawa furicin k'arshe yafita daga bakin baffan. Kowama awajen da addu'ar samun nasara yabisu, dakuma tasamun lafiya ga Aysha, Momy ma ta daure tayi, amma dukkan mai hankali ya kalleta yasan bata cikin nutsuwa, su Taheer kuma duksun lura da haka, amma basuce komaiba, Dan basu ta6a kawo zarginsu akan Momy ba, tunda sunsan mahaifiyar Khaleel Ce. Amma Samuel yad'auki alk'awarin bin kwakwkwafin Momy, Dan tund'azun duk wani motsinta akan idonsane, haka kawai yaji zuciyarsa bata amince da itaba, yana kuma kallon sanda take waya, dukda batayi maganaba wasu alamomi sun nunata. Koda suka tafi shidasu khaleel shi dawowa baya yayi. Cikin dabara yaytabin moticin gidansu khaleel abaya, wani guri nesa dagidan yasamu ya zauna, ya tabbatar inhar Momy batada gaskiya saita fito daga gidan. __ __ 👁 👁 👃🏼 . 👄 Nima ina nan sainaga fitowar hajia babba😉🤣😜. __________________ Yinin yau zumbur su khaleel basu hutaba, dukkan wata kulawa ta musamman kuma Aysha tana samunta, lokaci-lokaci ya khaleel kanje d'akin datake kwance Wanda keda fasifar tsaro ya dubata. ***** Sam.... Kuwa sarkin naci yana nan la6e har kusan bayan magriba😂. Harya fara hasashen Barin wajen saiga wata tafito daga gidan su khaleel, cikin dogon hijjab da Nik'af. Su Samuel sunsan kan aiki sosai, aikam baiyi k'asa aguywaba wajen bin matarnan, saida sukayi nisa da layin tatare taxi tashiga, shima tarewa yayi yashiga, adabara sukebinsu, har zuwa anguwar su hajia khaltum. Sam....yagane gidan hajia khaltum, Dan shine yasato sakeena lokacin. Da sauri ya sallami mai taxi, wayarsa yad'auka yakira number sakina, danya kar6i number d'inta alokacin, kuma ta tabbatar masa babu wanda yasan tanada waya agidan. Saida takusa tsinkewa tad'aga, murya k'asa-k'asa tace, "yalla6ai wlhy kad'an yarage akamani, ina wajen bama bak'uwar hajia ruwa kakirani". "Yauwa, wace bak'uwace". " hajia Laurah maman yalla6ai khaleel". "Da gaske?". " ALLAH kuwa". ''Yauwa Sakina, kisaka musu ido, idanma da dama kiyi recording d'in dukkan wata hira dazasu kituromin, ki kula sosai". "To shikenan, dama nazo had'a mata kunune, kuma nagama, zansan yanda zanyi Na ajiye wayar a d'akin idan nashiga". "Yauwa, saina jiki". ** Sakina tayi duk dabarar dazatayi ta ajiye wayar, bayan ta danna record, tabaro d'akin. Su hajia khaltum basusan mike faruwaba suka baje faifan hira kuwa, sosai suka tattauna akan abinda yafaru yau, dakuma meeting dazasuyi Na k'ungiya gobe, kuma duk akan su khaleel ne.. Itako waya babu ruwanta, tanata nad'e komai. Sai wajen around 11 hajia babba tabar gidan, driver zai maidata gida. Hajia khaltum tatafi rakata sakina tayi wufff tashige d'akin, ta d'auke waya ta 6oye bayan tayi hanzarin saving d'in recording d'inta. Tana k'ok'arin fitowa sukaci karo da hajia khaltum, kallon tuhuma Tamata, Dan babu wani d'an aiki da hajia khaltum ta yarda dashi agidan. " k miya shigo dake d'akinane?". "Wlhy babu komai hajia, nazo tartare kayan dakukayi amfani dasune, saboda zanyi wanke-wanke". " shine kuma bazaki jira nakiraki ki d'aukaba, Kodai la6e kikaimin?". "A'a Ammi, nicefa natasotama yanzu tana barci wlhy". Babie Ce mai maganar tana fitowa daga d'akinta. Shiru hajia khaltum tayi tana kallon babie, dawannan Damar sakina tazare jikinta tabar wajen, dama zuciyarta sai dukan 100-100 takeyi. Saida tagama wanke-wanken sannan tashiga toilet d'in d'akinsu Na 'yan aiki ta turama Samuel record d'in. Shikuma adaren yaturama Taheer. Bak'aramin tashin hankali Taheer yashigaba, dan lamarin ya rikitashi, mahaifiyar mutum mai gaskiya da sanin darajar aiiki takasance cikin manyan criminals da suka gagari k'asa, wannan wace irin rayuwace?. Shiyanzu yaza'ayi ya tunkari j da wannan batun?, kuma aii dolene yasan komai dangane da operation d'in, tunda bak'aramin aiki baneba. Hakadai yayta k'ullawa da kwancewa, daya kasa hak'uri saiya kira youseef da Joseph ya shaida musu, sumafa zancen ya firgitasu ainun, sukaita tattauna yanda zasu 6ullowa lamarin, aganinsuma gara khaleel d'in yakamata dakansa akan su sukamata. Sundai yanke shawarar sanar masa tawata sigar, amma ba gaba da gaba ba. ******* A setetion khaleel yakwana yau, haka suma su Doctor Abraham sunata aikinsu. *_Monday morning_* Ranar litinin misalin k'arfe 9am khaleel yazo gida a gaggauce yay wanka yakoma setetion d'insu, babuma wanda yasan yazo gidan, harya fice. Dama tunjiya babu walwala ga kowa, tamkar anyi mutuwa haka gidan yake, kuma kowa kwana yayi gaban ubangiji yanda mik'a kukansa akan wannan Matsala data tunkarosu. Masu aiki wasu sunfita, wasu kuma sunata shiri, hakama masu zuwa makaranta. Hajia babba tana cikin wad'anda suka fita. Khaleel Na dawowa office yawuce kawai, zamansa dakamar mintuna 27, saiga Dr Abraham, izinin shigowa yabasa. Dr Abraham yashigo, yay salute d'in khaleel sannan yabashi damar zama. "Sir! Tabbas bincikenmu ya nuna Madam taci guba da farko, kamar yanda likitocin General hospital suka tabbatar, kuma taci abinne da mintuna 19 kacal yafa aiki ajikinta, saboda kad'an dataci yahana gubar k'arfinsa tasiri ajikinta, munduba raken da'akace tasha kafin meatpia babu komai acikinsa, kuma tsakanin shan raken dacin meatpia yad'auketa awanni 5 dawasu mintuna, sannan meatpia d'in da sauran mutanene gidan sukaci babu guba aciki, hakama Wanda ka kwashe bayan madam ta 6arar babu gubar". " Amma gurinda meatpia d'in ya6are muka zuba ruwa tareda zuk'ewa ya nuna anan akwai guba, ('Yar zabura khaleel yayi, amma baice komaiba), Dr Abraham yacigaba dafad'in " dalilin dayasa muka gane gubar shine, akwai 6ar6ashin meatpia d'in awaken, Wanda ruwan damuka zuba ya narkar dashi har muka sami damar gane akwai guba. akwai kuma wani guntun damuka samu gabda zamu baro d'akin shima akwai guba aciki. Sannan kwanon shima maik'on mai daya manne ajiki yanuna akwai guba". "Tabbas abinda nalura dashi Annan shine bayan madam ta 6arar da meatpia d'in, inhar kunbar d'akin to wani yazo yakwashe meatpia mai guba, ya canja damara gubar, Dan kenan wanda mutanene gidan sukaci shi babu guba aciki, Wanda madam tacine kawai mai guba". " abin kuma mamaki Na uku shine gubar dake cikin meatpia d'in irintace aka bama David yasha aruwa.......... Babu shiri khaleel yamik'e tsaye tsaye, "doctor ka tabbatar hakane?". " yes sir!, babu kokwanto a cikin aikina, ga dukkan bayanan Na tattara a file d'innan Kaduba kuma, harda Na David ma nasaka maka duk da nasan kanadashi". Gyad'a kai khaleel yayi, shikuma doctor Abraham yafice. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai khaleel yake Ambata, kenan da gaske momyce tabada guba da hannunta dansuci? To Aysha tabamawa koko shi? Yasan Momy batason Aysha, amma baikawo zata iya yunk'urin kashetaba, to mima yasaka gubar tazama dai-dai da wadda Akabama David?. Komawa yayi yazauna, yana duba file d'in da dukkan bayanan ciki. Kusan awa 1 ya d'aukeshi. Saiga Samuel yayi nock d'in door. Izinin shigowa yabashi. Bayan ya k'ame tareda salute Na khaleel yabashi izinin zama. "Samuel yadai?, komun samu wani abunne?". " yes sir, mai muhimmancima kuwa, akwai wani meeting d'in sirri daza'ayi yau, kuma harda matarnan hajia khaltum wadda taturama barau modibbi sak'o aciki". " Masha ALLAH, a ina kenan Sam...?". "Ga dukkan bayanan inda taron zai gudana annan, nima nasamu bayananne a majiya mai k'arfi, tun sanda kabani aikin bibiyar hajia khaltum banyi k'asa aguywaba". " da k'yau sam..... Da irinku Muke alfahari a hukumarnan". 'Yar dariya Samuel yayi, yace, "aii tarbiyyarkace sir". Khaleel baice komaiba, yafara duba bayanan. Sosai yayi farinciki, duk da kwakwalwarsa da tunaninsa suna cikin wani yanayi, amma hakan bazai hanashi fuskantar wannan aikinba shima, tabbas yana kammalawa dashi zai maida hankalinsa kacokan akan Momy, daduk wani mahaluki dake gidansu. Nace hummm, khaleel kenan, kwantarma da hankalinka, ALLAH ya sauk'ak'a maka.🤪. __________________ *_4:30pm_* *_IDAN KERE NA YAWO🏒, ZOMO NA YAWO🐇, dolene wata rana agamu🏒🐇🤣🤣._* Su khaleel sungama shiryawa tsaf, anyima bindugu saves da bullet, hakama handcuffs and'iba dayawa. Motoci kusan 7 aka d'ibi ma'aikata aciki, amma duk sai suka rarrabu, ko'a cikin setetion d'in bakowa yasan inda zasujeba, saboda tsaro, amintattunsune kawai aka d'iba. Nesa dawajen taron suka ajiye motocin. Duk sanye suke cikin Uniform d'in aiki, babu mai fuskar rahama acikinsu kuwa. Cikin hikima suka sami wajajen mak'alk'alewa, Dan wajen meeting d'in cike yake da tsaron 'yan ta'addah. Tsitt d'akin meeting d'in yake, su Momy duksun nutsu suna sauraren jawabin shugaban k'ungiyarsu............✍ To yaudai kam, zamuce k'arshen tika-tika tik, masoyan hajia babba sainace amin afuwa, dominfa gobe itace ranar bankad'ar sirrikan 6oye, ranar bayyanar abubuwan mamaki, Wanda bakowama yayi zaton hakanba, mutane dayawa dazasu bayyana muku ta sigogi da dama👁. Tabbas akwai abubuwan mamaki, al'ajabi. Nikaina bilynku nak'agara gobe tayi aradu🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀😂😂. Happy day fan's *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ *_ASSALAMU ALAIKUM MASOYANA!!_* _Awannan ga6ar kam zan baku hak'uri, amin afuwa sosai, nasan wasu basajin dad'in yanda sukemin comments a groups amma bana magana, wlhy abubuwan yawa sukemin, zaka kula da Oga da safe, kafin yafita, yana fita aikin gyare-gyare zakayi, sannan nafita islamiyya, nadawo 12, wlhy ina dawowa typing kawai nake zaman yimuku, wahalar typing takan d'aukemu lokaci mai tsawo, saboda abune Na nazari, wani lokacinma saikin kusa gama page kiji baiyiba, ki goge kiyi wani kuma, kunga kafin mutum yagama kansa yad'auki zafi, sauri kake kagama ka fuskanci aikin gida kuma, wani lokacin kiyi bak'i, ko fita takamaki kekanki, ALLAH akullum ina gamo da messages Na PC samada 150, rasama ta ina zan fara nakeyi, gakuma Na groups, groups yakai 40 wanda nake a ciki, wasu kunyarsu take hanani fita kawai wlhy, lokacin dazan gama typing kaina yad'auki zafi sosai, saina dingajin gandan duba sakwannin PC, amma dankarkuga kamar inamuku wulak'anci nake daurewa naduba, shiyyasa nake d'auke idona ana groups, amma wlhy inajin dad'i sosai, kuna sakani farinciki ainun, badankuba banga amfanin rubutubba, tunda bazan rubuta danna karanta nikad'aiba, duk inda masoyina yake nima ina matuk'ar sonsa da alfahari dashi, babu abinda zance daku saidai ALLAH yabar zuminci, k'aunarkuce ke sakani wajen 6ata lokacin yin typing kullum da siyen data, I love you so much my fans, babu marubucin dabaison masoyinsa, duk muna k'aunarku wlhy💋💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤❤❤._ Amin afuwa please, kuna raina wlhy👁💘. 3⃣9⃣ Su khaleel sunada yawa sosai, amma dukda haka su hajia babba sunfisu yawa, danma ankama wasu aciki, sauk'in d'ayane bakowa keda makami acikinsuba. Dukda jikin ya khaleel a sanyaye yake, kuma baisan daliliba, amma hakan baihanashi aro jarumtaba ta musamman ya k'arfafawa kansaba, daboda gudun Matsala. Acikin kwarewar aiki suke shiga wajajen, duk wanda akayi karo dashi kuwa cikin dabarar aiki suke gamawa dashi, basuda mafitar data wuce kashesu, saboda suma suna samunsu kashesun zasuyi tunda akwai nakamai a hannunsu. Bawai k'aramar k'ungiya baceba, k'ungiyace data tara manyan mutane, masu muk'amai kala-kala, ga dukiya sun tara, saboda business kala-kala dake gudana cikin k'ungiyar, kuma Na manyan kud'i. Karya wuyan wani da khaleel yayi bayan nannad'e kansa aleda yasakani rintse idanu, sosai tsoro yashigeni, danganin yanda zukatansu khaleel suka gama bushewa, basajin komai wajen kisan garatan nan. Matsalar da aka samu shine cctv camera dake aiki acikin d'akin taron, wadda su khaleel basusan da itaba. Wad'anda suke kulada cctv camera d'inne suka ankarar da 'yan k'ungiyar. Tashin hankali kenan, wai Wanda ba'a saka masa rana, kusan shekaru 29 k'ungiyar Na aikinta. Amma basu ta6a gamo da makamancin tashin hankalinnanba, saidai amusu tsinci d'ai-d'ai badai gaba-da gababa, don ko kad'an basu aminta wani yafidda sirrinsuba, komai cikin ilimi ake yinsa. Hargitsewa hall d'in yayi, masu makamai suka fara d'ana kunamin bindugu, irinsu Momy kam sai neman wajen 6uya. Musayar wutane yafara gudana a tsakaninsu, bakajin komai sai k'arar harbe-harbe. 'Yan jarida kam dasu khaleel sukazo dasu sai d'auka sukeyi, lamarin kaikace film ne wlhy. Shirin ma'aikaci da d'an ta'adda bazaizo d'ayaba, dukda gawurtar k'ungiyar su hajia babba takai taringa bama matasa training saboda gudun zuwan rana irin wannan ta kota kwana. Tiyagas su khaleel suka fara jefawa cikin hall d'in, dama su sun d'auki matakan kare kai, dandanan wajen yakacame da tari da atshawa, gashi hayak'in yana saka hawaye, masu ciwon asma kuwa saidai addu'a kawai. Jefa tiyagas yaba su khaleel damar shiga hall d'in, dukda haka akwai masu taurin zuciya dake harbi har yanzun. Amma haka su khaleel sunata samun nasarar cafke wasu, Dan k'ungiyar ta tara maza da matane, harda wad'anda tunaninka bazai ta6a kawo maka ganinsuba awajen, saboda Girman milki ko dukiya. Akwai k'ofofin fita da dama acikin hall d'in, wannan ne yabama wasu dama sulalewa, amma ina, wannan shine angudu ba'a tsiraba, dankuwa cikinsu khaleel wasu sun bisu. Acikin masu guduwa kuwa harda hajia khaltum da hajia babba. Lamarifa yaci tura, komai yagama hargitsewa, acikinsu khaleel dayawa sun sami harbi, 'yan k'ungiyar kam ba'a magana, bayan wad'anda aka antaya barzahu akwai masu harbi a sassa daban-daban. Kusan awanni 3 aka d'auka ana Abu d'aya, lamarin kamarma bazai k'areba, kowa yafita hayyacinsa, Dan babu Wanda baiji jikiba, ansami cafke mafi yawa acikinsu, wad'anda suka samu raunuka akafiddosu waje, gawawwakinma haka duk an fiddosu, wad'anda suke k'alau kuwa handcuff aka saka musu, duk aka fito dasu waje, 'yan jarida sunata aikinsu. Ya khaleel yafara bin ma'aikatansu yana dubawa, Dan a tantance wad'anda suka mutu, dakuma rauni, duk a wahalce suke. Khalee yace, "amma akwai wad'anda babu acikinmu?". ''yes Sir! Wasu sunyi yunk'urin guduwane, shine suka bisu". "OK!, yakamata azuba wad'annan amotocin da aka kawo, suma akirasu aji?". " OK sir". Wad'anda basa wajen aka shiga kira, wasu suce sun kamasu, wasukuma suce sunadai binsu binsu abaya har yanzu, amma suna buk'atar k'arin ma'aikata. Taheer dai cayayi ahad'ashi da khaleel. Faruk yamik'ama khaleel wayan cikin girmamawa. A kunne yakara batareda yayi maganaba, daga can Taheer yace, "sorry sir idan bazaka damuba kazo da kanka, wasu mutane hud'u sun shiga gidanka, bazai yuwu mushiga babu izininkaba". " gidana kuma Taheer?". "Yes sir?". ''OK ina zuwa, kubani k'ank'anin lokaci". Saida khaleel ya tabbatar anzuba sauran a mota, wad'anda suke buk'atar k'arin ma'aikata aka tura musu, wasu kuma suka tafi da motocin wad'anda aka kama, ma'aikatasu kam tuni anyi gaba dasu Dan basu taimakon gaggawa. Ya khaleel kansa yasamu raunuka, amma bai damu da kansaba, Na k'asa dashi kawai yake son abama kulawa. Key d'in mashin yakar6a ahannun wani ma'aikacinsu, yanufi gida zuciyarsa Na dukan 100-100 saboda fargabar abinda zai Tatar, kenan zarginsa yazama gaskiya, acikin gidansu akwai mai mu'amullah da k'ungiyar? jiyake tamkar zuciyarsa Zata kama da wuta saboda bak'in ciki da fargabar wanda zai tarar amazaunin d'an k'ungiyar. Ak'ofar gida yay gamo dasu Taheer dake tsaitsaye, basu shiga gidanba, saboda girmama ogansu. Bai tsaya garesuba, horn kawai yayi d'an gwari yabud'e masa gate yashige da mashin d'in, suna su Taheer duk sai suka shiga. Tunda su hajia babba suka sami nasarar baro hall d'in kaitsaye nan gida suka nufo afirgice, sunyi imani da cewar idan anan gidan suka fake khaleel bazai ta6a kawosu aransaba, tunda bai gansuba, amma hajia babba da idanunta taga khaleel. Babu Wanda yasan sun shigo gidan, sai mutane kh'alilan, gaba d'ayansu arud'e suke, hajia babba kuka takeyi da idanunta, takasa zaune takasa tsaye, khaltum kam ba'a magana, dama kunsanta afagen tsoro, sai mutum biyu dasuka gudo tare, suma duk matane, d'ayama budurwace, d'ayar kam zata iya zama sa'ar khaleel. Ko kafe mashin d'in baiyiba yasakeshi anan, sai cikinsu Taheer ne wani yagyara farking d'in mashin d'in. Taheer ya nuna masa motar dasu hajia babba sukazo, khaleel baisan motarba, Dan bata gidan baceba, saikace mayunwacin zaki haka yanufi d'an gwari datun shigowar su khaleel yake arud'e, Dan yasan tabbas babu lfy yau agidannan, cikin daka tsawa khaleel ke tambayarsa waye yashigo da motarnan gidannan?!!. Hargowar khaleel ce tafara jawo hankalin mutanenen gida, suka fara fitowa d'ai-d'ai. Jikin d'an gwari rawa yakamayi, Dan yasan yau babu wargi ga khaleel, dama can bawasa yakeyi dawani acikinsuba, har taune harshe yakeyi wajen magana saboda tsoro, yace, "wasune, amma suna can ciki". Shigewa khaleel yayi cikin babban falon gidan, Wanda zai iya sadaka dakowanne part Na masu gidan, hankalin kowa yatashi agidan, Dan sunsan yau khaleel amatsayin ma'aikaci yazo musu ba d'an gidaba. Kowa yafito amma banda Momy, yagama binsu d'aya bayan d'aya da kallo, kad'anne daga cikinsu babu, kuma yarane, yace, " suwaye suka shigo gidannan awa 1:30 dasuka wuce?!!". Yanda yay maganar dolene katsorata komin kusancinka dashi. Hafiz ne yay namijin k'ok'arin fad'in driver yad'akko su Adeel daga school, sannan nima da ya muhseen yanzu muka shigo". "Saiwa kuma!!?". Umme Amarya tace, " nima bandad'e da shigiwaba, kusan tare kuma muka shigo da hajia babba". Arikice ya kalli ummi amarya, "umme acikinku wanene mai farar mota?". " hajia babba ce sukazo da ita, inaga motar bak'intace". Wani irin huci mai azabar zafi khaleel yafesar, kansafa yafara juyawa, akid'ime yanufi part d'in Momy, dak'afa yadaki k'ofar, amma yajita a kulle, kuma dukanta yayi, nanma ko gezau. Dukan k'ofarne ya farkar dasu Momy halin da ake ciki, hajia khaltum tace shikenan laura, dabararki bataciba, matsiyacin yaronnan yabiyomu. Dukda baffah hankalinsa atashe yake, baihana dakatar da khaleel ba daga dukan k'ofar, 6angarensa Yakoma yad'akko wani key d'in yabashi, Khaleel yakar6a yabud'e k'ofar. A tsaitsaye yatadda su Momy, yana shigowa Momy ta nunasa da bindiga, wlhy Ibraheem kana matsowa saina harbeka. Mutuwar tsaye khaleel yayi, kallon Momy kawai yakeyi abirkice, kansa yafara juya masa, Dan harya fara ganinsu dishi-dishi, tafiya yarink'ayi da baya-baya yana hawaye, harya fito babban falo inda kowa yake atsaye, harsu Taheer. Kowa zare idanu yayi danganin Momy nabin khaleel dake tafiya da baya-baya da bindiga. Atsawace tace, "ka ajiye bindigar hannunka kona harbeka". Sakin bindigar khaleel yayi yana hawaye, sannan yana nuna Momy da d'anyatsa d'aya, bakinsa yakasa furta komai, dukda d'unbin magana dake cikinsa. Ammah tafara sallalami tana tafa hannaye, laure!! Dama ke 'Yar fashi da makamice? Yo inba d'an fashiba wake rik'e bindiga shiba ma'aikacib.......... Ammah batakai k'arshen maganarba sukaji k'arar harbi da ihun Ammah lokaci d'aya. Momy ta harbeta ak'afa, tana fad'in "bara Na tabbatar miki hakan tsohuwar banza, aiduk kece sanadin komai". Tsoro kama kowa yayi afalon, amma banda baffah, khaleel kam akid'ime yake, kwakwalwarsa tsaye take cak ta daina aiki, bashida maraba da gunkin tsakkiyar hanya. Tabaya Aleeya ta daki k'afar Momy, saigata tazube ak'asa, bindigar tafad'i gefe, Auwal yay saurin d'auka. Kallon mamaki kowa kema Aleeya, Dan basuyi zatoba, itako ko'a jikinta. Ita kanta momyn baki bud'e take kallon Aleeya, dukda azabar zugi da k'arta keyi, cikin rawar baki tace, " Aleeya! Nikika daka? Ina matsayin wadda zaki auri d'anta". Wani murmishin k'asaita Aleeya tasaki, tafara tafa hannaye tana zagaye momy. "Hajia laurah, hajia laurah!, Aleeya bata shigo gidannan domin auren d'ankiba, nashigo gidannan domin yin aiki, aztonki kinsamo wadda zata taimaka miki wajen tarwatsa rayuwar Wanda kikeyin amfani dashi dason tara abin duniya, nasan bakisan darajar khaleel ba, tunda bakece kikayi wahalar rainon cikinsaba da nak'udarsa, shiyyasa kikaita yunk'urin kasheshi da wahalar da rayuwarsa........ Kowa afalon idonsa awaje yake, wasu tuni ruwansu yakai 180 saboda rud'ewar furicin Aleeya..... Ammah dake zaune mama Na rik'e da ita, sai zufa takeyi saboda harbinta da Momy tayi ak'afa, cikin karfin hali tace, ''ke 'yarnan mikike son fad'ane haka?". Murmishi Aleeya tayi tana kallon mama, hajia fad'ima lokaci yayi dazaki fasa kawai, lokaci yayi dakowa zaisan sirrin 6oye, lokaci yayi da khaleel zaisan mahaifiyarsa ta asali agidannan, lokaci yayi baffah zaisan komai, 6oye-6oye yak'are, dama burinmu bai wuce khaleel yakama Hajia laurah dumu-dumu da laifiba, to Alhmdllh, dakon shekaru 37 dakikayi kina rik'e wannan sirrin yakamata ayau ki fesar dashi kowa yasani, kodan khaleel yasan kansa shima, yakuma samu farin ciki irinna kowanne d'a aduniya. Kowa afalon kallonsa yadawo kan mama, dake k'ok'arin kwantar da Ammah, "a'a fad'ima barni azaune, aini abinda kefaruwama yahanani jin zafin yanzun". Kai jama'a, dakyarfa Ammah ke magana wlhy, amma bakinta yak'i mutuwa😂. Mik'ewa Mama tayi tana takawa ahankali cikin falon, gaban Anty Mamie taje tatsaya, ta had'e hannayenta waje d'aya alamar rok'o, Bilkeesu ki gafarceni, kikuma fahimceni, batajira amsartaba takoma gaban baffah, kaima kamin gafara Alhaji, kakuma fahimceni, banida za6i sainayin hakan, shima bata jira cewarsaba takoma inda khaleel yake uwa butun butumi, hannunsa takamo tarik'e, idonsa akanta, itama kallonsa takeyi, kayi hak'uri yarona, nayi hakane saboda nema maka kariya, idan bahakan nayiba nasan kasheka zasuyi, shiyyasa naza6i rik'e maganar araina har takawo yanzun, amma ban bartaba saida Na tabbatar kana zagaye daduk wani kulawata, had'eda kwakwkwaran bincike domin tabbatar da gaskiya yanda kowa zai fahimceni aranar dazan bankad'a komai". Ya khaleel bai iya cemata komaiba, saidai kwayoyin razanannun idanunsa masu kamada Na jan gauta daya zuba mata, badamuba taja da baya gaban Momy da hajia khaltum da'aka gurfanar ak'asa, bayan Taheer duk yasaka musu handcuff ahannu. Kukuma inason Ku maida tunaninku baya, shekaru 37 zuwa baya dasuka wuce". Harara hajia khaltum tazubama mama, momy kam rok'on mama tafarayi, please fad'ima kibar zancennan, narok'eki, zan biyaki konawa kike buk'ata, bank'i kowanne sirrina yafitoba amma banda wannan sirrin...... Baki isaba laurah, bakida kud'in dazaki biyani, ko a baya ba tsoronkine yasakani shiruba, bakuma biyana kukayiba, nayi hakane saboda yak'inin Ibrahim zai kwato mana 'yancinmu agurinki wata rana, Dan nasan ubangiji bazai ta6a barin azzalumi nasaraba, nasan CIKI DA GASKIYA, wuk'a bata hudashi. *_WANI LOKACI MAI NISAN ZANGO😢_* Bayan aurena da Alhaji Abdallah rashin zaman lafiyarmune nida laurah yasakashi auro Bilkisu, dukda kasancewar Bilkeesu k'arama acikinmu hakan bai canja komaiba, saima dad'a hargitsewa da komai yayi. Cikina yazube har karo biyu dukmun d'auka tsautsayine, hankalina bai fara karkata akan hajia laurah ba sai lokacin dasuka haihu tareda Bilkeesu, ALLAH ya jarabcesu da nak'uda rana d'aya, amma laurah tariga Bilkisu. Kuma tarigatama haihuwa, saidai k'in fad'a mana abinda laura ta haifa k'awarta khaltum tayi gatanan da ranta, har saida Bilkisu ta haihu. Kafin afad'a mana abinda Bilkeesu ta haifa doctor yabuk'aci kayan haihuwa, da ruwa dawasu magunguna daza'a sakama Bilkeesu. Ammah idan baki mantaba, kekad'ai muka bari, Alhaji yatafi d'aukar kaya damuka manto, nikuma natafi pharmacy d'in cikin asibitin, rabon inzo inga abinda ke faruwa Na yarda 'Yar takardar da doctor yabani, dawo nayi ina dubawa har k'ofar d'akin, ammah tarigada tajuyama d'akin baya shiyyasa bazata san mike faruwaba, naduk'a Na d'auki 'Yar takardar dana gani, d'ogowar dazanyi sainaga doctor shida wata nurse da khaltum sunfito da baby daga d'akin da Bilkisu ta haihu, suka shiga d'akin da laura take, da sauri Na afka d'akin, babu baby gaban Bilkeesu, itakuma tanata barcima, ina niyyar fita na fad'ama Ammah saiga nurse d'innan tadawo da da babyn ta kwantar gaban Bilkisu, jinayi hankalina bai kwantaba, amma nakasa cewa komai, gudun karyazam zargi nayi. Fita nayi ina sak'e-sak'e harna Sayo maganin nadawo, natarar Alhaji yadawo, yana rungume da jaririya yana hawaye. Tambayarsa nayi miya faru?, shine ya sashaidamin babyn Bilkisu batazo daraiba, hajia laurah kuma tahaifi namiji. Tun anan nasan tabbas zargina gaskiyane, su laurah sun canja yaranne. Amma bance komaiba har muka dawo gida, yaro yak'i shan nonon laurah, daga k'arshema da'aka matsa sai nononta yakoma fidda yellow ruwa maimakon milk, anyi-anyi kuma tak'i yarda Bilkisu ta shayar dashi, ga jariri nata azabar kuka. Saida Ammah Tamata tatas sannan tayarda, Bilkisu sarkin hak'uri kuma tayarda zata shayar dashi, dukda rashin k'auna da laurah ke nuna mana, ana bashi nonon Bilkisu yakar6a kuwa. Alokacinne naje hard'aki nama hajia laurah magana, nakuma fad'a mata subama Bilkisu d'anta kokuma Na fallasasu, ga laurah nan da ranta, itada khaltum sukaimin barazana da mutuwa, kuma sukace inhar maganar tafito wlhy saisun kashe jaririn da ita kanta Bilkisu, acewarta ita bata haifi namijiba wata shegiya acikinmu bazata haifaba. Ba tsoron kurarinsu najiba, tausayin Bilkisu naji, dakuma kashe jariri dasukace zasuyi, danhaka nayi shiru inata addu'a daneman mafitar yanda zan ku6tar da jariri Ibraheem wanda yaci sunan mahaifin Bilkeesu, (yamata alk'awarin idan ta haihu namiji zai sakama yaron sunan mahaifinta), dakuma aka samu akasin haka tunda basusan miya faruba, sai yacanja zai saka sunan mahaifin laurah, ni naita rok'onsa da lallashi har ya amince yasaka sunan mahaifin Bilkeesu kamar yanda yay niyya, Na nuna masa hakan zai ragema Bilkisu rad'ad'in rashin tata jaririyar, bamuwani kai ruwa ranaba ya amince, aikam ansha rashin hankali aranar, tamkar za'a k'ona gidanan, Dan saida laurah ta hargitsa kowa, Alhaji kuma yaburgeni yace babu canji. Ban fasa gayama ubangiji ba wajen Neman mafitar hanyar maidama Bilkisu d'anta, amma saiwata k'addara ta giftamin alokacin, nayi 6arin cikina, a sibiti kuma sukace magani nasha, dama shinake sha duk lokacin da cikina yazube, sun rufamin asirine kawai, kuma Alhaji yasamu maganin zuwabar daciki ad'akina, da wannan damar hajia laurah tace nice nayi yunk'urin zubda cikin Bilkisu abaya kuma, Alhaji Abdallah yanason yara, batareda binciken komaiba yasakeni alokacin. Abu d'ayane yasakani bak'inciki da sakin nan shine sanin laurah ce ta k'ullamin, ga wulak'aci da Alhaji yamin lokacin saboda 6acin rai dayake ciki. Natafi ina tausayin Bilkisu, dannasan zatasha wahala agidannan. Tunda nakoma Kano aketamin barazana da rayuwa, kuma nasan laurah ce ta sanya, Dan akwai lokacin da'aka saceni, aka 6oyeni kusan wata 1, hankalin iyayena yatashi sosai, har aka sanya malamai addu'a sosai lokacin, ciki harda tsohon mijina Malam Abubakar. Cikin ikon ALLAH nasamu ku6ta kuwa, munje yima Malam Abubakar godiya nida yayata ananne yaganni, yakumace yanaso. Babu wani 6ata lokaci akasha biki, badan inasonsaba, amma kyawawan halayensa yasaka cikin kwanaki kad'an ya mantar dani Alhaji Abdallah, dukda har lokacin ban hak'uraba wajen son ku6tar da khaleel da mahaifiyarsa. Mafita d'aya nasamu lokacin itace bintu, k'anwar mijina, dukda kowa yasan bintu jarababbiyace, nima tana nunamin halinta, sannan kuma tagogu da zaman bariki, ahankali naja bintu ajikina, wajen k'yautata mata, saida naga tasaki jiki sosai dani sannan nafad'a mata buk'atata nason zuwa tanemi aiki agidannan. Babu musu ta amince, saboda itadama 'yarson hutuce, babu wanda yasan mike tsakanina da bintu saboda Na nuna mata karta wani nuna hakan, saboda aikin sirrine tsakanina da ita. Bintu batadawo gidannanba saida aka haifi Amatullah, nikuma har sannan ban haihuba agidan Malam Abubakar. Bintu tacigaba damin aiki, wajen kallon kowanne shigi da fici agidannan, batareda sanin kowaba, duk sun d'auketa amatsayin 'Yar raino. Tafiya tayi tafiya bintu tazomin da labarin hajia laurah tashiga wata k'ungiya, kuma khaltum ce tasakata, itama la6ewa tayi taji hirarsu wata rana. Sannan k'ungiyar tanada had'ari, safarar yara mata sukeyi zuwa wasu k'asashen duniya, ana sakasu karuwanci. Wannan labari yata6a zuciyata, nasan laurah zatayi abinda yafima haka, saboda tanada son kud'in tsiya. Ancigaba da shurawa khaleel nata girma dawayo, lokacin yanada k'anne, Dan Bilkeesu ta haifi Rufa'i sultan mujahedeen, Amatullah, Ramadan, abinda yabani mamaki da laurah batayi yunk'urin kashe wad'annan yaranba, kokuma sacesu, wani tunanine yazomin, nafahimci laurah tabar khaleel ne danya zame mata wata Katanga nan gaba, tunda shine namiji babba. Ganin hakan ne yasakani amfani datawa basirar domin yin wasa da hankalin laurah nima. Bayan haihuwar Zunnurain da Mufeedah nasamo Saudah, k'awa ga k'anwata, Lokacin saudah tafara aiki, dan lauyace mai zaman kanta, narok'eta arzik'i akan ta auri Alhaji Abdallah, tunda dama tasanshi, yayanta abokinsane, , dafarko tak'i amincewa, saida Na zauna Na warware mata komai akan abinda ke faruwa, Na burin laurah dason tarwatsa gidan Alhaji Abdallah, dukda zai har sannan bansan kwakwkwaran dalilin laurah ba Na aikata hakan kaitsaye. Jin haka Saudah ta amince, akasha biki kuwa, kundai gane wanake nufi (Ummie Amarya😂)..............✍🏿✍ Kaina yafara ciwo, amin afuwa muhad'u tomorrow insha ALLAH, danjin aikin mama, (Maman aysha😉) 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀ Ayya my sweet Dota Aneeluv ALLAH yabaki lafiya, fans kuma Aneesa A rimi addu'a batada lafiya wlhy sosai, kuhad'o da kayan dubiyafa🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀💋💋💋💋 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ _gaisuwa agareku dafatan Alkairi, Ummu Ameer (comment naki Na k'ayatar dani) Maman Uswan (Ngd da k'yauna), fadeelah Ummu Amal (nagode kwarai da gaske da ziyarar daki kawomin hargida, ina alfahari dake), miss Maryam maintain (sak'onki ya iso gareni, thanks dear) mom of 12 (comment naki Na kasheni dear), Zarah maigari (keta dabance araina), Leemat (ngd sosai dear, ALLAH k'ara miki haske akan naki rubutun), Maman Aysha (ina k'aunarki sosai), fati tage (bilyn Abdul Na alfahari dake sosai wlhy) , Nana yakaku (comment naki nasakani Nishad'i da k'aunarki), Esha qadeer (ina k'aunarki wlhy), alkairin ALLAH yakaimuku aduk inda kuke, bilyn Abdul nayinku wlhy._ Kuna dayawa wlhy, amma insha ALLAH ahankali zakuga sunayenku💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤❤❤💘🤸🏻‍♀. 4⃣0⃣ "Mama da saninki kenan aka kaini karuwanci?". Gaba d'aya falon kowa juyowa yayi yana kallonta, Aysha ce tsaye abakin k'ofa, sai Khausar dake rik'e da ita, doctor Abraham kuma yana bayansu, kallo d'aya zaka mata tabaka tausayi, saboda rama datayi, sai uban haske da tsayi, idanu jajur saboda wahala. Aleeya Ce tak'arasa garesu da sauri takama hannun Aysha, saman kujera takawota ta zaunar. Doctor Abraham kuma yak'araso inda Ammah take, domin bata taimakon gaggawa. Da k'yar tayarda aka mata allurar rage rad'ad'i, dantace babu mai mata allurar barci yahanata jin *Sabon al'amaree*, saida baffa dasu taheer sukaita lalla6ata sannan. Ya khaleel kam nazaune tamkar wani hoto, shidai binsu kawai yakeyi da rinannun idanunsa, amma ko motsin kirki bayayi. Dukda Aysha taji tundaga farkon labarin hakan baihanata tsare mama da kallon tuhumaba, tarasa yadda zata fassara abubuwan. Ummi amarya tad'ora dafad'in........ ............Hakane Aysha, dasaninmu kikaje islands UK, ammafa bada nufin turaki karuwanciba. Bayan shigowata gidannan nacigaba dabin diddik'in hajia laura batareda sanintaba, saidai bangane komaiba saboda k'arfin rik'e sirrin k'ungiyarsu dasukeyi, babu wata kafa dasuka bari dawani zai samu shiga al'amuransu. Nayi iyayina nagaji. Saida Na zauna nayi dogon nazari sannan nagane yakamata ace munsami yarinyar dazataje anufin hajarsu, tawannan hanyarne kawai zamu ringa samun bayanan sirri. Nasamu Yaya fad'ima da bintu dawannan batun. Tashin farko bintu tace musamo yarinya daga k'auye. Yaya fad'ima tace a'a, bazai yuwu mu tsare 'ya'yanmuba mu tozarta nawasu, inhar bazamu iya saka 'ya'yanmu awannan had'arinba, to babu d'an dazamu saka aciki, mudaije musake nazari. Mun amince da maganarta kam. Kafin muyi zama Na biyu Alhaji yasakani binsa Saudia yin Umrah, Dan lokacin inacikin hutun aiki Na k'arshen shrkarah. A Wannan tafiyace ALLAH yahad'ani dawata matashiyar budurwa, masaukinta Na kusada namu, saiyazam kullum tare muke zuwa massalaci. Abinda nalura dashi ga wanan budurwa shine yawan kuka datakeyi dafad'in ALLAH ya canja mata rayuwarta, Dan ba'a son ranta takeyiba. Banta6a tambayartaba, sai ana jibi zamukomo gida, nadai kasa hak'uri Na tambayeta, dafarko tayi kamar bazata fad'aminba, saida naita lallashinta sannan takwashe labarinta kaf tasanarmin. Na tausayama yarinyar sosai, har hawaye nazubar mata, sannan kuma nayi farincikin jin tanada alak'a da k'ungiya mai tambarin🦂. Bayan dawowarmu saudiya muka iske tashin hankalin rasuwar Rufa'i, lokacin kwana d'aya tak, rasuwarnan ta girgiza Yaya Bilkisu da khaleel ainun, hakama dukkan jama'ar gidanan. Babu dad'ewa kuma sai mijin Yaya fad'ima ma yarasu. Bayan lafawar wad'annan rasuwa mai ta6a zukata nasake dawoma Yaya fad'ima da zancen baya, harma da labarin matashiyar budurwa nan damuka had'u a saudia. Lokacin kwanakin mijinta 5 kacal da rasuwa, gaisuwama naje mata. Atake anan Yaya fad'ima tacemin muyi amfani da Aysha d'iyarta kawai. Wannan magana bak'aramin razanani tayiba, nacema Yaya fad'ima hakan bazai yuwuba, yaza'ayi musaka rayuwar Aysha ahad'ari, tunda bamuda tabbas akan zata iya baro wajennan ba'a 6ata rayuwartaba. Bud'ar bakin Yaya fad'ima saitace hakane, kuma tayarda da zancena, amma ita bazata saka rayuwar d'an kowa ahad'ariba, itakuma nata 'ya'yan a killace, ta sadaukar da Aysha danta ceto rayuwar yara masu d'unbin yawa daga gararin rayuwa, inhar rayuwar Aysha ta lalace awajennan tad'auki hakan amatsayin k'addara, amma tana rok'on ALLAH yama tsare mata ita, kodan darajar maraicinta dakuma sadaukarwa datayi amatsayinta Na uwa agareta. Hummm Na jinjinama k'ok'rin Yaya fad'ima awannan lokacin, Dan masu irin zuciyarta k'alilanne aduniya, bakowane keda irin wannan k'yak'yk'yawar zuciyarba, kuma duk akan kishiya, wadda mutane dayawa suke d'auka amatsayin abin k'yama, (wlhy hakan datayi yakuma sakama zuciyata salama akan wani Abu waishi kishin banza, tabbas kishin taimakon juna shine kishi, ba kishin hauka Na wannan zamaninba), awannan lokacin naji araina ina addu'ar son dawowar Yaya fad'ima d'akinta Na asali. Haka nadawo Abuja cikeda al'ajabin jarumtar mace irin Yaya fad'ima. Kwanakina biyu da dawowa kacal saiga bintu d'ukeda Aysha kuwa. Aysha bata sanniba, saboda duk sanda zanje gidansu saida nik'af nake zuwa, ko Ummah abokiyar zaman Yaya fad'ima bazata ta6a shaida fuskataba bare yaran gidan, bama koyaushe nake zuwa gidanba, saidai Yaya fad'ima tafito muhad'u awani waje. Hummm wani al'amarin ubangiji hajia laurah naganin Aysha kuwa saita tanka, dama nasan dawuya hakan bata faruba, saboda Aysha tanada k'yau da tsarin halitta irinta mata, dukda alokacin yarinyace ita k'arama. Wannan tankawa datayi kuwa bintu ta sallama mata bisa yanda muka tsara. Hajia laurah suka d'auki mak'udan kud'i suka bama bintu, duk Na kar6ar Aysha. Dukda yarinyar tana bani tausayi, amma haka muka kauda kai nida bintu aka tafi da ita, da taimakon wata mai dillacin yara muka samu akabama kubrah Aysha kamar yanda muka tsara, ita kuma waccan mai dillacin ba 'Yar k'ungiyar baceba, suna amfani da itane batareda tasaniba, saisu sakata samo yara daga k'auye amatsayin za'a sakasu aikatau, data basu shikenan sai'a rarrabasu k'asashen duniya batareda sanin iyayenauba da ita kanta wannan mata. Alhmdllh Aysha taje islands UK, inda matashiyar budurwar nan take, kuma ana kaita ta ganeta, Dan nasanar mata komai akanta ta waya. Hummm kuyi hak'uri, bakowa baceba budurwa nan face meerah!!... Arazane Aysha tamik'e cikin dafe k'irji, tace, "Ummu amarya kina nufin Anty meerah ta?." "Yes lil sholyna haka zancen yake". Meerah tafad'a daga k'ofar part d'in Ummu amarya. Kowa saida yajuya ya kalli meerah dake takowa cikin falon inda kowa yake. " lil sholyna kiyi hak'uri, kuma kimin afuwa, banida za6in d'aya wuce hakan, saboda ceton d'inbin yara mata dake fuskantar mulkin mallaka irinnan k'ungiyar su hajia laurah, wadda akema lak'abi da saunan *('ya'yan kunama)*, tabbas sud'in 'ya'yan kunamane masu amsa sunan 'ya'yan sharri, Dan adalilinsu ALLAH kad'ai yasan yara nawa suka salwanta da matasanmu. Nadad'e ina neman hanyar ku6tar da 'yan uwana, amma babu mai taimakona, sai had'uwata da wanan baiwar ALLAH hajia saudah, itace ta k'arfafamin guywa da yak'inin zamu iya tarwatsa wanan k'ungiya da ire-irenta, amma saida k'arfin addu'a da taimakon juna. Aysha shugowarki rayuwata itace mataki nabiyu danagane ubangijina ya amshi addu'ata danakeyi adare darana, akan ALLAH ya canjamin rayuwa, dukda sanadin kwad'ayin mahaufiyata Na tsinci kaina, tabbas kece kika canjani, dukda kasancewarki k'aramar yarinyar akaina. Aysha nina shiga nafita nasamu aka sakaki makaranta, saboda ALLAH ya taimakeni john yanuna yana sonki, nasan kuma hakan daga ALLAH ne kawai, (maybi ALLAH yadubi sadaukarwar mahaifiyarkine, kokuma maraicinki, dakuma yawan ibadarki) yacusa soyayyarki a zuciyar john, harya kasa keta miki mutunci aranar daya fara ganinki, bayan kuma hakan baita6a faruwaba, Dan tunda nake banta6a ganin john yad'agama wata yarinyar da'aka kawo k'afaba komin k'ank'antarta kuwa, amma ke sai ubangiji yahanashi cutar dake. Nasarar dana samu tasilar abokinsa kika shiga makaranta shine yazama matakin nasararmu tafarko akan k'ok'arin mahaifiyarki da kuma hajia saudah. Alhmdllh saikema kika maida hankalinki, gakuma kwazo da ALLAH yabaki. Ya Naufal shine mutum na biyu damuka k'ara samun ha6akar nasarori ta silarshi. Dukda naso fahimtar kamar akan aiki yake bibiyarmu, amma yata 6oyemin hakan, nima saina tattara Na hak'ura saboda nakasa gano komai. ALLAH sarki Aysha aranar da kad'an yarage john ya keta miki mutunci bakiyi mamakin zuwan period d'inkiba?. Bata jira amsar ayshaba tacigaba dafad'in, nina baki magani dasafe saboda jininki yazo, nayi hakanne dalilin jin firar glory da kubrah awannan daren, suna labarin washe gari kema john zai d'and'anaki, hankalina yatashi ainun Aysha, adaren ranar saida Na nemo maganinan da k'yar, saboda komai Na turai akwai tsari da k'a'idoji. Hankalina yatashi sosai ganin har John yazo gidan banga alamar jininki yazoba, alokacin haka naita kuka, danna sadak'ar john zaici galaba akanmu, amma alhmdllh Shi ubangiji baya barci, kuma yanjin kukan bayinsa da taimakonsu, saiga jininki yazo, Wanda hakanne matakin nasara Na uku, john bai keta haddin mutuncin marainiyar ALLAH ba, wadda tafito daga tsatson uwa mai tsarkakakkiyar zuciya. ALLAH gafurun rahimun yabama ya Naufal damar ku6tar damu, bayan Na tattaro mafi yawa daga cikin sirrin k'ungiyar su hajia laurah, batareda yayi la'akari damu suwayeba. Mijina ngd sosai akan rawar daka taka arayuwarmu. Murmushi ya Naufal yayi, ya ida takowa ahankali zuwa cikin falon. Hajia babba da hajia khaltum dai jikinsu yagama yin sanyi dajin wannan gagarumin k'ulli Na Mama, wanda zasu iya kiransa kai tsaye da suna (takun sauro, mai kwana inda ake nemansa🤪) Maganar ya Naufal ce tasaka kowa maida hanakali kansa, yace. Nima an d'orani akan aikine, gaban ya khaleel yaje yay salute nashi tareda k'amewa, sannan yaja da baya. Bisa umarnin khaleel Na bibiyeku, har ALLAH ya k'addara soyayya tsakanina da Ameerah, Ashe 'Yar uwatace ma. Kamar yanda kowa yasani khaleel oganane awajen aiki, dukda nawa reshen aikin Na k'asar Canada, sannan kuma abokineshi tun Na yarinta. Yasamenine akan yanason namasa aikin bibiyar wata yarinya da'aka tura karatu islands UK, shi yana tsoron asamu akasi ta lalace a zamanta Na turai, kuma yagamsu da tarbiyyar yarinyar 100%, alokacin nayi dariya, harna dinga damunsa akan kodai budurwarsace, amma saiya nunamin bahaka baneba, k'anwarsace, sukda bawai Na gamsu dashi baneba, amma Na kar6i aikin nahad'a dawani na office. Tabbas nadad'e ina bibiyar rayuwarku keda Aysha batareda kunsaniba, abinda ya tada hankalina shine ganin irin rayuwar dakuke ciki, kuma nafahimci ko kad'an khaleel baisan da wanannba, shi duk azatonsa karatu Aysha takeyi, saboda dawanan akai amfani wajen yimata visa, banyi yunk'urin sanar masaba, Na duk'ufa addu'a dabin dukkan hanyoyin daya dace naku6tar damu daga wannan gur6a tacciyar rayuwa, Alhmdllh nasamu nasarar yin hakan, kukanku yakamata kuyi mamakin yanda nasamu visa d'in fiddaku awannan k'asar mai matakan tsaron tsiya cikin sauk'i. Gabda zaku baro UK khaleel yabani wani sak'one nabama Aysha🎁, dukda bansan minene cikiba, bankuma dubaba, harna tabbatar sak'on ya iso gareta ta hanyar Ariana k'awarki ta school, wadda nine nahad'ata da Aysha batareda Aysha tasaniba, nayi hakane danta taimaka mata ta hanyar karatunta. Har ALLAH yasa muka dawo Canada da zama, khaleel ne yacigaba da d'aukar nauyin karatun Aysha, kuma har sanan bansan manufarsa akan ayshaba, Dan baita6a nunamin wani abuba dake tsakaninsa da ita face dangan takar k'anwa da Yaya. Ban fahimci akwai alak'ar soyayyaba sai lokacin da meerah ta nunamin wani ring da tambayata yawan kud'insa, takuma tabbatarmin Aysha aka kawomawa cikin wani sak'o🛍. To daga wannan lokacinne zuciyata tafara hasashen Kodai khaleel son Aysha yakeyi?. Ban gaskataba sai alokacin dayazo Canada wani aiki, yabuk'aci ganin Aysha, dukda dama yakanzo ganinta lokaci-lokaci, amma baya yarda suhad'u, ko alokacin dakuke UK yazo sau d'aya, saidai makarantarku kawai yaje yaganki batareda kin saniba yajuya yatafi. Amma a Canada yazo kusan 3times. Ahad'uwarku ta k'arshene kika masa rashin kunya😂. Alhmdllh nasamu damar maidoku cikin ahalinku, bisa umarnin Khaleel, tareda iyayena. Wannan shine abinda nasani kawai. Aysha dai kanta yagama d'aukar charge, raba idanu kawai takeyi wajen kallon ya khaleel da Naufal, amma har yanzun khaleel Kansa Na a duk'e, bai iya koda d'ago ido ya kalletaba bare sauran mutamene dake falon, shikad'ai yasan cikin irin azabar rud'anin dayake aciki a yau d'inan Umme amarya tace, masha ALLAH, tabbas aikinmu yatafi cikin nasarori akan turbar taimakon ubangiji, Dan bayanan da meerah tasamu damar kwaso mana daga wajensu glory, da kuma wasu sirrika dasuka Sani itada ayshane suka cigaba da taimakonmu, saikuma kaifin basira da hazak'a Na Aysha, Wanda daga baya duksai muka zama 'yan kallo nida bintu da Yaya fad'ima. Dalilina nafad'in haka kuwa shine yanda Aysha tatashi da ak'idar tarwatsa k'arfin k'ungiyarsu hajia laurah, gata k'aramar yarinya amma sai kwazo da baiwar ilhama daga ubangiji. Dukda mund'an taimaketa batareda tasaniba, amma gaskiya itace k'arfin aikin nan. Aysha tanemi had'in kan meerah wajen bama khaleel bayanan sirri akan k'ungiyar su hajia laurah, saboda samuwar salwantar da yara dasukeyi, Wanda k'ank'antar Aysha da k'arancin shekarunta bai hanata son jagorantar taimakoba. Aysha tabi hanyoyi dayawa naganin tasamu damar sanarma khaleel amma bata samuba, nina ringa amfani da hankalinta bisa ilimin aikina Na lauya, Na 6oye number tareda nuna mata wasu hanyoyi masu sauk'i, sune internet, yanar gizo, Alhmdllh kuma Aysha ta amince dani, nasan hakan yanada nasaba da k'arancin shekarunta, har alokacin akwai wautar k'uruciya tareda ita, Dan datafi haka girma kaitsaye baidace ta yarda daniba, tunda zan iya kasancewa cikin criminals, nayi amfani da hankalinta Na zumrata rami. To saikuma ALLAH yadubi k'yak'yk'yawar zuciyarta yabata basira. Dakanta tasamo wani masanin computer, yataimaka mata wajen bama khaleel bayanan sirri. Ganin aikin yamata yawane muka sakko Aleeya aciki, Dan bamu ta6a tunanin aure zai shiga tsakanin khaleel d'in da Aysha ba, Dan wannan aure nasu kawai daga ALLAH ne, wata ayace ubangiji ya saukar akan hakan, ba wayonmu baneba, bakuma tsarinmu baneba, Dan babu hakan acikin tsare-tsarenmu kam. Afarkoma somukayi Aleeya ta auri khaleel, Dan tabbas munda yak'inin inhar mukayi yunk'urin nunama khaleel asalin mahaifiyarsa to tabbas dolene laurah tayi yunk'urin salwantar da rayuwarsa, ilai kuwa hakance ta faru, Dan karo uku laura Na harin rayuwar khaleel, ALLAH ne kawai ya k'addara kwanakinsa agaba shida Aysha. Yunk'urin kashe Aysha Na farko a kwanaki ukun farko datayi ad'akin mijinta khaleel, bayan laura tata pretending akan hana khaleel kwana tareda Aysha,, ganin kwa6arsu zatayi ruwa suka aika su gwaska su sato Aysha, ALLAH mai iko saiya nuna musu ikonsa, aranar sai shukurah ta sanarma Ammah abinda ke faruwa, amma kuma tad'auki matakin gaggawa wajen saka doctor Faisal yima laurah allurar barci, ALLAH kuma ya k'addara khaleel ya kwana a 6angaren nasu. Dalilin hakanne yasakamu kawo Aleeya ta zauna da hajia laurah amatsayin wadda tazo aiki, tunda tace mata itad'in likitace. Saidai nida yaya fad'ima mundad'e da fuskantar khaleel yana zargin Aysha, bisaga wasu abubuwa data ringayi agabansa, alhalin ita kanta batasanma tanayin wani abunba, har masu aiki yakawo gidannan su biyu, cikin wad'anda akayi canji bayan mama ta bayyana bintu amatsayin 'Yar uwarta. Zeenatu tadad'e tanabin kwaf-kwaf d'in Aysha, amma ALLAH baisa tafiskanci komaiba, saboda Aysha Nada wayo, irin Wanda sai an tona d'inan, saikuma Zaliha, itama tadad'e tana bibiyar Aysha har wajen aiki, hakama Afrah, amma basu ta6a samun komaiba agareta. Wayon Aysha ne yasakata cusa mashi'a jikin hajia laurah batareda itad'in tasaniba. Kuma tabbas mashia tayi rawar gani, Dan itace tahana khaleel cin alkubus da laurah tabashi ayunk'urinta Na kasheshi alokacin. Da Sauri khaleel yad'ago yana kallon aysha. Ba k'aramin tsorone yashigi ayshaba, saboda ganin idon khaleel yazama tamkar garwashin wuta saboda jaa, gashi duk fuskarsa tawani birkice. Batareda cewa komaiba yajanye idanunsa yamaidasu k'asa kamar yanda suke ada. Mama tacigaba dafad'in, ko meatpia da Aysha tahana khaleel ci ranar Masha'a ce ta turo mata massage akan karsuci, anzuba guba aciki, rud'ewar da Aysha tayine yasakata kasa control d'in kanta, harta ambaci sunan Laurah, rud'ewa dajin maganar Asama tasaka khaleel Marin Aysha. Wannan shine abinda nadad'e ina 6oyewa samada shekaru 30, Dan haka ina Neman afuwar Wanda Na 6atamawa acikin wannan aikin nawa, bankuma San dalilin laurah Na aikata dukkan wad'anan abubuwanba, tundaga kan sace khaleel har zuwa yunk'urin salwantar da rayuwar yaron, abinda nasani shikad'ai nafad'a. Yawancin duk Wanda yake falon kuka yakeyi, musamman Anty Mamie data rungume mama da Ummu amarya, shikansa baffah kwalla tacika masa ido, ya khaleel kam babu mai iya fassara halin dayake aciki, Dan tunda yad'ago ido ya kallo Aysha baisake d'agiwaba. Dukkan hankalin Aysha kuwa yana kansa, batada k'arfin tashi taje gareshine kawai..... Tunaninta baije k'arsheba khaleel yafad'o daga kujerar dayake zaune. Kaf falon kansa akayi kuwa, saidai babu ko alamar numfashi a tartare dashi. Da gaggawa aka d'aukeshi sai asibiti, harda Ammah dake fama da k'afa, danma tasamu taimako daga doctor Abraham, Ayshama ciwo sabo fil yadawo, Dan sanadin fad'uwar khaleel itama ta yanke jikin tafad'i alokacin da tajiyo Anty Mamie nafad'in karka mutu kabarni Dan ALLAH babana. Wannan kalmata ta daki Aysha kuwa sosai. Haka aka kwashesu akai asibiti dasu, sukuma su hajia babba su taheer suka tafi setetion dasu. Tana kuka da kallon 'ya'yanta suma suna kuka, da bak'incikin mugun halinta da dukkaninsu suke k'yamata, musamman Anty zuwairah dataji dukta tsani wanan rayuwa ta Momy maicikeda gallafiri da son zuciya. Agidan babu Wanda yadamu da tafiya da momy, hankalinsu duk yanakan khaleel...........✍ Amin afuwa🤸🏻‍♀, kaina bai daina ciwoba, Na daurene kawai namuku, Dan anzo ga6ar dabazaku juri hak'uriba nasani, muhad'u gobe idan ALLAH ya kaimu, Dan dolene musan dalilin Momy Na aikata dukkan wannan mumunan rayuwar, komai daka Sani d'an Adam yanayinsa bisa jagorancin dalili. To yakamata musan dalilin hajia babba, dakuma halinda khaleel yake ciki ayanzun😢. Wlhy inajin tausayin khaleel da Aysha, sunfi kowa shan wahala da jigata😭😭😭. Karku k'osa da kasancewa dani, Dan aski yafara zuwa gaban goshi👌🏼. *_ya ALLAH ka gafartama mahaifanmu baki d'aya._*😭😭🙏🏻 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of expert & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ 4⃣1⃣ Alhmdllh su khaleel sun sami taimakon gaggawa a asibitin general hospital, dukda su taheer sunso awuce da khaleel d'in Na station nasu, amma baffah yanuna musu Subari akaisa wannan d'in tunda bashi kad'ai baneba. Shida Aysha d'aki d'aya aka kwantar dasu, gadonsu kusada juna. Ammah jar wuya kam itakad'ai🤣. Kowa kagani a familie d"in yana cikin wani yanayi, kowa da sak'e-sak'en da zuciyarsa kemasa akan abubuwan mamaki dasuka faru yau, Wanda tunani ko hasashen su baffah baita6a kaisu nanba, balle irinsu Sultan dabasu San komaiba. Ko Anty zuwairah bazata iya dogon labari akan haihuwar khaleel ba, Dan gaba d'aya batafi 6years ba lokacin, to bare kuma Anty Shikurah.🤷🏽‍♀ Anty Mamie kam ita kanta daza'a bata gadon kwanciya zatayi, harma a zurara mata ledojin jini dana ruwa, ko'a mata allurar barci tasami Hutu Na wucin gadi, k'ila tunaninta zai dawo dai-dai, ayanzu kam kallon komai takeyi tamkar mafarki zuwa anjima zata farka taga ba hakaba🙅‍♀. Bawan ALLAH baffah, shiruma maganace gamai hankali, shikansa dauriyace kawai da juriya, amma kallon komai yakeyi tamkar acikin barci ko shirin film, kokuma labarin hik'ayoyi Na marubuta, zuwa anjima komai zai tsaya yaga dukba hakabane. Haka sukaita zaman asibitin suna dakon jiran farkawarsu suduka ukun, babu mai damuwa da yunwar cikinsa acikinsu, Dan babu Wanda yake a cikin duniyar mutane balle yatuna akwai ci da sha, kowa ya lula cikin gajimaren tunani, masu kukan zuci nayi, masu hawayen fili nayi, masu rad'ad'i da k'unar zuciya nayi, kowa tambayar zuciyarsa yakeyi miyasa hakan tafarune? Miyasaka Momy aikata haka?, babu Wanda yata6a kawowa aransa hatsabibancin Momy yakai koda quarter d'in hakama, kowa ya d'auka masiface dai tazafin kishi da yanayin halitta kawai, Ashe lamarin Na Momy yagama gawurta. Babu maibasu amsoshinsu, saidai sukaita juyasu da tattaunawa a zukata, dukkansu fatansu ayanzu bai wuce farkawar su khaleel ba gaba d'aya. Ganin yanda lokacin yatafi, har 8 Na dare baffah yace suje gida hakanan, subarshi shidasu Mujahedeen, idan suka farka za'a sanar musu. Gara suje su nemama yara abinci, dansu khaleefa sai kukan yunwa sukeyi, saidai asayi biscuit abasu, yara babu hak'uri, biscuit baya d'aukarsu suka fara k'ananun kuka. Badan sun soba suka tattara suka tafi, Zunnurain da Musleem suka tafi kaisu gida. Akabar baffah, Ramadan, sultan, Muhseen, mujahedeen, hafiz anan. Haka kowa yashiga gidan tamkar anmusu mutuwa, jikin kowa a sanyaye, duk da abinci dasuka Tatar 'yan aikin sunyi hakan baisa wani yadamu da Neman abincinba, yara kawai sukaci su Affan, dakuma yaransu ya Sultan, sai Ummunoor da Nuriddin. Amma irinsu tasleem ai duk haka kowa yanemi guri yazauna, suka d'ora tunaninsu daga Inda suka tsaya. Abindama Yakuma basu mamaki shine uban matakan tsaro dasuka Tatar agidan, tako ina anguwar da gidansu zagaye yake da ainahin police dakuma police Interpol, hakama asibiti dasuka baro, ko'ina matakan tsarone, musamman d'akinda khaleel da Aysha ke kwance, babu kuma Wanda ya Isa yashiga d'akin sai doctor Faisal kawai, ko nurse d'aya ba'a amince da itaba, shikansa doctor Faisal d'in akwai sa'idon ma'aikata akansa yake shiga. _______________________ Su Momy yaukam za'ayi kwanan sel, gashi ba'a had'ata da aminiyar tataba, kowa d'akin da'aka ajiyeshi daban. Kallon inda zata kwana tayi kawai saita fashe da kuka🤣. Akan dindinyar sumintine, ga uban zarnin toilet d'in dake d'akin da wari, ga d'an karen sanyi daya fara busawa alokacin, k'afarka kawai kasaka a Simintin sai tsigar jikinka tatashi bare kuma kwanciya, sauk'inma da sauk'in sauro, saboda sanyine sauro baya zama, amma akwai Baban sauro awajen, shine kud'in cizo, irin 6ula-6ula d'innan, wad'anda dasunji kamshin mutum zasu fara gudun fanfakak'e Na k'ok'arin isowa gareshi susha jini, su sanyinma bai koresuba. Kasa kwanciya hajia babba tayi, ko rayuwar yarinta datayi gidansu 'yan gatane, bare kuma rayuwar gidan mijinta Alhaji Abdallah daba'a cewa komai. Zarya taitayi ad'akin, ta zauna, ta kwanta, tamik'e tsaye, babu style d'in dabatayiba ranar, gashi tanata fama da toshe hanci sabida wari, daga k'arshe dole tahak'ura da toshen hancin tafara damuwa da inda zata kwanta tasamu barci, dukda d'umbin damuwa da juya abinda yafaru d'azu da zuciyarta keta mafan yi, towai yama akayi bata ta6a d'ago shirinsu mamaba?, kenan batayi aiki da hankalintaba? kokad'an bata ta6a kawoma ranta wani agidan zaisan tana cikin wata k'ungiyaba, Dan sosai takeyin taka tsan-tsan ko 'ya'yanta bata basu fuska tananba balle su fahimci wani Abu, Ashe ita tana shukane a idon makwarwa bata saniba. "Kai!! Jama'a🤦‍♀, miya faru danine haka?". Hajia babba tafad'a tana dafe kai, batada mai bata amsa, danhaka tashare kwallar data cika mata ido, wlhy datasan wannan ranar zatazo mata da hakaba, datun khaleel yana jinjiri zata kasheshi, datayi dukma yanda zatayi kar wata mata tasake nak'udar haihuwa agidan. Haka taita k'ullawa da kwance wasik'ar jaki maicikeda dak'ik'anci🙀😹 har garin ALLAH ya waye. ____________________________ Dole da dare yayi su baffah duk suka tafi gida, Dan su khaleel sun samun tsaro wajen yaransa. Saida baffah yashiga ya tofeau da addu'oi sannan suka tafi. Gwaggo bintu kawai aka bari wajen Ammah, saboda ita tafarka tun wajen 9:30. Har washe gari dai su khaleel babu Wanda yafarka acikinsu. ****** A can gidama bakowanne yay barcin kirkiba, Anty Mamie ma asaman sallaya ta kwana, hakama baffah da mama, kowa da nau'in addu'ar dayakeyi, mama tana mik'a godiyarta ga ALLAH dayaja ranta har zuwa wannan lokaci tafesar da abinda ke ranta, Anty Mamie da baffah kam duk addu'arsu akan mamace, sunma rasa irin rokon dazasu mata kasancewar itace silar komai daya faru, saikuma addu'oin samun lafiya da saukayi akan Ammah da khaleel da Aysha.👍🏻 Hakanan badan wasu sunsoba sukaje suka lallek'a su ya khaleel suka wuce wajen aiki, da ammah kawai suke samun damar gaisawa, amma su Aysha basu farkaba. Baffah dai you jingine aiki yayi, aka barsa shida mama da Anty Mamie, sai surukansu matansu Ya Sultan, saikuma Anty zuwairah data tattara tafiya ta jingine gefe, Anty shikurah ma tazo bayan Anty zuwairah takirata awaya ta shaida mata komai tana kuka. Baiwar ALLAH mufeedah takasa zuwama asibitin, tanacan kwance agida sai aikin kuka kawai takeyi, Dan ayanzune tasamo zaren dalilin abinda ya tarwatsa mata rayuwa, halin momyne, tanacan tana kacaccala rayuwar wasu, taya za'ayi mutuncin 'ya'yanta yatsira?, baga mamaba, dayake zuciyarta a tsarkake take dason ceto rayuwar 'ya'yan wasu, sai ALLAH yamata alfarmar kare mata tata d'iyar, dukda taje cikin manyan tantirai da yakamata ace ta lalaced'in. Lallai yakamata d'an Adam yayi k'yak'yk'yawan nazari awannan ga6ar, babu yanda za'ayi kazama sanadin tarwatsa rayuwar wani kai d'in kazauna lafiya, ko zuri'arka ta zauna lafiya, shiyyasa kullum tarbiyya keta kuma ta6ar6arewa aii. Yo kana majalissa kana antayama 'ya'yan jama'a zagi da aibantasu, hakama gulmar matan mutane da zind'ensu, budurwa zata wuce kaji har tushen uwarta sai an bada labari, so Dan ALLAH kana nufin naka zasu zauna lfy kenan?. Wlhy bazai ta6a yuwuwaba kuwa, lokacin dakake tozarci gawata zuri'a, sai ALLAH ya jarabci taka zuri'ar yaga yazakayi, tunda ga abin zagi da zund'e agidanka aisaikayi ko. basai kawahalar da kankaba wajen hangen gidajen wasuba🙄. *_wlhy nasan wani mutum agarinmu, kullum bashida aiki sai aibanta 'ya'yan jama'a, zagi da gugar zana akan iyayensu basa kulada tarbiyyarsu, kullum shi d'an kiran wane tsinanne, wane d'an iska, wane d'an shaye-shaye yake, ko hutawa bayayi mai bakin 🦆agwagwar, aikam rana d'aya saigayi anwayi gari d'ansa nutsatstse dakowa ke yabo yafad'a shaye-shaye, wlhy yanzu idan kukaga yaron saikun tausaya masa, saboda shaye-shaye Yakoma mahaukacin k'arfi dayaji. Shin wannan aikunga bakin mahaifinsane dabai fad'in alkairi akan 'ya'yan wasune yaja masa?.🤷🏽‍♀_* _please yakamata iyaye mu gyara harshenmu, karya zama takobi wajen yankan naman jikin 'ya'yanmu batareda munsaniba, aibanta wani bashida k'yau, ko Abu mara k'yau kaga yanayi kace kawai ALLAH ya shiryeshi, tafi sauk'i akan kaci naman jikinsa agefe. Barakuji illar gulma._ 👇🏻 *_"Masuyin gheeba (gulma) zasu shiga wuta ranar lahira, za'a dinga fincike naman jikinsu ana basu suna cinyewa, suna murtuke fuska tareda kurma ihu, kamar yanda aka nunama ANNABI su ranar isra'i yagansu awannan hali, har aka gayamasa cewa sune masu aibanta mutane, tareda yimusu nune. Duba hadisin Abu sa'id alkbudry (Abu dawud da Ahmad da ibnu abidduniya) kuma ya inganta"._* *_gheeba (gulma) k'azantace, saboda manzon ALLAH (SAW) ya kwatantata da cin mushen jaki a hadisin Abu huraira, (Abu dawud da ibnu hibba)._* *_dakuma mushen alfadari a hadisin Amru d'an Ass, (Adabul mufrad da ibnu hibba)._* Shin yakai bawa miye ribarka a gulmar mutum?, kazama mai gaskiya kawai, idan wani ya 6ata maka nemarsa kasanar dashi, yabaka hak'uri koku fahimci juna kawai, amma Dan ALLAH muringa tsare harshenmu daga cin naman 'yan uwanmu, kundaiji hukuncin mai aikatawa nan, ALLAH ka shiryemu. ______________________________ Sai kusan 11 Na safe ya khaleel yafara farkawa, ahankali yabud'e manyan idanunsa dasuka masa jingin da nauyi, yabud'esu jajur abin tsaro. Kalle-kalle yafarayi ad'akin, har idanunsa suka sauka akan aysha daketa barci, shiru yayi tsawon mintuna 2 yana kallonta, soyakeyi yatuna abinda yafaru jiya, amma kwalwarsa takasa tariyo masa komai, kusan mintuna 10 yana ahaka sannan ahankali komai yadawo masa sabo fil, tamkar mafarki kokuwa film, wai Momy ba mahaifiyarsa baceba🤔, shiyyasa take masa duk abinda tagadama kenan?, kai wannan lamari akwai d'aurewar kai, ya tsurama Aysha idanu tamkar ajikinta yakeson gano gaskiya maganar. Yaja mintuna masu tsayo sannan yatashi ahankali zaune, cire k'arin ruwan da'aka saka masa yayi, k'afafunsa yaziro k'asa ya sakko ahankali, dabin bango ya iso gadonda Aysha take kwance, yaja kujerar plastic fara yazauna, awahalce ya feso iska daga bakinsa, sannan yad'ora Kansa asaman shafaffen cikinta, maikama da babu wata halittar mutum acikinsa, ahankali yasaki kuka mai ta6a zuciya da ruhin mai sauraro, shikansa baisan dalilin kukan nasaba, bashida wani za6in daya wuce yayi kukad'in, Dan hakan shine mafi sauk'i agaresa, kwakwalwarsa takasa d'aukar abinda yafaru, Ajiyakam yamanta shikansa wane jinsine, namiji kokuwa mace?, Dan bashida wata aba jarumta ahalin dayake yanzun. Acikin barci Aysha taringa jiyo kuka sama-sama, ahankali tabud'e idanunta tasauke akan d'an kufan gashin sumarsa, gabantane yashiga fad'uwa ganin ya khaleel yana kuka, saidai batada wani kuzarin tambayarsa kokuwa matsawa jikinsa, saikawai tazuba masa idanu tana kallonsa. Da k'yar ta iya d'aga hannunta Na dama dababu k'arin ruwan tad'ora saman kansa, ahankali take shafa kwantacciyar sumar dabatada yawa, saboda askewa dayakeyi, itama hawayenne take zirararwa, tausayin ya khaleel yakamata, wannan wace iriyar rayuwace? Mi hajia laurah kenema itakuwa aduniyarnan? Miye dalilinta naraba d'a da mahaifiyarsa aranar datagama shan nak'udar haihuwarsa, bayan watanni Tara data d'auka Na azabar rainon cikinsa, amma saboda rashin tausayi atsige matashi batareda ta ko kallishiba taji sanyi aranta. Yanzu da ALLAH baisa hankali ajikin khaleel ba, dahaka kullum zaita cin zarafin mahaifiyarsa amatsayin kishiyar uwa? Wanda hakan hajia babba taso yakasance, takan takali Anty mamie tsiya kodan khaleel yaci mutincin Anty mamie, Amma ubangiji gafurun rahimun saiya dakatar dahakan, yasaka kunya daganin mutuncin juna tsakaninsu, tareda k'arfin soyayya irinta uwa da d'anta. Dr Faisal ne yaturo k'ofar, dasauri yak'arso inda suke, tausayinsu yakamashi, dukda baisan miya faruba, yafahimci tun ajiya family d'in suna cikin tashin hankali, yadad'e tare dasu, har ankai matsayin dazai iya sanin farincikinsu ko akasin hakan. Dabaya yakoma, yakira baffah. Jin sun farka yasaka su mama ma mik'ewa da sauri, saidai dole su suka tsaya ajikin window, baffah kad'ai yashigo. Jiyayi kwalla tacika masa idanu, jarumin d'ansa mai k'ok'ari da dakakkiyar zuciyar tunkarar kowanne irin had'ari shine ke kuka, shikansa sometimes yakan jinjina jarumtar Mu'azzam, saboda mutumne shi mara tsoro, komai girman mulkinka zai fad'amaka gaskiyane awuce wajen, shiyace bashida lokacin zaman gulmar wani, amma kalla yaushine ke kuka, kuka ajikin mace, kuka irin Wanda Duk Wanda yagani zaisan kukan bak'incikine da k'unar zuciya. Bayansa baffah yadafa shima yana k'ok'arin maida kwallar data cika masa nasa idon. Jin k'amshin turaren baffah yasaka khaleel d'ago kansa, dasauri yafad'a jikin baffah yakuma sakin kukan. Huci babbafa yafurzar daga bakinsa, yana shafa bayan khaleel da hannayensa, alamar lallashi. Aysha kallonsu takeyi cikeda tausayawa, itama har sannan kukan takeyi. Anty mamie tashigo itama, inda Aysha take kwance tak'arasa, ta zauna bakin gadon tareda d'aukar kanta tad'ora bisa cinyarta, tasaka hannayenta tana share mata hawayen. "Ya Isa kinji d'iyata, daina kukan hakanan, kinga bake kad'ai baceba, ba'a son mai juna biyu da 6acinrai kinji. Jinjina kai kawai Aysha ta iya yi, amma batace komaiba. Shima baffah yanata lallashin khaleel, saida yasamu yayi shiru sanan, saman gadon baffah yamaidashi ya zaunar, yasaka masa filo yajingina da bango. Dr Faisal yad'an duddubasu yace, " Alhmdllh. Yanzudai jikinsu normal, sai abasu abinci suci, ga magani susha, idanma ALLAH yataimaka k'ila mu sallamesu zuwa dare. Hamdala duk sukayi taredama Dr Faisal godiya. Mama da Anty zuwairah da Anty shikurah suka shigo, duk jikinsu asanyaye yake, sannu sukai musu, khaleel yad'ago ido ya kafe Anty zuwairah dasu, kallonta yakeyi tamkar Momy, Dan ita tana kama da ita sosai. Jikin Anty zuwairah saiya kuma yin sanyi, Dan ganin kallon da khaleel kemata, kusadashi tak'arasa, takama hannunsa ta rumtse anata, hawaye masu zafi suka ziraro akumatunta. Takasa magana, Dan batasan mizata cema khaleel d'inba, batada bakin furta komai, harshenta yamata nauyi. Ya khaleel yasaka hannunsa ahankaki yashiga share mata hawayen. Baffah dake kallonsu cikeda tausayi yayi murmushi, hakama mama da Anty Mamie. Mamace tazo ta janyeta tana lallashi, ya isa haka zuwairah, kukan ya isa haka, tunjiya aketa Abu d'aya, dolene muyi hak'uri, bamuda dalilin canja k'addara, abinda yafaru yarigada yafarun, saidai mu kiyaye Wanda zai faru anan gaba kuma. Ku sakama zukatanku hak'uri, muyimasu addu'ar samun lafiya kawai kunji. Duk Kansu suka d'aga mata. Anty shikurah tahad'amusu shayi, tamik'ama Anty Mamie dake tareda Aysha, Anty zuwairah kuma takar6i na khaleel, dakanta taringa bashi, baiyi musuba yakar6a tamkar wani k'aramin yaro😺. Aysha dai dafarko tace bazata shaba, saida Anty Mamie da baffah sukaita lalla6ata sannan tad'ansha, kur6artama baifi hud'uba tafara yunk'urin amai, da sauri Dr Faisal yakawo wata tasa, aikam saida ta amayar dashi tas sannan aka samu sassauci, dukta gama galabaita, sai numfashi take fitarwa da k'yar. Ya khaleel jiyakeyi tamkar yamata kuka, tausayi take bashi ainun, laulayin ciki yana bata wahala, gashi yazo ga6ar tashin hankalin dasuka tsinci Kansu aciki, duk Aysha tagama canja kamanni, tarame sosai, sai uban haske datayi, ko mak'iyinta dolene ya tausaya mata. Shima daganan daina shan tea d'in yayi, duk lallashinsa da Anty zuwairah keyi itada mama k'insha yayi, hankalinsa gaba d'aya yanakan Aysha. Bayan Anty Mamie ta taimakama Aysha ta wanke bakinta ta rungumeta ajikinta, saida tad'an huta sannan tashiga tambayarta mitake sha'awar ci yanzun?. Shiru nad'an wani lokaci, sannan Aysha tace, "Anty Mamie zan iya samun fura". " da guduma kuwa d'iyata, furama abu mai sauk'i". Anty shikurah tace, "bara naje nasiya miki kinji sholyn khaleel". 'Tayi maganar cikin 'Yar tsokana'. Saida kowa yayi murmushi kuwa, har khaleel d'inma, Aysha kam kanta ta 6oye ajikin Anty Mamie. Bayan Anty Shikurah tasayo furarne a Shop d'in dake cikin asibitin tadawo tagamu dasu meerah sunzo dubasu. Atare suka rankayo d'akin. Nanfa aka shiga gaishe-gaishe da tambayar masu jiki, harda Aleeya akazo. Sosai Aysha tasha furarnan, ALLAH kuma yataimaka ta zauna, batayi amanba. Babu dad'ewa kuma saigasu Amal amare, Adams yakawota, saikuma gasu Hamdiyya, kowa mijinta yakawota yatafi, bayan sunshigo sun duba masu jiki, har Ammah, Adams dai anan aka barsa, Dan baigama hutun amarciba, amma yanaji aransa dolene yakoma aiki kam. Bayan sun gaisa da kowa saisuka ragu, wasu suka tafi d'akin Ammah jar wuya, aikam tiryan-tiryan saida Ammah tabama su Shahuda labarin duk abinda yafaru ajiya, sunsha kuka kuwa, da tausayin khaleel da Anty Mamie, tareda jinjinama k'ok'arin mama da ummi amarya da gwaggo bintu, badai suce komai Akan momyba, kowa yabar tsinuwar dayake mata azuciyarsa. ************ Kowa yayi shiru, d'akin tsit idonsu akan TV suna kallon labarai a tashar NTA da ake maimaitawa Na jiya, labaran kamasu hajia babba dasu khaleel sukayine afarko. An nuna inda aka kamasu, dakuma makamai dawasu abubuwa irinsu kwayoyi da cocaine da'aka kamasu da'ita, sai yara kusan 64 da'aka samo awani gida, wad'anda an ajiyesune ana shirin kaisu wasu k'asashe. Saikuma aka nuno youseef yana tattaunawa da 'yan jarida. Yace. "Kwarai da gaske, mundad'e Muna musu tsinci d'ai-d'ai, saidai bamusan gawurtarsu hartakai hakaba, abin bak'incikinma shine samun manya-manyan mutane masu fad'a aji ak'asarnan, wad'anda al'umma suka d'auki ragamar Kansu da d'aukarsu iyayen k'asa, amma sukaci amanarmu da k'asarsu wajen aikata wanann ta'addaci, wannan k'ungiya tanada k'arfin gaske, danba'a Nigeria kawai takeba, akwaisu ak'ashe daban-daban Na duniya, babbar illar dasuke mana itace d'aukar yaranmu mata suna kaiwa karuwanci, dashigo mana da miyagun kwayoyi". *_'yan jarida:-_* "to amma yalla6ai, wane mataki kuka d'auka domin ruguza wannan k'ungiya mai k'arfin iko? Sannan zaku iya dawo da yaran dasuka salwanta tasanadin wannan k'ungiya?". " insha ALLAH munakan yin hakan kam, Dan zuwa yanzun sauran ma'aikatanmu dake k'asashe daban-daban sun duk'ufa akan aikin zak'ulo dukwani mai alak'a dawannan k'ungiya. Sannan zamu dawo da sauran yaranmu gida da'aka kai wasu k'asashe". *_'yan jarida:-_* "yalla6ai ance akwai jami'an tsaro dayawa ta fannonin kowanne aiki dake cikin wannan k'ungiya, kuma manya-manya masu fad'a aji, shin gaskiyane kuwa?". " hakane, akwaisu, kuma insha ALLAH nangaba kad'an duk za'aji sunayensu, bayan mun kammala aikin cikin gida". *_'yan jarida:-_* "yalla6ai dagaskene rad'e rad'in daketa fad'a cewar ankashe babban jami'in tsaronnan mai jarumtar aiki dakan tsorata 'yan ta'adda saboda rashin tsoronsa awannan gumurzu, Ibraheem Abdallah Jigawa, Wanda kowa yafi saninsa dasuna j!". " hummm", youseef yafad'a yana murmushi. "Gaskiya bahaka baneba, yalla6ai j! Yananan daransa, ko harbin bullet d'aya baishiga jikinsaba, Dan haka mutane su kwantar da hankalinsu, Ibraheem Abdallah bai mutuba". *_'yan jarida:-_* ''to amma miyasa yak'i yarda kowa yagansa har zuwa yanzun? Ko hakan yana cikin sirrin aikine?". Dariya. " kokad'an Bahaka baneba, bai 6oye Kansa dan bayason agansaba, saidai wasu 'yan dalilai, amma insha ALLAH nanda kwanaki kad'an za'a iya jin bayanaima kaitsaye daga bakinsa". *_'yan jarida:-_* "to ALLAH yasa hakan takasance, nasan kowa zaiyi murna da hakan, Dan zuciyar 'yan k'asarnan tana cikin jimamai dafargaba kam sosai, basuda burin daya wuce suka j! Darai ayanzu. Duka duka anan muka kawo k'arshen rahoton namu, jama'a kuma yakamata su kwantar da hankalinsu, kundaiji yalla6ai j yananan daransa, saidai wani daliline ya6oyesa. Munyi-munyi Nason jin dalilin 6uyar tasa hakan bai faruba, hakama munso jin tabakin shugaban wannan hukuma amma hakan yaci tura, munkira wayarsa har kusan sou hud'u bai d'agaba k'arfin had'a wannan rahoton. ALLAH ka zaunar dak'asarmu lafiya, kamana maganin 'yan ta'adda. Kowa ajiyar zuciya yasauke ad'akin, ya khaleel kam saiya lumshe idanunsama gaba d'aya...........✍🏻 *_Happy juma'at Mubarak my sweet fans_*😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘😘🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀. Duk wanda yaga yamin magana ta PC ban amsashiba yamin afuwa, mura nakeyi, typing d'in kawai nake dauriyar yi, amma zan duba. ngd sosai.💋💋 *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of expert & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀ *_yau ranarkuce masoya, kumarmatso kusa, ngd da k'auna da k'ok'arin bibiyata, inasonku irin trillions d'innan, kunanan manne azuciyar bilyn Abdul, bazan ta6a mantawa dakuba kona dak'ik'a d'aya👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤💋💋💋💋💋💋💋, kud'in nadabanne wlhy💪🏻._* Zainan umar, Mmn khadija, Hawwa, Aysha admin, Mmn siyama, Ummu hanan, Kbbello87, Amina isah n, Mycm, Zeeharuna, Mss calm, Maryam, mamu, Amina aliyu, Hanan yusuf, Haleema s adam, Ummu'assisdiq, Umar ruqaiyah, Precious, Hajara, Mmn fatima, Mmn beauty, Falmi k aliyu, Mariam a umar, Billy A A, Ummu barakat, Hajara isma'il, Fatima (zarah), Ummu Ahmad, Mommyn iman, Juwairi, Maryam Haruna, Mom muhaseen, Zubby Abdullahi, Maryam sulaiman, Mmn ihsan, Ummin sayeed, Nafisa salis, Amina musa, Aunty baraka, Mmn sanah, Mmn fkyht, Marnona, Aneesah Abubakar Rimi😎(👍🏻👍🏻👍🏻my Dota), Ummy fingers, Rashida tabacco, Maman ihsan, Zainab, Maman Ruky, Sa'adatu Aliyu, maman Abdallah😂. _ina mik'o gaisuwar ban girma da fatan alkairi_ 👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻💋💋💋😉 4⃣2⃣ Alhmdllh jikinsu yayi sauk'i sosai, maganar 'yan dubiya kam ba'a cewa komai, manyan ogannin ya khaleel Sai zuwa sukeyi dubashi, hakama wad'anda suke k'asansa, abokan baffah ma da matansu, koda yaushe asibitin FAM da mutane, saidafa idon securitys nakan kowa, gudun kar a cutar da ogansu. Ammah ma tanata samun lfy, Dan bakinnan yana nan rad'am🤣bai mutuba. Nagafa gayyar fans dadama awajen sunzo gaisuwa, su o'e akaita washemin hakwara😁, naganoki to😂, kunjifa su madam son gulma anbaza kunne aji wacece, to nak'i fad'a d'in😏. Da safe aka sallami su ya khaleel, amma banda Ammah, aikam tasaka rigima akan bazata zaunaba, aii k'afarta k'afar ironta, itafa baza'a barta a wannan asibitiba babu iro wani yabiyo dare yasakata abuhu. Anta lallashinta, aka nuna mata akwai securitys za'a bari suna tsaronta. "Yo duk tsaron mutum yakai ALLAH ne?, nidaifa bazan zaunaba, duk wad'annan dakake gani iro yafisu jarumta, ganinsa yasakasu wannan zazzare idanun, dasunga yatafi gida gyangyad'i zasu farama mutane, har aje asaceni basu saniba."😏 Babu Wanda bai daraba awajennan. Ya khaleel yataka ahankali gaban Ammah, hannunta yakama tasakko daga gadon batareda yayi maganaba, shiya taimaka mata takama sandunan dazatayi tafiya. Saida tarik'e da k'yau sannan suka fara tafiya ahankali, tana d'an d'ingisawa, suka fice. Kowa da kallo yabisu, baffah yay murmishi tareda kallonasu, " to tsayuwar mi mukeyine? Saimu tafi aii, Dan mu'azzam sunyi gaba da Ammah, muskilancin nakusa har yanzu, shiyyasa baza'a mana maganaba". Duk d'an darawa sukayi, sannan suka tattara komai suka tafi. Amotar Sultan suka iske Ammah da khaleel. Kowa saiya shiga mota, Anty zuwairah tabud'e kusada khaleel tazaunar da Aysha, sannan takoma gaba ta zauna kusada Ya Sultan dazaiyi tuk'i. Juyowa ya khaleel yayi yakalli Aysha data raku6e jikin murfin motar, talumshe idanunta. Tausayintane yakashi, ahankali yasak'alo hannunsa tabayan k'ugunta ya kwantota jikinsa. d'ago idanunta tayi ta kallesa, shima idonsa nakanta, ya d'age gira d'aya tareda k'anne idonsa d'aya. 'Dan murmushi Aysha tayi, tamaida kanta gefen hannunsa ta kwantar. Yad'anyi murmushi, tareda sumbatar kanta ahankaki. Duk abinda sukeyi Anty zuwairah da ya Sultan Na kallonsu, murmushi kawai sukayi, amma babu Wanda yace komai. Ammah dai batasan wainar da'ake toyawaba, hankalinta nakan danna wayarta, Wai tana neman number uncle ma'aruff.😹 Bawata tafiya mai nisace takaisu gidaba. Suna zuwa mama tace Aysha da khaleel suwuce 6angarensu kawai. Babu Wanda yace komai, khaleel yakama hannunta suka tafi. Tsaf suka tadda ko ina, da'alama kullum sai'an gyara ko ina. Aysha tazube saman gadon tana sauke numfashi, Dan har yanzu jikinta babu wani k'arfi. Kallo khaleel yabita dashi kawai, baice komaiba yafara k'ok'arin cire kayan jikinsa. Aysha nadaga kwance take kallonsa, harya gama, yad'auki towel ya d'aurama k'ugunsa, sosai Aysha taga ramar da ya khaleel yayi akwana ukunnan. Ruwan wanka maid'an zafi yahad'a, sannan yafito. Idon Aysha alumshe taji and'uketa cak. Da sauri taware idonta akansa, yad'age girarsa duka yana kallonta, bazata juri kallonba, sai kawai ta lumshe idanunta. Atare sukayi wankan, konace yamusu, Dan duk khaleel ne k'arfin komai, Aysha duk batada wani kuzari ajikinta. Dakansa yadawo da'ita cikin d'akin, yad'an Mirza mai, yasaka jallabiyya milk color mai gajeren hannu. Ayshama tad'an dage ta shafa man, amma duk awahalce, burinta kawai ta kwanta. Tana gamawa khaleel ya taimaka mata ta sanya doguwar rigar daya ajiye mata mara nauyi sosai, fara mai adon bak'ak'en furanni, batada hannu, sannan anmata d'inkinne kamar Na yara, rigar tamata k'yau, iyakarta kwaurinta, batakai k'asaba👗. Ita kanta saikuma kallon kanta takeyi amadubin, tasan rigar tagama amsar jikinta, kaikace saida aka gwadata aka d'inka, danma tad'an rame, tana mamakin a ina ya khaleel keta zak'ulo kayanan d'ai-d'ai hakane?. Bata samu amsarba, saima ajiyar zuciya data sauke, sakamakon jin hannun ya khaleel acikin sumar kanta yana warwareta, dukta cirkud'e saboda rashin samun gyara Na kwana biyu. Sai matse baki da rik'e hannunsa Aysha keyi, zafi takeji sosai, amma baice komaiba yad'auki cumb yana taje mata, bayan yasaka mai sosai, dukda haka zafi Aysha keji, sai shiii take fabaki tana rirrik'e hannunsa, amma muguntar khaleel saida yaga gashin ya warware sannan yamaida ribbon d'in ya d'aure mata a tsakkiya. Sai tunzura baki Aysha take gaba, wai ita zafi. Yatsansa yasaka ya d'alli bakin. Da sauri tadafe da hannayenta sabida zafi, tuni idonta sun cika da kwalla kuwa, murmushi yayi, yaduk'o ahankali yasumbaci bakin bayan ya janye hannunta akai. Harya cire bakin amma saiya maida. Hummmm lallai masoyanann sunyi missing juna kam, Dan Ayshama a wannan karon tabada gudunmawa🤫. Saida sukaji ana knock d'in k'ofa sannan khaleel yazare bakinsa awahalce . Jingina yad'anyi da madubin, yagama sauke numfashi Na Seconds sannan yanufi k'ofar fita. Itadai Aysha kunyarsace takamata, kanta Na k'asa takasa kallonsama. Yana fita tamik'e ta haye gado ta kwanta. Hasnah ya iske a bakin k'ofar falon bayan ya bud'e, sannu tamasa cikin ladabi, ya jinjina mata Kansa. Itakuma tamik'a masa basket k'arami dake d'aukeda kuloli, tace inji Ummu amarya, kar6a yay yakoma ciki, itakuma tajuya tatafi. Bin Aysha yayi dake kwance akan gado da kallo, aransa yace yarinyarnan dukta zama ragguwa wlhy. Saman sofa yazauna, yad'ora basket d'in abincin saman k'aramin table Na glass dake gaban kujerar. Ahankali ya furta "A'eesha". Tunda abinnan yafaru sai yanzu taji muryarsa, ko'a asibiti akazo dubasa bayama kowa magana, saidai d'aga kai ko girgizawa yayinda aka masa magana ko tambaya. Aysha tad'an d'ago idanunta dasuka fara shanyewa saboda barci, ta amsa da " na'am". Yace, "sakko kici abinci, saiki kwanta". Kanta ta girgiza masa alamar ta k'oshi, tana yatsine fuskarta. Baice komaiba yashiga bud'e abincin, jallof d'in macaroni ce dataji kayan vegetables da busashshen kifi, sai k'amshi takeyi kuwa. d'ago ido yayi yasake kallon Aysha, yace. " kingafa macaroni ce". Kallon abincin Aysha tayi, haka kawai taji tana sha'awar taci. Saita sakko tanufoshi. Zama tayi kusadashi, ta jingina ajikinsa, dukta koyi son jikin tsiya. Baice komaiba yad'auki fleet d'aya yazuba abincin, cokali d'aya yasaka yagyara zamnsa sosai, saida yafaraci sannan yad'iba yakai bakin Aysha. Bakin tabud'e bayan tayi bismillah. Haka sukaci abincin a tsanake, yanaci yana bata, har suka kusa cinyewa, amai Aysha tafaraji. Tsayawa yayi dabata abincin, yay saurin zuba ruwan lemon cittan a cup yabata. Kad'an tasha, ALLAH ya taimaka aman yatsaya batayiba, saikawai yadaina bata abincin, ya jinginata da kujera, tareda tartare kayan yafita dasu. Mintuna kad'an yadawo, akwance ya isketa saman sofa, tashinta yayi yana fad'in, "kibari mana abincin yad'an narke, babie yasamu cikin salama shima". Itadai batace masa komaiba, sai kallonsa datad'anyi, tamaida kanta gefen kafad'arsa ta kwantar tareda lumshe idanu. Shima ajiyar zuciya ya sauke, yajingina kansa da kujera ya Lula suniyar tunani daya zame masa aboki ahalin yanzu.☹ Bayajin dad'in komai sama da tunani, shikad'ai yakeyi yaji d'an sanyi aransa. Sun d'auki tsawon lokaci ahaka, hardai Aysha tafara isarsa da mutsu-mutsu saboda tagaji da zaman, gashi barci takeyi k'ak'as abinta. Bud'e idanunsa yayi akanta, ganin barcinta taketasha ya girgiza kansa, d'aukarta yayi suka koma saman gadon, bayan yakai dubansa ga agogon dake d'akin, ganin da sauran lokacin sallah shima saiya kwanta, yagyarama Aysha kwanciya ajikinsa. Hannunsa d'aya Na saman cikinta yana shafawa, tareda tunanin wai mutumne anan ciki?, yagadai randa cikin Aysha zaiyi girma😊. Itakam bama tasan yanayiba, tuni barci yakuma yin gaba da'ita. Shikam yakasa barcin kwata-kwata, abubuwane dayawa akan Momy suketa dawo masa, har yanzun zuciyarsa takasa fassara wasu abubuwan.... Shigewa jikinsa da Aysha takumayine yasakashi maida idonsa kanta, tausayinta yakamashi, k'aramar yarinya da ita amma tasha gwagwarmayar da wani namijinma bazai iyaba, yakai hannunsa d'aya saman kanta yana shafawa ahankali, wata k'aunarta da soyayyarta tana kuma ha6aka a zuciyarsa, murmushi yad'an su6uce masa daya tuna ranar daya fara ganinta, ahankali yakai bakinsa saman goshinta yasumbata, har yanzu fuskarsa d'aukeda sauran murmushin, shikad'ai yasan miyakeji a zuciyarsa, kuma k'ank'ameta yayi tamkar za'a kwace masa ita, har saida tad'an motsa sannan ya sassauta mata. Haka yacinye lokacin barcin NASA da tunani iri-iri, wad'anda suka shafi al'amuran rayuwarsa daban-daban. Kiran sallah ne yasakashi tashi, ahankali yazare Aysha daga jikinsa, danya lura tanajin dad'in barcin nata, filos yad'an sakamata sannan yashiga toilet ya d'auro alwala. Bai tashi Ayshaba yafice masallaci bayan ya kulleta tabaya, dukda akwai securitys zagaye dagidan, hakan baisashi jin yarda da kowaba, inhar matum irin Momy zata iya aikata abinda ta aikata, tokuwa baikamata zuciyarsa aminta daduk wani makusancinsaba ahalin yanzu, har yanzu baigama farkawa daga magagin barcinsaba, Dan maganar gaskiya har yaud'inna tunaninsa a birkice yake, yakasa samun nutsuwar warware komai dake dank'are a zuciyarsa ballantana ya fahimci komai dalla-dallah, saidai yana kamanta rashin fahimtar tasa da neman son dalilin momy Na aikata wad'annan abubuwan masukama da labarai kokuma tatsuniyoyi. Har yadawo daga massallaci Aysha nata barcinta, zama yayi gefen gadon saitin face d'inta, yakai hannusa saman sumar kanta yana kwantar daduk wadda tad'an tashi, d'ayan hannun kuma yanajan hancinta dashi. Bud'e idanunta tayi akansa, tad'an lumshe sannan takuma bud'ewa. "Sorry, nakatse miki barci ko? Daure kitashi kiyi sallah time Na tafiya kingani". Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka, "please sadauki, ALLAH barcin bai ishenibafa". Yad'an zaro manyan idanunsa tareda d'ora hannunsa saman bakinsa, "kai, bakiji minaceba kenan? anfayi sallar zuhur, duba 1:35pm". Batace komaiba kuma, ta yunk'ura dak'yar tatashi zaune, shine ya taimaka mata ta sakko k'asa, zai rakata toilet tace zata iya. K'yaleta yayi, yajingina da fuskar gadon yana kallonta yanda takebin bango ahankali, aransa yace ALLAH yarabaki lfy matana, yakaimu randa zanga kin haifamin baby girl ko boy d'ina, nasan dai zansha raki a d'akin haihuwa😊. _____________________________ Bak'aramar azabar wahala hajia babba tashaba akan cizon da kud'in cizo yayata mata adaren jiyaba, haka tatashi jiki dukyayi burd'ai-burd'ai, Dan kokad'an fatarta batason kwari dama, koyaya wani Abu yata6ata saikaga ya lalata mata fata. Duktayi wani iri da'ita, ga azabar sanyi da ciwon kai dake damunta. Kwana d'aya kacal amma dukta fita hayyacinta, sai soshe-soshen jiki takeyi, jitayi wata wutar k'iyayyar mama nak'ara zafafa zuciyarta, wlhy da ace zata samu damar fita awajennan saita tarwatsa kan mama da d'iyarta Aysha da bullet, hakama khaleel, tatsani shegen yaronnan, sannan tayi bak'inciki da takaicin rainon abinda yazama mata masifa arayuwa, inda har tasan haka Ibrahim zai zamema rayuwarta masifa datun yana jinjiri tagama murd'e kansa anwuce wajen, ta zabga kwafa tana zirar da hawayen bak'incikin barin Ibrahim aduniya. Nikam nace, "to Momy, zakaranfa da ALLAH yanufa da cara, ko'ana mazuru ana shaho saiya kai, khaleel yazama kainuwa dashen ALLAH, shifa mai arzik'i ko a kwara ya saida ruwa, sannan mairabon ganin bad'i........😜👌🏼. 🤪garama ki rungumi k'addara, danta k'are miki keda muk'arrabank. Saima Anfara muku sassafar gero a turmi🤣, sannan ne zakiji tsanar tasa mai dalili😜😹😹🤷🏽‍♀. ____________________________ Wuni guda haka yau suka kasance manne da juna, dukda babu wata fira dake shiga tsakaninsu, Dan gaba d'aya ya khaleel yamaida hankalinsa kacokan a duniyar tunani, saima Aysha tad'an gaji da shirunne take zungurarsa. Yakan juyo ya kalleta, wani lokacin yakan mata alamar tambayar miyafaru?, kokuma yamata murmushi. Bayanda Aysha ta iya dashi, haka tahak'ura suka taru sukai jugum-jugum, saidaifa Aysha nacikin tsananin farincikin kawo k'arshen Momy, tana kannewane kawai saboda kunyar khaleel, dantasan koyayane akwai shak'uwa tsakaninsa da Momy mai k'arfi, baidace takuma assasa damuwa aransaba, danta kula kokad'an bayason jin dukwani Abu daya shafi Momy, wannan yasaka Aysha kame kanta, tacigaba da ririta jikintama. Bayan yayo sallar isha'i suna zaune afalo, kan Aysha saman cinyarsa tana kwance a doguwar kujera, hannunsa Na cikin gashinta yana wasa dashi, idonsa kam akan TV yana kallon labaran ait. Kallonsa Aysha tayi, murya ashak'e tace, "ya Sadauki!". " uhhm". Yafad'a yana maido idonsa kanta. Shiru tayi itama tana kallonsa. Yace, ''ina jinki, akwai matsalane?". Kanta ta girgiza masa tana shagwa6e fuska. Ya tattaro dukkan hankalimsa akanta, fuskardai babu walwala, wannan yasaka Aysha jin Shankar masa tambayar dake ranta, dantasan halin kayanta sarai. Ganin tayi shiru saiya d'alli la66anta da d'anyatsa, baki taturo masa, ashagwa6e kuma ido cikeda kwallah tace, "kai ya khaleel, ALLAH mugunta babu k'yaudai". "uyimmm hakanefa, bara Na daina miki karfa nima ama d'iyata wataran". Kunya takama Aysha data tuna lokacin data fad'a masa maganar, hannu tasaka ta rufe fuskarta. Bakinsa yad'an ta6e yana guntun murmushi. Har yanzu idonta arufe yake, tace, " inban takurakaba, kafad'amin miyasa kayita bibiyata har k'asar Islands?". 'Dan murmusawa yayi, Dan dama tun d'azun yalura da abinda takeson tambayarsa kenan, danyaga kallon tuhuma datake jifansa dashi tun suna asibiti, ya lumshe idanunsa yanamai tariyo komai tamkar yanzun yake faruwa. Itakuma ta tsuramasa idanu tana sauraren amsarsa. Kusan mintuna 5 sannan yabud'e idon akanta, cikin murya k'asa-k'asa kamar mai gudun kar wani yajisu yace, "miyyasa kikeson ji? Miyasa kikeson tunomin abinda yawuce?, tuna abinda kike buk'ata tamkar tuno wasu muhimman abubuwan da zuciyarsa ke buk'atar mancewane, baki labarinnan tamkar ruguza tubalin hak'uri da juriya dana fara tanadama rayuwatane, fad'a miki tamkar sake dawo da abubuwa masu cimin zuciya da cizonsune, please & please my Noorulhayat d'ina, karkice saikinji, karkice saina fad'a, karki tono komai, barni Na manta, kid'auka Na manta komai, kid'auka nid'in sabon mutumne, Wanda yafara rayuwa daga shekaranjiya waccan zuwa yau, kimanta komai A'eesha, kimanta please, kimanta kamar yanda Na d'auka Na manta Nima............ Da sauri Aysha ta rungumeshi tareda sakin kuka, ''kayi hak'uri ya khaleel, ka gafarceni, bannemi kafad'a d'inba danna tada maka da ahankali, inason jine akwai, kaikanka Idan kafad'a zuciyarka zata rage nauyi, zakaji sassaucin abubuwan da suka maka dabaibayi azuciya, barin abubuwan arai sukan assasa bak'inciki da damuwa mai tsanani, sukan gusar da dukkan farinciki ko walwalawar mutum, sukan ruguza dukkan wani security mai kare lafiyar garkuwar d'an Adam, kafad'a koyayane ya khaleel, kafad'a please, karkacemin a'a, kafad'amin koda sau d'ayane domin fiddani daga rud'ani, kafad'amin kodan nayi farinciki, kafad'a kodan naji araina banyi nadamar aurenkaba, Dan ALLAH ya Ibraheem. Tsam suka rungume juna, zukatansu suna k'una, sunkai tsawon lokacin ahaka, saman khaleel yad'ago Aysha daga jikinsa. Amamkinta saitaga yana murmushi. Kallonsa takeyi cikin mamaki. Yad'age mata gira sama, muryarsa a sanyaye yace, "kinsan mizaisa Na iya fad'a miki?". Kanta ta girgiza masa. Ya kauda kansa yana furzar da huci abakinsa, dawo da kallonsa yayi kanta, yad'auki hannun damarta yahad'a da nasa yad'ora saman cikinta, " zanfad'ane kodan yarinyata ko yarona, zanfad'a domin idan sunzo duniya kibasu labarin wahalar da mahaifinsu yasha akan soyayyar mamansu, zanfad'a kodan suji cewa mamansu taciri tuta, kuma itad'in lucky ce wajen janye zuciyar mahaifinsu a KALLON FARKO, wlhy ked'in kinzamemin maganad'isu, zanfad'a koda kowa bazai yardaba, harke kanki matata. Domin kin tankwara zuciyar Ibrahim alokacin danakejin babu wata mace datakai isar hakan, kin ruguza dukkan kurina da cika baki alokacin dani kaina nakejina on top, kece kika canja komai A'eesha, kece kika sauya Ibrahim khaleel alokacinda nakejin babu wata mace datakai isa ko k'arfin ikon hakan, alokacin danake d'aukar soyyaya shirme, wasan yara, rashin aikinyi, da k'arancin k'arfin zuciya." Dolene yau d'inan kiji tushen soyayyar Ibrahim Abdallah *(J!)* akanki 'yammatana😉👍🏻...................✍🏻 *_Ayya jiya kunjini shiru, murace tamin kamun kazar kuku👩🏻‍🍳, da k'yar aka tsamoni a tukunya😂_*. Kumuje zuwa my guys😉🤪👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻. Bilyn Abdul ce🤙🏻👯‍♀. *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu baki d'aya._*😭😭😭😭🤲🏻🤲🏻. *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ *_kuna cikin zuciyar bilyn Abdul kuma, kuna dabbane wlhy my fans_* @⁨Maryam Muhammad⁩, @⁨Safiyya Danmusa⁩, @⁨Khadyinde.⁩ @⁨Fulani, Shamcydurling🥛🥛🥛,⁩ @⁨きαmiια チiκα💖⁩,@⁨Jamila zozo🧕🏼,⁩ @⁨Fadeelah Goje⁩, @⁨LAILA⁩ @, @⁨Mom Abdulmalik⁩ @⁨MOM MEENAL💃🏼⁩ @⁨Maimuna Ado⁩, @⁨Momyn Afnaan 😊⁩ @⁨Dallua⁩ @⁨Fadila DM⁩ @⁨Zainab Mshinkafi⁩ @⁨🎀ummu~ maryam🎀⁩, @⁨+234 703 972 6966⁩ @maijidda abbas. @SADDIQA BAFFA. Fatima saleh, khairat, karima, princes rasmah, habiba dakare,asiya saidu, marcy, 1, Sukhailah Hassan Umar or Ummu Sadeeq 2, Maryam Adam Abdullahi 3,Souraya,Nana yakaku, Mum shureym, 76uwaniy, Ummu iman, Mrs usman, Mahdauwalu, Anty saa, Ummu suhylerh, Munauwara bature, Zainab Gadaka, Mom Amar, Marry beauty, Maman khalil,, Mummyn ihsan, Itz sury d one, Safiyya Aminu, Maryam G wada Garba, Baby mommy, Rabiyat, Teemah, MamanHumaira, Hadizan baba, Babybluv, Saadatu Ibrahim, Rukayya bala kamilu, Beeky, Buy your chebe powder, Bilkisu isah, Maryam sulaiman, Ayshatu UST, Maman waleeda, Aisha, Khadijat umar said, Fauziyya sidi, Wisdom is a gift , Inna sokoto, Hafsat Ahmad Muhammad, Akori kishiya aci Daula, Mrs fawwaz, Mmn xee, Maryam yahya umar, Maryam Hassan, Hasana Ibrahim, Maimuna baba, Fatima ZANGINA, Mum rukky, SARATU SABO, Innan noor, Sadiya TELA, Maman faty, Dija dankakalo, Aisha yero, Sarauniya Fatima, Maman humaira, Ummu ameera, Umcycool , Umhana kabeer, Maryam Abdul aziz, Fazla ardo, Ummu salsabil, Jiddatul khairr, Rabi at nasir83, Ruquyya saleh, Ami, Nice one, Maman fati, Maman muhammad. _Alkairin ALLAH ya iso gareku cikin salama ababen alfaharina._ ❤❤❤💋💋💋👍🏻👍🏻👍🏻 4⃣3⃣ Idon Aysha k'yam akan ya khaleel, yayinda shikuma ya lumshe nasa, bayansa ya maida ya jingina da kujerar, tamkar mai karanta labarin novel ko maibada labarin wani film dayake shauk'i. Hannunsa d'aya nakan cikin Aysha, d'ayan kuma yana shafa sumar kanta ahankali.😉👍🏻 "Hummm karon farko da Ibraheem khaleel yaji fad'uwar gaba yayin kallon mace, wadda bama takai macenba. aranar dana dawo daga k'asar Tanzania bayan aikin kwanaki 70 danayi a can, kaitsaye nabama su Adams damar wucewa dani gida, saboda matuk'ar gajiya da kasalar jiki dake tartare dani. Ina cikin shauk'in son ganin mo... Momy aranar, saboda sayo mata wata sark'a data dad'e tana so, amma bata samu sayaba, nikuma cikin ikon ALLAH saina samu wannan sark'ar zinari acan, wannan ne dalilina Na d'okin ganinta." "Sabon labari a shafukan tarihina, koda Na sakko amota sainaci karo da tauraruwa mai wutsiyar alkairi........ Da sauri Aysha tabud'e idonta, shima yabud'e, suka kalli juna, cikin turo baki Aysha tace, " nice tauraruwa mai wutsiyar?." Guntun dariya yayi, yaduk'o ahankali ya sumbaci goshinta, "a'a fa, bakiji minaceba? Tauraruwa mai wutsiyar alkairi". Baki Aysha tamurgud'a tana kauda idonta daga kansa, shima kauda kan yayi yana murmushi. Yacigaba da fad'in, ''akanki idona ya sauka kaff yawan jama'ar dake harabar gidan, bak'aramin fad'uwa gabana yayiba lokacin dakika d'ago manyan idanunnan naki kema kina kallona kuna magana keda d'iyar iya hama, bansan yazan misalta miki halin dana shigaba alokacin saboda rud'ani, (small girl like you kina Neman sakani Na rasa tunanina) bak'aramar jarumta nayiba wajen tattare dukkan hankalina namaida kansu Ammah, gaisawa nakeyi dasu ammafa dukkan hankalina nakanki, burina kawai nasake kallonki, amma hakan batafaruba. Bamma sake ganinkiba saida Mamie takawoku domin yimin gyaran d'akina. Hummm bazaki ganeba A'eesha, wlhy lokacin dana bud'e k'ofa wa Anty mamaie naganki zuciyata bugawa tayi tamkar zata fito, saida Na had'a da addu'a gudun kar Anty Mamie ta fahimceni. Inakan Sani nasakaki wankin toilet alokacin, sannan kina shiga natura bishirah kar6omin tea badan inason shaba, saidan kawai nagankine atsanake. Zaman jiranki nazaunayi har kika gama kika fito, lokacin dakika fito kintadda ina latsa waya ko? Bakomai nakeyiba face video d'inki, duk abinda kikeyi inata kallonki ta wayane, harnabaki umarnin cigaba da aikin, da lokacin da kika d'auki bedsheet zaki shimfid'a Na hanaki........ ......."kadai dakamin tsawa". Aysha tayi maganar tana cije la66anta. Murmushi yayi, kawai yana cigaba da zagaya hannunsa akan cikinta. Daban Daka miki tsawarnanba da tabbas babu makawa saikin harbor jirgina alokacin. natsuwarki itace Abu nabiyu daya kuma zuzuta wutar sonki araina, inason mace mai yawan nutsuwa, gakidai k'arama alokacin amma komai naki mai ajine. Bank'i nakasance dakeba tun alokacin, saidai k'ank'antarki tamin katanga dahakan, kuma kodama kinkai girman dazan iya aurenki alokacin to tabbas, tarbarki nace inasonki shine babbar matsalata, Dan maganar gaskiya bazan iyabama. Aysha tace, "sabodami?". " saboda banason raini". 'Yay maganar yana jan hancinta". K'aramar dariya Aysha tayi tareda salute nashi, cikin salon kissa tace, "agaida boss". Dungure kanta yayi yana mata hararar wasa, shima yace, " agaida 6arauniyar zuciya". Atare suka tuntsure da dariya, saida sukayi mai isarsu sannan khaleel yacigaba da fad'in. "Kinsan wani Abu?". " a'a saika fad'a". Bak'aramin kamu kikaiminba A'eesha, abubuwa dayawan gaske sunfaru alokacin, Wanda tariyosu ayanzu 6ata lokacine, amma nasan kema kin sansu, bantsinci kaina adamuwaba sai lokacin dana daina ganinki gaba d'aya. narasa wanda zan tambaya agidannan yabani amsata, kwatsam ranar inacin abinci dainaji musleem Na tambayar Maman yara ina kike?. Sosai maganar tasu taja hankalina, ni saima ranar nasan Maman yara takawoki gidan. Yanda Maman yara take amsama musleem maganganunsa sainaji ban yarda da itaba, domin ni mutumne da inhar zakayi maganar dabata dace da tuharkaba saina ganeka, tawannan hanyar nakanyi saurin cafke mutum mai laifi. Daga wannan ranar nafara bibiyar Maman yara batareda tasaniba. Abinda nafara cin karo dashi akan Maman yara shine mu'amulla da momy a6oye, dakuma mu'amullah da Ummi amarya a6oye, bankawo komaiba sai munafunci irinna 'yan aiki akan masu gida, wannan ne yasakani rashin maida hankalina akan wannan matsalar, burina kawai nasan inda kike, dukda dai Maman yara tace kinje karatu. Acikin bibiyartane nagane cewa zaku bar Nigeria, kuma tabbas ta Abuja zaku tashi. Nayi amfani da wani abokina dake aiki a nan airport, kullum yana cikin sakamin ido akanki, har yagano ranar dazaku bar k'asar, alokacin bana nan, nima nayi tafiya. Yaturamin dukkan bayanai akan tafiyar taku, harda biye-biye wasu k'asashe Wanda bansan miye dalilin hakanba, inda ace aranar dazaku tafi INA nan, nagakuma Kubrah, to tabbas dolene nazargi wani Abu, kuma dolene nafara binciken kubrah, amma sai'aka samu akasin hakan, bana k'asar, kuma bayanai akanki kawai Na nema banda Wanda zakuyi tafiyar tare. Tunda nasan k'asar da aka kaiki nasaka Naufal fara bibiyarki, yana kawomin bayanai sosai akanki, amma baita6a sanarmin akwai wani sirri a tafiyar takiba. Naje Na dubaki a islands batareda kin saniba, sannan bayan kin kammala karatu alokacin narasa mizan baki amatsayin taya murna, koshi Naufal baisan komai gameda keba, kawaidai ina fad'a masa k'anwatace ke. Naje Spain alokacin nida Adams da Joseph, saimuka shiga wani shago domin munabin wani alokacin, babu abinda ake siyarwa a shagon sai irin furanni da kayan masoya d'innan, jinai kawai shauk'i yakamani, da tunanin nesa tazo kusa agareni, awannan shagon nasayi wannan ruwan mai d'aukeda k'ananun kifaye aciki, tareda flower, itakam wak'an dana rubuta ajikin takardarnan awajen Adams najita yanaji, kawai sainaji baitin yayi daidai da shauk'ina, shine narubuta nasaka a sak'on, nabada aka kaima Naufal domin yabaki. Nashiga rud'ani alokacin da baffah yatakura min akan maganar aure shida Ammah, saidai momy bata ta6a nunamin tadamuba, wannan ne yasakani samun k'arfin guywa, naje nasaka Dr Abraham yarubutamin takardar bogi ta rashin lafiya nabama baffah, Alhmdllh daganan nasamu baffah ya dainamin maganar aure, akayi bikin su Sultan. Kinsan wani Abu kuwa? Tun ranar dana fara ganin mama a Jigawa gabana yayta fad'uwa, dominkuwa zallar kamanninki nake gani a tattare da ita, ban gaskataba saida nabud'e wayata nakalli picture naki nakalleta, tun a sannan zuciyata tafara rawa alokacin, naso kauda lamarin azuciyata domin Na d'aukeshi amatsayin maganar nan ta bahaushe *kama da wane bata wane* amma saina kasa. Har muka dawo gida tunanin kamanninki da mama sunkasa 6acemin, daga time d'inne nafara bibiyar mama. Da sauri Aysha tatashi zaune tana zaro ido waje😱, "sabodami kuma?". Maidota yayi ya kwantar, cikin basarwa yace, " saboda inaji ajikina akwai alak'a mai k'arfi tsakaninki da mama, Dan kamanninki yawuce haka kawai, dolene akwai Na jini. Tsaf nasamu labari akan mama A to Z, nata kullawa da kwancewa alokacin, ga aikina kuma a gefe yad'auki zafi. Mafita d'ayace tadace dani alokacin shine maida auren mama da baffah, bak'aramar wahala naciba A'eesha naganin Na maida aurenan, Dan baffah ya amince dana kawo masa shawarar, amma mama dana had'a hannu da kawu bilyamin k'in amincewa tayi Sam, Alhmdllh ummi amaryama taita nata kai kawo akan mama, harta San yanda tayi takai bayanin komen mama ga hajia khaltum, itakuma tazo tasanar momy, momy kuma sukaje kano, wannan shine yazama sila Na komowar mama. Alokacin kuma nafara sanin tabbas akwai alak'ar sanayya tsakanin mama da ummi amarya, dukda basa nuna hakan ga kowa, nima kuma nayi-nayi nasan wani sirri akansu amma nakasa wlhy Aysha, dominsu Na yarda matane masu kaifin basira da k'yak'yk'yawan tunani, sun iya takunsu, sunkuma iya tafidashi yanda komai wanene wajan bin kwankwanto dolene kabarsu. Abu d'aya nafahimta atattare dasu, shine aiki sukeyi akan wani agidannan, saidai kuma wanene?. Wannan shine abin tambayar A'eesha. Harkika koma Canada da zama bansamu bakin zarenba. A Canada ma nata bibiyarki batareda kin saniba, sai lokacin damukayi karo dake, nakumayi hakanne da gayya, Dan ina buk'atar kusantuwa dake, kozan samu sassauci akan k'aunarki daketa azabtar da zuciyata, komai nakeyi saida tunaninki, duk mitsina wlhy A'eesha saikin fad'omin arai, har mamakin wannan soyayya nakeyi, nasan dazan bama wani labarin sonda nake miki wlhy saiya k'aryatani, nikaina daba Dan akaina tafaruba saina k'aryata akwai irin wannan soyayyar. Randa mukai karonnan badan nakai zuciyata nesaba da rungumeki zanyi, amma haka Na daure, alokacin kuma Na fahimci lallai A'eesha na ta girma, tunda har idonta yayi tsaurin yimin murgud'e😊. Lallai kinbani k'yak'yk'awan sak'o alokacin Wanda yazamemin abin tunani dayawan murmushi, bakomai baneba illah murmud'ennan. Cikin waro ido Aysha tace, "kai ya khaleel, amma shine alokacin hardamin mugunta?, harfa nakoma gida bakina baibar zafiba wlhy". Dariya yayi sosai tareda kuma k'ank'ameta, acikin kunnenta yace, " duk cikin sone burin zuciyata, hasken rayuwata." Shiyyasa muna rabuwa alokacin nabada tukuyci wa Naufal yabaki. Idan zaki tuna sak'on farko kifayene kawai k'anan acikin ruwan, sai flower, nabiyu kam tsuntsaye da rings guda biyu had'e da juna, saikuma wani ring d'in daban Na diamond💍. Sannan turare. Alokacin yakamatama ki gane nine saboda wannan turaren, Dan shine k'amshin turarena dakika faraji ajikina ranar Dana dawo, lokacinda Anty Mamie takaiku Ku gyaramin d'aki. Zaune Aysha tatashi, "tabd'i Jan, ammafa ya khaleel kasameni wlhy, ingaya makafa, nata tunani dason tuno inda nasan k'amshin nan, amma wlhy nakasa, gashi nasan tabbas nasanshi, amma nakasa tunawa, dole Na hak'ura, wlhy kadad'e kana wahalar dani", 'tak'are maganar da jan hancinsa." "To Amma, miye karubuta ajikin takardar nan? harna Gaza ganewa." " Bazaki ganeba aii, Dan banyi yanda zaki gane d'inba". *Æ* *_ALLAH ahsni leelahk meeharbI ratam ahsee'A_* _atayicuz aksah iam alitif ekay, asna'knij ad asramrafla nimod eknim akallam ay ALLAH._ _😘(j) halladbA meeharbI._ Wannan shine abinda narubuta aii ko?. yay maganar yana nuna mata tafin hannunsa. Da sauri Aysha tagyad'a kanta tana tashi zaune sosai. Murmushi yayi, yace to kar6i pen d'innan, kifara kwafar rubutun daga k'arshe, ma'ana k'arshe yakoma farko, farko kuma yakoma k'arahe, kiga mizai bakai". Kar6a Aysha tayi, tagyara zama sosai tayi copy d'in rubutun tafin hannun nasa. Ido tazaro tana kallon abinda yabata kai tsaye, tajuyo cikin mamaki tana kallonsa. Shima idonsa nakanta, ya kanne mata ido d'aya yana murmushi. K'ara maimaita karanto rubutun tayi afili, tamkar mai bitar karatu agaban malaminta...........👇🏻 Æ _A'eesha matar Ibraheem khaleel insha ALLAH._ _ALLAH ya mallaka minke domin alfarmarsa da jink'ansa, yake fitila mai haska zuciyata._ _Ibraheem Abdallah (j)😘_ Ayasha nagama karantawa saita fad'a jikin khaleel kawai tasaki kuka. Bashida za6in daya wuce kar6arta, saiya k'ank'ameta shima yana murmushi, cikin lallashin buga bayanta ahankali yace, "sorry kinji sholyna, dolece tasakani 6oye miki kaina, Dan inhar nanunama duniya kece za6ina, to tabbas babu makwa sai an cutarmin dake, sai mak'iyana sunyi amfani dake wajen ruguza komaina, wannan ne dalilin dayasa na nuna bijirema aurenki alokacin da baffah yataramu. Ashe hakan alkairine agareni, domin dana nuna inasonki, momyce zata fara salwantar dadukkan burina, dakanta zata tarwatsani alokacin, A'eesha na yarda da momy, amma taci amanata, matsayin uwa mahaifiya nabata, Ashe kuskuren hakane, nadad'e ina fuskantar wariyar launin fata daga gareta da innah jummai amma banta6a fasa bak'inba, nadad'e dakula momy tafison yaranta mata akaina, amma ban fassara zancenba. Nadad'e ina mamakin k'aunar Anty Mamie da shauk'in son kasancewa da ita dake d'awainiya dani, amma ban ayyana komai arainaba, A'eesha miye dalilin momy na aikata hakan? Miyasa tarabani da mahaifiyata? Mina tare mata tadawo farautar rayuwata? Wane burine yakai momy shiga k'ungiyar ta'addaci Irin wannan? Bayan babu abinda tanema tarasa arayuwarta?. A'eesha wanene zai fassaramin dukkan wannan k'ullin? Wanene zaibani amsar tambayoyina?, miyasa kika ringa aikata abinda zan zargeki ke kanki?". Mik'ewa Aysha tayi tana murmushi, dukda batajin k'arfin jikinta haka tadake, kallon ido cikin ido sukayi itada khaleel dake binta da kallo. Ta d'aure fuskarta tamau, cikin salon Aysha na jarumtar zuciya tace, "hajia laurah yakamata kama dukkan wannan tambayar? Tabbas amsoshinsu suna wajenta, itakad'aice mai amsoshinsu, bakai kad'aiba, kowama wannan yakesonji, minene dalilin faruwar KOMAI???????!!!!". Nikuwa bakomai yasakani yimaka wasu abubuwanba sai gane cewar kasaka ana bibiyata, tasaki murmushin basarwa. Ya khaleel nasan kaine kasaka Zeenat bibiyata agidannan dadukkan motsina, sannan kaine kasaka Afrah bibiyata awajen aiki, nasanka kai mutumne mai kwakwalwa da azabar bin kwakwkwafi Wanda kwazon aikine yad'oraka akan wannan nasarorin da kishin k'asarka da al'ummarka. Amma tabbas tunaninka baita6a kaimaka cewar Aysha da ido d'aya take barci agidannan ba. Ya khaleel nafara sonka aranda kafara sona, nata dakon soyayyarka kamar yanda kayita fama datawa, saidai ni tsoro da fargabar kafi k'arfina tahanani koda kwakwkwaran motsi na Isar maka da sak'o koda na sirrine Wanda kai kadinga min. Ya khaleel tun ina k'aramata ni mutumce mai bak'incikin RASHIN GASKIYA, banason munafuki ko azzalimi, inason rayuwar mutum tsayayye mai ra'ayin kansa, maiyin Abu kaitsaye batareda son birge wasuba ko k'untata wasu. Kaf halayennan saina samesu agareka, acikin d'an tsukun zaman danayi dakai aganin farko, dakuma abinda yayta faruwa agidannan narashin jituwar momy da Anty Mamie, tun alokacin nafahimci tabbas akwai 6oyayyan Al'amare tsakanin momy da Anty Mamie, Dan tafi nuna zafin kishinta akanta fiyeda ummi amarya. Naso samin damar bincike amma sai aka datseni ta hanyar barin k'asar dani. Tun randa nabar k'asarnan nad'auki aniyar tarwatsa hajia laura da hajia khaltum, daduk wani azzalumi dake kark'ashin mulkin masarautarsu, k'ank'antata baisa narasa kwarin guywan gaza Neman 'yancin mulkin mallaka da wasunmu ke samuba. _ya khaleel mata suna cikin bak'incikin rayuwa a nahiyar Africa, wad'anda suka samu damar yin aure basu tsiraba, matar k'auye kullum tana cikin wahalar bautar mulkin mallaka na d'a namiji, abincin kirkima baigama isartaba, basuda aiki saina d'aukar ciki da haihuwa, gashi babu wani tallafin da yaran ke samu, sukan saka namiji makaranta, amma mace data tasa sai aimata aure, shekara d'aya saikaji ayuriyiri ta haihu, kafin wata shekarar tadawo ankuma samun wani cikin, shekaru uku kad'ai zakabata agidan mijin idan kakoma bazaka ganetaba, saboda tagama lalacewa tafita hayyacinta, babu abinci babu kwakwkwarar kulawa gamijin, daganan sai afara kiranta tsohuwa, itakanta zuciyata ta raunana, atunaninta shikenan tagama yayinta, saikuma 'ya'yanta, musamman idan yakasance 'yarta tafari macece, saikaji ana fad'in kwana nawane itama tazama surukar wani. Hummm._ _Dazaka duba, duk k'auyancin k'auye saika samu mai suyar kifi, mai tukubar nama, sannan tebirin mai shayi, kuma kowanne saiyayi sana'arsa arana kuma tak'are._ _shin abin tambayar anan, suwaye ke siye tulin bread da indomin tebirin mai shayi? Harda kwai. Sannan suwaye kecinye gasashshen naman tukubar mai nama?, sannan suwaye kecinye kifin tebirin mai kifi?._ Amsar d'ayace, mazan k'auyen. _kullum da an idar da sallar isha'i saika gansu zagaye dawad'an nan tebiran, k'ilama harda k'arin mai soya doya da kwai da kaji agarin, amma kafin safiya duk ancinye, amma dazaka bincika babu matar mutum d'aya acikinsu dataci wad'annan kayayyakin, watama masarar tuwo ko dawa kad'ai aka bata, ita tayi wahalar k'ud'in nik'a dana daddawa dad'an barkono, koda babu manja da isashshen magi haka zata kad'a miyar suci itada yara su kwanta, mijin yadawo yana mazurai, bayan yagama kacaccala arayuwarta a tukubar mai kaji._ _da'an kwana biyu kuma yahango wata saikaji zancen zai k'ara aure, sukuma iyayen babu tunanin komai sud'auka su bashi waidon suhuta daganin wannan d'iyar tasu tana yawo agari ana zaginsu, kaico dawannan bahagon tunani._ _da tsautsayi zai gifta yasaki matar tasa, kwana biyu takoma gida saikaga tamurje takoma d'as yarinya d'anya sharaf da ita, da tsohon mijinta yaganta saiya rikice dafara hura hancin son komawa cikin masu takarar Neman aurenta._ " kasan miyasa hakan ke faruwa kuwa?". Kamar sakarai khaleel ya jinjina mata kai alamar a'a. Murmushi Aysha tayi, tacigaba da fad'in. ''Alokacin aii ya gama durk'usar da waccan amaryar daya aura yasaki wannan dominta, itama ya maidata tsohuwar k'arfi dayaji, kaga dole yakoma hange-hangen watakuma, koda ace waccan tsohuwar matar tasa bata koma garesaba, zai nemi auren wata kuma, dawad'annan abubuwan kullum aketa kashe rayuwar matan k'auye, da'an samu mai raunin zuciyata saita 6alle tazo takafa dabar 6arna da jagorancin tarwatsa rayuwar sauran 'yan uwanta dasuka tsinci rayuwarsu arin halinta. _Macen binni kuwa zaka sameta daci dasha, da suttura, amma babu kwanciyar hankali, koyaushe miji namata dodorido da sake auro irin jinsinta na mace domin k'untata, sannan yanacan awaje yanacin zarafin mutuncin 'Yar uwarnan tata mace a hotel ko'a office. datayi maganar Neman 'yanci yace zai saketa yamaye gurbinta da 'Yar uwarta mace, kullum mazan birni cikin had'a wutar masifa suke a tsakanin mata, dakaga mace tadage tana haki da hura hanci da taune harshe wajen tanki intaka to akan namijine._ Sannan kuma sai'a ringsla samun mata 'yan jari hujja irinsu hajia laura da hajia khalum suna safarar matannan domin kaisu k'ashen duniya amatsayin hajar siyarwa mafi tsadar farashi da yalwatuwar riba mai tsoka. Karka d'auka gwamnatin k'asashen Africa da jami'an tsaronmu basusan da wannan gur6atacciyar sana'arba. Sun Sani sarai, sunkuma son anayi. Kasan miyasa suka gaza d'aukar mataki kuwa?. Tasaki guntun murmushi mai ciyo, sannan tacigaba. Sungaza hanawane saboda suma suna amfanuwa da wannan kasuwancin, Koda amfanuwa ta fannin aljihu, kokuma amfanuwa ta fannin biyan buk'atunsu, da wannan kud'in cin zarafin Matan suke yima matayensu nagida hidima, dasu suke ciyar da 'ya'yayensu dake killace agida, dasu suke jar fata da mazurai acikin al'ummarsu, sannan dasu suke amfani wajen keta martabar sauran Matan dasuke killace agidajen iyayensu ko mazajensu, tunda anmaishe da mata 'yan tsaki, da'an watsa mana tsaba saimu fito muna tsatstsaga. Abin bak'in cikin bamuna tsatstsagar tsabar bane domin son murayu cikin salama, kosan mu k'arfafa rauninmu wajen Neman 'yancin ketama Junanmu mutunci, a'a muna tsatstsagar wannan tsabarne domin gyara halittar jikinmu ta daidaita mu burge mazajennan dasuka watsa mana tsabar, munyi hakane domin gobe mufito cikin nagartar burge wad'annan mazajen, haka zasuyita watsa mana wannan tsabar munaci nuna gyara kammu dominsu, ahaka har rayuwarmu ta lalace mukoma jagororin ingiza saida mutuncin sauran mata nak'asa damu. Inda za'a zauna tebirin tattaunawa saikaji ance mata sun lalata duniya, mata sunfi shaid'an shed'anci, shin idan mace shaid'aniyace? Dawa take shaid'ancin? Kuma danwa take shaid'ancin?. Wad'annan tambayoyin nakeasn duniya damazan duniya subani amsarsu😭. Ya khaleel Kasan kuwa d'umbin mata dake rayuwa cikin k'unci da bak'inciki kuwa?, kullum ana k'wasar yaranmu ana kaiwa saudia cibiyar addinin islama dasunan aiki amma hajace ta tallatarwa wa mazan wannan k'asa, kaimu akeyi domin k'ask'antarwa da tozarta Kimar 'ya mace da mutuncinta, ana amfani da rauninmu wajen wargaza dukkan martabarmu, shin bakwa tunanin raunin mazajen k'asarmu wajen sakacin rik'e mata agidajen aure yake kawo wannan kwad'ayin na mata Masuson tafiyar wasu k'asashe bayan angama yaudararsu?. Kuje kuga Matan dake zuwa saudiyya danufin aiki acan, a k'ask'ance suke, marasa daraja ake kallonsu, kullum cikin mulkin mallaka aikatau da fataucin mutuncinsu ake, (ita batayi zaman aureba, bakuma tayi bautar ALLAH ba cikin nutsuwa) haka ake binsu kamar tumaki dagudu ana kamawa, why? Ya khaleel. Mata why dabazaku farkaba?.😭 Inhar k'asa irin saudiyya bazata San mutuncin daraja rayuwar 'ya'ya mataba to bansan ina mace zataje tasamu mafakaba aduniya ya khaleel, inhar za'a iya tarwatsa mutuncin mace a k'asa mai tsarki to tabbas babu wata k'asa da 'ya mace zataje ayi tunanin dawowarta da mutuncinta. Inhar dagaske kakeyi ya khaleel, inhar da gaske kaid'in ka banbanta da sauran jami'ar tsaro dake k'asarnan to katashi domin ceto rayuwar mata dayawa da'aka salwantar da sanin iyayensu koda rashin saninsu, da yardar Matan koda tilastawar azzalumai 'yan jari hujja irinsu hajia laura, ninan namaka alk'awarin taimakonka da sirrika masu yawa danake dasu batareda sanin kowaba😭😭😭😭😭😭. Tak'are maganar dafashewa Dama tsanancin kuka mai cin rai da zuciya. Da Sauri ya khaleel yataso yatareta saboda tangad'in hajijiyar fad'uwa datakeyi. Cikin kakkasar murya tace, "karka ta6ani saikamin alk'awarin zakayi, saikamin alk'awarin bada kwakkwkwarar gudunmawa, saikamin alk'awarin fara nuna misali akan momy, karka duba wahalar raino datasha akanka, karka duba shak'uwar dake tsakaninka da ita. Katuna 'ya'yanmu masu tasowa, katuna wannan cikin dake jikina indan nahaifi mace wace irin rayuwa zata tsinci akanta?, katuna da su momy sunci nasarar tarwatsa rayuwata wane bak'inciki zaka tsinci kanka.............? Bai bari ta k'arasa ba yace..............✍🏻 😱😱😭😭💋💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤mata ku farka *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ *_kud'in nadabbane agareni, dolene gaisuwarkuma tazama tadaban, ina k'aunarku ainun, domin munzama 'yan uwan juna, ALLAH yabar mana zuminci 'yan group d'ina, my diamonda d'ina, kune gold d'in bilyn Abdul😉😉😉👍🏻👍🏻👍🏻💋💋💋💋😍😍😍😍❤❤❤_.* hajara gambo (uwargida), fatima Muhammad (mom Ammar), Zainab Zubairu Maitama( Zeezu byr Mytama, Ummu abdulnasirr(Ainah Buhkari), ummul Ahmad momy twice, khadija Auwal(maman Farhan), Hassernath Jalingo, zahra abbakar (Ummu unborn), Sadiya Aminu, 💅🏼teemahcute💅, Aysher Bello, Nanerh🧕, Beentahmk, khadija Muhd (Dee), Deeyerht, NANA YAKAKU, AISHAT UST, preety zee🧕🏼, zainab Gadaka, 👑💅🏼Ummu iman, Mrs usman, Beeky, mummyn ihsan, Mmn zeey baby, rahma salihu, Xynab, Hauwa magaji, Falmata Ibrahim, Falhat, xaenab ibrahim, Mmn walida, Fatee Ibrahim umar, ∂єєנαян✍, Smart lady, maman zeey, Falmata Ibrahim, Maryam Lanko, Zakiyat, Jamila Fika, Saddiqa musa, Aeasher2😍😘, Rukayyah R K Y😍🤝, Nanah😍, Deeyerht, Ameera😘,Rukky, Aysha Mustapha, Aeesha Isah, Zainab Ibrahim, Dr hairas H~, Mmn Khalid da sajida, RUKAYYA BALA SURU, binta a abubakar, Aysha rabiiu, khadija Mustapha, Bilkissu💋💄, Aisha Dantanko, Bilkissi Niger , Maman Umar, Aisha Awais, Meenasko, Maman sudais, Ommeetah, Hafcee, Amina lawal, Bilkis , Maijidda (mamin mua'azzam), Meenasko, Hadiza (mom yasmin), Teemah yola💅🏻, Asmy smiler , Hafsat Ahmad, Akori kishiya Aci daula, Aysher, Mom Afrah😍, Ummun Hajiya, Surayya Auwal, Eashan mamanta😍👸, Hassanat ismaeel🧕, *Muneerah Muhammad (M3)*, Aaeesha, xeeyhert Muhammad , Lawisa sani, Zeetah😘, Mrs Shariff, Mom aysher, faryderh ❣❣, Sadiya abdulwaheed, Deedee gwarzo, Zainab maman zainab. _bilyn Abdul ta gaisheku k'yauta😉👍🏻_. 4⃣4⃣ "Kinga nutsu muyi magana mana". Cikin kuka tace, "bazan ta6a nutsuwaba ya khaleel, sai mahukuntan k'asarnan sunyi tsawatarwa akan 6arnar dake faruwa ga mata, gidanjen aure bamu tsiraba, kullum mace tana fama da damuwa, idan zaka zauna da mata dubu to wlhy d'ari tara acikinsu dukzasu fad'a maka suna zaman aurene saboda 'ya'yansu, ammafa badan jindad'i agidan aurenba, kullum mace saidai ta karanta tattali da soyayya a cikin novels, shiyyasama wasuma suke ganin zak'ewar writers wajen rubuta yawan tattali da soyayya anovels, sabida su basa gani agidajen aurensu, shiyyasa mata sukafi kowa yawan kallon films, saboda anan kad'ai suke ganin ana sayyaya maiban mamaki, ba'a barmu agidaba, ba'a barmu amakarantaba, lectures da students 'yan uwanmu kullum suna farautar mutuncinmu, sunsan dukkan hanyoyin dad'in baki dazasubi domin janye hankalin yarinya su lalatata, lectures kullum suna kadamu a jarabawa idan mun hanasu kammu, sukan bama wadda tabiya buk'atarsu koda bata cancanci samun wannan makinba, ta wannan hanyar anruguza rayuwar wasunmu bada sonsuba, a offices ba'a barmu ba, kullum manya nasama damu farautar rayuwarmu sukeyi, idan kin bada had'inkai a k'ara miki girma, idan kin bijire a k'ask'antar dake ko'a koreki daga wajen aikinma gaba d'aya. K'ananun makarantu Na primary da secondary nanma mata basu tsiraba, komin k'ank'antarki sai'an samu malamin dazai dinga bibiyar mutuncinki, kan hanya kullum taremu ake ana mana fyad'e, yaranmu da manyanmu, amma koda ankai kotu babu wani Abu da alk'alan sukeyi, k'arshema sai a koro k'arar ace bakuda shaidu, idan kuwa an yanke masa hukuncin to bazai wuce Na shekaru uku ba, kuma harda tara, daya biya taran shikenan sai'a sakeshi ya tsira, itakuma ya haddasa mata bak'incikin dahar tamutu bazata ta6a mantawaba, hakama iyayenta, yanzu kuma abin bak'inciki anmaidamu tumakin ciniki akowacce kasuwa, daidai farashinka daidai aljihunka, dakabiya saika kama, shikenan kasamu dabban tirkawa, kullum kabata dusa domin tattalinta, itakuma yunwa da kwad'ayi yasakata lashewa, ribarka sada ita kazuba kud'in aljihu, kokuma kaita ga mahauta su yanka maka, aimaka filla-fillah da namanta kazo ka soya kanaci ahankali kana nishad'i. Haba ya khaleel, shin maza sunmata uwace ta haifesu? Inhar uwa nada daraja a idanunsu baikamata sudunga keta mutuncin sauran mataba, kosun manta sun haifi 'ya'ya matane? Sun manta matane abokan rayuwarsu? Sunmanta Nana Aysha macece? Sun manta Aminatu (mahaifiyyar Manzon ALLAH s,a,w) macacece? Sun manta Nana Maryam macece?, sun manta Nana fad'ima macece?, sun manta Nana khadeejah macece? Sun manta..... Sun manta dayawa?, shin miyasa darajar kimar mata tafad'i awannan zamanin???. Mata wannan tanbayar daku nake, kune yadace Ku amsata ba mazaba, domin kune lalacewar kanku, banta6a ganin gidan karuwai Na mazaba, banta6a ganin namijin da suturarsa ta mutunci ta banbanta data banzaba, haba mata, atunaninku shigar banzace wayewa? Atinaninku tallata kankune mutunci?, kwad'ayine da son asani yajefa mata duk cikin wad'anna had'arin Na rayuwa, kuzauna kuyi tunani, kuyi tunanin gyarawa sannan maza suji Shankar keta mutuncinku, kucirema zukatanku kwad'ayi dason burga inhar kunason tsira da muncinku wlhy, idanfa 6era nada sata, daddawafa nada wari, sai bango yatsage k'adandagare kesamun gurin kwana, duk Wanda yakwana lafiya shiyyaso, wani lokacin laifinmu yafi namazan yawa, bazaki ta6a ganewaba saikin nutsu akan kura kuranki.............. Da sauri yatareta tafad'o jikinsa, saboda juwar datayi hajijiya da ita, ak'asa suka zube, rungumeta yayi dak'au yana shafa bayanta, muryarsa a tausashe yace, "kiyi hak'uri hakanan A'eesha, tabbas da ace mata nada irinki dabasu tsinci kayinsu ahalin dasuke cikiba yanzu, namiki alk'awari insha ALLAH zanyi amfani da aikina wajen kawo gyara, koda ban gyara dukaba zanyi iya bakin gwargwado, nasan baza'a rasa mai irin burinaba dazai d'ora daga inda natsaya, ki kwantarmin da hankalinki, kinga bake kad'ai baceba, banason babyna yafara fuskanta damuwa tun yana ciki kema INA buk'atar lafiyarku kinji. Kanta ta jinjina masa, tana cigaba da zirar da hawaye, shikuma yana share mata, saida yaga tadawo cikin 'Yar nutsuwa sannan yad'auketa suka nufi d'akinta, shirin barci sukayi suka kwanta bayan khaleel yamusu addu'a, dukda yana buk'atarta haka ya hak'ura danya kula yau masu rigimarne akusa, shi baima ta6a tunanin haka A'eesha takeba, Ashe itama akwai zuciya, jiyayi k'aunarta nakuma ratsa dukkan sassan jikinsa da 6argo, ya furzar da huci tareda k'ara k'ank'ameta😉💋. _____________________________ Kwance take tana kallonsa haryagama tsane ruwan jikinsa, ya d'akko mai yadawo bakin gadon kusada ita ya zauna, idonsa akanta yad'ora hannunsa Na dama bisa gishinta. "My sholy tunda zazza6in ya sauka kidaure kitashi hakanan kiyi wanka ko?." Yatsine fuska Aysha tayi tana d'ora hannunta kan nasa, murya a sanyaye take magana, ''ALLAH Sadauki banajin tashinne, bank'i nawuni kwanceba batareda nayi komaiba, gaba d'aya sainaji jikina a kasalance." Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ''karki damu komai zai dai-daita idan cikin yay kwari kamar yanda Amman tace, amma kuma ahaka da kikemin kurin komawa aiki?". "ALLAH sadauki sonake nagama bautar k'asana cikin salama, kagafa wata biyu kacal ya ragemin". " hakane, insha ALLAH kuma zaki k'arasa kinji. tashi muje namiki wankan mu shirya, karya zam mukad'ai ake jira kuma". "Kai sadauki, ina zamujene haka wai? Kuma duk mutanen gidan?". " basai nafad'aba, kedai kawai tashi Na shiryaki zaki gani aii." Batace komaiba ya taimaka mata ta sakko, kayanta tacire ta d'aura towel. Yace muje to. "A'a kayi zamanka Na hutashsheka, gamma naringa k'arfafa jikina, yanzu kwatsam tafiya ta taso maka wazai dinga tattalina haka? gamma Na daureda koyaya inayin wasu abubuwan ko?." Kansa ya jinjina mata yana murmushi, azuciyarsa yana jinjina wayo da hikima irinnan Aysha, ita komai nata dabanne. Mai shima yashafa, sannan yafice d'akinsa domin shiryawa. Itama Aysha bata 6ata lokaciba tafito, adaddafe dai tad'an shafa mai, tasaka doguwar riga ta material, kayan sunmata k'yau, ta d'aukko madaidaicin gyale tayi rolling, tsaf tafito kamar wata balarabiya, tana cikin zuba d'an abinda zata iya buk'ata koda sun fita a jakka ya khaleel yaturo k'ofar yashigo da sallam. Bata d'ago ta kallesaba amma ta amsa masa sallamarsa. tsaye yayi abakin k'ofa ya jingina da bango yana kallonta, tamasa k'yau sosai, hardai yakasa hak'uri ya tanka. "Yanzunan da wannan shigar zaki fita?". d'agiwa tayi ta kallesa, sanye yake cikin uniform d'in aiki, sunyi masifar zaunamasa ajiki, tajanye idonta ahankali ta maida kan jikinta, " haba sadauki miye aibun wannan shigar tawa?, ko inafa Na jikina arufe yake, tafin hannuna da fuskatane kawai ake gani. Guntun murmushi yayi, yatako ahankali har zuwa gabanta, jawota yayi jikinsa ya rungumeta, a cikin kunnenta yace, "bazaki ganebane kedai, ina kishin aganemin wannan k'yak'yk'yawar surarne sholyna, ALLAH ya halicceki domin nine kad'ai, danhaka Na haramtama kowa ganeminke." Cikin jin dad'in kalamansa tashafo fuskarsa, akasalance tace, "ngd Sadaukina, bara Na canja to". ''No barsu, amma next time akiyaye". "Angama boss", tafad'a tana kanne masa ido d'aya, da salute nashi". Shima k'amewa yayi yay salute nata. Atare suka tuntsure da dariya, yakama hannunta suka fice suna cigaba da dariyarsu, idan kagansu dolene su burgeka. Cikin gida suka shiga, afalo duk suka tadda ahalin gidan, sunyi cirko-cirko suna kallon innah jimmai daketa zuba tsiya, ajiya labari ya isketa, da yamma ta'iso Abuja, saita kwana gidan wata mata dasuke mutunci, shine yau ta k'araso nan gidan domin jin ba'asin kama mata d'iya da'akayi. Daga Aysha har ya khaleel, babu Wanda ya kalli ko inda take, khaleel ma saiya nufi dining inda su sultan ke zaune suna breakfast shida muhseen da Ramadan. Duk gaidashi sukayi, muhseen yace, "ya khaleel wai baffah yahana atakama tsohuwarnan birki, please, kamana maganinta mana". d'an ta6e baki khaleel yayi, yad'au mug d'in shayi yana k'ok'arin had'a shayin, " to inbanda abinka muhseen, tunda baffah yace abarta, aii sai kowa yazuba mata Na mujiya, lokacintane tayi, anjima kad'an koda kud'i aka had'ata tayi tari bazatayiba. kaga mik'omin kularnan tagabanka Ramadan, minene aciki?." "Fankasunefa yau Anty Mamie tayi agidan, ALLAH nifa banason abinnan". " saika zauna da yunwa aii, koka saka matarka ta girkamaka wani abun, ai su Mamie nema suka barku, kunyi aure amma har yanzun kuna nane dasu suna wahalar girka muku abinci, Ni kaga Zubamin guda uku". Dariya mujahedeen dake k'ok'arin zama yayi shida Sultan, Sultan yace, "to ya khaleel kaimafa kana cikinmu, tunda gakanan a tebirin gandu". Guntun murmushi yayi yana kur6ar tea, idonsa akan Aysha dake zaune kusada Anty Mamie tana 6ata fuska, Anty Mamie nabata abinci abaki, da'alama tsareta akayi kawai. Ya kauda idonsa yamaida kan Sultan, " aini kasan lalurace yaro, dan matana batada lfyne kawai, amma soon bazaku ganniba anan". Dariya sukayi gaba d'aya, wadda tak'ular da innah jummai, azatonta da'ita suke. Dawowa tayi Inda suke tana zaginsu, babu Wanda yama kalli inda take acikinsu, bare tasamu amsa, saima cigaba da firarsu sukayi suna dariyarsu hankali kwance. Sai kawai innah jummai tafashe da kuka, wai baffah da Ammah Nagani su Khaleel Kecin zarafinta, dama tasan Ammah Ba sonta takeyiba, kaza......kaza...haka taita surutai marasa d'ad'inji, babu Wanda yay koda tari barema ya tanka mata. Har kowa ya kammala abinda yakeyi suka fito, motoci duk suka shishshiga, ganin haka itama innah jummai tabi ayari.🤣👍🏻 ********** Tafiyar mintoci kad'ance takawosu station d'in su khaleel, kowa yayi mamakin miyasa ya khaleel zai kawosu nan?. Ganin ya khaleel ma'aikatan wajen sukayo caaaa akansa, sai k'amemasa sukeyi da Salutes nashi, suna tambayar ya jikinsa. Su Aysha dai sai kallon ikon ALLAH sukeyi da girmamawar da khaleel kesamu daga ma'aikata nak'asa dashi, kuma sunsan wannan yana cikin adalcinsa da sassauci. Su Kansu sai gaidasu akeyi cikeda girmamawa, kuma abin birgewa musulmai da wad'anda ba musulmanba kowa girmamasu yakeyi. Ana cikin haka saiga Adams, saida yafara k'amewa da salute Na ogansa sanann Yakoma kan surukansa, ya gaishesu cikeda girmamawa. Suma cikin fara'a suka amsa masa, da tambayarsa yadawo aiki?. Yace eh. Su Joseph ma duksun k'arasu, sun gaida su baffa sannan suka maida hankalinsu wajen khaleel dake magana. Adams akaisu hall d'incan su zauna, ina zuwa, youseef ina buk'atar ganawa da momy". Yay maganar cikin d'acin murya. "OK sir". Youseef yafad'a a girmamame. Tafiya yake cikin karkashi da sassarfa, zuciyarsa Na harbawa da sauri da sauri, fuskarnan tamkar baita6a sanin miyema dariyaba. Youseef yabud'e d'akinda hajia babbah take. Kallo d'aya khaleel yamata ya kauda kansa saboda tashin hankali, dukta fita hayyacinta saboda k'aniyarsu da'akeci. Daka ganta kasan atsorace take, duk gadararnan da tink'aho yagudu, aii bakin rijiya bawajen wasan makaho baneba, amma kunsan mutuniyar takufa, ganin khaleel saita d'auka yazo fiddatane, danhaka saiwata sabuwar d'agawa ta iso zuciyarta, tawatsa masa muguwar harara maicikeda tsana da bak'inciki. Kauda kansa yayi yana k'ara tamke fusaka, yajuya yafita ahankaki, da yatsu biyu yayima taheer wata alama. Kai kawai taheer ya jinjina masa, danya gane miyake nufi. Tafiyarsa yacigaba dayi ahasale. Su taheer d'aukar hajia babba sukayi aka fito da ita, saitaji kanta yak'ara fad'i da girma, aidama tasan dolene khaleel yazo ya fiddata, kobayaso tasan sai baffah yasakashi dole. Wani k'aton d'aki aka kaita, suna ajiyeta suka fito. ................wata bajinta da k'arfin zuciyane ke k'arfafashi, sune suka taimaka wajen maidashi Ibraheem Abdallah d'insa jarumi, wanda baya d'aukar raini, cikin bajinta da jarumta jininsa ke zagayawa adukkan sassan jikinta, babu abinda fuskarsa ke nunawa sai fusata da harzuk'ar fushi. Tunda yashigo d'akin momy kebinsa da kallo, bata ta6a ganinsa awannan yanayinba sai yau, lallale dolene kowa yadinga fad'in yana tsoron Ibraheem, ita kanta zuciyarta sai bugawa takeyi da k'arfi. Da k'afa ya shuri kujerar dake kwance ak'asa yamaidata zaune dai-dai, cikin k'asaita irinta gadarar jarumta yazauna tareda crossing k'afarsa d'aya kan d'aya. Momy takalli kanta ak'asa zaune, wani d'acine ya ziyarci zuciyarta, wai itace a k'asa Ibraheem Na zaune asama cikin sarautar gadara. Zatayi magana ya dakatar da ita. "Kinutsu, anan bada d'anki kike tareba, da Ibraheem Abdallah (j) kike tare, shikuma baya d'aukar raini awajen aikinsa, so ki kiyaye". Cikin kwalo idanu waje momy tace, iyee, lallai Ibraheem, wuyanka ya Isa yanka, ka kalli tsabar idona kafad'amin haka?. Kauda kansa yayi gefe, yace, " hajia laurah, ina fad'a miki kinutsu!!!!!!". Yay maganar amatuk'ar tsawace. Arajane hajia babba tad'anja bawa, baki bud'e idanu waje😨. Saikuma taja tsaki tana watsa masa harara, "kai Ibraheem kashiga hankalinka, wlhy zan sa6a maka kammanni". " ban hanaki hakanba kuwa, domin har yanzu kinada kimar amsa sunan uwa a idona".... "Mtsoowww aikin banza, ina amsa sunan uwar takane kakecin zarafina ayanzu?, nagodema ALLAH daban 6ata lokacina wajen rainonkaba, wlhy Ibraheem danasan haka zaka zamema rayuwata, datun randa kazo duniya zan shak'eka kamutu, dabakazo gabana kanamin gadara da d'agawaba kuwa?. Murmushi khaleel yayi mai ciwo, ya furzo huci mai zafi daga bakinsa, k'ok'arin maida kwallan data cika idonsa yayi, sannan yajuyo yana kallon hajia babba da razanannun idanunsa masu matuk'ar kwarjini da kad'a hantar mara gaskiya. Aiko hajia babba ta razana ainun, dole tajanye idanunta daga kallonsa. Cikin kakkausar murya yace, " hajia Laurah! Tabbas da ace kasheni kikayi alokacin sainafi jin dad'in hakan, dace kin kasheni alokacin dabanyi rayuwa da wannan zilwa jahainin fuskar takiba, daban rayu cikin gur6atacciyar tarbiyar azzaluma irinkiba, wlhy hajia laurah, saikin gwammace kasheni kikayi akan barina araye dakikayi, ninan Ibraheem Abdallah, saina sakaki yin nadama keda ire-irenki.... Da k'arfi ya tafa hannayensa. Saiga Adams yashigo, da ido yamasa magana. Adams ya jinjina kai yana komawa da baya. Babu dad'ewa saigashi yadawo shidasu baffa, yajawo table dakecan gefe ya maido gaban khaleel, jakkar hannunsa ya ajiye, yashigo warwareta akan table d'in. Bindugune dawasu wuk'ak'e aciki. Su baffah sunyi cirko-cirki suna kallon ikon ALLAH, da tunanin mi khaleel zaiyi dawad'annan makaman. Shikam har yanzu yana zaune cikin k'asaitarsa, sai hura hanci yakeyi cikin zafin rai. Bayan Adams yagama khaleel ya kallesa, akausashe yace, "ina buk'atar khaltum anan wajen." "OK sir!, angama". Bindiga khaleel ya d'auka, yad'auki bullet hud'u yazuba acikinta. d'akin yayi tsit, kowa fargabace ta kamashi, kardai khaleel yakashe hajia babba, su Anty zuwairah duk sunyi k'asa da Kansu suna kukan zuci, kokad'an basuga laifinsaba, sunsan akan dai-dai yake, tunda akan aikinsa yake, summafi jin zafin momy da laifin data aikata, Su Hasnah ma sun kasa kallo, duk cusa Kansu sukayi acinyoyinsu suna kuka ahankali. Zuciyar inna jummai tashiga tsitstsinkewa dan tsoro. Ana haka saiga Adams yataso k'eyar hajia khaltum, ita harma tafi hajia babba jigata, duk raunukane ajikinta, sai layi takeyi ahanya tamkar mashayiyar giya. Rakwam tazube gaban khaleel kusada Aminiyarta. Khan khaleel na a d'uk'e. Kusan mintuna 3 sannan yad'ago idanunsa dasukayi jajur saboda 6acin rai, yazubasu akan hajia babba..... Nunata yayi da bindigar ya d'ana kunamar, cikin kauda kai yace, " zan kiraki da momy akaro Na k'arshe, momy miyasakaki aikata dukkan wad'annan abubuwan?. wlhy inhar baki warware wannan k'ullinba saina tarwatsa kanki da wannan bindigar, bawasa nakeba, bakuma burga nakemikiba ko tsoratarwa, abinda ke raina nake fad'a.............✍🏻 _please kuyi manage da wannan, yau ina busy sosai wlhy._ *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of expert & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ *_Gaisuwarku ta dabance sister, ALLAH yak'ara haske a rubutunku kuma, yasaka albarka arayuwar 'ya'yanmu baki d'aya, ngd da bibiyar buk d'innan dakukeyi, ALLAH yabar zuminci._* Aysha Manshat (Ummu Zunnurain) Ummu Basheer, Maman Khady, Kdeey, Reefat yahaya, Aysha Umar Abubakar, miss xoxo (tawan nikad'i😉) Aneesa Abubakar rimi, Ummah shehu (Mrs Hameesu Taura) Maryam (Ummu Affan), Bily Sarki, Bily s fari. _ALLAH yasaka albarka da haske arayuwarku._ _ban manta dakuba kuma 'yan groups d'in. *ZAMA NA AMANA* Na Admin Umar a Facebook da group d'insa Na WhatsApp, & *DEEJAH ABDUL NOVELS* da *UMMEE and AYSHA GARKUWA NOVELS*._ _nagode sosai da k'auna, wlhy nima ina k'aunarku aduk inda kuke, I love you wujiga-wujiga narantse🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀😂😂😍😍😍❤❤❤💋💋💋✋🏻✋🏻👍🏻._ 4⃣5⃣ "Ibraheem!! Kana nufin zaka iya kasheni?." "Ba Ibraheem ba, Ibraheem Abdallah, kokice j! domin samun sauk'i, kisa aranki baki ta6a sanin wannan Ibraheem d'inba kawai, yafi miki sauk'i". " iyeee, lallai d'an zaki yagirma". "Young tiger! Baya ja'inja da kowa". 'Yay maganar yana harbin gefen hajia babba". Rud'ewa tayi ta gigice daga ita har hajia khaltum d'in, su baffah kam duk rintse idanunsu sukayi, duk zatonsu khaleel ya harbi hajia babbane. Saiga mutuniyar taku jiki Na rawa, har taune harshe takeyi wajen fad'in " zan fad'a maka komai wlhy yalla6ai, bama saika harbeniba, ALLAH ya huci zuciyarka Oga". Wani murmushin mugunta khaleel yayi, yagyara zamansa yana wasa da bindigar a gefen kumatunsa, idonsa k'yam akan hajia babba. _kamar yanda kowa yasani sunana Laurah, innah jummai k'anwace ga Halima (Ammah), uwarsu d'aya ubansu d'aya. ayanda innah keban labari tun suna k'anana tafi Ammah k'yawu sosai, amma abin bak'inciki mutane sunfi son Ammah, sukance Ammah tanada nutsuwa da girmama mutane, innah jummai kuwa akwai rawar kai, ga rashin kunya, ko iyayensu sunfi nunama Ammah soyayya fiyeda innah, kafin innah jummai tasamu Abu sai Ammah tasami ukunsa, tun alokacin innah jummai tatashi da k'iyayyar Ammah aranta, kullum burinta tayaya zata fi Ammah komai, aganinta tunda tafi Ammah k'yau, ita yakamata tafara samun komai kafin Ammah tasamu, amma ina, kullum Ammah ce asamanta._ _haka suka cigaba da rayuwa cikin rashin jituwa, kowa yana d'aukar hakan amatsayin fad'an sako, amma ita innah jummai har ranta takejin k'iyayyar Ammah, gidansu bawani karatun boko akeyiba alokacin, sai makarantar Allo, wata rana sundawo daga makaranta da hantsi, saisuka gamu dawani bak'o akan besfa🛵, Ammah ce kawai ta gaidashi, amma innah jummai ta6ige da k'are masa kallo, saboda lokaci d'aya yasace zuciyarta, bak'onnan ya tambayesu gidan wani mutum dayazo nema, cikin ladabi Ammah tamasa kwatance, yamata godiya dasaka mata albarka, sannan yad'auki taro da sisin kwabo yabata, amma sai Ammah tak'i kar6a, yay magiyar duniya tak'i amsa, caraf sai jummai ta kar6e kud'inan, murmushi kawai yayi yaja besfa d'insa yatafi, itakuma Ammah tashiga yima innah jummai fad'a akan kar6ar kud'inanan, tun a hanya fad'a ya sark'e tsakaninsu, har sukazo gida._ _ALLAH yajik'an baba mai d'anwake mahaifiyar su innah, ta tambayesu abinda yahad'asu, Ammah ta sanar mata komai, fad'a baba tayima Innah jummai, sannan ta kwace kud'innan, ta aiki Ammah gidan da bak'onnan ya tambaya taje ta maida masa kud'insa. Wad'annan abubuwa dasuka farune suka saka Rufa'ee k'aunar Ammah, baiyi k'asa a guywaba yasamu Malam Saminu yayan mahaifiyarsa da wannan batu, shikuma yazo har gida yasanarma Malam yahuza babansu Ammah. Mutananda sunrigada sun gina 'ya'yansu akan tarbiyya mai k'yau, dan haka babu batun jin ra'ayin Ammah Malam yahuza yabadata. Saidaga baya aka sanar mata._ _wannan aure shine yazama sanadin k'arin k'arfin k'iyayya tsakanin Ammah da inna jummai, domin ita sosai takeson Malam Rufa'ee aranta, gashi awannan karonma Ammah takuma kwace abinda takeso a hannunta, daga wannan karon Innah jummai tad'auki aniyar tarwatsa Ammah dadukkan farincikinta, tadad'e tanamata bitada k'ulli amma babu nasara, har itama tasamu miji tayi aure, wato mahaifina, ALLAH ya azurtasu dasamun haihuwata, alokacin Ammah Nada 'ya'ya biyu, Abdallah da ma'aruff, Innah jummai Ce tayima Ammah asiri haihuwarta tatsaya, acewarta bazai yuwu Ammah tayita haihuwar mazaba itakuma gashi da mace tafara, ALLAH ya hukunta kwayayen haihuwar Ammah biyune kawai a duniya, shiyyasa bata sakeba, domin asiri yana tasirine da izinin ALLAH. Saidai kuma ubangiji ya nunama innah jummai iyakarta, domin itama tundaga ni saitaita haihuwar mazan suna mutuwa, wannan yasakata d'aukar burun ruguza 'ya'yan Ammah biyu._ _Tunda nafara zama budurwa ALLAH ya jarabceni dason Abdallah, har d'oki nakeyi idan yazo gidanmu, amma kullum innah jummai Na kwa6ata akan naciresama azuciyata, Dan bazata amince Na auresaba, bana saurarenta ko kad'an, dukda kullum karatunta naburin nayi kud'i yana tasiri azuciyata, Dan innah jummai batada burin daya wuce Na auri mai kud'i nima nazama hamshak'iyar mace, kodan ta nunama Ammah cewar tafita, ALLAH yatsareni daine kawai banta6a aikata siyar da mutuncinaba, amma ansha biyana kud'i nasamo budurwar daza'ayi iskanci da ita, idan nasamo kud'in kuma innah jummai bazata ta6a tambayata ina a samosuba, saima taita sakamin albarka da min kirari, *Laure, lauratun babanta, farar haihuwa adon kowace uwa*, kullum kirarinda Innah jummai kemin kenan idan akawo mata kud'i, wani zuwa da Abdallah yayi gidanmu gaida innah jummai na rud'e daganin yanda yazama cikakken mutum k'yak'yk'yawan saurayi San kowacce budurwa, tundaga wannan alokacin natada billi sai shi, inba hakaba kuma zan gudu daga gida, innah jummai namatuk'ar sona, alokacinne kuma taga yakamata ta yadda da aurenmu kodan mu mallake dukiyar da Abdallah Muke tunanin yanada ita, alokacinma shi bawani kud'ine dashiba, rufin asirin ALLAH ne kawai._ _nasan Abdallah bays sona, an tursasashi aurenane kawai, domin yanajin maganar iyayrnsa, itakuma Ammah tayarda da aurenmune domin k'arin k'arfin dank'on zuminci itada 'Yar uwarta, batasan burin 'Yar uwartata tarwatsata baneba. abinda ya tada hankalina nida innah jummai shine haihuwar mata Dana fara, domin burinmu bai wuce nahaifi 'ya'ya mazaba danmu mallake dukiyar Abdallah, bayan haihuwar Zuwairah inada cikin shikurah muka had'u da hajia khaltum taje sibiti ganin likita itama, tundaga nan muka kullah k'awance, tacemin a Abuja take aure, yanzuma tazo Kano bikine zazza6i yakamata tazo ganin likita._ _bayan haihuwar shukurah babu dad'ewa sai Abdallah yazomin damaganar k'arin aure, ankai ruwa rana sosai saboda Innah jummai da Khaltum suna zugani akan karna yarda nabar Abdallah k'ara aure. ALLAH ya rubuta fad'ima saita zama matar Abdallah, saigashi anyi bikinsu, tunda fad'ima tashigo gidan nahana kowa zaman lafiya, sannan duk cikin data samu saina zubar dashi ta hanyar bata magani batareda tasaniba, Dan banaso tahaifi namiji kafinni Na Haifa, bazai yuwu tagaji dukiyarsaba bayan nafita shan wahalar zama dashi, wannan rashin zaman lafiyar tamu yasaka Abdallah auro Bilkisu, nanma ansha fama kam sosai, zuwan Bilkisu gidan naso muhad'e kai da ita, danna samu nariga 6arar da cikin daduk zata d'auka cikin hikima, saboda aringa jingina hakan ga fad'ima, amma sai Bilkisu tak'i amincemin, dama can ba sonta nakeyiba._ _Alokacin kusan tare mukayi goyon ciki mu uku, saidai namu yana gabadana fad'ima, nayi yunk'urin zubarma da Bilkisu ciki hakan bata faruba, ALLAH yarubuta saikazo duniya, rana d'aya muka haihu nida Bilkisu, amma narigata haihuwa, nahaifi mace saidai batazo da raiba, banyi bak'incikin mutuwartaba saboda macece, saima khaltum dataita nuna jimaminta, ganin ban kulaba ta tambayeni dalili, nafad'a mata ba mutuwar 'Yar Dana Haifa bace damuwata, damuwata mi Bilkisu zata Haifa?._ _khaltum tace tabbas wannan abin dubawane aminiya, amma ga shawara, mizai hana muhad'a kai da likitan nan, idan Bilkisu namiji ta Haifa mu kasheshi kawai, banyi musuba, nan take naji Na amince dabatunta. Kud'i masu yawa muka bama likitannan sannan ya amince da buk'atarmu, bayan haihuwar Bilkisu sukaje shida wata nurse da khaltum suka sato mana jariri, aka ajiye mata d'iyata matacciya._ _saidai kuma da'aka kawo jaririn sainaji bazan iya kasheshiba, nacema khaltum baikamata mukashe jaririnba, gara kawai narik'eshi amatsayin shine Na Haifa, kinga zuwa nan gaba samu kori Bilkisu da fad'ima, shikenan jaririnnan yazamemin sandar dukan kowa, dukiyar Abdallah tazama tamu, nan take tayi na'am da zancena, harda min jinjina. Daganan kadawo hannuna, abin mamaki kuma kak'i kar6ar nonona, daga bayama sai nonona Yakoma fidda yellow d'in ruwa, Ammah tadage akan bilkisuce zata shayar dakai, ankai ruwa rana sosai, danni zatona za'a gane alokacin, Ashe kuwa fad'ima tagane komai. Alokacin datazo mana dabatun mu maidama Bilkisu d'anta mukai mata barazana da mutuwa, harda Bilkisu da jaririnma gaba d'aya, nasan badan tsoro fad'ima tabarmuba, saidon wani dalilinta nadaban, saidai bansan wane dalili baneba, (nasan fad'ima jarumace, wannan yasakanima nake mugun shakkarta, dukda bana nunawa agabanta kuwa)._ _wannan sirri namu da fad'ima tasani, mukagafa dolene musan yanda zamuyi tabar gidan, Idan bahakaba zata 6aro mana aikine, dama ga cikin jikinta yana bani haushi, kullum fargabata karta haifi namij, mun shareta alokacin, har zuwa wasu watanni sannan muka 6arar da cikin jiKinta, muka had'a kai da likita kuma yace dama tadad'e tana zubarwa, sannan Na ajiye mata maganin zubar da ciki ad'aki Abdallah yagani, domin nasan yanda yake da masifar son 'ya'ya dama. Munyi nasara kuwa, Dan alokacin Abdallah yasaki fad'ima, daganan muka koma burin ganin munraba Bilkisu da gidan itama, bayan muncigaba da bibiyar fad'ima muna ma rayuwarta barazana, har muka saka aka saceta dukdan dai tatsorata karta tona mana asiri watarana._ _banta6a goyaka abayanaba, banta6a cin kashinkaba, duk wani wahalar raino da uwa kanyima d'anta banta6a yimakaba, musamman na d'akko mai raino take rainonka, sai Bilkisu itama datakeyi idan ankaika kasha nono, tsakanina dakai nad'an d'aukeka, shima nata maka mugunta kenan kana kuka, amma babu wanda yafarga da hakan, bak'aramin k'ok'ari nadinga yiba wajen danne zuciyata ina nunamaka soyayya agaban mutane, dan wlhy nagama tsanarka tuni, natsaneka saboda kaid'in d'an mak'iyyatane, natsaneka saboda kowa yana nunamaka soyayya agidannan, Ammah, bilkisu, Abdallah, hakama su zuwairah, suk motsinsu nakanka, bada son ran innah jummai nake rainonkaba, dan bata ta6a d'aukarkaba tunda take, dukda namata bayanin dalilina na d'aukarka hakan baisa taji zata sokaba, yakamatama kakula da yanda nake nunama 'y'a'yana mata soyya fiyeda kai._ _Muncigaba da farautar cikin daduk Bilkisu tasamu amma ALLAH bai bamu nasaraba, babu dad'ewama tahaifi Rufa'ee (khaleefa), takuma yin Sultan, tayi mujahedeen, hakan yakuma haddasa wutar k'iyayyarta araina, gashi ALLAH yahananin damar d'aukar mataki, kuma nid'in haihuwar tama tsayamin cak, tunda muka haihu tareda Bilkisu tawa ta mutu bansake koda 6atan wataba har Bilkisu tayi haihuwa 5, sai bayan haihuwar Ramadan nasamu cikin Mugeedah ma, sannan kumane khaltum taja ra'ayina shiga k'ungiyarnan ta safarar yara mata, tacemin nabar wahalar banza akan jiran dukiyar daba tawaba, waddama alamomi sun nuna Bilkisu Ce zata gaje komai, inzo nanemi nakaina, harma sainafi Abdallah shahara, kamar yanda innah jummai take buri, ni inhar zan samu kud'i babu ruwana dawani tantance abinda zanyi, hakan yasaka Na sanarma innah komai, atake tabani goyon baya, dakuma jinjinamin, tanamai farincikin lokacinne zatafi Ammah komai, zata nunama Ammah itamafa karanta yakai tsaiko, ayanzu tafita komai da komai, lokaci yayi dazataga Ammah 'Yar uwarta ak'asanta, itama tadaina hawa samanta._ _wannan farincikinne danagani atattareda mahaifiyata ya k'arfafamin guywar Shiga wannan k'ungiya, Alhmdllh nasamu abinda kuma nake buk'atar samu, hakama mahaifiyata, dannafi Abdallah komai, dandai kawai bana nunawane, naginama mahaifiyata k'aton gida, nazubamata dukkan abinda take buk'ata, daga alokacin kuma takoma saka sutturar da Ammah bata saka koda kwatankwacinta, sannan bana jira Abdallah yamin komai, dan nafisa komai, nazama hamshak'iyar mace tamkar yanda mahaifiyata tayi buri, nashahara sosai, saidai girmankane yaso durk'usar dani, domin nakula kafara shigamin hanci tuni, wannan ne yasakani d'aura d'ammarar kasheka kafin kai kaga bayana, saidai kash, Ashe har zuwa yanzu fad'ima Na bibiyar rayuwata batareda nasaniba, duk zatona ta manta da komai, kosanda tace zata dawo gidan ba kishine yasakani binta kanoba, fargabata karta dawo da abinda yawucene kawai, banta6a jin kishin saudah ba, Dan lokacin data shigo gidan nasamu hanyoyin samun kud'i, Ashe munafukace ita, shiru-shirunta Na munafuncine itada Bintu, ALLAH ya Isa tsakanina daku, ziciyata bata ta6a kawo dabaibayin da fad'ima taminba kenan, saboda banta6a tunanin wani mahaluki agidan zaisan sirrin sana'ataba, tunda komai cikin taka tsantsan nakeyinsa, hankalina bai fara tashiba saida shegiyar yarinyarcan ta bayyana amatsayin d'iyar Fad'ima, harma tsohuwarcan tahad'a aurenku, saikuma fitar dare Dana kama mufeedah nayi, rushewar komaina shine cikin mufeedah😭, tak'are maganar da rushewa da kuka....._ Kowa kakalla awajen kallon mamaki sukema hajia babba da inna jummai, bakin Ammah bud'e tak'arasa gaban innah jummai. "Jummai yanzunan har lalacewar zuminci tawannan zamanin takai kiringa bak'inciki dani?, nid'infa yayarkice ciki d'aya, mukad'ai iyayenmu suka Haifa, yanzunan jummai sabodani kika rusa rayuwar d'iyarki tall guda d'aya?, saboda son ki fini kika dinga walagigi da tarbiyyarta haka? Haba jummai, miyasa baki fad'ama iyayenmu kinason Malam Rufa'ee ba alokacin? wlhy dakin fad'a saina barmiki shi, Haba jummai, miye duniyama bare abinda ke cikinta, yau INA iyayenmu? dukfa sun mutu, INA Malam Rufa'een dakikayi danshi? Yamutu tuni ya barni, mumafa dolene mumutu, inhar d'an uwanka zaita wad'annan k'ulle-k'ullen dankawai yafika, to tayaya duniya zata zauna lafiya? tayaya zuminci zaiyi k'arko aduniya? Shiyyasa babu Abu mafi lalacewa awannan duniyar kamar zuminci, hassada da bak'inciki tamaidamu mak'iyan juna, kullum burinmu muzama saman 'yan uwanmu, bamason kowa yafimu, bamason ace wane shine wane, yakamata kigane wani sirri awanan labarin jummai, *Hassada ga mai rabo takice*, kullum kina bak'incikin ALLAH ya d'aukakani samanki, burinki kifini, amma kuma ALLAH nata d'agani sama, koda kinsamu abin, sainikuma nasamu mafiyinsa tawata hanyar. kin tsaidamin haihuwa, dukda nayarda hakan tsarin ALLAH ne, amma sai ALLAH yabani jikoki, kusan talatin, ga 'ya'yan jikoki kuma, burinki ki mallake dukiyar zuri'ata domin kifini, sai ALLAH yabama d'iyarki dukiyar dazata zame muku masifa keda ita, kinraba baiwar ALLAH da d'anta, sai ALLAH ya azurtata da haihuwar ninkin baninkin d'insa, sannan yasaka soyayyar juna tsakaninsu cikin hikimarsa, kin d'aukesa Dan gur6ata rayuwarsa sai ALLAH ya shiryasa yazama shine dodon dazai dinga tsorata rayuwarki, k'arshema shine zai ruguzata gaba d'aya. Kin fidda fad'ima agidan mijinta sai ALLAH yabata ikon zuwa wani gida tahaifi wadda zatazama jagorar tarwatsa dukkan farincikin 'yarki da sarautar datake tak'ama da ita, sannan yahad'a Auren 'ya'yayen mak'iyanki domin yanuna miki ked'in bakomai baceba, wannan kad'an kenan daga ikonsa, cikin mufeedah ALLAH ya d'and'ana miki irin bak'incikin da iyaye kanjine lokacinda aka salwantar da mutuncin 'ya'yansu, duk wannan abubuwan kinsaka d'iyarki yinsu domin ki wargaza rayuwata, sai ALLAH ya nuna miki iyakarki, yaruguza dukkan taki rayuwar, gakunan acikin nadama dagake har ita, kai jama'a ALLAH yarabamu da hassada. Kowa da amin ya amsa, su Anty zuwairah suka fice suna kuka, dukda k'aunar dasukema mahaifiyarsu bazasu iya kallon su Ammah ba, ashema momy basu taso amatsayin 'ya'yantaba, maza taso ALLAH yabata su. Kowa da kallo yabisu, momy kuma tafashe da kuka tana fad'in innah kin cuceni, duk kece sanadin rugujewar rayuwata, dabaki d'orani akan wannan karatunba daban tashi akan dokin zuciyaba, wlhy bazan yafe mikiba keda khaltum, ALLAH ya Isa tsakanina daku, ALLAH yajik'an mahaifina, kullum nunamin yake karnabi hud'ubarki, Dan bazata kaini hanyar 6illewaba, watarana saina tsinci kaina a Dana Sani, gashi kuwa lokacin yazo, Takai 'ya'yanama NBASA buk'atar ganina, takuma fashewa da matsanancin kuka tana tari. Khaleel Kansa aduk'e, idonsa yayi jajur, hakama jijiyoyin Kansa sunyi rud'u-rud'u, yama rasa yanda zai fassara wannan *bashin gaba* haka, kawai gani akayi yamik'e, ya tafa hannayensa saiga Adams yashigo, Kansa aduk'e yace, "Adams kowa yafita, Ammah da baffah da Anty Mamie, mama, ummi amarya, Aysha sausu Mujahedeen kad'ai nake buk'ata". "OK sir". Adams yafitada su Tasleem, su hasnah, da 'yan uku, matansu ya sultan. Ahankali khaleel yatako har gaban Ammah, kowa kallonsa yakeyi da tunanin abinda zaiyi, gashi yayi k'asa da Kansa yak'i kallon kowa awajen. Hannun Ammah Yakama yaje har gaban hajia babba da ita, sannan yakoma bayan Ammah yatsaya, yakamo hannayenta yad'ora saman bindigar hannunsa, kaitsaye hajia babba ya saita, nanfa kowa ya rikice, baffah namasa magana amma bai sauraresaba, ita kanta Ammah jikinta rawa akeyi, azatonta khaleel zaisata takashe hajia babba ne, innah jummai kuwa kuka da kururuwar ihu tafasa akan ataimaketa zasu kashe mata d'iya. Dirimmm!! Sukaji fitar harbi da ihun hajia babba lokaci d'aya, khaleel yasaka Ammah rama harbinta a k'afar hajia babba kamar yanda itama ta harbi Ammah ranar.😂👍🏻 Hajia babba Na kwallah k'ara khaleel yamatsa daga kusada Ammah, yabatta da bindiga a hannu, yajuya yafita yana hawaye, duk binsa da kallon tausayawa sukayi, inkacire hajia babba dake ihun azabar shigar bullet cikin k'ashin k'afarta, saikuma innah jummai dataje tarik'eta tana salati. Tarine ya sark'e hajia babba, tafara yinsa babuji babu gani, saiga jini nafitowa, amatuk'ar tsorace ta kwallah k'ara tana kallon hannunta cikin zare idanu waje. Adams ya kar6i bindigar hannun Ammah, sannan yayi waya akazo aka d'auki hajia babba data fara galabaita, ga aman jini, ga jini nazuba ta k'afarta, sai aminiyarta khaltum daduk ta tsure da tsoron Khaleel, tunda har ya iya aikata haka ga hajia babba air kowama saiya shafama Kansa lafiya, tunda yakasa sauraren tsawatarwa da mahaifinsa kemasa akan karyabharbi hajia babba. Dole suma suka fito, duk suka Shiga motoci bisa umarnin Adams. Khaleel kam office d'insa yashige ya kulle kansa yana kuka tamkar mace. Haka aka maidasu gida jikin kowa a sanyaye, babu mai iya koda tari acikin motocin.............✍🏻 _wayyo, ALLAH nagaji, nak'agara nagama, kuhuta nima Na huta yasin😢._ *_ALLAH ka gafarma mahaifanmu baki d'aya._*😭 *_I miss you so much baba, nakasa hak'uri da rashinka wlhy, ALLAH ya kai rahama makwancinka._* 🤚🏻✋🏻😭😭😭😭😭 [10/26, 4:28 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ *_k'yak'yk'yawar addu'a da fatan alkairi su iso agareku, inasonku da k'aunarku wlhy._* Ashcute the group admin, Fauziya, Mrs abdul'azeez, Maman salma, Maman Adam, Binta Suleiman, Yusuf amina, Amina ali adam, MUMMIETIE, Maimuna kulloma, Auta khan, Fmujeedat9, Aisha yakubu, Maryam khamis, Aisha, Ummu basma, Aisha Mustapha maina, Momyn twins, maman haneef, Zahra maigari, Mmn Ahmad, Hauwa saleh, Hajara Iliasu musa, Jamila D Iliasu, mom ashraft, ummin assiddiq, safiya tanimu, Sauda, Aisha gambo, Hauwa chindo, Ummu mufeeda, Zainab (Nafzee), Rahmat, MMN musty, Yar mamanta, Sanzee, bbyn dady, Ummi Ahmad Iliasu, Hawwa zakari, mmn khady, Eman, ummu aysha, fadila, fauxiyya Hussain. maryam hassan, Maman salma, Zainab Yusuf Abdullahi aji, Adama Abubakar sumaye, Aysher wali, Maman muniba, Mrs Useef, Deeja mashi, Maman mus,ab, Meeral mash, Princess Ayeeesha, Maryam lawal, Hadiza Abbas, Yar Ammi💕. _alkairin ALLAH yakai gareku😍😍😍😍😍💋💋💋❤💃🏻👍🏻._ 4⃣7⃣ Yau bayan Anty Zuwairah tagama shirinta tsaf tashiga dukkan d'akunan matan gidan, tamusu sallam dasake neman gafararsu, musammam akan abinda taitamusu abaya narashin girmamawa, hakama tanemi gafarar gwaggo bintu akan k'untata rayuwarta dasukayi sanda ta zauna a Lagos, gwaggo bintu tace babu komai yawuce aii, kuma tayafe mata. Hakama d'akunan matansu Ramadan Duk saida tashiga tamusu sallama, sannan tashiga mota hafeez da Muhseen sukatafi kaita airport. Anty shukurah ma tanufi gidanta, dansuma sundawo nan Nigeria baki d'aya. _____________________ Dayake yau takasance asabar kowa yana gida babu aiki. Aysha dataji d'an k'arfi-k'arfin jikinta tatashi tunda safe tahau gyaran gidan, khaleel kam Na d'akinsa kwance yana shak'ar barcinsa. Bayan tagama tsaftace ko'ina dukda tagaji sosai haka tadaure tashiga kichin, duk tanayine domin faranta ran ya khaleel, aganinta itama yakamata yanzu ta maida hankalinta sosai wajen kulawa da mijinta kamar kowacce mace, burinta yacika akan mafi yawan tanadinta, to shima yakama ta fuskanceshi, Abu mai sauk'i ta shirya amma masu dad'i, bakuma tayi masu yawaba yanda zai zama almabazzaranci da abinci, dai-dai cikinsu tayi, sai kad'an data k'ara koda wani yashigo, dukda haryanzu takanyi amai idan abinci baimataba. Bayan tagama wanke kayan data 6ata tafara sharan kicin d'in, jiri takeji kad'an-kad'an amma haka taita dafe bango tana morphing, wani yuuuu dataji acikin kanta yasaka saurin zama akaujerar plastic dake kichind'in, tadafe kanta tana sauke numfashi. Ya khaleel datun d'azun ke tsaye yana kallonta ya jinjina kansa yana guntun murmushi, aransa yace agaida jaruma. Takowa yayi ahankali har inda take, ya durk'usa agabanta tareda d'ora hannayensa bisa guywoyinta, d'ago ido tayi ahankali tasauk'esu akansa. Ya d'age gira d'aya yana kallonta shima, da hannu yamata alamar mike faruwa?. Kanta ta girgiza masa tana murmushi. Yace. "banason k'aryafa". Murmushi tayi, tace, " jirine kawai, kuma nadainaji". ''Yanzu nan waya sakaki duk wannan aikin? ana lalla6a d'an cikin kekuma kina gingimo masa wahala". "Sadauki kenan, idanfa zan biye tawani lalla6awa babu abinda zanma kaina, insha ALLAH ma sonake wannan week d'in dazamu shiga nakoma aikina". " yayi k'yau babie". 'Ya khaleel yafad'a yana mik'ewa, morper d'in data ajiye yad'auka yak'arasa morphing d'in kicind'in, itakam sai binsa da kallo takeyi da mamakinsa. Bayan ya kammala yace, " oya tashi muje muyi wanka, yau zuminci zamuje". "Zumunci kuma sadauki? Ina da ina zamuje?". juyowa yayi yana kallonta, ya kashe mata ido d'aya, "to ganin babe zamuje, matar Joseph ta haihu baby boy". " woow! Sadauki da gaske Dan ALLAH". "I'm telling you my Angel". Cikin farin ciki Aysha ta rungumesa, kaikace itace ta haihun, sai gero addu'ar fatan alakairi takeyi akan jaririn. Cikin amsawa da ameen ya d'auketa cak, bai direta ako inaba sai toilet. Nidai najawo tsumman k'afata nadawo falo. 🚶🏻‍♀ Ganin sunk'i fitowa nad'an kwanta jiransu, 'Yar wayata nad'auka nabud'e data, banzame ko ina sai group d'in ciki da gaskiya fans daketa suburbud'a firarsu ya khaleel, can nahango 'yan BBC hausama, suma nad'an lek'a muka gaisa, pherty novels ma hirar suke, dansuma akwai k'ok'arin comments, nashagala sosai a charts najiyo dariya khaleel cikeda nutsuwa. Tashi nayi zaune nad'auk'i d'an takardana da alk'alami nacigaba daga Inda Na tsaya😉👍🏻😂. Cikin shagwa6a Aysha kefad'in "nidai kakema dariya ko? Babu komai zan ramane aii, kuma saina had'aka da Ammah jar wuya". Dariya yakuma tuntsirewa dashi, yamatso kusada Aysha, ''kinga sorry my Angel d'ina, aii had'ani da Ammah tamkar taro March ne." ''Kadai gaya musu saina fad'a d'in". "OK OK naji, fad'i mikikeso amatsayin cin hanci?". " la ila sadauki! Kaima kana karya doka?". Cikin d'age gira yace, ''aii kezan bama cin hancin bawaniba, yanzu dai zan saya miki ice-cream, saikuma mi bayanshi". "Dan ALLAH da gaske?". " eh mana, amma saimun dawo daga ganin baby". "Shikenan muje to muyi break fast". Break fast suka zaunayi, adaddafe dai aka gama, Dan anyi nisa dacin abincin zuciyar Aysha tafara tashi. Cikeda kulawa khaleel yake kallonta, yace, "lafiya kuwa?". 'Dan yatsine fuska tayi, da hannu tamasa nun amai. Tausayi tabashi, yasan tanason abincin wani lokacin, amma data faraci sai labarin ya canja. jikinsa ya zawota, ahankali yayta shafa bayanta, lokaci-lokaci yakan mata sannu. Kanta kawai take d'aga masa, talafe ajikinsa tana shak'ar k'amshin turarensa. Zuwa wani lokaci yad'agota. Idonsa akan fuskarta yace, " ya daina?". "Ya daina, amma nahak'ura da abincinnan kawai, k'arasa mutafi". Jinjina mata kansa yayi, k'asan ransa kuwa yana jinjina k'ok'ari da jarumta irinta iyaye mata, amma ahaka har ake samun azzalumai irinsu hajia babba dake iya raba d'a da mahaifiya, wani bak'inciki ya tokare mak'oshinsa, daurewa yayi ya danne, Dan bayason hankalin Aysha yatashi. Amma dukda haka taga fuskarshi ta canja, badai tace dashi komaiba. Shima tashi yayi, Dan duk abincin yafitarmasa arai. Ajere suke tafiya gwanin sha'awa, dolene kagansu su burgeka, domin sunyi bala'in dacewa da juna, lamarinfa zaaaaam fans😉👍🏻. Cikin gida suka shiga, afalo suka iske mama da ummi amarya, zaune suna hira, saisu Adeel daketa wasa agefe, rissinawa sukai suka gaidasu, cikin tsokana ummi amarya tace, " amarya da ango sai ina kuma da gayu haka?." Aysha tasaka hannu tarufe fuskarta tana 'Yar dariya, khaleel kam k'asa yay da kansa yana murmushi, akunyace yace. "Zamuje ganin babyn matar Joseph ne". " tofa, yanzunan matar Joseph d'in ta haihu amma baka fad'aba babanmu?". "Amin afuwa ummi, dama nazo sanar mukune yanzun, babu dad'ewa muma yakira yafad'a". " ayya to ALLAH ya raya, mi'aka samu?". "Baby boy". " masha ALLAH kuma kunfara zama iyaye, ALLAH ya raya", 'cewar mama dabatace komaiba tun d'azun'. Khaleel ya amsa da ameen. Saiga Anty Mamie tafito daga 6angarensu samarin gidan itama, hannunta rik'eda Khaleefa. Cikin ladabi duk suka gaisheta, ta amsa idonta akan Aysha. "d'iyata ya jikin? Incedai yau babu aman?". Akunyace Aysha ta jinjina kanta alamar eh. " to Alhmdllh, ALLAH ya d'orar da lafiya". Ummi amarya ta amsa da ameen, khaleel ma a kan la66ansa ya amsa, sannan suka mik'e, sallama suka musu suka fice. Anty Mamie tabi khaleel da kallo, danta hango damuwa atare dashi, batace komaiba dai. _________________ Haka suka tafi amotarma shiru, tuk'insa kawai yakeyi ahankali, Aysha ma tayi shiru, harsukaje gidan Joseph babu mai cewa uffan. Horn yayi maigadi yabud'e gat, khaleel yatura hancin motarsa ciki. Suduka duk suka fito domin tararsu, Ashe matansu youseef ma duk sunanan, rungume Aysha sukayi cikin farinciki, matar youseef ma ciki yatsufa, da k'yarma take takawa. Afalon Joseph suka Shiga, Dan Na joy akwai 'yan uwanta. Khaleel yakar6i jariri k'ato dashi masha ALLAH, kallon Aysha yayi yana murmushi, jiyake inama nashine, itama murmushin tayi, dantaji aranta abinda yake rayawa kenan, tasan ya khaleel akwai son yara, shiyyasa kullum cikin yima 'yan uku da yaran su ya sultan hidima yake. Addu'o'i yamasa ya tofama yaron, tareda fatan shiriya agareshi tareda iyayen nasa, Dan kullum khaleel saiyayi addu'a akan ALLAH yaganar da Joseph gaskiya akan muslinci idan yanada rabo, yanamasa kwad'ayin son kasancewa acikin wannan addini mai yawan ni'imomi. Yini guda yau anan sukayishi, ansha hirakam sosai. ******* Sai dare suka baro gidan, harsun gota shop rite Aysha tace, "sadauki ice-cream d'ina". Rage gudun motar yay yajuyo yana kallonta, "yanzu nan saboda ice-cream roba d'ayane zamushiga har shop rite?". Baki tad'an tunzuro gaba, ashagwa6e tace, " nidai koma rabine muje, aidai nayi kallo ko". "Uyim, salon muje agamu da 'yan fashi kice zaki nunamusu jarumtar kwace gun ko?". Dariya Aysha tayi, saboda tuno waccan ranar datayi, cikin dariya tace, " aii wancanma dominkane nayi". Murmushi yayi yana juyawa d'ayan hannunsa danya samu damar shiga shop rite d'in. Yace "Kin San yanaji aranar kuwa?". ''A'a''. 'Aysha tafad'a tana maido kallonta kansa'. "Hummm, dukda nasan kindawo k'asar, hakan baihananin jin wani nishad'iba dana ganki, tun awajen shopping damuka had'u, jinayi tamkar kawai na...... Uhm bara nayi shiru, ashe bamu kad'ai bane". " bamu kad'aiba kuma?, to mudawaye?." Saida yay parking motarsa sannan yajuyo yana kallonta, da d'anyatsa yanuna cikinta. Kallon cikin itama tayi, samnan tad'ago ta kallesa. ''Aikin gane". 'Yay maganar yana bud'e k'ofar motar, tareda zura k'afarsa d'aya waje'. Girgiza kai kawai Aysha tayi, itama tabud'e k'ofar suka fice, k'asan ranta tana mamakin halayyar khaleel, shid'in wani irin murd'ad'd'en mutumne, awani lokacin kisameshi mutum mai sauk'in kai, wani lokaci kuma saidai ahankali kawai, maganama wannan wuyar fad'a take abakinsa, tabbas yadace da aikinsa, amma ita koma Yaya yake tanason kayanta ahaka........... Kama hannunta dayayi yasakata dawowa hayyacinta, baice mata komaiba suka nufi cikin shop d'in. Saida securitys d'in wajan sukai searching nasu kamar kowa sannan suka shiga ciki. Amaimakon ice-cream dasukazo suye, saisuka 6ige da shopping mai zaman kansa, Aysha taita jidar kayan zak'i, ganin abun nata bana k'are bane khaleel yamata magana cikin had'e fuska. "K! Wai lafiyanki kuwa? bakisan yanzu shan zak'i had'arineba agareki?, toki ragesu kokuma kinemi mai biya miki, Dan badai kud'inaba". Shiru Aysha tayi tana kallonsa, saida taji zuciyarta ta sosu, kamar tafasa kuka haka taji, sauk'inma babu kowa akusadasu, ahankali kuma yayi maganar. Batace komaiba tafara rage chocolate d'in data jida, shikuma yajuya yacigaba da latsa wayarsa. Koda tagama batace dashi komaiba tayi tafiyarta wajen biyan kud'i, ta gefen ido yake kallonta, guntun murmushi yayi, aransa yace Aysha kenan, Zuma saida wuta, idan bahaka namikiba aisai ki cutar da kanki dawannan zak'in. Bayanta yabi, daidai angama duba abinda suka siya d'in, ana fad'a mata kud'in, gani kawai tayi ya khaleel yamik'o ATM d'insa. Tajuyo tad'an kallesa, fuskarsa a d'aure, danhaka ta kauda kanta, shikam baima kalletaba, bayan angama cirewa aka mik'o masa ATM d'in, yana kar6a yakama hannun Aysha yazare ledan yay gaba abinsa. Cikeda jin haushin abinda yake mata tabi bayansa tana k'unk'unai. Yana jiyota, saidai bayajin abinda take fad'a, aransa yace yarinyarnan dantaga ina wasa da ita takeson fara rainanifa, bara zan saitata kuwa. Baya yabud'e ya ajiye ledojin, sannan yadawo mazaunin driver yabud'e yashiga, kusan tare suka Shiga da Aysha, koda tarufe k'ofar saita juya masa k'eya, takoma kallon waje ta glass. Yi yay tamkar baisan da itaba amotar, yatada motar suka tafi. Har sukaje gida babu Wanda yakula wani, kuma ta 6angarensu yabi, baibi tacikin gidaba, haushi yakama Aysha, Dan tasiyoma su Anty Mamie Abu, tanason kaimusu. Koda yagama dai-daita parking sai Aysha tayi zamanta amotar tak'i fitowa, yakashe motar yafita abinsa tareda bud'e baya yad'auki ledojin. Ganin da gaske tafifa zaiyi yabarta amotar yasakata fitowa da Sauri, ashagwa6e tace, ''nika rakani nakaima au Anty Mamie abunsu". Kamar bazai tanka mataba saikuma yajuyo yana kallonta, ledojin yamik'o mata duka. K'in amsa tayi, tace, "to zaka rakani?". Kansa ya girgiza mata alamun a'a. " kai ya khaleel please mana". Gaba yayi yana fad'in "idan zaki kar6a kije ki kar6a, babu Inda zanje tundani ba yaronki baneba". Idon Aysha yacika da kwallah, tana hangensa harya bud'e k'ofar falonsu yashige, da sauri tak'arasa itama saboda tsoron kar wani Abu ya cafketa. 🤣🤣nikam dariya takamani, nace, " ho shollyn khalilullah.😂👍🏻 Afalo ta iskeshi zaune akan 1 seater yana cire takalmi da sock's d'in k'afarsa. Tazauna itama tana wani fiki-fiki da idanu tana tura baki gaba. Dariya takama khaleel, amma saiya danne yayi azuciyarsa kawai, yakula wannan 'Yar odar tasa sai a slowly. Mik'ewa yayi yad'auki takalman zaibar wajen, saida yay taku kusan uku sannan Aysha ta daddage ta kwallah k'ara, tareda dafe ciki tana fad'in wayyo cikinta, zata mutu, cikinta zafi. 🤣🤣 A 100 khaleel yazubda takalman hannunsa yadawo gabanta, hak'waransa har karo suke wajan tambayarta lfy?, ''mike damunki A'eesha? Kodai muje asibiti?". Ganin yarud'e dayawa yasaka Aysha kwashewa da dariya. Shiru khaleel yayi yana kallonta, wato tama maidashi wani soko, rankwashi mai zafi yazuba mata akai. Babu shiri tadafe kanta tana fad'in "wayyo mama zai kashe mikini". " kad'anma kenan yarinya, aii yau sakinsan wakika raina, zaki fad'amin yanda akayi muka zama abokan wasa"..... 'yak'are maganar da d'aukarta'. Wuysil-wutsil Aysha taitayi da k'afafu, tana bashi hak'uri, amma ina bai sauraretaba, saida yadireta agado. Da sauri tajuya zata gudu, ya cafkota tareda danneta. Rok'onsa tafara tana fidda numfashi dak'yar, please ya khaleel zan mutu wlhy, Dan girman ALLAH kayi hak'uri ka d'agani natuba wlhy". Ganin da gaske tana shirin shid'e masa saiya d'agata yana dariya, "matsoraciyan banza kawai, gobema ki sake". " murgud'a masa baki tayi tana share hawaye". "OK baki horuba kenan? Bara nak'ara". Kafin tayi magana ya had'e bakinsu waje d'aya, da zafi-zafi yake sarrafata, dama andad'e ba'a gamuba😉, tun randa momy tabasu meatpia.😱 Sum sum nafito dad'an takardana. Dan lamarin Nasu yafi k'arfin alk'alamin bilyn Abdul. 🚴‍♀ __________________________ *_Monday morning._* Tunda khaleel yadawo daga sallah bai koma barciba, Dan yau yakeson komawa bakin daga. Aysha daketa kurin aiki itama antashi anyi shiri. Yana tsaka da shiryawa cikin uniform d'in aiki saiga Aysha tashigo d'aukeda tire. Ta madubi yake kallonta yana saka ma6allan rigarsa. Mamaki ya kamasa harya d'an juyo ya kalleta itada tiren, sannan ya juya yacigaba da saka ma6allan. "Wai daga ina haka da tire?". ''Daga kichin mana, kad'anyi breakfast kafin kafita". Turare yad'auka yad'an fesa sannan yajuyo gareta gaba d'aya, kusada ita ya zauna akan sofa tana juya tea daketa turiri. Kumatunta ya sumbata, yana magana yana saka sock's da takalmi. " humm, nifa mamaki kike bani wlhy, wai dama ba barci kikeyiba ne?". "Lallai sadauki, inani ina barci yau Monday, insha ALLAH saina koma aikinnanfa, kamata yayima ka dinga k'arafamin guywa aii, saurafa wata biyu kacal nagama, nasha wahalar watanni goma, saida aski yazo gaban goshi sainayi sakaci kuma?". ''Inafa zan yarda Maman babies na, gara kigama kizo kinutsu wajen yimin tarbiyyan yara". " tab aikinfa?". "Gashinan zakiyi agidan mijinki". 'Yay maganar yana d'aukar doya yasaka abaki'. " sadauki banfa ganeba". Saida ya k'ur6i tea sannan yace, ''aii dama bazaki gane cikin sauk'iba, d'akko agogona gashi can saman mirror ki sakamin, nakusa makara, kuma inada meeting 8:0am wlhy". Tashi Aysha tayi tad'akko agogon, tadawo kusadashi ta zauna, hannunsa takamo tamaido saman cinyarta, tana d'aura masa agogon tana juya maganganunsa aranta, idonta nakan zara-zaran yatsun hannunsa masu dogayen farce dake a tsaftace kuma a yanke, kamar yanda addininmu ya koyar damu, (sa6anin samarin yanzu da 'yan mata dake barin farce wai danufin gayu, yo gayu kokuwa bama shaid'anu mafaka😏). Tana d'aura masa yana shan tea d'in a hanzarce. Tsaf ta d'aura, yadace da chocolate d'in skin nashi kuwa. Sauran tea d'in yakai bakinta tareda fad'in sha kema. Kauda kanta tayi gefe, "uhm uhm sadauki, banajin shan tea wlhy, zanje cikin gidane k'ila sunyi kunu saina sha." ''Kenan batare zamu fitaba?, dankuwa su Adams Na hanyar zuwa d'aukana, shima yafara koyan latti nakula". "Kaikam ya khaleel amaryafa gareshi, da shikad'aine, amma yanzu saiyad'anyi lallashi, saikuma an tsareshi yasha tea kamarkai". Dariya maganarta tabashi, ya ajiye cup d'in tareda jawota jikinsa ya sumbaci cikinta da goshinta, ahankali yace, "I love you so much cuty na, ked'in badai iya tsara zanceba." 'Yay maganar yanajan karan hancinta'. Kunya saita kama Aysha, tasaka hannu tarufe fuska tana murmushi. Shima d'aukar jakkarsa yayi yana murmushi, yace, ''bye, akula sosai, banda magana da maza wlhy, inhar batazama tilasba, daga wajen aiki kar acemin kinje koda gate, idan time d'in tashi yayi ki kirani zan turo a maidoki gida. kije zaku fita tareda ummi amarya." Baijira cewartaba yafice. Da kallo Aysha tabishi, batareda ta iya cewa komaiba harya fice. ******** Kamar yanda suka saba, cikin girmamawa suketa salute nashi da k'amewa, tuni Adams yatareshi ya kar6i kayan hannunsa, Samuel yabud'e masa motar da sauri. Shiga yayi ya zauna abaya cikin k'asaitarsa, suma sauran securitys d'in duk suka shiga. Saida suka fara tafiya sannan Adams yace, "sir! Akwai maganar kama guy d'inanfa Manner, kuma nasamu labari a majiya mai k'arfi yashigo Nigeria adaren jiya." Bud'e idanu khaleel yayi yana kallon Adams, yace, ''aikam zuwa Kano yakamamu dole a yau, domin Sa'eed ya tabbatarmin inhar yazo Nigeria to washe gari a Kano yake kwana, kaga kuwa yau kenan zaije Kano, idan mukayi saken har zuwa gobe to tabbas zamu rasashi, kuma guy d'in yanada muhimmanci akan bincikenmu, ta hanyarsane kawai zamu iya sanin wanene Alhaji Anas Jalingo, gashi kuma meeting d'inan zai kaini kusan awanni 8, Dan sai 1 zamu fito". Cikin huro iska abakinsa yace, ''yakake ganin za'ayi kenan?, ko shigar dare zamuyima Kano d'in?". "Duk yanda kace sir, kaga idan mun ajiyeka saimuje airport muyi biking jirgin yamma." "Shikenan, damun Isa kad'auki file d'in bayanan Alhaji Anas d'in ka kaima Basheer office yasaka hannu, sannan inaga kawai numbers d'in duk kan yaran Alhaji Anas ahannun Solomon, saiku duba number d'in Munner awajen, sannan su Solomon su bibiyar mana inda yake ta hanyar layinsa, dakuma duk indama zaije ayau har zuwa dare". " kukira Mustapha yabibiyeshi, kakuma gargad'esa akan karyamin wasa a aikina, idan yakuma kuskure irinna last time wlhy saiyayi nadama." "OK Sir! Babu damuwa". A dai-dai lokacin suka iso, bayan Adams yabud'e masa yafito, yakar6a wayarsa a hannunsa da lap-top, wad'annan akaisu office kawai, ka d'auki wasu files nanan a kan desk, nad'ora kamar wani book ne akai, nadai manta, kabama Samuel yakai office d'in Oga Victor, kace yatsaya yaduba yabashi ya maido maka, kaima kasamin hannu sannan kakaima Taheer akwai abinda zaije Ku bincika kaidashi da faruk da zeenatu a d'akin bincike, kafin nafito a tattaramin bayanai, bara naje suna jirana." "Afito lfy sir!". Kansa kawai ya jinjina Adams tareda d'aga hannu yanufi inda zasuyi meeting d'in, iyasu manya-manyan jami'an police Interpol, tareda wasu daga cikin immigrations da Customs, harma dawasu manyan ainahin police d'in, zasu tattaunane akan aikin had'aka dasukeson gudanarwa domin cafke wasu masu laifi dake k'asashen k'etare, dakuma goyon bayan wasu manya dake cikin Nigeria..............✍🏻 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🤚🏻✋🏻._* [10/26, 4:28 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ *_Bilyn Abdul bata manta dakuba, kunan acikin ranta zaune daram wlhy. Ina k'aunarku fiyeda tunanin mai hasashe._* Bilkisu saddiku shona, Asmeey*Jibreen, Zee*Matorh, haleemerh💖, Aysha*Bose, Sakinat Baba Didi, Hafsat I kari, halima, Shahida ibrahim, Khady fulani🐄, Sumee qasarawa, Saddiqa Dahiru. Zaynab, Maman Umar, Aysha Maman ta, Maman HAIDAR, Maryam Adam, abdullahi 002. Marcy bintu Muhammad Maman waleed maman shaheed. Ameera, Samina sulaiman lambu. Mmyn xahra. Ramlart ma'aruf.. Binta garba sakawa. Rukkyh Rky . Mrs uthman. Ummi haidar. Ummu Mahmud. Balkisu sulaiman . rashidart Abubarkar sultan. Khairat. Mom ismart, Rumanatobbr, Zainab Atiku, Auta nijar, Sameeran gaya, Hanan yusuf, Mardiya, Jamila sule, Zahra eabrahim, Farida ridwan, Mmn walida, Pherteemah, Maman islam, Anuty, Momy, Fancy honey, Khadeeja dantsoho, Hafsat wali, Aysha wali, Hussaina idiris maman amira. naima nura. hauwa umar. abubakar. nafisa yunusa saratu k, Muhammad habiba khaleel, Maryam, umar musa, Jamila Muhammad Adam, Zainab, Maman khalifa, Maman sudais, Ummu, abudull, Maman sajida, Farida gamco, Firdausi kabir, Momin Abdul malik, Momy zuwaira, Rukaiyya aliyu, Aysha m bello, Rahila abba, asiyya muregi, Fatima garba sule, Ummu ihisan, Ummu salma. _Na gaisheku ababen alfaharina😂👍🏻❤❤😍😍😍😍😍._ 4⃣6⃣ Dole likitoci suka rufu kan hajia babba, dukda ba'a bama wani criminal kulawa kamar haka, saidai inhar suna buk'atar wasu bayanai awajensa, amma darajar khaleel Taheer yace abama hajia babba kulawa, Dan lamarin yawuce k'aramin Abu, Amman jini taketa zazzagawa. Innah jummai sai kuka takeyi. Kusan awanni biyu likitoci natareda momy, bayan wasu 'yan mintuna saigasu sun fito, kowa yana yarce gumi. Sai hura hanci sukeyi. Taheerne ya tambayesu abinda ke faruwa?. Dr Abraham yace sir, akwai matsala, zuciyar matarnan ce tabuga gaskiya, shine dalilin aman jinin datakeyi, saidai munsami nasarar ceto rayuwarta, yanzu hakama tana barci, maganar gaskiya kuma, bamuda tabbacin tashinta normal. "Miyafaru da itane?". " uhm, inagafa tasamu paralysis, 6arinta Na dama munga duk jijiyoyin sun saki". " Ya salam!". 'Taheer yafad'a yana shafa kansa da huro iska abakinsa". Gaba Dr Abraham yayi abinsa. Nidai bilynku nace magana ta girma😱. _________________________________ Tunda khaleel yashiga office saiya kulle kansa, inda kujeru suke agefen office d'in yaje ya kwanta, Dan anhad'a wajenne tamkar falo. Idonsa alumshe suke, amma hawaye Na zurara. Yabani tausayi ainun, domin bansan mike k'ona zuciyarsa hakaba harta kaisa ga yawan kuka.😢 Haka yayta zama cikin office d'in, saidai yatashi daga nan Yakoma nan, saikuma sallan data zame masa tilas, komin knocking d'in da akamasa k'in bud'ewa yakeyi, su Taheer basusan yana nanaba, duk zatonsu yatafi gida. ___________________ Hankalin Aysha yafara tashi, ganin har 10 Na dare babu koda alamun ya khaleel, takira wayarsa yafi sau ashirin yak'i d'agawa, daga k'arshema idan takira saitaji switch up, duk motsinta nakan idon Anty Mamie ne, Dan tunda suka dawo ayshan bata koma 6angarensu ba, tana nan cikin gida, lokacin dazatayi barcine tadawo d'ankin Anty Mamie ta kwanta, ganin kuma bai dawoba tayi zamanta tana jiransa. Anty Mamie ta ajiye bowl d'in hannunta a saman dirowar gefen gadon, ta kalli Aysha dake kwance a gadon rik'eda waya tana hawaye, girgiza kanta tayi, sannan tace, "Aysha miyake faruwane?". Kokad'an Aysha batasan Anty Mamie tashigo d'akinba, da sauri tad'ago ido tana kallonta, saikuma tatashi zaune, komawa tayi jikin Anty Mamie takuma fashewa da kuka, cikin kukan tace " Mamie ya khaleel haryanzu bai dawoba, nakira wayarsa yafi sau ashirin yak'i ya d'auka, daga k'arshema wayan switch up". Ajiyar zuciya Anty Mamie ta sauke, ita kanta dukkan hankalinta Na kansa tun d'azun, daurewa kawai takeyi, lallashin Aysha tashigayi, da kwantar mata da hankali, saida taga Ayshan ta tsagaita da kukan sannan tad'akko bowl d'in data ajiye tamik'ama Aysha, fruit ne datace zatasha d'azun, saikuma tayi barci. Kar6a ayshan tayi Tanama Anty mamaie godiya. Shiru sukayi suduka, Aysha nashan fruit amma hankalinta nakan khaleel, kad'an-kad'an saita kalli agogo, saikuma gwada number sa takeyi. Anty Mamie dai tayi shiru, tausayin Aysha da k'aunarta nakuma ratsa zuciyarta da ruhinta. ganin har 11:30pm Anty Mamie tad'auka waya takira Sultan. Shi harma ya kwanta yaji kiran wayar, matarsa tamik'o masa wayan yakar6a yana fad'in waye a wannan lokacin?.... Ganin Anty Mamie yasakashi mik'ewa zaune da Sauri, bai d'aga wayarba ya d'auki jallabiya yasaka yafito da sauri. Aysha data gama shan fruit tamik'e tashiga toilet. Anty Mamie tabita da kallo, har ranta tana k'aunar yarinyar, tun a ranarda tafara ganinta da gwaggo bintu tazo da'ita, Ashe Aysha alkairice acikin rayuwarta, shiyyasa tana kallonta gabanta yafad'i....... Shigowar ya sultan a hanzarce ya katsema Anty Mamie tunaninta, tad'ago ido tana kallon yanda yashigo d'akin a birkice. Shima turus yayi yana kallon Anty Mamie, soyake yagamike damuntane?. Fahimtar hakan da Anty Mamie tayi yasakata fad'in "kwantar da hankalinka, yayankune bai dawo gidaba har yanzun, kuma anata kiran wayarsa yak'i d'auka, daga bayama saiya kashe wayar, to munata tunanin ko lafiya? Gashi matarsa dukta tayar da hankalinta, nikaina hankalina a tashe yake wlhy". " Kina nufin bai dawoba har yanzun Anty Mamie? to kodai aikine yamasa yawa a office?". .....bana tunanin haka, sultan, kasan zuciyar babana, kuma hankalinsa atashe yake yanzun, nafi tunanin badai lafiyaba gaskiya". ''Bara muga nakira Adams naji". Wayar Adams sultan yakira, ko gaisawa basuyiba yace, ''Adams ya khaleel fa?". Cikin muryar barci Adams yace, "bayana gidaba ya sultan? nazata tare kuka tafi d'azu da safe aii?". " A'a, kasan yama rigamu barin hall d'in". Babu shiri Adams ya janye Amal dake jikinsa tana barci yatashi zaune." "Ya sultan kana nufin baya gida?, barato naje office na duba, amma idan har Oga ba aikine dashiba bayakai wannan time d'in a office gaskiya." "OK nima ganinan zanzo, muhad'u a can, dukda nasan bazasu barni na shigaba". " A'a kajirani amota idan kaje, idankuma narigaka zuwa shikenan". "OK". Bayan ya Yanke wayar ya kalli Anty Mamie da Aysha dake tsaye tafito daga toilet, taji dukkan abinda yafaru, wannan yasakata cigaba da zubar da kwallah, tana addu'ar ALLAH ya tsare mata mijinta aduk inda yake. "Anty Mamie bara naje office Na duba, zamu had'uda Adams a can, Dan bazasu barni nashigaba idan nikad'aine". " hakan yayi, amma kira mujahedeen kuje tare, Dan dare yayi, har 12 takusa". "Anty Mamie da'an barsa, k'ilama yayi barci yanzu, zan iya tafiya nikad'ai babu damuwa". "Shikenan, amma dai daka duba ko Muslim ne kuntafi tare". "to bara Na duba idan baiyi barciba, saimun dawo". Addu'a Anty Mamie tamasa yafita yana amsawa, ta maido kallonta ga Aysha da har yanzu take a tsaye. " k'araso kiyi sallan kinji Aysha, insha ALLAH yana nan lfy, ki kwantar da hankalinki". Jin jina kai Aysha tayi, tak'araso tad'auki hijjab ta kabbara sallar isha'i dabatayiba tana barci. ******* 6angaren su muslim ya sultan yashiga, a falo ya iske Muslim yana kallon kwallo, cikin mamaki Muslim yace, ''ya sultan lfy kuwa a wannan time d'in?". "Da dai sauk'i Muslim, ya khaleel ne bai dawo gidaba har yanzu, shine zamuje office mu duba". Da Sauri Muslim ya mik'e yana fad'in "ya salam, mujeto ya sultan." _____________ A k'ofar gate suka iske Adams yana jiransu, yarigasu isowa. Fitowa yayi yashiga motarsu sannan suka k'arasa gaban gate d'in, dukda sun gane Adams hakan bai hanasu bincikensuba, saida suka tabbatar babu komai ajikinsu sannan aka barsu suka shiga. Kai tsaye office d'in ya khaleel sukaje, sunyi knocking yafi sau goma amma basuji ko motsiba. Komawa tacan baya Adams yayi yalek'a ta window, office d'in dind'um da duhu, ya kunna fitilar wayarsa ya haska, can ya hango khaleel zaune a kujerarsa ya kifa kansa bisa table d'in gaban kujerar, ajiyar zuciya Adams ya sauke, yazagayo wajen k'ofar indasu Sultan ke tsaye suna knocking har yanzu. Dukkuma knocking d'in dasukeyi khaleel najinsu, amma ko motsawa baiyiba barema yay tunanin tashi ya bud'e musu. Adams yace, "ya sultan yana ciki, amma nasan bazai bud'eba, bara nagani kozan samu Oga Victor Na nan asamo wani key d'in." "To Adams, ALLAH yasa adace". Kusan mintuna 40 saiga Adams yadawo da keys d'in, saida yagwada kusan 4 sannan aka dace k'ofar ta bud'u. Kunna fitilar office d'in Musleem yayi, haske ya gauraye ko ina, har alokacin khaleel bai d'agoba, kuma duk yanajin motsin shigowar tasu. Da sauri Sultan yak'arasa gareshi, " ya khaleel mike faruwane haka? kasaka hankalin kowa yatashi agida, Aysha sai kuka takeyi tun d'azun, hakama Anty Mamie hankalinta atashe yake". "Please ya khaleel katashi muje gida Dan ALLAH. kayi hak'uri ya khaleel?". Da k'yar khaleel yad'ago manyan idanunsa dasukayi matuk'ar jajur, ya zubasu akan sultan, sannan yamaida ya lumshe. " please mana ya khaleel ". Girgiza kai khaleel yayi, yamusu Alama da hannu alamar sutafi su barsa. " A'a ya khaleel, yazamu tafi mubarka a wannan halin, bayan hankalin kowa nacan atashe, kayi hak'uri dai mudafi gidan kawai". 'Musleem nevyay maganar muryarsa nazuga alamar tahowar kuka'. Adams yamatso kusada Sultan, murya k'asa-k'asa yace, "ya sultan inaga yakamata kakira Anty Mamie kawai, k'ila idan itace tamasa magana ya yarda yabimu, amma inhar damon mune bazaijeba". Cikin na'am da zancen Adams sultan yace shawararka tayi. Anty Mamie Na zaune akan sofa, Aysha ta kwanta ta d'ora kanta bisa cinyarta, barci 6arawo ya saceta batareda ta shiryaba, wayar Anty Mamie Ce tafara ring, ganin sultan ne tad'aga da hanzari. " Anty Mamie please kimasa magana da kanki, mudai yak'i saurarenmu, gashinan a office ya kulle kansa, dak'yar Adams yasamo wani key d'in aka bud'esa". "Bashi wayar". A Hans free sultan yasaka wayar, Dan yasan ya khaleel bazai kar6aba. Lallashi da ban magana Anty Mamie taitayima khaleel, saida k'yar ya amince zaizo gidan, sultan ya yanke wayar sannan suka taimaka masa yatashi suka fito, bayan musleem ya tattaro dukkan wayoyinsa da laptop d'insa, Adams ya kulle office d'in suka taho. " Adams kawuce gida kawai, Dan dare yayi". "Bara Na rakaku kawai ya sultan". " A'a kaje Kawai, saida safe". _____________ Gidan shiru kowa yayi barci, dama babu Wanda yasan sun fitama. Har khaleel zai nufi 6angarensu Sultan yace, ''aii Ayshan tana wajen Anty Mamie ". Baice komaiba yajuya yashiga babban falon, sukuma suka bishi abaya, zaune suka tadda Mamie Aysha kuma tayi barci ajikinta. Ahankali Anty Mamie tafurta Alhmdllh. K'arasowa khaleel yayi yazauna gaban Anty Mamie, shima d'ora Kansa yayi bisa cinyarta kusada kan Aysha. Ahankali Anty Mamie Takawo d'ayan hannunta saman kansa tana shafawa kamar yanda take shafa Na aysha. Jin hannun mahaifiyarsa bisa kansa sai yaji wasu hawaye masu zafi Na ziraro masa, ahankali suka ringa sauka bisa cinyar Anty Mamie. Rintse idanunta Anty Mamie tayi, domin jin saukar hawayen khaleel ajikinta, itama saiga NATA hawayen suna kwarara, jikin sultan da Muslim yayi sanyi k'alau, sultan KASA daurewa yayi yajuya yafita kawai, shima idonsa cikeda hawaye. Musleem kam jingina yayi da bango yana kuka shima, hakannne yak'ara k'arfin kukan Anty Mamie, da sauri musleem yafice ad'akin, Dan bazai iya sauraren kukan mahaifiyar tasuba. Har kusan 12:43pm suna nan zaune ahaka, babudai Wanda yace uffan, jin shirun yayi yawa yasaka Anty Mamie lek'a fuskar khaleel, murmushi Anty Mamie tayi, ta duk'o ahankali ta sumbaci kan Aysha, shima sumbatar kansa tayi sannan ahankali tace, "babana". Bud'e idanunsa yayi dasuka koma k'anan saboda barci, ya kalli Anty Mamie. Tashi kaga nasamo maka wani abun kaci, saika d'auki Aysha kuje Ku kwanta, dare yayi. Kansa ya girgiza mata alamar ya k'oshi. " ban yardaba, tashi kaidai". Bamusu yajanye kansa daga cinyarta, cikin dabara tajanye Ayshama ta maida mata kanta bisa filo. Maida kallonsa yayi kan Aysha, tausayinta yakamashi, ganin fuskarta duk jirwayen hawaye. Matsawa yayi yad'ora hannunsa akan gashinta yana shafawa ahankali, yakai fusakarsa kusada tata ya sumbaci goshinta da kumatunta, akan la66ansa yafurta I love you so much A'eesha". Babu dad'ewa Anty Mamie tadawo d'aukeda mug d'in tea, sai k'aramin fleet ta d'oro cake. 'Dan janye jikinsa yayi daga kusada Aysha saboda kunyar Mamie, itama guntun murmushi kawai tayi ta ajiye masa kayan hannunta, daure kad'ansha koda tea d'inne, saikasha magani ku kwanta, Dan jikinka kaima zazza6ine, Aysha dai nata ya sauka. Kansa ya jinjina mata yana kar6a, k'asan zuciyarsa nawani tsitstsinkwa saboda k'auna da tattali irin Na uwa mahaifiya, Wanda abayyane yake kallon nisan banbanci tsakanin momy da Anty Mamie. Wardrobe Anty Mamie tabud'e tad'auki kayan barci, sannan tad'akko magani tamik'a masa, "gashinan kasha idan kagama, saiku rufemin d'akin indan kunfita, baffanku Na jirana". Murya a shagwa6e wadda shikansa baisan dad'in yima uwa shagwa6aba sai yau, yace, ''Mamie anan zamu kwana kawai". Murmushi tayi, tace, " to ALLAH yabamu alheri, ni nayi nan." Bata jira amsarsaba tafice. Tana fita yashare hawayensa. Kad'an yaci cake d'in, amma ya shanye tea d'in, yasha magani sannan yamik'e, kayansa kawai yacire, yazauna dagashi sai vest da boxer, yashiga toilet, wanka yayi yay alwala yafito, har lokacin Aysha barcinta takeyi. Wayar Muslim yakira yace yakawo masa jallabiya d'akin Anty Mamie. Babu dad'ewa ko saiga musleem da jallabiya, dayake shima badaga bayaba wajen tsawo, haka yake shima tamkar khaleel d'in. Sallah ya kabbara, yana tsaka da sallan Aysha ta farka. Da sauri tabud'e idanunta akan khaleel dake sallah, babu shiri taduro a kujerar, gabansa tadawo domin son gaskatawa, ta zauna tazuba masa idanu tamkar yaune tafara ganinsa. Atsanake yake sallan harya idar, yay addu'oinsa sannan yamaido hankalinsa kanta, fuskarnan dai babu walwala ko kad'an. "Sholyna ya jikin?". 'Yafad'a cikin lumshe idanu'. Ajiyar zuciya ta sauke, saikuma tafara hawaye, " haba ya khaleel, inakaje haka? Kasaka hankalinmu dukya tashi, nata kiran wayarka kuma kak'i kayi picking call d'ina, why?!". Baice mata komaiba, sai jawota dayayi jikinsa ya rungumeta, ahankali yake buga bayanta. Itama saitayi luf ajikinsa batareda takuma tambayarsaba, Dan tasan bazai tankaba, kusan mintuna 10 suka d'auka haka, sannan yamik'e da ita ajikinsa, gadon suka koma, ya kwanta tareda kwantar da ita ajikinsa, yaymusu addu'a. Shiru nawani lokaci hardai barci farawo ya sacesu sudukan. To asuba tagari🤸🏻‍ ♀🚴‍♀. ____________________________ Hajia babba dai ciwo ya kankama, ko magana bata iya yi saida gefen baki, yawu kuma Na zirara, hakama 6arinta Na dama babu abinda ke aiki, hatta da idonta, sai'an kwantar sai an tayar, babu lalal6awar da su Taheer basima khaleel ba akan yashiga su dubata yak'i, saisu kad'ai sukaje, kuma yak'i fad'ama kowa halin datake ciki agidan. Yanzu yakoma wani shiru-shiru, ko magana kamasa saiya gadamar ansaka, kummlum fuska babu alamar yasan miye dariya. Dole baffa da Anty Mamie suka duk'ufa wajen tofa masa addu'oi aruwa yanasha, hakama Aysha tana nata k'ok'arin, Dan kokad'an itama takasa gane kansa. Anty zuwairah itada Anty shukurah dasu mufeedah har 6angarensa sukazo suka nemi yafiyarsa, musamman ma Anty zuwairah, har Aysha saida ta rok'a ta yafe mata, hakamasu mufeedah. Aysha tace babu komai wlhy, dama bata rik'esu araiba itakam. ********** Yau kuma Ammah tasaka baffah ya tara kowa agidan, bayan jawabi da nasiha mai ratsa jiki aka fara tattauna abinda ya had'asu. Kusan dai suk akan abinda yafarune, baffah da Ammah duksun yima mama godiya, hakama ummi amarya da gwaggo bintu, baffah yace bashida abinda zai saka musu dashi, musammanma mama, yana Addu'ar ALLAH ya sakakanka musu da aljannah, sannan yana neman afuwar mama akan abinda yafaru alokacin daya saketa, hakan tafaru akan rashin Sani da ajizanci irinna d'an adam,. Mama tace babu komai wlhy, dama tuni ta yafe masa, tunda tasan ba laifinsa baneba, kuma komai yawuce, tunda gashi har ALLAH ya k'addara zasu sake zama tare, gashima harda k'yautar 'ya'ya uku ya azurtasu dashi. Itama tabasu hak'uri akan 6oyewar datayi, sannan tayima ummi amarya da gwaggo bintu godiya akan taimakonta dasukayi, takumayi addu'a da fatan alkairi ga family d'in baki d'aya, sannan tabama su Anty zuwairah hak'uri akan su gafarceta, batayi hakan domin cin zarafin mahaifiyarsuba, batada za6in daya wuce haka, saboda rayuwar yara mata dabasujiba basu ganiba dataketa salwanta, inhar irin wad'annan abubuwan zasu cigaba da faruwa muna zuba idanu saboda 'yan uwanmu na a ciki, to haka zamuyita rugujewa, watarana kuma 'ya'yanmu za'a d'auka asaka acikin irin wannan gararin rayuwar, danhaka kumin afuwa Dan ALLAH. "Babu komai wlhy mama, muduka mun fahimceku, kuma hakan shine dai-dai, Dan gashi kuskuren momy harya shafi mufeedah, to watarana Kansu Najwa zai dawo, wlhy bazan ta6a bama momy goyen bayaba akan zama shugaba wajan yaryad'a mutuncinmu akan titiba, nasha damuwa dama akan amintakar dake tsakanin momy da hajia khaltum, amma kona nemijin ba'asin wani abunda sukayi dabai daceba sai momy tacemin sirrine, nadad'e inason Sanin wannan sirri nasu, Ashe bana alkairi baneba, khaleel Kaine kafi cancanta abama hak'uri, domin momy tayi walagigi da rayuwarka, ni nasan wannan tun ina yarinya, saidai zuciyata bata ta6a d'arsamin wani Abu dabanba, saboda nayi nisa wajen kwaikwayo da koyin halayen momy, Dan ALLAH kamin afuwa dagakai har Aysha, Dan itama nasaka hannu wajen k'untata." Jin jina kai khaleel yayi, yace, "babu komai Anty zuwairah, komai yarigada yawuce, har gobe kuma momy nanan dakima a idona, saidai hakan bazai hananin hukuntata akan laifintaba, nima Ku gafarceni tawannan ga6ar, sannan mama ina godiya agareki, kece tushen komai, lallai da ace akwai irinki dayawa agidan aure da kowacce mace tabar kishin banza da wofi, an sace d'an kishiyarki, amma kullum idonki abud'e yake wajen Neman hanyar ku6tar dashi, lallai ked'in jarumace, maihalin dayakamata mata suyi koyi, suzama masu kishin junansu, bamasu kishin abinda zai iya kaisu wutaba, Dan kishin yanzu babu komai cikinsa sai shirme. Ummi amarya kema dolene a jinjina miki, Dan kema kintaka rawar gani irinta jaruman mata masu zuciya Saliha, ALLAH yabiyaki da alkairinsa, gwaggo bintu kece fitilar komai, Dan dabaki bayyana firar momy da hajia khaltum ba babu Wanda zaisan wannan sana'ar tasu, ALLAH yabiyaki da mafificin Alkairi, wannan abin alkairin naki. Yasakani biya miki saudia, sannan namiki alk'awarin siya miki gida a Kano madaidaici tunda bakida 'ya'ya, daga yanzu kuma duk kan buk'atunki dakikejin zaki iya fad'ama d'anki yamiki toki sanar dani su, karkiji nauyin hakan." Kukan dad'i gwaggo bintu tafashe dashi, su Ammah Kuma suka shiga saka masa albarka, kowa kagani sai washe baki yakeyi saboda halaccin da khaleel yayi. Yamaida kallonsa akan Aysha, cikin murmushi yace, "ngd matata, tabbas nagama dacewa, babu abinda zance ga Ammah saidai godiya, kinsha gwagwarmaya domin ganin kin ceto sauran mata 'yan uwanki, gakidai k'arama amma mai kwakwalwa da tunanin manya, irinku k'asarmu take nema, namiki alk'awarin cigaba da sonki daganan har k'arshen numfashina, sannan Na tanadi k'yaututtuka kashi-kashi agareki, amma dagani saike zan bayar, inama iyayena albishir dacewa damacan Aysha ce za6in raina, tunkan sumin tayin aurenta, tun sanda tazo gidannan tana 'Yar mililiyarta...............................................................kaf yakwashe labari yabasu. Nanfa akaita masu dariya, Ammah tasakasu gaba da tsokana. Farincinkin kowa yadawo, kaikace wani Abu bak'in ciki baishigo familie d'inba. Daga k'arshe Anty Mamie tarufe taron da godiya mai yawa agaresu, tareda addu'oin fatan alkairi, sannan tace daga ranar tayima mama k'yautar ya khaleel gaba d'aya, Dan itace tafi cancanta da zama uwa agaresa, kodan wahalhalu datasha adalilinsa, dakuma sadaukar da d'iyarta jininta datayi wa duniya duk adaliln tushen abinda yafaru dashi, takumace daga wannan ranar Aysha ta zama daga cikin 'ya'yanta, dama tun sanda tafara ganinta saida taji hakan aranta. Gaba d'aya aka d'auki kabbara, baffah da Ammah duk suka saka mata albarka, baffah yace, "tabbas nima randa nafara ganin Aysha saida naji fad'uwar gaba, amma narasa tamicece, tunkuma alokacin naga tsantsar kamarta da fad'ima, nayidai shirune kawai Dan banida tabbas, amma lallai Aysha tayi namijin k'ok'arin data cancanci yabo da jinjina ga kowa". ' yak'are maganar da tsokana'. Yace. "Koda yake, kuganefa Aysha gadon jarumta tayi fa". Gaba d'aya aka saka dariya, Aysha ta saka tafin hannunta tarufe fuskarta saboda kunya. Annanne baffah ya yanke hukunci akan hasnah da Husnah su fidda mijin aure, sannan mufeedah takoma gaba d'aya 6angaren Ammah har ALLAH ya sauketa lafiaya itama tasamu mijin aure, yace kuma ya yafe mata, danya d'auki hakan amatsayin k'addara, daganan yakumayin nasiha agaresu, danuna musu illolin hassada, Dason zama wane, dakuma burin Tara abin duniya, Wanda duk ta dalilin hakanne hajia babba ta tsinci kanta a wannan halin, Wanda hud'uba irinta uwa tayi tasiri aranta, amatsayinku Na iyaye kudinga nunama 'ya'yanku abinda zai zama alkairi arayuwarsu ba sharriba, sannan karku ringa zagin wasu agaban 'ya'yanku ko gulmar wani agabansu, koda kuwa mutuminnan yamuku ba daidaiba, hakan nasaka 'ya'ya sutashi da k'iyayyar wani azuciyarsu, harma da burin d'aukar fansa akan laifin dabasu akayimawaba, muzama masu k'yak'yk'yawar zuciya dason junanmu, muruk'e zuminci domin babban abune da ALLAH yamana albishir Na zuwa aljannah a sanadinsa, muzama masu yafiya wa juna alokacin dawani yayma d'an uwansa laifi, ALLAH ya albarkaci rayuwarku gaba d'aya, yasaka k'aunar juna da hak'uri azukatanku, ALLAH ka gafarta mana." Gaba d'aya aka amsa da amin baffah, daganan dai kowa yanemi gafarar d'an uwansa, baffah yace, Anty zuwairah da Anty shikurah su shirya sukoma d'akunansu hakanan, tunda komai yalafa, sukuma cigaba dayima mahaifiyarsu addu'a. Ammah ma tasakama kowa albarka sannan tarufe taron da addu'a kowa yakama gabansa...................✍🏻 Jiya kunjini shiru, anguwa naje tareda Oga wlhy, nadawo kuma a late, babu damar typing a time d'in, ga gajiya kuma. *_ALLAH ka gafarma mahaifanmu baki d'aya, dadukkan 'yan uwa musulmai😭😭😭🤚🏻✋🏻._* [10/26, 4:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ _d'ingimemiyar gaisuwa ta iso agareku_ *_pherty xarah (ALLAH yakaimu ranar aurenki muzo sokoto musha shagali my kakus💃🏻🤸🏻‍♀) & Ummu Aysha (ALLAH ya kaimu ranar auren Aysha muyi rawar shaku-shaku😂🤸🏻‍♀)_*. _ALLAH yak'aro muku haske a rubutunku kuma, ALLAH katsare k'ungiyar Haske dadukkan writers d'in dake cikinta 🤚🏻✋🏻, wannan shafin nakune gwarazan marubuta👍🏻👍🏻👍🏻_ 4⃣8⃣ 'Dakin taron tsit yake, da alama khaleel ake jira kawai, Dan kowa ya hallara, kayan hannunsa ya ajiye tareda had'e hannayensa waje d'aya alamar ban hak'uri da Lattin dayayi🙏🏻. Duk manyansa ne awajen, shikad'aine k'aramima, kwazonsa da jajircewarsa akan aikice tasakasu shigo dashi cikin meeting d'in, Dan abinda za'a tattauna akai shine jigonsa. Bayan bud'e taro da addu'oi suka fara abinda ya tarasu kai tsaye. Jawabai sosai akayi, mafi yawa tashafi k'ungiyar su momyne kuma. Khaleel aka bama damar tashi yayi jawabi akan nasarorin dasuka samu, dakuma abubuwan da aka kama k'ungiyar dasu. Bayan khaleel yayi gaisuwar ban girma agaresu, yayi add'u'oi, sannan yafara jawabi cikin nutsuwa a harshen nasara ingilishi. _"munkama mutane 57 dake cikin wannan k'ungiya, tareda bindugu 16, sai hodar ibilis (cocaine) datakai nauyin cg 1800,0 dawani abu, sannan akwai kwayoyi masu had'arin gaske suma masu yawa, saikuma yara 'yammata damuka ku6tar awani gida su 84, wasu acikinsu anyimusu viza za'abar k'asar dasu, akwai kuma 21 damuka samo a wasu k'asashe guda biyu"._ _har yanzun muna farautar kusan mutane 109 dake k'ashe daban-daban tareda yara kusan kimanin 800 da aka fitadasu tawasu hanyoyi daban-daban ak'asarnan. Akwai uku cikin wad'anda suke hannunmu suna kwance babu lfy acikin asibitinmu, saikuma 26 da suka mutu tawasu dalilai, wasu aciki mune muka harbesu, wasukuma sunmutune kawai, akwai mutum d'aya da aka bashi guba yamutu, Wanda munan muna bincike akan hakan, insha ALLAH kad'an garage mukawo sunayen masu hannu acikin kisan nashi."_ Saikuma mutun kusan 78 dawasu k'asashe suka samu kamawa 'yan Nigeria, wad'anda aka tabbatar sunada alak'a da k'ungiyar, suma munata k'ok'ari wajen ganin mun kar6osu, andawo dasu nan gida Nigeria ammusu hukunci dai-dai dalaifinsu. Da akwai mutane 13 ahannunmu dasuka fito daga k'ashen k'etare suma, wasu k'ashen suna buk'atar mubasu 'yan k'asarsu domin sumusu hukunci a k'ashensu, to badai muce musu komaiba har yanzu, munanan muna tattaunawa akan batun dai. Saikuma jami'an tsaro dasuka fito a fannoni daban-daban guda 11 damuka samu cikin wad'an nan criminals, bincikenmu kuma ya tabbatar akwaima wad'ansu dabasu halarci wannan taronba aranar da'a kamasu, kuma gaskiya acikin manyane, dole saida had'inkan Ku za'a samu Damar kamasun, dukda akwai shirin damukeyi ta k'ark'ashin k'asa akansu. Wannan shine bayanan da k'ungiyar tashafa, saikuma wad'anda basuda alak'a da k'ungiyar, muna shirin mik'a wasu kotu. Suma d'in zamu shirya kaisu kotu acikin next week insha ALLAH. AKWAI mutane uku dake hannun hukuma sss, d'aya d'an k'ungiyarne, biyu kuma laifinsu daban, munason suma subamusu danmu saka d'ayan cikin 'yan uwansa. Yak'ame tareda salute Nasu Baki d'aya, sannan yadawo wajen zamansa ya zauna. Gaba d'aya aka d'auki tafi, jikake raff raff raff!!!. Lallai dolene hukumar police Interpol tamik'a gagarumin jinjina dayabo akan wannan gwarzon ma'aikaci nata, wannan hukuma da Nigeria harma da duniya baki d'aya bazasu ta6a mantawa da Ibraheem Abdallah ba, j! gwarzon ma'aikacine dayakamata ayi koyi dashi akowanne fanin d'ammara Na kaki, yakawomana nasarori masu yawan gaske, Wanda bamu kad'aibama duniya gaba d'aya dolene tayi alfahari dashi, yaje k'asashen duniya daban-daban yagudanar da aikinsa cikin nasarori, sannan wasu k'asashen sun gayyacesa domin taimakonsu duk Dan kwazonsane kuma, wannan k'ungiya damuke magana akanta ankai kusan shekaru 16 ana bincike akanta, amma bamu samu wani bakin zareba saida aikin yakoma hannun j!, jinjina agareka Ibraheem Abdallah, ALLAH yacigaba da haskaka rayuwarka kaji, ALLAH yasa ka d'ore ahaka kar watarana ka canja. Gaba d'aya aka amsa da ameen. Yacigaba da fad'in akwai ganawa da shugaban k'asa daza'ayi gobe a fadarsa, kowanne hukuma taza6i mutane uku dazasu wakilceta, sannan annad'a Wanda zaizama kwamitin shugabancin wannan zama baki d'aya. Mudai anan J! Yana ciki, sannan kuma shine shugaban wannan kwamiti gaba d'aya dazai jagoranci wannan zama har fadar shugaban k'asa. Nanma aka d'auki tafi gaba d'aya, kowa yayi na'am da hakan, saidai fuskar mutum biyu babu alamar sun amshi zancen, kuma koda khaleel yake bayani babu alamun jindad'in bayanan nasa, babu Wanda yakula da hakan sai khaleel da hankalinsa ke akan kowa, tunda dama yana zargin wasu manyansu acikin k'ungiyar, akwai guns kusan 6 acikin wad'anda suka kar6a duk Na jami'an tsarone, sannan ankama wasu acikinsu masu kaki. Haka sukaita tattaunawa, kowa yana kawo albarkacin bakinsa, da hanyoyin dazasubi domin dak'ile ta addacin da'akeyi acikin gida da k'asashen k'etare ana zubarma da Nigeria mutuncinta. Har 1:30pm suka kai ad'akin taron sannan aka tashi, amma khaleel yariga kowa fitowa, bama arufe taron dashiba yanemi excuse saboda time d'in sallah yayi, wad'anda suke musilmai awajen sai kunya Takamasu, dansu ko alamar tunawa da za'a shiga time d'in ibadarsu basu nunaba, saima k'ara 6ararrajewa suke suna sakin bayanai. Shi dai khaleel yamusu sallam yafito, akan idan basu kammalaba har aka idar da sallah to zai dawo, idankuma sun tashi shikenan. 🙂👍🏻irinku mukeso khaleel masu girmama addininsu samada uzurorinsu Na duniya, wad'anda basa shakkar gudanar da ibadar aduk Inda suka tsinci kansu, masu kishin bautar ALLAH. (Bawai ta addanci bane addini, Adinin musilinci ba addinin 'yan ta'adda baneba kamar yanda duniya take fad'a ahalin yanzun, duk Wanda kagani musilmi d'an ta adda to tabbas baya cikinmu, yana amfani dahakanne kawai domin kansa, sannan shid'in ru6a66en musulmine, mukuma maba d'aukarsa d'aya daga cikinmu, addininmu zaman lafiya da adalcin k'yautatawa junanmu yakoyar damu, yanunamana muhimmancin adalci gawad'anda bama addinimu d'ayaba, addinin musilinci adalin addinine, dake koyar damu k'yawawan ayyuka, sannan addinine mai sauk'i, danhaka duk wani d'an ta'adda dazai kira kansa musilmi munce k'aryane, shiba mabiyin addininmu baneba, ISLAM IS THE BEST RELIGION💪😭. Wlhy iyaye Ku kula sosai akan films da 'ya'yanmu suke kallo, musamman wad'anda ake nuna Muslim's amatsayin 'yan ta'adda, yaranmu kwakwalwarsu k'aramace, komai suka gani zasu iya d'auka hakane dai-dai, ALLAH yasa mugane.🤚🏻✋🏻😭 _____________ Koda aka fito sallah yaga sunfito saiya wuce office, zamansa babu dad'ewa youseef yay knocking d'in k'ofar, izinin shigowa yabashi. Ya k'ame tareda yin salute Na ya khaleel. Kansa ya jinjina masa sannan yamasa alamar ya zauna, bayan ya zauna khaleel yamik'o masa hannu sukayi musabaha🤝🏻. Takardun dake hannunsa yamik'a masa, sir! ga wad'annan bayanan, mun tattarasu duka, insha ALLAH komai zaka samu. Maganar Munner kuma munata bibiyarsa ta number d'insa, haryanzu kuma yana cikin abujarnan. Saidai yayi wata waya damukayi recording ". 'Yay maganar yana mik'a masa k'aramar wayarsa.' Kar6a khaleel yayi yakunna record d'in yana saurara. bayan yagama saurare yamik'ama youseef wayar yana furzar da isaka. " naji youseef, shima zaibi jirgin 6:30pm ne zuwa Kano, kiramin Adams". ''OK sir". Babu dad'ewa saiga Adams, cikin girmamawa yace, "gani sir". ''Ok, uhm dama inason naji katanadar mana jirginne?". " yes sir!". "Uhm Na k'arfe nawa?". " 6:30pm". "OK, bama saimunje kanoba, zamu kamashi a airport kawai. youseef kiramin Joseph, kace yayi shiri kune zakuje kama Munner, zuwa 6pm kaidashi Ku tabbatar kunzagaye airport, kaga insha ALLAH kafin akira sallar magriba kun gama da matsalar". " babu damuwa sir, barama naje nasamu Joseph d'in a office, amma sir danazone please akan hajia, kadaure muje ka ganta, kullum saita ambaci sunank......... Kasa k'arasawa youseef yayi, saboda wani mugun kallo da khaleel ya watsa masa. 🙏🏻" ALLAH ya huci zuciyarka sir". Khaleel baice komaiba ya kauda kansa daga kallon youseef d'in. Jiki a sanyaye youseef yamik'e, yay salute nashi sannan yafice. Adams natsaye baice komaiba dai, amma shima yanason yarok'eshi akan yaje d'in, saidai yana shakka. d'ago ido khaleel yay ya kalleshi, "akwai damuwane". 'Ya tambayi Adams yana maida idonsa a kan computer dayake latsawa'. " a'a sir!, amma........ ......Amman mi? Indai akantane karkacemin komai". Yak'atseshi da Sauri. Wani yawu Adams ya had'iye tareda girgiza kansa, shima saiyayi salute nashi yafice. Binsa da kallo khaleel yayi, ya sauke numfashi tareda dafe kansa, ahankali yafurta momy kingama da rayuwata, ALLAH ne kawai kerik'e da zuciyata, amma datuni ta tarwatse☹✊🏻. Agurguje inji Perty😉 ******** Alhmdlh aranar su Youseef sunsami nasarar cafke Munner, kuma cikin sauk'i da nasarori. **** Kusan 8pm khaleel yakoma gida, saida yafara shiga cikin gidan, Dan yanaso su gaisa dasu Anty Mamie, yau yafita da wuri basu gaisaba. K'annensa suna falon, harsu Hasnah, fira suketayi, su Affan naganin khaleel suka taso da gudu sukamasa oyoyo, rungumesu yayi shima yana farincikin ganinsu, d'ai-d'ai yabisu ya sumbaci kumatunsu, shima duk haka suka sumbaceshi. Manyan kuma suka gaidashi. Da 'Yar sakin fuska ya amsa, yabisu da kallo d'ai-d'ai amma babu Aysha. "Su mamafa?". 'Yay maganar idonsa akansu'. " mama sunfita itada baffah, ummi Amarya kuma kanta ke ciwo ta kwanta, Anty Mamie tana d'aki itama." Batareda yace komaiba yanufi d'akin Anty Mamie, saida yay knocking tabashi izinin Shiga sannan yatura k'ofar yashiga da sallama. Da Aysha yafara cin karo zaune kusada Anty Mamie tana bata dambu abaki. Suduka idonsu nakansa, duk suka masa sannu da zuwa. A sanyaye ya amsa yanamaijin k'aunar mahaifiyarsa har cikin ransa. K'arasowa yayi ya zauna d'ayan gefen Anty Mamie shima. "Babana andawo?". Kansa ya jinjina mata, ya d'ora kan nasa agefen kafad'arta yana kallon Aysha, yace, " Mamie kidaina shagwa6a yarinyarnan, jiyafa ta6ara taitamin iri-iri." Aysha tad'an murgud'a masa baki, tana fad'in "jealousy kawai". Anty Mamie kam 'Yar dariya tayi, " babana aidolene Na shagwa6ata, bakaga ba ita kad'ai baceba, yanzu hakama abinci taci tayi amansa, shine matar zunnurain tayi dambu takawo mata, inad'an lalla6atane tanaci". Rankwashi khaleel yamata agefen kanta, takuwa kware baki ta zabga k'ara tareda dafe kanta. Da sauri Anty Mamie ta rungumota jikinta, shima tamasa rankwashi biyu akansa. Dafe wajen yayi yana fad'in "uchhhh, dazafi wlhy Mamie". " oooh kasan dazafin amma kama yarinyata? duk wata mugunta ka iyata babana salo-salo ko?". "ALLAH Anty Mamie yarinyarnan batada kunya, kigafa murgud'en takemin harda gwalo? kibarni kawai Na caskalata". Cikin 'Yar dariya Anty Mamie tamik'e daga tsakkiyarsu, ''kunga kutashi kuje 6angarenku, bazan iyaba dawannan rikicin, kuje wajan Ammah Tamuku shari'a". " uhm tab, lallai Anty Mamie, yanzu naje wajan jar wuya aii bakina saiyaje gate, dama haushina takeji nak'i saya mata mota. "Hhh kunfi kusa aii". Jakkarsa Aysha tad'auka tafita tana dariya, tabarsu dansud'an gana. Binta khaleel yayi da kallo yana murmuahi da jinjina hankali irin nata, yamaido kallonsa ga mahaifiyar tasa, wadda itama ayshan tabi da kallo murmushi d'aukeda fuskarta. Khaleel yamatso kusada Anty Mamie, hannunta Na dama yakama ya sumbata, sannan yad'auki hannun yad'ora bisa kanta, murya amarairaice yace, " Mamie Na kisamin albarka, a office an za6eni cikin wad'anda zasu gana da shigaban k'asa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma nine shugaban dazai jagoranci kwamitin ma, wlhy duk fargaba tacikani, tunda safe naketa tattara bayanan dazanyi agaban shugaban k'asa ina kwancewa, narasa wanne zan d'auka, gashi inason kai kukana akan manyanmu danake zargi da hannu a k'ungiyar su momy." Murmuahi Mamie tayi, tashafa fuskarsa da d'ayan hannunta, murya a sanyaye tace, ''karkakji tsoro babana, nasan kaid'in jarumine kuma jajurtacce, kasaka aranka CIKI DA GASKIYA, WUK'A BATA HUDASHI, shugaban k'asa mutumne kamar kowa shima kuma yanada sauk'in kai, danhaka karkaji tsoro ko shakkar ganawa dashi, katuna bayaune kafara ganawa da shugabannin k'asashen duniyaba." "Duk inda kake addu'ata nabiye dakai, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, yatsareminku aduk inda kuka tsinci kanku, kaje kayi wanka kahuta danka samu isashshen lokacin kanka". " idonsa cikeda kwallah yace amin Mamana, farincikina, haske mai haska rayuwata, ALLAH yak'ara tsawon rai mai amfani da ingattacciyar lafiya", 'yak'are maganar da sumbatar hannunta'. Jiki a sanyaye yamata sallama yafice. Hawayenta tashare, tana murmushi, ahankali tace, "ALLAH Na gode maka". 6angarensu yanufa, dan baiga Aysha ananba, yasan tawuce. Agurguje😎 ___________________ Washe gari su khaleel suka samu damar ganawa da shugaban k'asa, sunsami tarba mai k'yau daga fadar shugaban k'asa, sunkuma tattauna muhimman abubuwa dazasu kawo cigaban k'asa, dakuma yanda za'a dak'ile ta'addancin dake faruwa ak'asarnan. Sund'au tsawon awanni kusan 5 taredashi, tarema sukayi lunch da president da tawagarsa, yamusu jinjinar bangirma tareda k'yaututtuka masu k'yau, musamman ma khaleel saboda k'ok'arinsa, sannan suka gana da 'yan jaridu Na awa d'aya. Sunyi sallama da shugaban k'asa suka tafi, bayan khaleel yabama wani makusancin shugaban k'asar short note domin yabashi.😎👍🏻 ________________ Akwana atashi babu wahala wajen ubangiji, kwanaki Na Sauri sati Na gudu, watani tamkar sati ya koma. Acikin wannan gudun fanfalak'e da suniya takeyi yau ga cikin Aysha yashiga watanni takwas. Abubuwa masu yawan gaske sunfaru awannan tsakanin, ciki harda kammala bautar k'asa da Aysha tayi, (Nysc) Alhmdlh tagama cikin nasarori. Rufaida da sadiya duksun haihu, Aysha kuma taje har Kano suna, kwannta 8 a can, saboda khaleel baya k'asar alokacin, amma da k'yar yabarta taje. Matar youseef ma ta haihu baby boy itama, hakama bishirah, ta haihu, da k'yar khaleel ya yarda Aysha tabi gwaggo bintu sukaje suleja suka mata barka. Mufeedah ma baiwar ALLAH, anata Jan ciki, ita harma tashiga watan haihuwarta. Ansaka bikinsu hasnah, watanni hud'u kacal, harda musleem dasu maleekah ma, baffah yace gwamma ya aurar dasu kawai yahuta baki d'aya, yazauna da 'yan k'ananun 'ya'yansa su ummunoor. ******* Momy dai ana nan anata shan jinya, amma jikin NATA da sauk'i, saboda tana samun kulawa, Idan tayi magana anaji yanzu, sannan tana motsa hannunta kad'an-kad'an. da k'yar khaleel ya yarda yashiga ya ganta tana barcima lokacin, danhaka batasan yajeba, yafad'ama su baffah suma sunje sun ganta. Babu wanda bai zubar mata da kwallaba ganin yanda duk ta lalace, ta canja kamanni kamar ba itaba, k'ibarnan dukta zube. Hawaye taita zurarrwa saboda ganinsu, magana take amma basajin mitake fad'a, dole suka hak'ura. Saida Baffah yayta lallashi daban magana sannan khaleel yayarda yasakko innah jummai, amma da yasaka anyi rammm da ita a station d'in su, yace anan zata k'are sauran rayuwarta. Saida k'yar da lallashi yayarda yasakota. Rasa inda zata nufa tayi kuwa, doledai tadawo gidan mak'iyar tata Ammah, suna zaune awani yammaci kawai saigata tamkar an jehota. ALLAH Sarki d'an uwa mai dad'i, saiga Ammah takar6eta da hannu bibiyu, suka rungume juna suna kuka, daneman yafiyar juna. Annan innah jummai tazauna sabodama batada isashshiyar lafiya, ciwon k'afa da hawan jini.😏 ____________ Su khaleel duksun gama shirye-shiryen kai k'ungiyar su momy kotu, sunsami nasarar cafke sauran mutanen dasuke zargi, dakuma kar6o Na k'asashen k'etare, ciki harda manya-manyan mutane wad'andama bazaka ta6a tunanin akwai saka hannunsuba............✍🏻 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀kumuje zuwa yanda zata kaya a kotu, dolene masu laifi su kar6i hukuncinsu ahannu😎🖐🏽. 🤕yanzu saboda buk yazo k'arshe, ankama muku hajia babba shine babu comments ko, aiko zan ajiye nak'i k'arasa typing d'in😎, rashin comments d'inkuma yasakani jin gandar typing d'in wlhy,☹. Idan naga ruwan comments yau, kwaji yanda takaya gobe, idan naji shiru, nima nawuni barci abuna yafimin dad'i😏😏. Yawan comments, yawan girman hukuncin su hajia babba😎😎😎👯‍♀ *_I love you all_*💋💋💋💋 [10/26, 4:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......._* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASSO......_* _(Home of experts & perfect writer's)_ *_part 2_* _(littafi na biyu📘)_ _ina kike *Asy khaleel*?, wanga page nakine, babanki khaleel namik'o gaisuwa ta musamman, taredani bilyn Abdul😊._👍🏻 Kuma banmanta dakuba wlhy. Fatima Abubakar, Ummi Alhassan, Rabi Sanusi, Aaliyah, Fatima, Zainab Ahmad, Xeety, Sameera Bello. Alkairin ALLAH ya iso gareku💋💋💋💋❤🤝🏻 4⃣9⃣ *_Monday morning_* _Cote_. A yau ranar litinin 8/9 aka shiga shari'arsu momy, abbabban kotun k'asa da k'asa ta Abuja. Anyi zammne misalin 10am, tareda lauyoyi masu kare gwamnati dakuma lauya mai kare 'yan ta'addar wannan k'ungiya. Bayan Alk'ali ya saurari k'arar dakuma jawabai abakin lauyoyin guda biyu. Am fafata sosai, amma ba a yanke hukuncinba, sai azama Na gaba insha ALLAH. Ran khaleel yad'an 6aci, soyayi ayita kawai yau ta k'are, amma babu komai, ALLAH ya kaimu randa alk'alin yasaka. Aysha Na zaune afalo zama da k'yar tashi da dabara, dukda cikin nata bawani uban girma yayiba, kunsan cikin fari dama bakowanne keyin k'atoba. Sallamar ya khaleel yasakata d'ago ido ta kalleshi. Cikin murmushi tace, "sannu da zuwa sadauki na, yau da wuri haka?". Kusada ita ya zauna yana murmushin shima, yadurk'uso ya sumbaci cikinta, " babies na inafata kuna cikin k'oshin lfy? Injidai maah-maah tabaku abinci?". "Tab abinma dariya, ALLAH Sadauki idan kana wannan abun dariya kake bani, waya gayamaka yara biyune to?." Matsawa yayi sosai, ya mannata da jikinsa, acikin kunne yarad'a mata abinda nima banjiba. Aysha ta tureshi tana fad'i ''kai kai ALLAH nidai babu ruwana, saima Na fad'aka da Ammah". "Hhh dubeta kamarma zata iya". " OK haka kake zaton bazan iyaba ko? Kajira sammaci". 'Tayi maganar tana komawa k'asa'. K'afarsa takamo tafara k'ok'arin cire masa takalman. Shikuma yana fad'in "kibari kawai, kinma tunamin wlhy, wai shegen alk'alinnan dukda hujjoji da lauyanmu yabayar yad'aga zaman kotun nan harsai next week". " to aii babu komai sadauki, dayau da wani satin duk d'ayane, insha ALLAH za'a yanke musu hukunci dai-dai dasu, wahalarmu bazata tafi abanzaba aii, mugodema ALLAH ma da nasarorin daya bamu duk aka kamasu". "Hakane kuma sholyna, su john ma k'asarsu hukuncin kisa ta yanke musu". " woow! Dan ALLAH da gaske sadauki!?". "I'm telling you". " kai alhmdllh, amma naji dad'i sosai wlhy, nasan Anty meerah saitafi kowa farinciki dahakan, tsinanne, dama dukmasu hali irinnasa k'arshensu kenan, sugama tara dukiyar kuma daga k'arshe tazama mara amfani agaresu, saidai wasu suci kuma". "Hakane wlhy sholyna, gadai su momy nan inda suka k'are, ita wannan ciwonma data tsinci kanta kad'ai ya isheta, munyi magana da Anty zuwairah akan dukkan kud'ad'e da kaddarorin momyn, kawai zamu kaisu gidan marayu, danbanga amfaninsuba, baffah yace babu Wanda zaiyi amfani dasu agidannan". ''Hakan shine dai-dai aii sadauki, to Amma su Lola fa? naga suma sakasu akayi bashiga sukayiba". " eh, hakane, amma kinsan mutanenmu da bushewar zuciya, dukda sunga an hukunta wad'annan bazaisasu dainaba suma, sunrigada sun saba da iskancin, dakuma kama kud'ad'e masu nauyi, yanzu koda an sakesu suma tasu dabar zasuje su kafa. Amma dai munan muna tattaunawa akansu, sauran yaran kuma duk mun maidasu hannun iyayensu". "Aii kunyi dai-dai wlhy, jaridun k'asarnan gaba d'aya wannan satin labarinkune kawai aciki, nasan gaba d'aya idanun al'ummar Nigeria Na kanku yanzu, kai duniyama baki d'aya, jira kawai akeyi aji irin hukuncin daza'a yankema wannan k'ungiya". "Hakane wlhy, yanzufa da k'yar Na kufto daga hannun 'yan jarida, Taheer nabar musu nagudo, saiya bar wajen yayta tsinemin azuciya d'an iskan". Dariya Aisha tayi, tace, " aiini wlhy birgeni kukeyi, yanda kuke tafiya da rayuwarku a tsari, idan fannin aiki kuke komai cikin girmamawa suke makashi, basa kallon kaid'in abokinsune, hakama idan aka dawo fannin abota kashige cikinsu kuyita barkwanci, baka kallon kai ogansune awajan aiki, lamarinku daban dana sauran jama'a sadaukina." "To miye duniyar Sholyna, watarana komai saikiga yazama tarihi, saidai atuna sunanmu badai mud'inba, su Youseef mutanene masu kwazo, kinga tunda nabasu shawarar mukafa k'ungiya taimakon matasa babu musu suka amincemin, yanzu haka nake fad'a miki mun samama matasa kusan 200 aiki wlhy, banda wad'anda muka samama sana'oi, dakuma wad'anda suka koma makaranta, aikinga wannan nasarace, watarana basaikiji sunkai irin dubu biyar d'innanba, inaga hakane yakamata masu kud'in k'asarmu sunayi, musamman ma 'yan arewa dan mutanan kudancin k'asarnan tuni sun waye da irin wad'annan taimakon, amma 'yan arewa ina, kowa burinshi akirashi wane, zakiga kowanne banki mutum yanada kud'i, gawasu agida, motocin hawa Na alfarma, saka manyan kaya masu tsada, agogo wannan saikiji Na million d'aya ahannunsa, 'ya'yansa kowanne yanada account nakansa, ga hannun jari a ma'aikatu daban-daban, shin dukmi zakayi dasu?, kasan dai baza'a gina rami arufeka dasuba ko?, kiga mutum yak'are rayuwarsa kaf aneman dukiya, babu kwakwkwarar ibadar dazai rik'e tazame masa guzurin shiga kabari, wlhy kaiconmu dawannan makauniyar rayuwa, bazakasan kana cikin babbar asaraba sai mala'ikin mutuwa yazo kanka, lokacin babu tsumi babu dabara kuma?". "Wlhy hakane Sadauki, ai gaskiyafa 'yan arewa muna cikin halin hau, kowa dagashi sai 'ya'yansa, shiyyasa kullum kuma mune abaya, masu k'aunarmu da gaskiya dason dawomana da martabarmu irinsu BUHARI kuma toshewar basira tahanamu ganewa, munfison awatsa mana tsaba mu tsatstsage alokacin, batareda munyi tanadi wa gobenmuba, inhar za'a cigaba da tafiya haka aii wataran sai'an shafe tarihin arewa da al'ummar cikinta, shiyyasa nake tausayin 'ya'yanmu wlhy". " dolene subaka tausayi, ayanzuma jibi yanda duniya take walagigi, inaga nanda shekaru 20 masu zuwa, ALLAH ka gafarta mana dai kawai." "Ameen to". 'Aysha tafad'a tana yunk'urawa zata tamik'e'. Saida ya taimaka mata sannan tasamu tatashi. "Sannu sholyna kinji, insha ALLAH saura kad'andai ki juyomin babies d'ina ki huta muma mu huta". "ALLAH ya kaimu, dama nagaji nikam, tashige kichin". Shima mik'ewa yayi yana dariya dafad'in ''k'ya gaya musu yarinya, kina juyewa zankuma ajiye wani aii".😂😜 ****** Rana bata k'arya....... Yaukam kotu tacika dank'am da jama'a, su Kansu 'yangidansu ya khaleel kwansu da kwarkwata sun halarci zaman, harda innah jummai datak'i komawa Jigawa har yanzun🤣, saboda tsoron dariyar mutane, da anamusu fafa su masu kud'i.🤪 Tunda hajia babba taga gayyar 'yan gidansu taketa zubda hawaye, tama kasa had'a ido da kowa awajen, su kansu duk hankalinsu nakanta, ko kad'an Aysha bataji tausayin kowaba acikinsu, musamman ma hajia babba da hajia khaltum, glory, kubrah. Saima d'an karan dad'i dake ratsa zuciyarta da ruhinta, yauga mak'iyanta gurfane agaban kotu, abinda bata ta6a zaton zai faruba ko a mafarki, dantasha jin labarin makamanta wannan cases d'in natafiya abanza, batareda ankama koda masu laifinbama bare agurfanar dasu gaban kotu. Kotu tayi tsit ana sauraren jawabi daga lauyoyin na 6angarori biyu, lauyan gwamnati yakawo kwararan hujjoji, tareda manyan shaidu irinsu ya khaleel, wad'anda ganaune ba jiyauba. Shiru nawani lokaci Alk'ali yana bincika hukuncin dazai yanke. Alfarma hutun mintuna talatin aka d'auka, Alk'ali da jama'arsa suka shiga wani d'aki domin tattaunawa. Kusan mintuna talatin saigasu sun shigo, alk'ali ya zauna, bayan wasu 'yan mintuna yad'ago idonsa dake sakaye acikin glass yana kallon jama'ar kotu, yay gyaran murya tareda gyara zamansa. "Wannan kotu mai alfarma tayankema wad'annan mutane hukuncin dai-dai da laifinsu, saboda fasa kaurin miyagun kwayoyi dasukeyi, dakuma safarar yara mata, tawani fanninma harda makamai, laifinsu yahad'u dayawa, wannan yasaka bamuda kwakwkwaran hukunci, bisa nazari dawannan kotu tayi, da taimakon manyan lauyoyi anyankema dukkan wani dake cikin wannan k'ungiya hukuncin d'aurin shekaru 40 babu Tara, sannan babu wani dakeda lasisisn fitar dasu koda wata gewamnati tazo annan gaba, akwai horo mai tsananin gaske da azabtarwa da'aka tanada musu agidan kaso. Mutun uku acikinsu basuda isashshiyar lfy, d'aya tasamu sauk'i, za'a wuce da ita gidan kaso, amma akwai alfarmar idan anga ciwonta yatashi amaidota asibiti tacigaba da kar6ar magani, idan tasamu sauk'i sai'a maidata cikinsu. Guda biyukam abarsu a asibiti sucigaba dashan magani harsu sami sauk'i sannan asakasu cikin 'yan uwansu. Akwai jami'an tsaro 26 acikinsu, wannan kotu tamik'a nasu case ga hukumominsu, zasumusu hukunci a cotes nasu, ga sunayensu kamar haka......... Tsaf Alk'ali ya lissafoau, harda Ak'ilu Abbas, dakuma wani ogan khaleel Wanda khaleel yata6a fad'a masa saiya binciko dukmasu hannun alamarin, dawasu k'ananun ma'aikata. Sai tsine musu akeyi, khaleel yay murmushin jin dad'i tareda fad'in Alhmdllh, yakai dubansa ga momy wadda itama shid'in take kallo, idonta cikeda kwallah, kasa jurar kallonta yayi, domin haryanzu tanada kima a idonsa, dukda tareneshi akan wata manufa tata tadaban, shi kallon uwa yake mata har gobe. Daganan kotu tatashi. Bayan duk an fito khaleel yaja tawagar 'yan gidansu har inda hajia babba take akan keke ana turata, saboda bata iya tafiya. Cikin takun k'asaitarsa da jarumta tareda izzar kwarjini Na nutsuwa da cikar kamala yake nufota, kallonsa takeyi wani tuk'uk'in bak'inciki Na azabtar da ruhinta, saidai babu damar koda magana. Baice komaiba yaja gefe yatsaya, tareda jingina da bango ya hard'e k'afafunsa da hannayensa ak'irji. Baffah ne yake magana cikeda 6acinrai, tunda abinnan yafaru saiyau bakinsa zai furta wani Abu kuwa. "Laure kinga k'arshen mutum mara godiyar ALLAH ko? Kinga yanda rayuwar mutum mai buri da hassada take k'arewa, komi katara, komin k'arfin ikonka saika dawo k'asan k'asa, mutum mak'ask'anci, shin miye ribar dakika samu laure?, nasan ko alhakin raba d'a da mahaifiya bazai k'yalekiba, ga alhakin salwantar da rayuwar yara masu d'unbin yawa dakikayi, kinmanta dacewa UBANGIJI Na gaggawar kar6ar addu'ar Wanda aka zalinta koda baiyiba." "Aike koda babu wani hukunci da'aka miki kin tsinci abinda kika girba tun adiniya dagake har aminiyar taki, kalli k'afar khaltum yanda take fidda tsutsotsi saboda ru6ewa datayi, kekam kalleki dukkin lalace, ga 6arin jiki baya aiki, ga hawan jini ga ciwon zuciya, ga 'ya'yanki sun tsaneki, zuwairah saboda halinki tace bazatazoba, Dan bata buk'atar ganinki, hakama shikurah, kinraba khaleel da mahaifiyarsa, kekuma ALLAH yarabaki danaki 'ya'yan, hummm bara nabarki haka, kije Na sauwwak'e miki aurena, dan bazan iya cigaba da kallonki amatsayin matata ta sunnaba, tabbas kinci amanata dayawa Laure, amma darajar 'ya'yan damuka Haifa dakuma zumincin iyayenmu, kije nayafe miki, ALLAH ya shiryi zuciyarki idan kinada rabon shiriya." Da k'arfi hajia laurah ta kwallah k'ara, wadda rabonda aji muryarta haka har an manta, kuka takeyi harda kururuwa, tana kiran tashiga uku ta lalace, Dan ALLAH amata rai, baffah yayi hak'uri, ya yafeta, karya saketa, wlhy tana sonshi har yanzun, innah kin cuceni, bazan iya yafe mikiba, kin tagayyara rayuwata tareda salwantar da'ita saboda son duniya da hassada akan abinda ALLAH ne kawai keda ikonsa, inama bakece uwataba innah, kaiconki innah keda masu hali irin naki, ALLAH ya Isa tsakanina dake da khaltum, kuncuci rayuwata, Khaltum kema ALLAH ya tsinemiki, yacigaba da tagayyara rayuwarki khaltum, insha ALLAH bazaki sake jin dad'in rayuwarkiba khaltum, innah sai ALLAH yamana hisabi nida k........ Maganarta takatse lokacin dasukaji fad'uwar Abu, koda suka waiga saiga innah jummai kwance wanwar. Tashin hankali kenan, aii sai hajia babba takuma rikicewa da ihu, cikin gaggawa aka d'auketa zuwa asibiti. Aysha tamatsa kusada su kubrah tana musu kallon raini, "manyan mata haka kuma rayuwa tak'are?, aiduk ABINDA KA SHUKA, SAIKA GIRBESHI glory da kubrah, ai babu mai babbar asara sama daku, garama su hajia khaltum, su sun haihu, kuko aurenma bakuyiba bare kubar Wanda zaimuku addu'a, ALLAH karabamu da asararriyar rayuwa irin taku dai, kud'in antara kuma babu amfanin cinsu, idan Na haihu zankawo muku babie har prison kukagani kunji😂👎🏻. Bak'inciki tamkar yakarsu, wai wannan 'Yar yarinyarce ke fad'a musu magana haka?, kai kaiconsu dawannan rayuwa. Khaleel kam kasa cema momy komai yayi, saidai kallon kallo tsakaninta dashi, a yaukam wani matsanancin tausayinta yaratsa zuciyarsa, amma yanaso tad'anyi zaman prison d'in koda Na wattannine ta d'and'ana taji, kodan zuciyarta takuma nadama da sassautowa, Kodan masu hali irin NATA karsuji sha'awar yi. yaja hannun Aysha sukabar wajen. Aysha tajuya tana musu gwalo😜.. Ho sholy, ho sholy🤣🤣🤣🤣🤸🏻‍♀ __________________________ Kulli nafsin za'ikatul maut... Sakamakon abinda yafaru zuciyar innah jummai tabuga da ajali, fad'uwar datayi ko shurawa batayiba awajen, koda sukaje asibitima dubwar farko doctor Faisal yace saidai hak'uri tarasu. Wayyo Ammah tasha kuka kuwa, itakad'ai gareta 'Yar uwa gashi tatafi tabarta, d'iya d'aya tilo data haifa kuma tak'are agidan prison, saidai jikoki da ALLAH yay nufin zata bari. Zuwan su khaleel gida dai-dai dakawo gawar innah jummai. Anmata suttura tareda sallah aka mik'ata makwancinta, sauran bayani yarage tsakaninta da ubangijinta. Mudai namu ALLAH yajik'anta, Dan babu maishiga tsakanin bawa da ALLAH.😊 ******** Bayan kai innah jummai kuma sai mufeedah tafara nak'uda, babu shiri aka kwasheta zuwa asibiti itama. Tasha bak'ar wahala kam, harma anfidda rai daita saikuma tahaihu, amma d'iyar batazo da raiba, wannan yasaka aka mata allurar barci domin tahuta. Sannan doctor yazo yasanar musu halin da'ale ciki. Aunkar6i jariri k'yak'yk'yawa, kamar mai rai, sukaje aka binneta itama. Mufeedah kuma tacigaba da jiyyar sati d'aya a asibiti, sannan aka sallamota. Zancen yanke hukuncin su momy yazagaya ko ina acikin duniya, gidajen jaridu da redio, TV, social media daduk wata kafar yad'a labarai, akuma lokacinne khaleel yayarda 'yan jaridu sukai hira dashi. Suma sauran jami'an tsaro d'innan anyanke musu hukuncin kisama a kotunansu. __________ Alhmdllh hankalin khaleel ya kwantakam yanzu sosai, saidai 'Yar damuwa daba'a rasaba, Dan haryanzu yakasa mantawa da momy, shak'uwar shekaru talatin dawani Abu bawasaba fans, saidai kawai hak'uri dayawan addu'a. Yanzunkam rayuwa tana cigaba da gara musu cikin farinciki, khaleel yana bama Aysha kulawa tamkar tsoka d'aya amiya, hakama su Anty Mamie, ammah jar wuya kam aiba'a magana, kayanta takwaso tadawo tana kwana 6angaren su khaleel, darana saita koma 6angarenta, duk tanayine dankar nak'udar dare takama Aysha, tace ya khaleel bashida hankalin sanin nak'uda🤣. Aikam yahad'e fuska yana zabga mata harara. "Yo mikika maidani jar wuya? haihuwarma saina kar6a, saidai kuji kukan jarirai". " kai da Allah can dogon banza, yo banda rik'e bindiga da makar 'ya'yan jama'a uwarmi ka iya, sai mazurai ko?". "Wanene zaibarka kar6ar haihuwa kamurd'e kan jaririn tunma baizo duniyaba". " hhhh amma kinga inda nake barci jar wuya, shikenan duk abinda kikemin abakacin motarki to". "A'a tsayamana kaji irorona, ainidaka babu haka, kaidai mik'o, indai kasiyi motarnan aizan barka, saina koma kan sultani d'in banzarcan". " wlhy Ammah ki kiyayeni". 'Cewar sultan'. "Ank'i kiyayarka d'in d'an kwal uba farin banza, gawasu shegun kunnuwanka falka-falka, gashinan ka gogama Sadiq wad'an nan kunuwan naka (d'ansa🤣)....." "Nid'in?". " eh kaid'in, kozakayi wani abune?". "Hhhh bazanyi komaiba jar wuya, amma nima nafasa miki k'yauta d'innan". "o, tsaya tsaya mutumina, kaikuma mizaka bani?". " aina fasa, badai nine Sultani ba, mai falka-falkan kunnuwa kuma?". "Kai haba, bafa kaiba gaye". Gaba d'aya falon aka shek'e da dariya, dama suna 6angaren ya khaleel ne sunzoma Ammah hira, tunda idan dare yayi nan take dawowa. ___________________________ Khaleel Na kwance afalo, hannunsa rik'eda hisnul Muslim yana dubawa, Aysha tafito daga kichin tana tafiya ahankali, daka ganta kasan batada isashshen lfy, dauriyace kawai irin tata. Ajiye kayan hannunta tayi bisa table d'in tsakkiyar falon, tad'an jawoshi gaban khaleel. Sai asannan yad'ago ido yana kallonta, "A'eesha kina lfy kuwa?". Murmushin yak'e tamasa, " mikagani Sadauki?, lafiyata lau, ciwon bayannan ne kawai, shikuma kasan kullumne babu fashi". Littafin ya ajiye yatashi zaune sosai, har lokacin idonsa akanta, yakamo hannunta yazaunar da ita kusadashi. "Kifad'amin gaskiya sholy, tunjiya da daddare nakula bak'yajin dad'i, mutsu-mutsufa kikaitayi awajen barci, nikaina banyi wani barcin kirkiba saboda motse-motsenki, hakama da safennan bakiyi barciba sosai, kodai wani gu namiki ciwo kuma?". Fuskarta d'auke da murmushi tace, " a'a, ka kwantar da hankalinka, inhar naji ciwon aii zan fad'a😊". "Shikenan my Angel". 'Yak'are maganar da furzo huci abakinsa'. Itakuma tafara k'ok'arin bud'e masa fruit d'in dayasa ta yanka masa k'anana. " gashi kasha, bara nak'arasa aikin danakeyi". Harta yunk'ura zata mik'e yaruk'o hannunta, "kinga zauna ki huta, idan nagama zanje nak'arasa". " kad'anfane aikin, kabarni ina motsa jikina, kaifa kayi komai d'azu da safe, please kahuta, bara nak'arasa, aii motsa jikin yanada k'yau shima." Jin jina mata kai yayi sannan yasaki hannunta. Tadafashi tatshi. Akichin tana aiki tana cije le6e, idan azabar ciwo ta isheta kuma tatsaya, sai zufa takeyi, amma taurinkai irinna Aysha tak'i fad'ar batada lafiya. *********** "Wlhy sainakeji kamar Aysha batada lfy". 'Anty Mamie tayi maganar tana kallon baffah'. 'Dan murmushi yamata, yace, " kai Bilkisu sarkin son 'ya'ya, ba mijinta Na nannaba agida?". ''Yana nan baffansu, ammani shirmen yarannan nake tsoro, zata iya kasancewa cikin ciwo tak'i fad'a, shikuma babana yakasa fahimta. tun ajiya nafara fahinmar tana nak'udar tsaye wlhy baffansu. kaga baradai naduba ko hankalina zai kwanta". Guntun dariya yamata, "to saikin dawo, ALLAH yasa muji alkairi". " ameen". 'tayi maganar tana saka takalmanta tafice da hanzari kuwa'. ******* Hankalin khaleel kasa kwanciya yayi, yanashan fruits d'in amma zuciyarsa nakan Aysha dake kicin, baiyarda k'alau takeba. Ajiye cokalin yayi yamik'e. Shikagarsa kichind'in dai-dai da sakin wani marayan kuka da Aysha tayi saboda wani juyi da abinda ke cikinta yayi. Da sauri nak'arasa yana kiran "A'eesha! A'eesha!! Lfy kuwa?..." Ina Aysha batasan yanayiba, ya tallafota zuwa jikinsa, saiga Anty Mamie tafad'o falon. Maganar khaleel tajiyo a kichin yana kiran A'eesha. da sauri tak'arasa kichin d'in, salati Anty Mamie tafara, dukta rikice, tak'arasa inda suke. Ya salam, babana garin Yaya haihuwa gadan-gadan amma bazaku iya kiran kowaba?". "Wlhy Anty Mamie bansan haihuwa baceba, Na tambayeta tacemin lfyarta k'alau, Anty Mamie numfashinta baya fita da k'yau, a d'akko Mota....... " ina, saidai akira Ammah, d'auketa kakaita bedroom, haihuwar tarigada tazo aii, maza da sauri..... Da hanzari khaleel yad'auki Aysha daketa nishi da cije la66a. Anty Mamie kuma takira Ammah arikice. Mintuna baifi 5 ba saiga Ammah. "Kai kajimin sakaran yaro, miye nad'orata kan gado itada take nak'uda, sakkota k'asa da sauri". Khaleel ya sakko da Aysha k'asa sannan Ammah tak'arasa waje. Cikin haushi yafita, danyafi son matarsa ta haihu agabansa, amma tsohuwarnan tawani korosa, saboda iyayi😏..............✍🏻 Kutanadi kayan babys🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀😜 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu, dadukkan musulmai baki d'aya😭._* [10/26, 4:30 PM] Aysha Galadima: *_📲Typing_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASS......._* _(Home of expert and perfect writers)_ *_part 2_* _(littafi Na biyu📙)_ *_yanda kike tadaban haka gaisuwarki tadabance my dear pinky pinky😜, Anty Zuwairiyya, k'awarki anty zuwairah ta gaisheki🤭. Alkairin ALLAH yakai miki har Kano auntyna ta mutunci._* 💋💋💋💋❤👍🏻 5⃣0⃣ Azaba ta ishi Aysha, duk addu'ar datazo bakinta yitake, tana kiran mama da khaleel suzo su taimaketa zata mutu. "Wayyo Ammah zan mutu, Dan ALLAH ki ciremin jaririnnan, zai kasheni wayyo Anty Mamie." "Daure Aysha kiyi nishi da k'arfi kinji, kinga kan yaro gashinan, insha ALLAH kinayin nishi zai fito ki huta, runga addu'a, bazaki mutuba insha ALLAH". " to Ammah, inayin addu'ar aii, hazbinallahu wani'imal wakil, ya khaleel kana ina?, shikenan kabarni da wahala? bama zakazo ka taimakenib......? kai ya salam, I love you mamana.....wayyo ALLAH Na. Duk surutannan da Aysha keyi dakiran sunansa khaleel najikin k'ofa yanaji, tausayinta yakuma kamashi, jiyake inama zai iya maido ciwon jikinsa, yanzu nan haka Anty Mamie tasha azabarnan, Amma momy bataji tausayintaba ta d'aukeni batareda ko ganina tayiba, momy kin cutar da Anty Mamie gaskiya, wannan alhakin kad'ai ya isa hanaki zaman lf.......... Tunaninsa yakatse lokacinda yaji kukan babie yacika d'akin, Ammah kuma tana fad'in kai Alhmdllh sannu da k'ok'ari Aysha, masha ALLAH barka dazuwa duniya....... Waigawa yayi yaga Anty Mamie bata wajen, tana kichin d'ora ruwan zafi, ai baiyi wata-wataba yatura k'ofar yashige. Ganinsa kawai Ammah tayi yafad'o. Shikam ko kallo batama isheshiba yanufi inda Aysha take kwance tana maida numfashin wahala da k'yar. Kanta yad'auka yad'ora bisa cinyarsa, yasaka gefen rigarsa yana share mata gumin fuskarta, sai jero mata sannu yakeyi . Sannu Humairah na, ALLAH yayi miki albarka, yasaka farinciki arayuwarki, kin faranta min, kema ALLAH ya faranta miki fiye da haka, ya ubangijina bazan daina godemakaba da wannan k'yauta dakamin". yaduk'o yasumbaci goshin Aysha, datake guntun murmushi idonta arufe. Ammah dai batama kulasuba, tana gama yanke cibi tamaida hankalinta wajen gogema jariri jiki saboda d'a na fad'owa uwa tabiyo baya. Muryar Aysha can k'asan mak'oshi tace, ''Sadauki zansha ruwa". "Ruwa?, tom inazuwa bara Na d'akko miki". Da sauri yafita, batareda Ammah ta kallesaba ta tuntsure dadariyar tsokana, baimasan tanayiba, Dan tuni yafice abinsa ma. " a'a babana lfy? Mizaka d'auka? Yama naga jini ajikinka?". "Anty Mamie ta haihufa, ruwa tace zatasha shine zan d'auka mata." "Alhmdllh Anty Mamie tafad'a cikin d'aga hannu sama, amma khaleel yabata dariya yanda yarikice, badai tayiba ta danne". " kaga baruwan sanyi zata shaba, kar6i wannan kakai mata". Tamik'o masa ruwa maid'an d'umi. Yana zuwa ya iske Ammah ta kulle d'akin, bugun duniya amma tak'i bud'e masa, haushi ya isheshi, hardai Anty Mamie tafito daga kichin tana tambayarsa lafiya?". Da hannu ya nuna mata d'akin. Murmushi tayi, dantasan shida Ammah ne, tunda sunsaba, "kaga kyale Ammah kaji babana, tashima kacire wannan kayan kayi wanka, kaga duk jini ya6ataka ko?". Kallon jikinsa yayi, shi saima yanzu yalura jinin ya6atashi. mik'ewa yayi yashiga d'akinsa, sai jero tsakin haushin Ammah yakeyi, batama barsa yaga koda jaririnba mtsoow, ALLAH tsohuwarnan tagama rainashi.😂 ******** Cikin mintunan dabasufi 30 ba Ammah tagyara maijego da jariri tsaf, d'akinma aka gyarashi, kaikace ba'a haihuba. 6angarenta taje ta d'akko turaren wuta data tanada domin wannan ranar, matan su Sultan ma duk haka tamusu, harda kayan sanyi Na jarirai masu azabar k'yau. Tazo ta kunna, Dan danan 6angaren Aysha yad'auki k'amshi, aka sakama jariri fararen kayannan Na sanyi, sunmasa k'yau, sai barcinsa yake zubawa hankali kwance, bashida wata damuwar data wuce hakan to🤷🏽‍♀. Sai a lokacin Anty Mamie takai labari cikin gida. Aifa kowa yarud'e da murna, Dan danan suka cika d'akin, jariri d'an dangi, harfad'an wazai d'auka akeyi. Suna tsaka da murnarsu ya khaleel yashigo, babuma Wanda yalura dashi, sai Aysha dake kwance akan gado tana kallonsu cikeda jin dad'i. Yunk'urawa tayi zata tashi zaune Dan ganin ya khaleel, amma saiya dakatar da ita, tareda zama kusada ita abakin gadon ya kamo hannunta yahad'e danasa. "Sholyna sannu da k'ok'ari kinji? babudai inda kemiki ciwo ko?". Akunyace ta jinjina masa kan, dansu ummi Amarya suna d'akin, ga matansu ya mujahedeen mamadai batazoba, Anty Mamie ma batadawoba duk sunama ummi amarya kara. Yasan sarai mitake jima kunya, amma yak'i sakin hannun. Ammah data shigo d'aukeda kofin tea ta balla masa harara, shima hararar tata yayi yana kauda kai. " yo iro, iyakarkadai hararar tawa, amma babu yanda ka iya dani, ka harareni son ranka, nasan yanda zanyi maganinka agidannan". Shiru yamata, yacigaba dama Aysha magana. "Yo karka tankamin d'in, dama masana sunce dogo da hankali dacene, mtsoow". Shi dariyama takoma bashi, amma saiya k'iyi, ya shareta. Kowa ad'akinkam fad'an nasu dariya yake bashi, kowa kuwa yana darawa k'asa-k'asa, Anty Mamie da ummi amarya ne kawai tasu tafito fili. Ummi amarya tamik'o masa jaririn tana fad'in kaga bar Ammah kaji babana, sotake kawai tabaka haushi. Ga maigida kamasa addu'a. Sai yanzune zai d'auki yaron, bakinsa d'aukeda addu'a yad'aukeshi, wani farinciki yaratsashi, wai wannan nasane, kai 'ya'ya k'yautar ALLAH, ya mannashi da k'irjinsa tareda lumshe manyan idanunsa. Ummi amarya dukta kad'a Kansu suka koma falo, akabar Ammah dasu ayshan kawai ad'akin. Cikin mamaki Ammah da Aysha suke kallon khaleel dake rungume da yaro yana hawaye, bakinsa yana d'an motsawa ahankali, dagani kasan ALLAH yakema kirari da godiya, yakai tsawon lokaci ahaka sannan yabud'e idanunsa akan yaron, yashiga sumbatarsa kuma. Ammah dai da Aysha sunzama 'yan kallo, Dan sun sakin baki sukayi suna kallonsa. 🤔kai masu karatu, lallai khaleel yanason yara, nifa harma narasa yanda zan musalta muku farincikin dayake aciki. Bayan Aysha tad'an huta khaleel yakaisu asibiti itada Ammah Dan a duba lafiyarsu data jariri maikama da babansa sak👍🏻. Ya khaleel an.......🤭koda yake bara nayi shiru kawai.😎 Alhmdllh, maijego da jariri lafiyarsu lau sai wasu magunguna da doctor Faisal yabasu susaya Aysha tasha, shima jaririn saboda 'Yar mura dayazo da ita anbasu Wanda zasuna bashi. Daganan suka dawo gida. Kasancewar haihuwar yammace, dare yafarayi makwaftane kawai suka shishshigo sukayi barka daganin jariri. __________________ Bayan sallar isha'i Baffah yashigo shima ganin jinjiri, daduk samarin gidan, yanata barcinsa aka kawoshi. Cikin tsokana baffah yace, "iye, kaga d'an gayu, barcima kakeyi? Idon maza biyu kaikuma naka arufe?". Dariya aka sanya gaba d'aya, zunnurain yace, " a'a baffah karfa kace haka, yarona jarumine, ba barci yakeba likimo yayi dai". Suka kuma tuntsurewa da dariya, baffah nata tsokanarsa sukuma suna kare masa, ya khaleel dai baicewa komai sai dariya. Addu'a baffa yamasa, sannan yad'ago yana kallon khaleel, "mu'azzam kamasa hud'uba ko?". " a'a baffah, kaidama ake jira". Baffah yay murmushi, yasan dama za'a rina, Dan ya khaleel tun yana yaro idan yasamu Abu, kafin wani yagani, koyayi amfani dashi saiya kaima baffah. Baffah yace, "wane suna kakeso?". K'asa khaleel yay dakansa yana murmushi, " baffa duk Wanda kaza6a masa shine dai-dai". Nanma baffa murmushin yayi, sannan yafarama yaron hud'uba. Yana gamawa yamik'ama Ramadan dake kusadashi yaron yana fad'in "ALLAH ya raya Takwarana Abdallah". Masha ALLAH Sukaita fad'a, kowa ya yaba da wannan suna. Haka sukaita d'aukarsa d'ai-d'ai suna masa addu'a amatsayinsu Na iyaye. Khaleel da farinci ya isheshi, dama sunan dayake burin sakama yaron kenan, gashi tunaninsa yazo d'aya dana baffah, dad'i yaji sosai, mik'ewa yayi yashiga d'aki yakira Aysha. Cikin ladabi ta durk'usa gaban baffah tana gaidashi, ya amsa da kulawa, yana tambayarta jikinta. Kasa amsawa tayi saboda kunya, takumayin k'asa da kanta tana d'an murmushi, baffa yanata zubamata addu'oi da albarka, ahankali take amsawa da ameen, su Muslim natayata. Muslim azuciyarsa yana tuna dayanzufa shi aka haifama yaronnan, wayyo ALLAH ya khaleel yamasa kwace😂😜. Bayan tafiyarsu baffah ma Anty Mamie da mama suka shigo sukaga jariri, suma sunmasa addu'oi. Nace, "kaga yaro d'an gatan dangi😃👍🏻. _________________________ Washe gari aiba'a magana, gida yacika da 'yan uwa da abokan arzik'i, su Amal amare, kowacce danata cikin, matansu Joseph suma da 'yan yaransu abin sha'awa, Anty zuwairah ma saigata tabiyo jirgi, danta kasa hak'uri, su Anty Shukurah ma anzo, 'yan Kano dai sai nanda kwanaki uku, ammafa tuni sunga hotunan baby da'aka tura musu, Anty Amatullah ma pictures d'in baby tuni suncika wayarta, kowa yagani dole yayaba. Fans ma pictures duksun zomuku nasani😉😃🤚🏻. 🤣🤣 Ammah tayi karnene ad'aki tahana khaleel sakewa, Bai isa yak'e6e dagashi sai ayshaba, daya shigo zatazo ta zauna itama, idan zaicika d'akinnan da harara bazata kulashiba. Takuma hana Aysha shiga d'akinsa. Haushinta sosai khaleel yakeji, yarasa kuma yanda zaiyi da'ita, duk wani motsinsu akan idon Ammah ne😂. Kai Ammah jidalice fans🤣🤣. ******** Masha ALLAH Abdallah yayi yayi goshi, kayan barka ba'a magana, baffa yayi nasa, Anty Mamie danata, mama danata, ummi amarya danata, to ballantana kuma iyaye su ya Sultan, duk basu manta rawar gani da d'an uwansu yataka anasu haihuwar 'ya'yanba, harma da bikin nasu, kowa saida yaymasa hidima ta bajinta, hakama Anty Zuwairah wannan karon tayi hidima kodan tawanke laifinta nabiki dabatama ya khaleel komaiba, kayan baby 'yan ubansu haka tahad'o, banda Na Aysha dashi khaleel d'in kansa, Anty shukurah, Anty Amatullah ma duk ba'a barsu abayaba. Abin tamkar fariyya, ya khaleel maiyine, shiyyasa shima ba'aji k'yashin masaba, koya kukace fans🤷🏽‍♀. Kumafa nasan kunan kuna shirya gifts😉😂. _____________________ Kwanaki hud'u da haihuwa saiga Anty Fadeelah da Anty Hafsat, sunyo gaba daga Kano. Zokaga murna wajensu dasukaga jariri. Aysha taji dad'in ganin 'yan uwanta, sunzo dakayan arzik'i suma, daga kawu bilyamin, Na Ummah ma daban, haka su ya Qaseem. Aikam ranar ansha hira. Ana gobe suna kuma su ummah suka iso suma, harda matar kawu Ahmad da Ummulkhairi autarsu Aysha dake hannunsa, yarinya tayi girma sosai, zasu iya zama sa'anni da ummunoor, bana zata jss 1 secondary, gwaggo Asma'u ma tazo daga katsina, da Matan su ya Qaseem, matan kawu bilyamin ma da 'ya'yansa, su Rufaidama ba a barsu abayaba, sunzo da 'ya'yansu masha ALLAH dunsunyi wayo. To saikuma ga 'yan jigawa, harda inna tsohuwa mairan k'arfe, dukda tasan duk abinda yafaru hakan bai hanata shan sabon kukaba ta rungume khaleel tana fadin "dama tanaji ajikinta khaleel jinintane, ba'a banzaba take k'aunarsa kamar tsoka d'aya amiya😂, shikansa saida kwalla ta tarumasa agefen idonsa. Matan uncle ma'aruff ma duk sunzo, da gayyar dangi Na 6angaren Ammah da Anty Mamie, gidafa yacika kaikace biki akeyi. Kowa burinsa ya kwatanta alkairi ga ya khaleel koda baikai Quarter d'in Wanda shi yake musubama. Saikuma ga 'yan Canada kamar wasa su Anty meerah, Aysha batayi zaton zuwan nasuba, aikam kamar ta had'iyesu saboda murna, babyn Anty meerah Raudat tagirma ko INA yawonta takeyi. Gidakam ba'a cewa komai, ranar kwanan hira akayi, musamman 6angaren Aysha dayazama dabar yaran mata, duk can suka kwana. Washe gari aka saka suna a massalacin anguwar bayan anyi sallar asuba. Akaita sakama yaro albarka. Muma munce ALLAH yaraya Abdallah Ibraheem Abdallah💋. Dagananfa shagali yadawo Na mata acikin gida. Aharabar gidan aka shirya walima iya mata zallah. Suma su khaleel sunyi tasu daga 10am zuwa 1:0pm, saboda abokan aikinsa da abokansa, aikam nasha mamaki, dannaba k'aramin cika akayi awajenba, shi harma mamaki abin yayta bashi.. And'auki Abdallah anje dashi, ALLAH ya taimakesu kuma baiyi kukaba, yanatama barcinsa, kunsan jariri da barci. Ansha hotuna kam sosai, lamarin harba'a cewa komai. 4:0pm Na yamma mukuma mukayi namu shagalin acikin gida, babu k'arya munfa cashe, lamarin harba'a cewa komai. Kai fans kunsha casu wlhy, babufa Wanda banganiba, munci rangam munsha zo6o, kowa saida yaciko jakka dakayan alatu, su o e ina kallonta harda guziri tayi a leda bakko😜, bandai fad'i sunaba ehe😏. Alhmdllh suna yayi suna, Aysha da Abdallah sunsha gayunsu, nimadai nasaka leshina Na k'aramar sallah nayi k'yau😎, ba'a d'aukar rahoto kawai natsayaba ehe😏. 😂😂😂🤣 Su Taheer sun taka rawar gani wlhy, abin arzik'i harba'a cewa komai, lallai Abdallah yayi goshi fans, ALLAH yabamu farar haihuwa irin tasa🤷🏽‍♀👍🏻. ___________________________ Kowa jikinsa yafad'a masa saboda gajiya, Aysha kanta agajiye take, saboda gidan yakuma cika dole tashiga d'akin ya khaleel dantad'an gasa jikinta susamu su kwanta, toilet d'in d'akinta bak'i nata layin shiga. Batayima zaton yana gidanba. Aikam babu kowa ad'akin, ta sauke Abdallahd dake goye abayanta yanata barci, Ammah tace dolene taringa goyashi yanajin d'umin bayanta, yanzuma ana kiran sallar magriba tace tad'aukesa tagoyashi, karkuma ta saukeshi sai anyi sallar isha'i, babu yanda Aysha zatayi dole tagoya gudun jarabar Ammah. Saman gadon ya khaleel ta kwantar dashi, barci yakeyi har yanzu, ta lullu6eshi sannan tashiga bayin. tana shiga kamar jira yaro yafara kuka yana wuntsila 'yan k'afafu sama. Ya khaleel ne yashigo d'akin danufin d'aukar Abu yafita, dan 6angaren baffa yakwanama jiya. Da sauri yak'araso gaban gadon yana fad'in ''ya salam, jenior miyafaru kaikad'ai ad'aki? Ina A'eeshan?". 😂ni dariyama yabani, kaikace yaron zai amsa masa tambayoyinsane🤣. Ya d'aukesa yasaka akafad'a yana jijjigashi, saikiran sorry yakeyi, sorry my Darling, bar kuka kaji". Aysha Na toilet tana jiyosu, aikam taita dariya, kusan mintuna 20 saigata tafito, bud'e k'ofarne yasaka khaleel juyowa yana kallonta. "Yanzu dama kina cikin d'akinnan Amma kika barsa yake zunduma kuka haka". " kai Sadauki, wannanne zunduma kuka? kumafa wanka nayi, ajiyesa kenan nashiga wanka yafara kukan, ALLAH yaronnan yacika wayon tsiya, shikenan dayaji babu motsin mutum kusadashi sayaytama mutane kuka? ALLAH akwai takura, shikenan banida aikinyi saina gadi, yanzuma damutane kenan, inaga kowa yatafi kuma?". "To minene aikin naki idan ba rainonmuba?". 'Yay maganar yana sakkoda junior daga kafad'arsa'. Aikam idonsa k'yar abud'e. Dariya ya khaleel yayi, yasumbaci kumatunsa, ''sholy zokiga abin dariya, waifa idon yaronnan k'yar abud'e". Dariya itama tayi, tamatso kusadasu. " to kallafa dan ALLAH, anya bakai jenior yabiyo wayoba". "Hhhhh, aikema d'in gwanace afagen wayon, kuma aii dama k'yan d'a yagaji babnsa ko". "Hakane kam". 'Aysha tayi maganar da dariya'. Kwanciya khaleel yayi akan gadon yad'ora jenior a saman cikinsa, ya kalli Aysha dake saka kayan barci " shi baza'a masa wankanba ne?". Juyowa tayi tad'an kallosu, sannan tamaida kanta ga madubi tana tufk'e gashinta, tace, "aii Ammah tamasa tun d'azun bayan anyi sallar magriba". " OK, Ammah ko fitina, yanzu dai datasan kina d'akinnan dayanzu tashigo, bansan miyasa takemin hakaba?". Zama Aysha tayi a bakin gadon kusada kan ya khaleel tana 'Yar dariya. "Kabar Ammah kaji, aii yanzu hira da innah ne ke d'auke mata hankali". " hakane, amma miyasa taketa wani kaffa-kaffa dake". "🙈catayi idanfa ina shige maka saika kuma min wani cikin, waikuma ga jenior k'aramine". Bashiri khaleel yatashi zaune yana 'Yar dariya, ''kai amma dai tsohuwarnan ta rainani, to bansan kina jego bane komi? Tama maidani wani bunsuru alkuran". Dariya Aysha taita masa harda tuntsurawa. Tuni dariyar ta Aysha tafara narkar da ya khaleel, dama gata acikin kayan barci, jegon kuma yasakata yin shar, takuma murjewa da 'yar k'iba, kasa hak'uri yayi, ya ajiye jenior agefe yamatso kusada Aysha. Tashagala cikin masa dariya taji ya kwantota jikinsa, kafin tayi yink'urin kwacewa kam bawan ALLAH ya had'e bakinsu waje guda. Tunfa Aysha nad'an tittirjewa sai jikin mutuniyar taku yasaki🤣, tafara badakai😎. Sun lula wata duniya kukan Abdallah yadawo dasu hayyacinsu, yaro kamar yasan mi'akeyi ya daddage ya callah kuka😂🤣. Dole suka saki juna suka dawo gareshi, kunya dukta ishi Aysha, khaleel yad'akkosa yad'ora mata acinya yana murmushi. ''Inagafa yunwa jenior yakeji". Kan Aysha ak'asa takar6esa tafara shayar dashi, cikeda sha'a khaleel yake kallonsu, jiyake tamkar ya had'iyesu donsi, waya yad'auka yamusu pic, sannan yamatsa tareda rungumo Aysha jikinsa ya manna mata kiss akumatu yad'aukesu ahaka. Nida nake ala6e nace "lamarin zaaaaam fans😂🤙🏻". Ranardai haka ya khaleel ya yaudare Aysha takwana d'akin, dukda baimata komaiba tasha jagwalgwala. Nace, "Ashe dai gaskiyar Ammah😱". _______________ Washe gari kuma bak'i sukaita tafiya d'ai-d'ai. Cikin kwana biyu kowa yakama gabansa, kaikace gidan baitara kiwaba, daganan kuma sai bikinsu musleem. Ammah tace sai Aysha takoma 6angarenta kokuma d'akin ummi amarya. Khaleel yay tsalle yadire akan bai aminceba, Ammah kuma tace bai isaba. Ankai ruwa rana kam kafin ya yarda dan dole Aysha takoma 6angaren Ammah, saida baffah yasaka bakima sannan. Aikam yayta fushi dakowa agidan, harma ita ayshan kanta. Daga k'arshema wani aiki yataso masa yashirya yatafi France, headquarter d'insu dake birnin Lyon. Bayan sati uku da haihuwar Abdallah (jenior).............✍🏻 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*😭🙏🏻 [10/26, 4:30 PM] Aysha Galadima: *_📲Typing_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASS......._* _(Home of expert and perfect writers)_ *_part 2_* _(littafi Na biyu📙)_ _alkairin ALLAH ya iso gareku kuma, bilyn Abdul bata manta dakuba._ *DUNIYAR MAKARANTA group & ATK hausa novels, Momiskoh hutu.* 5⃣1⃣ Kwana biyu kenan da dawowar khaleel Nigeria, har yanzu kuma fushi yakeyi da Aysha, zaidai shigo yad'auki junior yafita, Ammah ma baya kulata, yana dai gaisheta amma babu hira. Yau takasance monday, dawuri khaleel yay shirin office, ko cikin gida bai shigaba yafice da hanzari. Adams yabud'e masa mota yashiga, bayan sunyi salute nashi. Tafiyar mintuna k'alilance takaisu. Zamansa babu dad'ewa a office saiga kira yashigo wayarsa, dubawa yayi kasancewar wayar office ce, ganin ogansa yasakashi d'agawa da hanzari. Cikin girmamawa ya gaidashi. Saikuma naji yana fad'in "OK sir, ganinan zuwa to". Yana Yanke wayar yamik'e yad'auki wasu takardu yafice. Saida yayi knocking aka bashi izinin shiga sannan yatura k'ofar yashiga, ya k'ame tareda salute na ogansa. Fuskar Oga d'aukeda murmushi yanuna masa wajen zama bayan yamaida masa murtanin salute d'in. " J! Ya iyali?, da abokina Abdallah?". Murmushi ya khaleel yayi, yace, "yana nan lfy sir". " to ALLAH ya albarkaci rayuwarsa, ALLAH yasa yafika jarumta da kwazo". Murmushi sosai khaleel yakumayi, Wanda har hakwaransa suka bayyana, yanason ayaba masa d'an Abdallansa😃👍🏻. Yace, "to ALLAH ya amince sir". Oga yay 'Yar dariya, tareda mik'ama khaleel wata Leda mai azabar k'yau. "Ga wannan j!, gobe idan ALLAH ya kaimu su zaka saka, kuma kaida madam zakazo". Cikeda mamaki khaleel yakar6i ledan, yad'an lek'a cikinta sannan yakalli ogan nasa. " sir! wani abune za'ayi?". "A'a, kaidai kasaka kawai, kuma sai around 11 za'azo a d'aukeku insha ALLAH". kasa cewa komai khaleel yayi, sai jinjina kai yake tamkar k'adan gare. Oga yayi murmushi, tareda basar da zancen yace, " so ina takardun danace kazo dasu?". Mik'a masa khaleel yayi. Oga yakar6a yad'an dudduba, sannan yad'ago yakalli khaleel d'in, " ehm j akwai wani aiki daya taso mana again, so zamuyi meeting akan batun next week insha ALLAH, kuma aikin gaskiya dolene kaine keda zarrar yinsa, Dan wad'anda za'a kamad'in saida irinku awajen, amma gawad'annan kaduba wani 6angarene nabayanan, zan turo maka sauran ta network". "OK sir!". " zaka iya tafiya abinka". Mik'ewa yayi tareda k'amewa dayin salute na ogan, sannan yafice. ********** Tunda yadawo office yaketa juya maganar ogan nasu, baidai bud'e kayanba, yamaida hankalinsa akan binciken bayanan da oga yabashi akan aikin kuma dayake tunkarosu. Yaja tsawon lokaci a binciken yaji alamar shigiwar massage a wayarsa. Kamar bazai dubaba dai yad'auka. Number Aysha yagani, yasaki guntun murmushi sannan yabud'e sak'on. _"Amincin ALLAH ya tabbata agareka yakai sanadin farincikina, inafatan kana cikin kwanciyar hankali da walwala ahalin yanzu?, Alkairin ALLAH yacigaba da yalwatuwa aduniyarka, ALLAH yatsareminkai daga idon mata🤕, masu k'arema mazan mutane kallo😏."_ _"junior yace dadynsa yakasance cikin kwazon aiki da farinciki, gefe kuma yaringa tuna mamansa, yamata uzuri, adaina fushi da ita, ba laifinta bane, itama tana kewar bakandamiyar rayuwarta Abban junior💋."_ Baisan sanda wani murmushi ya su6uce masaba, yakuma maimaita sak'on sannan ya tuntsure da dariya, kai yarinyarnan sai'a barta, 'yar k'arama da ita ta'iya kishi. Cikin lumshe idanu ya sumbaci massage d'in, shikansa fushin dayakeyi dauriya kawai yakeyi, amma yana kewarta, yanaso kod'an kissing d'inta yayai, amma Ammah takafa tatsare. Bud'e idanunsa yayi, sannan yay dealing d'in number d'inta, harta katse bata d'agaba, kasa hak'uri yayi yakuma kira, bugu biyu kuwa tad'aga. Murya can k'asan mak'oshi tace, "Hii my lollipop". Lumshe idanun yakumayi, da k'yar ya iya furta " A'eesha kin rainani ko? kimin laifi amma kimaidashi wasa?". _"Ooo! my god, ni na'isa wasa da jarumi mai zarrah irin j!, karfa ka manta j! Ne, kuma j!! Bayason raini, amin afuwa, komai akaga nayi, akan kuskurene, amma bazan sakeba, junior nataya Amminsa bada hak'uri, kagama kuka yake shirinyi, harya fara ta6e baki"._ "Kai haba dai?". " ALLAH kuwa". "tayi maganar tana kara wayar kusada Junior". Aikam tamkar jira yake yafashe da kuka😂 " kai, dama da gaske kikeyi? Please banason jin kukansa, kibasa abincinsa". Shagwa6e murya Aysha tayi. tace, "to kadaina fushin dani please?". " ai wancan laifin daban, bamu abincinmu kuma daban". "Naji, to amma naci albarkacin junior". " sarkin wayo, shikenan na yafe miki, komai yawuce, amma saiki shirya tarbata yau ko?". "Lah Sadaukina, banfamuyi arba'inba". "uhm nasani aii, amma koda bazanje city ba, sai'a barni nad'an rage zafi". Kamar Aysha na gabansa tarufe idonta, ''kai ya khaleel, ALLAH kaima wani lokacin bakada kunya. " hhh ko sholyna?". "Eh mana". " tom nazama mai kunya, kibarni nayi aiki inba sokike nazabga musu shirmeba wlhy, duk kin wani narkar dani". "Wata 'Yar dariyar kissa Aysha tayi, tayimasa siririn kiss sannan tayanke wayar batareda yashiryaba, saidai yaji d'iifff." Da sauri yakalli wayar, yakoma yalafe jikin kujerar yana fad'in ya salam yarinyarnan zata karni wlhy🤦🏻‍♂. 🤣🤣🤣😜. Kina aljanna sholy, muna binki da addu'a, nida fans🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀. ALLAH yaba Xoxo irin khaleel kodan........🤭, bazan fad'aba to😜, su o e har an kasa kunne aji kanun labari😏. _______________________ Sai bayan isha'i yadawo gidan, 6angarensu yashiga yay wanka yakimtsa sannan yazura jallabiya kalan ash, yad'an fesa turare yad'auki ledar da ogansa yabasa dawata ledan dayad'an yima Aysha siyayyar toshin baki😂 yafito. Da sallama yashiga falon na Ammah, babu kowa aciki sai mufeedah dake barci a doguwar kujera, da'alama bada shiri barcin ya kwashetaba, Dan harda waya a hanunta. Jiyo Ammah yayi tana karad'i itakad'ai a waya, da'alama waya yakeyi da uncle ma'aruff kokuma wani. Sad'af-sad'af yashige d'akinta, yana k'yautata zaton Aysha nacan. Aikam kan gadon AMMAH yahangota zaune tana k'ok'arin sakama junior pampas. K'ofar yasakama key sannan yak'arasa gareta. Tad'ago ido tana masa sannu. Zama kusada ita yayi yana amsawa, tareda saka d'an yatsansa cikin hannun junior, shikam yakama yarik'e gam kamar yasan miye. "My sweet kawuni lfy?". Aysha data gama saka masa pampas d'in tad'agosa tad'ora masa acinya tana fad'in " k'alau ya wuni, saidai kewar Abbah ko baffanmu?". Ya khaleel yakar6esa yana murmushi, ya sumbaci fuskar yaron, "to nima nadawo inata kewarku". " humm yaronafa sai k'ara k'iba yakeyi, ALLAH nononki yanada k'yau 'yammatana, masha ALLAH, ingani". 'Yay maganar yanakai hannunsa kanta'. Baya tamatsa tana dariya. Shima dariyar yayi ya cafkota, jikinsa tafad'o, yana rungume da Junior yamatseta itama, kissing d'in wuyanta yafarayi, bata hanashiba, saima wani salo data fara masa. Aikam dandanan mutumin naku ya afka. Suna tsaka da hutawarsu Ammah taita buga k'ofar, shiru sukai mata kuwa, sukacigaba da faranta ran junansu. Dama tea takawoma Aysha, falo takoma tana mita, saikuma tayi shiru tana d'aga hanci sama, alamar son shinshino k'amshin wani Abu. Da sauri tace, "tabbas ja'irin yaronnan yazo, gama k'amshin turarensanan". mik'ewa tayi taje tacigaba da buga k'ofar, nanma shareta sukayi. Saida suka more iya morewa sannan khaleel yabar Aysha, kunya dukta isheta. Muryarsa asark'e yace, " nifa gaskiya kuyi ayi arba'in d'inan, akame nake wlhy". Aysha tayi 'Yar dariya tana kauda kanta gefe. "Uhmyim, dariyama nabaki ko?". " a'a fa". "To inma dariyar nabaki dai, zanyi maganinki, amma bayanzuba, d'auka wancan golden d'in ledan kiduba muga miye aciki?, Ogane yabani a office......... Yakwashe komai yasanar mata. 'Daukar ledar Aysha tayi tabud'e, tafito dawasu azababbun suit masu taushi da d'aukar idanu, blue da pink d'in riga long sleep, sai kuma gown itama blue har k'asa mai dogon hannu, sai d'ankwali pink. Aysha tad'ago tana kallinsa, shima idonsa akan kayan. ''Sadauki kodai wani taro suka shiryane akanka baka saniba". " to wlhy bansaniba sholy, amma bana zaton hakan, saidai giben zamu gani koma miye". "To ALLAH ya kaimu". 'Tayi maganar tana k'ok'arin maida kayan a ledan'. "No karki maida duka, cire naki, saiki shirya da wuri karyazam ina jiranku, shima junior kisamu kayan dasuka dace dashi sosai". " OK''. yadad'e baibar d'akinba, saida sukaci kayan dad'insu, Aysha tayo wanka, tayi shirin barci, yaga Aysha takwanta, sannan yamusu addu'a itada Junior ya tofesu, yasumbaci kumatun Junior, itakam saida aka k'ara kiss d'in kusan mintina uku sannan yafice. Cikin sand'aya yabud'e d'akin, ALLAH ya soshi Ammah nata gyangyad'i bayan tagama masifar rashin fitowarsa. Afalonma ahankali yafice. Mufeedah data farka ta tuntsure da dariyar data saka Ammah bud'e idonta. ''Kekuma ubanmi yabaki dariya?". "Hhhhhh ya khaleel mana". ''Yana ina d'an jakar uban?". " aii Ammah yanzu yakai d'akinsama, yafice tuni". "Aizan kamashine gobe, bara naje kan waccan ja'irar". Koda tashiga d'aki tanama Aysha fad'a shiru Tamata kamar tanayin barci, tayi mai isarta tayi shiru, batareda ko motsi Aysha tayiba😂😂🤸🏻‍♀. ____________________________ *_Washe gari_* Aysha tasha gayunta, kayan sunmata k'yau sosai, ammah saifad'i take wai Aysha kamar sabuwar amarya, taida kula kar iro yaga kwalli yarikice, aje amata sakkiyar daba ruwa.. Dariya Aysha da mufeedah sukaitayi. Junior ma ammasa gayu tsaf dashi. Suna zaune afalon Ammah suna jiran shigowar khaleel, Ammah tadage tanatama junior rawa. Ya Khaleel yay sallama, ahankali Aysha tace masha ALLAH, bak'aramin k'yau khaleel yayiba, dama afagen gayu Aysha tasan ya khaleel babu damane. Shima dukda yatoshe idanu da bak'in Google idonsa nakan ayshan, kayan sunmata k'yau sosai. Yana kallon yanda Ammah keta hararasa amma yay tamkarma bai gantaba. Mufeedah da Aysha suka gaidashi. Amsawa yayi yana fad'in tashi muje, su Adams najiranmu awaje. Aysha tamik'e, tad'auki babban gyalenta tayafa, sannan tarataya jakkar datad'an zuba abubuwa saboda junior. Shikuma yakar6i junior a hannun Ammah suka fice. Dawasu had'ad'd'un motoci suka fara cin karo, cikin mamaki ya khaleel ke kallon motocin da adams. Murmushi Adams yayi, yak'ame shida sauran securitys d'in, sukayi salutes nashi, sannan Adams yakar6i junior daga hannun khaleel d'in, yak'arasa yabud'e masa k'ofa. Kan ya khaleel ad'aure dawannan lamari Yakama hannun Aysha suka shiga motar. Suma su Adams daketa d'aukar junior suka shishshiga. "ehm, wai Adams mike faruwane? wad'annan motocinfa?". " wlhy sir nima bansaniba dai kam, da safennan Oga yakirani yabani keys nasu duka biyar d'in, hud'u iri d'aya, itakuma wannan daban itakad'ai". Aysha dake kwance jikin khaleel dai batace komaiba, sai murmushi datayi tana Murza yatsun hannunsa dake rik'e da nata. A gurguje please😏 ********* Sun isa station d'in, Wanda tundaga waje khaleel yaga canje-canje masu yawan gaske, dakagani kasan wani d'an biki akeyi hakannan. Khaleel baice kimaiba, yanatadai bin kowa da kallo, har motocin suka sami waje sukay parking. Adams yace, ''Oga yace karsu fito, sud'an dakata." Jinjina kai kawai khaleel yayi, yakar6i junior daga hannun Adams daya mik'o masa. Sunad'an hirarsu ahankali, dayima junior wasa kusan mintuna 30 sannan saiga Adams, da tawagar security's. Su khaleel suka fito, yana d'auke da junior ma yanzun, yayinda Aysha ke gefen hannun damarsa ta sak'alo hannunta cikin nasa. Wajen cike yake da jama'a, yana fitowa aka saki kunamin bindugu lokaci d'aya jikake drummmm!!!, har saida junior ya tsorata kuwa, yasaka kuka. Wajen zama Na musamman aka kai khaleel da Aysha, inda manyansa ke zaune da matansu suma. Can yahango tawagar 'yan gidansu, kowa da kowa, amamakinsama harda Anty zuwairah, tunani yake yaushema tazo garin?. Ba'awani 6ata lokaciba aka fara gudanar da abinda yatara jama'a, bayan jawabai Na share fage, manya-manyan mutane sukai jawabi, harda shugaban k'asa, da turawa, dawasu manyan mutane Na k'asashe daban-daban, musamman police Interpol. Bayan jawabin shugaban police Interpol Na duniya baki d'aya, da gagarumin yabo na musamman ga gwarazan ma'aikata irinsu khaleel, aka fara kiransu Taheer d'aya bayan d'aya ana basu k'yaututtuka. Khaleel shine Na karshe, bayan kiransa aka mik'a jinjina ta musamman agaresa, tareda yabon irin hazak'arsa da jajircewar aiiki, gashi mutum mai gaskiya da ruk'on amana, anyi kira ga Matasa akan suyi koyi da irin d'abi'unsa, Dan da'ana samun matasa masu halayya irintasa da k'asashen duniya sun zauna lfya, Dan irin wannan kwazon ake buk'atar matasa dashi. Raff raff aka d'auki tafi. Ya khaleel dai yanata murmushi. 🏆k'yauta ta Musamman aka bama khaleel, tarda k'arin girma Wanda baita6a zatoba. Kasa daurewa yayi kawai saiya saki kukan dad'i, yak'arasa indasu baffah suke ya rungume baffah, tareda sakin wani siririn kukan dad'i. Gaba d'aya 'yan uwansa maza suka taso suka rungumesa suma, nanfa 'yan jarida suka fara aikinsu. Guri kuma ya hargitse da tafi, masu bak'inciki kuma da hassada nayi agefe😜, saidai hak'uri, ya khaleel kam yayi gaba, gabanda baza'a iya kamosaba😱👍🏻. Tarokam yak'ayatar, k'yaututtuka khaleel yasamesu ta fannoni da dama, hardaga shugaban k'asa, da manyansu ta fannin aiki, dawasu manyan k'ungiyoyi masu fad'a aji Na duniya. Anci ansha awajen, ankumayi hotuna, saiga Aysha cikin manyan mutane tana zare idanu🤣. Junior kam aii yasha d'auka ranar. To ya khaleel saimuce ALLAH yasaka albarka, Yakuma baka ikon rik'ewa. Awajenne saiga Aleeya, tazo har inda suke zaune tareda saurayinta, cikin girmamawa tagaida khaleel, suka gaisa da Aysha kuma, ta d'auki junior tasaka masa albarka, sannan tagabatar da mijin dazata aura agaresu, shima khaleel yakar6esa da fara'a. Anan kuma Aysha tanemi gafarar Aleeya akan abinda tamata, itama Aleeya tabata hak'uri, suka rungume juna cikin fad'in komai yawuce. Sai yamma taro yatashi lfy. ******** Daga wajen taron prison suka wuce gaba d'aya mutan gidan, domin ziyarar momy. Hummm hajia babba dukta canja, tarame sosai tayi bak'i, damma ita ba'a mata wani horo, saboda jikinta, tarungume khaleel tana kuka daneman gafararsa, shima kukan yake yana tabbatar mata ya yafe mata, babu wanda bai zubda kwallaba ranar a 'yan gidan, duk saida hajia babba tanemi afuwarsu d'aya bayan d'aya, har 'ya'yanta, tad'auki Junior tana kuka dasaka masa albarka, wai wannan d'an khaleel ne, abinda bata ta6a fatar yafaruba, saigashi ALLAH ya nuna mata iyakarta. Hak'uri khaleel yayta bata. Takama hannun Aysha itama tana Neman gafararta. Aysha tace babu komai wlhy, tayafe mata, itama tayimata afuwa akan abubuwan dataita mata narashin girmamawa. Momy tace babu komai, aini najama kaina Aysha, kuma tabbas nayi nadama, ina ALLAH wadai damasu irin halina, Bilkeesu kuyafeni keda fad'ima Dan ALLAH, kema Ammah ki gafarceni." Gaba d'aya kowa yace ya yafe mata. Haka suka barota suna kewarta, itakuma tana kuka dak'arar nadamar abinda ta aikata, gashi inda rayuwarta tak'are abin bak'inciki da dana Sani. Amma taji dad'i da d'iyar mufeedah ta mutu, data rayu haka zata taso taji tarihin azzalumar kakarta, wadda tazama sanadin saka uwarta ahali mara k'yau. Ga ubanta a prison, yayar ubantama a prison duk cikin labari guda d'aya. ALLAH ngd maka. "Hummm ALLAH Sarki momy, yaukam tabani tausayi gaskiya😢, ya ALLAH karabamu da hassada. ******* Haka rayuwar tacigaba da tafiya, Su Aysha sun kammala arba'in, tasha gyara kam sannan aka maidata d'akinta, suka cigaba dakashe juna da soyayya itada Sadaukinta, suna tattalin d'ansu junior, Wanda kowama keso agidan. Ya khaleel yadage wajen k'yautatama mahaifiyarsa, hakama Aysha, ba'a barta abayaba, sosai take bama mama da Anty Mamie kulawa, hardama ummi amarya. Zuminci da 'yan uwanta kam ba'a cewa komai, kowa tana basa hak'insa. Ansha bikinsu musleem dasu tasleem. Saidai muce ALLAH yabada zaman lafiya kuma. Zuwa lokacin junior yayi 6ul-6ul dashi, abin sha'a da birgewa. Ya khaleel kam sai k'arin kwazo yake awajen aikinsa, nak'asa dashi sunajin dad'in rayuwa dashi, shima haka take agareshi. ___________________________ *_4year's ago._* Bayan shekaru hud'u nalek'a su Aysha. Natadda abubuwa dayawa sun canja agidan, amma suna cikin aminci da farinciki, tareda soyayyar juna. Ammah nanan bata canjaba😎, saima abinda yay gaba, ga tsufa sosai yakuma kamata, danma akwai kulawa daga 'ya'yanta da matan 'ya'yanta, da jikoki. Ganin kowa yana cikin aminci agidan saina zarce 6angarensu Aysha. A falo Na iskesu suduka. Khaleel Na kwance a doguwar kujera, yalumshe idanunsa tamkar mai barci, amma idonsa biyu, tsabar tunanine kawai. Aysha nazaune a kujera maizaman mutum d'aya, tana danna waya, gefenta kuma ga yankakken Apple tanaci, saidaifa tana fama da k'aton cikinta🤰🏻, haihuwa yay ko gobe.😂👍🏻 Junior yafito daga d'akinsa d'aukeda buk, yaro yagirma masha ALLAH, kamanninsa sunkuma fitowa da babansa sosai, gashi d'an orobo hakannan. Shekarunsa hud'u kenan aduniya amma sai wayon tsiya da surutu. Gaban Aysha yaje yatsaya, yata6a hannunta yana turo baki gaba. d'ago ido tayi tana kallonsa, yanuna mata khaleel dake kwance har yanzun. Murmushi tamasa, sannan tamasa magana da ido. Yasan mitake nufi, Dan haka kaitsaye yanufi inda khaleel ke kwance yahaye saman cikinsa. Firgigit khaleel yadawo duniyarsa, tareda sauke ajiyar zuciya, yasaka hannu biyu ya rungume junior sosai ajikinsa tareda sumbatar sumar yaron. "My j miyafune? dama ba barci kakeba?". Girgiza kai junior yayi, yad'an turo bakinsa alamar shagwa6a irinta yara. Yace, " Abbah batun d'azun nazoba amma kak'i kulani, sai Ummie ce tamin maganama". Murmushi khaleel yayi, sannan yatashi zaune dashi, kallon Aysha yayi fuskarsa d'aukeda murmushi haryanzu, itama kallonsu take tana murmushin, tareda d'age gira sama. Khaleel yajanye idonsa akanta yamaida akan junior, ''sorry my j, miyake faruwane?". "Abbah homework, gobefa Monday, Ummie tak'imin wai batada lfy, uncle Usama zai zaneni inbanyiba". " babu mai zanemin baba a school, bara yanzun muyi, Ummie kam barta, zamu ramane, zamuje yawo next week amma banda ita". "Yauwa Abbah, karmuje da ita, baffa ma yabani sweet d'azun bazan bataba itada unborn d'inta ko?". Daga Aysha har khaleel dariya sukayi kawai. Yagama koya masa homework d'in sannan ya lalla6ashi yay barci ajikinsa. Kwantar dashi yayi akujerar yakoma kusada Aysha dahar yanzun taketa latse-latsen waya. " waini mikikeyi hakane dakika sharenima?". Cikin dariya Aysha tace Kodai ka shareni sadauki, badan junior ba bansan sanda zaka dawoba." Cikinta ya sumbata. tareda kumatunta, ''sorry my sholyna, natafi tunani akan aikine, kinsan kullum matsalar kenan." "Hakanekam sadauk'ina, ALLAH yacigaba da tsaremin kai daga idanun mak'iya." "Amin sholyna, wai yaushene zaki haifomana sabon babynmune? Nida junior mun k'agara, kullum zuba ido muke." Kamar wasa Aysha tad'an yatsine fuska tana fad'in yauma zai iya zuwa, Dan tunjiya nakejin alamun hakan". Da Sauri ya khaleel yace, "da gaske?". Kafin tabashi amsa taji an tsikareta amara, 'Yar k'ara tasaki, wadda tasaka khaleel rudewa. Kamar wasa saiga k'aramar magana tazama babba. Adaren dai Aysha a hospital takwana, gabbanin asuba ta sunkuto d'iyarta mace, maikama da babanta Ibraheem khaleel, kuma yayanta Junior. Fad'a muku farincikin da wannan familie ma suka shiga aii 6ata lokacine, yarinya taci suna haleematu, sunan Ammah jar wuya😂👍🏻. Aikam bakuga murna wajen Ammah ba, ansaka sunanta. Har prison aka kaima momy baby haleematu, aikam tasha addu'a. Haihuwar haleematu babu nisa mufeedah ma ta haifi d'anta namiji, Dan tuni tayi aure itama, haihuwarce dai ALLAH baikawo dawuriba sai yanzun. ********* Wai nikam wane janrai akemin hakane? tun d'azun naketa jiranki amma kinwani manta dani?." Juyowa Aysha tayi tana kallonsa, saikuma ta kauda kanta tana murmushi, ''babu wani Jan raifa, banaga kana tareda abokan hiraba?". "Humm bayan sunyi barci tun d'azun, junior ma yariga haleematu yin barci, kinbarni inata dakon jira". 'Yay maganar yana rungumeta tabaya.' Hannu tasaka ta shafo fuskarsa, ahankali tafurta sorry my lollipop sadauki, aini takace, inanan ina shiri dominka". Cikin shinshina wuyanta yace, " shiyasa kullum k'aunarki sake k'aruwa take araina, tunda nafara ganinki bakibar zuciyata ta hutaba, I love you so much my sholy". Wlhy nima haka sadaukina, kamantar dani kowa, ka mantar dani komai. I love you trillions💋💋💋💋❤. To masoya nimafa I love you trillions agareku. Tammat bi hamdullah. _Anan nakawo k'arshen wannan labari nawa, Wanda naima ba daidaiba acikinsa ya gafarceni, banyi dancin zarafin kowaba, ALLAH yasa mu ammafana da sak'on dake cikinsa, kuskuren danayi ya ALLAH ka gafarta min, sannan kuma Ku watsar da kuskuren ciki gefe, Dan nima 'Yar Adam ce ajiza._. *_bansan irin godiyar dazan nuna mukuba akan k'aunar buk d'innan dakukayi, saidai nace kawai ALLAH yabar zuminci da k'aunar juna, ngd ngd harma babu adadi, inata k'aunarku har k'arshen numfashina. Bakuma zanta6a mantawa daku acikin ruhinaba da tarihin rayuwata, wad'anda basuga sunansuba Dan ALLAH sumin afuwa, bawai bana k'aunarsu bane, a'a wlhy, sunanan aran Bilyn Abdul koda ban sansuba.💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤❤❤❤._* _Masoyan UMMIE GARKUWA, saiku fara baza idanu, domin gwanar tamu tanan d'aukeda sabon buk d'inta mai suna KHAIRIYYA!!, shimafa zaizo muku da sabon salo tamkar yanda ta k'ayatar damu aciki buk d'inta mai suna JENNIFER._ _karku manta da sunan KHAIRIYYA, yana nan tafe insha ALLAH._ Alhmdllh ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻Daga alk'alamin Bilkeesa Ibraheem (Bilyn Abdul Ce)❤❤❤💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋 Sharhi👇🏻. *_📲Typing_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA!!......_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITERS ASS......._* _(Home of expert and perfect writers)_ *_part 2_* _(littafi Na biyu📙)_ *_MIYE MANUFAR BILYN ABDUL A LABARIN CIKI DA GASKIYA?_* _Tambaya mai muhimmanci, wadda kafin kowa yamin, niyakamata nayima kaina._ _ba burina idan kun karanta labarin *CIKI DA GASKIYA* kubarsa ananba, a'a, burina kud'auki muhimman abubuwan ciki Ku amfana dasu, labarin *ciki da gaskiya* dunk'ulallen labarine, amma mai tafiya da harshen damo. labarine dayazo muku da abubuwa da dama._ Bara nafara da jarumin matashi Ibrahim Abdallah, Wanda yataka rawar gani ajigon labarin. _Ibraheem Abdallah matashin saurayine dakowane matashi yakamata yayi koyi da tsarinsa dagashi har abokansa, Taheer, Joseph, youseef, harma da Adams._ _bashida tsoro ko kad'an, sannan da zuciya d'aya yake aiki, ko sigari wannan bayasha, baya neman mata, akullum kuma yak'i yake da k'arya, gashi da zuciyar taimakon nak'asa dashi, yana kuma girmama nasama dashi, a fannin familie nasa da iyayensa kowa yabonsa yakeyi saboda k'yawawan halayensa._ Shin abin tambaya anan, duk mi yakawo wannan?. _kai tsaye zan iya nuna muku yarik'e martabarsa ta matashine, wadda ayanzu hakan yayi k'aranci ga matasanmu, kullum idonsu nakan 'yammata, burin yin kud'i kota halin k'ak'a, d'aukar shaye-shaye amatsayin wayewa, raina nagaba dasu saboda sunaji da tashen balagar samartaka, rashin yin biyayya ga iyaye saboda jahiltar wayewar zamani, dakaga kakai tsawo shikenan iyayenka sunzama abokan wasanka, fifita ilimin boko fiyeda Na addini._ _Dan ALLAH tayaya za'a samu nasarori arayuwa? Tayaya zaku iya zama Ibrahim Abdallah j?, k'alilannefa acikinku masu irin wannan k'yak'yk'yawan tunanin, k'arancinsu yasaka kowa ganin tamkarma babusu._ _Dan Allah Matasanmu Ku gyara please, kune ginshik'in kowacce al'umma, daku duniya take alfahari, kudaina shaye-shaye, domin kullum ruguzaku yakeyi, yaruguza k'ashenmu da al'ummarmu, kudaina zina, kullum durk'usar daku takeyi tana k'ask'antar daku, kudaina barandar siyasa, inbahakaba kullum a 'yan Turin mota zaku k'are, Ku turasu sukoma kan mulki suna zaginku dafad'a muku kune lalatattun matasa, dole kuma kuringa amsawa, Dan bakuda za6in daya wuce hakan, rayuwar j abin birgewa daban sha'awa, amma miyasa yazama haka?, saida yakasance mai yawan hak'uri da gaskiya, yature Duk wani abun jin dad'i da samarin yanzun suke d'aukarsa amatsayin ado wa rayuwarsu, sannan yazama mai yawan nasara. Dan Girman ALLAH kufarka daga nannauyan barcin daya d'aukeku, Ku daidaita rayuwarku, kunutsu kuyi karatu, kudaina karatu domin burin aiki, karatu wata katangace agareku, idan kun mammala kobabu aiki Ku kama Sana'a, kubar girmankai, k'ila wannan sa'ar itace mafi alkairi arayuwarku, amma kullum idonku nakan k'aton offices, why?._ _Dan ALLAH kucanja kodan kuma Ku amfana, kuzama jarumai irin Ibrahim Abdallah, bafa wai jaruman littafi sunfuku wani abubane, suma mutanene tamkarku, muna kafa musaline dasu domin kuma kuyi koyi da halayensu, hartakai mun rubutaku duniya takarantai labarinku._ ALLAH yasa mudace. _Lamarin Aysha abin birgewa da k'ayatarwa ga kowacce mace, matashiya kokuma babbar mace. anrabata da iyayenta tana 'Yar k'aramarta, ankaita wata k'asa mai nisa, batada kowa awajen sai ALLAH daya halicceta, abin birgewa dukda k'ank'antarta bata mance dafad'ama ALLAH kukantaba, haka tadage dare da rana wajen kai lamarinta ga ALLAH, Wanda shikad'aine zai iya kawoma rayuwarta mafita, duk kuma Wanda yarok'i ubangiji zai amsa masa, Aysha tarok'a kuma ya amsa mata, datasamu damar k'aratu batayi wasa da damarba tanutsu tayi, cikin wad'anda ba k'abilarsu d'ayabama, amma bataji shayi ko burin kasancewar gazawarta ba agaba-gaba ba wajen nuna kwazonta da jajircewa_. _sannan kuma taginu akan wani k'yak'k'yawan buri nason ku6tar damata dayawa dasuka tsinci Kansu cikin irin rayuwar datake, walau dasaninsu, koda tirsasawar wasunsu, ahakan hartasamu ceto rayuwar meerah, wadda tafidda rai dagama shiriya baki d'aya, alokacin kuma data samu damar k'arfafa mijinta saitazama mai k'arfafashin, da nuna fushinta wajen son yataimaki matan wannan al'ummar damuka kasance cikin gararin rayuwa, bayan addininmu yamana gata, amma wasu tsiraru acikinmu suke nuna zalinci da k'arfa-k'arfa akan hakan._ _yakamata 'yan uwana mata muyi koyi da Aysha, muzama masu kishin junanmu dasanin darajar juna, muzama masu k'arfafa zukatanmu wajan fallasa asirin wasu 'yan jari hujja dake wargaza rayuwarmu komin kusancinmu dasu kuwa, da wannan jarumtar Aysha tasamu damar fallasa asirin su momy har aka d'auki hukunci akansu, datayi shiru tsoro yahanata haka rayuwar zatayita tafiya da walagigi da sauran mata. Kuma wlhy abinda su momyn nan suke aikatawa agaske yana faruwane yanzun, saidai shugabanninmu sunyi burus da lamarin😭._ Mata muzama Aysha, koda k'ar6ama rayuwarku 'yancinta🤷🏽‍♀. _Mama, mama ta birgeni kwarai da gaske, zan iya cemukuma tafi kowa birgeni, Dan bata d'auki kishin banza da wofi mara amfani da amfanar da matan wannan zamaninba ta yafama kanta, tazama adalar abokiyar zama, mai mutunta mutuncin zaman tare, danuna adalci irinna koyarwar addininmu, uwa tagari, maiso ceto wasu 'ya'yan dasuka shiga gararin rayuwa, tayi tawakkali dayin abinda bakowacce uwa bace zata iya, wajen hana cutar da 'ya'yan wasu, ta sadaukar da rayuwar tata d'iya._ _ALLAH mai alkairi, saiya dubi k'yak'k'yawar zuciyarta yatsare mata tata d'iyar kuwa, abinda yay k'aranci awannan zamanin kenan, wanima bai Isa tsawatarma d'an waniba, bare har takai ga sadaukarwar cutar kai wajan ceto wasu, iyaye mugyara Dan ALLAH, mudunga duba gobenmu bawai jiyanmuba, Dan tarigada tawuce saidai labarinta, ALLAH yabamu k'yak'yk'yawar zuciya irin ta mama, mai sauk'ak'ama kanta kishi da bak'inciki, dawatace saitace INA ruwanta, aii khaleel ba d'anta baneba, d'an kishiyane, idanma ya salwanta batada asara, amma baiwar ALLAH batayi hakaba, saita jajirce har saida tamaidashi hannun mahaifiyarsa._ _dolene Mamie ta birge kowa, kodan hak'urinta da kawaici akan cinkashi da hajia baba taita mata, sai bata zamo tanamata rashin kunyaba, komin zafin abinda Tamata bata daina girmamataba, amatsayin uwargidan mijinsu, tahad'a 'ya'yan agidan tarik'e baki d'aya, vata Nuna banbanci agaresu, hakan yasaka taita bama d'anta kulawa batareda tasaniba, tarage masa rad'ad'in rashin samun kulawar daga momy wadda yakema kallon mahaifiya, dabata jasa ajikiba koda gaskiya tafito bazaiji soyayyartaba aransa, saboda zaicigaba da kallonta amatsayin kishiyar uwane.._ _saimu gyara 'yan uwana mata, mudinga lura, idan Kane agidan miji amatsayin amarya karmu hantari 'ya'yan Uwargida, bakasan ranar dazasumakaba anan gaba, Dan doledai 'ya'yankane zasuzo amatsayin k'anana, idan Kana cutar da 'ya'yan Uwargida, sumafa zasu ringa huce haushinsune akan 'ya'yanka, ko bayan idonkane kuwa, please saimu kiyaye, kowacce Matsala kagani akwai tushen k'irk'irarta wlhy, mata muyi koyi da wannan baiwa Anty Mamie, ALLAH yasa Mugane amin._ _dolene ayabama Ummi amarya itama, Dan awannan zamanin bakowane zai iya abinda tayiba gaskiya, musamman idan mukayi dubi da yanda kishi yake awannan zamanin, yarinya kafin tashiga gida tafara kishin iyayen agidan, hakan ba daidai baneba, Ummie amarya tayarda da Auren baffah domin taimakon mama akan manufarta mai k'yau, mata masu irin zuciyar ummi amarya sunyi k'aranci, burin kowa ya Auri mai dukiya yazauna shikad'ai babu kishiya, please mugyara kafin lokaci ya k'ure mana_. _samun iyaye irin baffah awannan zamanin kad'anne, musamman idan akwai wasu 'yan canji a hannunka, zakiga kullum Baka maida hankali akan tarbiyyar 'ya'yanka, uzurinka yafi kulada familie naka, aganinka karigada katara musu dukiya, shikenan buk'atunsu da nauyinsu akanka yak'are, gobe kana waccan k'asa jibi kana wancan taro, bakada lokacin iyalinka ko kad'an, dasunzo maka da buk'atar kud'i sai zaka biya musu awuce wajen, maganar tarbiyyarsu kuma kabarma matan gidanka, bayan kuma hannu d'aya bayan d'aukar jinka, musamman awannan zamanin da duniyar tarikid'e gaba d'aya, iyaye Dan ALLAH kunutsu akan tarbiyyar 'ya'yanku, walau kaid'in talakane komai kud'in, Dan wannan zamanin bawai 'ya'yan masu kud'i bane kad'ai lalatattu, wlhy tawani fanninma 'ya'yan talakawa sunfi 'ya'yan masu kud'in lalacewar, Dan haka ko'ina akwai Na kirki akwai Na banza, ALLAH dai ya gyara mana kawai, ALLAH ka shiryemu dai baki d'aya._ _idan muka d'auki jigon labarin baki d'aya ZAMU kula yatafine akan hassada baki d'aya, domin hassada itace tazama tushen komai._ _badan innah jummai tatashi da hassadar Ammah ba da komai baikasance hakaba,, hasaada tasakata gur6ata tarbiyyar 'yarta d'aya tilo, hassada yasaka d'ora momy a keken 6era Na burin zama wani Abu wajen Tara dukiya domin akirata da suna hamshak'iyar mace, badan wannan dalilinba da momy bata Shiga k'ungiyar ('ya'yan kunama ba), datayi hak'uri tazauna agidan mijinta lafiya, dabatayi tunanin cin gadon Alhaji Abdallah jigawaba, bare harta dinga kallon haihuwar mata amatsayin dakushewar komanta, har takaita ga sace d'an abokiyar zamanta, domin kawai yazama jari a burinta, wannan hassadar Ce hartakai ga shafar mufeedah batajiba bata ganiba._ _hassada masiface wlhy, domin kunga innah jummaice kawai taginata, amma tacigaba da zagaye mutane masu d'unbin yawa acikin masifa, innah jummai ta Reni momy akan hassada, momy kuma tareni 'ya'yan ta gallabar rayuwar wasunta irinsu mama da Anty Mamie, hartazama sanadin salwantar wasu mutane dayawa._ _Amma abin kaico, dukkan abinda suke burin akansa ALLAH yabasu, daga k'arshe kuma saiya zama rugzajje, Mara amfani agaresu, saima yazame musu sanadin nadama da Dana Sani, k'ask'anci da d'umbin kunyar rayuwa, Yakamata Mugane hassada tamkar tubalin toka take, koda kaginata danisa watarana saita ruguzo idan tatashi da mutuncinka kuma zata rushe. Hassada babu k'arama babu babba acikinta, komin samanka kuma saika fad'o idan kakasance mutum mai hassada, koda bakayi k'arshe irinnasu innh jummaiba kuwa, kuma mafi yawan mai hassadama wlhy sanadin bugawar zuciya yake mutuwa, ko hawan jini._ _a wannan zamanin ko kishi damata keyi hassada tafi yawa aciki, Dan ba'a kishi irinna matan manzon ALLAH (s,a,w), wannan nabama kowacce mace dama tazauna tayi nazari akan hakan kuma._🤷🏽‍♀ _soyayyar Khaleel da Aysha abin birgewa, kowacce mace tana burin samun irin wannan rayuwa, gashi kuma itace tayi k'aranci, Dan mazajenmu sunfi fifita Neman kud'i akan iyalinsu, k'alilanne acikinsu ke bama matan kulawa, amma da anyi aure wata uku tayi yawa soyyaya tazama tarihi saikuma zaman hak'uri dana 'ya'ya, wlhy ko kar6uwar novels damaida hankali wajen son karatun buks Na soyayyar damukeyi yasamo asaline daga k'aranci kulawa ta mazajenmu akanmu, towatama batasan irin wannan soyayyarba sai novels, shiyyasa idan muka saka tayi yawa saikiji ana k'aryatamu, Dan ALLAH maza kugyara, ko yawaitar zinace-zinace da buri irin Na mata yana tafiyane wajen k'arancin kulawar damuke samu, kishin kansa damata keyi harda rashin kulawa, domin ita kanuna mata soyayyar awaje, amma tana shigowa gidan sai komai ya canja, kakuma koma hangen wata awaje, kana bata kulawar dabaka bama wannan tagidan, kaga kuwa kataro March wlhy, amma muma matan dazamu nutsu muyi hak'uri dasaikiga abin mamaki, itamafa tana shigowa gidan rabin shekara yayi yawa zata fara kwasan makamancin d'acin dakika d'iba sanadin shigowarta, Dan itama kwanaki kad'an idonsa zai fara komawa kan shinshino wata kuma awaje😂🤭, bulalar data doki uwargidafa, itace zata jibgi amarya watan watarana._ _mun kasa fahimtane kawai, amma maza sun maidamu sakarkaru wlhy, ahanaki zaman lfy da jituwa tsakaninki da 'Yar uwarki jinsinki, sannan sukuma kullum suna gefe suna dariya dakiranku mahaukata baki d'aya🤕._ Saimu farka idan munga zamu gane, idan bazamu ganeba kuma muyitayi, muke tareda wahala, sudai babu ruwansu. _kobabu komai Ammah jar wuya tsohuwar arzik'i ta nishad'antar daku😂, kowa zaiso yasamu kaka irin Ammah😉👍🏻🤣._ Bara nabarku haka, badan nagajiba, saidan watarana cikakken sharhin wannan labari zai iya zuwa muku kaitsaye daga k'ungiyar haske, bayan antaceshi an tankad'e kuma an rairaye. Takuce har kullum, mai sonku da k'aunarku. Bilkisa Ibrahim (Bilyn Abdul) Marubuciyar.✍🏻 *_Rashin sani!!._* *_auren k'addara ko biyayya?_* *_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?_* *_Nida aminiyata!!_* *_Nawaff!!_* *_Sabon al'aree!!_* *_kukan kurciya....!!_* *_Ban saketaba!!_*. *_Abdul-maleek bobi!!_* *_Karayar arzeek'i!!_* *_sanadin bikin sallah!!_* *_ciki da gaskiya!!_*. _duk zaku iya nemansu Ku karanta, karkuma kiji tsoro ko kunyar tunasar dani wani kuskure danayi acikinsu, kifad'amin ta k'yak'yk'yawar sigar dazan fahimceki vatareda cin zarafiba._ _banyi ciki da gaskiya domin cin zarafin kowaba, hakama sauran buks d'inna, saboda yanayin rayuwama nak'i fad'ar wani matsayi daga 6angaren aikin khaleel, shikansa ban fad'i girman igiyar kakinsaba, so hakan yafi sauk'i._ Idan kin karanta saiki gyara abinda kikeyi Mara k'yau, kodan gudun fad'awa hanya Mara k'yau, idankuma burin yi ne dake saiki cireshi aranki. ALLAH yasa Mugane, mu anfana da abinda muka samu aciki, Wanda yazama kuskure ALLAH ka yafe mana baki d'aya. ALLAH ka gafartama iyayenmu dadukkan musulmai dasuka rigamu gidan gaskiya. Duk Wanda na6atamawa ayayin rubutun wannan labarin ya gafarceni, nayine akan rashin sani, ALLAH ya yafe mana baki d'aya. Abaya nace next novel d'inna ABINDA KASHUKA.... Tom yanzun naga ana rubuta abinda ka Shika, so watak'il zan iya canja sunan nawa labarine idan hali yazo da hakan, idankuma naga babu sunan daya dace dashi to zanyi amfani da wannan sunan nafarko. Insha ALLAH a next year zakuga Sabon buk d'inna. Inama kowa fatan alkairi. Bilyn Abdul Ce.😉👍🏻👍🏻👍🏻 Ngd kwarai da gaske💋💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤