Compiled By Umar Dalha Funtua. Copied By Aminatu Hassan Oum-Deed at. [8/5, 8:19 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~* *Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat) *Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat) *Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare. *Godiya*---- Ga Allah subhanahu wata'ala daya bani rai da lafiya na rubuta maku wannan littafin mai dinbin fad'akarwa da nishadantarwa, yanda nafara lafiya ina rok'on Allah yasa in k'are lafiya. *Jinjina*--- ga 'yan Golden Pen writers association Allah ya k'ara hada kanmu ya qara mana zaqin hannu ya bamu ikon rubuta abunda zai amfani al'umma baki daya. *Matashiya*--- wannan labarin qirqirarre ne banyi da niyyar cin zarafin kowa ba duk wanda ya ci karo da abunda yayi daidai dashi yayi haquri. Page *_~1~_* • ∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆• Tsoro na Allah tsoro na muhadu dashi ahanya saboda ko ba komai dai ni nasan bana iya kallon cikin kwayar idanunshi,wani mugun kwarjini yakeman ta bangare guda kuma tsareni da idanunshi masu rikitar dani dayakeyi aduk lokacinda zamu hada hanya. dukda an bashi shedar tinda ake dashi ba'a taba ganin miskili ta bangare guda kuma kamilin saurayi aduk fadin unguwar ba irin shi. Unguwar da take cikeda 'ya'yan masu kudi 'yan gata, 'ya'yan masu fad'a aji a fad'in Nigeria, da yawa yawansu ma ba a qasar sukeyin karatu ba ta wani bangare kuma sha'aninsu sukeyi da 'yan matansu 'ya'yan k'usoshin gwamnati irinsu amman duk da haka acikinsu Ya Ameen daban yake. mata dayawa suna sonshi amman shi Sam basa gabanshi Aikinshi da kasuwancinshi kadai yasanya gaba, acewarshi har yanzu ba'ayi yarinyar dazai tsaya b'ata ma kanshi lokaci akanta ba, kai shi soyayyar ma gabaki dayanta bai yarda da itaba. Menene abunso a jikin mace? Kullum tambayar da ya keyi ma kanshi kenan. (Nidai nace bakaje hannu baneba lol🤣) """"""***************""""" Ahankali nake takawa cikin natsuwata da tafiya ta mai ban sha'awa da burgewa, ni ahakan ma gani nakeyi sauri nakeyi saboda aiken da ummata tayiman kasuwa banaso na rasa adaidaita din da zai kaini duba da yanayin unguwar tamu, akwai drebobi har guda uku acikin tanqamemen gidan namu ko nace nasu amman dukda haka ummana ta haneni da shiga motocin domin kaini inda zani, a cewarta in tsaya matsayina na diyar mai aikin gidan mara galihu saboda gudun wulaqanci dukda cewa su drebobin ba zasu wulaqantani ba kasancewar mu dasu duk matsalar mu daya na wulaqanci da muke fuskanta daga matar gidan, A wajen mai gidan da babban yaron gidan ne kawai muke samun sassauci amman ba daga su ba mudin da dabbobin dake gidan gonar bangare daya daga cikin gidan duk daya muke awajen iyalan gidan in kacire mutum uku rak cikin mutum bakwai daga cikin gidan watau Ya ameen Babban Dandan Gidan a maza, afnan watau autar gidan dashi kanshi kuma uban gayyar watau mai gidan Alhj Mustapha Dambulan Ban aune ba naji nayi karo da mutum kasancewar saurin da nakeyi kuma da son kaucewa idanun drebobin saboda banaso su yiman tayin kaini din, lokaci guda kuma nayi baya zan fadi bankai ga kaiwa qasa ba naji an janyoni dakarfi har na fada faffadan kirjinshi da yake cike da haiba, lokaci guda dad'edd'en kamshin turarenshi da ke kara taimakawa wajen rikitar dani ya yiman sallama a hancina. "Subhanalla" nace ina mai ja baya dasauri amman dukda haka damtsen hannuna na cikin nashi ba tareda ya sakeni ba, "yi hakuri don Allah yaya..." "Shiiii🤫" ya katseman hanzarin bashi hakuri da nakeyi, cikin isa da rashin son magana dinnan nashi ya bude baki dakyar yaceman "is ok ya wuce amman nan gaba ki dinga kula, bakyau ana tafiya ana tinani" ya fada ahankali yanda nikadai zan iyaji dukda dai cewa dama haka yanayin maganar tashi take don in ba saninshi kayiba saima ka dauka maganar zuci yakeyi labb'anshi ke motsawa Sakina yayi tareda zagayeni ya wuce kaman ma ba shine ya gama magana ba yanzu Girgiza kaina nayi yayinda har yanzu ban koma normal ba bugun zuciyata ya qara gudu lokaci daya kuma ina kokarin daidaita numfashina domin ji nayi kaman ya wuce tare da numfashin nawa, juyawa nayi nabishi da kallo har ya shige dan madaidaicin apartment din nashi da yake cike da kyau da qayatuwa a bangare guda na gidan. Ci gaba nayi da takawa mamakin shi fal araina, na godema mahalicci na da ba aunty sauda ko nihal ce wannan tsautsayin ya faru akansu ba da na kade har buzuna,bani kadai ba ma har ummata da take cen tana masu iyakar iyawarta cewa zasuyi na bangajesu na daidaita kafada ta da tasu ubanwa ya haifeni, oh "Allah ya soni" na fada afili ina mai sauke ajiyar zuciya daidai lokacin da na daidaita kaina ta gefen titi ina mai tafiya tareda waige waigen Inda zan hango abun hawa saboda inaso nayi sauri na amsoma ummana aikenta kada mukara yin laifi akan wanda mukayi dasafe wajen Hajiya matar gidan da muke aikatau. _Muje zuwa Wannan shine mafari_ ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~* *Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat) *Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat) *Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare. Page ~2~ •∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆• *Ya kamata musan wannan gidan dakuma rayuwa dake gudana agidan* _Wacece wannan yarinyar da takema kanta ikirarin marar galihu?_ _Wanene Ya Ameen?_ _Wanene Alhaji Mustapha Dambulan?_ """""""""""""""**********""""""""""""""" Alhaji Mustapha Dambulan asalinshi dan jihar Katsina ne A wani Local Government da ake kira kankiya, su shidda ne awajen mahaifinshi da mahaifiyarshi da suke zaune cikin rufin asiri daidai gwargwadon abunda Allah ya hore masu, mahaifinsu Alhaji Isuhu da mahaifiyarsu Hajiya zuwaira suma duk yan asalin karamar hukumar kankiyar ne. Alhaji isuhu manomi ne rikakke, kuma irin attajiran qauyen nan ne saboda yana noma ga kiwo yanayi, kuma ta bangare guda yana ba mutane jari sudinga sana'a suna raba ribar, akalla mutanen da yake wannan kasuwancin dasu sunkai mutum goma koma fi, sannan yana kasuwanci na auduga da kamfanin saqa kaya dake Lagos inda dakanshi yake siyen auduga da wadda yake nomawa ya hada yakai kamfanin a bashi kudinshi yazo ya sake juyasu kafin kakar audugar ta dawo. Yaranshi maza biyu ayayinda mata suke su hudu dukda cewa ya aurar da guda biyu manyan yanzu saura biyu ke gareshi a gabanshi. Dukda yake mutumin karkara Allah ya bashi matukar tinani hankali da basira, saboda alokacin karatun boko baiyi yawa ba azamaninsu amman ahaka yace insha Allah 'ya'yanshi duka mata da mazan sai sunyi tinda shi Allah bai bashi ikon yi ba, matan na gama makarantar primary yake aurar dasu ga wadanda sukeso saboda shi babu tsarin auren dole ko hadi a rayuwarshi tinda yace shima ba'ayi mashi dole ba wannan shi yasa yake zaune da matarshi kwaya daya rak kuma uwar 'ya'yanshi duka guda shiddan,ayayinda mazan kuma suke wucewa gaba da primary Allah ya taimakesu kuma suna gamawa suka samu aiki tinda alokacin ko baka gama secondary ba ma in kaso zaka iyayin aiki kuma abiyaka albashi mai tsoka saboda alokacin kudin sunfi daraja ba kaman yanzu ba. Aisha itace zuwaira tafara haihuwa daganan sai Fatima mai bimata sai kuma Auwalu daganan sai aka haifi Mustapha. Haihuwar ta tsaya mata kusan wasu shekaru masu dan dama inda har sun gama makarantar primary dinsu sannan Allah yabata haihuwar 'yanbiyu mata aka barmasu sunansu watau Hassana da hussaina. Kyawawa ne gabadaya gidan jajir suke ga hanci masha Allah wannan shiyasa ma yayinsu mata sukeda manema har Allah yasa aka aurar dasu sai kannensu mata da ake gab da aurar dasu suma kwana kusa. Aikin da auwalu da Mustapha suka samune yayi sanadiyyar barowarsu mahaifarsu suka dawo cikin garin katsina ayayinda shi auwalu ya dogara da aikin da yakeyi kawai shikuma Mustapha dayake shi ya gado mahaifinsa sak Allah yayi mashi zafin nema sai yake hadawa da kasuwanci ya saro kaya ya dinga sararwa ga masu shaguna inda nan danan Allah ya yi mashi ludufi abun ya bunkasa kawai sai ya fara gininshi a unguwa mai kyau saboda shi bayada ra'ayin zama gidan gwamnati ayayinda shi yayanshi auwalu bai damuba ganin cewa a albashinsu ake cire kudin Ganin ya gama gidanshi dan madaidaici yasanya yaso iyayenshi su baro karkarar sudawo maraya, sukau suka kafe kai da fata alambaram bazasu bar mahaifarsu da danginsu sukoma wani wuriba subar noma da kiwonsu, saidai fa in aure zaiyi ya sanya matar acikin gidan, yayinda shikuma yace lallai ba aurene gabanshi ba yanzu ma shirin qaro karatunshi yakeyi a qasar waje amman tinda yayanshi yasamu wadda yakeso ya aura yasanya ta acikin gidan alabasshi sai su warware ahankali. Lokaci daya akayi bikin auwalu da yan biyu inda su aka ajiesu anan cikin garin kankiya shikuma Mustapha alokacin ya ma dade da tafiya k'aro karatunshi, amman a gidan da Mustapha ya gina nan auwalu yasanya matar tashi maisuna Zainab alokaci guda kuma yana cigaba da aikinshi na gwamnati. """""""""""""""**********""""""""""""""" Mustapha ya kammala karatunshi cike da nasarori ayayinda arzikinshi na Nigeria ya cika ya tumbatsa saboda koda yaje karatunshi baibar kasuwanci ba sai ya koma saro kaya irin na kasar wajen masu masifar kyau yana turowa kuma asaukake inda yakeba babban amininshi da sukeyin kasuwanci tare yana saida mashi yana tura mashi kudin yasake saro wasu. Gininshi ya farayi tanqameme acikin unguwar GRA yayinda shikuma Auwalu yake layout amman gini ne na fada aji domin fintinkau yafi wanda auwalu ke ciki ya gina apartment guda uku manya aciki yayinda shifa ya kafe akan sai ya maido iyayenshi birni suma suzo su huta tinda suma sun kawo karfi komai zasu iya yima iyayensu harma su taimaka ma 'yan uwansu mata da suke gidan mazajensu da suka fara tara zuri'a Ganin ya kammala gininshi ga kasuwanci ya habbaka ya gina manyan store store na kayan masarufi da kuma kayan electronics sai kuma motoci daya fara shigo dasu daga qasar waje manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa na siye ta bangare guda kuma bai daina kasuwancinshi na qasar waje ba inda har ya zuba hannun jari a wani babban kamfani a China dayake saqa atamfofi da k'era wayoyin hannu. K'arin girma sosai ya samu saboda karatunshi da ya qaro inda ya hada digree dinshi na farko da na biyu afannin qere qere da kasuwanci wannan shi yasanya gwamnati tarayya tafara bashi kwangila ta gina gidaje da masana'antu abundai sai Sam barka ba'a cewa komai addu'ar iyayenshi tana binshi tinda Mustapha mutum ne nagari maison kyautata ma duk wanda Allah ya hada shi zama dasu kuma baya kyamatar talaka ko mara shi duk daya ne awajen shi saboda yasan Allah ne mai azurtawa kuma yana azurta wanda yaso alokacinda yaso. Wannan kenan *KUBRA* d'iya ce ga hamshaqin d'an kasuwa Alhj Nura, Alhj Nura tare suke kasuwanci da Alhj Mustapha dukda ba tsaranshi bane ko kusa amman dai shi harka ta kasuwanci babu ruwanshi da wannan ta bangare guda kuma yana damawa a siyasar qasar babban dan kwangila ne da Allah ya azurtashi da makudan kudaden da shi kanshi baisan iyakarsu ba saboda yafi Alhj Mustapha kudi nesa ba kusa ba, kubra kyakkyawa ce dukda bazata gwadama Mustapha komai ba, ahaka Allah ya hada jininsu suna soyayyarsu dukda ita taganshi tace tana sonshi wanda hakan tasa Alhj Nura yima Mustapha magana, baiyi qasa aguiwa ba ya amince duba da yanzu iyayenshi babu abunda sukeso dagani irin iyalanshi kada girma ya cimmashi ahaka batare da ya tara zuri'a ba. Kubra na da wani hali na kyamatar talaka da marar galihu inda Mustapha bayason wannan halin har yana mata magana akai irin yadda yaga in yaje fira gidansu tanama ma'aikatansu bayajin dadi sai yake dan tsawatar mata lokaci lokaci, to tana dai kokarin kiyayewa saboda irin son da take mashi saboda Mustapha kyakkyawane ajin qarshe ga naira ga Hutu dukda bazai nunama mahaifinta komai ba. Acikin haka ne Allah yasanya akayi auren Mustapha da amaryarshi kubra suna zaune kalau, wannan tasa ya jama yan aikinsu kunne ya gaggaya masu halinta saboda su kula kuma suna kokarin kiyayewa. Dangin Mustapha kaf sunason kubra (kundai San yanda akeson mai kudi) iyayenshi girma ya kamasu yayinda mahaifinshi ya koma ya zauna ya barma qaninshi duka hidimominshi tinda 'ya'yan sun kawo karfi, saidai fa Mustapha ya gyara masu gida ya maidashi na zamani tinda sun k'i baro mahaifarsu ya sanya masu masu aiki da masu gadi da dreba guda daya mai suna iro suna kula dasu tinda yanzu babu sauran kowa a gabansu in ka dauke jikokinsu yaran Aisha da Fatima harma da yan biyu dake zuwar masu Hutu kuma tinda akwai ma'aikata suke kula dasu don dai hajiya zuwaira girma ya kamata don ma dai jikin nasu ba irin namu bane ba 'ya'yan yanzu. Mustapha yaba 'yan uwanshi kaf jari kuma dukansu ya tattara su bayan aurenshi sukaje qasa mai tsarki suka sauke farali harma da wasu daga cikin ma'aikatanshi dayake ya bude babban kamfanin markada qarafuna a jihar legas yayinda ya dauki ma'aikata daga jiharshi ta haihuwa dakuma saura daga saura jihohin nigeriya Ahaka Allah ya azurta kubra da samun diya mace kyakkyawa aka sanya mata suna Nafisa suna cemata feena daga ita sai Al'ameen suna ce mashi Ameen sai saudatu ana cemata saudat sai mai sunan Hajiya zuwaira suna cemata Nihal saikuma namiji data haifa Yusuf ana ce mashi Abi sai autarsu mai sunan maman Hajiya kubra watau bilkisu ana cemata Afnan. Yara ne sun taso cikin gata da kulawa,kuma ga karatun arabi dana boko gabaki daya Allah ya basu saboda mahaifinsu mutum ne mai tsantseni yaran wasuma ya tsaya ya kula dasu bare nashi, Sam bayason abunda zai bata mashi tarbiyya da karatun 'ya'yan nashi, wannan ce ta sanya ya tattara kan 'ya'yan nashi ya tafi qasar waje dasu bawai don ya raina tashi qasar ta haihuwa bane a'a saidai kawai irin yanda yanzu karatun kasar namu ya tabarbare acen yasanyasu makaranta mai kyau da ta Haddar alkur'ani dasauran litattafai, ahaka nafisa tasamu miji a cen qasar ta Dubai inda akadawo nigeriya akayi bikin kasancewar shima dan nigeriya ne iyayenshi yan asalin garin zariya ne,amman acen yake kasuwancinshi dama karatu ya kai shi kuma ya gama harma ya fara aiki da wani kamfanin kera takalma da abaya irin na mata. Gabadayansu sun gama karatunsu inda mohd Al'ameen ya karanta fannin kasuwanci da fasaha (watau dai ya gaji mahaifinshi) ya hada masters dinshi ya jona yanaso yayi doctrine dinshi ita kuma sauda tayi degree na biyu yayinda Nihal da abi suka kammala degree na daya itakuma afnan tana aji na biyu secondary wannan ne ya sanya Alhaji Mustapha ya tattara kan iyalanshi ya dawo qasarshi ta haihuwa domin qasar ta amfana da ilimin da 'ya'yan nashi suka samu Amman sun baro afnan gidan aunty feena domin karasa nata karatun, suma su Nihal da abi zasu koma idan sunso su cigaba amman alhaji yace sai sunyi aure tukunna domin ya gaji da ganinsu haka zaga zaga dasu ba aure. Inda moh'd Al'ameen ya wuce qasar america domin karasa karatunshi daya dauko ta fannin fasahar zamani domin kasuwanci ya iya harma ya fara da taimakon mahaifin nashi Hajiya kubra tana nan da halinta dakuka Santa dashi tin farko saima abunda yaci gaba domin mahaifinta Alhj Nura Allah yayi mashi rasuwa bayan haihuwar Nihal aka raba masu gadonsu, kasancewar ta na diya daya tilo ta mallaki dukiya da qadarorin da suka kara mata girman kai da dagawa domin yanzu bata jiran Alhaji wajen komai saboda itama ta mallaki dukiyarta ta agani afada wannan shi ya qara sangarta 'ya'yanta dukansu in ka dauke yaAmeen da afnan da bama ta qasar gabaki daya saidai tazo Hutu Gida na nunama sa'a alhaji mustapha ya qera masu a garin abuja suka tarkato daga gidanshi na katsina, ya ba yayanshi alhaji auwalu da ya tara zuriya shima da matarshi Zainab abun dai sai sam barka yayinda ya sake siyan fili ya k'ek'ara ma iyayenshi gida a cikin kankiyan tunda tsufa ya kamasu kuma sunki barin mahaifar tasu ya kuma Gina masu gidan gona Inda aka cigaba da kiwon dabbobi kama daga su kaji,talo talo dawisu,shanu,awakai da duk wasu nau'in dabbobi da kuka sani ya kuma bada ana masu noma tinda itace tushen arzikinsu shiyasa basu yada ta ba. 'Yan uwanshi mata duka ya gina masu gidaje ya qara masu jari kuma duk shekara sai wasu sunje hajji su da iyalansu ya dauki nauyin karatun 'ya'yan gaba dayansu kuma sunayin karatunsu cikin kwanciyar hankali wasu ma ya fiddasu qasar waje suna karatun tinda Allah ya hore mashi yanzu duk fadin Nigeria babu dan kwangila sama dashi,ya gina ma'aikatu yana daukar ma'aikata ga sana'ar motoci da qarafuna duk ya nayi,kudi dai ko ta wacce hanya juyasu yakeyi wannan shine silar arzikin Alhaji Mustapha Dambulan din kudi kenan inda ya tara tarin masoya da mahassada arayuwarshi. YaAmeen ya dawo daga karatunshi hankali kwance da tarin Alkhairai,qasar ta amurka taso rikeshi saboda kaifin hankali da hazakarshi, amman ya qiya saboda irin tarbiyyar mahaifinshi dakuma kishin qasar tashi nigeriya. *Wannan Kenan Yanzu Aka Fara* 🌹🌺~Oum-Deedat ce~🌺🌹 [8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~* *Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat) *Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat) *Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, qanwa daya tamkar dubu,Allah ya barmu tare. Page ~3~ •∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆• Muje zuwa....... Ahankali zanmaku wacece "Suhan" ya labarinta yake kuma me ya kawosu irin wannan gida dayake cike da tarin gadara, shagwaba, mutumci, halarci,dakuma miskilanci """""""""""""""""***********""""""""""""""" Cikin hanzari na siya abunda duk nasan anada bukata na baro kasuwar da tarin idanu yayiman yawa, adaidaita na hau tare da fada mashi sunan unguwar da zai kaini. yayinda muka isa nace mashi ya ajiyeni nesa kadan da gidan, sanin danayi cewa YaAmeen yana gida, kuma zai iya tambayata dalilin dayasanya driver bai kaini ba, tinda shikuma ya hanani hawan okada, acewarshi drebobin basuda amfani in har wani acikin ahalin gidan zai dinga hawa hayis, (oh ko su wanene ahalin gidan oho😵) Ilai kuwa yana qofar gidan zaune bisa darduma, yana shan daddad'ar iskar dake busowa ta sanyin marece dakuma flowers dake busowa, a lokaci daya kuma yana latsa iPad din dake hannunshi, dagani wani abu muhimmi yakeyi,cikin sanyinshi da halinshi ko wayar ma sai an yi mata Jan aji da yanga?🙄 Suf suf na wuce, wuf na shige ta tamqamemen gate din dake kofar gidan mai double, saboda har ga Allah yanzu nidai kunyarshi nakeji tun abunda yafaru dazu dani akanshi,wai nice yau kwance a k'irjin yaAmeen...k'irjin da kowa ke mararin ganin mamallakiyarshi shi, k'irjin da mata da yawa keson kasan cewa bisa shi, ni nayi imani in ka kadauke kannenshi nice ta farko da na fara kwanciya bisa shi, nima fa a tsautsayi ne ba yin kaina bane ba tinda ko magana zamuyi bana yarda in kusanci inda yake kawai ina tsayawa ne ta inda zan iya jin maganar shi Shima kuma yana k'ok'ari wajen ganin ya ma baya ga duk wata d'iya mace da ba muharramarshi ba. ( yo wa ma zai iya rungumewa wannan sarkin 'yan miskilan🤔) Da wannan guntun tinanin nashige sashenmu damin isarma da ummarmu aikenta, nima inyi maza in hada ma aunty Nihal fruit salad d'in da ta ceman tana so,wanda saboda tsabar isa da taqama saidai tayiman text din in hada mata d'in. Shi kau ta bangarenta yana lura da ita tin sa'adda napep ya ajiyeta da sand'on da takeyi kada ya ganta, bata san ta riga ta makaro ba, murmushi yayi mai kama da an sanyashi dole, domin shidai lamarin yayinyar na bashi dariya, shidai har ga Allah ba shiga lamarinta yakeyi ba, amman ya kula mahaifiyarta na iyakar kokarinta wajen bata tarbiyya, ko motocin gidan ya kula mahaifiyarta ta hanata hawa. bai gasgata ba saida ya tambayi malam mudi shugaban drebobin gidan yabashi tabbacin hakan, shikuma ya gargadesu da matsa mata kada su sanya ta bijirema umarnin mahaifiyarta, matar da yake girmamawa fiyeda tinanin kowa, yana sonta har cikin ranshi yake tausaya mata saboda ya kula akwai wani sarqaqqen Al'amari mai girma tattare da ita, matar da kuma duk duniya mahaifiyarshi batada wadda take wulaqantawa irinta, amman ko menene ya sanya ta nace ma zaman gidan? Oho! Dukda lokuta da dama yasha taddata bangaren masu aikin, ya sanya su kebe ya yi mata tayin barin aikin shi zai kula da ita da duk bukatunta batare da kowa ya saniba Amman ta kan ce mashi " karka damu muhammadu komai lokaci ne". Iyakar abunda take fada kenan tayi mashi sallama tabar wurin "Huh" 😯 ya fada tare da guntsar iska ya fesar alokaci guda yana mai kad'a kafad'a "Haka ne umma kamar yadda kika fada Allah yasa lokacin yazo mana da Alkhairi" ya fada a fili yana mai mik'ewa tare da tattara shimfid'ar tashi. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• Wanene Moh'd Al'ameen? 'Da na biyu wajen Alhaji Mustapha Dambulan, kuma d'a mafi soyuwa a zuciyar Alhajin,ko dan ya gado shi ne ta fannin harkokinshi? Ko dan shine yaro mafi sauki tareda jinkai da taimakon na qasa dashi? Ko don shine kadai baya daukar irin zuga da halin mahaifiyarshi? Sau dadama ma yana mata nasiha wasu lokuttan dukda yasan ba ta dadin rai suke rabuwa ba, dukda yasan ba dauka takeyi ba, amman yana fata wani lokaci tagane gaskiya kuma tadawo kan hanya. Kyakkyawan namiji ne ingarman namiji ka fasalta duk wani kyakkyawa da kasani tau YaAmeen ya wuce shi d'an boko ne na bugawa a mujalla kuma dan gayu ne, mutum ne maison tsafta yana da ladabi sosai, bayason bacin ran iyayenshi, matashin mai naira ne domin wasu daga cikin abokanshi kan mashi laqabi da yaro da kudi..., miskili ne na gidan gaba sau dadama yana kallo anayin abu amman yakasa tankawa saboda k'yashin magana da Allah yayi mashi, kokuma yayi kaman ma baisan anayi ba, bashida business da mata mace komin kyaunki komin haduwarki Baki kai ya kalleki ba, yana da shekara talatin da biyu a duniya, idan an mashi maganar aure kaka zuwaira wadda suke kira da Hajiya kan ce akyaleshi komai lokaci ne, yayinda Alhj isuhu kan matsanta da maganar, ita ko Hajiya kubra tana ganin an matsanta ma d'and'anta ita har yanzu ma bataga matar da ta kwanta mata ba da zata iya barin d'and'anta mafi soyuwa a wajenta ya aureta ba ta zame mata suruka a ganinta har yanzu cikin masu cewa su a son YaAmeen din da wad'anda iyayensu ke son had'a su dashi har yanzu arzik'insu bai kai mata wanda zata iya had'a zuriya dasu ba,balle tana ganin Al'ameen dinta saurayi ne na nuna ma tsara, yaro ne da kowacce budurwa kan so ya zame mallakinta. Tanason suruka 'yar babban gida, 'yar masu naira, masu fad'a aji a fadin duniya. bama Nigeria kadai ba, in haka ta faru ita fiye da burinta ya cika saidai abunda ba'a rasa ba, tinda kishiyace mata ke gudu ita kuwa tasan ta wuce wannan level din koma kawo wannan tinanin a ranta batayi. Dukda halin YaAmeen na miskilanci hakan bai hanashi tausayi da jin qai na talaka ba, sau da dama ma zaiga su saudat na wulaqanta masu aikin gidan ya tsaya ya tsawata masu, saboda akwai ma lokacin da ya taba marin nihal saboda ta watsama wata mai gyara mata daki ruwa, (tin ma suna farkon dawowa k'asar, kafin zuwan su suhan gidan) saboda tayi mata mopping din daki, bata kunna air conditioner ba ta sanya mata room freshner shine ta taddata harabar gida ta watsa mata ruwa, akayi sa'a akan idanun YaAmeen din ne,aikau batayi aune ba ta ji saukar mari a kuncinta, wannan ne ya sanya sukejin tsoronshi, saboda ko sun fada ma hajiya kubra bata mashi fad'a sosai saboda irin son da take mashi. Da wannan ne ma'aikatan gidan suke samun salama indai yana qasar idan kuma yayi tafiya suke kaffa kaffa saboda sanin halin 'yan gidan. ======================= Da sallama na shiga tanqamemen falon da ya lashe kujeru saiti hudu acikinshi,dukda nasan babu mai jina kuma da wuya ma ka tadda wani a falon, shima a hakan wai an ginashi ne saboda sauke baqi, dukda hajiya kubra ta mai dashi na sauke baqin da sukazo daga kauyen su alhajin, amman batare da saninshi ba.dukda babu kowa dake zaman falon, dukda haka sai na shareshi kullum nayi mopping, wannan shiyasa kullum nake kwana da uban ciwon jiki, wani corridor mai zurfin gaske nabi, banyi wata tafiyaba na tadda kofar falon Nihal da saudat din, kwankwasawa nayi dukda nasan bazan samu amsa ba amman haka dokar take garemu dukkanmu ma'aikatan gidan, kuma ko ma a musulumci haka dokar take shiyasa ma abun baya b'ata man rai. sallama nayi tura qofar ahankali na shiga cikin salon tafiya ta (kamar ta masu akwai😜) falo ne madaidaici jere da kujeru kyawawa kalar sararin samaniya dukda cewa komai na falon haka yake, kama daga su labulaye Chinese carpet dakuma tiles din da ke malale a dandamalin falon. K'ofofi biyu ne rak cikin falon, karkatawa nayi nabi ta gefen haguna inda zai sadani da asalin dakin Nihal din, hannuna dauke ba bowl na ceramic cike da fruit salad daya sha madara da zuma, nayi sallama a dakin bayan na murd'a handle din dakin. Kwance na hangota nutse cikin gadonta da zan iya cewa yafi auduga taushi (🤔 oh ko ina suke samun irin wadannan katifun?) Ni kuma nace kaji suhan da k'auyanci😉. Hannunta rike da waya k'irar Samsung a hannunta tana waya ga wata ahannunta daya k'irar iPhone tana latsawa,dagani dai da wannan dan gayen saurayin nata takeyin waya. "Aunty Nee gashi" nafada ahankali saboda kada tace nayi mata ihu a kunne, ko kallona batayi ba balle tayiman magana,dama nasan hakan zata kasance, in kuma ban mata maganar ba ba zata sha ba, kuma nayi laifi, sai an hukuntani, wannan ce ta sanya nake cemata gashi tinda ni ke qasa da ita kuma nema nakeyi. Takawa nayi na ajiye mata a kan wani qaramin stool dake gefen gadon mai kyau kaman da gold aka qerashi tsabar kyau, na juya da nufin ficewa a d'akin. "Hey" abunda naji tace kenan cikin maganarta mai cike da shagwaba-shagwaba gadara gadara, isa isa, tinani na ya katse lokacin da naji tace "ki wanke mun toilet dina" abunda tace kenan ta cigaba da wayarta saboda nidai banajin me take cewa a wayar saboda munada dan tazara. Gaba na ne ya fadi tino danayi naga text din aunty saudat a waya ta,itama tanason meatpie dashi zatayi dinner gashi kuma yanzu lokaci yakusa qure wa inda Allah ya taimakeni ma akwai means meat a fridge..... "Ko bakiji bane?" Ta fad' a sound so harsh "To aunty" nace tareda shigewa toilet din wanda nidai a iya dubana na tsanaki babu abunda toilet din yayi, saboda dasafe na wankeshi kuma ita kadai take using abunta kawai tsabar mugunta da son sanya aikin. Agurguje na gama mata na fito tareda shigewa kitchen din da yake main falour din na gasa ma aunt saudat meatpie din tareda hada mata meant juice,saboda nasan k'a'ida duk dare saita sha shi,wai saboda batason tayi k'iba. Fitowa nayi tareda zuwa na sake wanka, nayi alwala na kabbara sallah tinda anriga anyi magriba ban tashiba saida akayi issha'i, na fito da niyyar zuwa inyi serving dinsu wajen cin abincin da ummata ce ke girka masu wai basu iyacin abincin kowa dagani sai na ummana shiyasa ma mu dakinmu daban ko acen boys quarters din masu girkama 'yan cikin gida abinci da gyara masu sashensu, wannan ka'ida hajiya kubra ce ta sanya ta dole dukansu suke haduwa, wajen yin breakfast da dinner ko da kuwa Alhaji Mustapha na nan hardashi ake haduwa wajen cin abincin Ummana ce ta katseman hanzarin barin sashen namu da nakeyi "mamana ga abincinki nan kizauna kici naga yau kaman a gajiye kike ni zanje na zuba masu abincin" ta fad'a tana mai kallona cike da tausayawa saboda tasan irin yanda yaran gidan ke gallaza man ta wajen sanyani girkinsu da aikace aikacensu na babu gaira babu dalili, "No umma banason ayi maki abunda zai bata maki rai, ko kinje zasu maki wulaqanci ne kiyi zamanki yanzu zan dawo ai YaAmeen yana nan basa min wulaqanci sosai in yana wajen jiya ya dawo k'asar kinsan" nafada ina kamo hannuwanta, gyada man kai tayi tareda cewa "Allah yayi maki albarka d'iyata yanda kikeyi man Allah ya baki maiyi maki kema ya baki miji nagari, kicigaba da hakuri watarana sai labari" "to umma nafada" tareda wucewa ina cemata "kije kici abinci kisha magani ki kwanta yanzu zan dawo insha Allah" "to" tace tareda komawa dakin namu, nikuma na wuce dasauri domin nasan suna cen suna jirana. Ilai kuwa a zaune na tadda su a dinning area din dayake yakusa girman wani qaramin gidan, kaitsaye kitchen din da yake cikin dining area din na shiga tareda kinkimo manyan warmers da plates plates nazo ina jerawa, har na gama na fara serving dinsu ko kallon fuskokinsu banyiba, saboda nasan ko kalla nayi saqon harara ne zan samu, masalan daga 'yan matan gida buyu kyawawa da suke jin Kansu babu ya su a fadin Nigeria, shagwaba kawai suke zubawa, yayinda Hajiya kubra ke biye masu tanata murmusawa irin na manyan hajiyoyi da suka yarda kuma sukejin sunkai ko ina, labarinsu ya baza ko ina a fadin qasar tamu, abie ne ke latsa waya abunshi ta bangare daya yanada kyalkyala dariya, shi ko YaAmeen baima wajen, ahaka na gama serving nasu nayi masu sallama zanbar wajen, Ya shigo fuskar nan tashi murtuk kaman kullum yake takowa cike da izza da kamala kai kace dandan sarkin kano ne sanusi lamido🤪 "Suhan zo kiyi serving YaAmeen" dayake itama hajiyar haka take kiranshi dashi......"No am ok green tea kawai zansha" ya fada kaman bayason magana yayinda sauran qannen nashi duk suka natsu suna cin abincin su bayan sunce "bigboo u are welcome" "OK ki jira mu gama ki tattara wurin" ta fad'a tana mai faracin abinci, "to Hajiya na fad'a ina mai dan rissinawa irin na biyayya sannan na juya na wuce babbanb falo domin jiran su gama din tinani fal araina, " Saudat had'a man Lipton din" naji ya fad'a daidai lokacin da nake idasa ficewa daga dining area din. Sun shafe awa biyu kafin duk suka tashi tareda yima juna sallama hajiya ta haye sama inda abi ya shige sashenshi suma su nihal suka shige nasu sashen sai kuma Allah ya kaimu. Tattara plates din nayi nakai kitchen na juya zan koma dauko sauran, naga ya shigo da wasu bance komai ba saima dukar da kai danayi na jaye na bashi hanya ya wuce cikin kitchen din nima na fice dan dauko wasu, ahaka ya tayani kwashe kayan dukda hankalina bai kwantaba saidai nasan cewa hajiya na iya saukowa taganshi aiko da na kade har buzu na, bansan me yasanya shi aikata hakan ba yau lokutta dadama naga ko kallo ban isheshi in ka cire 'yan kwanakin nan da yake yawan bina da ido, shima na dauka hakan na da nasaba da tausaya wa duk wani mai aiki ne na gidan daidai da masu sharar lambu, nikau ta bangarenta baisan wata irin kacha bace yake sanya wa yana daure illahirin jiki da jijiyoyon jikina ba,ba bazai hantareni ba amman ko kallo ban isheshi ba, babu fuskan tambayan yasanya naja bakina na tsuke, na isa wajen sinc din ina dauraye abun da suka b'ata naji maganar shi a bayana don har ga Allah na dauka ya fita. Wannan tasanyani zabura na juyo mamaki fal a raina wanda har saida ta bayyana fuskana Wace irin mai sa'a ce yau ni?🤩 ni suhan ce yau YaAmeen ke cewa zaiyi magana dani? Tau wacece irin magana? Kodai wani laifin nayi mashi? Kodai bai hakura ba dazu dana tureshi? Ko dai........"Ko baakijii ba ne? Nace inaso muyi magana" ya fada hankali kwance da maganar nan tashi ta rowa da muryarshi mai kama da goge a cikin kunnen 'yanmata "Too yaya" na fada a ahankali cikin dardar tareda juyowa na fuskanceshi zuciyata kaman za tayo tsalle ta fito waje, saboda tsabar kad'uwa Guntun murmushi yayi iya lebo shi aganinshi nan ya k'okarta hakan sai tasanya kyaun shi ya k'ara fitowa afili kasancewar ba halinshi bane ko da murmushin amman ko baiyi ba kyaun shi na d'aya daga cikin abunda ke fizgar yanmata. Kallona yayi na tsawon second biyu, gamida gyara jinginar da yayi da cabinet ya motsa bakinshi ahankali kaman mai maganar saidawa ya fara da cewa......... ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:20 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~* *Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat) *Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat) *Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare. *Page* ~4~ °^^^^^^^^^^^^° "Ajinki nawa a makaranta?" Ya jefa man tambayar bazata. A d'an firgice na dago ina kallon shi, gami da ɗan zaro idanu na, da sau da dama na sha jin ana cewa kaman na mai jin barci amman suna da girma sosai,tambayar ce ta zo man a bazata, ko da alama ban taɓa kawo tinanin magana makamanciyar irin wannan zata iya shiga tsakaninmu ba; "na'am, ni?" Na Maida mashi da tambaya a ɗan firgice kuma cikin sigar mamaki, Shiru yayi na wani lokaci, kaman ma baya da alamar sake tanka mani, nikuma alokaci guda tambayoyi suka ziyarci kwanyata, har banma san mun shafe kusan minti biyu a haka ba, Yayinda shikuma ya kafeni da idanunshi masu kama da na wanda soyayya taci ta cinye😜 "Banjin akwai wani da nake magana dashi a kitchen dinnan da ya wuce ke; Ai ina tinanin mu biyune kadai a nan ko?" Ya faɗa a gajiye kaman, wanda akeyi ma dole, "Na gama makaranta. " Na fada a gajiye ciki-ciki ina mai gyara tsayuwata, Tare da janyo hijabi na, na rufe gefen fuska ta, saboda kallon da yake yi man yana distracting din attention dina; Jina nakeyi kaman a gaban miliyoyin mutane, kai gara ma ace a kotu nake, da sainafi sake wa, Da ace a gaban mutum nake kaman YaAmeen muna magana dashi one on one. 'Yar guntuwar dariya yayi, "Wow kina fadin har kinyi degree da masters, A hakan nan yanda kike yar mitsitsiya?" Ya fada yana mai nuna ni da duk kan hannun shi yana sama da ƙasa da su saitin Inda nake tsaye, Da wani yanayi, wanda nidai nakasa ganeshi; don bazance zaulaya ba don nasan ba halinshi bane yin hakan. Sai a lokacin nagane kuskuren danayi,dan zaro idanu nayi alamar wayyo Allah, Gami da Jan sauran hijab dina, na ruge fuska ta ruf, ina dan mai sakin ɗan k'aramin murmushi; A hankali nace, "am sorry secondary nake nufi yaya" "OK good " ya fada a gajarce, Yana mai ƙara nazarinta, ko buƙatar da yake da ita zata samu karb'uwa awajenta? "Ina so kici gaba da makaranta, domin zaman ki a haka kina wahala ba abune mai dad'i ba; ko babu komai ilimi yanada dadi, zaki taimaki kanki ki taimaki ummanki" Ya tsagaita yana mai zura mata idanu da ke taimakawa wajen ƙara ruɗa ta; Domin yaga yanda zatayi, Nikau bansan lokacin da nabude fuskata ba gabaki daya, ina mai sakin murmushi har siririyar wushiryar dake saman hakora na ta bayyana. "amman kije ki shawarci ummanki, kuma ina so maganar ta tsaya iyakar ni, da ke, da ita; Don bana so wani ya sani kaf gidan nan, idan ta yarda sai ki kawoman takaddunki, da kuma zabin makarantar dakikeso kiyi da abunda kikeson karantawa, kibar sauran maganar a hannuna. Kome zamu ji, ko zaku gani, Ku kauda idanunku gabaki daya, Babu ruwanku a ciki, Ni nace zan yi, kuma insha Allah zanyi;" Yana gama fadar haka ya juya, Yana mai barin tanqamemen kitchen din, da kai ka rantse da Allah ba'a Nigeria yake ba. Dakallo na bishi, a yayin da kwalwa ta ta cunkushe, "tabbas tabbas mafarkina zai tabbata, tabbas lokaci yayi; Alhmdllh naketa faɗa, a cikin raina, saboda na ma rasa tinanin da zanyi, bayan wannan; Juyawa nayi, gami da ci gaba da aiki na. A gaggauce na gama na rufe kitchen din, gami da barin part din baki daya zuwa namu, Amman zuciya ta cike da tarabbabi, domin nasan halin umma ta, Sannan ni na san kafin in dosheta da maganar, Sai nayi nazarin abunda zance mata tukunna, Don na san ta da gudun duniya da abunda ke cikinta balle wulaqanci irin na hajiya kubra. Ko da na isa part din namu, Na tadda umma ta, tasha magani amman takasa yin barci, saboda taga na dade har wajen karfe goma da wani abu, Alla Alla take yi, ya kasance lafiya, Gashi ko abinci na ma ban ciba, ina shiga kuwa na taddata zaune bisa sallaya. Allah sarki umma ta, Mace kamila mai gudun duniya, Mace mai ibada, da rashin hayaniya, Amman dukda wannan halin nata, hakan baisa Hajiya kubra ta ɗaga mata ba, Ni gani ma nakeyi kaman babu wad'anda ta tsana irin mu acikin masu aikin dake gidan, Wanda munfi mu goma sha wani abu, ummata ce ta katseman saqa da warwarar da nake tayi cikin zuciya; "lafiya dai ko mama na?" ta faɗa tana mai miƙewa a hanzarce, sannan ta ci gaba da magana cikin dan firgici kaɗan; "Naga dare yayi sosai, ya kamata ace yanzu kin kwanta ki huta hakanan" Ta faɗa cikin sanyinta, mai sanya ni natsuwa, duk da a ɗan firgice take; Kome nake yi, ko ban fad'a ba, son da ummata keman yafi wanda nakeyi mata, Duk da kau a duniya babu wadda tafi soyuwa a raina kamanta, Tinda ita kadai na sani, ita kadai na tashi na gani , ita ce uwata, itace ubana, ita ce yayata, abokiyar shawara ta kuma, ta fanni daya kuma abokiyar wasa ta; "Ina hankalinki yake ne ummina? Ina ta magana kinyi shiru" ta faɗa tana kamo hannuna, bansani ba ashe har ta nade abun sallar ta iso inda nake tsaye daga bakin ƙofa a tokare. "Umma saida najira suka gama sannan na wanke kayayyakin kinga gobe in Allah ya kaimu mun rage aikin;" na faɗa, ina mai kama mata hannu nima, muka zauna gefen katifar tamu dake yade a tsakiyar dakin. "ga abincin ki tau, maza kici ki kwanta, kinga karmu makara gobe dasafe in Allah ya kaimu banaso kullum muke b'atawa hajiya rai;" ta faɗa tana jawoman kwanon abincin. Kwanon silver ne amman tsaf yake, kaman sabo sai sheqi da walwali yake yi, kaman yau aka budeshi a leda, Allah sarki ummana akwai tsafta, dakin namu ma sai k'amshi yake yi, an goge tiles dinnan sai daukar ido yake yi, abunka ga fari, dakinmu tsaf yake babu tarkace da karikitai, in ka cire katifarmu, sai labulaye da wani teburi a gefe, inda muke ajiye daddumar sallah tamu, da sauran litattafan addini himili guda, kasancewar ummata tayi karatun addini mai zurfi, sai take k'araman duk bayan sallar subhi, akwai wardrop ta bango a dakin, wannan shi ya tak'aita mana tarkace, tinda ba yaro ke garemu ba, kwata kwata ma babu yaro a gidan, kowa da locar ta inda ni biyuma ke gare ni, kasancewar guda uku ce a dakin, amman ajere suke, sai ummata ta dauki daya, tabar man biyu saboda ni budurwa ce zan fita karikitai. Abincin naci, naje na daurayo bakina na cenza kaya zuwa kayan bacci, muka kwanta umma tayi mana addua muka shafa kowa ya juya cikeda tinani kala kala. Nikam ta bangare na banyi bacci ba, amman ummana tayi baccinta saboda maganin da tasha, kuma ko ba hakaba, ita bata kwanciya da damuwa ko haushin wani a ranta, takance ba'asan gawar fari ba hakanan kaje lahira da haushin wani duk abun da gaƙuri bai bayar ba ai rashin shi baya badawa. Gari na waye wa muka gama komai, kama daga salla, karatu, da wanka; zuwa karfe bakwai, kowa yayi shirin fara aiki kaman yanda yake a al'adar gidan namu. Amman mu bamu kai ga fita ba, sabo da ƴan cikin gidan ma basu kai ga tashi ba, kuma ina so in yima umma ta maganar karatu na; sai dai ina zullumin tunkararta da maganar, sabo da na san halin umma ta sarai, wani d'an qaramin yak'i ne gabana, Amman duk da haka hakanan zan daure in tunkareta da maganar domin ga dama ta samu, kuma ko ba komai hakan ci gaba mu ne ni da ita baki daya, fata na dai da addu'a ta Allah ya ɗora ni akan ta, ta yadda ta amince mani, sabo da wannan karon ina tsoron YaAmeen ya ji haushi ya janye burin taimakon mu a ranshi, saboda ba wannan ne karo na farko ba da umma ta ke daƙile shi akan duk wani burin taimaka mana da yake yi, Wanda shi a ranshi har ga Allah taimakon ummana din ne kan ingiza shi ga hakan saboda rashin hayaniyarta da biyayyar ta ga iyayen nashi. ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~* *Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat) *Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat) *Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare. *Page* ~5~ °^^^^^^^^^^^^° Bayan mun gama karyawa ne, muna zaune a ɗaki ni da umma ta,Tana yanke farcen ta na hannu, Yayin da ni kuma nake zaune gefen katifar tamu da littafin hisnul musleem a hannu ina karantawa. Rufe littafin nayi tare da maida shi ma'ajiyar shi, na dawo na zauna daf da ita, tsawon second biyar na dauka ban iya cewa ƙala ba, tabbas abinda nazo mata dashi ni kaina na san mai girma ne, to sai dai ba yadda na iya, shahada nayi na bude baki na a hankali nace; "Umma don Allah ina so muyi magana dake" cike da mamaki ta ɗago idanun ta tare da tsare ni da su, take guntun tunani yazo a ranta, wacce irin magana ce wannan da maman tata bazata iya tunkararta kai tsaye da ita ba? Koma dai menene tana fatan ɗiyar tata ba zata zo mata da wani abu akasin tunani nata ba; "ina jin ki mama na" ta bani amsa tana mai dakatawa daga yanke farcen gami da sauke hannun kan cinyoyinta. "Umma don Allah ki saurare ni kuna ki fahimce ni, wannan karon izinin ki nake nema; ki duba halin da mu ke ciki na rashin sanin madafa, dama ce ta zo mana da zamu fita daga cikin wannan ƙangin bautar da mu ke ciki, dama ce da zata sanya mu dogara da kanmu har ƙarshen rayuwarmu." Tinda na fara magana ta tsira man idanu ba tare da tace kanzil ba, sai dai ni bazan iya karantar abunda ke cikin zjciyar tata ba; Ganin yanda ta kafe ni da idanu ya sanya ni sauke kwayar idanu na ƙasa ina mai murza yatsu na suna bada sauti ƙas, ƙas. " Uhm, ina jinki mama na, wannan wacce irin dama ce? Ina fatan dai zaki zo mani da buƙatar da kika san zan iya amincewa da ita, ba wadda kika san za ta iya sanyawa ranki ya ɓaci ba" Tinda ta fara magana bugun zuciya ta ya ƙaru, fargaba da zullumin yadda zata ɗauki maganar suka baibaye ni, dakyal na bude baki na cigaba da cewa; "Umma jiya ne Ya Ameen yace ya kamata in koma makaranta domin yana so mu zama masu tallafar rayuwarmu da kanmu, kuma yace in nemi izinin ki na bashi takaddu, da kuma zaɓin makarantar da nake so, tin jiya nake zullumin tunkarar ki da maganar, domin ban san yanda zaki kalli abun ba, wallahi umma ba nice nayi mashi magana ba, shine da kan shi ya same ni kitchen ina wanke wanke ya man maganar; Idan dai ba idanu na bane suke man ƙarya ba, wannan. Karon kallon da ummar tawa take man ya cenza salo, ya rikiɗa ya koma kallo ne mai cike da gargaɗi da kuma tuhuma; kafin ta bude baki ta cigaba da Cewa "Masu gadi ma da drebobi ban hanaki magana dasu ba? Balle Al'Ameen ɗanɗan masu gida? Miyasa kike son cenza hali ne Hauwa'u" A firgice na ɗago ina mai kallon ta cikin tsananin firgici damuwa fal a raina, yau ni ce umma ta ta ke kiran sunana kai tsaye; me ya sanya ni? Me ya kai ni? Me ya ja mani? "tsabar son zuciya da hangen gaba" zuciya ta ta bani amsa, tini kwalla suka soma shatata daga idanu na, wanda tini kalar su ta juye daga farare tas zuwa jajaye; Hannun ta na kamo gami da runtse su sosai sannan naci gaba da magana ba tare da damuwa da goge kwallar ba, gara na barta ta zuba ko zanji saukin raɗaɗin da zuciya ta keyi mani, "Don Allah umma kiyi haƙuri, wallahi tallahi bani na mashi magana ba, iskeni yayi har kitchen, kuma daga ni sai shi muka yi maganar, umma kiyi haƙuri in na bata maki rai insha Allah bazan sake ba" Na Faɗa wani tuƙuƙi na taso man daga cen ƙasan rai na, "Ni baki ɓata man rai ba Mama na, gani nayi kawai kaman baki gudun wulaƙanci daga wurin hajiya Babba ne, sanin kanki ne da ta ita ne ma da yanzu mun bar gidan, sabo da Alhaji ne kawai muke zaune har yanzu, tau minene yasa ba zamu kiyaye ba? Tabbas kinsan idan hajiya taji zaman mu a gidan nan ya ƙare kenan, zata ce ne mun mallake mata yaro gashi har yana wahala akan mu, kinsan kuwa ni bani son abunda zai haɗa ni da su dukkan su balle rayuwa ta ta ɓaci hakanan" Kuka na naci gaba da yi duk da na ji ta kai aya, Amman zuciya ta na kwadaito man samu ne gashi umma ta na lasa man ɗanɗanon rashi a baki, ban gama maganar zucin da nake ba naji ta cigaba da cewa "idan ya sake maki maganar kice mashi na hana ki, kuma nace mun gode da halacci da irin ƙoƙarin da yake yi a kanmu Allah ya ƙaro buɗi da arziƙi" Tana gama faɗar haka ta zare hannun ta ta fice a ɗakin, ita kanta cen ƙasan zuciyar tata bata yi mata ɗaɗi, kukan da suhan ɗin ke yi mata yana taɓa mata rai, sai dai babu yanda ta iya wulaƙanci abu ne da kowa ya kamata ace ya guda ba ma ita kaɗai ba, suhan ɗin yarinya ce dududu bata wuce shekara ishirin ba, bata fata wani abu ya shiga tsakanin ta da Al'Ameen, a matsayin ta na babba ta san abu ne mai sauƙi, domin daga tausayi komai ke chanza wa, dukda ta san Al'Ameen ɗin ya fi ƙarfin ɗiyar tata, sai dai ita ba zata so hakan yayi sanadiyyar ɗan zaman da suke yi a gidan ya zo ya gagare su ba. Ni kau tinda umma ta fice ta bar ni a gurin zaune, fashe wa na kuma yi da kuka tare da faɗawa na kwanta kan katifar tare da kifa kai na, na saki wani irin kuka mai tsuma rai, maraici bai yi ba, mahaifi daban ne a rayuwa, yanzu da yana da rai ko kusa bazan fuskanci irin wannan rayuwar ba, tabbas ummata akan gaskiyar ta take, Hajiya babba muguwar mace ce, yanzu zata sanya a ɓatar da kai a doron ƙasa indai ka nemi shiga gonar ta. Dukda yace shi kadai zai yi hidima ba tare da ta sani ba, wannan tunani shi ne, Hajiya mace ce mai cikakke iko, komai akeyi a gidan a tafin hannun ta yake, akwai 'yan gulma masu kai mata rahoton duk abin da yake faruwa a gidan; Ko ba haka ba ma ni mai ya shiga kaina? Mu da muke a ɗosane, sauran ma'aikatan gidan ma duk sun fimu galihu, me yasa nake hangen gaba ne? ALLAH ne kaɗai yasan yanda zai yi da mu, mu bar mashi komai, karatu na ba dole bane, ni cikakkiyar marainiya ce da ban ma san ya kalar mahaifi na take ba, ban taso na ganshi ba, ban taso naji umma ta na maganar shi ba, kuma bata so ina mata maganar shi, shin mai zai sa in ci gaba da damun kaina? A hankali na rage sautin kukan nawa, gami da goge hawayen, lokacin da idanu na suka kai kan agogo dake maƙale a bangon ɗakin namu, 09:30am, a hanzarce na tashi na shiga bayin dakin namu na wanke fuska ta, ban damu da in shafa ma fuskan komai ba, wa zan ma kwalliya? Rai na a cunkushe yake; Ƙofar ɗakin namu na fito na tadda umma ta tana tattara sharar tsakar gidan da su sauran ma'aikatan dama basa yi sai ita ko ni, sun ma bar mana mu kadai, a cewarsu ai dama aikinmu ne mu share tsakar gidan tinda ni ke sharar cikin gida, hakan ma baya damunmu in da sabo mun saba. Wata daga cikin amintattun Hajiyar ce ta zo wucewa zata shiga ɗakin nasu da ke kallon namu, watsa mana wani irin kallo tayi gami da cewa, "maman Suhana sannu da aiki, Hajiya babba tana neman ku, ya kamata ku tafi domin sun tashi tun ɗazu" "To uwani, mun gode,an tashi lafiya ko?" umma ta ta maida mata cikin sakin fuska, domin duk kwakwarka ba zaka iya karanto ɓacin rai a fuskan umma ta ba, ko da kayi don ka ɓata mata rai tana tura maka aniyarka ne a wuce wurin; taɓe baki tayi gami da cewa "lafiya" ta shige ɗaki abun ta, muna iya jiyo tashin sauti tsokin ta a hankali. Juyowa Ummata tayi ta kalle ni cikin sanyi ta tace "Mama na wuce kije gani nan zuwa, sai dai kada ki manta da maganar mu kinji ko?" "To umma" nace gami da juyawa na shiga ɗakin ɗauko hijab ɗina. ******************************* Yau dai haka na wuni yin aiki sukuku,duk wata hanya da zata haɗa ni da Ya Ameen na toshe ta, ina gama aiki na na koma sashen mu na kwanta yayin da umma ke can tana aikin abincin ranan su, bata bari in taya ta, sabo da Hajiya magana take yi, cewa take kowa yayi aiki shi, ƙarar ƴar mitsitsiyar waya ta rakani toilet ce ta katse man tunanin da nake ina ta juye juye bisa katifar tamu; Massage ne ya shigo man aunty saudat naso in raka ta shopping, wannan ne ya sanya na miƙe gami da shiryawa domin dama na saba dukan su biyun nice ke raka su, duk lokacin da muka dawo suna kwashe tsofaffin kayan nasu su bani kasancewar su basu da jiki ni kuma ina da ƴar murjewar jiki, dukda sun girmeni sai size din namu yazo daya, haka kuwa aka yi muna dawowa ta tattara tsofaffin abubuwa da bata so ta bani wanda ni a waje na kaman sababbi suke. ******************************* A haka sai da na shafe kwana uku ina wasan ɓuya da Ya Ameen, sabo da bana so magana ta ƙara shiga tsakani na dashi balle ya tado da maganar karatun nawa, ni a ganina in yaji shiru yasan umma bata barni bane kawai, Daman abunda na sani shine halin yaya Al'Ameen, ba zai man magana ba indai ba nice nayi mashi ba, wannan tasa na saki jiki na ci gaba da ayyuka na yanda ya kamata, na cire ma raina komai da tsammanin zanyi wani karatu a rayuwa ta, na sani dama sau daya take zuwa a rayuwa, ni tawa damar ta zo kuma nayi sake da ita shikenan kawai duk yanda Allah ya so yayi dai-dai ne. Tafe yake cikin salon tafiyar shi ta ingarman namiji, dan ƙwalisa, ga natsuwa, kamala cike da kwarjini; tabbas Al'Ameen ya kai namijin da za'a kalla a sake kallon shi, fuskar shi cike take da annuri dukda kasancewar shi ba ma'abocin murmushi ba, hakan bai hana tsantsar kyawonshi fitowa ba. Fari ne tas yana da tsawo daidai misali jikin shi ya dace da murzazzar fatar shi da take cike da gargasa kwance luf kai ka rantse bata taba shan zafin rana ba, yana da dogon hanci sosai domin ya dauko kyaun mahaifin shi da mahaifiyarshi duk a cikin su shiddan ya kere su a kyau da haske dukda suma suna da nasu kyaun, bakin nan nashi kuwa kaman gidan tsutsa gashi kalar maroon mai haske, kai kace jambaki ya shafa sannan ya goge, sam baya da girma sai dai sajen da ke gewaye da fuskar ya ƙara ƙawata fuskar, sam baya da sanƙo wannan ne yasa gyaran fuskar ya fitar da ainahin kyawon fuskar dimpul din shi na dashe das a gefen fuskar shi na hagu wanda tasa ko bai motsa fuskan ba kana iya hango kwarin shi kwance a kan fuskar shi, Ya Ameen ba dai miskilanci ba. Sanye yake da farar riga T-shirt ta polo da farin wando na lallausan jins ɗan kamfani gucci watau kayan botique, ƙafar shi Sanye da farin takalmi samfurin adidas, ni kaina mai Rubutun takalmin ya tafi da imani na, hannun shi riƙe da wayar shi samfurin Apple Phone, tare da sun glass ɗinshi sai makkulin motar shi ƙirar Benz, yana ɗan kaɗa shi a hankali. Waya yake amsawa cike da natsuwa yake taka wa a hankali, kai da ganin shi kai kasan ba RAGGON NAMIJI bane. (littafin Maman mamy) Falon ya shiga da sallama ɗauke a bakin shi Amman in ba kai da kake kusa dashi ba ba zaka san yayi magana ba, kai tsaye wajen da hajiya kubra take hakimce ya dosa, a hankali yake taka wa sai dai cikin zafin nama, irin na cikakke namiji, katse wayar yayi daidai lokacin da ya isa daf da inda take zaune saman sofa. "MOM" Ya faɗa daidai lokacin da yake zama kusa da ita, "Good morning Son" ta faɗa cikin murmushi mai nuna isa a duk lokacin da tayi shi, sam ba zata iya ɓoye son da take yi ma yaron nata ba, "Morning Mom, How Was Your Night" ya faɗa yana mai ɗan zamewa ya kishingiɗa a saman sofar, "Great dear, Hop there is nothing wrong?" ta maida mashi da tambaya. "Nothing Mom But i want to enrout to china today" ya faɗa da ƴar damuwa a fuskar shi, "Wat? Hop dai lafiya son" "Lafiya Ƙalau Mom, kayan da nayi order ne an samu matsala ne wajen shipping nasu so i need to go there, domin in san matsalar da aka fuskanta sabo da kaya ne na manyan kudi, gashi costomers sai magana suke yi sun ƙagara a basu kaya" "Well Allah ya kiyaye hanya, fatan dae kayi report wajen aiki?" ta faɗa tana dafa kan shi kaman ƙaramin yaro; "Yes Mom ba wani matsala bari naje sai munyi waya, yanzu muka gama magana da Dad ma shima yana hanya Amman ba zamu hadu ba sai dai na dawo, ban san tsawon lokacin da zan dauka ba acen" ya faɗa a gaggauce yana mai miƙewa gami da gyara zaman rigar shi a jikin shi, bai jira cewarta ba ya fice daga falon, yayin da ita kuma take bin shi da kallon ƙauna irin na uwa ga ɗanɗa mafi soyuwa a rayuwar ta, tana mashi addu'a da fatan nasara domin dai ita idan akwai abunda ta tsana a rayuwar ta tau bai fi ganin ɓacin ran Al'Ameen din ba. ***** A bakin dry centre na gidan muka haɗu ina shanya cottons na goge goge, aikina nake don ni har ga Allah ma ban kula da tahowar shi ba, tinani na ya tafi ga tinanin da ya zame man abun ci, abun sha, a kullum watau tinanin mahaifi na. Ƙamshin turarenshi ne ya man sallama, yayin da idanunu na suka gaza juyawa su kalleshi, gaba daya naji an zare man lakkar dake jikina, jinin jikina ya katse ya ci gaba da gudu cikin jiniyoyin jikina, domin dai in ban manta ba kwana uku kenan rabon da in sanya shi a idanu na, ni na ma dauka ko baya ƙasar ne kwata kwata ma; Tinani na ne ya katse daidai lokacin da ya matso daf da inda nake tsaye "Hey what are u doing here?" Haka naji kunnena ya faɗa man, ɗan rusunawa nayi a hankali nace "Ya Ameen ina kwana?" "Lafiya" ya bani amsa a taƙaice cikin salon maganar shi da ke ƙara mashi kwarjini a idona, "ya maganar mu ne ta rannan banji kince komai ba" ya faɗa yana mai tsare ni da idanun shi masu ƙara ruɗa ni, ɗan kauda fuska ta nayi, sabo da bana so mu haɗa ido dashi. "umma ta ta hana ni tace kuma nayi maka godiya ga irin ƙoƙarin da kake yi a kanmu Allah ya saka da alkhairi" na faɗa ina mai sadda kai ƙasa domin nima na san abun ba zai yi mashi daɗi ba; "its ok" Ya faɗa yana mai wucewa ba tare da ya tsaya ƙara jin wani abu da zai fito daga bakina ba, Ni din ma banyi niyyar ƙara tankawa ba, sabo da na san bani da kuma abun cewa. Kwalla ce ta taru a idanuna, nayi saurin goge ta ina mai fiƙi fiƙi da idanu,amman wata ke ƙara zubowa, shikenan na rasa dama ta, na rasa buri na, umma tafi so muyi ta zama cikin wannan ƙangin na bauta, Mu fa ba bayi bane da aka siyo a kasuwa, muma mutane ne kaman kowa, Ya Ameen yayi iya ƙoƙarinshi akan mu, sai dai duk yanda naso in karanci halin da zuciyar shi ke ciki akan fuskar shi, bai bani damar hakan ba, kallo na na maida ta saitin da yabi ya wuce, ko burbushin shi ban hango ba, sai dai Ƙamshin turarenshi irin na maza da suka amsa sunansu ya bar mani, "Nagode ya Ameen ko a haka ka bar mu mun san kaso taimaka mana na faɗa a fili ina mai durƙushewa, gami da sakin wani maraya kuka. Ba mu ba kawai, duk wani mai aiki dake cikin gidan yana ƙoƙarin taimaka mana, sam baya so duk wani dake ƙarƙashin shi yayi kukan baya kyautata mashi, Tabbas da duka masu arziki na duniya irin halin shi garesu da abubuwa sunyi ma mabuƙata sauƙi a rayuwa, duk da cewa halin mahaifin shi ya dauko, sai nake ganin ya ma fi mahaifin nashi kula da al'amurran mu a cikin gidan *Dukka buri na ya wargaje* *Mafarki na ya tafi* *Allah kai ne gata na* *Ka duba lamurra na* ****************************** ~Oum-deedat ce~ [8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~* *Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat) *Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat) *Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare. *Fage ~6~* °^^^^^^^^^^^^^° Tsawon kwana uku na shafe ban sake jin ɗuriyar Ya Ameen ba, hidimomi na nake yi hankali kwance. Yau gidan mun tashi da hidimomin aikin abinci, Alhaji Mustapha ne zai yi baƙi, abokan kasuwancin shi daga waje ne zasu zo. Abinci kala goma Hajiya Babba ta bamu umarnin muyi, mu duka ma'aikatan an rarraba ma kowa nashi aikin, masu gyara gida na yi, masu gogewa nayi, mu da mu ke aikin abincin mun hallara mu duka a babban kitchen ɗin gidan. Wannan karon harda su Aunty Saudat da Aunty Nihal ne a kitchen ɗin, sai dai banga amfanin su ba, yo eh mana basu da amfani domin kowaccen su kujera ta ja ta zauna suna latse latsen su,sai dai su bada command ɗin yanda zamuyi, wanda a zahiri ma mun fisu iyawa, salon iya yi ne kawai. Haka muka kammala abincinciccikan duk mun jigata; wannan ce tasa bayan mun gama jejjera abincicikan bisa tangamemen dining table ɗin da yake gefe guda a cikin falon sashen baƙin, na wuce sashen mu domin yin wanka da gyara jikina. Zuwan su yayi daidai da gama shiryawa ta, kiran Hajiya Kubra ne ya shigo waya ta, tare da bani umarnin zuwa sashen na baƙin domin taya su zuba abincin. A falon muka haɗu da Alhaji Mustapha ɗin da na kwashe watanni ban sanya shi a idanuna ba domin baya yawan zama; Durƙusawa nayi har ƙasa na gaida shi, yayin da ya amsa man cikin fara'a da sakin fuska, tare da tambayar umma na ko muna cikin ƙoshin lafiya. A ɗarare nake zuba masu abincin domin harda Hajiya Kubra zaune a wajen saboda baƙi ne abokan hulɗarsu na kasuwanci kuma ita ma tanada share a ciki, wannan ce tasa nake yi a hankali domin kada inyi laifi wajen Hajiyan. Gama zuba masu abincin yayi daidai da wanzuwar daɗaɗɗen ƙamshi, lokaci guda mamallakin ƙamshin ya bayyana fuskar shi ɗauke da maɗaukakin murmushin da ban taɓa ganin yayi irin shi ba; Sanye yake da lallausan farin tissue yard har kana iya hangen fara ƙal ɗin singlet dake jikin shi, kanshi babu hula hakan ya bayyana kwantaccen sumarshi luf da ita bisa kanshi har sheƙi take yi, hakan ya ba gyaran fuskar shi damar ƙawata fuskar shi da take ɗauke da madaidaici saje, ƙafar shi na Sanye cikin wani cover ɗin takalmi ɗan ƙasar italy sai sheƙi da walwali yake yi. Cikin hanzari yake takowa cike da kwarjinin shi, lokaci guda yana fadin "am so sorry wallahi na samu tsaikon jirgi ne" ya faɗa daidai lokacin da ya isa gare su yana mai jan daya daga cikin kujerun ya zauna. Da hannu Hajiya tayi man nuni da in serving ɗinshi, aiko ba ɓata lokaci na duƙa daidai saitin inda zai iya jin me make faɗa, saboda bana so in damesu saboda har wasu sun fara cin abincin; "Me za'a zuba maka Yaya?" Na faɗa ba tare da na bari mun haɗa idanu ba, "fried chicken with mixed fruit" ya faɗa shima yana kauda kai gefe cikin salon shi na miskilanci wanda ni na kula ma kwata-kwata shi haka halinshi yake; Ban ƙasa a guiwa ba kuwa nayi maza na zuba mashi, nuni yayi mani da ido da na bar wajen daidai lokacin da nake miƙa plate ɗin gaba shi, na daga ƙafa cikin sauri na bar falon domin wasu daga cikin baƙin sun fara tsare ni da idanu, ina tunanin shima abunda ya kula dashi kenan. ******************************* Bansan ya suka ƙare da baƙi ba, domin ni na fita batun su tinda dai na gama masu abin da zan masu, hutu aka bamu cikin gidan na kwana biyu domin family ɗin zasu yi wata tafiya da mu kanmu yan cikin gidan bamu san ina zasu ba, saƙon Alhaji Mustapha ne ya iso mana, dama duk in zasu yi tafiya koda ta yini ɗaya ce ya kan mamu alkhairi irin nashi da ya saba. Kudi ne masu yawa ya bayar a rarraba mana koda zamu buƙaci wani abu baya nan. "Allah sarki, Allah ya saka ma Alhaji da alkhairi ya ƙara buɗi na Alkhairi" umma ta ta faɗa lokacin da saƙon namu ya iso gare mu, su kau sauran ma'aikatan ƙananan maganganu suka hau yi, wai sun fi so Ya Ameen ya basu kyauta saboda shi bai Iya kyauta ba da yawa yake bayarwa. Kaji butulci irin na ɗan adam, mu dai bamu damu ba ai ance ma raina kaɗan ɓarawo ne, kuma ko ba haka ba umma ta tana da wadatar zuci abu kaɗan ke isar ta a rayuwa hakan ce tasa nima na tashi da irin wannan tarbiyyar. ******************************* Sun shafe kwana biyar babu su a cikin gidan hakan ce tasa muka samu sauƙin tsangwama da walwala acikin gidan, dama ba mu ke aikin abincin ma'aikata ba iyaka ayi mukai kwano in mun gama ci mu dauraye, iyakarmu gyaran dakinmu sai ko umma ta da take share tsakar gida, domin ita bata son ƙazanta Sam bata iya zama cikin ta, yayin da su kau sauran basu damu ba kitchen ɗin girki kawai suke share wa. Wani lokaci nakan shiga lambun gidan insha iska ko in katso gwaba ko Apple in ci idan nayi marmarin hakan, umma ta bata hanani domin ta san ko babu komai ba kullum muke samun irin wannan damar ba, hanani sake wa da sauran ma'aikatan kawai ta hanani shima mafi yawancin mazan ne, nima ban damu ba saboda da irin wannan tarbiyyar na taso ta rashin sake wa da maza. Shugabar ma'aikata mata ce ta leqo ɗakin namu, lokacin ina toilet wankan ƙa'ida na idan na tashi baccin rana ƙarfe uku wanda sake wa yanzu ya zame man kaman nafila cikin ƴan kwanakin nan da sukayi basa nan. " Maman Suhana Hajiya ce tayo waya, tace a faɗa maku ku gyara masu sashen su duka, Suhana ta gyara na Alhaji ƙarami da na Abie domin dukkan su gobe suna hanya idan Allah ya kai mu" Dam!! Naji gaba na ya ruguje ya faɗi, daidai lokacin da na fito ina goge kai da towel ɗina na wanka, shi kenan zasu dawo, shi kenan walwala zata ragu, Abunda zuciya ta ke ƙissima man. "To Talatu, insha Allah yanzu zamuje mu gyara, Amman gyaran zai kai goben tun da kinga yanzu marece ya riga ya kawo jiki" Ummata ta faɗa tana mai kallon Talatun, Talatun ta amsa mata da cewa "To shi kenan Maman Suhana ai ba damuwa gaskiya aikin da yawa, ku fara ɗin zuwa da safen kwa idasa" ta faɗa tana mai ficewa a ɗakin, da kallo na bita, matar kam kaman ta Allah to sai dai fa fuska biyu gareta, domin ita ce ta gaban goshin Hajiya babba a gidan Amman bata bari a sani,; nima na san hakan ne ta dalilin a cikin gidan nake nawa aikin kuma harda ɗakin Hajiyar nice ke gyarawa. Haka kau aka yi tuƙuru muka hau gyaran cikin gidan, ko ina yayi ƙal, ya rage gyaran ɗakin Abie ne da ya Al'Ameen ya rage, shima idan aka yi Magriba zanje na gyara na Abie, na Ya Ameen ne sai goben Saboda na san halin wannan sarkin ƴan tsaftan, tsaf zan gyara Amman yana zuwa zai ce baiyi ba. :::::::::: Washe gari tin da duƙu-duƙu na tashi gami da shiryawa na leƙa ɗakin Shugabar ma'aikata na amso makulli, an ma ci sa'a domin bai barin makullin ɗakin shi a hannun kowa wannan sarkin ƴan tsarin. Yanda yake na daban, haka ma part din nashi yake, komai dake shashen daban yake da sauran abunda ke cikin gidan, ba wasu tarkace amman an narka dukiya wajen;saitin kujeru ne a falon farare ƙal masu kwalliyar golden haka jefi jefi a jikin su, golden tiles ne malale a falon da ya ƙawatu da wani makeken chinese carpet da ya lashe fin rabin falon bayan su babu komai sai center table na zallan glass fari tar dashi mai haɗe da tumtum irin na gidan sarauta guda biyu tsakiyar falon, akwai stools suma kwara biyu tsakanin kujerun, sai saitin kayan kallo ƴan kamfani Samsung haɗe da Italian Tv stand, up White ne fentin falon yayin da ya dace da cottons masu matuƙar kauri suma kalar golden, sai na'urar sanyaya ɗaki da water dispenser dake maƙale a saƙo guda na falon. Kai kanka in ka kalla sai ka sake kallo, iya tafiya da imani falon ya tafi da nawa. Corridor ne gefe guda daga bangon hagu da ke falon, idan ka bishi shi zai sadaka da ɗaki ɗaya tal acikin shashen da yake mamallakin shashen, sai ƙofar ɗan ƙaramin kitchen da yake ta cen ƙuryar Corridor ɗin da yake ɗauke da madaidaicin dining area a ciki, kitchen din ya tsaru kaman na wata macen komai na aikin gida akwai shi ciki, sabo da Ya Ameen ya iya girki, in ƴan miskilancin nashi suka taso shi ke girkawa da kanshi yaci abun shi ko kuma in yayi baƙin shi yakan dafa masu abinci simple kuma ya wanke dishes ɗin da kanshi. Yanda falon ya tsaru sai naga ma kaman bedroom ɗin yafi ƙayatuwa, shima komai upwhite ne da kwalliyar golden, saɓanin toilet ɗin da yake kalar sararin samaniya da fitilu farare, sai ya zamana abun burgewa da ban sha'awa. Zagewa nayi na gyara ko ina na ƙalƙale, shi tas na kunna boner ta ruwan ƙamshi, take part ɗin ya ɗauki ƙamshi mai sanyaya rai, sannan na kunna na'urar sanya ɗaki domin ƙamshin ya kama ko'ina,bayan na gama na kashe komai na janyo part din na kulle gami da mayar ma da Mama Talatu makullin. ******************************* Ƙarfe biyar sakaliyya suka iso gidan, yayin da dukka mu ma'aikata muka fita taro su da yi masu barka da zuwa, harda umma ta baiwar Allah da take sanye cikin zurmemen hijab ɗinta, wanda bata ma lafiya kwance take zazzaɓi ne rau a jikin ta, Amman hakan bai hana ta fitowa ba, tinda haka aka saba kafin su shiga part ɗin nasu sai an gaggaisa da kowa tare da jin lafiyar kowa, wannan doka ce daga Alhaji mustaphan wanda a haka dole suke tsayawa suna zuzzunɓura baki suna aika mana da harara su sun dawo a gajiye amman baza'a bar su su shiga ciki su huta ba. Hakan baya damun Alhajin domin ya saba da halinsu tsaf halin mahaifiyarsu ne hakan ta saba masu dashi, halinta ne tin kafin ya aure ta kyamar talaka, masu aiki, sai dai yana tausaya masu har faɗa yana masu a lokutta da dama yakan ce "ku shiga taitayinku kuma ku natsu kusan inda yake maku ciwo, faɗi baya dauwama, haka ma wuya, kuma aure zakuyi ba kuma kusan gidan wanda zakuje ba" Hajiyar kan amshe da cewa "a'a alhaji ka rinƙa faɗar alkhairi a bakinka fa, yaran nan fa kai ka haife su" Wannan karon da Afan mutuniyata aka dawo, sai aunty Feena da yaran ta guda biyu ɗan shekara shidda mai suna Ayan sai ƴar karama da ba zata fi shekara biyu ba Nasreem. Aiko tana hangoni tayo kaina da ɗan gudun ta, maimakon in ce mata oyoyo sai itace ta rigani cewa "oyoyo aunty suhan sai kuma gaki" ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya gami da daka tsalle ta rungume ni sai kace wata 'yar yarinya, Afnan ba zata kai tsara ta ba, ko ba komai zan iya bata shekara uku haka, riƙe take da hannun Ayan, hakan ce tasa nima murmusawa gami da tsugunna wa bayan na bamɓare ta a jikina; tsugunna wa nayi na cicciɓi Ayan din ina cewa a hankali "aini fushi nake yi da ke, ko waya Afnan kinma manta dani kwata-kwata, sweet Ayan ne kaɗai nawa ni, shi da nasreem. Ƙyalƙyalewa tayi da dariya," Allah Aunty suhan ba haka bane, karatu ne yayi zafi Amman Allah Allah nake lokacin zuwan mu hutu yayi inzo inga ya kika koma, na san kina nan kin ƙara kyau abunki". Murmushi nayi ina cewa nima nayi missing ɗinki Autan Hajiya, ya kamata kuje ki huta hakanan". Ashe bamu sani ba duk hankalin su ya dawo kaina Alhaji da Aunty Feena sai murmusawa suke yi, ita aunty Feena ɗaukar da nayi ma Ayan ce ta burge ta kunsan mai ɗa wawa, yayin da su kuma su Aunty Nihal haushi ya cika masu rai, Afnan ɗin na basu haushi, tana zubda masu daraja, wai ace House maid ce take yi ma haka?, dubeta ita kuma dalla har da wani daukar Ayan salon ne ta shafa mashi datti. Tsoki suka yi cikin rai, su kuma sauran ma'aikatan haushi ne ya cika masu rai na fifita ni da Afnan ɗin keyi akan su,basu yi la'akari da cewar su sun girma ba sun manyanta. Gogan naku na gefe jingine da motar shi, ya harɗe ƙafafu yana ta kallon su, bai ko murmusa ba Amman dai sun burge shi cikin ranshi, shi yasa yake masifar son Afnan ɗin ita ce ƴar gaban goshinshi, saboda ko kusa ba halinta daya da sauran yayyen nata ba. Mu kuwa hankalin mu ma bai kai kanshi ba da yake gefe yana ta zuba mulki da miskilancin har aka gama gaggaisawa muka juya zuwa shashen mu su kuma suka nufi cikin babban apartment ɗin nasu, har sun kai babbar ƙofar da zata sada su da cikin gidan, Afnan ɗin ta juyo gami da kwalla man kira, "Aunty suhan.!, in na gama hutawa ina nan shigowa ki ajiye man abun daɗin nan" ta faɗa cikin ɗaga murya gami da yin ɗan tsalle ta kashe man ido daya, bata jira cewa ta ba ta shige cikin gidan riƙe da hannun Ayan yaro ɗan gayu ɗan hutu gashi mulmul dashi, hakan ce ta sanya kallo ɗaya yaron ya shigar man a rai tin Wancen zuwan da sukayi, tin kafin ma ayi mashi ƙanwa ne; murmushi nima nayi gami da ƙada kaina "hooo Afnan ba dai rigima ba" na faɗa a fili ina shige wa shashen namu, ko ba komai zan ɗan samu sassauci zuwan Afnan ɗin domin tana ɗebe man kewa, tin umma na hanani har ta haƙura ta barni domin ta kula cewa halin Afnan ɗin ya banbanta da sauran ƴan uwan nata. ********** "huh...." ajiyar zuciya yayi tare da guntsar iska ya fesar, a hankali ya fara taka wa gami da nufar nashi apartment ɗin domin ya gaji over, makullin dake hannun shi yayi using ya buɗe sashe nashi; Turus ya ja ya tsaya, wani sas-sanyan ƙamshi ne ya bugi dogon hancin shi, lokaci guda ya maida kallon shi bisa kowanne lungu da saƙo na falon, kaman dai an cenza komai?, Amman inaaaa..... Su ɗin dai ne, hmmmm? 🤔 Wanene yayi wannan aikin? Ta bayar kanshi yake Amman ya kasa lalubo amsa. Jiki a sanyaye ya nufi Corridor ɗin da zai sada shi da bedroom ɗin nashi, still dai nan ma haka, aah! Mamaki bai gama cika shi ba sai da ya murɗa handle ɗin ɗakin ya shiga.; gadon shi an lailaye shi da zanin gado mai kyau da yayi order daga dubai bai iso ba sai da baya nan, hakan ce ta sanya Talatu buɗe ɗakin ta ajiye a cikin wardroop, ni kuma da nazo gyara na gani na yaye na sama duk da baiyi dauɗa ba na shimfiɗa na saka Wancen cikin laundry basket. A hankali ya taka kaman mai tsoron ɗakin, gami da isa bakin gadon ya zauna a hankali. Taushi da sulbin zanin gadon gami da ƙamshin da suke tashi daga saman gadon ne suka sanya shi sulale wa ya kwanta bisa gadon sosai yana mai kallon POP din dake saman ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke a jere har sau uku gani da furta "Suhan" a hankali domin kuwa ya san wannan aikin ba na kowa bane sai ita....... ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:22 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI ƘARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven, No pain, so Magical Our creative golden pen, Be hold our words, A production of our pen, savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~* *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Gaisuwa ga ƴan golden pen, expecially ~Yaya Umar Dalhat Funtua~ muna godiya da ƙoƙarin editing, na baka kyautar wannan Page ɗin, kayi yadda kake so dashi. Allah ya ƙara haɗa kawunamu ameen* *Page ~7~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Haka kau aka yi, ina gama sallar magariba sai ga afnan saɓe da Nasreem a kafaɗa, riƙe da hannun Ayan tana jan shi a hankali, sallama tayi fuskar ta cike da annuri da fara'a ta shigo, yayin da ta ajiye Nasreem bisa katifar tamu, ta janyo Ayan shima ta zaunar dashi, wutsil yaro ya haye kan cinya ta da nake zaune bisa dadduma. "ku ji mu da yaro dan Allah, sai san jiki kaman mage" Afnan ɗin ta faɗa tana mai kama baki alamar mamaki, murmushi baiyane a saman kyakkyawar fuskar ta, lokaci ɗaya ta maida duban ta wajen umma ta da take zaune itama bisa tata daddumar domin bata tashi idan ta gama sallar magriba har sai ta kammala isha'i; "umma ina yini ya kwana biyu ya jiki-jiki, dan ko ba'a faɗa ba naga kaman baki lafiya" ta faɗa cike da girmamawa, Afnan yarinya ce mai cike da natsuwa, biyayya da girmama na gaba da ita ko da kuwa ta fishi da komai, shi yasa rayuwar ta da ta Ya Ameen ta kusan zuwa daya bambancin kawai shi akwai ɗan miskilanci a al'amuran shi in ya so, saɓanin ita mai walwala ce da zaulaya in taso, ta ɓangare daya kuma ga sangarta idan taso gami da shagwaba sabo da ita ce auta, tana da wani hali guda ɗaya da yake burge Alhaji mustapha, hakan ce tasa idan tazo mashi da buƙata ba dai ya Musa mata ba, yakanyi duba na tsanaki ga buƙatar tata, halin kuwa shine *manyance* watau tana da tinani irin na manya, lokutta da dama Alhajin kan zauna yayi magana da ita ta tsanaki idan ya je cen ko kuma idan ita tazo nan. "lafiya ƙalau Afnan, kun iso lafiya ko,? Ya gajiyar tafiya? Kunsha hanya, maimakon ki zauna ki huta Alabasshi idan mai duka ya kai mu kin shigo ku sake gaisa wa, shine kika kwaso yara kuka taho, kika rabo su da umminsu kika zo nan dasu kina kwasar masu sanyin nan" umman ta wa ta ƙarashe tana mai duban afnan ɗin tare da miƙa ma Nasreem ɗin hannu alamar ta taho, ai kuwa ba musu yarinyar ta muƙe cikin salon tafiyar ta irin ta ƴaƴan turawa ta isa wurin umman tawa tare da ɓangala mata dariya, cikin gwarancinta take ta mata jagwalgwalon surutun su irin na yara; Afnan ce ta amsa mata da cewa "Ai umma ba zama in har banzo mun gana da aunty suhan ba, in wanke laifi na sannan in sake kafa wani gwamnatin domin naga Ayan yana neman kwace man fada, don ma na san ba zaki barta ba da cen ɗakina muka tafi muka sanya labule Alabasshi sai ta kwana cen da safe ta dawo" murmushi kawai umman tawa tayi alamar ba zata bari ba, sannan ta maida hankalinta kan Nasreem ɗin lokaci daya tana cewa "to kiyi maza ki gama kinsan ba daɗewa za'a neme ki sabo da yaran da kika taho dasu" "toh umma insha Allah" Afnan ɗin ta faɗa tana maido hankalinta kaina da nake ta wasa da hannun ayan, son yaron ya shiga raina sosai na rasa dalili, kuma ni ba mugun daɗi ma nake da mahaifiyarshi ba duk da dai cewa tafi su Saudat kirki ko don ta girmesu ne, ta fisu hankali shi yasa? Oho "Aunty Suhan kinga yanda kikayi shar abunki? Hutu ya ratsa ki wallahi kin ƙara kyau fatar ki sai sheƙi take yi minene sirri?" ta faɗa muryarta cike da zaulaya, ni sai ma ta bani kunya wallahi, sunne kaina nayi cike da kunyar umma ta da take zaune wajen, kuma tana jiyo duk abun da muke faɗa, ita kau Afnan na lura da ko ajikinta ma........" ba wani nan afnan kece zan cema haka Allah" na faɗa cikin murmushi, har cikin raina ina ƙaunar afnan ɗin, sabo da ko ba komai zuciya tana son mai kyautata mata, Afnan ɗin na son mu har cikin ranta, bata gudun mu ko kyamatar mu kaman yanda sauran suke yi, hakan ce tasa daga ni har umma ta muka sakankance mata muka saki jikin mu da ita. "Humm,,, haka dai kika ce Aunty na, ya Maganar karatu kin ƙarashe kuwa?" ta jefo man tambaya cikin halin ta na manyance; Lokaci guda gaba na ya ruguje ya faɗi, saurin saisaita kaina nayi domin kada ta fahimci wani abu, sannan nace mata "har na gama fa Afnan" "wow, har kin kammala aunty suhan?, wane course kika karanta ne?, na fa dade rabo na da nigeria wlh" ta maido man tambaya cikin tsammanin samun amsa daga gare ni, hakan shi ya ƙara ruɗani har firgici na ya fito fili cikin inda inda na mayar mata da cewa " Secon. dry school fa na.. ke nufi Afnan" zaro idanu tayi jin abunda na faɗa "meh😳" ta tambaya cikin son jin ba'asi "eh" na mayar mata ina mai gyaɗa mata kai kaman ƙadangaruwa, "look aunty suhan kibar wasa, ni na san umma ba zata hana ki ba, kuma nasan tinda Ya Ameen yana ƙasar ba zai sa maki ido kina zaune baki aikin komai ba kuma ke ba karatu kike yi ba" (kuji Afnan ɗin nan ma, wai bata aikin komai🙄) ta mayar mani cikin ɗan ɓacin rai, sabo da na kula hakan baiyi mata daɗi ba. Tsam umma ta tayi tana mai son jin amsar da zan bata, yayin da ni kuma nayi ƙasa da kaina ina mai cije laɓɓa na kamar zan huda su, alama nake yi mata da tayi shiru, Amman kaman ma bata san ina yi ba, cigaba tayi da cewa "kinga kin girmeni, Amman kina nan kina kallo zanzo in gama makaranta ta, na fiki ƙananan shekaru amman na fiki sanin abunda zai amfane ni nan gaba, gaskiya in wani ya baki shawara tsaida karatun ki daga iya Secondry bai kyauta ba, sabo da dashi ne zaki tallafi rayuwar ki nan gaba har ma da ta umma" tana kai aya naji kaman in zunduma da gudu, kaman in ɗora hannu a kai🙆🏻 in ta zunduma ihu😵 "afnan ya kamata mu bar maganar karatun nan hakanan shi komai da kika gani muƙaddari ne, idan da rabon inyi nan gaba sai kiga Allah ya kawo wani sanadin" na faɗa ina mai son ta fahimci umma ce ta hanani, ta kuwa fahimta domin naga ta dan zaro idanu waje sai kuma ta gyaɗa kai gami da cewa "tau ai shikenan Allah ya kawo aunty Suhan, dama zuwa nayi in tambayi umma don Allah ko zata barki ki raka ni siyayya zuwa gobe insha Allah ba daɗewa zamuyi ba" ta maida maganar tata kan umma ta da take ta jijjigar Nasreem har ta samu tayi bacci, "Allah ya kai mu" umma ta bata amsa cikin yanayi da na kasa karanta, Sam ba zata iya nuna ma Afnan ɗin ɓacin ranta ba domin ko babu komai maso uwa tau lallai yaso ɗanta, Afnan ɗin na daga cikin mutanen da take ganin girman su duk da ƙarancin shekarun nata kuwa,. Miƙewa Afnan ɗin tayi gami da gyara gyalen dake saman kafaɗar ta, tana mai cewa "To umman mu, aikau godiya nake yi bari muje sai da safe kinga ma kuwa ta maganar ki har sunyi barci, bari in kai Nasreem ɗin in dawo in ɗauki Ayan ɗin, tinda ban iya ɗaukarsu su duka" "a'a bari Mama na ta ɗaukar maki Ayan ɗin ai ba kin ta jigila ba tinda ga wadda zata iya taimaka maki, kuje ta kai maki shi, sai da safe ki gaida hajiyan da yayar taku" umma na ta mayar mata cikin ɗan murmushi, "to umma aikau na gode, aunty na taso muje aiki ya ganki na ɗaukar wannan gabjejen saurayin haka gashi yayi bacci ya ƙara nauyi, ko in goya Nasreem ɗin muyi kama kamar Ayan ɗin" ta faɗa cike da zaulaya da son sanya ni dariya da ta kula kaman walwala ta duk ta tafi, tinda aka yi maganar karatu, aikau ta ci nasara murmusawa nayi ina mai Miƙewa tare da faɗin "ance maki kowa ma raggo ne irin ki, da sai munyi ma yaro na kama kama?" na mayar mata cikin nima tawa zaulayar daidai lokacin da muke ficewa daga cikin ɗakin a tare. Ko da muka isa muka kwantar dasu sai da tace zata rako ni, nice na hana ta, ganin dare yayi, nima ina komawa nayi sallah na kwanta tinani fal cikin raina na Afnan ɗin da ƙarfin hali, ko ma dai miye ina fatan ta bar maganar karatun nan haka nan, bana son Abunda zai jawo man matsala da umma ta muna zaman zaman mu lafiya ƙalau, tinda na kula har cikin ranta ba son maganar take ba. ~~~~~~~~~~ Bai san lokacin da bacci ya kwashe shi ba a haka, sabo da sanyi da tsaftar ɗakin gami da taushin zanen gadon, sai dai farka wa yayi yana mai jiyo kiraye kiraye sallar magrib na tashi a laud speaker ɗin masallacin da ke gefen gidan nasu, a kasalance ya tashi gami da cire kayan, ya faɗa toilet domin yin wanka da alwala, mamakin yarinyar yake yi sosai, a ina ta iya irin wannan tsaftar haka? Gashi komai a nutse, ta ajiye komai inda ya kamata, hatta da towels ɗin wanka ta cenza mashi wasu, ta dauraye waɗanda suka yi dauɗa ta shanya a ɓangaren shanya na toilet ɗin, ta kwashe tarkace robobin shower jel da hand wash liquid soap ɗin duk ta zuba su a shara taje ta zubar, toilet ɗin ƙar, kaman an cenza komai na ciki ya koma sabo, shi kanshi cikin jin daɗi yayi wankan, ya fito yana mai jin daɗin jikin shi da ƙamshi da jikin nashi yake yi, shi ya siyo product ɗin Amman ta zaɓi waɗanda suka dace ta ajiye mashi. (yo Al'ameen wannan ai aikin Suhan ɗin ne a cikin gidan ko baka sani ba?) Bai sha mamaki ba sai da ya buɗe wardroop ɗaukar kaya,, ya tarad da komai ta ware mashi wajen shi ta kimlace su, ta kwashe duk wasu tarkace masu datti ta zuba a laundry basket; cikin natsuwa ya shirya gami da taje sumar kanshi tayi luf abun ta, ya fesa turare, gami da zura Jalla biya, ya fito yana taka wa cikin salon tafiyar shi ta ƙaƙƙarfan namiji, domin zuwa sauke farali sallar magariba. ******************************* Washe gari ma da nake nawa aikin, haka Afnan ɗin tazo tana taya ni, rabi surutu rabi tsaukana, yo eh tsaukana mana zance, tinda da ta fara shara ko goge goge sai ta duƙe ko ta faɗa kan sofa tace "wash wlh aunty suhan na gaji da yawa, gaskiya kina ƙoƙari" na kan yi dariya ince "Afnan kenan, miye na gajiya a nan?, aikina ne fa" A haka muka gama tana mai ƙara tuna man da cewa ƙarfe biyar fa na yamma zamuje shopping ɗin nan don Allah inyi shiga ta kece raini, (Lol🤣 Afnan kenan) Ƙarfe biyar tayi daidai da shiryawa ta, doguwar riga na sanya irin dubai abaya ɗin nan, da Alhaji mustapha ya taɓa yo man tsarabar ta, abayar na matuƙar karɓa ta, baƙa ce sosai har ƙasa sai dogon wando daga ciki, haɗe take da gyalenta, saboda haka sai Kaga dama sannan ka sanya hijab, kwalliyar golden ne jikin ta da adon wasu duwatsu farare daga sama har ƙasa, wannan shi ya ƙara ƙawata rigar, banyi wata kwalliya ba sosai domin ni ba ma'abociyar shafe shafen nan bace rambatsai. Hoda kawai na murza, sai kwalli da na zizara ma idanu na, haɗi da shafa lipstick mai ƙamshin Apple shima fari ne da ɗan sirkin Light pink haka, parking ɗin gashina nayi, tini ni dama ba ma'abociyar kitso bace sabo da gashina irin na asalin Fulani ne, mai taushi da sulbi, ga yawa da tsawo, wanda saidai in wanke shi kawai in shafa mashi mai in haɗa shi in ƙulle hakan ya wadatar dashi, turare irin namu na mata mai taushin ƙamshi na fesa haɗi da shafa humra ƴar Sudan da aunty saudat ta bani kwanaki cikin kwalimar ta, sai ƙamshin ya haɗe ya bada wani ni'imtaccen ƙamshi. (ka ganni kaman ba yar aiki ba😅) Afnan ce ta shigo cikin saurin ta tana cewa "Aunty Suhan maza ki fito, ga yaya cen yana jiran mu na lallaɓo shi, zai kai mu kinsan halin nashi baya son jira, ɗan oya oya ne." Turus ta ja ta tsaya lokaci guda mamaki fal bisa fuskar ta, lokaci guda ta shiga taɓa hannuwa, 👋🏻 sannan ta shiga faɗin "Aunty Suhan wannan kyau haka? Dubeki dan Allah kaman wadda zata je gasar kyau, kina da irin wannan kyaun haka kike boye wa?" jan hannuna ta shiga yi tana faɗin masha Allah wannan ai ni sai ma inji kunyar jerawa dake wlh abu kaman ƙyanƙyasar inji? " ta ƙarashe da zaulaya Ja nayi na tsaya ina cewa "Afnan Allah in kwalliyar tayi yawa bari in rage, yo ni wa zan ma kwalliya har haka?" murmushi ta sake yi, da ya riga ya zama ɗabi'arta, "ke wasa fa nake maki, Ya Ameen ɗin ne zai tsaya wani jiranki? Har ma fa ya shiga mota mu kaɗai yake jira, kuma yace in na ɗaɗe zan ga wayam, saidai idi dreba ya kai mu" ta shiga faɗi tana mai sake jan hannu na, ni kuma na shiga binta kaman raƙumi da akala. A tsakar gida muka haɗu da umman tawa, tana shigowa dan shirya zuwa girkin dare cikin gida, da addu'a da fatan dawowa lafiya ta bimu, sannan ta mana gargaɗi da mu kula da kanmu ƴaƴa mata muke, to muka amsa mata gami da jerawa da Afnan ɗin kai ka rantse ƙawaye ne, domin Afnan ɗin ta taddoni a jiki, saidai ɗan tsawo ne kawai zan nuna mata, ba kowa ne ma za'a gaya ma na girme ta ba ya yarda. Bayan motar ta buɗe mani na shiga, wani sanyi ne mai ratsa zuciya ya mani sallama, ban san lokacin da na ja mun fashi ba, gami da runtse idanu na ba sannan na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya, mota ce mai suna mota, na tabbata ban taɓa shiga mota makaman ciyar wannan ba, duk kuwa da tarin motoci na alfarma da suke gidan. Tada motar da yayi, shi yayi sanadiyyar dawowa ta cikin hayyaci na, daidaita kaina nayi cikin sanyin magana nace mashi "ina yini Yaya" duk da bana iya hangen shi sosai bayan shi kawai nake iya gani don ta saitinshi nake zaune sai ayan da ya kwanta bisa cinya ta, ina iya hango motsawar shi da motsawar bakin shi ta cikin mirror dake maƙale na driver, "lafiya" ya bani amsa a taƙaice, ban kuma cewa komai ba, sai wasa da na shiga yi da ayan, yana bani labarin school ɗin su a hankali, ina jiyo Afnan ta cika shi da surutu da take zaune gidan gaba wani abun ya amsa mata, wani kuma yayi murmushi kawai ya share ta. A haka muka isa tanƙamemen super market ɗin da ya haɗa komai, komai na kayan more rayuwa ana saida shi a ciki; ɓalle murfin motar nayi naja hannun ayan muka fita, yayi daidai da fitowar Afnan ɗin tana cewa "Yaya kai ba zaka shiga ba?" girgiza mata kai kawai yayi yana miƙa mata ATM ɗin nashi gami da cewa "30mnt na baku kuma, kuyi maza ku fito ina jiran ku, ina da nawa uzirin rigimar ki ce kawai bana so Lil" (da yake ya kan ce mata Lil wani lokacin) "OK Bigboo, insha Allah, ta faɗa tana mai ƙamewa cikin zaulaya, zagayowa tayi gami da kama hannun Ayan tayi gaba ni kuma na bita a baya kaman wadda kwai ya fashe mawa, tinda sanyin ac da ƙamshin motar Yaya suka bugeni naji komai nawa ya kwance, kaman an zare man lakka, lallai Ya Ameen daban ne, komai nashi ma daban yake; Ban san mun isa ba saida naji Afnan ta girgiza ni tana cewa "Aunty suhan lafiya dai kuwa? Ko baki lafiya ne?" ɗan murmushi nayi na shiga girgiza mata kai, ina mai cewa "a'a Afnan babu komai kawai dai wajen ne ya burge ni, mu shiga kada mu cinye lokacin mu anan" Nacewa Afnan ɗin tayi saidai in taya ta zaɓe, haka kau aka yi, duk Abunda na zaɓa sai ta ɗauki biyu, kama daga kayan shafa, kayan maƙulashe, kayan sawa da su eaner wears, Ayan ma da Nasreem ta ɗaukar masu kayan ciye ciye sabo da su basa buƙatar komai. Haka muka fito masha Allah gaskiya wurin yayi kyau ya ƙayatar dani, haka nake faɗa ma afnan ɗin a hanyar mu ta komawa motar Yayan. "Ta bangaren shi baya so tinanin yarinyar kan nushe shi a lokutta da dama, sai dai yakan danganta hakan da tausaya masu da yake yi, dubeta don Allah gwanin burgewa yanzu, kaman tayi ta dauwama a haka, ya kula tin shigar ta motar tashi, kashin turarenta ya bayyana kanshi, ƙamshi mai cike da kwantar da hankali, yana so tayi karatu, yana so ta tallafi rayuwar umman tata, yana so su samu ƴanci, sai dai me yasa?, me yasa umman tata take da wani irin tinani, me yasa ta nace ga rashin son tallafa masu da yake yi? Ya haƙura, ya haƙura tin ma kafin ta fara zargin ko yana da wata manufa tashi ta daban akan su, Suhan yarinya ce mai cike da natsuwa, mai cike da kamewa, tana da gudun abun duniya, wannan kaɗai ya isa ya yaba ma mahaifiyar tata, ta nan fannin kuma ta ciri tuta, ta kai a yaba mata gaskiya, kuma yana ganin ƙoƙarin ta, tayi aikin ta na uwa ta haɗa harda na uban ma; "Huh" ya guntsi iska ya fesar, yana saisaita kanshi ga barin kallon ta tin ma kafin ta ankara don baya son raini ya shiga tsakanin shi da ita. 😂 ********* A haka muka isa gidan Afnan ta kama man kayan muka shiga dasu ɓangaren mu, don ta nace cen zamu ajiye kayan ta fitar ma da kowa nashi, a cewarta rabon mu yau ya rantse don duk siyayyar nan da aka yi, cikin kudin Yaya ne, shi yasa ta zage ta ɗibar mana son ranta tinda ba nata aljihun bane yayi kuka, ina jiyo ta tana cewa "Yaya ina so muyi magana, fa wallahi" amsa mata yayi yana cewa "To my Lil, mu bari zuwa dare in na dawo sai mu tattauna, yanzu dai ina da muhimmin uziri kinji auta" ya faɗa yana mai murmusa mata, "OK yaya, as u said bye-Bye, sai ka dawo, a dawo lafiya" ta faɗa tana mai manna mashi ɗan ƙarami peck a kumatu sannan ta sake ɓalle murfin ta fito, na kula ɗabi'ar turawa ta kama su, har basa jin komai su rungumi juna, ko sumbatar juna a goshi, ko kumatu a gaban bainar jama'a, Ni kau tini nayi nisa da ragowar kayan da Ayan saɓe a kafaɗa ta. Haka ta wawware ma kowa kayanshi, harta umma ta, ta ɗauko mata atamfofi masu shegen kyau ƙwara uku, da less guda biyu, sai hijabai masu ruwan kayan guda uku, da takalma ƙwara biyu, masu kyau zubin na manya, Godiya umma ta ta shiga yi da faɗan na biye mata ta kaso kuɗi da yawa, wannan ai ɓarna ce, "ba komai umma wallahi Albarkarku kawai muke nema" Abunda tace kenan sannan tayi ma umman Alƙawarin za mu kwashi kayan namu da nata masu buƙatar ɗinki, mu kai ma telan dake ma gidan ɗinki, umman taso ta hana ta a cewarta hakan ma ya isa zamu bada nan cikin unguwa ayi mana, ba sai ta ƙara yin wata hidima ba, Amman Afnan ɗin ta nace ai babu komai wallahi duk yi wa kai ne. Nima ta ware man nawa kayan, wanda sai da tsoro da firgici suka kama ni, rabi da kwantan siyayyar ma ni tayo ma wa, kai ni afnan wacce irin ƙauna take yi mani har haka?, "Godiya na shiga yi mata tare da faɗin sunyi yawa ta rage" ɓata fuska tayi tana cewa"ga duk kan alamu watan ɓatawarmu yayi, ai in tazo Nija bata da ƙawar da ta fini, don me zan maida hannun kyauta baya, banga yanda nake yin kyau ba idan nayi kwalliya? dama maƙasudin siyayyar nice, sabo da bata yo man tsaraba ba da zata taho" godiya muka shiga yi mata ni da umma ta, lokacin da take kwasar nata kayan da basa da wani yawa sai kayan ciye ciye kawai. Sallama muka yi da ita, tare da mani Alƙawarin gobe zata shigo musha fira in na gama ayyuka na na cikin gida, har bakin sashen namu na raka ta, ina mai walwala da annuri a fuska ta, domin duk wanda yace yana son ka ai ya gama maka komai a rayuwa, ina ganin sauran ma'aikata ana ta zunɗe na, to suma dai da zata wuce sai da ta gaida su, ta masu ɗan Alkahiri a cikin kuɗin da ke pos ɗinta, Amman duk da haka baiyi masu ba, masu mugun abun ganin wannan tarayya tamu ta watse suka ƙudura, masu gulma suka naɗa, domin a gaban su muka shiga da leda niƙi niƙi, Amman sunga ta fito da guda ɗaya tal a hannu, ita ma ba'a cike ba, ashe yau Hajiya Babba da labari kenan, wai don ma basu san Yaya Al'ameen ne ya kai mu ba, wai ni Allah ai da kashin mu ya bushe daga ni, har mahaifiya ta, a haka dai na tura masu aniyarsu, na juyo salin alin na shige namu ɗakin tare da turo ƙofa, domin ɓoye kayan namu, sabo da wasu daga cikin su ƴan ganin kwam ne, zasu iya leƙo wa ko don ganin wainar da ake toyawa a cikin ɗakin. *************************** Ƙarfe tara da rabi daidai, Afnan tayi sallama sashen Yayan nata, izini ya bata ta shiga daga ciki, kai tsaye kujerar da yake zaune kai yana latsa laptop ɗin shi ta nufa, sanye yake da 3quater ruwan kunun kanwa, watau army green, da fara ƙal ɗin singleti, sanyin falon madaidaici ne, har yanzu gyaran da Suhan ɗin ta yi ma ɓangaren nashi yana nan, tinda ba yara ke akwai ba a sashen, ba yawan abokai ya cika ba, (yo wannan miskilancin nashi zai bar shi yayi abokai ne?) fuskar shi tar cikin haske da yake fitowa ta laptop ɗin, lallai Yaya Al'ameen ƙaƙƙarfan namiji ne, hakan ko ya samo asali ne da jim ɗin da yake zuwa akai akai, a sashen motsa jiki na gidan, kyakkyawa ne na gaske, cikin kalar fatar shi fara tas tas da ita. Murmushi yake bin ƙanwar tashi da shi, har zuwa lokacin da ta iso wajen nashi, hannu ya miƙa mata tare da zaunar da ita dab da shi yana mai faɗin "Lil wannan magana dai wace iri ce, da har aka bata muhimmanci haka?" Kallo ta bishi dashi, tana mai ƙara jin ƙaunar yayan nata cikin ranta, shi kaɗai ne zai zauna da ita ya fahimci damuwarta, har yayi mata maganin ta, in ka ɗauke aunty feena da dama ita wannan kaman uwa ta ɗauke ta, tinda a hannun ta ta taso. " yaya so nake muyi wata magana mai muhimmanci, dafatan zaka saurare ni, kuma ka fahimce ni, kayi ma maganar tawa kyakkyawa duba na tsanaki, don Allah" Na ɗaya daga cikin dalilan da yake sanyawa yana ƙara jin ƙaunar ƙanwar tashi fiye da kowa a cikin ƴan uwan nashi kenan, manyance da natsuwa tsara zance ga kuma girmama na gaba da ita, "Yaya wata Alfarma nazo da ita, dafatan zaka taimaka ka biya man wannan buƙatar, na sani duk gidan nan babu wanda zan tun kara ya saurare ni, kaman kai, kuma na san zaka iya shi yasa na zo wurin ka Yaya" ta katse mashi tinanin shi, cikin marairaicewa. Murmushi yayi yana mai tattara dukkannin natsuwarshi zuwa gareta, "ina jin ki Lil wannan wace ALFARMA ce kike buƙata gare ni haka da kike ta kwana - kwana haka?" ya faɗa cike da murmushin da ke ƙara ƙawata mashi fuskar shi, tare da fiddo zallar kyawon fuskar tashi, dimfull ɗin shi yana mai ƙara nutsewa cikin kuma tun nashi. " Yaya Maganar SUHAN ce" ta faɗa cikin tarabbabin yanda zai amshi maganar tata....... "Ehem!, ina jin ki Afnan me Suhan ɗin tayi ne?" ya amsa mata fara'ar fuskar shi na raguwa, abun da ya ƙara tsorata Afnan ɗin kenan cikin in ina tace "maaaganaaar... Kara.. Tun,,, ta Yaaaya".... ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:22 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƘARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~* *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ _*Jinjinar ban girma ga mai gida na, Abbu-Deedat. Nagode da irin goyon bayan da kake bani da irin yadda kake ƙarfafa mani guiwa, a duk al'amurran da na sanya gaba. Godiya marar adadi Allahu ya bar ƙauna ya raya mana Ahmad Deedat🥰*_ _*Page ~8~*_ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° "Look afnan✋🏻" ya katse ta daga inda indar da take yi, sannan ya ɗora da faɗin "Na riga nayi duk iyakar ƙoƙarin da zan iya yi akan issue ɗin karatun yarinyar nan, tin ma kafin ke kizo, saboda haka bana jin zan iya maida kaina acikin al'amurran su, tinda har mahaifiyar ta bata son al'amarin karatun nata, zai fi kyau muma mu dakata hakanan, mu barta tayi ma mahaifiyar ta biyayya Allah ya sani mun riga mun yi iyakar iyawarmu" ya ƙarashe maganar cikin wani yanayi na ƙunar rai lokaci guda yana ɗan ƙutawa gami da janyo laptop ɗin tashi ya buɗe, ga duk kan alamu yana nufin ya gama magana kenan. Shiru falon yayi, in baya ga ƙarar Ac da take bada sanyi ƙaɗan-kaɗan baka jin komai, ita kanta Afnan ɗin shiru tayi kaman ruwa ya cinye ta, ta rasa minene tinanin umman suhan ɗin akan ɗiyar tata, amman dai koma minene ita bazata bar lamarin haka nan ba, za tayi iya yi ta tinda ta kula babban burin suhan ɗin kenan, don dai Allah yayi ta da kawaici da biyayya ga na gaba da ita. Muskutawa ta sake yi ba don ta gaji ba, sannan ta marairaice dama abunka da auta an saba shagwaba "Na sani wlh yaya na, sai dai ba zamu bi ta kan umman ba, ita ba sanin daɗin abun tayi ba, Yaya Pls, don Allah ba don ni ba, ka taimaka mani, bana so ma ta gane da sa hannuna" shiru yayi mata na wasu daƙiƙai, sannan ya nisa tare da faɗin "Toh Naji, yanzu ya kike so ayi?" tini fara'ar fuskar ta ta dawo, afnan kenan baiwar Allah, yarinya da kyakkyawa zuciya. "Yauwa Big boo" ta fada cike da jin daɗi sannan ta kamo hannuwa shi ta riƙe su gam, sana ta ɗora da faɗin " Dady, Dady zaka yi ma magana, shine kaɗai zai iya sawa umman suhan ta yarda, ba tare da samun wata matsala ba, Pls my Lovely yaya" shiru yayi sai daga bisani ya nisa gami da faɗin "Is OK dear, Consider it done, kar ki damu ina so ki bar maganar nan a hannuna zamu san yanda zamuyi, ni kaina ina tausayin Rayuwar su, mutane ne da suka cancanci a tausaya masu don ga duk kan alamu sun fi sauran ma'aikatan shiga halin damuwa, masalan ita umman suhan ɗin" ya faɗa cike da basarwa kai kace ma bashi ne yayi maganar ba, saboda bazaka taɓa kawo ma ranka cewa miskilancinshi ma zai bar shi fahimtar wani abu ba. Miƙewa tayi tsaye, gami da yin wani ɗan tsale cike da annashuwa, "Nagode Yaya, na gode Allah ya saka da Alkhairi ya bar ƙauna, I love u sooo much, Good night Swt Yaya" ta faɗa tana mai nufar ƙofa domin fita, saboda dare yayi, da murmushi ya bita, wannan zuciya ta Afnan da kyau take, tabbas shi ya san ko ba daɗe ko ba jima sai sun yi alfahari da yarinyar "Ameen" ya furta a hankali cikin salon san kauda tinanin abun a ranshi, domin aikin da yake yi Afnan ɗin ta shigo, mai muhimmanci ne. ××××××××××××××××××××××× Washegari bayan mun kammala aikin mu, mun dawo sashen mu munyi wanka wajen ƙarfe biyu na rana, aiken Hajiya Kubra ya iske mu, ni da umma ta wai tana neman mu, har ga Allah gaba na sai da ya faɗi, domin har jin daɗi nake inje in kammala aiki na tana sashen Alhajin ta yanda ma babu abin da zai haɗa ni da ita, sai dai wajen zuba abinci. Ummana ce ta amsa da cewa gamunan zuwa, lokacin da ƴar saƙon ta fita ne ta juyo da kallon ta gare ni da nayi fiƙi fiƙi da idanu, ina ta tinanin laifin me kuma muka aikata yau, saboda duk idan aka yi mana irin wannan kiran to fa ba lafiya ba. "ki kwantar da hankalin ki mama na, insha Allah lafiya lau, babu abin da zai faru sai alkhairi" da to na bita domin in kwantar mata da hankali saboda yanzu umman tawa sai a hankali ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, don ko jiya dakyar muka yi bacci, ciwon zuciyar ta ne ya kusan tashi. Hijabi na na ɗauko na sanya gami da wucewa gaba umman tawa na biye a baya na, babu mai cewa ƙala har muka isa babban sashen gidan, ta bangare guda kuma zuciya ta na luguden duka, domin na san rashin mutucin Hajiya Kubra sosai, fata na dai kada al'amarin ya shafi umma ta, ko minene dai ya tsaya iya kaina. Sallama muka yi daga bakin ƙofa, Mama Talatu ce ta amsa mana daga ciki tare da faɗin "ku shigo mana, kuka tokare daga bakin ƙofa kaman wasu baƙi" shiga muka yi, ina gaba Ummana na baya; zaune muka iske ta bisa ɗaya daga cikin sofar da suka yi ma falon ƙawanya, gefe na samu da niyyar zama ƙasa ta dakatar dani, "a'a Suhana, ku shiga dai daga cikin falon Hajiyan, tana daga ciki tana jiran ku" "Toh Talatu" Ummana ta amsa mata. Kai tsaye falon muka shiga tare da sallama, waeh Aljannar duniya kenan, tsayawa fasalta kyaun falon da dukiyar da aka narkar ma ɓata lokaci ne, kawai ka fasalta shi da duk falo mafi kyawo da ka taɓa gani a Rayuwar ka. Zaune take, hakimce cikin isa, izza da taƙama (Hajiya Kubra ba dai ji da kai ba) ko amsa mana sallamar da muka yi bata yi ba, sai ma cen gefe ɗan nesa da tayi mana nuni saman carpet din da ya lashe fin rabin falon tayi, bamuyi ƙasa a guiwa ba muka zauna, muna mai gaisheta cikin ƙan-ƙan da kai, shima bata amsa ba, sai ma shiru da ya biyo bayan hakan na tsawon wucin gadi, sannan ta nisa cike da gadara ta fara faɗin "ina so ku nisanci ɗiyata Afnan, domin duk abubuwan da suke faruwa cikin gidan nan tin zuwanta a kunne na suke, na hana ta taƙi bari, ina so ku sa ta tayi nesa daku, domin ko alama bana son zuwa sashen masu aikin nan da take yi, kuma na san ɗiyarki ke janta" ta faɗa tana maida duban ta kan umma ta da kanta ke sunkuye, sannan ta cigaba "kunsan ko alama ba da son raina kuke zaune a gidan nan ba, saboda har yanzu kin ƙi ki faɗa mana asalin daga inda kuke, daga ke har ɗiyar taki bamu san asalin ku ba, sannan ki shirya bayyana mana komai da ya shafe ku idan ba haka ba, ba jin zaman ku a gidan nan zai cigaba da ɗorewa, bazan lamunci a mallake man ƴaƴa ba idan kunne yaji...... " ta ƙarashe tana mai ajiye maganar cike da gadara, ko ɗar bata ji ba, duk cin mutumcin da tayi mana bata gani ba, wannan ai tozarci ne, ko ba'a faɗa ba, na san mama Talatu da uwani ne suka kawo wannan gulmar, watau ita dai duniya haka take kana barci ana maka mun shari, idan da sabo ma mun saba jin ire-iren wannan tozarci daga gurin Hajiya kubran, muryar Hajiyan ce ta katse man tinanin da na Lula "Kuna iya tafiya Maryama, Amman kada ki manta da buƙata ta a gare ki" Cikin mutuwar jiki muka taso muka fito, tabbas idan raina yayi dubu ya ɓaci, a bakin ƙofa muka haɗu da afnan ɗin, tana yi man magana amman ni Sam hankali na ma baya kanta, murmushi kawai nayi mata na raɓa ta na wuce, juyowa tayi da niyyar binmu, na sanya hannu na dakatar da ita gami da girgiza mata kai, sannan na sanya ƙafa cikin sauri na bi umma ta da har ta kusa ficewa a babban falon. Wucewa Afnan ɗin tayi zuwa cikin falon Hajiyan, tare da zama cikin tashin hankali don ta san halin mom ɗin tata sarai "Mom me kika yi masu? For God sake me kika faɗa masu?" ta faɗa kaman zata yi kuka, "ke dallah saka rai shashasha, me kika gani jikin waɗancen faƙiran da har kika liƙe masu, har kina ɗaukarta kuje siyayya tare? Su fa ƴan aikin mu ne, ko kusa ba tsararki bace, bata da wani amfani wajenn mu in ba tayi mana aiki ba mu biya ta, ko kaya sai mun sanya mun cire sana muke basu su sanya, Amman wai kece yau kike haɗa kanki dasu, har kike zuwa ɗakinsu ki zauna, to ahir ɗinki wlh in ba haka ba zan saɓa maki fiye da tinaninki wallahi" ta ƙarashe tana mai nuna zallan ɓacin ranta ga autar tata "mom, ni fa banfisu da komai ba, in fact ma, babu Wanda yafi wani wurin Allah sai wanda yafi tsoron shi, so ni gaskiya momy baki kyauta mani ba, ai su ɗin ma ƴan adam ne, wanda ya halicce mu ya bamu, suma shi ya halicce su, kuma bai manta dasu ba" ta ƙarashe cikin matsanancin ɓacin rai, domin ga alama mom ɗin tata magana marar daɗi ta faɗa masu, kuma akan ta ne, mom ɗin ce ta amshe da cewa "au haka kika ce? Ashe ba zaki dena ba kenan? Maza ki shirya kayan ki, in kin fita ki kirawo man Nafeesa kuzo ku koma inda kuka fito domin bazan lamunci wannan iskancin naki ba wallahi, kada in saɓa maki" Fashewa tayi da kuka gami da barin part ɗin ma gaba ɗaya, cikin gudu ta sashen yayan nata, ta tarad dashi dawowar shi kenan daga office, don ko takalma ma bai cire ba, faɗa mashi tayi cikin kuka mai fidda zallan ɓacin rai, cikin tashin hankali ya janyo ta gami da rungume ta ya shiga shafa mata baya, cikin sanyin shi mai haɗe da miskilanci yake faɗin " Is OK Lil, is OK, tell me what is happening ne, me ya same ki? Ina ke maki ciwo?" cikin wani sabon kukan ta zayyana mashi komai dake faruwa da Abunda mom ɗin tasu tayi, zaunar da ita yayi yana mai faɗin "is OK Afnan, kinsan halin mom sarai, no, bai ma kamata ki ɓata ma kanki rai ba hakanan, ko ni da kika ga ina gaya mata gaskiya ba saurarena take yi ba a times, sai muyi mata addu'a insha Allah zata gyara halin ta, kiyi shiru babu inda zaku koma sai hutun ku ya ƙare, Amman ina so kema ki ɗan ja baya da su, saboda kada ki dinga ja masu ɓacin rai wajen mom ɗin, kin gane ko? Gyaɗa mashi kai tayi tana mai faɗin "na gane Yaya, amman wlh maman Suhana ba lafiya gareta ba, ina gudun ɓacin rai ya sanya wani abu ya same ta, gashi na baro Phone ɗita ɗaki balle in kira su na basu haƙuri" ta ƙarashe faɗi tana goge kwalla da ke saman fuskanta kwance shaɓe shaɓe. Is OK, kwanta nan ki huta,bari in shiga in watsa ruwa, sai in fito mu san abun yi,; ya faɗa mata haka ne don ya san rikicin Afnan, tana iya cewa zata kuma zuwa sashen nasu, kuma shi ba zai so hakan ba, gara ace ta ɗan ja bayan dasu, ta bar mashi komai a hannun shi insha Allah shi zai daidaita komai. Ni kau muna fita na kama umma ta muka nufi sashen namu, ina kallon mama Talatu murna fal cikin ranta, ga duk kan alamu ma laɓe tayi mana, domin taji Abunda Hajiyan zata faɗa, dama ita ta kai mata gulmar, kuma tayi ta zuzuta Hajiyar tana ƙara ma labarin gishiri, har cewa tayi Afnan ɗin sai ta kai ƙarfe sha biyu a ɗakinmu, kuma wai kuɗi take kashe mana sosai muke yi mata wayau, kuma yanzu na fara jin kaina daidai da su Nihal, saboda irin sutura da afnan ɗin wai ta siyo mun daga cen ƙasar wajen. Lafiya muka isa ɗaki, duk da umman tawa na ƙoƙarin dannewa, tinda ta lura da kwallar da nake share wa akai, akai, Amman hakan bai hana ta kwantawa ba, ba tare da ta furta ko uffan ba, nima bazan tada maganar ba, saboda maganganu ne marasa daɗin ji, to kenan ma tana nufin ƙilan bama da asalin kenan?, me umma ta ke nufi da ɓoye mana salainmu da take yi? Me hakan ke nufi,? Ganin ta samu barci ne, ya sanya nima komawa gefen ta na kwanta ƙasa, nayi matashi da katifar tamu, ina fata in ta farka komai ya wuce guri ta, ina fata kada ta tashi da :a in rai, domin kafin ta kwanta saida na ɓalli maganin ta na bata, na ƙudurce a raina zan nisanci Afnan ɗin, ba tare da na bari ta zargi wani abu ba, sai dai don mu tsira da mutumcin mu. Afnan ɗin ce ta roƙi Yaya Al'ameen ɗin da ya ara mata wayarshi ta kirani, sai kuma ta manta bata riƙe number ɗin wayata ba, dole ta sanya ta haƙura da niyyar in mun haɗu cikin gida zata sake bamu haƙuri dangane da Abunda mom ɗin tata tayi mana. Ta ɓangaren Hajiya kuwa, ko da ta tuntuɓi Aunty feena da maganar komawa, cewa tayi gaskiya ita ba yanzu ba, duka ma yaushe tazo? Kuma wannan dalilin ma bai kai Abunda za'a ce an koma saboda shi ba, ai tinda an ja kunnen Afnan ɗin shikenan bazata kuma maimaitawa ba,; su kuwa su Aunty saudat da sauran ma'aikatan gidan daɗi suka ji, wai ko ba komai an nesa ta ni da afnan, dama ƙaryar tawa ta Afnan ɗin ce (oh🤔 wai ko ma yaushe Afnan ɗin ta dawo, duka duka?) Haka Ya Ameen ya ta lallaɓa Lovely sister ɗin tashi har ya samu sukayi kwana uku da faruwa Al'amari, dama Alhaji mustapha yayi tafiya, duk wainar da ake toyawa bai sani ba acikin gidan, wannan ce ta sanya bayan ya dawo Al'ameen ɗin ya kuduri niyyar tunkararshi da maganar karatun suhan ɗin, a ganin shi wannan ce kawai damar da zai yi amfani da ita wajen ceto suhan ɗin da mahaifiyarka a halin taskun da suke ciki. ********************** Ƙarfe takwas daidai 08:00pm yayi sallama falon abban nashi, tafiya yake cikin salo shi na cikakke ɗa namiji, duk da yana da sanyi, wannan ce ta ƙara ƙawata tafiyar tashi, murmushi Alhaji mustaphan ke bi shi dashi, har ya ƙara so ya zauna kujerar dake kallon ta Alhaji mustaphan. Ɗan sunkuyar da kai yayi alamar girmamawa tare da faɗin "ABBA barka da dare" miƙa mashi hannu Alhajin yayi suka yi musabaha, "barka ka dai Son, ya aiki ya jama'a?" Abban ya faɗa fuskar shi cike da annashuwa, "Lafiya ƙalau Abba , an dawo lafiya.?? " ya faɗa cikin girmamawa, "Lafiya ƙalau Son, ina fata dai lafiya? Al'ameen ɗin ne ya amsa da" Lafiya lau Abba, wata magana ce nazo muyi idan ka da lokaci". "To to to, bismilla ina jinka Al'ameen ince dai ko lafiya ko?" Alhajin ya faɗa cikin dattako, lokaci daya yana mai ajiye kofin coffe da yake sha a hankali, ya tattara duk kan natsuwarshi ya ɗora ta kan mafi soyuwa daga cikin ƴaƴan shi. Natsuwa Ya Ameen ɗin yayi tare da warware mashi komai da ake ciki, dangane da karatun suhan ɗin, sai dai bai faɗi Abunda mahaifiyarshi tayi ba, sannan ya ɗora da faɗin "Abba kuma ina so asamu wasu masu aikin da zasu mayi gurbin su, Kaga dai ita maman yarinyar ba cikakkar lafiya gareta ba, kowa kuma ya sani, sannan idan Allah yayi ita kuma Suhana makaranta zata tafi, Kaga akwai nbuƙatar wasu madadin su, sannan bana so mom ta san da hannuna ko na Afnan a ciki, ka shige mana gaba wajen ganin ka daidaita komai wajen hajiya" Murmushi Alhaji mustaphan yayi irin nasu na manya, sannan ya ɗora da faɗa ya aka yi ba'a faɗa mashi hakan ba tun farko? Ai da yanzu ma yarinyar tayi nisa a karatu, ko ma ya tura ta cen wajen Aunty feena tayi karatun ita da Afnan ɗin, Amman ko yanzu babu matsala, babu Abunda zai gagara da izinin Allah, wasu ma an temakesu balle waɗan da suke ƙarƙashin su?, shi ɗa ai na kowa ne, kuma baka san mai amfanar ka ba nan gaba. "Babu komai Al'ameen, ka bar maganar a hannuna insha Allah da kaina zan samu ita mahaifiyarka tata, zan kuma roƙe ta wannan alfarmar in har na isa tayi man" Alhajin ya faɗa cikin son ƙarfafa ma Al'ameen ɗin guiwa ga temakon da yake son yayi, ko bayan ba ranshi, shi ya san ya bar wanda Al'umma zasu amfana dashi, ya san ya bar ma dadi, ko ma yace mafi yi, domin Al'ameen ɗin yaro ne irin wanda kowanne uba yake da burin ace ya mallake shi, a matsayin magaji. Cikin jin daɗi da godiya yayi ma Abban nashi sallama gami da cewa "bari in barka haka nan Abba, ka huta na san ka gaji, a tashi lafiya, sai da safe" ya faɗa yana Miƙewa da niyyar barin ɗakin, da kallo Alhaji mustaphan ya bishi yana ƙissima wani al'amari da zai faru nan gaba ƙaɗan akan ɗanɗan nashi mai girma, tabbas yana da buri da fatan hasashen nashi ya zamo gaskiya. Murmushi yayi yana mai janyo kofin coffe ɗinshi ya cigaba da kurɓa cikin dattako gami da faɗin "Allah shi kaimu Son" _Toh fa Fans, magana ta girmama, lamarin ya kai kotun ƙoli, ko ta yaya Alhajin zai yi domin shawo kan maman Suhana?, Kudai kuci gaba da bin Alƙalamin Oum Deedat domin ta warware maku zare har abawa_ _~Oum-Deedat ce~_ [8/5, 8:23 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƙARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u nopain✍🏽~* *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Fans ina jin daɗin comment ɗinku, hakan na ƙara man ƙwarin guiwa, nagode akafta* _*Page ~10~*_ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Takowa ya cigaba da yi a hankali cikin salon tafiyar shi ta ingarman namiji, daf dani ya sunkuyo ta yadda zan iya jiyo shi, sannan ya shiga faɗin "pray for your mom, yanzu ba kukan ki take buƙata ba, sannan ki tashi daga wajen ki koma bisa chair kin tare hanya, wani zai iya bugeki" Abunda ya faɗa kenan a gaggauce ya koma inda yake zaune ya sake zama. A hankali na tashi ina mai haɗa hanya cikin jin juwa da ke neman yin haji-jiya dani, kujerar dake kallon tashi na zauna tare da juyar da kaina daga saitin shi, ta yadda ba ma zamu iya haɗa idanu ba. Akai Akai yake ɗaga idanu yana kallon kyakkyawa agogon dake hannun shi samfurin Apple, sai kuma kiran da akeyi mashi Akai Akai yana latse wa. Ƙarar buɗe ƙofa ce ta dawo da hankalin mu duka wajen, zabura muka yi mu duka biyun wanda a tare muka isa ga likitan da ya fito daga cikin ward ɗin "likita umma ta ta farfaɗo? Kaddai kace man ta mutu dan Allah" na faɗa ina mai matso wani sabon kwallar, "ummanki lafiya lau ta farfaɗo amman mun yi mata allurar barci saboda ta sake samun hutu, zaki iya shiga ki ganta nan da anjima idan ta farka" ya faɗa man yana mai maida hankalin shi kan yaya ameen ɗin da yake tsaye ta gefen mu, "a'ah yallaɓai ashe baka shiga office ɗin ba? Sai ka zauna waje?" dan guntun murmushi yayi sannan yace ma Ya Ameen ɗin "to muje sai in maka ƙarfin bayani ko" ya wuce gaba Ya Ameen ɗin ya bishi a baya, da idanu na raka su har suka shige office ɗin sannan na sauke ajiyar zuciya lokaci guda ina mai hamdala gami da sanya hijab ɗina na share dukkan ƙwallar dake kan fuskata, muskutawa nayi sannan na maida duba na kan mama Talatu dake tsaye tana binmu da kallo da kuma naɗe dukkanin motsin mu cikin fai-fain ta na gulma, ɗan taɓe baki nayi kaɗan ina mai rayawa a cikin raina "dukkan ku zaku gama ne, zaku gaji ku bari, ai Hajiya Kubra ba'a mata gwaninta. *************** Likita ne ya zauna a kujerar sa gami da nuna ma Al'ameen ɗin kujerar zaman patient," Bismillah yallaɓai ga wuri zauna" bayan ya Ameen ɗin ya zauna ne sannan ya muƙa mashi hannu suka sake yin musabaha gami da ƴan gaishe gaishe, dama sun san juna don shine family doctor ɗinsu, kuma a asibitin ne suke da file, Dr. Ashafa kenan kwararren likita ta kowanne fanni. "Yallaɓai garin yaya haka kuka bar matar nan cikin irin wannan hali? Abun yayi tsanani, zuciyar ta ta kusa ta buga, ta daɗe da ciwon zuciya duk da bincike ya nuna tana kan drugs, sai dai ba wasu masu ƙarfi bane, ba zasu yi tasirin hana zuciyar kumbura ba, gaskiya ba dan kunyi gaggawar kawo ta nan ba da abun ya munana, a dinga kulawa pls" ya sauke maganar tare da ɗora dukkanin idanun shi da natsuwarshi akan Al'ameen ɗin don jin amsar da zai bashi. "Dr wallahi ban san abun yayi worse haka ba, ban ma san wane asibiti suke zuwa ba, na dai san bata da lafiya Amman ban san me ke faruwa da ita ba, yanzu ya jikin nata? Ba zamu iya ganin ta yanzu ba, ina da uzuri ne tin ɗazu ma ake kira na" ya sauke maganar da gani dai cikin hanzari yake don ya ƙagara ya tafi "No babu wani damuwa yanzu mun shawo kan matsalar, sai dai gaskiya a kula, a dena yawan ɓata mata rai, in da hali ma adena bari tana aiki mai yawa da zai iya gajiyar da ita, yanzu ma zaku iya shiga ku ganta, sai dai zaku barta anan ne, ka san tsari asibitin ba'a zaman jinya" ya faɗa yana mai sake miƙa ma Al'ameen ɗin hannu dan musabaha, shima Al'ameen miƙa mashi yayi yana faɗin "Nagode Dr. Ashafa, sai dai alfarma zakuyi mana wannan karon, ita wannan yarinyar ɗiyarta ce, so ko mun koma da ita zata tashi hankalin ta ne, zata damemu da kuka, ku barta ta zauna wajen ta har muga yanda jikin zai yi, ni zan je, idan na taso daga office zan dawo inga yana yin jikin ko da Abunda ake buƙata" "OK shikenan yallaɓai" likitan ya faɗa, sannan suka juyo a tare suka fito domin shiga ɗakin da umman tawa take; ya ameen ɗin ne ya tsaya yana faɗa mana mu shiga muga jikin ta har da mama talatun domin ita zata koma ne gida. A tare muka shiga ɗakin da shi da mama talatun, likitan ne yake shaida mana banda hayaniya, kada kuma a tada ta har sai dai ita ce ta tashi dan kanta, kuma kada a bata komai taci, akwai sinadari abinci da ake bata ta iskar oxygen ɗin da yake maƙale a hancin ta. Duk iya rashin imanin mutum sai ya tausaya wa umma ta, kwance take tayi fayau da ita, numfashi take sauke wa a hankali, babu Abunda ke motsi jikin ta, jawo kujera nayi ta roba mai kyau na zauna yayin da na ƙure ta da idanu hawaye na ɗiga ɗis-ɗis saman hijab ɗina. Juyawa suka yi suka fita har mama Talatu da Ya ameen ya yafito da hannu, kuɗin taci ya bata tare da mata godiya sosai yace ta koma gida sai ya dawo, dawowa yayi ɗakin tare da kira na domin shi wucewa zai yi, a baya na bishi zarai-zarai har muka fita harabar asibitin da har mama Talatu ta samu abun hawa, ina kallon ta tana leƙowa taga shin ina zamu, sai dai ta makaro dan mai motar ma har yaja sunyi gaba, naso nayi mata godiya Amman ba komai ai bana ma fatan mu daɗe asibitin, zan yi mata idan mun koma gida. "Is OK Suuhaaan" ya faɗa a hankali bayan ya daidaita tsayuwarshi bakin motar sannan ya juya ya jingina da ita sosai, "Comon goge wannan hawayen naki, kukan ya isa hakanan, ki yi mata addu'a sannan ki guji ɓacin ran ta, a mamadin mahaifiya ta ina mai ƙara baku haƙuri, na san ita ce sanadi, Amman insha Allah komai ba zai ƙara faruwa ba" ya faɗa yana mai ƙoƙarin haɗa idanu dani, ni kau sauke kaina nayi ƙasa ina mai bin umarnin nashi na share fuskar tawa gami da jan majina a hankali na shiga faɗin "Mungode Yaya babu komai wallahi, dama umma ta tana da wannan ciwon, nima dashi na taso na ganta, ba Hajiya bace sila, Mungode da karamci Allah ya saka da Alkhairi" na faɗa ina mai ƙosawa da tsayuwar, ba zan iya jure tsayuwa wuri ɗaya dashi ba, kwarjini yake man, gani nake duk ya cika wajen, Al'ameen ɗin daban ne, akwai kamala da haiba tattare dashi, komai nashi da yake yi cikin hankali da natsuwa yake yin shi, daidai da magana kaman baya son yi, muryar shi, ƙamshin turaren shi na ƙara rikitar dani, bana son irin yanayin da nake shiga a duk lokacin da muka kasance mu biyu a wuri ɗaya, kula yayi da irin yanda duk nabi na takura, motsa bakin shi yayi a hankali ya shiga faɗin "ki koma wurin umman, zan je aiki in dawo tin ɗazu ake jira na babu Abunda zaku buƙata, akwai komai a ɗakin kuma akwai drinks a fridge zan sa a kawo maki break fast ki tabbata kunci don na san baki ci komai ba, sai na dawo" Ya faɗa, bai jira cewa ta ba ya faɗa mota gami da yi mata key, janyewa nayi na bashi hanya, ya zo yawuce bai ko kalli inda nake tsaye ba (hoooo Al'ameen miskilanci) ******************************* Mama Talatu kuwa na isa gidan sashen Hajiya kubran tayi, ta iske bata tashi ba Amman don tsabar san gulma sai da ta jira ta, bayan ta fito ne take tambayar ta ya bata ganni ba? Ban shigo aiki ba,me yake faruwa, "yo Hajiya ina ko zaki ganta? Ai bama su gidan gaba daya" cikin isa take kallon talatun, "ke Talatu bana son munafunci, faɗa man gaskiya me yake faruwa ne a gidan? Ta faɗa cikin gadara lokaci guda tana mai zama kan ɗaya daga cikin sofa na alfarma da sukayi ma falon ƙawanya, sanye take cikin wani ɗanyen lace mai azabar kyau, dama hajiya Kubra ba dai kyau ba, naira ta kwanta mata ta ko ina sai sheƙi take yi da walwali, nan mama Talatu ta kwashe ƙarya da gaskiya har faɗa mata take yi cen ta baro Al'ameen ɗin ai muna tare. Ranta ko in yayi dubu ya ɓaci, au ta hana taraiya da afnan shine muka koma ma Al'ameen? Al'ameen ɗin nata da take ji dashi tamkar tsoka ɗaya a miya, me hakan ke nufi? Dakatar da mama talatun tayi gami da miƙewa cikin takon isassu ta fita daga sashen zuwa sashen Alhaji da take barowa da sanyi safiya, Afnan ce ta fito tana kallon mama Talatu, ashe ta zo fitowa taji suna magana shine ta koma da baya take jin duk abubuwan da mama talatun ta faɗi ma mom ɗin tasu "mama kiji tsoron Allah fa, ashe ke ke hadda sa fitina tsakanin hajiya da masu aikin gidan nan? Kina shugaba baki so a zauna lafiya, to wallahi kema ba zaki ci gaba da zaman gidan nan ba muddin kika yi sanadiyyar barin su suhan ɗin gidan nan". Tana kaiwa aya bata jira cewar mama talatun ba ta koma ɗakin nata da gudu tana mai rarumar wayar tata gami da kiran Ya Ameen ɗin, tsaf ta kwashe komai ta faɗa ma gayan nata yanda taji mama Talatu na faɗa ma Hajiya, tare da faɗa mashi yanzu zata bar gidan zuwa asibitin ta taya ni zama, koma minene ya faru ai su ne sila; Dakatar da ita yayi gami da cewa ta bari sai ya dawo baya son wata matsala kuma, shi zai jawo hankalin hajiyar ta bar zancen bari ma ya faɗa ma Alhaji komai kafin Hajiyar ta isa. Da yake da tazara sosai tsakanin sashen nata da na Alhaji, lokacin da ta isa har Al'ameen ɗin ya kira Alhajin ta iske yana waya da Al'ameen ɗin ta nemi waje kusa dashi ta zauna, tana ta cika da batsewa, bayan ya gama wayar ne ya maida hankali shi kan Hajiya Kubran, da murmushi ɗauke kan fuskar shi ya shiga faɗin "uwargida ran gida, lafiya dai ko naga kin dawo, wannan kwalliya ai sai dai ace in biya" ya faɗa cikin zaulaya da murmushi a kan fuskar shi. Fuska a tamke take cewa "Alhaji ba wannan ba, yaron nan Al'ameen...." Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu gami da cewa "Abunda Al'ameen ɗin yayi shine daidai, ai suma mutane ne, ko kuma zai ƙyale ta ta mutu ne cikin gida yana kallo? Mutane su samu abun faɗa a gari? Kada in kuma jin kince komai akan zancen nan kuma anjima ku shirya ku duka muje a dubo ta, Allah ya bata lafiya shine fatan mu. Sannan ina so ki sanya a nemo maki wasu ƴan aikin da zasu zauna mamadin su, abarsu su huta hakanan ita yarinyar ta kula da mahaifiyarta." Yana zuwa nan a zancen ya miƙe gami da gyara zaman babbar rigar shi yana mai kallon ta sannan ya cigaba da cewa" Ni zan fita sai na dawo, kada ku manta ku shirya fa, sannan idan Allah ya kai mu gobe Asabar mu dukkan mu zamu je kankiya mu gaishe da su Alhaji tinda kowa yana ƙasar ki faɗa ma yaran ma su duka su shirya" da kallo ta bishi har ya fice, ita kanta ba tin yanzu ba ta san Alhajin kaifi ɗaya ne, dukkan isar ta da zartar da hukuncin ta, tana yi ne akan ƴaƴan ta kawai da masu aikin gidan sai kuma abokan kasuwancin ta. Amman Alhajin gagarabadau ne a wajen ta, duk abin da take taƙama dashi ya fita shi tsayayye namiji ne a cikin gidan sa, dukkanin hukuncin da ya yanke ya yanku kenan, ba shan ruwa ba ƙetare hanya. ****** Ƙarfe biyu Al'ameen ɗin ya koma gida bayan salla juma'a gami da yin wanka ya shirya, Afnan ya kira a waya ya sheda mata ta fito su tafi, aikau ta saɓo Nasreem ta kamo hannun Ayan, Afnan kenan sarkin ƴaƴa, ko MOM ɗin tasu bata faɗa mawa ba don ta san hana ta zata yi, biyawa suka fara yi, suka yi take away da sauran tarkace, sannan suka wuce asibitin kai tsaye. A ɗakin suka taddani zaune bisa kujera, na kifa kaina jikin gadon umman tawa da har yanzu bata farfaɗo ba, ban ma ko ji ƙarar buɗe ƙofar tasu ba, na yi zurfi cikin tunani, ƙamshin turaren shi ya sanya ni sauri ɗagowa, ilai kuwa su ne shi da afnan, sanye yake cikin dakakkiyar shadda fara ƙal, yau juma'a tu babbar rana, fuskar nan tashi fayau, idanun shi tarwai cikin farin glass ɗinshi mai kama da medical glass, idanun shi ƙyam a kaina, kallo yake man mai cike da ma'anoni da tuhume tuhume, tabbas na san laifi na, take away ɗin da ya sanya aka kawo man, tin bayan fitar shi da safe, yana ajiye bisa stool ɗin ɗakin ko taɓa shi ma banyi ba har gashi yanzu Ƙarfe uku saura; ba'a magana da ƙarfi ya sanya bai ce an komai ba, sai ma ɗan ƙutawa da yayi ya ajiye sauran ledojin da suke hannun shi ya fice gaba ɗaya a ɗakin. Gaisawa muka yi da afnan sosai kaman babu abin da ya faru, na shiga tambayarta sauran mutanen gidan, "suna gaida ki da mai jiki" ta furta ba dan taji daɗin ƙaryar da ta furta ba. Hannun Ayan na kamo ina cewa "zo mana Ayan in ba faɗa mi ya kawo gaba?" cikin ƙarfin hali har da ɗan murmushi na na yaƙe. Text ne ya shigo wayar afnan, Ya Ameen ne yake cewa lallai ta sanya ni inci abinci, shi ya wuce sai anjima zai dawo kuma lallai kar suyi hayaniya a ɗakin nan su tada umman tawa. _Kuyi manage da wannan please bana ɗan jin daɗi ne ku taya ni da addu'a fans_ ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:23 PM] Aminatu Hassan: 🌹 *_BAN FI ƙARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u nopain✍🏽~* *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ 🤸🏻‍♀💃🏻💃🏻 Kuzo ku taya ɗan ku Deedat murnar cika shekara uku cif a duniya, ina fatan Allah ya Albarkaci Rayuwar shi, ya shirya shi shirin addinin islam, ya bashi rayuwa mai Albarka, ya bashi ilimi mai yawa mai amfani, ya cika mashi burin shi na zama Soja😄😆 ya bamu ikon tarbiyyantar dashi. AMEEN ya Rab, Deedat yana gaida dukkan fans na *BAN FI ƘARFIN TA BA* _*Page ~9~*_ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Mu kau cikin ni da umma ta, babu wanda yayi runtsawar kirki, kowa da abunda yake saƙawa cikin rai, har gara ma umman tawa, tana ƙoƙarin ganin ta kau da komai, sabo da shawarwarin likita da ya bata na tayi ƙoƙarin ganin bata riƙe abun ɓacin rai a zuciyar ta ba. Ni kuwa Allah Allah nake gari ya waye, domin na yanke shawarar ƙundunbalan tambayan umman tawa ainihin labarin mu, da asalin mu, lokaci yayi da zata dena ɓoye mani komai, na mallaki hankalin kaina, yaci ace ta fito ta fayyace mana komai kowa ya sani, ko zata fita a zargin da mafi yawancin ƴan gidan ke mana, a kan kunnen mu mun sha jin ma wasu ƴan ƙanana maganganu akan umman tawa da ni kaina ma, kai wasu ma cewa suke yi ni shegiya ce bana da uba, tinda haka suka ganta tazo gidan a wahale ga ɗiya duƙu-duƙu kuma taƙi faɗin wacece ita da kuma ainahin daga ina take. Alhaji Mustapha kuma ya kafa dokar kada wanda ya tambaye ta, har sai ta gaji dan kanta ta faɗa, a cewarshi babu kyau shiga rayuwar wani, kuma hakan zai tada mata tsohon mikin dake ranta, gida dai nashi ne, tau tinda haka ne ya bata izinin zama har iya lokacin da take so, kuma tinda aiki tazo nema a zaɓa mata marar wahala a bata har sai ta murmure. Ciwon umman tawa ya so ya tashi cikin dare, amman cikin ikon Allah abun ya taƙaita, ban so ace zan tada mata maganar da safe ba, gudun sake faruwar tashin ciwon nata, tau sai dai babu yanda na iya, wannan karon haƙuri na da kawaici na yazo ƙarshe, ba zan iya jurar ganin irin wannan rashin mutuncin ba daga wajen Hajiya kubran; da haka na samu bacci ya ɗan figeni har zuwa asubar farko da kiran sallah ya tashe ni. ******************************* Ya Ameen yana shiga ɗaki waya yasa ya kira Afnan ɗin domin sheda mata yanda sukayi da Dad ɗin nasu, "Hello yaya" ta furta daga cen ɓangaren cikin muryar bacci "My Lil bacci kike yi ne?" ya tambaye ta cikin muryarshi mai daɗin sauraro a hankali, "eh Yaya na kwanta, lafiya dai ko? Ko wani abu kake buƙata? Ta tambaye shi tana mai tashi zaune da ƙara gyara ma Ayan dake gefen ta kwance bisa gadon nata lulluɓinshi," No Lil, ina dai son faɗa maki ne munyi magana da dad ne akan maganar waccen yarinyar, Amman tinda kin fara barci mu bari zuwa safe ki same ni part ɗina kinji, Good night dear" ya faɗa yana mai datse kiran ƙit, domin ya san halin zumuɗinta yanzu tana iya cewa ta taso ta taho, shi kuma baya jin ma zai iya doguwar magana yanzu ya gaji so yake ya kwanta, yana da muhimman ayyukan da zai aiwatar gobe, murmushi ya saki na gefen baki, wanda yayi sanadiyyar ƙara ƙawata fuskar tashi cikin hasken ƙwai mai launin dark blue na dare dake falon. Miƙewa yayi cikin salon tafiyar shi mai cike da aji, ya shiga bedroom ɗin nashi domin yin shirin bacci, kayanshi kawai ya cire ya faɗa toilet ɗin da baya gajiya da shaƙar daddaɗan ƙamshin da suhan ɗin ta sanya mashi har kawo yanzu. ------------------- Bayan mun kammala komai na Al'adar mu, kama daga sallah, wanka, sai muka zauna karatu ni da umman tawa, muna gamawa ne naga umman na ƙoƙarin tashi na dakatar da ita ina faɗin "Umma ina so zamuyi wata magana dake don Allah" na faɗa ina mai rufe littafin umdatul-Ahkam ɗin gami da maida shi ma'ajiyar shi, na sake muskutawa domin girman maganar, ba zan ɓoye ba zuciya ta kaman tayo tsalle ta fito nake ji ta ƙirjina, masalan ma da naga irin kallon da umman tawa ke bina dashi, mai cike da ma'anoni daban daban, komawa tayi ta zauna domin saurarar ɗiyar tata, da kanta yake duƙe kaman tayi ma sarki ƙarya, "Ehn ina jinki mamana, sauri nake yi domin kinga lokaci ya fara ja. Sake sunkuyar da kai nayi ina mai komawa kalar tausayi maganar tayi ma baki na nauyi, shahada nayi lokaci guda na shiga faɗin "Umma ki duba girman Allah ki faɗa mani asalin mu, wanene mahaifina? ina ne asalin garin mu, umma ke kanki su wanene mahaifan ki? Umma kin fi so mu zauna a gidan da ba'a san darajar mu ba? Kin fi so mu zauna ana wulaƙanta mu, ana zargin ki, ni kuma ana sheganta ni? Kada zuciya ta tafara yadda da maganar su fa!, na bani da asali, bani da mahaifi umma! Umma su nan ɗin ba dangin mu bane, basu san zafin mu ba, ƴaƴan su ma basa so su raɓe mu, suna kyamatar mu, suna ganin sun fimu umma, bazan iya jurar aci maki fuska a gabana ba, saboda kina ɓoye mana wani abu, kinƙi ki fito ki faɗa ma kowa mu ɗin su wanene ciki kuwa harda ni...... " marin da ta sauke man a kan fuska ta har guda biyu, su sukayi sanadiyyar datsewar maganar tawa, ɗif nayi dafe da kunci, kaman ruwa ya ci ni, yau ni ce umma ta ta buga, yau ni ce durƙushe gaban mahaifiyar tawa ina faɗa mata malaman da suke barazana ga lafiyar ta, ba zan iya tuna lokacin da umma ta ta ɗauki hannu ta bigeni ba, saboda ita mace ce mai san yin hali, Sam bata da zafi; kuka na fashe dashi lokaci guda ina mai ƙanƙame jikina, yanda naga ta hassala kaman zata rufe ni da suka. "Ashe ke shashasha ce hauwau ban sani ba?, ina tarbiyyar da na baki? Ina kika kaita, nan ɗin da kike ganin ana wulaƙanta mu, ya fiye mana cen, in kika koma kashe ki zasu yi, nace kashe ki zasu yi! Ni ma ba zasu barni ba, saboda ke nake zaune nan, dan ki tsira da mutuncin ki, ki tsira da rayuwarki yasa nake zaune nan, nima abun yana man zafi, Amman ko me zasu yi mana ba zasu iya kashe mu ba, zaki mutu ne muddin kika yarda kika koma cen" kwalla ce ke shata ta a idanun umman tawa, abun da ya ƙara matuƙar firgita ni kenan, rarrafawa na shiga yi ina mai zuwa inda take na rungume ta, ture ni ta shiga yi, jeki, je ki nemi mahaifin ki, ƙila zakiyi sa'ar ganin kabarin nashi, ƙila zai iya tashi ya faɗa maki komai, Hauwa'u ban tsammanin akwai ranar da har ke zaki iya zuwa ki sanya ni a gaba ba, ki titsiye ni sai na faɗa maki wacece ke ba, na ɗauka na gama maki komai, na ɗauka na ishe ki komai, ban tsammanin zaki gaji da zama a inda na zaɓa mana rayuwa ba, nace kashe ki zasu yi, muddin kika yarda suka san kina nan da ranki, jeki jeki ki nemo dangin mahaifin ki, ki nemo dangi na, Amman ni kar ki ƙara tambaya ta game da su, kar kuma ki sake ki dawo inda nake, kuma duk Abunda ya same ku ke ce kika siya da kuɗin ki, kar ki ƙara tambaya ta abunda ya shafe su; Ta shiga ƙara ture ni daga jikin ta tana mai share kwallar da take ta ambaliya a fuskar ta. Ƙara ƙwaƙume ta nayi, ina mai sakin gunjin kuka lokaci guda ina mai faɗin "Umma kiyi haƙuri ki yafe man, ki gafarce ni umma, nayi maki laifi, na aikata maki ba daidai ba umma, na cutar da zuciyoyinmu umma, bansan haka ba, bansan komai ba umma ki yafe man" shiru naji lokaci daƴa kaman ma bata numfashi, A firgice na ɗago, domin in ga me ke faruwa, abunda idanunwa na suka gani ne ya sani sakin razananiyar ƙara da sai da ta cika ilahirin sashen namu. Jikin ta gaba ɗaya ya saki, kaman wadda ta mutu bata numfashi Sam, "umma ki tashi" na shiga faɗi lokaci ɗaya ina mai jijjiga ta "umma ki tashi don Allah na bari, umma ki yafe man, umma kar ki mutu ki barni don Allah, umma ban da kowa sai ke, ke ce uwa ta ke ce uba na umma, ke ce komai nawa umma, kar ki mutu ki barni a cikin gidan nan umma, zan mutu nima in biki wallahi muddin kika barni, umma basa son mu basa ƙaunarmu, kar ki barni ni ɗaya a cikin gidannan" kuka ne gami da majina suka bi suka haɗe a yalwataciyar fuskar tawa, bama ta su nake yi ba, balle in mai da kai wajen share wa, gunjin kuka na nake yi mai cike da ruɗani kala kala, yayin da umman tawa take sharaf a jikina babu alamar numfashi tattare da ita, kwantar da ita na shiga yi lokaci guda ina mai girgiza kaina "umma ta bazata mutu ta barni nan ni kaɗai ba, bansan kowa ba umma sai ke" haka nake faɗa yayin da na tashi na fice da matsanancin gudu zuwa nemo wanda zai duba man ita, a tsakar gida muka haɗu da sauran ƴan aikin gidan da duk sun jiyo kuka na sun fito hankali tashe, hannun uwani na shiga ja ko sauraren ta banyi ba ina faɗin "mama uwani Kuzo ku duba man umma ta kar kuce man ta mutu, kar kuce man bata da rai, kar ku kashe man ita" mama Talatu Kuzo" na saki hannun mama uwani da nufi mama Talatu da gudu itama na shiga jan ta, ina mai sake sakin kuka mai tsuma rai, "me ya samu maman Suhana ɗin ne wai? " mama uwani take tambaya ta, ban iya bata amsa ba, domin naga sun yi tsaye sun ma ƙi shiga ɗakin, hanyar waje na nufa da gudu cikin kuka ina kwala ma baba idi kira, yazo ya duba ban umman tawa. Tin daga nesa ya hango ta, Ya Ameen ne da ya fito daga part ɗin nashi cikin shirin zuwa wajen aiki, suit ce sanye jikin shi kalar royal blue, ya matuƙar yin kyau cikin sanyin shi yake takawa da niyya zuwa ɗaukar motar tashi, ya hango ta tayi hanyar fita waje cikin matsanancin gudu, kuka ma take yi, duk ta cukuikuye hijabin tata kaman mahaukaciya, lelleƙawa nayi banga kowa ba, ga dukkan alamu ma basu baro sashen nasu na maza ba da yake cen gefe guda da namu Amman da tazara sosai, juyowa nayi da gudu zan koma sashen namu wajen umman tawa, kuka nake bil haƙƙi da gaskiya ni a tunani na umman tawa ta mutu ne, karo naci da mutum ba tare da sanin ko wanene ba na shiga jan hannun shi, idona ya kulle, bana ganin kowa bana ganin komai, umma ta kawai nake kira, lokaci guda Naji an kama man hannuwa duka an riƙe aka shiga girgiza ni, "ke ki natsu, natsu nace, ki faɗa man me ya sami umman taki? Tana ina ne?" amon murya shi ta bugi dodon kunne na lokaci guda na wara idanuna akan shi, shi dai ne, Ya Ameen ne riƙe dani ni suhan, yana girgiza ni, hannuwa na duka cikin nashi, duk da firici da halin kuka da damuwa da nake ciki, bai hanani jiyo ƙamshin turaren shi ba da kuma taushin hannuwan nashi da suke cike da wani sanyi mai ratsa zuciya, "umma ta, ba zata mutu ba, Ya Ameen kaje ka duba man ita don Allah, bata numfashi, bansan haka ba da ban mata maganar ba, kada ta mutu ta bar ni ni ɗaya cikin gidan nan bansan kowa ba sai ita duk duniyar nan" Na faɗa cikin kuka ina mai durƙushe wa kan ƙafafu na, gami da sake sakin wani marayan kuka mai ban tausayi ga mai sauraro, durƙusa wa yayi shima gami da kamo dukkanin damatsan hannuwa na ya miƙar dani "is ok, ya isa hakanan, ba zata mutu ba insha Allah muje in ganta" ikon Allah, maimakon ni da ke jan hannuwan waɗanda nake son su taimaka man, wannan karin wanda yake son taimaka man ɗin ne ya shiga jan hannuwa na, kaman makaho da ɗan jagora haka yake janye da hannuwa na, duk da nasan babu kyau hakan, ina jin babu daɗi a jikina duk kuwa da halin da nake ciki, Amman banyi yunƙurin janye hannun nawa ba, saboda da taimakon shi ne nake tafiya, jikina babu kwari Sam, kukan da nayi ya sanya har wata juwa-juwa nake gani, ƙala bance ba, na shiga bin shi kaman wadda bata san hanyar ba, har muka iso bakin ƙofar ɗakin da yake danƙam da ƴan kallon umma ta, dukkan su ma'aikata ne, Amman babu wadda tayi yunƙurin zuwa kusa da umman tawa ma da take yashe a tsakar ɗakin, duk sun tokare wasu daga ciki, wasu kuma daga bakin ƙofar dakin, wannan ƙiyayya har ina? To fa! Turƙashi, Alhaji ƙarami ne riƙe da hannuwan Suhana yana janye da ita? Me hakan ke nufi? Ita har ta kai ma tsayin wadda Al'Ameen ɗin zai ruƙo ya shigo da ita har cikin ɗakin ta? Take redio masu amfani da jini suka fara naɗar ƙarya da gaskiya, darewa suka shiga yi suna bashi hanya tare da ƙoƙarin gaidashi, ko kallon inda suke baiyi ba, domin shima sun bashi matuƙar mamaki, sai dai Al'Ameen ɗin ba irin mutanen da ke shiga sabgar da babu ruwan shi bace, hannuwan nawa ya saki yayin da yake kamo na umman tawa yana mai ƙoƙarin jin pulse ɗinta. Miƙewa yayi tare da maida kallon shi kan mama talatin dake tsaye tana recording ɗin duk wani motsi namu a ɗakin ko babu komai yau Hajiya Babba da labari kenan. "Mama ku kamo ta a sanya ta a mota muje asibiti, bari in fiddo motar" ya faɗa cikin sanyi halin shi mai cike da miskilanci, maganar ma kaman baya son yi, sannan ya juya inda nake tsaye yana faɗin "Muje" a taƙaice, lokaci guda ya shiga takawa da niyya barin ɗakin. Har yanzu kuma kuka nake, sai dai sauti kukan ya ragu sai dai kwalla da taƙi ta tsaya, bin shi na shiga yi a baya har zuwa parking lot da yake cike da motoci na alfarma; motar shi da tafi kowacce haɗuwa a wurin ya shiga tare da juyo ta daidai saitin da nake tsaye, sannan ya sanya hannu ta ciki ya buɗe man ƙofar gaba ta mai zaman banza, ganin da yayi ina ƙoƙarin shiga baya, banyi musu ba na shiga na zauna ina mai share kwalla ta akai akai, daidai lokacin da mama Talatu da mama uwani suka kamo umma tawa kaman matatta suka buɗe baya suka sanya ta, ya fita ya gyara masu sannan ya umarci mama Talatu da take shugaba ta shiga mu tafi tare da ita, yayin da mama uwani ta juya zuwa sashen namu tana mai taɓe bakin an mata buƙulun shiga haɗaɗɗiyar motar da take ɗauke hankalin duk wani dake zama sashen masu aikin. Horn yayi mai gadi da fitowarshi kenan daga makewayi, ya rugo da gudu ya shiga wangale tangaman gate ɗin, lokaci guda yana mai ɗaga ma uban ɗakin nashi hannu, ( da yake Al'Ameen ɗin mutumin shi ne sosai da sosai) shima mamaki fal cikin ranshi, ganin suhan ɗin a gaban motar Alhaji ƙarami da mama Talatu a baya sai wata mata da take kwance da bai iya tantance wacece ba bayan motar kaman matatta, Allah dai yasa lafiya ya faɗa yana mai furzar da dattin asuwaki daga bakin shi sannan ya shiga rufe ƙyauren gate ɗin da take turawa da ƙarfi saboda nauyin shi. Motar ya harba bisa titi, yayin da ya ƙara speed ɗin motar, mu da muke cikin motar gani muke tamkar baya gudu, Amman a zahiri gaskiya gudu yake wanda ya wuce ƙa'ida ma, hakan ce tasa nake ganin nawar tashi kaman in ƙwace tuƙin nake ji. Lokaci lokaci yakan juyo ya ɗan kalle ni da nake ta sharar kwalla gami da jan majina a hankali, tin kafin mu isa asibiti yayi masu waya gashi da patien emergency, aikuwa muna isa aka turo ɗan gadon ɗaukar marasa lafiya tare da gungura ta zuwa emergency ward, ɗaga ƙafa nayi da niyyar bin bayan su suka dakatar dani ta hanyar ɗaga man hannu, wannan ne ya sanya hankali na ya ƙara tashi fiye na da baya, ganin umman tawa kaman gawa sai yanda aka yi da ita, sake durƙushe wa nayi wurin ina mai sakin wani tsumammen kuka da ya karaɗe ilahirin reception ɗin, Ya ilahi, na shiga furta wa a fili ina faɗin "Ya Rab sa'idnee ya Allah" mama Talatu bata yi yunƙurin zuwa inda nake ba, kaman yanda shi ma gogan naku bai yi yunƙurin hana ni ba, sai ma waje da ya samu ya zauna ya tsura man idanu yana mai ƙara nazari na, lokaci guda ya miƙe tare da nufi inda nake durƙushen cikin sakon tafiyar shi mai kama da ta saraki..... *Fans Kuzo kuci cake ɗin deedat, fa u are All invited* ~_Oum-Deedat ce_~ [8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~11~* **********'********************* Kusan yini afnan tayi mana ita dasu Ayan, tafiya tayi wajen ƙarfe shidda saura, bayan ta sake bani haƙuri, na nuna mata haba ya wuce ai babu komai. Ya Ameen bai dawo ba har misalin ƙarfe shidda da wani abu kuma umma ta bata farfaɗo ba, hankali na ne ya tashi, office ɗin likitan na koma ya ƙara kwantar man da hankali, cewa yayi lafiya lau idan ta farka zata samu ƙarfi sosai, da wannan ne na samu naji ɗan sauƙi, babu abin da ke tadani kusa da umman tawa sai salla, ko abincin da afnan ta sanya ni inci, kaɗan na ɗan tsakura, ita ma da taga ba zan iya ci bane sai ta haƙura ta ƙyale ni. Ƙarfe bakwai daidai ya shigo bakin shi ɗauke da siririyar sallama da ni ƙaɗai na jiyo shi, kaina da yake duƙe bisa gadon umman tawa na ɗago a hankali na ɗora idanu na akan shi, idanun mu ne suka sarƙe cikin na juna nayi sauri janye nawa, kujerar da nake zaune kai na miƙe gami da tura mashi domin ya zauna. Dakatar dani yayi ta hanyar ɗaga man hannu da na lura sana'ar shi ce, watau maganar ma wahala take bashi, da ido nake bin shi har ya zauna kan sofar dake ɗakin ƙwara ɗaya tal doguwa 3seater, "ya jikin umman? Har yanzu bata farka ba?" na tsinkayi muryarshi yana jefo man tambaya cikin muryarshi mai daɗin saurare, ɗaga mashi kai kawai nayi, domin har ga Allah kwarjinn shi na hana ni sukuni, ƙamshin turaren shi duk yabi ya cika man hanci." OK" ya faɗa cen iya leaɓɓa, zaro wayar shi yayi ya cigaba da latsawa kaman ma baya cikin ɗakin. Sallama aka yi, gami da shigowa baki ɗaya, Alhaji Mustapha ne da iyalanshi baki ɗaya suka iso ta ƙarƙashin jagorancin Afnan da tace ta san ɗakin, miƙewa nayi cikin hanzari tare da masu barka da zuwa na ba Alhaji Mustapha kujerar da nake zaune, Gaishe su na shiga yi su da Hajiya kubra da take tsaye gefen Alhaji cikin isa da taƙama, "lafiya" Hajiyar ta amsa mani tana mai nufar kujerar da Ya Ameen yake kai ta zauna, tana mai sakar mashi murmushi yaƙeda wani irin kallo mai cike da ma'ano ni daban daban; Shi kau Alhajin amsawa yayi cikin sarkin fuska, yana mai tambaya ta jikin umman tawa, amsa mashi nayi ina mai ɗan murmushi iya fuska ta. Aunty feena ce ta ja kujerar da na bama Alhaji domin ya zauna sai bai zauna ɗin ba, gaishe ta nayi itama ina mai sa hannu na ɗauki Nasreem da take saɓe a kafaɗarta, ta ko wangale man baki tana wasa da hijabin jikina, Amsawa tayi cikin sakin fuska da har saida ta bani mamaki, (Lallai mai ɗa wawa inji Hausawa) jikin umman tawa ta tambaya na amsa mata kaina duƙe ina ɗan yaƙe, Allah ya bata lafiya, da Allah ya kyauta ta shiga yi man, Ameen mun gode na shiga jerawa Afnan da Ayan ne suka nufi wajen Yayan nasu tin shigowar su, dama ita ta hannun daman shi ce, Nihal ce ta dire wata ƙatuwar ledar da suka shigo da ita a hannu suna ta cin magani ko tanka man ba suyi ba, balle kuma in samu arziƙi tambayar jikin umman tawa, Angode na shiga faɗi lokacin da Alhajin ya ke faɗa man su zasu wuce Allah ya bata sauƙi. Da ameen na bishi ina mai masu rakiya har bakin ƙofar motar da suka zo da ita, wata danƙareriyar mota ce duk yawan su ta kwashe su tsaf, gaskiya motar ta haɗu iya haɗuwa, Nidai ba zance ga sunan motar ba, Amman Alhajin ne da kanshi ke tuƙawa. Hajiya Kubra ce ta kalli ɗan nata cikin wani yanayi na ɓacin rai Amman tana ƙoƙarin dannewa ne saboda kada Alhaji ya gane "Son ko zaka zo muje ne? Zamu yi ma su Hajiya siyayya ne gobe insha Allah zamu tafi cen mu duka muyi masu week end" ta faɗa tana mai gyara zama ta cikin motar, "No mom ina da uziri yanzu gaskiya, akwai inda zanje mai muhimmanci, zamu haɗu gida wajen dinner kawai" ya faɗa a dake cikin miskalancin shi, lokaci guda yana latsa wayar shi kaman ma ba da mom ɗin tashi yake magana ba; saboda ya kula da hajiyar ko jikin umman tawa bata tambaya ba, hakan bai mashi daɗi ba kuma ya kula ko Alhajin nasu ma hankalin shi bai kai wajen ba. "OK Al'ameen kayi ƙoƙari dai ka dawo kafin diner ɗin saboda zamu tattauna yanda tafiyar zata kaya" aAbban nashi ya faɗa cikin murmushi yana mai tada motar tashi, Saboda ya ji daɗin yanda ya iske Al'ameen ɗin a asibitn, ko babu komai ya san zasu samu kulawa da ta dace, kuma ya san tausaya war ɗanɗan nashi ga na ƙasa dashi. Juyawa muka yi ni da Ya Ameen ɗin muka shige asibiti n akan idon Hajiya Kubran, Cikin ɓacin rai da hajiyar ta kasa dannewa ta shiga faɗa tana faɗin "Amman Ahaji hakan ya dace ace kaman Al'ameen yana zaune suna jinyar ƴar aiki tare wannan yarinyar? Haba Alhaji, ya kake maida mu baya ne? Gaskiya Sam banji daɗi ba, iske shi fa nayi zaune hankalin shi kwance, shi ko iskar da take tasowa daga jikin su ma bai ji gurɓatacciya ce" Alhajin ne ya Dakatar da ita cikin ɗan ɓacin rai da yake ɗan taso mashi na halin Hajiyar "Ya isa Hajiya, kibar wannan maganar, wannan shine abun da ya dace kowanne shugaba yayi, na tsayawa tsayin daka ya tabbatar da lafiyar duk wani da yake aiki ƙarƙashin shi, ina Alfahri da Ameenun yana abunda yake dacewa" ƙutawa tayi cikin ɓacin rai da ƙudurce ɗaukar mataki akan al'amarin. Afnan da take cen baya sai zumɓura baki take yi tana ƙunƙuni, Saudat ɗin ce ta hamɓare ta gami da cewa "village gal, ai dama ke kullum kina bayansu kullum" Aunty Feena ce ta dalla mata harara gami da cewa a hankali "kedai kin cika baƙin hali Saudat" Shigarmu ɗakin yayi daidai da farfaɗowar umman tawa ta shiga motsa hannun ta gami da ƙoƙarin buɗe idanun ta. Cikin hanzari muka isa bakin gadon a tare, gami da furta sannu umma, lafiyar ki ƙlau? "Jiddah! Jiddah, kina ina? Matso nan Suhan, hannuna na saka cikin nata ina mai murmushin farin ciki da ke taho wa da ƴar kwalla ta," Gani umma, gani kusa da ke" na shiga faɗi ina mai durƙusa wa na ranƙwafa daidai kan ta ina mai rungumo ta cikin jikina "Hauwa'u ki yafe man kinji, na hana ki cikar burin ki, ki kira Alhaji ƙarami ki ce mashi na yarda da karatun ki, kiyi haƙuri da sannu kuma zaki san su wanene dangina, ahalina kuma, kiyi ma su Hajiya biyayya su ɗin iyayen ki ne, amanar ki na hannun su ko da bani da rai" ta ke faɗa cikin zafin ciwo idanu ta na a kulle har yanzu Kuka na fashe dashi ina mai furta "umma ni zaki yafe mawa, nice sanadin tashin ciwon nan naki umma, kiyi haƙuri umma, na dena tambayar ki komai wallahi insha Allah" Runtse hannuwa na tayi cikin nata tayi shiru a hankali tana mai sauke numfashi a hankali a hankali da gani bacci ne ta samu. Kasaƙe yayi yana ta kallon uwa da ɗiyar tata cikin tausaya wa ta ɓangare guda kuma yana mai sakin Sirrin murmushi har dimple ɗinshi ya loɓa, Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaga umman ta samu bacci, ko ba komai zai samu sauƙi da zuciyar shi take yi mashi na kukan da afnan ɗin take yi, ya tsani kuka, ya tsani kuka masalan na mace mai rauni, yanzu zai ruɗe ya rasa inda zai sanya kanshi. Tasowa yayi a hankali,, ya tako har zuwa gaban gadon da ya koma ya zauna bayan da yaga ɗiya da uwa suna magana cikin shauƙin so, ledar da Nihal ta ajiye ce ƙasa gaban gadon umman tawa ya shiga buɗewa, kayan ciki ya shiga fiddowa a hankali a hankali, yana jera su bisa kyakkyawa locar da take ajiye gefen gadon, kayan tea ne, sai ruwan gora, da plax sai mug na shan tea, sai kayan marmari da su cake da sauran kayan ciye ciye da marar lafiyar zai iya buƙata. Da gani dai wannan siyayyar ta abban shi ce, dan ko kusa ya san halin mom ɗin tashi ba zata iya tsayawa yima ƴan aiki soyayya ba. Sai da ya tabbatar da ba zasu buƙaci komai ba sannan yayi mata sallama a gajarce ya fice yana mai ja masu ƙofar, da idanu na bishi har ya wuce, tabɗi Ya Ameen Matarka zata sha miskilanci na raya a rai na ina mai miƙewa domin komawa inda ya tashi dan in samu in miƙe ƙafa ta, da kallo na shiga bin wajen da ya tashin, kaman yana wajen zaune, ƙamshin turaren shi yana nan liƙe kaman nan ya fesa shi, ajiyar zuciya na shiga sauke wa a hankali a hankali ina mai furta Alhamdulillahi! ****************************** Bai shiga babban part ɗin ba saida ya koma nashi yayi wanka ya kintsa sannan ya nufi part ɗin hajiyar cikin takon shi kaman na saraki; Sallama yayi ya shiga, duk sun hallara a dining table suna cin abincin da sai dai aka yi ma mama Talatu umarni da ta girka shi ita da mama uwani, kujera ya ja guda ɗaya ya zauna saitin abban nashi, Mug ya ɗauka gami da haɗa cofee, domin bai jin zai iya cin komai a wajen, tsaftar umman Suhan ɗin ce kawai ya yarda da ita. A hankali ya ke shan cofee ɗin yayin da Alhaji yayi gyaran murya duk suka maida hankali su akan shi, " Gobe idan Allah ya kai mu zamu tafi kankiya, kaman yanda muka saba in mun yi haɗuwa irin wannan, Hajiya ki rubuta list ɗin abubuwan da za'a buƙata da wanda za'a kai ma su Baba ɗin, sannan ku Saudat da Nihal sanin kanku ne cewa idan muka je sai anyi maku maganar fidda mazaje, idan kuna da tsayayyu ku tura su cen kankiya su gaida kakannin naku kafin mu taho, zan yi ma yaya Auwalu magana sai yazo su gaishe su tare, sannan kai kuma Al'ameen idan an amshi list ɗin ka tabbatar ka haɗa komai cikin daren nan dan ina kyautata zaton da safe zamu wuce don na riga nasa anyi booking flight. Ina fatan babu mai magana ko?" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran da take zaune tana ta cika tana batsewa," Alhaji shi Al'ameen ɗin baka ce ya fidda mata ba, don na gaji da ganin shi zaune haka nan, tsararrakin shi har sun yi aure, wasu ma harda ƴaƴa, don haka shima yayi gaggawa fidda wadda yake so, in mun duba munga cancantar ta, sai a haɗa bikin da na su Saudat kawai" Ɗan murmushi Alhajin yayi yana mai maida kallon shi kan Al'ameen ɗin da ya kafe mom ɗin tashi da idanu yana ɗan murmusawa, shi da ya gano ta, watau tana gudun ya so yarinyar cen dake asibiti tare da maman ta, humm Hajiya kenan, yana fatan Allah ya shirya da mom ɗin tashi ta gane annabi ya faku, koma dai minene shi dai ai ba za'ayi mashi auren dole ba, ba kuma za'a ƙayyade mashi lokacin auren shi ba, duk tsiya dai sai ya samu wadda tayi mashi, kuma har yanzu baya tinanin ya dace, duk cikin ƴan matan da suke cewa suna so shi, shi fa ba suyi mashi ba, bai yarda da natsuwa da inganci shi ba, don duk irin ƴaƴan hamshaƙan masu kuɗi ne, masu ɗabi'a irin ta mom ɗin tashi watau wulaƙanta na ƙasa dasu, Sam basu san babu ba basu kuma san daraja ɗan adam ba, abin da umman tashi bata sani ba shine, duk wacce ya auro cikin su ya kawo mata ba zasu taɓa daidaitawa ba, saboda halin su ɗaya ne, isa, taƙama, izza da son mulki, wa zai bi wani? Murmushi ya ƙara saki daidai lokacin da yaji Dad ɗin nashi na faɗin "Tau kaji fa Son, Mom ɗin ka na nuƙatar suruka" "Amman sai inga ai shi namiji ne ya kwantar da hankalin shi ya zaɓo wadda tayi daidai da ra'ayin shi, kada ya je yayo zaɓen tumu dare, kinsan matan yanzu ɗin yanda suke" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran. "Haka ne Alhaji, sai ya duba cikin lokaci, in bai yi yanzu ba, sai yaushe? Ko so yake ayi mashi tare da Afnan ne? " Ta faɗa tana mai goge baki da soft tissue dake ajiye gefe da gefen dining table ɗin, miƙewa tayi tare da faɗin Al'ameen ɗin ya biyo ta domin su rubuta Abunda za'a buƙata tare, gami da ficewa ta haye sama nata. Al'ameen ɗin ne ya bita a baya, tare suka isa falon yayin da ta wuce bedroom ta ɗauki wata jotter mai kyau ta zauna ta shiga zana abubuwan da za'a buƙata cikin isa da taƙama, yayin da suka baro Alhaji Mustapha ɗin da sauran ƴaƴan nashi yana jin damuwoyin su, domin shi mutum ne mai yawan jiɓintar Al'aamarin iyalan nashi, dama kuma haka ake so, haka ya kamata ace ko wanne mai gida yana ma iyalanshi, komin girman shi kuma komin matsayin shi. Bayan Hajiyar ta gama rubuta komai ne ta miƙa mashi, gami da cewa ya duba in da wani abu sai a ƙara, dubawa ya shiga yi cikin halin ko in kula da isar da mahaifiya tashi take ta zubawa, babu komai ya faɗa mata gami da miƙewa don barin ɗakin. Dakatar dashi tayi, tare da ce mashi ya zauna zasu yi wata magana ne, zaunawa yayi bisa sofar dake kusa da tata ya bata dukkain natsuwar shi, domin shi mutum ne mai biyayya da son gamawa da iyayen nashi lafiya, shiru ne ya biyo baya na ƴan dakiƙu, domin ta san abun da zata zo ma ɗan ɗan nata ba lallai ya ɗauka ba domin ita ta haife shi, ta san halin shi sarai. "Al'ameen watau na lura ka fiye shiga Al'ameen Suhan da maman ta, bana so fa raini ya shiga tsakanin ku, kuma da me suka fi sauran ma'aikatan gidan nan ne da kafi basu cikakkiyar kulawa, ko dan Kaga mahaifi ka ya ɗaure maka wutsiya ne? Tau fa ka sani ni bazan lamunta ba, tinda Alhaji ya ce a ƙyale su da aikin gidan, da ta samu lafiya ka faɗa masu su tattara su koma cen inda suka fito tinda ba zata faɗi ainahin daga ina take ba ita daƴar tata, kuma ina so ka samo mana kuku cikin ma'aikatan company ɗinka guda biyu, wanda ka san sun ƙware sosai, saboda Sam girkin talatun nan baya man daɗi" ta faɗa cikin muryar ta, da ta koma ta mulki gaba ɗayanta. "Mahaifiyar tashi ya tsura ma idanu har saida ta kai aya, ba tare da ya katse ta ba, sannan ya muskuta ya gyara zama," Mom ina so ki sani, ni duk cikin ma'aikatan nan babu wanda na fifita, duka matsayi su ɗaya ne a wuri na, mom rashin lafiya tafi gaban komai, kuma ko da sun bar aiki, bana da hurumin korar su, kin manta ne dad yace gidan shi ne? Kuma ya basu izinin zama har zuwa lokacin da suke so, ko kuma suka gaji dan kansu, babu wanda zai hana su tafiya, so mom ina ganin wannan maganar yafi da cewa ku tattauna ta da dad, duk hukuncin da ya yanke a kansu is better" ya faɗa kan shi tsaye, domin Al'ameen ɗin mutum ne da yake kai tsaye, watau babu munafunci ko ɓoye-ɓoye a al'amurran shi. Sannan ya cigaba da faɗin "maganar kuku kuma zan magana cikin ma'aikatan sai a turo su ko zuwa da safe ne" ya furta cikin salon miskilanci shi, tare da miƙewa ya bar ɗakin ranshi a cunkushe, bai san sai yaushe ne mom ɗin tashi zata bar halin ta ba, bai koma gidan ba ma ga baki ɗaya sai da ya tabbatar ya haɗa komai da aka bashi list, sannan ya kai ma Aunty Feena, domin yin packaging ɗinsu ko wajen mom ɗin tashi bai koma ba ya wuce part ɗinshi kai tsaye. Yana kai kafaɗar shi bisa gadon nashi, tinanin su yayi mashi sallama, kenan umman tata ta bata dama domin tayi karatun? To ko Dad ɗin yayi mata magana ne? Allah sarki umma baiwar Allah, har yanda take ma ba cikin hayyacin ta ba, maganar ta Suhan ɗin tabi iyayen shi, abun da shi kuma Mahaifiyar tashi ta gaza fahimta, me suka tsare mata? Menene ɓata fi su dashi ba? Koda yake ya lura akwai ƴan zuga cikin Al'amarin, dole ya taka masu burki, dole ya gargaɗe su indai suna son zama cikin gidan, ba zai lamunci munafunci da haɗa husuma ba, hakanan su sanya ma bayin Allah karan zuƙa ba tare da sunyi masu wani abu ba daidai ba. Yayi Alƙawarin taimaka ma Suhan ɗin domin jin ta yake kaman Afnan ɗinshi, da ƙaunar da Afnan ɗin ke mata da sanyi halin ta da kuma tarbiyyar da ta samu daga wajen umman tata, sai kuma halin da suke ciki da musguna masu da Mahaifiyar tashi ke yi, su suka ƙara mashi ƙaimi wajen ganin son ya taimaka masu bil haƙƙi da gaskiya, baya jin wani abu dangane da Suhan ɗin illa wani narkon tausayinta da ke malala cikin zuciyar shi, yarinya da ita, ba tafi shekara ishirin ba Amman tana fuskantar wannan waƙi'ar, wannan halin da suke ciki kan ƙara jefa zuciyoyin su a damuwa da shi kuma baya jin zai iya lamunta. A haka ya samu bacci ɓarawo ya sace shi, zuciyar shi fal da tinanin halin da umman ta Suhan ɗin take ciki. ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~12~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Washe gari kuwa tin da safe kowa ya shirya a gidan, wannan umarnin Alhaji Mustapha ne domin yana so su isa da wuri domin ticket ɗin safe aka samu, aika Afnan yayi tayi kiran Ya Ameen ɗin da shi kaɗai ake jira bai fito ba, sai gashi kuma cikin takun shi na ƙasaita da sanyin shi da kan ƙara mashi kwarjini a fuskar jama'a Sanye yake cikin wani lallausan yadi kalar sky blue, an mashi ɗinki Abuja style, da gani dai yana son ɗinkin, rigar iya rabin cinya ta tsaya bata kai guiwa ba, hakan ya ƙara fiddo da asalin kyawon halittar da Allah yayi mashi, kan shi babu hula sai dai gyaran fuskan da kan ƙara ƙawata fuskar tashi. Takalmin shi da hankachip ɗin da ke hannun sau ciki, shi duk kalar kayan ne sai zuba ƙamshi yake yi. Cikin ɗan sassarfa ya isa ga Lahajin dake tsaye da alama jiran shi yake yi ya fito. Gaida dad ɗin nashi ya shiga yi cikin girmamawa, yayin da Alhajin ya miƙa mashi hannu don suyi musabaha, na daga cikin halin Alhajin ne sauƙin hali da sauƙin kai, hakan kan ƙara mashi shaƙuwa da ƴaƴan nashi fiye ma da mom ɗin tasu. Matsawa yayi ga Hajiya Kubran da fitowar ta kenan cikin shigar wani ɗanyen boyel mai taushi da walƙiya, ɗan rungumo ta yayi cikin murmushi mai ƙara ƙayata kyakkyawar fuskar tashi, amsa gaisuwar tashi ta shiga yi cikin jin daɗi da ƙauna ga ɗanɗan nata, duk da bata manta ƙin yarda da maganar tata da yayi da a daren jiya, Amman ta bar ma zuciyar ta, ta kuma sha Alwashin ganin zargin ta da hasashen nata bai zama gaskiya ba. Sauran ƙannen nashi suka shiga gaida shi yayin da ya duka yana ma Nasreem wasa da miƙa ma Ayan hannu sukayi musabaha yana mai gaida yayar tashi cikin sakin fuskan da sai yana cikin family ɗinshi ne kawai zaka ganta. Shafo kanshi tayi tana faɗin "Brother fatan ka tashi lafiya" ta faɗa cikin murmushi da kan ƙara nuna tsantsar ƙaunar ta ga ƙanen nata. Alhaji Mustapha ne ya kauda masu gaisuwar da suke yi cikin cewa "Al ameen ina ganin ya kamata mu zo mu wuce ko kasan da ƙarfe 08:00am ne lokacin tashin flight ɗin. ɗan sosa kan shi ya shiga yi da ɗan makullin motar shi da ke hannun shi sannan ya shiga faɗin" Dad ina ganin ni ba zan biku ba sai dai ko zuwa gobe ko jibi ne zan iske ku cen ɗin, saboda aikin construction ɗin nan naga yana neman tsayawa, Eng ɗin ne naga yana san sanya shiririta dan yaga na cika mashi cikon kuɗin shi, and Bilal ma yace man yau zai iso ina jin ma sun taso yanzu, Ga kaya da kamfani zai fitar yau ina so inje ayi komai gabana, kasan yanzu rashin gaskiya ta yawaita" ɗan murmusawa Alhajin nashi yayi, sarai ya fahimci Ya Ameen ɗin baya son bin nasu ne, May be dan yana gudun maganar da Hajiyar tasu ta taso ita ne jiya, tana iya zuwa ta zuga Granny Zuwaira akan zancen; ɗan ƙara murmusawa yayi yana faɗin " is ok Al ameen Amman wanne kamfani ne zai fidda kaya yau?" (Domin Al'ameen ɗin shine manager ɗin duka kamfanonin Alhajin duk da shima yana da nashi) "Eh sabon na costimetics ɗin nan ne" Ya shiga faɗi da ɗan guntun murmushi akan fuskar shi yana mai son Alhajin nasu ya yarda da uziri nashi, "Tau ba matsala for now, Amman dai ina fatan zaka je cen ɗin cikin lokaci, Kaga ka kwana biyu ba kaje ba, duk da kuna waya, ya kamata kaje kaima Kaga lafiyar kakannin naka" "to Dad" ya bashi amsa yana mai buɗe mashi gidan baya ya shiga ya zagaya ya buɗe ma Mom ɗin tasu, da bata ƙara tankawa ba don duk ya tushe mata plan ɗin nata, amman ba komai, ai bata ma jin sai tayi kamun ƙafa da wani akan al'amari yaron nata, duk isar ta da dukiya ta, ita ta haife shi in ya san wata ai bai san wata ba; Mota biyu sukayi ɗaya Alhaji Mustapha da Hajiya kubra sai driver kawai, sai kuma ɗayar da ta ɗauke Aunty feena da yaran nata sai Saudat, Nihal da kuma Abie da ya hakimce a gaba. Kai tsaye motar shi ya nufa, bayan yaga ficewa mitocin daga cikin harabar gidan nasu, restaurant ya fara tsayawa ya siya abun break fast sannan ya wuce Asibiti da ya kwana tinanin su duk da son kauda tinanin nasu da yake yi daga cikin ran shi, sai dai baya iyawa, sau da dama shi karan kanshi kan shiga tinanin kan shi da kanshi, tabbas ya san yana tausayin na ƙasa dashi, da marasa galihu, da ƴan aikin nasu, tau sai dai yana mamakin kan nashi, su salon yanda yake tausaya masu ma daban ne, amman ya kan alaƙanta hakan ne da rashin lafiya da take damun Maman Suhan ɗin. Sallama yayi daga bakin ƙofa, tsam na tashi daga kan kujerar da nake duƙunƙune tin bayan da na gama sallar asubahin na kuma komawa na kwanta domin in ɗan rutsa, don cikin dare umman tawa ta farka, cikin ƙarfin hali irin nata har fira muka ɗan taɓa tana kara jaddada man maganar karatun nawa, da kuma roƙo na akan in bama dukkan Abunda zan gani a rayuwa ta ta gaba baya. Daga ciki na buɗe mashi, ina mai janyewa na bashi hanya domin ya wuce. Kai tsaye ya shiga har bakin gadon umman tawa, yana mai ajiye manyan ledojin take away da yayo mana; ɗan rankwafawa yayi daidai saitin gadon umman tawa, yana mai kallon bugawar lumfashin ta. "ta samu bacci ne?" ya jefo man tambaya yana mai janyo kujerar gefen gadon ya zauna idon shi cikin nawa, "Eh ta samu bacci, Amman ta farka cikin dare jikin da sauƙi, don har ma fira mun yi" na faɗa ina mai ƙoƙarin janye nawa idanu, tinani na ke yi, shi wanne irin mutum ne? Mutum mai daraja irin ta Ya Ameen da ba ko domin arziƙi shi ba da na iyayen shi, shi mutum ne daban ko cikin matasan garin na Abuja akeji dashi, shine yake bamu kulawa haka? Gaskiya ya cencenci a yaɓa mashi, ya cencenci a girmama shi, da dukkan iyawa. "Hop dai bata wahalar da kanta ba wajen magana? Kin dai san dokar likita, ki dinga kula" ya faɗa yana mai kauda idanu shi daga gare ni da har yanzu nake rakuɓe daga bakin ƙofa, kwarjini shi baya bari in sake a duk lokacin da nake gaban shi. "To zan kula insha Allah" na faɗa a hankali iya fatar baki, miƙewa yayi cikin halin ko in kula da tsayuwar da nake tayi, sannan ya shiga faɗin "Dictor ya shigo?" Lokacin da ya shiga ta kowa a hankali zuwa ga bakin ƙofar domin ficewa, amsar da na shiga bashi ce ta sanya shi ja ya tsaya ga barin ficewa, hakan ce ta sanya muke tsaye gaf da gaf, duƙar da kaina na shiga yi, bazan iya jurar haɗa idanu nashi ba, idan ma zan kula da jikina wata ƴar kyarma nake yi a hankali, me ke damuna ne ni Suhana? "Bai shigo ba yaya, Amman Nurse ta shigo sannan tace idan ta farka a bata abinci mai sauƙin nauyi, sannan mu kira ta, in kuma likita shigo shikenan" "Is OK Let Me Check On Him" Ya faɗa cikin salon turanci shi da yake kama da na turawan amurka da nake kallo a Tb ɗin babban falon gidan, ficewa yayi cikin salon tafiyar shi ta jarumin namiji, idan yaso komai cikin zafi zafi yake yin shi, idan kuma yaso kai kace wahainiya ce ke tafiya masalan ma idan yana jin ƴan miskilancin. Office ɗin likatan ya shiga yayi daidai da isowar shi kenan Dr Ashafa ne yayi azamar miƙa mashi hannu yana faɗin "Yallaɓai ba dai har ka shigo ba? Gaskiya waɗannan patient ana ji dasu, Fatan dai jikin na maman tamu da sauƙi? Ya faɗa cikin murmushi da san ɓoye wani abu acikin ran shi;" Zamu iya zuwa ka duba Dr saboda ina so idan jikin nata ya samu sauƙi kayi discharge nasu, zanyi tafiya ne kuma bana son barin su anan babu mai kula dasu, gara su koma gida" ya maida ma da likita amsa cikin ɗan ɗaure fuska, bai san me Dr ɗin ke nufi ba, Amman ya kula tin jiya da yanda yake kallon Yarinya da take ta fama da jinya mahaifiya tata, ko menene ma nashi na damuwa? "OK to shikenan muje rana ya daɗe" likita ya faɗa yana mai ɗan sanya shakku a ranshi, Amman dai koma minene ai zai fahimta, gaba Al'ameen ɗin yayi Dr Ashafa ɗin yana biyo shi a baya tare da kayan aikin su na likitoci Sake shigowa naga sunyi shi da likitan, watau sai da ya kira likitan kenan? Haka na cigaba da rayawa a rai ina mai janye idanu a ga barin kallon su, bakin gadon suka ja suka tsaya, hakan yayi daidai da farfaɗowar umman tawa. "Ƴan mata zo ki taimaka ma umman ki ta tashi zaune kinji, zamu auna ta ne" likitan ya faɗa yana mai waiwayowa ya kalle ni da nake zaune ina aikin binsu da idanu da nayi nayi ga barin kallon su Amman na kasa, Ya Ameen ɗin yayi kyau, wani abu ke taso man cen ƙasa rai duk lokacin da ya bayyana inda nake, tasowa nayi a hankali na kama umman tawa ta zauna sosai, shi kau gogan ko kallo na ma bai yi ba, kaman ma bai san ina ta wurin ba, ya koma mani Yaya Al'ameen ɗin da na sani tin cen baya, da baya ɗaukar wargi, fuskar shi Sam babu walwala saɓanin yanda ya fita ba daɗewa. Aune aunen su na likitoci ya shiga yi, sannan ya ɗago yana mai faɗa ma Ya Ameen ɗin komai normal, za ta iya cin komai, kuma ta kula da shan maganin ta akan lokaci, zamu iya tafiya gida, Amman nan da sati ɗaya mu dawo a sake gwada ta a gani, dokoki sosai aka shinfiɗa ma umman tawa, sannan aka hana ta cin wasu abubuwa da dama; wayyo likita, bai san ma abincin sai wanda aka ga dama aka bamu ba, in kace ba zaka ci ba sai yunwa ta kashe ka babu mai sani. A haka na kama umman tawa muka fito, bayan motar na saka ta, ta ɗan kwanta na koma na kwaso sauran kayan da suke mallakin mu, har da take away ɗin da yayo mana da ko kallon shi banyi ba, balle in buɗa inga Abunda ke ciki. Har zan shiga bayan ya tsattsare ni da idanun nan nashi masu rikita dani, sannan ya mani alama da in shiga gaba, haka kuwa aka yi shiga nayi na takure, masalan ma ga umma ta acikin motar kuma idanun ta biyu ba bacci take yi ba. Kai tsaye naga mun nufi hanyar kasuwa, ban da hurumin tanka wa balle in tambaya me zamu yo a kasuwa, ƙila uzirin shi ne zai kai shi; parking yayi bakin tanƙamemen suoer market ɗin da yake bakin kasuwar, fita yayi ya shiga ba dadewa sai gashi ya fito yaron shagon na biye dashi a baya, hannun shi niƙi niƙi da kaya, but ya buɗe mashi tare da Sanyawa ya rufe, ya zagayo ya tada motar muka shiga cikin kasuwar, nan ma soyayya yayi sosai, cikin ni da umma ta babu mai tankawa, kowa da abunda yake saƙawa cikin rai. Gida muka nufa kai tsaye, yayin da yake parking ya yafito mai gadi da hannu, cikin hanzari ya iso inda muke ƙoƙarin fitowa daga cikin motar; umarni yayi mashi da ya kira mama talatin a sashe namu na masu aiki, aiko ya ruga cikin hanzari, sai gashi da mama talatun ta taho cikin sauri, umarni yayi mata da ta kama man umman tawa mu kai ta ɗaki mu kwantar, yayin da ya kirayi mai gadin da isa da yake tsaye yana gyaran flowers da suka taimaka wajen ƙayata gidan, kayan yace su kwashe su shigar mana dashi cikin ɗakin mu, yayin da ya ja motar shi yana mai barin gidan. Kai tsaye ɗakin namu muka nufa da umman tawa da take ɗan iya taka wa a hankali a hankali, kwantar da ita muka yi, yayin da su isa suka shisshigo mana da kayan namu suka fice suna ma umman tawa sannu da Allah ya kyauta, ina kallon mama talatun tana jinjina kai tana mai ƙare ma niƙi niƙinbkayan da ta gani tare da mu, ta dai san wannan aikin Alhaji ƙarami ne, wato dama ya ƙi bin su Hajiya Babba ne domin ya tsaya bauta mana kenan ko? Wai menene haɗin shi da mu ne? Su dai basu ga wata alama da ke alamta masu akwai wani abu tsakanin Suhana ba da Alhaji ƙarami ɗin balle ace dan ita yake yi? Koma minene zata yi ƙoƙarin sanar da hajiya ɗin, me hakan ke nufi ne? Ya kamata hajiyar tayi wani yunƙuri akai wallahi, ita ta ma ga sanyar Hajiyar wannan karon akan yanda ta santa da in ta ƙi abu duk yanda zata yi akan taga bai faru ba ta sani, tana cike da tsantsar mulki da kuɗi, naira shegiya ce, mai maida tsoho yaro ta maida yaro babba. (Humm🤔🤔 Ya Allah kayi mana tsari da Hassada, ƙyashi, ganin gari da munafunci ameen ya Rab🤲🏻) Bayan duk sun fita ne, na gyara komai a ɗakin na adama komai inda ya kamata, kayan ciye ciye ne da basu da illa ga masu ciwon zuciya irin wanda likita ya bada umarnin aci, su ne ya kwaso mana su sosai da sauran kayan buƙatu har da kayan marmari ma da zasu yi ma mai rashin lafiya daɗin ci, gyaran ɗakin nayi nayo wanka na shirya kaina cikin baƙar doguwar riga mara nauyi na tattara gashi na na ƙulle cikin ribom sannan na ɗaura ɗan kwalin rigar a bisa kai na, nayi kyau daidai misali, sannan na ɗauko ledar take away ɗin da yayo mana tin asibiti na buɗe da niyyar zuba mana muci ni da umma ta, lafiyayyen chips ne da plantain, sai soyayyen ƙwai da miyar kayan ciki, sai ƙamshi take har yanzu da sauran zafin shi, saboda mazubin na glass ne, da gani dai abincin zai yi tsada, sai dai baya cuwuwa ga umma ta saboda farin mai da aka yi using wurin suyar, kaina kaɗai na zuba mawa na fidda sauran ga ƴan uwa na ma'aikata da har yanzu sun gagara shigowa yi mana koda sannu saboda tsabar hassada, Abunda na san zata iya ci wanda likita bai hana ta ci ba na zuba mata, saida na tabbatas taci na ɓalli maganin ta na bata tasha sannan na gyara mata kwanciyar ta, na koma gefen katifa na zauna ina ya ƙunar abincin ahankali Fira mukeyi jefi jefi da umman tawa da take bina da kallon tsantsar ƙauna ga ɗiyar tata, addu'a dai kam Al'ameen ya sha ta daga bakin umman tawa, godiya take jerawa wanda hakan ne ta sanya ni ɗan murmusawa a hankali dai ina ci gaba da cin abinci na; Sallama yayi daga bakin ƙofar ɗakin yayin da umma ta ta bashi izinin da ya shiga daga ciki, lokaci ɗaya tana mai umartata da shinfiɗa mashi darduma. Kasa tashi nayi, domin jikina babu hijabi babu gyale, gashi rigar mai bin jiki ce ta fidda duk surar jikin dake Sanye da ita, kuma a zahiri bai kamata ya ganni haka ba, saboda shi ɗin ba muharrami na bane, hakan ce ta sanya na shiga bin ko ina na jikina da kallo kaman mai son gano wani abu. "Hauwa'u dake fa nake magana fa, nace ki shinfiɗa mashi darduma ya zauna kin bar shi tsaye" umman tawa ta faɗa tana mai yunƙuri tashi, a haka ta samu ta zauna daidai domin Nidai na gagara koda motsi balle in taimaka mata har ma nayi mashi shimfiɗar Hankalin shi ya maida kanta da take ajiye plate ɗin abincin kaman mai tausayin ƙasar, ta shiga miƙewa a hankali, lura da yayi da Abunda take ɓoyo ko ji ma kunya ne ya sanya shi kauda kanshi gefe, ya maida hankalin shi kan umman tawa yana mai ɗan sakin guntun murmushi iya laɓɓa, ko me take ɓoyo? Wannan mitsitsiyar yarinyar ma, da yake kyautata zaton garin jiki ne ya kwashe ta, ita har tana ganin ma ta cika ta kai mace, ƙara murmusawa yayi daidai lokacin da take shinfiɗa dardumar ɗan nesa kaɗan da katifa tasu. "Nagode" ya faɗa iya maƙoshi maganar tana mashi wahala, yana mai zama ya tanƙwashe ƙafafun shi irin zaman salla, lokaci guda yana mai gaida umman tawa, cikin sakin fuska ta amsa mashi, sannan ya ƙara mata ya jiki da Allah ya sauwaƙe. Godiya ta shiga jera mashi da kuma fatan nasara da cigaba a rayuwa, harma da iyayen shi, hakan ce ta sanya shi jin daɗi, yana mai ƙara ƙaunar matar da son taimaka mata da duk ahalinta. Ikon Allah, abikan aikin mu da tin ɗazu suka kasa leƙowa su ga jikin umman tawa su gaida ta, sai gashi ɗaya bayan ɗaya yanzu da suka ga shigar Ya Ameen ɗin ɗakinmu suna shigowa gaida ta da ganin ƙwam, kowa ya fita kuma sai ya ƙara da abin da ya gani gaba. Sake natsuwa yayi yana mai ɗan yin gyaran murya a hankali, sai da ya maido kallon shi inda nake rakuɓe bisa katifa gefen umman tawa, sannan ya saki wani ƙayataccen murmushi ganin ta sanya hijabi da shi bai ma kula da lokacin da ta ɗauko shi ba, haƙuri ya shiga ba umman tawa, da mata Alƙawarin hakan ba zata sake faruwa ba, ya faɗa mata afnan ce ta sanar dashi komai; ɗan faɗa umman tawa ta shiga yi tana faɗin hajiyar ta isa ne ya sanya tayi masu faɗa, ai ba wani abu bane, gyara ne take so ayi, kuma mun ɗauka insha Allah. Haƙuri ya ƙara bata sannan ya shigo mata da maganar makarantar tawa, ta bacin yardar ta ta ƙara bashi, sai dai tana mai shawartar shi da yayi komai a hankali kada ran hajiyar ya ɓaci, ya alƙawarta mata komai ya wuce kuma babu abin da zia faru insha Allah. Maida kallon shi yayi yana mai cewa "Ki ɗauko man takaddun naki in gani ko, don mu san ta yanda zamu ɓullo ma al'amarin" ya faɗa yana mai kauda idanun shi daga kaina kaman ma ba dani yake magana ba. Miƙewa nayi cikin ɗan sanyi gami da nufar wardroop ɗin tawa, gami da janyo ƴar ƙaramar folder da takaddun tawa suke na miƙa mashi. Amsa yayi yana dubawa, mamaki fal a ranshi na yanda yarinyar take da ƙoƙari, gashi dai makarantar masu hannu da shuni tayi, saboda Alhaji Mustapha ne ya sanya ta a makarantar har ta gama, kafin abubuwa sukayi mashi yawa ya tafi wani aiki ƙasar Indiya daidai lokacin da Jarabawa tasu ta fito wannan shine ya sanya ya shafa'a da karatun yarinyar koda ya dawo kunsan mnyan mutane, ita kuma Hajiya Kubran bata tina mashi ba, a cewar ta hakan ma ya isa, wa yace ƴaƴan masu aiki na makarantar jami'a (🤔🤨😏 ke kika hana ko Hajiya Kubra) Takaddu sunyi kyau ya shiga faɗi da ɗan murmushi shi irin na miskilai, kai kace ma bai yi ba, sannan ya miƙe dasu a hannun shi yana mai cewa za'a siya jamb sai in cike tare da course ɗin da nake so, in naga ban iya ba sai in same shi ya koya man (kun ji ba Bigboo, ko ya manta da halin gidan nasu ne?) da to muka bishi da umman tawa, kuɗi ya ajiye kusa da umman tawa masu ɗan dama yana faɗin ko zata buƙaci wani abu, sannan ya ƙara jaddada mata kar taci Abunda likita ya hana, idan muna nuƙatar wani abu muyi mashi magana. Umman tawa ce ta shiga faɗin lallai ba zata amshi waɗannan kuɗi ba, cikin girmamawa ya shiga bata haƙuri da faɗin duk abin da yayi mana haƙƙinshi ne da yayi mana, wannan ba wani abun damuwa bane, duk ma in muna buƙatar wani abu mu tuntuɓe shi a shirye yake da ya taimaka mana. Godiya ta shiga ƙara jera mashi da yabanma dukkan in hidima da yayi damu ɗin "ba komai umma, Allah ya ƙara sauƙi" ya faɗa yana mai taka wa ya bar ɗakin riƙe da Takaddu na a hannun shi. Oh Allah🙏🏻 Ashe zanyi karatu a rayuwa ta? Ashe Ya Ameen na magana haka? Yanda naga ya zage suna ta fira da umma ta, kuma duk wata kalma da zai faɗa cikin taka tsantsan da girmamawa yake yin ta kaman yana magana da Hajiya kubra, murmushi na shiga saki akai akai, ina mai sauke ajiyar zuciya, mafarki a ya kusa tabbata, jikina na bani mun kusa fita daga cikin halin ƙuncin da muke ciki ni da umma ta, daga na gama karatu na samu aiki zan gina mana gida, na ɗauke umman tawa muje cen muyi Rayuwar mu, muma muci gashin kanku, mu rabu da takura da jaraba Hajiya kubra, Allah na gode maka, Allah ka saka ma wannan bawa da Alkhairi a rayuwar shi, ka haɗa ci da mata ta gari, da zata kula dashi, kuma tayi haƙuri da halin hajiya Kubran. "Tashi ki naɗe dadduman in kin gama murnar" u mata ta faɗa cikin murmusawa da ke nuna sallar jin daɗin ta, da farin cikin ta. Yunƙurawa nayi ina mai da rawa a fili na shiga faɗin "umma ai dole inyi murna kin gama man komai, Allah ya cika mana burin mu, ashe da rabon zan yi karatu nima in samu ilimi kaman yanda kowa ke samu?" Murmusawa tayi tana mai kishingiɗawa tare da faɗin "Ai wannan yaro ɗan albarka ne, Allah dai ya bamu ikon saka mashi da alkhairi kaman yanda yake mana shi da mahaifin shi, ki kauda kuɗin nan ki maida hankali ki ci abinci" da to na bita ina faɗin "ni wallahi ummana tsabar murna ma yasa naji na ƙoshi" "ki dai maida hankali" umman tawa ta bani amsa tana mai lumshe idanun ta murmushi fal a fuskar ta. Ta ɓangare guda kuwa Al'ameen ɗin na fita wayar Mom ɗin nashi na na shigowa, tare da umartar shi da cewa ko me yake ya tabbatas ya biyo jirgin yamma ya isa Katsina tana son ganin shi, shi kin mamaki ya shiga tambayar ta ko lafiya? "Lafiya lau" ta bashi amsa tana mai datse kiran, Layin Afnan ya nema gami da tambayar ta, ta faɗa mashi kawai dai taga an kira ta ne daga gidan Amman bata san ko wanene ba, kuma daga gani gulma aka kawo mata, "is OK" ya faɗa yana mai katse kiran ganin kiran babban Abokin nashi da zai kawo mashi ziyara yau ta shigo wayar shi. Amsawa yayi cikin son kauda zargin komai daga ranshi, bayan sun gaisa ne yake faɗa mashi ya iso gashi a airport, cewa yayi ya jira shi yana zuwa ɗaukar shi. Ko da ya isa ya tadda abokin nashi yana jiran shi, cikin son juna da tsantsar farin ciki suka rungume juna suna mai mararin juna da tsantsar ƙauna ga aminan guda biyu, basu bar airport ɗin ba sai da ya yanka masu ticket guda biyu tare da kallon Bilal ɗin ya shiga faɗin "yaro yau ƙauye zaka kwana, ka taddani tafiya ta gaugawa ta taso mani" cikin murmushi Bilal ɗin ya kai mashi ɗan ƙarami duka a damtsen hannu yana mai cewa "To ya zanyi Friend" ai ko ruga ka kai ni dole in kwanta, ya zanyi tinda na riga nazo?" Cikin walwala da jin daɗi suka bari airport ɗin direct gida ya wuce dashi domin yaje yayi wanka ya huta kafin lokacin sallar azahar ta ƙarasa. ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ _*Page ~13~*_ _To Readers_ --- *Abun da kuka ji da zai amfane ku ku ɗauka, wanda kuka ji akwai kuskure ciki, kuyi watsi dashi, mu ba muji wahalar zaunawa muyi amfani da idear ɗinmu ba mu rubuta maku labarin da zai amfane mu ba baki ɗaya ba, sai ku da zakuyi comment ƙarƙarinta layi biyu zuwa uku, shine zai ke maku wahala, Anya kuwa readers kuna kyautawa🤔? Muna maraba da gyara ko ƙorafi, Amman ba ta hanyar zagi, ko cin zarafi ba, kuskure kowa nayi indai kai ɗan adam ne, kuma ajizi, so saboda haka muna shawartar ku da ku dinga ƙarfafa mana guiwa, wadda kuma taga labarin baiyi mata ba, toh ta bar mana abunmu ba sai ta karanta ba, bamu sanya kowa dole ba, imfact ma babu dole sai rai yaso a rayuwa. fans muna godiya da irin supporting ɗin da kuke bamu 💓muna yinku over, Allah ya bar ƙauna, wannan saƙo ne daga ƴan ƙungiyar ~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Fira sosai suka shiga yi da aminin nashi da bashi da kamar shi, kaman ba Ya Ameen ɗin da kuka sani ba, har yana zaulayar abokin nashi, akan zancen bikin nashi da za'ayi watanni ƙalilan masu zuwa inda anan Abuja zai auri yarinyar ya tafi da ita cen. Sai da sukayi wanka suka shirya tsaf sannan suka wuce wani eatery mai bala'i kyau da tsada suka ci abinci sannan suka koma gida domin ƙara hutawa. Al'ameen ɗin ba mai yawan yawo bane indai yana ƙasa, yafi ganewa ya zauna a gida a part ɗin nashi yayi aiki. Yanzu ma hakan ce ta faru, yayin da ya jawo laptop ɗinshi ya shiga aiki, wannan ce ta sanya Bilal ɗin fahimtar cewa ƴan maganar sun bar kan aminin nashi, to ko wacce magana zai yi mashi fa zai yi mashi shiru ne, har sai lokacin da yaso tankawar kuma baya maido da zancen da ya riga ya wuce, wannan ɗabi'ar shi ce tin yana ƙarami, balle yanzu da ya girma. Kwanciya Bilal ɗin yayi domin yana jin baccin gajiya gashi ya ƙoshi har wani lumshe ido yake yi. Bilal ɗan gayu ne na ƙarshe, yana da hankali da tunani sosai duk da kasancewar shi cikin jajayen fata, hakan bai canza halin shi da mu'amala shi ba, wannan ce ta sanya abotar su da Al'ameen ɗin da take tin ta yarinta take daɗa ƙarko har kwanan zancen. Aikin shi yake yi cikin salo da kwarewa yake sarrafa kwamfuta, kaman dama cen shi ne ya ƙera ta, to ai dama karatun shi kenan kada ku manta. Kiran salla ne ya farkar da Bilal ɗin yayin da Al'ameen ɗin har ya ɗauro tashi alwalar, bayan Bilal yayo ne suka nufi masallacin da yake gefe ta jikin ɓari ɗaya na gidan nasu. Ƙarfe biyar daidai sukayi shirin barin garin, yayin da Al'ameen ɗin ya tara dukkanin ma'aikatan gidan domin bar masu jan kunne tinda za'a bar gidan ba kowa sai mu kaɗai. Ni da umma ta ce kawai bama wurin, ja masu kunne yayi sosai akan su kula da komai, Bilal ɗin na tsaye gefen shi yana ta murmusawa domin ya san abokin nashi kwarai da rashin son wargi, gashi dai ya iya mu'amala da ma'aikata dama cen, sai dai shi mutum ne mai son taka tsantsan da kula. Bayan ya gama dasu ne, ya nemi Bilal ɗin da ya raka shi ɗakin namu domin ƙara duba jikin umman tawa. Kwarai Bilal ɗin yayi mamakin ina yake nufa haka da yake ta ratsa sashen ma'aikata haka, sai dai bai ce mashi komai ba ya cigaba da bin shi a baya har zuwa bakin ƙofar ɗakin namu da yake tsaf a share tas, Sallama sukayi, yayin da umman tawa ta basu izinin shiga, kai tsaye suka cusa kansu cikin ɗakin namu da babu wadatar abubuwa. Miƙewa nayi ga barin karanta littafin *Jinnul Ashique* (na Harira ƴar fillo) domin littafin ya tafi da hankali na akwai tsantsar soyayya da abun al'ajabi da ban mamaki cikin shi, ina ma nima zan samu wanda zai gwada man irin wannan soyayya haka? (zaku iya neman shi ku karanta, zaku same shi online) Darduma mai ɗan girma na shimfiɗa masu lokacin da nake ficewa a ɗakin, Sam bazan lamunci zama na wuri ɗaya dashi ba, ƙamshin shi, idanun shi, ba ƙarami makami bane da kan taimaka wajen ruɗewa ta ba. Jikin umman tawa ya duba, Alhamdulillahi sauƙi ya samu sosai, faɗa mata yayi tafiya ta gaugawa ta taso mashi, da fatan dai babu abin da muke buƙata? Babu umman tawa ta bashi amsa sannan ta ɗora da godiya ta haɗa har da Bilal ɗin da tana ganin shi jefi jefi a gidan Amman sai ayi shekaru ma, in ba Al'ameen ɗin na gari ba. Harda Bilal ɗin a cewa babu komai Allah ya ƙaro sauƙi, kusan ma zamu iya cewa Bilal ɗin yafi gogan naku magana har ma da murmusawa, domin yau ƴan miskilancin na akai. Miƙewa sukayi suka baro ɗakin, tarin tambayi yi fal acikin ran Bilal ɗin, Amman ba lokacin yi su bane, matar ta burge shi, to wacece yarinyar da ta shimfiɗa masu darduma ta fita bayan ta gaishe su? Tsafta da ƙamshin ɗakin sun burge shi, abun ya ƙawatar dashi, matar kaman ya santa cikin ma'aikatan gidan fa, amman fuskar tata kaman ta ɓace mashi, any way🤷🏻‍♀ zai tambayi aminin nashi in sun natsu. Ta inda nake zaune jikin ɗan dandamalin flours suka zo suka gitta ni, tin daga nesa Naji tahowar su ta dalilin ƙamshin Ya Ameen ɗin da ya fara isowa hancina kafin ƙarasowar tasu, sadda kaina kawai nayi ƙasa har suka wuce, bansan barin garin zasu yi ba, wannan ce ta sanya ban masu adawo lafiya ba, kuma koda cen ma ba halina bane yawan tanka ma maza aduk al'amurran da basu shafe ni ba, sai dai ina ƙara ganin girman mutumin da ya kasance mana kaman uban gida ne a gare mu bama mu kaɗai ba, duk wani da ya kwana ya tashi ya amsa sunan ma'aikaci a gidan. Bilal ɗinne ma naga kaman zai tsaya sai kuma yaga abokin nashi bai tsaya ba, ya wuce kai tsaye zuwa ga motar tashi yana mai kwala ma Idi driver dake cen bisa kujeru dake wajen gate suna fira da mai gadi. Dagudu ya taso ya wuce ta inda nake zaune, hankalin shi ma bai kai kaina ba, ga motar ya isa yana mai russunawa tare da faɗin "gani yallaɓai" makullin motar ya miƙa mashi yana faɗin "airport zaka kai mu sai ka dawo da motar" "To" yace yayin da ya amshi makullin ya shiga mazauni driver ɗin, Bilal ɗinne ya shiga gidan gaba, yayin da Al'ameen ɗin ya shiga gidan baya, shiru ya ratsa motar in ka ɗauke ac dake yin aikin ta a hankali a hankali. Ban jira tashin motar tasu ba, na miƙe a hankali cikin salon tafiyar tawa na nufi sashen namu; ta gefen idanu ya bita da kallo yayin da suke ficewa daga cikin katafaren gidan nasu, shi kau Bilal juyawa yayi ya bita da kallo har suka fice yana ƙissima abubuwa da yawa a ranshi. Ƙarfe biyar da rabi jirgin nasu ya ɗaga zuwa Kaduna daga cen za'azo ɗaukar su domin ya ma mom ɗin tashi waya tin ƙarfe huɗu da ta turo driver ya ɗauke su. Shidda da wani abu suka isa, sun tadda driver na jiran su, basu wata wata ba suka nufo gidan nasu kai tsaye, da yake lafiyayyar mota ce sai gashi bayan isha'i da kaɗan sun isa state ɗin tasu ta hauhuwa, (Katsina ta Dikko kenan, garin tudu ɗan marna, ɗakin kara kunya gare mu ba dai tsoro ba) Mama zuwaira tayi murna da zuwan jikokin nata, masalan Al'ameen ɗin da Bilal dama ta kwana biyu bata ga Bilal ɗin ba, saboda ba yawan zuwa yake yi ba, family ɗinshi duka suna cen ƙasar, har ma da kakar tashi mace tinda namijin ya rasu. Aiko babu wata wata ta ta sanya masu aikin ta suka shirya masu teburin cin abinci, kala kala, duk da cewa da suke yi sai sunyi wanka sun huta hakan baisa ta kyale su ba, jikin tsufa ya kama ta dole su lallaɓa ta, haka suka ɗan yayyabiɗa sama sama, suka tashi, shi Al'ameen ɗin ma yafi shan coffe da salak ɗin da yaji ƙuli-ƙuli, 🤣kunsan gidan tsofaffi ko da me ƴaƴan su zasu zama, sun fi son abincin su na gargajiya da muhalli su na gado🤣 Da yake shi Al'ameen a nan gidan Alhaji Isuhun yake da part, wannan ce ta sanya basu haɗu da sauran ƴan uwan nashi da iyayen ba daidai zuwa safe. Bayan sun gama komai ne na al'adar kwanciya a ɗakin da yake mallaki Al'ameen ɗin suka kwanta domin gajiya ta baibayesu na zaman mota ga doguwar tafiya (a cewar su) Bilal ɗinne yayi gyaran murya yana daga kwance gefen gadon, hakan ce ta sanya Al'ameen ɗin miƙewa zaune yana mai fuskantar abokin nashi, da ya daɗe da Miƙewa zaune shima. Natsuwar da yaga yayi ce ta sanya shi gane cewa maganar mai muhimmanci ce, hakan ce ta sanya shi tattara dukkan Natsuwar shi shima a kan abokin nashi. "Bros ina so ne muyi wata magana da tin ɗazu nake so inyi maka ita, Amman na zaɓi nan ne saboda naga yafi da cewa muyi ta a natse" "Ehen ina jinka friend faɗa man minene kake son ji da baka san shi tattare dani ba" Al'ameen ɗin ya faɗa yana mai gyara zaman shi gami da jingina bayan shi da makarin gadon. Bilal ɗinne ya gyara zaman shi daga kan gadon sannan ya cigaba da faɗin "Ina so ne in san wacece matar nan da muka shiga ɗazu sashen ma'aikatan gidan ku muka dubo? Kuma wacece yarinyar da muka tada ɗakin? Menene alaƙarsu?" Da kallo Al'ameen ɗin ya bishi na tsawon mintina biyu, ganin abokin nashi na so ya ɗauko mashi dogon labari gashi shi kuma bacci yake ji. Ganin da yayi abokin nashi ya shiga koma ta tinani ne ya sanya shi sake faɗin" kayi haƙuri fa idan na shiga hurumin da ba nawa ba, Amman matar ta burge ni iya matuƙa, sannan bansan dalilin barin yarinyar ɗakin ba lokacin da muka shiga" "Huh" Al'ameen ɗinne ya gumtsi fuska ya fesar lokacin da yake zamewa ya kwanta akan bayan shi yana rigingine yana kallon pop ɗin dake liƙe sama ɗakin da aka ƙawata da fitili masu matuƙa kyau, sai dai a kashe suke saboda dare yayi bacci suke so suyi, hannun shi duka biyu yasa ya tallafo kanshi dasu yayi matashi, lokaci ɗaya yana mai lumshe ido cikin sanyi halin shi na miskilai, a hankali ya buɗe bakin shi ya shiga furta "Frnd bacci nake ji mu bar maganar nan zuwa safe, ni yanzu tinani na yafi karkata akan dalilin da ya sanya umma ta kiraye ni cikin gaugawa" Bilal ɗinne ya sauke dukkan ƙafafu nashi ƙasa daga kan gadon yana mai cewa "OK as you wish Bros, Amman ka sani na san halinka, baka komawa kan magana muddin aka yi ta ta wuce kenan, na lura baka son faɗa man ne, ina mai baka haƙuri akan shiga al'amurran ka da nayi, duk da na lura kana taka tsantsan" daga haka ya miƙe gami da shige wa toilet ɗin da yake ta cikin ɗakin. Tinani da tarabbabi ya sanya Al'ameen ɗin ciki, tabbas bai kyauta ma aminin nashi ba, ya so kanshi da yawa, babu abin da suke ɓoye ma juna, abokan shawarar juna ne, ko wanne hali ɗaya ya shiga suna taruwa ne su warware natsalar su a tare, me Bilal ɗin ke son sani?shima bai san ita ɗin ko wacece ba, bai san umman Suhan ɗin ba kaman yanda ita ma kanta ɗiyar bata san kanta da ko ita wacece ba. Bilal ɗinne ya fito yana tsane fuskar shi da ɗan ƙaramin towel, yayin da ya isa ga ƴar ƙaramar hangar kusa da mirror ɗin da ya mamaye kusan rabin bango ya maƙale shi cen, ya taka a hankali ya isa ga gadon gami da kwanciya yaja blanket ɗinshi mai taushi ya lulluɓe kusan rabin jikin shi "Suhan, Umma Maryama" Abunda Al'ameen ɗin ya faɗa kenan sound so husky, hakan ce ta sanya Bilal ɗin lamo yana sauraren shi, yayin da ya yi tsammani ma bacci ya kwashe shi, domin a yanda ya tafi ya bar shi a haka ya dawo ya iske shi, da alama ma ko matsin kirki baiyi ba, juyowa yayi yana mai fuskantar Al'ameen ɗin daga kwance. "Nima ban san su ɗin ko su wanene ba," Al'ameen ɗin ya cigaba da magana ba tare da ya jira cewar Bilal ɗin komai ba, to shi ɗin ma baiyi niyyar tankawar ba, saboda ya san halin aminin nashi sarai. "Shekarar su kusan sha bakwai a gidan namu, wannan baisa a san ko daga ina take ba tare da yarinyar dake hannun ta da take iƙirarin ita ce ta haife ta, sai dai sanin wanene mahaifi yarinyar, daga ina suke? Shine wannan sai ita umman, ciwon da Kaga mahaifiyar yarinya nayi Mom ɗita ce sanadi, wannan ce tasa Kaga ina basu kulawa daidai gwargwado" daga nan ya kwashe komai da ya sani ya faɗa ma Bilal ɗin na dangane da Rayuwar su Suhan ɗin, sannan ya ɗora da faɗin, "Bataso a taimaka masu ne ko alama, bansan minene matsala tata da hakan ba, na sha yunƙurin taimakon ta tana dakatar dani, Abunda na lura dashi ma, dukkan ma'aikatan gidan masalan matan, suna nuna masu wariya da ƙyarar su, Amman hali irin na Umman da take da haƙuri da tawakkali hakan bai nuna wata damuwa ko gazawa koda a fuskar ta ne kuwa, yanzun ma da ta amince da maganar karatun yarinya saida aka kai ruwa rana sannan, kuma ta gargaɗe ni da ɓoye duk wani taimako da zan masu dangane da karatun yarinya, ga dukkan alamu Mahaifiya ta ita ce babbar matsalar matar a gidan" Dakatar dashi Bilal ɗin yayi gami da tambayar shi "yarinyar fa? Naga kaman bata son mu'amalan tar kowa a gidan ayadda na lura ko mutane ma kaman bata shiga, ka duba tin daga gaisuwar da tayi mana bata ƙara tankwa ba duk da a gaban idon ta muka gitta ta inda take zaune, ƙarshe ma Miƙewa tayi ta koma cikin sashen nasu" Wannan karin, Al'ameen ɗin ne ya kalli Bilal ɗin ido cikin ido sannan ya shiga faɗin "Oho mata, ita wannan haka take, ban cika kula da al'amurran ta ba, Amman zan iya ce maka irin tarbiyyar da mahaifiyar tata ta bata kenan, bata saki jiki da kowa in ba mahaifiyar tata ba, hakan ya samo asali ne daga wariya da ƙyara daga sauran ƴan uwan nasu ma'aikata" ya faɗa yana mai ɗan taɓe bakin shi, sannan ya juya ya gyara kwanciyar shi gami da karanta addu'ar barci. Ganin haka da Bilal ɗin yayi, ya san ba zai ƙara tankawa ba kenan ya kuma wuce da maganar kenan. Shiru yayi shima yana mai hangen bayan kan Al'ameen ɗin da suma ta kwanta mashi luf abinshi, abun ka da farar fata sai yayi kaman wani ba'indiye, ta cikin haske dumlight ɗin da suka sanya mai ɗan duhu sosai kalar shuɗiya. Shiru ɗakin yayi in banda ac dake aikin ta a hankali a hankali, sai kuma Bilal ɗin dake ta saƙa da warwara, idanun shi ƙyam akan murɗaɗɗen abokin nashi, da tini bacci yayi awon gaba dashi, yana ta sauke numfashi a hankali, a hankali. Shima dai a haka baccin ya kwashe shi, washe gari duk suka haɗu a nan cikin gidan Alhaji Isuhun da duka nan suke karyawa da iyalan ƴaƴan nasu guda biyu watau Yaya Auwalu da Alhaji Mustapha Dambulan Sai da kowa ya gama karyawa, har da Bilal ɗin kuwa sannan aka koma babban falon domin sake sabuwar gaisuwa ga iyayen nasu guda biyu da kuma sanya lokacin da za'a zauna meeting da ƙarfe biyu rana, wannan karo harda ƴan uwan nasu mata,watau Gwaggo Aisha da kuma Gwaggo Fatima dake aure nan cikin kankiya da kuma kannen su mata watau Hassana da Hussaina suma duk an masu waya, saboda irin wannan taron babban taro ne da yake ƙara haɗin zumunci da ɗabbaƙa shi, hatta da yaran su matan an kikkira su a waya, tinda ƴan uwan nasu duk sun zo har da waɗanda ke ma'aura ya kamata kowa yazo a gana a kuma ƙara sanin juna. To sai mu ce Allah yasa ayi taro lafiya a kuma tashi lafiya Alhaji Isuhu family ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~14~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Zama ne da akan yi duk lokacin da ɗaukacin family ɗin suke nan, wannan ma karon kowa ya hallara, Alhaji Isuhu ne tare da ƴaƴan shi maza suka fara zama, sun tattauna abubuwa masu mihimmanci wanda mafi akasari Yaya Auwalun ne ke zartar da hukuncin, kasancewar shi babba namiji, sai da suka kammala tattauna war su sannan aka umurci kowa da ya hallara a babban falon sashen Alhaji Isuhun, kowa ya zazzauna Amman banda gogan naku, hakan ce ta sanya Alhaji mustapha ɗaukar wayar shi ya kirawo shi tare da umurtar shi da yazo sashen iyayen nasu. Taro ne da aka buɗe da addu'a bayan zuwan Yaya Ameen ɗin, inda aka gabatar da gaishe gaishe da kuma ƙara sani ga juna duk da dai kowa ya riga ya san kowa. Alhaji Auwalu ne ya fara da godiya ga Allah subhanahu wa ta'ala, sannan ya ɗora da faɗin, "Ba dan komai muka tara ku anan ba sai dan kuji maƙasudin tara ku anan da hukumci da tsarin da muka zartar, kasancewar kowa ya san ba shawara muke tambayar ku ba, amman dai hakan ba zai hana mu jin naku ra'ayin ba, idan mun gama sanar daku Abunda muka tattauna da shi Alhaji gashi nan" ya faɗa yana mai nuna farin tsohon da yake zaune bisa kujera irin ta alfarma yana ta faman murmusawa da kallon jikokin nashi har ma da surukkan nashi guda biyu watau Hajiya Kubra da Mama Zainab dake zaune ɓangare guda, duk da kasancewar Mama Zainab ɗin babba ga hajiya Kubran, Amman kai kace ita ce babba, saboda jin daɗin da gogewar kai harma da suturar ba ɗaya ba. "kai Aliyu, munsan buƙatar ka na anema maka auren Khadeeja, wanda mun yanke hukuncin nan ba da jimawa ba zamu je a nema maka auren" ya faɗa yana mai kallon babban ɗanɗan nashi namiji da ya sunkuyar da kai yana ɗan murmusawa, Yaya Auwalun ne ya cigaba da faɗin "sannan ku kuma Saudatu, da Nihal sai Hafsat (Ɗiya ga yaya Auwalun ta uku domin ta biyun mai suna Amina itama tayi aure har ma da ƴaƴan ta guda biyu, kuma itama tana zaune ne a wurin) kuma muna da buƙatar ku turo mana da manema aurenku zuwa gobe ko jibi domin mu tattauna dasu kuma mu basu izini" gabaki ɗaya sunkuyar da kai sukayi yayin da saudat ta zumɓuro baki ita fa bata shirya yin aure yanzu ba, dama Nihal ɗince mai saurayi, sannan ita hafsat dama tana da maneman ta masha Allah kasancewar ta nutsattsiyar yarinya ga kunya da girmama na gaba da ita, kyakkyawa ce masha Allah, domin su Nihal ɗin babu abin da zasu nuna mata. Dakatawa yayi yana murmusawa tare da cewa idan Alhaji mustapha yana da magana yayi yana sauraren shi, to shi ɗinma cewa yayi babu sauran wani abu sai dai ko a cikin yayyen nasu mata idan da mai magana. Goggo Aisha ce ta shigo da buƙatar tallafin karatun ƴaƴan nata maza da suka gama makarantar secondry yayin da Goggo Fatima tace ita kam babu abin da take buƙata, duk buƙatocin nata ƙannen nata sun gama mata komai sai Sam barka, tau suma ɗin dai haka Aunty Hassan a da hussainar babu abin da suka buƙata, sai godiya da suka shiga yi. Yayin da aka tambayi su Hajiya Kubran dake Zaune gefe, Hajiya Zainab dai cewa tayi babu komai, yayin da Hajiya Kubra ta buɗe baki cikin isa, ta shiga faɗin "Maganar Al'ameen fa? Banji kunce komai ba dangane dashi, shima ya kamata ya fiddo mata cikin wannan lokacin, in ba haka ba zan zaɓo mashi da kaina cikin family ɗin ƴan uwa na ko kuma cikin ƴaƴan ƙawaye na" Alhaji mustapha ne ya shiga kallon ta cikin ɗaure fuska yayin da Yaya Auwalun ya shiga girgiza kai a hankali yana ɗan murmushi, kasancewar duk sun san halin ta ne ya sanya abun bai basu mamaki ba. Shi kau Ya Ameen bazan iya fasalta yana yin da ya shiga ba, "wai me yasanya Mahaifiyar tashi take haka ne? Me yasanya idan zata yi abu bata tinani akai? Me yasanya, me ya sanya?" haka ya shiga furta wa cikin zuciyar shi da take ta kai komo, bugun zuciyar shi ya ƙaru, idan ko haka ne zai rufe bakin ta, zai bata mamaki, yana so ya cenza mata tinani, yana so ya cenza mata kallon da take yi ma kowa na bai isa ba sai ita kawai, yana son Mahaifiyar shi, ba zai so yana kallon ta tana tafiya bisa turbar da ba ita bace kuma ya sanya mata idanu ba. Hajiya zuwaira ce ta sanya baki a karo na farko, tin zaman da aka fara kusan awa guda kenan da suka shuɗe, ita ɗin ma murmusawa tayi, yayin da ta kalli Hajiya Kubran ta shiga faɗin "Ke kau Kubura me yasanya kika sanya ma wannan mijin nawa ido ne wai? Mai mata kaman ni har a ce ya fiddo da aboki yar rayuwa, ko ba haka ba ma ai shi Ameenun baki ga yanda yake ba, wannan ma mai tsoron matan? Ina ce ma ni ban taɓa ganin ya tsaya kula ƴan mata ba ko jin labari" kowa sai da ya murmusa banda Hajiya Kubran da take zaune hakim ce gefe guda yayin da Hajiya Zainab mata ga yaya Auwalun ta ɗora da faɗin " wannan gaskiya ne Mama, kamata yayi a bashi lokaci ya fiddo a tsanake, kaman yanda Aleeyu yayi, gashinan abokanan shi har da masu mata biyu Amman shi sai yanzu ya samu ya lalubo, zaɓen aboki yar rayuwa ai abune mai wahala sai an bincika sosai. Kowa yayi na'am da wannan maganar yayin da Hajiya Kubran ta Sake ɗaure fuska tana faɗin "Akwai ɗiyar Abokin wasa na Sen. Abubakar ɗan Malam, yarinya ce mai natsuwa, duk abin da ake buƙata mace da shi itama tana dashi, ta fito daga babban gida babban Family na yardar mashi yaje ya neme ta ni zan shige mashi gaba wajen aiwatar da komai" toh fa, Hajiya Kubra kenan, ita a ganin ta dukiyar ta arziƙin ta ya kai ta aiwatar da duk abin da take so, ta manta itama a ƙarƙashin wani take. Wannan karon cikin ɗan zafin rai Alhaji Mustapha ya shiga faɗin "Babu wanda zai sanya in ma yaro na auren haɗi, bamu taso munga ana yi mana shi ba anan gidan, kuma duk mu muka zaɓo ku, haka su Yaya Aisha duk su suka kawo mazajen aure, in ma haɗin ne ai muna da yaran da suka taso gaban mu a cikin family ɗin gasu nan duk sun isa aure, Meyasa bamu ce ya zaɓa a ciki ba?" Yaya Auwalu ne ya kamo hannun shi ganin abun na neman kwaɓewa, bai kamata a samu irin wannan saɓanin ba gaban yara, shi kau gogan naku, zaune yake kaman mutum mutumi, me yasa Mahaifiyar tashi take haka ne, mahaifan shi ke saɓani akan shi? Lallai babu wadda tayi mashi, baya kuma jin zai iya auren yarinyar da take nufi, kai shi Sam ma tarbiyyar ta bata yi mashi ba, dama ya kula da yanda take shisshige mashi idan yaje gidan, ashe da biyu ma Mahaifiyar tashi ke aikenshi gidan, itama yarinyar dalilin da yasa take mashi wasu abubuwan kenan? Sai yanzu ma zuciyar shi ta shiga hararo mashi wasu abubuwan, yayi nisa a cikin tunanin yayin da idanu wan shi suke rufe ya tsinkayo maganar wan Mahaifin nashi yana cewa "ya isa Mustapha, Ya isa su ai mata ne, tinanin su ragagge ne, kuma duk wannan abun dake faruwa shi yaron ai gashi gaban ku zaune, har yanzu bai tanka ba, bama mu sani ba shin ko akwai wadda tayi mashi cikin rai? Ko akwai wadda suke tare? A bari aji ta bakinshi tukunna" yayin da ya maida kallon shi ga Al'ameen ɗin sannan ya cigaba da faɗin "Shin Kai Al'ameen a cikin ranka akwai wadda kake so kuka yi maganar aure da ita? Ko akwai wadda ka yima Alƙawarin aure ne? Falon yayi tsit, baka jin komai sai ƙarar ac da take ta aikin ta ahankali ahankali, kowa ya maida hankalin shi da natsuwar tashi akan Yaya Al'ameen ɗin, yayin da kanshi yake ƙasa, da yawa daga cikin ƴan matan da suke falon suna so ace sune ya zaɓa a matsayin aboki yar Rayuwar shi, Al'ameen ɗin ɗaya ne tamkar da dubu, komai ya haɗa, kyau, natsuwa, ilimi, gayu, ga uwa uba naira, runtse idanu shi ya sake yi gam, yayin da yake jinjina girman maganar da zata fito daga bakin shi, ahankali ya buɗe idanun nashi ya fara ɗora wa akan kakan nashi, Alhaji Isuhu da shima kaf natsuwar shi na akan jikan nashi, kaka zuwaira ya kalla ta sakar mashi murmushi irin nasu na dattawan da suke cike da natsuwa da kuma dace da ƴaƴa nagari, sannan ya ɗauke kallon shi kacokam ya ɗora shi akan Mahaifiyar tashi da ta cika fam, uwa zata fashe, dan dai wayewa da kuma halin tarin rai irin nata, Sam bata kawo ma ranta cewa yaron nata zai bijire ma buƙata tata ba, na amsar tayin ƴar ɗan uwanta da tayi mashi ba gaban kowa, bata yi tinanin zai watsa mata ƙasa a ido ba. Kallon shi ya maida kan iyayen nashi maza biyu da suke zaman jiran cewa shi, sake ajiyar zuciya yayi ahankali, yayin da ya gyara zaman shi kan lallausan carpet ɗin da ya malale ilahirin falon, sannan ya nisa ya cigaba da faɗin " Eh ABBA, Akwai wadda muka yi Alƙawarin Aure, sai dai kuyi haƙuri jin ko wacece, Nidai ita nake so, kuma itama tana so na, kuma ina mai roƙon alfarmar da aura man ita, ita na zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa ta, uwar ƴaƴa na, tarbiyyar ta tayi mun, komai nata yayi mun, kuma, kuma ina mai roƙon ta yi maku kaman yanda tayi mun" Ya faɗa cikin salon maganar shi mai kama da ta saraki, sannan ya ƙara she yana duƙar da kai alamar roƙo da girmamawa ga iyayen nashi har dama kakannin nashi da suke zaune a wajen. Murmushi Alhaji Isuhun ya sake cikin halin dattako ya shiga faɗin " Alhamdulillahi Faɗi kanka tsaye Ameenullah, nan kowa jiran yaji taka zaɓen yake yi, in da hali sai a haɗa da na shi Aleeyu baki ɗaya ma a wuce wurin. Toh fa! kan kowa da yake zaune a falon ya ƙulle, har da mahaifan shi Al'ameen ɗin watau Hajiya Kubran da Alhaji Mustaphan, Aunty Feena ce ta kalli ƙanen nata cikin wasiwasi da tarabbabi, kada ya janyo masu wani abun kuma, ita ta san bayada wata budurwa da yake so, kuma ta san babu wacce yayi ma Alƙawarin aure, toh fa! Kaman zata ce wani abu sai kuma tayi shiru, ganin Al'ameen ɗin ya fara magana "Abba Hauwa'u ce ta gidan mu watau Suhaann.. ɗiyar Ma.. Ma Maryama ta ɓangare masu aiki" Salati Hajiya Kubra ta sake tana mai miƙewa tsaye tana taɓa hannuwa kaman wata sakarai, jin maganar tayi kaman saukar aradu, sakin baki tayi, yayin da su kuma su Nihal suka ƙwalalo idanu, ba su ba har Aunty feenar ma ta shiga komar mamaki, Afnan kuwa murna da farin ciki ne suka mamaye ranta, Aunty Suhan fa! Ko dai kunnen ta ne ke gaya mata ba daidai ba? Nihal ce ta shiga zumɓuro baki tana faɗin wallahi yaya a'a mai aikin mu ce fa? Murmushi Alhaji Mustaphan yayi, ko babu komai ya san dalilin yaron nashi na yin hakan, tabbas ya jinjina ma yaron nashi, yayi na'am kuma da buƙatar tashi, sannan kuma ya bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, jinjina kai ya shiga yi yana faɗin "Masha Allah, haka ake so Al'ameen yarinya tayi, kuma ina tare da kai, insha Allah zan shige maka gaba wajen ganin komai ya daidaita" yayin da Hajiya Kubran ta koma ta zauna bisa kujera inda ta tashi tana faɗin "kai shashasha ne Ameenu? Ashe baka da hankali? Me zaka ci da wannan yarinyar? To bari kaji ban yadda ba ka auri yarinyar da bata da asali koda kuwa ace mata sun ƙare ne a duniya, Ban yadda ba Sam, idan ba haka ba kuwa zaka gamu da fushi na, au ashe dama munafintata kake yi? Kana cen kana soyayya da wannan ƴar jariri yar abun? Sam ban lamunta ba, Alhaji har kana faɗin ka yarda, tau bari kuji ni Sam ban yarda Bako sama da ƙasa zasu haɗe bazan lamunci wannan auren ba" Alhaji Auwalu ne ya shiga kwantar mata da hankali yana faɗin "Kai Mustaphan bamu gane yarinyar da yake faɗi ba, kar dai ace yarinyar da aka zo da ita a goye gidan ka, ɗiyar wannan mai aikin?" Jinjina mashi kai Alhaji Mustaphan yayi cikin son bashi tabbaci, yaya Auwalun ne ya shiga faɗin ai ko hajiya ta yadda mu ba zamu yadda da wannan abun ba har sai an nemo asalin ita yarinyar, kai Ameenu ka bamu lokaci zamuyi ƙwaƙƙwaran bincike akai, kuma bamu ce ka cigaba da neman yarinyar ba har sai mun samu cikakke bayani akan ta, Alhaji Mustaphan ne ya shiga faɗin hakan yayi daidai, zamu bincika bayan wannan yarinyar bata da wani abun da za'a ce an kasa auren ta, kasancewar ta ɗiyar mai aiki, wannan ba hujja bace, ni na yarda da yarinyar da kuma tarbiyyar ta, Allah yayi maka albarka Al'ameen kayi Abunda ake so, ina alfahari da kai da wannan tausayi da jin ƙai da kake tare dashi, Allah ya ƙara ma Rayuwar ka Albarka duniya da lahira" Da ameen kowa ya amsa, yayin da Hajiya Kubra ta miƙe ta fice daga falon kaman zata fashe, da kallo kowa ya bita yayin da wasu suka shiga jinjina kai, shi kau Al'ameen ɗin duƙar da kanshi ya sake yi ya maida idanu shi ya kulle, me ya sanya shi yin hakan? Me ya janyo mashi? Yana so ne Mahaifiyar tashi ta canza halin ta akan masu aiki, yana so ne ta gane mecece duniya da Abunda ke cikin ta, Suhan ɗin alkhairi ce duk da kasancewar irin taƙaddamar dake cikin auren, ba soyayya tsakanin shi da yarinya Sam, bata ma san wainar da ake toyawa ba, kuma da wanne ido ma zai kalle ta yace mata ita ce ya zaɓa a matsayin wadda zai aura? Ta yaya zata kalli abun? Ta yaya ummanta zata fassara abun? Baya tinanin idan har umman bata yadda ba ko ta bada goyon baya ba abun idan zai yuwu. *Wacece Suhan ɗin???* Tambayar da ya shiga yi ma kanshi kenan Nisawa yayi yana mai sakin ajiyar zuciya ahankali ahankali, yayin da ya kai kallon shi kan sauran ƴan uwa nashi, tashin hankali da ƙyara ƙarara ya hango cikin idanu saudat da Nihal ɗin tau sai dai shi ba tasu yaje yi ba, yana hango Abunda zai faru ne nan gaba, da irin ƙalubalen da zai fuskanta nan gaba wajen Mahaifiyar tashi, gashi har ta fusata ma tabar falon, dama ya san hakan ce zata kasance, kuma shi baya jin idan zai iya janye maganar shi, hakan ma wata dama ce da yarinyar zata iya tantance wacece ita. Alhaji Auwalun ne ya shiga kwantar mashi da hankali, yana faɗin ba zamu ƙi amince maka ba, muddin muka ga babu abun ƙi tattare da asalin yarinyar, sannan muna mai baka shawara ka koma ku sasanta da Mahaifiyar ka, saboda abun yayi maka albarka, idan babu mai magana zamu rufe taro da addu'a da kuma sanya ran cewa manema auren saudat da Nihal ɗin zasu zo gobe idan Allah ya kai mu. Babu wanda yace komai, kowa da Abunda yake saƙawa acikin ran ta, abie ma ba zamu iya tantance halin da yake ciki ba, mutum ne mai zurfi ciki, kusan ma yaso yafi Al'ameen ɗin, tau sai dai shi ɗan ɓangare Hajiya Kubran ne, sai abin da tace, ko ta zartar, saɓanin Al'ameen ɗin da komin yake biyayya yaga za'a kauce ma gaskiya baya bin wannan ayarin. A haka aka kulle taro da addu'a yayin da iyayen nasu maza suka cigaba da zama wannan karon har da mama zuwaira ɗin domin su ƙara tattaunawa Kowa ɓangare shi ya wuce, wannan ce ta sanya suma su Nihal ɗin komawa cikin nasu sashen inda suka tarar da hajiya Kubran zaune tana ta faman cika, zaman jiran Alhaji ya shigo domin ita ba da Al'ameen ɗin zata yi ba da wanda ya ɗaure mashi gindin yin abun zata yi, zata ji dalili, kuma tabbas zaman munafukar matar cen ya ƙare a gidana tinda so ake a mallake man ɗanɗa na. Abunda take ta faɗa kenan yayin da ta miƙe ta shiga safa da marwa, su dai aunty Feena da afnan ɗaki suka shige yayin da su saudat suka zauna suna ta ƙara yi mata famfo da ingiza mai kantu akan al'amari, muddin aka ce yarinyar cen ta auri yayan nasu ai sun kaɗe, yarinyar da babu irin wulaƙanci da tozarcin da basu yi mata ba, Amman ace wai zata zama aunty su, tabɗijam "lallai Mom baki ga ta zama ba" cewar Saudat ɗin °°°°°°°°°°°°°°°°°° Kai tsaye ɗaki shi ya wuce, kayan shi kawai ya cire ya faɗa toilet ɗin ya sakar ma kanshi shower, ko sauraren Bilal ɗin baiyi ba, da yake ta mashi magana, shi ɗin ma ya san halin ƴan kayanshi, ba zai samu amsa ba, balle ma ya lura da condition ɗin abokin nashi, anya kuwa wani abu bai faru ba a zaman taron na family ɗin? Yana cikin tinani Al'ameen ɗin ya fito daga toilet, ƙugunshi ɗaure da fari ƙar ɗin towel, yana ɗauke da ɗan ƙarami yana tsane kanshi, jikin shi ko ina gargasa ce kwance luf, baƙa siɗik, abun ka da farar fata, sai tayi mashii gwanin kyau, ko kaya bai tsay Sanyawa ba, balle ya cire towel ɗin ya faɗa kan gadon yayi rigingine fuskar shi na kallon cilling. Kafaɗarshi Bilal ɗin ya dafa yana daga kwance "Man me ya faru ne? Ka gaya man na lura baka cikin natsuwa" kaman yana jiran cewar Bilal ɗin ya shiga faɗin "Friend na yanke ɗanye hukunci, ba tare da nayi tinani ba, Friend why? Me yasa nayi haka? Anya kuwa ban sha wani abu ba? Friend gaya man" ya faɗa yana mai tashi zaune ya juyo sosai busa gadon yana fuskantar abokin nashi, idanu shi sun kaɗa sunyi jajur dasu "Yarinyar tausayin su kawai nake yi, babu soyayyar ta ko ɗigo cikin raina game da ita, me yasa haka? Na jawo ma kaina raini, duk dan in faɗa kar da mahaifiya ta akan illar tsanar mutum haka kawai, yaya Mahaifiyar ta zata kalli abun, miƙewa yayi yana mai gyara zaman to wel ɗin a jikin shi, ya shiga taka wa a hankali cikin ɗakin, kai komo ya shiga yi cikin ɗakin kaman yana neman wani abu. Miƙewa Bilal ɗin shima yayi yana mai kamo hannun abokin nashi, tabbas ya san duk lokacin da yaga abokin nashi cikin irin wannan halin yana buƙata neman taimako ne. Zaunar dashi yayi bisa sofar dake ɗakin mai zaman mutum biyu, "Cool down Friend, ka natsu ka gaya man meke faruwa ne?" kaman yana jiran shi ya ɗan zabura ya zamo daga bisa kujerar kaman zai zauna ƙasa, yayin da ya kama hannun Bilal ɗin ya runtse shi sosai, kaman zai tsinke hannun "Friend ni na zaɓe ta da kaina, ni na amince ma auren ta da kaina, yarinyar da ka gani jiya a gidanmu, na amince zan aure ta, Friend ka bani shawara, how am i going to do? Wannan ƴar yarinyar Friend, ko aure zanyi Ai tayi man kaɗan, Amman nine da bakina nace su Abba su nema man auren ta Friend ya zanyi? Bata san meke faruwa ba, bata san zan iya yanke wannan ɗanyen hukunci a kanmu ba, zata so ni? Zata yarda dani? Mahaifiyarta zata amince mani? Ya faɗa yana miƙewa tsaye, shima ɗin dai Bilal ɗin a kiɗime ya miƙe jin abin da abokin nashi yake faɗa mai kama da almara, mai kama da tatsuniya. *"WHAT"* *Al'ameen Are U In Your Sense?* Bilal ɗin ya shiga faɗi a kiɗime cikin ɗaga murya, yana fatan kunnen shi basu ji mashi daidai ba, yana fatan ace mafarki yake yi, ina Al'ameen ɗin ina ƴar aiki, marar galihu, jiya jiya nan fa da daddare Al'ameen ɗin ke ce mashi ba'a san asalin yarinyar ba, inko haka ne me ya ja ma abokin nashi? Me ya shiga kanshi, saɓanin abin da yake son yaji ne ya shiga faruwa, lallai Al'ameen ɗinne ya shiga gƴaɗa mashi kai cikin tabbatas wa, da kuma neman mafita. ~Oum-Deedat ce~ [8/5, 8:25 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~* *Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat) *Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat) *Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare. *Page ~15~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° "Hajiya Laila kina jina ko? Ki bani way out please ƙawata, ɗan cikina ne zai auri ƴar talaka? Talakan na ma'aikaciyar gida na? Wadda bata da komai, bata da asalin kirki ma? Kai ina ba zai taɓa yiwuwa ba sam wallahi" Hajiya kubra ce riƙe da waya a hannun ta da alama waya take yi tin bayan shigar ta sashen nasu, ko zama t akasa yi sai kai kawo take yi a tsakanin tanƙamemen falon nasu da yaji kayan alatu kaman ba za'a mutu ba "ina jin ki Hajiya Kubra" daga ɗaya ɓangaren aka bata amsa cikin isa da izza ga dukkan alamu dai ƙawarta ce. "Ba kina jina zaki ce ba Hajiya Laila, mafita nake nema, kin dai sanni, kinsan buri na, kin kuma san yanda nake ƙaunar Al'ameen a duk cikin ƴaƴa na" Ta tari numfashin Hajiya Laila cikin sauri "Gaskiya ne Hajiya ta, ai wannan maganar ba ta waya bace, anya ma kuwa ba asiri sukayi mashi ba? Kin san fa tin lokacin da kika kula da shisshige masun da yake yi ya kamata ace kin taka ma abun burki, Amman son da kike mashi ya hana" "Hajiya Laila wallahi nayi ƙoƙarin hakan tin lokacin, Amman ɗan banzan yaron nan yaƙi bani haɗin kai, kin dai sanshi da shegen zurfi ciki, da kuma miskilanci, ni kaina rasa gane kanshi nake yi" Hajiya Laila ce ta tari numfashin hajiya kubran da cewa, "ba kince su keyi maku girki ba?". "Eh kwarai kuwa hajiya, in ba girkin su ba baya cin na kowa wlh" humm, Hajiya laila ta numfasa gami da sakin wani ɗan guntun murmushi ta cen ɓangaren, sannan ta ɗora da faɗin "To wallahi ina mai tabbatar maki a nan suka samu, suka samu abin da suka barbaɗa mashi yaci, yanzu abin da nake so dake ki kwantar da hankalin ki, abun zai zo mana da sauƙi, kedai kiyi ƙoƙarin dawowa akan lokaci" Nisawa Hajiya Kubra tayi cikin ƙunar zuciya da tsanani ɓacin rai, kaman zata haɗiyi zuciya ta mutu, sannan ta cigaba da cewa "Shikenan Hajiya Laila, ina so please kiyi tinanin neman mafita, saboda ni duka ma kaina ya ƙulle wallahi, gabaki ɗaya yaron nan so yake ya birki ta mani lissafi, na yarda dake ne, insha Allahu kuma zanyi ƙoƙarin ganin na dawo akan lokaci, yanzu ma zuwan maneman su suhan ne kawai zai tsaida ni" "Is OK Hajiya Kubra, baki da damuwa ki kwantas da hankalin ki, ina mai tabbatar maki da maganar nan zata sha ruwa, ko shi Alhajin da ya goya mashi baya, ba zai ma ƙara tada maganar ba, balle wani Alhaji Auwalu cen, da zaki ɗaga hankalin ki aka shi;To ko Isuhun ma bai isa ba balle ƴaƴanshi"😒 Hajiya Kubran ce ta murmusa mai cike da yaƙe, "Humm Hajiya Laila kenan, baki da dama, haka nake so, Shiyasa nake son ki nafi yadda dake akan kowa cikin ƙawaye na, na mayar dake aminiyata ta hannun dama ta, wuƙa da nama na hannun ki, a fara komai kafin in dawo, zan tura maki duk abin da za'a buƙata" "Ba damuwa Hajiya Laila, ke dai sai kin dawo dai, ƙibar komai a hannuna, sai mun yi magana" "OK shikenan a huta lafiya Hajiya Laila, sai Naji daga gare ki" ta faɗa tana mai datse kiran gami da zama cikin ɗan samun sassauci, saboda sanin halin hatsabibancin ƙawar tata, komai take so mai sauƙi samu ne, indai tabi ta hannun amini yar tata. ************** "Look Friend kayi gaggawar yanke hukunci, aure ba abu bane da akeyi mashi hawan ƙawara, yarinya r zaka iya taimako ta, ba sai ka aure ta ba, ina so ka sani aure babu soyayya ba abu ne da ke ɗorewa ba, masalan yanda zaka yi manage na zama da ita, a yanda na san ka yarinyar bata yi daidai da ra'ayin ka ba, beside ma mahaifiyar ka...... " Dakatar dashi Al'ameen ɗin yayi, ta hanyar ɗaga mashi hannu," Bilal! Please mubar maganar haka, kayi man addu'a kawai" abin da ya faɗa kenan, ya miƙe a hankali ya zura kayanshi, gami da zarar keys ɗinshi na mota ya fice daga gidan ma baki ɗaya. Da kallo abokin nashi ya bishi dashi, "Hooo Al'ameen kenan, ko sai yaushe zai cenza? Kaman bashi bane yanzu yake neman way out, yaro kaman mai bira'izai? Wannan ko auren yayi wahalar da yarinyar kawai zai yi, bai iya wata soyayya ba, balle ya tsaya bata kulawar da ta dace, kullum kai kenan a murɗe? A baibai? Humm" ya faɗa a fili yana mai miƙewa shima ya fice daga ɗakin zuwa cikin lambu. *********** Da sallama ya shiga sashen nasu, fuskar shi a matuƙar ɗaure, ko babu komai ya san bata kyauta mashi ba, a gaban kowa ciki har da iyayen shi ma, Amman taso tayi jayayya dashi, har tana ɗaga murya akan kowa da ficewa ma baki ɗaya daga perlour ɗin, dole ya nuna mata ɓacin ran shi, alwashi ne ya sha shi aure sai anyi, zai ga wanda yake gaba, cikin shi da ita; ko ɓangaren da take bai kalla ba, ya wuce kai tsaye zuwa bedroom ɗinshi domin wanka da shirya ma zuwa sallar magariba da ta gabato. Haka yazo ya sake wuce ta, tana zaune tana kumburin ta da kaɗa ƙafa ɗaya dake kan ɗayar, Hajiya Kubra kenan, ai shi duk abin da Allah ya tsara baki da kuɗin da zaki cenza ikon shi akan komai Itama tana kallon shi, Amman yanzu kam duk son da take ma Alhajin, zata danne shi ne, ba zata taɓa bari da girman ta, da ajinta ba, ta tozarta, to ai ajinta ma ya zube in har ta bari ƙawayenta suka ga wadda ɗanɗan nata yake son auro mata a matsayin suruka, yarinyar ƴar ƙauye da babu abin da ta iya sai bauta, sam Suhan ɗin ba ajin *Moh'd Al'ameen Al-Mustapha Dambulan* ɗin nata bace. Wannan ce tasa har ya kuma fitowa ya fice baki ɗaya daga gidan bata kula shi ba, tasha Alwashin yi ma abun tufkar hanci, ba Alhajin ne yake taƙama dashi ba? To wannan karon har shi ba zata ƙyale shi ba. ----------- Haka kuwa aka yi, washe gari da wuri maneman auren su Nihal ɗin suka iso, masha Allah yara ne ƴan gayu, ƴaƴan masu faɗa aji, kaman yanda hafsat ɗin take kamila da sanyin hali haka shima saurayi nata yake, kowa yayi mamakin shi duk da, da alama naira ta jiƙa shi sosai, Amman baya da jin kai irin na sauran masalan saurayi Nihal ɗin, ahaf, ai kowa yana samun daidai dashi ne, basu jima ba sosai bayan sun gabatar da kansu, iyayen na su saudat suka ga, ai iyayen nasu ba baƙi ma bane a wajen su, umurtar su sukayi da su turo su domin tsaida lokacin aure, Abun Alkhairi sosai suka ba yaran su Goggo Aisha, sukayi ta Sam barka da sanya alkhairi, basu tafi ba sai da Kaka zuwaira ta zo ta zazzaulaye su, cikin wasa irin na kaka da jika, hakan ya ƙara faranta ran su, domin su ɗin dama sangartattun ƴan gata ne, sun saba zaulayar granny ɗinsu at any moment. Atare suka koma zuwa Abuja gabaki ɗaya, bayan kammala zumuncin irin na wannan lokacin, da yazo da saɓani da abubuwan farin ciki da dama. Ta ɓangaren Hajiya Kubran kuwa, har yanzu sama sama suke da Alhajin, domin ya sha Alwashin gargaɗar ta da kuma yi mashi katsalandan acikin Al'amari auren yaron nashi. Kowa da Abunda yake saƙawa cikin zuciyar shi har ƙarasowar su zuwa cikin gidan, wannan ce ta sanya bamu san da labarin dawowar tasu ba, kowa part ɗinshi ya wuce kai tsaye, duk da suna farin cikin gabatar da masoya nasu ga iyayen su, Amman ta ɓangaren guda, ƙudirin yayan nasu ya kasa barin zuciyar su, haƙiƙa wannan labari ne mai muni, labari ne mafi ƙona zuciya da suka taɓa ji tin bayan mallakar hankalin kansu. Al'ameen kuwa, Daurewa kawai yake yi wajen amsa ma abokin nashi duk maganar da yayi mashi, ziyara ya kawo mashi, baya so yaga kaman yana wulaƙanta shi ne, ta ɓangaren Bilal ɗin kuwa yayi mashi uziri, ya san damuwar abokin nashi, ya sani sarai, ya yanke hukunci ne cikin fushi, gashi abun yazo daga baya yana damun shi, kuma shi ba irin mutanen da suke amai su lashe bane, ya sani, koda za'a dinga yankar naman jikin shi, ba zai koma yace ya fasa ba, ba zai warware nuƙatar tashi ta auren Suhan ɗin wajen iyayen shi ba,koda kuwa hakan na nufin faruwar mummuna abu ne a gareshi. ***** Tura ƙofar aka yi, gami da shiga cikin ɗaki kai tsaye, wucewa tayi i zuwa ga bakin gadon ta samu ta zauna, sanye take cikin kayan bacci irin masu mugun tashin nan, sai walƙiya take, Hajiya kubra kenan, ikon Allah, "Alhaji nazo ne muyi magana da kai" Shiru yayi mata kaman ma baya cikin ɗakin Bata saurare shi ba, ta cigaba da faɗar Abunda ke cikin zuciyar ta. "Alhaji ina so ne fa ka sani, ina nan kan baka na, lamarin auren Al'ameen da yarinyar cen ta sashen masu aiki, ban yarda dashi ba har yanzu, bana kuma tinanin zan yarda har abada, ni ce na haife shi, baya da ikon yin abun da ban yarda mashi yayi ba, mu ne gaba dashi, ba shine gaba damu ba, mune muka haife shi, ba shine ya haife mu ba, ina so ka sani muddin ya sake ya auri yarinyar nan, zan mugun saɓa mashi, bana so ka bashi goyon bayan auren baiwar mu..... " " Ya isa Kubra, ya isa hakanan nace" ya katse ta cikin tsanani ɓacin rai, da tsawar da ta gigita ta, har ta miƙe tsaye bata sani ba, to ita ai bata ma san lokacin da ya miƙe zaune ba. "Idan baki son in saɓa maki ƙibar maganar nan, ina so ki sani muddin baki bashi damar auren yarinyar ba, to fa lallai ne ki bashi dama ya zaɓi wadda tayi mashi, namiji ne, mata ma bamuyi masu dole ba balle maza, namijin ma kaman Moh'd Al'ameen, Kubra me yasa baki tinani ne wai in zakiyi abu?kin gama tozarta ni gaban ƴan uwan nawa da ƴaƴan nawa, shine kika biyo ni nan ki sake ƙarawa? Yaushe har abun naki ya kai haka ban sani ba? Toh ina so ki sani, duk hukunci da na yanke nan gidan akan ƴa] a na ya yanku, ni ne sama dake acikin gidan nan, kuma dole kema kibi abin da nake so, ina so ki sani, maganar sake yin aikin Maryama da yarinyar ta acikin gidan nan na haramta shi, kaman yanda na faɗa maki acen baya, ban barsu sunyi aiki ba, ada cen saboda lafiya su, balle yanzu da suka zama *Surukkai na"* A razane ta kalle shi, "Alhaji Surukkai fa kace? Yaushe har suka zama surukkan ka?" "Ah to nadau faɗa maki, kuma abin da nace kenan, na gama magana, zaki iya cigaba da faɗar dukkan Abunda ke ran ki, ruwan ki ne ki ƙyale yaro yayi Abunda yaga ya fiye mashi, ko kuma ki sanya ya fara bijire ma umarnin ki, da biyayyar da yake maki" yana gama faɗar haka ya koma ya kwanta, gami da jan bargo ya lulluɓe jikin shi, sannan ya sanya hannu ya kashe dumlight ɗin ma gaba ɗaya, ɗakin ya gauraye da duhu. Ƙutawa tayi, gami da tashi ta fice daga ɗakin zuwa nata, tana mai ƙudurce abubuwa da dama acikin ranta. ********* "Son" Alhajin ya kira sunan yaron nashi da yake zaune bisa kujera mai cin mutum ɗaya, hakan ce ta sanya shi ɗago kyawawan udanun nashi ya ɗora su akan dad ɗin nashi, shigowa shi kenan part ɗin mahaifi nashi domin har yanzu ya kasa tun ƙarar mahaifiyar tashi, "Ina so ka ƙara tabbatar mani da maganar da ka faɗa a cen kankiya kan yarinyar nan, shin da gaske kana so ta?" Alhajin ya jefa mashi da tambayar bazata da ta ƙara ruɗa shi, ƙasa yayi da kanshi yana mai murza yatsun hannun shi, ya ma rasa me zai faɗa ma dad ɗin nashi. " Eh Abba, da gaske nake, ina so ta, kuma a shirye nake da in taimaka mata. " Ya faɗa ciki-ciki, sai dai duk da haka Alhajin ya ji shi, "OK Son, Abunda nake so da kai, kabar maganar nan for now, saboda hajiya ta huro wuta, hakan zai sanya ta matsa ma zaman su acikin gidan nan, akwai abubuwa da dama gabanmu, na san mahaifiyar ka ko wacece, hakan zai sa tayi tinanin mun bar maganar ne, to sai dai zamu shirya dukkan Abunda zai yuwu ne bayan mun gano asalin ita yarinyar, talauci ko rashin mahaifi ba zai sanya in kasa barin ka ka aure ta ba, ina so ka sani, ni ba kaman mahaifiyarka nake ba, kuma itama ina mata addu'ar Allah ubangiji ya shirya ta, ta gane gaskiya" da ameen ya amsa iya maƙoshi, sannan Alhajin ya ɗora da faɗin "Maganar karatun yarinyar, ina so kayi dukkan mai yuwuwa ta tafi makaranta, hakan zai bamu damar bincike na haƙiƙa, dole kuma sai da haɗin kan mahaifiyar yarinyar, sannan kaje ku daidaita da mahaifiyar ka, ga nemi gafarar ɓata mata da kayi, hakan ba yana nufin ka janye maganar auren naka ba, ina so kuma ka cire dukkan wata damuwa da ke cikin ranka, komai Kaga ya yuwu yi ne na Allah, na san dalilin ka na son auren yarinyar, nima na bada goyon baya ɗari bisa ɗari, Allah ya tabbatar mana da Alkahirinsa. Nan ma da ameen ya amsa cikin zuciya, Alhajin ne ya wayance ya shiga janshi da firar kasuwanci, da shirin buɗe sabon estate ɗin su mai suna *Dambulan estate* da za'ayi zuwa ƙarshen shekara, wadda take mallaki Al'ameen ɗin. Da haka ne ya samu ya saki jiki dashi, nan suka karya su uku, har da Bilal ɗin da ya shigo daga baya gaishe da Alhajin, bayan sun gama ne suka fice atare da Alhajin kaman wasu abokan shi. Jikin Ummantawa yayi sauƙi sai Sam barka, hankalinmu a kwance, saboda ƴannkuɗaɗen da ya Ameen ɗin ya bamu, su ne muke riritawa da siyan abubuwan da likita ya gindaya ma umman tawa cinsu, tin bayan tafiyar su hajiya da kwana ɗaya bamu sake jin ɗuriyar shi ya Ameen ɗin ba, sai bayan dawowa su ne, saƙo ya iske mu, na dakatar damu daga aikin gidan gabaki ɗaya da aka yi daga bakin mama talatin, a cewar ta wai saboda jikin umman tawa, to mu dai duk da haka jikinmu yayi sanyi kwarai matuƙa, sai dai gudun sanya zargi wani abu, ko damuwa ya sanya muka kauda dukkan wani shakku a cikin ranmu game da hakan. Hankalinmu bai ƙara tashi ba saida aka dena bamu abinci gabaki ɗaya, mun gane hakan ne ta yau da safe da na kai cooler ɗinmu kitchen a zuba mana abinci, sai mama sauden (mai girkin ma'aikata) tace man ya ƙare, abun ya bani mamaki sosai, sai na share na koma ɗaki na haɗa tea cikin kayan da ya ameen ɗin ya siyo mana kafin ya tafi na sha. Da rana ma hakan ce ta kasance, wannan karon free ta fito ta faɗi man cewa an dakatar da bamu abinci a cikin gidan, saboda yanzu mu ba ma'aikata bane, abun ya bamu matuƙar mamaki, me hakan ke nufi ne? Ko dai wani ne ya ja mana wani sharri kuma? Umma ta ce ta bani haƙuri, da unurtata kada in sake komawa amso abinci, har saida suka mula, suka sha iska dan kansu suka bamu. Ɗan Abunda ke gare mu a ɗaki, shi muka dinga ci ni da ni da umma ta, sai gashi nima na koma cin abunda masu ciwon zuciya suke ci; amman ya zamuyi? Dole mu haƙura, babu, ce da zama ƙarƙashin wani ya ja mana. Amman ace a gida irin wannan ya wuce ace ana irin haka ga masu aiki, sai dai in da wani abu a ƙasa. **************** Da sallama ya shiga cikin ƙayataccen sashen nata, tana zaune bisa kujera tana waya da ƙawarta Hajiya Laila, cewa tayi ta bata minti biyu zata sake kiran ta, kashe wayar tayi tana mai amsa mashi gaisuwar da yake mata ciki ciki tayi, sannan ta ɗora da faɗin "ya aka yi ne Al'ameen?" "Mom kiyi haƙuri please, babu kyau iyaye na fushi da ƴaƴansu nazo ne in baki haƙuri" ya faɗa a taƙaice idanun shi na bisa fuskar ta don ganin yanda zatayi Ɗan guntun murmushi ta saki, cikin duniya ci tace "haba son menene haka? Ai ya riga da ya wuce, na san ba zaka yi Abunda zai ɓata man rai ba, Allah yayi maka Albarka" ina so kaje ka yankar ma su Afnan ticket saboda zuwa anjima zasu wuce, hutun nasu ya ƙare kada su rasa flight" "OK ya faɗa yana mai miƙewa cikin salon tafiyar shi ya taka ya fice daga part ɗin na mahaifiyar shi, da tin dawowar su bai shige shi ba sai yau, saboda bai san abin da zai je ya tada ba, zuciyar shi cike da wasu wasu, me mahaifiyar tashi take ƙullawa ne? Shi fa yayi mamakin sauri saukowa ta, Amman koma minene zai bita ta ƙarƙashin ƙasa in ta san wata ai bata san wata ba. Ita kuwa a ɓangaren ta, da murmushi ta bishi tana faɗin "yaro yaro ne, koda kuw ɗan giwa ne, kaman yanda ka bari cikin cikina, Al'ameen ka bar maryam da ɗiyar ta har Abadan abada, hhhhh" ta kyalƙyale da dariya shu'umanci, domin kuwa hajiya Lailan ta bata tabbacin hakan, ita kuma ta yarda da hajiya Lailan ɗari bisa ɗari, in tace zata yi, to fa zata yin ne, koda kuwa sama ce zata haɗe da ƙasan. ~Toh fa! Anya kuwa Hajiya Kubra Alkhairi take ƙullawa kuwa 🤔~ ~Ya makoma Suhan da Umman ta a Rayuwar da ake ciki na hana su abincin da zasu ci ma?~ ~Al'ameen kuwa ya bar maganar auren suhan ɗin? Ko dai irin abun nan yayi mata na yaro bari murna...~ ~Oum-Deedat cee~ [9/15, 7:36 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *_Page ~16~_* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Komawar Bilal ɗinne ya sanya abubuwa suka ƙara yi mashi yawa, ginin shi da kuma kayayyakin su da suka iso, wannan ce ta sanya hankalin shi ɗauke wa daga kan su suhan ɗin, to dama dai taimako ne kawai tsakanin shi dasu acikin ranshi, ba kaman yanda yayi iƙirarin soyayyar ba gaban mahaifan nashi. Ta ɓangaren mu kuwa, komai yayi tsanani, rashin abinci ai ba ƙaramar barazana bace ga ɗan adam. Idan hankalina yaso ya tashi umman tawa ce ke taɓo ni, da nasiha da wa'azoji da dama, dole ne in daure in maida komai ba komai ba, gudun ɓacin ran nata. Bamu da wani aiki a yanzu sai sallah, wanka da kuma bacci, mu kan share tsawon yini biyu bamu ci komai ba, saidai ruwa da kuma ɗan farau farau ɗin da muke kaɗawa mu sha, saboda rashin kuɗi a hannun mu, sai umma ta ce ta bani ƴan abunda suka rage a hannun ta na siyo mana fura cen cikin gari, muka dama muka ajiye in munji yunwa mu ɗiba mu tsiyaya ruwa mu kwankwaɗe, da haka har muka kwashe tsawon yini biyu Idan ma fita muka yi tsakar gida haka zamu dinga fuskantar ƙananan maganganu da habaice habaice daga sauran ƴan uwan namu ma'aikata, hakan ce ta sanya umma ta hanani fita, idan ba aike ba to fa mun gwammace muyi zaman mu a ɗaki umma tayi ta ƙara man karatu in mun gaji mu kwanta Ko wanki a banɗakin ɗakin namu nake yi mana, iyaka shanya ce zanyi a tsakar gida, sai sharar ɗakin namu da ƙofar ɗakin. Mun zama bare na ƙarfi da yaji a cikin gidan, gashi shi wanda ke ɗan tausaya mana ɗin ma ya ɗauke ƙafar shi ɗaf daga gare mu, afnan kuma sun riga sun koma tini, saidai kafin tafiyar tata, tayi dabara zuwa sashen mu, duk da ba kuɗi ta kawo mana ba, abubuwa ne masu yawa nata ta tattara ta bani, irin su kaya da kayan kwalliya. Ta ɓangaren su hajiya Kubra kuwa, komai ya mata yanda take so, magana ta mutu murus, su ɗin da ta tsana ko jin ɗuriyar su yanzu bata yi, lallai Hajiya Laila ƙawar tata hatsabibiya ce, gashi ko Alhajin ma ta dena jin zancen auren Al'Ameen ɗin a bakin shi, gashi ya sake mata sun koma kaman da cen yanda suke To dama dai ita ɗin wannan ne kawai burin ta, tini Al'Ameen ɗin ya samo masu kuku har biyu suna masu aikin abinci, Wannan ce ta sanya ta ci gaba da harkokinta cikin kwanciyar hankali, ta ci gaba da zuba mulki da isa da ikon ta kaman yanda take so Likafa ta ci gaba, yanzu bata ko zama sosai a gidan, tanƙamemen shagon kayan ƙyale-ƙyale da make-up ta buɗe, irin na manyan mata da riƙaƙƙun yara masu tashe da watayawa a faɗin Nigeria. Yara ta ɗiba kyawawa ta zuba suke aikin, wannan ce ta sanya wurin haɓaka, duk wata mace da ta amsa sunan ta a faɗin garin na Abuja shagon take zuwa ayi mata gyaran jiki, da kuma siyan kayan ƙyale-ƙyale da take yo order ɗinsu daga ƙasashe mabanbanta To shima Alhajin baiyi yunƙurin hana ta ba, asali ma, shi ma ɗin ba mazauni bane, gara ma Al'Ameen ɗin, yafi zama a gida Nigeria, yana kula da sauran ma'aikatan nasu da suke ma'aikata da kamfanoni daban daban. Duk da cewa ya fara jan Abie yana koya mashi abubuwan da suka danganci kasuwancin, shi kaɗai ba zai iya ba, ina zai kasu? Gashi yanzu amana tayi ƙaranci a wajen jama'a. ********* Duk wannan abubuwan dake faruwa, Al'Ameen ɗin bai san dasu ba, tsarin da aka ɓullo dashi a gidan na hana mu abinci, Yana iyakar ƙoƙarin shi ganin cewa babu wani ma'aikaci acikin gidan dake fuskantar matsala, Wannan ce ta sanya ya shafa'a Sam damu da al'amarin namu, gashi yanzu ko a hanya bama haɗuwa dashi, saboda babu inda nake zuwa, haka umman tawa, kullum tana ɗaki tana karatun ta, kuma tana iya bakin ƙoƙarin ta, wajen kauda tinanin komai, gudun sake tashin ciwon ta. Tafe yake cikin takunshi mai ɗaukar hankali, sanye yake cikin fari ƙal ɗin wandon jeans da riga ƙirar polo mai ruwan makuba. Cikin sauri ya kwala ma mudi driver kira, da ɗan gudun shi ya iso wurin, yana mai russunawa cikin girmamawa ga uban ɗakin nasu yake faɗin "Gani Alhaji" "Mudi gashi" ya miƙa mashi ƴan makullayen motar, "yau bana jin daɗi sosai, so bazan iya driving ba, ina so ne ka kai ni office, aikin gaggawa ya taso mani, da bazan ma iya fita ba" mudin ne yayi saurin amsar makullin, yana mai ƙara russunawa yake faɗin "Angama ranka ya daɗe" Buɗe mashi ƙofa yayi, ta mai zaman banza ya zauna sannan ya sake zagaya wa ya shiga yayi ma mota key, tare da danna horn ga mai gadi, cikin daƙiƙa da basu Gaza biyu ba ya wangale masu gate, yayin da mudi ya harba motar bisa titi, yana mai sake danne ma mai gadi horn alamar sai sun dawo, shi kuma ya shiga ɗaga masu hannu yana mai washe haƙora. Mudi ne ya shiga kallon ubangidan nashi ta gefen ido, dafe yake da kanshi dake sara mashi, kaman zai faɗo, gyaran murya yayi sannan ya shiga faɗin "ranka ya daɗe ko dai asibiti zamu fara zuwa ne?" Girgiza mashi kai Al'Ameen ɗin ya shiga yi cikin rashin son Magana irin tashi, sannan ya buɗe baki daƙyar yana faɗin "Naje jiya mudi, na sha magani ma ai" ɗan guntun murmushi mudin yayi kasancewar ya san ubangidan nashi yanda yake tsoron asibiti da Allura tin ba yanzu ba, idan akwai Abunda ya tsana baifi ace za'ayi mashi Allura ba Sake nisawa yayi cikin san gulma, "ummmmm yallaɓai nace, dama...... Uhm" ya faɗa yana mai ɗan haɗiye miyau cikin in-ina, "Ina jinka" ya tsinkayi muryar Al'Ameen ɗin yana faɗa a hankali. "Yallaɓai ka gafarce ni, na san in bani ba, babu mai zarafin gaya maka wannan maganar, dama ina ta son samun dama, ayyuka ne da naga sun yi maka yawa ne yasa ban tinkare ka ba" Ya isa mudi, kawai ka gaya man meke faruwa ne? " ya faɗa har yanzu idanun shi na a lumshe, hannun shi har yanzu yana a bisa kanshi, ya to kare shi da murfin motar " Maganar su Suhana ce Yallaɓai, yarinyar nan da suke zaune ita da mahaifiyar ta, da aka dakatar dasu daga aikin gidan..... " Cikin hanzari ya buɗe idanun shi, da suka kaɗa sukayi ɗan ja, hakan ce ta sanya suka ƙara shanye wa. Kallon muɗi ɗin yake yi cikin alama ta son jin meke faruwa dasu ne kuma? Baice ƙala ba, hakan ce taba mudi tabbacin yana sauraren shi kenan "Yanzu fa ba'a basu abinci a gidan nan, bama asan halin da suke ciki ba, gashi har yanzu lokacin albashi baiyi ba, nima a bakin saude mai dafa abincin naji, kasan su da ƙananan maganganu, kuma wai........ " Ya salam" ya furta cikin tsananin firgita, sauke hannun shi yayi bisa cinyoyin shi, hakan yayi daidai da ƙarasawar tasu bakin gate ɗin tanƙamemen company ɗin, mudi na shirin danna kan motar cikin gate ɗin da tini an riga an buɗe masu "Mudi" "Na'am Yallaɓai" "Mu koma gida, muyi gaggawar komawa gida, me ya sanya baka faɗa man ba tini? Wanene ya bada wannan damar ta hana a basu abinci?" Ya jefa ma mudi tambaya cikin ɓacin rai, "Magana nake yi maka mudi" Cikin sanyin jiki, da nadamar gaya mashi zancen da yayi muɗi ya duƙar da kanshi ƙasa yana faɗin "Allah ya huci zuciyar ka yallaɓai, Amman Hajiya Babba ce ta hana tin waccen tafiyar da kuka yi, mu kuma muna tsoron gaya maka a samu matsala, hajiya ta gane daga bakin mu maganar ta fito" Ya faɗa a sanyaye yana mai juya akalar motar zuwa inda suka fito. "Haƙiƙanin gaskiya raina ya ɓaci mudi, menene laifin yarinyar da mahaifiyar ta? Aikin ai basu ne suka ce basa yi ba, wannan ɗaukar alhakin yayi yawa mudi, ya kamata ka dinga sanar dani abubuwan dake faruwa a gidan, saboda na kula munafunci yayi yawa a tsakanin mata ma'aikatan gidan nan" Mudi ne ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya, yana faɗin "haka ne yallaɓai, Allah ya kyauta gaba, kayi haƙuri idan irin hakan ta ƙara faruwa, za'ayi gaggawar sanar da kai" Shiru ne ya biyo baya cikin motar har zuwa lokacin da suka isa zuwa ga gidan, ko daidaita tsayuwar motar mudin baiyi ba, Al'Ameen ɗin ya ɓalle murfin motar, cikin sauri da azama ya isa zuwa ga sashen na masu aiki. Cikin sallama yake ratsa sashen namu har zuwa bakin ƙofar ɗakin namu Kwance nake nayi matashi da cinyar ummata da take zaune gefen katifa tana ƙara man karatun umdatul ahkam, Nikam har ga Allah bana gane karatun Sam, yunwa ce kawai ke cina, ko motsin kirki na kasa yi, sauraren ta kawai nake ba tare da gane abunda take faɗi nake ba Ita ɗin ma ƙarfin hali take, rabon da mu sanya abinci acikin cikin mu anfi sati, kullum saidai farau farau wanda tin jiya ma furar tamu ta ƙare Sallamar shi ce ta dakatar damu daga karatun da mukeyi, banyi yunƙurin tashi ba, haka ma umman tawa bata matsa man ba, saboda ta san halin da nake ciki, ita ce ta yunƙura dakyal ta miƙe, bayan ta zame kaina daga saman tata cinyar. Ɗakin da yake sakaye ta buɗe, da ɗan murmushi a kan fuskar ta, sannan ta shiga faɗin " a'ah Muhammad ne? Shigo mana, ka tsaya daga bakin ƙofa?" Jiki a sanyaye ya sanya kai cikin ɗakin yayin da ummata ke shimfiɗa mashi yalwata ciyar dadduma a gefen ta katifar daga ƙasan tiles ɗin Zama yayi yana mai gaida umman tawa, cikin natsuwa da girmamawa, haka itama umman tawa ta shiga amsawa da ɗan murmushi a kan fuskanta, kai daga gani ka san na yaƙe ne. Nikau dakyal na ɗaga na zauna gami da ja na jingina jikin bangon ɗakin "Ina kwana?" na faɗa a hankali, murya ta har bata fita sosai, kallona yayi cikin ido sosai yana mai amsawa, ya ɗauke kanshi zuwa ga umman tawa. "umma nazo ne in baki haƙuri, a bisa Abunda yake faruwa acikin gidan nan" ya nisa sannan ya ɗora da faɗin "Sam bansan me ke wakana ba, sai yanzu ne mudi driver ke faɗa mani, umma menene ya sanya in irin haka ta faru ba kwa sanar dani da gaggawa? Idan an dakatar daku aiki, ai ba hakan yana nufin ba kwa cikin gidan bane, kuna nan kaman yanda kuke a da" Ya tsagaita yana kallon umman tawa da kanta yake ɗan duƙe tana murmushi, dame zata saka ma Al'Ameen ɗin? Lallai yaro ne ɗan albarka da bai biyo halin mahaifiyar tashi ba Sam, murmusawa tayi ta shiga faɗin "kai haba babu komai ai Al'Ameen, Hajiya bata yi komai ba, ni ban ma so muɗi ya faɗa maka maganar ba, bana so hakan ya kawo saɓani tsakanin ka da mahaifiyar ka Muhammad, don Allah ina so ka bar zancen nan, Mungode da alkhairi ka gare mu, Allah yasa ka gama da iyayen ka Lafiya, ka cigaba da yi masu biyayya, insha Allah zaka ga haske a rayuwarka" Cikin jin daɗin addu'ar da umman tawa tayi mashi ya murmusa yana faɗin "Ameen Umma, nagode kwarai da addu'ar ki, ina mai ƙara baku haƙuri insha Allah komai yazo ƙarshe, ina so komai ya tsaya iya mu ne dake nan, ku siyo abubuwan buƙata da Abunda zakuyi girki iyakar naku, ku dinga cin abinci, duk abinda kuke buƙata kuma insha Allah ku tuntuɓeni kai tsaye ina tare daku. Kuyi haƙuri da halin mahaifiya ta, ina mata Addu'a Allah yasa ta gane gaskiya" Miƙewa yayi tsaye gami da ajiye mana kuɗi masu yawa sosai, gami da complement card ɗinshi da yake ɗauke d suna da number tashi ta waya, sai kuma matsayi shi na MD Dambulan And CEO Dambulan Estate and More, sai Address ɗin Office ɗin nashi. Murmushi umman tawa tayi tana mai Cewa "a'a Muhammad ba zamu karɓa ba gaskiya, abun yayi yawa, ai ana hidima damu, kwarai da gaske, Allah ya ƙara buɗi" Ameen ya amsa yana daga tsaye, yake faɗin "Umma ki amsa Alkhairin da nayi maku, ba kowa ya sanya ni ba, ni na sanya kaina, ba roƙona kuma kuka yi ba, ni ne naga dacewar hakan, indai kin ɗauke ni ɗanɗan ki da kika haifa, ki amsa ki sanya man Albarka umma" yana gama faɗar haka ya juya ya fice cikin azama, har yanzu kan nashi na sara mashi matuƙa gaya Da kallo nabi bayan shi har ya idasa ficewa gaba ɗaya daga ɗakin namu, ajiyar zuciya na sauke a hankali ina mai zamewa na kwanta lamo abubuwa da dama na man kai kawo cikin ƙwaƙwalwa game da wannan cukurkuɗaɗɗiyar rayuwa da muke yi. Watau ni na ma rasa gane kan wannan mutum wallahi, Ya Ameen daban yake cikin mutane, kallona na maida kan uban damin kuɗin da ya ajiye, in ba gizo idanuna keyi man ba, raper ce ta ƴan dubu ɗaya har guda biyu, sai katinshi da ke bisa kuɗin ajiye, Ba ɓala lokaci na mirgina ina mai wawurar kuɗin, na sanya hannu na zaro masu ɗan yawa ina Miƙewa kaman zan faɗi Mun daɗe bamu da ko sisi a daƙin, me zamu tsaya jira tinda ga dama tazo ta iske mu har inda muke? Ban bi ta kan ummata ba, na zari hijab ɗina ina mai ɗaura wa bisa kayan dake jikina na atamfa ɗinkin doguwa riga bubu dake jikina "Umma me zan fara siyo mana muci kafin mu nemi mafita?" na furta daga tsaye ga dukkan alamu ma ba sauraren cewa da take yi "ke suhan menene haka?" nake yi ba Ɗan murmushi tayi cikin tausaya war mahaifiya ga yaron ta ta shiga faɗin "Ko me kika nemo mana suhan zanci" "To umma" Na faɗa ina mai ficewa a daƙin, da zallan kallon tausayi ta bini dashi hawaye na biyo kuncin ta suna silalowa, "Allah yayi maki Albarka Hauwa'u ya ƙara shirya man ke, ya baki miji nagari, mai tausaya ma maraici ki, Allah ya ƙwato maki haƙƙin ki, ya kuma saka ma zalumcin da aka yi maki Ameen. Ta daɗe zaune tana kuka tana share wa, gami da jera ma gudar tilon ɗiyar tata adduo'i na alkhairi da take fatan su bita ko bayan babu Rayuwar ta, sannan ta miƙe gami da kauda sauran ragowar kuɗin da kantin kada ƴan bani na iya su leƙo su gani, ɓalli ya tashi, Abundant bata sani ba, tin bayan shigar Al'Ameen ɗin sashen ma'aikatan, mama uwani, da mama Talatu sun gashi, suna laɓe bayan ƙofar ɗakin su suna hangensu, saidai basa iya jiyo me yake faɗa ko kuma me yake wakana acikin ɗakin, fitowarshi, da kuma fitowar suhan ɗin ba jimawa da fitar Al'Ameen ɗin duk sun gani, Cikin sauri mama uwani ta fito ta bi bayan Suhan ɗin, saidai cikin rashin sa'a ta tadda Al'Ameen ɗin ya fice cikin motar shi, da matsananci gudu yayin da ita kuma suhan ɗin tabi ta gefen titi tna tafiya alamar ma tafiyar tasu bata zo ɗaya ba, tinda su a tinanin su ko Al'Ameen ɗinne zai ɗauki suhan ɗin su tafi tare da ita. Abinda duk basu sani ba shine, Al'Ameen ɗin dukan su tara su yake yi, lokaci yake jira yazo da dukkan su zai shayar dasu Madarar mamaki. _Masu karatu kada fa ku manta har yanzu fa a cikin ma'aikatan gidan, babu wanda ya san da maganar auren Suhan ɗin da Al'Ameen ya bijiro da ita, har ita kanta suhan ɗin da umman ta_ ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:36 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~17~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Tini rahoto ya isa kunnen Hajiya kubra, wannan ne ya sanya ta wakilta mama talatun da ta kai mata tsogumin zuwa ɗakin namu ta duba mata me ke wakana, domin dai ita dakanta ba zata iya taka sashen masu aikin ba. Cikin sa'a kuwa, ko da ta isa ta tadda umman tawa zaune bakin katifa tana jan carbinta a hankali yayin da idon ta yake kulle haka ta jingina bayan ta da jikin bangon ɗakin, bata yi sallama ba har saida ta isa tsakiyar ɗakin tana mai ƙare ma dukkanin lungu da saƙo dake cikin ɗakin kallo, cikin matuƙar mamaki umman tawa ta buɗe idanun ta tana mai bin mama talatun da kallo wadda har ta samu gefen katifa ta zauna, Amman duk da haka bata bar bin loko loko na ɗakin da kallo ba, ko zata hango wata leda ko wani abu. "A'a Talatu ce yau a ɗakin namu? Sannu da zuwa" umman tawa ta faɗa cikin ɗan murmushi haka kaɗan a fuskar ta, domin dai ta san me ya kawo mama talatun ɗakin namu "Eh wallahi kuwa Maryama, nazo duba jikin naki ne, ya ƙarfin jiki?" ta faɗa cikin ɗan ruɗewa kaɗan kama ta da umman tawa tayi tana mata kalle kalle a ɗaki. "Aikuwa Naji sauƙi sosai Alhamdulillah wallahi Talatu, kinga kaman ba ni ba Naji ƙarfin jiki na, Allah dai ya saka da Alkhairin sa" Umman tawa ta faɗa tana mai komawa ta jingina da bangon, daga haka ta ja bakin ta ta tsuke, hakan da mama talatun ta fahimta ne ya sanya ta cewa "Madalla Madalla, Allah ya ƙaro afuwa" ta miƙe cikin hanzari zata fice yayin da umman tawa ta bita da ameen tana mai kallon bayan ta, gami da girgiza kai a hankali a hankali Daidai bakin ƙofa muka haɗu da ita, gaida ta nake yi ma, Amman Sam hankalin ta na ga ƙatuwar ledar da na ciko mana ita taf da siyayyar abinci da zamu ci kafin muyi tinanin mafita. Har na gitta ta na shige ɗakin tana tsaye tana bin ledar da kallo, domin sanin menene ciki, niko ba ta ita nake yi ba, sanin halin ta da nayi, sai ma na tsinci kaina da baƙin cikin shiga ɗakin namu da tayi, koda yake ba zuwan kanta bane turo ta aka yi. Jiki a matuƙar sanyaye ta wuce direct zuwa sashen hajiya Kubran ta zauna zaman jiran ta fito, domin taji ba'asin aiken da tayi mata. Ta ɓangaren mu kuwa ba ma ta ita mukeyi ba, abincin mu muka ci cikin jin daɗi, da sanya ma Ya Ameen albarka, ko babu komai ya zo mana a lokacin da muke buƙatar shi, mu bamu damu da halin mahaifiyar shi ba, ko ma me zata yi ai yunwa bata da hankali. Ƙarya da gaskiya ta shiga zayyane ma Hajiya Kubran, yayin da ita kuma take zaune hakimce tana sauraren ta, take gyaɗa kai a hankali, lokaci guda ta sallami talatun da take faɗa mata ƙarya da gaskiya gami da kiran hajiya Laila aminiyar ta, kuma maganin kukan ta. **************** Washegari tin da sassafe sai ga mudi driver ya mana sallama, gami da miƙo man fararen takaddu ƙal dasu, yake shaida man Alhaji ƙarami yace in cike zai aiko shi ya amsa anjima Amsa nayi gami da mashi godiya, na koma cikin ɗaki fuska ta fal da annashuwa, farin ciki nake yi sosai matuƙa, domin dai ko ba komai na fahimci ya danganci karatu na ne, umma ta na shiga nuna mawa, itama tayi murna sosai, gami da ƙara gode ma Al'ameen ɗin da ya tsaya ma Al'amarin mu kai da fata. Bamu kaɗai yake ma haka ba, kowa a cikin gidan yana taimaka mashi, muddin abun ya sha kai, domin kwanaki ma sai da ya biya maƙudan kuɗi aka yi ma yarinyar mama saude mai girki aiki, muma cikin gida ne muke ta jin raɗe raɗi, da irin taimakon da yake ma ma'aikatan baya ga albashin su. Cikewa na shiga yi, da gani dai kaman Jarabawa ce zan rubuta watau Jamb, inda naga ban gane ba sai in tsallake, a haka har na gama na maida cikin folder ɗin na ajiye jiran mudi yazo ya amsa. Wannan ce ta bani damar yin aikace aikace na cikin jin daɗi, lallai ina dab da cika buri na, abun ya matuƙar ƙarfafa man guiwa, saidai na nazo wajen zaɓen choice na Abunda zan karanta tsallakewa nayi, na bar mashi ya zaɓa man, duk abinda ya zaɓa man daidai ne. Zuwa azahar na gama komai, har list ɗin abinda zanje in sissiyo mana na buƙata nayi, wanka nayi cikin shiri na simple ba mai ɗaukar lokaci ba, doguwa riga ta material ce jiki na, Afnan ce ta bani ita cikin kayan da ta kawo mani kafin ta koma, da gani ma bata taɓa sanya ta ba, ta amshe ni matuƙa, gyale na ɗauko zan yafa, umma tayi man wani irin kallo, ba arziƙi na ajiye ina ƙumshe dariya a ciki na, oh umma bata so taga nayi gayu, ita har kullum gani take yi ba'a matsayin kowa muke ba, in ana ganin ka ƙwas-ƙwas ma sai ayi ta gulmar ka acikin gidan, dama ga shi ga irin zaman da mukeyi acikin gidan. Sallamar mudi ce ta katse man dariya da nake yi a zuciya, ɗauko takaddun nayi na miƙa mashi ina ƙara mashi godiya, amsa yayi yana dariya tare da ƙara ma umma ta ya jiki, saboda ɗazu da yazo basu gaisa ba. Sai da na gama kitsawa sosai, sannan na ɗauki ƴar jikka ta gami da takadda ta list ɗin abubuwan buƙatar, sallama nayi ma umma gami da ficewa daga ɗakin namu kai tsaye zuwa ga barin gidan cikin salon tafiyata da lokutta da dama umma ta kace Allah yayi mani nawar tafiya, su kuma sauran ma'aikatan kance ya ga ce, kai ba kowa kowa ba Galadima kashi🤣 Tin daga nesa na hango shi tsaye jingine jikin motar shi, mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, baƙa ce wuluk sosai, saidai gilassan ta masu sauƙi duhu ne, ni ban ma taɓa ganin shi a cikin wannan motar ba, da gani dai sabuwar siye ce, to abu da masu abunsu Sanye yake cikin riga ƴar shara, da wando dogo har ƙasa, kanshi babu hula saidai baƙin gashin shi da akoda yaushe yake kwance luf bisa fatar kanshi, hannun shi na riƙe da makullan mota da takaddun nawa a hannun shi yana dubawa, Baƙin sun glass ɗin da ya sanya ma idanun shi, su ke katange ka daga kallon cikin ƙwayar idanun shi, kaman kullum dai yana tsaye cikin kwarjini shi, da kamalar shi, Al'ameen mutum ne da idan ka kalle shi sai ka ƙara kallon shi Duk da ba ni yake kallo ba hakan saida ya jaza mani harharɗewa, cikin son gyara tafiyar tawa na isa daidai saitin inda suke tsaye shi da mudi driver "Ahaf, yallaɓai ai gama ta nan tafe" mudi ya shiga faɗa mashi, ga dukkan alamu magana suke yi ko kuma aika mudin yayi ya kirawo ni. "OK ce mata tazo ina kiran ta" Abunda ya faɗa kenan, har yanzu idanun shi na kan takaddun ko sau ɗaya bai ɗago ya kalle ni ba, Kwala man kira mudin yayi "Ke Suhana, kizo yallaɓai na kiran ki" chak naja na tsaya, da ɗan ɓacin rai a fuskanta, in ma kiran ne ai sai ya isa inda nake ba ya kwala man kira ba haka gatsau kowa na saurare. A hankali na juya akalar tafiyar tawa daga nhfar gate ɗin zuwa wurin su inda suke tsaye, da sallama a bakina na isa lokaci guda ina mai gaida shi "Yaya ina wuni?" bai ɗago ba har yanzu idanun shi na kan takaddun yana nazari su ya amsa mani da "Lafiya" a gajarce Gyara tsayuwa ta nayi duk a takure nake wallahi, kwarjini shi kan ƙara ruɗani, ɗan guntun murmushi naga ya saki, yana mai juyawa kai tsaye zuwa ga bakin motar tashi ya sanya makullan da suke hannun shi ya buɗe tare da ɗauko wasu biruka guda biyu ya dawo inda nake tsaye Still bai kalle ni ba, ya shiga man tambayoyi wasu ina bashi amsa, wasu ina yin shiru dan ban sani ba. Choice ɗina ya tambaya na Abunda zan karanta, nan ma shiru nayi mashi, murya ta har rawa take idan zan bashi amsa da ya kula, inda Allah ya taimake ni mudi da yake tsaye ta gefen mu yana sauraren mu. Maimaita man tambayar yayi, cikin san kauda shirun da nayi na duƙar da kaina sannan na shiga faɗin "Yaya na bar maka zaɓi, duk abinda ka zaɓa man, ni bani da wani zaɓi, ko wane course ne dai insha Allah zan iya kuma zanyi" Ɗan shiru yayi jin ta kai aya, ɗagowa yayi a hankali ya zare glashin dake manne a idanun nashi yayi, kafe ni yyai da idanun shi, aikau na ƙara sadda kaina ƙasa, ko alama bana iya ɗago fuskata balle in kalli cikin ƙwayar idanun nashi da har wani zaiba zaiba suke yi "OK zaki iya tafiya" Abunda yace kenan ya maida idanun shi kan paper ɗin, alamar ya sallame ni kenan Cikin ƴar sassarfa na bar wurin ina mai hamdala da tambayoyi ba suyi tsawo ba, ba zai iya fahimtar yanda nake ji da aduk lokacin da magana ko tsayuwa ta haɗa mu wuri ɗaya dashi ba. Cikin san kauda tinanin na tare abun hawa na hau, ina mai faɗa mashi inda zai kai ni, saidai duk yanda naso inbar tinanin ya kasa bari na, ko wanne course ne zai zaɓa man ni suhan? Koma dai minene kuma koma dai wanene zanyi insha Allah, da haka har na isa inda zani,na gama abinda nake yi na juyo gida da tarin siyayya ta *************** Abubuwa sunyi mana matuƙar sauƙi, yanzu kam Alhamdulillahi, kwana biyar kenan ban kuma jin ɗuriyar hajiya ba, balle ƴan baran dan ta, hidimar bikin su aunty Saudat aka shiga yi ga dan gadan, abun ka da masu dashi, bikin dududu sati huɗu aka sanya shi, bayan iyaye sun shiga al'amarin, matuƙa Hajiya Kubra taso Al'ameen ɗin ya fidda matar aure, Amman fir ya nace shi fa indai bata kyale shi ba, tau ya riga ya zaɓi mata, kuma a shirye yake a ɗaura auren shi ko ma yaushe ne, in ma dasu Nihal ɗin za'a haɗa duk ɗaya ne Hakan ya tada hankalin hajiya, ta ƙara kafa mana karan zuƙa, gashi yanzu ta fiye ta fiye suke ta yi, yin oder ɗin kayan ɗakin su Nihal ɗin, nima na samu ɗan sauƙi, domin yanzu na rabu da wahalhalun su, bama kullum muke haɗuwa ba, duk da duk lokacin da zamu haɗu ɗin saƙon harara ne kawai za'ayi ta aike mun har sai na wuce sannan a bini da daigon tsaki wani lokacin harda tofar da miyau, sannan ace Allah shi kyauta mu haɗa iri da waɗannan mugayen talakawan ƙasƙantattu. Duk da bana jin me suke faɗa, hakan na mani ciwo, na dai san magana ce marar ɗaɗi suke faɗa a kaina da umman tawa, wannan ce ta sanya bana ma rawar ƙafa ko ɗokin zuwan bikin nasu, duk da wani lokaci ina jin sanyi na zasu bar gidan zan ɗan samu sauƙi, saidai nima ɗin ai ba zamana kenan ba a gidan Ƴar ƙaramar waya ta ce ta ɗauki ringin, ajiye gugar da nake yi nayi, cikin mamaki na ɗauki wayar ina duba number ɗin da ta kira ni, na kasa ɗagawa har ta katse, ɗan taɓe baki nayi na ajiye, cikin zuciya ta ina mai faɗin koma waye in ya masu ya kira, Nidai bana da kati a waya, kuma bana da wannan number ɗin a waya ta, dama in Naji kira, ko dai Afnan, ko Aunty Saudat, ko Aunty Nihal, sai kuma ita uwar gayyar Hajiya Kubra, ko cikin ma'aikatan banda number kowa sai ta Mama Talatu, itama dan ita ce shugabar mu. Cikin ko in kula na cigaba da Abunda nake yi, ina kallon umma ta na bina da ido har wayar tawa ta sake ɗaukar tsuwwa, cikin natsuwa na danna madannin amsawa da sallama a baki na "Assalamu Alaikum wa Rahmatullah" Abunda nace kenan naja baki na na kulle, shiru ne ya biyo baya na tsawon daƙiƙa biyar, cikin mamaki na ɗaga na kalli fuskar wayar, Still dai wayar na tafiya alamar ba'a datse kiran ba, har zan danna da niyyar kashewa ganin nayi sallama ba'a amsa ba, kuma ga dukkan alama koma wanene yana jinya yayi man shiru Muryar shi ce ta karaɗe illahirin kunne na, cikin salon maganar shi dake tafiya da hankalin mai sauraren shi ya amsa man sallama cikakkiya kaman yanda addini ya koyar. A ɗan zabure na ɗaga wayar ina mai ƙara kallon number, kaman mai son gano ainahin kamannun shi a fuskar wayar, natsuwa na nema na sanya ma kaina, gudun kada ya gane mamakin da nake yi, ko ba'a faɗa ba shine, ina ya samu number na? Zuciya ta ta shiga saƙa man, "Afnan" wani ɓangare na zuciyar ya bani amsa, ganin ba zai ce komai ba, na kauda shirun ta hanyar gaida shi "Yaya ina kwana?" "Lafiya" ya bani amsa a gajarce, ga dukkan alamun shi ne yin magana a gajarce, ya kauda man tinanin da nake yi ta hanyar faɗin "Ki shirya Gobe kuke rubuta Jarabawa, zan aiko mudi ya kawo maki abun buƙata, ƙarfe takwas na safe, in kin shirya ki kira ni da wannan Layin" yana gama faɗar haka ya datse kiran. Da kallo nabi wayar, kaman mai son gano wani abu, a sanyaye na ajiye wayar daga kunne na, ina mai kallon umma ta d take bina da kallon tana buƙatar ƙarin bayani, "Eh umma, yaya ne, yace gobe zan rubuta jarawaba, muɗi zai kawo man abubuwan da zan buƙata" na ɓata amsa, ina mai sanya hannu na kashe Iron ɗin da nake gugar gami da silalewa na kwanta bisa tantagaryar tiles ɗin dake manne da ƙasan ɗakin, nayi matashi da hannuwa na. Umman bata ce man komai ba, ta miƙe tsam gami da shige wa toilet ɗin dake cikin ɗakin tana mai mani addu'ar nasara acikin zuciyar ta. Na daɗe ina muɗiɗɗika a tsakiyar ɗakin, nama rasa tinanin da zanyi, mudi yayi sallama a bakin ƙofar ɗakin, tsam na miƙe gami da buɗe ƙofar ina mai gaida shi, ya miƙo mani leda irin ta botique gami da cewa "gashi inji Oga" Amsa nayi gami da gaida shi, ya man sallama ya wuce, yana mai cewa in gaida umma ta, da kallo na ishi, ko babu komai mudin yana daga cikin mutanen da nake ganin girma da daraja shi a idanu na, ganin cewa ban taɓa samun shi da koda alamun munafirci ba, irin na sauran drebobin gidan da zaka ga suna ƴan ƙusƙus da su mama mama Talatu da mama uwani. Zaune nake ina ta juya ledar na gagara buɗewa, har u mata ta fito daga cikin banɗakin ga dukkan alamu dai wanka ta gama, "Menene haka? Kin Gaza buɗewa ki duba, ko kin fasa karatun ne?" umma ta jefo man tambaya tana mai zama gami da janyo kwandon kayan shafan ta tana mutsittsika mai a jikin ta. Ban amsa mata ba, na shiga buɗe ledar bina fiddo kayan dake ciki, uniform ne ma su masifar kyau, da sandal da socks farare ƙal, sai ƴar ƙaramar jikka ta goyo Amman irin ta zamani an yi mata ado da flowers masu ƙyau da ƙyalƙyali, sai litattafai tili guda na karatu, da suka danganci physics, chemistry, biology, english mathematics ds. A hankali na shiga warware kayan da suke a goge tas, da gani sababbi ne, skirt ne iyakar guiwa, sai riga longslip da belt da gani tok-in akeyi sai ƴar ƙaramar hijab, da zamu iya kiran ta kai tsaye da himar, cikin kwalalo idanu na kai duba na kan ummata da ta dakata da shafa man tana mai bina da idanu, baki na a buɗe na shiga girgiza kai, "bazan iya sanya waɗannan kayan ba, da gani ma wannan makarantar ba ta musulmai bace" Umma ce ta wurga man wani irin kallo sannan ta shiga faɗin "kar ki sanya ɗin, sai ki canza wasu ai, tinda tsarin ki zasu bi, ko ba ta musulmai bace, ai rana ɗaya ne sai ki sanya dogon hijab, in kinje can kya cire, kada kiyi wasa da damar ki suhan" Linke kayan na shiga yi ina mai jinjina yanda zan sanya kayan nan in rasa mutane, kaman wata ƙaura, Amman ba zance ba zan sanya ba, ko don gudun wasa da dama guda da Allah ya bani. Haka na kwana karatu, lallai na yarda in ka bar karatu da yini guda zai barka da shekara ne, haka na dage nayi ta cusawa ina criming da joting har na samu na samu iya abinda zan iya ɗauka, san nan na duƙufa salla da addu'ar neman nasara, da da cewa duniya da lahira ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:37 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~18~* *Kyautar Page gare ki _Fatima Batula_ marubuciyar BUGUN ZUCIYA TA Nagode da ƙauna da kuna sadaukar da Page da kika yi mani, ina sonki tsakani da Allah kaman yanda kike so na, haka nagode da Alkhairin ki gare ni, Page ɗinnan naki ne, in kinga dama ki hana kowa karantawa* 🤣 ~Masu karantawa Bakwa comment, kuna yi ma kanku, in mu marubuta mun yi maku yajin rubutu, naga me zaku karanta kuma har ku share?, in kunyi mana comment kun ƙara ƙarfafa mana guiwa dame kuka ragu? Ai ka nuna kaji daɗin Abunda akeyi maka ma wani ɓangare ne na godiya, haba jama'a, ai ko Allah da ya halicce mu yana son godiya balle mu da ya halitta ya sanya mani hali irin na ɗan adam, da kuma son a gode mana, da nuna Abunda mukeyi kuna amfanuwa dashi, please ku gyara ba don mu ba~ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Shawarar umma na bi, bayan na gama shiryawa, ni kaina kunyar kaina sai ta kama ni, ina kallon umma tana satar kallo na tana girgiza kai. Riƙe nake da wayar tawa sai jujjuya ta nake yi ina daga tsaye, na kasa kiran shi, gashi lokaci yana daɗa ƙurewa, har takwas saura, shahada nayi na danna ma Layin nashi kira, wannan ne karon farko da hannu na zai soma kiran wani ɗa namiji a rayuwa ta, shi ɗin daban ne, abubuwa da dama shine mai buɗe man ƙofofin yin su. Na zurfafa a tinani har wayar ta katse ban sani ba, sai dubawa nayi naga ashe ma bai ɗaga ba, ban ƙasa a guiwa ba na sake gwada kira, still dai bai ɗauka ba, haƙura nayi na koma gefen katifa na zauna, ina mai gyara safar dake ƙafa ta da take fara ƙar, sai ɗaukar idanu take yi. Ci gaba nayi da craming ina mai gyara zaman jikkata a saman kafaɗa ta, idan ka kalle ni kai zaka rantse da Allah ba ɗiyar Hausawa bace, kayan sun matuƙar fidda man shape, skirt ɗin da yabi lafiya ƙuguna ya zauna ɗas kaman a wajen aka ɗinka shi, nayi matuƙar mamakin yanda aka yi har ya gane size ɗin kayan da zasu iya yi mani Miƙewa nayi ina gyara zaman belt ɗin a saman ƙhgu na da yabi shafaffen cikina, kai kace bana cin abinci, duk da ni ba siririya bace hakan ce ta sanya kayan suka cika ni nayi ɗas ɗas dani. Waya ta ce ta ɗauki tsuwwa alamar ana kira na, cikin hanzari na ɗaga kasancewar naga har takwas saura minti sha biyar tayi, gashi yace ƙarfe takwas ne ake shiga Jarabawar, sallama kawai nayi ko amsa mani baiyi ba, cikin hanzari yace "Fito" Abunda ya faɗa kenan ya datse kiran Sallama nayi ma umma, ta shiga bina da addu'a kuwa, gami da gargaɗa ta da in kama kaina, in tsare mutumci na, kasancewar makarantar wadda take haɗe maza da mata, da murmushi na bita, ina jaddada irin ƙaunar da umman tawa take mani, da son kasancewa ta ta gari a duk inda na shiga. Hannu na sanya na ɗauki gogaggiyar zumbuleliyar hijab ɗita da take ajiye gefen katifa nayi, na warware ta na sanya, ba ɓata lokaci na fice daga ɗakin namu addu'a ɗauke a bakina. Kasancewar safiya ce, babu kowa a harabar gidan, balle ƴan tsurku su samu na rahoto, ko ba haka ba ma kuma ɗaukacin mutanen gidan basa nan, wai sun tafi turkey siyayya, cikin hanzari na isa ga motar da take fake tsakiyar harabar gidan, da gani a cikin ta ne za'a kai ni makarantar. Baya na buɗe zan shiga, har ga Allah na ɗauka muɗi driver ne zai kai ni, "dawo gaba" muryar shi ta doki dodon kunne na, ba gardama na maida murfin na rufe gami da buɗe gidan gaba na shiga. Ko zama ban daidaita ba ya fizgi motar gami da ficewa daga harabar gidan da tuni mai gadi ya wangale mashi gate. "Kina cen kina shiririta har kin so ki makara" Abunda ya faɗa kenan ya maida bakin shi ya rufe kaman ba shine ya mani magana ba, ɗan ɗagowa nayi gami da ɗan waiwayawa ta gefen da yake zaune yana tuƙi na ɗan kalle shi haka, tuƙin shi yake cikin kwanciyar hankali da kwarewa, sharara gudu yake yi kaman waɗanda zasu bar gari, yayi kyau abun shi, cikin manyan kaya, da dukkan alamu yana son manyan kaya kaman ya san suna matuƙar da cewa dashi, ɗinkin dakakkiyar shadda ce mai masifar kyau da ɗaukar idanu, zamu iya kiran ta da royal blue, hakan ce ta sanya fatar shi haskawa sosai, fatar nan tashi kaman bata shan rana, lumui ga gashi da yake kwance saman ta, hannun shi na ɗauke da zoben azurfa mai kyau da ɗaukar idanu, yayin da agogon shi ƙirar iphone take ta walƙiya cikin hasken ranar da ya riga ya gama hudowa. Maimakon in bashi ansa, sai na kauda zancen da cewa "Yaya Ina kwana?" Bai bani amsa ba, sai ma ɗagawa da yake yi yana kallon agogon dake maƙale a hannun nashi, yana sarkin ɗan siririn tsaki. Daidai bakin gaye ɗin makarantar yayi parking, yana mai waiwayo wa ta inda nake zaune yake faɗin "Ki tabbatar kin cire wannan hijabin kafin ki shiga makarantar nan, doka ne gashi nan rutuce a jikin gate"da" to" na bashi amsa ina mai ficewa Tsayawa nayi tinanin ta ina ma zan fara cire wannan hijab ɗin ni na ma rasa ta yanda zan ratsa tsakiyar mazan dake ta wucewa zuwa cikin makarantar ga dukkan alamu dai mun soma makara. Ban aune ba Naji muryar shi ta baya na yana cewa "ba zaki hanzarta ba sai sun rufe shiga? Bani hijab ɗin nan, ba zasu bari ki wuce da ita haka ba, zasu ga kaman exam malpractics zakiyi da ita, bana son ƙauyanci" ya faɗa yana mai ƙara sowa ta inda nake tsaye Ɗan waiwaya wa nayi ina mai kallon shi cikin ɗan marairaice fuskar da babu komai samanta, daga hoda sai kwallo da lip balm, Miƙoman hannu yayi alamar in cire na bashi. Soma kiciniyar cire wa nake yi Naji yana faɗin "ai bake kaɗai bace a haka, haka dokar makarantar take, su a kamarantar su ake rubuta jamb ɗin, student ɗinsu basa zuwa ko ina, kiyi maza ki shiga bana so a samu wata matsala" Miƙa mashi na yi, gami da juyawa na fara taka wa a hankali zuwa ga shiga makarantar da duk na tsargu, gani nake kaman kowa ni yake kallo, Amman a zahiri ba haka bane, wasu ɗaliban ma harda ɗan gudun su, zuwa cikin makarantar hankalin su duk baya jikin su, tafiya nake yi ina ɗan ƙara jan skirt ɗina ƙasa har ga Allah a takure nake. Daf da zan shiga makarantar ne na ɗan juyo haka, yana nan dai tsaye inda na bar shi, ni yake bi da kallo duk wani taku na ɗaya akan idanun shi suke, wuf na faɗa cikin gate ɗin gami da ƙara ɗaga ƙafa cikin sauri na doshi babban hal ɗin makarantar da naga kowa na nufa. Ɗan jingina bayan shi yayi da jikin motar yana mai sauke ajiyar zuciya, tabbas sai yanzu ne yake na damar menene ya zaɓa mata wannan makarantar da uniform ɗinta suke haka? Kayan sun matse ta da yawa, yanzu a haka kowa zai ta kallon ta? Amman baya da yanda zai yi, makarantar ita ce makaranta mafi girma da kyau da ƙayatuwa a duk faɗin garin na Abuja, makaranta ce da aka yi recomending akan irin ƙoƙarin ta da hazaƙarta, ɗaliban makarantar basa faɗuwa exam duk wahalar ta, saboda suna follow-up da kuma jajircewa wajen ganin ɗaliban nasu sun kai ga gaci. A hankali ya shiga taka wa har zuwa ga motar murfin motar ya buɗe gami da zama, tada motar yayi yana mai ajiye hijab ɗin kujerar da shan ɗin ta tashi. Ya rasa dalilin shi na damuwa da halin da yaga suhan ɗin ta shiga na tsarguwa da kanta, ya san tarbiyyar ta ce haka, shi in ba yau ba ma zai iya cewa bai taɓa ganin ta da ko gyale ba ma balle kayan da suka matse ta haka ba, ɗan runtse idanun shi yayi yana buɗewa gami da ɗan bugun sitiyarin motar, ji yake kaman yaje ya maida mata hijabin ta ta ɗora saman waccen da ita da babu duk ɗaya ne. A haka har ya isa office ɗin nashi tinanin bai bar shi ba, yaji duk ya rasa sukuni, bai san menene haka ya tsaya ya to kare mashi zuciya da maƙoshi haka ba. To ko bayan ya shiga office ɗin kasa taɓuka komai yayi, sai jujjuya kujera yake yi idanun shi a rufe ya ɗaga kanshi sama, duk da ya rasa tinanin da zai yi, ƴar ƙaramar ajiyar zuciya yayi yana mai jawo wayar shi ya latsa kiran lambar Bilal domin yaji ya shirye shirye nashi bikin ke tafiya. *************** Cikin ikon Allah, ba zance banji wahalar exam ɗin ba, saidai zan iya cewa ta zo man Da sauƙi ba kaman yanda na zata ba, karatun da nayi ya matuƙar taimaka mani, inda na ɗan samu matsala kaɗai cumputer ɗin da ban san yanda ake amfani da ita ba, inda Allah ya taimake ni an nunnuna mana yanda duk zamuyi, sai gashi kafin lokaci ya cika ma na gama duka, ina dai ta addu'a cikin zuciya, saboda Jarabawa dace ce, ba ƙoƙarin ka ko hazaƙarka ke baka ba, iko ne kawai na Allah. Bayan mun futo ne, ina jingine jikin bangon hall ɗin tsaye rataye da ƴar jikka ta, wayata tayi tsuwwa. Ina ɗauko wa naga Afnan ce, cikin hanzari na amsa, gaisa wa muka yi cikin mutu ta juna da ƙaunar juna ta shiga zaulaya ta, tana ceman ya exam ta kira yayan ta yace mata ina cikin exam, kuma ga lokacin da zan fito shine tace bari ta kira taji ya wasa kwalwa, cikin dariya nace mata "haba ai wlh ba wani wasa kwalwa, komai masha Allah, sai fatan fitowar ta lafiya" itama dariya tayi ta ɗaya ɓangaren tana mai cewa "kai aunty na, ko dai yayan nawa ya samo maki satar amsa ne? Baya so ki wahalar mashi da kanki? Ɗan sororo nayi ina mai sauraren ta, to me hakan ke nufi? Me maganar tata take nufi ne? Ɗan murmushi nayi ina cewa" Haba afnan wace irin magana kike haka? Kaman ya in wahalar mashi da kaina? Wai tsaya ma yaushe ne na zama auntyn taki? Cikin kwalalo idanu afnan ɗin tace "wai sorry" ɗif ta datse kiran tana mai maida numfashi da ajiyar zuciya ta maida kallon ta ga aunty feena dake zaune tana tsefe ma Nasreem kai, murmushi aunty feenar tayi nata cewa "Ah to uwar surutu, ina tinanin fa yarinyar da mahaifiyar ta basu san menene ke faruwa ba a gidan nan, gashi ke kin kira zaki gwangwaɗa mata, ke da Al'ameen ai, indai yaji katoɓarar da kika aikata mashi" cikin ƴar shagwaba irin wacce suka saba ta shiga diddire ƙafafu, Allah kuwa aunty ba zai ji ba, saidai in kece kika faɗa mashi, kinga ita suhan ba surutu ke gareta ba, hasali ma ban taɓa ganin suna magana da yaya ba, wallahi shaf na manta ance a bar maganar na ɗauka Mom ta amince ne" "Ah to kedai kika sani da shegen surutun ki" Aunty Feenar ta faɗa tana mai sake murmusawa alamar zolaya. Ta ɓangaren na kuwa sototo nayi da waya a hannuna, bayan na fahimci Afnan ɗin ta riga ta datse kiran daga ɓangaren ta, ɗan taɓe baki nayi ina mai sauke kafaɗa ƙasa, afnan da shegiyar shiririta take, bari Ya Ameen yaji mai take faɗa zata gane kuren ta ne, ni ce zata ding haɗawa da yayan? Abunda ta san wutsiyar raƙumi tayi wa ƙasa nisa, haka kuma sama tayi wa yaro nisa har a badan abada, ci gaba nayi da taka wa har zuwa bakin gate ɗin, naja na tsaya ina shawarar tarar abun hawa da zan koma gida. Ta bayana Naji sallama, ɗan juyawa nayi, su uku ne tsaye sai faman murmushi suke irin nasu na ƴan gayu sakatattu alamar son suke suyi magana dani. Kayan uniform da na gani jikin su irin nawa ne ya sanya ni amsa masu sallama tawa ina mai kauda kai gefe, ganin bani da Case dasu ne ya sanya ni fara taka wa da niyyar basu waje, ga dukkan alamu irin ƴan makarantar nan ne marasa kunya da duk yarinyar da suka gani sai sunyi mata magana. Gaba na suka sha, suna mai faɗin "Haba beb, ya zamuyi maki magana kiyi banza damu ki kyale mu, har kina shirin gudu wa?" ɗaya daga cikin su ya faɗa yana mai ɗan girgiza kai da jiki haka, alamar ya daɗe cikin iskanci irin nasu na ƴaƴan masu kuɗi. Bance mashi ƙala ba, na kuma zagaye su da niyyar wucewa, ɗaya daga cikin su ne ya sanya hannu gami da janyo hijab ɗina, dole naja na tsaya ina mai wulla masu manyan idanun a, alamar su kyale ni, basu ma kula da Abunda nake nufi ba, su a tinanin su ma fari nayi masu da idanu, Abunda ya ƙara burge su kenan. "Haba beby, tin shigowa ki hall muka ji kinyi mana, kin kwanta mana, duk faɗin makarantar babu yarinyar da ta kaiki kyau da sura, ki kalle ki fa sama har ƙasa" ya faɗa yana nuna ni da hannu sama zuwa ƙasa Gudan ya amshe da cewa "Ni sunana Adnan, wannan kuma Mujaheed, sai wannan Umar ana kiran shi U-Boy, in kinji ana cewa triples to mune, makarantar nan babu wata mace d zamu kalla muce muna so ta ƙi amsa mana balle ke da kike sabuwa zuwa makarantar" Tsoki naja ba tare da na ce masu komai ba, na kuma zagaye su na wuce ina mai Allah wadarai da irin tarbiyyar su, ga kansu duk askin banza, hatta da wandon su duk sun saɓulo shi ƙasa ass down, to ni ko maza sun ƙare zan tsaya sauraren waɗannan ƴan tautsin yaran ne? Ƙila ma duk in ka bincika na girme su.. Basu haƙura ba suka sake biyo ni suna janyo mani jikka, cikin rashin sa'a kuwa har hannun jikkar ya katse, dama ɗan sirri ne, littattafan da waya ta ne suka watse ƙasa, cikin hasala na zuƙunna na shiga tattara wa, bana so in masu magana ne abun ya yi ƙamari, ina so mu rabu lafiya ne, tinda na san da wuya idan zan kuma komawa makarantar a rayuwa ta, dariya Naji sun kece da ita suna mai cewa "kanburauba, baba Kaga wata iphone waya nan? Ɗaya daga cikin su da bazan iya tina sunan da aka faɗa mashi ba ya shiga faɗa yana mai nuna waya ta da hannu yana tin tsira dariya harda buga ƙafa ƙasa. Hannu ne kawai naga ya shiga tattara mani sauran takaddun da littattafan ya niƙo mani, cikin ɗan firgici na ɗago ina mai kallon shi, kwalla da nake ɓoyewa ta wulaƙanci da suke mani ce ta shiga silalowa, wata na bin wata, hannu ya sanya yana ɗauke mani hawayen cikin isa da kwarjini irin nashi ya miƙe yana mai zaro sabon hanky daga aljihun shi yana mai miƙo mani, amsa nayi ina Miƙewa gami da share kwalla tawa da ta fara yawa a fuska ta. Sake zuƙunnawa yayi ya ɗauki wayar tawa da take gefe, ga dukkan alamu dukkan abubuwan da suke faɗa akan kunnen shi ne, da bansan yaushe ya iso wajen ba, saboda ban kawo ma raina zai dawo ɗauka ta ba. Hannuwa na kawai Naji an shiga ja a hankali har zuwa bakin mota, ya buɗe man gidan gaba na shiga na zauna, ya zagaya ya buɗe ya shiga gami da yima motar key, saida muka hau saman babban titi sana ya sanya hannu ya jawo hijab ɗina da ya maida gidan baya, ya ɗora mani bisa cinya, alamar in sanya kenan. Su ko yaran da kallo suka bishi, su kansu basu san lokacin da ya iso wajen ba, daidai suka gan shi zuƙunne, hankalin su na gare ni da suke ta yi man shaƙiyyanci. Ɗaya ne daga cikin su ne yace shi kuma wannan waye? Ko dai ƙanwar sa ce? Ko kuma budurwar shi? Wanda aka kira da U-Boy ne yace "kai baba yanzu baka gane wannan gayen ba? Dambulan ne fa, shine babban ɗanɗan Alhaji mustapha, ai ni ta bayan layinsu muke, bansan wannan acikin ƙanen shi ba, ai su basa karatu Nija ma, ba dai san menene haɗin shi da ita ba, Mujaheed ɗin ne ya riƙe baki," kai haba U-Boy, ashe da mun ci ubanmu, yanda na san gayen cen baya da wasa ko alama, yana iya Sanyawa a kulle mu fa wallahi, baya son rashin kunya" "Muje Baba, Allah ya so mu ba gaban sauran guys ɗin aka yi ba, ai da mun sha kunya" Adnan ɗin ya faɗa yana mai jan hannun su suka cigaba da tafiya domin barin makarantar *************** Muna isa gidan ya sauke ni baƙin gate, bai ceman ƙala ba, haka nima ban tanka mashi ba, na Miƙa mashi hanky ɗinshi, ɗaga man hannu kawai yayi alamar in bar shi, fita nayi na kulle motar, gami da ɗan ja baya, ina jiran ya miƙo mani wayar, motar shi ya ja ya wuce ba tare da ya ko kalle ni ba, jiki a saɓuke na shige gidan zuciya ta a cunkushe, har saida umma ta fahimta Aiko ta shiga tambaya ta lafiya? Ko Jarabawar ce tayi wahala? Girgiza mata kai nayi, ina mai ƙaƙalo murmushi dole nace "a'a umma, Jarabawa Alhamdulillah, kawai gajiya nayi, gashi kaina yana ɗan ciwo, kinsan na kwana karatu jiya ban samu isasshen barci ba" cikin tausaya wa ta shiga ɗan ɗaga man kai alamar eh, sannan ta shiga cewa "to maza kiyi wanka da sallah, kici abinci ki kwanta ki huta, ai an daɗe ba'a gamu da karatun ba, dama sai a hankali" da to na bita ina mai kwaɓe kayan na shiga ban ɗaki domin yin wanka. Sai da na kammala komai, sannan na shiga cin kafiyayyen abincin da umma ta girka mana, duk da zuciya ta babu daɗi akwai tinanin da nake son yi nafi so sai na natsu, gashi waya ta dake hannun Ya Ameen ɗin, naso in kira Afnan domin jin me take nifi da kalama ta na ɗazu? Saidai wata zuciyar tana mai ƙwaɓa ta, gami da tunatas da dani shirme da shiriritar afnan ɗin lokutta da dama. Da haka bacci ya kwashe ni, bayan gama yabiɗar abincin, dama da tarin gajiya fal acikin a jikina. ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:37 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~19~* *Gaisuwa da ɗaukacin marubutan Golden Pen Writer s Association, Ina matuƙar yinku a ko ina kuke, kuci gaba da rubuta mana litattafai masu ma'ana, mu kuma muna suburbuɗa karatu Insha Allah, Allah ya ƙara maku ɗaukaka da zaƙin hannu. _Love u All_* *kyautar Page gareki _Khadeeja s. Dogarai (Lipton Girl)_ shafinki ne wannan kiyi kaca-kaca da ɗan Albarka, abu naka maganin a kwaɓe ka* 🤷🏻‍♀ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Bacci yayi daɗi, nice ban tashi ba sai da kiran sallar la'asar ya tada ni. A gurguje na sake watsa ruwa domin in ƙara jin daɗin jiki na, na maida komai na adana daya danganci karatu na. Mamaki nake yanda umma tayi mana girki a cikin ɗaki nake, kasancewar umma ta mace mai tsafta da kula, ya sanya bama a gane anyi girki a wajen har ta kauda ɗan ƙaramin gas cylinder ɗin da na siyo mana, aka ciko ta da gas, saboda stove akwai ɓata wuri, ga warin kerosine. Wuraren ƙarfe biyar na yamma ne, abun duniya ya isheni, ina son waya ta a kusa dani, gashi abinda yaran nan suka mani ɗazu a makaranta ya tsaya mani a rai, ai duk shi ya ja mani da ya bar mani hijab ɗita a mutumce ba ɗan iskan yaron da yaso ma tunkara ta. Naji mutum da ƙarfin hali, wai har cewa yake ina cen ina shiririta na kusa makara, ko sau nawa ma na kira shi bai ɗaga ba? 😡😏 Shashantar da zancen nayi, gami da miƙewa na janyo kayan guga ta da ban ƙarasa ba jiya na hau idasa wa. ******************* Ya daɗe office zaune yana jujjuya wayar a hannu, ƙare mata kallo yake tsaf, shi dariya ma abun yake bashi, lallai mace sai dai a barta, bai ga abun kuka ba anan, ita bata san ma kukan da take masu zai ƙara masu ƙaimi wajen Abunda suke shirin aikata mata ba? Tin farkon biyo ta da sukayi yake kallon su ta cikin mota, har kawo inda ɗaya ya janyo mata ƴar hijab ɗin dake saman kanta, baiyi niyyar fita ba, Amman kasancewar hangowa da yayi abun nasu na neman wuce makaɗi har ta kai ga sun janyo mata jikka ta katse, shi ya tunzura shi ya fito a sukwane zuwa gare su, yayi niyyar hukunta su, sai kuma ya fasa ganin cewa zai iya ja mata, wata rana ko a hanya suka haɗu da ita su so su rama abinda ta sanya aka yi masu, hakan ce ta sanya bai ko tanka masu ba lokacin da ya isa wurin. Hannun shi ya ɗaga gami da kallo, cen ƙasa zuciyar shi na raya mashi, me yasa ya kama mata hannu? Har da goge mata kwallar dake zirara saman fuskar ta? Me hakan ke nufi? Shi dai ya san in afnan ce ba zai iya bari yana kallo a so aci mata mutumci ba, ba zai iya jura ba, ita kuwa suhan ɗin yana mata kallon kamar afnan ne, ko don saboda tsananin ƙaunar afnan ɗin ga suhan ɗin. "Sai dai kada ka manta, ita ɗin ba afnan bace, ba muharrama ka bace" Abunda wani sashe na zuciyar shi yake tinano mashi kenan, ɗan murmushi ya saki yana mai girgiza kanshi irin na gamsuwa. Murmushi ya sake saki har saida kuma tun shi gabaɗaya suka loɓa, tinowa da yayi da hajiyar shi ƴar drammer, da yanda ya rufe mata baki d damun shi da zancen aure da take yi, nisa wa yayi gami da jawo wayar shi, ya kamata ma ace sun dawo hakanan, gidan baya mashi daɗi ya kasance babu kowa daga shi, sai masu aiki, Alhaji nasu ma baya ƙasar duk da shima gaf yake da dawowa ko don hidimar bikin su Nihal ɗin. Kira biyu yayi Alhajin ya ɗauka yana dariya "Yaya dai Son? Kwana biyu kajini shiru ko?" Murmushi ya saki yana mai cewa "Nothing Dad, good afternoon, Ya aiki?" "Aiki Alhamdulillahi Ameenullah, ya fama da jama'a? Fatan dai komai yana tafiya normal?" Amsa mashi yayi suka ɗan taɓa fira haka mafi yawanci da ya danganci aiki ne, yana kuma sanar dashi shirye shiryen kammala ginin gidajen nashi, da yanda za'a shirya ƙaddamar dashi, Alhajin ne yace su bari tukunna su gama da hidimar bikin su Saudat ɗin, saboda kada ayyuka su rincaɓe masu, ba haka yaso ba, yaso ya cigaba da shirye shiryen shi, hidimar biki ai ba tashi bace shi da yake namiji, kuma ba bikin shi ba ko na abokin shi Bilal, da to ya amsa ma Dad ɗin nashi, sannan ya sa yo buƙatar shi ta son Alhajin yayi ma Hajiyar tashi magana su dawo gida hakanan, duk abinda basu gama siya ba, akwai a gida nigeria, shi bai ga dalilin da za'a ce siyayyar kayan gida ba, sai an kwasa zuwa wata uwa duniya, murmushi Alhaji Mustaphan yayi, ko ba komai ya san yaron nashi wajen kishin ƙasar tashi ta nigeria, amsa mashi yayi da zai kira su ya sanar dasu, sallama sukayi suna mai marmari da begen juna, ƙauna ce mura ran mai tsafta Alhajin yake ma yaron nashi, ko dan kafin hankali da zurfi tinani irin na ɗanɗan nashi, duk ayyukan dake gaban shi, baya taɓa gajiyawa, ko ya nuna ya sare, balle ya gaza, addu'a yaci gaba da bin yaron nashi, Allah ya cigaba da taimaka mashi da haskaka mashi a dukkan al'amurran da ya sanya a gaba. *********************** Ko da Alhajin ya kira su akan su koma gidan, a cen ƙasa ran Hajiya Kubran ba haka taso ba, saidai isa da izza ba zasu bari ta bari ta nuna ba har ma waɗanda suke tare su gane, watau su Hajiya Laila, da kuma wata ƙawar ta makusanciya watau Hajiya sa'a, dama su shidda ne sukayi tafiyar sai sabuwa ƴar aikin da suka samu itama yarinya ce duk da zata ɗara ma Saudat kanta a shekaru, idanun ta a buɗe yake, dama bata aiki sai gidan masu hali, ga iya tuggu da munafunci, wannan ce ta sanya ta ƙara shisshigi ma hajiyar, duk da tana jin haushin mulki irin na hajiyar, su bakwai kenan, Hajiya Kubra, Hajiya Laila, Hajiya sa'a sai Nihal da Saudat sai hafsat ɗiyar Alhaji Awwalu da za'a haɗa bikin nata da su Nihal ɗin sai kuma sabuwar ƴar aikin tasu mai suna Maria, ana ce mata Maree. Ko da Hajiyar ta faɗa masu batun komawa tasu, basu ji daɗi ba matuƙa, kumburi suka shiga yi, harda cewa zasu kira Dad ɗin nasu su roƙeshi ya ƙara masu sati, Hajiya Kubran ce ta hana su, saboda mulki da taƙama na kai kawo acikin jinin jikin ta, kuma bata isa saɓa ma Alhajin ba, saboda shi ɗin namiji ne tsayayye a gidan shi, baya ɗaukar wargi ko saɓa dokar da ya gindaya akan kowa dake zaune a gidan. Ta ɓangaren Hafsat kuwa abun yafi kowa faranta mata rai, cikin zuciyar ta dama ta ƙagara su koma ƙasar tata ta haihuwa, ta samu ta koma gidan su cen Katsina, dama abban ta ne ya tilasta mata zuwa, ko mahaifiya ta ba don taso ba, saboda ta san yanda family ɗin na ƙanen mijin nata suke da bala'i jin kai da sangarta, uwa uba kuma mahaifiya su da dama ba wani shirin arziƙi suke ba, domin ita ba zata iya binta ba, a matsayi ta na wadda take gaba da ita, ko ba komai daga ita har mijin nata basa jiran komai daga garesu, don dai ma kawai ƴan uwantaka, da kuma shi Alhaji Mustaphan da ba halin shi ɗaya ba Sam da matar tashi. Ware ta suke yi, komai za'a siya ko za'a zaɓa ra'ayin su ake ɗauka, ba kuma komai bane in an siya masu ake siya mata ba, to don dai itama mahaifiya tata tayi ƙoƙari wajen ganin ta haɗo ta da ƴan kuɗaɗe daidai ƙarfin ta, gudun faruwa hakan, Hafsat yarinya ce mai natsuwa da kawaici, hakan ce ta sanya ko sunyi waya da mahaifiyar tata bata faɗa mata komai da halin da take ciki, ta riga da ta san Allah ya bata miji da gari, mai natsuwa na nuna ma sa'a, ita ba wannan abun duniyar ne yake gabanta ba, fatan ta dai kawai ɗaya ta koma ƙasar tata ta haihuwa, ko zata ga mahaifiyar ta mai share mata ku kanta, tana kewarta sosai, dan wanda zata aura bata jin shi, saboda kullum suna tare a waya ko kuma we-chat. Saboda haka yanda suke ware ta ko kuma suke nuna mata halin ko in kula bai dameta ba, duk da abun na mata ciwo, wai ace waɗannan ƴan uwanka ne, Amman babu wata alaƙar arziƙi da zata haɗa ka dasu, kai su dai waɗannan ba suyi da cen hali ba, nazajen su sun kwasar ma kansu, yara babu abinda suka sani daga sangarta sai jin kai? Ta lura ita kanta ƴar aikin tasu Maree munafuka ce, bata cen bata cen, wannan ce tasa ta ja jikin ta bata sake masu sosai su kansu, balle su wulaƙanta ta, duk da ta san maƙudan kuɗi Alhajin ya haɗo su dasu, kuma Yayansu Al'ameen na sake turo masu wasu akai akai, hakan bai sanya mata kwaɗayin abun su ba Sam, kuma shi Alhajin da sunan siyayyar yara uku yake bada komai, har shi Al'ameen ɗin yana sake haddada masu duk da Abunda suka siya su siyawa Hafsat itama, Amman basa ji daga su har mahaifiyar tasu, da ta kwaso ƴan barandanta saboda kankan a suka wani taho siyayyar aure. ************ Cikin kwana na biyun da basu umarni sai gasu sun tarkato sun dawo dukan su da tarin siyayya raga raga, tare suka taho da kayansu, hayaniya ƴan taron su ne ya alamta mana da dawowar tasu, ba zance bamuji daɗi ba, saidai lallai gabanmu ya faɗi, daga ni har umman tawa. Jiki ba kwari muka fito taron su muma, gefe mukaja muka tsaya gami da gaishe su, cikin su ba wadda ta amsa mana, sai a tsaki da Saudat tayi ta shige war ta cikin gida, Hajiya Laila ce naga tana mani wani irin kallo da na Gaza gane ma'anar shi, ita kau Hajiya Kubran ko kallo bamu isheta ba, Hafsat ce kawai ta matso inda muke tsaye cikin girmamawa ta gaida umma ta, cikin fara'a ta amsa tana mai tambayar ta Mamanta, Lafiyarsu lau ta tabbatar mata, sannan ta janyo hannuna da nake tsaye gefe guda cikin zaulaya tace "Ƴan mata ya ake ciki?" murmushi nayi ina jan hannun ta zuwa gefe, na shiga cewa "ke Hafsat zakiyi laifi fa, ki bari zamuyi magana anjima" da to ta bini, tana mai matsawa gefe, hakan ce ta sanya ta ƙara basu haushi, bata ko kula su ba ta shige cikin gidan. Bamu bar wajen ba muna tsaye har saida suka shige cikin gidan, sauran ma'aikatan duk suka watse suka barnu nan tsaye, umma ta ce ta matso inda nake tsaye ta shiga kallo na cikin gargaɗi, "Ki kula suhan, kar ki ja mana wani abu daban, kinga dai yadda suka dawo, tin anan ya alamta maki yanda abun yake, ki kiyaye" gyaɗa mata kai na shiga yi cikin gamsuwa da maganar ta, wucewa tayi gaba Ina binta laƙwai-laƙwai har zuwa sashe namu. *************** Al'ameen da yake tsaye ta jikin window ɗinshi, yana kallon duk abubuwan dake faruwa, tin daga shigowar shi gidan har watsewar su, ya sauke ajiyar zuciya, lallai Abunda yake gudun afkuwar shi ne yake faruwa, tsanar mutanen guda biyu ce yake hange cikin kayar idanun mahaifiyar da ƴan uwa nashi. Tabbas ya san shine ya jaza masu, ba tare da sanin su ba, ta yaya zai bi ya warware wannan tsanar da suke fuskanta? Laifin shi ne, ina ma ace da wata yayi wannan trap ɗin ba suhana ɗin ba, "Huh" ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin jiki ya ja ƙafafu shi daƙyal ya isa ga bakin gadon ya zauna yana mai dafe kanshi cikin matsananci yar damuwa, menene ya sanya yanzu yake yawan kula da al'amarin yarinya ne? Menene ya sanya yanzu tinanin ta baya fita a ranshi? Hannu ya sanya gami da jawo wata farar leda, fiddo Abunda yake ciki yayi ya shiga juyawa a hannun shi, waya ce mai masifar kyau, sabuwa dal a kwalin ta, ƙirar Samsung galaxy. Tunani yake ta yanda wayar zata isar mata ba tare da kowa ya fahimta ba yanzu, tinda ƴan gidan sun dawo, su kansu munafuka masu aikin yanzu zasu dinga kai komo acikin gidan, wani tinani ne ya faɗo mashi arai, maida wayar yayi cikin ledar ya miƙe gami da aza ta bisa mirror ɗin da yake ɗakin ya fice domin zuwa yi ma Mom ɗin tashi barka da zuw. A babban falo dukan su ya tada su, sun baje gajiya tayi masu ligif, Hajiya Kubra ce kawai bata wajen ita da aminan nata, suna cen sun ƙule a sashe na Hajiyar suna tattauna wa, gaida shi suka shiga yi, ya amsa masu babu yabo babu fallasa, sannan ya maida hankalin shi akan Hafsat ɗin da take jingine da kujera saman carpet, cikin ɗan dakin fuska yace "Hafsat ya gajiyar tafiya, fatan kun dawo lafiya?" ɗan murmushi tayi tana mai cewa "lafiya ƙalau yaya, ya muka same ku?" Lafiya lau ya bata amsa, yana mai nufar upstair domin zuwa ga Mom ɗin tashi. Ƙwanƙwasa ƙofar ya shiga yi, daga cen ciki aka bashi umarni ya shiga, cikin takun shi na ingarma namiji ya taka ya shiga bakin shi ɗauke da siririya sallama, da kallon ƙauna mahaifiyar tashi ta bishi, ɗan nesa dasu ne ya samu kujera gami da zama, ya shiga gaida su harda ƙawayen mahaifiyar tashi, cikin fara'a suka gaida shi suna tambayar shi wajen aiki, ya amsa masu da lafiya, yana mai tambayar su hanya, duka lafiya suka shaida mashi, miƙewa yayi gami da cewa "Mom zan ɗan fita kafin ki gama dasu, ina dawowa anjima" Bai jira cewar ta ba, ya fice daga falon, cen ƙasan ranshi, haushi fal na abokan mahaifiyar tashi, domin shi fa in ba zuga ta ba, da ƙara kambama mata kai baiga abinda suke yi ba, baiga dalilin ta ba ma na kwasar su su wani tafi siyayyar aure ba, Abunda ko daga nan gida nigeria zaka iya Kyi order ɗin duk abinda kake so, ya iso maka kuma har gida, salon ɓarnatar da kuɗi kawai, da son neman suna😒 Da kallo suka bishi dukan shi, har ya idasa ficewa a falon, ajiyar zuciya suka shiga sauke wa, sa'ilinbda Hajiya sa'a ta kalli Hajiya Kubra, "Lallai Hajiya ta, Al'ameen ne ya ƙara girma haka? Kina me da har yake neman jawo maki magana da raini, ta hanyar auren waccen koɗaɗɗar? Kiyo iya yin ki duk yanda zakiyi kiga kin daƙile wannan maganar wallahi, yaro mai jini a jiƙa kaman wannan ga naira ga kyau ga gayu? Tabɗi gaskiya kinyi sake, ni ba ma ga amfanin zaman da suke yi a cikin gidan ba, har ma zai dinga iya ganin ta kullum, kiyi amfani da damar ki, tin kafin kina kallon ruwa kwaɗo yazo yayi maki ƙafa, kina dai gani irin waɗannan yaran su ne yaran masu kuɗi da faɗa aji a faɗin duniya suke so su samu, ba ma nigeria ba, yo wannan ko a India yaga wata yace yana so ai wallahi ba zata yi mashi musu ba, balle waɗancen talakawan" Hajiya Kubra ce ta nisa gami da cewa " Humm bari dai Sa'a, wallahi kina ganin shi haka shegen tarin kai ne dashi kaman mahaifin shi, ba yanda banyi ba Amman abun yafi ƙarfi na, dama da dukiya nake taƙama, tau duk kansu daga shi har mahaifin nashi babu wanda bai fini ba a halin yanzu, nayi ƙoƙarin nuna ƙarfin uwa akan shi, Alhaji yana man ba razana da aure na, ni kau kjnga ba zanyi sake in rasa alhaji ba, samun kaman Alhaji a yanzu zai yi mani wahala... " Hajiya Laila ce ta katse ta da cewa ki bar mana komai a hannun mu Kubra, ba zai gagara ba, me aka yi a kayi Maryama balle wata ɗiyar ta cen, bari a gama hidimar nan zamu san abun yi, in ance ya ƙara kallon su ma ba zai kalla ba ko da kuɗi, kuma beside ma ni bana tinanin son ta yake yi, kinsan fa waɗannan miskilan yanda suke, nafi tinanin dai yana so ya kulle maki baki ne akan zancen aure da kike mashi" duk kansu sun gamsh Sa da hakan sun kuma sha alwashi ɗaukar mataki bayan kammala bikin Saudat da Nihal ɗin da yake saura sati biyu ayi. Kai tsaye sashen shi ya koma, baya jin ma mararin fitar, idan ma ya fita ba inda za shi, shi ba mutum bane mai yawo, Shiyasa ma ko abokan kirki baya dasu, sau tari yafi buƙatar ya zauna gida yana aiwatar da dukkan muhimman abubuwa a cumputer ɗinshi akan ya fita ya ɓata lokacin shi ga banza wajen abokai, duk kuwa da yanda samari da dama ke fatan ace shi ɗin abokin su ne, koda kuwa na wucin gadi ne. Bilal ya kira suka sha firar su, yake sanar dashi shigowar shi satin sama, domin su fara tsara yanda tashi hidimar zata kasance, "Abokina kayi ƙoƙari kaima ka fidda matar aure, duk da na san kai mata basa ga anka, Amman ai ba zaka ci gaba da zama haka ba, ko so kake yi ne sai mun haɗa ka da abie ne sannan zaka yi auren, ka kuwa san lokacin ka tsufa babu wadda zata gani ta ƙyasa" Murmushi yayi irin wanda ke ƙara ƙawata mashi kyakkyawa fuskar shi, sannan ya shiga maida mashi da amsa "Ai sai kazo kayi mani malan, na lura kaima team ɗin Mom kake, Kaga mubar maganar nan sai kazo zamu tattauna, bari in tashi in fita wajen mata san cen da na sanya a tattara mani zamuyi meeting dasu da ƙarfe biyar na yammaci kasan yanda abubuwan suke yanzu wallahi, ina tinanin zan basu hutu ne har agama hidimar nan ta bikin yaran nan, kada kwalwa ta ta buga hakanan" "Is ok Friend sai kunyi magana" Bilal ɗin ya amsa mashi ta ɗaya ɓangaren, sallama sukayi yayin da ya tashi ya fice hannun shi ɗauke da ledar wayar nan. Muɗi driver ya ba, ya umarce shi da ya kawo mani, shi zai fita ne sai ya dawo mmanka kula. Cikin hanzari kuwa ya russuna ya amsa yana mai cewa "To yallaɓai" kai tsaye motar shi ya nufa, yayin da mudinya nufi sashen namu ba tare da ya damu da ya san menene acikin ledar ba. Sallamar mudin ce ta katse ni daga shirya mana kaya da nake ta faman yi a wardrop, amsawa nayi gami da zura hijabina na leƙa ina mai gaida shi, amsawa yayi yana mai miƙo manledar dake hannun shi, "Gashi inji Alhaji ƙarami yace in kawo maki" amsa nayi ina mai cewa tou Mudi an gode, juyawa yayi ya bar wajen tin kafin wani ya gashi, yayin da na koma cikin ɗaki ina mai nuna ma umma ta dake zaune bisa darduma tana karatu. "Wai Ya Ameen ne yace ya kawo mani" na faɗa ina dire ledar gabanta, ba tare da na damu da sanin menene ciki ba, duk a zato na Abunda ya danganci karatu na ne. "Ki buɗe mana kiga menene a ciki" cewar umman tawa, tana mai ɗan ɗaure fuska haka kaɗan bansan menene dalili ba. Kwalin dake cikin ledar na fiddo, gaba na ne ya faɗi, na ɗan ɗago na saci kallon umma ta da ta tura mani idanu taga yanda zanyi, hannu na kuma Sanyawa na zaro ƴar mitsitsiya waya ta da Naji tana vibrating a cikin ledar. Saƙo ne ya shigo, number ce ban damu da in buɗe ba balle inga Abunda aka rubuta, durkushe nake gaban umman tawa kawai ina so inji hukuncin da zata yanke a kaina game da amsar kyautar waya daga hannun yaya Al'ameen ɗin. ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~20~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Sai faman zare idanu nake yi, kaman wadda tayi ma sarki ƙarya, hukuncin umman tawa kawai nake jira inji me zata yanke akai. Shiru tayi na tsawon minti biyar, nazari ɗiyar tata take yi, fatan take ace ba ita ce ta roƙeshi ba. Nisawa tayi kaɗan a hankali ta muskuta, tana mai ajiye littafin dake hannun ta, har yanzu bata ɗauke idanun ta akai na ba. " Suhan! Ina fatan dai ace ba kece kika roƙeshi waya ba, ba zaki iya haƙuri da wadda Allah ya baki ba" na tsinkayo muryar ta kwatsam cikin kunne na. Girgiza mata kai na cigaba da yi, ina cewa "a'a umma wallahi ban roƙeshi ba" kwashe yanda muka yi da yaran nan nayi a makaranta kwana biyu da suka wuce, har zuwa kan inda ya ɗauki wayar bai bani ba, Amman ban gaya mata ya goge man ƙwalla ba, balle ince ya kama man hannu, don na san tashin hankalin da zan fuskanta. Shiru ta sake yi sannan tace "Allah shi kyauta, an gode, Amman ina so ki riƙe talaucin ki, ki dinga juya ma abun duniya baya, wannan ƴar ƙaramar ta isheki, sai dai bazan hana ki amfani da wannan ba, saboda zamani ne yazo da ita" Cikin ɗan murmushi nace "to umma nagode" sake kallo na tayi da wani irin yanayi, sannan ta shiga cewa "sai ki kira shi kiyi mashi godiya ko? Sannan ki kula ba zan gaji da cewa ki kula ba, kindai san zaman da mukeyi a gidan nan" "Eh umma haka ne, to zanyi mashi godiya insha Allah" na faɗa murya ta fal farin ciki, sai dai cen ƙasa zuciya ta, wani irin tsoro ne da fargaba, me zai faru idan aka ce maganan Afnan ce ta fara tabbata?, me ne ya sanya shi share man hawaye Wancen lokacin? Me hakan ke nufi?" Jikina ne yayi sanyi ƙalau, komawa nayi na zauna, ina mai zaro wayar daga cikin kwalin ta, waya ce mai matuƙar kyau da tsada, ko a cikin ƴaƴan masu dashi ɗin ba kowa ne ke riƙe irin ta ba. Gashi tana da girma, har ina jin tayi ma hannuna mugun girma wajen riƙewa, saidai ko babu komai nayi farin ciki, ɗan chatting ɗin nan da kowa keyi nima zan fara, zan ga me duniya ke ciki, lokaci ne nima da zan fita daga cikin wannan duhun kan zama waje ɗayan. Ban mantawa, lokacin da nake secondry school, dukka kusan ƴan ajinmu na da waya, kasancewar ta makaranta da ƴaƴan manya, wasu ma biyu ne suke da ita. Ɗan murmusawa nayi, tinowa da nayi yanzu fa har afnan zamu dinga magana da ita kullum, ga wata ƙawata tin ta makaranta mai suna khairat, ta soni sosai, tana tausaya mani, ita gidan su masu hali ne, har wayar taso bani, nice dai na ƙiya don na san halin umma ta, yanzu gashi da nayi haƙuri na samu irin wadda ban zata ba ban tsammani ba. Kunna ta nayi, aiko ta ɗauka kaman jira take yi, nayi mamakin da layi ciki guda ɗaya, saidai babu komai a kanta sai Numbers guda biyu an masu saving da AMD bansan me hakan ke nufi ba. Niyyar goge su nayi, sai kuma wani tinani ya ɗarsu a zuciya ta, in shi ya ajiye su da? In suna da muhimmanci fa? Share wa nayi ban ko taɓa mashi abun shi ba, na jawo waya ta ina maida numbobi na ciki, har da ta khairat ƙawa ta da na janye mawa kusan shekara nawa? Itama ganin hakan sai ta haƙura ta ƙyale ni, kada ta jaza man matsala, fahimta da tayi umman tawa bata son tarayya ta da ita. Ko tana ina ma yanzu haka? Dukkan motsi na umma ta na kula dashi, tausayi na ne fal acikin ranta, tana addu'a Allah ya kawo lokacin da nima zan zama wata abu, lokacin da zamu fita a halin ƙuncin da muke ciki, lokacin da muma zamu zama mutane masu cikakken ƴanci kaman kowa. Sallamar Hafsat ɗince ta katse mana zaman shirun da muke, niko ina ta faman jujjuya waya a hannu, mamaki ya cika ni, ta yadda naga kuɗi tsababa cikin wayar, yanzu ko na tabbata wayar tashi ce, ƙila siyan ta yayi yana amfani da ita ya bani, bata san shine ya siya domin ita ba, ya zuba kuɗi domin ita, saboda harga Allah cin mutumcin da aka yi mata yayi mashi ciwo, ace kaman wanda yake gidan su ace ana ci mashi mutumci saboda wani abu wai waya, menene amfanin arziƙi nasu in har ba zai kare mutumcin mutanen dake rayuwa cikin shi ba? Da murmushi na bita ina mai cewa "A'a Hafsy ce? Shigo mana" na faɗa ina nuna mata gefen katifa inda nake zaune, alamar ta zauna, murmushi tayi ta ƙara so ta zauna tana gaida umman tawa, itama cikin dakin fuska ta amsa tana mai sake tambayar ta maman su, duk suna lafiya tace, a hankali suka shiga fira da umman tawa, yayin da ni kuma hankali na na kan waya, har umman tawa ta miƙe ta shiga ban ɗaki, sai a sannan ne ta maido hankalin ta kaina. Hannu ta sanya ta amshi wayar, tana murmushi take faɗin "Ya Suhan, wannan mai zafin fa? Yaushe kika shiga yayi ban sani ba? Domin dai ina da number ɗinki, Amman naga ko WhatsApp bakyayi kuma kina da irin wannan babbar waya haka, ko ni fa bana iya riƙe irin ta" ta faɗa fuska cike da murmushi, ta ƙara she da zaulaya. Hafsat ɗin dai kaman yanda kuka sani ɗiya ce ta yayan Alhaji mustapha Dambulan, watau Alhaji Auwalu da yaje zaune cen Katsina, tana zuwa gidan akai akai, in suna ƙasar, saboda iyayen su masu zumunci ne akai akai, suna yawan tura ƴaƴan su gidajen nasu, hatta su saudat ɗin ana tura su Katsina, duk da dai basa so, suna cewa takura suke yi wai basa walawa a gidan yayi masu ƙarami, duk da kuwa irin girman gidan nan da kayan more rayuwa dake cikin shi shima, domin yanzu Alhaji Auwalun ya kai matsayi director a ma'aikata tasu,ya samu rufin asiri daidai gwargwado, duk da kuwa bai ko kama ƙafar Alhaji Mustaphan ba. Bana hafsat kaɗai ba, dukkan in ƴaƴan Alhaji Auwalun da hajiya zainab, yara ne masu sanyin hali, girmama naga a dasu, da kuma kawaici, basa da girman kai Sam, wannan ce ta sanya tamu tazo ɗaya da Hafsat ɗin da ko zata girme mani tau fa da kaɗan ne. Ita dai ba'a isa a hana ta zuwa sashe namu ba, hasali a In tazo ba wani damuwa da al'amarin ta suke ba, ba ta ita suke yi ba, lokutta d adama ma haushin ta suke ji, suna cewa duhun kai yayi mata yawa, itama ta gama karatun ta tsaf a makarantar ummaru Musa ƴar adu'a dake jihar Katsina dabon. Sai gashi kuma Allah ya bata miji nagari, na nuna ma sa'a, hasali ma dukka mazajen daga na Saudat, har Nihal ɗin babu Abunda zasu nuna ma nata, sai ma shi ya nuna masu tarbiyya da kuma dattako. Murmushi na ɗanyi ina cewa "Uhm Hafsy kenan, nima yanzu wayar ta iso mani wlh" kasancewar ta mutum da ta san halin da muke ciki, da irin zaman da mukeyi, ya sanya na kwashe labarin yanda aka yi na samu wayar na faɗa mata. Aiko murna ta fara yi, tana ce an "kinga kada ki damu, rabon ki ne ya rantse, ai Ya Ameen ɗin mutumin kirki ne, Sam shi ba halin su ɗaya dashi ba, yana taimakon na ƙasa dashi, ko bayan dawowar mu Naji ana cewa ya raba ma dukkan in ma'aikatan kamfanoninshi kayan abinci da tufa fi masu kyau da tsada, a bakin su Hajiya Naji da tana waya da wasu ɗazu. Amsar wayar tayi ta shiga buɗe man abubuwa irin su WhatsApp, Facebook, da wani chat wai shi duo, nice nace ta bar shi hakanan, har sai na iya waɗannan tukunna. Fira muka shiga yi sosai, har take cewa zata dawo ɗakinmu da zama kafin lokacin tafiyar tata yayi, nake ce mata tayi haƙuri ta rufa mana asiri, kwanciyar ta tayi tana cewa "uhmm, kanki kuma akeji Suhan, KEDAI Allah yayi maki tsoro kaman farar kura" Koda ta sanar da umman tawa da ta fito daga banɗaki, murmushi kawai tayi, ai kaso mai sonka ka kuma girmama duk wanda yace yana sonka. "Umma wata Alfarma nake so in roƙe ki don Allah, ki ara man suhana ta taya ni zuwa wajen gyaran jikin, da ƙarashe siyayya har zuwa lokacin da zan koma gida, kinga dai su Saudat ware ni suke yi, bana da aboki ko ɗan uwan da zan tun kara, Suhan ɗin dai ita ce" Hafsat ɗin ta faɗa tana marairaicewa, kaman wadda zata yi kuka, lokaci guda tana kallon umman tawa. Ba matsala umma ta tabbatar mata, saidai taja hankalin u akan mu kula da me mukeyi, idan mun fita mu san ina zamu, kuma kada mu sake mukai magariba a waje waɗannan sune sharuɗɗan ta. Da to muka bita, hafsat ɗin kuwa taji daɗi, dama ko ba komai bata kawo ma ranta umman tawa zata hana, saidai ta san halin umman tawa, wani lokaci kaman mai aljannu take, zata iya hanawa a lokacin da ba'a tsammata ba. Faɗa mata nayi ina son in kira yayan in mashi godiya Amman ina jin kunya, harara ta tayi cikin wasa tana cewa "menene na kunya Suhan? Ai ya yanki ne yanzu an riga an zama ɗaya, ki kira shi kawai wlh, ko kuma ki tura mashi text ai zai gani godiya daɗi gareta, balle yayan namu da yake miskili yana iya dakin fara godiya ya katse wayar" Amincewa nayi da gara in mashi text, in mun haɗu a zahiri na ƙara gode mashi, sai dai fa inda gizo ke saƙar, bansan me zan rubuta ba, sai jujjuya wayar nake a hannu. Hakan da ta fahimta ne ta fizge wayar a hannu na tana cewa "Dallah kawo nan, kai a tukunya, ai gara ma kizo kije makarantar ko kin ƙara wayewa, godiya ma kin gagara yanda zakiyi ta, wannan duk lokacin da kika yi saurayi naga yanda zakiyi dashi" ta faɗa cikin zaulaya da dariya, Nidai bance mata komai ba, sai a kishingiɗawa da nayi ina mai ɗan murmusawa a hankali. Ban san me ta rubuta ba, na dai ga kawai ta jawo wayar ta ta ɗauki number ɗinshi ta tura, sannan ta miƙa man wayar tana faɗin "Done, saƙo ya isa" Firar mu muka cigaba da yi, tana faɗ man yanda tsare tsaren bikin nata zai gudana, duk da ba wani pherty zata yi ba illa iyaka traditional day da za'a gudanar lambun gidan, wanda su kau su saudat sun haɗa pherty ya kai kala biyar wata rana ma sau biyu za'ayi. Ita dai tace ba zata shiga ba, cikin hidimar su, bata da ra'ayi, duk da mijin nata yaso ayi ko kala biyu ne saboda abokan shi, Amman ta kafe kawai tace kowa ya sanyo kayan gargajiya, yazo yaci goruba ya sha rake🤣🤣 Nan ne na ƙara fahimtar sauƙi hali irin na hafsat ɗin, lallai duniya da Abunda ke ciki ta basa gabanta, tana tausaya ma mijin nata, tace wannan kuɗin da zai kashe sun isa yayi hidima da baƙin shi har su tafi. ******************** Shigar shi kenan part ɗin nashi, a matuƙar gajiye yake, waya kawai yayi ma Nihal ta kawo mashi snacs yunwa yake ji, kai tsaye ɗakin shi ya faɗa ya shiga kwaɓe kayanshi, wanka yake son yi ko zaiji sauƙi gajiyar dake nuƙurƙusar shi, gashi part ɗin nashi yayi matuƙar dauɗa, rabon da ya samu kyakkyawa n gyara tin wanda Suhan ɗin tayi mashi. Bayan ya gama wankan ne, ya shirya cikin pajmas na maza, saboda sauƙin nauyin su, gashi yana so ya kwanta ya ɗan huta, sallama yaji ta baƙuwa murya daga cen falin nashi, a hankali ya miƙe gami da fita domin ganin wake sallama, kaman muryar mace yake iya jiyowa. Maree ce tsaye, hannun ta ɗauke da farar roba mai garai garai, kana iya hango Abunda ke ciki, a tsakiyar falin ya iske ta tsaye tana ƙare ma sashe nashi kallo, ita asali ma bata taɓa shigowa cikin shi ba, saidai kawai ta hango shi daga nesa, duk da a zahiri kasan zubin nashi dama zai yi kyau, saidai ya zarta yanda take tunani. Ƙamshin turare ne, ya alamta mata lallai akwai wani tsaye kusa da ita, ɗan zabura tayi kaɗan tana cewa "Yallaɓai barka da hutawa, gashi inji Aunty Nihal tace in kawo maka" ta faɗa tana miƙa mashi robar cikin ƴar rissinawa tana wani far-far da idanu, ko kallon ta baiyi ba, ya nuna mata stool dake gefen kujera ajiye, alamar ta ajiye bisa, gami da juyawa da niyyar komawa cikin ɗakin yana cewa "Ki turo mun Nihal ɗin" Da kallo ta bishi ta baya har ya shige ɗakin nashi, ajiyar zuciya ta sauke, dama haka Al'ameen ɗin yake? Lallai dole ne ta sake taku, wannan ai kalar nasu ne, ko ba zai aure ta ba, lallai dole ne ta ɗanɗana zumar shi, zata san yanda tayi ta jawo hankalin shi gareta, saidai ita kanta ta san da wuya, da wahala, domin a yanda ta ganshi ba zai yi wasa ba ko ya ɗauki wargi, ƙafafunta ta ja gami da barin sashe tana ta saƙa mugun nufi da mugu nƙuduri akan bawan Allah Al'ameen. Har ɗaki Nihal ɗin ta tadda shi, kwance yake ba bacci yake ba Amman idanun shi a kulle suke, ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa, sannan ya shiga balbake ta da faɗan, ya sanya tayi mashi abu, ta sanya wata ƙazama cen ta kawo mashi Abunda zai ci, mamakin shi take yi, ai ita a sanin ta yana cin abun hannun ƴan aiki, tinda yana cin na Suhan da mama Maryamar. Katseta yayi daga tinanin da take yi, "dole ki amshi hukuncin, gobe in Allah ya kai mu ki tabbatas kin gyara mani sashe na tsab, kaman yanda kika ga Suhan nayi mashi, bana son ƙazanta, baƙi zanyi cikin satin nan zaki iya tafiya" Juyawa tayi tana kumbura baki, har ga Allah in har Yayan nasu na ƙasa yana takura masu, ya sanya sun dawo ƙasar kuma yana neman ya sanya su wahala? Aikin gyaran wannan sashen ai ba ƙaramar wahala bane, ita da ko toiket ɗinta bata iya wankewa, yanzu saidai ta sanya Maree tayi mata, duk da bawai ta gansu da tsaftar mareen ba kaman suhana, zuciyar ta na raya mata ta sanya Maree ta gyara mashi, wani sashe na zuciyar nan kwabar ta, tabbas zai iya ganewa ba ita tayi ba, inko hakan ta faru ta kaɗe har buzunta, ba zasu rabu ta daɗi ba, ɗan guntun murmushi tayi, mafita da ta samo, ai yace irin yanda Suhan keyi ko? To ba matsala, ai Suhan ɗin ce ma zata yi maka yaya sha kuruminka, tinda aikin nata kake so. Da haka har ta isa sashen nasu, tana labarta ma Saudat ɗin yanda sukayi da yayan nasu, murmushi kawai saudat ɗin tayi gami da cewa "gara ki sanya ta tayi shegiyar, kinga yanzu daga dawowar mu har ta janye Hafsy, ai wannan yarinya wallahi akwai mayya". (😝😝 kunji fa readers ashe sun damu hda hafsat ɗin🤔) ******************** Bacci yake son yi, saidai yunwa ta ishe shi, gashi bai jin zai iya cin abinda yarinya ta kawo mashi, miƙewa yayi a hankali ya isa kitchen ɗin da yake mallakin shi, kaman wata macen, fridge ya buɗe ya ɗauko lemo kwali da ceramic cups ya fito, kai tsaye bedroom ɗin ya koma gefen gado ya zauna, gami da tsiyaya lemon ya sha, kaman wanda aka yi ma dole. Wayar shi ce tayi tsuwwa, alamar saƙo ya shigo, share ta yayi ya cigaba da shan lemon shi har ya gama, gami da miƙewa ya maida kitchen, ya dawo daƙin gami da saisaita ƙarfin Ac ɗin dake aiki cikin ɗakin. Gadon nashi ya haye, tare da jan lallausan bargon nashi ya rufe ƙafafun nashi ruf, wayar shi ya jawo gami da maida ta sylent, har zai ajiye sai kuma ya lura da ɗan akwatin saƙo da yake cen sama wayar a maƙale. Cikin kasala ya buɗe, yayi mamakin ganin sunan ta ɓaro ɓaro a wayar, bai ƙara shan mamaki ba har saida ya karanta Abunda saƙon ya ƙunsa, karantawa yayi ya sake maimaitawa, ita ɗin ce kuwa? Zaune ya miƙe bisa gadon, gami da jan bayan shi ya jingina shi jikin lallausan tissue foam ɗin dake jikin wood ɗin gadon. Sake dai maimaitawa yayi, lallai ita ce ta turo idanun shi ba gizo suke yi mashi ba. Hannu ya sanya gami da ɗan yin typing a hankali ya maida mata reply, unlight ɗin wayar yayi, gami da tura ta ƙarƙashin fillow. Zamewa yayi ya kwanta idanun shi a lumshe, zuciyar shi na ta kai komon karanta saƙon nata, su kansu idanun nashi sun gaza dena nuno mashi hoton Rubutun, tiryan tiryan yake karanta shi cikin idanun shi, kaman yana kallon scream ɗin wayar ne, a hankali bacci mai nauyi ya kwashe shi. Niko da muke cen ɗakin mu mun bararraje muna ta fira da Hafsy, ko ba komai dai Naji sauƙin kaɗai ci yau, na samu aboki yar fira, tana ta bani labarin tafiyar su, ina ji daman nice ace yau na ganni a ƙasashe ƙetare, mu biyu ne cikin ɗaki, domin umma ta ta fice ƙofar ɗaki gami da shimfiɗa tabarma ta zauna tana yanke farce. Sabuwar waya ta ce ta ɗauki tsuwwa, alamar shigowar saƙo, hannu na sanya gmi da jawo wayar, na buɗa. Cikin ƙwalalo idanu nake kallon wayar, hakan ce ta jawo hankalin hafsat ta tashi zaune tana tambaya ta ko lafiya? "ina fa lafiya Hafsy?" na faɗa bayan na gama karanta Abunda ta ta tura da shi kuma wanda ya turo. "To menene a ciki Suhan? Naga ai godiya kawai nayi ba wani abu ba, menene na damuwa, shima ko kinji yace wani abu ne?" ta faɗa bayan ta amshi wayar ta karanta reply ɗin da yayo. "A'a Amman ni kin sa har na fara jin kunya, waɗannan kalama ai irin naku ne na masoya hafsat, kada fa ki sanya yayi tsammnin wani abu" na faɗa hankali na aɗan tashe, har ga Allah kunya duk tabi ta baibaye ni, kaman ina gaban shi, sai yanzu nayi na damar barin ta ta tura Abunda ta rubuta ba tare da na amsa na karanta ba. "kinga karki wani damu kanki Suhanan umma, ki kwantar da hankalin ki Yayan namu wayayye ne ba zai kawo ma ranshi komai ba akasin Abunda aka rubuta" Ta faɗa cikin son ƙarfafa man guiwa, Nidai lafewa nayi jikin bango ina sauke ƴar ƙaramar ajiyar zuciya, gami da ce mata "To Hafsat Allah ya sanya" ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~21~* *Ina ma ɗaukacin Al'ummar musulmi barka da shigowa sabuwar shekara a musulunci, Albarka dake ciki Allah ya sada mu da ita, sharri da tsautsayin da yake ciki, Allah yayi mana tsari dashi Albarkacin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° _Assalamu Alaikum, Yaya ina yini, ya gida da aiki? Ya fama da jama'a? Ina fatan komai lafiya, na rubuto in maka godiya da abun arziƙi da alkhairi da kaman, bani da bakin godiya a gareka, irin kyakkyawar kulawa da kake bani, i do appreciate Yaya, Allah ya ƙara arziƙi da wadata_ Ya kai sau biyu kenan ina ƙara maimaita karanta saƙon da Hafsat ɗin ta rubuta ta tura mashi, ina hango rashin dacewar kalaman, idanun a kaman zasu faɗo ƙasa saboda yanda na ƙura ma scream ɗin idanu, kunya tana baibaye dani, gashi dai tini hafsat ɗin ta fice taje ta kwaso kayan ta, Amman duk kina nake yi wani iri, a hankali idanun a suka kai ƙasa kan nashi saƙon da ya maido tin bayan tura saƙon da mintoci kaɗan _OK ba damuwa, Ameen_ Iya abunda ya rubuta kenan, sai nake ƙara ganin rashin dacewar hakan, fata na dai ace baiyi mani wata fahimta daban da. Tare da Hafsat ɗin muka kwana a ɗakin mu, wanda saidai umma ta shimfiɗa tabarma gefe cen ƙasa tiles ta kwanta, ta bar mana katifar. Yau mun hutar da umman tawa, ni da hafsat muka yi komai muka kammala har abun kari, sannan muka yi wanke wanke a cen gefen ƙofar ɗakin namu, kallo ake ta binmu dashi sauran ma'aikatan wasu na zunɗen mu da baki, mu dai bamu damu ba, harkar gabanmu kawai mukeyi. Hafsat ɗin na kula dasu, shaye da mamaki ta kalle ni lokacin da muka gama wanka muka zauna zaman shafa, "Suhan wai dama haka ma'aikatan gidan nan suke yi maku ke da umma?" ta faɗa mamaki fal a fuskar ta. "Eh nace, ina mai basar da zancen, saboda umma ta bata so ake zancen su. Girgiza kai kawai tayi gami da cewa" Allah shi kyauta" daga haka itama ta ja bakin ta ta kulle lura da tayi Suhan bata son maganar tasu. Muna cikin shafar ne Naji waya ta tayi ƙara a hankali na jawo gami da dubawa, saƙon nihal ne take sanar dani wai inje in gyara ma yaya ameen ɗakin shi, in turo hafsat ta amsar mani makulli. Cikin tsantsar mamaki na kai kallo na kan umma ta, aiko ta ƙure ni da idanu alamar tana neman ƙarin bayani. Sanar da ita nayi saƙon, sannan na ƙara da cewa, umma ina ce an dakatar damu aikin gidan, me zai sanya ba zata sanya maree taje tayi mashi ba?" kuma umma........, shiiiit🤫 ta dakatar dani, gami da cewa" Suhan bana son Abunda zai kawo tashin hankali, Hafsat je ki amso makullin ki kawo mata, kije ki taya ta ku gyara mashi ɗakin, ai ba wani abu bane don kin gyara mashi, yaron da yake mana alkhairi ai ba zamu ji kyashin kyautata mashi ba" "Haka ne umma" cewar Hafsat da ta miƙe tana ficewa zuwa Amso makullin. Umman tawa ce ta maida kallon ta gareni, sadda kaina nayi ƙasa, ni fa har ga Allah bana son Abunda zai ke haɗa ni dashi, masalan ma yanzu da afnan ta rubuta mashi wannan text ɗin, umman ce ta katse man tinanin da nake yi gami da cewa "Suhan ki kula fa, kinga Hafsat ƴar'uwarsu ce ba zata ji daɗi ba idan taga kaman bama son kyautata masu, ita ba lallai ta fahimci komai ba, ki saki ranki, kije ki gyara mashi, yafi gaban nan a wajen mu, shine ya zame mana kaman uba yanzu, ni na san Alfarmar shi ce ko zaman da mukeyi a gidan nan" Jikina yayi sanyi ƙalau, lallai gaskiyar umma ta kuma, dole zan ajiye kunyar in gyara mashi ɗakin nashi, wannan ne kawai Abunda zanyi in faranta ranshi ko dan in biya kaɗan daga cikin Abunda yake yi mana. Shigowar Hafsat ce ta katse mana maganar da muke, miƙewa nayi gami da zira hijabina. Tare muka ɗunguma zuwa sashen Ya Ameen ɗin muna tafe muna firar mu gwanin sha'awa kaman wasu ƴan uwa ko ƙawaye. Santin sashen Hafsat ta shiga yi, lallai ya ameen ɗin daban yake, watau sashen ma ko datti baiyi ba sosai, ba don ma shi ɗin mai tsafta bane, kaman yanda sauran maza suke, ai da ba sai ma an tsaya ɓata lokacin gyaran ɗakin ba, komai tsaf yake a ajiye a muhalli shi, kaman Wancen gyaran da na taɓa yi mashi, da alama dai ya kula da mazaunin komai ne ya sanya yanzu yake kula wajen misplacement ɗinshi. Hafsat na bari ta gyara falon, yayin da ni kuma na shige bedroom na shiga gyara, hai bathroom duk saida na gyara, na kwal kwale komai tsaf, ko kafin in fito har ta gyaro har kitchen komai tsaf, room freshner na fesa, gami da sakin Ac a hankali a hankali. Jawo ɗakin muka yi, har yanzu Hafsat bata dena santi ba, ga dukkan alamu Ya ameen ɗin mutumenta ne, sai yaba kirki da halin kwarae nashi take yi, anan ne take faɗa man irin taimakon da yake yi masu cen gidan nasu, dama duka mutanen garin kankiya, duk mai buƙata shi yake nema kai tsaye, kuma baya gazawa wajen taimaka masu bil haƙƙi da gaskiya. ************* Tsaye yake tsakiyar ɗakin hannuwa shi duka biyu soke a aljihun farin yadin da yake jikin shi an yi mashi ɗinkin osimbanjo, yayi matuƙar kyau, masalan yau da ya kafa hular dara a bisa kanshi, saboda ja ce sai ta ƙara ƙawata fuskar tashi, ko ina na sashen yake bi a hankali, a hankali. Tabbas wannan gyaran ya san ba na Nihal bane. "Suhan" zuciyar shi ta raya mashi, Amman As How? Ya tambayi kanshi cikin zuciya, "Huh, any way" ya faɗa a fili, yana sauke ajiyar zuciya, gami da kaɗa kai a hankali ya nufi bedroom ɗin. Mamaki ya kama shi, kanshi ya kulle, a hankali ya isa ga gadon da yaji bedsheet yayi limui, zama yayi gefen gadon yana mai mamakin irin gyaran da yarinyar ta iya, kaman inji, Alwala yake son yi, hakan ce ta sanya shi miƙewa gami da isa toilet ɗin. Alwala ya ɗaura, ji yake kaman kada ya fita a toilet ɗin, ɗan ƙaramin showel ya ɗauko yana mai tsane fuskar shi hannuwa shi da suke lulluɓe da gashi luf luf dasu. Idanun shi ne suka kai kan wani abu dake cen gefe yade yana ta ɗaukar idanu. Hannu ya sanya gami da ɗauko wa, ɗan kunne ne mai matuƙar kyau da tsada, tsohon abun kunne ne, da ko wajen siyar dashi yake da daraja, mai ruwan gold, sai sheƙi yake yi, ɗan murmushi yayi na gefen baki, kallo ɗaya yayi mashi ya gane ba gold bane, saboda yana da katafaren shagon siyar da gold da changin kuɗaɗen ƙetare. "Nata ne" yaji wani ɓari na zuciyar shi yana sanar dashi, saidai tayaya zai bata ɗan kunnen ta? Fitowa yayi dashi a hannun shi riƙe yana mai jujjuya shi, a aljihun wandon shi ya saka shi, da niyyar idan ya fito ya haɗu da ita a harabar gidan ya bata ko ya tura mudi ya kai mata, sallar da yaji an tada ce ta sanya shi hanzari ficewa daga gidan baki ɗaya zuwa masallacin f Ban tashi gane ɗan kunnen baya kunne na ba, har saida naje cire wa zanyi wankan rana, sake laluba wa nayi, still dai baya kunnen, bayan na fito ne a wankan na dudduba ɗakin baya nan, sai lokacin na tambayi Hafsat da take zaune tana cin abinci, Abunda ke bani mamaki har kawo yanzu babu wanda ya damu da zaman hafsat ɗin sashen namu kaman yanda aka yi ma afnan lokacin da tazo. "Ban ganshi ba kuwa Suhan gsky, Amman tin lokacin da kika cire hijab ɗinki naga ba ɗan kunnen a kunnen ki, anya kuwa kin sanya shi kafin mu fita?" Hafsat ɗin ta bani amsa, ta ƙara she da jefo man tambaya, "Aikuwa tabbas na sanya shi a kunne na, Allah dai ya sanya ba cen sashen na yaddo shi ba, kinsan kuwa wannan ɗan kunnen ya daɗe, umma ta tace tin irin na da ɗin nan ne, itama gadon shi tayi. Shiyasa ma bana fidda shi a kunne na, sai in zanyi bacci kawai" na ƙara she ina mai dafe ƙirji alamar ƙirjina ya faɗi. Shigowar umma ce ta sanya na wayance tare da yima Hafsat alama da tayi shiru, aiko ta ja bakin ta ta tsuke, saidai da umman tawa ta kula zata gane alamun rashin gaskiya a tare damu. Tinani na shiga yi ta yanda zan bi in samu ɗan kunnen ya dawo gareni ba tare da umma ta kula ba, gashi an mayar ma Nihal ɗin da makullin, kenan ba damar in koma ba tare da kowa ya kula ba in ɗauka, kuma ko ba haka ba ma ina zullumi zuwa ya kasance yana sashen nashi. Hafsat ce take sanar dani in shirya zan raka ta siyayya anjima idan anyi sallar la'asar, da to na bita a zahiri, cen kau cikin zuciya ina ta laluben hanyar da zan bi abun kunne na umma ya dawo gareni. Daga masallaci bai dawo gidan ba wuce wa yayi wajen harkokin shi, ya manta da bai kulle ɗakin ba shaf, abu ne mai muhimmanci ya taso mashi. Ganin ana ta salla a masallacin gidan namu, ya sanya ni tinanin zuwa ɗakin nashi, da yanzu nake tunanin ma mallakin ɗakin baya ciki in ma har yana gidan to lallai yana masallaci. Fakaitar idanun kowa nayi, da hafsat muka shirya ko zata kula da umma kada ta gane bana nan, zata ɗauke hankalin ta. Cikin sa'a kuwa na tadda part ɗin a buɗe ɗan murɗawa nayi a hankali na tura na shiga ina ɗan waige waige. Fara dubawa nayi ko ina ban gan shi ba, dama na san bani ce nayi aikin falon ba, ya sanya kaɗan kaɗan na duba falon na wuce kai tsaye zuwa bedroom ɗin. Sai dai me duka ko ina na duba bangani ba, har toilet, bashi ba alamar shi, hankali na in yayi dubu ya tashi, Sam duk na firgice ko ganin kirki bana yi nice leƙa hada ƙarƙashin gado. Gadon na haye baki ɗaya, gami da yaye zanen gadon🤣🤣 duk cikin nema ne, ina tinanin ko ya faɗa ta bayan gadon, nan ma ban ganshi ba, jawo gadon na shiga yi, da yake gado ne irin mai tayoyin nan, aiko ba wahala na jawo shi, katifar na shiga ɗagawa cikin hanzari, gudu nake mai ɗakin ya dawo ya iske ni. Al'ameen da yake bakin ƙofa tsaye tin bayan shigar ta ɗakin nata ya shigo, da mamaki sama fuskar shi lokacin da ya jiyo motsi a ta bedroom ɗin nashi, a hankali ya shiga takawa har zuwa buɗe ƙofar. Da yake bata da ƙara ya sanya Sam bata ji ba, duk ta haɗa zufa sai aikin janyo gado take yi, ɗakin nan fa tayi mashi watsa watsa, hatta da bedsheet ɗin bisa side drower ta ɗora shi, filaluwan kuwa da katifar duk ta jingina su jikin wardroop ɗin tana ta faman leƙawa cen ƙasa gadon ko zata hango shi, da yake da zata gyara har gadon ta ɗaga ta sharo, sai tayi tinanin ko cen ya faɗa. Gyaran murya yayi a hankali, cak na ja na tsay, in ba kunne na bane yake man gizo, kaman gyaran muryar Yaya Al'ameen ɗin nake iya jiyowa. Kasa juyowa nayi, kurkusa nake jin shi, kaman ma ya shigo ɗakin, a slow na juyo, aiko idanuna suka faɗa cikin nashi, kasa ɗauke idanuna nayi akan shi, aiko kafe ni yayi da mayatattun idanun shi, wani irin kallo ya shiga bina dashi a hankali ya shiga takowa zuwa inda nake tsaye. Ja na shiga yi da baya ina yarfe hannu, na shiga uku kada fa ya ɗauka sata na shigo yi mashi, buɗe baki na shiga yi da niyyar kare kaina. Hannu ya ɗaga man alamar inyi shiru baya son jin komai, kuma har yanzu bai daina matsowa ta inda nake tsaye ba....... ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~22~* *Wannan Page ɗin sadaukar wa ne ga ɗaukacin WRITERS ɗin Golden Pen, Allah ya ƙara mana ɗauka ka, basira, da zaƙin hannu, Allah kuma ya bamu ikon rubuta Abunda zai amfani Al'umma baki ɗaya. AMEEN* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Ban dena ja da baya ba ina yarfe hannu, haka shima bai dena matsowa inda nake ba, har saida na dangane da bangon ɗakin, ba arziƙi na ja tsaya ina ta ƙwalalo idanuwa kaman uwar da yaranta suka ɓata. Daf dani ya ja ya tsaya, har ina iya shaƙo ƙamshi turaren da ke jikin shi, saurin sadda kaina ƙasa nayi, yanda ƙjrji na ke bugawa, har ina jin kaman zuciya ta zata tsago ƙirjina ta fito tsabar yanda take bugawa. Bai ce man ƙala ba, nima bance mashi ba, sai ma nake ganin dukkan abunda zan faɗa don kare kaina ba yarda zai yi ba, tinda tin farko ya nuna man baya buƙatar hakan. Hannun shi ya sanya a aljihu wandon nashi gami da ɗauko waren ɗan kunnen nawa da yake ta walwali cikin hasken farin ƙwan dake ɗakin yana ta sheƙi da walwali. Miƙo man yayi, kaman wadda ƙwai ya fashe mawa a ciki na sanya hannu gami da amsa, duk da yanda zuciya ta ke bugawa, hakan bai sanya murna da farin cikin da nake ciki sun ɓoyu ba daga fuska ta, murmushi na saki, har saida siririyar wushirya ta ta bayyana, fararen haƙora na da suke jere reras ya bi da kallo, lokaci guda yana mai ɗauke idanun shi gami da juyawa yana nufar ƙofar fita cikin salon takun tafiyar shi. Kaman ance ya tsaya, ya kuwa ja ya tsaya, gami da juyowa, Allah sarki, ta kuwa ƙure warin ɗan kunnen wanda yake cikin tafin hannun ta da idanu, ga dukkan alamu dai taji daɗin ganin abun kunnen, kuma ko babu komai ya ameen ya gane dalilin bincika mashi ɗaki da ya tadda ta take yi. "Sai ki gyara man ɗaki na tsaf, kaman yanda kika tadda shi" Abunda ya faɗa kenan gami da juyawa ya idasa ficewa zuwa falon. Da kallo na bishi, zuciya ta na raya man, wai in gyara mashi kaman yanda na tadda, kaman ba nice na gyara ɗin ba😠 Cikin sanɗa ma shiga bin shi a baya, bayan na maƙala ɗan kunnen nawa a mazaunin shi watau kunne na. Leƙawa nayi falon a hankali, hango shi nayi zaune bisa kujera mai cin mutum biyu, gaban shi da laptop yana ƙoƙarin kunna wa, ga dukkan alamu aiki zai yi cikin ta. Rufe ɗakin nayi, gami da murza mashi key, a hankali ya ɗago jin ƙarar sanya key a ƙofar, ɗan murmushi ya saki na gefen baki, yana girgiza kai bayan ya kauda idanun shi daga ƙofar ɗakin zuwa laptop ɗin. Nikau dalili na nayin hakan, ba zan juri in gyara mashi ɗaki harda gado ba, alhali yana cikin sashen kuma mu biyu da gani sai shi, ina ai ba zai yuwu ba. Gyaran da nayi ma yafi na farko wanda nayi, saboda wannan karon ɗakin ya samu canje canje da nayi, hatta gadon na canza mashi mazauni, da ba a saitin taga yake ba, gashi muna yanayi na zafi, wannan ce ta sanya na maida kan gadon saitin taga, yanda fresh air zata ringa shigowa, zai samu sauƙi kunna ac ɗin da yake yi, wanda kowa ya sani tana da illa ga lafiya ɗan adam. Ina gamawa, ban jira komai ba, na fito da niyyar ficewa, yanzun ma ban tanka mashi ba, shima bai ko ɗago ya kalle ni ba, duk da yaga gittawa ta, Amman ƴan maganar basa kusa, koma suna kusa me zai ce mata? Yarinyar da ƙiri ƙiri ya nuna bata yadda da shi ba a zahiri. Ina daf da ficewa na tsinkayi muryar shi yana cewa "Ki kira man Hafsat in kin fita" & an waiwayowa nayi ina cewa to gami da idasa ficewa gabaki ɗaya a part ɗin. Fita ta ne yayi daidai da fitowar maree daga babban sashen gidan, direct ɗakin Ya Ameen ɗin ta nufa, Nikau da idanu na shiga binta, wasu irin kaya ne ta sanya matsattsu, dinkin ya kama ta sosai, bayan nan kau an wawashe kusan rabi, haka ma gaban rigar, kai abun dai babu kyaun gani, ɗan gyale ne ta yafa wanda dashi gara babu, takalman ta masu tsinci ne, wannan tasanya duk takon da tayi sai ya bada sauti "ƙwas" Itama bata yi sanya ba ta bini da kallo, mamaki fal a cikin ranta, me naje yowa sashen Yayan ne? Gashi kuma ni kaɗai ta gani, wani wulaƙantaccen kallo ta shiga jefo man, tanayi tana tauna chewin gum tana ƙas ƙas dashi tana farfara idanu tana wata yatsina, ni wallahi sai ma ta bani dariya. Wucewa nayi ina mai waiwaye ta, lallai kuwa ɗakin ta ke da niyyar shiga, Amman taja ta tsaya tana ƙara gyara zaman riga da skirt ɗin a jikin ta, ikon Allah, yau ina kallon abu, to me zata je yowa sashen nashi a haka? Har ga Allah dai na san duk da ba'a shedar ɗan mutun, na san shi ya Ameen ɗin bai da wannan ɗabi'ar, kuma ma dai na san ko neman matan zai yi, ba zai tsaya ma wannan ballagazar ba, wanda ko jirin kirki da kyaun kirki bata da. Ban aune ba naga har na isa ɗakin namu, sallama nayi na shiga, naki yi sa'a umman tawa bata nan ta fita, Hafsat kawai na tadda a zaune tana ta faman yin waya da wanda zata aura, murmushi tayi gami da cewa "Laa gata nan ma muna maganar ta" miƙoman wayar tayi tana faɗin "gata ku gaisa ma" Amsa nayi ina mai ɗan harararta cikin wasa, alamar ban shirya ba haka kawai ta dunguno man wayar tana dariya shaƙiyyanci. Ba laifi mun gaisa cikin raha, harda ɗan wasa haka, yana tambaya ta "ya shirye shirye biki, tace yau zaku fara ko?" da eah na bishi don bansan ta kan zancen ba, muka yi sallama yake faɗa man ya kusa shigowa ƙasar zai zo mu ƙara tattauna wa. Itama ɗin sallama tayi dashi, bayan na miƙa mata, ta ƙagara taji ina na samo ɗan kunnen da ta hanga a kunne na bayan na cire hijab ɗin dake wuya na. Aikau na kwashe komai na faɗa mata, na ƙara she da faɗa mata saƙon na yayan namu. Me ko zata yi in ba dariya ba, nan ta shiga zaulaya ta, ta miƙe tana cewa bari inje inji kiran da yayan namu yake yi mani, in kaji kiran shi ai samu ne wallahi, kiyi maza ki shirya lokacin fitar tamu ya ƙarato. Sallama tayi cikin shaƙaƙƙiyar murya, ga dukkan alamu ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba wajen siranta muryar tata, bai ko ɗago ya kalle ta ba, shi duk a zaton shi hafsat ce, gashi kuma yaga ana nufo inda yake zaune ba tare da ɗar ko wani shayi ba, tin daga ƙafafun nata yake bi da kallo, sun kuwa sha mai sunyi da bare da bare abun su🤣🤣 sai sheƙi suke yi cikin man da ta shafa. Aiko cikin hanzari ya ɗago yana bin sauran jikin nata da kallo, har zuwa kan fuskar ta, runtse idanu yayi gami da juyar da kanshi, ko babu komai dai yayi mugun gani, domin kuwa kusan rabin nonuwan ta a waje suke, show me your breast kenan🤔 "Keeee" ya miƙe a fusace yana mai daka mata tsawa, sannan ya ɗora da faɗin "me ya kawo ki nan? Wani abu kike buƙata? Ko wani ne ya kira ki? Ya faɗa cikin fushi da matuƙar ɓacin rai. Rau-rau da idanu tayi alamar tausayi, wanda hakan da tayi ne ya ƙara ƙular dashi ma, sannan ta shiga faɗin" Suhan ce ta ce inzo wai kana nema na" ta faɗa cikin yanko ƙarya tana mai lailaya mashi. "Get out from here" ya faɗa yana nuna mata ƙofar fita, ba ke nace ta kira mani ba, Hafsat nace, ke me zan maki in nace ta kira mani ke? Ko ni kike ma aiki ne?" ya faɗa yana mai jefo mata tambaya kaman zai make ta. Girgiza mashi kai ta shiga yi, har ga Allah jikin ta yayi sanyi, domin ko kafin tazo nan saida ta shisshirya, hatta wankan da tayi da ruwan magani tayi shi, tayi matse matse da dama, domin tana tinanin Al'ameen ɗin kanwan lasa ne, da har zata jawo hankali shi ta ruwan sanyi haka. "A'a yaya, kayi haƙuri" ta faɗa kaman wata baiwar Allah, sannan ta juya tana wata irin karairaya har zuwa ficewa ta a ɗakin. Da kallo ya raka ta yana mai jan wani irin tsoki, baya son wulaƙanta mutum masalan ma wanda yake ƙarƙashin shi, Amman wannan dole ce ta sanya, in banda tana sakarya ma ya za'ayi ta yi irin wannan shigar sannan tazo gaban shi tana karairaya kaman zata faɗo mashi? Sallamar Hafsat ɗin ce ta katse mashi dogon tinanin da ya shiga, zama yayi yana mai amsawa a hankali, rufe laptop ɗin yayi yana mai kurɓar ruwan tatattun ƴaƴan itatuwa masu sanyi da suke gaban shi yayi. Ɗan nesa da shi kaɗan ta samu ta zauna tana mai cewa "yaya gani Suhan tace kana nema na" Da idanu ya bita yana mai ƙirƙiro murmushi dole cikin son kauda ɓacin rai da yake ciki, kenan waccen Yarinyar da ta fita yanzu ƙarya take ma Suhan da tace ita ce tace tazo yana neman ta? Sake kauda tinanin yayi cikin ranshi, yana mai gyara zama ya fuskanci hafsat ɗin sosai, tambayar ta ya shiga yi shirye shirye da sauran abubuwan da take buƙata wanda bata idasa ba, yana gargaɗar ta da kiran nasu gidan domin neman wani abu, duk Abunda take so yana iya yi mata, ta tunkare shi kai tsaye kawai. Da yake akwai fahimta sosai tsakanin su da ƴar shaƙuwa, yana son hafsat ɗin, ko don sanyin halin ta da kuma girmama na gaba da ita, ba kaman sangartattun ƙannen nashi ba, ta shiga zayyane mashi dukkan abubuwan da take buƙata, take yayi mata trnsfer na kuɗaɗen duk da zasu isheta ta kammala hidima ta har ma tayi saura, sannan ya shiga sanar da ita hukuncin Alhaji na cewa ba zata koma gida ba, har sai an ɗaura auren nata, suma duka sauran mutanen nan ba da daɗewa ba zasu tarkato su taho Abuja acen za'ayi duk wasu shirye shirye da hidima bikin, hatta da su kaka zuwaira duk nan za'a taho dasu domin suma su ɗan shaƙata, zaman wuri ɗayan ya isa hakanan. Ƴar fira sukayi kaɗan kaɗan, abun ka da wanda bai damu da magana ba, hakan ce ta sanya ta yi mashi godiya gami da miƙewa ta fice harda tukuicin ja mashi ƙofar, wani ɓari na zuciyar ta na tambayar ta me maree taje yi sashen yayan nasu? ************* Maree da take zaune ɗakin mama talatun da ta kasance ita ce mahaifiya ta, Amman ba kowa ya sani ba, ƙwalla take share wa, cikin ƙunan rai ta shiga zayyane mata Abunda ya Ameen ɗin yayi mata, aiko ashar ta lailayo ta zunduma tana faɗar baƙaken maganganu, "kika ce har Suhan kin gani a sashen nashi?" ta jefa mata tambaya, tana daga tsaye riƙe da ƙugu. "Eah mama, na ganta lokacin da ta fito, har ma harara ta ta dinga yi.... " ta faɗa cikin ƙunar zuciya, uwar tata ce ta katse mata maganar da take yi "ke dallah ja cen ki ba mutane wuri, ki tabbata duk yanda zakiyi kiyi, ki jawo hankalin yaron nan a gareku, ki tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi maki ƙafafu, ki dai san a nan gidan babu wanda ya san nice na haife ki, ko shiga hidimarki kika ga bana yi, bana so kwabar mu tayi ruwa, Amma billahillazee duk yanda zamuyi sai mun mallaki ƙaramin yaron nan attajiri, sai mun mulka da juya gidan nan fiyee ma da yanda Kubra keyi" ta faɗa tana huci da hurtai. "Kyalesu, na san abun yi, ba dai ke ya wulaƙanta ba,? Zai dawo ne yana neman soyayya ki da roƙon ki, a yayin da zamu juya shi kaman waina a cikin tanada, goge hawayen ki, ki koma bakin aikin ki kada su dawo su tadda baki kammala Abunda suka sanya ki ba, ina so ne ki shiga jiki su, kaman yanda jini yake gudana a jikin nasu, kuma ki tabbatas duk magungunan da na baki kina zuba masu a abincin da suke ci, ki kula fa, kinsan kukun nan basu da mutumci, kinsan ƴan kudun nan, shegu ranakun banza" ta ƙara she tana gyara zaman za in ta da har ya warware tsabar bala'i gab yake da faɗuwa, har ɗan kaman ta kana iya hange. Da too mareen ta bita, tana mai tashi ta fice daga ɗakin, ko da zata gifta ta inda ɗakin nasu Suhan yake saida ta wurga mashi harara kaman Suhan ɗin ce a ciki. ******* Kammala shiryawa tawa, yayi daidai da shigowar Hafsat ɗin ɗakin namu tana mai cike da farin ciki, rungume ni tayi tana faɗin "kin gani ko Suhan, kingani dama nace maki kiran yayan Alkhairi ne a gare mu" kuɗin soyayya ya bamu wadda zamuyi har sai mun gaji da kashewa" cikin murmushi na zame jikina daga nata, domin tana niyyar kadan ne, na bita da kallo ina cewa "aiko kin gode wallahi hafsat, don Allah to karki kira gida a ƙara maki wasu tinda waɗannan sun isheki, ko shi Abdul ɗin (sunan saurayi hafsat ɗin wanda zata aura) kar ki amshi masu yawa a wurin shi." da to ta bini, tana mai ƙara gyara fuskar ta, sallama muka yi ma umma da take zaune tsakar gida tana sauraren radio sallama, addu'a tayi mana da sake faɗa mana kar mu kai magribawaje mu dawo da wuri. Ranshi har yanzu a matuƙar ɓace yake, me Yarinyar ke nufi dashi ne? A cikin gidan nan ma zata dinga yin irin wannan shigar tana matsayi mai aikin gidan da yake wadace da ƴan aiki maza, kama daga masu gadi, drebobin da masu gyaran lambu da ba flowers ruwa da share gida?, miƙewa yayi gami da shigewa ciki domin canja kaya, so yake ya fita ko zai shaƙo iskar da zata sanyaya mashi rai. Bai ko kula da yanda ta canja ma ɗakin tsari ba, har ya canja kayan ya fice, da yake wardrooo ɗin ta cikin bango ce, mai azabar kyau da ƙayatuwa. Keys kawai ya zara, gami da kwasar wayoyin shi na hannu, ya fice daga sashen nashi, gami da murza mashi makulli ya rufe😅 Tin daga nesa ya hango su, ya sheda hafsat, Amman gudar ce bai gane ba, har saida ya matsa daf dasu, inda suke tsaye suna jiran driver yazo ya kaisu, saboda yau ba ita kaɗai bace, ita da hafsat ce ya sanya ta yadda zata shiga motar gidan, shima saida suka kai ruwa rana sannan. Ƙala bai ce masu ba har ya isa ga motar tashi da take gefe tana ta ɗaukar idanu, horn ya danna masu, hafsat ɗin ce ta kula dasu yake kira, ƙara sawa tayi wurin shi, tambayar ta ya shiga yi tsayuwar me suke wurin, sheda mashi tayi driver suke jira ya ƙara so, yace ya kusa isowa gidan. (da yake muɗi sun fita da su Hajiya Kubra da amare) "Ku shiga in ajiye ku, idan ya ƙaraso sai yaje ya ɗauko ku in kun gama" Abunda ya faɗa kenan yana mai bin agogon hannun nashi da kallo don sanin ko ƙarfe nawa. Juyawa tayi gami da ya fito ni da hannu, a hankali na shiga taka wa gami da ƙara sawa inda take tsaye bakin motar Hannu ta sanya gami da buɗe man gidan baya, "ki shiga, yaya ne yace zai kai mu, in mun gama mun kira driver ɗin ya maidamu" Ba a son raina ba na shiga, "ya salam" na furta cikin raina, sanyi da ƙamshi motar sun tafi da imani na, ɗan lumshe idanu nayi, lokacin da Naji motar ta daidaita a saman kwalta. Ta baya nake satar kallon shi, tuƙin ma a natse yake yin shi, yayi kyau cikin riga marar nauyi kamfanin Adidas da baƙin wandon jeans a jikin shi, kai shi duk yadda ya sanya kaya ma kyau suke yi mashi. Duk yanda naso in hana idanu na kaiwa gare shi, basa jin magana, saidai in samu kaina dumu dumu ina mai ƙare mashi kallo tas, har baƙi siɗik ɗin kwantaccen gashin kanshi. Wani irin sanyin ni'ima ne gami da gaurayayyen ƙamshi turaren shi ne yake busowa, hakan ce ta sanya ni lafewa daga baya, ina tsura ma kyakkyawar fuskar shi idanu ta cikin madubi, tunanin nika ne masu yawa suke kai komo a zuciya ta, inda na taɓa faɗa mashi a ƙirji, inda na taɓa cakumo shi da umma ta bata lafiya, da kuma a makaranta kwanaki kaɗan da suka wuce. Ban aune ba na tsinkayo muryar shi daga cen gaba yana cewa " *kallon fa?*" Ɗan duburcewa nayi, ina mai faɗa a zuciya ta cewa na shiga uku ni Hauwa'u, Ya ameen ya kama ni dumu dumu ina kallon shi, Sam bansan idanuna na kan madubi ba, ban Kuma kawo ma raina cewa zai iya hango ni ba ta baya, da yake motar na da ɗan duhu haka. Tsaf ya tsare ni da idanu ta cikin madubi yana ɗan cije bakin shi da haƙoran shi kaɗannkaɗan. Hafsat ce da hankalin ta ya kai kanmu, kuma taji abinda ya tambaya, ɗan juyowa tayi kaɗan tana waywaye na, hakan ce ta sanya ni ɗauke kaina na maida idanuwa na kan glass ɗin da yake gefe na, gami da ƙure titi da idanu, ba tare da ko alamun bayar da amsa ba. *indai kunya ce, tau nidai yau na riga na shata ni Suhan* _Share_ _like_ _Comment_ ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page~23~* *Page ɗinki ne maman sadeeq, kiyi yanda kike so dashi, asha karatu lfy* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Fuska ta a ɗaure, ko da muka haɗa idanu da hafsat, harara na sakar mata, ita kau juyawa tayi tana ƙunshe dariya a ciki, harda rufe baki, saboda ta fahimci Abunda duk ya faru. Har yayi parking ƙofar katafaren supermarket ɗin ban ƙara yadda mun haɗa idanu dashi ba, ina ƙoƙarin sauka ne idanun A suka kai kanshi ta madubi, ya ƙureni da kallo ko motsi baya yi, hannun shi duka akan stiyarin motar ya jingina jikin shi da marfin motar ta ɓangaren shi, yayi kyau kaman saraki, saurin ficewa nayi har ina harɗewa da zumbulelen hijab ɗina Allah ma yaso ban kifa ba. Lumshe idanu yayi, ya sake buɗewa lokacin da yaji duk sun fice hafsat na jero mashi godiya, da kallo ya raka su, a zahiri gaskiya ba ita yake kallo ba, tinanin abinda maree tayi mashi kawai yake yi, ita kau mutuniyar tawa sai ta ɗauka still ita yake kallo. Jan motar yayi a matuƙar fusace ya bar wajen, dole ne ya ɗauki mataki, ba zai lamunci ƙaramin iskanci a cikin gidan nasu ba. Mun sha soyayya, abinda ke bani mamaki yanda hafsat ta ragargazo mani siyayya sosai da sosai, kayan fitar biki ne masu tsada ta siya man, harda kayan Fulani da za'a sanya ranar tradutional day da za'a gudanar a lambun gidan nasu. Kwanan mu biyar muna fita siyayya, har ɗinkunan mu duk mun amso, saboda kuɗin shap-Shap Hafsat ɗin ta biya aka yi mana. Gyaran jiki Hafsat ɗin ta tursasani saida na biye mata aka yi tayi mana tare, wanda a zahirin gaskiya ma gyaran jikin yafi karɓa ta tinda na fita haske sosai. Ban sake jin ɗuriyar Ya Ameen ba, haka suma mutanen cikin gida bama jin ɗuriyar su, hidimar biki ta sanya su gaba, ko ta kanmu ma basa bi. Tini gida ya ɗauki harama, dukkan kayan dake cikin gidan nan saida aka fidda shi aka cenza wasu, hatta fentin gidan baki ɗaya saida aka cenza. Kullum da kalar baƙin da za'ayi a cikin gidan, muma ta ɓangaren mu ba baya ba, muna shirya daidai ƙarfin mu. Gida ya fara tara jama'a, wanda hatta mutanen kankiya sun iso, da family ɗin Alhaji awwalun, da aka buɗe ma babban sashe guda, dole hafsat ta tattara ta koma sashen da aka basu, inda aka mallaka mata babban ɗaki guda ɗaya da komai da komai a ciki. Ba yanda bata yi ba don inzo muje tare nace aa, umma ta ma da ta tambaya cewa tayi a'a, indai tana buƙatar wani abu daga safiya zuwa dare tazo ina nan Amman banda kwana,dole ta haƙura ba don taso ba, muka cigaba dayin shirye shirye yanda ya kamata, daga safiya har dare kaman yanda umman tawa ta faɗa muna tare, domin nice na zame mata babbar ƙawa kaman yanda ta faɗa. Su kau sauran amaren ma ba ganin su mukeyi ba, suna sashen da aka buɗe masu su da ƙawayen su kawai, Shiyasa in ficewa zasu yi har sun fita ta ƙaramar ƙofa ma babu wanda ya gansu.to dama dai mu bamu damu da al'amarin su ba, babu abinda zai haɗa sai tradutional day da Hafsat ɗin tace shi kaɗai zata yi. Hajiya Kubra tare da manyan aminan ta da ƙawayenta sai shige da afice akeyi, bikin fa na manya ne, mata kake gani manya jugunannu daga kowanne ɓangare suna fitowa, zo Kaga ruwan ƙaryar gudunmuwa, har saida ta wakilta ƙawata Hajiya Laila ta dinga karɓa domin ita ta gaji da hayaniya. Ana saura kwana bakwai biki su Aunty Feena da Afnan suka iso, karkaso kaga murna, ba ma kaman yanda suka tadda gidan ya cika da ta kowanne fanni ƴan uwa da abokan arziƙi, dangin Hajiya lailan ma sun iso suna babban sashen ta aka sauke su, yo ai su nata ne ko, su kuwa ƴan kankiya ɓangaren kusa da na Hajiya zainab maman Hafsat aka basu, to dama dai sun fi shiri da jituwa da ita, saboda tafi Kubra sauƙi da girmama dangin mazajen nasu. Afnan ce ta rungume ni ta baya, tana "oyoyo Aunty na, wow kinga yanda kika yi kyau kika haska kuwa? Allah kaman ba ke ba, minene Sirrin?" ta faɗa tana kashe man ido ɗaya. Murmushi nayi na sanya hannu na jawo ta gabana, "Afnan yaushe zaki bar ce an auntyn nan? So kike a jiki ki jaman?" na ƙara she alamar tambaya. Murmushi tayi, sannan ta buɗe baki da niyyar magana, dakatar da ita nayi ina mai cewa "to yanzu dai ya hanya? Ya shirye shiryen biki?" "Shirye shirye ai sai ku, ko aunty Hafsat?" ta maida tambayar tata akan hafsat, bata jira cewar hafsat ɗin a ta zauna tana mai cewa "tau yanzu dai minene shirin ku? Ya ban ganku a sashen amare ba ku? Shiru muka yi mata ni da hafsat ɗin, ɗan nazarinmu tayi na tsawon second biyu, sannan ta ɗaga hannu alamar dakata-dakata " Bama wannan ba, gara da kukayi zaman ku nan ɗakin umma ta, (Tana nufin umman suhan) ku ƙyale su cen da ƙawayensu ƴan fafa, mu cigaba da hidimarmu anan kawai mu share su". Dukkanmu murmushi muka yi, umma ta dai tana gefe zaune, ƙala bata ce mana ba, da yake mun samu sauƙi tsangwama yanzu hidimar biki tasha kan kowa, sai ba'a damu da shigar afnan ɗin cikin mu ba mu kayi ta shirye shiryenmu daidai gwargwado. Afnan ɗin fa ta shige cikin mu, kaman ma ba ƴar gidan ba, ko wajen yayyen nata bata zuwa, komai mun kammala, hatta da kayan da amarya zata sanya tsawon kwana biyar da za' a fara hidimar bikin zuwa bayan kai ta gidan mijin nata, muma haka ta taya mu muka shirya su mu duka muka adana abunmu. Yau ne za'a kawo lefe, hakan ce ta sanya muka shirya zuwa wurin ƙunshi a yau, tau suma ɗin sauran amaren dai duk yau za'ayi masu, Amman su har gida za'a zo ayi masu, saboda a gobe ne za'a fara program ɗinsu tinda mu tradutional day ne kawai, saura kwana biyu biki ne za'ayi shi shi. Afnan ce ta jamu zuwa wani shago inda aka ƙware da zanen lalle, ɓaki da ja, aka yi ma amarya, masha Allah, gaskiya yayi kyau sai ɗaukar idanu yake, duk da hafsat ɗin ba fara bace, Amman kunsan amarya yanda take, kuma ƙunshi yayi daidai da kalar fatar jikin ta, sai aka yi ma afnan, ita fara ce tas, su tace baƙi take so duka, haka aka yi mata, masha Allah kaman ka sace ƙafar da hannuwan nan. Nice ƙarshe, hakan ce ta sanya nace ni ja nake so duka, ɗan kaɗan, cikin hannuwa da yatsu sai tafin ƙafa ya ɗan hau kaɗan, haka aka yi man shi, sunce yayi kyau sosai, nima na san yayi kyau ɗin, dama ba don wani nayi ba don kaina nayi. Haka muka dawo da yamma lis, mun tadda an kawo lefe, a bakin umma ta muka ji, wanka muka yi muka sake kaya sai ɓangaren maman Hafsat, mun gaishe ta da duk wanda ke sashen, da yake sashen ba hayaniya, bikin da za'ayi ba a gidan ta ba, Shiyasa batayo gayya ba sosai, duk da itama ƴaƴa biyu zata auras da Hafsat ɗin da yayan ta. Sashen su kaka zuwaira muka shiga, abun ka da wasu daga ƙauye suka zo, an fa yi ma sashen diƙi diƙi, abun ka da farin tiles da fenti sai dattin ya fito fili, tin kaka zuwa Iran na magana har ta haƙura ta gaji, shima saida Giggo Aisha, yayar su Alhaji mustaphan tayi mata magana, tace ta ƙyale su don Allah duka kwana nawa za'ayi kowa ya tattara ya koma? Jawo Hafsat ɗin kaka zuwaira tayi, tana mai cewa "Zonan ja'ira, ina kika samo miji malaniya haka? (Wai millioneire take sabon cewa🤣), kin kau ga kayan da aka kawo maki? Akwati ashirin da huɗu? Ko su iyayen kankambar ba'a kawo masu haka ba, sunkuyar da kai hafsat ɗin tayi tana mai ɗan murmushi, Giggo Fatima ce ta ce "Haba Hajiya, ya isa hakanan ki ƙyale ta, kowa ba da goshin shi yake zuwa ba?" Duk da haka saida ta danƙwashe kanta tana ƙara zaulayar ta, ita kuwa da taga haka sai ta sulale ta kwanta bisa cinyar tsohuwar tana mai cewa bari inyi hawan ƙarshe 🤭 Dukansu dariya suka sanya suna cewa ta ɗaga masu tsohuwa kar ta karya masu ita, da yake amarya farin jini gareta, sai kowa ya dawo nan aka yi ta fira da ita, to ko babu komai ai hakan yafi, dama su saran sarakan basu ko leƙa sashen ba tin bayan da suka je suka gaida su ranar da suka zo, saɓaninnhafsat ɗin da kullum sai taje, ko in raka ta ko ta tafi ita kaɗai. Nayi nisa cikin gyaran sashen da ya kusa komawa kwalta tsabar datti, cen an zubda tea, cen abinci, cen an jiƙa bredi an zubda, gida ne ba wanda ƙuda ya saba zama ba, Amman zuwan ƴan kankiya saida sashen ya koma matattarar zaman ƙudan, duk da wasu na kiyaye wa, Amman wasu kau sai a hankali, yo an kwaso ƴaƴa an taho dasu cin duniya 🤣 Saida na gyara ko ina tsaf, harda falon da suke zaune saida suka ɗaga na gyara, sannan muka bar sashen zuwa namu domin magariba ta kawo jiki. Goggo Aisha ce ta kalli Goggo Fatima tana cewa "wai ni kau Fatima, wannan ba yarinya nan bace da Muhammadu na wajen Mustapha yace yana so ba?" "ita ce kuwa, nima da farko ban gane ta b, sai da uwar tata ta shigo gaidamu ne sannan na gane ta, ai kinsan ita ce ta rako ta" kaka zuwaira da take zaune gefen su bata sanya masu baki ba, sai yanzu ta tanka tana mai cewa "haba, ni kau da har zan tambaya ina Hafsatu ta samo wannan yarinya haka mai natsuwa da son aiki, yarinya tana da tarbiyya wallahi, ku duba duk lokacin da tazo sashen nan sai tayi mana aiki, ko gazawa batayi" Goggo Aisha ce ta shiga jinjina kai alamar gaskiya ne zancen mahaifiya tasu sannan ta shiga cewa "aiko in haka ne, ni banga abun ƙi ba a tattare da yarinyar, yarinya kyakkyawa da ita masha Allah, ga hankali da natsuwa, ai irin ta ce kowa ke burin samu a matsayi suruka, in banda hauka irin na kubura" "kema kinnfaɗa Yaya, Allah shi kyauta yasa ya ta gane gaskiya" Ameen kowa ya amsa. nan suka bar zancen suka kama wata tashar kuma, yayin da cikin zuciyar hajiya zuwaira ta yaba da natsuwar Suhan ɗin sannan ta ƙhdurce abubuwa da dama akan lamarin. Washegari da wuri muka farka, domin yau ne ƙawayen Hafsat ɗin zasu fara zuwa, duk da ba wani event zata yi ba, Amman sunyi mata kara sosai sun zo da yawa kuwa. Bamu san wanene ya tsegunta zaman hafsat ɗin sashen su ba, ba cikin amaren ba, sai ga mama Talatu an aiko ta, cewa Hafsat ta koma sashen da aka ware ma amaren, ita da gayyar ta, ba don son ranta ba ta tattara ta koma cen, aka ware mata ɗaki ɗaya babba dazai isheta har zuwa ɗaurin auren nata. Komawa sukayi ita da Afnan roƙon ummata akan ta barni in tafi tare dasu, da farko ta hana, sai kuma ta barni tare da shara ɗin duk Abunda za'ayi mani kar in kula, in yi haƙuri in share, da haka muka ɗunguma zuwa sashen amaren Amman a ɗakin u nake komawa inyi wanka in shirya. Umma ta ta kan leƙa sashen Mama zainab ɗin, kama mata wasu ƴan ayyukan, da haka har suka saba, in ma bata ga tazo ba ta kan aika a kira ta. Mun shiga cikin hidimar bikin dumu dumu Dukkanmu, albarkacin Hafsat da mahaifiyar ta, Abunda banyi zaton umman tawa zata lamunta ba, sai gashi ita dakanta ke ƙara gaya man irin halin kirki da karamci irin ma Hajiya zainab ɗin, da gani dai Hafsat ɗin ita ta biyo. Abunda na kula dashi shine, duk lokacin da zan gifta ko zan wuce ta falon shine shewa da ƴar guɗa da ake Sanyawa haka ana zunɗe na sai kuma ayi tafi a kashe, manyan yara ne masu ji da kansu, ban ma yi tinanin zasu tsaya kula ko zunɗena ba, tinda Nidai bansan me suke mawa ba, bansan me na aikata masu ba da har suke yi man haka. Share su nake yi kaman yanda umman tawa ta umurceni. "Hahaha, Wannan? Yo me haɗaɗɗen saurayi kaman wannan zai ci da wannan? Haba Nihla, kisan me kike faɗa mana, dubeta fa, kaman alhaja, har koɗa take yi, ni anya ma ba sadaukar yalla bace, irin waɗannan masu muna bara muna karuwanci bace? Ni wallahi na tsani yarinyar bansan dalilin da ya sanya Dad ya sanya suka dawo nan ba, kishin ta nake ji sosai har cikin raina, bansan dalilin shi na son auren ta ba, bayan gani." Ɗaya daga cikin ƙawayen su Saudat ɗince ke cewa haka, ban ko kalli inda suke ba nayi saurin wucewa, fatana dai ace ba dani suke ba, yo me ma zai sa inyi tinanin dani suke? Bayan banji sun kama suna ba, kuma ni na san babu wanda yace zai aure ni balle har wata tayi kishina a banza. Share zancen nayi, ina mai shige wa ɗakin amaren da suke ta shirye shiryen zuwa bridal shiwer ɗin da aka shirya za'a gabatar a yau, duk da ita amaryar tasu tana kwance, tace ba da ita ba, bai hana su cewa wallahi sai sun je ba sun kashe ƙwarƙwatar idanun su. Harda Afnan aka shirya sunyi shiga ta jar riga da straigh skirt Black, sai hula itama baƙa an ɗaura wani abu mai kyalkyali a hannu shima ja, sunyi kyau ba laifi, Amman a haka wai ƴaƴan musulmai zasu fita, Allah shi kyauta. Motoci aka kawo aka shiga ɗaukar amaren, dama even ne na mata, wani ƙerarren gida dake ta bayan Layin su aka shirya ma abun, shima ya sha decoration Red and Black, sai amaren da sukayi complet White, ba ƙaramin daɗi suka ji ba da hafsat tace bata yin even ɗin, dama wai suna gudun a cika masu wuri da ƴan ƙauye, Shiyasa suka bata getpass guda biyar kacal. To ita cewa ma tayi bata zuwa, sai ƙawayenta ne su huɗu suka shirya aka tafi tare dasu, suka saje cikin ƙawayen amaren, saura getpass guda kuwa ajiye shi aka yi baya da wani amfani, gidan fa yayi tsit, duk masu rawar kan an da ƴan ƙaryar na sun kwashe sun tafi, sai Naji dama gidan ya cigaba da zama a haka Ohh🤔🤔 su suhan da ƙarfin hali ake. Washegari sukayi arebian night, hall aka kama mai kyau da tsada, acen aka gabatar da shirin, wannan haɗe yake maza da mata, sunyi yadda suke so, da yake ba ya ameen babu mai kwatsa masu, abie ƙanen su ne y bai isa yace gyadda za'ayi ba duk da Aunt Feena na wajen, to itama bata ce ga yadda za'ayi ba, tinda Rayuwar turawa ta shiga kansu da yawa. Mothers eve, aka shirya washegari, zo Kaga yadda aka ƙawata gidan da yake a haraba gidan za'ayi, anyi ɓarin kuɗi kaman da gayya, makaɗa da mawaƙa sun sha daloli, dole ne asan da bikin ƴaƴan Hajiya kubra Dambulan akeyi, rawa dai da juyi sunyi shi, manyan mata ko kunya basa ji haka suke juyi suna watsi da kuɗi, babu Abunda kake hangowa illa, gwala-gwalai, da ɗanyun lesussuka malam, masu video coverage nayi, masu hotuna nayi. Duk abun nan da akeyi Ya ameen ɗin na tsaye ta window ɗin falon nashi yana hango su, hannuwan shi duka soke cikin aljihu wandon bugaggiyar shadda tashi, fuskar nan tashi murtuk, bai san me ke damun mahaifiyar tashi ba, bidi'a da alfahari kawai ne acikin ranta, in banda haka duk wannan watsi da kuɗin da akeyi duk na menene? Wa za'a burge? Wa ke bai san suna da kuɗin ba? To indai haka ne shi a ganin shi wannan almubazzaranci ne. Makullan motar shi ya zara gami da ficewa ta ƙofar baya, jin kiɗan dake tashi a cikin gidan zai fasa mashi dodon kunne duk kuwa da girma da faɗin gidan. Zaune nake kunnuwa na toshe da headphone, ƙira'ar Sheik abdurrahman sudais ce nake saurare. Ina jin daɗin muryar bawan Allahn, a hankali nake bi shi cikin suratul baƙara, nayi nisa cikin bin shi karatun, ɓangaren ɗaya kuma tinani ne barkatai cikin ƙwaƙwalwar ta, a hankali Naji wani abu na bimanta cikin ƙafa, saurara wa nayi, lallai wani abu ne ki bi man jiki dagudu, a zabure na tashi ina kwalla ƙara gami da fara dire dire da ƴan tsale tsale. Bai aune ba yaji an kai mashi cakuma, zuwan shi kenan ta wurin yaji ihun mace, ni kau da dai Naji na samu wanda zan kama sai na kuma ƙwaƙume shi ina ta kurma ihu da tsalle tsalle, duk na cukuikuye hijabi na da fuska ta, wayata datayi tsallen baɗake gefe ta faɗi har headphone ɗin ya zare, karatun ta take ci gaba da rerawa a hankali a hankali. Ƙoƙarin raba ni yake da jikinshi, ni kau sai ƙara ƙwaƙumeshi nake yi cikin murya ta mai cike da tsoro nake faɗin "wani abu na bina, ƙila kunama ce, a taimakeni" "Ke ke wai meye haka ne, ya isa babu abinda ke binki, ba kunama bace, gidan nan babu kunama, ana yin feshi ki natsu" Ban ko saurare shi ba, har saida na cire hijabi na wurgar da ita ta gefe, kama zanin nayi da niyyar kwance wa ya daka man wata irin tsawa, ba azziƙi na dawo cikin hankali na. Sai sannan ne wata irin kunya ta kama ni, ganin Abunda nake shirin aikatawa, gani tsaye ko hula babu a kaina balle ɗan kwali, duk nayi wurgi dasu harda hijab ɗin. Kaina kuwa kaman wata sabuwar mahaukaciya, dama ɗazu muka je akayo mana saloon, babu wanda baiyi santin kyawon da kaina yayi ba da tsawon da yayi har kusan tsakiyar baya, dama ban taɓa yi ba wannan ne yina na farko, duk da cika da yawan da gashin nawa yake dashi haɗi da tsawo. Tattara gashin nawa na fara yi, na maida baya, sannan na wawuro hijab ɗita na sanya gami da ɗaukar wayar tawa da har yanzu sautin ƙira'ar malamin ke tashi. Juyawa nayi da niyyar barin gurin ina mai cewa "Yi haƙuri yaya" dakatar dani yayi fuskar na tashi murtuk "Ko kin koma cikin gidan basu gama kaɗe kaɗen nasu ba, zo muje" Yana gama faɗar haka ya juya ya cigaba da tafiya, zuwa ga ƙofar da zata sadaka da bayan gidan, wanda sai kayi doguwar tafiya kafin ka shawo kwana zuwa bakin Gates. Mamaki ne cike da raina, in bishi muje ina cikin wannan daren, ko ba ma haka ba, in ummata ta ganni ince mata me? Ko idan wani ya ganni yaje ya faɗa mata fa? Ganin yaja ya tsaya ne gami da ɗan waigowa ya sanya ni ɗaga ƙafa cikin sauri na shiga binshi, juyawa yayi gami da cigaba da tafiya, duk da ɗan hasken farin wata da fitilu jefi jefi dake bayan gidan, da naga zai yi man nisa na kan ɗaga ƙafa a sukwane in bishi, har muka ɓulla ta fuskar gidan. Hamdala nayi ganin mutane jefi jefi a ƙofar gidan da alama ma wasu zance sukeyi, bugun zuciya ta ne ya ƙaru, ganin ya nufi motar shi dake fake gefe guda ya kunna ya shiga, alama yayi man da in zagaya in shiga nima. Ba musu, dole na buɗe gidan gaba na shiga shiga na zauna, ɗan kwali na a hannu, sai raba idanu nake yi. Tada motar yayi gami da ficewa daga Layin, bai tanka mani ba haka nima ban ce mashi ƙala ba, kowa na fama da ƴan miskilancin shi a kai, ni gani ma nake yi ya cika ƙarfin hali, haka kawai sai yasa ni in shiga motar shi ya ɗauki hanya dani alhali bansan inda zai kai ni ba? "Sai daki zanyi" Abunda yace kenan ya ja bakinshi yayi shiru, ɗan zaro idanu nayi, bansan zancen zuci ya fito fili ba, ɗan waiwaya wa nayi na kalle shi, ina mai sadda kaina ƙasa, "kayi haƙuri, ummata bata san na fito ba Kaga dare yayi, Shiyasa nake jin tsoro" Maimakon ya bani amsa, sai shiru da yayi yana mai maida hankali shi kan tuƙin da yake yi, shiru ne ya biyo baya acikin motar kaman ma ba zai tanka ba, sai kuma cen Naji yace *"Kallon me kike yi mani rannan??? "* ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~24~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Shiru nayi mashi ban tanka mashi ba, har yanzu fa ni a tsorace nake, yo naga muna ta sharara uban gudu hanyar ba kowa, bansan ina muka nufa ba, sai aikin murza yatsu nake, ganin ban bashi amsa ba na ɗauka ya bar zancen kenan. *"Kallon me kike man rannan?* Tambayar ta ƙara zo man a bazata, bayan duk tsawon lokacin da muka ɗauka ban tanka ba. Shahada nayi wajen cewa" kayi haƙuri" "Ba haƙuri na tambaye ki ba, so nak insan dalilin kallon, ko nayi maki kama da wanda kika sani?" Ya jefo man maganar da banyi tinanin zata iya fitowa a bakin shi ba. Shiru na sake yi mashi ina sun ne kaina, ni sai ma ya bani ƴar dariya, bansan sautin dariyar tawa ya fito ba sai ji nai yana cewa" Dariya ma na baki ko?" Ɗan juyawa nayi ina mai sake kallon shi, shi ɗin dai ne, Ya Ameen ne yake ta tuƙin shi hankali kwance yake zaroman magana kaman ba shi ba, ashe dama yana magana haka? Tinani nake ta faman yi, yayin da shi kuma ya sake maida hankalinshi a kan tuƙin shi, ban tashi farfaɗowa daga kogin tinanin da na shiga ba saida naji tsayawar mota alamar dai mun iso inda zamu. Ɗaga idanuna nayi ina mai ƙare ma wajen kallo, yayin da shi kuma har ya fita gami da kullo ƙofar. Airport ne muka zo, lallai wajen ya ƙayatar dani, ba ƙaramin ƙaramin kyau wajen yayi mani ba, na saki jiki ina ta more kalle kalle na, tinda na san baya cikin motar, Naji maganan shi kaman daga sama. "Malama sai ki fito" Ɗan zabura nayi, kunya duk ta dabaibayeni, domin Sam bansan yana tsaye yana kallo na ba, ashe glass ɗin motar ƙasa yake kaɗan. Fitowa nayi, zullumi da fargaba duk sun cika man zuciya, na san yanzu umma ta suna cen suna nemana, wayyo Allah na, na san kuma Hafsat zata ce mata bata san inda na tafi ba. Gaba yayi ina bin shi a baya, sai harɗewa nake ta cikin hijab, yana kallo na kuma bai ce man komai ba, sai nayi kaman zan faɗi, sai ya juyo ya ɗan kalle ni Amman ba zai ce an komai ba. Mutane ne ke ta hada hadarsu, ga wajen tar da hasken ƙwan fitilu mashi masifar haske kaman rana. Wasu da ƴan alluna, an rubuta su aye, ga mutane suna ta fitowa daga wani ɗan ɗaki na glass, tin daga nesa ya hango shi, da ƴar sassarfa ya ƙara so inda muke gefe tsaye Ya Ameen yana ta gabana haka. Tafasa sukayi lokaci guda suna sakar ma kansu murmushi na tsabar ƙauna irin ta aminai "Ya dai Friend? Ai ban ɗauka zakazo haka da wuri ba, na Ɗauka sai ka shanya ni kaman yanda ka saba" Ɗan murmushi na gefen baki ya sake yi, sannan ya shiga cewa "wallahi ai kasan gidan mutane sun yi yawa, duk an cika gidan da Bidi'o'i sun dameni, suna neman fasa man kunne Shiyasa ma na fito haka da wuri" Juyawa sukayi suka shiga tafiya suna riƙe da hannayen juna. Da alama ma ƙila ya manta da wata abu wai ita Suhan a bayan shi tsaye. Ganin haka nima sai na shiga binsu, mu yi tafiya mai ɗan nisa, sannan muka isa ga motar tashi. Sai sannan ya tina da ita, juyawa yayi a hankali yana kalle kalle alamar yana neman wani abu. Da yake ina ta gudan ɓarin mota bayan Bilal ɗin sai bai lura dani ba, ganin ya juya alamar zai koma ta inda muka fito ne ya sanya ni cewa "gani nan yaya" Tsayawa yayi, gami da juyowa, ya sanya key ya buɗe motar, Bilal ɗinne ya juyo a ɗan razabe jin wata irin siririyar muryar mace ta bayan shi. Kallon tuhuma ya shiga yi ma Al'ameen, yayin da shi kuma ya basar yana mai shige wa motar, bayada zaɓi illa shima ya shiga, zamana cikin motar ne yayi daidai da tashin motar yayi revos ya halba ta bisa titi. Ba wanda yace uffan har muka yi nisa, ganin shirun tayi yawa ne kowa da Abunda yake saƙawa cikin rai, ya sanya Bilal kauda shirun ta hanyar cewa "Mutumena ya hidimar biki" "Suna cen suna yi" ya bashi amsa a taƙaice, shiru Bilal ɗin yayi don ya san halin Al'ameen ɗin, tinda ya ji ya fara amsa mashi a gajarce ya san ƴan maganar basa kanshi. Har muka isa gidan ba wanda ya kuma tankawa, an tashi daga mothers eve ɗin da ya tashi daga evening ya koma night, sai aje ayi ta faman ƙara'in salloli kuma. Da kwai sauran mutane, Amman jefi jefi, har cikin gidan ya shiga gami dayin parking, dama abunda nake jira kenan, nayi saurin ɓalle murfin motar gami da ficewa, kai tsaye sashen amaren na nufa da yanzu cen ɗakinsu Hafsat nake kwana. Duk agaji anyi tuɓus, wasu ma duk sun kwakkwanta, hakan ce ta sanya ba kowa ne ya lura dani ba, Hafsat ce kawai zaune tana waya da angonta, ita kau Afnan ta shiga watsa ruwa toilet. Lallaɓawa nayi gami da kwanciya kafin Hafsat da take tsaye bakin window ta ganni. "Tashi Tashi na ganki wallahi, gaya man daga ina kuke?" Abunda Naji hafsat ɗin ta faɗa kenan, bansan ma lokacin da ta katse wayar ba, sai ganin ta nayi har ta ƙara so inda nake kwance bisa katifa. Tashi nayi duk borin kunya ya kama ni, cire hijab ɗin na shiga yi, ina cewa" uhmm wai daga ina muke? Ko dai daga ina nake, ko kin ganni da wani ne da zaki ce daga ina muke?" " Eh" ta bani amsa kai tsaye, sannan ta ɗora da cewa "ke da Yaya Al'ameen da Yaya Bilal da ganku kun dawo yanzun nan" Ɗan zaro idanu nayi, kaman ƙasa ta tsage in shige nake ji uwa wadda tayi wa sarki ƙarya. "Kinga fa wallahi shine ya......" fitowa afnan ce daga toilet ɗin ɗaure da towel ya katse man maganar da nayi niyyar faɗa ma hafsat ɗin. "Humm" kawai afnan ɗin tace tana ɗan murmusawa, da alama duk taji zancen da mukeyi, saidai ƙala bata ce ba. Lura da ita ne da Hafsat ɗin tayi ya sanya ta basar da zancen itama, tana mai miƙewa zuwa toilet ɗin. Duk ina zaune ina saƙawa da warwarewa, har afnan ɗin ta gama shirin kwanciya, lokacin ne Hafsat ta fito da alama itama wanka tayo, "Ki tashi ki bar tinanin hakanan Aunty Suhan kije kiyo wankan kema" Abunda afnan ɗin tace man kenan, ta sake gyara kwanciyar ta gami da juyawa tana murmushi. Duk fa na bi na tsargu kaina, kaman wadda kwai ya fashemawa haka na miƙe ina jan ƙafafun nawa har na shige toilet ɗin. Da murmushi itama Hafsat ɗin ta bini, tana fatan Abunda take zargi ya tabbata, da tafi kowa jin ɗaɗi, kuma taga ƙarshen Hajiya Kubra da ta ɗauki son duniya da burin duniya ta aza shi akan yaron nata. Makullin sashen kawai ya miƙa mashi, yana mai cewa "bari in nemo mana Abunda zamu ci" Amsa Bilal ɗin yayi gami da juyawa ya nufi sashen aminin nashi, yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya kaɗa kan motar gami da sake ficewa daga cikin gidan. A bisa kujera 3seater ya zube, gajiya fal a cikin jikin shi, Amman ba ita ce tafi damun shi ba, ganin aminin nashi da yayi da yarinyar da yake iƙirarin auren ta, kar dai ace da gaske abokin nashi yake akan zancen yarinyar, saidai lura da yayi da yanda ya gansu, da kuma irin zaman da aka yi cikin motar har kawo dawowar su gidan babu wata alama dake nuna maka cewa su ɗin soyayya suke, Amman in ko haka ne, menene dalilin Al'ameen ɗin na yawo da ita cikin mota da daddare haka? Ya daɗe nan kwance yana saƙawa da warwarewa har Al'ameen ɗin ya dawo, nan ya tada shi kwance yayi zurfi a tinani, ɗan dukan shi yayi a cinya yana "tashi yallaɓai, ba dai bacci kake yi ba haka, ko wanka ba kayi ba balle kaci abinci" Tashi yayi yana murje ido, yayin da Al'ameen ɗin ya wuce kitchen ɗauko spoons da plate da lemo da ruwan sha, a haka ya dawo ya tada abokin nashi zaune yana narai narai da idanu. Zuba masu abincin yayi, yayin da ya jawo stool ya ɗora masu akai, Al'ameen ya san darajar baƙo, duk da kasancewar Bilal ɗin ɗan gida kuma aminin shi, haka yake in yaso har ruwan wanka yana haɗa mashi in ya kawo mashi ziyara. Har suka gama cin abincin, Bilal na ma Al'ameennɗin kallon tuhuma, to abunka da aminai, tini Al'ameen ɗin ya ɗago shi, murmushi yayi yana mai goge baki da tissue "Bari in gaya maka Abunda kake son tambaya ta tin kafin ka tambaya, yarinyar da ka ganni ɗazu ya ita, na san dai ka santa kasan komai a kanta, kuma har yanzu ina kan baka na a kanta, saidai ita bana tsammani ntasan komai, dalilin da ya sanya kuma ka ganni tare da ita, shine....... " nan ya kwashe komai ya faɗa mashi a gajarce. Murmushi yayi yana faɗin" Mugu, watau har kasan Abunda nake son tambayar ka ko? To ai shikenan Allah ya zaɓa mafi alkhairi a cikin Al'amarin, Amman dai ka kula gudun ja ma yarinyar matsala ko a wajen mahaifiyarka, kadai ga yanda take iya ƙoƙari wajen bata tarbiyya" yana faɗin haka shima ya ajiye spoon ɗin dake hannun shi ya tashi gami da shige wa bedroom domin yin wanka da rama salloli dake kanshi, sannan ya kwanta, shi kau oga Al'ameen, maida komai yayi kitchen, gami da wanke na wankewa, ya gyara komai tsaf, dama haka yake, baya son ƙazanta ko kaɗan, duk wani abu da ya san zai yi na tsabta baya jira ayi mashi shi keyi da kanshi, saidai Abunda ya san zai ɓata masa lokaci ne. Hatta da girki ba Abunda bai iya dafawa ba, saboda shi ba abincin kowa yake iya ci ba, ko zaman da yayi ƙasashe waje shi keyi a kanshi abinci, matuƙar bai yadda da wanda aka kawo mashi daga cikin hotel ɗin ba. Sun daɗe suna fira kafin su kwanta, yayin da ni kuma har bayan na kwanta ɗin juye juye kawai nake yi, hafsat ɗin na kula dani, har yanzu bata gaji da wayar ba haka, tinani nake yi na abubuwa da dama, Amman tinanin nawa yafi karkata ma ga Jarabawa da na rubuta kusan kwanaki da dama baya. Sai daga baya ne tinanin Al'ameen ɗin ya faɗo mani, lallai ni bansan ma me zan kira Abunda yayi mani dashi ba Gashi in akula har yaja hafsat ta fara mana wata fassara ta daban, ɗan guntun tsaki naja ina mai sake gyara kwanciya ta gami da karanto addu'oin barci, banga dalilin ma ɓata lokaci yin tinanin abun ban haushi ba, ko in kalle shi inji me? Ko ya ɗauka nima ina cikin ƴan matan da suke rububinshin ne oha? 🤷🏻‍♀ Washegari ansha bacci, yayin da maree da mahaifiyarka mama talatun baccin su ragagge ne, suna ta saƙa yanda zasu yi su mallaki Al'ameen ɗin, domin suna hango ma kansu rayuwa ta jin daɗi da zasu iya fuskanta nan gaba kaɗan ba da jimawa ba, saidai Abunda ya ƙara ɗugunzuma hankalinau shine ganin da mareen tayi ma Suhan ɗin a motar Al'ameen lokacin da suka dawo, haka ta koma fa tayi ta rusa kuka, da gaske son Al'ameen ɗin ya kamata, yayinda ita kuma mama talatun ba ta wannan take ba, abun duniyar kawai take hange, haka kawai ta shiga ce ma mariyar zauna nan abun duniy ya kashe ki, akan waccen kucakar da na san ko kyauta aka bashi ita ba amsa zai yi ba, kawai dai ita ce da uwar ta ke shisshigi mashi, Amman zanyi ma abun tufkar hanci. Kowa hidima yake yi fafa, gida fa ya kacame, wasu irin garƙama garƙaman tuƙwane ake ɗorawa, bayan abincin da ake yo order ɗinshi daga manyan restourent. Ƴan kankiya sunyi bajinta ta nan fannin, domin duk wata sanwa da za'ayi suna kamawa, yayinda ƴan uwan Hajiya kubra kejin sun wuce nan, kaman su ba zasu iya fitowa yin girkin hidima ba, rarraba ake da abinci kaman ba'a so. Kowa sai shirin yin ƙauyawa yake yi yau, da yake duka amaren yau zasu yi, ko wanne ɓangare shiri akeyi, sai shigowa akeyi da dami damin kara, da su goruba, magarya ɗinta, nan cikin gida kuma an sanya ayi lafiyayyen dambu, da zogala ɗanya, ga lafiyayyar fura da amma da taji lafiyayyen nono da yoghurt da madarar ruwa, abun dai gwanin ban sha'awa. Hajiya Kubra taji haushi wannan event ɗin, saida taga cewa kowa na murna dashi ne sannan ta sake, to muma ta ɓangare namu mun yi murna, saboda yau ne za'a zama ɗaya, da mai ji da kanshi da mara ji da kanshi duk za'a zama ɗaya, matan sunyi shiga irin ta Fulanin usul, musamman suka ɗauko wasu Fulani suka zo sukayi masu kwalliya irin tasu ta filani, an zane masu fuksokinsu ram da kalli baƙi da ɗige ɗige, sai suka ba kansu dariya, kuma suka burge kansu, masalan da suka ji angunan na cewa sunyi kyau. Banso banso nake cewa, Amman a haka saida Hafsat da afnan suka matsa aka yi man saisa saisa, nima kayan Fulanin na sanya sun matuƙar amsa ta, sun yi man cif cif, dama saida Hafsat ɗin ta zaɓo mana saƙi mai kyau harda jikkarsu ta Fulani. A haka kowa ya hallara aka fara event, kasancewar da marece ne, da sauran Haske kuma ga maza a tattare guri guda, ya sanya ni takura, gefe na koma gami da zama bisa wani kututture ƙarƙashin bishiyar gwaba, ina ta kallon su ina dariya, hannuna riƙe da ƴar sandarsu ta Fulani ina wasa da ita. Kwallon su nake tayi, ina tafaman murmusawa, yanda maza ke gatsar rake suna sha suna santi, gefe mata masu ji da kansu su wasu ne, sun dage suna ta gwaguyar goruba duk don su faranta ma amaren rai, gefe wasu gunsu ne suna ta faman afa tambu baka, ga wasu dandalin gefe suna ta faman shan fura cikin ƙorai masu matuƙar kyau da suka sha zanen wuta. Wasu kuma suna zaune gefe wasu kuma a tsaye suna zance da samarin su, kai abun dai kaman a ƙauye, sai abun ya burgeni, hannuna riƙe da taura guda ɗaya ina ta faman jujjuya ta, ina so inci ina jin kunyar ɗimbin maza, abokan anguna da suke ta wajen. "Allah kuwa Friend ina son leƙa wa wurin cen fa, Naji kiɗan mu na gargajiya na tashi fa a wajen, har ma na ƙagara inje," Bilal ne da yake tsaye bisa kan Ya ameen ɗin, shi kuma yana kishingiɗe yana latsa waya yake bashi amsa "To kaje mana, ai ni dama ban hana ka ba, Nidai na gaya maka, hidimar yara ce ba zan shiga ba." Ɗan murmushi yayi, son zuwa wajen na ƙara tsuma shi, "Pls Pls Al'ameen Dont do that to me please i beg u Friend" Ɗan tsaki yaja a hankali yana mai miƙewa "Muje na lura kai in maye ne ya kama mutum sai ya lashe mashi kurwa tas wallahi" "Eah Naji ba komai shege, tinda fa ba kai kayi niyya ba, ai komai ma zaka iya faɗa" Je rawa sukayi suna ci gaba da tafiya, har zuwa tafkeken lambun nasu da ya wadatu da mutane da ɓawon rake da wasu suke gefe suna ta fama n fere bayan suna rage mashi baƙi. Da ƙafar dama Bilal ɗin ya shiga wurin, domin yana saka ƙafa ya hango one of his colique a cikin abokan ango, ya ja area cen gefe yana ta zuƙar zaƙin rake, hannun Al'ameen ɗin yaja suka isa har inda yake zaune bisa wani dutsi shida abokan shi. Ji yai an taɓo shi ta baya, ai waigawar da zai yi sai suka haɗa ido da Bilal ɗin, a sukwabe ya tashi yana ihu, "Wow wa nake gani nan kaman Bilal Musaddiƙ ja?" ya faɗa cikin murna, yanayi yana murza ido da gudan hannun da bai riƙe karan ba. "Nine son Ubanka Mubin, long time not see, ka ɓace ɓat fa baba, ya rayuwa?" y a faɗa yana mai kamo hannun Bilal ɗin. "bikin wa kazo nan?" Wanda aka kira da Mubin ɗinne ke tambayar Bilal, dariya Bilal ɗin yayi gami da cewa "Kai zan tambaya Mubin ai ni nan gidan mu ne, duka amaren ƙannai ma ne, wannan shine Abokina Moh'd Almustapha Dambulan da kuke jin labarin shi" ya faɗa yana mai juyawa gami da nuna Al'ameen ɗin da yake tsaye yana ta faman doka murmushi. Su kansu miƙewa sukayi gami da miƙa ma Al'ameen ɗin hannu suna mai girmamawa, "Nyc to meet you our gallant Yaya" suka faɗa cikin barkwanci, har yanzu basu bar shan ka ransu ba. "Bikin fa Sadeeq Mufti akeyi angon Hafsat, ai mu so mu gayyace ka shi sadeeq ɗin ya hana a cewarshi ayyuka sunyi maka yawa, da wahala ka shigo Nija withing this Period of time" Mubeen ɗin ya faɗa cikin jin daɗin ganin abokin nashi. "Braboo, ai banga ta zama ba, muje ka nuna man shegen surukin namu" ya faɗa yana kamo hannun Al'ameen. Sun gaggaisa sosai, nan suka shiga firar yaushe rabo, shi dai Al'ameen ɗin sai faman murmushi yake, mutane sai zuwa suke gaida shi, da waɗanda suka sanshi a zahiri da waɗanda ma sunanshi kaɗai suke ji, nan da nan fa aka shiga kallon Moh'd Al'ameen ɗin gami da nuna shi, waɗanda ma basu san shi ba yau duk sun sanshi kuma sun ganshi. Duk abubuwan dake faruwa ina zaune gefe ina kallo, nayi mamakin yanda sunan Al'ameen ɗin ya buɗe wajen cikin ɗannƙanƙanin lokaci, koda yake shi ɗin mai yi ne, na matsa ne, domin kafin ka samu matashi kaman shi da yake da kishin matsa da samar masu da ayyukan yi sai ka tona. Wani ƙadangare ne da bansan da tahowa shi ba, ga dukkan alamu ma faɗa suke yi, irin manyan nan ne masu jan kai da bindi. *Jiffff* Ƙarar fadowar ƙadangare ne bisa kaina ya zabura dani daga faman murmushi da nake yi, ƙara na ƙwalla gami da daka tsalle, bai sauka ba ma, sai ƙara maƙalƙaleni a yayi yana neman shige wa cikin riga ta. Wata razananniyar ƙara na kuma saki da saida ta karaɗe illahirin lambun nan baki ɗaya, lokaci guda na saki ajiyar zuciya ina mai sulale wa ƙasa sumammiya. Rige rigen isa inda nake yaushe suka shiga yi, Al'ameen ne, da Bilal sai Hafsat da afnan, tini suka ƙaraso inda nake kwance a sume, Afnan ce ta tallafi kaina tana sakin wani tsumammen kuka, lokacin da ƙadangaren ya sauka daga bisa jikina ya sulale abin shi yanayi yana gyaɗa kai. "ta suma Yaya ta suma ka taimaka mata" Abunda afnan ɗin ke faɗi kenan, daidai lokacin da su Saudat da Nihal suka iso wurin su da tawagar ƙawayen nasu, da sauran angunan nasu. Baiyi wata wata ba ya sun kuce ta, hankalinshi a tashe ya nufi cikin gidan da ita, har yanzu bata ko motsi bata san inda kanta yake ba. Sakin baki sukayi gami da bin shi da kallo, tini ƴan maganganu suka baibaye wurin, wasu na cewa ƙanwar shi ce, wasu na cewa budurwar shi ce. *To koma dai miye ku biyo alƙalamin ~Oum-Deedat~ domin jin yanda zata kaya* ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~25~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Rasa inda zai nufa yayi da ita, daya kalle ta yaga yanda take sake a hannun shi, sai ya ƙara ɗaga ƙafa, sashen shi da yafi kusa da lambun ya nufa da ita kai tsaye. Bai ajiye ta a ko'ina ba sai bisa gadon shi, Bilal Sadeeq Afnan da Hafsat amarya da suke biye dashi, cikin su babu wanda baiyi mamakin shi ba, to saidai shi ɗin ba tasu yake yi ba. Ruwa yace Afnan ta ɗauko masu sanyi, miƙewa yayi daga bisa gadon yace Afnan ɗin ta shafa mata a fuska. Ajiyar zuciya na sauke, jin saukar ruwan a fuska ta, har saida ƙirjina ya ɗaga sosai, ƙoƙarin miƙewa nake yi afnan ɗin ta sanya hannu ta maidani kwance. Lamo nayi ina sauke ajiye zuciya a hankali a hankali, har yanzu jikina rawa yajeyi, tsoro gami da firgici har yanzu bai sake ni ba. A hankali zazzaɓi mai zafi ya lulluɓeni, ganin ina rawar sanyi ne ya sanya ta jawo bargo ta lulluɓeni ruf, ga tashin bargo ga laushi katifa, uwa uba wani daɗaɗɗen ƙamshi da nake shaƙa suka taru suka sanya nayi luf abuna. Juyawa Ya Ameen ɗin yayi gami da fita daga ɗakin, ganin haka ne Sadeeq ɗin da Bilal suka mara mashi baya wajen ficewa su bamu wuri. Afnan ce ta kalli Hafsat gami da cewa "Aunty Hafsat ya kamata ki koma wajen baƙi, kinga ke amarya ce, ba kin baro mutane kizo ki zauna nan ba, gashi ba'a tashi daga event ɗin ba, ga kuma angonki da baƙin shi" Miƙewa hafsat ɗin tayi gami da cewa "bari inje in sallama kowa, ni na tashi hakanan" girgiza mata kai Afnan ɗin tayi, kiyi haƙuri, Aunty Suhan ta samu lafiya, kinga ma bacci take yi, kar kiyi haka, kije nima gani nan zuwa" Hafsat ɗince ta shiga gyaɗa kai, sannan ta juya gami da fita itama, a falo ta taddasu zazzaune ba mai ce a ɗan uwanshi kanzil, gara ma Bilal da yake ta fama latsa waya, ganin fitowar ta ne ya sanya Sadeeq ɗin shima miƙewa yana cewa "ya jikin ta ne?" "Ta samu bacci ne, kasan Suhan da mugun tsoro, ita fa abu kaɗan ma kan firgita ta balle wannan ƙaton ƙadangaren" "Haka ne kam, gaskiya dole ta firgita, Allah ya bata lafiya" binta yayi suka fice tare gami da komawa wajen baƙin nasu. Sun tadda an cigaba da hidima kaman ba Abunda ya faru, baƙin nasu dai ne sai a hankali, ganin yanda amaryar tasu ta firgita ya nuna masu cewa lallai itama ƴar gidan ce, hakan ce ta sanya jikin su yayi sanyi, saida suka ga dawowar su sana suka saki jiki aka yi ta kwasar gara da nishaɗi, su kau dama su Saudat ɗin taɓe baki sukayi, gnai da cewa Allah ya bata lafiya, suka koma wajen ƙawayen su aka cigaba da shagali, domin Suhan ɗin bata kai wadda zasu tashi hankalin su a kanta ba, ko mutuwa tayi balle ta ruguza masu farin cikin da suke ciki. Har aka tashi Afnan bata dawo ba, ita kau Hafsat dama tinda ta koma bata saki jiki ba, ƙawayenta sai bata haƙuri suke yi gami da ban bakin ƙawar tata zata samu lafiya. Cikin hanzari ta nufi sashen na Yayan nasu bayan duk ta sallama baƙi masu komawa, na cikin gidan kuma ta raka su sashen nasu na amare, gami da ɗaukar excuse ɗin cewa zata je ta dawo. Miƙa nayi, salati ɗauke a bakina, sannan na karanto addu'ar tashi daga bacci, wara idanu nayi, gami da saurin yaye bargon da aka lulluɓeni dashi. Nazarin ɗakin na shiga yi, ba ɗakin umma ta bane, ba kuma ɗakin Hafsat bane, ba kuma asibiti bane, to ina ne nan aka kawo ni, har bisa gado harda kuma lulluɓeni? Zumbur nayi na tashi, ina mai ƙoƙarin sauka daga kan gadon, dafe da kaina dake saramun alamun ciwo. Afnan ce ta shigo ɗakin da saurin ta jin alamun motsi, kamfani tayi gami da taimaka man na zauna, ƙafafu a a ƙasa. Bin ɗakin na shiga yi da kallo, ɗakin Ya ameen😳 bisa gadon shi🤭 ni Suhan??? Aikau a sukwane na miƙe har ina harɗewa da zanin gadon da ya maƙale man a ƙafa. "Yi a hankali Aunty Suhan" Abunda afnan ɗin ke cewa kenan "Afnan nan kaman ɗakin Ya Ameen? Wa ya kawo ni nan? Me yasa?" na shiga jero mata tambayoyi a firgice ina mai jiran amsar ta. Ɗan murmushi tayi gami da jan numfashi, "to miye? Ai ya ameen ɗin ne ma da kansa ya ɗauko ki ya kawo ki nan kuma......." Katse mata hanzari nayi daga amso shin da take bani, " me? Ya ɗauko ni fa kika ce? Au shine ma ya ɗauko ni ya kawo ni nan?" na faɗa ina ɗan jinjina kai gaba jiran ƙarin bayani. " To miye ne? Kaji aunty Suhan da wani zance, ke ba ƙanwar sa bace? Kuma ai nan yafi kusa akan cen cikin gida, hankalin mu fa duk ya tashi wallahi, masalan ma shi, mu ai mun ɗauka abun yafi haka, ashe razana ce kawai" Gaba nayi ina mai cewa "ai na warke, wajen umma ta zanje ni" jawo hannuwana ta shiga yi, ki bari su dawo yaje siyo maki maganin zazzaɓi, kar yazo ya tadda baƙya nan inda ya ajiyeki" Girgiza mata kai na shiga yi, kayan kunya iri iri ina shan shi ƴan kwanaki nan, kaji fa wai shine ma ya ɗauko ni da kansa, kaman wata baby, kuma wai kar yazo ya tadda bana nan inda ya ajiye ni, kaman wata kayansa😗 "ya baki ki kawo mani, ina sashen mu" Abunda nace kenan ina mai ficewa daga sashen, kai tsaye ɗakin namu na tura na shiga, umma ta da bata nan kuma bata kulle ɗakin ba, hakan ce ta sanya ni kwanciya dafe da kaina da yake ta sara man kaman zai faɗo. Ɗan murmushi Afnan ɗin tayi, gami da gyara gadon, ta nayi tana zancen zuci, "lallai ya Ameen da gaske yake, kaji fa yanda ya ruɗe, ko mune dai bama lafiya ai iyakar ruɗewa da zai yi kenan" 😉☺ Bilal ne da yake zaune kujerar mai zaman banza, ya kalli abokin nashi gami da muskutawa ya gyara zama. "Abokina it seems fa labari yana neman ya cenza, naga fa ka damu da lamarin yarinyar nan over, wai whats going on ne? Yayi maganar in a serious tone. Ɗan kallon shi Al'ameen yayi yana mai maida hankalin shi kan tuƙi, baya da Abunda zai ce ma Bilal ɗin, ba zai fahimta ba, shi ba zai gane tsabar tausayin da yarinya take bashi ba, halin da suke ciki ita da mahaifiyarta kaɗai abun dubawa ne. "Oh ba ma da amsa ko" ya faɗa cikin son kauda shirun da Al'ameen ɗin yayi mashi. Ya fara ƙule shi da waɗan nan maganganu nashi, ashe shi ba mai bashi goyon baya ne ba kan taimakon da yake son yi. "Idan Kaga kare na shinshinar takalmi...." "ɗauka zai yi" Bilal ɗin ya ƙara sa mashi yana ɗan murmushi. Gefen damtse hannun shi ya kaima bugu, "watau shege tini ka fito kayi man bayanin Abunda ke faruwa ka tsaya sai kwana kwana kake yi, nima ai na fara gundura da zaman naka hakan a babu mashinshiniya, saidai fa kasan ka ɗauko dala ba gammo, ka ɗebo ruwan dafa kanka mutumena, ina tsoron Allah ina tsoron Hajiya, bana son Abunda zai baka matsala, kuma hakan ba yana nuna bana tare da kai bane, aa am 100% with you abokina" Ɗan guntun murmushi na gefen baki Al'ameen ɗin yaja, ga dukkan alamu ya zama al'ada shi. "Tinda haka kake so kaji, na faɗa hankalinka sai ya kwanta, banza magulmaci" Dariya Bilal ɗin ya saki, saida yayi mai isar shi sannan ya tsagaita. "Kana nufin don inji daɗi kenan ka faɗa ba gaskiya bane" "Duk yanda ka ɗauka, naga babu haramci a ciki inma cewa nayi ina so" "ai ba cewa aka yi haramun bane Alhaji, ana so ne dai a nuna maka matsayi ka yafi gaban ace wannan yarinya kake so da aure, shi fa aure ba abun wasa bane, abu ne for life, zama ne na dindindin" "Naji malam bilalu, ai sai ka faɗa man yanda yake tinda kayi kaji yanda yake" ya faɗa cikin ɗaure fuska da gundura da zancen. "Oho dai, ai ko banyi ba ina kan hanya, kuma na fika tinda ina da gurin yi" "Nima ai ina da burin yi ɗin, tinda gashi na samo" Tsoki Bilal ɗin yaja cikinbƙuluwabyake cewa "kai dai Kwallon ɗan iska ne wallahi, ana cewa ga ruwa kana ga wuta" "Eh Naji a barni in faɗa wutar in ƙone ba shikenan ba, kowa ya huta, tsuntsu dayaja ruwa ai shi ruwa kan doka" ya faɗa yana mai ficewa daga motar da tini ya isa gidan. Afnan ya shiga kira a wayar shi, tazo ta amsar mata maganin, tinda shi tinanin shi har yanzu suna sashe nashi, Shiyasa bai shiga ba. Bayan ta amsa ne ma take faɗa mashi cewa ai ta koma ɗaki su, wai ba zata iya zama ba kunya take ji. Bajce komai ba ya nufi sashen nashi Bilal ɗin na biye dashi, "Kudai tabbatar tasha maganin, kinga dare yayi, ciwon daren ake gudu" da to ta amsa mashi tana mai nufar sashen su Suhan ɗin. Umman tawa ma a haka ta tadda ni, ban gaya mata me ya faru ba, illa dai iyaka nace mata kaina ne yake ɗan man ciwo. Sannu tayi man tana cewa hayaniya ce. Saida na sha maganin da Afnan ɗin ta kawo man sannan na kwanta, dama ina fashin sallah ne. Sannu Afnan ɗin tayi man, bayan tayi tayi dani muje cen ɗakin nasu na ƙiya, a haka ta fice tana ƙara man sannu, gami da cewa Hafsat ɗin na gaida ni, baƙi ne sukayi mata yawa. Duk yanda mama talatin taso ta danne gulmar tata abun yaci tura, gani take yi abun na ƙara gaba, ga maree sai tazo ta sanya ta gaba tana ta mata koke koke, idan har taga Al'ameen ɗin da Suhan ɗin, masalan ma yau da kan idon ta Al'ameen ɗin ya sunkuci Suhan ɗin kaman matarshi ko kuma wata ƴar baby, ai ko daƙin nasu bata gama shiga ba ta fasa kuka, ba yanda mama talatun bata yi ba akan tayi shiru ta kasa. Hakan ce ta sanya ta miƙewa ta doshi sashen hajiyar da yake cike da baƙi, a haka ta kutsa har zuwa ɗakin hajiyar. Taci sa'a ba kowa, domin tin isha'i ta shiga ta huta, duk ƴan baran dan nata suna ɗakunan su, balle da yanzu kusan ƙarfe goman dare ne. Ƙwanƙwasawa tayi, daga ciki hajiyar ta buɗe, tana mai cewa "a'a Talatu, kece cikin daren nan, ba mu gama magana ba, ta shirye shirye da za'ayi gobe" "Eah hajiya, ba wannan ce tafe dani ba, labari na kawo maki" dakin ƙofar hajiya tayi gami da juyawa ta isa ga tanƙamemen gadon nata ta zauna. Maida ƙofar mama talatun tayi ta rufe, tana mai bin bayan hajiyar har gaban gadon zan nan ta zube ƙasa, gami da tanƙwashe ƙafafun ta cikin salon koro gulma da munafurci. Ƙarya da gaskiya ta shiga koro ma hajiyar, harda cewa yanzu ma Suhan ɗin har tallar kanta take kaima Al'ameen ɗin har ɗaki shi, ko ɗazu ma da kanshi ya ɗauke ta cikin bainar jama'a ya shiga da ita sashen nashi ya kullo, alamar sun fara cin galaba kenan a kanshi. Salati Hajiya Kubra ta rafka, tana mai miƙewa ta shiga tafa hannuwa, ɗanta? Ɗanta ne ya lalace haka? Yaro ma kaman Al'ameen? Baya san lokacin da ta zari hijabi ba, ta tsallake mama talatun da take durƙushe tana ta fama hakin ƙaryar da ta shirga, ita kanta ta san da gaskiya zata bayyana, babu Abunda zai hana ta barin gidan, don idan kowa ya barta ta sani Al'ameen ba barin ta zai yi ba. Sashen Alhaji ta nufa kai tsaye, yayi mamaki da ya buɗe yaga ita ce, tin kafin yace komai ta fasa kuka, salati ya sanya cikin ruɗewa yake tambayar ta menene? Kuka take fafa, ta ma ƙi ta tsaya ta bashi bayani, waya ya ɗauka gami da kiran Al'ameen ɗin yace ya same shi sashen shi, ga Hajiya na ta kuka taƙi magana. A firgice ya zabura, gami da zura jallabiyar shi, Bilal ɗin na tambayar shi bai tsaya bashi amsa ba, kawai dai yace Alhaji ne ke kiran shi. Ko da ya isa, ya tadda tana kuka, haƙuri shima ya shiga bata, yana cewa tayi masu bayanin me ke faruwa. Ko da ta shiga koro bayani, irin wanda mama talatun ta kai mata gulma, shiru Al'ameen ɗin yayi yana ta faman kallonta, Alhaji ne ya shiga jifan shi da wani irin kallo na tuhuma, shi ya ma kasa buɗe baki balle ya kare kanshi. "Ka bamu kunya Moh'd, ina tarbiyyar da muka baka? Abunda zaka yi mana kenan ka lalata ma ƴar yarinya tarbiyya, me ka nema ka rasa? Mene baka mallaka ba? In ma mata huɗu kace kana so a aura maka, wallahi ina mai tabbatar maka zamu aura maka su, kuma zaka iya riƙe su, me kake nema wajen waccen ƴar tatsitsiyar yarinya? Kucaka ƴar aiki, marar galihu? Wallahi *kafi ƙarfinta* nayi matuƙar baƙin ciki, nayi nadamar sanina dasu a rayuwa, yau ba zasu kwantar mani a gida ba, zasu bar gidan nan koma wace duniya zasu bana da damuwa, domin cece ɗana, domin in ceceka daga halin da kake ƙoƙarin jefa kanka, babu abinda ba zan iya yi ba. Alhaji mustapha da yake tsaye, ya gaza gazgata gaskiya ko akasinta, domin dai ga moh'd ameen zaune Amman ya kasa musantawa ko ƙaryata Abunda mahaifiyar tashi take faɗa da bakin ta, illa iyaka ma dai miƙewa da suka ga yayi ya nufi ƙofar domin fita daga ɗakin. "ka gani ko Alhaji, ka gani ko? Yana aikatawa, ya gama bada kanshi gareta, sunci galaba kanshi, ashirin da suke yayi tasiri kan yaro na, ina gab da rasa shi, Alhaji kayi wani abu" Daf da bakin ƙofa ne suka ga y a yanke jiki ya faɗi, babu alamun rai a tare dashi. Da gudu suka zabura inda yake kwance, rige rigen taɓa shi suka shiga yi, Alhaji ne yayi da dabarar kiran Bilal da abie yace su fidda mota Al'ameen ba lafiya, ita ko mom kuka ta ƙara ruahewa dashi, ba zata juri rasa ɗan nata ba akan wata banza yarinya, saidai ayi ɗaya cikin biyu. Bilal ybatashi a firgice, yaga fa lafiya lau abokin nashi ya bar ɗakin, kuma Alhaji ne ya kira shi, gashi kuma ya sake kira yace baya lafiya, baiyi wata wata ba ya tashi a hanzarce ya zura kayanshi, gami da ɗaukar ma ƙullin mota babba da suke zube kanbstool ɗin falo, ko tsaya kulle sashen baiyi ba ya fice gami da juya mota. Daidai nan Alhaji da Abie suka fito ɗauke dashi babu fa alamun rai a jikin shi, babu ɓata lokaci suka saka shi cikin motar gami da shiga, mai gadi ya wangale gate suka fice cikin matsananci Gud. Shima hankalin shi a tashe ya kulle gidan yana fatan dai lafiya uban ɗakin nasu yake. Wata private hospital da tafi kusa suka kai shi, da gudu nurses suka zo suka tura shi bisa gadon ɗaukar marasa lafiya, har yanzu Hajiya Kuba kwalla take mataewa, shi kau ABBA sai binta da kallo yake yi, duk laifin na kanta ya ɗora shi, baima yadda da Abunda tazo mashi dashi ba tin asali, da ya san wannan shashashar maganar zata kawo mashi da bayyi ma gigin kiran Al'ameen ɗinba. Tin a hanya suka maƙala mashi oxygen, Abunda ya ƙara firgita su kenan, suka sare da Al'amarin, su kau Bilal da abie tambayoyi ne fal a ransu Amman babu wanda zasu yi mawa, basu sare ba saida suka ga ana goga wani abu kaman dutse guda ana man nawa a ƙirjin Al'ameen ɗin, shi kau sai ya yunƙuro kaman zai tashi sai ya koma, duk cikin son samo numfashinshi ne, dukan su ba wanda idanun shi ba suyi ja ba, Abie da har ya fara kuka, Bilal ɗin ya shiga bashi baki, duk da shima zuciyar shi kaman zata fito saboda tsabar ƙuna. Kukan da Hajiya Kubra keyi ne, ya sanya nurses ɗin zagyowa suka ce don Allah a janye ta, suna kan aikin su ne, dole tasanya suka janye ta gami da komawa reception suka zauna Kusan ƙarfe goman dare na farka a firgice, umma ta dake gefe na kwance ce tayi azamar tashi gami da kamo ni, har nayi hanyar fita daga ɗakin, lafiya, ta shiga tambaya ta, ba zance komai ba, mafarki nayi mai ban tsoro, saidai ba zance ga Abunda na gani ba a mafarki, saidai naga fuskar Ya Ameen a ciki, addu'a tayi man gami da maidani ta kwanta. Lamo nayi ina mai sauraren ta tana ta tofa an adduo'i, abun ya dameni, menene nawa na mafarki shi? Kuma fa kaman yana cikin wani hali ne, Allahu a'alamu. Runtse idanun a nayi, Amman fa har yanzu shi nake gani cikin mawuyancin hali ya na miƙo mani hannu alamar in fiddo shi, miƙewa nayi gami da shiga tiolet na ɗauro alwala, gami da zuwa na kabbara sallah, ina addu'ar Allah ya sanya dai lafiya, domin ban taɓa yin irin haka ba Itama umman tawa ganin sallah na tada sai ta rabu dani ta koma ta kwanta, Amman ta kasa runtsawa, tinani take yi me ya samu ɗiyar tata da tin ɗazu ta ganta wani iri, Amman taƙi bayyana mata halin da take ciki. *koma dai miye tana fatan ya kasance lafiya ko kuma yazo da sauƙi* _To sai mu ce dai Ameen Mama Maryam_ ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~26~* Kyautar Page gareki Safiyya, na cika Alƙawari, na baki shi halak malak, ina sonki fiye da yanda kike son littafin nan, Allah ya bar mu tare. 🤝🏻😍 °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, lokaci guda yana mai ƙoƙarin buɗe idanun shi, likita da nurses ɗin dake kanshi duka suka maida dubansu a kanshi, tini fara'a ta bayyana a fuskokin su suka fara cema juna congratulation, sanin shi ɗin wanene da sukayi, da ceto Rayuwar shi da sukayi, taimaka mashi suka cigaba da yi, har numfashinshi ya daidaita, sannan suka ɗan ƙara mashi allurar barci, lamo yayi yana sauraren su har dai nannauyan barci yayi awon gaba dashi. Hajiya Kubra da tini tabar kuka, saidai ajiyar zuciya da take sauke wa, to dama dai Bilal da Abie ɗinne masu lallashi ta, shi kau Alhaji tsabar ɓacin rai da Abunda taja masu ya sanya ko kallon ta ma ya dena yi, ba yanda likitocin ba suyi ba akan su shiga office ɗinsu su zauna, Amman hakan ya gagara. Bilal da yake ta safa da marwa hannuwan shi goye a bayan shi, fuskar nan tashi ba annuri Sam, ya san ba ƙaramar matsala bace yin hakan ga Al'ameen, ya sani duk lokacin da aka faɗa mashi wata magana ne ta ɓacin rai ko mummunan abu ne yakanyi haka tin yarintar su, likitocin cen ƙasar sun sha gargaɗin a dena ɓata mashi rai irin haka, amman dai hajiyar bata ji, tinda zai iya cewa ya lura kaman ita ce sanadi a yanda yaji Alhaji na cewa "hankalin ki ya kwanta, ke har abada ba zaki dena ɗaukar jita jita ba, ba bincike ba komai kin laƙaba ma ɗanki ƙazafin da aka yi mashi, to inaso ki sani, ni ban yadda da Abunda kika zo dashi ba, ba kuma zan yarda ba har abada, ko daga baya kika ƙara tada zancen nan, ko su Maryamar kika yi mawa ban yafe maki ba, kuma wallahi kika yi sanadin da yarona ya mutu sai nayi shari'a dake, tinda Nidai tini nace ƙibar maganar, da yake bakya jin magana kika yi kunnen uwar shegu, su masu kawo maki gulmar ai gashi sun zura ki zaki kashe ɗanki da kanki, in ke kin lamunta ni Sam ba zan iya lamunta ba, dole ne in aka gama bikin nan in yi bincike da kaina, duk wanda na samu da hannu cikin Al'amarin nan zai sha mamaki na wallahi, ashe ni ina cen ina ta yadda zamu samu rufin asiri, ke kina nan kina fama da magulmata munafukai a cikin gida da ma wajen gidan, kin kasa riƙe gida kina cen kina ta zuba mulki da isa, in ma hakan ta faru wanene keda sila? Ai kece tinda saida yace a aura mashi ita, atafau ke kika ce ba haka ba, kin manta ƴaƴan yanzu duk yanda suke maka biyayya, zasu iya bari akan Abunda suke so, kuma hukuncin Allah rubutacce ne" Yana gama faɗar haka ya koma gefe ya zauna, hannayen shi harɗe cikin na juna, sai karkaɗa ƙafa yake yi ƙasa, ita zata iya cewa tinda take duniya ma bata taɓa ganin ɓacin ran Alhaji haka ba, shi mutum ne mai sauƙi, duk da yadda yake tsaye akan al'amarin gidan shi, dawowar Al'ameen ɗinne ma ya samu sauƙi ya janye ya bar mashi wasu al'amurran. Ba tace ƙala ba a lokacin sai faman share kwalla take yi da gefen gyalenta, to me zata ce? Ai kuma yanzu ta lafiyar shi akeyi, amman fa ita tasha alwashin ɗaukar ma abun mataki, ta san mama talatun ba zata yi mata ƙarya ba, gudun kada Alhaji yace bata ji maganar shi ba, zata yi nata binciken itama ta ƙarƙashin ƙasa, ba zata taɓa lamunta yaron nata mai ji da kyau, ilimi, kwarjini, da wadata ya ɓige ga auren maƙasƙanciyar mai aikinsu ba, ɗiyar mai aiki, kai ina ba zata yuwu ba, tasha Alwashin ko dukkan Abunda ta mallaka zai ƙare sai ta raba yaron nata da waccen shegiyar yarinyar, yo shegiya mana, in banda haka duk duniya wanene ya isa ya nuna wani yace ga ubanta? Yarinyar da ko asali bata dashi balle ma uba. Cikin dare misalin uku saura ya farka, lokacin duk an bar su sun shiga ɗakin, shi dai alhajin kujera ya nema ta gefe mai cin mutum ukku ya zauna shi da Abie, ita kau Hajiya kubran kujera taja irin ta silver mai soso da mugun taushi, gefen gadon ta ajiye ta gami da zama ta tura ma yaron nata idanu, ita kanta ta yarda yaron nata ya rame fara ɗaya, a hankali yake sauke numfashi, ya sake yin fari ƙwal kaman ba jini, Amman fuskar tayi jawur kaman an gaggaura mashi maruka, Bilal ma kasa zama yayi ya koma ta gefe guda kusa da kan Al'ameen ɗin yaja ya tsaya, abokin nashi yake kallo da duk ya fita hayyacinshi lokaci guda, kuma ya san duk akan yarinyar nan ne, a yanda ya fahimta Alhajin na ma hajiya magana, in ko haka ne, Soyayya na ɗawainiya da abokin nashi, ba zai yadda bane kawai, ai in har taimako ne ba zaka yarda ka dinga shiga irin waɗan nan haɗarurrukan ba, ba tare da ka sallama wannan taimakon ba. Ganin da sukayi ya farka ne yana neman tashi lokaci guda gami da ƙoƙarin buɗe ido ya sanya Abie rugawa office ɗin likitocin domin ya kira su, ita kau Hajiya miƙewa tayi gami da kamo hannun Ameen ɗin ɗaya mai ɗauke da canula ta riƙe gam tana "Son buɗe idanun ka mune nan wurin da Alhajinka da Abokin ka Bilal🤣, don Allah ka tashi Son karka mutu ka barni". A hankali ya shig buɗe idanun nashi ya wara su akan mahaifiyar tashi, saurin maida idon yayi ya kulle, sai da Bilal ɗin yayi mashi magana ne ya sake buɗe idanun ya ɗora su kan Bilal ɗin da ya zagayo ta ɗaya ɓarin shima gami da ranƙwafowa sosai kusa da Al'ameen ɗin, hannu ya miƙa ma Bilal ɗin a hankali, shima ya kama gami da sakar mashi murmushin ƙarfafa guiwa, Soyayyar abokan guda biyu, abun burgewa ce da ban sha'awa, hakan ba ƙaramin ƙona ran hajiya kubra yayi ba, duk yanda tayi akan yaron nata ya kalle ta yaƙi kallon ta. Alhaji Mustapha da yake gefe cen zaune, yana kallon duk Abunda ke faruwa, hamdala yayi ga Allah, domin ya san dole ne ta fuskanci hakan ga ɗanɗan nata, tinda har zata iya yarda da ƙazafin neman mata da aka laƙaba mashi kuma ta hau ta zauna akai, hakan ce ta sanya sai bai taso ba bai kuma tanka ba, har saida yaga shigowar likita cikin ɗakin. Dudduba shi yayi gami da yi mashi ƴan aune aune, sannan ya ɗaura mashi ruwa gami da tsira Allura cikin ruwan, a hankali baccin ya sake ɗauke shi, to dama dai ya kulle idanun nashi gam, duk da sun san cewa ba bacci yake ba, Amman akwai Abunda ke kai kawo a zuciyar shi da har yake sa baya son kallon su. Jikin Hajiya kubra yayi sanyi matuƙa, gashi da ta kai kallon ta kan Alhaji ya kan auna mata harara har sai ta ji ba daɗi ta janye idon nata, Abie fa har yanzu kanshi a kulle yake saidai da yake shi ɗinma halin shi daban, baya shiga Abunda babu ruwa shi duk da sangartar shi, bakin shi yaja ya kulle gami da kishinhiɗawa kusa da alhajin tinda ance ya samu lafiya daya farfaɗo za'a basu sallama,tini bacci ya kwashe shi shima, tau an sha ƙauyawa day an gaji matuƙa, ga rashin barci, shi kau har yanzu Bilal ya kasa koda zama ne, duk da ƙafafun shi da sukayi matuƙar sanyi, baya jin zai iya zama har sai yaga farkawa Al'ameen ɗin. Har aka yi kiran salla suna nan zugum, ganin za'a tada sallah ne ya sanya Bilal tashin Abie suka nufi masallacin dake cikin asibitin, a daidai lokacin kuma Al'ameen ɗin ya sake farkawa, ganin mahaifiyar tashi a kusa dashi ne ya sashi saurin maida ido ya kulle, magiya ta shiga yi mashi akan ya buɗe idanun koda sau ɗaya ne ya kalle ta, hakan ce ta sanya shi buɗe idanun da suka koma ƴan ƙanana ya shiga kallon ta. Ba zai iya jure kallon nata ba ya maida ya kulle, ganin tinani zai dame shi ne ya sanya shi sake buɗewa gami da tashi zaune sosai, ya zare robar ƙarin ruwan da daf yake da ƙarewa, ya jingina bayanshi jikin bango, gami da jawo ƙafafun shi ya soke kanshi ciki. A haka suka tada su zaune ba mai cewa ƙala, da sauri Bilal ɗin ya isa bisa gadon gami da zama ya kamo hannuwan Al'ameen ɗin duka, shi kau Abie ganin haka sai ya koma zarce wa kiran likita yayin da Alhajin ya ƙara so yana faɗin "son ya ƙarfin jikin? Akwai inda ke maka ciwo?" Ɗago wa yayi yabi Alhajin nashi da kallo, gami da ɗan murmushin ƙarfin hali a fuskar shi, Amman bai ce kanzil ba, likitan ne ya shigo ya sake duddubawa gami da rubuta magunguna ya sallame su, da gargaɗin abar shi ya sake hutawa, kuma a guji tada mashi zancen da aka yi mashi har ya faɗi. Da to suka bishi, inda Abie da Bilal suka kama shi har zuwa cikin mota, a haka suka isa gidan babu mai tankawa kowa da Abunda yake saƙawa cikin ranshi. Har suka isa gidan babu wanda ya fito illa mai gadi da mudi driver, harda muɗi naka kama shi suka isa dashi sashe nashi gami da kwantar dashi suka ja mashi bargo, duk da ba barci yake ji ba, ya sha barci a asibiti hakan baisa ya Musa ba, illa iyaka kwance da yayi yananshaƙar ƙamshin humrar ta da ta bari ɗazu a sama gadon, abubuwa da dama na kai komo a ranshi, shi da yake ɗanɗanta tayi mashi haka ina ga ita baiwar Allah? Ganin ya juya masu baya ne, ya sanya su ficewa, jiki a sanyaye itama Hajiyar ta fita zuwa sashe nata, gami da yin sallah, kwanciya tayi bata so a dameta ne ya sanya ta kashe wayoyinta gami da kulle ɗakin baki ɗaya, shima Abie sashe shi ya koma haka Alhajin ma kwanciya yayi domin ya ɗan samu yayi bacci tin kafin abokan shi su fara isowa. Shima Bilal ɗin raɓawa yayi ya kwanta ta bayan Ameen ɗin gami da jan bargo, bacci yake so yayi, ya sha Alwashin ba zai taɓa tada mashi maganar ba in har ba shine yayi mashi ita ba, tinda likita yace a guji yin hakan, da haka har bacci Ɓarawo ya sace shi. Tin da safe aka fara shigowa ya shanye, da raguna sai kaji da aka kawo mota guda, to dama dai an sallama komai har masu gyara na nan gefe, masu suya kuma basa wahala tinda yau ne daren biki gida ko ina a cike yake, aiki aka hau yi fafa, bayan anyi break fast, dama yau babu wani event da zasu gabatar sai gobe idan an ɗaura aure ne zasuyi dinner, wannan kuma harda iyaye, ko da aka yi ƙoƙarin neman hajiya mama Talatu da Hajiya Laila ne suka hana suka ce tana bacci, su sukayi tsaye wajen komai har Hajiya sa'a ta iso itama suka cigaba da bada command, ita dai Hajiya Zainab da ƴan sashe ta saidai kallo da taimakawa, suma su Goggo Aisha duk sun fito a cewarsu ma ai sune masu tsayawa ayi komai kan idonsu tinda gidan ƙanen su ne, hatta su Goggo Hassana da Hussaina ba'a bar su a baya ba, kowa ta ɗebo zuri'arta kaf zuwa gidan bikin domin Alhaji Mustapha mutum ne na jama'a ba ruwan shi da nuna halin ƙyamar talaka ko mara shi, hakan ce ta sanya kowa ke matuƙar jin daɗin raɓarshi. Umma ta da domin Hajiya Zainab take yi, ganin itama taja baya sai itama bata je wajen aikin naman ba, duk da ba yanda zasuyi da wannan naman don ma dai akwai ma'aikata da aka ɗauko na musamman aka ƙara dasu mama sauden. Tin da nayi salla na koma na kwanta, jikina duk a mace yake na rasa dalili, da safe sai ga Afnan da Hafsat sun zo dubani, Naji sauƙi, na kuma ji daɗi sosai, sune ma suka sanya ni tashi har ma na karya gami da yin wanka, a haka suka janki dole ba don naso ba na bisu sashe nasu na amare, itama dai ummata taji daɗin hakan, domin bata son kwanciyar da nake yawan yi, gashi ta kula jikina a sanyaye, in nazauna nan kuma ba abokin fira saidai inta tinani. Itama wanka tayi ta fice zuwa sashe nasu Hafsat domin ta gani ko da Abunda zata kama. Wata ƴar matashiya yarinya ce tayi sallama ɗakin namu, amsawa mukayi mu duka da muke zazzaune ana ta fama fira da bada labarin event ɗin da aka yi jiya, "Wacece Suhana a cikin ku?" ta faɗa cike da yatsina, nuna ni Hafsat tayi gami da cewa "gata nan lafiya dai ko?" "eh lafiyar kenan, Saudat ce ke kiran ta" tana gama faɗar haka ta juya gami da ficewa. Afnan ce ta miƙe gudun kada a wulaƙanta ni bayan naje, "muje in raka ki" jerawa mukayi har ɗakin nasu gami da sallama, mun taddasu zazzaune bisa gado wasu a sama carpet, sun yi break oast ko ina gaja gaja, wasu ma duk babu kaya jikin su illa na barci ƴan yalolo. "Ɗakin nan zaki gyara mana ki wanke mana toilet yayi datti gashi muna son yin wanka" Saudat ɗin ta faɗa cikin gadara da nuna isa, binsu nashigayi da kallo, su su ɓata don son neman magana Amman nice za'a kira in gyara bayan an dakatar damu daga aikin da mukeyi a cikin gidan? Afnan ce tayi saurin cewa "Amman fa Aunty Saudat an hana suhan aiki a cikin gidan nan, ko dai maree za'a kira maki?" "Ke" ta daka mata muguwar tsawa da har saida na razana, su kau sauran ƙawayen nasu ƙyalƙyalewa sukayi da dariya, wasu na latsa waya wasu ma system ce a gaban su ba Abunda ya sha masu kai. "Je na kira da zaki biyo wa? Ko kin biyo ta ne ki gani in aiki zan sanya ta ki hana ta? Zaman me suke yi mana a cikin gida? In banda son su mallake mana yaya su mallake Abunda ya mallaka? To dole ne ayi mana aiki wallahi ko a tattara a ƙara gaba" ta faɗa cikin matuƙar ɗagawa da karara zance yanda zai shiga har cikin ƙwalwa ta, ya kuwa shiga a sanyaye na kalli afnan ina mai cewa "Afnan bashi kawai zanyi, ki koma ɗaki don Allah" Afnan ɗince ta ƙuta gami da ficewa a hasale ta koma ɗakin nasu, ni kuwa tattare hijab nayi na shiga aiki, wata daga cikin ƙawayen nasu, wadda na kula tana yawan zubda mannhabaicinlomuta da dama in suna falo zaune ce tayi ƴar dariya cikin salo na son cin mutumci ta shiga faɗin "Haba Saudat bari wannan maganar mana, ai yayan namu ya wuce ajin wannan yo in banda ma ke da abunki me zai ci da ƴar aiki irin wannan? Dubeta fa ai in ba don Allah ya sanya tana da ɗaske ba da ba ƙaramar mummuna aka yi nan ba, duk tarin matan da suke sonshi a faɗin garin na Abuja da kewaye ya rasa wadda zai kula sai wannan? " ta ƙarshe tana mai nuna ni da hannu. Shewa suka sany gami da tafawa, ni kuwa zuciya ta zo man iya wuya, saidai bana son tashin hankali ummata ba lafiya ce gareta ba, inko har na tanka abun kanta zai koma, gara a lallaɓa a rabu lafiya duka saura kwana nawa ne a rabun? Girgiza kaina nayi gami da cigaba da aiki, raina na matuƙar ƙuna, Allah sarki Ya Ameen a kammu fa zai gamu da ƙalubale da dama tinda yace yana so ya taimake mu. A haka na kammala masu gami da ficewa daga ɗakin a matuƙar sanyaye, maganganu marasa daɗi dai yau na sha su, a hakan ma wani abun baya faɗuwa, har kwalla saida nayi ta baƙin ciki, Amman Allah ya san damu bai manta damu ba. Ina komawa sashe namu Hafsat ta balbaleni da faɗa wai akan me nayi aikin ban ce mata banayi, ni kau ce mata nayi nayi aikin ne saboda ummata kada abun ya shafe ta, tana jin haka taja baki tayi shiru Amman fa ranta ya gama ɓaci, ita kuwa afnan haƙuri ta bani tana cewa sai ta gaya ma ya Ameen ɗin, nice na hana ta ina mai cewa haba ai ko ba komai su ɗin yayye na ne ba Abunda ba zan iya masu ba, saidai in har basu buƙata ba. Muna cikin haka ne wayata ta ɗauki tsuwwa alamar an mani saƙo, dubawa nayi mamaki fal a fuska ta, Ya Ameen ne ya turo mani saƙo kaman haka _Ya ƙarfin jiki, kin dai sha magani ko?_ Ɗan murmushi na sauke, raina yyai fari ko ba komai dai idan wani ya ƙi ka wani zai soka, duk da su ɗin sun nuna man halin ƙiyayya ga ƴaƴan su nan yana nuna man halin kula. Ban maida mashi da reply ba na share, muka cigaba da fira, wani saƙon ne ya shigo _"kina dai lafiya ko?"_ Wannan karon nima maida mashi nayi da cewa _" Eh yaya ina lafiya, nagode da kulawa"_ Shigowar saƙon nata ne ya sanya shi tashi zaune, dama dai yana son yaji halin da take ciki ne, kada ace mahaifiyar tashi ta koma ta sake yin wani abun kuma. Bilal ɗin dai na kallon shi kanzil bai ce mashi ba, sai faman ɓoye murmushi da yake yi, ajiye wayar tashi yayi gami da shige wa toilet domin yin wanka saboda yanzun kusan ƙarfe sha biyu da rabi lokacin sallar juma'a ya ƙara to. Saida Bilal ɗin yaji alamar ya fara watsa ruwa sannan ne ya ɗauki wayar tashi ya shiga duba saƙonni. Tiryan Tiryan ya shiga bin saƙonnin da suka aike wa juna, saidai shi baicin karo da wani saƙo dake nuna soyayya ba, illa iyaka kulawa da kuma saƙon godiya da ta taɓa aike mashi da daɗewa bayan ya bata waya. Jin alamar fitowa ya sanya shi saurin kashewa ya ajiye, shi dama ya riga ya shirya Al'ameen ɗin yake jira, miskilancin na na na a kai, ya sanya bai tanka ma Bilal ɗin ba har ya gama shiryawa, saidai yana kula da Bilal ɗin da irin kallon da yake bin shi, basarwa yayi yana faɗin zaka ci ubanka ne ai. Daidai parking lot muka haɗu dasu, tin daga nesa na hango su, hakan ce ta sanya ni ƙara ɗaga ƙafa, afnan ce taja ta tsaya tana cewa Laa ga yaya bari yazo mu gaisa tin jiya rabona dashi, Ganin Hafsat ɗinma ta tsaya dole nima naja na tsaya. Cikin tafiyar shi ta ingarma namiji suka ƙaraso gare mu, afnan bata yi wata wata ba ta rungume shi tana faɗin oyoyo yaya, shima rungume ta yayi kaɗan yana mai janye ta daga jikin shi ya shafi gefen fuskar ta "Ya kike sweet Heart? Ya faɗa cikin kulawa hannuwan shi cikin nata," Lafiya Lau Bro love" Mu kau ganin hankalin shi na ga Afnan ɗin sai muka shiga gaida Bilal, Bilal ɗin da ya kafe ni da ido ne ya amsa mana, duk hankalin shi na a kaina, har saida na tsargu na duƙar da kaina, Hafsat ce na ji tana gaida Ya Ameen ɗin shi kuma ya amsa mata cikin kulawa, ɗago kaina nayi da niyyar gaida shi idanun mu suka sarƙe cikin na juna, wani irin shirk ne Naji ya jani kaman an jona man wutar lantarki, yayi kyau cikin dakakkiyar shadda shi ruwan sarari samaniya, hula da takalmin dake kanshi duk kalar shadda ne, saidai hannun shi dake ɗaure da haɗaddiyar agogo ƙirar kamfani gucci riƙe yake da makullan mota, fuskar nan tayi fayau da ita, sai ƙasumbar da take kwance a haɓarshi ce ta ba fuskar damar ƙara haske idanun shi manne ikin fari tar ɗin glass da ya ƙara fiddo da kyaun fuskar tashi. Saurin sadda kaina nayin ƙasa ina mai matse ƴan yatsu na, domin wani abu Naji ya tsira mani tin daga kai har tafin ƙafa ta, "Ba gaisuwa?" Naji ya faɗa, saurin ɗaga kaina nayi gami da kallon shi ina addu'ar dai ace ba dani yake ba. Idanuwan shi kuwa fes a kaina, "Ina yini" na faɗa ina mai son kauda kaina ga barin kallon shi, ji nake yi duk ya cika gidan, irin Abunda nake fuskanta kenan a duk lokacin da zan ɗora idona a kanshi. "Ba zan amsa ba, tinda saida na roƙa" ya faɗa yana mai zagaye mu ya wuce zuwa ga motar shi, da tini Bilal ya isa yana jiran shi, da kallo na bishi har ya wuce, lallai ya Ameen ya haɗu ta ko ina, cikakken namiji ne mai tarin kwarjini.... Ɗan ɓangazata Afnan tayi da kafaɗa ganin yanda nabi yayan nata da kallo tana murmushi cikin zaulaya take cewa "Lallai Aunty Suhan yayan nawa yana yin ki, ga dukkan alamu kema kina yin shi na gani" Ɗan firgigit na dawo hayyaci na daga da tinanin da na tafi na wucin gadi, buɗe baki nayi da da niyyar cewa wani abu muka ji cikin kakkausar murya daga bayan mu ance *Al'ameen* Dukanmu juyawa mukayi gami da maida hankalin mu wurin Hajiya Kubra da take tsaye tin ɗazu tana nazarin mu ta fara tako wa a hankali cikin isa da taƙama fuskar ta tam babu fara'a ko alama a fuskar Sanye take cikin wata haɗaɗɗiyar atamfa anyi mata ɗinkin nan mai A shape marar breast cup, sai ɗan kunne da sarƙar gold gami da abun hannun su danƙara danƙara sai walwali takeyi. Tini jikina ya fara ɓari naja baya a sukwane, ni da Al' ameen kawai na lura take kallo, Al'ameen wanda har ya sanya key zai buɗe mota ya fasa gami da dawowa inda taja burki ta tsaya gami da cewa "Gani mom Lafiya dai ko?" Ya faɗa yana mai kafe ta da idanu, cikin fushi ta buɗe baki gami da cewa........ 😛😝😜🤪😜🤪😛😝🤪😜😛😝 ~ku tara a Page na gaba~ ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~27~* *Page ɗinki ne Aishatu Babayo, muna matuƙar yinki, kuma muna jin daɗin comment ɗinki matuƙa, ɗaukacin ƴan golden pen suna gaisheki* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° "Kasha maganin ka ne da kake ƙoƙarin fita?" Mom ɗin tashi ta faɗa, har yanzu fuskar ta a matuƙar ɗaure take. Gyaɗa mata kai kawai yayi, ba tare da ya tanka mata ba, kallon ta ta maida kan Bilal da yake tsaye ta bayan Al'ameen kaɗan haka, yana gaida ta. Amsawa tayi gami da cewa" Bilal ka kula fa da abokin ka sosai, kada ka bari ya wahala Kaga dai Abunda Dr. Yace". Ɗaga mata kai Bilal ɗin ya shiga yi yana cewa "consider it done Mom" Hafsat na tsinkayi muryar ta tana gaida ta, hakan ce tasa nima na gaishe ta, gaisuwar Hafsat ɗin kawai ta amsa, itama a daƙile, hakan ce ta sanya na ƙara shan jinin jikina gami da ƙara ɗan matsawa baya. Afnan ce ta ruga kusa da yayan nata, daidai lokacin da Mom ɗin ta juya da niyyar barin wurin, maganar Afnan ɗince ta dakatar da ita da barin wurin da take niyyar yi. "Yaya me ya same ka? Baka lafiya ne? Yaushe kaje hospital bamu sani ba? Duk ta jero mashi tambayoyi tana mai kamo hannuwan shi gami da dudduba jikin shi da idanu. Ɗan zare hannun shi yayi yana mai shafo gefen fuskar ta kaɗan," Am OK Dear Love, ba Abunda ke damuna" ya faɗa yana mai juyawa ya nufi jikin motar tashi, domin ya kula sosai da rashin amsa gaisuwar da mahaifiyarshi tayi ma Suhan ɗin. Bai jira komai ba ya buɗe motar gami da shiga, shima Bilal ɗin shiga yayi, ganin haka ne Hafsat ɗin ta shiga jan hannuna tana cewa "zo muje Suhan, Afnan ɗin zata tadda mu" Binta na shiga yi, muka shiga tafiya, daidai lokacin da Mom ɗin ta bimu da kallon tsana da jin haushi ƙarara a fuskar ta. Afnan ce ta bita da kallo daidai lokacin da ta juya da niyyar wucewa sashe kaka zuwaira, girgiza kanta ta shiga yi tana mai ɗaga ma yayan nata hannu har ya fice daga gidan. Bayan an sauko masallacin ne kiran Alhaji Mustapha ya shiga wayar tashi, umurtar shi yayi da yazo gidan gonarshi yana son ganinshi yanzu shi da Bilal ɗin. Sai da ya ɗauki hanyar gidan gonar ne, yake sheda ma Bilal ɗin kiran da dad ɗin nashi keyi masu. Har suka isa babu mai tanka ma wani. Sun tadda falon cike da manyan mutane, sai firar su suke cikin nishaɗi, ga sanyin Ac na ratsa su, wucewa sukayi cen gefe gami da zama ƙasa domin girmamawa ga iyayen nasu. Miƙa mashi wata kyakkyawar emvelop mai ado da ruwan gold dad ɗin yayi yana mai cewa duba nan ka gani. Amsa yayi cikin girmamawa ya shiga dubawa, bayan ya gama karantawa ne ya miƙa ma Bilal ɗin, ya maida duban shi kan mahaifin nashi yana mai neman ƙarin bayani. Dad ya gyara zama gami da duban yaron nashi cikin soyayya, farin ciki fal a kan fuskar shi, sannan ya cigaba da cewa"Daga sarkin Katsina ne, haɗin guiwa da sauran sarakunan yankin namu na arewa, saboda yanda kake taimakon matasa ƴan uwanka da basu ayyukan yi, da taimaka masu da jari, da koya masu sana'oi, suka ga ya dace su girmama ka domin suma sauran matasan masu hannu da shuni suyi koyi da kai, sun yanke shawarar naɗa ka sarautar *yariman matasan arewa* kuma suna buƙatar daga yau zuwa gobe ka shirya komai domin a goben ne zasuyi maka naɗin bayan kammala ɗaurin aure, sannan kuma akwai hawan daba bayan kammala lunching ƙarfe biyar na yamma, da fatan zaku je ku shisshirya komai da ake da buƙata, sannan inaso ka aika manyan motoci guda biyu Katsina da zasu kwaso iyayen matar Aleeyu tin da safe su juyo dasu ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~27~* *Page ɗinki ne Aishatu Babayo, muna matuƙar yinki, kuma muna jin daɗin comment ɗinki matuƙa, ɗaukacin ƴan golden pen suna gaisheki* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° "Kasha maganin ka ne da kake ƙoƙarin fita?" Mom ɗin tashi ta faɗa, har yanzu fuskar ta a matuƙar ɗaure take. Gyaɗa mata kai kawai yayi, ba tare da ya tanka mata ba, kallon ta ta maida kan Bilal da yake tsaye ta bayan Al'ameen kaɗan haka, yana gaida ta. Amsawa tayi gami da cewa" Bilal ka kula fa da abokin ka sosai, kada ka bari ya wahala Kaga dai Abunda Dr. Yace". Ɗaga mata kai Bilal ɗin ya shiga yi yana cewa "consider it done Mom" Hafsat na tsinkayi muryar ta tana gaida ta, hakan ce tasa nima na gaishe ta, gaisuwar Hafsat ɗin kawai ta amsa, itama a daƙile, hakan ce ta sanya na ƙara shan jinin jikina gami da ƙara ɗan matsawa baya. Afnan ce ta ruga kusa da yayan nata, daidai lokacin da Mom ɗin ta juya da niyyar barin wurin, maganar Afnan ɗince ta dakatar da ita da barin wurin da take niyyar yi. "Yaya me ya same ka? Baka lafiya ne? Yaushe kaje hospital bamu sani ba? Duk ta jero mashi tambayoyi tana mai kamo hannuwan shi gami da dudduba jikin shi da idanu. Ɗan zare hannun shi yayi yana mai shafo gefen fuskar ta kaɗan," Am OK Dear Love, ba Abunda ke damuna" ya faɗa yana mai juyawa ya nufi jikin motar tashi, domin ya kula sosai da rashin amsa gaisuwar da mahaifiyarshi tayi ma Suhan ɗin. Bai jira komai ba ya buɗe motar gami da shiga, shima Bilal ɗin shiga yayi, ganin haka ne Hafsat ɗin ta shiga jan hannuna tana cewa "zo muje Suhan, Afnan ɗin zata tadda mu" Binta na shiga yi, muka shiga tafiya, daidai lokacin da Mom ɗin ta bimu da kallon tsana da jin haushi ƙarara a fuskar ta. Afnan ce ta bita da kallo daidai lokacin da ta juya da niyyar wucewa sashe kaka zuwaira, girgiza kanta ta shiga yi tana mai ɗaga ma yayan nata hannu har ya fice daga gidan. Bayan an sauko masallacin ne kiran Alhaji Mustapha ya shiga wayar tashi, umurtar shi yayi da yazo gidan gonarshi yana son ganinshi yanzu shi da Bilal ɗin. Sai da ya ɗauki hanyar gidan gonar ne, yake sheda ma Bilal ɗin kiran da dad ɗin nashi keyi masu. Har suka isa babu mai tanka ma wani. Sun tadda falon cike da manyan mutane, sai firar su suke cikin nishaɗi, ga sanyin Ac na ratsa su, wucewa sukayi cen gefe gami da zama ƙasa domin girmamawa ga iyayen nasu. Miƙa mashi wata kyakkyawar emvelop mai ado da ruwan gold dad ɗin yayi yana mai cewa duba nan ka gani. Amsa yayi cikin girmamawa ya shiga dubawa, bayan ya gama karantawa ne ya miƙa ma Bilal ɗin, ya maida duban shi kan mahaifin nashi yana mai neman ƙarin bayani. Dad ya gyara zama gami da duban yaron nashi cikin soyayya, farin ciki fal a kan fuskar shi, "Daga sarkin Katsina ne, haɗin guiwa da sauran sarakunan yankin namu na arewa ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~27~* *Page ɗinki ne Aishatu Babayo, muna matuƙar yinki, kuma muna jin daɗin comment ɗinki matuƙa, ɗaukacin ƴan golden pen suna gaisheki* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° "Kasha maganin ka ne da kake ƙoƙarin fita?" Mom ɗin tashi ta faɗa, har yanzu fuskar ta a matuƙar ɗaure take. Gyaɗa mata kai kawai yayi, ba tare da ya tanka mata ba, kallon ta ta maida kan Bilal da yake tsaye ta bayan Al'ameen kaɗan haka, yana gaida ta. Amsawa tayi gami da cewa" Bilal ka kula fa da abokin ka sosai, kada ka bari ya wahala Kaga dai Abunda Dr. Yace". Ɗaga mata kai Bilal ɗin ya shiga yi yana cewa "consider it done Mom" Hafsat na tsinkayi muryar ta tana gaida ta, hakan ce tasa nima na gaishe ta, gaisuwar Hafsat ɗin kawai ta amsa, itama a daƙile, hakan ce ta sanya na ƙara shan jinin jikina gami da ƙara ɗan matsawa baya. Afnan ce ta ruga kusa da yayan nata, daidai lokacin da Mom ɗin ta juya da niyyar barin wurin, maganar Afnan ɗince ta dakatar da ita da barin wurin da take niyyar yi. "Yaya me ya same ka? Baka lafiya ne? Yaushe kaje hospital bamu sani ba? Duk ta jero mashi tambayoyi tana mai kamo hannuwan shi gami da dudduba jikin shi da idanu. Ɗan zare hannun shi yayi yana mai shafo gefen fuskar ta kaɗan," Am OK Dear Love, ba Abunda ke damuna" ya faɗa yana mai juyawa ya nufi jikin motar tashi, domin ya kula sosai da rashin amsa gaisuwar da mahaifiyarshi tayi ma Suhan ɗin. Bai jira komai ba ya buɗe motar gami da shiga, shima Bilal ɗin shiga yayi, ganin haka ne Hafsat ɗin ta shiga jan hannuna tana cewa "zo muje Suhan, Afnan ɗin zata tadda mu" Binta na shiga yi, muka shiga tafiya, daidai lokacin da Mom ɗin ta bimu da kallon tsana da jin haushi ƙarara a fuskar ta. Afnan ce ta bita da kallo daidai lokacin da ta juya da niyyar wucewa sashe kaka zuwaira, girgiza kanta ta shiga yi tana mai ɗaga ma yayan nata hannu har ya fice daga gidan. Bayan an sauko masallacin ne kiran Alhaji Mustapha ya shiga wayar tashi, umurtar shi yayi da yazo gidan gonarshi yana son ganinshi yanzu shi da Bilal ɗin. Sai da ya ɗauki hanyar gidan gonar ne, yake sheda ma Bilal ɗin kiran da dad ɗin nashi keyi masu. Har suka isa babu mai tanka ma wani. Sun tadda falon cike da manyan mutane, sai firar su suke cikin nishaɗi, ga sanyin Ac na ratsa su, wucewa sukayi cen gefe gami da zama ƙasa domin girmamawa ga iyayen nasu. Miƙa mashi wata kyakkyawar emvelop mai ado da ruwan gold dad ɗin yayi yana mai cewa duba nan ka gani. Amsa yayi cikin girmamawa ya shiga dubawa, bayan ya gama karantawa ne ya miƙa ma Bilal ɗin, ya maida duban shi kan mahaifin nashi yana mai neman ƙarin bayani. Dad ya gyara zama gami da duban yaron nashi cikin soyayya, farin ciki fal a kan fuskar shi, sannan ya cigaba da cewa"Daga sarkin Katsina ne, haɗin guiwa da sauran sarakunan yankin namu na arewa, saboda yanda kake taimakon matasa ƴan uwanka da basu ayyukan yi, da taimaka masu da jari, da koya masu sana'oi, suka ga ya dace su girmama ka domin suma sauran matasan masu hannu da shuni suyi koyi da kai, sun yanke shawarar naɗa ka sarautar *yariman matasan arewa* kuma suna buƙatar daga yau zuwa gobe ka shirya komai domin a goben ne zasuyi maka naɗin bayan kammala ɗaurin aure, sannan kuma akwai hawan daba bayan kammala lunching ƙarfe biyar na yamma, da fatan zaku je ku shisshirya komai da ake da buƙata, sannan inaso ka aika manyan motoci guda biyu Katsina da zasu kwaso iyayen matar Aleeyu tin da safe idan Allah ya kai mana ranmu sai su juyo dasu, sannan ina so ka tabbatar da cewa an gama tsara komai na wurin da za'ayi lunching ɗin, akwai manyan mutane da zasu halarta harda shugaban ƙasa da sarkin musulmai, sannan muna da baƙi da zasu fara isowa a yau ɗinnan muna so a kama hotel mai kyau da zasu ji daɗin zama saboda mutanen waje ne" Ya faɗa yana nazarin yaran nashi guda biyu da suke durƙushe gaban shi. Fara'ar dake fuskar Bilal zamu iya cewa ma tafi ta kan fuskar Ya Ameen ɗin, wannan ai wata ɗauka ka ce da Allah yayi ma abokin nashi, ko ba komai dai ya san ayyukan Alkhairin da abokin nashi keyi ya zaga dukkan sassan nigeria ba ma arewa kaɗai ba. Cikin matuƙar jin daɗi suka shiga yin godiya basu fita ba saida dad ɗin nasu ya sallame su, shi fa Al'ameen mamaki kawai yake yi, a ina manyan ƙasar nasu suka san da duk abubuwan da yake yi, bai ƙara sarewa ba saida yaji ana sanarwar naɗin nashi da za'ayi a gobe idan Allah ya kai mu, a hanyar su ta komawa gida. Sun isa gidan ne, sannan suka kira mudi driver gami da bashi makullin gare jin nasu dake cen gefen gidan gami da umurtar shi da ya fiddo manyan mitocin nan ƙirar homa bomber ya bada a wanke su ɗauki hanyar Katsinan a yanzu nan. Ficewa suka sake yi daga gidan, saboda gidan ya ƙara ɗinkewa da jama'a ta ko'ina duk mata ne ga wasu manya manyan canofee da ake ta kakkafawa a harabar gidan gefe guda kuma wasu manyan speakers ne aka kakkafa kaman za'a tashi gidan. "yanzu ina muka dosa ne? Ni fa wallahi duk ma na rasa ta ina zamu fara, kayan da nayi niyyar Sanyawa yanzu dole in cenza su in nemi masu babbar riga, duk yanda kuwa nake gudun ta saboda zafin nan da akeyi" Al'ameen ya faɗa yana mai kallon Bilal ɗin da hankalin shi yake kan tuƙin da yake yi. "Ni na san ta ina zamu fara, kai dai kayi kallo kawai" ya faɗa da ƴar Fara'ar shi, mamakin abun har yanzu bai gama sakinsu ba. Da kallo ya shiga binnhanyar da suke bi har kawo lokacin da sukayi parking daidai wani tanƙamemen shago an rubuta *Your Choice* a jiki. Je rawa sukayi har cikin shagon da aka ƙawata shi da farin glassai suna ta ɗaukar idanu. Kaya ne maƙilbiya kallon ka, shaddoji ne ƴan ubansu an masu ɗinku a irin na manya, sun sha aiki matuƙa, kowacce tare da hula tangaras kalar zaren aikin shaddar, gefe guda kuma ƙananan kaya ne iya kallon ka da hange ka, yayin da sashe guda na shagon kuma bugaggun takalma ne kalar na sarakai da manyan masu kuɗi. Miƙewa mai shagon yayi gami da tarar su cikin farin ciki, domin ya daɗe da sanin Al'ameen ɗin tin ba yanzu ba, hasali ma Al'ameen ɗin shine ya fara bashi jari a rayuwar shi, bayan ya gama makarantar design da Al'ameen ɗin ya buɗe tin yana ƙasar america. Gaishesu ya shiga yi cikin girmamawa, basu ɓata lokaci ba Bilal ɗin ya faɗa mashi me yake tafe dasu, da taimakon shi suka zaɓi kayan da suke so. Shaddoji ne farare ƙal suka ɗ auka, duk da cewa ta Al'ameen tafi haɗuwa, sai ƙamshi take yi da walwali, anyi mata aiki da riyal blue ɗin zare, yayin da hular ma take kalar royal blue ɗin, sai takalmin shi irin na sarauta mai half cover da lanƙwasa ya sha adon farare duwatsu sai ɗaukar idanu yake yi. Shima Bilal ɗin ya zaɓi masu kyau, saidai shi kuma kalar nashi farar shadda ce da aikin Brown, hakan ne ya sanya shi ɗaukar takalmi Brown masu matuƙar kyau da tsari, sai Abie da suka ɗaukar ma kalar sararin samaniya da aikin bula mai ruwan omo. Sashen masu haɗewa aka miƙa kayan, daidai jikin su aka auna sannan aka haɗe, Al'ameen ɗinne mai cewa a maida mashi babbar rigar fitted yayin da Bilal ɗin ke cewa a ƙyale shi ayi mashi yanda zata yi kyau. Su sha mamaki matuƙa lokacin da suka zo biyan kuɗin yace ba zai amsa ba, ba yanda ba suyi ba yace Sam Allah ya sauwaƙe ya amshi kuɗin su, ganin ba zasu yarda ba ya sanya shi faɗin bari ya gaya masu dalilin shi na ƙin amsar kuɗin nasu. Tiryan Tiryan ya basu labarin Alkhairin da Al'ameen ɗin yayi mashi, sannan ya ƙara da faɗin "Haba yallaɓai, ni wane irin butulu ne kuwa da har zan iya amsar kuɗin kaya a hannun ka? Bayan dukkan shagon nan da yanda na zama a rayuwa kai ne sila, yanzu haka ƙanena yana aiki a kamfanin ka na sarrafa hatsi a Lagos, dama ban daɗe da gama sauraren radio ba, Naji irin gagarumin naɗin da za'ayi maka a goben idan Allah ya kai mu, bansan zaka zo ba i da har gida zan kawo maka da kaina, Amman ko yanzu bata ɓaci ba, insha Allah kuwa zan halarta harda iyali na baki ɗaya, Mungode Mungode Allah ya shirya maka zuri'abyasa ka gama da iyayen ka lafiya" Ko ba komai wannan kaɗai ya isa ya ƙara sanya shi farin ciki, ashe dai shi alkhairi ko ya yake baya da kaɗan kuma daɗi ke gareshi, gashi Alkhairin da yayi ma mata san a lokacin da aka yaye su, har shi ya girbi abinda ya shuka. Sun mashi godiya matuƙa, yayin da Al'ameen ɗin ya bashi ƙaton shi, gami da cewa bayan hidima ta kwaranye ya neme shi su sake gaisa wa sosai, har bakin motar su ya raka su, yana mai ɗaga masu hannu har suka fice daga plazar, sannan ya juya da maɗaukakin farin ciki, dama tini ya daɗe yana addu' ar Allah ya haɗa shi da Al'ameen ɗin ko a hanya ne ya ƙara mashi godiya, domin ya san ba lallai bane in ya neme shi ya same shi. Daganan suka zarce kasuwa, inda suka shiga neman kayan kwalliyar doki, da ƙyar suka samu, domin har Al'ameen ya gaji har ya fara faɗin su koma gida hakanan shi fa ya fara gajiya da wannan wahalar sannan suna da sauran ayyukan da zasu aiwatar da yawa kafin zuwan daren. Kalar kayansu kowa ya ɗauka, sun kwaso kayan kwalliya doki sosai, bayan da Bilal ɗin ya tambayi abokin nashi dokin da zai hau, "Farar Goɗiyar" ya bashi amsa a taƙaice cikin gajiyawa. Ɗan murmushi yayi shi kuma yana faɗin "sai in hau gwaska ni, shi kuma Abie ya hau kule" Bai tanka mashi ba har suka iso gidan, Barde mai tsaron barar suka kira gami da bashi kayan dokin suna faɗin ya shirya su goben bayan gama cin abincin ɗaurin auren, sannan suka faɗa mashi dawaman da zasuyi amfani dasu a cikin dawakan dake gidan. Saida suka ajiye kayan sannan suka watsa ruwa gami da cenza kayan jikin su zuwa ƙananan kaya sannan suka fice daga cikin gidan bayan sun ajiye motar suka cenza wata. Ganin yau bamu da aikin komai, ya sanya mu kwanciya muka huta bayan mun ware duk Abunda muka san zamuyi amfani dashi gobe, to bamu da yawa dama, mu bakwai ne harda amaryar sai mai kwalliyar mu da suka taho ta ita tinda ga Katsinan yasa muka kama mu takwas, ɗaki ne tanƙameme da toilet, bamu takura ba sosai komai namu tsaf yake, kaka zuwaira kaɗai muka fita muka gaida yau sai hafsat ɗin da taje Sashen mamanta, cen ta tadda ummata har take tambayar ta ina ina? Take ce mata ina ɗaki lafiya ta lau. Washegari tin da asubar fari aka farka kusan ince dukka gidan, bayan gama sallah ne aka shiga ɗora Abunda za'a karya, tinda dugu-dugu aka yi break fast, sai kuma aka shiga hidima wanka, masu girka abinci nayi masu sake shirya harabar gida inda za'ayi zaman cin abinci nayi. Mu dai bamu tashi ba sai wajen ƙarfe takwas na safe, mun tadda an kawo mana kayan karin mu, hakan yasa saida muka gama wanka duka sannan muka zauna zaman karyawa, amarya aka fara shirya mawa, mai kwalliya ta hau aikin ta na cakare amaryar, yayi da muku a muka hau gyara ɗakin namu tsaf. Tin da aka fara hidimar biki banga afnan ɗin taje sashen nasu ba, Sam ta fita harkar su kaman ba ƴan uwanta ba, koda yake hali ya bambanta Shiyasa basa shiri, Amman da yake halin na Saudat da Nihal ɗin ɗaya ne gashi nan kansu a haɗe yake kaman ƴan biyu, saidai wani lokacin aunty Feena kan aiko mata da Nasreem da Ayan masalan ma in tana wata hidimar da yake ita a ɗaki ta ta sauka da yake cikin babban sashen gidan inda aka sauki ƴan uwa Hajiya Kubran. Dama tini ta maido kayan ta kaf da ta san zata yi amfani dasu cikin hidimar bikin. Mun gama gyaran kenan muna hutawa wata ƴar matashiya budurwa tayi sallama, yaran dangin hajiya kubran ne, da suke cike da jiji da kai da tinƙahon su ɗin wasu ne, babu wanda ta gaida ta shiga faɗin "wacece suhan wai? To taje Aunty Saudat na kiranta a ɗakin nasu" tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta tsaya jin me za'a faɗa ba. Tinawa da wulaƙanci da sukayi mani shekaranjiya ne ya sanya ni zamana ba tare da na raya ma raina zuwa ba, har aka gama ma Hafsat ɗin kwalliyarta aka fara ma Afnan da tace lallai sai an fara yi mani ai ina gaba da ita, kuma nice babbar ƙawa, daƙyal dai ta haƙura aka fara mata, ganin yanda nakafe sai an gama mata sannan za'ayi mani. Ba sallama saidai muka ganta tsulum cikin ɗakin. Da matuƙar fushi ta maida kallon ta a kaina, bayan tabo kowa dake cikin ɗakin da kallon baku isa ba. "Dame kike taƙama ne da har zamu sanya a kira ki kiƙi zuwa? Ta jefo man tambaya, Afnan ce riƙe da ƙugu ba'i na cin ta cikin zuciya, ko kallon inda take banyi ba, haka in bangon dake ɗakin ya tanka mata tau nima na tanka mata. Hakan yayi bala'i ƙona mata rai kuwa, cikin hasala tace "Aikin mu anan gidan shine aikin ki, kuma a ƙarƙashin Alfarmar Ya Ameen kuke zaune acikin gidan nan, sannan ina so ne in faɗa maki cewa ke baki kai matsayi da har mu zamu ce ga Abunda mukeso kiyi mana ba ki ƙiya, kuma ba zaki taɓa kai matsayi ba, kwaɗayayyun banza da wofi, ke da waccen sululu kasa ɗin uwar taki..... " *" Aunty Nihal ya isa"* *"Ya Isa Hakanan, in ba haka ba wallahi zanje na faɗa ma Ya Ameen ɗin"* Afnan ce take dakatar da ita cikin ƴar tsawa, ranta in ya kai dubu tau ya ɓaci, bata ma san ta ƙwace fuskar taba daga kwalliyar da akeyi mata, ni kau tini fuska ta ta jiƙe da ruwan hawaye, ji nake kaman ƙjrji na zai tsage zuciya ta ta fito. Wannan cin fuska yayi yawa, gaban ƙawayen Hafsat da basu san ko ni ɗin wacece ba ta biyo ni nan tana ƙasƙantar dani, tini na ruahe da kuka mai sauti, domin ina jin in har banyi ba zuciya ta zata iya bugawa, Hafsat ɗince ta ƙara so wajen da nake zaune bisa gado bansan lokacin da na tashi zaunen ba. Bubbuga baya na ta shiga yi, ganin haka ne ya sanya ni rungume ta, Allah ma yaso bata kai ga sanya kaya ta ba, da tini zan cukuikuye su, iri. Daƙumar da nayi mata. Ita kau Nihal jin hakan da tayi ya sanya ta ficewa tana mai saukin maganganu masu zafi a kaina da umma ta, Afnan ɗince ta miƙe gami da ƙarasowa inda nake ta shiga bani haƙuri, gami da cewa "Bari inzo, ai sai na faɗa ma Yayan tinda su dai basa son zaman lafiya" Nice na riƙo hannun ta ina mai girgiza mata kai cikin kuka, fasawa tayi gami da shiga lallashi na, daƙyar suka samu nayi shiru, babu wanda bai tausaya man ba a cikin ɗakin Allah wadai suka shiga yi ma Nihal ɗin Afnan na jinsu ƙala bata ce ba, to me zata ce ai halinka shi ake faɗi ko bayan ba ranka kuwa. Manyan kuloli ne aka shiga shigowa dasu cikin gidan, rumfa guda aka ware da aka jejjera abinciccikan, sai ma'aikata masu serving da aka zube saidai Abunda mutum yake da buƙata a kai mashi, babu kalar nau'ikan abincin da babu acikin gidan nan, har ma da na gargajiya ga masu buƙata, kama daga su Alkubua, fankaso, waina, dambun shinkafa lafiyayye da ya sha zkgala da kayan lambu, to dama dai kowa ya san Katsina wa da wannan cimaka kuma bikin nasu ne, wannan ce ta sanya basu yada al'adar tasu ba. Kaman yanda aka jejjera abinci cika da lemuka kala kala, haka ma acen tanƙameme hall ɗin da yake mallakin Alhaji Mustapha inda za'ayi walimar cin abincin aka har haɗa komai da taimakon su Al'ameen ɗin da Bilal, basu bar wurin ba hr saida suka ga komai ya kammala, kuma an ware ma manya iyayen ƙasa nasu ɓangaren ta inda babu ma mai ganin su, sannan suka wuce gidan domin shiryawa Ƙarfe ɗaya ƴan Katsinan suk iso iyayen khadeejar Yaya Aleeyun da yake ma harda shi aka je ɗauko suruka nashi, ya sanya shima saidai abokanan shi ne suka taimaka mashi har haɗa komai. Har zuwa ƙarfe ɗayan ban yadda anyi mani kwalliya ba, yo ni kwalliyar ma me zanyi? Saida Afnan da Hafsat ɗin suka matsa ne gami da tsoratar dani zasu gaya ma Ya Ameen ɗin Abunda ya faru to, sannan na yarda aka yi mani ƴar Light ba mai yawa ba, duk da haka nayi kyau ba laifi kam. Kowa na ɗakin namu ya haɗe cikin ƴar ubansun ashoben yinin da ta kasance ƴar ubansu atamfa, fara ce tas sai ƴan pattern na dark blue da Orange, atamfar bata da hayaniya, hakan ce ta sanya tayi matuƙar kyau da haskawa gashi zanenta ba mai irin yawan nan bane jefi jefi ne. Haka muka shirya cikin atamfar, Nidai kasa tashi ma nayi saboda Hafsat ce ta bada mana ɗinkin da aka yi mana, kasancewa ƴar ƙibar dake gareni ya sanya skirt ɗin kama ni tsam, duk nabi na tsargu kaina, yayin da su kuma sauran suka ruɗe da ganin ƙirar da Allah yayi mni suna cewa dama su. Gyalena da takalma na masu tsinci duk blue ne, yayin da siririyar sarƙar dake wuya na ta kasance fari tar ɗin duwatsu da kar ta Orange, lallai munyi kyau, kaman yanda vail ɗina yake blue haka na kowa dake ɗakin namu ya kasance, banda Hafsat da ita kalar golden ne gabaɗaya jikin ta hatta sarƙar gold ɗin dake wuyan ta da Sadeeq ɗin ya zubo mata su cikin lefe kaman ba kuɗi ne ya siya ba. Masu aiki ne suka leƙo sashen namu gami da faɗa mana mu fito za'a fara cin abincin kaman yanda aka tsara. Tin daga nesa ake kallonmu, domin dai yau duk hassadar ka ba zaka kushe mu ba haka ma amaryar tamu, runfuna ne guda bakwai kaman yanda aka tanada, Hajiya Kubra, Hajiya Zainab, Kaka Zuwaira da tawagarta, sai ta Saudat, Nihal Da Hafsat ɗin. Kowa da tawagar shi yake zaune. Hajiya Kubra ce na fara hangowa, saboda wani irin kwarjini da cika idanu da take yi, ta kame ɗaya daga cikin kujerun Alfarmar dake ƙarƙashin haɗaɗɗiyar rumfar tata da taji ado da silkin yadi da balam balam. Sanye take cikin wani ɗanyen pink ɗin lace anyi mata ɗinkin bubu, wuyan nan nata babu Abunda yake yi in banda walƙiya, haka ma kunnuwan ta da hannayen ta da suke cike taf da zobuna da abun hannuwa na gold Yau ko gyalen ma babu a wuyan ta, sai ƴan fadan ta da suke zaune kujerun da suke gefen nata, sauran kuma duk kansu kujerun ƙarfe ne anyi masu ado da fararen ƙyalle in ka cire na kaka zuwaira da na Hajiya zainab, sai na amare da suke royal chairs kaman na kamu haka. Rumfar da babu kowa sai kujeru muka nufa gami da zama idanun kowaa kammu masalan ma ni da bani da alama da ƴar aiki ayau, ba wata wata ma'aikata suka fara serving ɗin mutane, baka jin komai sai ƙarar chokulla, ni kau na kasa cin ma abincin sai juya cokali nake ta faman yi. Da na ɗaga idanu na kuwa sai su faɗa cikin na Hajiya Kubra, data ƙure ni da kallo tana so ta gano Abunda yaja hankalin yaron nata a jikina, saidai duk iya kallon nata bata gano komai ba, domin in hasken fata ne ko hanci babu kalar wanda yaron nata bai gani ba har cen ƙasashen ƙetaren Da mun haɗa idanu kuwa zan saurin sadda kaina ƙasa saboda irin kallon tsanar da take bina dashi, sa'a ta ɗaya ummata bata wurin domin dukka ƴan aiki acen sashen nasu suke in abincin, hakan ce ta sanya su zama sashen namu, ita kau ummata ma ɗaki ta shiga gami da kwanciya saboda ta gaji gashi har juwa take ji.. Ƙarfe biyu daidai dubban mutane suka shaida ɗaurin auren Saudat Almustapha da Kamal jamu, akan sadaki naira dubu Hamsin, sai Zuwaira (Nihal) da Nuradden Baffa itama akan sadaki naira dubu hamsin, sannan Hafsat Auwalu da Abubakar Sadeeq Muftee itama akan sadaki naira dubu Hamsin ɗin Sannan na Aleeyj Auwalu da Khadeeja Ibrahim akan sadaki Naira dubu ɗari domin su ne suke da alhakin sanya ma ɗiyar tasu sadaki ba Alhaji Auwalu ba, tinda su cewa sukayi ba kuɗin ke gaban su ba albarka auren da ɗorewa shi suke so. Bayan kammala ɗaurin auren ne, haka dubban jama'ar suka shaida naɗin ya Ameen ɗin a matsayi *Yariman Matasan Arewa* Bayan kammala naɗa mashi rawani ne da miƙa mashi sanar girma sai aka lulluɓa mashi alkyabba fara ƙal da surkin royal blue Tini fa Yariman namu ya Faso, cikin salon tafiyar shi ta ƙasaita, yau kam tafiya ta tabbata, shi ba gadon sarauta ba Allah ya ci dashi, bayan ya kai gaisuwa ne ga dukkanin sarakunan dake wajen mai girma shugaban ƙasa ya mallaka mashi makullin dunƙulalliyar mota ƙirar royce - royce 2019 da lambogini 2019 collection a matsayi kyautar shi shi kuma, nan fa aka yi ta mashi kyaututtuka, fadawan da aka mallaka mashi suna mashi godiya, a haka ya nufo cikin gidan Bilal ɗin na take mashi baya domin zuwa kaima tashi mahaifiyar gaisuwa. Matasa kuwa ya gansu kowa so yake ya gaida shi, don ma fadawan na buɗe mashi hanya, a haka ya ratso dimbin mutanen nan har zuwa cikin gidan nasu. Tin daga nesa mahaifiyar tashi ta hango shi, Miƙewa tayi gami da isa wajen shi, baiyi wata wata ba kuwa ya sunkuya ya kai gaisuwa gareta, itama bata yi wata wata ba ta sunkuya gami da rungumo shi cikin ƙirjinta ta miƙe tsaye dashi, sowa aka ɗauka da tafi kowa sun burge shi, yanyameshi aka shiga yi ana ta kai gaisuwa, abokan wasa na yankar shi, hatta da kaka zuwairan da take tafiya daƙyar saida ta taso ta iso gareshi. Sa hannu yayi ya rungumo ta gami da ɗora mata peck a tsakiyar kai, dungureshi tayi tana mai cewa "ja'iri girma ya hau kanka yanzu saura mata" Haka yabi yana rungume ƙannen nashi amare da suka kai gareshi Hafsat ce kawai bai runguma ba, saidai ya kamo mata hannu yana mai cewa "Congrat ƙanwa ta" da murmushi ta bishi tana mai cewa " Same Yaya" Duk yanda dogarawan nan suke kaffa kaffa da daƙunar da ake kai mashi, dole suka haƙura, domin sabon babin ɗaukar hotuna ne aka buɗe kowa so yake ya shiga ayi dashi, masalan dangin Hajiya Kubran da suke ji su wasu isassu ne. Nikau da nake zaune sai sarkin murmushi nake yi akai akai, domin sun matuƙar burgeni, sarauta yayan namu tayi mashi kyau matuƙa, sai naga har girma kaman ya ƙara da cika ido, sai faman murmushi yake yi, shi kau Bilal bakin nan nashi kaman gonar auduga. Maida kaka zuwaira aka yi aka zaunar da ita, domin ta gaji sosai gashi shi kin rana suke sosai, domin duk sun baro wurin zaman nasu. Binshi kowa ya shiga yi da idanu ganin ya sulale ya fara tafiya, ƴar razana nayi ganin ya nufo inda nake zaune, waigawa na shiga yi domin ganin ko akwai wani kusa dani da yake nufo inda nake zaune. Ganin da gaske yake yi ni yake tunkaro wa ya sanya ni sauke kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuwa na duka biyu, bansan ma me zanyi ba, wane kalar tinani zanyi, gashi dai kowa mu yake kallo. Hannuwan nawa Naji an kama, bansan lokacin da na miƙe tsaye ba, jana ya shiga yi zuwa wajen mai ɗaukar hoton, saboda tsabar ruɗewa ni kuwa har gyale na yana sumɓulewa, daidai cikin taron jama'a yaja burki ya tsaya, hakan ce nima ta sanya ni tsayawa don dole, uwa ƙasa ta tsage in shige nake ji, gashi kowa ya zuba mana idanu, Hajiya Kubra kuwa kaman idanun ta zasu faɗi ƙasa saboda tsabar yanda ta ƙwalalo idanu tana kallonmu. *Ke ba zaki zo ki ɗauki hoton bane da mijinki?* Maganar da ya raɗa mani a kunne kenan daidai lokacin da ya zuƙunna yana mai ɗauko Gyalena daya sumɓule ya shiga yafa mani. Ai bansan lokacin da na ƙwalalo idanu ina mai Binshi da idanu ba na shiga rufe bakina da hannuwa na ina girgiza kai na. Ɗaga murya yayi sosai yanda kowa zai iya ji ya shiga faɗin *Alƙasim ga mata ta ina son ka ɗauke mu ni da ita kaɗai bana son kowa ya shiga in banda amini na Bilal* Ya faɗa da wani killer smile a saman fuskar shi yana yi yana cije leɓon shi guda ɗaya gami da kafa ma Mahaifiyar tashi idanu..... 🤣🤣🤣🤣🤣 ~Oum-Deedat ce~ [9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~28~* *A madadin ƴan Banfi ƙarfin ta ba Fans* Gaisuwa da saƙon ta'aziyya zuwa ga ƙawarmu kuma ƴar uwarmu mai bada goyon baya da ƙoƙarin comment, (Salamatu Muhammad) a bisa rasuwar mahaifinta da tayi, Allah ubangiji ya jiƙanshi ya sanya ya huta y baku haƙurin rashin shi, ya sanya kwanciya hutu ce, ya bashi ikon amsa tambayoyin kabari,ya raya Abunda ya bari yayi masu Albarka Ameen. 🤲🏻 °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Hajiya kubra wadda ta zabura da niyyar isa wurin da yake tsaye riƙe da hannuwan Suhan ɗin, da sauri Hajiya Sa'a ta riƙo hannun ta, domin ta kula sarai da niyyar hajiyar yanda take fitar da huci kaɗai ya isa ya shaida maka Allah ne kaɗai zai kare Al'ameen ɗin daga marukan da taso zazzagba mashi. Ganin za'ayi abun kunya ne a wurin Hajiya sa'ar ta shiga jan hannuwan ta zuwa cikin gidan ba tare da kowa ya ankare ba, domin kuwa kowa hankalin shi na kan Al'ameen ɗin da dogarawanshi suka zage suna ta gyara mashi malum malum da take suɓulewa. Rasa inda zan tsoma rain inji daɗi nayi, lallai wannan maganar tayi man tsauri, ƙwaƙwalwa ta har bana jin zata iya ɗauka, tini naga duniyar na juya mani, duk da hasknn flasher ta ko ina da take ta haske mu, ƙoƙarin zare hannuwa na nake yi domin in samu in ruga, na kula ma saboda tsabar yanda na tsorata numfashina har wani ɗauke wa yake yi. Gabaki ɗaya hankalin ƴan matan dake wurin ya tashi, waɗanda ma basu kula da ko waceceni ba, son sanin ba'asi suke yi. Ran kaka zuwaira kwal, lallai yau kowa ya shaida Al'ameen ɗin akwai wacce yake so, mutane da dama zasu dena yi mashi kallon mai ɗaga ma ƴan mata kai, saidai ita ɗin wannan wacece? Daga baƙin ƙofar gate, makaɗa da mawaƙa ne da masu kirari suna ta wasa Al'ameen ɗin da mahaian shi, Abie ne ke ta masu ruwan kuɗi fuskar nan taf da fara'a, duk wainar da ake toyawa a harabr gidan ma bai sani ba. Bilal ne ya zare jiki daga wurin da yake tsaye zuwa sashn Al'ameen ɗin, sannan ya ɗauko waya ya latso lambar Al'ameen ɗin. Daga cikin Aljihu yaji wayar tashi na vibrating, hannuna ya saki da niyyar ɗauko wayar, ni kau ganin wannan damar ta samu na zare hannuwan nawa gami da nufar sashnn namu kai tsaye harda haɗawa da ƴar sassarfa. Ganin Bilal ɗinne ya sanya shi ɗan juyawa bai hango shi ba, domin shi dai ya san tare suka shigo gidan, to ina kuma ya nufa? Bai ɗaga ba har ta katse, yana ƙoƙarin bin kiran wani ya sake shigowa ɗagawa yayi sannan ya kara akunne "Malam wai me kake yi ne haka? Menene dalili ka nayin hakan? Baka gudun kaja ma yarinyar wata matsala kuma? Ka saki yarinyar mutane hakanan, kuma ka shirya amsar hukunci daga wajen Mom domin ba don Allah ya tsare ka ba an janye ta da kasha maruka a gaban bainar jama'a" Bilal ɗin ya faɗa ta ɓangare ɗaya, shi kau gogan kasaƙe yayi da wayar har bai a san Bilal ɗin ya kashe ba, ƴar dariya yayi mai cike da yaƙe lokacin da yaji "ƴaƴan Goggo Fatima na yankar shi wai dole sai sun ɗauki hoto dashi tinda amaryar tashi mai kunya ce ta gudu, shi kau da baya da kunya dole ya tsaya. Ganin da yayi zai ɓata ma kanshi lokaci ne wajen ɗaukar hoton ya sanya shi juyawa kai tsayezuwa ga sashen nashi, baya ma jin yunwa, ko da yana ji kuma baya tinanin ma in zai iya kai wani abu bakin shi. Daga bakin ƙofa dogaransuka ja suka dogare, kai tsaye ya kutsa kanshi har cikin bedroom ɗin nashi inda ya tada Bilal ɗin nata faman kaiwa da komowa. Da ƴar sassarfa ya isa inda Al'ameen ɗin ke tsaye, cikin ɗan ɗaga murya ya shiga faɗin "me kayi haka ne? Hakan da kayi kana ganin daidai ne? Kana nufin zaka ja da mahaifiyarka ne? Ta wanna sigar ya kamata ka ɓullo ma Al'amarin?" ya ƙarshe yana mai zagaye Al'ameen ɗin ya nufi jikin window ya tsaya ba tare ma da ya san ya isa wurin ba. Yana tausaya ma abokin nashi, Abunda zai je ya komo baya hasashen idan zai zo ma abokin nashi da sauƙi, amsar shi kawai yake jira, saidai jin Al'ameen ɗin bai tanka bane ya sanya shi juyawa domin yaga halin da abokin nashi yake ciki. Shi kau ta ɓangaren shi, duk da kalamnn abokin nashi sun Dakar mashi zuciya kuma ya jisu har cikin ƙwaƙwalwar shi hakan bai sanya yaji ko ɗar a cikin zuciyar shi ba, karaya da wuri ba nashi bane ba, wannan karon dole ne ya nuna ma magulmata cewa hassadr su da baƙin cikin su babu inda zasu kai su sai fagen nadama. Takawa ya shiga yi har zuwa gaban gadon nashi, har yanzu bai ko tanka ma abokin nashi ba,baya so ne ya kai shi ga faɗin dukkan Abunda ke cikin zuciyar shi a fili, shi yafi so saidai kawai aga yana aikatawa. "Kanajina malam kayi mani banza, wato baka ma da lokaci na ko? To inaso ka sani dukkan Abunda ya taso kar a ƙasa ran zaka tunkaro ni ka samu mafita, maganin kar ayi to fa kar a soma" Bilal ɗin ya faɗa sannan ya juya da niyyar barin ɗakin. Al'ameen ɗin da yake ta ƙoƙarin cire kayan nashi domin ya watsa ruwa, barin cire kayan nashi yayi sannan ya juyo a hankali yana faɗin "Dakata Malam" Dakatawa bilal ɗin yayi ga barin ɗakin da yayi niyya. A hankali Al'ameen ya shiga ta kowa kaman mai jin tausayin ƙasa, har zuwa inda bilal ɗin yake tsaye, a hankali ya sanya dukkan hannuwan shi ya dafa ka faɗar bilal ɗin, sannan ya shiga faɗin "Ni Moh'd Al'ameen nine mazinaci, fasiƙi mai neman yarinya da lalata har cikin ɗaki na, ni take tallata ma kanta ni kuma nake biye mata alhali ina cikin hankali na...." Bilal ɗinne ya dakatar dashi ta hanyar sauke dukkanin hannuwan da yayi amfani dasu wajen dafa kafaɗar bilal ɗin " Dakata Friend, kana cikin hankalina kuwa? Kasan me kake faɗa? Ya zaka dinga jifar kanka da waɗannan mugayen kalaman? Ko dai ka fara shaye shaye ne ban sani ba?" Bilal ɗin ya faɗa cikin ɗaga murya, ga dukkan alamu kalaman abokin nashi sun ɓata mashi rayuwa gabaɗaya. " Na sani Bilal, na san me nake faɗa, kuma waɗannan magangannn ba daga bakina suka fito ba, daga bakin mahaifiya ta suka fito, and kuma bansan wanene ya faɗa ba, shine naga tinda har neman yarinyar akeso inyi to zan fa nema ɗin Amman ba ta hanyar da su suke nemana da ita ba, ta hanyar da shari'a tazo mana da ita, watauta hanyar *Aure*" Ya faɗa shima cikin ɗan ɗaga murya kaɗan, saidai Sam na bakin ƙofa ko na cikin falon ba lallai ne ya iya jiyo Abunda yake faɗa ba. " Huh" Bilal ɗin ya sauke ajiyar zuciya mai matuƙar ƙarfi, a hankali shima ya shiga takawa har zuwa gaban gadon, daɓas ya zauna yana mai dafe kanshi da yake sara mashi uwa zai rabe gida biyu, wannan shine dalilin rashin lafiyrr abokin nashi? To indai haka ne munafukan na acikin gidan, lallai tausayin abokin nashi da na yarinyar da ake neman a laƙaba ma sharri bata ji ba bata gani b ya tsira mashi har cikin zuciya. Sake miƙewa yayi gami da isa ta inda abokin nashi ke tsaye ya haɗe kai da bango yana ta faman maida numfashi yayi, da dukkanin alamu ɓacin ran nashi ya sake komawa sabo fil a cikin zuciyar shi. Da dukkanin hannuwan shi yayi amfani wajen kamo abokin nashi har zuwa lokacin da ya zaunar dashi bisa gadon nasu, shima zaunawa yayi a hankali, shi ya ma rasa tinanin me zai yi a ranshi, llai abokin nashi na buƙatar wanda zai taya shi wannan yaƙin da ya tunkaro ka, ace wai a wurin aiki baka samu matsala ba sai a cikin gida. Ummata da take kishigiɗe bisa darduma, gama sallar ta kenan ta jawo cesbaha tana ja idanun ta a lumshe, tsulum na faɗa ɗakin namu ina ta faman haki, ni ban ma san umman tawa na cikin ɗakin ba, ai da bari nayi sai na saisaita kaina sannan in shiga. Da hanzarin ta ta tashi tana mai cewa "ke lafiyar ki kuwa? Ko wani abu ne ya same ki? " Ganin ban bata amsa ba ya sanya ta ficewa da niyyar zuwa taga menene yake faruwa, saidai bata fahimci komai ba, saboda ko da ta isa wurin mutanen ta tadda wasu suna ta faman cin abinci yayin da wasu ke ta faman ɗaukar hoto da Al'ameen ɗin. Hakan ce ta sanya ta dawowa zuwa ɗakin gami da share ni ta cigaba da laziminta, in na matsu na faɗa mata Abunda ya tashi hankalin nawa. Ban gama warwarewa ba sai ga Hafsat da Afnan sun shigo cikin ɗakin, cewa sukayi in biyo su muje ko suyi mani tonon silili wurin umman tawa. Ba arziƙi na miƙe gami da yafa mayafi na na bi bayan su, ina kula da Afnan wacce take Ƙunshe dariya a cikinta. Da kallo umman tawa ta bimu tana kaɗa kai, koma miye in tayi wari taji. Masifa da bala'i ba kalar wanda Hajiya Kubran bata sha ba cikin ɗaki, haƙuri suka dinga ɓata, kada ta ɓata taron bikin nan DON Allah, da ita cewa ma tayi aje a sallami kowa tinda an gama cin abincin. Shawarwari ba kalar wanda ba'a bata ba, daƙyal suka samu tayi haƙurin zuwa dare ayi wacce za'ayi, cikin gidan zata ga mai zaman wani a cikin su ko ita ko su, lallai wannan aikin asiri ne tsab, kenan ma Abunda aka faɗa ɗin ya tabbata gaskiya ne, inko hakane wallahi Sam ba zata saɓu ba bindiga a ruwa. Abunda ya faru ɗin sai ya sanya ƴan ƙanannn maganganu suka shiga yawo a cikin gidan bikin, duk inda Kaga gungu an haɗa kai maganar akeyi, lallai Hajiya Kubra ta faɗi ƙasa babu nauyi inko har ta bari ɗanɗanta da aka yi ittifaƙin tafi son shi akan dukkanin sauran ƴaƴan nata ya auri talakrr ƴar aikin su. To dama itama dai Abunda take gudu kenan, kuma tini labarin gulmammakin da akeyi cikin gidan ya isa kunnen ta, domin duk inda ka zaga maganar akeyi. Hakan ce ta sanya bata ƙara fitowa harabrr gidan ba, duk wanda yazo saidai a shiga dashi sashen nata, shima ɗin saidai in manya ne, inko jigari jigari ne iyakar su babban falo a basu abinci suci ba ta gudunmuwar da suka kawo take yi ba, Alla Alla take yi dare yayi domin ayi wacce za'ayi. Kusan ma zamu iya cewa bikin sai ya koma sashen hajiya zainab da kaka zuwaira, dama su ta fannin su abun yayi masu 100% sun yaba da yarinyar da kuma tarbiyyar ta, alwashi dai sun sha shi indai da gaske Al'ameen ɗin yake yi yana son yarinyar itama tana son shi to fa babu makawa da izinin Allah sai abun ya tabbata, tinda sun san yaron nasu ba irin raggwayen mazan nan bane. Haka har suka sake shiryawa suka fice dogarawanshi na biye dasu a baya suna mashi kirari da wasa shi wannan karon harda ce mashi Angon Hauwa'u sai dubu ta taru. Domin duk akan idon su Abunda ya faru ya faru. Ɗaki suka sanya ni gami da titsiyeni suna tambaya ta wai in faɗa masu lokacin da muka fara soyewa da yayan nasu basu sani ba. Ba kalar rantsuwrr da banyi masu ba, Amman fir suka ƙi yarda, dole naka bakina nayi masu gum, ina jinsu suka cigaba da zaulaya ta. Afnan ɗince mai cewa "Ni fa tin lokacin da yaya yazo da maganar auren aunty suhan ɗin na yarda dashi, dama na daɗe ina addu'ar hakan a zuciya ta..." Hafsat ta amshe da cewa "Kedai bari Afnan, kuma ke fa don ma baki nan, baki ga yanda yake kulawa da al'amarin ta ba ke dakin gani ma kinsan ba banza ba wlh" "Welcoee to our Family Aunty Suhan" Afnan ɗin ta faɗa tana mai rungumi ni zuwa jikin ta. Nan suka shantake suna ta zaro fira, ni wani abun ma in sun faɗa saidai in kwalalo idanu, gani nake yi kaman sharrinsu ne kawai Al'ameen ɗin ba zai iya yin hakan ba. Sauran ƙawayen Hafsat ɗin duk sun dawo ɗaki, nan fa aka buɗe sabuwar fira, cikin su ma har akwai wadda tayi man congrat gami da faɗin "Lallai kunyi matuƙar da cewa, ku duka kun iya zaɓen abokin rayuwa" dariya kawai aka sanya maganar gaskiya zukatn Afnan ɗin da hafsat ɗin cike suke taf da farin ciki marar misaltuwa, yayin da ni kuma ta ɓangareaa na ma rasa kalar tinanin da zanyi, har yanzu ba wai na gaskata bane, gani nake yi kaman mafarki nake yi ko kuma yaudara ce irin ta ɗa namiji akwai Abunda yake son cimma wa. " ba zata taɓa saɓuwa ba wallahi, ashe yaya bai bar zancen nan ba har yanzu, gaskiya ya zubda mana aji at All wallahi, duk da yau ta kasance ranar farin ciki a gare mu ta wani ɓangaren ranar tazo da akasi" Nihal ɗin ta faɗa tana mai faɗa wa kan jibgegen gadon nasu inda Saudat da sauran ƙawayen nasu suke ana ta maida yanda akayi "menene ba zai faru ba? Ai ya riga ya faru saidai Allah ya kyauta gaba kawai, Amman ke kina kallon cikin idanun yaya wallahi kinsan har cikin zuciyar shi ne sonta yake da gaske" Wata daga cikin ƙawayen nasu ce da ta kasance ƴar uwarsu ta fannin Hajiya Kubra ke faɗin haka, ta bala'n so shi itama a da, ganin ba kula ta yake yi ba, hasali ma ba ta ita yake yi ba, duk iya yin da take dashi da fi'ili lokutta da dama gwasale ta yake yi ko kuma yayi ma kaman bai san ta nayi ba, ya sanya ta dole ta watsrr da makaman soyayyrr nata rabi wani sarkin. Wata daga cikin ƙawayen ce ta sake amshe zancen da cewa "dalla bari wannan maganar khairi, ai ke kinsan wallahi Ya Ameen ya wuce da ajin wannan ƴar aikin, ni ina gani ko dai asiri sukayi mashi ya aikata a cikin jama'a ba tare da ya san ya aikata ba" "Confirm cewrr Saudat da take kishigiɗe sai lokacin ta tashi zaune, gaskiya Yaya bai kyauta mana ba Sam, haba ina shi ina wannan kucakar? Duk tarin ƴan matan da suke rububinshi ace bai hango kowa ba sai wannan ruɓusar, ke kiga jikin ta ma fa ko ina a sake take ko irin slimming ɗinnan ma ita bata iyawa saboda duhun kai anfj so a zauna tuɓs ko ina tsoka" Shewa suka sanya suna faɗin Amman fa Saudat baki da dama wallahi, "Amman fa ni kinsan ina tsoron irin wannan jikin, komai fa suka sanya zama yake das yayi masu kyau daidai jikin su" Cewar ɗaya daga cikin ƙawayen nasu da suka zo masu hidimar bikin tin daga ƙasar ta ta America. Nan fa aka buɗe sabon babin yin zancen suhan ɗin duk kusan rabin firar aibantawa yafi yawa a ciki (Hmmm Allah shi kyauta, Hassada ga mai rabo taki) Ana gama sallar la'asar aka fara shirin hawan dabar, bayan an ci an sha, anyi hani'an. Sarakunan jihohin namu na arewa suna nan sai washegari zasu koma gruruwan nasu, inda aka yi masu masauki a fadar shugaban ƙasar namu ta nigeria. Hawan daba fa ya ƙayatar, tashohin gidan talabijin suna ta ɗauka live, matsa dai an gansu a wurin, kowa yayi mamakin irin yanda dawakai suka yalwata a wurin kaman dama an san da naɗin sarautar. Ƙarfe shida suka gama zagaya duk inda zasu zagaya, manyan namu suka samu suka koma masaukin nasu domin su huta, yayin da cikin gidan yake ɗinke da jama'a gefe guda ga masu kiɗin ƙwarya suna ta chashewa ana masu ɓarin kuɗi, abinci kuwa har kawo yanzu shigowa akeyi da sababbi, duk Abunda kayi sha'awrr ci akwai shi. Gudun sake tada gulmammaki ya sanya Hajiya Kubran ta dage ta cije, Amman fa har kawo yanzu da magariba ta kawo jiki bata saki jikinta ba, walwalarta har yanzu ragaggiya ce, don ma su Hajiy Lailan na bata baki da shawarwari akan yanda za'a ɓullo ma 'amarin. Hajiya sa' ar ce tayi mata alwashin ta bar komai a hannun ta nan da kwana uku zata ga Abunda zai faru a cikin gidan. To da haka ne fa ta samu ta lalubo walwala ta yafa a kan fuskar ta Amman ba don har cikin zuciyar ta haka yake ba. Wannan karon sashen na Al'ameen cike yake da baƙi, abokanan shi da suka zo mashi ɗaurin aure da naɗin sarautar tashi, da yawa ma daga cikin abokan yanzu sunan shi ya tashi daga Ameen ko Dambulan da suke kiran shi dashi ya Koma Yariman Matasa, duk da baya so Amman a haka yake amsawa, saidai kowa ya kula da rashin walwalar tashi, Amman sun mashi uzuri akan cewa hayaniya da jama'a ne. Gida yayi tsit tin bayan da aka tashi sallar isha'in Yo kowa ya gaji wasu ma har sun fara bacci, har yanzu zuciya ta a cunkushe take na kasa gane kaina, Alfarmar su Hafsat ɗin na roƙa akan su barni inje in kwana tare da ummata ko Naji sauƙi. Basu hanani ba, saidai sunce su ba zasu rakani ba, a haka na ratso tsakiyar gidan zuwa sahen namu, ummata har ta kwanta na kwankwasa mata ta buɗe na shiga. Da kallon ke lafiya kuwa ta bini, yi nayi kaman ban kula da ita ba, kai tsaye na haye katifar na kwanta, yayin da itama ƙalau bata ce mani ba ta hawo itama tare da kwanciya. Saidai me? Bacci Sam yayi mani ƙaura, idanun a kaman an soya, saboda rashin baccin har wani raɗaɗi suke yi mani. Saidai in juya in sake juyawa, idan na tinank kaɗan sai in ɗan ja tsoki kaɗan in sake juyawa. Ƙwaƙwalwa ta fa har yanzu a cunkushe take, ina buƙatar wanda zai yi mani fashi baƙi dalla dalla fa, saidai wanene shi? Wayata ce ta ɗauki haske alamar saƙo ya shigo, da hanzari na jawo ta gami da buɗewa, banyi mamakin sunan shi da nagani ɓaro ɓaro kan screan ɗin a, saidai Abunda saƙon ya ƙunsa shi ne ya bani mamaki. Ummata wadda bansan da ta tashi zaune ba, kwatsam saidai Naji muryar ta tana mai ceman "Mamana na kula dake fa tin da rana, ga dukkan alamu akwai Abunda yake damunki, Amman in kinga ɓkyemun shine Abunda yafi ɗin, sai ince Allah ya sanya hakan ne, domin bana so kizo kiyi danasani akan dukkan Al'amurranki, idan kuma kin yanke shawarar faɗa mani tau ina saurarenki" Cikin ƴar razana bakina na rawa na tura wayar tawa ƙarƙashin follow, bansan lokacin da na shiga ce mata "umma fa ba komai, kawai na gaji ne, kuma gashi kaman ba ɗan jin daɗi ne..." Na ƙarashe cikin in ina wadda take alamta ba gaskiya a cikin maganar tawa, wanda ni kaina bansan dalilin nawa na ɓoyema umman tawa ba, da duk duniya bani da abokiyar shawarar da ta wuce man ita. Gyaɗa kai kawai tayi, bata sake ce mani komai ba ta koma ta kwanta, tana fatan Abunda na faɗa ɗin ya kasance gaskiya, duk da bata taɓa kamani da laifin yi mata ƙarya ba. *_"ki dena yawo cikin dare, sannan ki shirya fuskantar duk wani ƙalubale da ka iya tunkaro mu"_* Abunda ya rubuta mani kenan, ban iya bashi amsa ba, duk kuwa da karanta saƙon da nayi sau ba adadi. Ni ya ma ƙara sanya ni cikin wani duhun wallahi, wai ni shin me yake nufi dani ne? So yake ne ya tarwatsa mani ƙwaƙwalwa ne ko kuma me? ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~29~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° A haka dai na kwana juye juye, zan mabiya cewa ko baccin kirki ban samu nayi ba, umman tawa duk tana kula da dukkan motsi na Amman ƙala bata ce mani ba. Washegari kuwa tin dasafe aka tashi aka hau shirye shiryen walima da za'a gabatar itama dai a farfajiyar gidan, wannan karon harda dangin anguna duk zasu halarta, daganan ne za'ayi buɗar kai, bayan an gama sai a basu amaryar su su tafi da ita. Tin da safen kuwa sai ga su Afnan wai sun zo ƙara tafiya dani, aikuwa fir naƙi binsu, ba irin magiyar da basu yi mani ba, Amman na ƙiya, bana so in koma wurin ne a sake samun matsala gashi naga ga dukkan alamu ummata tana shirin zuwa wurin ne. Kwanciya ta nayi ko bayan fitar su, har itama umman tawa ta kammala shirin ta ta fice, gyara kwanciya ta nayi gami da jan abun lulluɓa domin baccin da ban samu nayi ba a daren jiyan. An ƙawata wurin fiye da na jiya, tini dangin angunan sun iso tin wajen ƙarfe goma na safiya. A sashen Hajiya kubran aka yi masu masauki, saidai dangin sadeeq ɗinne suka ce a nuna masu wajen surukar yaron nasu acen ne zasu zauna. Ba musu aka nuna masu, ganin su manyan mutane kowacce cikin shiga ta alfarma. Hajiya Zainab ɗin bata yi tinanin haka ba, Shiyasa ba'a shirya masu tarba ba dukkanin kayan tarbar suna cen sashen Hajiya Kubra. Nan fa ta shiga ina taka saka su. Lura da sukayi ne ya sanya suka ce karta damu kanta, ba wannan ce ta kawo su ba, su yarinya kawai suke so a basu. Rumfuna bakwai aka kafa ayau, sunsha deciration kuwa, rumfa ta farko ta hajiya kubra ce, sai ta kaka zuwaira, sai ta Hajiya Zainab, sai ta dangin anguna guda uku, gefe kuma ta anguna ce da abokaninsu maza An zagaye farfajiyar gabaki ɗaya illa iyaka hanyar da za'a bi a wuce. Ƙatuwar darduma aka shimfiɗa tsakiya inda gefe aka jera amaren kowacce tasha lulluɓi da kalar nata kayan da sukayi masu matuƙar kyau, gefe guda kuma aka jera ƙawayen amaren a yau babu bambanci duk kansu wuri guda suke zaune, cikin atamfar su english, kalar ta yarbawa yellow ne da ɗige ɗigen ja a jikin ta. anyi masu ɗinkin buba duk kansu, hakan ce suka sanya jan gyale da sarƙar murjani a wuyan su ɗaurin zanen ma bisa riga aka yi shi, hannuwan su riƙe da ɗan mafici mai ƴar bazar gashi gashi haka. Kowa ya hallara, nan fa aka fara gabatar da jawabai da kuma gabatar da kai. Kowa ka kalla yana cikin farin ciki, banda hajiya kubra da fuskar nan take ba yabo ba fallasa masalan ma data kula dangin iyayen mijin Hafsat ɗin sun zarce na yaran ta gabaki ɗaya a komai kuma. An kira kowanne ango yazo ya nuna amaryar shi, gami da kama hannun ta zuwa gaban dangin shi ta kai gaisuwa, sannan sauran mutanen, haka suma angunan amaren suka kama su har gaban nasu iyayen suka gaida su. Kaka zuwaira ce duk wanda yaje kusa da ita sai ta zaulayeshi tace ita ba sadaki take so ba na goro take so, haka suka babbata kuɗi gami da komawa suka zauna. Bayan ƴan abubuwa da aka gabatar aka buƙaci iyayen anguna da su kawo kayan aure. Nan fa idanun mutane ya shiga buɗewa ganin iyayen kaya na ƙarya da kuma kuɗi da ake ɓari kaman wanda ba'a so. Ba'a sha mamaki ba saida iyayen mijin na Hafsat suka taso, nan fa wuri ya hau tafi da sowa, ganin irin iyayen kuɗin da suka ajiye gabanta, daloli ne iya kallon ka, tare da sarƙar gwal da abun hannunta da zobunan ta wasu irin manya ne ko daga ina kake zaka iya hango su, tare da makullan mota guda biyu, ita ɗaya mahaifiyarta ɗaya, sai makullin tanƙamemen gida da yake nan cikin abujar da suka mallaka ma mahaifin Hafsat ɗin. Nan fa ƙaryar iyayen su Nihal ta ƙare masalan dangin Hajiya Kubran, saidai ita ce tayi ƙarfin hali ita kuma taba dangin mijin ƴaƴan nata motoci da kujerar Makka a matsaynn tukuicin kayan auren da aka kawo masu. Hajiya zainab bata san da wannan al'adar ba, hakan ce ta sanya bata tanaji komai ba, gashi kuma mijin nata baya kusa. Shiru aka yi, kowa naso yaga me su Hajiya Zainab ɗin zasu bada tukuicin wannan babbar kyauta da aka yi masu. Takawa ya shiga yi har gaban iyayen mijin Hafsat ɗin ya ajiye check gami da wata takadda ya koma ya zauna, Ya ameen ne da yake zaune cikin rumfar abokan angunan, tini kuwa kallo ya koma kanshi, Hajiya Kubra tsabar ƙuluwa kaman idanun ta zasu sauka kan Al'ameen ɗin. Mai jawabi ne ya taka har gaban iyayen mijin Hafsat ɗin ya sanya hannu gami da ɗaukar check ɗin da kuma farar takardar da take ƙar babu komai akai sai Rubutun Al'ameen ɗin jiki da ya gaji da ƙayatuwa. "Masha Allah, Alhaji Moh'd Al'ameen Almustapha Dambulan ya bada tukuicin Zunzurutun kuɗi Naira Million Biyar tare da kujerar hajji ta kimanin mutane biyar da kuma upper ta ɗaukar matasa aiki a cikin Zuriyar angon Hafsat ɗin ƙarƙashin jagorancin kamfanin, suma kimanin mutane Ashirin" Tafi aka saki, gefe guda wata zabiya ta saki guɗa, babu Abunda kake ji a wurin illa iyaka hayaniyar mutane data kauraye wurin kowa na faɗin Albarkacin bakin shi. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Hajiya Zainab ɗin ta sauke, ganin cewa yaron nasu ya fidda su kunya, duk da ta san cewa ba da son ran hajiya kubran da take zaune cen cikin mutanen ta tana ta sakin yaƙen dole bane, Amman ko ba komai ta san Al'ameen ɗin mutum ne mai alkhairi da zai yi ma daman shi ba tare da hagun shi ta sani ba. Mutum ne mai hangen nesa da kuma kakkaifan tunani, baya buƙatar in zai fidda family ɗin nashi kunya sai ya jira shawara da wani. Ta ɓangaren Al'ameen ɗin kuwa idanu sukayi mashi yawa, ilahirin ɗaukacin mazan dake rumfar nan ya matuƙar burge su harda mazajen ƙannan nashi kuwa, wannan ta sanya suka ƙara gane B ƙaramin gida sukayi aure ba. Bayan kammala wasu Al'adun ne aka yi addu'a tare da ƙarin godiya, sai kuma aka fara shirye shiryen miƙa amaren ga dangin mazajen nasu bayan yi masu huɗuba mai ratsa jiki da Alhaji Auwalun da Alhaji Mustaphan sukayi. Hafsat tasha kuka, da kyar aka ɓanɓareta jikin mahaifiyr tata, babu wanda bata ba tausayi ba, yayin da su kau sauran ƙemadagas iyayen su ne ma suka sanya su mota babu wacce take kuka cikin su. To a ganin su dai auren so ne, kuma na wayayyu, auren ma sunan anyi ne, Amman suna da ƴancin da zasuyi komai a sadda suka so, kuma a lokacin da suka so. Kkwacce cikin su an mallaka mata jibgegiyar mota harda Hafsat ɗin kuwa, wannan kuma kyauta ce daga hannun Alhaji Mustaphan bayan gama masu huɗuba da sukayi. Har aka tafi kaisu kuma basu ma da alamar kukan saɓanin Hafsat da take ta kuka kuma tana laluben ina zata ga Suhan ɗin Amman ko alama bata hango mai kama da ita ba ma. Abun ya ɓata mata rai matuƙa, har saida tayi ma Afnan magana, wadda ita Hafsat tace zata bi Alabasshi daga baya zata je gidan ƴan uwan nata. Motoci ne aka zube bayan wadda su mazajen nasu suka kawo, kowacce amarya kake so kabi akwai mota free da zata kaika ta maido ka, duk da dai galibi wasu acen zasu kwana masalan ƙawayen amaren gashi kuma magariba ta doso ta kawo jiki. Hatta Hajiya kubran saida taji wani iri rabuwa da yaran nata da zata yi duk da ta san cewa koda yaushe zata iya ganin su matuƙar suna ƙasar. Bayan kammala komai ne da tafiyar dangin angunan da amaren su, aka hau gyaran gidan Gidan ya rage ƴan tsiraru sai masu aiki kaɗai ya rage don sashen Al'ameen ma babu kowa duk an kammala hidimar biki sun wuce masu jirgin gobe kuma sun koma hotel ɗin da suka sauka sai a goben zasu wuce. Kafin isha'i fa tas an gyara ko ina an wanke ko ina, wannan karon harda umman tawa da Hajiya Zainab da wasu daga cikin DANGIN alhaji Mustaphan ne suka sanya hannu aka yi dasu. Nikau ta ɓangare na, Naji matuƙar daɗin yau, kuma ina cikin farin ciki sosai duk da hayaniyar cen cikin gidan dan loud sleaker da ta dameni kusan ma ince hanani bacci tayi. Ƴan latse latse na na cigaba da yi ni kaɗai a ɗaki, salla kawai ke ta dani. Ko abinci saidai na sha complax da yake ni ba mai yawan ciye ciye bace ba. Ina cikin latse latse na a Internet naga alamar kaman an saki Jarabawar mu ta jamb da muka zana kwanaki. Aikuwa cikin sa'a na tabbatas da gaskiyar Al'amari, wata yarinya da muka zauna kusa da kusa mai suna Samira, ita na kira gami da tambayar ta, cikin farin ciki take sanar dani cin Jarabawar tata, wai ashe ma tin numu'a aka saki ban sani ba. Roƙonta nayi ko zata je ta dubo mani Alabasshi sai in bata kuɗin scratche card idan na fito, ba gardama ta amsa mani da zata duba mani ma yanzu ba sai na ɓata komai ba, saboda na taimake ta sau ba adadi a yayin zaman namu da ita, nan ne take faɗa man numb ta ce tayi loosing tin bayan canza wayar tata, waccen ta faɗi ne, jajanta mata nayi gami da cewa ina jiran ta sai na jita. Ko awa uku cikakka ba'a yi ba ta kira ni, tin daga muryar ta na gane kan zancen, ko saurarena ma bata yi ba ta shiga yi mani murna, muryar ta cike take taf da farin ciki ga dukkan alamu har cikin zuciyar ta ne. "Ƙawata kina da sa'a wallahi, zamana kusa dake ya taimake ni kwarai da gaske, ina alfahari da sanin ki a rayuwa ta, dad da mom duk sunce in miƙa saƙon godiyr su gareki takanas zasu zo har gida suyi ma su mom ɗinki godiya, kuma ina farin cikin sanar dake cewa duk school ɗinmu babu mai highest Mark kamarki insha Allah damun gama zan turo maki score ɗinki ki gani, zan kira ki insha Allah in mun tashi zuwa" Ko jiran godiyar da zanyi mata batayi ba ta kashe wayar, mamaki na shiga yi wannan wace irin yarinya ce, dama ko da muka zauna kusa da Juna duk da lura da nayi ita ɗin ɗiyar wani ƙusan gwamnati ce, Sam hakan baisa ta ɗauki kanta wani abu ba, tana da yawan dariya ga sauƙin kai don itace ta fara yiman magana ma da roƙon in taimake ta don Allah, wannan ce ta sanya na taimaka mata da iya gaskiya ta tinda ita ta karya kanta ta roƙeni. Ina hawa WhatsApp kuwa sai ga saƙon ta ya shigo wayar tawa, tayi screanshoot ta turo mani. Ai bansan lokacin da na miƙe ina sujada ga Mahalicci na ba, Sam ƙarar loudspeaker ɗin bata damuna ta murna ta kawai nake yi, ni kaɗai ace naci 280 Abunda ma wasu 180 suke nema? Lallai Allah buwayi gagara misali ne, kana taka Allah na tashi, Amman ni kaina in an faɗa man naci hakan zan iya musantawa ba don na gani ba. Saidai ada kam nayi mamaki da tace duk nafi kowa maki a duk faɗin makarantar da take cike taf da ƴaƴan manya wanda su za'a ma iya bi masu kadin abun, ni kuma da bani da kowa sai Allah gashi ya kwato mani ba don na isa ba. Kaman in tura mashi saƙo, sai kuma naga ai gani da kai yafi aike, nima tur a mashi nayi kaman yanda ta turo mani, naga ma kaman baya online, kusan ma ince rabon shi da hawa tin kwana biyu da suka wuce, to Allah yasa ma zai gani, gashi banda mail ɗinshi da sai in tura mashi ta cen na san zai fi saurin gani. Na mashi uziri ne tinda na san yana Cikin hidima da jama'a gashi kuma Naji kaman ance bayada lafiya rannan a bakin Hajiya Kubra duk da Nidai banga alamun hakan ba a jiya da ya bani kunya a gaban mutane, har yanzu saƙon shi na jiya yana kai kawo acikin ƙwaƙwalwa ta, saidai na Gaza gano mai yake nufi duk kuwa da kwana laluben da nayi. Umman tawa bata shigo sashen namu ba sai bayan isha'i bayan sun kammala gyara ko ina, a bakin ta ne naji tana cewa su Hajiya Zainab ɗin gobe zasu wuce, tace wallahi gidan ta zata koma, saboda gidan duk ya isheta dan ma ƴan kankiyar na nan ko ba komai tana jin ɗuriyar waɗanda ta sani. Sannan ta shiga yiman faɗan rakiyar Hafsat ɗin da banje nayi ba, tace tana jin Hafsat ɗin ta kira maman tasu tana mata tsogumi, kuma da gaskiyar ta "lallai kinyi laifi mamanta, ai kin san dai ba zan hana ki raka Hafsat ɗakin miji ba, yarinyar da ta fifita ki akan kowa na gidan nan har su ƴan uwan nata, to maza idan Allah ya kai mu kiyi sammakon shiryawa ki kira ta tayi maki kwatance kije mata ki gano ɗaki, Naji ance wucewa zasuyi ita da mijin cen ƙasar da yake aiki" To nace mata, ni yau fa zuciya ta fes, duk da umman tawa ta lura, ita fa harma ta fara zargn anya yarinyar tata lafiya take kuwa, yau farin ciki gobe akasinshi? Kaman ba ita ce ba jiya ta kasa barci, yau kuma ta kasa shiga jama'a, koma dai miye zata zuba ido ta gani. Ita Abunda ma yafi ɗaure mata kai, wasu ƴan maganganu da taji suna tashi daga bakin ƴan bikin masalan dangin Alhaji Mustaphan, har kaka zuwaira na cewa ita ce wannan? Lokacin da taje gaida ta dayi mata saida safe, sai gashi har tana bata saƙon gaisuwa zuwa wajen Suhan ɗin da tace mata yau bata ga giccinta ba, Allah dai yasa lafiya. Dariya tayi, zuciyar ta cike da wasi-wasin Abunda taji ɗin, harda wata taji tana cewa "ance fa ƴar aikin gidan ce, amman sun naniƙe ma Al'ameen ɗin" gabanta ya tsananta faɗuwa kaddai tinanin ta ya kasance gaskiya, domin maganganun sunyi yawa kuma ta fahimci duk akan ƴar tata ce, tinda ba kowa ya san ita ɗin wacece ba a wurin suhan ɗin, Shiyasa wasu ma a gabanta suke gulmar. Sheda mata nayi naci Jarabawa gami da nuna mata sakamakon a cikin wayata, tayi murna matuƙa Amman fa jikin ta yayi laƙwas, to ko shine dalilin da nima na kasa bacci jiya, kuma dai gashi taji ban tunkareta da maganar ba, saidai bata kyautata zaton haka ne, ƙila dai ƴan maganganu ne da gulmace gulmace irin na gidan biki da kuma jama'a Hakan ce ta sanya ta share wa da batun, sai a take tambaya ta ko na tura ma Yayan namu? Amsa mata nayi da cewa na tura mashi saidai ƙila bai gani ba, tinda har yanzu bai ce komai ba. A haka muka kwanta tinani fal zuciyar ummata yayin da ni kuma yau nasha bacci na harda saleɓa. A sashen Hajiya kubran kuwa dangin ta kawai suka rage sai ita kanta, duk da wasu suna cen gidan yaran nata, suma kusan duk gobe zasu wuce, su Hajiya Sa'a ɗinne dai sai bayan isha'i suka tafi suna mai kwantar mata da hankalin cewa tasha kurumin ta, zata ga me zai faru bada jimawa ba, ta yarda da hakan tinda ta san hatsabibancin ƙawayen nata, wannan ce ma ta sanya suke juya akalar mazajen nasu, sun zama hotiho a cikin gidan, tini itama suka so su rinjayeta Amman ita tana tsoron shirka, kuma ko ba haka ba in Alhajin nata yaji zai yi mata bore ne sosai kuma ta san halin shi. Bayan kammala shiryawarta ce da daddare ta doshi ɗakin mai gidan nata, so take taje ayi wacce za'ayi, tana so ayi ta ta ƙare su tattara su bar mata gidan ta, lallai tabbas ta yarda da maganar ta mama talatun cewa sun saba taɓa juna, in ba haka ba harma wani yafa mata gyale yake yi a bainar jama'a kuma yake kuranta matarshi, ko a gidan ubanwa ta zama matar tashi,? Ita zata ga yanda wannan al'amarin zai kaya, ko da kuwa zatabar duniyar ne ta kwammace indai ba zata haɗa jini da waɗancen maƙasƙantan Talakawan ba. Saidai Takawa take yi zuwa sashen zuciyar ta taf da wasu wasin ko zai amshi maganar tata, bata ma ko tadda shi a sashen nashi ba, yana cen suna fira dasu kaka zuwaira da Alhaji Auwalu ya sauran ƴan uwansu matan, suna jin damuwoyinsu, saidai Abunda hajiya Kubran bata sani ba kaka zuwaira tazo da maganar Al'ameen da Suhan ɗin kuma duk kansu sunyi na'am da zancen, shi kuma shi da yaya Auwalun sunce abar lamarin a hannun su tukunna har sai sun kammala bincike. A haka firar ta tashi kowa ya nufi sashen nashi, shima yaya Auwalun ya nufi wajen Hajiya Zainab ɗin domin dukkanin ƴan uwanta sun wuce yau bayan kammala tafiya da amaren, jirgi suka hau tinda ana fama da matsalar hanya masalan ma ta Abuja. (Allah ka kawo mana ɗauki, ka bamu zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar tamu) Baiyi mamakin taddata a sashen nashi ba,ya san hakan ce zata faru dama, kuma yana kyautata zaton maganar yaron nata ce ta kawo ta. Bai nuna mata ba Sam, sai a wayan cewa da yayi ya shiga zaulayar ta, bata biye mashi ba tinda ita ba wannan ne gabanta ba. Koda ta fara mashi mitar bai dakatar da ita ba har saida ta gama, shi mamakin ta ma yake yi wallahi, ace mace kaman Hajiya Kubra ta tsaya tana tada jijiyrr wuya akan mutanen da ko abincin da zasu ci basu da, mutanen da suke aiki ƙarƙashin ta abun a tausaya mawa, ita ko ta tara dukiyar da ko mutane dubu zata dinga iya ciyarwa a kulli yaumin har tsawon wasu shekaru ba tare da ta durƙushe ba, saidai da ita Abunda bai sani ba, jinin talakan ne ta tsana, Sam bata so ta haɗa iri dasu kar su goga mata talauci. Tinda yayi hargagin yayi kuma barazanar bataji ba, ya san kuma aikin abokan shawara ne koma ince mazuga, tau ya san ta inda zai ɓullo ma Al'amarin nata. Lallashinta ya shiga yi gami da nuna mata cewa yana sane fa da zancen kuma zai ɗauki matakin da ya dace Amman ba abu bane ba gaggawa, karfa ta manta duka gidan akwai baƙi, tayi haƙurin zuwa goben idan sun bar gidan sai ayi mai yuwuwa, da haka ya lallaɓa ta, ta fice daga ɗakin tana mita, ita lallai atafau ba zata taɓa lamunta ba. "mama fa wallahi ya kamata kiyi wani abu, kina gani fa jiya Abunda yayi ma waccen shegiyar yarinyar a cikin jama'a har yana kiran ta matarshi, kuma naji ƴan uwan Alhajin sunce sun yadda da al'amarin ɗazu da ina gyara masu sashen nasu, gaskiya na fara sarewa da dukkan alamu ba zamu samu nasara ba.... " Mama talatun ce ta buge ma mareen baki, cikin ɓacin rai ta shiga cewa" Kiji ja'irar yarinya ke har baki ma kike mana? Kinsan sharrin da na ja mata kuwa? Ai dolenta ma su bar gidan daga ita har shegiyar uwarta, kuma wallahi ba zata taɓa wankuwa ba a wurin hajiya, Abunda yayi ɗazun ɗin ni ai burgeni ma yayi, bansan ina da sa'a ba sai ɗazu ɗin da ya kamo yarinyar gaban hajiya, wannan shi ke nuna cewa lallai suna aikata baɗalar kenan... " Mareen ce ta katse mahaifiyar tata cikin zaro idanu " umma ba dai sharri kika ja masu ba? Kada fa abun ya shafi masoyin nawa kuma mama, gaskiya ki sake dai, kije kice ba haka aka yi ba, yarinyar kawai ke da laifi.. " " Ke jiman shegiya ƴal banza.. Kina nufin in koma in ƙaryata kaina kenan? Ke wace irin shashasha ce ne? Kinfi son shi a kaina kenan? Tinda gashi har kina neman ki ja mani kora a cikin gidan nan, duk fa Abunda nake yi don ke ne... " " a'a mama kedai faɗi gaskiya, naira kike so dai kici, Amman ni wallahi banji daɗin Abunda kika yi ba har ga Allah, ai ba zan so ace ya taɓa kusantarta ba wallahi, Allah ma ya kiyaye, insha Allah nice nan zan ɓare Abunda dal a leda" Rankwashi mama talatun ta sakar mata a tsakiyar kai, ta kuwa dafe da ƙarfi tana cewa "wash, karki kashe ni mama ai gaskiya na faɗa, gaskiya ki canza wani tsarin dai" bata ce mata ƙala ba sai ma juyawa da tayi ta kwanta, sai kuma cen abun ya ɗaɗimo ta ta juyo tana ba ƴar tata amsa. "Tinda kince haka shikenan na ƙyale ki, kiyi da kanki, ai ina ce ko kuɗin muka samu tare dake za'a ci.." "A'a mama, ni da zan aure shi ai saidai ke ince maki za'a ci tare dake, saidai Abunda na wawuro inzo in ɗan lasa maki a baki don ki ƙara ƙaimin nemo magani" ta faɗa hankalin ta a kwance kaman ba mahaifiyarta take faɗa ma haka ba. (Hmmm Allah shi kyauta, inda akuyar gaba tasha ruwa....) Zaune yake yana ƴan latse latsen shi cikin computer, kaman ance ya kunna datar, ya kuwa kunna gami da shiga WhatsApp ɗin, sai kuma ya ajiye domin massages ɗin su gama shigowa ya gani in da waɗanda zai ma reply, domin da yawa wasu abokanan kasuwancin nashi ta online suke magana. Bilal kuwa yana zaune daga ƙasa bisa carpet ya tankwashe ƙafar shi ɗaya ya miƙe gudar, mug ne a hannun shi yana sipping cofee, ɗan sanyi sanyin Ac ɗin dake aiki ya sanya shi yake jin daɗin cofee ɗin, hannun shi riƙe da remote yana kallon wrestling a tashar MBC Action ɗin, lokaci lokaci yana ma Al'ameen ɗin magana da hankalin shi ya ɗauku ga aikin da yake yi, shima lokaci lokaci yana bashi amsa, duk da sai a daɗe bai tanka mashi ba. Rufe computer ɗin yayi gami da ɗaukar wayar, sannan ya ɗan zama bisa kujerar ya kishingiɗa, daki daki yakebin saƙon in da aka turo mashi, wasu yana basu amsa daidai da saƙon wasu kuma yana wucewa ko ma karantawa ba yayi masalan ma waɗanda ya san ba masu matuƙar amfani bane. Har ya wuce number ɗinta, sai kuma ya dawo ganin kaman ya san number ɗin, domin a wayar da numb ɗin tata take ba'a ita yake chat ba. Buɗewa yayi gami da dubawa Abunda yaga an rubuta kawai shine _*Yaya Result ɗinmu ya fito*_ Sai kuma wani hoto da yagani daga ƙasan Rubutun, buɗewa yayi gami da dubawa a tsanake. A hankali ya shiga faɗin "very good Suhan, Allah yasa ma abun albarka" Bilal ɗinne ya ɗago gami da kallon shi alamar magana kake yi. Baice mashi komai ba sai miƙa mashi wayar da yayi. Amsa yayi gami da dubawa " Wow, wacece wannan?" "Suhaaan.." ya bashi amsa, saidai shi kanshi bai san dalilin nashi na jan sunan haka ba. Da kallo Bilal ɗin ya bishi yana cewa "congrat" sannan ya miƙa mashi wayar yana sake faɗin "Gaskiya tayi ƙoƙari, zata iya samun duk course ɗin da take so" Jinjina mashi kai Al'ameen ɗin yayi yana mai yin typing wani abu ya tura mata, fuskar nan tashi ba alamun dariya fa, duk da yaga cewa tayi ƙoƙari kuma ya jinjina mata, gaskiya za'aje da ita, ga dukkan alamu tanada matuƙar ƙoƙari sosai. "Friend inaso muyi wata magana Pls, Amman inaso ka fahimce ni nima in fahimce ka" Bilal ɗin ya faɗa bayan ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar da Al'ameen ɗin yake kai. "gyara zama yayi alamar ina jinka, domin ya san duk lokacin da Bilal ɗin yayi mashi haka tau fa magana ce mai amfani. Ganin bai tanka ba kuma ya tattara dukkanin natsuwarshi a kanshi ya sanya bai damu ba da rashin tankawar tinda ya san hali, ya fara magana. "Bro bawai nace ka sauka akan bakanka ba ko kuma niyyar auren yarinyar cen don ka fidda su a halin da suke ciki ba, a'a na san kai mai biyayya ne ga iyayen ka, ka sani sarai mom ɗinka tana matuƙar sonka kuma tana ji da kai fiye da dukkanin sauran ƴaƴan ta, kuma tana son dukkanin Abunda kai kake so koda bata nuna maka ba, sai nake ganin wannan al'amarin tinda ta nuna bata so kuma bata goyon baya, mai zai hana ka dakata kagani har zuwa lokacin da zata yarda don kanta ta amince maka? Babba babba ne kuma yaro yaro ne koda kuwa ɗan giwa ne, bamu san Abunda ta hango ba, ba kuma kusan Abunda take hararo maka ba zuwa nan gaba, kuma inaso ka sani yarinyar nan dai ahe's innocent bata san komai ba, dukkanin Abunda ke faruwa ma in ka kalli fuskar ta zaka gane ba wai ta fahimta bane, in banda jiya da kayi Abunda kayi, yau kaga koda giccinta ne? Na tabbata wannan saƙon ma da tayo maka, bata da yanda zata yi ne, baka tinanin zata yi maka kallon mugun mai son raba su da inda suke cin abinci? Me mahaifiyarta zata ɗauka, wanne irin kallo kake so tayi maka? Baka tinanin zasuyi maka kallon kafi ƙarfin su ƙila dai kana da wani buri ne a kansu? Ka taɓa zama kayi tinanin haka? Yeah for sure na san kaman yanda mahaifiyarka ɗin take faɗa, lallai fa kafi ƙarfin wannan yarinyar, kafi ƙarfin aure ta ita ba sa'ar auren ka bace. Kasan baka buƙatar sai na tina maka kalar ƴan matan dake rubibi a kanka, Nidai shawara ta anan ka dakata da dukkanin yaƙin nan daka ɗauko ka saurari mahaifiyarka, lallai zaka ga nasara, Amman ba wai nace karka aure ta bane, saidai inaso tin wuri tin kana wasa, kada abun yazo ya kasance ya zama da gaske ka fara son yarinyar nan a ranka, abun sai yafi rashin daɗi" ya ƙarashe yana waiwaya wa ya kalli cikin ƙwayar idanun abokin nashi. Lallai ko Bilal ɗin bai faɗa ba zantukan nashi sun ratsa zuciyar abokin kuma aminin nashi, shiru yayi yana sauraren maganar da zata fito daga bakin shi. Nisawa Ya Ameen ɗin yayi yana Sauke wata gagarumar ajiyar zuciya, saidai ya kasa buɗe bakin shi balle yace wani abu. Lumshe idanu yayi a karo na biyu yana sake sauke ajiyar zuciyar sannan ya sauko ƙasa ya zauna yana fuskantar abokin nashi cikin ɗaki ya irin ta maza ya fara magana kaman baya so "Na fahimce ka abokina kuma nima na daɗe ina nazarn hakan, saidai zuciya ta ba zata iya jure ganin su cikin wani hali ba, su ɗin mutane ne masu tawakkali Amman inaso kayi mani wata Alfarma guda ɗaya" ya ƙarashe yana kamo hannuwan abokin nashi duka. Sannan ya ɗora da faɗin "bana so ina raɓarta nima, bana so ina jiɓintar al'amarin su sosai, gudun ja masu matsala, saidai ba zan iya jure ganin su a mawuyancin hali ba, inaso zamuyi masanyar aiki ne, zan je in cigaba daga inda ka tsaya, ni kuma inaso ka cigaba daga inda na tsaya, inaso in nisanci gidan nan gabaki ɗaya, inaso ka ɗauki alƙawalin kula dasu da karatun Suhan har zuwa gamawarta, ka riƙe mani alƙawali da amana" Cikin ɗan zaro idanu bilal ɗinmke cewa "Wat? Me kake nufi ne Friend? Kana nufin a kanta zaka bar ƙasar taka da mahaifn naka? Kasan ne kake faɗa kuwa? Jinjina mashi kai yayi alamar tabbatas da Abunda yake faɗa ɗin sannan ya ɗora da faɗin " Zuciya ta, ta fara saba wa da bauta mata, ta fara saba wa dajin ɗuriyar ta a kullum, ba zan iya jure zama a muhalli ɗaya da ita ba, ba tare da na kusanci inda suke ba, Nidai kawai inaso ka amince, gobe goben nan nake son barin ƙasar da asuba zan faɗa ma abba zanje yin wani abu, kai ne zaka cigaba da kula da komai, tini na daɗe ina wannan nazarn, wannan tasa na gama shirya komai yanda zaka fahimta" Ya faɗa yana jawo laptop ɗin tashi, gami da kunna ta ya shiga nuna ma bilal ɗin schedule ɗin aikin, duk da ya ɗan san wasu, saidai ayyukan da aka ƙirƙiro daga baya, "zaka gane abokina, kuma mu cigaba da waya duk Abunda baka gane ba, bayan auren yarinyar na maka alƙawari zan dawo kai kuma ka koma bakin aiki ka" Ɗan jim bilal ɗin yayi, sai kuma ya nisa yana cewa "Ba damuwa Al'ameen zanyi maka yanda kake so, nima na fuskanci gara tafiyar taka, akan ka zauna matsaloli su taru suyi yawa, gara ka tafi, ita kuma insha Allah ba zan taɓa bari tayi kewar rashin ka ba, zan kula da ita kaman yanda kake yi, harma da mahaifiyar tata. Ɗan murmushi yayi da iyakar shi leɓo, yana jin wani ƙuna daga cen cikin ɓargonshi, gani yake yi kaman yayi sallama da ita ne. Ya ƙudurta a ranshi cewa zai warware matsalar da ya sanya yarinyar da mahaifiyarta kafin barin shi ƙasar a gobe. Cikin daren yaba Bilal ɗin number ɗinta gami da goge ta a cikin wayar shi baki ɗaya yayi blocking ta yanda koda ta kira shi ma ko ta neme shi ba zata samu ba. A haka suka kwanta kowa jigum babu mai tanka ma wani. Duk da kafin su kwanta ɗin saida ya haɗa traveling bag ɗinshi, da duk abubuwan da zai iya buƙata. To dama dai ƙasar ba baƙuwarshi bace a, hasalima kamfanin da bilal ɗin yake running na Alhaji Mustapha ɗinne, wannan ne ta sanya komai zai zo da sauƙi baya buƙatar amincewar kowa. Bayan an taso sallar asuba ɗinne ya biyo mahaifin nashi har sashen shi, ganin hakan ne Alhajin ya san cewa da magana, sauraren shi yayi tsab, gami da fahimtar yaron nashi, Allah sarki ashe ma babu wata maganar soyayya ko makamancin ta a tsakanin shi da yarinyar, gamsuwa yayi da bayanin Al'ameen ɗin yayi da yace idan Allah ya bata miji kafin ya dawo kawai a aurar da ita ga wanda take so, kuma yana buƙatar ya gaya ma hajiya kubran cewa ya janye sukda daga nan sashen Alhajin wajen Hajiya kubran zai wuce. Addu'a da fatan nasara ya bishi da ita, yana mai faɗa mashi lallai kafin ya wuce yaje yayi ma kaka zuwaira sallama kuma duk ya jejje gidajen ƙannan nashi domin yaga muhallin nasu. Hajiyar ba wai ta yarda da maganar da yazo mata da ita bace, saida taga fa lallai shi da gaske yake yi, ba kunya ta rungume shi tana sanya mashi albarka gami da nuna mashi zallar farin cikin ta, harda irin abun nan na Munafurci take cewa "Allah sarki yarinya da har na ƙullace ta, to ai ba komai zasu iya komawa ma bakin aikin su in Alhajin ya amince" To shi dama burin shi kenan ya warware ƙullin da ya san duk kanshi ne ake ta wannan dambarwr, ko ba komai daga baya idan suhan ɗin ta gane dalilin tafiyar tashi zata sanya mashi albarka da gode ma bakin nasu da ba zai rasa abinci ta dalilin shi ba. Sashen nashi ya koma yana ba bilal labarin yanda sukayi da hajiya, sunyi mamaki kwarai matuƙa, oh shi kenan ashe shi talaka ba mutum baneba? Sai da ya kira yayi booking flight kafin gari ya idasa wayewa, aka sanar mashi sai ƙarfe biyar na yamma jirgin zai tashi, hakan ce ta sanya ya gane cewa yana da sauran time da zai gama aiwatar da dukkanin abubuwan da zai yi ɗin. Bayan na tashi ne na share ko ina na gyara, umman tawa ce tayi mani tuni da zuwa gidan Hafsat ɗin, hakan ce ta sanya ni kiranta domin tayi mani kwatance, ta shaida mani zata turo sadeeq ɗin ya ɗaukeni, ita da har ma tayi fushi, gashi afnan yanzu zata tafi gidan Aunty Saudat, za'a barni ni ɗaya, ƙawayen nata sakkon tafiya sukayi ha yar bata da kyau. Ƙarfe sha biyu kuwa sai ga sadeeq ɗin, umman tawa ce tayi mani a dawo lafiya gami da cewa in kula kada in kai marece, da to na amsa mata ina mai ficewa daga gidan. Daga nesa ya hango fitowarta har zuwa shiga motar tata, kauda kai yayi, baya so ya sake shiga Al'amarin ta tinda anyi Wancen ta kwaranye, bilal ɗin na kula dashi, dama tare zasu fita zuwa office ɗin tare suke da dogarawan da aka bashi, wanda yace duk kansu suit zasu sanya ɗaya daya iya mota ya dingabjannbilal ɗin ɗaya kuma ya zama massinger ɗin office ɗinshi kowanne zai biya shi albashin shi mai tsoka, aikuwa sunyi murna, kuma sun yaba da karamcin ubangidan nasu da kullum suke jin labarin tarin alkhairanshi ga mutane Office ɗin suka isa ya nunnuna mashi komai, sannan yayi mashi maganar ɗaukar matasa ƴan family ɗin sadeeq mijin hafsat ɗin, sannan suka wuce ya nunnuna mashi building ɗinshi na estate da aka kammala komai sai lounching da za'ayi, sannan ya kikkira manajojin shi na sauran kamfanonin da suke sauran jihohnn ya haɗasu da bilal ɗin ta yadda komai zasu tunkari bilal ɗin kai tsaye. Daganan suka wuce gidan Aunty Saudat bayan sunyi sallar azahar, sun matuƙar yabawa da tsarin gidan, gida ne tanƙamemen babu Abunda babu na kayan more rayuwa, cen suka tadda Afnan har yanzu akwai sauran mutane ƙawayen Saudat ɗin a gidan, daganan suka wuce tare harda Afnan zuwa gidan Aunty Nihal ɗin, Afnan kuwa tin a gidan Saudat take rigimar barin ƙasar da zai yi, sukda zai koma kusa dasu ne, kuma zasu fi saurin ganin shi anan, saidai bata so yayi ma suhan ɗin nisa, gani take yi idan suhan ɗin ta kucce mashi da wuya ya iya samun wata mai nagartarta, ita kau Saudat ɗin a take tayi murna, ko ba komai sun san waccen maganar ta wuce. Itama Nihal gidan ta yayi matuƙar kyau, kowa da kalar kaya ta wanda su suka zaɓosu da kansu, basu wani jima ba, saboda suna sauri ne, kuma itama akwai dangin mijin ta sosai a gidan kusan ma cike yake sosai da yake ita dangin shi suna zaune ne Abuja. Gidan hafsat ne na ƙarshe don haka daga cen zasu koma gidan yayi ma iyayen nashi sallama. Bamusan da zuwan su ba, da yake abokan sadeeq ɗin na gari yau zasu wuce suma, ya sanya na kama mata mukayi masu special girki ko ƙarasowa ba suyi ba sai ga su Ya ameen ɗin. Ko ba komai taji daɗin zuwan su, dama tana so ta ƙara yi masu godiya akan irin hidimar da suka sha da su da dangin mijin nata. Ceman tayi in shirya masu abinci, nace mata ban iyaka kunya nake ji, tace ai dole inji kunya na san Abunda muka tafka rannan, sai dole kowa ya gane kuna soyayya. Ƙyaleta nayi ban tanka mata ba, har ta gama shirya masu abincin, da sunce ba zasu ci ba, Amman jin ƙamshin girkin yasa bilal cewa ta zuba masu kaɗan, har yake tambayar ta ita kaɗai a gidan? Cemashi tayi mu biyu ne, baƙi zata yi ne ma Shiyasa Suhan ɗin tayi masu girki, don da ita cewa tayi sunsha lemo, Amman suhan ɗin tace masu akwai fa masu barin ƙasar ke kin yarda azo maku kara kubar mutum ya tafi da yunwa. Duk zubar da take yi Ya ameen ɗin na jin ta bai tanka ba, ya dai ɗan ci abincin, duk da test ɗin abincin ya mashi daɗi, saidai kuma bai san Abunda ya to kare mashi maƙoshi ba da ya hana shi walwala ayau. Hafsat ɗin ce take ta kawaici ganin bai nemeni ba duk kuwa da ta sanar dashi cewa ina gidan, ni kuma na kasa fitowa daga kitchen tin da ɗazu naga text ɗinshi yana tambaya ta wai ne ya hanani fitowa ɗazu? To ban dai bashi amsa ba tinda banda abun cewa ɗin. "Yaya ko in turo maka Suhan ɗin?" ta tambaye shi daidai lokacin da yake goge baki da ƴar tissue. "Ɗan kallon bilal ɗin yayi sannan yace" Ƙyaleta kawai Hafsatu Sauri mukeyi tafiya zanyi n.... "." Kirawo ta" cewr bilal ɗin da ya tari numfashi abokin nashi. "To tace gami da miƙewa ta shiga kitchen ɗin da nake tsaye zafi duk yabi ya isheni. " Kije inji Ya Ameen da Abokinshi" haka kawai ta faɗa tana mai juyawa zata fice Saurin jawo hannunta nayi ta dawo baya, cikin ɗan waro idanu waje na shiga cewa "Ke... Kina nufin a haka zan fita babu ko gyale jikina? Kalli fa skirt ɗina ya kama ni sosai... " To miye? Ba yayyenki baneba?" ta faɗa tana janye hannuwan ta gami da idasa ficewa ta ƙyaleni tsaye ina ta rarraba idanu. Ganin ba mafita kuma na kusan share minti biyar ya sanya ni shahadar fitowa Daidai lokacin da Al'ameen ɗin ya kai duban shi ga agogon da yake ɗaure a wutsiyar hannun shi na hagu "Kaga fa Malam idan ba zata fito ba mu wuce kawai kasan fa...." Maganar ta maƙale daidai lokacin da na fito ina ta matse matsen jiki da dukkan alamu ni kaina kunyar kayan nawa nake ji. Idanunmu suka sarƙe cikin na juna, ya kai kusan second biyar yana kallon a, lokaci guda ya janye idanun nashi ga barin kallon nawa, daidai lokacin ni kuma na kai zaune bisa kujera ina gaida su. A gaggauce suka amsa gami da tambaya ta lafiyar mu lau dai ko? Lafiya na amsa mashi, bilal ɗinne ke ƙara mani congrat na Jarabawa lokacin da Al'ameen ɗin ya kai kallon shi kaina yana mai cewa "Tafiya ta kama ni, ga Bilal nan ko me kenan sai ki tuntuɓe shi, zai gama maki komai insha Allah" yana gama faɗar haka ya miƙe yana shirin ficewa. Hafsat ɗince ta fito riƙe da wata jikkar kwali mai kyau a hannuwan ta, ta ƙara sa ga Al'ameen ɗin gami da miƙa mashi tana mashi fatan Allah ya tsare ya kiyaye hanya. Bilal ne ya maida kallon shi kaina shima yana mai miƙewa gami da ce mani "Ya bani number ɗinki insha Allah zan kira ki" ya ƙara sa shima yana mai juyawa ya fice. Har gaban danƙareriyar motar tashi da his excelency ya bashi ta raka su tana mai waving ɗinsu har suka fita a harabrr gidan da mai gadi ta wangale masu gate. Domin gidan na Hafsat duk yace ma na sauran ban wuri a kyau da haɗuwa. Hatta kayan da aka yi ma hafsat ɗin saida sadeeq ɗin ya cire su ya cenza mata wasu sabbi dal masu masifar kyau ba tare kuma da dangin shi kun sani ba gudun ƴan tsogunguma. A falin ta iskeni zaune jikina sanyi ƙalau, to me ke shirin faruwa ne? Nidai na san Al'ameen ɗin ba haka yake yi mani ba, na kula ma ko kallon a baya son yi a yau, ko na bashi haushi ne rannan dana ruga ɗaki? Ko dai banyi ƙoƙari bane...... "Ke Suhan lafiyarki ƙlau kuwa? Naga jikin ki yayi sanyi, da ɗina dake wallahi wani lokaci ke baƙauya ce, ko irin ƴar rakiyar nan ma baki Iya ba" Firgigit nayi ina mai binta da ido bansan lokacin da na samu kaina da tambayar ta ba "wai da gaske Ya Ameen tafiya zai yi?" "eah mana Suhan, waike da kina nufin baki sani ba? Bai gaya maki ba?" "Huh..." Na sauke ajiyar zuciya lokaci guda ina mai ce mata "wallahi ban sani ba Hafsat" Mamaki ta shiga yi, har tana zaulayar ta wai wannan wace irin soyayya ce?banza nayi mata ban tanka mata ba, Amman fa gaskiya zan faɗa jikina ya mutu murus wallahi. Su kansu ƴan kankiyan sunyi mamakin tafiyar, Amman da yake sun san yana yin aikin nashi sai sukayi mashi fatan alkhairi, sun ɗauka zuwan na aje a dawo ne. Ƙarfe biyar bilal ɗin ya kai shi airport ɗin, ba ɓata lokaci jirgin nasu ya ɗaga zuwa america..... #cying Wash gaskiya na gaji fans gashi nan nayi maku na kwana uku. ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~30~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Zaune yake cikin jirgin, saidai ya ma rasa tinanin da zai yi, gaskiya wani sashe na zuciyar shi na raya mashi yayi wauta, idan har sonta ne baiyi bai kamata ya baro ƙasar ba, sai yayi tinanin hanyar da zai warware ƙullin da shine ya ƙulla shi da kankin kanshi. Har jirgin su ya dira ƙasar ya kasa natsuwa a zuciyar shi, sai yayi kaman ya juya ya yanki ticket ɗin komawa sai wata zuciyar kuma ta hana, da haka dai har driver ɗin da zai ɗauke shi ya ƙara so bai lalubo mafita ba. Haka ko da ya isa zuwa gidan, komai a sanyaye yake yin shi, gani yake yi kaman yayi sallama da ita kenan. Shi me ma ya hau kanshi da har tinanin barin ƙasar yazo kanshi? Bayan ya san mahaifiyar ta Suhan tana da gagarumar lalura ta ciwon zuciya, me zai faru in tashi mahaifiyar ta cigaba da ƙuntata masu da gallaza masu? Meyasa ya baro ƙasar ba tare da ya gano munafikin cikin gidan ba mai ƙulla dukkanin makircin? "Ooops* Ya faɗa yana mai dafe kai, lokaci guda ya faɗa bisa tafkeken gadon da yake mallakin shi, tsuru yayi yana mai lumshe ido, kewar gidan har ta fara damun shi, saidai ya gaza gane kewar ta mecece, tin da mai yasa idan ya baro gidan baya jin irin wannan kewar? Waya ya lalubo gami da danna ma Bilal ɗin kira, ringing biyu kuwa ya ɗauka, shaida mashi yayi ya sauka lafiya, sannan ya ke tambayar shi sauran abubuwa. So yake ya tambaye shi suhan ɗin da ya san dai iyanzu bacci take yi domin idan ya kintata daidai yanzu zai kama kusan ƙarfe sha biyn dare a ƙasar tashi nigeria. Saidai ya kasa tambayar, ganin Bilal ɗin bacci yake ji sosai, ga dukkan alamu ma ya fara baccin ya tashe shi ya sanya shi datse kiran yana mai ce mashi zasuyi waya dasafe idan Allah ya kai mu. Shima Bilal ɗin da yake ya fara bacci bai wani ja ba, ya kashe wayar tashi yana mai tura ta ƙarƙashin fillow ɗin, shi kau ta ɓangaren Ya Ameen jifa yayi da wayar tinani fal a ranshi, ya rasa dalilin shi na tinanin ta har haka, to me ma ya hana shi tambayar abokin nashi ita? Saidai kuma fa yana tsoron kada Bilal ɗin yace bai fita sabgar yarinyar ba, gashi kuma har ya sanya shi zama ƙasar tashi domin ya taimaka masu. Jawo wayar yayi yana mai ɗan sakin ɗan ƙaramin tsoki, ji yake yi kaman yayi unblocking ɗinta ko status ɗinta ne ya dinga dubawa, saidai fa so yake yi ya manta da Al'amarin ta, so yake yi lokacin da zai koma ta riga da tayi aurenta ta yanda ma ba zai sanya ta a gaban shi ba balle yayi cousing wata matsalar tsakanin shi da tashi mahaifiyar. Saki wurga wayar yayi bisa gado yana mai miƙewa ya shiga tuɓe kayanshi, so yake yi yayi wanka ko yaji sauƙin Abunda yake ji a jikin shi da kuma zuciyar tashi, domin tinda ya baro ƙasar tashi tsikar jikin shi take a tashe ya rasa kuma dalili. Da haka ya wuce zuwa toilet ɗin zuciyar shi na raya mashi zuwa dasafe zai kira iyayen nashi domin su san ya isa lafiya. Ban san wa zan tambaya ba game da tafiyar Ya ameen ɗin ba, beside ma ni meye nawa a ciki? Ai yana yin aikin shi ne, ko yaje zai dawo ne, saidai na rasa dalilin da yasa nake jin zuciya ta ba daɗi sam, duk da yace Ya Bilal ɗin zai mani komai na dangane da karatu na, shima na kula yana da kirki don ma zance yafi Ya Ameen ɗin sakin fuska nesa ba kusa ba. Washegari da tafiya ta Yayan namu koda Afnan tazo mani da maganar cewa suma Yau zasu wuce ban ko wani damu ba sosai, bansan kuma dalili ba, saidai ta yiman Alkhairi kaman yanda ta saba, a bakin ta ma ne nake jin wai Ya ameen ɗin America ya tafi yin wani aiki, Amman wai ba zai daɗe ba zai dawo. To sun wuce dai, haka ma Hajiya Zainab da Alhaji Auwalun sun koma Katsinan da motar da dangin mijin Hafsat ɗin suka bata. Su Goggo Aisha ma da Goggo Fatima da iyalan su duk sun koma, tare suka tafi da ƙanen nasu watau Yaya Auwalun, sai ƴan biyu ne aka bari da Kaka zuwairan su sai ƙarshen sati za'a maida su. Kafin tafiyar Hajiya Zuwairan tayi ma Ummanmu sha tara ta arziƙi, ganin yanda umman tawa ta tsaya mata ka'in da na'in wajen hidimar bikin nasu, duk da ta san ba don abun duniya tayi ba, Amman saida ta bata maƙudan kuɗi da kaya sosai harda ni ma, fafur taƙi amsa har saida tace zata je ta gaya ma kaka zuwairan ne yasa ta amsa suma ba duka ba, a cewarta ai an zama ɗaya. Gidan ya koma shiru tsit kaman babu mutane, inda ma zaka ji hayaniya shine sashn kaka zuwairan da akwai ƴan yara ƴaƴan su Aunty Hassana da Hussaina ɗin, shima ba wani fita suke sosai ba, in Kaga sun fito to wajen wasa zasu su hau lilo. Hnakalin ummata ya kwanta ganin babu wanda ya kuma tada maganar da taji ɗin harma mutane sun watse kowa ya koma muhallin shi, bamu da matsalar komai ga kuɗin da ya Ameen ya bamu kwanaki basu ƙare ba, ga kuma sha tara ta arziƙi da Hajiya Zainab tayi mana, ya sanya hankalin mu kwance bamu da matsalar komai. Kullum sai umman tawa ta sanya ni naje sashn kaka zuwairan na gyara masu, to suma basu taɓa tada man wani zance ba, illa iyaka dai sanya mani Albarka da kullum suke yi tinda Alhaji Mustaphan ya gaya masu yanzu yana kan bincike ne su ajiye maganar gefe. Ta fannin Hafsat kuwa kullum muna waya sosai, har take sheda mani suma ƙarshen wata zasu wuce don Allah in zo kafin ta tafi, nan nake ce mata saidai yanda hali ya bada, domin yanzu kaman an zareman wata tsoka daga jikina nake ji na kuma rasa dalili. Duk da umman tawa ta kula da rashin walwalrr tawa, sai ta dangana hakan dankaɗaici, da ke damuna a kwana biyun ga kuma kwazzabar maree da nake fuskanta, ba damar in fita sai an yada man habaici ko an jefeni da kalma mai muni. Da su kaka zuwairan suka tashi tafiya, bansan inda ummata ta samo daddawa da kuka dasu kuɓewa masu kyau ba taba kaka zuwairan, aikau tasha Albarka kuma taji daɗin kyautar domin su tsofaffi ne basa yi saida tuwo. Har mot amuka rakasu da duka sauran ƴan gidan muma ɗaga masu hannu har suka fice. Alkhairi daɗi ne dashi wai wannan ɗan abun da ummata tayi ma mahaifiyar Alhajn saida ta faɗa mashi, aikau yana dawowa sai ga wata sha tara ta arziƙin ya aiko mana dasu jin daɗin kyautata ma mahaifiyar tashi da mukayi da kula da ita a ɗan zaman nata a cikin gidan wanda ko ita matar tashi ma bata yi saboda tsabar girman kai da jin ita ɗin wata ce. Mun samu sauƙi kam ta fannin hajiya Kubran sosai, kwana uku tsakani da tafiyar su Kaka zuwairan sai ga Mama Talatu da saƙo wai daga wajen hajiyar an maida mu bakin aikinmu. Ummanmu baiwar Allah sai jin daɗi take yi, tana kimtse kimtsen komawa bakin aiki, domin ita kanta Hajiyar ta sheda cewa Mahaifiyar tawa ta iya girki ba kaɗan ba, Sam basa jin daɗin girkin kukun nan masalan ma Alhaji. Lokacin da ta sheda mashi maganar son a maida mu aikin bai musa mata ba, sai a cewa yayi hakan yayi daidai. Nikau a cikin zuciya ta Sam banji daɗi ba gani nake yi kaman za'a daƙile mani maganar karatu na ne, saidai kuma a ranar ne sai ga kiran Bilal ɗin wai in miƙo mashi takaddun na, saboda ayyuka sun rincaɓe mashi ne ya sanya bai amsa ba saida ya gama daidaita komai a office sannan. Tambaya ta ya shiga yi bamu da matsalar komai dai ko? Babu kam na bashi amsa gami da juyawa na nufi cikin sashen namu, ko ba komai hankali na ya ɗan kwanta, naga alama kaman Bilal ɗinma zai tsaya mani kaman Ya ameen ɗin, to nima dai dama Abunda ya dameni kenan, bana son dukkan wani abu da zai yi mani katanga da cikar nawa burin. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Baya buƙatar tambayar abokin nashi komai akan lamarin karatun Suhan ɗin domin ko ba komai ya san amini nashi zai riƙe amana yayi mata dukkanin Abunda ya dace. Hakan ce ta sanya bai kuma tambayar shi ba akan lamarin nata, ko waya sukayi tau fa zancen da ya shafi kasuwanci ne da ma'aikata sai kuma Abunda ya shafi gida, tinda Yanzu Bilal ɗinne mai yin komai, shi ma Alhajin hidimarshi tasha kanshi da yawa sosai, gashi mai girma shugaban ƙasa ya bashi Ambasador a ƙasar ta Ƙatar, saboda yanda ƙasar take da arziƙin man fetur ya sanya yake ayyuka biyu ga aikin da yake yi ga kuma hidimar mai da ya shiga ka'inbda na'in nan fa likafa ta cigaba arziƙi ya linka nada, tini ya cema Hajiya Kubran ban wuri, duk da itama ba zaune takeba Business ɗinta kawai take yi hankalinta kwance. Hankalin Al'ameen ya ɗan kwanta tinda yau Bilal yayi mashi maganar an samu admission ɗin Suhan ɗin, tinda ya baro Nigeria ɗin yau tsawon wata biyu cikin na uku kenan Bilal ɗin bai taɓa mashi maganar ta ba sai yau, har ya fara tinanin anya kuwa yana yin alƙawalin da ya ɗauka? Saidai ya san dole ne yayi mashi uziri tinda ya san irin tarin ayyukan da suke gaban shi, wannan ce ma tasa Bilal ɗin ya roƙu su iyayen yarinyar da zai aura ɗin akan A ƙara mashi wata biyu ya gama settling duk wasu muhimman abubuwa dake gaban shi, lallai shi kanshi ya jinjina ma Al'ameen ɗin ga irin ayyukan da yake fama dasu kusan yana running kamfanoni kusan aƙalla bakwai a faɗin nigeria kuma yana da ma'aikata ba iyaka wanda kullum fama yake da tarin jama'a matasa da kuma ƙorafe ƙorafe su. Yaji daɗin jin wannan kalamn saidai shi inda yaso ta samu ABU zariya, sai gashi ba cen Allah ya cida ita ba, ansha daga da Umman akan nisan da suhan ɗin zata yi da ita kuma ba mai kula da ita ce sai Allah, Bilal ɗinne ya tausheta yace ta bara Allah ɗin, atafau tace ita in karatu ya wuce nan Abujan ba zata yarda ba, dole tasa ya kira Alhaji Mustapha saida fa yace mata zai sa masu kula da ita ne yasa ta yarda saboda ganin girman Alhajin, Amman shi Al'ameen Sam baisa baki ba ganin Alhajin nashi ya sanya, kai shi fa tinda ya tafi bai ƙara ji daga garesu ba, dama Suhan ɗin ba number ɗin shi ta cen ƙasar take da ita ba, balle ta kira ta samu, ko a WhatsApp ɗinma ta dena ganin ɗuriyar shi sai ta bar ma kanta cewa ayyuka ne sukayi mashi yawa in ba haka ba ai Al'ameen ɗin na wajensu ne, ta san haka kurum ba zaiƙi sanya baki akan a shawo kan umman tata ba. Hafsat tini sun wuce, dakyal na samu naje mata sau ɗaya tin bayan bikin. Nima yanzu abubuwa sunyi mani yawa shirye shiryen tafiya makaranta ta nake yi, bani da matsalar komai, saidai kula da nayi har yanzu umma ta jikin ta baya bata tafiyar tawa, idan na lura da hakan nima jikina kanyi sanyi, albarka nake so ta sanya mani ba wasu wasu ba, hakan ce ta sanya na zauna na nutsar da ita a hankali, tau ta dai ɗan saurareni kuma ta ɗan fahimce ni harma addu'a tayi man da fatan samun nasara akan Abunda zanje nema ɗin, kunsan a koda yaushe addu'ar iyaye itace abun so ga ƴaƴan nasu ba addu'ar banza ba ko Kaga uwa tana ta ƙunduma ma yaron ta ashar tana la'antar shi cikin zagi kuma tana so ace ya girma yayi albarka kuma ya jiƙanta ya sota, ai da wuya Kaga uwar da take la'antar yaron ta kuma ya girma yayi albarka, saboda addu'ar uwa ƙarɓaɓɓiya ce ba shamaki. A kulliyaum sai Nihal tazo gidan nan, itace bata tafiya sai dare, kai in taƙaice maku tin bayan bikin nata da kwana biyu ta fara sintiri a cikin gidan, kuma Hajiya Kubran na kallon ta, ta kasa kwaɓa mata, a cewarta ai ba kurkuku ta kai yaran nata ba balle ace ba zasu fita ba, Saudat ɗin cema mai yin kwana biyu bata zo ba, Amman in ta kama suka zo ɗin har kwana suke yy. Ba wadda bata da jarin kanta take juyawa, hasali ma yanzu duk kansu suna aiki ne a wasu kamfanoni da aka buɗe suna jagorantar shi, saboda ɗimbin ilimn dake kansu, da yake Allah yayi ma yaran na Alhaji Mustapha ƙwaƙwalwar, Abie Kuwa tini ya koma ƙaro karatu cen ƙasar ta america tare suke da Al'ameen lokuttan da baya da lecture ya kan bi Ya Ameen ɗin Office yana taya shi ayyuka. Bikin Bilal ɗin ya matso, duk a gidan su Ya ameen ɗin ake komai, saboda shi iyayen shi ba anan ƙasar suke zaune ba suma, babu Abunda ba'a aiwatar ba na Al'ada, nayi mamaki da ya Ameen ɗin bai zo ba, bashi har ina daf da tafiya makarantar. A cikin estate ɗin da 'ameen ya gina wadda ya sanya Bilal ɗin yin lunching ɗinta kwanaki ba daɗewa ya ajiye matar tashi, Ummi ɗin yarinya ce mai hankali sosai da sosai, ga fara' a da son mutane kaman mijin nata, lokutta ya kan roƙi umman tawa akan ta barni inje gidan nashi wajen matar tashi, da yake yanzu sun saba da ummata sosai harma dani ɗin, na ɗauke shi kaman ya yana ne komai idan ina da buƙata na kan tunkareshi kai tsaye ne, ba don kar ace nayi butulci ba sai ince yafi Ya ameen ɗin daɗin mu'amala, domin shi akwai sakin fuska da faram faram, ba kaman Ya ameen ɗin ba da lokutta da dama magana ko murmushi ma sukan yi mashi wahala, duk da ba wai yafi Al'ameen ɗin kirki bane da hangen nesa. Mun saba da Ummin Matar Bilal ɗin domin idan tazo kusan ma ince sashen mu take yini, saboda Hajiya Kubran yanzu bata cika zama ba, sai mu yini muna fira, har kitso na kan yi mata wani lokaci da yake na iya, sai kusan marece mijin nata kanzo ya ɗauke ta. Wani abu ɗana kula dashi shine, yawan zuba man idanu da Ya Bilal ɗin kanyi lokutta da dama, masalan ma idan ya tadda ni ba hijab, gashi ni kuma ganin sabon d a mukayi dashi ne ya sanya ni bana ganin hakan a matsayin wani abu, ashe ban sani ba kuskure nake yi, ɗana kula da hakan ne sai na fara janye jikina ko in sanya hijab idan ya shigo ɗakin namu, ko gidan shi na rage zuwa, shima bansan dalili ba sai naga ya rage kawo Ummin tashi gidan namu. Ban damu da hakan ba, illa iyaka dai bana yarda wani abu ya haɗa mu, ko maganar shirye shiryen makaranta ta ni nake yin abuna bana tsayawa jira, Tinda yanzu ina ɗan samun kuɗin aiki na, kuma an koma bamu abinci a gidan. Ko ya kula ne shima? Sai naga duk ya sha jinin jikinshi, sai dai fa a zuciyar shi wani abu kan bijiro mashi a duk lokacin da yake tare da suhan ɗin, ba don yana so ba, tinda sai a yanzu ne ya ƙara yarda d a maganar Abokin nashi, Suhan ɗin nada wasu abubuwa da suke kaman maganaɗisu ga maza, duk namijin da zai ɗora idanu akan fuskar ta to fa abun nan zai ja shi har zuwa gareta. Sau da dama abokan shi kan mashi maganar Suhan ɗin saidai bai san dalilin shi na rashin ba maganar tasu muhimmanci ba. *************************** Ƙarfe takwas a rabi na safiyar ranar Litinin ɗin da ta kama itace ta ƙarshen wata, wayar Bilal ɗin da take ajiye bisa side drower ce tayi ƙara, Ummi ce ta ɗaga ganin sunan da yake jiki *Friend* taga an rubuta, cikin sallama ta kara wayar a kunnen ta. Daga cen ɓangaren aka amsa mata cikin sakin fuska da gani fara'a mutumen dake wayar da ita yakeyi "Friend ya kike? Ina angon naki ne? Ko har yanzu bai tashi ba? Cikin dariya itama ta mayar mashi, yau kam abun nashi ya bata mamaki wai Al'ameen ɗinne yau da zaulayarta haka? " Ya tashi Ya Ameen yana toilet ne yana wanka, ya aiki?" " Lafiya lau Pls idan ya fito ki faɗa mashi ya kira ni" daga cen ɓangaren ya amsa mata, to tace mashi tana mai bashi saƙon gaisuwa ga ameen ɗin. Baisan dalili ba, yau kam hakanan ya tashi da kewar gida, duk da suna waya da sauran ƴan gidan har ya kan tambayi mudi driver Lafiyr umman suhan ɗin, Amman ita ko da alama bai taɓa tambayar ta ba. Saidai yau ba zai iya jurewa ba, tin cikin daren ne tinanin ta ya matuƙar damun shi, sai mafarkai marasa daɗi da yake yawan yi kwanakin nan, shi kanshi ya rasa dalilin son tafiyar tashi ƙasar tashi. Amman gaskiya bai jin zai iya tsallake yau bai bar ƙasar ta amurkan ba. A hannun Abie yanzu da ya riga ya ƙware da komai ya bar office ɗin, har ya haɗa jikka sai kuma ya koma ya zauna ya kira aminin nashi, fuskar shi babu walwala Sam, saidai wani fari daya ƙara, fatar nan ta murje kaman bature don in ba hausa kaji yayi ba babu Abunda zai hana kace mashi ba'indiye, ga gashin nan baƙi siɗik daya kwanta mashi har ƙyeya, ba aski kanshi saidai gyaran fuska. Sanye yake cikin lallausan yadi ɗan ƙasar Turkiyya mai walwali anyi mashi ɗinkin gudluck, Al'ameen ɗin mutum ne mai kwarjini da haiba, duk wanda ya kalle shi sai ya sake waiwaya wa ya kalle shi. Wayar shi ne da take cikin aljihun gabar rigar tashi ta ɗauki tsuwwa, ƙirar iphone 11 pro max ce da ko ƙasar tamu ta nigeria bata kai ga shigowa ba, sai faman tallar ta da ake tayi. Ɗagawa yayi gami da cewa "Friend how far?" Bilal ɗinne ya shiga cewa "Shegen kaya, kayi wuyar ji fa mutumena, na san ayyuka ne sukayi maka yawa" "Wallahi kuwa, Amman gani na shirya yanzu zuwa Nigeria nan da ƙarfe uku kazo ka ɗaukeni, domin yanzu haka kai tsaye airport na nufa" "Wat?". Bilal ɗin ya amsa mashi ta ɗaya ɓangaren bai tsaya jin me zai ce mashi ba ya cigaba da faɗin "Gaskiya bakayi shawara dani ba da ban barka kazo ba, yanzu haka kana dawowa komai zai kwaɓe bros, ina mai baka shawara, gobe ne Suhan ɗin zata tafi makaranta, ka bari har sai ta tafi sannan kazo, kasan yanzu abubuwa sunyi masu sauƙi sosai, sanin da Mom tayi yanzu baka nan, yarinyar na shirin ta a tsanake, domin yanzu babu damuwar komai a ranta, Amman fa ni a ganina" Shiru yayi ta cen ɓangaren, sai kuma lokaci ɗaya ya koma ya zauna, yana mai sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi har saida Bilal ɗin ya jiyo shi, dafe kanshi yayi, lallai fa shi wannan abun ya fara damunshi, yana buƙatar yaga kowa nashi, kusan yanzu wata bakwai kenan fa, lallai ashe ya yaudari kanshi da har yake tinanin sai Suhan ɗin ta gama makaranta tayi aure sannan zai dawo, sai gashi ko tafiya ma batayi ba ya fara kewar su. Jin da Bilal ɗin yayi Al'ameen ɗin yayi shiru, ya san ya yarda da maganar shi tankawa ne kawai ba zai yi ba, ya sanya shi shiga lallashi shi, saidai fa shi a ganinshi Al'ameen ɗin na zuwa zai dagula komai, gashi yanzu baya son duk wani abu da zai taɓa mashi suhan ɗin tashi duk da ya kula da janye jiki da take yi dashi. Kuma tabbas ya san yanzu Al'ameen ɗin nayin arba da ita mikin dake cikin ranshi zai tashi ne, domin yanda hankalinta ya ƙara kwanciya, ta sake yin ɓul-ɓul da ita, ga kyaun ta daya ƙara fitowa a fili, yana so ne ya kafa gwamnatin shi gareta duk da ya san abu ne mai wahala a yanzu kam har sai ta fara karatun nan tukunna, domin yanzu ita karatun ne gabanta. Bai ƙyale shi ba har saida ya tabbatar ya kwantar mashi da hankali sannan ya kashe wayar, shi kau Al'ameen ta ɓangaren shi zama wa yayi ya kwanta rigingine kan bayan shi, ya rasa dalilin shi na amincewa abokin nashi, ya rasa kuma me ya hana shi gaya mashi hankalin shi ne ya kasa kwanciya, gani yake yi kaman wani abu zai same su, duk da Bilal ɗin ya shaida mashi cewa yanzu komai lafiya lau? Baijin zai sake fita ko ina, kallon shi ya kai kan jikkarshi da take ajiye gefe wadda ya haɗa ƴan abubuwan buƙatar shi, ji yake yi kaman ya tashi ya tafi, Amman wata zuciyar na bashi cewa yabi shawarar abokin nashi, da haka har wani ɗan bacci ya sure shi a wurin yana saukar da ajiyar zuciya a hankali. Bilal ɗin na kashewa ya cigaba da shirin shi, ummin dake zaune bakin gado ce ta kalle shi cikin rashin jin daɗin barin abokin nashi yazo yaga iyayen shi. "Nikau dear sai inga kaman ka basshi yazo ɗin, alabasshi ko kwana biyu sai yayi ya koma hankalin shi dai zai kwanta atlist" Baibar Abunda yake yi ba ya shiga bata amsa "ba zaki gane ba ne cwthrt, a halin da ake ciki yanzu yarinyar bata buƙatar zuwan shi, shi kuma ya fake ne da iyayen nashi Amman a zahirin gaskiya zuwan nata ne, ni kuma ba zan lamunta ba ya dagula lissafin bayin Allah, yayi haƙurin har ta tafi" nan ne yake faɗa mata duk halin da suka shiga cen baya da dalilin tafiyar Al'ameen ɗin american. Ajiyar zuciya ta sauke tana mai cewa Allah ya zaɓa mata Abunda yafi zama Alkhairi a Rayuwar ta, da ameen ya amsa mata har yanzu yana mai ɗaura links a hannun shi, saida ya gama ne sannan ya ɗauki briefcase ɗinshi ya fice. Har bakin ƙofa ta raka shi, saida taga fitar shi ne sannan ta juya zuwa cikin gidan tana mai tausaya ma Suhan ɗin. °°°°°°°°°°°°°°°°°°° Shiri na nake yi hankali kwance, na gama haɗa komai, saidai fa akwai Abunda yake muntsili na a zuciya, tinanin Ya Ameen ya dameni cikin kwanakin nan, ba waya ba aike ba saƙon gaisuwa? Saidai wani lokaci idan na tambayi mudi yaceman suna waya, ko da na amshi numb shi In kira shi in gaya mashi batun karatun nawa da inda na samu admission da Abunda zan karanta duk da shi ya zaɓa man tin wajen cike jamb, ban same shi ba, na kira sau ba adadi shiru, hakan ce ta sanya na haƙura duk sanda Allah ya kawo shi zan faɗa mashi baki da baki, tinda ba wai don Bilal ɗin ya gaza bane ta kowanne fanni. Kwanaki ne ummata taje ma da Hajiya Kubran maganar tafiyata makarantar, bata hana ba Abunda ya bamu mamaki kenan, saidai tace Albashi zai dakata da shiga har sai lokacin da na koma bakin aiki, ummata bata da zaɓi illa iyaka ta amince, ta taimaka mani wajen shirya komai ta yi tana mani wa'azi da faɗan in kama kaina inyi Abunda naje nema, banda shashanci banda kula ƙawaye barkatai banda kula samari. Karatu shi ya kai ni shi kuma zanyi. Yau Bilal ɗin bai zo gidan namu ba, saidai ya kirani akan cewa in shirya gobe zai zo ya kai ni da kanshi, umman tawa zata rakamu, Naji daɗi har na gaya mata, to itama ɗin ta amince da hakan saboda tana so taga inda zanje koda Allah zai sa ta buƙaci zuwa wata rana ta subani. Har dare yayi ina ƴan tattare tattare na, ita kuma ummata tana kwance tana kallona har take bani wasu ƴan labari, kewar ɗiyar tata na tsira mata a cikin rai, tana jin kaman tace ta fasa, saidai ba zata iya yin wasa da Rayuwar ɗiyar tata ba. Kaman an zabureta naga ta tashi, ba tare data ceman komai ba, naga ta zari hijabin ta ta fice, ban kawo komai a raina ba, har na gama na koma na kwanta, bansan lokacin da ta shigo ɗakin ba domin bacci tini yayi awon gaba dani. Da asubar farko kiran sallah ya tashe ni. Da mamaki nake bin ko'ina na ɗakin da kallo. Komai namu an tattara shi guri guda hatta da kayanmu duk an ƙuƙƙule, bokitan mu duk an rafke su guri guda, katifar da nake kai ce kawai ta rage, itama ina tashi ta jingine ta. To me hakan ke nufi ne? Lafiya kuwa? Tambayar kaina na shiga yi, ganin tana ta ƴan haɗe haɗen kaya ne nayi shahadar murtsike idanuna na shiga tambayar ta. "umma lafiya kuwa?" ina zamu ne naga kin haɗa kaya duka? Bata tanka mani ba ko alama, ko kallona ma batayi ba, tambayar ta na cigaba da yi, kaman ina magana da kurma. Sallama najiyo daga bakin ƙofar ɗakinmu, ban tantance muryar wanene ba, sai Naji ana cewa" Maman Suhana wai dreban ya iso, ku fito" to tace gami da cewa "muna zuwa" bata bi ta kaina da nake tsaye ba mamaki ya kashe ni na kasa tankawa, ta shiga kinkimar kaya zuwa wajen, ta dawo ta ƙara kwasa, to dama kayan ba wasu yawan kirki ne garesu ba, hakan yasa tini ta fice dasu tas, illa katifa da take ba mallakin mu ba, kai hatta da kayan ɗana haɗa na tafiya makaranta yau ta fice dasu zuwa motar. Ban abune ba, naji ta kama hannuna, zan ƙwace hannuna ne in ƙara jefa mata tambaya, naga ta juyo tayi mani wani irin kallo, sannan tace "Nan gidan ubanki ne?" Ƙwalalo idanu na shiga yi, tinda nake ban taɓa jin irin wannan kalmar a bakin ummata ba, ai bansan lokacin da na girgiza mata kai ba, na shiga binta kaman wadda aka zare ma lakka, har zuwa lokacin da muka fita gare ɗin, mai gadi na kallonmu yana ta yi a umman tawa magana ko sauraren shi batayi ba, ta danna ni cikin mota data kasance ƙirar bus mai cin mutum goma. Itama shiga tayi gami da zama, ba tare da ɓata lokaci ba tace ma dreban "Muje Malam" Baiyi wata wata ba ya tada mota gami da danna ta da gudu muka bar cikin unguwar motar sai wata irin ƙara take saki. Daidai lokacin ne ni kuma na haɗe kaina da guiwa ta gami da sakin wani irin kuka mai matuƙar cin rai.... *Ya Rab wannan wace irin Jarabawa ce take bibiyar rayuwa ta ni Suhan? Shikenan kuma nayi bankwana da cikar buri na, nayi bankwana da Ya Ameen, nayi bankwana da Afnan, nayi bankwana da Ya Bilal ɗin* Ai bansan lokacin da na ƙara rushewa da kuka ba kaman raina zai fita a jikina.... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~31~* Motar na ta faman sharara gudu da burari irin na babbar mota, yayin da ni kuma kukana yake daɗa lunkuwa, tin inayi da dukkanin ƙarfi na har muryar ta dusashe na koma share kwalla kawai, idanu na kuwa sunyi luhu luhu sai faman raɗaɗi suke yi mani. Ummata bata ko kula ni ba, sai ma faman sakin tsoki take yi a hankali a hankali, kaman yanda shima dreban ya dage sai bama mota wuta yake yi. A hankali gari ya soma wayewa, rana ta soma hudowa ta gabas, har wajajen ƙarfe takwas Nidai ina nan dunƙule a kujerar tsakiya tinda ta cen baya an cika ta da kayanmu. Ban aune ba naji an jefo mani leda gami da robar nutri milk, tini dama muna dasu a ɗaki, tinda aka fara hidimar biki Hajiya Zainab taba ummata su da yawa, to da yake ba wani sha mukeyi ba, har ma gara ni domin ummata ko sau ɗaya bata kashi a bakin ta ba. Na san shine yau ta fiddo mani, bredi ne a cikin ledar, tin da na buɗa na gani, na ajiye shi gefe ban kuma bi ta kanshi ba, dreban lokaci zuwa lokaci ya kan yi parking ya duba motar, yayin da har kusan ƙarfe uku muna tafiya, salla kawai muka tsaya yi. Har yanzu ban ɗauki bredin naci ba, shi kau dreba saida ya siya shinkafa da wake ya afa lokacin da muka tsaya salla a wani ƙauye da bana ce ga sunan garin ba. Itama ummata har yanzu ban ga ta sanya komai a bakin salatin ta ba, saidai lazumi da take ta faman yi ko kallon a ta ƙiyi. Da naga ba sarki sai Allah ne bansan lokacin da na jawo ledar da gorar madarr ba na shiga kwankwaɗa, bata ko kula ni ba illa ma taɓe baki da tayi ta juya abun ta. Ƙarfe takwas a cikin gidan tayi mashi, saida ya leƙa ya gaida hajiya sannan ya wuce sashen Alhajin domin gaida shi ya faɗa mashi yanzu zasu wuce makarantar ta su Suhan ɗin da yake kyautata zaton ma jirgi zasu bi domin su isa Kaduna daganan su wuce zariyn kai tsaye. Addu'a yayi mashi da fatan dawowa lafiya, sannan yace suzo shi da yarinyar yana son ganinta. Hakan tasa ya wuce kai tsaye sashen na su Suhan ɗin. A tsai tsaye ya tadda dukkanin ma'aikatan ana ta maida yanda aka yi, maree na gefe taja ta tsaya sai faman taɓe baki take yi tana ta faman jijji ga jiki murna fal a ranta har fuskar ta saida ta nuna. Da ɗan sauri ya ƙara sa garesu yana tambayar su lafiya kuwa? Gaida shi suka shiga faman yi, bai ko amsa ba domin hankalin shi ya matuƙar tashi, ga dai dukkanin ma'aikatan gidan mata Amman babu su Suhan ɗin. Maida duban shi yayi ta ɓangaren da ɗakin namu yake, aiko ya hango shi haihan, babu ko tsinke ciki in ka ɗauke katifa da take jingine. Da ƴar sassarfa ya isa wurin kaman zai tashi sama, lelleƙawa yayi ko ina sannan ya dawo inda suke tsaye, mamaki da tashin hankali kwance kan fuskar shi yake sake tambayar su ina suka je? Mama talatin ce cikin halin ko in kula ta shiga cewa "wallahi yallaɓai muma bamu san ina suka je ba, haka muka tashi muka ga ɗakin, hasali ma ko fitar su bamu gani ba" Cikin ɗaga murya ya dakatar da ita... "Ne kike nufi da hakan mama? Ba kece shugabar su ba? Zasu fita ne ba da saninki ba? Anya ko kina yin aikin ki yadda ya dace?" Bai ko jira amsar da zata bashi ba ya juya a sukwane ya bar sashen, kaman zai kife ya nufi bakin gate, domin dai babu yadda za'ayi ace sun fita mai gadi bai sani ba. Ya kuwa ci sa'a duk mazan sun firfito sun fara aikinsu, tin daga nesa yake kwala ma maigadin kira, kaman zai tsuntsuwa ya isa inda yake zaune riƙe da radio a hannun shi ya karata a kunne yana ta faman saurare yana gƴaɗa kai. Daga nesa ya jiyo muryar abokin mai gidan nasu yana ta faman kwala mashi kira gashi kuma yana nufi inda yake. A hanzarce ya tashi gami da nufar inda ya hango Bilal ɗin na tahowa. "Gani Yallaɓai, Allah dai yasa lafiya" ya faɗa yana mai isa ta inda Bilal ɗin yaja tunga ya tsaya. "Ina su Suhan?" Tambayar da ya jefa mashi kenan cikin hargagi da ɗaga murya. "Yallaɓai wallahi tin asuba suka fita, ba yanda banyi dasu ba su tsaya, don ita Yarinyar ma kuka take yi lokacin da uwar tajata suka bar gidan domin....." " *MMe?" "Me kake faɗa ne haka da hankalin ka, me yasa kabarsu suka fita ba tare da sanin kowa ba, kasan aikin ka kuwa? Meyasa baka tada kowa ba ko kaje ka faɗa cikin gidan?" Ganin yanda Bilal ɗin ya hayayyaƙo mashi kaman zai bigeshi ne ya sanya shi fara rantse rantse gami da zuƙunnawa ƙasa, daidai lokacin ne sauran ma'aikatan da matan duka suka firfito suka tsaya suna kallon ikon Allah Bilhaƙƙi da gaskiya Bilal ɗin ke shrfa bala'i wa maigadin da mama talatun da yace duk basusan aikinsu ba, su ajiye aikin nasu domin bayada amfani. Sai kaiwa da komowa yake yi daga wajen mai gadin zuwa inda mama talatun take tsaye kanta duƙe hankalin ta kuwa a matuƙar tashe taji ance ta ajiye aikinta. Ƙarasowar Alhaji mustaphan ne ya dakatar da Bilal ɗin daga masifar da yake balbale su da ita. Alhajin yayi matuƙar kyau cikin shadda fara dakakkiya anyi mata ɗinkin babbar riga da hula dara a kanshi, da alama dai fita yakeson yi, dama shi baya jiran dreba ya tuƙa shi, cewa yake yi ayyukan shi da hulɗoɗinshi na buƙatar sirri, ba ko ina bane idan zai je yake buƙatar a sani saboda insecurity na ƙasar tamu. Tambayar Bilal ɗin yake yi me yake faruwa ya gansu cirko cirko haka tsaye, bayan shi yana cen yana fama jiran zuwan Bilal da Suhan ɗin da yace yana son gani. Nan kuwa Bilal ɗin ya shiga zayyane mashi Abunda ke faruwa, idanun shi kuwa sun kaɗa sunyi jajur, ga dukkan alama ko ina su Suhan ɗin suka tafi basu da niyya ko alamar dawowa, shi ya ma zai ce ma Abokin nashi da ya bar mashi amanar su? Me yasa ya hana Al'ameen ɗin tahowa a jiya? Me ma ya sanya su barin gidan, bayan har yana murna ganin yanzu sun fara samun sauƙi a zaman gidan? Shima Alhaji Hankalin shi ya matuƙar tashi, a karon farko a Rayuwar shi da yace a nuna mashi ɗakin nasu ya gani, Bilal ɗinne ya wuce gaba Alhajn na biye dashi a baya, cikin sauran ƴan aikin kuwa babu wanda yayi alamar motsawa ma balle ace su bisu, jikin su duk yayi sanyi, yau sunga tashin hankalin da basu taɓa gani ba, wai sauƙin ta ma ace Al'ameen ɗin bai nan da duk sunyi imani yau ƙarshen aikinsu yazo a gidan. Hatta da maree ɗinma hankalin ta a matuƙar tashe yake, an sallami maman tata a nan take kuma? Saura ita in har asiri ya tonu na irin abubuwan da suke yi ma su Suhan ɗin. Ta kuwa san maman tata sarai wajen shegen son kuɗin tsiya, yanzu idan taji sallamar ta tabbata zata tona masu asiri ne, hakan kuwa zai iya shafar nata aikin da take matuƙar so. Yanzu in tabar nan gidan ina zata dosa? Gashi dai tini ta san bata da mahaifi balle ace ta nufeshi hakan ta ta taso a rariya, sai daga baya ne data gano inda maman tata take shine fa tazo aka yi kutun kutun da aka sama mata aiki a gidan ba tare da kowa ya san alaƙar ta da mama talatun ba. Mamakin Alhaji Mustaphan ya daɗa lunkuw ganin ɗakin ƙwalam babu komai ciki, gashi dai tsaftsaf kaman ba'a taɓa rayuwa ciki ba, cikin al'ajabi ya juya ga Bilal ɗin da yake ta faman leƙe-leƙe gani yake yi kaman fa zai hango su a wani saƙo na ɗakin laɓe. "Ka kuwa kira layin su?" Alhajin ya faɗa yana mai kallon Bilal ɗin da yafi kowa rikicewa, tsoron shi ɗaya kada abokin nashi yace saboda haka ne ma ya hana shi tahowa jiya daya buƙaci zuwan, tsoron shi ɗaya kada Al'ameen ya zarge shi akan shine dalilin shi na rabuwa da Abunda ya san yana so, kuma yake da burin taimaka masu, to ina alƙawalin da ya ɗaukar ma aminin nashi? Zai ce ya yaudare shi ne gashi ta dalilin shi sunbar gidan. Tinanin haka da yayi ne ya sanya shi zaro wayar shi daga aljihu, hannun shi na karkarwa ya danna kira zuwa ga Layin Suhan ɗin, saidai fa not reachable ake daɗa faɗa, yana share zuba da take daɗa tsattsafo mashi yana sake kira, kaman ya kurma ihu haka yake ji, Rayuwar shi kaf ta gama ɓaci ayau, lallai mutanen nan biyu zasu bar gidan nan ayau muddin ba'a gano inda suka tafi ba, a ganin shi ai basu san aikinsu ba. Alhajin ne daya kula da yanda hankalin Bilal ɗin ya tashi, kamo hannuwan shi yayi duka biyun yana kwantar mashi da hankali gami da gargaɗar shi kada a gaya ma kowa wannan maganar dake waje, ciki kuwa harda Al'ameen ɗin da tin safe ya kira shi a waya cewa lallai fa ayau ɗinnan zai taho domin jikin nashi yana bashi ba daɗi, Allah sarki bawan Allah, dama Alhajin koda shi Al'ameen ɗin ya faɗa mashi ba soyayya tsakanin su bai yarda ba, sai gashi kuma ta tabbata, so da kusancn da zuciyar shi take da tata ya sanya jikin shi yake gaya mashi lallai fa wani gagarumin abu zai faru ayau ɗin Shiyasa ya matsa da tahowar. Hannun Bilal ɗin yaja yana faɗin yazo suje wajen hajiyar yaji ko tan ada masani yar barin gidan nasu Mama Maryam ɗin, domin shi fa jikin shi na bashi harda sa hannun Hajiya Kubran wajen tafiyar tasu. Domin yasan ko wacece matar tashi, in ta tsani abu, tau fa sai taga ta rabu dashi hankalin ta zai kwanta. **************************** Wayar ta ce ta shiga burari alamar kira ya shigo, cikin barci ta sanya hannu da niyyar latse wa, saidai ganin mai kiran ne ya sanya ta tashi zaune sannan ta ɗaga. Daga ɗaya ɓangaren aka yi ta magana, yayin da ita tayi shiru tana ta faman ɗaga kai, alamar gamsuwa da maganar da ake faɗa mata. An kusa minti biyar ana maganar daga cen ɓangaren, lokaci guda Hajiya Kubran ta saki wata shu'umar dariya tana ɓaɓɓakewa da muguwar dariya cikin isa, har ta zuro ƙafafun ta daga bisa gadon gami da miƙewa ta nufi window ta zage labulayen da suke masu matuƙar kyau. "Allah ya raka taki gona, kin biya ni Hajiya Sa'a, don haka ki saurari tukuicin ki zuwa anjima" Abunda ta faɗa kenan ta datse kiran, hango Alhajin nata da tayi riƙe da hannun Bilal sun nuof sashen nata cikin sauri, wata shu'umar gajeriyar dariya ta saki tana mai sakin labulen ta koma gami da ɗaukar hular ta ta aza a kanta jikin ta sanye cikin lallausar farar doguwar riga ta barci, saidai bata kama jikin ta ba sosai. Tana saukowa daga bisa benan suna isowa cikin falon, cikin salon Munafurci ta shiga tambayar Alhaji ko Lafiya? "Kubra Inaso ne inji ina Su Maryama suka tafi ne? Don na san dai duk inda suka tafi da sanya hannunki ciki" Alhajin ya faɗa yana jifan ta da wani irin kallon tuhuma idanun shi na a kanta ko ɗauke wa ba yayi. Cikin ɗan firgici da son nuna bata san me ke faruwa ba ta shiga dafe ƙirji "Alhaji ni kuma? To ina suka tafi? Wallahi bani da masaniya a cikin Al'amarin nan, ni fa tashina kenan yanzu" "Yau ne aka tashi ba'a gansu ba, kuma banyi mamaki ba domin kinsha yin iƙirarin sai sun bar maki gidan ki, bayan kina manta wa cewa lokacin da zan gina gidan nan babu ko sisin ki a ciki" "To fa Alhaji yau harda gori abun? To inaso ka sani ni bani da masaniya akan komai, tafiya kuwa sun daɗe basu tafi ba, ƙila gajiya sukayi ne Shiyasa suka cenza sheƙa, dama ai a haka muka gansu kwatsam sun zo mana, yanzun ma a haka kwatsam muka gansu sun tafi, menene na tada hankali a ciki? " Da kallon mamaki ya shiga binta, shi kau Bilal da yake ta faman safa da marwa a cikin falon, bai san lokacin da ya matsa kusa da hajiyar ba yana faɗin " Haba Mom? Kinsan kuwa irin alƙawalin da na ɗaukar ma Al'ameen? Nace zan kula dasu zan basu dukkanin Abunda suke buƙata, ba zan iya faɗa mashi cewa sun tafi ba yanzu, ki taimaka in kinsan inda suke ki kira su kice masu su dawo" "Au dama ashe ƙarya yake yi mani bai rabu da yarinyar ba, ashe dama yaudara ta kukayi, me kuke shiryawa ne? Bilal ka fita a cikin idanun a fa in kulle tin wuri, dama kai ke zuga shi kana ɗaure mashi gindin Abunda yake yi, gashi kai kayi auren ka hankalin ka kwance da yarinyar da kake so ƴar gidan manya sai shine zaka so haɗa shi da wannan ƴar matsiyatan" Cikin sauri Alhajin ya dakatar da ita, yayin da shi kuma Bilal ganin ba zai iya jure kalaman Hajiyar a kansu ba ya sanya shi juyawa da niyyar fita, dakatar dashi Alhajin yayi yana faɗin "ka jira mugama magana Bilal, zata kira su ne yanzu su dawo" "Ni babu wanda zan kira, domin bansan a wace ma duniyar suke ciki ba, na ji daɗin faruwa hakan don haka suje cen su mallake ƴaƴan wasu Amman dai ba na Kubra bB, kuma inaso ku sani babu wanda zan kirawo ai kuna da waya a hannuwan ku duka" Tana gama faɗar haka ta juya cikin isa zuwa ga upstairs ɗin domin komawa ɗakin nata, su kuwa da kallo suka bita galala, shi Alhajin ma mamaki yake yi yaushe Kubran tashi ta koma haka? Yasan halin ta duka, Amman bai san na ta tsaya tana fuskantar shi take faɗa mashi magana ba haka a gaban yaro. Girgiza kai kawai Bilal keyi, yana binta da kallo, daf da zata shiga ɗakin nata ne wayar ta dake hannun ta riƙe ta hau ƙara, ganin Abie ne ya sanya ta ɗauka tana mai ƙara ta a kunnen ta. *********************** Ba yanda Abie ɗin baiyi dashi ba na akan ya tsaya ya kai shi airport ɗin, tinda ya matsa lallai lallai yau sai yaje ƙasar tashi, ganin Abie ɗin zai ɓata mashi lokaci ne ya sanya shi cewa yabarshi kawai zai tau taxi, idan ya shirya kawai ya wuce office kai tsaye, shima ba wani daɗewa zai yi ba zai juyo. Ba yanda ya iya, shi ɗin mai biyayya ga yayan nashi ne, saboda yawan jiɓintar Al'amarin shi da yake yi a kulli yaum, hakan ce ta sanya shi haƙura ya shiga shiryawar shi a tsanake bayan ya raka yayan nashi ya hau taxi ɗin. Saidai ko minti ashirin baiyi ba da tafiya, wayar Bilal ɗin ta soma ruri, bai ɗaga ba har ta tsinke aka kuma kira domin lokacin yana sanya kaya ne, tankawa yayi a hankali da niyyar duba wanda ke kiran shi, Telephone ɗin landline ɗin ta ɗauki burari itama. Fasa ɗaga wayar tashi yayi kuma ya juya ya nufi falon domin ɗaga kiran, saboda duk a zaton shi daga hotel ɗin da ake kawo masu abinci ne, niyyar shi ma yace su bar shi kawai domin ya riga ya shirya zai yi break fast ɗin a office. Kafin ya isa ta katse kuma, ɗan tsoki yayi yana mai juyawa, daidai lokacin door bel ɗin gidan ta ɗauki ruri itama. Cikin Al'ajabi ya juya ya nufi ƙofar yana faɗin what co-insidence is that? Daidai lokacin da ya buɗe ƙofar, ɗan sanda ya gani tsaye sanye cikin kakin shi kalar na ƙasar american, gaisawa sukayi cikin turancn da ya riga ya zauna a halshen su, id card ɗinshi ya nuna mashi yana mai cewa ya biyo shi suje domin ɗan uwanshi ya samu accudent a hanyar shi ta zuwa airport ɗin, yanzu haka ma bai san wanene ke a kanshi ba. Cikin tsanann firgita ya dafe kanshi, yana mai rugawa ɗaki ya ɗauko wayar tashi, ko kulle gidan ma bai tsaya yi ba, ya fito gami da bin bayan ɗan sandan yana ta salati. Motar ƴan sandan suka shiga kai tsaye zuwa wajen, daidai isar su tayi daidai da isowar Ambulance ɗin, da gudu suka ɗauke shi gami da aza shi bisa ɗan gadon ɗaukar marasa lafiyar gami da tura shi zuwa cikin motar, Abie ɗin baiyi wata wata ba ya shige shima inda aka ajiye gadon yana riƙe da Hannuwan Al'ameen ɗin da yake kwance samɓal ko numfashi ba yayi, ya sake yin haske fayau idanun shi a kulle. Jini ne yake ta zuba daga hancin shi da kunnuwan shi, hakan ce ta sake gigita Abie ɗin ya shiga rusa kuka rurus, bai ma san Abunda zai iya yi ba kuma, faɗi yakeyi "Yaya ka tashi don Allah, kada ka tafi ka barni ni ɗaya Yaya, su wanene sukayi maka haka? Me kayi masu? Ina shi dreban yake yaya? Me ka aikata masu haka da suke neman Rayuwar ka?" Baisan ma har sun isa ba asibitn, saida yaga an buɗe ana kiciniyar ɗaukar gadon, hakan ce ta sanya shi dirowa, shima ya shiga binsu da gudu yana riƙk hannuwan ɗan uwan nashi. Tin a waje suka maƙala mashi robar shaƙar iska, ko ta kan Abie basu yi ba suma suna ta dalla gudu da keken har zuwa ɗaki da aka rubuta Emergency a jiki. Daga bakin ƙofar ne suka dakatar da Abie ɗin suka shige suna mai rufo ƙofar, saidai da yake ƙofar ta glass ce yana hango yanda suke ƙoƙarin samo numfashin shi, jikin Abie ɗin kuwa ya ɓaki da jini sosai, saboda yada ya rinƙa rungumo Al'ameen ɗin a jikin shi lokacin da suna mota. Zubewa yayi a wurin yana sakin gunjin kuka, da yake ƙasar ta turawa ce, babu ma mai kula dashi sai ɗaiɗaiku, ganin kukan ba zai fisshe shi bane ya sanya shi kiran Alhajin nasu, sai akaci sa'a shi kuma ya manto wayar tashi ɗaki da zai fito, sai kuma ya fito ya tadda Wancen tashin hankalin, hakan ce ta sanya Abie ɗin cenza akalar kiran zuwa ga Mom ɗin tasu. ******************** "Wat Abie, me kace? Yanzu ina Son ɗin yake? Kadai kace man ya mutu?" ta faɗa cikin matuƙar tashin hankali, a sukwane ta juyo zuwa ƙasan inda tabar su Alhaji Mustaphan da ɗinbin mamakin ta yanda ta rinƙa zuba masu ruwan rashin mutumci. "Alhaji kaji Al'ameen yayi haɗari, yanzu ma yana asibiti Baisan inda kanshi yake ba" ta faɗa cikin tashin hankali, ruwan hawaye har sun fara ɗigowa a daman fuskar tata. Zaburowa Bilal ɗin yayi yana faɗin " WHAT? Me ke faruwa damu ne yau? Ina Friend ɗin yake yanzu?" Girgiza mashi kai ta shiga yi bata ma san tana yi ba, hankalin ta a matuƙar tashe, miƙa ma Bilal ɗin wayar tayi, ya amsa yana mai tambayar Abie ɗin Abunda ke faruwa, shima ta cen ɓangaren cikin kuka ya zayyane ma Bilal ɗin Abunda ya faru, jin hakan da kuma kukan da Abie ɗin keyi yasan abun yayi worst cikin salati ya miƙa ma Alhaji wayar da yake tsaye baka ma gane Abunda ke kai kawo a ƙwaƙwalwar tashi. Hannu ya sanya gami da amsar wayar, yayin da Bilal ɗin ya juya a sukwane ya bar sashen. A inda ya bar su nan ya tadda su, cewa yayi kowa ya koma bakin aikin shi har zuwa anjima idan komai ya lafa, jiki a matuƙar sanyaye suka juya zuwa bakin aikin nasu, bama kaman mama talatun da zata iya kintatar dalilin da yasa su Suhan ɗin barin gidan. Kai tsaye ticket yaje ya yankar masu, ya kuwa ci sa'a ƙarfe 11 jirgi zai tashi, don haka uku ya yanka harda Alhajin da Hajiya Kubran sannan ya juyo zuwa gidan shi, domin faɗa ma ummin Abunda yake wakana. "Hajiya kiyi mani shiru hakanan da kukan nan naki fisabilillahi, da wanne kike so inji ne? Da ciwon yaron ko da ɓatar wannan matar. Iye" Alhaji mustaphan dake zaune dage da kai ya ɗago yana mai kallon matar tashi da take ta safa da marwa tana fama rusa kuka. "Ya za'ayi kace inyi shiru? In yarona ya mutu fa? Ko don kai baka son shi ne yasa baka san zafin shi ba?" "Eh bana son shi ɗin, ke ai son da kike mashi ne ya sanya gashi nan nagani kina son sa bauta mashi rayuwa, duk Abunda yake so ke bakya son shi, su waɗancen da kikayi sanadin barin su gidan su ba mutane baneba ko. Wallahi Kubra kiji tsoron Allah, gabaki ɗaya yanzu kina neman canza hali, kina neman ki nuna baki jin magana ta ko? Na san irin matakin da zan ɗauka akanki wallahi, kuma abun ba zai yi maki da daɗi ba" Suna cikin haka ne Bilal ɗin ya kira wayar ta hajiyar yake shaida mata su shirya an samu jirgin sha ɗaya, zasu tafi su dubo jikin na Al'ameen, tana jin haka kuwa ta juya gami da hayewa sama tana faɗin "Duk fa Abunda zaka yi Alhaji wallahi ko a jikina, yaro na kawai nake so a bar mani kayana, muddin ina raye bashi ba waccen kilakin mai mallaka ma maza jikin ta" Da fatan shiriya ya biya yana mai miƙewa ya fice daga sashen nata, zuciyar shi a cunkushe shi ya ma kasa gane daga inda zai fara neman waɗannan bayin Allah. ************************ Bansan sunan garin da muka dosa ba, kawai dai naga har ƙarfe shida na yamma muna ta faman tafiya a mota, tin ina ƙorafin kuka na har na gaji na dena. Gashi umman tawa ta ƙi koda kula ni ne ma, saidai ta siya mana abinci munci a wani gari da muka tsaya da bazan iya cewa ga sunan garin ba, duk da dai cewa babban gari ne. Duhu yayi lokacin da naga mun doshi wani ɗan ƙauye marar girma haka, na kula ma kaman bukkoki ne a cikin shi. Jikin wani ruɓaɓɓen guda naga munja mun tsaya, hamdala Naji umman tawa nayi, hakan ce ta sanya na gane mun iso kenan, fitowa mukayi mu duk kanmu, dreban na sakin wata uwar miƙa gami da hamma. Sauke mana kayanmu ya shiga yi, da yake ba wani yawa ne dasu ba, duk ƙulluka ma sunfi yawa a kayan. Ummata ce Naji tana cewa ya kamata dai ya tsaya ya kwana dare ya fara rufawa, ce mata yayi a'a ta sallameshi kawai ya wuce. Kuɗi da bazan iya faɗar yawan su ba ta ƙirga gami da bashi yanƙilga yaga sun cika cif cif yanda sukayi da ita, juyawa yayi gami da shiga motar bayan yayi mata godiya yaja motar shi yayi gaba. Nimau saboda tsabar gajiya takalmi na na cire gami da zama bisan su, yayin da umman tawa take tsaye riƙe da ƙugunta da na fahimci ga dukkan alamu ya ƙage mata ne. Juyawa tayi gami da shiga cikin gidan a hankali ba tare daya ce mani komai ba, ganin hakan ne ya sanya ban ko yi yunƙurin binta ba, na dai san duk wuya ba zata barmu mu kwana anan ba. Gashi waya ta ta ɗauke tin muna mota, da na kuka ma babu service a hanyar bare inyi yunƙurin kira wani. Sallama ta shiga kwaɗawa, gada cen cikin ɗaki na bukka aka amsa mata, wata dattijuwa ce ta fito riƙe da Aci balbal tana ta fama karewa da hannu kada iskan sanyin da akeyi ya kashe wutar. "Wacece?" ta faɗa daga bakin ƙofar ɗakin d ataja ta toge. Ba tare da umman tawa tace mata komai ba, ta shiga matsawa kusa da inda take tsaye sannan ta buɗe baki a hankali ta shiga faɗin "Nice Hajjo" Jin matar ta kira suna ta, gashi kuma bata ɗauki murya ba ya sanya ta matso wa, ko ba komai dai tinda taji an ambaci sunan ta, to ta san ba mai cutar da ita bace. Salati ta saka lokacin da tayi arba da fuskar umman tawa, ai tini ta yarda acibalbal ɗin gami da artawa a na kare zuwa cikin ɗakin tana ƙwala kiran "Malam fito Kaga fatalwar Maryam" Cikin hanzari ya miƙe yana faɗin "Ke Hajjo bana son shirme da shiririta, ina kika baro fitilar ne kin barmu a duhu?" ya faɗa yana laluben inda yaji hajjon na zunduma ihu gami da faɗa wa cikin shirgi. "Wallahi malam itace, ita ce malam kuma je ka gani, wayyo Allah na Maryama me nayi maki haka ne?" Malam ɗin baibi ta kanta ba ya nufi inda suke ajiye ashana cikin laluba ya ɗauka gami da dosar ƙofar fita yana faɗin "Yau Naji sakar ci, wace Maryamar kuma banda wadda muka binne da hannuwan mu, shekaru da dama?" A bakin ƙofar ɗakin ta inda yake jiyo warin kalanzir ɗin ya zuƙunna gami da lalubo ƴar fitilar sannan ya koma cikin ɗakin nasu ya sake kunna wa, yana miyar ta sakar masu fitila wajen sakar ci duk ƙasa ta ɓata lagwanin da ya murza ba jimawa. Duk abun nan fa da akeyi, umman tana tsaye tana kallon shi, hawaye tuni ya jiƙe mata fuska, nima dai da nake tsaye ta jikin ƙofar gidan ina iya hango Abunda akeyi cikin gidan, kaina ne ya sake ƙullewa, hango umman tawa nayi ta sake matsawa jikin ɗakin nasu tana mai sake yin sallama lokaci guda tana faɗin "Nice Malam, da gaske Hajjo keyi, nice Maryamar Muhammadu" Jin kalaman dake fitowa daga waje ne, ya sanya shima jinin shi ya tsinke ya fara gudu, lokaci guda ƴan cikin shi suka fara yamutsawa, kaman zawo ma yake ji, saidai yayi ta maza yana cewa "Kiyi ma Allah Maryama ki tafi abunki, i ma fansa kika zo ɗauka wallahi ba nan ya kamata kizo ba, bamu da hannu ko alhakin ki a kanmu ko ɗaya" Ya faɗi hakan ne, sanin da yayi cewa da hannuwan shi suka birne Maryamar da ɗiyar ta, yanzu kuma ta yaya za'a kuma zuwa ace mashi Maryama ce? Ganin ba zasu yarda da ita bane, ya sanya ta ɗaga labulen kai tsaye ta shige cikin ɗakin, a sukwane nima na biye bayan ta, domin ganin yanda zata kaya a cikin ɗakin To me kalaman su ke nufi ne? Me suke nufi da kiran umman tawa fatawa? Basu yi aune ba saidai suka ganta tsulum cikin ɗakin, "Malam ka kalle ni da kyau, nice Maryama, bamu mutu ba ni da yarinya ta Hauwau gata cen waje ma" Cikin salati ya buɗe idanun shi yana mai sake ƙullewa, addu'a yake yi ace mafarki yake yi, domin shi fa bazai taɓa lamunta da wannan al'amari ba. Ita ɗin daice tsaye a gaban shi, gashi dama shi cen baiyi imani da akwai fatawa ba a zahiri, matsowa ya shiga yi kusa da ita, duk da jikin shi har yanzu karkarwa yake yi, hannuwan shi riƙe da fitila yana mai haske ma umman tawa fuska. Lokaci guda ya saki wani ƙaton salati yana faɗin " *ikon Allah sai kallo, shin Maryama kece da gaske?, ina ita Hauwa'un?*" _A yiman uziri, wallahi wasu ayyuka ne suka taso man masu yawa, ina barar addu'ar ku_ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~32~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Cikin sa'a kuwa lokacin da suka isa har dare ya rufa, duk da haka har yanzu Hajiya Kubra bata bar kuka ba, Bilal ɗinne ke bata baki, domin shi dama Alhaji Mustaphn cewa yayi suje zai taho daga baya sai ya tsaya ya bada cigiyar su Suhan ɗin. Aiko suna isa asibitin suka hango Abie zaune bisa kujerar silver ya haɗe kanshi cikin ƙafafun shi, duk isar nan ta hajiya Kubra sai gata tana gudu zuwa ga Abie ɗin, koda ta ƙara sa ba tayi wata wata ba ta ɗago yaron nata ta rungume tana mai sakin kuka da tambayar inda mafi soyuwa a cikin yaran nata yake. Da hannu kawai ya iya nuna mata ɗakin da yake kulle, saidai zaka iya hango komai ta fari tar ɗin glass ɗin da aka zagaye ɗakin dashi. Da hanzarin ta ta saki Abie ɗin tana mai wucewa kaman zata faɗi zuwa jikin glass ɗin, da dukkanin hannuwan ta ta sanya ta dafe glass ɗin tana mai sakin wani tsumammen kuka, hango yaron nata da tayi samɓal, an jojjona mashi wasu na'urori wuyan shi ɗaure da wani abu kaman dai ya samu matsala a wuyan nashi, jikin shi suna sanye ne da bulan yadi, kwance yake samɓal, hatta da hancin shi toshe yake da abun shaƙar iska. Bilal ma da yake tsaye ta gefen ta, hawaye ne suke ta zurarowa daga ƙwarin idanun shi, hnakalin shi a matuƙar tashe, saidai ya sanya hanky yana sharar kwallar lokaci guda yana jan majina. Abie ɗinne ya matso yana mai janye mahaifiyar tashi jin ta fara surutai marasa ma'ana, baya so yaji tana ba yayan nashi guda ɗaya tal mutuwa, yafi so ta bishi da addu'a. Bilal har yanzu bai bar bakin glass ɗin a, yana tsaye hannayen shi soke cikin Aljihu, Alhaji Mustaphan ya kira wayar shi yana tambayar shi jikin Moh'd ɗin. Sanar dashi kome ake ciki yayi, sun ɗan tattauna kaɗan Bilal ɗin ya nemi da alhakin yayi haƙuri zai kira shi anjima, hango wasu Police su uku da yayi suna nufo ta inda suke. Suma bakin glass ɗin suka tsaya suna ɗan nazari haka kaɗan, sai kuma suka juya suka ba Bilal ɗin hannu, ganin haka ne ya sanya Mom ɗin tasowa ita da Abie. Cewa sukayi idan ba zasu damu ba suna so a basu mutum ɗaya zasu je dashi office domin akwai ƴan binciken da suke so zasuyi. Ba damuwa Bilal ɗin yace masu yana mai ƙoƙarin bin bayan su ne likitan ya ƙara so, shima hannu suka sha dashi suna mai bashi umurnin ya buɗe masu ɗakin zasu yi wani ɗan bincike. Bawata gaddama likitan da yake farar fata ya shiga buɗe masu ƙofar, shiga sukayi suna ƴan dube duben su da kuma ɗauke ɗauken hotunan su, sannan suka buƙaci likitan da yayi masu ɗan ƙarin bayani dangane da ciwon na Al'ameen ɗin. Nan ma ba gaddama ya shiga masu ƴan bayanai, duk abun nan da akeyi billa da su Mom ɗin suna cen waje suna hangen su, bayan kammalawar su ne, suka fito tare da cewa bilal ɗin ya biyo su suje. Bayan sun isa ne suka shiga yi mashi bayanin accident ɗin da yanda ya faru da kuma kyautata zaton da sukayi cewa lallai da sa hannun wasu akaso aga bayan Al'ameen ɗin, domin dukkan abubuwan da akeyi camera ta sirri cctv tana naɗar komai, tin daga zuwan motar zata gitta har zuwa lokacin da suka ga motar ta tsaya dreban ya fito yana dudduba motar alamar matsala ta samu, da lokacin da Al'ameen ɗin ya fito daga motar yaja gefe ya tsaya, sai suka ga dreban ya matsa kusa da Al'ameen ɗin ya mashi magana, sai kuma suka ga Al'ameen ɗin na gyaɗa mashi kai yana mai duba agogon da take ɗaure wutsiyar hannun shi ƴar traveling bag ɗinshi na a hannu. Ba suyi aune ba sai suka ga mai motar na tsaida wata taxi dreban ya fito suna magana, shi dai Al'ameen na tsaye gefe yana ta famn duba agogo, sai suka ga wannan mai taxi ya ɗaura igiya yaja taxi ɗin da Al'ameen ɗin ke ciki, sai kuma camera ta ɗauke ɗif, lokaci guda kuma ta kawo biji biji haka sai kuma ta koma normal, to fa a lokacin ne suka hango wata mota tayi sama sama da Al'ameen ɗin ta tsere, ko numb ta ba'a gani yayin da shi kuma Al'ameen ɗin ya faɗi ƙasa yana murmula sosai, jini duk ya wanke mashi jiki. Salati bilal ɗin ya saki, yana mai miƙewa tsaye hannayen shi goye a bayan shi. Bai a san yana kaiwa da komowa ba, har saida ƴan sandan suka buƙaci da ya zauna. Zama yayi yana mai sauraren su, lips ɗinshi cikin bakin shi, domin kanshi ya riga ya kulle, bai ma san wane kalar tunani zai yi ba kuma. Nna suka buƙaci da ya sanya hannu akan binciken da suke yi, sannan ya basu haɗin kai duk lokacin da zasu buƙata gami da ƙoƙarin lalubo su victims ɗin, sannan ba zasu iya kammala bincike ba har sai Al'ameen ya farfaɗo sun ji daga bakin shi. Haka ya koma asibitin wurin da su Mom ɗin suke, nan dai ya sake iske su, duk da dare yayi Amman likitocin sun hana su shiga, saida suka ga lallai lallai anan zasu kwana ne ya sanya suka basu ɗakin kusa da na Al'ameen ɗin da yake empty saidai zasu iya hango dukkan Abunda ke wakana a cikin ɗakin. To koda dai suka shiga ma kasa taɓukabkomai sukayi, yayin da bilal ɗin har yanzu hankalin shi a tashe, to wanene ke son ganin bayan aminin nashi a ƙasar ta amurka da take ba baƙuwar su ba? Mom ma saida ta tambaye shi, bai ɓoye mata komai ba, ya zayyana mata dukkan Abunda ke faruwa, wani kukan ta saki, tana mai tsine ma dukkanin mai hannu acikin son salwanta mata Rayuwar yaro (Hmmmmmmm) ***************************** Atare da umman tawa suka rankayo har ƙofar gidan da nake tsaye, da yake tin lokacin da naji suna shirin fitowa na ruga da gudu cikin sanɗa na fice a gidan. A tsayn suka tadda ni, har yanzun ba wai malam ɗin ya gama yadda bane, haske ni yayi da acibalbal ɗin da take saura ƙiris ta mutu saboda iska da hunturun sanyi. Ƙure ni yayi da ido, shi dai a gaskiya ba zai iya sheda ni ba, Maryamar kawai zai iya ganewa shima kuma ƴar kamar ce da kuma muryar, sai kuma hasken da take ɗauke dashi har yanzu, Amman gashi girma ya kama ta, ba kaman da da take ƴar matashiya ba. "Yarinya zo mu shiga gida kinji? Nan akwai sanyi sosai" cewar malam ɗin da yake ta ƙoƙarin sai yaga fuska ta cikin ɗan hasken farin watan daya hudo, da yake tini ƴar acibalbal ɗin ta idasa mutuwa. "Kayanmu fa baba?" na faɗa ina mai zuƙunnawa na kinkimi ƴar gana mustgo ɗin da kayan sawar mu yake ciki. "Eh fa hakane, tau ku kwaso mu shiga daga ciki, akwai sanyi nan ba mun tsaya nan ba, banda haka ma yanzu masu farauta zasu fito, kuma akwai matsala idan suka gammu nan" Ya faɗa yana mai zuƙunnawa shima ya ɗauki wani ƙaton ƙwali da kayan provision ɗina na makaranta suke ciki. Jin hakan ne ya sanya jikin mu fara ɓari, tsoro ya kama zuciyar mu, da sauri muka shiga jifar kayan har zuwa cikin gidan, saida muka kwashe tas ne sannan ya maida ƴar ƙofar wacce aka yi da zallan kara da itatuwa ya saya gidan. Tsakar gida muke tsaye, hakan ya bani damar ƙare ma gidan kallo, ƴan ɗakuna ne guda uku kaman rumbu, sai madafa da take gefe guda da bayan gidan da idan kana wanka ka miƙe tsaf za'a hango rabin jikinka. Shi kau Malam wucewa yayi zuwa ɗakin yana faɗin "Hajjo fito ki buɗe masu wanga ɗakin da yake haka su sanya kayansu, duk da yayi ƙura a kakkaɓe shi a haka zuwa wayewar gari, bari in kaɗa masu lagwani suga haske" Fitowa tayi tana faɗin. "To malam" Amman fa har yanzu ɗari ɗari take yi damu, ƴar dattijuwa ce itama don zata fi ummata da kaɗan amman, wucewa tayi kai tsaye zuwa ɗakin da yake gefen nasu ta fara kiciniyar buɗe shi, ga dukkan alama ma ana jimawa ba tare da buɗe ɗakin ba. Ƴar fitilar acibalbal ɗin da ta sake kunna wa da ita tayi amfani wajen buɗe ɗakin da haska shi, duk da ba wani haske ne ya wadata ba, ga dukkan amu ma dai basa da wata fitila da tafi wannan Aci balbal ɗin. Kayanmu muka fara kwasa muna kaiwa zuwa cikin ɗakin da sai mun duƙa zamu iya shiga, masalan ma ni da nake da ɗan tsawo. Har yanzu dai bata tanka mana ba, da gani dai a tsorace take damu. Ɗakin kam yayi ƙura, a haka ta koma ta ɗauko mana tsintsiya ta kakkaɓe mana muna tsaye gefe ni da ummata da har yanzu bata wani kula ni. Ƴar yalolon tabarmar kaba ce shimfiɗe a ɗakin dagani dai ana nufin a bisa ita zamu kwana, gashi ba wani girman kirki ne da ita ba, sai ɗan yalolon filon da ta shigo mana dashi guda ɗaya a hannun ta riƙe da ƙwarya mai kyau da fura ciki wadda tasha nono kindirmo. Zama mukayi muna bismilla, cikin mu ma babu wanda yabi ta kan furar, daf da zata fita ne ummata tace mata "Hajjo muna so muyi salla ne" Da to tabi umman tawa tana fita, bata daɗe ba ta miƙo mana ƙatuwar buta ta tasa cike da ruwa, amsa umman tawa tayi tana mai ficewa daga ɗakin. Zurut na tashi ina mai biye bayan ta, domin Nidai harga Allah tsoro nake ji, bata ko kalle ni ba, da yake ta san kan yanda gidan yake bayan ɗakin kawai ta nufa ta kamo ruwa gami da fitowa ta ɗaura Alwala, bayan ta gama ne ta miƙa man da niyyar nima inyi. Amsa nayi ina mai cewa "Umma Don Allah ki jiran in gama, wallahi tsoro nakeji" bata ceman ƙala ba sai ma ja da tayi gefe ta tsaya tana mai bin ko ina na gidan da kallo da dukkan alamu dai tana fahimtar ba'a samu kowanne sauyi ba acikin gidan illa ma ƙara ruɓewa da gidan yayi. Koda na shiga bayin, rasa inda zan zuƙunna inyi fitsarin nayi, domin ko ina ƙasa ce kwance, a haka dai na samu na raɓa nahau wani shimfiɗaɗɗen dutsi mai ɗan tudu da aga alamar wanda ake zama ne bisa in za'ayi wanka. A kanshi na hau na tsula fitsari na, na gama na fito tare da ɗaura Alwalar sannan muka ranka ya zuwa cikin ɗakin. Har muka gama salla babu wanda ya kuma shigowa, ganin hakan da mukayi ne ya sanya muka gane ba zasu dawo ba, sakaya ɗakin mukayi saboda sauro gashi babu maganin sauro, mu kuma namu dake cikin kaya yana cen ƙasa bama mu san ta inda zamu fara neman shi ba. Hakanan dai muke zaune, cikin mu babu wanda yake da niyyar kwanciya, ganin hakane umman tawa ta miƙe gami da zaro wani zaninta cikin Ghana must Go ɗin tamu ta shinfiɗa mani gami da cewa idan ba zan sha furar ba in kwanta in huta. Allah sarki mahaifiya, duk duniya babu yake, haka nan kasa kwanciya, itama ta kasa kwanciya, tana ta ƙare ma ɗakin kallo. Cen kaman an buɗe mata baki an zaro maganar Naji tace " *Anan fa aka Haifeki* " Ai bansan na zabura ba na tashi tsaye, har saida Naji tace "to miye na tashi tsaye? Ni kar ku faɗo mani" Sannan ne fa na koma na zauna, tinani fal cikin raina da tarin tambayoyi. Ban ce mata ƙala ba, sanin halin ta da nayi, yanzu ina iya tambayar ta cibi ya zama ƙari, koma ta fasa faɗa man Abunda tayi niyya. An kusa awa bata ƙara ceman komai ba, sai nice nayi shahadar fitowa in mata maganar karatuna ganin mun samu lokaci mu da ita. "Umma ya maganar makaranta ta? Ki taimaka mani umma kada wannan damar ta kucce mani, bani da kowa sai Allah sai kuma ke, wannan karatun da zanyi zai taimaki Rayuwar mu ya tallamu ta ni dake baki ɗaya" Shiru tayi tana mai nazarn kalaman nawa, cikin tausaya wa irin na uwa ta buɗe bakin ta ta shiga cewa "Mamana, nice nan na yarda kiyi karatu, saidai kuma yanzu bana buƙatar karatun ki a waccen makarantar da suka sanya ki, dukkan Abunda ya shafe su ma bana buƙatar shi atare damu, kuma inaso kiyi mani Alfarma da alƙawalin cewa zaki manta dasu duk kansu, kuma ki binne labarin su da babinsu a Rayuwar ki" Gabana ne ya tsananta bugu, me umma ke nufi, Amman dai koma minene tinda Naji tace zata barni inyi, ai ina tinanin zai zo mani da sauƙi "To umma hidimar karatun fa waye zai yi mani? Kada ki manta fa, nan ba aiki mukeyi ba, ba kuma albashi ake bamu ba, umma Meyasa kika zaɓi mu baro cen gidan dukkan irin muzguna mana da akeyi, kika zaɓi muzo nan muyi Rayuwar mu?" Na faɗa ina mai saddar da kaina ƙasa domin bansan da irin ɗauka da fassarar da zata yi ma maganar ba. " Hauwa'u ke yarinya ce har yanzu, ba zaki gane ba, ba zaki fahimta ba, Hajiya Kubra bata da zuciyar imani, ta sanya su Hajiya Sa'a suyi dukkan yanda zasuyi mubar gidan nan, har Rayuwar mu ma zata iya Sanyawa a hallaka saboda tana tunanin ke ɗinnan zaki mallake mata yaro ne, a yayin da take kallon shi ɗin yafi ƙarfin ki ba sa'an yinki bane, ni kuma na kwammace mu bar gidan tin kafin mu nemi rasa Rayuwar mu a karo na barkatai, ki bar maganar su, dasu da Abunda ya shafe su gabaki ɗaya yanzu bana son maganar su, Alkhairin da Alhaji da Shi Ameenullahin yayi mana Mungode Allah ya saka, Amman bana kyautata zaton akwai Abunda zai ƙara haɗa mu dasu" Tinda ta fara magana bata tsaya ba, haka kuma bani take kallo ba, hasali ma idanun ta a kulle suke gam, nikau da kwalla take shatata da zuraro mani sai faman ajiyar zuciya nake sauke wa, Ban aune ba naji ta sake cewa "Karatun ki Allah ne zai yi mana, Allah ne zai bamu iko da Abunda zakiyi karatun dashi, Mamana inaso ƙibar sanya ma ranki cewa dole sai dasu ne zamu iya, inaso ki sani su ɗin da Allah ya basu kuma ba zai manta damu ba, kiyi ta addu'a komai zai zo da sauƙi insha Allah, wannan halin da muke ciki zai zama tarihi da izinin wanda ya halicce mu" "Ameen Umma" Shi kaɗai ne Abunda bakina ya samu ya iya furta wa, duk kuwa da tarin kaman da suke cikin shi. Kusan a haka muka kwana zaune, kowa da Abunda yake saƙawa, saidai daf da asuba ne wani nannauyan barci ya kwashe ni, cike da mafarkai masu ban tsoro kuma duk Al'ameen ne nake hangowa a ciki, koda na tashi na tadda har gari ya fara wayewa, sanin da ummata tayi cewa baccin na gajiya ne ya sanya bata tadani ba, ta bari idan na tashi nayi sallar. ****************** To kusan muce yanda su Suhan ɗin suka kwana zaune cikin ƙututun ɗaki, haka suma su Umman suka kwana, duk da ga gado ga Ac Amman hakan bisa ɗaya daga cikin su ya runtsa ba, gashi kuma Al'ameen ɗin fa har yanzu bai motsa ba, haka umma ta kwana a tsaye jikin glass, Allah ya isa dai Suhan tasha ta, domin ita a gani ta duk itace sila ko ince sanadin da ya sanya Al'ameen ɗin yabar ƙasar tashi, gashi yazo ya haɗu da mahassada masu neman ganin bayan shi, ai gara ma da ta tafi cen daga cen ayi cen insha Allahu ba dai yaron nata da wannan matsiyaciyar yarinyar ba ƴar matsiyata. Saidai likitocibsu shiga su dudduba shi, gami da gyara mashi kwanciya su fita, Abunda ya ƙara ɗaga hankalin su shine ganin da sukayi wasu gungun likitocin kusan su biyar sun rugu a kanshi, dagani ma manyan likitocin ne da ba'a asibitin suke aiki ba kiran su aka yi. Bayan sun gama ne suka fito su duka, fuskar su babu walwala suka ce su Mom ɗin su biyo bayan su zuwa office ɗin. Hajiya Kubra ce da bilal ɗin suka bisu, yayin da aka bar abie nan zaune yana hango Al'ameen ɗin. Bayanin komai sukayi masu, ai tini Hajiya Kubra ta rushe da kuka, tana cewa "wai ina Alhaji ne? Yazo yaji, yazo yaga yaron nan kada ya mutu, me ke damun Al'ameen haka da har ciwon zuciya ya kama shi har ta kumbura? Tunanin me yake yi haka? Me ya nema ya rasa? Bilal kira man alhajin kace don Allah yazo yaji Abunda likitocin nan ke faɗi. Ai cikin hanzari shima jikin shi na rawa ya latsa number ɗin Alhajin, koda ya gaya mashi shima salati ya sanya yana mai cewa yana nan tahowa yau-yau ɗin nan kuwa insha Allahu, zai bar dukkanin Abunda yake yi yazo ya iske su a american. Faɗa ma Mom ɗin yayi yanda sukayi da alhajin, taɓe baki tayi cikin kuka take faɗin "ai ga irin ta nan, yaushe za'a ce maka yaron ka yana kwance rai hannun Allah kace sai ka tsaya neman wasu matsiyata marasa galihu cen, Rayuwar yaron namu batafi rayuwar su ba su duka?" Runtse idanu bilal ɗin kawai yayi yana mai girgiza kai ya tashi ya fice daga office ɗin ma baki ɗaya, kalaman na hajiya kubra sun rasa shi, sun girgiza shi matuƙa, ko wannan kaɗai ya isa ya sanya Al'ameen ɗin ciwon zuciya, samun wannan irin uwa haka ai ba abun daɗin ne ba. Ganin yanda ranshi ma ya ɓaci ya sanya shi fita cen harabr asibitin ƙarƙashin wata bishiyar umbrella ya zauna yana mai nanata kalaman hajiyar a zuciya. ******************** Koko da ƙosai aka miƙo mana masu zafi, bamuyi ƙwaron baki ba muka sha, duk da ba wani sugan kirki ne a ciki ba, har yanzu dai tinda malam da Hajjo ɗin suka leƙo muka gaisa bamu sake ganin kowa ba, sai cen wajen ƙarfe goma ne a kintata ta, saboda waya ta ta ɗauke ba chaji, gashi kuma banga alamun wuta ba a ɗan tsukukun ƙauyen. Ruwan wanka Hajjo ɗin tace in fito in ɗiba a cikin waccen tukunyar, irin ƙatuwar tukunyar nan ce ta ƙasa, hakan yasa na fiddo bokitin robar mu na wanka da soso da sabulu, sai dai fa da naje ɗibar ruwan na kai minti goma ina kallon ruwan nazari nake yi ta yaya ma mai rai zai iya wanka da waɗannan ruwan? Hajjo da take tsaye daga cen ƙofar ɗakin ta ce ta ce mani. "Ki ɗiba mana, ko ba yanzu zakiyi wankan ba?" Ban ƙasa a guiwa ba wajen juyawa nace mata "Mama waɗannan sune ruwan wankan?" "Yo Eah mana sune, dasu mukeyin komai a nan ƙauyen mu, ko rijiya bamu da ita, sai rafi shima safko nayi naje na ɗebo, har girki dashi mukeyi, ke ko kokon da kika sha yau dashi na dama, ƙosan ne kawai aka siyo a cen bayan layi" Baya naja da dukkanin sauri da ƙarfi na ina mai dafe ƙirji, cen kuma sai ga amai kwarara ya taho man, duƙawa nayi da sauri kada in ɓata jikina, ban tashi ba saida na amaye dukkanin abincin dake cikina, ɗan kokon da ƙosan kuwa sun dame babu kyau gani. Nasha Wahala domin ni da kaina na dinga ƙaƙalo shi, bansan sanda hawayen wahala da tausayn kaina suka wanke mani fuska ba, ummata dake tsaye bakin ƙofa jin maganar mu da hajjon ne ya sanya ta fitowa. A hankali ta tako har inda nake durƙushe ina mai idasa ƙaƙalo sauran kokon "Kinga Mamana, dole fa zakiyi haƙuri, haka Rayuwar su take ciki anan ƙauyen, gwamnati ma bata san da zaman su ba duk tsawon wannan lokacin, in ma ta sani to babu Abunda take aiwatar masu, illa iyaka idan zaɓe ya tashi kiga annkawo rimfuna da sabullai ana raba masu su zaɓi wanda ya basu. Amman ruwa da wuta kam saidai in kin bar garin nan, ko ruwan rijiya basu dashi saboda suna kan tudu ne, ba'a samun damshi a ƙasan, haƙuri zakiyi ki daure har Allah ya iyakance, domin ko ɗazu ma dasu mukayi Alwalar salla, yanzun ma dasu zaki ɗauraye bakinki ki tashi hakanan ki ɗiba kiyi wankan" Bansan lokacin da na kalle ta ba kwalla na zuraro mani, raina fa duk a dagule yake, mamadin inyi shiru sai a sake ɓarkewa da kuka da nayi, ashe cen inda muka baro muna cikin rahma ne, ashe bawa ya gode ma Allah a duk inda ya samu kanshi, hakan ma wata baiwar ce? Me yasa ya ummata jawo mu nan wurin? Me hakan ke nufi da rabo mu cikin rufin asirin mu? Duk da ada kallon muna cikin wahala mukeyi? Sake dafa kfaɗa ta tayi cikin tausaya wa irin ta uwa, sannan ta shiga goge man hawayen tana mai cewa kinga maza ki ɗibi ruwa kije kiyi wanka kizo ki tafi makarantar taku ki gano ya zakuyi?" Dasauri na kalle ta," Umma nan fa bansan sunan garin da muke ciki ba, bansan a wane state ma muke ba tukunna, tayaya ma zan gano hanyar da zata fidda ni daga nan surƙuƙin? "Zaki ita Suhan, zaki iya, ke ɗin mai ƙoƙari ce akan Abunda kike so, akwai masu babura acen ƴar yara da zaki hau su fidda ki babban titi, sannan nan muna ƙauyen sunkui kenan dake cikin jihar Jigawa. (Na sanya sunan littafin ne gudun kada wasu suce na faɗo sunan ƙauyen su na aibata shi). Ɗan murmushi nayi ina mai matsawa na ɗauko moɗar gami da zuba ruwan a cikin bokitin na wanke wurin duk da ƙasa ce, sannan na ɗauraye bakina ina yi ina runtse idanuna jin ruwan a bakina. Sannan na zuba ruwan na shiga bayin, aiko bisa ɗan dutsen nan na haye nayi wankan, sannan har na gama ban miƙe ba, jikina kam sai ƙaiƙayi nake yi, ina zuwa ɗakin na tadda umma ta fiddo mani mantheletor na zafi wai in shafe dukkan jikina. Haka kuwa aka yi ina shafawa Naji sauƙin ƙaiƙayin, haka umman tawa ta fice itama domin yin wankan, ina gamawa na sanya kaya na gami da shan nutri milk ɗin da umman ta ajiye mani da ragowar bredin jiya, aiko naji dam, duk da har yanzu zuciya ta tashi take yi kaman zan sake wani aman. Saida nabari umman tawa ta gama wankan ne ta shirya ta sanya kaya, sannan nace mata zan wuce, kuɗi ta ɗauko masu ƴar dama ta bani tana mai cewa Allah ya kiyaye hanya, duk runtsi kada in bari dare yayi mani a hanya batare da na dawo ba, in kuma har ban gama ba da wuri in kwana a hostel ɗin da aka riga aka bamu Alabasshi gobe in yo sauko in dawo. Da addu'a ta bini har ƙofar ɗakin, saida nayi ma Hajjo sallama da take zaune tana tsintar shinkafa ƴar hausa, itama cikin ƴar fara'a ta amsa mani, sannan na tambayeta kwatancen inda zai hau babur ɗin. Wani yaro ta ƙwala ma kira da yake cen waje yana wasan ƙasa shi da ƙanen shi, dukkanin yaran jikin su gaja gaja yake da datti ga majina a hancin shi, saurin kauda kaina nayi, ina jin zuciya ta na sake tashi. "Isa maza je ka raka wannan yayar taka ƴar yara ta hau babur ya fidda ta a hanya" da to ya bita ya ruga da gudu yana mai kaɗa ƴar tayar shi, sallama nayi masu nabi bayan yaron, yayin da umman tawa ta kai zaune bisa ƴar tabarmar kabar dake shimfiɗe ƙasa tana mai cewa "Hajjo kawo tsintar mana in tayaki" Ba musu ta miƙa mata, sunayi suna cigaba da ƴar firar su ta yaushe gami, dagani dai yanzu ta ɗan saki jiki da umman tawa, jira kawai take yi mijin nata ya dawo daga cin kasuwa da yayi sammakon tafiya suji ta bakin Maryamar. Nikau bamuyi wata tafiya mai nisa ba muka hango ƴar yarar, masu babur ukku ne rak a wurin kwance bisa machinan su suna ta fira, hango mu da sukayi ne ya sanya su zabura suka bukako mashin ɗin zuwa gabanmu suna cewa "Hajiya Tafiya ne?" Ganin ɗaya daga cikin su ya fisu zaƙalƙalewa ya sanya sauran biyun haƙura suka koma suna ƙunƙuni, nikau ya juya man nahau ina mai cewa "bakin babban titi zaka fidda ni inda zan samu mota" "To hajiya saidai fa akwai nisa, gashi hanyar bata da kyau yashi yayi yawa, sai kin riƙe mashin ɗin sosai" Aiko na kama mashin ɗin na maƙalƙale ina mai juyawa nace ma yaron ya koma gida sai na dawo nagode Yaron ya juya da gudu ba tare da ya jira wani ihisani daga gareni ba, saɓaninnyaran mu na yanzu ƴan cikin birni ko mun ƙanƙantar Abunda sukayi maki sai suyi maki ƙerere suna jiran ki basu kuɗi, Allah shi kyauta mana da wannan zamani. Hanya muka ɗauka ɗoɗar, kusan tafiyar awa guda mukayi sannan muka fito bakin hanya, titi ne samɓal, nan na sauka ina mai ce mashi nawa ne? "Jikka biyu" ya faɗa yana mai ɗaure fuska, banyi musu ba saidai na tambaye shi ƙarin bayani nawa ne jikka biyun da Hausa? "To ai malama hausar nayi maki, saidai in baki gane ba sai ince ɗari huɗu kenan" To nace mashi gami da ɗauko ɗari biyar na bashi, saidai bayada ko sisi a aljihun, cewa nayi ya bar shi kawai, godiya ya shiga zabga mani yana cewa "Allah ya kiyaye a dawo lafiya, ai bana tafi ba banga shigar ki mota ba hajiya" Muna tsaye kuwa sai ga mota golf ta shararo da gudun tsiya, tsaida mani yayi na shiga ina faɗin sunan garin da zani. Na kuwa ci sa'a suma cen suka nufa, mai mashin ɗinnan yana ta ɗaga mana hannu har muka ɓace ma ganin shi sannan ya juya, ga dukkan alamu dai yaji daɗin kuɗin nan da ya samu daga gareni. *_Allah ka yafe mana kura kuranmu, ya sanya mu gama da duniya da iyayen mu lafiya Ameen_* ~Oum-Deedat ce~ [9/21, 12:27 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~33~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Ƙarfe uku daidai muka isa garin na Zaria, Nidai bana ce ga sunan garuruwan da muke ta wucewa ba, har Allah yayi mana isowa. Muna sauka ne na gane inda zan dosa, mai a daidaita sahu na tare har zuwa cikin makarantar ina saɓe da ƴar jikka ta. Bayan na sallame shi ne kai tsaye na wuce zuwa admin block na foculty ɗinmu, saidai abun da har yanzu yake ɗaure mani kai tin shigowa ta makarantar, ƴan tsirarun mutane ne suke ta kai komo, wasunsu kuma a zazzaune. Saida na isa ne zuwa Office ɗin HOD ɗin namu ne na ganshi a kulle, kaina ya ƙara kulle wa, dole na juyo zuwa inda na hango wasu zaune ƙarƙashin bishiya, maza da mata ne zaune abun su suna ta fira da raha, duk da sun bani mamaki yanda suka saki jiki da waɗanda ba jinsin su ba, sallama nayi masu gami da tambayar su ko lafiya makarantar ba kowa har malaman? Ƴar dariya suka saki, lokaci guda ɗaya daga cikin su ya fara bani amsa. "Haba baiwar Allah, yanzu ke fisabilillahi duk yajin aikin da aka shiga baki sani ba? Hala ke sabuwar zuwa ce?" Ya jefa man tambaya a ƙarshen maganar tashi, ban samu damar bashi amsa ba, saboda yanda Naji jikina yayi sanyi ko ƙafa ta ma nema take ta gaza ɗauka ta, gyaɗa mashi kai kawai na samu damar yi, sannan nace masu nagode. Juyawa nayi a matuƙar gajiye, ga yunwa ga tashin hankalin komawa gida a yanzu, ga tashin hankalin ban samu Abunda nake so ba, ga kuma waya ta babu chagi. A haka har na fito bakin gate duk tsawon tafiyar nan, na matuƙar galabaita jikina har ƴar kyarma yake yi. Cen nesa kaɗan na hango mai ɗan shago yana saida provision da su lemuna, sai dougnut ɗana hango cikin bokiti. Da ɗan sauri na na isa ga inda yake zaune na fiddo kuɗi gami da cewa "A bani a haɗa mani da lemo." Alfarma na roƙa wurin da yake zaune, akan ya tsira mani chaji na wayar ta ɗan kawo, duk da ba wai don in kira wani ba, aiko sai gashi kafin in gama cin dougnut ɗin da na shige hijab ina ta faman turawa, wayar ta samu kusan 20% da yake chargre ɗin tana da kyau. Godiya nayi mashi gami da karɓa na wuce, shawara kawai nake yi ta yanda zan nemi komawa a yau ɗinnan gashi har la'asar tayi, kuma ban hango wurin da zanyi salla ba ma, dole a haka na nufi tasha, na tadda mota na lodi, a haka nima nabi su wurin zaman jiran sauran passingers ɗin bayan na gaya masu inda zani. Saida dreban yace mani "Amman kinsan inda zaki cen cikin lungu ne ko? Saboda dole a hanya zamu sauke ki" Ce mashi nayi na sani, a haka har motar ta cika muka ɗauki hanyar komawa gida. *********************** Alhaji Mustapha sai cikin dare ya isa, har yanzu dai babu wani cigaba, duk da Bilal ya fita yayo masu take away ɗin abunda zasu ci, har yanzu babu wanda ya iya cin wani abu, saidai ruwa kawai da hajiya kubran ke kurɓa, idanun ta sunyi mata luhu luhu,ko buɗe su bata iya yi, ya zuwa yanzu kowa dake nigerian ya san da rashin lafiyar ta Al'ameen. Isar shi ce tayi daidai da isar su Aunty Feener da Afnan, aiko suka dasa wani sabon kukan, duk da ba'a bari a shiga inda yake saidai suna hango shi ta cikin glass, duk da yanda Alhajn ke lallashin su Akan suyi shiru, kasawa sukayi, gani suke kaman sunyi bankwana da ɗan uwan nasu ne. Tini dai Alhaji Mustaphan ya nemi da a cenza mashi asibiti mai zaman kanta inda mafi ƙwarewar likitocin suke, ba musu kasancewar sunsan yadda su Alhajn suke a ƙasar ta amurkan. Asibiti mai kyau da tsaruwa aka maida shi, nan ɗinma kimlace shi aka sake yi wuri na musamman, saidai yanzu kam basa iya hango ta inda ma yake kwance, har yanzu bai san wake kanshi ba, hakan ya ƙara tada hankalin Hajiyna, gani take yi kaman za'a fito ace mata ya mutu, shi kau Alhaji Mustapha bai ma bi ta kan hajiyar ba, saidai afnan da take maƙalƙale dashi tana kuka, sai faman lallashinta yake yi. Da yake an basu ɗaki na musamman akace suyi amfani dashi, duk da asibitn ba'a zaman jinya, saidai Alfarmar Alhaji Mustaphan da ya daɗe cikin ƙasar ya sanya aka basu, a haka suka kwana zaune, Bilal ne kawai ya tafi gida ganin Alhajn ya iso ga kuma su Aunty Feenar. Tin da safe washegari sai ga Saudat da Nihal gabaki ɗayansu da mazajen su, ai fa nan sani sabon babin kukan ya buɗe, Alhaji Mustaphan har ya gaji da lallashinsu ya sanya masu idanu. Ya san dole suyi kuka, Al'ameen ɗin ɗan uwa ne nagari, duk da kasancewar shi ba mai yawan fara'a ba ko shiga hidimar mutun, shi ɗin mai tausayi ne, mai jin ƙan na ƙasa dashi ne. Ana haka sai ga kira daga mataimakin shugaban ƙasa da sauran sarakunan sun zo ganin Al'ameen ɗin. Kusan muce tare suka isa da Alhaji Auwalu da kaka zuwairan da ta tada rigima sai an taho da ita, haka ba yanda ya iya dole ya tattago ta tazo taga jikin jikan nata, yayin da ta baro ɗan tsoho isuhun nata a gida. To su ɗin dai an bar su sun shiga, saboda a ranar suke so zasu juya, banda su Alhaji Auwalun da zasu zauna a nan har sai Abunda hali ya nuna. Su kansu sun girgiza da yanda suka ga jikin Al'ameen ɗin, kaka zuwairan kam kuka ta sanya tana faɗin "su wanene sukayi maka haka Muhammadu?" Saida aka fidda ta waje, saboda ba'a son hayaniya a kusa dashi, sun mashi Addu'a tare da bada saƙon gaisuwa da dubiya ta shugaban ƙasar, sannan suka juya suka tafi. Yayin da Bilal da Abie suka raka su har airport cikin tasu motar. Zuwa yanzu dai kam, kowa ya sare da Al'amarin Yariman Matasan Arewan, su kansu likitocin sunyi mamakin da har yanzu bai farfaɗo ba, duk da sun dudduba gabaki ɗaya raunukan dake jikin shi sun fara warkewa, kuma komai nashi ya koma normal kawai bugawar zuciyar tashi ake so ta koma Normal. Ya zuwa yanzu dai sai zaman jigum-jigum, daƙyar aka lallaɓa su Aunty Feenar ɗin suka tarkata suka tafi gida, Amman kuma tin da farar safiya suke dawowa su dasa zaman jiran tsammani. A yanzu dai kam, su Nihal ɗin sun sheda Allah ɗaya ne, sun gane rai ba'a bakin komai yake ba, Amman har ya zuwa yanzu a hakan Allah bai basu ikon barin halin nasu na jin kai ba, wannan kuma sai Allah ya yaye. Ƙawayen Hajiya Kubran ma da dangin ta na ɓangaren Mahaifiyarta duk sun zo, saidai suma jiki a sanyaye suka koma zuwa ƙasar tasu, inda Nigeria ta ɗauki addu'a daga bakunan mutane da dama akan Allah yaba shugaban Matasan nasu lafiya, masallatai makarantu da coci-coci ko ina addu'a kawai ake ta faman yi, saboda su kansu sunsan in suka rasa Al'ameen ɗin ba ƙaramin rashi sukayi ba. ********************** Mun sha tafiya a hanya kam, har duhu yayi magariba ta soma kawo kai, a daidai lokacin ne kuma motar mu ta soma bamu matsala, hankali na fa ba'a kwance yake ba, nafi tunanin in ma yanzu aka sauke ni, to ta ina ma zan fara shiga wannan surƙuƙin lungun namu har in kai gida? Na tuno uwar tafiyar da muka sha kafin mu fito titi ɗazu da zan taho. Tinani na yayi zurfi, kwatsam saidai Naji ana ta hayaniya a cikin motar, wasu na cewa " Wai ya haka ne? Dreba me ke faruwa ne?" yayin da dreban ko amsa masu baiyi ba, ya dai samu ya gangara bakin titi ya faka motar, ya fice domin duba meke faruwa. Ai tini naji ƴan ciki na na yamutsawa, gamu dai a cikin dokar daji, kuma ni kaɗai ce mace, sauran mazan sai hayaniya suke yi, Dreba dai bai ko kula su ba, sai faman gyara yake yi, har duhu ya rufa ruf, kowa ya fiddo wayar shi yana haskawa, yayin da duk sauran mazan sun fice, ni kuma na takure cikin motar ina ta rawar sanyi da makyarkyata, nadama duk ta rufe ni, shin menene ma dalilina na tahowa ayau ne? Bayan na san dare ya riga yayi? Tinani barkatai suka taru suka yi mani yawa. Tin daga cen ɗan nesa damu muka ga an dararo mana wasu irin fitilu masu mugun haske, sai kuma ƙarar bindiga ta soma tashi, ai bansan lokacin da na ruɗe ba, har fitsarin da nake ta matse wa ya soma zirarowa, da gudu na diro daga cikin motar, hannu na riƙe da ƴar waya ta da tin ɗazu nake neman service, ko dokar ummata ce yau dai in karya in nemi Bilal ɗin tinda cen ƙauyen babu wanda zan kira babu ma mai wayar hannu saboda rashin service ɗin. Kasheta ma nayi baki ɗaya ganin bazan samu damar kiran ba, na cusata cikin breziya, jikkata na saƙalo ta ta wuyana da hannu na ɗaya, ai bansan lokacin da na fara gudun ceton rai ba, kaman yanda naga sauran mazan duk sun fashe sun watse kowa ya kama gaban shi. Gudu muke yi ba ƙaƙƙautawa, yayin da suka rufa mana baya, suna ta halbe halbe da faɗin "Ku tsaya kawai," tini suka fara kama waɗanda basu da ƙarfin gudu, gashi dai duhu yayi sosai, baka ganin ko gabanka sai hasken fitilun su. Wani rami da bazan iya cewa ga zurfn shi ba, shi kawai nagani ta gefen hanya, ai bansan lokacin da na dira ta ciki ba, sai faman haki nake yi, kukan ma ya ƙi zuwa, ko ba'a faɗi ba dai na san ƴan kidnapping ne yau Allah ya haɗa mu dasu. Abunda kake ji ana waiwai a ƙasar sai gashi yau ni Suhan nice gani gasu. Cen ƙurya na takure kaina, sai faman kyarma nake yi, yayin da suka ƙaraso jikin ramin suka shiga haskowa, wani daga cikin su ne yace "Kaman fa nishin mutum nake ji anan ciki baba" "Sauran ne suka ce mashi zo muje gaba dalla ai ba kowa, baka gani ba, ba zasu shiga nan ba ai, ga su shago cen sun kama wasu, mu juya kawai mu koma, watarana a haɗu" Haka ya juya ya bisu ba don ranshi ya gamsu da babu kowa ɗin ba, saida sukayi nisa ne sosai na lallaɓa na fito da wata ƴar hanya da nagani, ina iya hango su ta cen nesa sun tattara mutane da suka kusan kai su biyar ciki harda dreban, yayin da suka chaje motar baki ɗaya basu samu komai ba, iza ƙeyar su sukayi zuwa cikin dajin. Ban tsaya sauraren komai ba, na sake zurawa da gudu na tattare doguwar riga ta da zata kusan ma kaiwa guiwa, kaman guguwa nake falla gudu, ni Hauwa'u ban ma san ina da gudu ba irin haka sai yau. Na gaji iya gajiya, gashi gefen titi nake bi, ina gudun shiga ta cikin dajin su sake kama ni. Tinani nake yi ya zasuyi da sauran mutanen da suka kama? Sauran kuwa tini sun ɓace ma gani na, kowa ta kanshi yake yi, basa ma ko tinanin ni mace ce bari su tsaya su taimake ni, kowa Nafsi-Nafsi. Na gaji tuɓus, har bansan lokacin da na zube saman titin ba ina ta maida haki da numfashi, bana iya motsa komai na jikina, gashi saboda tsabar tsorata numfashi na har wani ɗauke wa yake yi, na riga na sadaƙat, yau kam tawa ta riga ta ƙare, na rasa wannan ikon Allah, hakanan kana cikin zaman zaman ka lafiya cikin ƴan awannin da ba zasu Gaza biyar ba komai ya dagule mani. Tin daga nesa nake hangen fitila na dallowa ta inda nake yashe, na sadaƙar cewa sune suka dawo sake kama ni, yifff, mota ce tazo ta gitta ni da wani irin matsanancin gudu, kaman zata tashi sama, buɗe idona nayi a hankali ganin basu bane, da har tsoro ya sanya ni kulle idanun har sai sun ƙara so, sun tasa ƙyeya ta gaba. A hankali na hango motar nayi ribos tana dawowa daga baya a hankali, daidai inda nake kwance motar ta dawo ta tsaya, da gudu na cikin motar ya fito yana haske ni da fitilar wayar shi daya kunna. "Ke baiwar Allah lafiya kuwa? Da hankalin ki kike kwance nan? Zo taso taso maza" Bai jira cewa ta ba, ya kamo ni da dukkan ƙarfin shi yayin da yaga ina niyyar miƙewa Amman na kasa, ƙofar gaba ya buɗe ya cusa ni ciki, shima da mugun gudu ya koma motar, yayin da ya fizge ta mukayi sama a sukwane. Baice man komai ba, nima sai faman haki nake yi, cen kuma sai wani tsumammen kuka ya taho mani, aikau ban hana kaina yin shi ba, domin na san ba zan iya haɗiye shi ɗin bane. Kuka na fashe dashi mai cin rai, ni suhan wacce irin ƙaddara ce haka take bibiyar rayuwa ta? Me na aikata ma Ubangiji na ne da yake jarabta ta ta kowanne fanni? Shima mutumen Baice mani komai ba, har mukayi nisa sosai muka bar cikin daji muka fara ratsa ƙauyuka. Duniyar tsit, in banda haushin karnuka da kukan tsuntsaye. A hankali ya kai duban shi gareni da naci kuka na ƙoshi ina ta sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali. "Daga ina kika fito? Kuma ina zaki? Me ya sanya na ganki a wancen wurin kwance? Ya jero mani tambayoyi, sannan ya kafeni da idanu ta cikin hasken fitilar motar daya sanya hannu ya kunna. Cikin son share hawayen da tsaida kukan na fara cewa " Daga zariya nake, naje makaranta ne, ashe yajin aiki akeyi, banda inda zan kwana ne ya sanya ni neman komawa gida, a ƙoƙari na nason komawar ne muka haɗu da ƴan kidnapping......" "Wat?" Ya faɗa yana mai saurin kallo na, tini wani irin tausayi na ya tsirga mashi, sake kafeni da kallo yayi, saidai baice mani komai ba saidai "Allah shi kyauta gaba, yanzu ina kika nufa?" *"Sunkui"* na bashi amsa ina mai duban hanya, zuciya ta a cunkushe take ga hawaye dake ta faman zarya a idanuna. Baice mani ƙala ba, ya kuma zaro tissue ya miƙa mani, amsa nayi ba gardama na shiga goge kwallar, saidai ina gogewa wata na sake ɓulɓula a cikin idanun nawa. Daidai ya karya kan motar tashi ne, zuwa hanyar da zata sada mu da ƙauyen namu ne, sai kuma ya sake ɗan kallo na haka a gajarce, sannan ya kuma ceman "Gaskiya kinyi matuƙar kuskure, a matsayinki na mace bai kamata ki biyo hanyar dare ba, ko ina ne ya kamata ki nema ki kwanta zuwa safe, iyayen ki zasu matuƙar yi maki faɗa, muddin suka ji abunda ya faru" Gyaɗa mashi kai nayi, ina mai cewa "Haka ne, nima na sani, kuma nayi nadamar yin hakan, saidai ba zan kuma ba insha Allahu, nagode da taimako na da kayi" Nan ma baice komai ba, sai ma miƙo mani waya da yayi yana mai cewa in sanya mashi number ta, in an koma yajin aikin zai kira ya gaya mani. Amsa nayi gami da danna mashi numbobin, sannan na ƙara da faɗin "Saidai ko ka kira ba zaka samu ba, saboda ba service a ƙauyen namu" Ɗan shiru yayi, yana mai amsar wayar ne yake ce mani "Ba komai in an koma zanzo da kaina in faɗa maki, nima lecturer ne a makarantar da kika je ɗin, Sunana Salim Bawa. Ya sunan malamar?" "Suhan" na faɗa mashi a hankali, "Wow, what a nice name?" ya faɗa da ɗan murmushi akan fuskar shi, sannan yace ki share hawayen ki, insha Allah kin iso gida babu abunda zai same ki anan kuma" Ganin mun ƙaraso ƙauyen ne, ya sanya na shiga kwatanta mashi gidan, har ƙofar gida ya dire ni, fita nayi ina ce mashi "Nagode, ko zaka kwana ne anan? Idan gari ya waye sai ka wuce? (kaji su Suhan da ƙarfin hali. Lol) Kallon gidan yayi, sai kuma ya ɗan girgiza kai yana mai cewa "Ah No dear, zan wuce ne, ina sauri ne, shine ma ya sanya ni tafiyar daren" Godiya na shiga yi mashi, ina tsaye har ya juya kan motar tashi ya fice yana mamakin ace mutane ne ke rayuwa a cikin wannan kangon gida. Yayin da ni kuma na ɗan matsar da kararen na shige, kai tsaye ɗakin namu na dosa, hannu kawai na sanya na buɗe gami da shiga, a zaune na tadda ummata tana lazimi, tabbas umman tawa mace ce mai yawan ibada, ga addu'a da maida lamirn ta ga Allah, ni kaina na san kawo mu ƙauyen nan da tayi akwai wani Al'amari mai girma ne, Amman koma menene zamu zuba ido muga Abunda Allah zai yi. A ɗan ma makance ta taso cikin ɗan zaro idanu ta shiga cewa "mamata kece cikin tsakar daren nan? Garin yaya kika yo tafiyar dare ke da nace ma ki kwana zuwa safe kin taho?" Kai zaune na kai ina mai sauke ajiyar zuciya mai nauyi ina cewa "To umma ai yajin aiki suke yi, hostel ɗinma a kulle suke" "Ikon Allah, to yaya aka yi kika shigo nan? Na dai san da wuya ki samu mashin yanzu cikin daren nan, shine ma yasa nace ki kwana, kuma kinga hanya yanzu babu kyau, ɓata gari sunyi yawa" "Umma Allah ya tsare wallahi, wani malami ne ya maido ni, a cewar shi nayi kuskure ai hanyar bata da kyau, yace ma idan an koma yajin aiki zai zo ya faɗa man tinda yaga gidan" "Malami fa kika ce mamana, ki dai kula gaskiya, duniyar nan babu gaskiya a cikinta, Naji ma muryar ki a shaƙe ko iskan mota ce?" "Eah umma, na gaji ne sosai, bari inyi salla sai in kwanta, zuwa safe zan faɗa maki komai" To tace mani tana mai nuna mani buta dake ajiye, fita nayi na wanke jikina tas da fitsari ya ɓata man ɗazu, sannan na ɗauro alwala, gami da cenza kaya na tada salla. Bayan na gama ne, umma tace mani ga tuwo idan zanci, na ƙoshi nace mata, domin ina tsammanin babu wani abu da zai iya shiga bakina a halin yanzu. Bisa shimfiɗar tabarmar kaban namu na kwanta, har yanzu jikina ƴar kyarma yake yi, Amman ina iya ƙoƙari na kada umman tawa ta gane halin da nake ciki. Ko minti talatin banyi ba da kwanciya baccin wahala ya ɗauke ni cike da mafarkai barkatai iri iri marasa daɗi, ciki kuwa harda na mutanen da ƴan kidnapping suka kama akan idona. _(Masalar da ake fuskanta kenan a ƙasar tamu Nigeria, suna nan, kuma an san su, suna fitowa a lokacin da suka so, kuma su koma a lokacin da suka so, ba tare da gwamnatin Nigeria ɗin nayin wani yunƙuri na azo a gani ba, domin daƙile afkuwan hakan._ _Jinjina ga gwamnan jihar tawa ta Katsina *RT HON: AMINU BELLO MASARI* a ƙoƙarin shi nayin sulhu da ɓata garin, shi sulhu a ko'ina alkhairi ne, idan har yunƙurin nashi na kawo gyara bai yuwu ba, to hakan na nuna dole ne a ɗauki doka sosai AKANSU. _ _Haka kuma ina mai jinjinr ban girma ga *DCP ABBA KYARI* a bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen kamo ɓata garin, ba dare ba rana yana aiki, munji mun gani mun kuma yaba, Allah ubangiji ya ƙara taimaka mashi, ya kauda mashi idon maƙiya da mahassada a ko'ina yake a faɗin duniyar nan, Alherin Allah ya isar mashi, ni Oum-Deedat na sadaukar da Page ɗinnan ga mutanen guda biyu, Allah ya ƙara basu ikon jajircewa a bisa dukkanin ayyukan Alkhairin da suka sanya gaba. AMEEN)._ ******************* Yau Iyalan Alhaji Mustaphan sun tashi da matuƙar farin ciki na farfaɗowar sahibin zuciyar tasu, kuma ya tashi tangarau saidai Abunda ba'a rasa ba, kowa na matuƙar murna da farin ciki, duk sun zagaye shi, kowa kaman ya faɗa kanshi, da ɗaiɗayan suka dinga rungume shi, ita kau hajiya kubra sai faman shafa mashi kai take yi, kai ga dukkan alama soyayyar Al'ameen ɗin nata a cikin zuciyar ta, daban take harma bata iya ɓoyuwa. Bilal ma cikin murna da farin ciki yake duban abokin nashi, sashe ɗaya kuma na ɓangaren zuciyar shi yana mai tino mashi da ɓatan su Suhan ɗin da kuma idan aminin nashi ya tambaye shi mai zai ce mashi ne? Ƴan kankiya duk sun zo duba jikin na Al'ameen, inda Alhaji Mustaphan ne ya sanya su biyo jirgin domin suzo ganin shi, harda kaka isuhun kuwa suka taho, lallai duk wanda ke cikin asibitn nan ya shaida cewa Al'ameen ɗin ɗangata ne gaba da baya. Tini Alhaji Mustapha ya nemi a basu sallama, Amman likitocin sun hana sunce sai nan da kwana biyu, idan ya sake gyagijewa. A hakan ma dai murna suke yi, duk da bawai magana yake yi ba, hasali ma har yanzu baice komai ba, saidai faman ɗan murmushi da yake yi na gefen baki, ganin irin ƙaunar da dukkanin zuri'ar tashi suke nuna mashi. Iyayen Bilal ma sun zo, harda ummin Bilal ɗin, da yake yarinya ce mai shiga rai, da faram sannan gata wayayya sosai, uwa uba mahaifan ta masu kuɗi ne sosai, ya sanya ta samu sauƙin su Saudat ɗin, duk da dai bawai shiga al'amarin nasu take yi ba itama. Kowa dai yana tsaye, sai faman sannu akeyi mashi, shi kau sai faman binsu da idanu yake yi, yayi mamakin da yaji ance gungun Matasan kamfaninshi shi ɗin sunzo sun duba shi tin daga nigerian lokacin bai farka ba, ba'a bari a kawo ma marar lafiyan komai, asibitn sune suke ba marar lafiyan abunda suka san ya dace da yaci. A haka suka kusan yini, dukkan su suna zaune anata fira harda Bilal ɗin da kuma sauran ƴan uwan nashi, yayin da Alhaji Mustapha ya tafi cikin gari wajen abokanan shi, tinda jikin na yaron nashi yayi sauƙi masha Allah. Wajen ƙarfe biyar ne likitan ya shigo gami da basu umurnin su fita abar marar lafiyan ya huta, dama amfanin riƙe shi asibitin kenan. Daf da zasu fice ne, suka ji a karo na farko tin farfaɗowar tashi yayi magana. *"INA SU SUHAN?"* Maganar da yayi ce ita ta sanya kowa dakatawa daga tafiyar da yake yi, a sukwane Bilal ɗin ya juyo yana mai kafe Al'ameen ɗin da kallo lokaci guda kuma ya janye idon shi ya maida kan Hajiya Kubran da take kallon yaron nata da wani irin yanayi, Tausayi ma ya bata, tabbas ta san basu bar shi hakanan ba, yaron nata maiji da ilimi, dukiya, uwa uba yanzu ga sarauta, shine mai kwallafa ranshi akan wata marar galihu a rayuwa Buɗe baki tayi da niyyar magana, Bilal ɗin ya riga ta da sauri wurin cewa *Suna Nan Lafiya Ƙlau, Sunma Ce A Gaidaka* Yana gama faɗar haka ya juya ya fice sauran suka rufa mashi baya, su kuwa su Nihal kaman zasu fashe, dole ba don taso ba ta shiga bin bayan su itama Hajiya Kubran, ganin ya maida idanun nashi ya lumshe gami da sauke wata ƴar ƙaramar ajiyar zuciya..... _ina mai ƙara bada haƙuri dai, wallahi rashin chaji ke damuna, Amman insha Allah dama samu zaku sake jina_ ~Oum-Deedat ce~ [9/26, 9:43 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~34~* _Masu kirana da masu yi mani Dm da masu comment, nagode kwarai da addu'o'in ku, Allah ubangiji ya saka da Alkhairinsa, ya kuma bar zumunci, na samu sauƙi sosai kuma Naji daɗin yanda kuka damu da rashin lafiyata, ina yinku kaman yanda kuke yina, addu'o'inku da comment ɗinku kan ƙara mani ƙwarin guiwa._ _Kyautar Page gareki @Lubabatu ta *BANFI ƘARFINTA BA FANS* Haƙiƙa damuwar ki a kaina bata misaltuwa, babu abunda zan iya cewa, saidai ince ALLAHU YABAR ƘAUNA_ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Haka dai rayuwa tayi ta garawa damu, yau daɗi gobe babu, duk kuwa da cewa irin halin takura da matsantuwa na rayuwa da muka shiga, hakan baisa mun gaza ba, ko nuna ma Allah bijirewa akan jarabawar da yake yi mana, saidai fatan Allah yasa mu iya cinye ta lafiya. Ummata mace ce mai kawaici, da sanin ya kamata, zaman mu a gidan baisa umma ta zura idanu akan komai sai malam ɗin da matar shi hajjo sun bamu ba, ƴan abubuwan da muka zo dasu, tini umman tawa take ta fiddosu ɗauki ɗai-ɗai har suka zo suka ƙare muka cinye. Ganin hakan ne, kullum ummata cikin tunani cikin damuwa, don watarana idan malam ɗin baiyi sa'ar kasuwa ba, mu kan kwana bamu zuba ma bakin salatin mu wani abu ba, saidai ruwan da tin inasha ina amai, a haka har na daure ma rayuwa ta. Wannan ce ta sanya ni cema umman tawa ko zamu fiddo kayan provision ɗina na makaranta, saidai ta gane ni, a cewarta in yau aka zo aka ce in fito da me zamu siya? To dole nima dai na haƙura, saidai fa inayi masu ɗauki ɗai-ɗai, duk da umman tawa tana kallo na, amman ta kan Gaza ceman uffan, saboda wani irin tausayi na da ya kan ratsa ta, har kwalla take yi a kai-kaice bataso in gani, saidai fa nima ɗin wani lokaci idan abun yayi yawa ya isheni nakan shige banɗaki inyi kuka mai isa ta, in wanke fuska ta in fito don kada umman tawa ta lura, amman fa ance yaro yaro ne, koda kuwa ɗan giwa ne, tana lura tsaf dani, saidai bata tankawa, saboda tasan komai mai wucewa ne. Sana'ar wankuu ta fara yi, ta kan je bakin rafi ta wanko ta dawo gida ta shanya akan danni. To saboda ƙauyen ba wani babba bane ba, bata cika samun wankin ba, bayan haka da wani ya bada wankin gara ta auno shinkafa ƴar hausa ya watsa wake ko dawa a ciki an dafa ansha shagali. Hakan ce ta sanya ta haɗawa da surfau, a ranar da ta fara surfau ɗin kuwa, ba irin kukan da ban sha ba, abun ka ga fara, fuska ta tayi suntum kuwa, tayi jajur, kaman ka taɓa jini ya ɓalle, tausayin ummata nake ji da irin rayuwar da muke ciki, tabbas idan guri na ya cika babu abunda zai hanani gina ma ummata gida a Abuja in ɗauke ta, muje cen muji daɗin duniya, saboda irin wahalar da muka sha a rayuwa. Da wannan ɗan aikin da ummata take yi, nakan taya ta kullum, wani lokacin harda hajjo ɗin, saboda ƙauyen ana bala'n sarrafa dawa da gero da masara, kusan ma ince sune abincin nasu, wasu ma ko surfawa ba'a yi, a haka ake cinta datsa, wai tafi auki. To da wannan ƴar sana'ar ce muke samu mu ɗora tukunya kafin fa malam ɗin ya dawo. Malam yana matuƙar sona, yana ji dani kaman shi ya haifeni, haka tsakanin shi da ummata sai girmamawa da mutuntawa, ya ɗaukemu kaman wasu jinin shi, duk da na kula babu abunda ya haɗa shi da umman tawa ta fannin ƴan uwantaka. Sai ince mun samu so da ƙauna, da tattashi a inda basu dashi, basu da abun bamu, ko don saboda suma ɗin talakawa ne kaman mu? Oho... Nima saboda haka na fara yin ɗan kitso haka, ana bani naira ashirin ko shabiyar idan yara nayi mawa, manya kuma har talatin, ko a bani sabulu ko omon wanki, ko kuka ko kuɓewa, to dai mun gode, mun i-iya dasu tinda abun kuɗi ne, muma sai mun siya. Tini kayaaa suka fara dafewa, saboda tsabar rashin kyaun ruwan wankin da sabulu, dama wuta kuwa tinda muka je ƙauyen ban ganta ba, da idanuna kuwa. Haka muke ta ƙundunbala, rayuwa fa babu daɗi, matsatsin yayi mana yawa, a ƙauyen kowa da Hauwa yake kira na, saboda dashi Malam da Hajjo ke kirana, ita kuwa umma saidai tace man Mamana. Da ummata hanani fita take yi, duk da bansan dalili ba, saidai nafi alaƙanta hakan da wancen zaman da ummata tayi, a lokacin da akace an haifeni, gudun tsogunguma irin na karkara ya sanya suka shawarta hakan da malam. Saidai fa ban tsira ba, duk lokacin da na fita, haka zaka ga an hau danni ko ƴar katangar ƙasa, ana nuna ni da baki ana gulma ta, da zunɗena, har saida na samu ummata da maganar, ita kuma ta shawarce ni da kar indamu, dama dole hakan ce zata faru, saidai hakan ba wani abun damuwa bane, idan nayi la'akari da yanda aka yi aka haifeni har zuwa barin Umman tawa ƙauyen, da kuma dawowar ta katsahan.. Ta ƙara sanya ni cikin tunani mai zurfi, saidai banga fuskar tambayar warwara ba, nayi imani dai cewa ko badaɗe ko bajima dole ne komai zai fasu, dole akwai ranar ƙin dillanci, ranar da dukkanin ɓoyon da umman tawa take yi mani komai zai bayyana kanshi da kanshi... Muna cikin wannan halin ne, wata ranar talata da sassafe, sai ga wani yaro "wai ana sallama da Suhan" tinda naji hakan gabana ya faɗi, don dai a duk faɗin ƙauyen ba kowa ne ya san da wannan sunan nawa ba. Tin kafin in leƙa tsakar gidan, ummata da take zaune tana iza wutar ruwan kunu, tin jiya taci sa'a aka samo mata niƙan dawar da geron, da yake idan an haɗa su sunfi auki, ba ta daɗi ake ba tukun, niƙan ma da sai afi sati ba'a samo man da za'a tayar da injin ɗin ba, duk kuma ranar da aka samo, tofa ana kai wani lokaci ana niƙan saboda layi. "Inji waye?" Ummata ta jefa ma yaron tambaya gami da tsattsare shi da idanu, domin jin amsa. "Oho nima ban sanshi ba, wani ɗan gayu ne dai da mota, yana ƙofar gida" Yaron ya faɗa kai tsaye, batare da ya tauna maganar ba, ko ya kula da *Yo* ɗin da yace hakan ba tarbiyya bace ba. "Jeka abin ka" ta faɗa, tana mai zarar hijabin ta da take bisa igiya. Nidai ina tsaye bakin ƙofar ɗaki sai faman raba idanuwa nakeyi, hankalina fa duk ya tashi kar ace Bilal ne ko Ya Ameen suka gano inda muke. Tsaye ta tadda shi jikin mota, ganin babbar mace da yayi ya sanya shi saurin isa ta inda take tahowa ya durƙusa har ƙasa yana mai cewa "Ina kwana?" Cikin ƴar sarkin fuska jin daɗin ladabin da yayi mata, da kuma ƴar natsuwa data hanga tattare dashi ya sanya tace "Lafiya lau, wa kake nema ne?" "Tace mani Sunan ta Suhan" ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, saidai har yanzu kanshi a duƙe yake ƙasa, ƙare mashi kallo tayi tsaf, ba manyan kaya ne ba jikin shi, hasalima ƙananan kaya ne, daidai da gani yana cikin hutu, kayan shi ma sun nuna da yanayin shi, da kuma motar da yazo a cikin ta. Gabanta ne ya tsananta faɗuwa, tana tsoron masu kuɗi, tana gudun su, wasu kuɗin bala'i ne, wasu kuɗin masifa ne, masu kuɗin na zuwa wuta ne, lallai koma minene dole ta daƙile alaƙar nan da take shirin faruwa da ɗiyar ta. "Yaro Suhan ƴa ta ce, saidai kuma gashi ni ban waye ka ba" ta faɗa cikin manyance da dattako irin nata. Gaskiya yaji daɗi, ko haka aka tsaya ya fahimci tabbas yarinya ce mai gata da galihu, yarinya ce mai natsuwa, ko a sadda ya ganta wancen karon ya kula da haka, saidai ƴan matan na yanzu ba tuƙwane bane balle a kwankwasa su aji. "Eah mama, wato nayi mata alƙawarin cewa duk sanda aka koma makaranta zanzo in faɗa mata, gashi anyi sati da komawa wani uziri ya riƙeni, ni malami ne a makarantar da take, na kula ita sabuwar zuwa makarantar ce, shiyasa gashi kuma ga dukkan alama batasan kowa ba, ko hanya ma bata sani ba, shine nazo in faɗa mata, in ba damuwa ku bani izini in tafi da ita, gudun faruwar wani abu a hanya ko kuma a cen makarantar, nayi alƙawalin cewa da izinin Allah babu abunda zai faru, Amman fa in kun amince" Tinda ya fara magana bata katse shi ba, har ya kai aya, sannan ta jinjina kai, tana mai gyara tsayuwar ta, bayan ta ƙara nazarin shi. Ba ƙarya ko alamar rashin gaskiya a tattare dashi, duk da yanzu mugu baya da kama a fuska. "Tabbas ta faɗa mani hakan, kuma lallai batasan makarantar ba sosai daga nan, to saidai bana jin zan iya barin ta ta bika, alhalin kadai san ba muharramar ka bace, sannan ba sanin daga ina kake mukayi ba, kuma bamu da tabbacin kai ɗin malamin ne, saboda haka kayi haƙuri don Allah, mun gode da Alkhairin ka a gare mu baki ɗaya. Ka gaida gida" Tana gama faɗar haka ta juya zata shige gida, shima ganin hakan ne ya sanya shi saurin shan gabanta yana faɗin "Mama don Allah kiyi haƙuri, wallahi hanyar bata da kyau, naji idan ba zaku iya barin ta ita kaɗai ta bini ba, a haɗa ni da wani sai ya raka mu, alabasshi shi sai in sanya shi mota ya dawo nayi alƙawari" Dakatawa tayi ga barin shiga gidan da take da niyyar yi, sai kuma ta juyo ta fuskance shi "Kasan girman alƙawari kuwa?" Ta jefa mashi tambaya, gyaɗa mata kai ya shiga yi, ba tare da ya iya furta komai ba, zuciyar shi nata faman duka, sai kai komo take yi. Ko ba komai ya ƙagara a barta ta fito ko ya samu sa'ida, akan tunanin da yake wuni da kwana nata. " To shikenan tinda kace haka, Suhan zata fito yanzu ku tafi, na baka amana, kai da Allah kuma idan kaci, sannan inaso ka shige mata gaba wurin samun transfer da take so tayi, zuwa wata makarantar, ina so kayi mani wannan alfarmar" Gabanshi ne ya tsananta duka, shi yaushe ne zai iya barin ta ta samu transfer, yana kallon ya dace ya samu daidai inda yake so, burin shi ya cika, yaushe yana kallon ruwa kwaɗo zai yi mashi ƙafa? "Mama banyi katsalandan ba, ki gafarce ni, amman ba abune mai yuwuwa ba, duk kuwa da nake malami a jami'ar, saidai idan zaki iya faɗa mani dalilin ko damuwar, nayi maki alƙawarin zan san yadda aka yi aka kauce ma faruwar al'amarin" Ya faɗa cike da zullumin ko zata yarda da hakan. Saidai ga mamakin shi yaji ta fara cewa. "Eah, duk da bansan dalilina na yarda da kai ba, inaso ne ta samu canjin makaranta saboda bana so kowa ya gane tana makarantar, kuma koda wani zai zo ya binciki inda take, ba zai samu bayanin komai ba" Ɗan murmushi ya saki, duk da kanshi ya ƙulle sosai, to ta yaya za'ayi ace wani yaje neman yarinyar da take wannan surƙuƙin, ta yaya ma aka yi ya santa? Kenan akwai wani bayan shi? Lallai dole duk yanda za'ayi ya ture gwamnatin wancen ya kafa tashi, kai inaaaa, ai bama zai yuwu ya cire yarinyar a rayuwar shi bb,tayi mashi, kuma ya san irin zaɓin Ammin shi ce. "Insha Allahu umma, ai bama bada wani imformation ga wani na waje a cikin makarantar, akwai tsaro sosai, kuma nayi alƙawarin yin iyakar iyawata ta a kauce ma hakan, ita kuma ta samu Abunda taje nema insha Allah" Jinjina kai ta kuma yi tana mai cewa "Mungode kwarai, ina jaddada amana a hannun ka, marainiya ce, idan kaci amanar ta Allah ba zai barka ba kaima" Baisan lokacin da ya haɗe hannayen shi ba don daɗi, ai tini ya fara zuba godiya, duk son ya kauce ma fiddo farin cikin shi a fili, saboda wani zargin gazawa yayi. Itama ta ɓangaren umma ta tinanin hakan ta juya ta shige gidan, zuciyar ta na ta saƙa mata wannan farin cikin da ta gani akan fuskar shi na menene? Kauda mugun tinani tayi, tare da maye shi da na alkhairi, ta cigaba da addu'a har zuwa shigar ta gidan. A bakin ƙofar ɗaki dai ta tadda ni tsaye, sai zaro idanu nakeyi, "Jeki shirya ki fiddo kayan makarantar ki, malamin ku ne" Ta faɗa tana mai wucewa kai tsaye wurin tukunyar ta, da ta riga ta ta fashe tuni. Cikin murna da ɗoki na juya zuwa cikin ɗakin, ai ko ba komai ma, na ɗaga ma wannan ƙauyen da ya zame mani ƙarfen ƙafa, ba ruwa ba wuta, ba abinci mai daɗi, ba wurin kwanciya mai daɗi. A haka na shirya tsaf, na fidda kayan tsakar gida, ko ruwan kokon ban tsaya sha ba, saboda zumuɗin makaranta. A haka ummata ta har haɗa dubu uku da take ta maƙalo maƙalo da ita, gudun faruwar hakan, miƙo mani tayi gami da yi mani addu'a. Har tsakar gida ta biyo ni tana mai jaman kunne gani da cewa in kula. Hajjo da malam ma da bai tafi kasuwa ba, suma sun man ihisann su, na kuma ji daɗin shi, suma har waje suka raka ni, suna mai tayani ɗaukar kayana. Yana ganin fitowar mu, ya zabura ya buɗe mana but muka saka kayan ya kulle, ya zagaya ya buɗe man gidan gaba, na shiga gami da maida ƙofar ya kulle, shima zagayawa yayi ya shiga bayan ya gaishe da malam ɗin. A haka motar tayi ribos, ina ɗaga ma ummata hannu da take ta faman share kwalla da bayan hannuwan ta, nima ai sai naji kwallr ta cika mani idanuwa har bansan ta fara zuba akan fuskata ba. Har motar ta ɓace ma ganin su Umman sannan suka juya zuwa gida, yayin da ni kuma na sauke hannun ina mai sake rushewa da kukan da nagaza gane ko na menene, shin na rabuwa da ummata ne? Ko na murnar cikar buri na? Ko na halin da na bar umman tawa a ciki ne? Ko kuma mikin su Ya Ameen ne ya taso mani. (Hummm Suhan kenan) ******************* Cikin kwana biyun kuwa da aka ɗibar mashi jikin yayi sauƙi, haka aka lallaɓa dashi aka koma gida, duk da yanzu babu abunda ke damun shi, sai rashin ƙarfin jiki. Tin da Alhaji Mustapha yaga haka, yace zaman da su Nihal ɗin suke yi ya isa hakanan, su wuce kowacce ta koma ɗakin ta, haka duk ya tarkata su ya fafutuka su gida, ya rage daga shi sai Bilal da Abie sai Hajiya Kubra. Zaman hakan baya mashi daɗi, ya rasa dalilin da yasa tinanin Nigeria ɗin yayi mashi yawa, kuma kullum idan ya tambaya sai ace mashi lafiya lau, idan ya tambayi su Suhan kuma ace mashi tana makaranta, wai me ke faruwa ne? Wayar shi da number ɗin ta ke ciki kuma ta fashe kwatsa kwatsa bata ma moruwa, tin ranar da abun ya faru, gashi baiyi saving a mail ba, balle ya nemo. A haka ya tada balli cewa, shifa zai tafi nigeria yaga ya abubuwa suke ciki, hankalin su fa ya matuƙar tashi, Alhajin ne yayi dubarar hanashi, yace Bilal ɗin yazo ya tafi ya gano komai, amman shi da barin ƙasar kuma sai yanda hali ya nuna. Hikimar Alhajin nayin hakan kuwa shine, don Bilal ɗin yaje ya nemi su Suhan ɗin kafin komawar su ƙasar. To shima dai Bilal ɗin ya gane hakan, wannan ce ta sanya shi tarkatawa ya koma Nigeria ɗin, wanda tare da Hajiya Kubran suka tafi, saboda ta koma ma harkokinta tinda yanzu jikin yayi sauƙi, ba abunda ke damun shi illa su shegiyar yarinyar nan, to indai don wannan ne ba kuwa zai taɓa warkewa ba, saboda yanda suka sanya ƙafa suka tafi, sun tafi ɗin kenan fa. Bilal ya sha wahala sosai, duk inda ya san zai je yaje nema, har makarantar yaje lokacin da aka koma yajin aikin, Amman bai samu gamsasshen bayani ba, cewa sukayi har yanzu bata dawo ba, koma suce su basu sake ganin ta ba, da haka ya koma gida, tabbas ya shiga tashin hankali ba ƙarami ba, shi bama ta son da yake ma Suhan ɗin yake yi ba yanzu, ta rayuwar aminin nashi daya kula cewa lallai za'a sha darga idan ya gane cewa ta ɓata, bama asan inda za'a ganta ba, gashi kullum ya gwada layin nata akan ce mashi switche up, baya gajiyawa kullum sai ya kira ta kai sau goma. A haka ummin shi ke sanya shi gaba da ban baki, da ban haƙuri da kwantar da murya akan al'amarin, shi bai ma san ta yaya zai ɓullo ma al'amarin ba, ko kusan alama, bai taɓa tunanin idan zai iya shiga wannan irin halin ba a rayuwa. Ko aiki ya dena zuwa, gashi Al'ameen ya matsa akan yaje makarantar su Suhan ɗin ya bata suyi magana, ko ya haɗa shi da umma, idan ita Suhan ɗin tayi nisa. A haka abubuwa suka taɓarɓare, ba ga aikin kamfanonin nigeria ɗin ba, ba kuma ga na cen american ba, tinda tini shi Alhaji Mustapha ya koma cen ƙasar da yake aiki, ya bar shi daga shi sai Abie. Ƙarfe goma na safiyar litinin, Bilal ne zaune bisa kujera mai cin mutum ɗaya, ya zabga uban tagumi, ga stool ajiye gabanshi cike da kayan breakfast, so take yaci ko ya samu ya leƙa wurin aiki yau, rabon shi da zuwa office ita har ba zata iya tunawa ba, komai daga gida yake yi, ko kuma yace aje a samu mataimakin shi Peter, itama ummin zaune take gefe ta zuba mashi idanu, tabbas mijin nata yana cikin damuwa, to saidai ya zata yi dashi? Babu wani taimako da zata iya bashi a halin da ake ciki yanzu. Kaman ance ya latso number ɗin Suhan ɗin, aikuwa sai ta fara ringin, firgigit yayi ya miƙe daga tagumin da yayi, baisan ya fara kai komo ba, yana mai cewa "Comon pick it Suhan please" Itama ummin a zabure ta miƙe tana mai cewa "Ta shiga ne? Ta ɗaga ne?". Bai ko kula ta ba, ya cigaba da zagaye tanƙamemen falon, bata ɗauka ba, hakan ne ya sanya shi dunƙule hannu ya naushi iska dashi, gami da guntsar iska ya fesar, sake kira yayi Amman ta shiga ba'a ɗauka ba. Da hanzari ya fice daga falon, mota ya nufa da niyyar barin gidan, zuwa zai yi ya kai number ɗin ayi mashi tracking ɗinta, koma ina Suhan ɗin take yau ce ranar da zata bayyana, baya jin idan zai iya yafe ma duk wanda yayi sanadiyyar barin su gidan gabaki ɗaya a rayuwa. Ko ta kan ummi baibi ba, ya danna ma mai gadi horn, da gudu yazo ya buɗe mashi gate, ya ja motar a fusace yabar gidan, daidai ƙarasowar ummin da gudu tana ɗaga mashi hannu. "Wash" tace tana mai kai hannuwan ta bisa guiwoyinta kaman zata yi ruku'u, saboda tayi gudu ta gaji, daga falon zuwa harabar gidan da ƴar tazara, hakan ce ta sanya ta gajiya, ga kuma laulayi da take fama dashi. *Adai yi mani uziri, a kuma bini da Addu'a please* ~Oum-Deedat ce~ [10/1, 8:25 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)* *Page ~35~* *_Happy Indipendance Day To All Nigerias, Allah ya ƙara mana zaman lafiya kwanciyar hankali da wadata, yaba shuwagabanninmu ikon yi mana aiki da adalci bisa gaskiya. AMEEN_* ~Gaisuwa ga Lubabatu Funtua shima wannan Page ɗin naki ne, nagode da kulawa da ƙauna baki ɗaya~ *Aishatu Babayo Jos Mrs: Abubakar Yakubu (Ɗanjuma Master) ƴan golden pen suna yinki, ba zamu iya fasalta ƙaunar mu a kanki ba, saidai muce Allah ya bar mana ke, kiyi ta suburbuɗa mana comment Ameen* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Munyi nisa a tafiyar tamu da mukeyi zuwa makarantar, saidai ba wanda ke ceman wani ƙala cikin ni dashi,tin bayan gaida shi da nayi, lokacin da na shiga motar. Jefi jefi ya kan ɗan juyo ya saci kallo na haka, ni kuma sai in kauda kaina, tunani na yayi zurfi sosai, abubuwa da yawa nake saƙawa cikin raina, lokaci guda tunanin in sanya waya ta cikin caji a motar ganin cazar da nayi ya faɗo a raina. Jikkata na jawo gami da ɗauko wayar, a hankali na jona ta a cikin chajin,kaman jira take yi kuwa ta ɗauka, kunna ta nayi, lokacin da na kula ta kai kusan 5% na ajiye ta kusa dani. Har yanzu dai bai ce man uffan ba, tuƙin shi kawai yake yi, ganin hakan da nayi ne ya sanya ni janyo hijab ɗita na rufe kusan rabin fuska ta,gami da jingina kaina jikin ƙofar motar ina mai lumshe idanu, sanyin Ac na ratsa ni, haɗi da ƙamshin freshner ɗin dake cikin motar sun haɗu sun cakuɗe da ƙamshin turaren mutumen da ya kira kanshi da suna *Salim Bawa* Ban aune ba naji muryar shi kwatsam yana cewa "Maman ki ta burgeni matuƙa, haka nake son mace mai jajircewa akan ƴaƴanta, nima haka Ammi na take" Ɗan ɗagowa nayi a hankali, ina mai kai idanuna bisa ƴar kyakkyawar fuskar shi, sannan nace "Nagode" a hankali. Ɗan murmushi ya sake yi, sannan ya cigaba da cewa "ya kamata ki sake sanin ko ni wanene ko? Gudun kada in sace ki a rasa inda kike, gashi ba'a haɗo mu da kowa ba" Dam gabana ya faɗi, sake kai dubana nayi gareshi, ɗan murmushi na hanga saman fuskar shi, ga alama ma bai wani damu da abunda ya faɗa ɗin ba. Gyaɗa mashi kai kawai nayi ba tare da na samu zarafin ce mashi wani abu ba. Ganin hakan da yayi shima ya sanya shi sake sakin murmushi mai sauti. "Kaman yanda na faɗa maki gaskiya sunana *Salim Bawa Bala* mahaifi na shine Alhaji Bawa Bala idan zaki iya sanin sunan?" Ya faɗa da alamar tambaya a kan fuskar shi. Nan ma ɗan sake girgiza mashi kai nayi, duk da har yanzu ban ɗago ba, saidai na tattara dukkanin natsuwa ta akan shi. Jinjina kai yayi yana mai sakin murmushi da na kula hakan Al'adar shi ce, sannan ya ɗora da faɗin. "Ni ne ɗa ɗaya tilo a wurin Alhaji Bawa Bala, da Hajiya Khaltum Bawa Bala, duk kuwa da cewa mu biyu suka haifa ni da ƙanwata Asiya da taci sunan Kakata wadda ta haifi Babana Alhaji Bawa Bala, Shiyasa muke kiranta da Suna Imtihal ko kuma mu ce Imti. Ni haifaffen garin Adamawa ne a ƙaramar hukumar Yola, ni bafulatani ne Usul, duk kuwa da kasancewa ta baƙi. A gaskiya zan faɗa maki ina da aure harda yara biyu. Aisha Sholy da Usman muna ce mashi usi. Munyi auren soyayya da matata kaman me, iyaye na kowa na ƙaunar ta, saidai kasancewar faruwar wasu abubuwa ya sanya yanzu nake searching ina so in ƙara, saboda haka ina barar ko da acikin ƙawayen ki ne masu hali da natsuwa irin taki, a taimaka mani" Duk wannan maganar da yake yi, idanuna ƙur a bisa titi, dukkanin garuruwn da muke wucewa hankali na yana a kansu, saidai kuma kaf ina sauraren shi da kunnuwan basira. Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya na sauke, ina mai cewa "Allah sarki, nikam bani da ƙawaye, ka gaida man da yaran idan kaje gida da maman su" "Zasuji" Ya faɗa a gajarce cikin wani murmushin Ya buɗe baki kenan da niyyar sake cewa wani abu, sai kuma wayata ta ɗauki ƙara alamun kira ne ya shigo. Nima ƴar firgita nayi, ina mai sake waro idanu waje, lokaci ɗaya na yunƙura gami da wawuro wayar. Sunan *Yaya Bilal* na gani ɓaro ɓaro a bisa fuskar wayar yana yawo. Ba zan iya cewa ga halin da na tsinci kaina ciki ba, saidai a zahirin gaskiya na shiga matuƙar halin damuwa da firgita, ina cikin wannan halin ne har ta katse, wani kiran ya sake shigowa a lokaci ɗaya. Nan ma ban iya amsawa ba, har ta kuma katsewa, ai kafin wani kiran ya shigo nayi saurin kashe wayar gabaki ɗaya ma, gami da zare chajin na warware wayar gami da zaro sim ɗin sannan na maida batirin gami da sake jona ta cikin caji. Sim ɗin yana riƙe a hannu na, shawarar in jefar dashi nakeyi, ko kuma na adana, saboda kaman yanda ummata ta nuna mani a zahirin gaskiya bata so su san inda nake, ko kuma wata alaƙa ta kuma shiga tsakani na dasu. Shiru ne ya biyo baya cikin motar, babu abinda kake ji sai ƴar ƙarar Ac da kuma saukar numfashin mu. Duk da yana lura da abunda ya faru amman baiyi yunƙurin tambaya ba, domin yana ganin ba hurumin shi bane, ko kuma lokaci bai yi ba tukunna da zai kutsa kai a al'amarin yarinyar daga haɗuwa da ita. Daidai bakin gate ɗin makarantar yayi parking gami da ficewa ba tare da ya kashe motar ba, ba daɗewa ya dawo cikin motar hannun shi riƙe da layin Sim na Glo, miƙo mani yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba. A sanyaye na amsa gami da yi mashi godiya a hankali, lokaci guda na kuma zare chajin da har ya riga ya cika, sanya sim ɗin nayi da na kula yana da rigister already. Har cikin makarantar da department ɗin namu muka isa, shi ya shige mani gaba wajen cuku cukun komai, sai naga ashe ma HOD ɗin namu abokin sh ne sosai da sosai, ina zaune gefe ba wahalar komai aka kammala komai. Umurtata yayi da na bishi ya nuna mani hall ɗin da zamu rinƙa amsar lectures. Ko bayan dana fito daga office ɗin sai da ya tsaya suka sake wata magana da bazan iya cewa ga abunda suka tattauna na ba, sannan ya fito na bishi a baya har zuwa lecture hall ɗin namu da muka tarad da wani malami a ciki yana ba sauran ɗalibai lecturers, duk da na kula ɗalibai basu da yawa sosai, haka nayi sallama na shiga na zauna a kujerar da take gefe babu kowa a bisa ita. Shi kuma a daidai lokacin ya juya ya koma haɗi da yiman inkiyar yana jira na. Da idanu na bishi, lallai mutumen ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar karatun nawa, mutum ne shi mai zafin nama da yawan barkwanci a yadda na kula, sannan ɗalibai da dama sun sanshi duba da yadda naga ana ta gaishe shi bisa hanya sannan ana bina da kallo ganin ina binshi zarai-zarai a baya duk inda yayi. Hankali na na maida bisa kan lecturer ɗin namu dana lura sosai cewa ya iya koyarwa sosai, cikin salon turancin shi da yake fita sala-sala. Wata ajiyar zuciya na sauke, cikin son kauda tinanin komai a raina, zuciya ta fal da zumuɗi da farin ciki yau ni Suhan ce zaune a ɗakin ɗaukar karatu ina gaban malami yana koyar dani. *Ya Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar ta rayuwa, ka sanya hakan ya zamo mafi alkhairi a rayuwa ta, Ya Allah ka dubeni da idon rahma ka bani abinda nazo nema, ka bani ikon jure dukkan wani ƙalubale na rayuwa daka iya kutso kai a cikin rayuwar karatun nawa anan gaba* A haka muka cigaba da ɗaukar lectures kusan yinin ranar, ban kuma neman Sir, Salim ba kaman yanda Naji student na kiran shi. Daga Hostel ɗinmu zuwa lectures Hall da ɗan tazara ba sosai ba, hakan ce ta sanya na saki niƙab a hankali nake taka wa zuwa Hostel ɗin bayan mun gama dukkan darussan ranar. Waya ta ce ta ɗauki ƙara, da mamaki nake kallon fuskar wayar, ganin baƙuwar number, gashi dai na san yau na sanya layin babu wanda ya sanni da number ɗin. Ɗagawa nayi cikin siririyar sallama a bakina, daga cen ɓangaren Naji ance "Assalamu Alaikum. Idan kin gama kada ki wuce gani ta nan bayanki ina jiran ki" ɗaga wayar nayi a kunne na, gami da juyawa, ko ba'a faɗa ba na gane mai magana Sir Salim ne, shi komai nashi cikin zaulaya yake yin shi. Ɗan juyawa nayi a hankali, cen bisa bayan boot ɗin motar shi na hango shi zaune, kallon second biyar nayi mashi, har na ɗaga ƙafa da niyyar komawa ta inda yake, sai kuma naja na tsaya. Shima ganin hakan ne ya sanya yayi ɗan murmushi gami da dirkowa ya tako cikin tafiyar shi mai sauri ya iso inda nake tsaye kaman an kafe ni. Da murmushi ya ƙara so yana faɗin "Ya da haka kuma? Shikenan da ban ganki ba sai kuma gobe?" Ɗan girgiza kai nayi, sannan nace "A'a dama zan kira ka ne in na shiga ɗaki" daga haka ban sake cewa komai ba. "To ai shikenan, zan iya yin rakiya cen bakin hanya?" ya sake jefo mani tambaya cikin wani salon zaulayar Ɗan murmushi na saki ina mai jinjina mashi kai, sannan na juya muka fara tafiya, duk da akwai ƴar tazara tsakanin mu, kuma ba mai cema kowa ƙala, illa dai ɗan kallo na da yake yi akai akai, wannan ce ta sanya duk na takura, tinda hasali ni ba sabawa nayi da hakan ba. Har hanyar da zata sada ni da ɗakin mu ya raka ni, sannan yayi mani sallama ya juya yana faɗin zai kirani anjima idan na huta. Naji daɗi, ko ba komai dai na samu mai shige mani gaba, na samu mai tsaya mani da kula da dukkanin motsi na, wanda in nayi ba daidai ba zai iya cewa in bari. Da haka har na ƙara sa ɗakin da yake mallakin mu mu uku, ga dukkan alamu ma dai za'a iya ƙaro wata nan gaba mu zama mu huɗu. Waɗanda na tadda cikin ɗakin da gani dai basa da hayaniya, shiru shiru suke dan duk kansu karatu na tadda sunayi da litattafai a hannu, sallama nayi masu haɗo da yi masu sannu, sannan na hau shirya kaya na a ɓangare na, na gyara komai na kimlace. Sannan na shige banɗaki domin yin Alwala. ************************ Da matuƙar hanzarin shi ya isa ga tracking office ɗin, Allah Allah yake yi a kammala komai ya samu ya samo yarinyar nan tin kafin abokin nashi ya kuma tuburewa. Saidai babban tashin hankalin da ya same shi, lokacin da aka sanar dashi an fidda layin a kan wayar, kusan faɗuwa yayi, saida ya dafe bangon dake kusa dashi. A hankali ya jingina bayan shi da bangon, Ya Salam! Wannan wace irin rayuwa ce? Me hakan ke nufi? Menene dalilin su na aikata hakan? Da gangan sukayi kenan? Laifin ne suka aikata masu? Ina ita Umman take? Da hankalin ta zata ja yarinya su shiga uwa duniya inda basu da kowa?. "Huh" ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi jiki ba ƙwari yaja ƙafar shi ya bar wurin. Koda ya shiga mota yafi minti sha biyar ya gaza tada motar, hankalin shi bai sake tashi ba, saida kiran Al'ameen ɗin ya shigo wayar tashi, kaman ba zai ɗaga ba, sai kuma yayi tunanin kada Al'ameen ɗin ya zargi wani abu kuma, tinda ya san halin shi, shegiyar ƙwalwa Allah ya bashi. A haka ya ɗaga wayar, sukayi gaisuwa irin wadda suka saba da taɓa firar yanda abubuwa ke tafiya, har yake shaida mashi yaso zuwa Abba ya hana shi, shi ya rasa gane wannan dalilin hana shi ɗin. Kwantar mashi da hankali Bilal ɗin ya kuma yi tare da cewa yayi haƙuri har ya sake samun sauƙi. Yau ma dai saida ya tambayi yanayin karatun Suhan ɗin da ummr, ce mashi yayi suna nan ƙlau kaman koda yaushe, umma kuma tana cikin ƙoshin lafiya. Jin hakan da yayi ne, ya san aminin nashi ba zai yi wasa da amanar da ya bar mashi ba, ya sanya shi amincewa nan suka saki firar suka kama wata, sun kai kusan rabin awa suna magana mai muhimmanci sannan suka kashe wayar suna masu ƙaunar juna a ransu. Bai ma jin zai iya zuwa office ɗin, don haka gida kawai ya wuce kai tsaye, koda ummin ta ganshi ba irin tambayar da bata yi mashi ba, amman yayi mata banza dole ta haƙura ta ƙyale shi. Kwanciya yayi abun duniya duk ya ishe shi, yanzu haka rabon da ya ko leƙa gidan nasu Al'ameen tin bayan dawowar su ƙasar, to me zai je yayo? Alhaji Mustapha baya ƙasar, ba kowa sai masu aiki a cikin gidan, ko ita Hajiya Kubran ba zama take yi ba, kullum tana cen wajen harkokin ta arziƙi sai daɗa bunƙasa yake yi. Su mama Talatu an samu Abunda akeso, ana saka ta a wala, tashin hankalin su ɗaya ita da maree da har yanzu Al'ameen ɗin yaƙi ya dawo ƙasar balle su san yanda zasuyi su shawo kan matsalar tasu na yadda zasuyi su karkato da hankalin shi, koda kuwa da ƙarfin asiri ne, wannan daular basa jin zasu iya barin ta ta tafi a ɓagas. Tinda Hajiya Sa'a da Hajiya Laila suka tabbatas ma da Hajiya Kubran cewar, su umman fa sun tafi tafiya ta har abada ba waiwaye, sai hankalin ta ya sake kwanciya, kuɗi masu yawa ta narka masu wai tukuici, yanzu tana jin ta bata da matsala sai guda ɗaya, yayi yazo ya fidda matar daya dace ya aura kawai, ƴar manyan guda ƴar wani ƙusa a gwamnati ko ɗan kasuwa, ta yadda za'a dinga labari a ƙawaye cewa ita surukar wance ce a ƙasar ta nigeria. Saudat basa ƙasar ita da mijin ta, Nihal ce kaɗai, itama kullum tana gida, ganin mijin ba zama yake yi ba, data dawo daga wurin aiki gida take wucewa ko gidajen ƙawayen ta, sai ta muka tasha iska sannan ta koma gidan. Hakan ce ta fara sanyawa ƴan ƙananan maganganu tashi a family ɗin mijin nata har maganar ta koma kunnen shi, duk da suke sangartattu ƴaƴan masu dashi, hakan baya mashi daɗi, ai auren ta yake yi, yana da haƙƙin duk inda zata je ta sanar mashi koda kuwa ba zai barta ba. Sun fara samun saɓani akan hakan, inda ta nuna mashi Sam hakan fa ba mai yiwuwa bane, tana da ƴan cin da zata iya aiwatar da komai batare da ya sani ba, tinda auren ta yayi ba siyen ta ba. A haka ya ƙyale ta yana mai ƙudurce ɗaukar mataki domin kuwa shi fa Sam ba zai iya lamunta ba, ko ba komai ai yana kallon matayen abokan shi ba haka suke yi ba, kullum suna gida ko wurin aiki kawai, Amman ace mace kullum ta fita sai taje gidan su? Wata rana ma acen take kwana koda kuwa yana ƙasar? Kuma iyayen ta na kallon ta ba tare da sun saɓa ko tsawatar mata ba? Shi a gaskiya ba zai iya ɗaukar wannan rainin wayon ba, gashi ace mace bata iya komai ba, duk tabi gida ta cika da ƴan aiki maza da mata, duk da hakan ba wai baƙon shi bane ba, amman shi sam baya da ra'ayin masu aiki barkatai a cikin gida saboda halin tsaro na rayuwa. ***************** Cikin Hafsat ya tasa inda Sadeeq ɗin ya maido ta nigeria ɗin yace ta zauna, saboda yana ji da cikin baya son dukkan abunda zai dame shi ko ya taɓa mashi lafiyar ɗa, to itama ɗin tafi son hakan, domin yanzu idan Kaga Hafsat ba zaka ce ita bace, tayi ɓulɓul duk da dama ita ɗin ba wai mai rama bace dama cen, fatar ta ta kuma haske da sheƙi, yanzu ta samu aiki da Federal Goverment, mijin nata shi ne ya sama mata, saboda rage zaman kaɗaicin. Hafsat tasha kuka lokacin da taji labarin ɓatan su suhan ɗin, kuma tayi imanin ba banza ba, hakanan Umma ba zata buƙaci da su bar gidan ba, a daidai gaɓar da Suhan ɗin zata tafi makaranta. Tana addu'a Allah ya bayyana su, ya kuma saka masu zaluncin da aka yi masu a koda yaushe. Bata da kaɗai ci sosai, yanzu Alhaji Awwalun da Hajiya Zainab sun tattara sun dawo gidan da dangin Sadeeq ɗin suka basu nan Abuja ɗin, kaman yanda su kuma kamfann Al'ameen ɗin suka ɗauki matasan da aka alƙauranta masu aiki daga cikin dangin sadeeq ɗin. Hafsat ɗin na zaune da dangin mijin ta lafiya, kowa na son ta yana yabonta, to su ɗinma mutanen kirki ne, sun san haƙƙin ɗan adam, masalan ma ita da take mata ga ɗan uwansu, suna mata kallon kaman ɗan uwan nasu duk da sun kasance sun fi su Hafsat ɗin komai hakan baisa suke nuna mata sun fita ba, ko kuma wariyar launin fata. ***************** Haka rayuwa ta dinga garawa,awanni sun shuɗe, kwanaki sun shuɗe, makonni sun shuɗe, gashi har muna fuskantar wata biyu da zuwa makaranta, karatu nakeyi ba ji ba gani, duk da yanzu na fahimci dukkan Abunda Sir, Salim yake yi mani da biyu yake yin shi, tinda sau da dama zaka ji labari na tashi wai ni budurwar shi ce, babu Abunda ke shiga tsakanin mu in ka ɗauke taimako wani lokacin da kuma ƴar fira ta barkwanci haka, to nidai ta ɓangare na babu Abunda zan iya cewa ina ji game dashi, duk da yake kasancewar shi mai barkwanci da yawan ban dariya, bayada matsala da kowa da komai, saidai Abunda na kula, ki dai baya tare da matar shi, ko kuma baya jin daɗin ta ne, domin baya yadda ya bani labarin ta, kullum dai labarin bai wuce na Ammin shi ko kuma na Sholy da Usee, to nima nafi son hakan tinda sha'ani ne na iyali. Har da Ammin shi ya haɗa ni na gaida ta, yanda naji muryar ta mai sanyi sosai, da yanda ta amsa mani kaman zata rungume ni cikin wayar hakan yayi mani daɗi, ashe a duniyar nan akwai wanda zai soni ya tattashe ni kaman yanda Sir, Salim da mahaifiyar shi suke yi, tin kwanaki da yaje gida, sha tara ta arziƙi da kuɗi sosai ta bashi ya kawo mani, da kam bazan amsa ba, har saida ya kira ta, aiko tace ya bani wayar, ya kuwa bani ta hau faɗa, wai ashe ban ɗauke ta uwa ba, da har zata bani abu inƙi ƙarba, haƙuri na shiga bata gami da yi mata godiya. Kewar ummata ta addabeni sosai, ji nake kaman in buɗe ido in ganta a inda nake. Ban ƙwauron baki ba, na faɗa ma Sir Salim kaman yanda ya zama abokin shawara ta a yanzu, duk yanda zai yi ya shiga jikina yayi, ina jinshi kaman ɗan uwanka yanzu uwa ɗaya uba ɗaya, masalan da na kula dashi kamilin mutum ne, ko a makarantar kaf an bashi shaida, ba dai kiji ance yana kula mata ko hulɗa dasu ba, duk da an sanshi da barkwanci, wanda barkwancin ma ne ya sanya ni sakin jiki dashi ba tare da na kula ba. Kaf makarantar babu wacce zan nuna ince itace ƙawa ta ko aboki ya ta, saidai wanda muke ɗan gaisa wa dasu sama sama sai kuma ƴan ɗakin namu da suma ba hayaniya ce ta sha masu kai ba, kowa karatun shi yake yi hankali kwance. Haƙuri ya bani gami da cewa insha Allah zanga ummata very soon, nidai kawai inyi karatu, ban da matsalar kayan abinci ko kuɗi, duk Ammin Sir, Salim ta aiko mani dasu masu yawa, tin bayan daya bata labarin gidan namu, da kuma ƴar fahimtar da yayi cewa karatun dai ne nakeso inyi aman ba tare da muna da ƙarfin hakan ba. To itama dai burin Hajiya Khaltum ɗin shine dai yaron nata ya samu ya daɗa wani auren, ko hakan zai sa Ma'un ta cenza hali, domin Sam basa jin daɗin ta, mace ce wadda zamu iya cewa rako mata tayi. Sam bata da Sirrin kanta, batasan yanda zata zauna da kowa lafiya ba, ga bala'n kishi kaman zata mutu, kasancewar mijin ta lecturer, ya sanya ta sanya ana binciken shi ta bayan fage ba tare da ya sani ba. Masifar ta tayi yawa, saboda haka ne, ko lokacin daya koma gidan ta same shi da maganar cewa ta san dukkan Abunda yake aikatawa a makarantar na neman wata yarinya, Sam bai ɓoye mata ba, yace aure yake so ya ƙara, aikuwa masifa da bala'i babu wanda ba'a sha ba, har barin gidan nashi tayi, ta kuma bar mashi yaran, hakan ce ta sanya ya kwashe su ya kai ma Ammin shi, to ita ɗin ba mai masifa bace, ce mashi tayi yake ya lallashi matar shi, da taga ya kafe ne akan ba zai je ba, sai tace mashi ya tafiyar shi, idan Ma'un ta huce ta dawo an maida mata yaran. Haka kuwa aka yi ya sake juyo ma da Suhan sha tara ta arziƙi daga Ammin tashi, bai ƙara so ba saida ya tsaya ya taho da Ummana domin tazo taga inda nake karatu. Yanzu kam ta fara yarda da Al'amarin yaron, tin bayan da suna cikin mota ya haɗa ta da Ammin shi suka gaisa sosai, har tana ce mata sai ta kawo mata ziyara har gida. Murmushi ummata tayi tana sake yi mata godiya da ɗawainiya da yaron nata yake yi da Suhan, sannan tace mata sai tazo, sallama sukayi suka kashe wayar, da ɗan murmushi ta miƙa ma Sir, Salim wayar da yake cen gaba yana driving, ita kuma ita da Hajjo a bayan motar har zuwa shigar su makarantar tamu. Kwatsam sai ga ummata daidai lokacin da na fito da niyyar zuwa masallaci sallah, aikuwa da gudu na ruga na rungume ta, kwalla na shatata a samn fuska ta, janye jikin ta tayi tana girgiza mani kai, Hajjo na gaida, gami da ɗan kallon Sir, Salim da ya kafe ni da mayatattun idanun shi, da a yanzu na fara jin nauyin su a kaina bansan dalili ba kuma. "Zamuje ɗaki Sir, Nagode Kwarai" Abunda na faɗa kenan ina mai sauke kwayar idanuna ƙasa. Ɗan jinjina mani kai yayi yana mai juyawa ya shige motar shi gami da barin wurin bayan yayi masu umma sallama akan cewa zai je ya dawo. Haka muka ranka ya har ɗakin namu. Ba kowa ciki duk suna wurin lectures, rasa inda zan ajiye su umma nayi, salla suka fara yi, ni kuma na fara nema masu Abunda zasu ci. Wata yarinya ce tayi sallama da manyan ledoji a hannun ta ta miƙo mani wai inji Sir, Salim. Amsa nayi ina mai godiya gami da buɗe ledojin, take away ne manya, shinkafa ce jalop da taji kayan haɗi, sai manyan kaji guda biyu da lemuna masu sanyi, ai sai na kashe stove ɗin ba jawo plate na juye masu gami da sanya masu chokulla na ɗauko cups na shan lemon na ajiye masu. Basu ɓata lokaci ba wajen cin abincin, so suke su juya saboda kada suyi dare. Nasiha da wa'azi da jan hankali babu wanda ban sha ba, nan umma ta kawo kuɗi dubu goma ta bani tana mai ƙara bani haƙuri, akan cewa yanzu taga wuri akai akai idan ta ɗan samu wani abu zata dinga zuwa tana kawo mani insha Allah. A haka suka gama, na kira Sir Salim ɗin, cewa yayi yana waje yana jiran su. Kaman kar mu rabu haka naji, aiko saida bayi kuka sosai har na ƙaryar ma da ummata zuciya, itama saida tayi kwalla Hajjo ce taje bamu baki, haka na juye masu sauran naman da lemon nace ko Malam ne sa kai mawa, aiko Hajjon taji daɗi sosai ta yadda ban manta malam ba, to nikau ina zan manta mahaifi na? Tinda yanzu shine nake ma kallon uba a wuri na. Har bakin mota na raka su, da kanshi ya fito ya buɗe ma ummata ni kuma na buɗe ma Hajjo, bayan sun shiga ne ya tsattsare ni da idanu wa alamar tuhumar kuka na menene nakeyi? Girgiza mani kai ya shiga yi, alamar kar nayi kuka, ya shiga motar yana mani inkiyar zai dawo. A haka ina ɗaga masu hannu har motar ta fuxe daga harabar makarantar, juyawa nayi jiki ba kwari, zuwa ɗakin namu. Kuka nasha kaman ba gobe, ummata duk wahala ta sanya ta ƙara tsufa, kaman ba ita ba, Allah ya sani tausayn kanmu da kanmu ya kama ni, dole in maida hankali inyi karatu ko hakan zai zama silar fitar mu a wannan ƙangin rayuwar. Saida ya tabbatas ya sanya su mota mai kyau ya biya kuɗin motar, sannan ya basu wani abu yace su riƙe su sha ruwa a hanya, ummata ƙin karɓa tayi, sai Hajjo ce ta sanya hannu ta karɓa, suka sake jaddada godiya, ummata ta sake bashi amana, sannan ya juyo ya dawo makarantar. Kirana yayi na fita, nan ya shiga sake lallashi na, da yake mutum ne shi mai barkwanci, sai gashi bamu rabu ba, saida ya sanya ni dariya sosai da nishaɗi. Sannan ya kira Ammin shi da yaran shi muka gaisa yana ce masu ga Auntyn su su gaida ta suka hau tsalle suna mani gwarancin da bazan iya ganewa ba, da yake Ma'un bata koma gidan ba har yanzu, ita kuma Ammi taƙi zuwa, tace ai tinda babu abunda aka yi mata idan ta huta ta koma da kanta. A haka mukayi sallama ta kashe wayar, ƙaunar yarinyar na malala a cikin zuciyar ta, ga dukkan alamu yanzu ne yaron nata ya samu mace mai hankali da natsuwa wadda zata iya kula mashi da gidan shi da yaran shi, don ita talaucin su ba matsala bane a wurin ta, tinda ta san mai duka ne ke yin komai. Haka rayuwa take tafiya, ɗan adam ba don ya kula ba, saidai kawai yaji shi a cikin kabari. Gashi har zamu fara semester exam, karatu ya ɗauko zafi sosai, don ma Sir Salim na taimaka mani sosai, lectures take mani a duk lokacin da muke free bama komai, kuma ina ganewa sosai da sosai, kwatsam sai ga Ma'u a makarantar mu, lokacin muna zaune ta cen baya inda ɗalibai ke zaman karatu. Mun duƙufa muna ta karatu sai naji an ja hijab ɗita ta baya sosai kaman za'a shaƙe ni, aiko da hanzari na ɗaga domin ganin ko wacece, ganin bansan fuskar ba, sai na zare hijab ɗin baki ɗaya na sakar mata ita a hannu, gami da miƙewa na fuskan ce ta ina mai cewa "Baiwar Allah lafiya kuwa? Me na aikata maki haka da zafi da kike beman shaƙe mani wuya?" Da hannu ta nuna mani Sir, Salim wanda ya riga ya miƙe mamaki ya kama shi har ya gaza cewa komai "Me ya haɗa ki da mijina?" Ta jefo mani tambaya cikin hargagi ta nayi tana jijjiga jiki. Kallona na maida kan Sir Salim da har yanzu ya gaza cewa komai "Au Malam? To ai gashi tsaye shi zaki tambaya ba wai ni ba" na maida mata da amsa cikin son kawar da tsoron ta daga zuciya ta. "Au dama kece yarinyar da akace kinbliƙe mashi kin hana shi saƙat a makaranta?" irin ku dama ba karatun ke kawo ku ba, neman mazan mutane kuke zuwa nan yi.... " " Asma'u" Sir, Salim ya katse ta cikin ɗaga murya yayi kanta kaman zai bugeta. Sai kuma ya dakata yana faɗin "Me kike yi ne haka? Me ya kawo ki nan makarantar? Kinzo ne ki ɗaga mani hankali ne? Ki kiyaye ni fa, da izinin wa kika zo?" "To dama da izinin wa kake so nazo ne? Ko har yanzu da bana zaune gidan ka nema kake yi in nemi izinin ka idan zan fita?" Nikam sun ma ɗaure mani kai wallahi, gani dai tsaye ba hijab jikina yana hannun ta duk ta cukuikuye shi, inda Allah ma ya taimake ni kayan jikina doguwar riga ce mai faɗi, sai na sanya hannu na warware gyalenta ɗana ɗaura bisa kaina. " Eh ko da baki gidana, ai da aure na a saman kanki, idan baki sani ba yanzu ki sani, kuma wannan ita ce yarinyar da kikaji labari, kuma ki sani ba liƙe man tayi ba, ba naniƙe mani tayi ba, hasali ma nine na liƙe mata na naniƙe mata, Abunda nake so ki sani, da batasan me ke faruwa ba, batasan dalilin da yasa nake tare da ita ba, Amman yanzu kinja zata sani. Wannan ita ce Suhan wadda kikaji labarin ina nema, kuma wadda na faɗa maki cen baya cewa *Son ta nakeyi, kuma auren ta zanyi har Ammi ma ta san da zancen* " Cikin matuƙar tashin hankali da jin kalaman Sie, Salim ga matar tashi na ɗago idanu ina binsu da kallo, ga kuma student ta duk suka zagaye mu suna kallon mu, sai ƙus-ƙus suke yi, waɗanda dama cen sun jima suna son Sir Salim ɗin murna suka fara yi, suna gode ma Allah da basu ne hakan ta faru dasu ba. "Ai wallahi ko wacece ta san da zancen ba Ammi ba, bata da hurumi a gidana, baka isa ba, wallahi kayi kaɗan Salim, ni zaka tozarta ka wulaƙanta kan wannan ƴar abun?" ta faɗa tana mai nuno ni da hannun da hijab ɗin tawa yake kai, sannan ta ɗora da faɗin. "Wuuu Amman dai wallahi kaji kunya, inaso ka sani wallahi tallahi idan ta kuskura ta shigo gida na, sai ta kwashi kashin ta a hannu, kuma mu zuba mu gani shege ka fasa" ta faɗa tana mai maida kallon ta bisa kaina da nake tsaye kwalla ta cika man ido taf, Amman na kasa barin ta ta zuba, saboda gudun raini daga wurin ta, jefo mani hijab ɗita tayi tana mai kyasta mani yatsu alamun in kiyaye, sannan ta juya a sukwane ta nufi motar ta, ta shiga ta fisge ta da matsanancin gudu tabar wurin. Rasa abund zanyi nayi, saidai na zuƙunna na shiga tattara litattafai na, da kayan karatu na, na ɗauki hijab ɗita da duk ta duƙunƙune ta, na juya da niyyar barin wurin. Gabana ya sha, haƙuri ya fara bani, girgiza mashi kai na shiga yi alamun babu komai, wani tsumammen kuka yana mai taho mani, duk kunya ta gama kama ni, masalan da ma abun ya faru akan idon ɗalibai, yanzu makaran ta zata ɗauka, yanzu zan fara rashin sukuni a makaranta, ai bansan haka halin matar shi yake ba, da ko alama ma bazan yadda in saki jiki dashi haka ba sosai. Zagaye shi nayi da ɗan gudu na, na nufi hanyar da zata sada ni da ɗakin namu, yayin da na bar shi na tsaye sororai abun duniya duk ya dame shi. Dole ne kuwa yau yayi ma abun tufkar hanci, dole ne ya dakatar da kuma faruwar hakan, shima a matuƙar zuciye ya shiga taka wa kaman ingarmn doki zuwa wajen da motar tashi take ajiye ya shiga gami da fizgar ta kaman zai taka mutane haka yabar makarantar da matuƙar ɓacin rai. Nasha kuka na, ƴan ɗakin mu na bani baki, lallai sunga Abunda ya faru dukan su, domin an taru sosai a wurin, saboda haka ne ma suka bani shawara da in ɗan ja jiki da Sir, Salim indai ina so in tsira da mutumci na, saidai fa har yanzu mamakin kalaman shi basu sakeni ba, yaushe ne ya fara sona har haka da har yake cewa Ammin shi ta sani? Yaushe yaje masu da maganar son aurena ni Suhan? Anya kuwa ba ɓatan kalamai yayi ba kuwa? Da haka na zame na kwanta idanuna rufe ruf, babu abunda ke kai komo a ƙwalwa ta illa iyaka maganar da ya faɗa ma Matar tashi. Wayata ce ta ɗauki tsuwwa, sunan Ammi na gani a bisa wayar, sai na Gaza ɗagawa, illa ma wani sabon kukan daya zo mani, gashi ummata bata da waya, koma tana da ita ƙauyen babu service da ko ita ce zan kira ta inji muryar ta ko naji sauƙi. Daga wannan sai wannan, na rabu da cen da duk abunda ya shafi cen, sai ga kuma wata ta kunno kai nan, ya zanyi da rayuwa ta? Ya zanyi da wannan al'amari dake faruwa dani ne? Karo na barkatai kenan da tinanin Ya Ameen ke faɗi mani a cikin ƴan kwanaki nan, tinani na ne ya tsaya cek, lokacin da Fuskar Al'ameen ɗin da yanayin shi suka faɗi mani a rai, ko yana ina?ko a wanne hali yake yanzu ciki? Ko ne yake yi? Ko ya yaji lokacin da ya samu labarin tafiyar mu? Wani abu Naji yana kwarara a dukkanin ɓargon jikina, malala yake yi zuwa dukkanin wani ɓangare na jikina. Ai tuni na fara rawar sanyi, zazzaɓi mai zafi ya lulluɓe ni, wani Al'amari nake ji ayau dana tuna da jigkn Rayuwar tamu a da...... Ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba a haka.... ~Oum-Deedat ce~ [10/2, 1:28 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)* *Ahmad Deedat yana gaida duk masoya shi, da masu cewa suna so shi, da masu cewa sunan shi na burge su, da masu cewa a basu shi, da masu cewa sun kama ma ɗiyar su, da masu cewa Allah ya basu irin shi. To duka dai ina maku fatan alkhairi, da fatan nasara a rayuwa. Mungode kwarai da gaske Allah ya bar ƙauna da zumunci. AMEEN YA RAB.* *Page ~36~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Juye juye yake ta faman yi, ya rasa abunda ke mashi daɗi a duniyar nan, shi fa gabaki ɗaya hankalin shi ya karkata zuwa ga ƙasar tashi, ga wani al'amari cen ƙasan zuciyar shi dake ta faman taso mashi. A hankali ya sanya hannu ya ɗauko wayar tashi dake bisa side drower. Gallerry ya shiga, tini hotunan bikin su Saudat suka bayyana. A hankali a hankali yake bin hotunan da kallo har yazo kan daidai nasu, lokacin da yake riƙe da ita ranar yinin biki. Hoton ya ɗauku iya ɗaukuwa, sunyi matuƙar kyau kaman wasu couples, ɗan yatsan shi ya sanya yana shafa fuskar wayar, a hankali yake sauke numfashi, ya kamata ya san halin da take ciki, sai yanzu ne ya gane ashe maganar aurenta da yayi, maganar son ta da yace yanayi a cikin wasa ashe ba wasa bane, zahiri ne, shi mai yasa ma bai fahimta ba a duk tsawon lokacin da ya kwashe da ita a rayuwa. Minimize yayi tare da shiga contact, ya san wa zai kira, ya san inda zaiji haƙiƙanin abunda yake aukuwa a rayuwar suhan ɗin dama ummata tata. Ya kula sarai da Bilal akwai abunda yake ɓoye mashi shi da Dad ɗinshi, to koma dai miye yau zaiji, yau ne ranar da ya yanke ma kanshi sanin koma meke faruwa, faɗuwar gaban shi tazo ƙarshe yau da izinin Allah. Daidai kan sunan ta yaja ya tsaya, kiranta yake son yi, amman hannuwan shi sun gaza latso number ɗin. Shahada yayi wajen kiran, saidai zuciyar shi kaman zata tsago ƙirjinshi ta fito saboda tsabar dukan da takeyi. Bai aune ba yana ta faman tunani, sai jin muryar ta yayi ta cen ɓangaren tana sallama. Hankalin shi ya maida kacokam kan wayar, yana mai amsa mata sallamar da takeyi mashi "Yaya ina kwana ya ƙarfin jiki?" Bai ƙasa a guiwa ba wajen bata amsa, duk da kasancewar shi miskili na bugawa a mujalla, sai gashi yau yana rawar baki wajen amsa ma ƙanwar tashi. "Jiki Alhamdulillahi Hafsat Ya Sadeeq ɗin ya kuka koma gida kuma?" "Lafiya Lau Yaya, to Allah ya ƙaro sauƙi". Ta faɗa mamaki fal cikin ranta jin wai yau Ya Ameen ne ya kira ta a waya. Katse mata tunanin yayi wajen cewa "Hafsat wata magana na kira ki muyi cikin sirri, amman inaso ki taimaka mani wajen sanar dani gaskiya, ke kaɗai ce na san ba zaki ɓoyeman komai ba gudun cutar da Ƙawar taki" bai jira cewar ta ba ya cigaba da cewa "Maganar ƙawarki Suhana da kuma ummanta, kwana biyu na bar jin ta, duk da Bilal ya faɗa man tana makaranta Umman kuma tana cikin ƙoshin lafiya, saidai zuciya ta ta gaza yarda da hakan, nakan gazgata shi a duk lokuttan da yake sanar dani hakan, sai nake ganin kaman akwai wani abu da yake binne mani ne shida Dad, shine dalilin da yasa ke na kira ki domin ki bani cikakken bayani, kuma ki turo mani number ɗinta saboda in nemeta" Ɗan shiru yaji tayi ta cen ɓangaren, ga dukkan alamu dai ta shiga komar tunani ne, ga mamakin shi cen kuma sai yaji ta fashe da kuka ta kashe wayar. Ai bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba, jikin sh na ɓari, "Hello Hello Hafsat" Abunda ya cigaba da cewa kenan, duk da ya san ba fa lallai bane ta amsa mashi ba, tinda ta riga ta kashe wayar. A fusace yake taka wa ya shiga kai komo a tsakiyar tanƙamemen falon da babu komai ciki daga gado sai mirror da labulaye, ko sif ɗin ta cikin bango ce, ba wani hayaniya mai yawa a cikin ɗakin. Hannun shi ya zura cikin sumar shi mai taushi da santsi yana shafa kan a hankali, yayin da gudan ya dafe ƙugu dashi a haka yake ta faman safa da marwa, idan ya gaji sai ya dunƙule hannu ya kaima iska naushi. "Oooops Ooops Bilal why? Meyasa kayi haka? Me yasa ka ɓoye mani da matsala ne? MOOOOOOM Mom, Mom tabbas koma me ya faru da sanya hannun ki, Dad why? Meyasa ka taimaka wajen ɓoyeman komai ne? Na cencenci haka kuwa daga gareku? Cikin hanzari ya jawo jikkar shi ya shiga ɗibar kaya daga wardroop ɗin yana cusawa, ba tare da ya tsaya ma shirya su ba. Abie yayi ma waya akan ya baro Office ɗin yazo ya same shi gida. Da mamaki Abie ɗin ya taho akan kiran gaggawa da yayan nashi keyi mashi. A tsaye ya tadda shi kaman zai sanya gudu, da hanzari ya ƙara so yana mai tambayar yayan nashi ko lafiya? "Abie akwai wani muhimmin aiki ne daya taso mani a nigeria, so bana so kowa ya san na tafi har Dad da Mom kai ko Bilal bana so kowa ya sani har inje in dawo, saboda idan suka sani ba zasu barni bane" ya ƙarshe yana mai ɗaukar makullin mota gami da cewa "Muje ka kai ni Airport yanzu ka dawo da motar" "Amma yaya jiya mukayi waya da Bilal bai ce mani akwai wani aiki ba da har zai sa ka tafi, bayan kasan Dad baya son tafiyar taka har sai ka ƙara jin sauƙi" A sukwane ya juyo gami da dakatar da Abie ɗin ta hanyar ɗaga mashi hannu "That Is what i said, koma minene ayau ɗinnan zan bar ƙasar nan insha Allah, idan Kaga dama ka faɗa ma koma waye ne kada kaja bakinka kayi shiru" Yana gama faɗin haka ya sake jan jikkar shi ya fice daga ɗakin, to shima dai Abie ɗin baya da zaɓi, illa bin bayan shi yayi ya iske shi yana saka jikka mazaunin baya, gami da cilla ma Abie ɗin ɗan makullin. Caɓewa yayi sannan ya shiga shima ya zauna bayan Ya Ameen ɗin ya zauna, ya harba motar bisa titin da zai sada su da Airport ɗin..... Bai sha wahala ba, kasancewar lokaci zuwa lokaci ana mashi renewing ɗin bisa ɗinshi, hakan ce ta sanya ticket kawai ya yanka nan da rabin sa'a jirgin nasu zai ɗaga. Abie bai bar Airport ɗin ba, saida yaga tashin jirgin su Al'ameen ɗin sannan ya juya zuwa office zuciyar shi na ta saƙa mashi tana warwarewa, saidai yayi imanin babu wanda zai faɗa ma wannan tafiyar ta ɗan uwan nashi, kai koda kuwa ace Dad ne zai kira ya tambaya ba zai taɓ bari ya fahimci Yayan nashi baya ƙasar ba. (To gadai su Al'ameen an nufi nigeria ko ya zata kaya kuma?) ******************* A haka na kwana juye juye, Sam bana da walwala, ina ganin kiran Sir Salim na shigowa a wayar tawa, Amman na kasa ɗauka, so nake in kiyaye shi, bana so in sake komawa cikin wata matsala daban kuma bayan wadda na baro. Tabbas Sir Salim bai ɓoyeman ba akan cewa yana da mata, to saidai bai sanar dani halin ta ko kuma yadda take ba, bai faɗa man zata iya aikata hakan ba, tin farko ma da ban saki jiki dashi hakan ba. Ina kallo text ɗinshi ya shigo wayar tawa, amman na kasa buɗewa balle in karanta inga abunda ya ƙunsa. A haka har gari ya waye nayi shiri na zuwa darasi, Amman jikina a sanyaye yake ƙwarai matuƙa, duk inda na gitta da kallo ake bina hakan ce ta sanya ni komawa ɗaki na ɗauko niƙab na sanya a saman fuska ta, gudun mayen kallo daga ɗalibai, kunya duk ta riga ta gama cika ni. Ba don Jarabawar da zamu fara ba, to da bana jin ma idan zan iya zuwa wata lecture ayau saboda abunda ya faru jiya, to saidai koda ma ace na zauna ne, babu abunda zan iya taɓukawa sai tinane tinane, tinda ƴan ɗakin mu basa wasa da karatu ba wani zama muke muyi ta fira ba, karatu shine kashi 80 a cikin ɗari na firar tamu. Har muka gama lecture ta farko muka shiga ta biyu, itama muka gama, ban kuma jin ɗuriyar Sir Salim ba, ƙarfe huɗu ne bayan mun fito masallaci muka nufi hall ɗin domin ɗaukar lecture ta 4-6. Saidai kafin in idasa shiga hall ɗin wata budurwa ta ƙara so tana tambaya ta wai nice Suhan Moh'd? Da Kai na amsa mata, saboda magana ma yau mai ƙarfi gagara ta takeyi, da hannu itama ta nuna mani wata dunƙulalliyar mota jikin ta wata mata ce tsaye, saidai da yake da ƴar tazara tsakanin mu, bana iya shaida fuskar ta ko kuma ta maza guda biyu da suke tare da ita, sannan ta shiga cewa "Waccen matar ce tace in kira mata ke" tana gama faɗin haka ta sanya kai tayi wucewar ta. Ɗan jim nayi kaman ba zani ba, sai kuma na juya a hankali na shiga taka wa ina nufar wurin, mota ce mai masifar kyau sabuwa dal Ash colour, matar da take jikin motar ta jingina bayan ta jikin motar, hannun ta ɗaya jikka ce da take riƙe da ita ƴar madaidaiciya, sai hannun ta da yasha jan ƙunshi cije yake taf da zobuna da awarwaron gold riƙe take da waya tana latsawa, kaf hankalin ta yana a kaina da nake nufi ta, hakan ce ta sanya bugun zuciya ta ya kuma tsananta, lura da nayi cewa Sir Salim ne yake tsaye ta gefen ta, sai wani mutum da kaman dreba ne yake tsaye cen gefe ya jingina shima da motar. Duk kansu murmushi ne ɗauke akan fuskokin su. Hakan ce ta sanya ni sadda kaina ƙasa, matar tayi masifar kama da Sir Salim, saidai ita ɗin fara ce tas, ga dogon hanci a bisa fuskar ta, ga dukkan amu zata yi sauƙin hali. Da sallama ɗauke a bakina na ƙarasa ina mai ɗan durƙusawa na shiga gaida ta, dukka hannuwan ta guda biyu ta sanya ta ɗagoni tana mai ƙara ni bisa jikin ta, ni sai ma Naji wani banbaraƙwai wallahi, murmushi sosai saman fuskar ta, a kunyace na maida kallona kan fuskar Sir Salim, aiko ya kashe man ido ɗaya cikin zaulaya, gami da ɗan yiman ƙaramin gwalo. Zame jikina nayi gefe a hankali ina mai sake duƙar da kaina ƙasa haɗi da fara wasa da yatsun hannuwa na da suke samɓal farare tas dasu. Ɗan kallon ta ta kai kan Sir Salim ɗin tana cewa "Marar kunya ka wani tsura mana idanu kana kallon mu, ku jira mu nan mu shiga daga ciki mu fito ko" Jin hakan da nayi ne ya sanya ni juyawa ina mai nufar hanyar da zata sada mu da ɗakin namu. Itama bina ta shiga yi daga baya, cikin tafiya irin ta ƴan gayu masu ji da kansu, jikin ta sanye da wani irin ɗanyen boyel mara zane da akayi ma aikin duwatsu dukan shi, kai kace lace ne, sai walwali yakeyi , kai da gani ba sai an faɗa maka ba yasha kuɗi, gyalen boyel ɗinne a jikin ta shima ba zanen komai sai cin bakin duwatsu da akayi mashi shima irin na kayan. A haka har muka isa ɗakin, na sanya hannu na buɗe ina mai ce mata bismilla. Mun tadda Khadeeja Da Raihana abokan zaman ɗakin nawa, ganin nayi baƙuwa ne ya sanya suka tattara littattafan su gami da gaida ta suka wuce, cikin sakin fuska itama ta amsa da maganar ta kalar ta ƴan gayu. Bakin gadona da yasha gyara na nuna mata, ina mai jawo kwalin lemo na ɗauko ɗaya haɗi da cup, shine kaɗai abunda nake dashi da zan iya bata a take, saboda yau banyi abinci ba, a capteria nima naci abinci ɗazu. Sake gaida ta nayi, ga mamaki na itama a sake ta amsa mani, tana mai ɗaukar kofin lemon ta kai bakin ta tasha duk da babu sanyi, ban taɓa tinanin cewa zata iya sha ba, saboda ga dukkan alamu naira ta jiƙa matar kai bama sai ance maka ba. Da murmushi ta fara kallona tana cewa "To Suhan ki cire niƙab ɗin ko sai muga juna da kyau, sauri nakeyi akwai maganar da ta kawo ni, gashi marece yayi ko" A kunyace na duƙar da kai, ina mai zare niƙab ɗin daga inda nake zaune ƙasa na shimfiɗa dardumar sallah. "Waw Masha Allah Laƙuwata Illa Billah" Abunda ta faɗa kenan tana mai tasowa ta sanya hannu ta kamoni ta miƙar tsaye, sannan ta shiga jana har zuwa bisa gadon kusa da inda take zaune. "Ɗiyata kina da kyau masha Allah, ga kunya, yanzu ne na tabbatar Son ya samu kalar matar da yake da buri, nima nake da burin ta zama suruka ta, ina son dukkanin abunda Salim yake so, matuƙar bai saɓa ma shari'ar musulunci ba, shi ɗin yaro ne mai biyayya da kawaici, duk da yake mai yawan tsokana da wasa. Abunda matar shi tazo jiya tayi maki ne ya sanya ni tasowa takanas saboda hakan, kuma in baki haƙuri abisa kuskuren ta, kada ki hukunta yarona saboda laifin matar shi, kuma ina fatan hakan bai tsorata ki ba, saboda ita yarinya ce mai hargagi, sai daga baya tazo kuma tayi nadama, bance maki bata da sauƙi ba, to saidai wasu halayya dake gareta da bata yi daidai da ra'ayin mu ba daga ni har shi Salim ɗin, yana neman aure ne ba don ya gaza samun komai ba sai don ke ɗin ya gani kuma kin kwanta mashi, Amman yace yana buƙatar ayau ɗinnan naje na nema nashi izini a wurin mahaifiyar ki, idan ta amince ina fatan kema zaki so mu ki yarda damu kaman yanda muma mukayi maki" Ta ƙarashe tana mai leƙen fuska ta da take ƙasa, har yanzu hannuna yana cikin nata taƙi ta sake. Sai naji dukkanin ɓacin raina kaso 80 ya fice, har bansan lokacin da na sauke ƴar ajiyar zuciya ba, ina mai ɗan murmushi gami da jawo gefen hijab ɗita na rufe fuska ta. Hakan da nayi ya alamta mata cewa na haƙura kuma na yarda da yaron nata. Godiya ta shiga zubawa tana mai cewa "Masha Allah ɗiyata, da fatan zaki yafi yaron nawa da matar tashi, abisa kuskuren da suka aikata maki jiya, idan ma harda mai laifi to Ma'un ce tinda ita ta biyo ki har inda kike, kuma ni nama yi mamakin da har ta gano komai, duk da naji labarin akwai mai ɗaukar mata rahoto anan makarantar, saboda haka sai ki kiyaye, kuma kiyi duk yanda zakiyi ganin cewa wani bai shiga tsakanin ki da yaron nawa ba, shi yaro ne mai yawan kyautata ma wanda suke tare dashi, ina faɗa maki haka ne ba don yana ɗanɗa na ba, aa sai don ina maku sha'awar zama tare ne. Bari in wuce sai na kuma dawowa, daganan gidan ku wajen umman ki zamuje, acen ma zan kwana sai gobe in wuce" Ta faɗi hakan ne tana mai miƙewa ta ɗauki jikkar ta, hankalin ta kwance, ga fara'a har yanzu saman fuskar ta, tabbas yanzu ne Salim ya samu mata ɗaya da ɗaya, yanzu ne take tunanin zai samu kwanciyar hankali da walwala a tattare dashi, tabbas ta shaida cewa kuɗi ko mulki basa sanya kwanciyar hankali muddin baka tare da iyali mai natsuwa da sanin ya kamata. Har wajen mota na raka ta, wannan karon Sir Salim ɗin yana gefe shida wasu ɗalibai suna magana, dreban kuma ya buɗe gaban motar ya shiga sai faman gyangyaɗi yake. Hangomu da yayi ne tafe hannuwa na riƙe cikin na umman tashi ya sanya shi sakin murmushi, sannan ya sallama ɗaliban da suka same shi akan yayi masu afuwa basu samu rubuta accessment nashi da yayi jiya ba. Ƙarasowa yayi yana mai faɗin "Lallai Ammi naga alama yarinyar nan rana neman ƙwace man fada, gaskiya ba zan yarda ba, da sakyal gaskiya" Ya faɗa cike da shagwaba, ni sai a ya bani kunya, ɗan murmushi nayi na gefen baki, ina mai yima Ammin sallama da ya buɗe mata bayan motar ta zauna, tana mai miƙe mani fara ƙar ɗin emvelop, ban amsa ba, sai shine ya amsa yana mai godiya cikin zaulaya, ga dukkan alamu ya saba zaulayr Ammin tashi kuma tana ji dashi matuƙa gaya. "Ka kiyayeni fa Son, na faɗa maka kada kayi ƙoƙarin shiga tsakani. Suhan jeki kiyi Lecture ɗinki mun sanya ki makara, sai munyi waya" Ta faɗa tana mai jan murfin ƙofar ta rufe Juyawa nayi ina mai mata sallama gami da ɗaga mata hannu, ban bi ta kan emvelop ɗin da ta bani ba, wadda Sir Salim ɗin ya zura ta cikin Aljihu gami da zagayawa ya shiga kujerar mai zaman banza dreban yaja motar suka ɗaga. A haka na isa hall ɗin, raina fari tas, ko ba komai matar ta nuna mani ƙauna, ta nuna mani zallar soyayya kuma ta soni da yaron nata, ba kaman hajiya Kubra ba, mai ƙyamatar mu, mai zallan son zuciya, mai ɗaukar talaka ba a bakin komai ba, zullumi na ɗaya da tace wai gidan mu wurin ummata zata kwana, gashi ba waya balle inyi maza in kira umman tawa asamu a shirya mata wani abu ko kuma a san inda za'a ajiye ta ta kwana. Da haka har aka tashi lecture ɗin na koma ɗaki su Raihana ɗinne masu ceman gaskiya sun yaba da kirkin matar ganin yanda ta amsa masu fuska sake duk da ita ɗin wata ce ga dukkan alamu. Wannan ne ya sanya ranar nayi kwanan farin ciki da na rabu dayin irin shi a rayuwa da tin bayan shuɗaɗɗen lokaci a gidan su Ya Ameen ɗin. Ban kuma jin ɗuriyar Sir Salim ba har nayi bacci ina ta faman tinane tinane, yanzu fa suna nufin Sir Salim shine mijin da zan aura nan da wani lokaci ƙanƙani kenan? Ya zama saurayi na kenan a karon farko a rayuwa ta, wata irin kunyar shi ce ke kwarara a sassn jikin nawa duk kuwa da cewa baya a tare dani. Su ma su Raihanan da murmushi suka dinga bina, ganin da sukayi ina cikin farin ciki, duk sai suka ji daɗi, kasancewar kanmu a haɗe yake babu wanda ke shiga hidimr wani gudun samun saɓani. **************** Kai tsaye gidan hafsat ya nufa, ko gida ma baya jin zai iya zuwa har sai yaje gidan ta ta bashi cikakken bayani. Tana zaune shirim da uban ciki a jikin ta taji ana latsa door Bell, da ƙyar ta ɓaɓɓaka ta nufi ƙofar gami da leƙa wa ta ƴar ƙofar da zata sada ka da mai latsa doorbell ɗin, to saidai bata ga kowa ba, hakan ce ta sanya ta buɗewa domin ta san ba abun cutar wa bane tinda akwai mai gadi. Baya tayi mana zata faɗi ganin ko wanene, sanye yake cikin ƙananan kaya, baƙin wando ne, sai rigar polo kalar sararn samaniya, idanun shi daɗe cikin baƙin glass sosai, fuskar nan babu alamun walwala ko annashuwa tattare da ita, yayi fari tas ya ƙara kyau, fatar nan tashi har salƙi takeyi ga baƙa suɗik ɗin gargaza da ta samu wuri ta lafe abunta, kan nan kuwa nashi yasha gyara yayi luf dashi har ya kusan sauka ƙyeyar shi, da gani dai sumar nan tana shan gyara yanda kasan ta shahrokhan ko Omair na cikin tarkon ƙauna. Hannu ya sanya ya taro ta, ganin yanda ta firgita har tana neman faɗuwa ga uban ciki a jikin ta. Saida ya tabbatar da ta daidaita tsayuwar ta, sannan ya sake ta tyaa mai raɓeta ya shiga ciki zuwa falon kai tsaye. A hankali ta maida ƙofar ta kulle, ta shiga bin bayan shi, saidai kafin ta zauna ta wuce kitchen ta haɗo mashi abun Sanyawa a baki da lemo da ruwa ta kawo mashi ta janyo stool ta ɗora bisa, haɗi da zama tana mai gaishe shi cikin rawar murya. Bai ko bi ta kan abunda ta ajiye mashi ba, ya sanya hannu ya matsar da stool ɗin gefe, yana mai ɗan zamowa daga bisa kujerar alamar magana zasuyi mai muhimmanci, haɗi da amsa mata gaisuwar a gaggauce. "Magana zamuyi Hafsat, tinda Naji kina kuka na san da akwai wani abu dake faruwa, ki natsu Hafsat ki gaya man dukkanin abunda ya faru bayan tafiya ta, muddin kinsan wani abu ban yarda ki ɓoye man shi ba komin ƙanƙantar shi" Ta ruɗe ita ruɗewa, yaron dake cikin cikin ta ne ya shiga dunƙukewa yana curewa wuri guda saboda tsabar kaɗuwa da tayi, gashi kuma Dad ya hana a sanar dashi komai, idan aka ji a bakin ta yaji, ita yanzu ina zata sanya kanta Lura da hakan da yayi ne ya shiga kwantar mata da hankali yana mata alƙawarin babu wanda zaiji cewa a bakin ta yaji, kai babu ma wanda zai san ya shigo ƙasar in ka ɗauke ta da Bilal shima idan ya kama ya sani kenan. Saukowa tayi ƙasa haɗi da zama bisa tiles inda zata fi jin daɗi daɗi, sannan ta miƙe ƙafar ta, ko ba komai tana so ya nemo mata Suhan ɗin, tayi kewar ta sosai, tana tausaya ma rayuwar ta, bata so ta shiga wani mugun halin ko kuma yana yin da zai iya Sanyawa ta faɗa cikin wata Rayuwar, duk da kasancewar umman tata mace tsayayya. A hankali ta shiga warware mashi dukkanin Abunda ta san ya faru bayan tafiyar shi, har kawo inda ake yanzu, kuka take wiwi tinowa da Ƙawar tata da tayi. Tini kalar idanun shi suka cenza, wata jijiya ta taso mashi raɗau bisa kai, yayin da kanshi yake ta sa rawa, idanun nan kuwa sunyi jawur, hannun shi ya dunƙule yana bugawa a cikin gudan cikin tsananin tashin hankali, lallai aiki ja ya ganshi, duk inda suka shiga a faɗin ƙasar nan dole ne ya binciko su, ashe burin da Mom ɗinshi ta ɗauka na ganin sai sunbar gidan, bata barshi ba, Meyasa Bilal ya ɓoye mashi? Shi a tunanin shi zai nemo su ne, ya maido su ba tare da shi ɗin ya sani ba? Wannan itace amanar daya bashi? Lallai kuwa Mama Talatu zata gane kuren ta, tabbas dole ne dukkan mai hannu acikin wannan al'amari ya gane kuren shi, koda kuwa Mom ɗin tashi ce ba zai lamunci wannan zaluncin ba, yarinyar marainiya da ita ace ba za'a tausaya mata ba, har sai an koresu an raba su daga inda suke samu suci abinci. Miƙewa yayi a matuƙar fusace da niyyar ficewa, bata san lokacin da ta miƙe ba tana mai taro shi gami da shiga yi mashi magiya akan ya rufa mata asiri. Da dukkan hannuwan shi ya sanya ya tallabo fuskar ta, sannan ya shiga cewa "Hafsat kar ki damu, ba zanyi Abunda zai sanya ki shiga matsala ba, hasali a yanzu ba guda na nufa ba, zan bar garin ne baki ɗaya in shiga neman su da kaina, ko Bilal bana so ki faɗa mashi nazo kai koda kuwa ace Sadeeq ne tinda kinga shi ɗin abokin shi ne" Da alamar gamsuwa ta shiga jinjina mashi kai, tana mai zame fuskar tata ta shiga buɗe mashi ƙofar gami da cewa "Allah ya tsare hanya Yaya sai munyi waya" Har bakin gare ta raka shi, da yake ba da mota yazo ba, har ya fice tana mai kallon shi zuciyar ta a matuƙar cunkushe, saidai ma ko menene ta san lokacin gano su Suhan ɗinne yazo, kuma tayi matuƙar farin ciki da hakan. Saida taja ma mai gadi kunne akan kada ya faɗa ma Sadeeq ɗin Ya Ameen ɗin yazo, sannan ta juya cikin gidan tunani fal a ranta... ******************* Ya matuƙar daɗewa a cikin makarantar, duk inda yake sa ran zai nemo wani bayani daya Ƙunshe ta ya kasa samun cikakken bayani saboda tsaro, kusan yini yayi yana zarya ofisoshin makarantar, babu wani cikakken bayani dai, rashin sani, kuma ta gaban shi Suhan ɗin ta wuce zuwa masallaci da niƙab a fuskar ta, Sam bai gane ta ba, bai fahimci komai ba, tinda bai kawo ma ranshi komai ba, itama ɗin bata lura dashi ba, tinda yana ta cikin mota ne zaune, har ya gaji yabar makarantar zuciyar shi na raya mashi cewa Suhan ɗin na kusa, kuma tana cikin makarantar idan dai har Umman tata ta barta akan ta cigaba da zuwa makarantar. A haka yaja motar shi ya fice, zuciyar shi cunkushe, ya kusan kai kwana nawa yanzu yana shigowa makarantar ko zai dace da ganin ta, Amman babu wani labari. Ya yanke hukuncin komawa abujan ko kuma yaje ya roƙo Hajiya Kubran akan cewa idan tanada masaniyar inda suke ta taimaka mashi ta bayyana masu, ko zasu samu su fita daga cikin halin da suke ciki tin kafin aminin nashi ya Samu labari. Ya yanke shawarar nan da zuwa wani lokaci kaɗan, idan har bai ganta ba, to fa zai shaida ma Ameen ɗinne asan wacce za'ayi, domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa, ya gaza, ya gaza cika ma aminin nashi alƙawarin daya ɗauka, kunyar abokin nashi tana cike a cikin zuciyar shi tin kafin ma su haɗu. ******************** A tare suka isa ƙauyen da Sir Salim ɗin, da taimakon shi ma ne suka samu suka gane gidan, da kallo ita kanta Hajiya Khaltum ɗin tabi gidan, to saidai koma menene su dai sun ji sun gani kuma a haka suke so, ba kuɗi ne matsalar su indai za'a amince a basu auren yarinyar da ta kwanta mata arai fiye da duk wata ɗiya mace da ta gani tana son yaron nata. Da sallama ta shiga gidan, yayin da tabar su Sir Salim ɗin nan jingine jikin mota. Umma ta ce zaune tana tanƙaɗen dawa, ita kuma Hajjo tana iza wutar miya bisa murhun duwatsu da yake cen madafa. Da ɗan sakin fuska umman tawa take amsa mata sallamar da tayi mata, ko ba'a faɗa ba ta shaida umman tawa, hango tsantsar kama dake saman fuskar tamu, da kuma sanyin dake tattare damu daya kasance iri ɗaya. Ajiye tiren tayi ƙasa gami da yima matar maraba, duk da bata shaida ta ba, tabarmar kaba ta janyo gami da shinfuɗa mata daga gefen ɗakin namu. Cikin mutunci suka gaisa harda Hajjo data fito, itama ganin bata shaida ta ba, ya sanya ta janyo kujera ƴar tsugunno ta zauna kaman yanda taga umman tawa tayi. Sake sabuwar gaisuwa sukayi, yayin da Hajjon ta miƙe ta ɗebo mata ruwa cikin kofin silver sai ɗaukar ido yake. Ga mamakin su Umman tawa, matar kafa kai tayi tasha ruwan nan a haka da yake fari fat duk laka a cikin shi, wai nan haka ma don sai sun dafa suke zubawa a randar ya kwanta. Hajjo da umma ce suka kalli juna, saidai basu ce komai ba, har ta gama sha ruwan tayi hamdala tana mai cewa "Aikuwa Ruwan fa da daɗi gwanin garɗi" Su dai da kallon mamaki suka bita, gata dai ƴar gayu Amman bata da jin kan masu kuɗi. Hajjo ce tayi ƙarfin halin tambayar ta daga ina take? Ɗan murmushi ta sake saki tana mai cewa "Eh gaskiya ba zaku shaida ni ba, kaman yanda nima yau ne karon farko ɗana sanya ku a idona har ita ɗiyar tawa, Sunana Hajiya Khaltum, kuma nice Mahaifiyar Salim Bawa, malamin su Suhan yarinyar wajen ku" Toh fa! "Ikon Allah, yaron kirki kuwa ɗan albarka, Allah dai ya biya shi abun alkhairin da yake yi mana, yana ta ɗawainiya da yarinyar tamu". Cewar Hajjo da yanzu ta shaida ko wacece matar kuma sai yanzu ne ta hango ƴar kamar da suke yi. Umma ta ma saida tayi mata godiya sosai, tana mai cewa Salim ɗin ya shigo mana, ai yanzu ya zama ɗan gida, bayan Ammin tashi ta shaida masu tare suke ma. Harda dreban Hajjo ta leƙa tace su shigo, suma tabarmar kabar suka shimfiɗa masu suka sake gaggaisawa, shi dai Salim kanshi a duƙe yake duk kunyar ummata ta cika shi, duk da har yanzu bata san me ke tafe da su ba. Shaida ma Ammin sukayi akan cewa zasu fita cen hanya ko zasu samu Hotel ɗinda zasu kwana, kafin zuwa goben su wuce. Da to tabisu yayin da sukayi sallama dasu umman tawa suka fice, har Hajjo ke ce masu ba zasu tsaya suci tuwon dawa ba? A kunyace suka ce sun ƙoshi, gami da shiga motar su suka bar ƙauyen, hakan ce ta sanya Ummata da Hajjo gane cewa anan gidan matar da ta kira kanta da Hajiya Khaltum zata kwana kenan, Hajjo ce ta karɓi girkin daren, yayin da Ummata ta shiga ɗakin nata domin gyara mata inda zata kwanta daidai ƙarfin ta. Har aka gama tuwon aka kwashe babu abinda ya tada Hajiya Khaltum sai Sallah, bayan ta gama ne ta jawo wani mai, wanda ke hana sauro cizon mutum duk ta shasshafa jikin ta, dama ummata ta shigar mata da ƴar ƙaramar jikkar ta ɗaki. A haka aka gama tuwon aka zuba mata, nan ma babu wani ƙyanƙyami taci abunta hankali kwance, harma tana zuba santin cewa ta daɗe bata ci tuwon dawa da miyar kuka da manshano haka ba. Duk kansu sun ji daɗin sakin jikin nata dasu, gashi bata nuna masu komai ba ko ƙyama, balle har ta kasa cin abincin su. Bayan ta gama cin abincin ne take shaida masu da akwai maganar da ta kawo ta mai matuƙar muhimmanci, wanda take so tayi da su da kuma mahaifin Yarinya Suhan. Nan fa gaban Ummata ya shiga faɗuwa, Hajjo ce tayi ƙarfin hin cewa to su jira shi ya dawo daga kasuwa domin ko ina yake yanzu fa yana hanya ne.... Da haka suka shiga firar su ta manya da kuma halin da duniya da ƙasa take ciki, masalan na rashin abinci da kuma kidnapping ɗinnan da ake fama dashi a arewacin nigeria ɗin. Sallamar Malam na daga cikin Abunda ya ƙara tsananta faɗuwr gaba ga Umman tawa, domin batasan ko da wacce wannan matar take tafe ba, duk da kuwa ta yaba da hankali da natsuwar matar, kuma tayi imanin bata tare da abun cutuwa ko da zai iya zama barazana ga lafiyar tata data yarinyar tata..... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~37~* *YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)* *Ammin Islam Pls ki sassauta ma Hajiya Kubra, 🤣🤣ai indai kina yin Ya Ameen dole ne ki so Mom ɗinshi, kiyi mata addu'a Allah ya shirya ta. Team Sir, Salim ina gaishe ku muna mugun tare🤝🏻🤝🏻👌🏻* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Kai tsaye ɗaki malam ya shige, bayan sun gaisa da Ammi wadda bai wani waye ta ba sosai. Sai bayan da ya kammala cin tuwon daren ne, sannan Hajjo take shaida mashi ko wacece Ammin da abunda yake tafe da ita kuma. Cewa yayi ta shimfiɗa mashi darduma zai fito suyi magana, saboda ɗakin akwai zafi. Daga cen gefe ta shimfiɗa mashi dardumar, sannan ta shaida masu ga malam ɗinnan fitowa. Bai wani ɗauki lokaci ba, ya fito haɗi da zuwa ya ɗauraye hannuwan shi, sannan ya koma ya zauna suka sake sabuwar gaisuwa. Cikin salon magana irin ta manyan ƴan boko da suka iya tsara kalamai Hajiya Khaltum ɗin ke bayyana ma malam ita ɗin wacece, da kuma dalilin zuwan nata gidan. Tsaf ya tsaya ya saurare ta da kunnen basira da kuma fahimta, ummata da Hajjo dai suna zaune basu ce ƙala ba. Malam ne yayi gyaran murya gami da muskutawa, sannan ya fara magana. "Ah Hajiya munji dalilin zuwan ki gidan namu, a haƙiƙanin gaskiya munji daɗi kuma mun yaba, duk wanda yayo tattaki daga nesan duniya yazo inda kake, da kuma ƙoƙon barar soyayya, kuma irin ta aure, a gaskiya ya cencenci yabawa da kuma karramawa, saboda haka ne muke cewa mun gode. To saidai kuma akwai wani hanzari ba gudu ba, ban sani ba ko an shaida maki yarinyar marainiya ce? Ni ne nan nake zaman mahaifinta, wanda kuma anan gidan aka haife ta, saboda wasu dalilai ne ya sanya bata tashi a gaba na ba, wanda duk da haka na yaba da tarbiyyar da ita Maryamar ta bata, sannan kuma shima yaron na wajen ki lallai mun yaba dashi kuma munyi na'am dashi. Idan dai har kun yarda da hakan, to ta ɓangaren mu babu wani damuwa, zai iya zuwa su daidaita kansu, zuwa wani lokaci bayan sun gama fahimtar juna sai a turo manyan nashi maza domin suzo mu sake tattaunawa" Tinda malam ya fara magana Ammi ke sakin murmushi, lallai ita kanta babu Abunda zata iya cewa da wannan zuri'a saidai fatan Alkhairi. Godiya ta shiga zubawa tana cewa wannan ai ba matsala bane, Allah ya bar zumunci kuma ya ƙara haɗa kawunan su yaran. Nan malam ya tashi ya shige ciki ya bar su, duk da ummata ta ɗan sha jinin jikin ta, bamu sani ba ko sarakutar ce ta fara? Da haka suma suka miƙe suka shiga ɗaki domin kwanciya, ummata ta gyara ko ina tsaf, dama kasancewar ta mace mai tsafta, sai ta shimfiɗa ma Ammi manyan barguna masu taushi a ƙasn ta ajiye mata matashin kai da kuma marar nauyi na lulluɓa. Saida Ammi ta cenza kaya zuwa doguwar rigar bacci sannan ta kwanta, tana mai yima ummata sai da safe. Cikin dare umman tawa ta farka domin yin ƙiyamul laili kaman yanda ta saba, saidai ga mamakin ta, Ammi ce tsaye tana salla, lamoo umman tawa tayi tana ta ƙare mata kallo duk ba tare da ta lura da ita ba. Ta Kai kusan awa guda tana sallar sannan ta tsagaita, gami da ɗaga hannu ta dinga kwararo addu'a cikin harshen larabci da ƙanƙan da kai wajen Allah. Tabbas ta burge ummata ta ƙayatar da ita, sai taji ta sake amincewa da lamarin matar, tabbas indai haka ne abunda ta gani, Allah yayi ma Suhan ɗin zaɓi mafi alkhairi, saidai fatan nasara da dacewa. Saida taga Ammin ta koma ta kwanta ne, sannan itama ta miƙe domin gabatar da tata, wanda itama Ammin tana kula da ita, itama hankalin ta ya sake kwanciya da auren yarinyar matar, saboda ummata mace ce mai dattako da kamala, sai taji hakan ya matuƙar taimakawa wajen ƙara amincewa da mahaifiyar yarinyar. Washegari ma babu ƙyama ba komai aka kai mata ruwan wanka tayi, duk da har yanzu ummata bata ƙara sakin jiki da Hajiya Khaltum ba, saidai hakan bai dameta ba, tabar hakan ne a rashin sabo da basu yi ba. Sai da tasha ruwan koko da ƙosan da aka ajiye mata ne, sannan sai ga su Sir Salim Sun dawo domin tafiya da Ammin. Kaman kar ta rabu da gidan take ji, rayuwar tasu a sauƙaƙe ta burge ta, ga karamci ga dattako, a haka sukayi sallama harda Malam da bai riga ya fita ba, ya bari sai yaga tafiyar ta. Tin daga murmushn da Ammin tashi keyi, ya tabbatar da nasara da dacewa a al'amarin. Wannan ce ta sanya shi jin kunya da ta sanya dole ya dinga duƙar da kai lokacin da yake gaishe su cikin girmamawa. Sun sake saki da al'amarin ko ba komai suna kyautata zaton ƙila lokacin fitar Suhanan ne yazo daga ƙuncin da take ciki. Basu bar wurin ba, saida aka buɗe but suka dinga shiga da kayan abinci kala kala da kayan amfanin gida, sai kuɗi da umman ta ajiye masu rafer ta ƴan 1k guda ɗaya. Dakyal suka amsa, ummata kuwa komawa tayi gefe akan fir ita ba wannan suke buƙata ba, sai da magiya da komai ne ya sanya Hajjo amsa ta shiga yi masu godiya da addu'a Basu bar wurin ba har saida suka ga ficewar motar su Ammin daga Layin sannan suka koma gida cike da al'ajabin wannan mata mai cike da abun ban mamaki ********************* Saida ya gama juye juye da tunane tunanen shi, sannan ya kira waya akan a kawo mashi mota zuwa a hotel ɗin da ya sauka. Aiko sai ga mota sabuwa dal tear ledar, mai masifar kyau, an mata glass tint sosai ta yadda ba zaka iya fahimtar wanda yake ciki ba. Bayan ya fito ya gani ne, ya koma ɗakin shi, saboda baya so su haɗu da idon sani, labari ya bazu a gari akan shigowar tashi ƙasar, tinda shi mutum ne na mutane, gashi matasa kowa ya san da zaman shi yanzu, tin bayan da akayi mashi naɗin babu inda hotunan shi basu zagaya ba a sassan ƙasar. Laptop ɗinshi ya jawo ya shiga bincike sosai, saidai ya manta ƙasar tamu, ba ko ina bane ba ma wireless ke shiga ba, iya binciken shi da neman shi a yanar gizo, bai iya gano komai ba, har dai ya haƙura ya ajiye ya shiga wanka. Shiryawa yayi cikin ƙananan kaya, sannan ya ɗauko wata baƙar jacket mai hula ya sanya gami da rufe kanshi da hular, face mask baƙi ya sanya ma baki da hancin shi, sai sun glass daya ɗora ma idanun shi, Sam ba zaka taɓa shaida shi ba, in har ba kyakkyawan sani kayi mashi ba. Cikin salon tafiyar shi ya taka zuwa bakin mirror, saida ya gama kalle kanshi tsaf, yaga ba ta inda ya kuskure wajen barin wata alama da zata sanya a gane shi, sannan ya ɗauki makullin motar tashi ya fice haɗi da jan trolly ɗin kayan shi. Kai tsaye yabar cikin hotel ɗin, bayan ya maida masu da makullin ɗakin nasu. (To Su Ya Ameen Ko Ina Kuma Aka Nufa?) ******************** Yanzu wata irin kunyar Sir, Salim nake ji, duk da dai nasan cewa bana jin komai game dashi, saidai kuma akwai nauyi tattare dani, yanzu dai bana da matsalar komai, har mun gama zana jarawar mu, da yake hutun semester ɗin ba mai tsawo bane, ya sanya ban koma gida ba, da taimakon kuɗin da Ammi ta bani, da kuma hidimar da Sir, Salim yake yi mani, ya sanya karatuna na sanya a gaba. Yanzu dai na samu ummata tana da ƴar wayar hannu, itama saidai duk in zata kira ni, sai taje tabhau cen bisa wani dutsi sannan zamuyi waya, amman idan ni na kira ta bana samu. Matsala ɗaya ke damuna, yawan text da nake samu daga Ma'un Sir Salim, tana man barazanar shiga gidan ta, saboda taji labarin cewa har aure an je nema kuma iyayena sun bada. Har kirana takeyi a waya bana ɗagawa ne, text ɗinma in tayo mani saidai in goge kawai bayan na karanta, ban taɓa faɗa ma Sir Salim ba, kullum Ammin shi kan kirani ta haɗa ni da yaran shi mu gaisa, zuwa yanzu dai Ma'un ta koma gidan Sir, Salim ɗin, wannan ce ma ya sanya yake zuwa weak end, amman ba wani kwanciyar hankali ko jin daɗi, yaran ma duka suna hannun Ammin shi, har yanzu ba'a maida ma Ma'un su ba, to bata tsaya ta kula da kanta ba ma balle yaran? Duk wannan abun dake faruwa bai sanya naji ko ɗar cikin zuciya ta ba, miji dai ne na samu kuma ba zan taɓa wasa wannan damar ta kufce mani ba, tinda banga amfanin zaman haka ba, bayan Allah ya riga ya kawo mani mai sona da ƙaunata da zuciya ɗaya. Sir Salim irin mutanen nan ne masu shiga rai farat ɗaya, yana da yawan fara'a, gashi baya da girman kai duk da kasancewar shi mai abun hannun shi, sannan yana da kyauta, ga iya mu'amala da mutane, wannan ce ta sanya ko a cikin makarantar mutane da dama suke girmama ni, kasancewar ya zuwa yanzu kusan kowa ya fahimci alaƙar dake tsakani na dashi. Dogo ne daidai misali, don zamu iya cewa yafi ya Ameen da kaɗan, yana da ƙira irin ta cikakkun maza, ba baƙi bane cen wuluk, hasken shi daidai misali, yana da haiba da dattako. Ya iya shiga kala kala, hakan ce ma ta sanya mata da yawa macewa a soyayyar shi, acikin makarantar baya da kula ƴan mata, kuma baya son wasa da karatu, dalili kenan daya sanya ya tsaya man kai da fata, wajen ganin ban samu wata matsala ba. A wurina soyayya ba abu bace da akan iya samu farat ɗaya, saboda ƙakubalen rayuwa da nasha fuskanta, idan ma ba yanzu ɗin ba, ai ni soyayya wurin mutane uku zuwa huɗu na santa tin tasowa ta a rayuwa, ummata sai Ya Ameen, sai kuma Afnan da Hafsat, waɗannan mutanen komin yanda na kai da son in manta dasu a rayuwa ta, ba zan iya ba, saboda sun taka muhimmiyar rawa a rayuwa ta, ba kuma kaɗan ba. Wannan ce ta sanya na Gaza manta Ya Ameen ɗin, sau da dama in muna tare da Sir Salim na kan yi imagining cewa da ace Ya Ameen ne ya zata kasance a rayuwa ta? Duk da shima Sir Salim ba baya ba a wajen komai, cikas ɗinshi ɗaya matar shi, shima kuma bana ɗaukar hakan a wata matsala tinda ba'a kanta zan zauna ba. Ammi na gwada man tsantsar Soyayya, butsu-butsu tayo mani aike ta hannun yaron nata, kai hatta da Abban shi Sir Salim ɗin Alhaji Bawa Bala, wanda ba ɓoyayye bane a ƴan siyasar ƙasar nan, saida Ammin ta haɗa ni dashi a waya na gaida shi, na yaba da yanda yake amsa gaisuwar tawa, don ga dukkan alamu na samu karɓu wa a cikin wannan family ɗin. *Ikon Allah kenan. Inda wani yake ƙi da yini, nan wani ke so da kwana* Hankalin Bilal ya gaza kwanciya, masalan ma idan ya kira wayar Aminin nashi yaji ta a kashe, idan kuma ya tambayi Abie, ya kan ce mashi yana lafiya, basa tare, ko yace yana office ko yace ya fita cikin gari, ko yace ya baro shi a gida. Ya san halin Aminin nashi sarai, ba ƙaramin ƙyalle bane, wannan duk ɓoye ɓoyen da yakeyi mashi ma, ta ita yuwuwa ya fahimci komai, wannan ce ta sanya shi shirya faɗa mashi gaskiya, to saidai ta ina? Ta yaya zai ganshi? Idan ma ya ganshi to ta ina zai fara yi mashi bayani? Yana cike da kunya da nadamar amsar wannan amanar da ya gaza cikawa, hakan ce ta sanya shi shirya tafiya American domin yaje ya samu abokin nashi, domin a samu mafita. Ko a cikin jirgi ma wasi-wasi yake ta faman yi,ji yake kaman ƙasa ta tsage ya shige , bai shirya amsar duk wata ɓaraka daka iya aukuwa a tsakanin shi da Aminin nashi ba, a karon farko tin tasowar su daga ƙuruciya. ********************** Hajiya Kubra likafa taci gaba, yanzu akai akai tana zuwa cen ƙasar ta Turkiyya wajen Alhaji nata, ganin basu kuma tada mata maganar ba, ya sanya hankalin ta ya kwanta, bata da matsalar komai, yanzu komai nata sai ƙara bunƙasa yakeyi, ta zama hajiyar da duk faɗin ƙasar ake labarin ta, mafi yawan mata suna ji ace dama sune ita, yawan ma'aikatun ta, da kuma hannun jarin da take dashi a kamfanoni ya sanya kullum shaharar ta ƙara haɓaka takeyi, Alhaji Mustapha ba mutum bane mai damuwa sosai ba, balle yanzu da baya da ko yaro ɗaya gaban shi idan ka ɗauke Afnan da take hannun yayar ta, shi kuma Abie yana wurin Yayanshi acen ƙasar ta amurka. Wannan ce ta sanya ya maida Al'amurran shi kacokam kam ƴan uwan nashi dake Katsina dama sauran garuruwa, sosai ƙasar ta Nigeria ke amfana da Alhaji Mustapha ɗin dama iyalan shi baki ɗaya. Su kaka zuwaira suna cikin jin daɗi ita da ɗan tsohon mijin ta isuhu, sai dangi da kusan duk ya sanar ma waɗanda suka gama karatu aikin yi, waɗanda kuma basu ƙarasa ba yana taimakawa wajen karatun nasu. Hakan ce ta sanya hankalin shi bai kai kan kwana biyu da yaron nashi bai kira shi ba suka gaisa, Abie ne ke kiran shi, to shi ɗinma dai kaman yanda yake faɗa ma Bilal ɗin shima haka yake faɗa ma dad ɗin nashi, hakan ce ta sanya bai kawo ma ranshi komai ba, illa iyaka dai ya haƙura da Suhan ɗinne kaman yanda Mom ɗinshi ta buƙata, tinda shima babu irin binciken da baiyi ba, da kuma sanyawa ayi, Amman Allah bai sa an dace ba. *************** A mota yake tafiya zuwa wasu garuruwan, photon ta dake cikin wayar shi ya sanya aka wanke mashi, matsalar dai da babu wanda take ita kaɗai saidai wanda suke tare dashi, to akan ce mashi dai ita yarinyar ba'a santa ba, amman mafi yawa sukan ce mashi ai wannan shine Yariman Matasa Arewan da akayi ma naɗi watannin baya, ya kan sha mamaki, ashe haka mafi yawan mutane suka sanshi a faɗin ƙasar tashi? Lallai tafiya mabuɗin ilimi ce, a wannan tafiyar da yayi, ya haɗu da ƙauyukan da suke matuƙar buƙatar tallafi koda kuwa ace na ruwa ne kawai, sannan ya ƙudurta a ranshi cewa zai iya bakin ƙoƙarinshi wajen ganin ya taimaka masu, muddin ya koma normal *Al'ameen Almustapha Dambulan* ɗin da yake ada. Idan KagaYa Ameen a yanzu ba lallai ne ka shaida shi ba, shi mutum ne mai yawan tohon gashi, muddin yayi cikakken sati baiyi aski ba, to baya kalluwa, wannan ce ta sanya yanzu da yake ta faman yawon neman su, bai ko damu da yayi askin ba, indai ya samu yayi wanka ya cenza kaya, salla kuwa daman ƙasaru yakeyi, gashi sosai ya firfito mashi kaman ba shi ba, duk ya yamutse ko abinci bai damu da ya zauna zaman ci ba. Saidai wannan haiba da kwarjini da yake dasu tin tale-tale tana nan daram babu inda taje, kome yakeyi cikin halin nan nashi da kuka sani yakeyi, hatta da tafiyar shi idan ka tsaya ka kula tsaf bata cenza ba, kuma abar kallo ce, wani lokaci a cikin motar shi yake kwana idan dare ya rutsa dashi inda babu hotel. Ya gaji matuƙa yana so ya kwanta ya huta, yana so yayi aski, yana son aiwatar da abubuwa da dama. Hakan ce ta sanya shi neman hotel ya kama ɗaki, tunani yake so yayi, yana so yayi tunanin ta ina zai ɓullo ma wannan yawon gararin neman nasu. Da daddare ne bayan ya gama cin abinci yayi wanka haɗi dayin sallar shi, gado ya nema ya kwanta, duk ya zura saboda irin wannan wahalar da ba sabawa yayi da ita ba, ko zaman tuƙin ma kanshi aiki ne. Kaman an kunna mashi redio, haka yaji labarin da hafsat ta bashi yana ta faman dawo mashi tiryan tiryan cikin ƙwaƙwalwar, idan har bai manta ba, yaji tana cewa ranar daren da zata tafi makaranta suka bar gidan, kuma idan ba wai ya manta bane, an riga an gama kammala mata komai, to kenan idan har hasashen shi zai bashi daidai, yanzu Suhan ɗin tana makarantar ta ABU zariya, muddin Umman tata ta yarda da karatun nata, to kuwa tabbas zata kasance a makarantar a daidai wannan lokacin, shine ya rubuta mata course ɗinda ya dace tayi da hannuwan shi, kuma yaji Bilal ɗin yana cewa basu cenza mata shi ba, zumbur yayi ya tashi, haɗi da ɗaukar makullin motar shi, ya ja jikkar shi ya fice, a cikin daren ya sake maida masu makullin ɗakin nasu, ya kama hanyar zariya, duk da irin halin rashin tsaro da ake fama dashi a ƙasa, duk da irin duhun daya mamaye duniya a daidai wannan lokacin, duk da irin hatsarin da yaka iya haɗuwa dashi a tafiyar shi ta wannan daren. Wannan ba shine matsalar shi ba, wannan ba shine abunda yake ji ba, Suhan ita kaɗai ce damuwar shi, ya sanya ta a idanun shi, ya ganta koda sau ɗaya ne, ta amince mashi, koda ba zata koma gidan su bane, ta amince ta aure shi a hakanan idan hakan ta faru ya cika burin shi kaso 80 a yanzu na rayuwar shi. Ƙarfe bakwai na safen ranar talata a cikin makarantar tayi mashi, akan idanun shi jefi jefin ɗalibai suka fara fitowa zuwa cikin makarantar, sannu kan hankali har suka yawaita, kowa na hidimar shi, zuciyar shi ce ta tsananta duka, tabbas tabbas idan har abunda yake ji a jikin shi haka ne. To *Suhan ɗinshi tana cikin makarantar a daidai wannan lokaci* _Hmmmmmmmmmm_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)* *Laweexar ina matuƙar jin daɗin comment ɗinki, nagode Allah ya bar ƙauna. Saƙon gaisuwa gareki keda Ammin Islam daga bakin Ya Ameen, yace a sanar daku cewa yana sane daku a rayuwa, kuma watan watarana zai kawo maku ziyara shida Suhan ɗinshi, Amman fa sai bayan komai ya kwaranye idan ya samu nasarar auren ta. Lol* *Page ~38~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Tin da na farka da safe gabana ke yawaita faɗuwa, har sai na dafe gurin nayi a'uziyya sannan nake samun sauƙi Har dai khadeeja ta kula da hakan ta shiga tambaya ta ko ina da wata damuwar ne, da zasu taimaka mani wajen magance ta? Gyaɗa mata kai kawai na shiga yi, ina mai cigaba da shiryawa ta. Har na kammala na fita domin zuwa hall, sai kuma na dawo ɗaki na ɗaura niƙab, gami da zura zumbuleliyar hijab ɗita har ƙasa, duk da zafin da akeyi, na kwammace hakan tinda munyi da Sir Salim akan anjima zai zo yayi mani wata lecture bayan la'asar. Ta jikin motar ta Ya Ameen nabi na ratsa na wuce har zuwa department ɗin namu. Hatta da idanuna ba'a ganin su, hakan ce ta sanya ba kowa ne zai iya gane ni ba farat ɗaya. Fitowa yayi daga cikin motar gami da kulle ta, Admin block ɗin ya nufa direct, ya kuwa ci sa'a ya tadda HOD ɗin namu. Bayan sun gaisa ne, ba zai iya shaida fuskar Ya Ameen ba, saboda face mask baƙa dake fuskar shi, Amman wannan karon ya cire tabarau ɗin. Photo na ya nuna ma HOD ɗin Mai suna Malam Sani, cikin ɗan girgiza kai bayan ya gama kallon hoton nawa ya dubi Ya Ameen ɗin. "Wannan itace yarinyar da wani yake yawan zuwa nema a makarantar nan, kuma mu kanmu bama da masani ya a kanta, tin bayan shudedden lokaci bata kuma dawowa makarantar nan ba" Ya faɗi haka ne saboda doka ce, kuma Sir Salim ya roƙeshi akan ya ɓoye dukkan wani abu daka iya bayyana wanzuwar Suhan ɗin a makarantar saboda wani dalili, kuma shi kanshi malam Sanin da ya kasance aboki ne ga Sir Salim, ba zai taɓa lamuntar abunda ka iya jawo cikas a al'amarin abokin nashi da matar da yake da burin aure ba. Cikin kallon tuhuma ya Ameen ya fara kallon shi, bai ce ƙala ba, har Malam Sani ya kai aya a zancen nashi. Yana da wata irin baiwa ta daban da Allah ya bashi, wadda ba kowa ne yaba irin ta ba, muddin ka faɗa mashi ƙarya ko abunda ba haka bane a cikin zuciyar ka, to kuwa lokaci guda farat ɗaya zai gano ka, saidai idan yayi niyyar share wa ne kawai ya share. Ba tare da yace komai ba, ya miƙe gami da zaro complement card ɗinshi ya ajiye bisa teburin HOD ɗin. Shima bai kuma cewa ƙala ba, ya sanya hannu ya ɗauka gami da dubawa, a ɗan firgice da kuma alamar mamaki ƙarara kan fuskar shi yake duban Ya Ameen ɗin, kaman ma dai bai gasgata abunda ya gani ba rubuce a bisa katin. Lura da hakan da Ya Ameen yayi Ya sanya shi, zare face mask ɗin a hankali daga fuskar shi, ai tini Malam Sani ya miƙe cike da tsantsar girmamawa, hannu na rawa ya miƙa ma ya Ameen ɗin suyi musabaha Bai ƙi ba, shima ya miƙe gami da miƙa mashi hannun, fuskar shi ɗauke da ɗan murmushi irin wanda ke ƙara ƙawata fuskar tashi. A tare suka kuma zama, saidai har yanzu tsantsar mamaki bai saki Malam Sani ba, tinani yake yi wai ita wannan yarinyar wacece da har ake nemanta haka? Shin ma menene dalilin Sir Salim ɗin na roƙon shi Malam Sanin akan ya ɓoye labarin Suhan ɗin koda wani zai zo nema? "Nine Muh'd Al'ameen Almustapha Dambulan. Yarinyar da nake nema ƙanwa ta ce, tayi mana ɓatan dabo ne bamu san inda ta nufa ba, ita da mahaifiyar ta, wannan ne dalilin da ya sanya kace ana zuwa nemanta nan, kuma muna da yaƙinin tana makarantar nan, shi wanda ke zuwa nan ɗin Sunan shi Bilal Amini na ne, kuma ɗan uwana, inaso ka bani haɗin kai, wajen shaida mani inda Suhan take domin mu sadu da ita da gaugawa. Mun zaɓi zuwa nan ɗinne ta ruwan sanyi, domin munsan dukkan bayanan da muke nema kana dasu" Ya faɗa cike da ƙwarin guiwa, ƴar fara'ar dake kan fuskar shi tuni ta kau, saboda baya ko fatan Abunda kan kawo tarnaƙi a haɗuwar shi da Suhan ɗin. Malam Sani ne ya shiga jinjina kai, sannan ya ɗora da cewa "Tabbas Yallaɓai tana makarantar nan tamu, to saidai su da kansu ne suka nemi da muyi hakan, zan ji daɗi ace koda ka gano ta, ka nuna bansan da zancen ba, hakan shine kawai alfarmar da zan iya roƙa a wurin ka" Cike da gamsuwa Ya Ameen yashiga jinjina mashi kai ba tare da ya kuma cewa komai ba. Miƙewa Malam Sanin yayi yana faɗin, Yallaɓai me za'a kawo maka kayi break fast dashi? Girgiza mashi kai Ya Ameen ɗin yayi, domin shi dai burin shi ya sadu da Suhan ɗin a daidai wannan lokacin. Komawa Malam sanin yayi ya zauna, gami da jawo wani folder ya buɗa, tiryan tiryan har yazo kan files ɗin na suhan. Jawoshi yayi, gami da miƙa ma ya Ameen. Cikin ƴar taƙamar da ta zama jinin jikin shi, da kuma sarauta dake yawo yanzu a jinin shi ya sanya hannu ya amsa. Malam Sani dai yana kallon shi, burge shi yake daɗa yi, abun alfaharin shi ne, ace yau kaman Ya Ameen ɗin Yariman Matasan Arewa ne zaune a office ɗin nashi, a kuma gaban shi. Ajiyewa yayi, yana mai zaro wayar shi ya kwafi number ɗinta, sannan ya miƙa ma Malam Sani File ɗin, godiya ya shiga yi mashi kaman baya son sake magana, ya miƙe da niyyar ficewa bayan ya sake ba Malam Sanin Hannu. Har waje bakin motar shi ya raka shi, yana gaba shi kuma yana binshi a baya, saboda girmamawa Malam Sanin ne ya buɗe mashi ƙofar motar da kanshi, wadda tin fitowar su daga Office ɗin Ya Ameen ɗin ya buɗe motar ta hanyar ɗan maƙullin dake hannun shi. Shi kanshi motar ta bala'in tafiya da imanin shi, in ko haka ne, dole ya nemi abokin nashi Sir Salim Yayi mashi murnar ƴar babban gida irin haka da zai aura, duk da shima yana da abun hannun shi sosai, kuma ya fito daga babban gida, Amman sai yake ganin kaman wannan daya zo ya dama su ya shanye har romon nasu. Brown emvelop ya miƙa ma Malam sanin, yana faɗin "wannan tukuicin ka ne, saboda nuna mani ƙanwata da kayi, sai mun sake haɗuwa" Hannu na rawa Malam Sanin ya sanya ya karɓa, bakin shi har kunne sai zuba godiya yake yi, dama gashi wata yayi tsakiya komai ya tsaya. Har saida yaga fitar motar Ya Ameen ɗin daga makarantar sannan ya juya ya koma office ɗin nashi da zummar kiran abokin nashi. **************** Hankalin Bilal idan yayi dubu ya tashi, har saida ya dafe ɗan madaidaicin teburin da Abie ɗin yake kai, lokacin da yake labarta mashi tafiyar Ya Ameen ɗin Nigeria. Shima Abie ɗin kwatsam saidai yaga Bilal ɗin a office ɗin nashi, aiko nan ya titsiye shi akan ya faɗa mashi inda Ya Ameen yake, sanin Bilal ɗin ko wanene a gurin Ya Ameen ɗin ya sanya Abie ɗin sanar dashi gaskiya kawai. "Subhanallah, me yake faruwa ne Yaya?" Abie ɗin ya faɗa cikin sauri yana mai kamo Bilal ɗin ya nufi wata sofa dake gefe ajiye ya zaunar dashi, komawa yayi ya ɗauko mashi ruwa cikin wata gora haɗi da mug fari tar, ruwan ya tsiyaya mashi ya miƙa mashi. Baiyi gardama ba ya amsa ya kwankwale, sake zuba mashi yayi, nan ma shanyewa yayi tas, ko da dai Abie ya kula kaman ruwan bai ishe shi ba, sai ya miƙa mashi gorar ruwan baki ɗaya, aiko amsa yayi ya kafa kai, saida ya shanye ta tas, sannan yayi jifa da robar gefe yana faɗin. "Why why?" Zanewa yayi ya kwanta, shi dai Abie yana tsaye yana kallon ikon Allah, Amman kanshi gabaki ɗaya ya kulle, tambayoyi yake son yi ma Yayan nashi, Amman ya kasa ta ina ma zai soma farawa? Saboda haka ya juya ya koma wurin zaman nashi, gami da zama ya jawo laptop ɗin tashi ya cigaba da aikin shi. Bilal ɗinne ya miƙe tsaye gami da faɗin "Ni zanje gida Abie, sai ka dawo" bai jira cewar Abie ɗin ba, ya juya haɗi da ficewa daga Office ɗin. Da kallo ya raka shi, yana mai girgiza kai, dole da akwai wani abu dake faruwa ko dai yake shirin faruwa, waya ya jawo domin ya faɗa ma Dad ɗin nashi, tin kafin komai ya kwaɓe dashi a ciki. Aiko cikin sa'a Dad ɗin ya ɗaga, tiryan tiryan Abie ɗin ya feɗe ma Dad ɗin biri har wutsiya, shima hankalin shi ya matuƙar tashi, kashewa yayi yana mai cewa bari ya nemi Bilal ɗin yaji koma menene. To shima Bilal ɗin, koda Dad ɗin ya kira shi bai ɓoye mashi komai ba, ai abokin kuka ba'a ɓoye mashi mutuwa, in ma bai sanar da Dad ɗin ba wa zai sanar mawa? Cikin tsantsar ɓacin rai da Alhaji Mustaphan kan daɗe bai yi ba, yake sanar da Bilal ɗin cewa kada ya sake ya faɗa ma kowa, kawai su haɗu a nigeria ɗin asan abun yi. Kashewa yayi gami da kwanciya domin ya huta, kafin anjima ya tashi yayi wanka ya ɗauki hanyar komawa Nigeriyar. Mama Talatu an saki jiki a gida ana zuba isa da mulki, idan Hajiya Kubran bata nan, ita ce kan gaba akan komai, ta samu yadda take so, wani lokaci ma har ita ake ba ɗan ihisanin da ake ba ma'aikata ta rarraba, sai kuma Abunda taga dama take kawowa ta basu. Ta ɗaya ɓangaren kuma Maree har yanzu tana kan bakanta na son auren ɗan masu gidan ko ta wacce hanya ce, jiran dawowar shi ƙasar kawai take yi, ta aiwatar da abunda ta ƙumso tin tini tana zaman jiran zuwan nashi. Ita ko Hajiya Kubra ma bata ko kula da komai dake faruwa ba, su Hajiya Sa'a da Hajiya Laila sun ƙara zama mata aminnai, koda Hajiya Zainab suka koma Abujan da zama ba kasafai ma suke haɗuwa ba, shima sai dai ita Hajiya zainab ɗin taje gidan Hajiya Kubran, har dai ta gaji, ta kula cewa ita ce zata dinga zuwa gidan ƙanen mijin nata? Alhali babu abunda take nema daga matar gidan? Sai ta haƙure ma kanta, indai wata sabgar ta haɗa su, sun gaisa, ko da yake ma ba komai ne da akeyi ba kankiyar wanda Hajiya Kubran ke zuwa, kuma a haka kowa ya sanya mata ido, to tana da kuɗi, tafi ƙarfin wulaƙanci ta kowanne fanni. Hannun jari ta zuba sosai a kamfanin matatar mai ta Nigeriyar, arziƙin yanzu fa yaci uban nada. Ko ina kayi labarin irin shaharar Hajiya Kubran akeyi, ya zuwa yanzu ta kuma samun ƙawa da take mai irin halin ta komai da komai, kuma itama tana da masifar kuɗi, sai suka ɗinke suka zama su huɗu kenan idan kaji ana cewa 4Hajiyas to su ake nufi, ciki da bai na Abuja babu inda labarin su bai karaɗe ba, mata ne masu ji da kansu, wanda duniya take kaɗa masu gangi a tsakar ka, basu damu da su taka wanda suke so ba, su muzgunawa wanda suke so, ko wanene kai, kuma ko me kake taƙama dashi indai ka shiga shirin su 4Hajiyas to fa ka bani, ka kaɗe har buzun ka. ******************** Ƙarfe biyu muka tashi lecture ta farko, salla kawai mukayi muka koma ta biyu, sai 4 muka fito, ina fitowa ne text ɗin Sir Salim yana shigowa wayata, akan in shirya zuwa 5 yana zuwa, domin yanzu mun cenza akalar inda muke karatu, library muke zuwa domin mun fi sake wa a cen muyi Abunda zai amfane ni. Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "Hooo Sir Salim, ba hutu kenan? Gaskiya fa kada ka fasa man ƙwaƙwalwar saboda karatu" Da haka na isa ɗakin, wanka kawai nayi, na jawo biscuit da fresh Yoo nasha, ban cika cin abinci ba sosai, duk da kasancewa ta ba mai rama ba, jikina yunwa ko wahala baya sanyawa ya cenza daga yanda yake. Wanka nayi gami da shiryawa, a karo na farko kenan a rayuwa ta da zan fara yima Sir Salim kwalliya, ya sha roƙo na akan hakan, ni kuma sai nake ganin ba kwalliya ko soyayya ce ta kawo ni ba. Tsayawa nayi na tsara kwalliya mai tafiya da hankali, riga da skir na wata jar atamfa mai ratsin shuɗiya na sanya, riga da skirt ɗin sun ɗan kama ni, hakan ce ta sanya na fara tsarguwa da kaina, da tunanin ba zan iya fita a haka ba. Su Raihana ne suka shiga koɗa ni, ganin ina shirin tuɓe kayan in cenza ne, ya sanya suka shiga yiman magiya akan in bar shi, ai hakan ma ba wata damuwa, ko ba komai ya kamata in ɗan dinga yima Sir Salim ɗin kwalliya, tinda shi dai namiji ne mai son gayu, gashi ɗan gayu, dukkan matan dake skul ɗin bai zaɓi kowa ba sai ni. Da haka ne yasanya sukayi comvincing ɗina akan in bar su, na bar su ɗin amman nace hijab zan sanya, nan ma nunawa sukayi basu yarda ba, khadeeja ce ma mai jawo mani shuɗin gyale, harda ƙoƙarin yafa mani, Raihana na fesa mani turare. Muna cikin wannan dramer ɗin shiryawar ne, sai ga kiran shi akan in fito yana jirana zamu wuce library. A haka na fita, ina ta jajjan gyalena saboda rashin sabo. Gashi kaina a kwance yake, duk yanda nayi akan in rufe gashin, ɗan kwalin baya da girma, hakan ce ta sanya dole na haƙura, Amman sai na yafa gyalen bisa kaina, ni kaina na san nayi kyau, kaman wata amarya, ban ɗauke da jikka, saboda karatu zani ba biki ba, waya ta ce kawai a hannuna, sai litattafai na na text book da handout, a haka na fito har na isa ga motar. Yana daga ciki ya sanya hannu ya buɗe mani. Shiga nayi ina mai sakar mashi ɗan ƙaramin murmushi, shima yayi kyau cikin dakakkiyar shadda mai ruwan makuba, kanshi sanye da hular ƙube, sai zuba ƙamshi yake da fara'a kaman yanda ya saba. Jan motar yayi yana mai cewa "Gimbiya ta barka da fitowa" Sake sakin murmushi nayi, ina mai ɗan sunne kaina ƙasa. Gaishe shi na shiga yi, da salon koyon magana ta ya shiga amsa mani, na daga cikin abunda ke ƙara burgeni da Sir Salim ɗin kasancewar shi mutum mai ban dariya, tin baka sakin jiki dashi, har sai ka koma kana sakin jiki dashi, har in ma baka ji ɗuriyar shi ba ka bincika, masalan in kana cikin hali na ɓacin rai. Kai tsaye bakin library mukayi parking, littattafan ya amsa daga hannuna, muka jera har cikin library ɗin muka samu kujeru muka zauna. Kowa dake library ɗin mu yake kallo da ban sha'awa, mun dace da juna sosai, gashi daka kalli fuskokin mu, kasan muna cikin zallar farin ciki. Ba ɓata lokaci muka fara abunda ya kawo mu, har zuwa kusan ƙarfe shida. Littattafan muka rufe, yayin da Sir Salim ɗin ya kirawo Ammin shi video Call muka shiga gaisawa, ga dukkan alamu taji daɗin ganin yaron nata yana yaɗa manufar shi ga Suhan ɗin. Ɗan barkwanci tayi mana tana mai kashe wayar haɗi da cewa bari tabar mu mu tattauna, ni sai ma duk ta sakar mani kunya. Shi kaɗai ke surutun shi, nikau daga eh sai a'a sai murmushi da nake ta fama doka wa. Yaba ƙofar shigowa baya, yayin da ni kuma nake zaune ina fuskantar wanda suke shigowa, hasken fitilar library ɗin tar a kan fuska ta, masalan yanzu da marece ya soma kawo jiki. A wayar tashi dai still ya buɗo hotunan yaran shi yana nuna mani, yaran masha Allah, farare tas dasu, kaman ƴaƴan larabawa, da gani dai wannan Hasken Ammi ne suka biyo yaran, tinda ko ita ma'un bata ko kai ni haske ba, gashi shima Sir Salim ɗin kai tsaye bazaka ce mashi fari ba, ko baƙi. Yaran sun burgeni, har ƙanwar shi dake karatun likitanci a Sudan mai suna Asiya Saida ya nuna mani. Amsar wayar nayi a hannu na ina kallo haɗi da faɗin "Masha Allah, ta fika kyau, tayi maka wayau, ita ta biyo kyawon Ammi sak" Na faɗa ina mai ɗan sakin dariya. Shima dariyar yayi cikin wani irin salo, yana faɗin "Kedai faɗi gaskiya, ko kowa zai ce Lil ta fini kyau, ai ke ba zaki faɗi haka ba, ko kuwa?" Ɗan jinjina kai nayi ina mai cewa "Umm gaskiya kam Yallaɓai salim" "Wuuuuuuuuuuu" Abunda naji kowa na faɗa kenan a library ɗin, ga dukkan alamu dai wani abu ne suka gani daya basu mamaki ko ya burge su, sai kuma naga duk suna Miƙewa mazan su da matan su. Hakan ce ta sanya ni kai kallo na zuwa ga ƙofar da nake fuskanta, har yanzu murmushin bai bar kan fuska ta ba, bansan dalili ba yanzu indai ina tare da Sir, Salim ɗin nake tsintar kaina cikin irin wannan farin cikin. *Dummm* Gabana ne ya ruguje ya faɗi, ganin ko wanene tsaye ƙofar shigowa library ɗin yana fuskanta ta, a hankali ya shiga takowa cikin salon tafiyar nan tashi da bazan taɓa iya mantawa ba. Sanye yake cikin ƙananan kaya fari ƙal ɗin wandon jins mai bala'in taushi, rigar shi ƙirar kamfanin gucci mai matsakaicin tsawo, kalar yellow ce mai masifar kyau ta ɗan sirka da orrange, hannun ta kuma gajere ne sosai, hakan ce taba damatsan hannuwan shi damar fitowa tar tar dasu. Ƙafafun shi sanye cikin snickers masu masifaffen kyau da tsada, farare ne suma tas dasu masu adon yellow mai orrange a ciki. Fuskar nan tashi Sam babu walwala ko annuri a ciki, hasali ma idanun nashi daɗe suke cikin wani baƙin glasa mai sheƙi da walwali. Hannuwan shi ɗauke da makullin mota, sai kuma wayoyin shi guda biyu ƙirar Iphone 11 Pro Max. Ni yake nufowa kai tsaye, duk takunshi ɗaya daidai yake da bugawar zuciya ta sau kusan ɗari. Yana nufo ta inda nake zaune ne, ya shiga zare glass ɗin dake saman fuskar shi, ko da zan suma in farfaɗo, koda zan mutu inbar duniyar sannan in dawo. Koda zan shekarar annabi Adamu ban sanya shi a idanuna ba, bazan taɓa iya mance ƙamshin turaren nashi ba, ba kuma zan taɓa iya mance salo da izzar tafiyar tashi ba, ba kuma zan taɓa iya mance kalar da fuskar shi kan bada ba a duk lokacin da yake cikin matsanancin ɓacin rai. Hannun shi marar ɗauke da komai sanye yake cikin wani silver ɗin abun hannun azurfa anyi mashi ado da ƙaton stone ɗin dymond mai masifar kyau da walwali sai ɗaukar ido yake, soke yake cikin aljihun wandon shi, yayin da gudan yake ɗauke da baƙar agogo ta kamfanin Iphone ɗin. Ban san lokacin da na miƙe ba zunbur, ina mai dafe bakina da dukkanin hannuwa na, 🙊tsoro ƙarara da firgita suka bayyana a kan ƴar zagayayyar fuskar tawa, wayar Sir, Salim ma dake hannu na, bansan lokacin da na sake ta ba ta faɗi ƙasa wanwar. Ganin hakan ne da Sir Salim ɗin dake ta faman zuba man surutu yayi, shima bai san lokacin da ya juya da kujerar ba, domin ganin Abunda ya firgita ni haka lokaci guda har ina sakar mashi wayar shi ƙasa. A hankali shima ya shiga miƙewa , daidai ƙarasowar Ya Ameen ɗin ta wajen Kujerun da muke kai zaune. Kowa ya maida mu talabijin a library ɗin, duk mu suke kallo, gabaki ɗaya attention ɗinsu ya dawo kanmu kacokam. 👀 Ganin hakan da Ya Ameen ɗin yayi ne, ya sanya shi jawo kujera ɗaya ya sanya ta tsakiyar tamu ni da Sir, Salim ya zauna yana mai ciƙa ma Sir Salim ɗin hannu alamun suyi musabaha. 🤝🏻 Jiki a matuƙar sanyaye shima Sir Salim Ɗin ya shiga miƙa mashi hannu ɗin sukayi musabaha. "Sunana Al'ameen Almustapha Dambulan* Ya Ameen ɗin ya faɗa yana mai sakin wani kiler smile a saman fuskar shi, ina kula dashi har yanzu da na gagara zama. Murmushin da naga yana saki ne saman fuskar tashi ya ƙara taimakawa wajen ruɗewa ta. Miƙewa tsaye naga Sir Salim Yayi, cikin girmamawa gami da ƴar jinjina kaɗan haka,👍🏻 hannuwan shi daidai kunnen shi, ya shiga faɗin "Allah yaja zamanin Yariman Matasan Arewacin Nigeria" Sake kwalalo idanu nayi,😳har yanzu fa na gagara zama, kuma ban sauke hannuwa na daga bisa bakina ba. Da hannu Al'ameen ɗin yayi ma Sir, Salim Alama da ya zauna da hannu, ba musu ya kuwa zauna. Niko da nake tsaye sai faman tsiyayar zufa nakeyi, zuciya ta sai faman bugawa takeyi fat fat kaman zata tsago ƙirjina, har yanzu kuma gogan nawa bai ko kalli ta inda nake tsaye ba, sai ma zaro wayar shi da yayi ya shiga daddannawa....... *Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa.* 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *Ga akuya ga kura.* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)* _Laweexar Abdullahi da Aishatu Babayo, ina matuƙar jin daɗin comment ɗinku, ina matuƙar godiya da addu'o inku da ƙaunar ku a kaina da novel ɗina. Allah ya barmu tare ya ƙaro danƙon ƙauna a tsakani. Ameen_ *Page ~39~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Kusan zamu iya cewa a tare suka sauka ƙasar. Mudi ne yaje ya ɗauko Alhaji Mustapha daga Airport, ita kanta Hajiya Kubra taji matuƙar mamakin ganin mijin nata, to sai dai isa da mulki irin nata ba zaya iya bari ta tambaye shi ba, masalan ma yanzu da harkokinta suke ta ƙara bunƙasa, ita kanta bata da lokacin kanta balle na wani mijin nata. Bayan sun tattauna ta yanda zasu ɓullo ma al'amarin nasu ne, har zuwa yanzu dai basu samu matsayar ta yanda zasu faro ma al'amarin ba. Bunciken komai suka fara yi, hatta dasu mudi ɗin sun shaida cewa Alhaji ƙaramin bai zo gidan ba, basa so Hajiya Kubra ta ankare da abunda yake faruwa, wannan ce ta sanya su barin binciken ta gidan, sai kuma suka koma sauran kamfanonin Al'ameen ɗin da kuma duk wanda yake da access dashi. **************************** "Ina fatan dai ka gane ni?" Al'ameen ɗin ya faɗa cike da basarwa, bayan ya bar latsa wayar da yakeyi, ya maida duban shi kan Sir, Salim. Cikin kulawa sosai Sir Salim ɗin yake duban Ya Ameen ɗin duba na tsanaki, a hankali ya miƙa hannu, jawo kujerar da nake zaune kanta kafin in miƙe ya tsaye yayi. "Zauna sweet heart" Sir Salim ɗin ya faɗa cike da kulawa da zallar soyayya a idanun shi. Bani da zaɓi illa zaman, domin a yanzu dai bana iya cewa ga abunda ke kai komo a cikin zuciya ta, tunani ne haɗe da mamaki da fargaba suka haɗe suka bada wani yanayi a saman fuska ta. Ya zuwa yanzu na saki hannuwa na dukka a bisa cinya ta, saidai na kasa bari in haɗa ido da Ya Ameen ɗin, wata irin kunya ce ta taso mani ta baibaye ni, ga tsarguwa da nake fama da ita, duk da har yanzu shi gogan bai ko kalle ni ba. Sir, Salim ne ya maida hankalin shi akan Al'ameen ɗin bayan ya sakar mani wani ƙayataccen murmushi, duk da har yanzu a cikin zuciyar tashi tarin tambayoyi ne a ciki. Sai a lokacin ya kalli Ya Ameen gami da bashi amsa. "Ayya Yallaɓai, Saidai fa bana da labarin ka a wajen Yallaɓiyar tawa" Ya faɗa shima cikin son dakar da zuciyar shi, cike da ƙwarin guiwa. Ɗan murmushi iya leɓo Ya Ameen ɗin yayi, yana mai ɗan juyo da kujerar shi yana fuskantata, turo mani wayar shi yayi bisa table ɗin yana faɗin. "Number ɗin Umma zaki sanya mani anan. Ga dukkan alamu dai baki Iya gaisuwa ba, duk da dai ni ba wajen ki nazo ba, Umma nake son gani" Cikin rawar baki, murya ta na sarƙewa na shiga bashi amsa "Umma bata da waya, inda take babu network". Daga haka na duƙar da kaina zuwa ƙasa, bansan me ke shirin faruwa dani ba, amman wasu hawaye ne naji suna yankowa ta cikin idanu na, haɗa idanun da nayi dashi, sai na gaza tantance ko na menene, a hankali na shiga maida su, ina mai miƙewa da niyyar barin wurin. "Ki bani Address" ya faɗa a gajarce cikin dakiya da son kauda zargin wani abu daga cikin zuciyar Sir, Salim ɗin. Cak naja na tsaya, shawarar in faɗa mashi ko kada in faɗa nakeyi a cikin raina, to saidai ya Ameen ɗin ya wuce haka a wuri na, bana jin akwai wata alfarma a wajena wadda zai iya nema in kasa yi mashi a rayuwa ta. A sace na ɗan juyo da niyyar kallon shi, idanun mu ne suka sarƙe cikin na juna, gaza ɗauke idanuna nayi, kaman yanda shima har yanzu bai janye waɗannan mayatattun idanun nashi ba akaina. A hankali na fara janye nawa, ina mai buɗe baki dakyar cikin sarƙewar harshe na shiga cewa "Sunkui, Jigawa State" Ina gama faɗin haka, sai gani nayi ya miƙe gami da sake ba Sir, Salim hannu suka sake yin Musabaha, har yanzu dai ba wanda yace da kowa komai. Juyawa yayi ya raɓe ni ya wuce gami da ficewa daga library ɗin. Kai na a ƙasa na shiga bin shi da kallo a sace. Ƙamshin turaren shi har yanzu bai bar wurin ba, ga wata irin tafiya da yakeyi cikin salon shi, irin na cikakken ɗa namiji. Ajiyar zuciya na saki, daidai lokacin da na hangi tashin motar tashi, ya ja ribos yabar wurin. A sanyaye na koma zuwa ga table ɗin na shiga tattara litattafai na, domin dai a yanzu bansan abunda zan iya faɗama Sir Salim ɗin ba, idan har ya jefo mani wata tambaya. Shima da kallo yake bina, menene alaƙa ta da Yariman ne? Shin a taƙaice ma wai wacece ni? Dambulan ɗin, family ne daya shahara a faɗin ƙasar, da wuya ka tara mutane goma ciki ba'a samu biyu ba da suka ce sun sanshi, ƙaramcin su, da irin yadda suke taimakon matasan ƙasar ne ya sanya da wuya kaji family ɗin da suka ce basa da tabon alkhairin su. Miƙewa yayi ya shiga bin baya na, ganin na wuce shi ba tare da na ce mashi uffan ba, watau ma kenan bata so ta shiga motar tashi ya mayar da ita Hostel? Sake ɗaga ƙafa yayi ganin har na gitta motar tashi da niyyar wucewa cikin sanyin jiki matuƙa. Shiga motar yayi gami da shan gabana da motar, ya sanya hannu ya buɗe mani gaban motar. To nima ɗin dai gudun zargi ko wani tunani daban, ya sanya ni shiga motar, ko ba komai dai Sir Salim ɗin har ga Allah bai san wanene Ya Ameen ɗin a guri na ba, kuma ko da wasa ban taɓa mashi makamanciyar maganar data shafi kaf Family ɗin Alhaji Mustaphan ba. Kaman daga sama naji yayi parking, gami da ɗage glassan motar da suke tint, ya sakar mana Ac, a hankali naji wata ni'ima da sanyi na shiga ta, ajiyar zuciya na shiga saukewa a hankali a hankali, ina mai jingina kaina da murfin motar tashi, haɗe da runtse idanuna gam. "Menene alaƙar ki da Yariman Matasan?" Naji ya wurgo mani tambaya cikin bazata. Ban ce dashi uffan ba, shima bai kuma cewa komai ba, buɗe idanuna nayi a hankali na aza su akan Sir Salim ɗin. Wasu abubuwa naga suna yawo a cikin ƙwayar idanun nashi, kishi ne, tattare da tarin tambayoyi acikin idanun nashi. A hankali na janye idanun, cikin ƙwarin guiwar da bansan ina da ita ba, na shiga cewa "Yayana ne" "Yayanki ta ina?" Nauyi tambayar tayi mani, beside ma ban taɓa tinanin irin tambayar ba daga gareshi. Ban da zarrar ce mashi komai, hakan ce ta sanya ni jan bakina na ɓame. Nannauyar ajiyar zuciya Naji ya saki, sannan ya sake cewa "Meyasa baki taɓa bani labarin shi ba?, anya hakan da kikayi yayi daidai? Ashe ban kai matsayin da zan iya sanin komai da ya shafi rayuwar ki ba?" Maganganun shi sun yiman nauyi a zuciya, ga wani miki dake taso mani cen ƙasan zuciya ta, wani al'amari da na daɗe rabon da in ji shi a jinin jikina ya shiga taso mani. Ban san lokacin da na saki wani tsumammen kuka ba, rufe fuska ta nayi da dukkanin tafukan hannuwa na, ina mai sauke waya ta bisa cinya ta. Bai ceman ƙala ba, kaman yadda bai yi yunƙurin hanani ba. Bai san dalilin kukan ba, ya barta ne tayi koda zata samu sauƙin raɗaɗin da take ji a cikin zuciyar ta. Na kai kusan minti goma ina yi, har saida na gaji don kaina na daina, tissue wadda ta ɗauki sanyin ac ɗin dake cikin motar, gami da wani ni'imtaccen ƙamshin turare ya miƙo mani. Amsa nayi ina mai goge hawayen dake fuska ta, lokaci guda ina mai juyawa na kalle shi, sannan nace "kayi haƙuri, na tuno da wani abu ne, tabbas shi ɗin wannan yayana ne" Har yanzu dai ba wai ya gamsu bane, kuma koda ba komai tabbas akwai wata alaƙa tsakanin shi da ita, duk da dai ba zai iya cewa ya karanci wani abu ba daga fuskar Yariman Matasan ba. Kunna motar yayi, gami da jan ta, fuskar nan tashi ta haɗe kaman bai taɓa dariya ba, yana da kishi, yana da matuƙar kishi, masalan ma akan abunda yake so. Har bakin hanyar Hostel ɗin ya ajiye ni, bai ceman ƙala ba, nima bance mashi ba, na ɓalle murfin motar gami da ficewa, har waya ta tana faɗuwa ƙasa cikin motar ba tare da na kula ba. A matuƙar sanyaye na isa Hostel ɗin namu, su khadeeja babu tambayar duniyar da basu yi mani ba, amman ban kula su ba, har wayata da na kula bata tare dani, saidai nasan tana a motar Sir, Salim na baro ta. Daren dai a haka nayi shi cikin wani irin yanayi, dana kulle idanu na sai fuskar Ya Ameen ɗin ta bayyana a cikin ƙwayar idanun nawa. ********************** "Wai ance ana sallama a waje" Hajjo dake tsakar gida tana ta faman shara, yaro yayi sallama, ajiye tsintsiyar tayi tana mai gyara ɗaurin zanen ta. "Inji waye?" ta maida ma yaron daya shigo lokacin. "Nima Wallahi ban sanshi ba, da dai ƙatuwar mota yazo" Ya faɗa cikin son juyawa, yana mai gara ƴar tayar shi, da niyyar ficewa. Jin haka ne da hajjon tayi, ya sanya ta saurin tattara sharar ta juye cikin wani buhu da yake ajiye gefe. Leƙawa tayi ɗakin Umman tawa, gama shiryawr ta kenan, da nufin zuwa wata barka da akace anyi haihuwa nan bayan gidan su. Sanar da Umman tawa tayi wai ga Malamin Su Hauwa'u nan yazo yana waje. Umman ce ta amsa mata, tana mai zura hijabin nata, gami da ficewa domin shigowa dashi. Turus taja ta tsaya daga bakin ƙofar gidan. Murna da farin cikin ganin matar fal a cikin ranshi, sannu a hankali ya shiga takawa zuwa wajen da umman tawa take tsaye. "Muhammadu??? Kai ne?" Umma tawa ta faɗa cikin son gasgata abunda idanuna ta suke nuna mata, gani takeyi kaman gizo idanun nata suke mata. "Nine Umma, na same ku lafiya?" Ya faɗa cikin girmamawa, yana mai daidaita tsayuwar shi ɗan nesa kaɗan da inda umman tawa take tsaye. "Shigo daga ciki mana" Abunda ta faɗa kenan, tana mai juyawa zuwa cikin gidan. A baya ya shiga binta har zuwa cikin gidan, rana ta kawo tsakiya, hakan ce ta sanya babu inuwa ko kaɗan a tsakiyar gidan. Ɗakin da yake nata, shi ta sake turawa tana mai ɗage labulen, sannan ta shiga gami da shimfiɗa mashi tabarmar kaba. Shiga yayi ya zauna, yana mai tankwashe ƙafafun shi. Fita umman tayi da niyyar zuwa kiran Hajjon da ta riga ta koma ɗaki. Da kallo ya shiga bin ko ina na ɗakin, wani irin tausayn su ne yake taso mashi cen ƙasn zuciyar shi, Meyasa suka zaɓi rayuwa a irin wannan halin? Ashe har muzgunawar da akeyi masu acen sun kwammace su zauna a irin wannan yanayin? Dubi ɗakin fa? Kalli gidan. Zuciyar shi ce ta cigaba dayin zafi, tabbas ya zama wajibi ya cire su a wannan yanayin, ya zama wajibi yayi iyakar ƙoƙarin shi wajen ganin ya inganta rayuwar su, wannan haƙƙin shi ne, alƙawari ne kuma ya ɗauka. Har yanzu ji takeyi kaman almara, har yanzu bata gasgata Muhammad Al'ameen ɗinne zaune a ɗakin nata ba. Ta yaya akai ya gano inda suke? Ta ina ma yasan da wannan ƙauyen kuma har yazo? To ko dai wani ɓalli a labarin nata ya fita a duniya ne? Da haka ta ƙarasa ɗakin da Hajjon take, ta sanar da ita tayi baƙo tazo su gaisa. Daganan ta wuce ta ɗauko kwanon sha, ta kandamo ruwa a cikin randar ta nufo ɗakin, inda ta tadda Hajjon har sun gama gaisawa da Al'ameen ɗin cikin girmamawa da mutunta juna, duk da ba wai ya san ko ita ɗin wacece ba, ko kuma ita ta san ko shi ɗin wanene ba. Fitowar ta yayi daidai da shigar umman tawa ɗakin, zama tayi gefen ƴar yaloluwar tabarmar dake yade gefe guda na ɗakin, da alama nan ne wurin kwanan su. Sake gaisawa sukayi sosai cikin girmamawa, har take tambayar shi mutanen gidan da wajen su Saudat da Afnan. Cikin son kauda komai yake murmusawa yana faɗin suna lafiya. Ɗan shiru ne ya biyo baya, sai kuma Al'ameen ɗin ya muskuta, tare da sake duƙar da kanshi ƙasa ga matar da yake fata da burin ta zama surukar tashi. Sannan ya shiga cewa *"Umma nazo ne takanas domin in baki haƙuri a bisa dukkanin Abunda suka faru bayan tafiya ta, haƙiƙa banji daɗi ba ko alama, hasalima dawowa ta nan ba da daɗewa ba na ji labarin barin ku gidan, nasan koma minene ya faru da sanya hannun mahaifiya ta, umma nasan kunyi haƙuri, ina mai ƙara baku haƙuri a madadin mahaifiya ta, ki taimaka umma ki dawo gare mu a karo na biyu, ina mai tabbatar maki da insha Allahu komai yazo ƙarshe, umma ki taimake ni umma, nasan ba'a kyauta maku a gidan nan, saidai ina iya ƙoƙari na ganin hakan bata faru ba. Nazo ne musamman domin in nemi yafiyar ki, sannan abu na biyu da yake tafe dani, ina so ki taimaka ki bani auren Suhan nayi alƙawarin riƙe ta amana, zan tallafi Rayuwar ta umma, zan sanya ta manta da duk wani maraici da wahala da tasha a kaf rayuwar ta umma"* Tinda ya fara magana umman ke ɗan sakin murmushi, saidai maganar shi ta ƙarshe ya sanya gabanta rugujewa ya faɗi, da ƴar firgita ta cenza akalar kallon da take mashi. Bata ce komai ba, ƴar nisawa tayi tana mai muskutawa a hankali ta sauke ajiyar zuciya. Tabbas kallon shi takeyi, iyakar gaskiyar shi kenan, abunda ya kawo shi kenan, Al'ameen ɗin ba tin yanzu ba, ta riga ta sani mutum ne da baya da ɓoye ɓoye a rayuwar shi, ta san za'a rina, ta san hakan zata faru ko ba daɗe ko bajima, na daga cikin abunda ya sanya ta barin gidan kenan gudun faruwar hakan. Amman da yake Muhammadu daban yake a cikin mutane, tinanin shi ya sha banban dana sauran, tabbas ba tantama da gaske yake wannan maganar har cikin zuciyar shi. Nisawa tayi a karon farko kenan da zata ce wani abu tin bayan gaisawar da sukayi dashi da farko. "Naji duk bayanin ka Muhammadu, haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki da jin wannan zancen naka, ko ba komai nasan irin ƙoƙarin da kayi a kanmu, da kai da mahaifin ka harma da mahaifiyar taka babu abunda kuka yi mana, kawai yanayi na rayuwa ne ya sanya mu cenza wurin zama, to saboda haka babu abunda kuka yi mana. Maganar Suhan kuma babu abunda zaka nema wurin mu mu Gaza baka shi, saidai yanzu haka akwai maganar wani a kanta, tana cen makaranta tana karatu, malamin ta ne, don harma manya sun shiga cikin Al'amarin, bana jin ko kai idan zaka iya bada gudunmuwar ruguza wannan auren nata, yana matuƙar sonta, kuma kowa nashi yana sonta, Kaga kai kuwa mahaifiyar ka ba zata yi na'am da wannan al'amarin naku ba, da haka ne nake mai baka haƙuri, ka bita da addu'a da fatan alkhairi, har abada ba zamu taɓa iya mance alkhairin ka gare mu ba" Tin da ta fara magana shima kanshi yake sunkuye ƙasa. Bai taɓa jin kalami da suka ratsa kunnuwan shi ba kai tsaye suka wuce kai tsaye zuwa cikin ƙwaƙwalwar tashi ba irin waɗannan. Umman Suhan, ita ce yau take bashi haƙuri, da jaddada mashi cewa Suhan ɗin nada tsayayye, lallai wannan al'amari duk yanda ya kai da ɗaukar shi ƙarami ya zarce yanda yake tinani. Jikin shi har ƴar rawa yakeyi, ƙarfin halin ce ma umman yayi "Umma nine na fara neman ta, nine farko, in ma akwai wanda ya nema to bayan nine, umma ki taimaka mani" Itama sake girgiza kanta tayi, "Muhammadu bana jin daɗin yanda kake mani magiya akan abunda nasan kafi ƙarfin shi a gurina, saidai sanin kanka ne cewa bakyau nema kan nema" "Umma nine na fara nema, Umma ki tambayi Dad kiji, ya san da maganar, ya san da zancen" Shiru tayi cike da mamaki, idan ada aka faɗa mata cewa Al'ameen ɗin zai yi magiya agaba akan Suhan ɗin, to fa lallai ba zata taɓa yarda ba, kallon shi takeyi da wani irin yanayi. Al'ameen ɗin ba irin yaran nan bane mayaudara, hasalima ita bata taɓa jin ance yau ga budurwar shi ba, tinda take a rayuwar ta, balle ta ɗauka da yaudara yazo. Al'ameen yaro nutsattse ɗan gayu, mai ji da kuɗi, sarauta,ga uwa uba ilimi. Matasa da dama na fatan ina ma ace sune shi ɗin, dukkan qualities ɗin dake tattare da Salim ta san Al'ameen ya doke shi ya shanye. Saidai bata fatan Abunda zai sanya ta karya ma Salim ɗin da Hajiya Khaltum ɗin alƙawarin data ɗaukar masu. Ta sani cewa tuni Al'ameen ɗin ke son Suhanan, to saidai bai furta ba, koda ya furta, ita bata san da hakan ba, koda taji ƴan maganganun ta ɗauka zance ne irin na mutane da yaɗa jita jita. Shiru ɗakin ya ɗauka na wani lokaci, kowa da abunda yake saƙawa a cikin zuciyar shi, ganin shirun yayi yawa ne ya sanya shi miƙewa gami da yima umman sallama ya fice. Itama da kallon tausaya wa ta shiga bin shi, bata da yanda zata yi, tana tsoron kaidin hajiya kubra, tana tsoron kai ɗiyar ta inda zata koma ƴar gidan jiya, hajiya kubra ba lafiya bace, duk da bata so ace Al'ameen ɗin ya nemi alfarma ba a karo na farko a duk zaman da sukayi tare ya rasa ba. Shima dai dakyal ya isa ga motar tashi, juwa yake gani da jiri, fuskar nan ta kaɗa tayi jajur, haka ma idanun. Biyu biyu yake gani har ya kai ga shiga cikin motar, saidai ya kasa tadawa balle ya ɗauki hanyar barin ƙauyen. Dole ne ya nemi Dad, dole ne ya koma gidan nasu, wannan karon baya jin idan zai iya kuma haƙura, masalan ma daya ganta jiya ta ƙara kyau da wayewa, ga ilimi daya fara ratsa ta, hasken ta ya kuma fitowa fayau, sanyin ta da natsuwar ta har yanzu suna nan tattare da ita. Kenan shine wanda ya ganta dashi jjiya? Kenan shine wanda yake ƙoƙarin yi mashi juyin mulki? Ba laifin kowa bane sai na Bilal, ta yaya akayi ma har hakan ta faru ba tare da yayi gaugawar faɗa mashi ba? Kenan da yanzu bai rasa ta ba! Wani sashe na zuciyar shi ne yake sanar dashi cewa "Ai har yanzu baka rasa ta ba, kada ka sare da wuri Al'ameen, kai ba irin wanda zaka nemi yarinya mace bane da sunan aure ka rasa" Ashe haka matan duk da suke cewa suna son shi da aure suke ji, a duk lokacin da ya ƙi sauraren su? Daƙyal ya samu ya kunna motar, ya jata yana mai ficewa daga ƙauyen. Hanyar Abujan ya ɗauka kai tsaye ba tare da shayin komai ba, Dad shi kaɗai ne last hop ɗinshi, wannan karon zai nemi taimako daga wajen mahaifin nashi, ba tare daya tsaya tunanin komai ba. _Bayajin wannan karon idan har Hajiya Kubran zata iya zama shamaki a gareshi wurin samun Suhan ɗin tashi a karo na biyu........._ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~40~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Kai tsaye gida ya dosa, baya son abunda zai ɓata mashi lokaci ko alama. Har bayan da yayi parkinga harabar gidan, babu wanda ya gane shi sai mai gadi da ya buɗe mashi ƙofa. Basuyi mamakin ganin Alhaji ƙarami ɗin ba, saboda su dai sun san da wuya ace ya ɓata a faɗin nigeria ɗin. To saidai mamakin su ɗaya sabuwar mota da suka ga Al'ameen ɗin ciki. Mudi driver yaso ya tsayar dashi da surutu, to saidai ganin Alhaji ƙarami ɗin kaman yana cikin hali na sauri ko ujila ne ya sanya ya kyale shi har sai ya fito. Kai tsaye sashen Alhaji ya nufa cikin takun shi na sauri da ya ƙara mashi wani irin kyau da kwarjini. To saidai Alhaji Mustaphan basa gida shida Bilal a daidai wannan lokacin. Sashen Mom ɗin tashi ya nufa, lallai yayi missing ɗinta ba kaɗan ba, kasan ɗa da mahaifi, saidai wannan dambarwar da ake ciki da ya riga ya san ita ce ummul aba'isi, kuma ya san suna daf da raba gari da ita, ya sanya shi kaf fara'a da walwala da sukayi saura a fuskar tashi gushewa. Ta gaban maree da take duƙe tana matse mopper ya wuce, idanun ta kaman zasu faɗo ƙasa tsabar kallo. Har batasan lokacin da ta buɗe baki ba cikin shaƙe murya ta shiga gaida shi. To bai ma ko kula da ita ba, koma da ya kula ɗin bana jin idan har zai iya tsayawa sauraron ta a daidai wannan lokacin. Da gudu ta kwasa tayi sashen nasu na masu aiki, a kwance ta tadda mama Talatu tana barcin ƙalula, faɗa mata tayi bisa jiki kaman zata karyata, ta shiga sakin uhun murna. A firgice mama talatun ta farka tana cewa"jakar uba, ke shashasha uban ne kuma ya faru?" Bata ma ko kula da ashar ɗin da mahaifiyar tata ta ɗura ba, ta shiga faɗin " Mama wallahi Yariman Matasa ya dawo, Ya Ameen ɗina ya dawo yanzu na ganshi har gaida shi nayi, ya kuma tsaya ya saurareni sosai" Itama wani uban ihun murna ta saki, jin cewa wanda suke jira ya dawo, kuma ma wai har ya saurari ɗiyar tata. Su mama Saude ne da suke tsakar gida suna aikace aikacen su, ta wani ɓangaren kuma suna ƴan gulmace gulmacen su tsakanin su, da gudu suka kwasa zuwa ɗakin, jin sautin ihuna na tashi. Saidai koda suka je, basu ga wani abun agaishe ku ba, sufa sun fara zargin wani abu, dole tsakanin maree da mama talatun kaman akwai wata alaƙa mai ƙarfi, sannan sun kula da mama talatun yanzu da yanda take cutar su akan komai da ake bata ana cewa ta raba masu. Juyowa sukayi suna mai sakin tsoki, koda suka koma ga aikin nasu, gulmar mama talatun suka dasa, harma da maree ɗin, yanda take fitsararra mara tarbiyya, mama talatun kuma tana kallon ta bata tsawata masu. Su kau jin daɗin su suka cigaba da yi, suna masu tsara yanda abubuwan zasu cigaba da wakana bayan dawowar Alhaji ƙarami ɗin. Sun shirya amsar gidan, sun shirya su gaje gidan, ta yanda babu wanda zai faɗa aji a gidan bayan su. ************************************ Kai tsaye ɗakin ta ya nufa da yake upstairs, koda yayi sallama falon babu kowa balle a amsa mashi. Kwankwasawa ya shiga yi. Ba daɗewa ta buɗe ɗakin, da gani ma bacci take ɗan taɓawa. Cikin mamaki ta rungume shi, tana mai farin cikin ganin yaron nata ya samu sauƙi yana tsaye a bisa ƙafafun shi. Ɗan zame jikin shi yayi, yana mai kai zaune bisa wata haɗaɗɗiyar sofa da take ƙwalli ƙwal a cikin ɗakin, cikin ajin da ya riga ya zama jinin jikin shi,yake gaida Mom ɗin tashi. Amsawa ta shiga yi, tana nuna farin ciki ta zalla cikin nuna isa irin tata. Tambayar jikin nashi ta shiga yi, yana mai amsa mata, ta kula da rashin walwala da baya yi, saidai ta bar hakan da ko gajiya ce da yayi. "Son ka ƙarasa part ɗinka kayi wanka ka huta ko, zan sanya maree ta kawo maka abinci yanzu, kaman na san kana hanya na sanya ta jiya ta gyara ɗakin." "No mom, bana buƙatar komai, kada ki aiko ta, bana son yarinyar nan na shiga man sashe" ya faɗa yana mai miƙewa da niyyar wucewa. "OK ita ce baka so tana shigar maka ko? Da yake ba waccen koɗaɗɗar bace ba ko? Ta faɗa tana mai bin shi da kallo, cikin matuƙar ƙuluwa, to saidai da yake ƴar duniya ce ta ƙarshe, bata bari hakan ta bayyana ba akan fuskar ta. Ɗan murmushin gefen baki yayi, yana mai wucewa zuwa ga fita kai tsaye. Ɗann kaɗa kanshi yake yi da makullin da yake hannun shi, yana rayawa a cikin zuciyar shi "Mom kibar ma wannan maganar ta kusa zama surukar ki da izinin Allah" ya faɗa a fili yana mai idasa ficewa daga sashen nata. Koda ya isa ɗakin nashi, bai iya yin wankan ba saida ya kira Alhajin nasu domin yaji ko yana ina yaje ya same shi. Da mamaki Alhajin ke tambayar Son ɗin nashi yana ina ne.? Cemashi yayi yana gida. Cikin mamaki Alhaji Mustapha ɗin da yake zaune a guest House ɗin nashi shi da Bilal yake ce mashi ya zauna gida gasu nan zuwa shi da Bilal. Sai da gaban shi ya faɗi jin an ambaci sunan Bilal ɗin, amman dai koma miye zai tsaya yaji wane uziri zai bashi kuma. ********************** Har washe gari bana da wata walwala, haka kawai sai in tsinci kaina da wata irin muguwar faɗuwar gaba. Ban san dalili ba, sai ga hawaye na shatata a idon nawa, alhali ba wanda yace man komai, hasalima su Raihanan na lecture. Ban ƙwari kaina ba, nayi mai isata, sannan naje na wanko fuska ta, bansan dalilin kukan ba, kuma ba zance ga dalili ba. Wata yarinya ce tayi sallama ta kawo mani wayata wai inji Sir Salim yace tace man zai kira in amsa mashi. Da "To na bita, yayin da ta juya tana mai ficewa. Komawa nayi na kwanta lamo bisa gadon nawa. Ilai kuwa sai ga wayar shi ta shigo, har ta katse ban ɗaga ba. Sake kira yayi, cikin kasalar jiki na ɗaga kaman bana son yin magana. " Assalamu Alaikum" na faɗa murya ta cen ciki sosai. Daga ɗaya ɓangaren ya amsa mani. "Good morning sweet heart" "morning Sir" Abunda na iya bashi amsa kenan, ina mai jan bakina nayi shiru. "Dear ta ko baki lafiya ne? Naji muryar taki cen ƙasa" "Lafiya ta lau" Na bashi amsa, har yanzu muryata bata fita sosai. "me ya hana ki attending lecture ɗita yau? Gashi har nayi accesment" Ya faɗa daga ɗaya ɓangaren. "Hummm" kawai na samu zarafin ce mashi. Bai gaji ba ko nuna ƙosawa akan rashin amsa mashi sosai da banayi, ya sake cewa "Sweat Heart ko nayi laifi ne?uhm idan nayi laifi ne a yafe mani, in kuma maganar nan ta jiya ce, ki barta kawai ni na janye tambayoyin nawa, bana son abunda zai kawo mana matsala a tarayyar mu, inaso ki fahimceni, ni ba zargin ko wani abu nakeyi ba, kawai dai tsabar sonki da kishin ki ne nakeyi, amman tinda kince yayan ki ne abarshi a haka, ina fatan na wanke kaina yanzu? Ya faɗa yana mai sakin ɗan murmushi da yake al'adar shi ce Wata irin kunya ce ta kama ni, idan ma laifi ne ni na san nice nayi, kuma nice na cencenci in bashi haƙuri, ba shine ya cencenci ya bani ba, ko ba komai babu wani laifin da yayi mani. Tabbas nuna kishi akan abunda abunda kake so ba haramun bane, hasalima hakan sunna ce mai ƙarfi. Kuma ko ba komai yanzu ne na tabbatar da haƙiƙanin son da Sir Salim ɗin yake mani. Shikau gogan Ya Ameen isa da mulki ma ba zasu bari ka fahimci haƙiƙanin Abunda yake zuciyar shi ba, harda wani ce mani ma wai ga dukkan alamu ban iya gaisuwa ba, kuma ma wai ba wurina yazo ba, to sai kace ma kiran shi nayi. Gashi ina zaman zama na, duk da naji daɗin ganin shi, ko ba komai na san wata waraka ce ta sake dawo mana a karo na uku a rayuwa, tinda samun Sir Salim itace waraka ta biyu da muka samu a rayuwar mu, duk da yanzu ma zan iya cewa Alhamdulillah babu Abunda Sir Salim da mahaifiyar shi Hajiya Khaltum suka rage mu dashi. Amman gashi zuwan nashi yana neman dagula mana lissafi gabaki ɗayan mu, to ko in yaje gidan namu ma mai zai ce ma umman tawa? Jin nayi shiru ne har yanzu bance mashi komai ba, ya sanya shi sake cewa "Hello Jaan kina juna kuwa. Ko sai nazo ne lallashi?" Ƴar ajiyar zuciya na sauke ina mai faɗin "Ina jinka Sir, komai ya wuce, nima kayi haƙuri idan na ɓata maka" Dariyar jin daɗi yayi, domin gaskiya jiya ko barcin kirki bai samu ba, wayar ta ita ce ma ya rungume yayi bacci, yana mai shinshino ƙamshin ta ta jikin wayar. Koda sukayi waya da Ammi taji yanda muryar shi take kaman ba'a daidai ba, ba irin tambayar da bata yi mashi ba, amman bai faɗa mata ba, baya so taga kaman Suhan ɗin na wahalar dashi ne, kada ta fara wani tinani daban, sanin irin son da takeyi mashi, kuma bata son dukkan wani abu da zai taɓa mata tilon yaron nata. Saidai ko da bai faɗa mata ba, ta fahimci wani abu, faɗa ne dai irin na masoya ba'a shiga, tana zaman zaman ta za'a ce mata an shirya. Dariyar jin daɗi ya kuma saki, nan ya shiga jana da fira, da labarin ban dariya, har saida yaji na dara, na saki jiki kuma mun cigaba da fira. Na daga cikin abunda kan ƙara sanya ni amincewa da Sir, Salim ɗin, na san banyi zaɓen tumun dare ba, komin yanda bana cikin walwala ko nake cikin damuwa, indai zan biye mashi muyi magana ta minti biyar, to duk hanyar da zai bi yaga na saki jiki, kuma na dara sai yabi, mutum ne mai barkwanci, gashi mutum ne mai sanyin hali, sam baya da damuwa, lallai matar shi ba ƙaramin asara tayi ba, irin su Sir Salim ɗinne baka fatan ya faɗa son wata, saboda komin yanda budurwa ta kai da jin kai ko jan aji idan ya fara sonta, ya san ta duk yanda zaibi ya shawo kanta, ta faɗa tsananin son shi tsundum, harma in suka samu saɓani ta shiga damuwa, saboda zata rasa wannan barkwancin nashi koda na yini guda ne. Bai kashe ba, har saida yaji alamun na warware, kuma yaji maganar su Khadeeja a ɗakin alamun sun shigo. To baya son yana fira dani sosai a gaban su, ko ba komai dai su ɗaliban shine, kuma ba wani sanin haƙiƙanin halin su yayi ba, gudun halin su na ɗalibai yake kada aje ana yayata shi,ko ba komai yana gudun wulaƙanci da surutai daga wurin ɗalibai. Kuma gashi da akwai waɗanda suke son shi da jin haushin shi, jira kawai suke wani abun magana ya ɓullo daga ɓangaren shi a cigaba da yayatawa, saboda kawai yace yana son Suhan ɗin kuma da aure. *To dama haka rayuwar ta gada, abincin wani gubar wani,duk yanda ka kai da tarin masoya dole ta ɗaya ɓangaren a same ka da maƙiya, fatan mu dai a rayuwa shine Allah yayi katangar ƙarfe mai ƙwari tsakanin mu da maƙiyan namu, ta yanda saidai su dunga hango bayan mu cen nesa dasu. Ameen* ************************* Har yayi wanka ya shirya cikin riga fara ƙar mai samfarin amless da wando tree quater mai ruwan ƙasa sosai wanda ya ciza, yayi kyau matuƙa, kaman a ƙasar waje yake. Sai tashin ƙamshin nan nashi mayatacce yake yi. Harabar gidan ta ɓangaren ɗaya inda akayi wani ɗan ƙaramin lambu shimfiɗe da grass carpet tsanwa shar da ita, ga wani ni'imtaccen ƙamshi da yake tashi ta jiki fulawoyin da aka yima wurin ado dasu. Zama yayi bisa wata kujera mai kyau da akayi da zallar duwatsu, harda ɗan table a tsakanin kujerun shima na duwatsu ne. Ɗan lemon power horse ne a hannun shi riƙe yana ɗan sipping a hankali, hankalin shi kacokam na kan wayar da yake ta latsa wa. Motar tasu ta shigo gidan a guje. Da kallo ya bita, har zuwa lokacin da tayi parking kusa daf da sashen Alhaji Mustaphan. Bilal ne ya fito a mazaunin dreba, sai Alhaji Mustapha da ya fito daga kujerar baya. Ɗan tsayawa yayi yana kallon yaron nashi da ya taso yana nufo ta inda suke tsaye. Gaban Bilal ne ya cigaba da faɗuwa, ta yanda zai haɗa idanu da abokin nashi kawai yake yi. Ƙarasowa yayi, yan mai ɗan duƙar da kanshi ga Alhajin nashi ya shiga gaida shi cike da girmamawa. Sannan ya juya yana mai kallon Bilal ido cikin ido, miƙa mashi hannu yayi ba tare da yace komai ba. Ko bai faɗa ba, kallon tuhuma ne yake yi ma Bilal ɗin, kuma shima ya fahimta, to saidai sanin da yayi ne cewa Al'ameen ɗin bai san komai dake faruwa ba, indai ba bayan ya dawo bane ya sani. Amman a majiya mai tushe ai an sanar dasu cewa bai ko zo gidan ba, kenan dai ba wannan ce ta kawo shi ƙasar ba. Alhaji Mustaphan ne ya jawo hannun shi, yana mai faɗin "Muje ciki ka amshi hukuncin wahalar damu da kayi nida abokin naka wajen neman ka" Duk da cikin ƴar zaulaya yayi maganar, Amman saida abun ya nasheshi a cikin zuciya, to ta yaya akayi suka san yana ƙasar da har ma suka ce ya wahalar dasu wajen neman shi? A haka ya shiga bin Dad ɗin nashi, Bilal ɗin na bayan su har zuwa cikin tanƙamemen falon Alhaji Mustaphan daya kasance girma ɗaya ne sashen nashi ɗana Hajiya Kubra. Wanda daga baya ne aka ƙara faɗaɗa sashen Alhajin tinda ada bai kai na Hajiya Kubran ba. Bayan sun zazzauna ne, Alhaji yace Bilal ya miƙo mashi lemo a cikin fridge. Lemon roba na 5alive Bilal ɗin ya ɗauko haɗi da cup, ya ɗora a bisa wani ɗan trey mai kyau da ƙyalƙyali. Saidai fa duk yasha jinin jikin shi, yanda ya kula da duk abunda yake yi hankali da idanun Al'ameen ɗin na akan shi, yana mashi wani irin kallo cike da tuhumomi kala kala. Bayan ya zuba mashi Lemon ne ya miƙa mashi, kujerar da Ya Ameen yake kai ya koma shima ya zauna, yana mai ɗan sadda kanshi ƙasa. Ya san halin mutumen nashi sarai da shegiyar zuciya ta tsiya, ga zafafa abu idan ya faru ko da kuwa ace ba da son ran mutum ba, saidai shi zai yi ƙoƙarin ganin yayi controlling ɗin kanshi koda kuwa ace shi Al'ameen ɗin ya hau, ta yanda zasu fahimci juna, kuma su fuskanci koma menene a tare. Gyaran murya Alhaji Mustaphan yayi cike da dattako, bayan ya kurɓi ruwan lemo da ya wadata da zallan lemon zaƙi. "Son Meyasa kayi haka? Me yasa ka taho ba tare da ka sanar dani ba? Takamaimai ma ina son sanin abunda ya sanya ka baro ƙasar ka taho ba tare da sanar damu ba" Ɗan guntun murmushi yayi iya leɓo, shi ba maganar da yake so ayi ba kenan. Shi ba abunda ya kawo shi ba kenan, beside ma yana ganin ya girma ya kawo ƙarfin da zai iya zartar ma da kanshi hukuncin abunda ya dace dashi, ba don ma iyaye na iyaye ba. Bai ce ƙala ba, sai ma duƙar da kanshi da yayi ya shiga wasa da hannun shi alamun ba maganar yake son ayi ba. Abun ka da ɗa da mahaifi, tuni Alhaji mustaphan ya gane abunda yaron nashi ke nufi, tun yana yaro wannan itace alamun da yakan yi idan baya son maganar da akeyi mashi. Ɗan murmusawa yayi yana mai gyara zama, sai kuma ya saki gyaran murya yana mai ɗan kai kallon shi kan Bilal ɗin alamun za'a shiga daga fa! "Al'ameen ya zuwa yanzu dai na san ka fahimci me yake faruwa a cikin gidan nan, tinda Allah ya kawo ka, Bilal yaƙi sanar da kai ne a bisa umurnina, nima kuma nayi hakan ne saboda rashin lafiyar taka da kake fama da ita, to saidai fa yanzu haka cikin binciken inda suka shiga muke, muna fatan zaka yi mana uzuri" Bai katse Alhajin nashi ba, har saida ya kai aya, sannan ya muskuta, yana mai cewa "Dad duk naji wannan, kuma na ga su to saidai nima ina da Alfarma guda ɗaya, wannan karon bada wasa nake ba, ba kuma zan koma nace na janye maganar ba, sannan inaso ayi dukkan abunda za'ayi cikin lokaci, sannan bana so a tsaya sauraren Mom, tinda dai nine mai yi, kuma nace zanyi ɗin." Alhajin ne yake kallon Al'ameen cikin matuƙar mamaki akan fuskar shi. Shima Bilal ɗin dukkanin idanun shi da hankalin shi na akan abokin nashi. Bai tsaya sauraren suba gabaki ɗaya, ya cigaba da cewa " Dad inaso in ƙara sanar da kai cewa inaso a nema man auren Suhan a karo na biyu, ba zan janye ba, ba kuma na faɗa bane wannan karon saboda tausayi ko wani abu ba, *Ina Son ta ina ƙaunar ta* nine zan zauna da ita, bana son Mom ta san abunda yake faruwa, saboda bana son ta rikita mana abun akaro na biyu" Gabaki ɗayan su su biyun, babu wanda gaban shi bai ruguje ya faɗi ba, ya ana mashi maganar ba'a gansu bama, shi yana maganar a nema mashi auren ta? To ina za'a nema mashi auren? Wajen wa za'aje a nema mashi? "Son ana maka maganar ba'a gansu ba fa, ba'a san inda suka shiga ba, amman ana kan binciken inda suke ɗin" "Dad naji dukkan bayanin ka, kuma nace na gamsu, saidai Dad kasan garin masoyi baya nisa. Ni na gano su, na gano inda suke kuma naje har inda suke, infact ma daga inda suke nake" Baki Alhaji Mustapha ya buɗe yana sauraren shi, sai bayan har daya kai aya ne Alhajin ya dunƙule hannu ya watsa mashi daƙuwa cikin ɗan mamaki haka, Shikau gogan sai ma sunnar da kanshi da yayi, yana mai sakin ɗan murmushi, duk da shima sai bayan daya faɗi kalmar sannan kunya ta kama shi. Saidai a fannin so, masalan ma shida yake sabon shiga a soyayyar yana ganin babu gaban wanda ba zai iya faɗa ba. Bilal wanda bai san lokacin daya buɗe baki ba, yana mai miƙewa tsaye, Al'ameen ɗinne yayi mashi wani kallo na ai sai ka zauna ko! Zama yayi cikin sanyin jiki da mutuwar jiki. Lallai soyayyar Abokin nashi ga Suhan ɗin daban take, kuma daga Allah ce, tausayin shi matuƙa ne ya kama shi, yana mai jin cewa wannan karon zai mara mashi baya akan komai har ya kai da samun abunda yake da muradi. Duk da shima ta ɓangare ɗaya na zuciyar shi, yana kwaɗaita mashi suhan ɗin, kyawawan halayyar ta, da tarbiyyar dake gareta sukan ƙara mashi ƙaimi wajen ganin ta zama mallakin shi. Saidai ba zai taɓa iya cin amanar abokin nashi ba, masalan ma yanzu da yaga ya tsunduma tsulundum a soyayyar ta, ya zama wajibn shi, tilas ɗinshi yaso abunda Aminin nashi keso. Shiru falon ya ɗauka kusan na minti biyar, kowa da abunda yake saƙawa. Sai cen Alhaji Mustaphan ya nisa yana mai cewa su tashi suje, yaji dukkanin bayan an Al'ameen ɗin kuma zai duba akan su, sannan zai shawarci Alhaji Auwalun akan komai, saboda baya yanke hukunci karon kanshi sai ya shawarci yayan nashi da kuma mahaifan shi. (Abunda masu kuɗin mu na yanzu basa yi kenan, suna ganin tinda Allah yayi masu nasibi ko luɗifi ba zasu iya bin kowa ba, su saidai a bisu, kuma basa jin zasu iya neman komai a wurin wani, bayan ba haka rayuwar take ba, gabaki ɗayanta ita rayuwa juyawa take, idan babu masu kuɗi babu talakawa, haka idan babu talakawan babu masu kuɗin, kowa na buƙatar kowa a sha'ani na rayuwar yau da kullum) Miƙewa sukayi gabaki ɗayan su suna mai ficewa zuwa sashen Al'ameen ɗin. Saidai fa babu mai cewa da kowa komai, har suka shiga sashen nasu. Ganin da Bilal ɗin yayi Al'ameen ya share shi ne, ya sanya shi jawo hannun shi, yana mai maido shi baya. "Kai don Ubanka laifin me na aikata maka haka ne da har kake mani wani shariya? Kasan irin wahalar da nasha wajen nemo maka budurwar taka? Ko kasan har America naje in sanar da kai gaskiya ba tare da sanin Dad ba, ganin kada in biye ma Dad ka cutu, Amman shine ka dawo kana ta wani basar dani. Pls kayi mani magana mana ko Naji sauƙi" Ɗan ɗaura mashi idanu yayi, ganin ya idashe maganar tashi cikin damuwa da take har cikin zuciyar shi. Ɗan zare hannun shi yayi yana mai wucewa, sai kuma ya dawo da baya ya dunƙule hannu ya kaima Bilal ɗin naushn wasa yana mai rungume shi yake faɗin "Komai ya wuce Friend, ai nace na gamsu da dukkanin bayanan da Dad yayi ne, dama don inga yanda zaka yi ne don Ubanka" ya faɗa cikin yalwatacciyar fara'a da yake jinshi saƙat tinda ya samu Dad ya faɗa mashi damuwar shi da dukkanin buƙatar shi. Shima Bilal ɗin rungume shi yayi yana mai faɗin "kaji shegen bisa, ashe dama hawan ruwana ne kake so ya tashi, to kada dai ka karya ma Ummi ni, saboda kasan fa na kusa zama Dad" Da mamaki Al'ameen ɗin ke kallon shi, lokaci guda yana mai ɗan zare jikin shi daga Bilal ɗin, sai kuma ya sake rungume shi yana mai faɗin "Kace mun kusa zama Dads, ƙilama kafin lokacin na angwance" Da dukkanin farin ciki Bilal ɗin ya sanya hannu yana mai zagayo Aminin nashi zuwa gareshi sosai, yana mai jin daɗin shiryawar tasu, farin ciki fal a zukatan abokan biyu, kuma aminan da suka taso tun ƙuruciya babu mai jin kansu....... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~41~* *Hahaha Lol, kaji wai ƴan Team Ya Ameen har sun haɗa masu suna wai _Suhameen_ kaji fa ko daɗi babu, to mu ƴan Team Sir Saleem mu kuma munce _Suhaleem_ don Allah Fans wanne yafi daɗi nan ciki?* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Da misalin ƙarfe uku na yamma saƙon shiga yajin aiki ya iske ɗaukacin ɗaliban makarantar, kuma ana umurtar ɗalibai da su tattara su tafi gida har sai an buƙaci ganin su. Hakan baiyi mana daɗi ba, domin duk wani ɗalibai mai kwazo da son karatu baya fatan abunda ka tsaida mashi karatun nashi. Hakan ce ta sanya mu fara tattara komatsan mu. Kiran Sir Salim ne ya shigo wayata yana sanar dani in maza in shirya zai ajiye ni sannan ya wuce. Ko awa ban ɗauka ba, na shirya komai nawa, sallama mukayi dasu Raihana wanda har gaban mota suka rakani, sannan suka juya suma domin idasa shirin barin makarantar. Cikin ƴar walwala na gaida shi, ya kuwa tsare ni da idanu, domin shi a ganin shi har ya zuwa yanzu walwala ta bata koma yanda take ba ada. "Lafiya Lau Jaan, sai kuka ji an shiga strike ko?" "uhmm, Sir, ai mu hakan baiyi mana daɗi ba, masalan mu da muke ƙoƙarin cenza aji" "To ya za'ayi ai sai haƙuri, gwamnatin ce bata da cika alƙawari, muma ba da son ranmu hakan ke faruwa ba, saidai fatan Allah ya kyauta kawai, ƙasar ce gabaki ɗaya sai yanda Allah yayi kawai" Ya faɗa cikin ɗan murmushi da kan ƙara ƙawata fuskar shi. Sir Salim mutum ne da yake da kyawon hulɗa da jama'a, Sam bashi da tsanani irin na sauran maza, hakan ce ta sanya yake lallaɓa ni kaman kwai, ko yanzu da muke tafiya shine yake ta bani labari, wasu inyi dariya, wasu inyi murmushi. Mune bamu isa ƙauyen namu ba, sai wajen ƙarfe takwas na dare, wai a hakan ma domin lafiyayayar mota ce muke ciki. Umma ta tayi matuƙar mamakin ganina a daidai wannan lokacin, shaida mata nayi tare muke da Malam Salim, miƙewa tayi ta shige ɗaki, haɗi da sanya hijab ɗinta sannan tace ince ya shigo, dama Hajjo batanan ta tafi gidan su da akayi masu rashi, bata dawo ba har yanzu. Har cikin gida ya shiga, zama yayi bisa tabarmar da umma ta shinfiɗa mashi gefe, cikin girmamawa yake gaida Umman tawa, hakan na ƙara sanya ni jin daɗi, ko ba komai na san Allah ya haɗa ni da wanda ko nan gaba ba zanyi wani kuka ba a rayuwa. Bayan sun gama gaisa wa ne ya miƙe haɗi da fita waje, saboda har yanzu ummata bata wani sakin jiki da Sir, Salim ɗin, ina jin Kunyar sarakuta ce take nuna mashi. But ya buɗe, haɗi da ciro kayan masarufi masu yawa, shiga dasu cikin gidan ya fara yi da kanshi, ina taya shi da abunda zan iya ɗauka. Hatta da ruwa masu yawa ya kawo mana nasha, ummata kuwa sai godiya da shi albarka take zuba mashi, domin dai ya riga ya kawo ba zata ce bazata amsa ba. Ko bayan da na raka shi, kuɗi masu yawa ya kawo ya bani, a cewar shi, zaiyi ke wata kuma idan an koma zai zo da kanshi ya ɗauke ni. Ƙin amsa nayi, ina mai cewa "haba abun ai sai yayi yawa" Saida ya nuna mani tsananin ɓacin ranshi sannan na amsa ina mai ƙara mashi godiya. Akan idanuna yaja motar tashi yabar ƙofar gidan namu. Nima da kallo na kuma bin gidan namu, rayuwa kenan, wai ace ni da nake zaune a wannan kangon har Sir Salim ya ganni kuma ya amince da aure na a haka ba tare da yayi dubi da tsananin talaucin mu ba, har mahaifiyar shi tana iya kwana a wannan ruɓaɓɓen gidan da katangar ban ɗaki ce kawai ta ƙasa, sauran duk danni ne, domin kuwa ko ɗakin da muke kwana na bukka ne. Babu Abunda zance da Sir Salim saidai godiya, ya so ni haƙiƙa, ya nuna mani ƙauna, kuma sun mana halarci daga shi har mahaifiyar shi, ko da zai tafi saida yana yin fuskar shi ya cenza, lallai na yadda da ƙaunar da Sir Salim ɗin ke nuna mani. A zahirin gaskiya nima na yadda da auren nashi ɗari bisa ɗari, saidai fatan Allah ya bamu zaman lafiya. Ko dana ba ummata kuɗin, faɗa ta hau yi kaman zata burgeni, wai "bana da tunani, abun ai yayi yawa, tinda ba siyenki zasuyi ba, ko kwanaki da Ammin shi tazo ai baki ga iyayen abun alkhairin da tayi mana ba, kar in sake inga kin kuma karɓar wani abu daga hannun shi in ba haka ba sai na saɓa maki wallahi" Nidai da kallo nake binta, yanda ta fututtuke tana faɗa, kai kace roƙonshi nayi, to abun bai ma dameni ba, saboda na san halin kayata, dole in lallaɓa ta in samu mu rabu lafiya tinda abu ya kusa saura ƙiris ya rage. Hajjoma da ta shigo ta tadda kaya tuli tsakar gida, saida ta girgiza, to koda ummata ta nuna mata kuɗin itama faɗa ta hau yi, a cewarta itama gaskiya abar amsar abun hannun su, har sai ran da Allah yasa aka mallaka masu ni. Hajjo mutuniyar kirki ce, Sam bata da baƙin hali, lafiya ƙlau suke zaune da ummata kaman wasu ƴan uwa, to shima malam ɗin haka yake, ko ba komai zuwan namu ya ɗan sama masu waraka daga cikin halin da suke ciki, sune yanzu harda cin shinkafa ƴar gwamnati da shan ruwan roba? Ai sai Sam barka wallahi. A haka muka kwana firar makaranta da ummata, tana daɗa jan hankalina akan in maida hankali akan Abunda ya kai ni, banda kula ƙawaye barkatai ko samarin makaranta. Ce mata nayi wace ni? Yanda duk makaranta ta ɗauka akan cewa ni Budurwar Sir Salim ce, kuma ni ce wadda zai aura, ai su kansu ma samarin shakka ta suke yi, domin Sir Salim ɗin a makarantar Malami ne daya san Abunda yakeyi, Sam bashi da kula ƴan mata duk kuwa da barkwancin shi, samarin ma baya sake masu sai ƴan kaɗan gudun raini irin na ɗilibai. ***************************** Basu tsaya neman abunda zasu ci ba a cikin gidan, a tare da Bilal ɗin suka fita zuwa nashi gidan, saidai duk yadda ummi ta kai da son Al'ameen yaci abincin nata, saidai ya yabuɗa, shi kau Bilal sakin jiki yayi ya kwashi girkin matar tashi, sannan suka sake fita zuwa kamfanonin su domin su duba ayyuka, duk da an tashi aiki kuwa. Hajiya Kubra bata bi ta kan Alhaji Mustapha da yake ƙasar ba, ta sanya kai tayi ficewar ta wajen harkokin ta, su 3hajiyas ne ma suka zo suka ɗauke ta har gida. Akan idon shi suka fita, hakan ce ta sanya shi shima shiryawa ya fita zuwa wajen Alhaji Auwalu domin su tattauna akan batun Al'ameen ɗin. To koda ya same shi akan batun, bai hana ba, domin dukkanin Abunda ke faruwa Hajiya Zainab ta faɗa mashi, hatta da halin yarinyar da nagartar mahaifiyar yarinyar, basu da matsala akan tarbiyyar yarinyar, domin haka ne ya sanya suka yanke shawarar nema ma Al'ameen ɗin ita yarinyar, alabasshi asalin nata a hankali zasu nemo shi. Kiran Al'ameen ɗin sukayi da misalin ƙarfe takwas na dare, lokacin suna tare da Bilal a hanyar su na komawa gidan Bilal ɗin domin ya sauke shi. Karkata kan motar yayi zuwa gidan Alhaji Auwalun, a tare suka shiga da Bilal ɗin har cikin gidan. Hajiya Zainab suka tadda zaune a falo tana kallo, gaida ta suka shiga yi cikin girmamawa, itama amsawa takeyi cikin sakin fuska tana tambayar Bilal iyali, tana tambayar Al'ameen ƙarfin jiki. Bayan sun amsa mata ne, ya sanya ta cewa su shiga Falon Alhajin suna ciki. Sallama sukayi, suka koma gefe cen ƙasa suka zauna, Al'ameen harda duƙar da kai ƙasa, suka shiga gaida iyayen nasu. Alhaji Auwalu ne yayi gyaran murya "Al'ameen mahaifin ka yazo ya same ni akan wani batu, alal haƙiƙa naji daɗin jin wannan zance daga gareka, kuma ko ba komai muna alfahari da kai ta wannan fannin, kaf zuri'ar mu babu yaro mai tunanin manya da hangen nesan ka, saboda haka mun yanke shawarar gobe idan Allah ya kai mu, zamuje da kai ka nuna mana inda ita mahaifiyar yarinyar take, sannan magana ta biyu, kaman yanda kace baka so mahaifiyar ka taji, to ba zamu taɓa bari taji ba, sannan muna so, duk Abunda Kaga mun aiwatar ka sanya mana ido, kaidai yarinya kake so a aura maka, kuma insha Allahu zamuyi dukkan iya ƙoƙarin mu, muga ka same ta kaman yanda ka buƙata. Allah yayi maku Albarka ya sanya kufi haka, ya baku ikon taimakon na ƙasa daku a ko'ina kuke a rayuwa" Haƙiƙa ba Al'ameen ba, har Bilal yaji daɗin wannan maganar ta wan mahaifin shi, yana matuƙar Alfahari da iyayen nashi a ko'ina yake, su ɗin masu son su ne, masu girmama ra'ayi da muradin su ne, dama ko ba komai ya san Alhaji Auwalun da mahaifin nashi ba zai taɓa samun matsala dasu ba, ga dai wadda za'a sha dabi da ita cen duk ranar da taji, saidai koma minene ya shirya ma hakan, ya shirya ɗaukar dukkan wani ƙalubale da tarnaƙi da kan iya tasowa anan gaba. Muryar Mahaifin nashi ya tsinkaya yana tambayar shi ko da akwai wani abu kuma? Girgiza mashi kai ya shiga yi, yana mai godiya da sanya ma mahaifn nashi albarka, shima Bilal ta ɓangaren shi, daɗi yake ji, ko ba komai yanzu ne zai shawo kan abokin nashi tin bayan shigar shi soyayyar. Umurtar su sukayi da su tashi su tafi zuwa goben zasu wuce. A mota ne Al'ameen ɗin ke cema Bilal ya shirya lallai fa dashi za'ayi wannan tafiyar, gyaɗa mashi kai yayi yana mai cewa "Allah ya kaimu" Har yanzu mamakin Al'ameen ɗin yakeyi, kai idan ada akace maka Al'ameen zai faɗa soyayya irin haka zaka ƙaryata, mutumen da ƴan matan da suka kawo mashi ƙoƙon barar su, ƴaƴan masu kuɗi, ga kyau ga ilimin boko, Amman shi duk basu yi mashi ba, Suhan ita yagani tayi daidai da muradn shi, to dama haka duniyar take, duk inda tausayi yake to fa akwai soyayya a tsakani, dama shi jin abokin nashi kawai yakeyi, Amman tabbas ya san wannan lokacin ya a zuwa. Kuma ko ba komai dai Suhan ta cencenci a sota, ta cencenci zama uwar ƴaƴayen ka, yarinya ce mai tarbiyya da biyayya da girmama na gaba da ita, duk wani namiji wanda ya san abunda yakeyi zaiyi fatan ace Suhan ɗin ta zamo uwa ga ƴaƴayen shi. Har ƙofar gida ya sauke shi, yana mai kaɗa kan motar shi zuwa nasu gidan. Mama Talatu da maree an sha barbaɗe barbaɗe a cikin girki, an jera ma Al'ameen a dinin table ɗinshi, wanda hajiya kubra ce ta sanya su yin hakan a cewar ta idan ya dawo ba sai ya nema ba, saidai da ta san Abunda zasu barbaɗa ma yaron nata, to da ko kusa bata fara barin maree na shiga sashen Al'ameen ɗin ba idan baya nan. Saidai kallo ɗaya yayi ma abincin yaji zuciyar shi na matuƙar tashi, duk kuwa da irin kyawon abincin da na momin da suke cikin miyar.Iro mai ba fulawowi ruwa ya kira a waya, yace yazo ya kwashe abincin suje suci idan suna so. Da gudun shi ya taho ɗakin na Al'ameen domin ya san cimar da za'a shirya ma uban ɗakin nasu daban ce da wadda za'a basu, balle yanzu da mama talatun take ƙwange wajen bada kayan abincin masu girkin. Duk da harda ita za'a ci Amman ta kwammace suci ba daɗi tana tara sauran a ɗakin ta, in sun taru taba maree a sace taje cen wasu ƙauyakun ta siyar a banza. Cemashi yayi idan sun cinye su bar warmers ɗin a wurin su, godiya ya shiga zubawa yana mai ɗauka ya fice. Saboda mugun abu irin na mutanen yanzu, shi kaɗai yaje ya ɓoye yaci abincin shi yayi ƙat, harda halshe yake sanyawa yana lashe warmer ɗin, dama Al'ameen ya san irin ƙazantar Iro, hakan ce ta sanya shi cewa yabar su a wajen shi. ********************** Washe gari zamu iya cewa Al'ameen ɗin ya riga kowa tashi, bayan ya gama sallolin shine ya koma ya ɗan kwanta, tuni bacci mai nauyi ya sure shi, zamu iya cewa bai samu baccin kirki ba, daya kulle idanun shi, Suhan ɗin kawai yake hangowa zaune da saurayi suna fira, har tana dariya, abun ya matuƙar tsaya mashi a rai, sai kuma maganganun umma da suke yi mashi amsa kuwwa a kunne, wai wannan da ya gansu tare shine saurayin ta, wanda har an nema mashi auren ta, kuma umman ta bashi. Sai ya tashi zaune ya jawo fulo ya matse shi kaman zai yaga shi, sai kuma ya koma ya kwanta yana mai sakin ɗan guntun tsoki. Mamakin kanshi yakeyi, wai ashe haka soyayya take. Ashe haka kowa keji? Tin farkon asalin asali me ya sanya shi janye maganar tashi saboda wani hargagi na Mom ɗin tashi? Ai gashinan wankin hula na neman kaishi dare. A haka dai ya kwana har aka kira sallar Asubahi. Wajen ƙarfe takwas na safe ya fito cikin shirin shi na manyan kaya, fara ƙal ɗin shadda ce gizna sai tashin ƙamshi da walwali takeyi, anyi mata ɗinkin doguwar riga kusan har ƙasa, tasha aiki Golden a jikin ta, takalmin ƙafar shi ma golden ne haɗe da hular dake bisa kanshi. Yayi masifar kyau, idan ka hango shi daga nesa zaka iya cewa ango ne, harabar gidan ya fito riƙe da waya da ɗan ma ƙullin sashen nashi da ya kulle, domin ya kula ana shigar mashi ɗaki idan baya nan, hakan ce ta sanya tin jiya ya aika aka amso mashi makullan ɗakin wajen mama talatun. Bilal yake ta faman kira yana sakin ɗan guntun tsaki a fili saboda rashin ɗaukar wayar tashi da baiyi ba. Gate yaga an buɗe sai ga motar Bilal ɗin ta danno kai a guje cikin gidan. Bayan yayi parking ne ya fito shima sanye da shadda ruwan Army Green sai ɗaukar idanu yakeyi Da ɗan sauri ya ƙara so wajen da Al'ameen ɗin ke tsaye yana faɗin "Ran ango ya daɗe" Ya faɗa yana mashi alamar jinjina haka cikin wasa. Ɗan tamke fuska Al'ameen yayi, yana mashi alamun to ya tona masu asiri, ɗan waiwayawa Bilal ɗin yayi bayan su, yaga babu mai kallon su, sai kuma ya saki dariya mai sauti yana faɗin "Shegen gora, wannan kyau haka kaman yau ne ɗaurin auren?" Sai a lokacin ya saki ɗan murmushi yana faɗin "bana cike da iskancin ka Friend, bakaji yanda gabana ke ta faman faɗuwa ba, gashi ina ta kiran ka baka ɗaga ba" "Ai ina ganin kiran, to na riga na kusa ƙarasowa shine nace bari kawai in bari in iso, sai inji menene?" Sashen Alhaji Mustapha suka ranka ya, sun tadda ya shirya cikin shadda skyblue mai babbar riga, shima yayi kyau ainun, dama Alhaji Mustapha ba dai kyau ba. A tare suka fito, mudi suka sanya ya fiddo masu wata mota mai ƙirar jeep da tun jiya Al'ameen ɗin ya sanya shi wanke ta. Bilal ne ya shiga mazaunin driver sai Al'ameen a gefen shi, yayin da Alhaji Mustapha ya shiga baya, suka nufi gidan Alhaji Auwalun. Shima sun tadda ya shirya, ba ɓata lokaci suka ɗauki hanya, yayin da Alhaji Mustaphan da yayan nashi suke ta firar su daga cen baya, shi kuma gogan naka ya luluƙa duniyar tunani. ************************** Nasha baccin ƙalula yau, ba tashi da wuri tinda ba'a makaranta nake ba balle ince lecture, kafin in tashi Hajjo da ummata sun gama komai, yau tea muka sha da bredi harda wainar kwai, bayan na gama karyawa ne na fita na share tsakar gida, haɗi da gyara ɗakin namu. Ruwa Hajjo zata je ɗebowa, hakan ce ta sanya ni ce mata ta bari idan na kammala komai nayi wanka zanje in ɗebo mana, tinda na aikin gida ne, kuma naga da ɗan saura. Sai kuma muka zauna muna ƴar fira haka da hajjon, ummata na sanya mana baki jefi jefi, sai kuma ta miƙe haɗi da yin wanka, a tare muka fita da ita wajejen azahar zata je gidan ƴan uwan hajjon yi masu gaisuwa da yake an yi masu rashi kwanaki, shine zata koma yi masu gaisuwa, hajjon ce ta zauna gida haɗi da ɗora girki. Muna tafe muna ƴar firar mu, har zuwa inda zamu rabu da umman tawa. Ko da na isa rafin, na ɗebo ruwa kwatsam ina cikin tafiya, sai na kula kaman ana bina, na ɗan waiwaya sai naga wasu samari su uku, ƙara sauri nayi, sai kuma Naji ana ta faman tsayar dani. Ware ƙafa nayi zan taka da gudu naga sun sha gabana "Haba ƴan mata, ya ana ta maki magana kina wani share mutane kaman baki ji ba? Daga zamu taimaka maki? Tinda mun kula kinyi kwantai da sunan kin tafi wai karatu binni, Amman wa ya san abunda kike aikatawa acen ɗin?" "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Shi nake ta maimaitawa, domin dai ga dukkan alamu waɗannan ba mutanen arziƙi bane ba, gashi wurin ni kaɗai ce, ga dukkan alamu wulaƙanci suke neman yi mani, gashi su uku ni ɗaya. Tulun dake bisa kaina na saki, haɗi da tattare zani zan sake kwasawa a guje naji ɗaya daga ciki yaja mani hijab ta baya. "Malam Lafiya? Wai minene haka ne? In na saurare ku me zance maku?" Na faɗa ina mai tattare dukkanin dauriya da ƙwarin guiwa ta. Dariya suka sheƙe da ita, suna mai faɗin "Tin kwanaki muka ganki a ƙauyen nan kuma muka ji muna sonki, mun bincika sai muka gane ashe ke ƴar wannan matar ce mai nuna ita ta Allah ce, sai kuma gashi ta tura ki bunni neman kuɗi da sunan karatu, muna so dai ki bamu haɗin kai, babu wanda yaji ba wanda ya gani, kinga cen bayan bishiyar cen? Nan zamu ɗan kewaya, mintina ne ƙalilan mun gama, zamu kula dake a ƙauyen nan, duk wani mai neman shiga hurumin ki zamu kare ki" "Innalillahi wa 'inna ilahi raji' un, la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Abunda nake maimaitawa kenan, ai tuni hawaye suka shiga zarya akan fuska ta. "Kuyi haƙuri, ku dubi girman Allah, wallahi ni ba ƴar iska bace ba, wallahi karatu nakeyi a bunni ba iskanci ba, wallahi ban iya ba, kuyi haƙuri don Allah, kada ku keta mani daraja ta" Na faɗa cikin kuka riris, gashi sun cukuikuye mani hijab ɗita, sai faman kokowa nakeyi da guda ɗaya daga cikin su da yake neman kaini ƙasa. Kokowa sosai ta ɓarke tsakanin mu dasu, maza ne su ba mata ba, har dai saida sukayi nasarar yada ni ƙasa cikin yashin da yake shinfiɗa ta gefen rafin. **************************** Baisha wahalar gane gidan ba, sai gasu har ƙofar gidan, su duka babu wanda baiyi mamakin har ta yaya akayi Al'ameen ya iya shigowa nan ba, neman su Suhan ɗin, har kuma ya same su anan ɗin. To su ta yaya ma tunanin su zai iya basu akwai wani ƙauye nan ciki haka da har mutane ke rayuwa a ciki? Sallama suka sanya akayo masu a cikin gidan, bayan sun firfito. Shi dai Al'ameen bai san dalilin faɗuwar gaban shi ba, shi kau Bilal sai ƙarema gidan kallo yakeyi yana mai ɗan murmusawa shi kaɗai yana tunanin ƙarfin hali irin na Aminin nashi da har ya iya gano wannan wurin. Yaron ne ya dawo yace "wai ance ana zuwa" Alhaji Mustapha ne ya zaro ƴan dubu dubu guda uku ya ba yaron yana faɗin "an gode maza gida kaji kaje ka kaima maman ka" Cikin su babu wanda yayi mamakin kyautar, saboda sunsan ya saba da irin haka, taimakon marasa shi, shi kau yaron ganin kuɗi masu yawa duk da ba sanin su yayi ba sosai, sai ya ruga da gudun tsiya zuwa gida yana ta murna. Hajjo ce ta sanya Hijabinta ta leƙo wajen, ganin ƙatuwar mota da manyan mutane tsaye ya sanya idasa fitowa tana gaida su. Cikin sakin fuska Alhaji Auwalun ya Amsa yana faɗin "Mu baƙi ne, wajen Maryama muka zo, mune waɗanda ta zauna a gurin mu shekaru da daɗewa" Sakin fuska sosai hajjon tayi tana masu maraba, sai kuma ta juya zuwa cikin gidan tana mai cewa su shigo. Da yake rana ta kawo sasai, ɗakin umman ta buɗe tayi masu shinfiɗa ciki, tana mai cewa Aiko gashi Umman taje unguwa, Amman bari ta je ta kira masu ita. Da to suka bita, cikin su babu wanda baiyi mamakin inda muke rayuwa ba a yanzu, masalan ma Bilal da Alhaji Mustapha, jinjina dalilin da ya sanya suka zaɓi suyi wannan rayuwar suke yi a cikin zuciyar su. Al'ameen ne yake shaida ma mahaifn nashi cewa zasu koma mota su zauna, basu hana su ba, tinda sunsan a takure suke wajen ga kuma tsananin zafi da ake fama dashi. Fitowa sukayi, saidai basu shiga motar ba, Al'ameen ke cewa Bilal yazo ya raka shi su zagaya garin suga yanda yake. Bilal yasha tuƙi ya gaji, ga zafi yanaji, cema Al'ameen ɗin yayi ya tafi shi dai ya gaji dayawa, yana nan cikin mota yana jiran shi. Ba tare da ya kuma cewa ƙala ba ya juya ya tafi, shi mutum ne da bai san yanda ake magiya ba, hakan ce ta sanya shi ƙyale abokin nashi, ko ba komai yayi mashi uziri, zafin ranar da akeyi kaman ana tafasa ƙwaƙwalwa. Hannun shi soke cikin aljihun wandon shi yake ratsa ƙauyen, yana ta ƴan kalle kalle, har zuwa ƙasan wasu bishiyoyi da sukayi ma wani wuri ƙawanya, baya kyautata zaton babu ruwa a wurin, hakan ce ta sanya shi taka wa a hankali ya doshi wurin. A zabure na miƙe, ina mai sake sakin wata razananniyar ƙara da saida wurin gabaki ɗaya ya amsa kuwwa ta. Kuka nakeyi ina roƙon su, kaman ma ba da mutane nake magana ba, jana suke yi a ƙoƙarin su na kaini bayan bishiyar da suka nuna mani ɗazu. Cikin sauri ya shiga taka wa har yana ssssarfa, wurin da yake jin ƙarar na fitowa yake nufa, idan ba kunnuwan shi bane keyi mashi gizo ba, sautin muryar mace ne yake ji yana fitowa, ihu takeyi, tana naiman taimako. Sai ga Al'ameen yana ɗan gudu kaɗan haka, kaman mai four-fourty haka. Tin daga nesa ya hange su, maza ne zarata har uku, suka rufa akan yarinya ƙwaya ɗaya tallin tal, janta suke ko ina zasu kai ta? Tin daga nesa yake daka masu tsawa cikin wata irin murya da bansan yana da ita ba. "Kai kai ku tsaya, ina zaku kai ta? Me zakuyi mata?" Ya faɗa yana mai ƙarasawa inda suke tsaye, Nidai hijab da ɗan kwali sun rufe mani fuska, ihu kawi nakeyi ina "Ku sake ni ku ƙyale ni, ni ba ƴar iska baceba, kada ku keta mani haddi don Allah" Tausayin ta ne matuƙa ya kama shi, bai san lokacin da ya kai hannu ba bisa jikin ta, haɗi da fizgota daga hannun su ya maida ta bayan shi, yana mai fuskantar su. Nikau tinda Naji na tsira daga hannun su, sai na sanya hannu haɗi da ƙwaƙume shi matau, kaman zai tafi ya barni a wurin. "Kai malam, ƙanwar mu ce fa, kai ina ruwan ka ne?" suka faɗa cikin zaro idanu da matse baki cikin magana irin ta ƙauraye Daga bayan nashi nake faɗin "Ƙarya suke yi ni ba ƙanwar su baceba, wai sai na basu haɗin kai, na faɗa masu ni ba ƴar iska bace, Allah ne ya kawo mani kai da bansan halin da zasu jefa ni ba" na faɗa ina mai sake ƙwaƙume shi daga baya cikin wani irin tsumammen kuka. Bai shaida murya ta ba, saboda wani irin ɓacin rai da yake ciki, idanun shi sun kaɗa sunyi jajawur "Malam Kaga ka miƙo mana ita nan, gida zamu kai ta, guduwa tayi, ƙarya takeyi, kuma kai wanene da zaka zo ka katse mana hanzari?" "OK kuna son kusan ko ni wanene?" ya faɗa cike da ƙufuluwa Ganin yana ƙoƙarin zaro wani abu daga cikin aljihu ne ya sanya su ruga wa suna faɗin "zamu haɗu nan gaba ne ai" Daƙyar ya sanya hannu ya jawo ni daga bayan shi, wanda na rirriƙe shi gam kaman zasu sake ƙwace ni, kuka kawai nakeyi da hamdala da Allah ya kawo mani mai ceto na. Gaban shi ya maido ni, yana mai sanya hannu ya yaye hijab ɗin da duk ta cukuikuyeni da ɗan kwalin nawa. A firgice ya ja baya, ganin ko wacece, sai kuma ya sake kulle idon shi ya buɗe ya azasu a bisa kaina. Nikau kunya da ɗacin rai suka sanya ni durƙushewa a wurin ina mai sakin wani sabon tsumammen kukan. Jin kukan yakeyi har cikin zuciyar shi, tarin tambayoyi ne kawai a cikin ranshi, Suhan ɗin da take cen makaranta me ya kawo ta nan kuma? Menene haɗin ta da waɗancen ƴan iskan? Yana tsaye ya tsura mani idanu, sosai kukan nawa yake ratsa mashi zuciya, baya son kukan mace, macen ma wai Suhan. A hankali ya duƙa haɗi da ɗagoni da dukkanin hannuwan shi, baya jin idan zai iya komawa da ita gidan haka gaban iyayen nashi. Jana ya shiga yi har bakin wata bishiya da take ɗauke da wani ƙaton dutsi mai faɗi a jikin ta. Zaunar dani yayi, sannan shima ya koma ya zauna a gefena. Har yanzu bai ce mani ƙala ba, nima kuma na rage sautin kukan nawa sai shessheka da nake ta faman yi, da sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali. Shiru yayi yana mai nazartar yana yin ta, har yanzu idanun shi jajur suke. Wani bala'i kishin ta da ƙaunar tane ke taso mashi a cikin rai, wannan ne karo na farko da zai iya aikata wani abu daya san ya saɓa ma addinin nashi, saidai bayada yanda zaiyi. Hannu ya sanya yana mai ɗan rungumoni zuwa jikin shi ya shiga bubbuga mani baya cikin sigar lallashi, idanun nashi har wani ruwan hawaye suke tarawa saboda tsananin ɓacin rai. "Me ya kawo ki nan? Bayan kinsan akwai ƴan iska a wurin nan? Ya jefo mani tambaya cikin salon maganar shi, da kansa inji jinin jikina ya katse ya fara gudu. A sanyaye cikin dusasshiyar muryar da kuka ya gama cinyewa nace " Ruwa nazo ɗiba yaya" "Dole sai ke kaɗai ce zaki zo ɗibar ruwan anan wurin da yake ihunka banza? Shiru nayi mashi, domin na kula ranshi a matuƙar ɓace yake. Saidai koma minene ni na gode ma Allah daya kawo mani shi a daidai wannan lokacin. Ɗankwalina ya miƙa mani domin in rufe kaina, gashina duk ya warwatse dama gashi ba kitso a kaina, da kallo ya shiga bina ganin yanda na sanya hannu na tattare gashin duk uban yawan shi da tsawon shi na duƙunƙune shi na cusa cikin ɗan kwalin, ina mai gyara zaman hijab ɗin bisa kaina. Har yanzu hawaye sun kasa tsayawa a idanuna. "Yaushe kuka zo yaya?" Na furta cen ciki, har ina kyautata zaton ma bai ji ba. Sai kuma naji ya amsa mani da cewa "Yanzun nan, tare muke da su Alhaji da Bilal, Mun tarar umman bata nan sai kuma na shigo zaga gari, ashe ma kin dawo daga makarantar" Dukkanin maganar da yajeyi har yanzu akwai tsananin ɓacin rai a tare dashi, fuskar nan da take fara ta kaɗa tayi ja sosai. Duk da yanda nake gani a fuska ta, kaman ya ƙara kyau, sumar nan tashi ta kwanta luf a saman kanshi, ga fatar shi da ta ƙara murjewa kaman ka taɓa jini ya zuba, farar shaddar dake jikin shi ta ƙara fito da ainahin kyawon shi na asali. Ya Ameen yana da kwarjini da haiba, hakan ce ta sanya ni kasa haɗa ido dashi, cikin sadda kai na shiga cewa "Zanje na gaida su Dad ɗin" Da sauri ya kalle ni yana mai nuna ni da yatsa "A hakan? Ko baki san yanda kike ba? Kalli idanun ki fa" Ya faɗa cikin wata irin murya dake ƙara sanyawa jikina sanyi matuƙa. Miƙewa yayi yana faɗin "Muje ki wanke fuskar ki sana" Jerawa mukayi har bakin rafin, ta inda tuluna ya fashe muka bi, ina kallon shi yana kallon tulun, saidai bai ce mani ƙala ba, dama na san ba zai tanka ba, yau ma sa'a naci kuma na san harda tausayi na, daya lulluɓe shi. Shi ya zuƙunna ya sanya hannuwan shi duka biyun yana mai ɗebo mani ruwan rafin ina ɗauraye fuskar tawa. Har na gama sannan muka miƙe gabaki ɗaya, ya sanya hannu a aljihu ya fiddo hancarchip fari ƙar ya miƙo mani wai in goge fuska ta. Ba gaddama, na amsa ina mai kai hancarchip ɗin fuska ta, saida naja dogon ajiyar zuciya, yanda ƙamshin turaren shi ɗan asali ya bugi hanci na. Ban san lokacin da na duƙunƙune shi ba a fuska ta, in mai sake sakin wani kukan, tunowa da Abunda akayi shirin yiman yau a rayuwa ta, ni Suhan da nake daf da aure. In ce ma Sir Saleem me? Idan duka duniya kunnuwa ne a jikin shi zai taɓa yadda dani? Me yasa wasu mazan basa da adalci ne a rayuwa? Kayi ma mace fyaɗe ko ƙanƙanuwar yarinya kaji daɗin me? (Matsalar da muke fuskanta kenan a Rayuwar mu ta yanzu, fyaɗe cin zarafi mata, keta ma mata haddi, luwaɗi da yara maza ƙanana, ya zama ruwan dare a faɗin duniyar nan, ko saboda haka Allah ya isa ya kama mu, wallahi mu tuba mu daina, mu koma ma Allah subhanahu wa ta'ala, zamu ci riba a rayuwar mu, zamu rabauta) Matsowa ya shiga yi a hankali ya sanya dukkanin hannuwan shi yana mai sauke man hannuwana daga saman fuska ta, ya san da ciwo, ya san ba daɗi, ko shi ya shaideta akan ita ɗin yarinya ce nutsattsa ko sutura banza matsattsa bata Sanyawa, yabar hakan a muƙaddari ne, da kuma gurɓacewar matasan yanzu a rayuwa. Kaina ya aza bisa kafaɗar shi yana mai jijjigawa a hankali kaman wata baby. Ban san lokacin da na kai hannu na idasa rungume shi ba ina mai sakin wani tsumammen kuka, ya Ameen ɗin Yayana ne, tin da na taso a rayuwa ta nake ganin shi, kallon Yayana nakeyi mashi, shi ɗin daban yake a cikin maza, in wani ne ba zai taɓa fahimta ta ba. Lallashi na ya shiga yi cikin shigar tausayawa yana mai ƙarfafa mani guiwa da umurtata akan in bar maganar anan wurin da gani sai shi sai Allah daya halicce mu, sannan in kiyaye koda nan gaba, tinda na kula akwai ɓata gari a ƙauyen. Shi ya shiga jan hannuna, kaman makaho da ɗan jagora. Saida mukayi nisa ne sannan ya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo ya kalle ni sosai "Ki daidaita Kanki Suhaaan, bana so kowa ya fahimci komai, akwai maganar da nakeso muyi kafin mu isa gidan" Dakatawa nayi nima ina mai gyara fuska ta, na goge wasu ƴan matasan hawaye da suke sake gangaro mani. Sannan nace "ina jinka yaya" Juyowa yayi sosai yana fuskanta ta, har saida Naji bugun da zuciya ta takeyi ya kuma lunkuwa, kwarjinin shi da cika idanun shi, su suka taru suka baibayeni. Hannuna ya cika yana mai yiman kallo na sosai, sannan ya buɗe baki a hankali yana mai cewa _*"ZAKI AURENI SUHAAN?"*_ a matuƙar firgice haɗi da bugawar zuciya lokaci guda na ɗago da dukkanin fuskanta, idanuna sun kwalalo kaman zasu faɗo ƙasa saboda tsabar firgici nake kallon shi. Gyaɗa man kai yayi, yana mai lumshe kyawawan idanun shi da suke cike da gashin idanu Zara-Zara alamar tabbacin abunda ya faɗa shi yake nufi. A hankali na sauke ƙwayar idanuna daga kanshi zuwa ƙasa ina mai........ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~43~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Haka muka kwana da umma, ba mai umm ba mai un-un Washe gari tin da safe naga sun tashi ita da hajjo suna ta ƴar hada-hada. Wajen ƙarfe sha biyu naga an fara fiddo kayan mu zuwa tsakar gida. Kaina fa ya kulle, da idanu kawai nake binsu, har malam yau yana nan bai fita ba. Jikin Hajjo da umman tawa yayi sanyi ƙlau, ɗan zaman da aka kuma yi ya sanya shaƙuwa mai tsanani tsakanin Umman tawa da hajjon. Saidai a cikin zuciyar ta, bata jin zata iya barin wannan damar ta kufce mata, bata jin zata iya ɗaga ƙafa a wannan karon. Zata ja, zata kara da koma wanene tinda yanzu akwai tsayayye a bayan ta, dama cen rashin galihu da rashin tsayayyen mai ƙarfi ne ya sanya ta ja baya, ya sanya ta yin shiru, kaman marar ƴanci. Sun duƙar da kai sunyi rayuwar ƙasƙanci, bayan tasan komai, zaman ta a gidan dama da biyu tayi shi, yanzu kuwa bata neman wata ƙarin hujja illa ta ɗaura ɗambar neman abunda yake halalin su. Azahar nayi naga wata irin hadadɗiyar mota tazo ƙofar gidan mu, sai kuma naji ana cewa mu fito. Haka muka kwashi ƴan kayan namu da ba wasu masu yawa ba, dreban da kanshi ya shigar mana but, sai kuma Umman tawa ta tsaya yima su Hajjo sallama, sun ɗan daɗe suna tattaunawa, sannan suka rakota bakin mota ita da malam suna mata Allah ya kiyaye hanya. Nima sallama nayi masu, ba tare da na kawo komai a raina ba, saidai ina tunanin inda zamuje kuma haka daganan. Tafiya mukayi miƙaƙƙa, saidai mu tsaya salla, abinci ma take away muka tsaya muka amsa. Hankalina bai tashi tashi ba saida naga mun shiga garin abujan cikin dare, sai kuma naga mun doshi gidan su Ya Ameen ɗin. Toh fa! Umman tawa da hankalin ta ta dawo damu cikin gidan nan? Bayan itace da kanta ta sanya mu barin shi da kanta? Horn driver ɗin yayi mai gadi yazo ya buɗe mana. A harabar gidan muka tadda Alhaji Mustapha da Ya Ameen suna zaune ga dukkan alama magana suke yi, Amman hankalin Alhaji Mustaphan gaba ɗaya yana kan ƙofar shigowar. Da mamaki Ya Ameen ya miƙe yana kallon mu, tare suka miƙe da Alhaji Mustaphan yayin da naga ya nufo mu fuskar tashi cike fal da farin ciki. Gaida Alhaji Mustaphan nayi, ya amsa cikin sakin fuska sosai, Abunda ke ƙara ma Alhajin Daraja kenan a idanun mu. Sai kuma ya shiga takowa a hankali cikin salon tafiyar shi mai cike da natsuwa. Yayi masifar kyau cikin hasken fitulun da suka haske ilahirin gidan tar kaman rana. Daidai inda muke tsaye yaja ya tsaya, sai kuma ya shiga gaida ummata cikin girmamawa, sautin muryar shi na futa a hankali cikin wani irin amo da ya ƙara rikita ni da birkita mani tunani na. Itama Umman tawa amsawa tayi, saidai wannan karon ba irin amsawar da nasan tana yi ma ya Ameen ba, Amsawa ce mai cike da dakiya irin ta ɗa da uwa. A'ah Me yake shirin faruwa ne wai? Bai ko kalli inda nake tsaye duƙe da kai ba, ya sanya kai ya wuce zuwa sashen nashi. Da idanu nake bin ilahirin gidan da ya wadatu da shukoki masu ban sha'awa. Gine ginen ma kusan zamu ce an cenza su, ko ina tsit kake ji ba ƙarar komai sai na kukan tsuntsaye masu daɗin sauraro. Alhajin ne ya kwala ma Mudi dreba kira, da gudun shi ya taso yana mai faɗin "ranka ya daɗe gani" Kayan mu da driver ɗinda ya kawo mu mai suna Mahi ya fiddo mana ya shiga nuna mashi da hannu yana mai cewa su kwaso kayan su shigo mana dasu. Maimakon inga mun nufi sashen masu aiki, sai naga mun nufi wani ɓangare mai kyau, wanda ada sashen Alhaji Mustaphan ne na sani a wurin. Da makullin da yake hannun shi yayi amfani ya buɗe sashen. "Masha Allah". Itace kalmar da na fara furtawa lokacin da na saka ƙafar tawa cikin tanƙamemen falon da ya wadata da kaya masu masifar kyau kalar royal blue da maroon. Umma ta na biye a bayana, itama ga dukkan alamu sashen nata ya matuƙar burge ta. Sai a lokacin na fara dawowa hayyacina. "wai ba dai ummata ce ta auri Alhaji Mustaphan ba" na faɗa a cikin zuciya ta ina mai kai zaune bisa wata luntsumememiyar kujera da ta wadatu da fuloli burjik kaman na gidan sarauta. Gaba na ne ya shiga faɗuwa, Alhaji Mustaphan ne ya shiga gaba, umman tawa tana biye dashi har ɗan corridor ɗin da yake ɗauke da ɗakunan bacci guda uku. Na farko ɗakine da yake ɗauke da kaya gwanin ban sha'awa, komai kala ɗaya ne dana falon, sai na biyu kuma shi gabaki ɗaya kalar maroon ɗinne da surkin Ash colour masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Na cen ƙurya shine yafi kowanne tsaruwa, kaya ne ƴan uban su, ba kalar na ƙasar tamu bane. Komai na falon fari ne tas, hatta da kalar fentin upwhite ne. Kuma ko wanne ɗaki da toilet ɗinshi. Gaskiya sashen yayi ba ƙarya, na biyun shine aka nuna a matsayin nawa, sai na farkon wai na ummata ne ɗana cen ƙurya ɗin. Da matuƙar mamaki nake binsu da kallo, yau Ummata ita ce a matsayin amaryar Alhaji Mustapha Dambulan??? Falon muka dawo inda muka tadda ƙofofi guda biyu, ɗaya ta balcony ce, yayin da ɗayar take ta makeken kitchen ɗin da yasha carbinet mai masifaffen kyau, ba tarkace a cikin kitchen ɗin, saidai komai akwai. Duka ɗakunan suna da Ac da manyan tagogi, sai falon shima haka, Amman shi ac ɗinshi Central Ac ce tana daga cen saƙo kusa da inda dining table da water dispenser take ajiye. Amman sanyin ta ya wadaci falon gabaki ɗaya, harma kusan mu ce yayi yawa. Sallama Alhajin Yayi mana ya fita yana mai cewa yana zuwa. Da kallo nake bin Ummata ina ta raya abubuwa da dama acikin zuciyar tawa. Ita ko ko sau ɗaya bata kalle ni ba, wata irin ƙarfin guiwa ne nake hangowa tattare da umman tawa, ta yanda naga ta shiga ƴan aikace aikacen ta hankali kwance. Toh fa, ikon Allah saidai kallo. Ceman tayi in tashi in shiga ɗakina inyi wanka in kwanta in huta kafin a kawo mana abinci. A sanyaye na tashi ina mai nufar ɗakin da akace wai mallaki na ne, da ban gama yadda ba, har yanzu gani nakeyi mafarki nakeyi, nice yau a gidan Su ya Ameen ɗin da irin wannan matsayin na mallakar ɗaki sukutum. "To amma shi ya sani kuwa?" Tambayar da nake ta nanata ma kaina kenan, gashi naga sai wani ɗaɗɗaure mani yake yi kaman na kashe mashi uwa. ******* Kai tsaye ɗakin Ya Ameen Alhajin ya nufa, ba zan iya cewa ga tsayin lokacin da ya ɗauka bai taka sashen yaron nashi ba. Ba kowa falon sai Ac da take ta faman yi a hankali a hankali. Bedroom ɗin ya tura, hango shi yayi zaune tsakiyar gado, har ya cenza kaya zuwa na bacci, laptop ɗinshi ce gaban shi yana ta faman latsawa. Tura ƙofar da akayi ne ya sanya shi maida hankalin shi wurin. "Dad" ya faɗa da mamaki, yana mai saukowa cikin hanzari, yana fatan dai ace lafiya, saboda tin bayan shigowar tashi ɗakin zuciyar shi ke kai kawo akan dawowar su Suhan ɗin a cikin gidan, ba zai ce baiyi murna ba, to saidai fa shi yaso ne ace sun dawo a matsayin masu matsayi a cikin gidan ba ƴan aiki ba, saboda yanzu baya jin idan zai iya lamuntr irin wancen wulaƙancin da akayi masu a Wancen zaman nasu. "Lafiya ƙlau kake kuwa son? Naga ina ta magana kana cen kana tunani" Dad ɗin ya faɗa yana mai jawo stool ya zauna bisa, yana mai ɗora hannun shi kan madubi da yake ajiye gefe irin na maza. "komawa yayi ya zauna bakin gadon, yana mai faɗin" Lafiya lau dad" ai na ɗauka ka kwanta ne" "A'a ban kwanta ba, baƙi nake so ka nemo ma abinda zasu ci" "Baƙi kuma Dad? Su wanene baƙi?" "Umman ka" Alhajin ya faɗa kai tsaye ba tare da wani shayi ba. Bai kawo komai ba, yana mai faɗin "To Dad, yanzu kuwa insha Allah" Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye haɗi da zaro jallabiyar shi ya sanya yana mai nufar ƙofa da niyyar ficewa. "am Al'ameen, idan ka kawo ka miƙa mata sashen ta" Ɗan dakata wa yayi daga barin tafiyar da yaje yi, sai kuma ya ɗan waiwayi yana kallon Dad ɗin nashi "Dad ina ne sashen nata?" ya faɗa cike da mamaki "Zo nan" Dad ɗin ya faɗa yana mai kiran shi da hannu Dawowa yayi da baya ya samu gefen gado ya zauna, yana mai tattara dukkan natsuwa shi ya ɗora ta kan Dad ɗin nashi. Ɗan gyaran murya kaɗan Dad ɗin yayi yana mai gyara zaman shi. "Umman taka yanzu ai ba ƴar aiki baceba, *Matata ce* Daga yanzu kafin ta zama taka surukar ta zama uwa a wurin ku gabaki ɗaya" Cikin sakin baki da ƴar gigita wadda Al'ameen ɗin be bari ta bayyana a kan fuskar shi ba, yake kallon Dad ɗin nashi. Bakin shi yayi matuƙar nauyi harma ya gaza iya magana. Jin Al'ameen ɗin bai ce komai bane ya sanya shi ɗorawa da faɗin "Wannan shine tsani, shine matakin samun auren yarinyar a wurin ka, domin ko da muka je ma mahaifiyar da maganar ta auren naku ƙiyawa tayi, tace akwai maganar wani a kanta, to sai muka yanke shawarar hakan da Babanka Auwalu akan cewa bari in auri ita maryamar kaga alabasshi ko yaya ne ina da ɗan iko akan Al'amarin yarinyar. Amman ku fahinceni, masalan ma kai da duk dan kai ne nayi wannan abun, da kuma tausayawar da muke yi ma matar" Tabbas ya gamsu iyaka da zancen Dad ɗin nashi, to saidai ba'a nan matsalar take ba, Mom, Mom ita ce babbar matsala, tabbas yanzu ne za'a fara tashin hankali, duk da cen ba'a yi komai ba. Tuni zullumi da fargaba suka shiga Al'ameen ɗin, to saidai bai ce komai ba, ya shiga ɗaga ma Dad ɗin nashi kai alamar gamsuwa. Miƙewa yayi yana mai faɗin "to Dad Allah ya sanya Alkhairi, don Allah kayi ta haƙuri da Mom saboda gaskiya za' a fuskanci wani irin yanayi a cikin gidan" Da kallo Dad ɗin yake bin Ya Ameen ɗin da har ya fice daga cikin ɗakin. ******** Sai dai koda ya shiga motar kwalwar shi Sam ta cunkushe, rasa inda zai nufa siyen abincin yayi ba kuma wai don babu wurin siyarwa bane, tsabar tunani ne kawai da zullumi. Karkata kan motar tashi yayi ya nufi gidan Aminin nashi. Har sun kwanta ya sanya mai gadi ya buɗe mashi ya shiga. Parking yayi, yana mai zaro wayar tashi daga aljihu ya danna kiran Bilal ɗin. Cikin ɗan bacci da ya fara fizgar shi, yaji wayar tashi na ruri, sunan Friend da yagani ne jiki ya sanya shi tashi zaune, sannan ya ɗaga. Sanar mashi yayi da gashi harabar gidan shi, cikin ɗan ruɗewa ya sauko daga gadon a hankali kada ya tada Ummin da ta samu bacci ya kwashe ta ga ciki da yayi matuƙar girma a jikin ta. Fitowa yayi daga shi sai singlet da boxer. Ilai kuwa motar Al'ameen ɗin ce fake gefe. Ba wata wata ya shiga motar yana mai faɗin "Friend Lafiya A Daidai Wannan Lokacin?" Ɗan shiru Al'ameen ɗin yayi idanun shi a kulle, sai kuma ya buɗe su yana mai wara su akan abokin nashi. "Friend akwai matsala, Dad ɗina ya ƙara aure, bama wannan ce matsalar ba, Mom, Mom ita ce matsalar, idan har taji maganar ƙarin aure kuma da wadda ya aura" Da mamaki Bilal ɗin ke kallon Al'ameen, saidai shima ya gaza cewa komai, saida aka kusan ɗaukar Second ashirin sannan ya iya cewa "Friend gaya mani wacece ya aura? Kuma yaushe? Ya akayi kowa bai sani ba? Ko dama kai ka sani faɗa man ne baka yi ba?" Girgiza kai Al'ameen ya shiga yi, yana mai faɗin "Umman Suhana ya aura, kuma yau ta tare, ya kake gani idan Mom ta dawo gobe ƙasar ta tadda wannan al'amari? Kadai san wacece Mom ɗita ba sai na baka labari ba, kasan halin ta kasan ne zata iya aikatawa, beside ma ina tausayin yarinyar, hakan na iya zama tarnaƙi tsakani na da ita, duk da shi Dad a ganin shi wannan ce hanya mafi sauƙi ta samun Suhan ɗin a wuri na, shi ko tunanin Mom ɗin ma baya yi, da Abunda zai iya zuwa ya dawo" Al'ameen ɗin ya faɗa cike da ƴar damuwa a saman fuskar shi. Ajiyar zuciya Bilal ɗin yayi, tabbas ya san Mahaifiyar abokin nashi, Sam mutumci ko karamci bai cika taba, da akan yaronta takeyi, gani takeyi kaman zasu mallake nata yaro, sai gashi abun ya juye ya koma kan mijin nata, kafin yazo ga kan ɗan nata. Lallai akwai cakwakiya zalla a gidan nan, saidai fatan Allah ya kare kawai. Muskutawa yayi yana mai faɗin. "Friend ka kwantar da hankalin ka, kada wani abu yazo ya same ka kawai, kayi ta addu'a, kuma kabar lamarin a hannun Abba, a shawarce kada ka sanya kanka ciki, in da hali ma, kada ka zauna a gidan gobe..." " Bazan iya ba Friend, ko ina zanje hankali na yana a kanta, gani zan kaman wani abu zai same ta, a yanda na gani a saman fuskan ta, kaman itama bata san komai ba, Friend mafita nake nema please" Ya ƙarashe ya mai bin kwayar idanun abokin nashi da kallo. "To kuwa dole kayi kaman baka san me ke faruwa ba, dole ka bar zancen yarinyar for now, kada ka sake ka nuna ma Mom ɗin buƙatar taka akan Suhan, in ba haka ba kuwa abun zaiyi zafi sosai, ko da komai zai faru a gaban ka, kada ka nuna kana da intrest akan yarinyar, ka daure ma ranka, ka daure ma zuciyar ka please, komai zai zo da sauƙi, yanzu bari in zuro jallabiya muje mu nemo masu abincin" "a'a ka bar shi kawai, zamu haɗu zuwa da safe, kana bacci na tada ka, ka koma ni zanje in nemo masu" Al'ameen ɗin ya faɗa yana mai tada motar, fita Bilal ɗin yayi yana mai rufo mashi ƙofar ya matsa baya, har Al'ameen ɗin ya fice sannan ya koma cikin gidan. ******* Abinci mai rai da lafiya ya siya masu, harda ruwan sha na gora masu yawa da kayan tea, sannan ya nufo gidan. Tura ƙofar falon yayi cikin sallama ya shiga, zaune nake bisa kujera na takure saboda ɗan sanyin da yake ratsa ni, ummata kuwa tana cikin ɗaki bansan Abunda takeyi ba. Bai ko kalli inda nake ba ya wuce kai tsaye bisa dining table ya ajiye manyan ledojin hannun shi. Juyawa yayi da niyyar zai fice na taso a hankali ina mai kiran sunan shi cen ƙasan maƙoshi "Yaya" Ɗan tsayawa yayi, sannan ya juyo yana mai fuskanta ta, "Lafiya?" Ya faɗa cikin amon murya dake nuna kaman na takura mashi. "Yaya ina jin tsoro, bansan Abunda zai iya faruwa ba, please kaba Dad shawara a warware auren nan don Allah" Na faɗa murya cen ƙasan maƙoshi. Wani irin tausayin tane ya tsirga mashi, lallai ya ƙara tabbatar wa ba tare da sanina komai ya faru ba. Takowa ya shiga yi har inda nake tsaye, duk da kaina yana a ƙasa, wasu irin siraran hawaye ne masu ɗumi ke sauka akan fuskar tawa, har ina iya juyo saukar numfashin shi a hankali. A hankali ya sanya hannun shi duka ya ɗago fuskar tawa, wara idanu ya shiga yi saman tawa fuskar yana son gano dalilin da ya sanya ni kuka haka lokaci ɗaya. Runtse idanuna nayi, wasu hawayen na ƙara malalowa. Da hannayen shi yayi amfani wajen ɗauke mani hawayen. "Is ok Suhan, babu Abunda zai faru sai Alkhairi kinji" ya faɗa cike da tausayawa, wata irin soyayya na fizgar shi, ji yake yi kaman ya rungume ta ko ya samu sassaucin Abunda yake ji a cikin zuciyar shi. Ɗan girgiza kaina na shiga yi, ina mai janye kaina daga ruƙon da yayi mashi. Sai na juya da baya da niyyar tafiya ɗakin nawa. "suhhaaaaan" ya faɗa cikin murya siririya tana cracking Tsayawa nayi ban juyo ba. Ƙafa ya ɗaga taku biyu ta kawo shi ta inda nake tsaye. Da hannuwan shi yayi amfani wajen kamo nawa. "Nasan Mom ɗita kike tsoro, kibar jin tsoro, yanzu zaman Dad kuke yi a cikin gida nan, kuma Dad shine mai iko a gidan nan ba Mom ba, kiman alƙawarin ba zaki kuma yin kuka ba saboda haka, nasan yanda kike ji a zuciyar ki, Amman kada ki manta ina nan, Dad ma yana nan" Ya faɗa da ɗan murmushi cikin son kwantar mani da hankali. Ban iya zame hannuwan nawa ba, na shiga ɗaga mashi kai alamar gamsuwa. "A'a Muhammadu kai ne?" muka tsinkayi muryar umma daga bayan mu tana tahowa. Da sauri ya zame hannuwan shi cikin nawa, yana mai ja baya yake faɗin "Eh Umma nine, ga kayan amfani cen ku fara kafin zuwa safe muga dame dame za'a buƙata, kuna iya yo list ma" Ya faɗa kanshi a ƙasa cike da kunya, wai yau umman ce yake magana da ita a matsayin matar mahaifin shi, Un bleavable. Ɗan murmushi ta saki tana mai cewa "To an gode kwarai Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi" Da "Ameen" ya amsa yana mai juyawa ya fice ko ta kaina baibi ba, itama umma juyawa tayi ta nufi inda ya ajiye kayan ba tare data ce mani komai ba. To nima ɗin da kallo na shiga bin umman tawa, yanda take komai kai tsaye, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci umma tawa ta cenza kaman ba ita bace wadda na sani ada ba, me hakan ke nufi? Lallai akwai wani babban al'amari da yake a cikin zuciyar Umman tawa, babu shakka ko ɗar a cikin zuciyar ta? Allah yasa koma me zai je ya dawo yazo mana da alkhairi Ameen....... _Kuyi haƙuri da wannan a matuƙar gajiye nake wlh._ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~44~* *Kyautar Page gareki One lurhv, ina jinjina maki a bisa soyayyar da kike mani Allah ubangiji ya bar ƙauna, ya tsole idanun maƙiya a kai, ya bamu ikon zama cike da so da amanar juna. AMEEN* @Salamatu, Lubabatu, and Daura tnz for your personal Support, hearted u All guiz, ia ina yinku over and ove_ ~_@Shalele (Raggon Miji Return) ki fita a idona in kulle fa tam, ni da One lurhv nan gani nan bari takalmin kaza, a tom_~ *Jinjina ga ƴan golden pen haƙiƙa haɗin kai da ƙaunar junan mu abu ne mai matuƙar ƙayatarwa, we are the best among the rest insha Allah, Allah ya bar mu tare* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Sama sama muka yabiɗi abincin daga ni har umman tawa. Ƙala bata ce mani ba, ina kula da ita sai bina da kallo takeyi. Jikina har yanzu a matuƙar sanyaye yake, amman ita umma na kula ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba wajen ƙarfafa tata zuciyar. Kasa kwanciya nayi a ɗakina ni ɗaya ban saba ba. A hankali na tashi daga bisa makeken gadon nawa da ya wadata da katifa mai matuƙar taushi. Ɗakin umman na ƙanƙwasa, daga ciki ta bani umurnin in shiga. Tura ƙofar nayi a hankali ina mai shiga ɗakin, gefen gado na samu na zauna ina mai faɗa ma umma na kasa bacci ni ɗaya. Cewa tayi in kwanta nan bisa gadon nata, zuciyar tata fal da tausayi na, ta kula yarinyar tata gabaki ɗaya kaman bata yi murna da wannan auren nata ba,tsoro ne fal acikin zuciyar yarinyar tata, saidai ba zata taɓa fuskanta ba, dalilin zaman nata a wannan gidan, da dalilin auren Alhajin da tayi duk yana da nasaba da ita Suhan ɗinne. Ban yi baccin kirki ba, kaman yanda itama umman bata yi ba, tana kula da dukkanin juye juye na. Saidai bata tanka mani ba, sai ma miƙewa da tayi ta dosa sallolinta. To shima dai ɗin gogan zamu iya cewa bai runtsa ba ko sau ɗaya. Abubuwa ne fal yake damun shi cikin zuciya. Ɓangare ɗaya Mom ɗin tashi ce ke kai komo. Wani Al'amari irin na uwa da ɗa ke taso mashi, sai kuma cen ƙasan zuciyar shi Suhan ɗin ce tayi tsaye ƙiƙam, duk son da yayi na ya matsar da ita ya kasa. Sai kuma tinani da taraddadin dalilin Dad ɗin nashi na son auren Umman Suhan ɗin, wanna amsar dai a yanzu kam baya da ita. Zai jira har lokacin da Alhajin nashi zai warware mashi zare da abawa. Tin da farar safiya yayi shiri ya fice daga gidan, Bilal ya tsaya ya ɗauka sannan suka wuce. Mu kau tin bayan munyi wanka, sai kuma muka koma zaman jigum jigum. Nikam miƙewa nayi na koma falo, domin yana yin da nake ciki ba zan iya fasalta komai ba, cikin raina tausayin yanda rayuwa ke walagigi dani nakeyi, a hankali a hankali nakan sanya yatsa in share kwallar da take bi mani fuska, sai nayi kaman in kira Sir Salim ko zai sanya ni dariya ko da kuwa sau ɗaya ne sai na kasa. Ina jin Kunyar ince mashi mahaifiya ta ce tayi aure, Amman kuma ya zama dole ya san inda nake ko don saboda sanin halin da makaranta take ciki. Dirin mitoci ne ya karaɗe ilahirin gidan, sai kuma muka ji hayaniya ta ɓarke a gidan. Miƙewa nayi a hankali na isa ga wangamememiyar tagar da take falon, leƙawa nayi, saida gabana ya ruguje ya faɗi. Ƴan kankiya ne su da yawa, ƙwansu da kwarkwata, duk wani wanda zai iya zuwa saida yazo. Hajiya Zainab ce gaba gaba, sai kuma Hafsat a gefen ta daƙyar take cira ƙafa saboda girman da cikin ta yayi. Gaza matsawa nayi, ita kuwa Ummata tinda taji hayaniya ta tashi ta shige ɗaki ta barni nan tsaye ina mai binta da kallo. Hafsat ta riga kowa shigowa, da sauri ta shigo tana mai dube dube kaman tana neman wani abu, sai kuma naga ta saki murmushi ta nufo ni, tana mai rungume ni tsam a jikin ta. Shigowa suka fara yi, lallai suna da yawa, hannuna Hafsat ɗin taja alamun inzo mu shiga ɗaki, ganin bata san ɗakin bane ya sanya na shiga wucewa gaba, tana biye dani. Ɗaki da yake mallakina wai muka shiga, bakin gado muka zauna, tana mai bina da idanu kaman zasu faɗo ƙasa. Sai kuma na saki kuka mai cin rai, Hafsat ɗin ƙawa ce, aminiya ce gareni. Bata ce komai ba sai ma sake bina da tayi da idanu. To ita ai bata ma ga abun kuka ba anan, murna ma ya kamata inyi, Allah ya kawo ranar da muka samu ƴancin mu a cikin gidan. Sake rungume ni tayi tana mai ɗan bubbuga bayana a hankali alamun lallashi. "Suhan menene na kuka kuma? ko Auren Umman ne baƙya so." A hankali na ɗago ina mai kallon ta, sai kuma na shiga ɗaga mata kai, alamun bata tabbacin Abunda ta faɗa. "Kin jiki? To menene a ciki? Umma fa ba wuce aure tayi ba, kuma bayan haka, Babana Mutum ne da kowacce mace take fata da burin ta samu a matsayin miji, saboda yana da kirki da mutumci matuƙa. To ke menene dalilin da yasa zaki ce bakya son hakan?" "Hafsat, Hajiya Kubra, Hajiya Kubra ba zata ɗaga mana ƙafa ba, ba zata ƙyale mu ba, ga su Aunty Nihal, da Aunty Saudat. Da cen ma da muke ƴan aiki bata ɗaga mana ƙafa ba sai yanzu da Umma ta aurar mata miji?" Na faɗa ina mai sake matso wani kwallar daga idanuna. Ɗan murmushi ta saki tana mai faɗin" Ke da zaki auri yaron nata ma tin yanzu kin fara karaya balle?" Ɗan zabura nayi ina mai ce mata" Inji wa? Waya faɗa maki?" " Mama Mana, a bakin ta naji, tin lokacin da su Baba suka je neman auren naki" Ta faɗa tana mai ƙumshe dariya Ohh ni Allah, ashe wancen zuwan da su Alhaji Auwalun sukayi a ranar da abun nan ya faru dani wai aure na suka je nema ma ya Ameen? Ashe Shiyasa yace mani zan aure shi? Kenan don kada a kirani jin ta bakina ince bana so ne ya sanya shi tara ta da wannan maganar Gaske fa, ni dama nayi mamaki, ashe ba har cikin zuciyar tashi son nawa yake ba. Dama wace ni da Ya Ameen??? Ai ni kaina nasan yafi ƙarfina har gaba da abada ma. Kawai da zancen zucin da nakeyi nayi, ina mai share kwalla ta. Ɗan duka na kai mata ina mai cewa "Banason haka hafsat, ba don babyn mu ba da sai kinji jiki" Dariya ta saki iya ƙarfinta, sai kuma tace "Ya naga wai baki fara shiri ba? Haka zaki ci walimar?" Da mamaki nake kallon ta ina mai cewa "Wace walima kuma?" "Bakiga baƙi ba? Ƴan uwa ne duk suka zo za'ayi walima yau, ƴan uwan ango Dad" Ta faɗa cikin zaulaya tana mai kanne mani ido ɗaya. Hayewa nayi bisa gadon ina mai ce mata "A gama lafiya ƴaƴan ango" "To ɗiyar amarya" ta faɗa tana mai wucewa gaban akwatina na da suke gefe ajiye. Jawosu tayi ta shiga buɗewa. Dudduba komai ta shiga yi, sai cen ta fiddo wani material mai kyau matuƙa ta ajiye ta haɗo harda gyalen da zai iya shiga dashi. "Kinga kayan da zaki sanya nan please ƙawata, don Allah ki saki ranki, na rana ɗaya ne zamu yi tafiyar mu mu barku" Kallon ta nake in mai taɓe baki, Ƙala bance mata ba, sai ma juyawa da nayi ina mai kulle idanu na. Da dai taga alamun rigima nake ji da ita, kuma har cikin raina tsoron auren nan ya kama ni, sai ta miƙe haɗi da ficewa daga ɗakin. Hajiya Zainab ma kai tsaye ɗakin ummata ta shiga, sai a na biyun ne ta hango ta zaune bakin gado. Isa tayi suka shiga gaisawa cikin mutunta juna da ƴar firar yaushe gamo,sannan tayi mata Allah yasa Alkhairi ya bada zaman lafiya. Bata ce ma Umman komai ba akan walimar da za'ayi, domin komai na a hannun ta ne. Wai Ashe har mai make-up aka kira zata yi ma umman tawa, abun ban dariya. Hajiya Zainab ce gaba gaba wajen haɗa komai, ƴan aikin dake gidan kaf saida aka kikkira su, kowanne da aikin da yake yi, duk da suma mamaki ya cika ransu fal, gashi sun san Hajiya Kubran bata ƙasar, saidai sun san duk inda take tana bisa hanya. Canopee ne aka kakkafa manya masu kyau, anyi masu ado sosai, sai kujeru da aka jejjera. Daga wani eatery aka dinga shigowa da abinciccika suma duk jejjera su aka shiga yi, ƴan kankiya ma har sun zazzauna. Kowa ya sha kwalliya daidai gwargwado, nima daƙyar Hafsat ta lallaɓa ni na sanya kayan, Amman fuskanta babu wata kwalliya, ko kwalli babu daga mai sai farar powder. Bamu kai ga fita ba, saidai ance da anyi sallar azahar za'a fara gabatar da walimar cin abincin, kafin a gabatar da Umman wurin ƴan uwa. Ma'aikatan gidan sai ƴan maganganu suke yi, saidai ba damar a faɗa fili, duk da har yanzu cikin su ba wanda ya san abunda ke faruwa sai mudi ne kawai ya sani, shima da yake ba surutu gareshi ba yaja bakin shi ya tsuke kada aji maganar sarki a bakin shi. ************ Yana tsaka da aiki wayar tashi ta soma ruri, saida ya kai kallo sashen da Bilal yake zaune shima yana latsa laptop. Sai kuma ya ɗaga yana mai sallama ganin Sunan Mom ɗin nashi yana yawo a bisa screan ɗin, saida gaban shi ya faɗi. Sallama yayi cikin dakiya da son kauda komai a cikin ranshi kada ta fahimci ko yana da damuwa. "Son na dawo kazo ka ɗauke mu a airport yanzun nan" Ta faɗa cikin bashi umurni kai tsaye. Miƙewa tsaye yayi yana mai tattara wayoyin shi bayan ya kashe wayar. "Friend akwai matsala" Ya faɗa cikin wani irin yanayi mai nuna alamun ya kusa sarewa. Cikin ƙarfafa guiwa Bilal ɗin yake tambayar abokin nashi. "Mom ce ta dawo yanzun nan, kuma wai ni zanje in ɗauko su in kaisu gida, may be ita da ƙawayen ta ne" "Toh fa! Menene abun matsalar a ciki? Friend mahaifiyar ka ce fa" Ya faɗa yana mai ɗan tallafe kanshi da hannuwan shi. "Anyway, bari inje in gani ko zan samu in dawo da wuri in idasa aikin nan" Ya faɗa yana mai wucewa cikin salon takun tafiyar shi mai ɗaukar hankali. Koda ya isa lallai hasashen shi ya zama gaskiya. 4Hajiyas ne cikin shiga ta alfarma sai zuba ƙamshi suke yi, tin daga nesa zaka iya hango isar su da hamshaƙar su. Cikin murmushi irin na ɗa da uwa ta shiga taka wa tana nufar inda yake doso su kai tsaye. Ɗan rungume shi ta shiga yi, tana faɗin "I missed you My Lovely Son" Ɗan murmushi yaƙe ya saki yana faɗin "Mee Too Dear" Motar suka ɗunguma gabaki ɗayan su bayan ya gaida ƙawayen Mom ɗin nashi. Cikin Murmushi da ban sha'awa suka shiga amsawa, ko ba komai suna matuƙar alfari da yaron Ƙawar tasu kuma hamshaƙiyar tasu. Tin da suka doshi gidan gaban shi ke faɗuwa, cikin mamaki take kallon shi, hango motoci da tayi ƙofar gate ɗin gidan nasu, gashi kuma ita batasan abunda akeyi ba, kuma ko da safe sunyi waya da Alhaji Mustaphan Amman bai ce mata ana yin wani abu ba. Ɗan kallon shi ta shiga yi, alamar son ƙarin bayani. Janye idanun shi yayi yana mai runtse su, Abunda zai je ya dawo a daidai wannan lokacin yake gudu, ina ma ace yabi shawarar abokin nashi wajen barin garin ma gabaki ɗaya. A hankali ya shiga gangarawa cikin gidan, bayan mai gadi ya wangale masu gate. Tsabar mamaki tsantsa ne a kan Fuskokin 4Hajiyas ɗin, tin kafin ya idasa parking Hajiya Kubran ta ɓalle murfin motar ta fito, gyalen ta saman kafaɗa guda ɗaya, sai ƴar mitsitsiyar jikkar dake hannun ta kaman ta wasan yara, da tafka tafkan wayoyin dake hannuwan nata riƙe Abokan nata ne suka shiga mara mata baya. Kusa da Canopee ɗin taja ta tsaya, tana iya hango ƴan kankiyar a cikin runfar, walima akeyi, abinci ake ci mai rai da lafiya, kowa sai hidimar shi yake yi, duk da sun kula da ƙarasowar ta wurin. Waiwayawa tayi tana mai kallon Al'ameen ɗin da yake tsaye bakin motar tashi, ya gaza ɗaga ƙafa balle yabar wurin. Sai kuma ta maida kallon ta kan mutanen da suke cikin rumfar. Wata kujera mai matuƙar kyau, ruwan gold ce ajiye gefe guda ba kowa a kanta, sai kuma kanta ya ƙara ƙullewa. Ta rasa wanda zata tambaya, gashi tana son tambayar Amman isa da mulki sun hana ta tambayar. Hajiya zainab ce kan gaba, sai Goggo Aisha da Goggo Fatima a bayan ta, sun sanya wata mata tsakiya. Tasha ɗanyen leshi mai matuƙar tsadar da tasan kuɗin shi sun haura ma naira dubu ɗari biyar, wara idanu ta kuma yi sosai, daga sashen da Alhajin yace mata nashi ne aka fito da ita, kanta lulluɓe da mayafi mai kyau da walwali. A bayan ta yara ne guda biyu, ta shaida Hafsat da take cira ƙafa daƙyar, sai kuma gudar da ta kalle ta a fige ba tare da ta shedata ba, saboda hankalin ta ba'a kanta yake ba. Kai tsaye kujerar da take ajiye suka zaunar da ita. So take taga fuskar matar, hankalin ta in yayi dubu ya tashi, ƙawayen nata ta maida kallon ta wurin da suke tsaye suma cike da tsabar mamaki. A hankali ta shiga takawa har gaban matar da aka zaunar bisa kujera, hannun ta duka ta sanya ta ɗage gyalen da yake lulluɓe saman fuskar Umma tawa. A matuƙar zabure taja baya, har tana shirin faɗuwa. Wa take gani haka? Maryama ce zaune bisa kujerar tasha kwalliya har ta gaji, wuyan nan nata cike da ɗanyen gwal ɗinda kuɗin shi saidai a kira miliyoyi, hannayen ta kaf cike suke da awarwaro na gwalagwalai "Ayuririririririri" Taji wata mayyar guɗa ta saki guɗa cike da ƙwarewa matuƙa, sai kuma taji an shiga faɗin "Uwargida ke nan a wurin Alhaji Mustapha Dambulan ɗin, ita ce da kanta ta siyi wankan da Amaryar tata tayi ayau domin faranta ran dangin mijin nata. Ayau Allah ya kawo mu shagalin bikin Amaryar ta Alhaji Mustaphan Farar mace alkyabbar mata, Uwargidan ki na tsaye a gaban ki tazo kawo gaisuwar ban girma da yi maki maraba da shigowar taki gidan nasu da yake cike da ɗumbin wadata da arziƙi haɗi da soyayya da zaman lafiya." Gabaki ɗaya muka waiwaya domin ganin wacece wannan zabiyar haka? Wata mata ce tafe jikin nata sanye da atamfa mai matsakaicin kuɗi, da gani dai zabiyar ce da gaske, to ko wa ma ya gayyato ta kuma? Oho! Hajiya Sa'a ce ta matsa haɗi da kamo hannun Hajiya Kubran da ta tabbatas tayi mutuwar tsaye ne, idanun ta sun firfito kaman zasu faɗo ƙasa, ita kuwa umman tawa murmusawa kawai takeyi cikin ƴar kwalliyr da akayi mata Light mai ban sha'awa, ashe haka Umman tawa take da kyau masha Allah. Bata da zaɓi illa ɗaga ƙafa ta shiga bin abokiyar tata, ƙafafun ta har suna harɗewa, to sanin da kowa yayi akan halin hajiya Kubran ne ya sanya basu kawo komai ba, sun ɗauka isar tata ce ta motsa, kuma gashi babu wanda tayi ma magana. Ya Ameen da yake gefe, nannauyar ajiyar zuciya ya saki, yana mai kai idanun shi bisa fuska ta da take tar babu ko ɗigon kwalliya bisa, hakan ne yasanya haskena ƙara fitowa, da idanuna suka yi ɗan ja saboda kukan da nayi gashi kuma babu kwalli a jikin su ko ɗis. Kallona yayi na tsawon Second goma, sai kuma ya ɗaga ƙafa cikin sauri ya nufi sashen nashi, yana mai ɗan sauke ajiyar zuciya ganin Mom ɗin tashi bata saida hali ba. ************* Suna shiga sashen nata, ta fizge hannun ta daga na Hajiya Sa'ar, sai kuma ta shiga kai komo. Cikin wani irin yanayi na tsantsar ɓacin rai, zuciyar ta kaman zata tsago ƙirjin ta ta fito, ga wani irin ja da farar fuskar tata tayi. Kai komo ta shiga yi cikin falon da ya wadatu da kayan alatu. "Ni?? Ni?? Ni???" "Ni Alhaji zaiyi ma haka? Ni Alhaji zai cima amana? Ya rasa wadda zai aura sai ƴar aikin gida na tsawon lokaci? Ƴar aikin ma wadda nafi tsana a rayuwa ta? Ƴar aikin ma marar galihu da asali irin Maryama?" "Niiiiiiiiii???" Ta faɗa tana mai zama bisa kujera ta shiga dafe kanta, sai kuma ta miƙe ta wawuro wayar ta ta shiga danna kira. "Hello Saudat, kinji Abunda mahaifin ku yayi? Aure yayi, kuma ma wannan shegiyar ƴar aikin marasa asali, Eh ki kira Nihal yanzun nan kuzo ku same ni a gida" Sai kuma ta kashe wayar tana mai danna ma Ya Ameen kira. Gabaki ɗaya ta fita kamannin ta da hayyacinnta, lallai ma Alhaji ya zubar mata da ajin da mata dayawa suke ganin ta dashi. Yana ganin kiran nata ya kasa ɗauka, ya san abunda zai faru, zama yayi yana mai dafe kanshi da dukkanin hannuwan shi da yake jin kaman zai tsage mashi. Hajiya Laila ce ta amshe wayar a hannun ta "Hajiya Kubra ki tsaya muyi magana, ki zauna mu nemi mafita" A zafafe Hajiya Kubran ke kallon ta, sai kuma ta shiga cewa "Duk laifin kune Laila, ku kuka ja mani, wane irin kuɗi ne ban ba ku ba akan a ɓatar dasu a cikin ƙasar nan? Kuma kun mani albishir ɗin sun tafi kenan? Ta yaya zasu dawo mani cikin gida, kuma ma wai a matsayin matar gida? Kunci amana ta Laila da Sa'a kunci amana ta bazan taɓa iya ɗaga maku ƙafa ba har abada" Ta faɗa cike da hargagi tana mai watsar da tukwanen plowers ɗin dake ajiye bisa wata pula gefen falon. Kaman zata yi hauka haka take ji, ta watsar da gyalen da jikka harda wayo yin nata, abun kunya ne a wurin ta ace kaman ta mijin ta ya auri ƴar aikin ta. Hajiya Sa'ar ce zata fara magana ta shiga dakatar da ita.... "Kiyi mani shiru Sa'a, har maci amana ma irin ku zaku iya bani uzirin ku? Amman nasan mai laifi, ba kowa keda Laifi ba asai Al'ameen, shine ya fara bijiro da maganar Aure a gidan nan, zai zo ya iske ni, sai na ci mashi mutumci wallahi zai tadda ni. Mai gadi ne ya shiga buɗe gate ɗin gidan, a guje motar ta shigo haɗi dayin parkin kaman zata murje mutanen dake gurin tsaye. A fusace suka fito suna yima kowa kallon banza, Nihal ce da Saudat ɗinda aka ci sa'a sunzo ƙasar ita da mijin nata. Fuuu suka shige cikin gidan, kowa da kallo ya bisu yana mai girgiza kai haɗi da Allah wadai a cikin zuciya. A sukwane suka isa wurin da mahaifiyar tasu take ta faman safa da marwa tana sakin ajiyar zuciya sukayi. "Mom me kike faɗa mana haka a waya? Taron me akeyi cikin gidan nan haka? Nihal ɗin ta faɗa cike da rashin kunya da tsiwa. Hajiya Kubra ce ta kuma zaburo mata, ji takeyi kaman tayi hauka fa yau. " Na faɗa maki Dad ɗinku ne yayi aure, Maryama ƴar aikina ya aura don cin amana" "What Mom? Waɗannan Talakawan faƙiran? Me Dad ya gani ya burge shi jikin su?" Umman ce ta kuma matsowa jikin Saudat ɗin kaman zata kai mata duka. "Yo me kuwa ya gani banda asiri? Asiri suka yi mashi, da sun yima Al'ameen basu ci galaba ba, shine yanzu suka koma kan Dad ɗinku mai gaba ɗaya, to wallahi ba zata taɓa zama gidan nan ba, ba zan lamunta ba, ai kiran ku nayi ku gani da idanun ku" Ta faɗa tana mai kwasawa ta nufi hanyar waje kaman zakanya. Su Hajiya Sa' a basu nemi hana ta ba, saboda uwar watsin da tayi masu yanzu, duk jikin su yayi sanyi, dama ita sabuwar Ƙawar tasu ba'a sanya ta ciki ba, bata ma san meke faruwa ba, duk da itama cike take da ɗinbin mamaki. Rufa mata baya sukayi suma, saidai daga bakin part ɗin nata suka ja suka tsaya, su kau su Nihal har bakin rumfar suka isa. Ja tayi ta tsaya cike da isa tana yima kowa kallon wulaƙanci, harda yayyen mijin nata da suke ta sha'anin su ba tare da sun kula ta ba ma. "To taron maciya amana, taron kwaɗayayyu, taron ƴan kuci ku bamu, ku kuma ku rasa auren da zaku zo mawa sai wannan auren na maciya amana? Auren ha'inci? Auren da bana da masaniya akan shi? Ta faɗa tana mai bin su da idanu gabaki ɗayan su. Goggo Fatima ce ta buɗe baki da niyyar bata amsa, sai Goggo Aisha ta zunguro ta alamun tayi shiru. Hakan ba ƙaramin ƙona ran Hajiya Kubran yayi ba, sai kuma ta shiga cewa "Ba dole kuyi mani shiru ba, anci amana ta an zalunce ni? An auran mani ƴar aiki? Ke kuma na dawo gareki, ki sani baki kai matsayin da zan iya haɗa miji dake ba, wallahi saidai yazo ya zaɓa ko ni ko ke, cikin ɗaya ayi biyu. Dama munafuntata kike yi zama gidan nawa da kika yi ashe? Gaskiya naji na tsane ki, da anso a liƙa ma yaro na wannan koɗaɗɗiyar ɗiyar taki Allah ya tsallakar dashi, ashe kince dole dai ki zauna a gidan bayan barin nashi da kikayi kaman gaske, ashe wani tsafin akaje aka ƙullo? To wallahi ahir ɗinki kurwa ta kur data mijina data ƴaƴana" Umman tawa tinda Hajiya Kubra ta fara magana take ta fama doka murmushi abun ta, Sam hakan bai ɓata mata rai ba, bai kuma bata mamaki ba, wannan ƙaramin abu ne akan wanda ta shirya ma gani, saidai koma minene ba zata taɓa sarewa ba, wannan shine mafari ma, wannan shine masomi, zama daram kaman ɗuwawu. Nikau tinda ta fara magana hawayen da nake ta faman riƙewa suka soma zarya akan fuska ta, wannan shi nake gudu, wannan shi nake tsoro, ina gudun abunda zai je ya dawo, inda Allah ma ya so mu babu wanda ya tanka mata duk wulaƙancn da takeyi, hatta da su Goggo Aishan sun haƙure ma kansu. *** Tin da ta fara sonsomin bala'n ta yake tsaye ta taga yana kallon ta, gabaki ɗaya kalar fuskar shi ta sauya, me Mom ɗin tashi ke nema a rayuwa? Wane irin abu ne takeyi a haka? Gashi kaman sun maida ta mahaukaciya tsaye ita kaɗai tana ta zuba bala'i? Ina ta baro isar tata yau? Ina ta ajiye girman kan? Da rashin son maganar? Juyawa yayi a hankali yana mai sakin labulen ɗakin ya koma ya zauna bisa sofa, kanshi yake ji kaman zai tsage biyu, Gaza zama yayi sai kuma ya tashi ya koma bakin tagar yana hangen komai tar. Hangota yayi ta tashi cikin ɗan gudu ta nufi sashen nasu, da alamu dai kuka takeyi sosai, sai kuma yaga Hafsat ta ɓaɓɓaka ta bita daƙyar. Runtse idanun shi yayi yana mai sake sakin labulen ya zarce zuwa bedroom ya kwanta rigingine yana kallon POP ɗin da yake fari tar saman rufin ɗakin da ya wadatu da fararen ƙwayaye tas. Wayar shi ya jawo haɗi da kiran Bilal ɗin, yana mai ce mashi yabar ko me yake yi yazo ya same shi please. Runtse idanun shi ya kuma yi, idan duk duniya farin ciki ce, zai iya cewa shi yau baƙi ƙirin yake gani tsabar ɓacin rai. Ranshi gabaki ɗaya a dagule yake, ya san ba zai taɓa fita ba, ya san zasu kai ruwa rana da Mom ɗin tashi, tinda yaga kiran ta ya san kwanan zancen Shiyasa ma bai ko iya ɗagawa ba. Baiyi gigin kiran Dad ɗin nashi ba, domin a yadda Mom ɗin tashi keji da bala'i, ko Alhajin ne yazo a daidai wannan lokacin zata iya yi mashi, kishi da baƙin ciki na cin ta tsanta. Ganin ba wanda ya kula ta ne ya sanya ta juyawa cikin ƙufula da hassala ta koma sashen nata. Cikin ƙawayen nata babu wanda ya iya ce mata komai, suma su Nihal mara mata baya sukayi, ransu a matuƙar dagule ga wani kallon tsana da suke bin ummata dashi, Abunda ya kuma ƙara ɓata masu rai shine murmushi da suka ga tanayi, kenan ma ta maida su sakarkaru kenan. Cikin minti Goma sai ga Bilal ɗin ya bayyana sashen Abokin nashi, duk mutanen da suke harabar gidan haka ya ratso su cikin sauri. Kwance ya tadda shi yana dafe da kai. "Al'ameen Lafiya kuwa?" Ya faɗa yana mai hawa gadon haɗi da tallafo kan abokin nashi. "Ba lafiya Bilal". Al'ameen ɗin da ya buɗe idanun nashi daƙyar, sun cenza kala sun koma kaman garwashi, ya aza su bisa kan fuskar Bilal ɗin da yake tallafi da kanshi. "Friend nace maka ka sanyaya zuciyar ka, babu Abunda zai faru insha Allahu, ka dena tunani Mom ba zata yi wani abu....... " She has done it" Abunda ya iya faɗa kenan ya maida idanun nashi ya kulle. "What?" Bilal ɗin ya faɗa cike da kaɗuwa. Muryar Al'ameen ɗin ya tsinkaya a hankali yana faɗin "Am sick Friend ka kira mani doctor, kaina zai tsage" Cikin bala'n firgici ya diro daga bisa gadon, jikin shi har rawa yakeyi ya zaro wayar tashi daga Aljihu ya shiga laluben number ɗin doctor ɗin. Ya san matsalar Abokin nashi, ya san da uwar shi, dole kuma ya shiga wani hali na tashin hankali, damuwa dole ce, to saidai shi da yake da matsala bai kamata ya sanya ma ranshi damuwa har haka ba. "Cool your mind friend, nothing will gonna happen insha Allah" Abunda Bilal ɗin yake faɗa kenan da ƙarfi yana mai girgiza Al'ameen ɗin da idanun shi suke daɗa kullewa a hankali har suka idasa rufewa kirif....... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~45~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Cikin minti goma sha biyar Dr.ya ƙaraso. Ta ƙofar baya Bilal yaje ya buɗe mashi, saboda gudun jawo hankalin mutane. Duba shi sosai yayi, yana mai kwantar ma Bilal da hankali akan cewa ranshi ne ya ɓaci, kuma ba'a son haka, saboda ga alamu nan har yanzu jikin nashi bai ida warwarewa ba, ga kuma stress da ya sanya ma kanshi, gaskiya a kiyaye abunda ke ɓata mashi rai haka nan da nan. Ruwa ya ɗaura mashi haɗo da allurai, yana mai bada shawarar a bar shi ya samu bacci sosai kaman na awa biyu. Sai a lokacin hankalin Bilal ɗin ya kwanta, jin matsalar ba mai yawa bace. Wai me yake faruwa ne haka? Wa zai tambaya, ashe abokin nashi bai bi shawarar tashi ba? Ko dayake ba lallai bane yanzu ya dinga bin shawarar tashi ba kai tsaye. Nan ɗakin ya zauna yana watching abokin nashi, gashi gidan kuma da ƴar hayaniya, duk da bata cika damun su ba kai tsaye da yake da ƴar tazara haka kaɗan daga inda suke. *********** "Suhan kiyi shiru hakanan, kiyi haƙuri don Allah, bana so inga kina kukan nan, aure dai an riga an ɗaura, saidai muyi Addu'ar Allah ya basu zaman lafiya, ya kauda duk wata fitina dake neman kunno kai, ita kuma Mom Kubra Allah ya shirya ta." Hafsat ɗin wadda ta zauna gefen gadon nawa, tana mai & ora hannun ta kan gadon baya na da nake kife ina mai rusa kuka haiƙan. Abunda nake guje ma Umman tawa kenan, cin mutunci a gaban kowa, har yanzu ban gano dalilin wannan auren ba. Ɗagowa nayi ina mai kallon ta haɗo da cewa "Hafsat wannan wane irin aure ne? Auren da yake barazana ga kwanciyar hankalin mu, wancen karon ma wace Allah cika? Balle yanzu da ta auran mata miji? Wane irin zama kike tunanin zamuyi a cikin gidan nan? Hajiya Kubra na da kuɗin da Ummata da bata da komai ba zata iya ja ko karawa da ita ba..." " Suhan mace fa bata auran kanta, kuma na tabbata Umman ba itace ta bijiro ma da Dad maganar auren nan ba, ƙila akwai abunda ya hango tattare da umman ne, kasancewar ta mutuniyar kirki, ga sanin ya kamata, kuma Abunda nakeso dake ki sani shine, kowa a zyri'ar mu yayi na'am haɗi da farin cikin wannan auren, har su kaka zuwaira, kasancewar Dad na buƙatar mai taimaka mashi da kula dashi, saboda irin hidindimun shi, da kuma ayyukan shi, kinga kuwa ita Mom Kubra business ɗinta ya fiye mata tsayawa da kula da Dad, hasalima idan ta sanya ƙafa ta bar ƙasar sai an ganta, gashi taƙi yarda ta zauna dashi acen Istanbul ɗin, saboda haka babu wanda ya soki lamirn auren nan, share hawayen ki ƙawata kiyi farin ciki, babu Abunda zai faru insha Allah in ba alkhairi ba, kuma itama Mom Kubra insha Allah zata yarda kuma ta amince." Ɗan runtse idanu nayi, wasu hawayen na daɗa zirara a idanu na, Hafsat ɗin ba zata taɓa fahimta ta ba... Wayata da take ajiye bisa gadon ce ta ɗauki ruri. Number ɗin Sir Salim ce naga tana kai kawo a bisa fuskar wayar tawa. Kafin in kai hannu Hafsat ɗin ta kai hannun ta ta ɗauko gami da duba mai kirana, saboda ita a zaton ta ko Ya Ameen ne, saboda tin da suka shigo da Haj Kubra bata ƙara ganin shi ba, amman dai ta kula yana cikin gidan. Kallon tuhuma ta bini dashi tana mai miƙo mani wayar. Tashi nayi zaune sosai, sannan na amsa ina mai matsawa na jingina bayana da makarin gadon. "Assalamu Alaikum" Na faɗa cikin siririyar muryar da tasha kuka ta gaji. Daga ɗaya ɓangaren akan amsa mani cikin muryar da ayanzu nafi muradi da inji ko zan samu sauƙin Abunda nake ji cikin zuciyata "Wa'alaikumussalam my Jaaan, ina kika shige ne haka? Naje Sunkui ance kun tashi, gashi ina ta kiran wayar taki, sai yanzu Allah ya sanya ta shiga" Ya amsa mani cikin salon kwaikwayon murya ta. Ɗan murmushi nayi kaɗan har sau tina ya fita haka, sai kuma na shiga ce mashi. "Sir Ina yyini" "Ba zan amsa ba, sai kin faɗa mani kina ina ne haka?" "Please Sir answer me First" Na faɗa nima cikin ƴar shagwaɓa, a ƙoƙari na na in manta damuwar da nake ciki. "Lafiya Lau Jaaan, baki ko nema na for Godsake, haka akeyi?" Shima ya faɗa cikin barkwanci irin nashi, har ina iya jiyo sautin murmushn shi. "Yauwa Sir, Ya labarin makaranta?" "wayo kike son yiman ko? Ki faɗ aman kina ina? An koma makaranta ɗaukar ki ma naje yi na tarar bakwa nan" Cikin ɗan zullumi da faɗuwar gaba nace mashi "Abuja" da mamaki yake sake tambaya ta. "Abuja kuma?" "Cen kuka koma? Gaskiya Jaan na gaji hakanan, su Abba zasu zo ayi magana, in ɗauke ki kawai in huta da wannan jan ajin Naki" Ƴar dariya na saki ina mai cewa "haba dai Sir, sai kace ƴar babyn roba? Wai ka ɗauke ni" Na ƙarshe ina mai sakin dariyar da bansan nayi ba. Idan una ne suka sauka akan Hafsat dake ta faman bi na da kallon tuhuma, fuskar nan tata tamau. Maida hankali na nayi akan shi, jin yana cewa "To me ai you are a baby kid, kinga kaman babyn robar ce, yanzu dai ki faɗa mani inda kike insha Allah gobe zan zo mu tafi makaranta" "Nooo Sir, na hutar da kai, yanzu ina inda ba wahalar samun mota, don haka zan taho insha Allah ko zuwa jibi haka, ko nan da kwana uku" "To ban yarda ba" Ya faɗa kai tsaye cikin ɗan ɗaure murya irin serious ɗin nan. "Sorry Sir, Please akwai ƴan abubuwan da zan kammala ne Shiyasa.." "To zanzo in taya ki, kinsan bana so ma kike wahala" Cikin ɗan kaɗuwa na shiga bashi haƙuri akan ya bari idan mun koma zamuyi magana, tubure mani da yayi lallai fa shi sai yazo ko ya turo su abba kawai ayi a wuce wurin, Ammi ma ta matsa, tace ta ƙagara ta ganni a matsayin suruka wai. A haka muka rabu akan cewa anjima zai sake kirana, tinda yanzu ana samu na, ai yanzu fa sai na gaji da wayar shi. A hankali na sauke kan wayar, ina mai ɗan bin hafsat da kallon gefen ido. "Dena satar kallo na malama, bayani zakiyi mani wanene wannan mutumen wai wani Sir Saleem ko?" Ta faɗa cikin gyara zama, har yanzu fuskar ta a ɗaure take. "Malamin mu ne, shi ne wanda maganar ahi take akai na" Na faɗa mata kai tsaye nima, ba tare da damuwar komai ba, jin zata kawo mani wata magana daban kuma. "Bamu san da zancen ba mu, kin dai san ba'a nema kan nema ko?kuma kinsan babu kyau me yasa zakiyi haka? Me yasa zaki kula wani bayan kinsan akwai wanda ke son ki tin tini? Da mamaki na kuma kallon ta. " Wa kenan?" na tambayeta nima ina mai ɗan ɗaure fuska. Ba shayin komai tace mani "Ya Ameen ɗinmu, na dai san duk nagartar shi wannan ɗin bai kai Yayan namu ba, kuma kin sani wallahi saidai in wulaƙanci kika shirya yi mana, duka yanzu shi wannan ɗin watan ku nawa tare dashi? Da har zaki wani ce maganar shi na akan ki? Yaushe akayi haka kuma?..... " Katse ta nayi da cewa " Shi yayan naku ne bai samu shiga ba, beside ma bana tunanin miskilan ci zai bar shi yin soyayya, balle har ya soni, bayan ni dake mun sani sarai irin tulun ƴan matan da ke cewa suna sonshi masu aji da kyau, bai soau ba ma balle ni? Kada ku yaudari kanku mana please" Da mamaki Hafsat ɗin ke bina, yaushe na sauya har haka? Kodai soyayyar Wancen ta rufe mani ido, saidai duk da ba ganin shi tayi ba, Tasan har ga Allah da wuya ya iya zarta ɗan uwan nata. Suhan yaushe kim zama haka?mu a haka muka gani muka ce muna so, kuma ba tin yanzu ba Ya Ameen ya shigo da buƙatar auren ki, tin lokacin da akace mu fidda mazajen aure, shi kuma ya ce ke yake so, wallahi kiji na rantse" Da mamaki na ɗaga ina kallon fuskar Hafsat ɗin da take cike da gaskiya da kuma ƙwarin guiwa. Ɗan ware idanu nayi akan ta ina mai cewa "Hafsat ya she kika zama ƴar campaign haka ne ban sani ba?" "Suhan ba maganar Campaign, ki yadda dani, kowa ya san fa Ya Ameen na sonki har ranshi, kawai dai bayyanawa ne baya son yi, gudun ja maku matsala a wancen karon, kuma lokacin bikin namu, kowa ya shaida haka, kawai dai su Dad ne suka ce ya bar maganar zuwa wani lokaci" Ta faɗa tana mai kamo hannuwa na duka gami da marairaice mani, ta koma kalar tausayi harda wani karyar da kai gefe. Zare hannuwa na nayi cikin wani tashin hankalin, ina mai sauka daga bisa gadon na shiga takawa a hankali Uwa ga jikin tagar. Hannu na sanya gami da yaye dukkanin labulen da ya sha ƙawa jikin tagar zuwa gefe, wata sanssanyar iska ce ta kaɗa ni a fuska, bansan lokacin da na shiga sauke numfashi da ajiyar zuciya ba a hankali,a hankali. Itama Hafsat ɗin, tasowa tayi daƙyal tana mai dafa kafaɗu na a hankali ta shiga cewa "please Suhan ki amince damu, ki bamu wani yanki a cikin damar ki, insha Allah zaki faɗa da bakinki cewa babu wanda ya iya nuna soyayya sama damu please" Na buɗe baki ne da niyyar in ce mata wani abu, sai muka jiyo hayaniya ana shigowa sashen namu, ga dukkan alamu dai an gama walimar ne, da yake yau zasu tattara su wuce Gidan Alhaji Auwalu, zuwa gobe su wuce Katsinar. Juyawa nayi a hankali ba tare da nace mata komai ba, na shige toilet ɗin, haɗi da kunna fanfon sink na shiga watsa ma fuska ta ruwa, ko zan farfaɗo daga dogon suman mamakin da na tafi. Itama ganin hakan, a hankali ta shiga cira ƙafa tana mai barin ɗakin nawa, zuciyar ta Ƙunshe da abubuwa, tayi ma kanta alƙawarin taimaka ma Ya Ameen ɗin wajen kafa kanshi ga Suhan ɗin, tinda ta kula shi yana yin soyayyar tashi ce take haka, ga kuma miskilanci da rashin ba soyayyar muhimmanci. ********* Ina zaune gefen gado, har yanzu maganar Hafsat ɗin baya bar cikin zuciya ta ba, ga shi ina ta tunanin to wai zaman ne zanyi a cikin gidan ne? Me zan tsinta banda tashin hankali? Kawai gobe in wuce in komawa ta school kawai, saidai wata zuciyar na tunatas dani cewa "Hakan zaki tafi ƙibar umman ki a cikin irin wannan halin?" "Huh" na faɗa a hankali ina mai fesar da isa daga baki na, gami da ɗan girgiza kai na a hankali ina mai cewa "Ai haka ta zaɓa, ban da yanda zanyi da ita" Turo ƙofar akayi aka shigo, Hajiya Zainab ce gaba, sai Hafsat dake binta a baya, tana cira ƙafa daƙyar. Tashi nayi tsaye saboda girmamawa, har saida ta zauna gefen gadon. Ga mamaki na, kamo hannu na tayi ta zaunar dani gefen ta. Sai kuma tayi ma Hafsat alama da ta zauna. Tini jini na ya tsinke ya fara gudu, kar dai ace Hafsat ɗin taje ta faɗ ambata wata kalma ne akan maganar da mukayi da ita yanzu, duk da nasan ba halin ta bane ba. Katae mani zancen zucin da nake Naji tayi wurin cewa "Suhana mun gama komai zamu tafi gida yanzu, saidai ina son inja hankalin ki kaman yanda naja na Umman ki, kuyi ta haƙuri dai, auren nan muƙaddari ne, kuma muna fatan Alkhairi ne insha Allah, naga kina kuka ɗazu akan Abunda Kubra tayi, to ina so ki sani, insha Allah itama zata koma kan hanya mafi daidai, zata gane zuwan Maryama gidan nan alkhairi ne, kuyi ta haƙuri da duk abunda zaku gani, insha Allahu mai wucewa ne, kada ku biye mata duk Abunda zata yi Nidai ina mai daɗa ƙara jan hankalin ku akan haƙurin nan" Tana mai gama faɗar haka ta miƙe, haɗi da cema Hafsat "Taso muje Hafsat" Miƙewa tayi, ba tare da ta ko kalli inda nake zaune ba itama, ga dukkan alamu taji haushin abunda nayi mata ɗazu kenan, na ƙin amsa ma maganar Ya Ameen da nayi, aikau ta gaji ta sauko wallahi, ni ina ni ina bala'n hajiya Kubra? Ai da sai ta sanya mashi ta tsire mu a cikin gidan. Haka suka fice ina kallon su, a hankali a hankali na jiyo sautin hayaniyar na raguwa, har zuwa lokacin da naji gidan ya sake ɗaukar tsit. Zamewa nayi a bisa gadon na kwanta rigingine, hannuwa na kaf dasu nayi amfani wajen tallafe kan nawa. Ƙarfe shidda daidai Umman tawa tayi sallama a ɗakin nawa. Ta sake wanka tayi shar abubta, sai walwali takeyi kaman ta fara amarcin ne. Janye idona nayi akan ta, ina mai tashi zaune haɗi da gaida ta. Kai zaune tayi gefen gadon tana mai amsa mani gaisuwar da nayi mata, sai kuma ta buƙaci in natsu da zamuyi magana. Hankali na duka da natsuwa ta na tattara akan ta, ina mai wasa da hannuwa na, fuska ta har yanzu jajur take saboda tunani da kukan da nasha bayan tafiyar su Hafsat, har yanzu zuciya ta ta gaza natsuwa ko amsar wannan auren da zamu iya kiran shi na ƙaddara akan mahaifiyar tawa. Ga wani zancen kuma da yake neman kunno mani kai ya dagula mani lissafin a, Ya Ameen ɗin namiji ne har da rabi, ya zarce mace ɗiya mace ta kalle shi ta ƙi amsa tayin soyayyar tashi, ko da ya faɗa mani ban kai da gasgata ba, sai gashi ɗazu Hafsat ɗin na ƙara tabbatar mani, na tabbata ba zata taɓa yiman ƙarya ba, kenan in haka ne, Al'ameen ɗin shine na farko da ya fara bijiro da maganar auren nawa kenan? Gabaki ɗaya zuciya ta ta cunkushe, a ma'auni ɗaya nake aza Ya Ameen ɗin, da Sir Salim, saidai na gaza banbance wanda yafi nauyi daga cikin su. Muruar Umma na tsinkaya lokaci guda tana mai cewa "Suhan tunanin me kike yi ne?" Da mamaki nake kallon Umman tawa, kirana da Suhan da tayi kai tsaye yau, hakan ce ta sanya ni maida hankali na akan ta. "Nasan har yanzu ba wai kin amince da aure na bane, kuma nasan zaki dinga yi mani wani kallo na daban, wala alla kema ki ambata ni da mai kwaɗayi ko mai son abun duniya, ko wadda ta shigo gidan Alhaji Mustapha da wata manufa ne, Amman ina so ki sani duk ba haka bane, zamana a gidan nan yana daga cikin ɓari na ƙaddara ta da kuma ke tin bayan aurena na mahaifin naki, da ƙaddarar da ta sanya ya rasu, da ƙaddarar da ta sanya nabar gidan namu da kuma ƙaddarar da ta sanya na haife ki a ƙauye, da ƙaddarar da ta sanya ni zama a gidan nan a karo na farko a matsayin ƴar aiki, duk kuwa da ba aikin ne takamaimai zamana a wancen lokacin ba, sai gashi ƙaddarar ta juye ta zama wata aba daban a yanzu. Zan ja hankalin ki ne akan haƙuri, ki bani haɗin kai, inaso ki sani nan ba da jimawa ba, zaki san ko ke wacece, zaki san ko ji wacece, Amman ina so ki sanya zakiyi zama ne anan gidan, zaman haƙuri da dukkanin Abunda zai je ya dawo, ko me kika gani ki kauda idanun ki, ke ba wadda ta cencenci wulaƙanci bace ga dukkan wani mutum dake rayuwa a ƙarƙashin rufin gidan nan bace. To saidai akwai wani abu ɗaya. Muhammad Al'ameen, kada ki kuskura in sake ganin ki dashi tsaye ko kuna magana, wannan alaƙar na datse ta, indai ba kina so wani sabon abu ya kuma bijirowa bane nan gaba, kwanaki mahaifin shi sunzo sun same ni akan maganar auren ki dashi, to saidai ban bada dama ba, saboda wasu dalilai na, inaso ki sani, mahaifiyar shi ba zata taɓa lamuncewa ba, kina da mai sonki da gaskiya shine Saleem, na bada dama ya turo mahaifn shi a koda yaushe ne, Amman maganar Al'ameen ban yarda da ita ba, bana kuma jin zan yarda da ita koda anan gaba ne kuwa." Cikin matsanancin furgici na ɗago ina mai kallon Umman tawa, to saidai ba bakin yi mata magana a yanzu, yanda nake jin zuciya ta na halbawa, ga kuma wani irin abu dake taso mani cen ƙarƙashin zuciyar tawa. Ina ji ina kallo ta miƙe, har ta fice ɗakin ban iya ce mata komai ba, bana da wannan ƙwarin guiwar, bana da wannan zarafin. Hawaye na sulalowa a saman fuskn tawa, da bansan ko na menene ba, Nidai nasan bana jin komai dangane da Ya Ameen ɗin, to saidai kukan ne nakeyi? Gashi umman t a mani albishirin zanin ko ni ɗin wacece, kuma ta faɗa man ni ba wulaƙantatta baceba, to mi ya sanya ni kuka? Minene na damuwar kaina? Tattara dukkanin kayan makaranta ta na shiga yi, ba zan zauna a gidan ba ma, balle har in shiga wani hali na ɓacin rai, saidai wani ɓangaren na zuciya ta, Ya Ameen shine mutumin da yayi mani kaka gida a cikin ilahirin zuciyar ba tare da na san dalili ba. Ya Allah ka dafa mani a al'amari na, ya Allah ka dubi maraici na, ya Allah ka tallafa mani a kowanne yanayi. ************* Kaman an masu mutuwa, gabaki ɗaya ilahirin hankalin su baya cikin jikin nasu, Mom kuwa kaman zata fashe, sai faman jinjiga ƙafa da takeyi tana daga zaune, Su Hajiya Sa'a tuni suka fice suka bar gidan, ba yanda ba suyi ba da ita, akan ta saurare su, amman fir taƙi ko kula su, sai kai komo takeyi, da ta gaji ne ta koma ta zauna. Gashi tin ɗazu taje kiran Al'ameen ɗin yaƙi ɗaga wayar, me yake nufi ne? Saudat ta aika akan taje ta gano mata ko yana ɗaki, zuwa tayi ta tadda baya lafiya, komawa tayi ta sanar da Mom ɗin tasu, Amman saboda bala'i da yanda take ganin hadda hannun shi akan wannan cin amanar da akayi mata ya hana ta ko taje ta gano shi, jira ma takeyi ya samu sauƙi ta huce haushn ta akan shi. Shi yanzu har ya zaɓi ƴan aiki akan ta? Ashe duk ƙaunar da suke ma juna ta tashi a banza, ya fifita ƴar aiki da ɗiyar ta akan ita da ta zuƙunna ta haife shi.. ***** Ƙarfe huɗu Ya Ameen ɗin ya farka, da salati ɗauke a bakin shi, sai kuma ya ɗaga hannun shi da ƙarin ruwan ya ƙare Bilal ya cire mashi Amman bai zare canula ɗin ba, bisa kanshi ya ɗora shi yana mai dafe kanshi haɗi da ƙoƙarin tashi zaune. Bilal dake zaune gefe yana latsa system ne ya taimaka mashi ya zauna, yaji daɗin ganin jikin abokin nashi da ƙarfi ba kaman ɗazu ba. "Ina Mom?" Abunda ya fara faɗa kenan. "Tana part ɗinta" Bilal ɗin ya bashi ansa. "Zanje in ganta Bilal" "Nooo Friend, yanzu tana cikin wani hali, ka bari sai ta huce sannan, ba zaka taɓa fita ba a wurin ta, zata ga kaman da kai aka haɗa baki, masalan ma da baka sanar da ita ba" "Bilal bana jin daɗin Abunda takeyi a cikin taron mutane....." "Dr. Yace ka daina tunanin komai friend, zaka jawo ma kanka wata matsalar ta daban, ka bari sai zuwa dare muje mu same ta" Komawa yayi ya kwanta ba tare da ya kuma cewa komai ba. Saii kuma ya tashi a daddafe ya shige toilet ya ɗauro alwala duba da yayi lokacin an kammala sallah. Bayan ya kammala ne ya koma ya zauna gefen gadon, yaji sauƙi sosai, masalan ma wannan sallar da ya ƙara yi. Tashi yayi gami da cire kayan nashi ya sanya bathroob ya shige toilet haɗi da sake yo wanka. Bilal dai bai ce mashi komai ba, sai a aikin shi da ya cigaba da yi, wanda wata kwangila ce Federal Goverment ta basu aproval akan ta, shine suke ta faman aiki a kanta. Shiryawa yayi cikin ƙananan kaya, samfurin ƙasar Holand, kayan sun amshe shi matuƙa, sai agogo da turare da ya fesa. Fuskar nan tashi fayau, kaman wanda ya shekara yana ciwo, baƙin sajen dake fuskar shi ya sake fitowa raɗau akan fuskar, saidai babu wata walwala ko annuri a jikin ta, kaman wanda aka sanar dashi mutuwar kowa nashi. Falo ya koma ya zauna, haɗi da kunna dstv ɗin dake falon. Duk da kallon yakeyi , amma Sam hankalin shi ba'a tattare dashi yake ba, so yake yayi tunanin abubuwa da dama. "Suahana, yanzu a wanne hali take? Umma, itama a wanne hali take? Mom...... Ɗan tsoki yaja yana mai tashi ya shiga zagayen falon, hannayen shi goye a bayan shi. Da gudu yaji an shigo haɗi da ruƙunƙune shi ta baya. Cikin hanzari ya juya domin ganin ko wacece, saboda ya san duk duniya yarinya ɗaya ce keyi mashi hakan. Ilai kuwa ita ce. "Afnan! Yaushe kuka zo? Ina Aunty Feena?" "Ɗan ja kaɗan tayi tana mai ƙare mashi kallo " Yaya are u sick? Naji jikinka da ɗan zafi, me ya same ka? Ta faɗa tana mai bin dukkanin jikin nashi da kallo, sai kuma ta ɗora idanun ta akan fuskar shi. Kamk hannuwan ta yayi dukkanin su, yana mai ja ta zuwa bisa Sofa. Zaunar da ita yayi yana mai zama shima. "Afnan am fine, yaushe kuka zo?" "Yanzun nan yaya, ko cikin gidan ban shiga ba, Aunty Feena ta wuce ciki, na ƙagara in ganka ne" "Afnan yanzu ba lokacin hutu bane, ya akai na ganku kuma?" "Yaya Dad ne yace muzo yau, tin jiya ya faɗa mana, so tin jiya ma da daddare muka taso ai" Da mamaki yake binta da kallo. "Me ya faɗa maku? Yace anyi wani abu ne?" "Kai yaya Wannan duk tambayar ta mecece? To nidai banji Aunty Feena tace komai ba, kawai dai tace in shirya zamuje gida ne cikin gaggawa" ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke yana mai cewa "Afnan Go inside am coming now insha Allah" "To Yaya am waiting for u" Ta faɗa tana mai Miƙewa ta fice. Ƙarfe takwas Alhaji Mustapha yayi parking a harabar gidan nashi. Mai gadi da dukkanin sauran ma'aikatan maza suka taso suna yi mashi barka da zuwa. Suma mamakin shi suke yi, duk da sunsan tsaye yake a gidan nashi, to saidai ba suyi tunanin zai iya ƙara wani auren ba, duk da har yanzu basu kai ga sanin wacece amaryar ba, domin ba'a basu damar hakan ba, tin bayan dai da suka gama jera komai aka sallamesu har matan ƴan aikin kuwa. Kai tsaye sashen nashi ya shiga, bayan ya ɗaga waya ya kira Al'ameen. Saida suka jira shi ya gama wankan, sannan ya umurce su da su ɗungumo har sashen Hajiya Kubran kuwa, harda Bilal. Gaban su dai faɗuwa yake yi yayin da suka bishi a baya, shi kau da yake namiji ne tsayayye ba tare da shayin komai ba ya durfafi sashen da uwargidan nashi yake mallakin ta cikin takun shi irin na tsayayyn namiji a faɗin duniyar..... A falon suka tadda su jigum jigum, har Feena da Afnan ɗin da uwar ta gama karanta masu komai, duk da hankalin su ba wani tashi yayi ba, a ganin su ai hakan ba wai abun tada hankali bane, ko ba komai Mom ɗin ta samu abokiyar zama wadda zata na kula da komai idan bata nan. To saidai uwa da ƴaƴa sai Allah, ganin yanda Mom ɗin tasu ta tada hankalin ta, da bala'n da take ta faman yi tin ɗazu ya sanya jikin su sanyi. Bama kaman Feenar da duk ta fisu hankali da sanin komai, ko ba komai ta mallaki hankalin kanta, kuma Tasan halin Mom ɗin tata, tana gudun Abunda zai je ya dawo masalan akan ƙanin nata mai bi mata da ta fuskanci shima Mom ɗin tasu cike take dashi. Waje ya samu ya zauna, duk suka shiga gaida shi, amsa ma kowa yayi cikin fara'a da sakin fuska. Ita kuwa Afnan wajen da yaje zaune ta ƙara sa3ta zauna haɗi da ɗora kanta bisa jikin shi, tana mai ɗan rungumo shi take faɗin "I missed u Dad" "I missed u auta" Ya faɗa shima cikin jin daɗin zuwa kiran da yayi masu. Nasreem ce ta ɗan gangaro da ɗan Gudu irin nata, sai ya sanya hannu ya cafe ta, yana mai ɗaga ta sama yake mata wasa "Afnan je ki kira mani Umman Suhan" Ya faɗa ba tare da ko ya kalli ɓangaren da Hajiya Kubran take zaune ba tana ta zuba isa. "To Dad" ta faɗa tana mai ficewa. Tin da su Al'ameen ɗin suka shiga falon take aika mashi da wani irin kallo. Nan fa hankalin shi ya ƙara tashi, Amman da yake namiji ne, sai ya aro dakiya, juriya da natsuwa ya yafa ma kanshi. Bai ma ko sake kallon sashen da take ba, saboda guje ma irin kallon da take binshi dashi. Shima Bilal yana lura da ita, Amman bai ce mata ƙala ba, har su Afnan ɗin suka shigo tana riƙe da hannun Suhan ɗin kanta a ƙasa. Shigowar Umman ce ta ja hankalin kowa dake falon ya maida hankin shi kanta. Sanye taje da atamfa, anyi mata ɗinkin riga da zani. Sai hinabi a kanta, fuskar ba kwalliya ko ɗis, sai zallar kyau da Allah ya mallaka mata. Cikin taku irin na kamala take tahowa har zuwa bisa wata kujera mai zaman mutum ɗaya da tafin kusa da ita. Zama tayi bismillan ɗauke a bakin ta, hakan ne ya ƙara ƙular da hajiya Kubran, ya faranta ran Alhaji Mustapha da Bilal da abokin nashi. A hankali ta shiga gaida Alhaji Mustaphan cikin girmamawa, sannan ta maida akalar gaisuwar tata ga uwargidan tata. Fuskar nan tata babu wani abu dake nuni da alamun tsorata ko fargaba ko ɗin a cikin zuciyar Umman. Duk da Hajiya a kubran bata amsa ba, sai a wani wulaƙantacccen kallo da ta bita, sai bai da wata ba, ta juya wurin da Feena ɗin take zaune, haɗi da gaida ta ba tare da fargabr komai ba, haɗi da yi mata sannu da zuwa. Sai abun ya ba Feena kunya haɗi da mamaki. Ya matar da ta girme ta nesa ba kusa ba, gashi kuma tana matsayin matar mahaifin ta zata gaida ta? Lallai ba mai zafi baceba, ba irin wadda Mom ɗin tata ke faɗi bace, bata fahimce ta bane, amman ko a yanayi da yanda fuskar ta ta nuna ita ɗin ba mai zafi bace. Kowa dake falon ya gaida Umman tawa, banda Saudat da Nihal suma da suke bin mu da wani irin kallo na tsana. Nikau da nake zaune cen ƙasa gefen Afnan ta kama hannuna ta matse taƙi saki, nima jikina da hijabi, fuskata tayi luhu luhu, Allah ya sanya lokacin da afnan ɗin ta shiga kirana Salla na gama ba kukanba, saida tayi ihun murnar ta mai isar ta, na jin daɗin gani na, sannan ta faɗa mani saƙon Dad ɗin nasu. Kallon shi gabaki ɗaya da hankalin shi yana kanta, yana kula da yanayin ta, watau tasha kuka kenan bayan wanda yaga ta tanayi ɗazu. Saida Bilal ya zungurobshi sannan ya iya janye idanun nashi a kanta, wanda har Hajiya Kubran ta lura da Kallon da yake yi ma a Suhan ɗin. Gyaran Murya Dad ɗin yayi, yana mai muskutawa ya fara buɗe taro da addu'a Sannan ya fara jawabi kamar haka. "Na tara ku ne anan ba don komai ba, sai don in gabatar maku da abokiyar zaman mahaifiyar taku, daga yanzu wannan itace a matsayin abokiyar zaman Mahaifiyar taku, ina fatan zaku yi mani biyayya wajen bata girman ta, da kauce ma duk wani abu da zai kawo saɓani. Ku sani yanzu ba matsayin ta na mai aiki take ba, matsayin matar mahaifin ku take,kaman mahaifiya take a wurin ku, ku girmama ta kaman yanda zakuyi ma mahaifiyar ku nan da take zaune, sannan ki darajta ta, ga Suhan nan, ku ɗauke ta matsayin ƴar uwa, bana so inga wani banbanci a tsakanin ku, masalan ma ku Saudat Da Nihal, ina fatan zaku kiyaye....... *"Alhaji dakata"* Hajiya Kubran ta faɗa cikin kashin murya, tana mai zaburowa daga inda take zaune bisa Sofar. *"Ni ba abokiyar zaman ta bace, kuma ita ba kaman mahaifiyar ya rana bace ba, ni a wuri na maci amana ce, kuma ina sonka sani daga yanzu har yaumuttanadi ba zan taɓa amsar ta ba a matsayin kishiya, san amshe ta ne a matsayin aiki wadda taje zaune a gudana cikin rigar alfarma ta, tana cin dukiya ta da nufin ta kare kanta daga Raɗaɗin talaucin da take fama dashi tin shekara da shekaru, muddin tana zaune a ƙarƙashin rufin gidan nan nawa, ba zata taɓa amsa sunan matar guda ba, saidai ƴar aikin gida, tinda wannan auren babu Abunda yake cikin shi sai cin amana da mugunta kawai* Ba Alhaji Mustapha ba, hatta Afnan da Feena, Bilal da uwa uba Al'ameen da suke zaune a falon saida maganar tata ta Dakar masu zuciya. Cikin tsananin furgici Al'ameen ɗin ya ɗago kai yana mai ƙure Mom ɗin tashi da idanun ta ya rufe ga kallon gaskiya yake yi. Shi kau Bilal saidai sauke kanshi ƙasa yayi yana mai ɗan girgiza kai, yayin da Feenar take kallon Mom ɗin nata da wani irin kallo kaman ta nutse ƙasa. Ni kau tare da Afnan a lokaci guda muka kai kallon namu a bisa fuskar Umman tawa, domin ganin yanda ta karɓi maganar Hajiya Kubran. Ga ɗin bin mamakin mu, murmushi ne kwance bisa fuskar Umman tawa, har kana iya hango fararen haƙoran ta, a lokaci guda na janye idanuna na maida su kan su Saudat ɗin da farin ciki fal a zuciyar su kaman zasu taka kan jariri.... _Ku godewa Allah fa, nima na fara koyon ƙyuyar typing, tinda kuma kun iya ƙyuyar comment. Sai kuma sati na sama_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~46~* *Aslm Alkm.Fans da fatan duk kuna cikin ƙoshin lafiya. Sabili da yawan ƙorafe-ƙorafe da nake samu daga gareku, da yawan roƙo na, da masu kirana a waya, da masu mani Dm da masu bina Pc akan in taimaka inyi typing, na yanke shawarar baku koda kaɗan ne ba yawa, ba don na kammala uziri na ba, ba don ayyuka na sun koma normal ba, sai don in faranta maku rai, haƙiƙa har kullum masoyi yafi maƙiyi, Rubutun nan dan ku nakeyi, domin jin daɗin ku ne, domin idan babu ku, tabbas fa babu mu, Amman sai wasu daga cikin readers su kasa gane haka, su sun ɗauka idan kace zaka yi rubutu baka da aikin yi ne (Jobless). To inaso ku sani ba haka abun yake ba, kawai dai sa kai ne wanda yafi bauta ciwo. Masu yawan damuna akan nayi typing wannan Page ɗin naku ne har abada, kuyi yanda kuke so dashi. Daga ƙarshe ina mai roƙa ma sister ta lafiya a wurin Allah, ina so kuma ku taya ni da addu'a, duk da nai nasan kuna yi, inaso ku ƙara sosai my fans. Allah ya barmu tare Abadan da'iman. Ina sonku tsakani da Allah. Ngd* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Babu wanda ya katse ta har ta kai aya, haka babu wanda ya tanka har kawo yanzu da falon ya ɗauki shiru. "Kubra ke ba zaki cenza ba ko? A gaban yara kike faɗar irin waɗannan kalaman? Maryam dai matata ce, itama auren ta nayi kaman yanda na aure ki, kuma ba ƴar aiki bace ma a yanzu kaman yanda kika faɗa, Amman wannan ba irin maganar da zamuyi bace a gaban yara, ki kiyaye hakan ko don gaba" Muka tsinkayi muryar Alhj Mustaphan yana mai maida ma Hajiya Kubra maganar tata. Ƙara duƙar da kan namu mukayi ƙasa, yayin da su Saudat jin haushi ji suke kaman su rufe Dad ɗin nasu da duka, zunɓura baki suka hau yi sun murguɗe murguɗen baki. Umma ta dai har ila hazar yanzu bata ce komai ba, sai dai ɗan murmushi da take ta faman yi, babu ko alamun damuwa akan fuskar ta. Ita kanta tasan abunda tayi ba daidai bane, ta sani abunda tayi don Hajiya Kubra ta kira shi cin amana ba laifi bane, kowa ma zai iya kiran shi hakan, muddin yaji yanda abun yake. To saidai bata jin wannan dalilin ya isa daƙile nata dalilin da take dashi cikin zuciyar ta. Alhj Mustaphan yayi maganganu masu daɗi da fa'ida, ya kuma ja hankalin Haj kubran da yaran nata akan su haɗa kansu, baya so su kawo mashi wani tashin hankali a cikin gida, duk wanda ya samu da hakan, zai mugun saɓa mashi. Sannan ya umurce mu da mu tashi kowa ya koma part ɗin shi, yayin da ya buƙaci Hajiya Kubra da Umman akan su su zauna yana da magana dasu. Sannan yace Ya Ameen ɗin kada yayi bacci yana son ya ganshi idan ya kammala da iyayen nashi. Haka muka tashi da niyyar ficewa. "Suhan yaushe ne zaki koma makaranta?" Muryar Alhaji Mustaphan ce ta doki dodon kunne na daidai lokacin da nake ta faman sauri domin barin falon, da nake ji na kaman a ɗaɗɗaure, yawan aika mani da harara da Hajiya Kubran takeyi. "Gobe idan Allah ya kaimu" Na faɗa kaina a ƙasa, bayan na dakata daga tafiyar da nakeyi,ina mai ɗan waiwayawa na kalle shi. "To Allah ya kaimu" Ya faɗa yana mai nuna alamun da in tafi. Cikin matuƙar sakewa kaman kaman yanda yake yi ma yaran nashi. Da hannu ya yafuto ya Ameen da bai kai ga miƙewa ba shi. Inda yake ya isa, gami da ɗan russunawa domin sauraren Dad ɗin nashi. "Kuje ka kai ta tayo shopping ɗin komawa makaranta, zuwa gobe ka maida ta makarantar da kanka, bana so a haɗa ta da driver" Ya faɗa ta yanda ba wanda zai iya jin me ya faɗa, gudun wata fitinar ta daban. A hankali ya miƙe yana mai faɗin "to Dad." Da hannu yayi ma Bilal alamun da suje. Shima a hankali ya miƙe yana mai yima su Dad ɗin sai da safe. "Bilal zamu je mu kai yarinyar cen shopping inji Dad" Ya Ameen ɗin ya faɗa daidai lokacin da suke barin sashn mom ɗin tashi. "Kai bros, kuje kawai wallahi bacci nake ji, ina so in ƙara sa gida ne, Kaga Ummi ba lafiyar kirki" Ya faɗa cikin son kauce ma rakiyar, yayi hakan ne saboda kada ya shiga haƙƙin masoyan. "Muje sai mu sauke ka" "To ai shikenan, ina jiran ku a mota", ya faɗa yana mai amsar key ɗin motar a hannun Ya Ameen ɗin. Yayin da Ya Ameen ɗin ya juya kai tsaye ya nufi sashen su Suhan ɗin. A falo ya tadda ni, tsaye nake na juya baya, hijab ɗita na a hannu na da na riga na fidda tin shiga ta sashen. Zuciya ta cunkushe, bana so Haj Kubran ta ƙara ci ma Ummata zarafi a kalaman ta, in da son samu na ne, ƙafata ƙafar Umman muyi dawowar mu a tare, domin nasan dukkan Abunda Alhaji Mustaphan zai faɗa ma Hajiya Kubra ba wai ganewa zata yi ba. Ya ɗan jima tsaye daga baya na yana ƙare mani kallo. Hannayn shi duka soke cikin aljihun wandon nashi. A hankali ya shiga takawa yana nufar inda nake tsaye. Jin takun tafiya daga bayana, ba ƙaramin tashin hankali da tsoro na shiga ba. A firgice na juyo da niyar kwarara ihu, domin Nidai nasan babu kowa a sashen namu, gashi naji takun tafiya, kuma yanzu na baro ummata Sashen Hajiya Kubra. Cikin azama ya sanya hannu gami da toshe mani baki na duka, yana mai ɗan tallafo ni zuwa jikin sa kaɗan, ganin kaman nayi baya zan faɗi. "Matsoraci ya" Abunda ya faɗa kenan, yana mai bin duka fuska ta, da idanuna da wani irin kallo, da na gaza fassara ko na menene. Ajiyar zuciya na sauke, ina mai ɗan matsawa baya kaɗan daga jikin nashi. Sai kuma na koma bisa kujera na zauna, ina mai dafe kaina da har ya fara sa rawa, tsabar tsorata. Da kallo yake bina har yanzu, ganin bance komai ba, sai kuma ya fara takawa zuwa fita daga falon "Ki shirya ki same ni mota yanzu, zan kaiki kiyi siyayyar makaranta" Bai jira cewa ta ba, ya idasa ficewa daga falon. Nima da kallo na bishi, oooh Ya Ameen, mai hali baya barin halin shi, komai nashi da yake aiwatar wa, cikin miskilanci yake yi kaman ma baya son yi, a hankali na miƙe ina mai zura hijab ɗita zuwa cikin ɗakin domin na duba fuska ta. A mota ya samu Bilal ɗin yana ta faman jiran shi. "Friend ya dai? Hankalin ka yayi gida wajen ummi ko?" ya faɗa cikin ƴar zaulaya da ya kan yi idan ya so, yana mai zama cikin motar, ƙafar shi ɗaya a waje bai kullo ƙofar ba. "wallahi friend tana jin jiki ne, ni ina ma tunani ko gida zan maida ta, domin a kula da ita sosai, nauyi take ji sosai yanzu na jikin ta" "Gaskiya kam Friend, idan kana ganin ba matsala, You can allow her to go, Kaga kai ba isasshen time ɗin zama gidan ke gareka ba" "ehhh kuma....." Ƙarar buɗe motar ne ya sanya su juyawa gabaki ɗaya. Ƙamshin turarn ta ne ya fara yi masu sallama, kafin kyakkyawr ƴar madaidaiciyar zagayayyar fuskar ta ta bayyana cikin motar. A tare Bilal da Ya Ameen suka kalli juna, sai kuma ya Ameen ya janye tashi yana mai gyara zaman shi, gami da maida ƙafar shi cikin motar ya rufo ƙofar motar. Nima rufowa nayi ina mai gaida ya Bilal ɗin, saboda lokacin da muka haɗu sashn Hajiya Kubra bamu samu damar gaisawa ba.. Amsawa yayi cikin sakin fuska, yana mai ɗan zaulaya ta da cewa na ɓoye. Ɗan murmushi kawai nayi mashi, ina mai wasa da yatsun hannuwa na. Sai kuma motar ta ɗauki shiru, na tsawon wani lokaci har muka ƙara sa bakin gate ɗin gidan na Bilal. Ya Ameen na ƙoƙarin danna horn, mai gadi yazo ya buɗe ne Bilal ɗin ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Kaga malam ajiye ni nan, ya isa, kada kuyi dare fa" Dakatawa yayi ba tare da yace komai ba, saida Bilal ɗin ya fita ya zagaya ta ɓangaren shi, sannan sukayi musabaha tare da yin sallama. Nidai kallon su kawai nakeyi, Amman ƙaunar junan sun na matuƙar burgeni, duk duniya banga wanda Ya Ameen ke sake wa da sakin jiji dashi ba kaman Ya Bilal ɗin. Haɗuwar jini, ƙauna, abota daga Allah. Har ya shige gidan muna iya hango shi, rufo ƙofar gidan ce tayi daidai da sauke ajiyar zuciyar Ya Ameen ɗin. Sai kuma Naji yace "Dawo gaba" Da ɗan mamaki nake kallon shi, sai kuma nace "I am comfortable here" "Am not asking you dear, i am jst commanding you, ko kin manta ni ba driver bane?" Ɗan murmushi na sauke, yau ya Ameen ne da yin faɗa har haka? Ji yanda yaje magana kaman ana karanta mashi... Sauke kaina ƙasa nayi, bana da niyyar ma ko motsawa. Ji nayi ya kawai kashe motar. Sai kuma ya jawo wayar shi haɗo da kunna data, yana mai ɗan kwantar da kujerar sit ɗinshi ya cigaba da latse latsen shi. A hankali na ƙure shi da idanuna ta bayan motar, hasken wayar tashi ba mai yawa bane, amman duk d a haka zan iya hango farar fatar fuskar tashi, da take cike da siririn sajen da ya kwata luf akan fuskar, gashin idanun shi Zara Zara, sunyi ma kyawawan idanun shi, masu kama da yana jin bacci kyau, girar nan tashi kaman an zizara mata kwalli, ta tsaru iya tsaruwa. A hankali na janye idanuna, ina mai sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, ganin ya kashe hasken wayar yana mai lumshe idanun nashi tare da ɗora Zara zaran yatsun hannun shi bisa fuskar shi. Mu biyu haka acikin mota mai duhu? Ga Ƙamshin turaren shi, da ya haɗe da Ƙamshin humra ta da sanyin cikin motar ya saukar mani da wata irin kasala. A hankali na ɓalle murfin motar, ina mai ficewa daga cikin motar naja na tsaya, ina mai jingina baya na da ƙofar motar. Duk motsin ta yana kula dashi, ganin ta fice ne ya sanya shi tashi zaune, yana mai sakin ɗan murmushi na gefen baki. Wato ita taurin kai zata nuna mashi, ko kuma jan aji ne irin na mata? Tinda ya furta mata yana sonta, ya kula da wani shasshare shi da takeyi da ba zai iya cewa ga ko na menene ba. Shima ɓalle murfin motar yayi ya fito. Cikin takun shi mai ƙara kada mani gaba ya iso ta inda nake tsaye. Sai kuma ya ja ya tsaya, hannayen shi zube cikin aljihun wandon nashi, idanun shi dukan su bisa fuskar tawa da hasken farin wata ya haske. Sai kuma ya zaro hannun yana mai duba agogon dake ɗaure bisa wutsiyar hannun nashi. Baice mani komai ba, sai naga ya sanya hannu ya buɗe sit ɗin gaban, yana mai nuna mani da in shiga. Sake ɗauke kai nayi, nima bansan menene haka ya shiga kaina ba yau, Amman jina nakeyi a sama, kaman wata sarauniya mai mulki. Ban aune ba naji ya kamo ni duka na, yana mai saka ni cikin motar gabaki ɗaya na, sai kuma ya rufe yana mai danna key. Zagayawa yayi shima ya shiga motar, ba tare da ya ko kula ni ba, ya fizgi motar kaman zai tashi sama, har yanzu fuskar shi bazaka taɓa cewa ya taɓa dariya ba. Har muka ƙarasa daidai super market ɗin ba wanda yace da kowa komai. Ɓalle murfin motar yayi yana mai ficewa kai tsaye, nima ban da wani option illa na fitowr. Gaba yayi ina biye dashi a baya. Na ɓata mashi rai na sani, Amman hakan ba shi ke nuna nice mai laifin ba. Tsabar girma da jin kai nashi, shine abu na farko dake ɗawainiya da Ya Ameen ɗin. Wato shi yana da kuɗi, yana da kyau, yana jin cewa dole abi umurnin shi ko? Ga miskilanci yana fama dashi. A haka har muka ƙarasa ciki. Nuni yayi mani da ɗan ƙeƙen da ake zuba kaya. Alamun in ɗauka in ɗebo kayan. Kenan dai ba zaiyi mani magana ba yake nufi? Ɗan murmushi nayi ina mai wucewa kai tsaye ga zaɓen kayan. Yayin da cikin girmamawa aka sanya aka ajiye mashi kujera ya zauna daga gefen accounter ɗin. To nima dai ba komai na ɗina ba, kasancewr abincin ma ba damuna yayi ba, kuma ni ban iya almubazzaranci ba, nasan idan ummata taga siyayya da yawa ma, faɗa zata yi. Haka na turo keken wani gulu gulu, har zuwa wajen accounter ɗin. Da kallo ya shiga bina, ganin na taho ina turo keke duk da kayan basa da yawa, amman kaman zan kife. Miƙewa yayi yana mai bina da kallon tuhuma. Sai kuma ya ƙara gimtse fuska tamau. "Wuce mu koma" Ya faɗa cikin wata irin murya, da gani har yanzu yana cike dani sosai. Ba musu na sake juyawa, ina mai wucewa. Hannuwan shi naji kwatsam a bisa nawa, yana mai kama handle ɗin keken. A hankali na zare nawa ina mai ɗan ja da baya. Me ke damun shi ne wai? Ɗabi'ar turawa na neman yin tasiri a Al'ada da addinin nashi. Gashi dai mutum mai addini, ga yawan ibada, Amman bai ɗauki haɗa jiki dani ba a matsayin komai. Ji na da yake yi kaman Afnan, ai ni ba Afnan ɗin baceba. Kenan ma yana ganin don Mahaifiyata ta auri mahaifin shi hakan ke bashi lasisin haɗa jiki dani a koda yaushe kenan? Ban ankare da har yayi nisa ba, sai hango shi nayi cen nesa dani. Yana ta ɗaukar abubuwan amfani cikin salon shi mai ban sha'awa Haka na cigaba da bin shi, har yanzu bai ko juyo ya kalli inda nake ba. Ba ra'ayi na ko zaɓi na yake bi ba, saidai na kula dukkan abubuwan da yake ɗauka masu matuƙar amfani ne. Har ya gama ya cika keken taf, har wasu suna zubo wa. Haka na sake bin shi har teburin accounter. ATM card ɗinshi ya miƙa masu, zasu, zasu cura ta Pos Sun matuƙar yi mashi discount, saboda Alfarmar dake gareshi a garin. Sannan aka zuba mana su sit ɗin baya. Har yanzu bai ko ceman ƙala ba, ya shiga motar. An cika sit ɗin baya, ba damar jan magana. Hakan ce ta sanya ni buɗe sit ɗin gaban na zauna, nima ina mai basarwa tare da shassharewa. Zama a kusa dashi ko a tare dashi, ba ƙaramin abu yake jaza man ba. Kuma ni ba wai zan iya cewa ga abunda nake ji ba. Haka muka shiga tafiya zuwa gidan babu mai kallon wani. Saidai lokaci zuwa lokaci na kan muskuta in gyara zama, daga baya ma sai na jingina kaina jikin makarin kujera ina mai ɗan lumshe idanu. Kaman ance in buɗe idanu na, idanun nashi na bisa fuskar tawa tar dasu, bai ji kunya ba, kaman yanda bai ɗaga idanun nashi ba. Sai nice na janye fuska ta, ina mai maida ta bisa titi ganin yanda yake tafiya a hankali kaman wanda yaba so mu isa gidan da wuri. Mai gadi yayi ma horn yaje ya buɗe mana, har muka sulala cikin gidan ba wanda ya tanka ma ɗan uwan shi. Fitowa mukayi mu duka. Ganin ya zagayo ta inda nake ne ya sanya nayi tunanin ko kayan zai fiddo mani ne. Miƙo mani makullan motar naga yayi, sannan yace "Idan kin gama kwashe kayan ki rufe mani motar, ki shirya da wuri da safe Dad yace in kaiki kamarantar da kaina. So kun katse mani ayyuka na, bana so kiyi keeping ɗina delay ok?" Amsa nayi ina mai cewa "To yaya" Sai kuma Kunyar abunda nayi mashi ta shiga kama ni. Mutum ne mai ƙoƙarin kyautata ma duk wani wanda Allah ya haɗa shi zama dashi. Da kallo na bishi, ganin ya juya ya nufi part ɗin Dad ɗin nashi, ya bar mani makullan motar a hannu na Ya Ameen mutum ne mai matuƙar sauƙin hali. Miskili ne, Amman yana jin haushn kiyi mashi miskilanci. Da kallo na kuma raka shi. Har gobe na rasa abunda zance yana burgeni tattare da Ya Ameen ɗin, saidai zan iya cewa shine mutumen guda da ko bacci nakeyi tunanin shi baya saki na. Har ya shige part ɗin idanu na suna a kanshi, a hankali na saki ajiyar zuciya ina mai fara sauko da kayan zuwa ƙasa sannan na kulle motar. Cikin part ɗin namu na nufa, sai kuma naja na tsaya ƙirjina yana dukan uku uku, ko a wanne hali zanje in tadda Umman tawa? Ko ya sukayi da Alhaji Mustapha da Hajiya Kubran? A kasalance na ɗaga ƙafa na shiga takawa a hankali har zuwa cikin part ɗin namu...... _Kuyi manage, wannan ma squizing nayi na maku typing_ *Muna tare My Fans* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~47~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° A falon na tadda Umman tawa zaune, kayan kallo a kunne suke, amman Sam hankalin ta baya kansu, har na ƙara sa inda take zaune na shiga ajiye kayan. Bance mata komai ba, saida na juya na gama shigo da kayan, sannan na zauna kusa da ita ina mai kamo hannuwan ta nace "Umma lafiya kuwa?" Sai a lokacin ne ta ɗan firgita ta dawo hayyacin ta. "Lafiya ƙlau mamana, kun dawo?". Ta faɗa cikin son kauda wani zargin daga zuciya ta. Ɗaga mata kai nayi, ina mai cewa "eh Umma, ga kayan da Ya Ameen ya siyo mani nan" Ɗan kallon kayan tayi kaɗan, sai kuma tace "baki dai takura mashi ba ko?" "a'a Umma, shine ma ya zaɓo da kanshi, wai waɗanda na zaɓa sunyi kaɗan" To Mamana aikuwa an gode, je ki kaisu ɗaki kizo zamuyi magana dake. Sai da gabana ya faɗi jin Abunda ta faɗa, hakanan na daure na miƙe, gami da kwasar kayan na nufi ɗaki. Sai da na kwashe su duka, sannan na koma inda taje na zauna ƙasa ina mai cewa "gani Ummana" "Taso ki hau kujera, banson kina zama ƙasa mamana, nan sashen Umman ki ne" Haka ta faɗa cikin wani yanayi da na Gaza fahimta. Sai da na miƙe na hau kujerar, sannan ta sake kallon a sosai tace "Mamana inaso ki bani aron hankalin ki sosai, akwai maganar da nakeso muyi dake, kinga dai dukkan abunda ya faru, ba sai na faɗa maki komai ba, zama a cikin gidan nan abu ne mai wahalar gaske, masalan ma gareki, da za'a dinga maki kallon agola, kiyi haƙuri da Abunda na faɗa, amman zaman ba zai iya cigaba a haka ba, Shiyasa nake so da ki faɗa ma Saleem yayi gaugawar turo da manyan shi, akan azo a tsaida lokacin biki, shima ba wani lokaci mai yawa za'a sanya ba, saidai kafin hakan dole ki toshe kunnen ki, zaki iya fuskantar matsaloli ta ko ina, maganar Muhammadu ki ajiye ta gefe, ban hana ki auren shi da wata manufa ba, na tabbata babu mahaifiyar da zata samu suruki kaman Muhammadu ta ƙi shi, to saidai abubuwan da zasu iya biyowa baya, da kuma irin matsaltsalun da zaki shiga bayan auren, wannan ne dalili na naƙin amincewa, mahaifiyar Saleem mutuniyar kirki ce, tasan darajar ɗan adam, zaki samu sauƙi zama da ita, shima kanshi Saleem mai ƙaunar ki ne, don haka kiyi biyayya, kibi umurni na, insha Allah zaki ci nasara a rayuwar ki. Ki tabbatar kin gama haɗa komai da wuri don Alhaji yace shi Muhammadn ne zai maida ki, amman ina so ki kula, babu komai tsakanin ku, in banda yana matsayin yayanki a yanzu. Kuma don Allah ina so dukkan Abunda zakuga anyi mana acikin gidan nan ki toshe kunne, ki kauda kai, insha Allahu komai mai wucewa ne" Da idanu kawai nake binta, sai dai na rasa irin fassarr da zan yi ma maganganun nata, ban dai san me ke faruwa ba, illa iyaka dai na tsinci kaina da gangarowar hawaye a saman fuskan tawa. Me kalaman Umma suke nufi, tabbas nasan Saleem shi nake so, shi ne muka shirya Rayuwar aure dashi, to saidai duk lokacin da ta furta ko ambata mani rabuwa da Ya Ameen na kan ji wani irin dafi ya soke ni a ƙahon zuciya ta, bansan dalilin hawayen ba, amman na ta'allaƙa abun da maganar aure, da rabuwa da ita ne data sako mani a yanzun. Girgiza kai na fara yi, ina mai cewa "To Umma insha Allahu, zaki same ni mai biyayya gareki, kuma in Allah ya yarda ba zan baki kunya ba kaman yanda kika buƙata" Ɗan murmushi tayi tana mai shago kaina kaman ƙaramar yarinya, ni kuma ganin hakan sai wani irin kuka yaso ya ƙwace mani. Zamewa nayi ina mai kwantar da kaina bisa cinya ta, share kwalla nake ta faman yi, Amman bana so ta gane, saidai na riga na makaro, tini ta fahimci hakan, saidai bata so wannan hawayen nawa ne ya ɗore har ƙarshen rayuwa ta. Mun kusan kai ƙarfe sha biyu anan zaune, ƴan labaruka take bani masu daɗi, rabon da in samu sake wa da Umman tawa kaman haka, har na manta, ina so in tambayeta yanda sukayi da Hajiya Kubra, wata zuciyar na garbaɗi na, ai ba hurumi na bane, saboda haka naja bakina nayi gum abu ba, kada ƴar fara'r da na samu takeyi mani in kauda ta da kaina. Sai lokacin ne ta miƙe tana mai cewa "Mamana je ki haɗa kayan ki, kinga da wuri zaku tafi, kada ku tafi kuma kina jin bacci. Da haka muka miƙe ina yi mata sai da safe, kowa ya shige ɗakin shi, bayan ta kullo ƙofar shiga falon. **************** " Wai ni kuwa kunsan Abunda ke faruwa ne a cikin gidan nan kuwa?" Mama saude ta furta cikin tsabar mamaki. Suna zaune su duka ma'aikatan a ɗakin mama talatun da bata lafiya duk sun shiga gaida ta, sai kuma aka buɗe sabon babin gulma. Da mamaki suma sauran suka kalle ta " Me ke faruwa ne?" Cewar Uwani da take zaune gefen katifar mama talatun "Maryama mana, wallahi ina jin fa ita ce tayi auren cin amana, ita ce amaryar da Alhaji fa ya aura, wadda kuka ga anyi walima jiya" Cikin tsanann mamaki, firgita da kaɗuwa su duka suke kallon ta. Mama Talatu kuwa bata san lokacin da ta tashi zaune ba, tana mai wara idanu kan mama Sauden "Ke Saude kice Allah kin tuba, wannan ma Hajiya babba ta jiki ai wallahi sai kin bar gidan nan, ba fa ita bace, matar da ba'a san inda take ba ma a halin da ake ciki? Na fa ganta, ita waccen wata mata ce mai kyau, jiya saida na sai jiki naje ganin kwam wallahi, gaskiya ba ita bace... " Cewa Uwanin da har yanzu mamaki ne fal a fuskar tata. " Ke Uwani wallahl azim ita ce, ai na ganta, kwalliya kawai akayi mata, kuma dama kinsan Maryama da kyaun ta, kawai wahala da babu ne yasa kika ga ta koma wata tsohuwa guda, yo Alla na tuba Suhan a ce fa kawai ɗiyar ta, ita kanta Suhanan dududu nawa take? Wallahi dai to ita ce, nima na daɗe ina mamakin yanda wannan al'amari ya juye haka" "Ke Saude kin tabbata da Abunda kike faɗa?" Cewar Mama Talatun da kamar ta sanya kuka take ji saboda tsabar baƙin ciki "Wallahi kuwa shugaba, ai nima nayi mamaki, Amman muna nan daku zakuga Abunda zai biyo baya, ai Hajiya Babba ba kanwar lasa bace ba, hakan ma da dauke zaune wace Alla cika balle yanzu dataci amanar ta? Kuɗi zasuyi mata aiki yanzu don wallahi kunsan ba ƙyale ta zata yi ba sai ta hukunta ta" Mama Talaun bata samu zarafin cewa komai ba, sai a komawa da tayi ta kwanta, jikin ta duk yayi sanyi, ashe hassada ga mai rabo taki ce? To ita yanzu da wane irin ido zata kalli Maryama a matsayin matar Alhaji? Bayan duk irin abubuwan da sukayi mata a baya? Lallai sunyi wauta, sunyi kuskure, baka raina ɗan adam duk min yanda yake, sai gashi su Alhajin bai kalle su yace yana so ba, su da suke cikin gidan, sai ita da ta sanya ƙafa tabar gidan shine yaje ya nemo ta ya aura, lallai akwai dabi, zasu sanya idanu suga yanda Al'amurra zasu kaya, Amman ita kanta tabbas tasha Alwashin ba zata taɓa ajiye makaman yaƙin ta ba, sauƙin ta ma ɗaya da maree bata nan taje ƙauye ai da yanzu ta ɗaga mata hankali. ********* Washe gari kuwa tinda na tashi sallar asuba, ban kuma komawa ba, saida na shirya komai nawa sannan nayo wanka, mai kawai na shafa ma fuska ta, sai kuma na koma na kwanta. Misalin ƙarfe takwas na sake tashi, a gaggauce na wanko baki na, gami da zura kaya na, hijab na sanya har kusan ƙasa, babu kwalliyar komai a fuskar tawa. Ina daga ɗaki na jiyo shigowar shi, suna gaisawa da Umma ta da take falo Saida gabana ya yanke ya faɗi, jiyo muryar shi da nayi, sai Naji duk jikina yayi sanyi, bansan ko menene dalili ba. A haka na jawo akwatn kayan nawa na fito. Yana ɗan zaune bisa kujera, hango fitowa ta daga ɗakin ne ya sanya shi miƙewa yana mai nufi ni da niyyar amsar akwatin daga hannu na. Ja nayi na tsaya, ya masifar yiman kyau, fuskar nan tashi tar kaman wata ɗan daren sha huɗu, da mayatattun idanun shi, masu kama da yana jin bacci yake kallo na, ɗan bakin nan gum dashi kaman an ɗisa mashi, sai dogon hancin da ya ƙara ƙawata fuskar. Ƙananan kaya ne jikin shi, baƙar riga sosai mai rubutun C-Blue a jiki an rubuta *Be my love* sai kuma blue ɗin wandn jeans mai kyau sosai, ƙafar shi soke cikin tomps masu masifar kyau suma C-Blue ne. Kai masha Allah 🤝 Ya Ameen mutum ne mai kwarjini da haiba, ga cika idanu. Hakan ce ta sanya ni sauke kaina ƙasa, kama ni da yayi dumu dumu na shagalta da kallon shi. "Ina kwana?" na faɗa daidai lokacin da ya ƙara so ya amshi akwatin. Ban jira amsawar shi ba, na juya na shige ɗakin da niyyar kwaso wasu. Ɗan bin baya na yayi da kallo, sai kuma ya juya yana mai fita zuwa motar tashi, bayan yayi ma Umma ta sallama. Cikin sakin fuska matuƙa ta amsa mashi, ita kanta tana yi ma yarinyar tata sha'awar Muhammadun, yaro ne nutsattse, ga kamala da girmama na gaba dashi, Sam baya ɗaukar kanshi a wani ko wanda Allah ya mallakawa dukiya har haka. Kwaso kayan na shiga yi ina mai kaiwa bakin motar inda naga ya ajiye akwatin, saidai fa baya wurin bansan ina ya nufa ba. Umma ta ce ke cewa in tsaya ko tea in kurɓa saboda yunwr safe. Girgiza mata kai nayi, Umma ba zan iya cin komai ba, kinga doguwar tafiya zamuyi insha Allah da mun isa zan nemi wani abu inci. Da to ta bini, sabida Tasan dama bana iya karyawa tin da safe, sai ma inyi amai, har bakin motar ta rako ni, daidai lokacin da na hango Alhaji da Ya Ameen ɗin sun fito daga sashen Alhaji Mustaphan Ƙarasowa sukayi inda muke tsaye da Umman, cikin Wasa da ƴar zaulaya Alhajin yake tambaya ta har na shirya? Sauke kaina nayi ƙasa ina mai gaida shi, haɗi da yi mashi godiyar ɗawainiya. Kuɗi masu yawa ya miƙo mani wai in riƙe a hannu na, kasa amsa nayi, har yanzu kaina a ƙasa yake, ina matuƙar jin Kunyar Alhajin tin da cen ma, balle yanzu da ya zama miji ga mahaifiyar tawa. Ɓata rai yayi yana mai miƙa ma Ya Ameen, "Tunda ni ba zata amsa a hannu na ba, gashi kai ka bata idan kun isa cen, ku kula Al'ameen, banda gudu sosai, Allah ya tsare hanya" Gidan baya ya buɗe ya saka kayan nawa, wasu kuma ya zuba a boot, sannan ya zagaya ya shiga, nima sallama nayi ma Umman tawa, miƙo mani wani abu tayi a cikin keda, ina kyautata zaton dai kaza ce gasassa, "amshi wannan kunci a hanya, tinda kin ƙi tsayawa ki karya" amsa nayi, jikina a matuƙar sanyaye sannan na shiga motar tana mai ɗaga mani hannu har muka fice daga gidan, sannan ta juya ita da Alhajin suka nufi sashen nata. "Ba wanda ya tanka ma wani, sai a kunna ƙira'ar sudais yayi a hankali a hankali ƙira'ar ke tashi, jawo hijab ɗita nayi na rufe fuska ta, wani irin bacci ne ke fizga ta, ga sautin ƙira'ar da yake ratsa ni, ina mai nishaɗantuwa, jingina kai na nayi jikin kujerar, wani irin bacci na fuzga ta. Ban san lokacin da baccin ya kwashe ni ba, haka shima bai san yanda akayi ba, sai gani yayi na gyara zama na, ina mai sauke kaina bisa ka faɗar shi da take kusa gani. Ɗan waiwayowa yayi yana mai ƙare mani kallo, sai kuma ya saki murmushi, ganin da tayi bacci na nakeyi bilhaƙƙi da gaskiya, ba tare ma da na san na kwanta bisa jikin nashi ba. Mun kusan tafiyar awa guda waya ta ta ɗauki ruri, a hankali na buɗe idanun nawa, kina kwance sosai bisa jikin mutum ya sanya ni ɗan wara idanu na, ina mai tashi zaune, kunya ta baibaye ni, wai ashe bisa jikin shi nake baccin, haba gaske naji baccin yayi daɗi, ga kuma wani ni'imtaccen ƙamshin turare da yake dokar mani hanci na. Bai ko kalli inda nake ba, nayi tsilli tsilli dani, kaman in buɗe motar in fice saboda kunya. Sunan Sir Saleem da nagani yana yawo a saman fuskar wayar, ya sanya na saci ɗan kallon shi haka kaɗan. Har wayar ta katse ban ɗaga ba, na gaza saboda wani irin kwarjini da Ya Ameen ɗin yayi mani, ga Kunyar shi, wai yau nice kwance bisa jikin shi ina bacci. Wayar ce ta sake ɗaukar tsuwwa, kallon wayar kawai nakeyi ina tunanin ta ina ma zan fara ɗagawa, kada yaga kaman naci mashi fuska ne, ina amsa wayar wani a gaban shi. "Ki amsa mana" Naji ya faɗa ba tare da ya ko kalli inda nake ba, hankalin shi da fuskar shi na akan titi. A hankali na ɗaga ina mai karawa a kunne "Assalamu Alaikum" Na faɗa a hankali, daga cen ɓangaren ya saki wani sanyayyen Murmushi, sannan ya amsa mani da "Wa'aikisalam my Jaan, kina ina ne haka ina kira baki ɗagawa?" "Ina hanya Sir" Abunda na iya faɗa kenan "Wow my dear, shine baki jirani inzo ba, kika taho? Allah dai yasa ba motar haya kika hawo ba?" Ya faɗa cikin son ƙarin bayani. Sai da na kuma satar kallon Ya Ameen sannan nace "A'a Yayana ne zai kawo ni" "OK tou zan jira ki insha Allahu, sai kun iso, take good care my Jaan" Yana gama faɗar hakan na latse wayar na kashe, sai kuma na ɗan juya na kalle shi, bai ce man ƙala ba, daidai lokacin da muka isa Kaduna, naga ya ɗauki wata hanya ta daban. Ƙofar gidan wani abinci mai matuƙar kyau naga mun tsaya, bai ceman komai ba, ya ɓakke murfin motar ya fita, sai zuwa cen kuma gashi ya dawo, ya ɓangaren da nake zaune ya zagaya gami da buɗe mani ƙofa yana mai cewa "Fito muje" Ban mashi musu ba, saboda bana iyawa, har yanzu Kunyar shi bata gama saki na ba. A hankali na shiga bin bayan shi, har zuwa wani ɗan ɗaki mai kyau sosai, dining table ne ƙwara ɗaya a ɗakin, sai kujeru guda huɗu, an ƙawata ɗakin da flowers vase masu kyau sosai, sai ƴar ƙaramar tv plasma, da sinc na wanke hannu a gefe guda, ga dispenser. Ɗakin yayi matuƙar kyau, bamu jima da zama ba, waiter tazo da list na kayan abincin da suke dashi. Amsa yayi yayi ma kanshi ticking sannan ya turo mani ɗan littafin Ɗauka nayi nayi ticking ɗin lipton kawai, sannan na miƙa mata book ɗin, tana mai juyawa ta fice. Ɗan shiru ɗakin ya ɗauka yana mai ta faman latsa wayar shi, da kallo nake binshi, lallai Ya Ameen ɗin miskili ne sosai, wato ya kwammace ya latsa waya, kaman ma bai san ina zaune ba a wurin, tabɗi a hakan ne zamuyi soyayyar da ya buƙata kenan? Wata ƴar budurwa ce ta shigo hannun ta ɗauke da serving tray mai kyau, bisa plate ne ƙwara ɗaya, shi ta sauke ma ya Ameen a gaban shi, sannan ta koma ta sake shigowa da mugs guda biyu bisa ceremics, shima ta ajiye mashi guda ɗaya nima ta miƙo mani guda ɗaya. Green tea ne, a cikin nashi, yayin da ni kuma lipton ne kawai, juyawa tayi ta fice, bai ceman ƙala ba, ya jawo plate ɗin shi ya shiga cin abincin shi, sandwitch ne kaɗan sai cocumber da take falle guda biyu a saman plate ɗin. Da kallo na shiga binshi, yanzu don Allah ta yaya mutum zai ci wannan ya ƙoshi? Ganin naja mug ɗina ne na fara sipping ya sanya shi ajiye sandwitch ɗin da ya riƙe da tissue ya shiga mani kallon tuhuma "Ina abincin? Ko dama shi kaɗai kika buƙata?" ɗan ɗaga mashi kai na shiga yi. Haɗe fuska yayi tamau "Banson sakarci fa, wannan shine zai riƙe ki?" Ya faɗa cikin cin serious, bance mashi komai ba, sai ma sauke kaina nayi ƙasa ina mai wasa da tea spoon ɗin hannu na. Turo mani plate ɗin nashi yayi yana mai cewa "have it" Da mamaki nake kallon shi, sai kuma nace "Na ƙoshi fa Yaya" "Ai ba tambayar ki nayi ba, cewa nayi kici, bana son jin wani uziri naki" ya faɗa cikin ƙara haɗe fuska A hankali naja plate ɗin gaba na, ina mai fara ɗan gutsiri haka kaɗan ina ci. Baya yaja da kujerar shi, yana mai ɗaukar Mug ɗin nashi, ya shiga shan tea ɗin shi hankalin shi a kwance. Kaman dole haka nake ta tura sandwitch ɗin, ban ci cocumber ɗin ba, gashi daƙyar nake turawa. "Na ƙoshi yaya please" Na faɗa cikin ƴar shagwaɓa Ko bai faɗa ba, yanda nayi maganar na burge shi, bai ce mani ƙala ba, ya kuma jan plate ɗin gaban shi, ya shiga cinye sauran da na bari. Da mamaki nake kallon shi, ya Ameen ɗinne ke cin sauran abinci na ayau? Tabɗijam, lallai kuwa, namiji saidai a bar shi, watau duk yanda naso in zayyana halin Ya Amee kullum sabuwar sanin shi nake komawa. A haka muka gama, ya muƙe gami da nufar inda ake biyan kuɗi, ni kuma na isa bakin motar ina mai ɗan jiran shi. A haka ya ƙara so ya buɗe motar, shiga nayi ina mai zama, shima ya shiga ya zauna yaja motar muka cigaba da tafiya. Ƙarfe sha ɗaya da wani abu muka isa makarantar, ba wata fira da mukayi cikin mota, Shiyasa Naji zaman ya gundureni, saɓanin Sir Saleem da ko baka tanka mashi, sai ta jan fira da kai ne, har sai ka saki jikin shi da naka. Muna yin parking shine mutum na farko da na fara hange, bansan lokacin d ana saki wata irin dariya ba, har sauti na yana fita a hankali, ganin inda nake kallo ne, ya sanya shi kai idanun shi wurin. Zaune yake bayan mota ƙarƙashin wata bishiya, yana duba wani littafi,amman hankalin shi gabaki ɗaya yana kan hanyar shigowa. Tin da motar tamu tayi parking hankalin shi ya ɗauku gareta, hango ni da yayi na fito ne ya sanya shi ɗan dirowa, sai kuma ya nufo wurin da muke. Shi kau Ya Ameen tinda ya kalle shi sau ɗaya sai kuma ya ɗauke kai, ya buɗe boot yana sauko mani da kaya na, sannan ya dawo gidan baya yana fiddo sauran. Ƙarasowa yayi yana mai sakin murmushi sosai, shi ya ma mantatare da wani nake, hakan ce ta sanya shi faɗar "You are welcome my Jaan, ta hanya? Ya su Umma?" Wata sabuwar kunya ce ta lulluɓe ni, ganin ko bai kula da Ya Ameen da yake sauke kaya ba, ko kuma ya ganshi salo ne irin na ɗa namiji? "Ga Yayana Sir, zaku gaisa" Na faɗa cikin son kauda tashi maganar Sai kuma ya sake sakin wani murmushi, yana nufar inda ya Ameen yake tsaye jingine da motar yana fuskantar ƴan makaranta. "Assalamu Alaikum" Sir Saleem ɗin ya furta, yana mai miƙa mashi hannu daidai lokacin da ya ƙara sa ga Ya Ameen ɗin. Shima ɗan basarwa yayi, yana mai ɗan sakin guntun murmushi iya leɓo, tare da miƙa mashi nashi hannun sukayi musabaha. "Ya hanya Yayan mu?" cewar Sir Saleem "Alhmdllh" cewar Ya Ameen yana mai ɗan kauda kai gefe ya wulla mani wani irin kallo mai cike da ma'anoni. Sauke kaina nayi ƙasa. Hoooo Sir Salim, gaskiya yana neman bani kunya, shi totaly haka rayuwar shi take, sauƙin kai, da zaulaya haɗi da fara'r shi har sun so suyi yawa. Zagayowa ya Ameen ɗin yayi ta inda nake tsaye, cikin salon tafiyar shi, inda nake yaja ya tsaya, yana mai zaro kuɗin da Dad ya bani, haɗi da miƙo mani. "nagode" na faɗa ina mai amsa. Gyaɗa mani kai yayi ya zagaya ya shiga motar yana mai faɗin "Take care" Sir Saleem ne ya duƙa ta cikin motar yana miƙa mashi hannu, nan suka sake yin musabaha yaja motar shi da wani irin gudu yabar harabar makarantar. Da kallo na shiga bin motar, lallai ranshi ne ya ɓaci, to ji banma ga abunda akayi na ɓacin rai ɗin ba. Wasu ƴan mata Sir Salim ɗin ya kira suka kama mani kayan muka nufi Hostel ɗin namu. Da murmushi ya shiga bin baya na, har muka ɓace ma kallon shi, yana mai faɗin zamuyi waya. Wani irin mutuwar sonta ne yaji ya ƙara kashe shi, lallai samun Suhan ɗin a gareshi ba ƙaramin nasara bace a rayuwar tashi. Sanyin hali, girmama na gaba ga kunya da biyayya, na ɗaya daga cikin Abunda suke ƙara rura wutar soyayyar tata a zuciyar shi. Su Raihana ma sunyi matuƙar murna da dawowa ta, khadeeja ce mai faɗin "Ai na Ɗauka sai munje mun taho dake Suhana" da dariya duka na bisu, kwanciya nayi in ɗan huta gajiya, in samu in ɗan yi tunanin Abunda akayi ma ya Ameen ɗin da ya ɓata mashi rai. ******** Yana fita daga school ɗin ya samu wuri yayi parking. Kanshi ya ɗora bisa steary yana mai zurfafa tunanin shi, lallai yarinyar ga dukkan alamu soyayya suke ita da malamin nata, kenan dama shine Umma ke faɗa mashi akwai maganar shi akan ta? Ta ina zai fara ne? Baya jin idan ma zai iya haƙurewa da auren nata. Dole ne yayi wani abu, dole ne ya san ta inda zai ɓullo ma lamarin, sai yanzu yake jin haushin kanshi da bai tsaya shima ya nuna akwai wani abu tsakanin ta dashi ba. Ɗan runtse ido yayi, yana mai ɗan dukan kujera haka dashi. Yana rasa tunanin da zaiyi, a haka yaja motar tashi yabar wurin, idanun nan nashi masu kama da na mai jin bacci, sun rikiɗe lokaci guda sunyi jawur dasu. *********** Wajejen ƙarfe huɗu ne na yamma, Sir Saleem ɗin ya kira ni, akan wai inzo yana jira na. Dama na sake yin wanka, hakan ce ta sanya ni ɗaukar hijabi ta na zura, kai tsaye inda muka saba zaman karatu na nufa. Cen na hango shi zaune, a hankali na gangara ina mai zama ɗan nesa kaɗan dashi, na shiga sake gaida shi. Ji yake kaman ya haɗiye ni tsabar so, da fara'a sosai ya shiga amsawa yana mai tambaya ta gida da su Umma. Duk lafiya ƙlau na faɗa mashi. Sai kuma ya shiga cewa "My Jaan dama dalilin da yasa nace kizo shine, Ammi ta matsa akan in maki magana za'a tura manya, shine nace mata ta bari yau zaki dawo, to ɗazu ma ta sake kira akan maganar, shine nace bari in tuntuɓe ki domin in sanar dake." Ɗan shiru nayi ina mai sauke kaina ƙasa, sai cen kuma nace" To Sir, nima Ummata tayi mani maganar, ba damuwa Allah ya kaisu Lafiya, amman wannan karon ba cen ƙauyen za'aje ba, Abuja ne, gidan Alhaji Mustapha Dambulan" Da mamaki yake kallo na, ganin hakan ne ya sanya ni gyaɗa mashi kaina, sannan na shiga faɗin "Eh, shine Mijin Ummata a yanzu, don haka shine wanda za'a nemi aure na a wajen shi, haka ummata tace" "To shikenan Jaan ai wannan ba matsala bane, su Abbu ma ai sun sanshi sosai, don haka zan faɗa mata insha Allahu, nasan zuwa gobe ne zasu je, sai ki kira Umman ki sanar da ita" Cikin sanyin jiki na amsa mashi da "to" nan ya shiga jana da fira, a ƙoƙarin shi na son ganin na saki jiki dashi, tinda ya kula kaman dawowar nan da nayi har yanzu a darare nake dashi. Sai kusan 6 mukayi sallama na koma hostel ɗin namu, nan na kira Umma na faɗa mata yanda mukayi da Sir Saleem. Cewa tayi "To masha Allahu, insha Allah zan tuntuɓi Alhaji da maganar, sai musan yanda za'ayi. Ina so in tambayeta Ya Ameen ya dawo? In ajin nauyi da kunya, kar tace banji maganar ta ba, hakan ce ta sanya ni share wa, mukayi sallama. Facebook ɗina na hau, nayi searching sunan Ya Ameen ɗin, ai kuwa sia gashi na gani, direct Massage naje na rubuta mashi na ban gajiya, ina mai shaida mashi yayi haƙuri ban kiraa ba tin ɗazu ne saboda bani da number ɗinshi. Nagode Haka na kwana juye juye ranar, tin da safe na tashi da faɗuwar gaba, wai ni Suhan yau nice za'aje neman aure da Sir Saleem ɗin. Komai nakeyi haka nake yin shi a kasalance, har kai lokacin da Sir Saleem ɗin ya kira ni yana mai shaida man iyayen nashi sun nufi Abujar yanzu yanzun nan.... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~48~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Sai a lokacin kuma dukan da gabana yakeyi ya ƙaru. Saboda haka ne ma, ko da naje lecture ba abunda nake ganewa, har dai lecturer ɗin namu ya gama ɓaɓatun shi ya fita, ban iya fahimtar me yake nufi ba. Saboda haka ne ma na tattaro na dawo ɗaki, ganina da su khadeejan sukayi ne wani iri sukuku, ya sansu matsanta tambayar gareni. Bani da zaɓi illa iyaka kawai shaida masu anje tsayar da magana ta da Sir Salim ɗin. Aikuwa nan suka hau uhun murna, rai hana ce harda maƙalƙale ni, wai suna taya ni murna nayi miji ɗaya da ɗaya, abun muradin ɗaukacin student mata dake makarantar. Nidai kawai da yaƙe nike binsu, na gaza ma ko cin abinci. Haka na lalubo waya ta, ina mai kiran Umman tawa duk da ban san me zan ce mata ba. Har saida ta ɗauka, sai kuma na Gaza ce mata komai, tin bayan gaidatan da nayi. "Hello Mamana, kina jina kuwa?" "Eh Umma, nace ya gida, wai kuwaaaa... Umm um nace Ya Ameen kuwa.. Kinji ɗuriyar shi kuwa.. Tin dai daya kawo ni ban ki... ra shi ba nayi mashi ammm an ban gajiya" Na ƙarashe cike da in'ina, saida na dire ne kuma sai tunanin kada tace na damu dashi ne, ya sanya na kira ta ina mata maganar shi. Kafin tace komai sai kuma nayi saurin cewa "Umma gani nayi ya kamata in kira shi inji yanda ya koma ko?" Na ƙarashe da alamun tambaya. Bata kawo komai a ranta ba kuma, ba kaman yanda na tsammata ba. Sai kuma naji tace "Eh mamana, aikuwa Muhammadu ya shigo ko da safen nan ya gaida ni, Amman fa kaman baya da lafiya nake gani, don ko da Alhaji yayi mashi maganar ya shirya guest House nashi ce mashi yayi baya jin daɗi,to ban dai sani ba ko jikin ne ya kai shi ga kwanciya, saboda ban kuma jin ɗuriyar shi ba, tin dai lokacin, gashi kuma har baƙin sun tafi, amman da yake dai ko shi Alhajin bai kai da ƙarasowa ba" Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauke, wani abu na tsira mani cikin zuciya, na Gaza tantance ko menene. "To Umma ayi mashi sannu in ya shigo, ina gaida Dad ɗin...." na ajiye maganar a hankali, sai kuma na sake tarar numfashin ta. "Amm.. Umma nace ko zaki turo man number ɗin Ya Ameen ɗin, dama wani abokin shi ne da ya hango shi jiya, kafin ya ƙara so har ya tafi, shine yace mani in bashi number ɗin, nace bana da ita, shine fa yake mamaki yace in samo mashi to.." Cikin yanko ƙarya duk fa na zage ina yi ma ummata wannan bayanin, saidai ni kaina bansan dalilin da ya sanya ni neman number ɗin ya Ameen ɗin ba, kuma wai wurin Ummata, bana ma ko tunanin ta zargi wani abu. Ta ɓangaren Umman tawa, murmushi kawai ta saki irin nasu na manya, sai kuma tace "to bari in Alhaji ya shigo zan amsar maki wurin shi, don dai ni a yanzu bana da ita gaskiya" Ɗannjinjina kai nayi, kaman tana gaba na ne, sai kuma nace "To Umma, ina gaida Dad in ya shigo" Sallama mukayi, kowa mamaki fal a cikin zuciyar shi, Umma tana mamakin wai ka haifi yaro a cikin ka yace zai yi maka wayo, ni kuma ina mamakin saurin amincewar Umman tawa da wuri haka, akan batun turo number ɗin. Ni me ma ya sanya ni cewa ta turo man number shi? Me zan mashi? Ko hakanan zan ajiye a cikin waya ne? Ajiye wayar nayi bisa cinya ta, ina mai sakin ɗan murmushi, ko dai Umman tawa ta gani wayon da zanyi mata ne? Ya sanya bata turo mani ba? Khadeeja ce ta kalle i cikin ɗna mamaki haka a saman fuskar ta " *Suhalim* wanene kuma Ya Ameen? Mu bamu san shi ba? Ko dai ko dai? Naga zaki ce a baki number ɗin sai kwana kwana kike yi, gaskiya mu bama son haka, kada fa ayi mana snatching" Raihana ce ta amshe maganar da cewa "Kinji ki Khadee, yo wane ƙwace kuma magana har taje kunnen manya? Wayyo Allah, zamu raƙashe a bikin mu, ke har Adamu zango, da Umar M. Shareef, da Ado gwanja zamu kira, ke ranar fa kamu Shahrokhan na gidan biki zamu kira ya haɗa mana jugunannen hall, bani mu kashe, wai na ganni a bikin Sir, Salim, gaskiya kun bala'i dace da juna, Allah dai ya nuna mana lokacin" Da "Ameen Khadeen ta bita, tana mai miƙa mata hannu suka kashe. Nidai da kallo nake binsu, har kusan ƙarfe huɗu suna zaune suna ta soki burutsun su, yayin da nikau jikina sai daɗa sanyi yakeyi ganin har yanzu Sir Salim ɗin bai kira ni ba. Ina cikin tunanin ne kuwa, sai ga kiran Sir Salim ɗin ya shigo waya ta. Tsam na tashi ina mai ficewa daga ɗakin. Ina jiyo su Khadee na sanya shewa, wai kaji fa salo na masoya, shine ba za'a zauna ayi zancen gabanmu muji ba? Sai da na ɗan juyo ina mai tulla masu daƙuwa sannan na idasa ficewa. A bisa wani slao mai ɗan faɗi da tudu, inda mafi yawan cin student ke zama suyi wanki na zauna, kasancewar yamma ta kawo jiki, ga kuma ƙarancn ɗalibai a wurin, Shiyasa na zauna ina mai amsawa gami dayin sallama cikin ƴar siririyr muryar da zullumi ya kusa cinyewa. "Hello my Jaan, kina lafiya ko?" Ɗan murmushi na saki ina kai cewa "Lafiya Ƙlau Sir, ina wuni?" "Lafiya Lau, my Love, wai ni sai yaushe ne za'a dena ce mani wannan Sir ɗin ne?" ya faɗa yana mai sakin wani irin killer smile, wanda ke ƙara taimakawa wajen rusa plan ɗin ƴan mata. Nima ɗan murmushn na saki, ba tare da nace komai ba. Sai kuma ya sake cewa" Koda yake saurin me ma nakeyi? Saura kaɗan fa, wannan Kunyar zan cire ta ne,kinsan bana so bikin nan namu ya ɗauki lokaci mai tsawo insha Allah, don haka ki zaɓi suna mai daɗi da zaki dinga kirana dashi bayan munyi aure, kuma ki shirya, ba zaki kuma zama cikin makaranta ba, ina da gida cikin zariya babba mai kyau, nasan zai burge ki, acen zaki zauna, sai ki dinga zuwa kina komawa, ko in kawo ki da kaina ko kuma in siya maki mota" Wani murmushin na sake saki. Nasan idan har Allah yayi aure na da Sir Salim ɗin, matsala saidai Saura kawai, saboda shi mutum ne mai girmama mace, mai girmama ra'ayin mace, yana da kula sosai, da plan, duk Abunda zai sanya ni insha wahala na kula baya so. Ban san lokacin da nace mashi "TO Sir, as u wish, duk yanda kace, Allah dai ya kaimu lokacin" Wata irin dariyar jin daɗi ya saki, har sautin shi na fita sosai a wayar, sai kuma yace, "Kinsan me? Ammi fa ta kira ni, tace duk Abunda nake in baro shi yanzu in taho, saboda magana mai muhimmanci su Abbi suka dawo da ita, so bata yuwuwa a waya, saidai naje kawai, nasan dai bai wuce maganar date, Shiyasa gani ma har na shirya zan wuce, kiyi mani addu'a idan na isa zan kira ki, insha Allah" Samun kaina nayi da jero mashi addu'a sosai, shi kuma sai Ameen yake amsawa cikin jin daɗi, da godiya ga Allah daya bashi mata kaman Suhan ɗin. A haka mukayi sallama, yana ta faɗi mani zaiyi missing ɗina, kada in kashe waya, komin dare zai kira ni. Da to na bishi, domin dai nasan ai yana da wata matar cen, da wuya ace ya samu ya kira ni cikin dare, saidai ni ɗin ba mace bace mai musu, ya sanya ni amsa mashi kai tsaye. To ba ta matar tashi nakeyi ba, ai kuma na riga da naga lagon ta, Tinda tin kafin in shiga ta iske ni, na kuma ga salon ta, da kula kalar haukan tata, da dai ace shiru Naji, ban san kalar ta ba, sai inyi shayin yanda zan tadda ta, acikin gidan, ko tana da wani matsayi ne na daban, Amman yanzu kuma ai ta ɓarar da garin ta ƙasa, da wuya kam idan zata iya kwashe shi duka. Muna gama wayar, saƙon Umma ya shigo cikin waya ta, Number ce kawai ba tare da tace mani komai ba. Na kai tsawon wani lokaci ina mai shawarar in kira ko kuma in haƙura, kada ya ɗauka da wata manufa kuma. Shahadar kira nayi, waiting call aka sanya mani, sai kuma ban jira ba na sake danna wani kiran. Still dai waya yakeyi, Amman wannan karan kiran ya shiga wayar tashi. Bai amsa ba, har saida na fidda rai, ina mai miƙewa da niyyar shiga ɗakin. Sai kuma ga kiran nashi ya shigo waya ta. Ƙarar wayar ce tayi daidai da rugujewar ƙirji na ya bada wani irin sauti. Ban san lokacin da nayi kwana ba, na miƙe tiryan tiryan ba tare da nasan inda zan dosa ba, tafiya kawai nakeyi. Sai da ta kusa katsewa, sannan na iya ɗagawa. "Cikin wata irin sassanyar murya, mai cike da kwarjini da haiba Naji yace. " Assalamu Alaikum, Sunana Muhammad Al'ameen Dambulan, ko zan iya sanin da wa nake magana?" Kuttttt Wannan dogon bayanin fa? To ai nasan wanda na kira, saida na cire wayar a kunne na, na Harare ta, sannan na mayar ina mai cewa "Suhan ce" Kaman ma cikin tsiwa nayi maganar, sai kuma naji kaman ban kyauta ba, sannan nace "Yaya Ina wuni?" Murmushi iya leɓo ya saki, cikin son basarwa kaman ma bai gane wake magana ba ya shiga cewa "Suhan!? Suhan? Wace Suhan kenan?" Wayar na cire a kunne na, ina mai sake kallon number ɗin, lallai dai, daidai na rubuta ta, gashi kuma har ya faɗa man sunan shi, kuma. Ma dai beside, wannan muryan ko a cikin bacci na jita, zan iya shaida ta. "Yaya Suhan fa ta Umma ta" Na faɗa cikin salon ƴar shagwaɓa kaman zanyi kuka. Murmushi ya saki mai sauti, ita dariya ma ta bashi, Amman da yake dariyar ba ɗabi'ar shi bace, a cewar sa murmushin ma kawai ya isa, sai kuma ya shiga kwaikwayon irin maganar tawa. "Nifa ban gane ba malama, kiyi cikakken bayani mana" Zaune na kai, bisa wata grass carpet mai ban sha'awa, tayi tsanwa har abun tt,ina mai cewa "Kai Yaya, Allah kuwa ka gane, gashi ma Naji kana murmushi" "Suhan fa kika ce ko? Yaushe kikaji nayi murmushi? Ko dai aljanna ce ban gane ba? Kinga sai anjima tinda ba zakiyi bayani ba. Ya ƙarashe yana mai ɗauke wayar a kunnen shi kaman zai kashe, sai kuma yaji nayi saurin cewa " tsaya, tsaya yaya, to nice Suhan ƙanwar ka, da take makaranta Zaria" Wannan karon dai dariya ta bashi sosai, kuma saida ya ɗan dara kaɗan yana mai cewa "Oho, to ai haka zakice, Yarinya ta girma, ina saurayin naki?" "Kai Yaya, wane irin saurayi kuma?" "Oh baki ma gane shi ba?" "Uhummm". Kawai na iya faɗa, kaman ina gaban shi, ya saukar mani da kunya kaman in nutse ƙasa nake ji na. Cen na tsinkayi muryar shi yana cewa "Ya na barki to? Fatan dai kina karatu? Naga massage ɗinki ɗazu, ina wani abu ne yasa banyi maki reply ba, am sorry" Nan ma ban iya cewa komai ba, wai dama haka Ya Ameen ɗin yake? Ɗan zaulaya ne? To me yasa ma tun tuni ban kula ba? "kina jina kuwa?" na sake tsinkayo muryar shi, cikin salin maganar shi mai burgewa. "Eh yaya, na kira in maka ya gajiya, nagode da ɗawainiya, Allah yabar zumunci" "Ba komai ƙanwata, nagode kiyi karatu lafiya" Abunda ya faɗa kenan ya datse wayar, ba tare da ya kuma cewa komai ba. Da mamaki na sauke wayar ina mai binta da kallo. Wani salo kuma Wai ƙanwata, hummm Sabun na yaya fa har ya fara bani tsoro, na zaton zaiyi mani maganar baƙin da suka je gidan, sai kuma naga ya share bai ceman komai ba, kuma dai bana tunanin zai ce bai san da zuwan nasu ba. Sauke kafaɗa nayi, cikin ƴar basarwa na miƙe, sai lokacin ne na fuskanci irin tsawon tafiyar da na shawo. Tabɗi, lallai ma ni Suhan, to da ina zani da na kawo kaina nan na zaune? Duk da akwai tsirarun student, Amman banyi tunanin tafiyar har ta kawo nan ba. Jikina a mace na kama hanyar ɗakin namu, ina ta saƙe saƙe a cikin zuciya ta, na kuma ƙagara Sir, Salim ya kira ya shaida mani yanda akayi da magabatan nawa. *********** Da yake cikin dare ya isa sosai, sai bai takura wajen zuwa gidan nasu ba, gidan shi kawai ya zarce, kaman yanda ya tsammata, Ma'un bata yi wani shiri na tarbar shi ba, baccin ta ma ya tadda tana shaƙa, da makullin hannun shi yayi Using ya buɗe gidan, har ya saka motar shi bata ji ba, ko kuma taji share shi ne tayi oho? Da yake yaran na gidan su wurin Ammi ɗinshi, sai bai ma ko bi ta kan Ma'un da take ta kwasar bacci ba. Kai tsaye ɗakin nashi yayi ma dirar mikiya, saidai fa ɗakin gashi yaji ƙura, kaman anyi yaƙin badar a ciki. Haka ya shiga kakkaɓewa, ya share duk cikin daren, sannan ya gyara gado. Duk da tana jin motsi, Amman bata yi niyyar tasowa ba, wai a haka mijin ka ya dawo kenan daga doguwar tafiya, kai Allah yayi wadaran naka ya lalace. Wanka ya shiga, saida ya fito ne ɗaure da tawul ya isa ga water dispenser dake falo ya matso ruwan zafi ya jefa lipton. Sannan ya koma ɗaki, bakin gado ya zauna ya sha lipton ɗin, sannan ya ajiye mug ɗin yana mai zura kayan bacci ya saki ac a hankali a hankali ya kwanta. Tunowa yayi da yace zai kira ta, sai kuma yayi tunani ai ba ita kaɗai bace a ɗakin, kada ya takura su, gashi kuma su ɗin ɗalibai ne, wasu ɗaliban basa raina abun magana da yayatawa. Text kawai ya tura mata, ya jawo blanket ya lulluɓe ƙafafun shi, yana mai furta addu'ar barci Da yake yayi doguwar tafiya, ai tuni bacci ya kwashe shi, ba tare da ya an kare ba. ********* Yana sauke wayar, murmushi ya kudce mashi, wai sai yaushe ne Suhan ɗin zata bar wauta a rayuwar ta? Na daga cikin Abunda ke ƙara sanya ta burge shi kenan. Ji wai, shi zata yi ma shagwaɓa. "Hummm" Ya furta a fili, yana mai sakin wata ajiyar zuciya. Zaune yake bakin swimming pool, hankalin shi na akan ruwan da take garai garai kaman kasha, lokutta da dama, idan yanayin marece ya kawo jiki, wurin ya kan je ya zauna, iskar ruwa haɗe da sanyin lambun da yake gefe yana buso mashi. Murmushi yake saki akai akai, tin bayan da ya sauke kiran wayar nata. Muryar Mom ɗinshi ya tsinkayo tana tahowa inda yake, cike take da taƙama da izza kaman yanda kowa ya santa, babu abunda ya ragu daga cikin halin ta. Kujera taja ta zauna, rana mai fuskantar shi. "Mom barka da gida" Ya furta mata cikin girmamawa, tare da soyayya irin da ɗa da mahaifi. "Yauwa Son, barka da hutawa" itama ta furta, cike da duniyanci. Shi kanshi yayi mamakin ta, sai kuma yaga ta sake kallon shi cikin ƴar dariya ta izza tana mai cewa "Son ina so ne ka kai ni unguwa" "Unguwa kuma Mom? At this late hours?" "Eh ba daɗewa zanyi ba, gidan Hajiya Sa'a zaka miƙa ni" Da mamaki yake kallon ta, Hajiya Sa'r da tayi ma uwar watsi? Yanzu kuma me zata je yi gidan ta? Da mamaki yake kallon ta, har ta miƙe, tana mai miƙa mashi makullin motar ta, ƙirar pomatic. Amsa yayi ba tare da yace komai ba, ya miƙe gami da nufar motar da take ajiye gefe. Yana kallon ta, saida ta wurga ma sashen Umma harara, sannan tayi kwafa ta wuce. Mamaki yake, da addu'ar Allah ya shirya mahaifiyar tashi, domin dai shi bai ga wani abu da Umman tayi mata ba, wanda ya saɓa ko ya kauce ma shari'a, balle har take iƙirarin taci amanar ta. Hum. Ba zai iya fassara yanda abubuwa zasu wakana ba, muddin taji lamarin auren nashi da Suhan, Abunda har ta riga ta sanya ma ranta cewa an wuce wannan babin. *********** Sai da ya gama baccin shi sosai, misalin ƙarfe tara na safe ya farka, wanka ya fara shiga, sannan ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda gizna Ash colour, yayi matuƙar kyau, dogon namiji alkyabbar maza. Ɗakin Ma'u ya leƙa, bacci take ta shaƙa, ga plate cen gefe kan gado, tare da mug na tea, ya tintsira, ga Alama ma karyawa tayi ta bar kwanonin bisa gado. Ɗan ƙaramin tsoki taja, yana mai ficewa daga gidan, kai tsaye gidan Ammin shi ya nufa. Da gudu kyawawan yaran nashi suka rugo suka maƙalƙale Sir Salim ɗin suna faɗin "Oyoyo Oyoyo ga abbanmu" Da ɗaiɗai ya shiga ɗaga su, yana mai miƙa ma kowa ledar tsarabar da yayo mashi, Da gudu suka haura sama suna dariya da godiya. Da kallon farin cikin ganin yaran nashi ya bisu, yana mai faɗin "Kuce da Ammi na shigo" Sai gata kuwa yaran na shiga da tsaraba. Mace mai yawan fara'a, ga kamala, kyakkyawa da ita, fara tas. A hankali take saukowa tana faɗin wannan saukon fa haka malam? Ɗan zamkwa yayi daga bisa kujerar da yake zaune, lokacin da take zama ne ya shiga gaida ta cikin girmamawa. Amsawa tayi itama, tana mai rage fara'r dake saman fuskar ta. Ina Ma'un? "Bata tashi ba na baro ta Ammi" "Amman dai Tasan ka dawo ko?" "Ammi tana jina fa tayi banza dani ta ƙyale ni, ni kuma ban mara magana ba na fito, ki sanya a kawo man break fast nan, yunwa nake ji, ko jiya lipton kawai nasha" Cikin wani irin kallo take faɗin "Salim ka dena zama da yunwa, nasha faɗa maka" ta faɗa tana maibƙwala ma mai aikin ta kira. Sai fata kuwa, cikin girmamawa ta gaida Salim ɗin. "Ki kawo mashi breakfast, kada ki cika suger a tea ɗin" "To Hajiya" mai aikin ta furta tana mai juyawa. Ba'a daɗe ba kuwa sai gata ɗauke da tray, cike da kayan abinci. Tashi yayi tsaye ya amsa, yana mai ajiyewa ƙasa, ya sauko bisa carpet ɗin, yana mai cire hula ya ajiye, sannan ya zare links ɗin, yana mai kalmashe hannun riga. Miƙewa yayi yana mai wa ko hannu cikin sink da yake ajiye gefen falon tare da gogewa da towel, sannan ya dawo ya zauna. Sai da yaci ya ƙoshi, sannan Ammin ta sake kiran mai aikin tazo ta kwashe, sannan ya sake miƙewa ya wanki hannu ya dawo ya zauna. Tattara dukkan natsuwar shi yayi kan Ammin tashi, yana mai faɗin "Ammi gani, kince inzo kina son ganina" Itama ganin ya bata dukkanin hankalin shi, ya sanya ta gyara zama, tana mai fuskantar shi, cike da tausaya ma yaron nata, akan abunda zata faɗa "Salim, yarinyar nan kayi ta addu'a, idan rabon ka ce sai kafa Allah ya baka ita" Gaban shi ne ya yanke ya faɗi, cikin tsananin firgita yake kallon Ammin tashi, idanun nashi har sun cenza kala. "Ammmii bann.. Fahimta.. Ba, wani abu ne ya faru kuma?" Ya tsinci kanshi cikin in'ina yana mai jefa ma Ammin tashi tambaya. Tsam ta miƙe daga inda take, tana mai dawowa bisa kujerar da yake zaune, sai kuma ta kamo dukkanin hannuwan shi. "Wato jiya Su mahaifin ka, da su Alhaji Basheer (Wan mahaifin shi) su je cen Abuja gidan Iyayen yarinyar nan, to Amman dai su abunda sukace, yarinya dai sunyi mata miji, Amman dai idan basu daidaita kansu ba, to zasu neme mu" Cikin tsananin firgita ya miƙe yana mai sauke hular dake kanshi, salati ɗauke a bakin shi yake furta "Ammi anya kuwa cen suka je? Suhan fa na ƙauna ta, kuma mahaifiyar ta da bakin ta tace maki ta bani, yanzu kuma ya zasu ce haka? Ko dai ba cen suka je ba Ammi?" Kamo hannuwan shi tayi duka, tana mai cewa "Zauna Salim, zauna, ya zaka ce ba cen suka je ba Alhaji Mustapha Dambulan ɓoyayyu ne a ƙasar? Kana sane da mahaifin ka ma ya sanshi tin da daɗewa ko? To dai haka suka ce, sannan Baffan ka ma ya riga ya yanke hukunci, yake ka haƙura, su ba ƙananan mutane bane da zasuyi magana biyu ba, kuma ma banda abun ka, ai ba mace ke bada aure ba ko?" " Ammi ki roƙe su su koma, ina cikin wani hali please Umma, Suhan ita kaɗai ce zata iya gyara mani gida na, da tsaftar ta, da kawaicin ta, da biyayyr ta, da haƙurin ta, Ammi ki taimaka mani don Allah" Ya faɗa cike da kaɗuwa, yana kuma ƙoƙarin sake miƙewa. Amman Ammin tashi ta damƙe hannun nashi kam, ta yanda ba zai iya kuma miƙewa ba. "Nima Salim naso ka da yarinyar nan, na maka sha'awar ta, tarbiyyar ta, da hankali da natsuwar ta ta burge ni, saidai har yanzu ban fidda ran bazaka same ta ba, ban kuma fidda maka ran ko ka rasa ta, ba zaka samu wadda ta fiye maka ita ba, ina maka addu'a Salim, kuma zan cigaba da yi maka Addu'a, Allah ya shirya maka matar ka, sannan ya baka wadda zata kawo kwanciyar hankali a cikin gidan naka. Wanna shi e fatana a gareka a kida yaushe." Ta ƙarashe maganar tata itama cikin ƙunar zuciya. Har ga Allah bata ji haushin Umman a Suhan ba, saboda ita uwa ce, har kida yaushe zataso ta Aurar da ɗiyar ta ga wanda take so, to saidai itama kanta ƙarƙashin wani take, dole ne tayi biyayya, komin yanda take son abun, addu'a ita kawai zasuci gaba da bin yaran nasu da ita. Rabon ko da taga Salim ɗin yayi hawaye an daɗe, duk yanda yake shan wahala da azabe zama da Ma'un baya damun kanshi har haka, Salim mai barkwanci, Salim mai yawan fara'a, Salim bai fidda wasu daga damuwa da zaulayar shi, tau sai ga Salim na hawaye gaban Ammin shi. Guiwoyin shi duka ya sauke ƙasa, har yanzu hannayen shi na cikin na Ammin nashi, Tunowa yakeyi da wayar su ta ƙarshe da ita, Tunowa yakeyi da kallon shi da ita na ƙarshe, Tunowa da Kunyar ta, da yawan son karatun ta, yanzu shikenan ta tashi ba'a mallakin shi ba? Anya kuwa zai iya haƙura kaman yanda iyayen nashi suka buƙata? A sanyaye ya miƙe tsaye, yana mai faɗin "Ammi zanje gida in kwanta, kaina yana yi mani ciwo" "Ba inda zaka Salim, shiga ɗaki na ka kwanta, zuwa anjima sai ka tafi." Ba musu ya fara taka matattakalar upstairs ɗin, yana mai jin kanshi yana wani mugun sara mashi. Wanene wannan? Wanene wannan mai sa'ar da har zai iya mallakar yarinyar daya ƙwalkafa rai a kanta? Yarinyar da ya tsara yanda zaman gidan nashi zai kasance da ita? Shin tana ma son shi kuwa? Zata yarda da auren itama kuwa? Saidai yasanta, yarinya ce mai kawaici da biyayya, ba zata taɓa bijire wa umurnin iyayen nata ba. Koda ya isa ɗakin, ciki ya tadda yaran nashi, suna ta faman wasan su, hankalin su kwance, ga kayan ciye ciye daya kawo masu, sun baje bisa gadon kakar tasu Ammi, sai cin abun su suke suna wasa. Haka suka sake hawa kanshi, kowa da abunda yake faɗa, kowa ƙoƙarin bashi biscuit yakeyi yaci, hakan na burge shi da yaran, Amman sai gashi yau yana ture su, yana faɗin suje ƙasa suyi wasa kanshi ke ciwo..... Hhhhmmmmmmmm ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~49~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Tin dai da naga text ɗinshi da daddare, sai na kawo ma raina ba zai kirani ba sai zuwa safe. Hakan ce ta sanya, banyi gigin kiran shi ba, har kusan ƙarfe goman safiya. Ya kamata ace ya kirani, ko don inji yanda akayi da maneman auren suka je. Ban dai kira ba, amman zuciya ta na ta saƙa man in kira shi inji halin da ake ciki. Har yanzu gabana bai bar duka ba, sai kuma hankalina ya fara tashi, gashi munyi waya da Umma da safe itama bata ce man ga yanda ake ciki ba. Hakan ce ta sanya ni kiran Hafsat, saidai muka gama gaisawar da ita Amman itama bata ce man komai ba. Ban iya tambayar ta ba dai, kunya nake ji sosai, tun da dama nasan ita bata ra'ayin abun a cikin ranta, ɗan uwanta kawai take so. Haka nayi shahadar kiran Sir Salim ɗin. Kira na sau biyu amman ba'a ɗaga ba. Kasaƙe nayi da waya riƙe a hannu, ga su khadee suna ta tambaya ta wai ko an sanya bikin ne? Rasa abunda zance masu nayi, saidai na miƙe tsaye ina mai ficewa daga ɗakin, wayata riƙe a hannu. Sake jaraba kiran nashi nayi, wannan karon ma ta shiga, saidai tana fara ringing aka katse. A'ah me ke faruwa ne? Sake kira nayi, amman sai ba'a katse ba, aka barta ta cigaba da ringing, har said ata gaji ta katse don kanta. Gashi dai ina jin kunya, bana iya kiran Ammi, hakan ce ta sanya dole na koma ɗaki na kwanta, nan na tarar su Raihana sun tafi lecture. ************ Baya jin zai iya ɗaga kiran nata a daidai wannan lokacin, hakan zai iya ƙara karya mashi guiwa. Muryar ta kaɗai yake da muradin ji, Amman idan ya tuna da hakan ba zai wani amfane shi ba, mallakn wani ce, sai ya runtse idon shi ya sake buɗewa, har yanzu dai wannan abun da ya tattaru ya dunƙule mashi a maƙoshi ya kasa wucewa. Har Ammi ta gama tattara yaran nashi ta shirya masu zuwa makaranta, driver ya ɗauke su, yana nan kwance bisa gadon nata, shi ba bacci ba, shi ba ido biyu ba. Babu sauran kuzari ko walwala tattare dashi, yana tuno farko haɗuwar shi da ita. Sanyin ta, tarbiyyar ta, duk waɗannan abubuwan idan ya tuna wai ya rasa su, sai yaji kanshi ya ƙara yi mashi nauyi. A haka Ammi ta shigo ɗakin ta same shi. Bakin gado ta kai zaune cikin sanyin jiki itama, ƙura ma yaron nata ido tayi, har yanzu tana iya hango irin Abunda take gani a cikin idanun shi, aduk lokacin da ya nemi wani abu ya rasa, tin yana yaro, saidai da yake shi ɗin mai haƙuri ne, tasan zata iya shawo kanshi da izinin Allah. "Salim" ta faɗa a hankali. Ganin hakan da yayi ne ya sanya shi tashi zaune, yana ƙure Ammin tashi da kallo irin na ban tausayi. A take tausayin yaron nata ya kuma tsira mata. Duka hannuwan shi ta kamo. "Salim Abban" sunan da take yawan kiran shi kenan duk lokacin da rashin irin wannan ya same shi. Da gefen baki ya ɗan murmusa mata, irin yadda shima ya kan yi mata. Hakan ne ya ƙara mata ƙwarin guiwar ci gaba da abunda take da niyyar faɗa. "Nasan ba daɗi Salim, to saidai bamu da yanda zamuyi, dole ne kuyi biyayya ga iyayen ku, masalan ma ita da take mace, ba ita zata aurad da kanta ba, wannan yasa nake matuƙar so ka taimaka mata wajen yin biyayyr ga iyayen nata. Ba zan ji daɗi ace ka koma mata ba a yanzu, inaso ka sanar da ita dukkan abunda ke faruwa, sannan ka yanke duk wata alaƙa ta soyayya dake tsakanin ka da ita, ina maka addu'ar Allah ya baka wadda ta fita" Da idanun shi da suka cenza kala yake daɗa bin Ammin tashi da kallo. "Ammi ina son Suhan matuƙa, nayi rashi Ammi, ya zanyi? Naso ta shigo gidana, ko da hakan zai zama silar samuwar haske a cikin gidan nawa, nima in zama mai gida kaman yanda sauran maza keyi, Ammi ita kaɗai ce zata iya..." Girgiza mashi kai ta shiga yi. "Salim kada ka sare, da izinin Allah zaka samu wadda ko bata fita ba, itama ba abunda zaka nema a wajen ta ka rasa, insha Allah" Sauke ƙwayar idanun shi yayi ƙasa, ji yake kaman ya saki kuka, ko ya samu maƙoƙon da ya tokare mashi ya wuce. A hankali yake haɗiye wasu irin miyau masu zafin gaske. "shikenan Ammi, ki cigaba da taya ni addu'a, nagode ƙwarai, ina alfahari da samun uwa ta gari, nagartatta kaman ki, ki faɗama su Abba cewa *Na janye kaman yanda suka buƙata* Allah ya zaɓa mana Abunda yafi zama alkhairi, ya sanya hakan shine alkhairi gare mu baki ɗaya" Cikin tausayawa take bin shi da kallo, ita kanta tasan tayi rashin suruka ta gari. "Ba komai Son, Insha Allahu zan cigaba da yi maka addu'a, ita kuma Ma'u Allah ya shirya mana ita, ya sanya ta gane gaskiya, kuma ya bata ikon yin aiki da ita, ko yanzu ka kawo wadda kake so, a shirye nake da na mara maka baya ka same ta Salim, sannan inaso idan kaje makarantar ka haɗa ni da Suhan ɗin zamuyi magana" Jinjina mata kai ya shiga yi, ko ba komai ya ɗan samu relief, wani sashe na zuciyar shi yayi sanyi, Ammin tashi mace ce wadda ba kowa Allah yaba irin ta ba, a matsayin Uwa, samun ta kaɗai a rayuwa ya gamsar dashi. Shiyasa a kullum yake daɗa alfahari da ita a rayuwar shi. Zuro ƙafafu shi yayi daga bisa gadon a hankali yana mai miƙewa, sannan ya maida kallon shi kan Ammin tashi, da ta riga da ta saki hannun nashi. "Ammi Abban fa? Bamu gaisa ba, gashi ina so in wuce, ban ɗauki excuse ba" "Ayya, Gashi kuma tin safe ya wuce majalisa (Senate) saidai ko ka kira shi, yace ne suna da muhimmin Meeting ta yanda za'a shawo kan matsalar wannan ƙarin harajin da gwamnati tayi, sannan da rufe boder" Ɗaga mata kai yayi alamun gamsuwa, sannan ya fara takawa zuwa sauka down stair. A baya ta biyo shi har suka sauko tana mai ƙara yi mashi nasiha akan yadda da ƙaddara. A bakin ƙofa ya tsaya, yana mai kamo Ammin ya manna mata peck a goshi, sannan ya fice tana mashi fatan Allah ya kiyaye hanya. Ba Abunda zai koma gidan yayi, hakan ce ta sanya shi ɗaukar hanyar zariyar kai tsaye ba tare da ya kuma bi ta kan Ma'un ba. ******** Sanye yake cikin dakakkiyar shadda, ruwan bula, sai hula daya aza bisa kan nashi itama bula ce. A hankali yake takawa zuwa sashen amaryar tashi. Ƴan aiki sai kallon shi suke yi, suna kuma gaida shi, haɗi da jinjina irin jajircewar Alhajin ta fannin tsaya ma gidan nashi, gashi dai kowa yayi tunanin wata fitinr zata ɓullo ta fannin Hajiya Kubra, Amman ga mamakin su, duk sai suka ji shiru kuma, kaman ma babu abunda ya faru a cikin gidan. Ba kowa a falon, sai kayan kallo da suke ta aikin yi, da kallo yabi sashen, ko ina tsaf-tsaf, ga ƙamshin girki da yake tashi, wanda ya haɗe da na room freshner da ta fesa a ɗakin ta Naseem. Duka ɗakunan ya leƙa bata ciki, hakan ce ta sanya shi nufar kitchen. Ta gama soya dankalin ta lafiyayye, ta haɗa coleslow da ƴar stew ta anta da kwai, sai tea data haɗa wanda ya sha lemon grass da kayan ƙamshi. Ta juye kenan zata fito sukayi kiciɓis. Da murmushi a saman fuskar ta, sai kuma ƴar Kunyar shi da har yanzu bata gama sakin ta ba. A hankali taja baya tana mai gaida shi. Cikin murmushi ya sanya hannu ya amshi plate ɗin, ita kuma sai ta koma ta ɗauko Mug ɗin tea ɗin da wani fork. Gaba ya shiga tana bin shi a baya, har bisa dining table ɗin. Kujara yaja ya zauna, itama tana mai zama, ƙara gaida shi ta yi, ya amsa cikin sakin fuska da walwala irin ta dattawn arziƙi. "Alhaji bismilla mana, ka karya don nasan dai da wuya idan kaci wani abu, don naga ka fito da wuri yau" Ta faɗa a kunyace irin tasu ta manya. Da kallo yake binta, tayi kyau, duk ta cenza abun ta, kaman wadda ta shekaru a cikin hutu. Atamfa ce jikin ta, an mata ɗinkin zamani mai kyau, sai yake ganin kaman ma bata taɓa haihuwa ba, balle ace ta ajiye kaman Suhan. "Kin bani ne? To wa zai bani idan ba ke ba?" Ya faɗa cikin zaulaya. Itama dariya tayi a hankali, tana mai tura mashi Mug ɗin tea ɗin gaban shi. "Afuwa Alhaji, to gashi, ai bansan yanda tsarin yake ba, naga duk tare kuke cin abinci ne cikin gidan, Shiyasa nayi tunanin ko ka karya" Bai ce ƙala ba, in banda murmushi da yake yi, yaja cup ɗin gaban shi, yana mai ɗaukar cokalin ya fara cin abincin. Ba sabon abu bane a wurin shi, cin abincin nata, to saidai yau yake jin kaman abincin nata ya ƙara daɗi, gashi dai ba wani tarkace a ciki, Amman ɗanɗanon yayi mashi daɗi a baki. "Magana nazo muyi dake Umman Suhan, to Amman dai kafin nan kije ki haɗo naki tea ɗin, tinda na ƙwace maki wannan" Itama murmushi ta sake saki, tana mai tura kujerar baya, sannan ta miƙe ta nufi kitchen ɗin. Da kallon jin daɗi ya bita, yana ayyanawa a ran shi, yanzu ne aure ya tabbata a gareshi, ko bayan hakan ya samu natsuwa da kulawr da yake da muradin samu a wurin Umman, wanda tun tuni yake fatan ya samu, masalan idan yaga yanda matan abokan shi ke ba mazajen nasu kulawa, kai ko Alhaji Auwalu da ya fishi manyanta, kuma itama Hajiya Zainab ɗin tafi hajiya Kubran Manyanta, Amman kulawar da suke samu Sam bama a haɗawa. Bata daɗe ba sai gata ta fito, hannun ta ɗauke da madaidaici Mug ɗin itama. Zama tayi, tana mai sake sakin murmushi, sannan ta sauke kanta ƙasa, suka ci gaba da karyawar, duk da dai a matuƙar takure take. Ta riga Alhajin ajiye cokalin ta, sai bayan da ya gama ne shima ya tattara dukkanin hankalin shi a kanta. "Maryam Magana nake so muyi dake ta fahimta, ina fatan kuma zaki bani dukkanin goyon bayan ki, a matsayi na na wanda yanzu na tashi daga mutumen da kuke ma aiki, na koma mijinki mai gidan ki, ina fatan kin fahimta?" Gyaɗa mashi kai ta shiga yi, cikin girmamawa da mutuntawa. Hakan ne ya sanya shi jin daɗi, gyara zaman nashi yayi bisa kujerar yana mai fuskantar ta, da yanda zata so maganar ko kuma yanda zata fahimce shi, har ta ɗauki al'amarin. "Maganar Auren Suhana dai ce, jiya maneman aure sun zo daga Adamawa, kaman yanda kika sani, to saidai ban samu sanar dake yanda mukayi dasu ba, saboda muna shawara wani al'amari ne da yaya Auwalun tin jiyn. Amman alal haƙiƙa bamu amsa masu ba, daga ni har Alhaji Auwalun, dalili kuwa shine, yaron ki Al'ameen tin farko tin kafin ma ta shiga makarantar da suka haɗu da shi wancen yaro, shi Muhammadun shine ya fara zo mana da buƙatar auren Suhanan, to Amman saboda wasu dalilai acen baya, ya sanya muka dakatar dashi, sannan muka hana shi bayyana maku, har sai lokaci yayi, to kafin lokacin ne duk Abunda ya faru, ya faru. Saboda haka, inaso ki bani damar ba Muhammadu izinin neman ita Suhan ɗin, idan Allah yasa sun daidaita kansu, tana sonshi to falillahil hamdu, kinga ai gida batanƙoshi ba ba'a kaiwa dawa. Har ga Allah ni dai na yarda, kuma na amince da tarbiyyar da kika bata, hakan ce ta sanya kuma bana tunanin har zaki iya bijire wa wannan buƙatar tawa, nasan zaki ce Hajiya Kubra ita mahaifiyar Muhammadun, to inaso ki sani, ke babu ruwanki a wannan maganar, ki bar komai a hannu na, yanzu dai amincewar ki muke buƙata" Da tsananin kallo take bin Alhaji Mustapha ɗin, saidai kwarjini, girma haiba tashi, ba zasu iya barin ta bijire wa buƙatar tashi ba, kaman yanda ya furta. Ƙasa ta sake yi da kanta, tana mai jinjina wannan al'amarin, anya kuwa hakan zata yuwu? Ko ba hajiya Kubra ba, ai duniya sai ta zage su, sai ace son abun duniyar nasu yayi yawa, gashi dama har yanzu ta kasa fita waje balle su haɗu da su Mama talatun. "Ko in baki lokaci ne kiyi shawara?" Alhaji Mustaphan ya faɗa cikin son jin ba'asi. Tabbas Al'ameen yaro ne nutsattse, duk wani abu da ake buƙata wajen ɗa namiji ya tattara su, kusan ma zamu iya cewa idan ana zartarwa to shi fa ya zarta, Amman Hajiya Kubra ba lafiya bace... Miƙewa Alhaji Mustaphan yayi, har yanzu da sauran murmushi a kan fuskar tashi, Allah sarki, dattijon arziƙi kenan. "To shikenan ni zan fita, muna da Meeting da shugaban ƙasa, kiyi shawara da zuciyar ki, Amman inaso ki sani *Ni Alhaji Mustapha Yusuf Dambulan, ina nema ma yaro na Muhammadu Al'ameen Mustapha Dambulan, auren yarinyar ki Suhan* da fatan za'a amshi ƙoƙon barar namu da hannu bibbiyu." Yana gama faɗar haka ya sanya kai ya wuce, yana mai faɗar "Nagode da abinci, lallai yau kada ki sanya in ta bacci a office ɗin shugaban ƙasa" Miƙewa tayi itama, tana mai sakin fara'a, raka shi tayi har bakin ƙofar fita daga sashen nata, daga nan ta tsaya tana mashi a dawo lafiya hannun ta ɗauke da briefcase ɗin tashi tana miƙa mashi. Amsa yayi yana mai sanya mata albarka, har ya juya zuwa ga motar tashi, sai ga mota ta shigo cikin harabar gidan. Ɗan dakatawa yayi da shiga motar da driver ɗin nashi ya buɗe mashi ƙofa, domin ganin ko su wanene. Hajiya Zainab ce ta fito daga cikin motar, Sanye take da tsadadden lace, hannun ta ɗauke da jikkar ta, cikin mutun ta juna ta isa ga motar ƙanin mijin nata, yayin da shima ya fasa shiga motar ya nufe ta suka shiga gaisawa. Sai bayan da suka gama gaisawar ne sannan ta nufi sashen Umma dake tsaye tana iya hangen su. Ɗan runguma juna sukayi, alamun gaisawa sannan suka rankaya cikin falon gabaki ɗaya, yayin da motar alhaji Mustaphan ƙirar Range Rover 2019 fara ƙar ta sanya kai ta fice daga cikin tanƙamemen gidan. Hajiya Kubra da take tsaye jikin window ɗinta ta ɗaki daga upstair ta saki labule tana mai komawa baya, cikin ƙutawa take faɗin "ayi dai mu gani maciya amana" Bayan ƴan gaishe gaishe irin na mata, Umman tawa ta buƙaci ta kawo ma Hajiya Zainab ɗin kayan breakfast, Amman sai tace a'a wlh sauri takeyi zata wuce ne. Dama akwai Abunda ya kawo ta ma yanzu. Cikin kulawa Umman tawa take kallon ta. "Umman Suhan, akan maganar yaran nan ne, ina roƙon ki da girman Allah ki amince masu su auri junan su, shi Al'ameen ɗin yaje mani da maganar wai kin hana, saboda mahaifiyar shi, haba Maryama, mahaifiyar shi ce zata zauna da ita ko shine zai zauna da ita? Ba'a aure ita aka aure ta? Ina ce itama ita taga Alhaji Mustaphan ta nuna tana son shi? Don haka ni banga abun hanawa anan ba, yara dai suna son junan su, ba tin yanzu ba, tin lokacin da aka fara kawo maganar auren su Hafsatu shima yace Suhanan yake so, aka dakatar dashi, wanda tin lokacin ni banji daɗi ba, tinda yaro yace aure yake so, kuma ga wadda yake so ba sai a bashi ba? Ko yarinyar ce tace bata yi?" Ta ƙarashe da jefa ma umma tambaya. Ita dariya ma abun ya bata, gaskiya ba abunda zata iya cewa da waɗannan mutanen sai godiya, ƙauna dai sun nuna mata ita, ita da yarinyar ta, har wani lokaci ta kan ji babu abunda zasu iya nema a wurin ta, ta kasa basu. "To Alhaji Auwalu ne ya turo ni, yace inzo da kaina, kuma saƙo ne, muna neman auren Suhanan, don Allah ki bamu asamu ayi a wuce wurin, duk abunda zai biyo baya a shirye muke da mu ɗauka, indai mun samu anba yaron namu" Da murmushi Umman ke kallon ta, sai kuma ta shiga cewa "A hajiya Zainab ya da haka kuma? Ba komai Allah ya shige mana gaba, Allah kuma ya zaɓa Abunda yafi zama alkhairi, ai Muhammadu yaron kirki ne, kuma yaro ne nutsattse Sam ba don komai na hana ba, sai don gudun zagin mutane, da kuma siya ma ita Suhanan mutunci, bana so ta sake shiga wani halin ƙunci kuma anan gaba, Shiyasa ma na amsa ma Wancen yaron malamin su, Amman tinda anyi haka Allah muke roƙo da ya shige mana gaba." Farinciki fal a ran Hajiya Zainab ɗin take cewa" Yo wace irin maganar mutane kuma? Mutanen yanzu da idan kika biye ma faɗar su babu abun ariziƙin da za'a ƙulla, ki ƙyale su duk wanda bai zaga ba, bai shirya bane" sai kuma ta miƙe tana faɗin" yauwa ko ke fa ƙanwata? Allah ya basu zaman lafiya, kar ki wani damu, insha Allahu auren nan alkhairi ne a tattare damu baki ɗaya, nabarki lafiya, bari in leƙa sashen Kubra ɗin sai in wuce" Itama Umman miƙewa tayi tana faɗin "to ko in raka ki ne?" "a'a wallahi yi zaman ki, bari inje ai sauri ma nakeyi, itama dai don kar ace nazo gidan ne ban shiga ba mun gaisa" Duk da haka har saida ta raka ta ƙofar falo, sannan ta koma ciki, yayin da Hajiya Zainab ɗin ta wuce sashen Hajiya Kubra. Bakin gado ta koma ta zauna, tana tunano halin karamci irin na Ammi, gashi bata da wayar ta balle ta kira ta ta bata haƙurin yanda al'amari ya juye lokaci ɗaya, su duka ta tausaya masu, masalan ma shi Salim ɗin da ta kula yana ƙaunar Suhanan da zuciya ɗaya. Runtse idanun ta tayi, tana mai kwararo ma Suhanan addu'ar zaɓin Alkhairi a cikin Al'amarin. Ta daɗe tana sallama a sahen, sai cen ne Afnan ɗin ta fito, ga alamu ma bacci takeyi, don kayan bacci ne a jikin nata. Cikin fara'a ta ƙara so tana gaida Hajiya Zainab ɗin. Sai kuma ga Aunt Feena ɗauke da nasreem, jaye da Ayan, itama gaishe ta ta shiga yi cikin girmamawa. Cikin jin daɗi Afnan ɗin take ce ma hajiya Zainab ɗin, bari taje ta kirawo Mom ɗin tasu. To tace mata, tana mai zama ta ɗauki Nasreem tana mata wasa, tana ce ma Ayan mijin da babu cefane kyaun shi bola Cikin fara'a suka shiga ƴar fira da Aunt Feena ɗin, ita mace ce da abubuwan duniya basu cika shan kanta ba, bata cika kula da abubuwa ba, saidai wani lokaci halin Mom ɗin tata kan ɗanyi tasiri a kanta, shima ba wai yarda takeyi ba duka, saidai halin ɗa da mahaifi, wasu abubuwan idan Mom ɗin ta cika faɗa kan yi mata zafi, duk da itama wani lokaci bata mara wa Mom ɗin tata baya. Afnan ce ta sauko tana mai faɗin "Tace tana zuwa" Da to Hajiya Zainab ɗin ta bita, itama zama tayi suna ɗan fira, har ake zancen Hafsat, suna so ne zasu je gidan nata kafin su wuce. Har kusan rabin awa, Hajiya Kubran bata sauko ba, har Hajiya Zainab ɗin ta miƙe cikin ƙunar zuciya, tana mai cewa su gaida Mom ɗin tasu idan ta sauko, sai kuma gata, cikin takun ta na isassu take saukowa daga bisa matattakalar. Bisa wata kujera mai cin mutum ɗaya tayi ma kanta mazauni. Hajiya Zainab ɗince ta fara gaida ta cikin sakewa. Cikin shan ƙamshi take amsawa kaman wadda akayi ma dole. Sai kuma ta maida kallon ta kan su Aunt Feena ɗin da suke zaune, alamun su bata wuri. Cikin mutuwar jiki su duka suka miƙe suna mai ficewa harabar gidan, basa so Mom ɗin tasu ne ta yima Hajiya Zainab ɗin wani abu, ko ba komai dai gaba take da ita, kuma Hajiya Zainab ɗin ba mace bace mai yawan damuwa da al'amurran kowa ba, tana da matuƙar sauƙin kai, sannan ga girma da ya fara kama ta, duk da cewa wani lokaci hutu baya bari a gane. Mom ɗin ce ta maida kallon ta kan Hajiya zainab ɗin da take ƙoƙarin miƙewa. "Dakata Hajiya Zainab, bana son sake ganin ƙafar ki cikin gida na, haka duk wanda ya dangance ki, kun yi ma Alhaji aure cin amana kun ji daɗi? , saidai ina so ku sani, Abunda zai biyo baya ba zai taɓa maku daɗi ba, kunyi matuƙar kuskure, kun manta wacece Kubra ne, ba wanda ya isa yaja dani ko ya taka ni, don haka bana son munafunci ki kiyaye shigo mani gida... " Murmushi Hajiya Zainab ɗin ta saki, tana mai gyara zaman gyalen ta bisa kanta, sai kuma ta shiga takawa a hankali har gaban Hajiya Kubran da take zaune bisa kujera. " Kubra kenan, ba zance ma Hajiyar ba, kin manta ne, kin manta nan gidan ƙanen miji na ne, kin manta nan ba gidan ki bane, kaman yanda nake da masani yar babu ko sisin ki acikin ginin gidan nan, ke baki isa ki hanani shigowa gidan nan ba, saidai idan kika ce kada in shigo sashen ki, wannan bana da ja akai, saboda mallaki ki ne, kuma ki sani dama cen ba don ke nake zuwa gidan nan ba, saboda mijin ki, Ayanzu kuma zan shigo ne saboda mutum biyu *Mijinki da kuma Kishiyarki* a domin haka, ki sani shigowa yanzu ma na fara, kiyi Abunda kike ganin zaki iya yi, kin manta bana neman komai a wajen ki ne, kin manta duk Abunda kike taƙama dashi baki kai mai gidan naki ba, Amman shi haka kika ga yanayi? Saboda me yasa baya yin haka? Saboda shi ya san kima da darajar ƴan adam, kuma ya san ba shine yaba kanshi ba, kuma kema yanzu baki wuce ya ƙwace ya ba ma wanda kike ganin bai kai ba, ko bai isa ba. Kince mun ma Alhaji Mustapha aure, eh lallai aure fa anyi, kuma nan gani nan bari, ba abunda kuka isa kiyi, da ana tausaya maki, ashe ke ɗin ba abar tausayi bace, mu ba mune muka ce kada ki tsaya ki kula da mijin naki ba, kina nan zaune, Maryama zata ƙwace Alhaji da duk wanda yake tare da Alhaji ki rubuta ki ajiye. Amman shigowa gida yanzu ne ma muka fara, tinda yanzu ne zamu san munje gida ba kango ba" Kuttttt Hajiya Zainab yau ita ce ta zage tana zuba ruwan bala'i haka? Lallai mai haƙuri bai iya zuciya ba. Da mamaki ita kanta Hajiya Kubran take kallon ta, ita dai a iya zaman ta da ita, ba zata taɓa cewa ga ranar da taga tayi faɗa ba. Tana gama faɗar haka kuma ta juya tana mai saɓar jikkar ta, ta nufi ƙofa da niyyar ficewa. "Ke kika ɗauke ta a matsayin kishiya, bata isa ta mallaki mijina ba, na auren saurayi da budurwa ba ta zauna lafiya, wallahi zaku san dani kuke yi dukanku" Ta faɗa daidai lokacin da Hajiya Zainab ɗin zata fice daga sashen nata. Itama bata ce komai ba, ta idasa ficewa tana sakin dariya. Afnan dake shilla Ayan a shillo, yayin da Aunt Feena take zaune ɗauke da Nasreem da har tayi bacci a jikin ta, bisa wani ɗan dandamali da akayi da zallar kankare, hankalin ta yana a kan sashen Mom ɗin tasu, don tasan komai zai iya faruwa, har yanzu Mom ɗin tasu bata huce ba, tinda gashi tin ranar ta kankara masu worning akan zuwa sashen Umman, duk yanda Afnan ɗin taso akan taje, tin kafin ma Suhan ta koma makarantar, Amman dole ta haƙura, koda suka sanar da Dad ɗin ma cewa yayi, su dakata har sai komai ya koma normal sun dinga shiga. Hango Hajiya Zainab ɗinne, yayi sanadin tasowar Aunt Feena ɗin, ta nufo ta tana mai mata magana. Bata share ta ba itama, haka suka jera har zuwa bakin motar Hajiya Zainab ɗin, har ta shiga motar ta tabar gidan cike da tausaya ma ƴaƴan Hajiya Kubran, masalan ma Al'ameen, Feena Afnan da Abie da yake cen american ɗin. ********* Hankali na fa ya tashi matuƙa, gashi tun ina kiran shi tana shiga, har ta koma ma tabar shiga, a'a wai meke faruwa ne? Haka su Khadeen suka dawo suka tada ni jiki a mace, tambaya ta suka shiga yi, banda zaɓi illa shaida masu, ko ba komai ina buƙatar wanda zamu tattauna dashi. Suma hankalin su ya tashi, Amman sai suka shiga kwantar mani da hankali. Jinsu dai kawai nakeyi, Amman bana cikin natsuwa Waya ta ce dake saman cinya ta ta ɗauki tsuwwa, alamun saƙo ya shigo, da sauri na wawura in gani ko shine. Saƙon MTN ne, hakan ya sanya nayi wurgi da wayar bisa gado, aikin banza ma kenan, su MTN ɗinnan basa gajiya da shirme, sai a lokacin da kake tunanin ganin alert ko wani muhimmin saƙo ne zasu ke damun ka da ture turen banzan su. Miƙewa nayi ina mai ficewa daga ɗakin, komai ya dagule mani, gabaki ɗaya duniyar ta mani ƙut, ya kamata ace ko ba komai Salim ɗin ya ɗauki waya ta. Magriba ta riga tayi, dole na shiga ɗakin na ɗaura alwala, yau fuska ta ko mai bata gani ba, tin dai bayan da nayi wanka na zura kaya na shikenan, ban tashi daga bisa sallayar ba, har aka yi isha'i. Saida na gabatar da duka salloli na, sannan na miƙe ina mai naɗe sallayar, wanka na shiga, watsa ruwa nayi, koda zanji sauƙi. Su khadee an duƙufa da karatu, sai gashi cikin sa'a akwai wutar nepa kuma. Suma basu kuma ceman komai ba, sai karatun su da suke yi, ganin bana cikin Mood ne ya sanya suka ƙyalenin, har in warware sana. Kwanciya nayi ina mai jawo littafi na, saidai babu abunda yake shiga kwalwa ta, hakan ne ya sanya ni ajiyewa na shiga jan bargo na lulluɓe jikina duka. Wayata na jawo da niyyar kashewa, sai na hango ɗan akwati maƙale saman wayar, alamun ina da saƙo, kaman in share, sai zuciya ta ta gaza daurewa "Idan Sir Salim ne fa?" zuciya ta ta raya mani. Buɗewa na shiga yi a hankali. Yana yin tsarin Rubutun, da kyawun shi ne suka ɗauki hankalina, na gaza wucewa ban karanta ba. Rubutun turanci ne a tsare, cikin grammer mai kyau, ga words ɗin sun tsaru iya matuƙa. Ga Abunda ya rubuta. _"Zuciya ta bata laƙanta man son abu, muddin tasan ba zata samu ba, ina mai yi maki albishir da cewa Alhaji, Umma da kowa da kowa sun yarda sun amince da auren namu. Ki shirya ma karɓar soyayya ta a koda yaushe, salon ta daban ne, kaman yanda ke ɗin kike daban a cikin zuciya ta. Ina alfahari da samun ki a matsayin uwar ƴaƴana. Kiyi bacci cikin natsuwa, ina fatan zakiyi mafarki na"_ Wuuuuuuuuu Ai bansan lokacin da na duro daga bisa gadon ba, Sir Salim ne, Sir Salim ya turo mani saƙo, Su Dad sun yarda. Abunda nake faɗa kenan, ina tsaye tsakiyar ɗaki kaman wadda akayi ma allurar tsayuwa. Dukansu litattafan nasu suka ajiye, suna mai tasowa domin duba saƙon, sannan suka rungume ni suna mai faɗin "wow Suhan, waɗannan zafafan kalamai haka? Wallahi sun tafi da imanin mu, dama haka Malam ya iya kalamai?" Komawa nayi bisa gadon, ina mai zama, cikin tsabar farinciki, gashi gabana dai bai bar faɗuwa ba, amman murnar da nake ciki ta hana ni kula ko ankara. Ba da numb shi ba kenan yayo mani saƙon. Abunda zuciya ta ta raya mani kenan, ƙoƙarin kiran layin nakeyi, Amman ana faɗa man ba zai iya shiga ba. Layin shi na ainahi na kira, ya shiga Amman ba'a ɗaga ba, ban damu ba, sai ma sake sakin murmushi da nayi ina mai cewa "Ƙila wani abu yake yi." A haka muka zauna muna ta fira mai daɗi da su Khadeen da suka kula ina cikin farinciki..... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~50~* _Kai gaskiya *masoyan banfi ƙarfin ta ba* ina matuƙar farin ciki daku, ba zan iya lissafi sunayen ku ba da ɗaiɗai, Amman in kinsan kina ciki, tau bansan irin godiyar da zanyi maku ba, ina ganin ruwan comment, kuna ƙayatar da Oum-Deedat. Nagode kwarai Allah ya saka maku da alkhairi, ya bar ƙauna, fatan za'a dinga faɗa mana kura kuran mu, saboda shi ɗan adam a ko'ina yake ajizi ne, tara yake bai cika goma ba_ *Gaisuwa ga ɗaukacin ƴan golden pen Writers Association, da bazarku nake taka rawa a ko'ina kuke a faɗin duniya. Allah ya ƙara haɗa kawunan mu, ya kauda idon maƙiya da mahassada. Ameen ya Rab* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Bacci fa mai daɗi na kwashe shi yau, har saida su khadee suka tada ni. Ko bayan dai da na tashi walwalar bata bar fuska ta ba, haka nayi salla nayi wanka, da yake muna da lecture ɗin safe, tea kawai na iya kurɓa na fice ɗauke da tsantsar farin ciki. Ina hanya ne wani text ɗin ya sake shigowa. Ganin number ɗin jiya ce, ya sanya ni dakatawa daga tafiyar da nakeyi A hankali na ƙara hasken waya ta, ta yanda zan iya ganin komai tar. Sannan na buɗe _Abubuwa biyu ne suka assasa man barci mai daɗi a daren jiyan, amincewar Umma da Dad, yanzu kuma abu ɗaya ne zai raya wannan hasken ranar ta yau a gareni, ganin fuskar tauraruwar tawa, ki shirya ma zuwa na a koda yaushe. Take care with my love_ Cikin tsabar murmushi, har ƴar siririyar wushiryata ta bayyana, nake kallon wayar. Saida na kuma tusa karanta abunda ya rubuta, sannan na samu bisa wani block na zauna, jikina duk ya mutu tsabar farin ciki. Ta ina Sir Salim ya iya waɗannan kalaman tun tuni bai taɓa yi mani irin su ba sai yanzu. Kenan Sir Salim ɗin zai dawo ayau kenan? Cikin hanzari na kuma miƙewa na isa ga hall ɗin namu, Allah ma ya taimake ni lecture ɗita 8-10 ce sai kuma 12-2. Ina da isassshen lokacin da zan iya komawa ɗakin ma har inyi wanka, don dai nasan sai marece yake zuwa shi. Yau kam na fahimci lecture ɗin sosai, abokiyar zaman tawa mai suna Sumy itama kuwa ta fahimci hakan, har take tambaya ta minene sirrin fara'ar tawa ta yau, murmushi kawai nayi mata bance da ita komai ba. Har muka gama kaf lecture ɗin tamu, sannan na nufo hostel. Daf da zan ƙarasa hanyar da zata sada ni da ɗakin namu ne na hango tsayawar motar tashi. To fa, ashe da wuri zai zo? Kallon jiki na na sake yi, atamfa ce jikina ɗinkin riga da skirt, sai hijab ɗita kalar atamfar, Amman ba mai tsawo bace sosai, domin da kaɗan ta wuce hannuwa na. Ba kwalliya ko laƙo a saman fuskar tawa, to saidai ba sabon abu bane a wajen Sir Salim ɗin ganina a haka, saboda ko lokacin da ya ganni ma yace yana sona, bai ganni da kwalliya a fuska ba. Ja nayi na tsaya jikin wata bishiya haka mai ƴar inuwa. Tafe yake cikin shadda saƙar gizna, na kula yana bala'n son shadda gizna, ba yabo ba fallasa yake nufo inda nake tsaye bayan ya kulle motar. Ɗalibai sai gaishe shi suke yi, Amman da hannu kawai yake iya amsa masu. Haka ya ƙara so inda nake tsaye, sadde da kaina ƙasa, ko ido ma na kasa bari mu haɗa, bansan dalili ba, yau Kunyar tashi da nake ji a jikina, ta linka wadda nake ji ada cen baya sau kusan goma. Wai wannan shine wanda zan aura? Mijina uban ƴaƴana, kalaman da ya faɗa jiya ne suka sake dawo mani, sai kuma wanda ya turo mani ɗazu da safe. Gefen hijab ɗita na jawo ina mai ɗan rufe fuska ta, haɗi da ɗan juyawa haka. Da mamaki yake binta da kallo, Kaman ma fa bata san Abunda ke faruwa ba, muryarta ya tsinkayo tana mai gaishe shi. "Sir Ina yini? Ya hanya? Ya su Ammi?" Duk ta jero mashi tambayar, Amman fuskar ta har yanzu a rufe take, duk iya yanda zaiyi su haɗa idanu taƙi bashi wannan damar. "Suna lafiya Suhan, Ammi tace a gaida mata ke sosai, ina so ne zamuyi wata magana, ina sauri ne zan wuce" A ɗan mamakance na juyo ina mai kallon shi, to ai dole inyi mamaki, Suhan fa ya kira ni kai tsaye, kuma wai yana sauri, ba kasafai yake faɗa man haka ba, wani lokaci har nice ma zan ƙagara ya tafi saboda in samu inje in huta. Gashi Sam wannan zaulayar, da walwalar da na saba gani a saman fuskar tashi, yanzu duk sun kau, babu ko ɗaya a cikin su. Tsayuwa ta na ɗan gyara ina cewa "To Malam" "Muje ko?" ya faɗa yana mai nuna mani wasu ƴan kujeru da take na zaman student saboda karatu, ƙarƙashin wata bishiya. Kunya duk ta kama ni, yanzu a tsakiyar makaranta zamu zauna mu tattauna ɗin? Saidai ban mashi musu ba na shiga bin bayan shi. Zama yayi, yana mai ɗan tura mani kujera ɗan nesa kaɗan dashi. Ja nayi na zauna, ina mai tattara dukkanin natsuwa ta a kanshi. Ganin hakan, sai bai ɓata ma kanshi lokaci ba ya shiga kora mani jawabi. "Watau Suhan iyaye na sunje gidan ku, sun samu mahaifan ki, Naji daɗin yanda komai ya faru, basu yi wani ɓoye ɓoye ba suka shaida masu cewa sunyi maki miji, saboda haka suna mana addu'a da fatan alkhairi..." A firgice na ɗago ina mai kallon shi, lokaci guda kuma ina mai ƙoƙarin tashi daga zaunen da nake, ji nayi kaman an buga mani guduma a tsakar kai. Da hannu yayi mani alamun da in dakata, sannan yace" koma ki zauna, ai ban gama ba" "a zahirin gaskiya Suhan na soki, na ƙaunace ki, saidai ina ganin hakan shine yafi alkhairi, domin dama kullum zaɓin alkhairin muke addu'a, banso rabuwa dake a wannan yanayn ba, saidai bana da yanda zanyi, bana son shiga tsakanin ki da mahaifan ki, bana kuma so a dalili na ki bijire ma umurnn su, don haka kiyi biyayya, indai nine Salim, to *Na anye maganar aure na dake* saidai bana fata hakan ya shafi zumuncn mu, ko da yaushe kike buƙatar taimako a makarantar nan, ƙofa a buɗe take, kizo ki same ni, insha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na magance maki ita, don Allah Suhan ki amshi zaɓin iyayen ki, wata ƙila shine mafi Alkhairi a gare ki. Ammi tace in bata ke a waya zakuyi magana" Ya faɗa yana mai zaro wayar shi, ya shiga kiran layin Ammi ɗin. Nidai kawai zaune nake kaman mutum mutumi, to kenan ba shine ya turo mani text ba jiya, kenan wanda suka zaɓa mani ne? To ta yaya? Ta ina ya samu layi na? Cen na tsinkayo muryar shi suna gaisawa da Ammi ɗin, sai kuma ya shiga cewa "to Ammi gata" A hankali na miƙa hannu na ina mai amsa na kara a kunne, sai kuma na fashe da kuka, shiru Ammi tayi tana mai saurare na, saida nayi mai isa ta, Allah ya soni ma an shiga lecture ɗin 2,ɗaliban ƴan tsuraru ne suke wucewa, suna ɗaga ma Sir Salim ɗin hannu, wanda shi hankalin shi ma Sam baya kaiwa kansu. Sai da nayi mai isa ta, sannan na tsagaita, bansan ko kukan menene ba, idanuna sunyi jawur, haka fuska ta, kaman wadda aka faffalawa mari, abun ka da farar fata. "Ya isa hakanan Suhana ta, yi shiru goge hawayen muyi magana" Ammi ɗin wadda take zaune a tanƙamemen falon nata bisa wata sofa mai kyau, ta faɗa. Share hawayen nayi, ina mai jan majina a hankali, sai kuma nace "Ammi ina yini?" cikin karyayyar murya da tasha kuka. Saida ta ɗan runtse idanun nata, kukan nawa ya taɓa mata har cikin zuciya, wannan ke tabbatar mata da cewa Salim ɗin ya faɗa man komai, kuma hakan ya ƙara tabbatar mata da nima ina son yaron nata. "Suhan haƙuri zakuyi ku dukanku, ƙaddara ta riga fata, dama cen Allah bai rubuta ke matar Salim bace, Allah ya sani mun soki, mun ƙaunaceki da zuciya ɗaya, tin jiya naso in kira ki, nayi tunanin gara ki fara ji daga bakin shi, kinsan zuciya bata da ƙashi, mun san ba laifi ki bane, haka kuma mun san ba yaudara bace, ke ɗiya ta ce Suhan, ko baki auri yaro na ba, inaso ki ɗauke ni a matsayin uwa, zan zame maki gata Suhan, zan zame maki kaman Umman ki insha Allahu, a koda yaushe muna tare dake a rayuwa, yanzu abunda nake so dake shine, ki amshi zaɓin iyayen ki, kada ki sake kice zaki bijire masu, saboda soyayya, kada ki sake ki rabu da iyayen ki akan ɗa namiji, su kansu wani lokacin basa da tabbas, koda yake ɗanɗa na, ba zan iya bada shedar shi ba 100% saboda batare dashi nake kwana nake tashi ba, saidai zan iya bada shaidar wasu daga cikin halayen shi, kasancewa ta uwa a gareshi, uwa kuma mai kula da al'amurran yaran ta. Suhan insha Allahu ba zaki yi nadamar zaɓin iyayen naki ba. Don haka nake baki shawarar da kibi Allah kibi iyayen ki, kiyi haƙuri kibar kuka, Allah zai baki wanda yafi Salim komai da izinin Allah" Ta tsagaita cikin tausasawa, sai kuma itama zuciyar ta ta karye, bata bari na fahimci haka ba, ta shiga ƙara kwantar mani da hankali, har saida taji ina mai ɗan sauke ajiyar zuciya cikin wayar a hankali a hankali. Mun ɗau tsawon lokaci tana bani baki, har saida na gaji da riƙe wayar a kunne na. Sallama tayi mani, bayan na shiga zuba mata godiya, ina ƙaunar matar har cikin zuciya ta, baya ga Ummata banga matar da take mani ƙauna irin wanna ba, bayan bamu haɗa komai da ita ba, sai soyayya da ɗanɗan nata. Cewa tayi in bashi wayar. Miƙa mashi nayi, ina mai ƙara share hawayen da har yanzu sun kasa tsayawa a fuskar tawa. Amsa yayi shima, kamar ya zuba kuka, ganina da yayi gaban shi, gashi ina kukan rabuwa dashi, hakan sai ya ƙara katse mashi jijiyoyi, ji yake kaman yace bai yarda ba, ji yake kaman ya tashi yaje gidan namu da kanshi ya samu Umman tawa, duk da dai ya san iyayen nashi ba zasuyi mashi ƙarya ba. Shima sun ɗau tsawon wani lokaci suna waya sannan ya katse wayar yana mai maidata aljihu. Yanzu na ƙara tabbatar wa, saƙon jiya da na yau ba shine ya turo mani ba. *Zaɓin iyaye na* shine ya turo mani saƙon kenan, wanda zan iya kiran shi da *ɓoyayyen masoyi* Hankalina na maida kanshi, ganin ya miƙe saboda ɗalibai da suka fara fitowa daga lecture suna kallon mu. "Suhan zan tafi, Allah ya haɗa kowa da rabon shi na Alkhairi, don Allah ki ɗauke ni a matsayin yayanki uwa ɗaya uba ɗaya a makarantar nan, bana so ki ɗora ma kanki laifi da damuwa har hakan ya shafi karatun naki. Ina sonki har cikin raina" yana gama faɗar haka ya juya ya nufi motar tashi,ba tare da ya bani damar cewa wani abu ba. Saidai ya kasa tashin motar tin bayan shigar shi ciki. Kanshi ya ɗora saman steary, wani irin ƙululun abu ne yake jin yana mashi sama da ƙasa a cikin maƙoshi, ɓacin rai zalla, sai yanzu yake jin wasu ɓoyayyu hawayen soyayya na tsattsafowa daga kwarmin idanun nashi. Yana iya hango ta, ita kanta har yanzu ta kasa tashi daga wurin, lokaci zuwa lokaci takan sanya hijabin ta tana share kwallar ta, da yake university ce, saidai a kalle ta a ɗauke kai, waɗanda suke tsaye suna kallo na basu da yawa. Ganin an fara taruwa ne ya sanya ni miƙewa jiki a sanyaye da niyyar barin wurin. Wasu jibga jibgan mktooci ne suka yo shigar burgu zuwa harabar makarantar a guje, ƙurar su kawai kake iya hangowa, saidai daf da zasuyi parking sai kuma suka rage gudun su, zuwa a hankali a hankali. Ban iya cewa ga sunan motocin, saidai ni kaina nasan a irin fina-finan ƙetare ne kawai nake ganin irin su. Motoci uku ne, guda biyu watau ta gaban da ta bayan dukan su farare ne sal, sai kuma ta tsakiyan da ta kasance ɓaka wuluk, a tare suka yi parking a kuma jere, da gudu naga wasu irin bodyguard suna fitowa zuwa jikin baƙar motar domin su ba mai fitowa daga ciki kariya da kuma tsaro. Sai wasu mutane masu saye da rigunan fadawa suma riƙe da bulalai irin na dorina, sai zare idanu suke yi. Kallo fa ya koma sama. Anyi cirko cirko zaman jiran wanda zai fito daga cikin wannan motar da ta riga ta tafi da imanin kowa dake faɗin makarantar. Sai da na kusa faɗuwa, gani wani bodyguard guɗa ɗaya, da hannun shi ke riƙe da ƴar bindiga ya sanya hannun shi ya buɗe bayan motar. Ganin wanda ya fito daga cikin motar ne, ya sanya ni ƙara wara idanu na akan shi. *ya Ameen* na furta cen ƙasan maƙoshi, ina mai ƙara ƙwalalo idanu na, kaman zasu faɗo ƙasa, lokaci guda litattafan hannuna suka sulale zuwa ƙasa. Sanye yake cikin wasu irin baƙaƙen suit, hatta da takalmin da yake ƙafar shi cover shoes baƙaƙe ne, sai ɗaukar idanu suke yi da walwali. Fuskar shi Sanye take da wani irin baƙin Sun Glass, da baka iya hangen kwayar idanun nashi. Hakan ce taba farar fatar shi daman sheƙi da walwali. Gashin kanshi kwance yake luf luf,har zuwa saman wuyan shi, duk da kan nashi babu aski saidai gyaran fuska, kai in ka kalle shi sai kace ya haɗa iri da fararen Larabawa ko kuma indiyawa. Kai tsaye idanun shi bisa ni suka sauka, hakan ce ta bashi damar fara takowa a hankali kuma cikin ɗan sauri sauri da zafin nama irin na cikakken namiji. "wow, wow, Al'ameen dambulan, yariman matasa" Abunda naji wasu ƴan mata dake kusa dani sun faɗa kenan, suna mai zuba mashi dukkanin idanun su. Shima Sir Salim dake zaune cikin mota, y kasa tuƙawa balle ya bar wurin, hankalin shi ne ya kai kan motocin tin shigowar su, gabaki ɗaya an rubuta *Yariman Matasa* a jikin number ɗin motocin. Kallon shi ya sake kaiwa inda nake zaune, domin ko ba komai ya san wurina suka zo, tinda ƴan gidan mu ne. Ga mamakin shi nima tsaye nake, ga litattafai na a ƙasa yashe, har kai lokacin da Al'ameen ɗin ke takawa yana nufar inda nake tsaye, watau inda Sir Salim ɗin ya barni zaune. Bodyguard guda biyu ke biye dashi, sai fadawan da suke biye dashi da ɗan guntun gudun shi, da niyyar su isa su gyara mashi wurin da zai zauna, hannun ɗaya daga ciki riƙe da wata irin kujera da ake naɗewa kaman keke mai masifar kyau. Har yanzu dai da kallo nake binshi, bakina a sake, kaman gaula, ya koma mani Ya Ameen ɗin da na sani tin cen baya. Wannan comvoy ɗin duk na menene? Ƙila hanya ce ta kawo shi, shine ya biyo ya ganni, to amman duka yaushe ya kawo ni? Duka yaushe muka rabu? Bansan ya ƙara so inda nake tsaye ba, sai ƙamshin mayataccen turaren shi Naji a kusa dani. Fuskar nan ba yabo ba fallasa, duk da har yanzu tana ƙunshe cikin Glass ne. Kujerar suka warware haɗi da ajiye mashi suna mai matsar da tawa kusa da wadda suka ajiye. Da hannu ya dakatar dasu, yana mai faɗin "you can go" Baya sukayi su duka, suna mai komawa jikin motocin, hadda dogarawan kuwa. Sai kuma abun ya ƙara ba student mamaki, ai su duk a tunanin su wajen VC yazo, sai kuma suka ga ya dakata a wajen da nake tsaye. Su kuma sun san alaƙa ta da Sir Salim, kuma ga shi cen tsaye bakin motar shi, yana iya hangen dukkan abunda ke faruwa. Ai sai suka zuba mana idanu, kunsan ƴan makaranta da gulma, gashi kusan ƙarfe huɗu duk sun firfito. Hatta dai da su Raihana da Khadeejan tsaye suke suma sun zuba ma sarautr Allah idanu. Kujerar da suka ajiye mashi, ita ya ɗauka ya ajiye mani, sannan ya duƙa ya shiga tattara mani litattafai na da suke ƙasa, ya aza su bisa ɗan table ɗin, yana mai jawo kujerar da suka ajiye mani ya zauna. "Zauna mana malama, ko Soja ce ban sani ba? Kina wani kallo na kaman kinga baƙon ki" Ya faɗa cikin basarwa, kaman ba shine yayi maganar ba. Banda zaɓi illa zaman. Kaman sauna dai, haka kuma nake kallon shi, ga idanuna da sukayi luhu-luhu tsabar kuka. Wayar shi ya zaro yana mai latsawa, kaman ya manta dani a wajen. "ina yini? Na furta a hankali kaman wadda bata son yin maganar. Bai bar latsa wayar ba, haka ma bai amsa mani gaisuwar da nayi mashi ba. Sai cen ne naji yace " ai na ɗauka baki Iya gaisuwa ba" Da mamaki nake kallon shi, au Shiyasa bai amsa mani ba? Sadda kaina ƙasa nayi ina mai ɗan sakin ajiyar zuciya. Ganin ba zan tanka ba, sai ya ajiye wayar bisa ɗan teburin dake gaban mu. Sannan ya maido hankalin shi a kaina. "Bakiga text ɗina ba jiya da yau?" ya furta yana mai zare Glass ɗin idanun shi. "Na gani Yaya" Na faɗa nima a hankali. "Meyasa baki yi mani reply ba? Ko bani da amsa ne? Ke yaushe ne zaki bar ƙauyanci ne?" Ya faɗa still shima dai kaman ba shine yayi maganar ba. Ɗan kallon inda student suke tsaye nayi, kunya duk ta baibayeni. Sai kuma na maida kallo na kan Sir Salim da yake tsaye jingine jikin mota, kaman an dasa shi, mu kawai ya zuba ma idanu. Ganin inda nake kallo ne, ya sanya shi shima maida idanun shi wurin. "Oooh! Wancen shine saurayin naki da aka je nema mashi auren matata jiya?" Ya faɗa cikin I dont care tune. Sadda kaina na kuma yi ƙasa ba tare da nace mashi komai ba. Salon da yayi ya matuƙar burge ƴan matan dake tsaye, kowacce tana fata da burin ina ma ace ta mallaki ya Ameen ɗin. Tsaye sukayi suna mai more ma kallon shi, wanda suke gani a gidajen talabijin yau shine a zahiri a cikin makarantar tasu. Tsam naga ya miƙe yana nufar inda Sir Salim ɗin yake tsaye. Hannu ya miƙa mashi sukayi musabaha. Sai kuma yace "kaman naso in gane ka ko?" Da mamaki Sir Salim ɗin ke kallon shi, lallai jin kan wannan gayen ma yayi yawa, watau haka dai yake kenan ko a zahiri, lokacin da suka haɗu dashi a library bai kamata ace har ya manta shi ba, da kuma duka yaushe ne suka gaisa dashi ya maido Suhan ɗin makaranta? "Eh kwarai kuwa ka gane ni, ba kai ne yayan Suhana ba?" "Eh kwarai kuwa nine. Malam ko?" ya furta cikin salon muryar shi da ba mata ba kaɗai har maza burge su takeyi. "Sosai kuwa nine" Al'ameen ɗinne ya sake bashi hannu suka gaisa, kowa da Abunda yake ƙunshe cikin zuciyar shi. Juyawa yayi ya koma inda ya tashi, baki sake nake binshi. Lura nayi da dogarawan sun fara korar ɗaliban da suke tsaye suna kallon mu, wanda wasu daga ciki har sun fara fiddo waya suna haska Ya Ameen ɗin. "Nace zanzo ki shirya ma zuwan nawa, sai gashi kuma na tadda ke a haka? Me ya same ki? Kaman ma kinyi kuka ko?" Ya faɗa cikin tsattsareni da idanun shi da suke sanya jikina ƙara sanyi. Ɗan kallon jikin nawa na kuma yi a karo na biyu. Sai kuma kunya ta kama ni, Amman sai na share ina mai cewa" Yaya daga lecture fa na fito yanzu, to wacce kwalliya zanyi kuma?" na faɗa cikin ɗan narkewa alamun ƴar shagwaɓa. Da kallo yake bina. Na matuƙar burge shi. "Bana son Yayan nan, ya zuwa yanzu nasan kin fahimci matsayi na a wajen ki, so don haka ina buƙatar a cenza mani suna" Ni dariya ma ya bani, Amman bari ayi mashi boko, mugani idan zai iya kubce wa. "Wanne matsayi kenan yaya? Ban fahimta ba? " Na faɗa cikin wayancewa. "au baki gane ba?kina so inyi abunda saisa kowa ya tabbatar da matsayin nawa ne? " Shima ya faɗa cikin wani salon na basarwa. Kai tsaye nace mashi "Eh" ban ko rufe baki ba, naga ya nufo fuska ta da fuskar shi, fuskantar Abunda yake niyyar yi ne ya sanya ni ja baya, ina mai faɗin "Nagane yaya, Allah na gane" Yar dariya ya saki yana mai ɗan wayancewa ya kauda fuskar yana mai faɗin "Matsoraciya kenan, ai naso ki bari har shi Wancen saurayin malamin naki ya fahimta, duk da yanzu nasan ya riga ya janye, mai wuri yazo ai dole mai tabarma ya naɗe" Da kallon mamaki nake binshi, wai Ya Ameen ɗin da na sani ne da kuwa? Kaman ba shine ya saki jiki yana zaro maganganu haka ba. To ada ma idan ance man ya iya magana haka ai bazan iya yarda ba, yo to ai ni kallon miskilanci nake mashi, ashe ba kowa yakeyi mawa ba? Ashe ba a ko'ina yake miskilin ba. "Anyway ya kamata inyi Abunda ya kawo ni, don naga kin faɗa komar tunani." Ya faɗa yana mai gyara zaman shi, sai kuma ya ɗan haɗe fuska, alamun maganar ba wasa a cikin ta. Bai bani damar magana ba, sai ma cigaba yayi da cewa *"All the way from Abuja na taso yau, ba don komai ba kuma sai domin in ganki, bana buƙatar sake tambayar ki amincewa akan batun auren nawa, Amman All what i want is your Love. Soyayya nakeso mai tsafta, Soyayya mai ƙunshe da ƙauna, bana son ƙauyanci fa, zaki ajiye wannan Kunyar taki ne a gefe, saboda ni ban ganin abun Kunyar indai har muna son juna, we have to show it and prove it a gaban kowa, hakan ne zai sa iyayen mu su yarda mun amince da juna. Maganar soyayyar ki tada, ki mance da ita, ki ajiye ta gefe, salon zai cenza ne a wannan karon, I am Al'ameen Almustapha Dambulan as u know, so ba lallai ki iya ganewa ba, Amman zan iya ce maki bansan micece soyayya ba sai akan ki, bansan ya ake yin ta ba, na ɗauke ta shirme ce, na ɗauka sai marasa abun yi ne suke wata abu wai ita soyayya. Amman yanzu duk ba haka bane, na fahimci kuskure tunani na, tin shigowar ki rayuwa ta. Ina Sonki Suhan, zan aureki, kuma zan kasance tare dake a kowanne hali. Da fatan zaki bani goyon baya kema, zan bari kiyi tunani a koda yaushe zaki iya ganin na dawo, domin a yanzu na fahimci cewa garin masoyi baya nisa ko ina yake a faɗin duniya"* Tabɗiiiiiiii Ya Ameen ne yau zaune a gaba na, a gaban ɗumbin mutane haka yake faɗa mani irin waɗannan kalaman? Ina miskilancin? Ina sarautar? Ina haɗuwar? Ina izza da kuɗin? "Duk ya ajiye su a gefe." Wata zuciyar ta bani amsa. Idanuna cikin nashi, hakan ne ya sanya ni saurin janye nawa idanun. Ya Ameen ya haɗu iya haɗuwa, hatta da fuskar shi ba zan iya jure ma kallo ba, balle kwayar idanun nashi. Kallona na maida wajen da motar Sir Salim take. Baya wurin, kaman yanda ban ma ji ko tashin motar tashi ba. A hankali na sauke kwayar idanuna gefe, sai kuma na saki wata nannauyar ajiyar zuciya kaman wadda aka shaƙe sannan aka saki. Yakai tsawon minti biyar yana kallo na, har saida Naji kallon yayi mani yawa, ga kwayar idanuna tana yawo a ƙasa, kaman wadda take ƙoƙarin gano wani abu. Wani Ya tafi wani Ya zo. Ikon Allah kenan. Lallai rayuwa tana garawa dani kaman garin tayar yaro. Miƙewa tsaye naga yayi, yana mai ɗan sakin murmushi iya gefen baki, wanda ya ƙara ƙawata mashi fuskar tashi, lokaci guda yana mai ƙoƙarin saka glashin idanun nashi. "Muje ki raka ni ko?" ya furta a hankali cikin wata irin salon murya, kai kace da wata sarauniya yake magana. Ban miƙe ba, kaman yanda ban kalle shi ba. "Kada kisa inyi Abunda zai baki kunya fa" Ya furta cikin wani irin salo, na san zai iya aiwatar da Abunda ya faɗa ɗin. Zumbur nayi na miƙe, ina mai kwasar litattafai na, sannan ce "To yaya muje, yi haƙuri" Ƴar dariya ya saki, muka fara takawa a hankali yana mai ƙara gaya man wasu kalaman da ni fa ina tunanin saida ya rubuta sannan yayi haddar su. Kai idan ka hango mu sai kace irin masoyan nan ne da suka shekara biyar suna soyayya har aka sanya masu rana. Ko ba komai ni a wajena jerawa da Ya Ameen ɗin muyi tafiya a bigire ɗaya abun alfahari ne a wuri na, saboda haka sai na dayaye kawai, gudun kada ƴan tsogumi su fahimci halin da ake ciki. Har bakin motar na raka shi. Ni na buɗe mashi bayan motar, bai zauna ba, saida ya kalleni da wani irin ƙayataccen murmushi alamun ya gode, sannan ya shiga motar ya zauna yana mai kallo na. "Nagode Gimbiya ta" ya faɗa cikin salon da ya ƙara sanyaya mani jiki. Ɗan baya naja a hankali, har yanzu fa mamakin shi bai sake ni ba, Allah gani nakeyi kaman mafarki nakeyi, a hankali ya ɗan ɗaga man hannu alamun bye, sannan yayi salute ɗina, daidai lokacin da motocin suka juya a hankali suna mai barin cikin makarantar. Tsaye nayi kaman wadda aka dasa, da kallo nake bin motocin har suka ɓace ma gani na, daidai lokacin da su Khadee suka ƙaraso inda nake tsaye khadeen ke faɗin "wow Suhan wannan gayen kuma fa? Yariman matasa ne fa! Dama kin sanshi ne? Wallahi gayen ya haɗu, ya tafi da imani na, please ki haɗa ni dashi, wallahi lokaci guda son shi ya kama ni, ina yawan ganin shi a instagram, gayen yana da followers sosai wlh ga kuma naira" A hankali na juyo ina mai maida kallona kan khadeen dake faɗin wannan kalaman. Ga mamaki na kuma, sai kalaman nata suka bani haushi. Bance mata ƙala ba, na shiga zagayesu ina mai wucewa kai tsaye zuwa ɗakin namu. Zuciya ta a cunkushe, saboda na rasa ma tunanin da ya kamata inyi. _Na tafiyar Sir Salim_ Ko _Na zuwan Ya Ameen?_ ~Toh Fans ga Suhn fa ta shiga ruɗu, ku bata shawara please~ _Please Share_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~51~* *Salamatu wannan Page ɗin naki ne, kaman yanda na alƙauranta, kiyi yanda kike so dashi, kuma a dinga karantawa oga shima. Nagode Allah ya bar ƙauna* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Kai tsaye ɗaki na zarce, jina fa nake kaman na wani zauce,Ya Ameen? da kanshi? Bakin gado na samu na ɗan ɗosana. Sai kuma me? Tafiyar Sir Salim ke mani kai komo. Sai kuma hango tahowar Ya Ameen with full confidence. *"Huh"* Na saki wani irin huci mai tare da ɗan sauti. Daidai shigowar su Khadee ɗin. Gani na da sukayi zaune dafe da kai, ya sanya suka nufi inda nake. Tsakiya suka saka ni, Khadeen ce ta ruƙo mani hannuwa,sannan ta fara cewa "Suhan kiyi haƙuri, naga kaman kinji haushi don nace ina son Yayan cen naki, Nidai nasan ba wani abu tsakanin ku, tinda maganar Sir Salim ta riga taje gidan ku, kuma ni ina ganin wannan ba wani abu bane, wanda yace yana son naka ai kai yake so, wallahi ganina dashi na farko naji ya kwanta mani, tin kafin ma in ganshi a zahiri, duk da nasan cewa yanda yake da masoya, sannan gashi da kyau uwa uba yana da kuɗi, kada kiyi tunanin dalilin da yasa nace yayi mani kenan, a'a wallahi ko ɗaya, so ne na tsakani da Allah ya kama ni a take, ki taimaka mani koda number ɗinshi ce, insha Allahu ni zan ganin nayi ƙoƙarin na kafa kaina, duk kuwa da cewa ni kaina nasan ya wuce da ajina. Amman hakanan nake sonshi, koda kuwa zai wulaƙanta ni, haka kuma koda yana da mata uku, wallahi na yarda zan shiga a ta cikon huɗun" Ban kalle ta ba, saidai tabbas nasan kalaman ta suna ratsa zuciya ta, wani kumbura naji zuciya ta nayi, sai kuma Naji kaman ƙofofin hancina na ƙara buɗewa, kaman iskan da nake shaƙa tayi mani ƙaranci. Raihana ce ta maida kallon ta kan Ƙawar tata, ita mamaki ma take bata, daga ganin bawan Allah sai ki ruɗe har haka a kanshi? "Khadee ki dena faɗar haka, sanin kanki ne cewa Al'ameen dambulan har Samira ɗiyar shugaban ƙasa tace tana sonshi ya ƙiya, ke shaida ce, ko a Instagram ma mata faɗa suke akanshi, ke wallahi akwai matan auren da naji suna cewa muddin Al'ameen zai kalle su yace yana so, zasu iya kashe auren su su koma mashi, Khadee kin daɗe kina wannan maganar tin ma kafin ki ga Al'ameen a zahiri, sannan tin ma kafin kinsan yana da alaƙa da Suhana, to don Allah kibi komai a hankali, tinda yanzu kin samu link ɗin haɗuwa dashi, insha Allahu komai zai zo maki dasauƙi" Har yanzu dai zaune nake dafe da kaina da hannu ɗaya, yayin da Khadeen ke riƙe da ɗayan. Ganin bam tanka ba ne, ya sanya Khadeen cigaba da magana. "Raihana kin fi kowa sanin na daɗe da ƙaunar Dambulan acikin raina, ke shaida ce, nasha gwada yi mashi magana a kafafen sadarwa amman ko dubawa ma baya yi, nasan kuma ba ni kaɗai bace, muna da yawa. Suhan please ki taimaka ma Ƙawar ki, wallahi ina cikin wani hali" Sai a lokacin na ɗaga idanu na na kalle ta, duk tabi ta koma kalar tausayi, lallai soyayya banzar abu ce, raɗaɗin rabuwa da Salim ɗin bai sakeni ba, gashi Khadeen kuma tana tara ta da wata magana ma marar amfani. To koni dai daya ce yana so ban gama gasgatawa ba, gani nakeyi kaman yana da wani ƙudirin daban, ƙila so yake sai Mom ɗinshi ta yanka ni, ta kakkatsa namana sannan. Ummata ma da tayi aure a gidan don bani da yadda zanyi ne. Daƙyal na buɗe baki na da yayi mani nauyi na fara cewa. "Khadee kiyi haƙuri don Allah, ni yanzu ba wannan ne a gabana ba, Al'ameen da kike magana kuma Sam bashi gabana, saboda bana fatan kai kaina inda Allah bai kaini ba, kuma ko ba Salim bana tunanin zan iya yadda da Al'ameen, domin kuwa ni nasan yafi ƙarfi na" Da mamaki duk kansu suke kallo na, masalan ma Khadee da bata kai ga fahimtar inda zancen nawa ya dosa ba. "Excuse me Suhan, wai me kike nufi ne da wannan maganar taki? Bamu fahimce ki ba fa" Cewar Raihana da tsabar mamaki ya cika ta. Maida kallona nayi kanta. "Eh Raihana, ina nufin iyaye na basu yarda da maganar aure na da Sir, Salim ba, Al'ameen shine wanda suka zaɓa mani, shine suke so in aura, kuma suna fatan ace nayi masu biyayya, ko wannan zuwan da Al'ameen ɗin yayi, yazo ne wai ya bayyana mani soyayya, Abunda bana tunanin kuwa mai yuwu wa ne" Zumbur Khadeen tayi ta miƙe daga kusa dani. "What?, me? Me kike faɗa ne Suhan? Dambulan ne wanda zaki aura? Are u sure? Shine yazo bayyana maki soyayya kika tsaya kina tarabbabi?" Tana gama faɗar haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice a sukwane. Raihana ce ta maido hankalin ta kaina, tin bayan da muka raka Khadeen da kallo. " Masha Allah Suhan nayi maki matuƙar murna, baki buƙatar wani tunani, ki amince, Al'ameen ba irin mazan da zasu ce suna son mace bane ta tsaya masu yanga ko jan aji, wasu ma neman irin tasu soyayyar suke da kuɗi basu samu ba, ƙaramn musali ki kalli Khadee, yanzu ta zama abun tausayi, ta daɗe tana dakon soyayyar shi, maganar ce dai bamu taɓa yi ba, gashi yau da ta ganshi a zahiri ji take kaman ta bishi, kaman tayi hauka, kinsan da inda kuke zata je ta same ku? Nice na hana ta? Kiyi haƙuri Suhana kibi zaɓin iyayen ki, shi kuma Sir Salim Allah ya bashi daidai shi, Amman wallahi baki buƙatar sai na faɗa maki kunfi da cewa da Dambulan" Itama kuwa kalaman nata sun ratsa ni matuƙa, to saidai.... Kallon ta nayi, ina mai cewa "Raihana please ki gaya mani ni ba mace bace? Ban kai a soni ba? To ta yaya zai ɓullo da kalmar soyayya a gareni da niyyar cimma wata manufa tashi?" Da mamaki take kallo na. "Shi wa?" Ta tambaye ni. "ya Ameen" na bata amsa kai tsaye. Girgiza kai ta shiga yi. "Ke kanki Suhan kinsan idan ba don soyayya gaskiya bace, to da babu Abunda Dambulan zaiyi dake, kiyi haƙuri ba cin zarafi bane" "Kin fi kowa sanin irin matan da suke rububi da faɗa akanshi.Sai gashi duk ya tsallake su, ya kawo kanshi gareni, so bana tunanin ma idan har zaki wani tsaya ɓata lokaci wurin amsawa" Har yanzu fa ina tababa. Ga wani irin mugun tausayn Sir, Salim dake ratsa mani zuciya. Bance mata komai ba, na jawo waya ta na shiga neman number ɗinshi. Bugu uku ya ɗaga, cikin sanyayyar murya yake ce mani "Suhan baƙon naki har ya tafi ne?" Ban iya bashi amsa ba, sai ma rumtse idanu da nayi. Da mamaki Raihanan ke kallo na, bata kai ga fahimtar wanda na kira ba, saida taji ina cewa. "Am sorry Sir, wallahi ba laifi a bane, kayi haƙuri don Allah" Cikin wani irin yanayi, shima tausayin ta yake ji, duk da yasan cewa wanda Allah ya bata, ya fishi komai, infact ma ko abota ya samu yayi da Al'ameen abun alfaharin shi ne. Cikin wata irin murya ya shiga cewa "I understand Suhan, please dont burder your Self, let the bygone be gone please, bama da zaɓi illa hakan" Bai kai ga ƙarasawa ba wani irin kuka ya ƙwace mani. Kashe wayar nayi, ina mai faɗa wa jikin Raihana. Rungume ni tayi tana bubbuga bayana alamun lallashi. Shi kau ta cen ɓangaren kashe wayar ma yayi baki ɗaya, ko zai samu salama acikin zuciyar shi. Ba daɗewa dama Ammi ta kira shi ta ƙara kwantar mashi da hankali. A haka Khadee ta dawo ɗakin ta same mu, Raihana nata lallashi na, da kallon idanun ta kuka tayi, ko ba komai tasan ta rasa Al'ameen ɗin kenan, ashe ma tana rayuwa da wadda zata zama matarshi a ɗaki guda, ba tare da ta san hakan ba. Bata ce mana ƙala ba ta haye gadon ta ta kwanta. ********* Ƙarfe takwas a gida tayi masu, kai tsaye sashen Mom ɗinshi ya nufa, saboda duk yau basu gaisa ba, ba wanda ya tadda, su Afnan ma basa nan, sun je gidan Nihal amman driver yaje ɗauko su. Hakan ce ta sanya shi hayewa saman zuwa ɗakin Mom ɗin kai tsaye. Kwankwasawa yayi, daga ciki ta bashi izinin shiga. Ita kanta bata ɗauka yaron nata bane. Tana zaune bisa wata sofa ƙwaya ɗaya tal, da table a gaban ta, lissafi take ta faman yi, saboda busness ɗinta yanzu yanda take ta sake haɓɓaka. Bakin kujera ya zauna kai tsaye. Barin abunda takeyi tayi ta taso. Kusa dashi ta zauna cikin murmushi ta kamo hannun nashi tana faɗin "Son barka da shigowa, daga ina kake haka? Naga kaman ka gaji. Shima ɗan murmushn ya saki iya leɓo, sannan ya kamo hannuwan ta yana mai ɗan basu peck haka kaɗan " Mom wallahi kaman kin sani, wata ƴar tafiya nayi, gashi na gaji shine kafin in kwanta nace bari inzo in ganki" Ya faɗa a gajiye sannan da ƴar sha-gawaɓa irin ta yaran masu kuɗi. "Ayya Son, gashi ko abinci baka ci ba kana maganar kwanciya, bari in sanya Maree ta kai maka abincin.." "Mom! Sau nawa zance banson kina barin yarinyar nan na shiga man sashe wai? Baki ga yanda take ba? Ko tsabtar kirki fa bata da, please Mom, ina Afnan ne? Taje ta kai mani mana" Ƴar dariya ta saki, wai wanda ke son Ƴar aiki, shine yanzu yake nuna yana ƙyamar ƴar aiki. "Afnan basa nan, sun je gidan Nihal da Feena, Amman suna hanya, na tura driver yaje ya ɗauko su, idan ta dawo sai ta kawo maka, kada fa kayi bacci Son" Miƙewa yayi yana faɗin "Better Mom, Good night" Bai jira cewar ta ba, ya fice abinshi, yana mai sauka daga saman ya nufi part ɗinshi kai tsaye. A harabar gidan ne yaci karo da Maree ɗin, sake ɗaure fuska yayi, domin ya kula yarinyar tana neman shisshige mashi, Amman soon zaiyi maganin ta ne" Ita kuwa Maree tsaye tayi galala, kai in banda so ma yana shashasha, ita kanta tasan gayen ya wuce da iyawarta sau million ma ba sau dubu ba. ******** Saida ya gama komai, wanka da duk Abunda zaiyi, wajen cin abinci ne ma ya ɗan ɓata lokaci, saboda Afnan data zo ta tsare shi da surutu, anan ne har take ɗan faɗa mashi Hajiya Zainab tazo gidan jiya, kuma tana tunanin Mom tayi mata wani abu marar daɗi. Sam bai ji daɗin labarin ba, komai akace Mom ɗin tashi tayi, ba zai musa ba, ya san halin ta sosai, fata dai yake yi Allah ya shirya mashi Mom ɗin tashi, domin yana matuƙar ƙaunar ta, ko dan irin yanda take nuna mashi so a fili muraran a ko ina kuma, don dai wasu halayya nata da baya so kwata kwata. Har saida ya kulle ko ina, ya sallami bodygurd ɗin nashi da ya basu wani ɗan ƙaramn flat kusa dasu, duk da baya so yanda suke binshi ko ina zai je, Amman Mom ce da Dad suka matsa akan dole ya samu masu kula da lafiyar shi, gudun sake faruwar abunda ya faru dashi a America. Yau kiranta yayi niyyar yi, baya jin idan text kawai zai iya bayyana mata saƙon zuciyar tashi. Wani irin shauƙi yaje jinshi a ciki, tin bayan barowar tashi wurin ta. Shi kaɗai sai ya samu kanshi da sakin murmushi akai akai, abunda ba halayyar shi ba kuma, koda cen idan yaga Bilal ɗin ya zage soyayya da Ummi a waya, sai ya ɗauka kaman baya da abun yi ne. Yau gashi shine ya faɗa komar son Suhan ɗin *Abun kamar da wasa* yarinyar da ta taso gaban shi, yarinyar da yake ma kallon kaman Afnan, Saudat, ko Nihal, yau ita ce wai yake so, yana jin wani tiririn sonta na dakar mashi zuciya. Ko bayan da ya ɗauko wayar, ya daɗe yana jujjuya ta a hannun shi, shawarar yake ko ya kira ko ya ƙyale ta, kada ta raina shi, ko taga kaman ya cika takura ne, bayan gashi ya san yaune ranar da ta rabu da Saurayin nata, kuma bata da tabbacin cewa bata sonshi, Amman duk dai yanda zaiyi ya kafa tashi gwamnatin sai yayi, shine fa Al'ameen Dambulan, matashin da kowa ke ganin ya kai, to ta yaya zai nuna gazawar shi akan abunda yake so? A hankali dogon ɗan yatsan shi ya sauka kan number ɗinta. Bai yi mata saving ba, saidai ya haddace number ɗin tin lokacin da kiran nata ya shigo wayar tashi a karo na farko. Tayi ringing kusan sau shidda ba'a ɗaga ba. Har ya ynke ma kanshi cewa ko tayi bacci ne? Cen cikin murya mai kama da ta wadda ta gaji, ko tayi bacci ta ɗauka yaji ƴar siririyar muryar ta tana mashi sallama. Saida illahirin jikin shi ya amsa, lumshe ido yayi yana mai sake buɗe su, daidai lokacin da yaji ta kuma doka mashi wata sallamr. Wai dama haka soyayyar take? Shiga takeyi cikin jiki tayi gunduwa gunduwa da sassan jikin mutum? Ta yaya akayi ma tuni bai shaida cewa tana da zaƙin murya har haka ba? Ashe dai ilimi, kuɗi kyau ba sune abunda ake kallo a jikin mace ba ace ana sonta. Sai gashi shi, yarinyar da kowa ke mata kallon bata kai ba, shi ita ce zuciyar shi ta naƙalta mashi sonta har haka, kuma yake ganin ta kai ɗin a idanun shi. Yaushe ne ma ya faɗa cikin rububn son nata har haka bai sani ba? Jin zata kashe wayar ne ya sanya shi saurin cewa "Hold on dear" Wayar na cire a kunne, na sake kallo, lallai number ɗinshi ce, to ya san bacci yake ji kuma ya kira ni? Kallona na maida kan Khadee da take riƙe da littafi Amman ba karatun takeyi ba, kaf hankalin ta yana a kaina. Samun kaina nayi da sake narkewa, bansan dalilin nawa nayin haka ba, illa iyaka dai kaman ina son in ɗan ba Khadeen haushi ne ko yaya ne,kaman yanda ta bani ɗazu itama. "Shine kanaji ina ta sallama kayi mani shiru?" Nima na samu kaina da faɗa cikin ƴar shagwaɓa. Murmushi ya saki mai aji, kai kada fa yarinyar nan ta zauta shi. Tashi yayi zaune yana mai jingina bayan shi da makarin gadon. "Please wake magana ne? Naga ana ta kira na da wannan number ɗin tin ɗazu, please ko zan iya sanin wa kike nema?" Cikin mamaki na ƙwalalo idanu,😳 nice ke kiran shi tin ɗazu,🙄 to yaushe ma na kira? Nasan nidai tinda ya tafi ban kira shi a waya ba. To ko na latso ne ban sani ba? Minimize nayi na shiga call log, saidai babu wani alamun kiran da nayi ba tare da na sani ba. Maida wayar nayi a kunne, shikau jin nayi shiru, sai ya cire wayar a kunne ya danne mouse ɗin ya shiga ƙyalƙyala dariya. Yau sai ga Ya Ameen ɗin bisa gado, har yana ƙyaƙyatawa da kuma yin jifa da fillow alamun jin daɗi. Jin ina magana ne ya sanya shi maida wayar a kunne. "Ya Ameen ni fa ban kira ka ba, ni yaushe ma na kira. Bayan nace bazan kira ba" Na faɗa cikin suɓutabbaki. Sai bayan da na faɗa ne, sai kuma na ankare da kasassaɓar da nayi. Cikin ƴar dariya da zaulaya ya shiga cewa. "faɗi gaskiya yarinya, ko baki kira ba ai kina zaman jiran kiran nawa, Shiyasa ma bakiyi bacci ba ko?" Turo baki nayi kaman yana gabana. Sai kuma na shiga cewa "ni Allah ma sai na kashe wayata, sai zaulaya ta kake yi" na faɗa cikin shagwaɓa sosai, wadda ko Umma ma ban taɓa yi mata irin ta ba. "Yi haƙuri, yi haƙuri my dear, wasa nakeyi" ya faɗa yana mai ɗaga hannu kaman ina gaban shi. "Ban gaji da ganin ki ba dear, please ya za'ayi, tinda na taho sai nake jin kaman nabaro maki gabaki ɗaya zuciyar tawa my wife" Ɗan murmushi na saki, ina mai komawa na kwanta. Cikin ƙwaƙume fillow ɗin da bansan nayi ba nace "Kai Yaya, kana sani ina jin kunya fa" "Huh". Ya saki ajiyar zuciyar da har saida Naji fitowar hucin ta a cikin wayar. "Video my dear wife please" "Bangane ba Yaya" "Au baki cenza sunan ba ko? Dont ever call me Yaya please. On your data" Ya faɗa yana mai katse wayar. Da kallo nabi wayar, ina mai ɗan satar kallon Khadee da ta juya mani baya, ban iya hango fuskar ta, Amman yanda take motsi ya tabbatar mani da ba bacci takeyi ba.Hannu na sanya kaman wadda akayi ma dole na kunna datar. Ban gama tunanin ba naga kira ya shigo waya ta ta application ɗin We-Chat. Ban san ya yanayin fuska ta yake ba, balle gashi ma nayi kuka ɗazu, duk da dai nayi wankan kafin in kwanta. Gaza amsawa nayi, Nifa har yanzu ban yarda Ya Ameen bane wannan. Wani kiran ne ya sake shigowa wayata. A hankali na ɗaga, ina mai tashi zaune. Tar nake kallon fuskar yi. Hasken shi har wani koɗa koɗa yakeyi, duk da dare ne, saidai Hasken farin glop ɗin ɗakin nashi da yake tar, ya taimaka wajen ganin fuskar tashi fes a idanun nawa. Sajen shi ya sake kwanciya luf a saman fuskar, kaman an zana mashi shi, gashi baƙi wuluk gashin kuma gazar-gazar. Bakin nan nashi kaman ya shafa Light pink ɗin lipstick, har wani walƙiya yakeyi. Gashin idon nashi Zara-Zara, kaman zai tsole mani idanu, ni da nake ta cikin wayar. "Kallon me kike mani haka?" Ya faɗa, cikin hura ma screan ɗin laptop ɗin tashi iska, kaman yana a gabana. Sai kuma naji kaman da gaske iskan ta fito a gaske. Ɗan lumshe idanun nayi ina mai kauda fuska ta. "Ya kika kauda fuska my wife?, please ki kalle ni mana" Ya faɗa shima cikin wani irin salo da ɗan rage girman idanun nashi, alamun yana cikin tsabar soyayya. Hakan ya sanya yayi masifar kyau, har dimple ɗinshi na loɓawa Ɗan waigowa nayi, ina mai kallon shi ta gefen ido. Jan Laptop ɗin yayi kusa dashi, yana mai kwantawa a ruf da ciki,ya kara fillow mai taushi a ƙasn haɓar shi. hakan ya sake ba fuskar shi damar fitowa ta cikin screan ɗin. Wani irin duka naji gabana yana yi, kaman yana a gaba na. Dukka hannuwan shi ya sanya yana mai tallafo haɓar shi dasu. Idanu ya zuba ma ni, waɗanda suke taimakawa wajen ƙara rikita ni. A hankali na janye idanun nawa ina mai faɗin "Ya hanya?" "Ki bari sai in ke kika kira, sannan ki tambaya, ba kince ba zaki kira ba? Kin cika wauta Suhan" Ya faɗa yana mai son ganin yanda zanyi da fuska. Har yanzu na kasa kallon shi, cen na tsinkayo muryar shi yana mai cewa "Baki jin zafi haka kike zaune da hijab? Duk da dare yayi, gashi kuma ku kaɗai ne a ɗakin" Bansan lokacin da na kalle shi ba. "Ai yanzu da kwai maza" Na faɗa cikin ɗan tura baki. "maida bakin, kafin inyi abunda zai baki kunya. Ina mazan suke?" Ya faɗa cikin ɗan ɗaure fuska, saboda ya kula da abunda nake so ince. Da hannu na ɗan nuna shi, ina mai faɗin "Gakanan" Ɗan waiwaya wa yayi yana mai faɗin "ban ganshi ba fa" Ya faɗa alamun yana neman wani abu. Bansan lokacin da na ƙara turo baki gaba ba, sai ji nayi yana cewa "zaki bar wannan al'adr ta turo baki gaba, don duk lokacin da kikayi shi a gabana hum...." Ya faɗa yana mai ɗan kanne ido ɗaya. Kunya ya bani sosai, har saida na kife wayar a kan cinya ta. Khadee ce ta juya ta sake kwanciya, ta yadda zata iya gani na kai tsaye. " Yaya bacci nakeji" na faɗa, bayan na ɗaga wayar. "Saidai kuma ni gashi ban gaji da ganin wannan ƴar kyakkyawar fuskar ba" Ya faɗa kai tsaye, yana mai ɗan ɗaure fuska. Bance komai ba, illa sauke kaina da nayi ƙasa. "In faɗi wani abu?" Ya faɗa cikin salon tambaya, sannan da ƴar zaulaya. Kai na ɗaga mashi, ba tare da nace komai ba. "tashi yayi zaune sosai, ya ɗauko laptop ɗin zuwa bisa cinyar shi. "Suhan na dawo lafiya, saidai na taho tare da matuƙar kewar ki, ban ƙi ba ace gobe ne za'a ɗaura mana aure dake, banaso kina mani wani kallo daban, illa kallon masoyn ki, mijin ki, kuma uban ƴaƴanki, ina ƙaunar ki har cikin zuciya ta, wanda bansan lokacin da hakan ya fara faruwa ba a rayuwa ta. Suhan ki yarda dani don Allah, nayi maki alƙawarn kulawa dake da rayuwarki fiye da yanda nake kulawa da rayuwa ta, da kuma kaina, amincewar ki nake buƙata, insha Allahu gobe zan samu Dad da maganar ayi bikin mu kwana kusa, saboda Na ƙagara inga na mallake ki a matsayin mata, ko ba komai shekaru na sun fara ja, ina buƙatar mace a kusa dani, ina da abubuwa da yawa da nake buƙatar mataimakiya a kusa dani, ba wadda naga ya dace, ba wadda naga ta cencenta, *Sai ke* kece daidai ni Suhan, ke nagani kuma nace *ina so,* don Allah ke zan aura Suhan, ba zan iya cenza wata a madadin ki ba, ki amince mani Suhan" Ya faɗa cikin wani yanayi, wanda dab zuciyar shi take kusa da tsinkewa saboda tsabar wata irin wutar soyayya dake azalzalar zuciyar shi. Ajiyar zuciya muka sauke kusan a tare. A hankali na ɗago kaina ina mai kallon fuskar shi. "Talk Suhan" ya faɗa cikin alamun roƙo. Bana iya jure kallon nashi, a hankali na kuma sauke wata ajiyar zuciyar. Sai kuma nace "Ya Ameen Allah ina jin Kunyar ka, kaifa *Yayana* ne" "Stop Suhan,Stop, better Stop please; mubar maganar kunya or something like that, ki amince kawai nake buƙata, I promise u, zan sanya ki manta da wata abu wai ita kunya a tsakanin mu, ki bani kwana uku rak Suhan, Amman fa duk da haka zan tuntuɓi Dad da maganar zuwa safe insha Allah" A hankali na shiga ɗaga mashi kai, alamun na yarda, cikin wata irin kunya dake daɗa malalowa a cikin zuciya ta. "Yessssss" ya faɗa, yana ɗaga hannu kaman wanda yaci wasan kwallo, sai kuma yace "Thanks u my Love nagode Allah ya barmu tare my Wife" Ya faɗa cikin tsabar farin ciki, ni sai ma ya bani mamaki. Kaman ba shine ya Ameen ɗin da yazo ba ɗazu, kaman ba shine ake tsaron lafiyar shi ba, kaman ba shine ake ma kirari ba ɗazu. Sai gashi yanzu zaune yana zuba man zallar kalaman soyayya, sai gashi bisa gado shi kaɗai yana ƙure ni da kallo iyakar gaskiyar shi, sai gashi wai ni Suhan yau ni Al'ameen ke bayyana ma Sirrin zuciyar shi. anya kuwa..... Har yanzu na kasa yarda da haƙiƙanin gaskiyar wannan al'amari, dole ne zuwa gobe in kira Umman tawa inji abunda yake shirin faruwa, idan Abunda yake faɗa gaskiya ne, ya labarin Hajiya Kubra? "Wife ki kwanta kiyi bacci, but make sure u dream with me" ya faɗa cikin wani salo. A hankali na sauke hannu na kan screan ɗin da sauri ina mai faɗin "Nagode Yaya, i will" ko kafin in kashe wayar ya manna mani wani irin hot peck, yana faɗin "I Love U With All My Heart Wife" ya faɗa yana waving ɗina da hannu. Zamewa nayi na kwanta, bayan na tura wayar a ƙarƙashin fillow. Gabaki ɗaya na rasa yanda zan fasalta wannan al'amari, anya kuwa Umma tasan da wannan zance? Kaddai ace shi kaɗai ke kiɗinshi, kuma yana rawar shi. A hankali idanuna suka kuma sauka kan Khadeen. Tausayi ta bani, duk maganganu da yake faɗa tana ji fa, kada ma taga kaman saboda cin fuska ne nayi. A hankali na tashi daga bisa gadon nawa ina mai nufar inda take kwance. Zama nayi kusa da ita ina mai dafa jikin ta. "Khadee tashi muyi magana" "Bacci nake ji Suhan, ki bari sai da safe" Ɗan jim nayi, sannan na miƙe ina mai cewa "To Khadee as you wish" Komawa nayi bisa gadon nawa, ina mai zare hijab ɗin na kwanta, cikin ɗinbin mamakin abubuwan da suka faru duka tsawon yau ɗin. ***** Tin bayan da ya rufe laptop ɗin, sai kuma ya faɗa kwance bisa gadon, shi yau jin shi yakeyi sakayau, kaman ba shine ya gaji ba, kaman ba shine yake jin bacci ba. Kwana uku rak ya ɗaukar ma kanshi, kafin nan insha Allahu sai yasa ta fara kiran shi da kanta. Blanket ya jawo, yana mai ɗaukar remote ɗin Ac ya ɗan ƙara ƙarfin gudun ta, yana mai kwanciya ƙwaƙume da fillow, assuming yakeyi dama ace Suhan ɗince..... Wani irin farin ciki da annashuwa ce ke shigar shi, yau Al'ameen Almustapha Dambulan ya faɗa soyayya....... *Allah ya kauda idon waɗanda zasu kawo cikas a al'amarin* _Share Please_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~52~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Koda na farka washegari, abubu da dama ne ke kai kawo cikin zuciyar tawa. Sir Salim, Ya Ameen Waɗannan sune mutanen da suka saka ni tsaka mai wuya ayau. Koda muka gaisa da khadee, kaman ba ita bace wadda ta birkice mani jiya, duk da dai naga suna magana da Raihana da safe, saidai bansan abunda suke tattauna wa ba, tinda baus sako ni ba. Ganin ta da yaye dani ne, ya sanya ni nima share wa, nayi mata ta ƴan duniya. Karatun namu da ya ɗauko zafi, muna ƙoƙarin cenza aji ne zuwa aji uku, saboda haka komai yake neman dagule mani, ga wannan issue ɗin da ya taso. Hakan ne ya sanya ni bama kaina shawara, zan ajiye komai in fuskanci karatu na, duk Abunda Allah yayi mai kyau ne, Sir Salim kuma na rungumi ƙaddarar rabuwa dashi, biyayya ga iyaye na dole ce, balle ga Umma wadda tasha matuƙar wahala a kaina. Duk da ayau ɗinnan, dole ne in kira ta, domin inji haƙiƙanin zance, ti da ita dai har yanzu bata kirani tace mani komai ba. Shi kuma Ya Ameen zan zuba idanu inga iya gudun ruwan shi, kwana uku rak ya ɗauka ma kanshi wai zai sanya ni in so shi, hmm kaji fa kaman a tatsuniya. Tattara shi nayi na share shi baki ɗaya, har na fito lecture, nazo nayi wanka na zauna karatu. A haka ne zuciya ta ta shiga saƙa mani in kira Umman, in ban kira ta ba, tunani ma kawai ba zai barni inyi wani karatun kirki ba. Duk da duk inda na nufa yau sai inji ana magana ta data Ya Ameen ɗin, ko kuma inga ana nuna ni da hannu, sai abun ya ɗan tsaya mani arai, ni da yabi ta shawara ta ma da bai iske ni makarantar ba, kaman yanda kowa ya san alaƙa ta da Sir Salim. Bugu uku nayi ta ɗauka cikin sallama mai cike da natsuwa, umman tawa ba dai dattako ba, komai take yin shi cikin natsuwa ne, duk da nima na biyo halin ta, amman sai nake ganin kaman ma ban kai ta ba, tinda nesa ba kusa ba, ta fini kauda kai a al'amurran yau da kullum. Cikin ladabi na gaida ta, tambaya ta ta shiga yi karatu ina mai bata amsa. Cen kuma sai nayi shiru, ban kuma katse kiran ba. Hakan ne ya sanya ta ɗan murmusawa, ita ta haifeni don haka ko gyaran murya nayi tasan abunda nake nufi. Ɗan gyaran murya tayi tana mai faɗin "Mamana ina fata dai lafiya ko?" Muskutawa nayi bisa ƴar daddumar ɗana shimfiɗa ƙasa, da yake ɗakin ba kowa sai ni kaɗai, hakan ya bani damar sakin jikin yin wayar. "Umma maganar Malam Salim ce, yazo ya same ni da maganar wai an dakatar dashi ga nema na, kuma yana faɗa man wai shi ya riga ma ya janye, kun zaɓa mani wani. Sai kuma ga Ya Ameen ya kuma zuwa mani da wata maganar jiya Umma, shine na kira ki inji Abunda yake faruwa" na ƙarshe cikin ƴar jin kunya, duk da bata gabana. Ɗan jim tayi, sai kuma ta sake murmusawa. "Hakane Mamana, saidai ina fatan zakiyi mana haƙuri, mun yanke hukunci akan kanmu, ba tare da jin ta bakinki ba, nasan ke ɗin mai biyayya ce, ko da Alhaji yazo mani da maganar ba zan iya musawa ba kaman yanda kema nasan ba zaki ƙi yaron nashi ba" "Hum" nace sai kuma na cigaba da cewa "Umma Hajiya Babba fa, ni ina jin tsoro, bata son mu fa Umma ta yaya zan auri ɗanɗanta?" na faɗa cikin wani yanayi, wani miki mai ciwo na taso mani daga ƙasan rai, abubuwan da Hajiya Kubra tayi mana tin tasowa ta ne ya shiga ɗgao mani. "Ba ruwan ki da Mamana, kedai biyayya ce taki, kiyi mata biyayya, insha Allahu watarana zata soki, bana iya watsa ma Alhaji ƙasa ne a ido Shiyasa kawai na amsa mashi, yaron na ƙaunar ki, tinda shine ma yaje ma Alhaji da maganar, kuma koda ya shigo cin abincin rana ya sake tuntuɓa ta da maganar sun tsaida ranar *Auren naku* nan da wata ɗaya mai kamawa, saboda haka sai kinsan irin shirye shiryen da zakiyi. Mamana ki toshe kunnuwa ki, wannan auren ni nasan zai zo da ƙalubale da yawan gaske, sai mun daure gabaki ɗayanmu, sauƙi ta ma shi Alhajin yace mubar komai a hannun shi, kada mu sanya tunanin komai a ranmu, insha Allahu babu Abunda zai faru. Saboda haka ni dai a kullum addu'a itace tawa a gare ku, ina maku fatan alkhairi, Allah kuma ya kaɗe duk wata fitina da ka iya tasowa a cikin al'amarin" Cikin wata irin masifar faɗuwar gaba nake sauraren ta, sautin dukan da gaban nawa keyi ma, ya ci ace umman tawa ta jiyo daga cikin wayar, tuni wata irin zufa ta shiga karyo mani, sai kuma wani irin sanyi ya kama ni, bansan lokacin da jikina ya fara kyarma ba. Sanya biki? Ni da Ya AAmeen??? Wane irin aure ne haka gagab ya zo mani ni Suhana? "Hello Mamana, kina jina kuwa?" Umman tawa ta sake faɗa. Cikin rawar murya na shiga ce mata "Eh Umma ina ji, bana lafiya ne Umma, zan sha magani. Amman Umma don Allah ku duba wannan al'amarin, ina jin tsoro, Ya Ameen ya wuce da ajina Umma, ni ba tsarr auren shi bace na sani, kaman yanda Hajiya Babba ke faɗi Umma" Na ƙarshe cikin wani yanayi. "subhanallah, to maza kisha magani Mamana, insha Allahu babu wani abu da zai faru, ki kwantar da hankalin ki, Muhammadu yaro ne nutsattse ba zai bari wani abu ya faru dake ba, nasan zai ƙoƙarin fahimtar da mahaifiyar shi, kiyi mana biyayya Mamana, zan kuma kiran ki anjima inji yanda jikin yake" Ta faɗa cikin son ƙarfafa mani guiwa. "To Umma sai anjima" Na faɗa in amai katse wayar, sannan na zame na kwanta a wurin ko fillow babu. Wani irin sanyi ne ke rasa ni, bansan irin yanayn da nake ciki ba. Aure ni da Ya Ameen??? Kaman wasa. Kuma shine ya yarda da kanshi? Zan iya cewa Ina da sa'a a rayuwa ta wani fannin, nasan samun Ya Ameen a rayuwa ta ba ƙaramin gata ne Allah yayi mani ba, kuma duk wata ɗita mace zata so ace ita ce a matsayin da nake kai, to saidai al'amarin na tafe da abubuwa masu ruɗarwa masu rikitarwa, sannan ina tunanin tashin hankalin da zai iya biyowa baya. Tin da cen da bai ce yana son a ba ma, munga tasku balle yanzu da zan zama surukar ta?mata ga yaron da tafi so a duk cikin rayuwar ta? Haka su Raihana suka dawo suka same ni, kwance ringis masassara jikina, siada suka taimaka suka kaini clinic aka bani magunguna da allurai, sana na samu bacci ya ɗaukeni. ******** "Friend kasan kuwa mai kake faɗa? Aure a cikin wata guda? Yaushe ma kuka fuskanci juna kai da ita? Ya zaka yi da Mom?" Bilal ɗin da yake zaune bisa kujerar falon ya Ameen ɗin ya faɗa. Tin bayan da abokin nashi yake sanar dashi batun auren nashi mamaki ya cika shi. Cup ɗin dake hannun shi cike da lemon champaign ya kurɓa sannan ya ajiye bisa stool ɗin dake kusa dashi. "Kaga Friend, ni ba dalilin da yasa na kira ka ba kenan, shawara zaka bani, yanda hidimar nan zata tafi, kaga dai yanda abubuwan suke, kuma Mom har yanzu da nake maka maganar nan bata sani ba, Amman Dad yace in bar shi da ita, shine zai sanar dani yanda sukayi. So forget about that matter. Ina so ne a tsara mani biki fiye da tunanin kowa, ina jin ƙaunar Suhan har cikin raina, Shiyasa nake so komai nata ya kasance daban ne a rayuwa" Da mamaki Bilal ɗin ke kallon abokin nashi, lallai soyayya gaskiya ce, watau ita makantar da mutum takeyi gabaki ɗaya, ta sanya ya mance da wani abu wai shi kunya ko? Dariya ya ƙyalƙyale da ita, yana mai dukan hannun kujerar da hannun shi. Ko kallon inda yake Ya Ameen ɗin baiyi ba, ya cigaba da katse latsen shi a waya. Saida yayi mai isar shi, sana ya tsagaita, yana mai ɗan zamiwa daga bisa kujerar yake faɗin. "Watau Friend Abunda yake bani mamaki shine, ka manta wata ranar bida Ummi muna......" "Close that chafter guy" Ya katse Bilal ɗin,lura da yayi iskanci yake so yayi mashi. "OK, OK" Bilal ɗin ya faɗa yana mai sake yin dariyar. Ya san halin mutumen nashi da ƴal banzr zuciya, yanzu za'aji kansu, abun arziƙi ya kona na tsiya. "To friend yanzu ya ake ciki? Me kake so ayi?" Bilal ɗin ya faɗa yana mai daidaita kanshi ga barin dariyar. "Sai wani lokaci kuma" Ya Ameen & in ya faɗa yana mai tashi tsaye. Kai tsaye hanyar fita ya nufa, hakan ya tabbatar ma da Bilal ɗin haushi yaji kenan. Shima miƙewa yayi, yana mai faɗin "Zakaci ubanka ne friend, indai soyayya ce bakaga komai ba ma," a hankali yake maganar. Sannan ya shiga bin bayan Ya Ameen ɗin. Har suka shiga mota bai ko ƙara kallon Bilal ɗin ba. Saida suk bar gidan ne Bilal ya juyo ya kalle shi yana mai faɗin "To ina zaka kaini kuma?" Ɗan ɗaga ka faɗa yayi kaɗan," ina ce kai ka biyo ni? Baka san inda zani ba ka biyo ni?" Shima ya faɗa cikin dakewa. "Sorry Friend, am sorry Ameen, ni fa dariya kawai ka bani, gani nake kaman ba kai bane ka zauce akan soyayya, cikin lokaci ƙanƙani, Amman komai ya wuce, yanzu ka faɗa man yanda kake so ayi" Bai kula shi ba, har suka isa wani katafaren plaza mai matuƙar kyau da tsaruwa. Da mamaki yake kallon abokin nashi, duk da baisan dalilin su ba na zuwa nan ɗin, hakanan ya shiga bin bayan shi har zuwa ɓangaren da yake na turarurruka masu kyau. Ɗauka ya fara yi yana duddubawa. Guda uku ya ɗauka masu masifar tashin ƙamshi da tsada. Sannan ya nufi ɓangaren gold. Banguls, zobuna sarƙoƙi masu kyau. Saida ya gama duddubawa sannan ya zaɓi wadda yake so a bashi. Set ne na sarƙa da ɗan kunne, sai zobe da awarwaro guda uku manya ƙirar Dubai. Sunyi masifar kyau sai ɗaukar idanu suke yi. Haka aka sanya mashi cikin wata farar cover mai kyau da ɗishe ɗishen pink. Shi dai Bilal sai bin shi takeyi kaman zariya, har yanzu kuma yaƙi ko kallon shi. Saidai yana yin da yake ciki ya nuna mashi abokin nashi yayi nisa baya jin kira, watau irin kyautar nan ce ta masoya za'a fara tin yanzu. Wuuu, wani abun sai Al'ameen Dambulan, komai nashi cikin aji yake yin shi, hatta da siyayyar komai mai aji yake zaɓa, classic one. Haka ya nufo mota, Bilal ɗin nata bin shi a baya. Kai tsaye Office ya nufa, yana buƙatar kiran Abie, ɗazu yaga kiran nashi lokacin yana part ɗin Dad suna tattauna wa. Saida ya sanya gift ɗin nashi cikin cupboard sannan ya koma bisa kujerar tashi yayi kira, yayin da Bilal ya kwanta bisa sofar Office ɗin. Abie ɗinne ya ɗaga ta cen ɓangaren yana mai gaida yayan nashi, saida suka gama gaisa wa sannan Abie ɗin ke sanar dashi dalilin kiran. Shi dai Bilal na kwance yana jin su, idanun shi a lumshe suke. Har saida Al'ameen ɗin ya gama wayar sannan ya tashi zaune yana mai fuskantar shi. Shima Al'ameen ɗin shi yake fuskanta, fuskar tashi ba yabo ba fallasa yake sauke wata irin ƴar ƙaramar ajiyar zuciya. "Friend saidai fa ina jin kai ne zaka je, domin Abie ya sanar dani zuwa jibi za'a zauna Meeting akan kamfann nan da suke so mu zuba masu hannun jari, So Kaga ni ina da abubuwan yi sosai, ka shirya ticket, zuwa gobe in Allah ya kaimu sai ka wuce, kaje ka zauna dasu, duk abunda zai yuwu kawai ayi" Shima Bilal ɗin gyaɗa mashi kai ya shiga yi, ko ba komai ya san Al'ameen ɗin a yadda yake ji shi yanzu, ba zai iya matsawa ko nan da cen ba, muddin ba gani yayi an ɗaura auren ba, hankalin shi ba kwanciya zaiyi ba. Saida ya ajiye shi gida, sannan ya wuce gidan shima, da zummar goben kafin ya wuce zai fara biyowa ta office ɗin yaga Al'ameen ɗin sana, saboda akwai muhimman abubuwan da yake so ya tattara mashi ya wuce dasu zuwa goben. Wanka kawai yayi ya zura jallabiyar shi zuwa masallacin da yake mallakn gidan nasu. Shine ma yana sallar, masallacin na tara mutane, go ba komai idan Har Al'ameen ɗin na ƙasar da wuya Kaga wani yaja manyan mutanen salla in bashi ba, wannan ce ma tasa kaf manyan mutanen dake Layin suna matuƙar ƙaunar shi da martaba shi, a matsayin shi na matashin da yake ji da dukiya, ilmi da asali, gashi yana tsayawa jan Salla, Abunda ba kowanne matashi bane zai iya. Ɗakin shi ya koma, kai tsaye kallo ya kunna, Amman Sam hankalin shi baya kan film ɗin Expendable 2 ɗin da suke haskawa a tashar MBC Max ɗin. Wayar shi ya jawo, ya rasa dalilin shi na jin bai kyauta ba, yau ko sau ɗaya bai kira ta ba, baiyi tunanin ita ba zata kira shi ba, saidai Tasan wannan yana ɗaya daga cikin halayyar matan, masalan idan su ne aka nuna ana so, kaf text ɗin da suka shisshigi wayar tashi ya bincike, babu nata ko ɗaya, kai ko na mai kama da number ɗinta babu, wasu daga ƴan matan dake wahala ne a kanshi, wasu kuma daga abokanan shi ne, masalan ma wanda suka san ba lallai ya ɗaga wayar tasu ba. Ji yake kaman ya kira ta, Amman hakan baya daga cikin tsarin nashi na yau, ko ba komai bai tsara kiran nata ba gabaki ɗaya ayau, wannan yana daga cikin salon tashi soyayyar, yana daga cikin salon dasa tashi soyayyar a zuciyar ta. Text ya rubuta lafiyayye ya tura mata. Bai ga reply ba, kaman yanda bai tsammata ba. Sharewa yayi yana mai ajiye wayar, sai kuma ya tuna da soyayyar shi da ya manta cikin mota. Ficewa yayi zuwa motar domin ya ɗauko. Daidai parking lot ɗinne yaci karo da Mom & in tashi ta shigo gidan, cikin haɗaɗɗiyar motar ta take. Kai tsaye shi ya isa ga motar ya sanya hannu yana mai buɗe mata marfkn motar, bayan tayi parking. Da murmushi ta fito tana kallon shi, sumar kanshi ta shafi tana mai faɗin "Son are u at home?". Ɗan gyara tsayuwar shi yayi, fuskar shi babu walwala sosai yace mata "yeah mom, please Mom from where are u at this late hours?" Ɗan ɗaure fuska tayi tana mai faɗin "To ubana, daga inda ka aikeni nake" ta faɗa tana mai dungura mashi jikkar ta, alamun ya riƙe mata kenan. Gaba tayi ya shiga bin bayan ta yana mai girgiza kai, ba son kai, ba son zuciya, dole Dad ya nemi wani ƙarin auren, Mom ɗinshi mace ce har mace, Amman bata iya tsayawa tsayin daka ta kula da mahaifin nashi, in ma a ci sa'a tana ƙasar kenan. A falo suka tada su Aunt Feena da Afan. Ayan ne ya ruga da gudu ya ɗafe jikin Mom ɗin, ɗan ɗaga shi tayi tana mai bashi peck, sai kuma ta ajiye shi tana mai ce mashi "Oya go and play my boy" Sannu da zuwa suka shiga yi mata, Afnan ce ta isa ga yayan nata tana mai amsar jikkar daga hannun shi take cewa "Sweet Bro you Welcome" Ɗan shafo kumatun ta yayi yana mai faɗin "thanks Lil, maza ki kai ma Mom jikkata ɗaki. Gyaɗa mashi kai tayi, tana mai bin bayan Mom ɗin da har ta riga ta yaye ɗan fingilin gyalen dake jikin ta, sannan ta zare fari tas ɗin glass ɗin, tana mai hayewa sama, Afnan na biye da ita. Kujerar da Aunt Feena ke zaune ya zauna bisa yan mai faɗin "Big Sis, ya ake ciki? Ina son magan dake fa" Cike da kulawa take kallon shi, sai kuma ta sanya hannu ta ɗan daki kafaɗar shi. "Gaske kuwa, naga kaman kana man ladabi yau" Ƴar dariya ya saki, wacce ba kasafai yake yi ta ba, yace "Please Lovely sis, ki taimaka, muyi ta a ɗakina, secret ne, bana so kowa yaji" "Amman sai anjima ko?" "Eh Aunt ko zuwa bayan isha'i haka. Please ko Mom bana so taji" Ya faɗa yana mai kamo hannuwan ta. "U Dont have to warry my Bro, zanzo insha Allahu, Allah yasa muji alkhairi" "Alkhairin ne ma, tinda kunyi suruka" Ya faɗa yana mai miƙewa, sannan ya shafo kumatun Nasreem da take ta wasan ta da teddy, sannan ya fice. Kai mashi bugu tayi, saidai bata same shi ba, take faɗin "Bayani zaka yi, kai ɗinne kake wani iya tsayawa kula mace? Aikau da anyi ruwa hadda ƙanƙara" Yana jin ta bia ko tsayawa kula ta ba, ya sanya kai ya fice. Da kallo take binshi, har yanzu dai shine Al'ameen ɗin da ta sani, bai cenza ba ko alama, wannan miskilancin yana ɓata mata rai, some times ma ko wani abu akayi mashi, ba'a gane yana yin ɓacin ran shi, yo miskilanci ma ai ba zai bar shi ba ko kallonka yayi. ********** Na samu sauƙn jikina sosai lokacin d ana tashi, ana daf da fara sallar magariba. Su Raihana ne ma suka taimaka man da ruwan wanka, aikau na ƙara jin daɗin jikina sosai, nayi matuƙar mamakin yanda khadeen ke kulawa dani sosai, kaman wani abu bai haɗamu ba jiya. To koma dai minene dama nayi niyyar sharewa. Abu ɗaya ke damuna, yanda ɗazu Sir Salim ɗin ya shigo yi mana lecture, saidai ya ɗaga mani hannu kawai, kaman yanda yayi ma sauran ɗaliban, ko alama bai bari na fahimci raunin shi ba, ko kuma in fahimci yana cikin damuwa. Kenan ma bai damu da rabamun da akayi ba kenan? Me hakan yake nufi? Salla nayi sannan na ɗan ci indomie ɗin da raihana ta dafa mana. Sake kwanciya nayi, duk jikina ba daɗi, duk da zazzaɓn ya sakeni, sai ɗan ciwon kai dake damuna haka kaɗan. Ƙarar shigowar text ne a waya ta, ya sanya ni ɗan firgita daga duniyar tunanin da na shiga, magangann Umma ne ke ta kai komo cikin ƙwaƙwalwata, kenan da gaske Ya Ameen yake, Soyayya ni dashi? Aure nan da wata ɗaya?to ta ina ma za'a fara ne? A hankali na jawo wayar ina mai duba saƙon da ya shigo mani. Kaman yanda number ɗin take special, haka ta zauna das a cikin ƙwaƙwalwa ta. Da kallo na shiga bin rubutun. _"My Moonlight fatan kina lafiya? Yanda zuciya ta ta yini tinanin ki, nasan kema ta ɓangaren ki hakan ne, Dont worry, insha Allahu gobe akwai special outing, kiyi mani kwalliya sosai, see u tumorrow. Bye take care with full of my love"_ Na maimaita karantawa bansan ko sau nawa ba, shi dai ne ya turo mani. "Hmmmm" na nisa ina mai miƙewa tsaye na fice balcony ɗin ɗakin namu. Ɗan sanyi sanyin iskar bayan magariba ne ya shiga busowa yana shiga jikina a hankali a hankali. Wayar na a hannu na, na rungume duka hannuwan, sama nake kallo, taurari har sun soma bayyana, ga haske wata tar dake haske mani fuska. "My Moon Light" Sunnan da ya kira ni dashi ne ya shiga amsa kuwwa a kunnen nawa. Da kallo na sake bin watan dake maƙale a sararin subhanan. Haske ne mai kyau, mai ban sha'awa, baya kashe ido, sannan zuciya na aminta da kallon shi, ba tare da ta gaza ba. Kenan hakan yake nufi a kaina? Kenan ni haskn zuciyar shi ce, kwatankwacin yanda ya faɗa ɗin, kwatankwacin yanda nake kallo a yanzu ɗin. Bansan lokacin da na saki ƴar siririyar dariya ba, har haƙirana suna bayyana. Runtse idanu na nayi, Meyasa lokacin da Sir Salim yace mani anje neman auren nawa na dinga jinbfaɗuwar gaba? Amman yanzu Ya Ameen ya shaida mani da ranar shi a kaina, sai kuma bana jin komai sai ma wani feeling da bazan iya kwatanta shi ba?. A hankali na kai zaune bisa wani ɗan dankali da akayi ma student na zama, ina mai ɗora duka ƙafafu na duka na rungumo su da hannu, ina mai jingina kaina jikin bango na runtse duka idanun nawa. Fuskar shi ce ta fara kai komo a cikin idanun nawa. Kyakkyawa ne sosai. Zuciyata ta shiga raya mani. Idanun shi masu matuƙar kyau, sune nake gani suna yawo a bisa tawa fuskar. Kaman fa yana jin bacci, kaman wanda yake ma mutum kallon soyayya, to ai shi dama tinda na sanshi haka idanun nashi suke. A hankali na buɗe idanun nawa, ina mai tashi jiki a sanyaye na shige Ɗakin namu. ********* Bansan yanda akayi ba, washegari kuma sai na ganni ina mai tsara wanka, sa'a ta ɗaya bana da lecture a ranar. Saidai su Khadee suka tafi suka barni ni kaɗai a ɗakin. Su kansu saida suka tambaye ni wai sunga ina cikin walwala, dariya kawai nayi masu nace "Kaman zanyi baƙi ne yau daga gida" Khadee na jin haka ta fice, raihanan ce tayi murna, tana mai cewa "agaida shi idan yazo, Allah yasa mu dawo mu tadda shi." Da "Ameen" na bita ina mai shigwa toilet ɗin. ******** Tin safe ya shirya sosai, Office ya wuce bayan ya shiga sashen Dad ɗin gaida shi, acen ya tada Mom ɗin tashi, Baisan dalilin faɗuwar gaban nashi ba. Gaidata yake yi, Amman daƙyal ta amsa tana mai jifan shi da wani irin mugun kallo, shima don Alhaji Mustapha ɗin yana wurin ne. A haka ya fito jiki a sanyaye. Saida ya shiga sashen Umma, itama a falo ya tadda ta, cikin matuƙar ladabi ya gaishe ta, abun har yaso bata kunya, duk da yanzu yaro yake a wurin ta, Amman dole ta wani fannin yayi mata kallon suruka. Saida ya shaida mata zai je wajen Suhan idan tanada saƙo. Cewa kawai tayi ya gaida ta da jiki, saboda jiya tace mata bata jin daɗi, taso ta kira, kuma sai tayi ta neman wayar ta taƙi shiga. Da mamaki sosai ya fito daga part ɗin Umman, ashe bata lafiya, shine kuma bata iya kiran shi ta sanar mashi. Yana jin masu aiki na ta faman gaida shi, saidai ya ɗaga masu hannu, haka ya isa office ɗin cikin ƴar damuwa, ga damuwn kallon da yaga Umma nayi mashi, gudun shi ace kada Dad dai yaje mata da zancen ne. Sai kuma da uwar rashin lafiyar Suhan ɗin, duk shirin da yayi kada fa ace ya tashi a banza kenan, to ba lafiya ina Kaga magana. A office ɗin ya tadda Bilal har ya iso, cikin shirin shi yake na barin ƙasar, suit ce jikin shi baƙa da ƴar ciki Light blue sosai, sai tight dark blue, Bilal ɗin yayi kyau sosai, gashi dama ɗan gayu mai ji da ilimi da wayewa sosai. A gaggauce Al'ameen ɗin ya fitar da komai ya haɗa mashi cikin brief Case ɗin, sannan ya ɗauke shi zuwa Airport. Bai sanar dashi komai ba, dama kuma shi mutum ne mai matuƙar zurfin ciki. Bai jira tashin su Bilal ɗin ba ya baro shi cen, kai tsaye hanyar zariyan ya ɗauka cikin matuƙar gudu. Ko ba komai hankalin shi ya karkata kuma wajen ganin ya isa ya duba yanayin jikin nata. ******** A guje motar ta shigo gidan, dama kaman zata ɓalle murfin gate ɗin take ji, yanda take ta danna horn ya sanya mai gadi gane cewa ba lafiya. A gaggauce ya wangake mata ƙofar gate ɗin, tinda ya ga Nihal ce gaban shi ke dukan tara tara, ko ba komai ya san zai sha zagi yau. Saidai ga mamakin shi, ko parking daidai bata gama ba, ta ɓalle marfin motar ta shige cikin gidan cikin kuka, ko marfin motar bata tsaya kullewa ba. Ga gudun ta ta shige sashen Mom ɗin tata. Mom dake ɗaki tana shafa hoda a kan fuskar tata, ita har gobe fa bata yarda ba, jinta takeyi zam, ko ƴar 30 ba zata nuna mata ƙuruciya ba. Jin an banko ƙofar ɗakin nata ne, ya sanya ta miƙewa cikin hanzari tana mai fuskantar ƙofar. "Nihal?" Ta faɗa cikin matuƙar tashin hankali, yana mai sakin hodar dake hannun ta, ta tarwatse a ƙasa, cikin tashin hankali ya kamo ɗiyar tata ta rungume. "Nihal Is Ok... Ki faɗa mani me ke faruwa ne? Ya akayi ne? Me ya sa yaki kuka?" Duk a lokaci guda ta ke tambayar ɗiyar tata. Wani kukan ta sake rushewa dashi. A hankali ta shiga janta zuwa bisa gadon. "Nihal i said is Ok" Ta sake faɗa cikin wani tashin hankali. "Faɗa mani mai ke faruwa?" "Mom ba baby bane...." "baby what? Faɗa man me babyn yayi maki?" "Mom cewa fa yayi wai in taho gida sai na koyi girki da wanke wanke da shara da mopping" ta faɗa tana mai sake sakin kuka, da gani dai abun na mata zafi cikin zuciya. Aiko cikin ƙaunar zuciya Mom ɗin ke faɗin "Shi baby ɗinne yace ki taho gidan ku?" Girgiza mata kai ta shiga yi. "To ina house maid ɗinda na kai maki guda biyu?" "Mom duk fa yace su tafi gidan su, tinda ban gode ma Abunda suke yi mani, kuma fa mom basa da tarbiyya ne, basa jin magana, kuma sun cika ƙazanta, gashi basu iya abinci ba, kullum indai yana ƙasar yaci sai yayi mani complain" "ya kore su? Shi ya ɗauke su? Ko shi ke biyan su albashi ne? Dama irin zaman da kike yi kenan a gidan? Shine dan ubanki baki taɓa faɗa mani ba saida ya koro man ke?" Ta faɗa kaman zata doke ta, sai kuma ta jawo wayar ta, tana mai miƙewa tsaye ta shiga tattakawa. Wayar Alhaji Mustapha ɗin ta kira. Bayan ya ɗauka ne ta shiga zayyana mashi Abunda ya faru, cikin masifa take magana, kaman ita ace an koro mata yarinya daga gidan aure? Wannan abun kunya har ina? Kuma ma wai don wulaƙanci yace tazo wani ta koyi aikin gida? Duk irin gatan da take nuna ma yaran nata? Basu taɓa samun wani abu suka rasa ba? Ga issue ɗin Al'ameen da take ta so taci mai garin su? "Ai yayi kyau, sai tazo ta zauna ta koya" Abunda Alhaji Mustapha ɗin ya faɗa kenan yana mai kashe wayar. Da kallo ta shiga bin wayar, kaman ya tazo ta zauna ta koya? Kaji wani zance, cikin harara take bin Nihal ɗin da kallo. "Tashi ki tafi ɗakin ki, kafin Dad ɗinku ya dawo" Ba zaɓi illa miƙewar, a haka ta sauka zuwa falo tana mai sakin wani kukan. Aunty Feena na zaune, itama cikin tashin hankali ta shig bin ƙanwar tata da kallo. "Ke Nihal zo nan, me ya faru?" Ƙarasawa tayi wurin ta, tana mai share kwalla. "Aunty Feena baby ne yace wai in taho gida, sai na iya wanke wanke da shara da girki sannan in koma" Da mamaki Feenar ke binta da kallo. "Shi bby ɗin? To duk ina soyayyar?" Jin Abunda Aunty Feenar ta faɗa ne ya sanya ta wucewa kai tsaye, tana mai sake sakin wani kukan. Cikin girgiza kai Aunty Feenar ke cewa "Nasan za'a rina, ai ba kowanne namiji bane zai iya da halin Nihal da saudat ba, Allah shi kyauta" itama tashi tayi ta fice daga part ɗin baki ɗaya ma, ta nufi garden. Cikin tsabar masifa, ta shiga kiran Al'ameen ɗin. Saida gabanshi ya faɗi ganin kiran nata. Da bismilla ɗauke a bakin shi ya amsa kiran, ya san sauran zancen, ya san Abunda ka iya faruwa, tinda yaga kallon da takeyi mashi da safe gaban shi ya dinga faɗuwa, ko ba komai ya san mai raba shi da ita yau a gidan saidai Allah. Cen ya tsinkayo muryar ta tana faɗin. "Duk abinda kake yi ka baro shi, kazo yanzu maza maza ina son ganin ka" Ta faɗa cike da gadara cikin masifa. "Mom nayi tafiya zuwa Kano, wani abu ya taso mani na gaugawa, Amman insha Allahu dana kammala zan juyo" Ya faɗa cikin son ɓoye gaskiyar inda yake nufa. Ba tace mashi komai ba ta datse kiran. Gabanshi ne ya cigaba da faɗuwa, ko ba komai ya san kwanan zancen. Abu ɗaya zaiyi ya tsira daga masifar Mom ɗin tashi yau, tunkwa da Abunda zaiyi ne ya sanya shi sakin ajiyar zuciya yana mai maida hankalin shi kan tuƙin da yakeyi. ******** To wai kwalliyar ma me nakeyi? Na tambayi kaina, ina mai zirara kalli a idanun nawa. A hankali na ajiye, ina mai tattara kayan shafar na maida su muhalln su. Kayan dake jikina na shiga bi da kallo. Material ne mai masifar kyau, Hafsat ce ta siya man shi, tin lokacin bikin su, yana daga cikin kayan data ɗinka mani, sau ɗaya na taɓa gwada kayan na cire, saboda sai nake ganin kaman ya kama ni sosai a lokacin, gara ma yanzu, tinda ƴar wahalar karatu ya sanya na ɗan rame, kai kayan sukayi mani kaf da kaf, kaman an gwada su a jikina. Gashin kaina a tsefe yake, hakan ya sanya na ɗauke shi da ribom mai faɗi na tuttura shi ciki. Ɗaurin ɗan kwalin ma ban tsaya mashi kyanare ba, ɗaura wa kawai nayi bisa tulin gashin da yake kumshe a bayan ƙeyar tawa. Ga mamaki na kuma sai naga yayi masifar kyau, kaman in saka hijabi, kuma sai na jawo gyale da yayi matching da gyalen na yafa. Ba babban madubi sosai a ɗakin, hakan ya sanya bana ganin kaina sosai, Amman ni kaina nasan nayi kyau, ga wani murmushi da nake yawan saki, don dai ƴar faɗuwar gaba da nake ɗan yi akai akai. Ƙarar wayar tawa ne ya sanya ni juyawa inda take bisa gado na ɗauko. YA Ameen ne. Ga ana ne ya sake faɗuwa. A hankali na ɗaga ina mai furta mashi sallama. Amsa mani yayi yana mai faɗin, "Gani a inda muka haɗu shekaranjiya" "To" kawai na iya furta wa, ina mai katse wayar. Sai kuma na samu kaina da fesa turaruka har kala uku, tini jikin nawa ya ɗauki sassanyan ƙamshi, ni kaina ina jin kaina adaban ayau, saidai dole ne in daure, ba wanda dama cen ya kamata yake ganin kwalliyar tawa illa mijin da zan aura. Saida na ɗauki wayata na cusa ta cikin wata ƴar hand force mai kyau, sannan na rufe ɗakin. A hankali na kulle ɗakin, sannan na shiga taka wa kaman wanda ke jin tausayn ƙasa. Tin da na sha kwanar gabana ke faɗuwa. Cem nesa dani sosai na hango shi. Tsaye yake jingine jikin wata ƴar dunƙulalliyar mota, ƙirar royce-royce 2018. Sanye yake cikin kayan turawa yayi masifar kyau, ƙafar shi Sanye da wasu irin arnan tomps na zallar fatar maciji mai roɗi roɗin ash da baƙi, sai baƙin wando jins dake jikin shi, da ash ɗin riga mai ɗan duhu da baƙin rubutu jikin ta. Haka idanun shi Sanye cikin baƙin glass ba abunda kake hange a cikin su. A haka na shiga taka wa har jikin motar. Turaren dake jikin mu, shine ya fara mana sallama a hanci. A hankali ya zare glass ɗin idanun shi, cikin wani salo ya kuma sakin ɗan murmushi iya keɓo yake cewa "You welcome my Heart beat" Da ɗan kallo haka nake binshi, duk kunya ta baibayeni, wai ni ba zai iya kirana ne da suna ɗaya ba? Kullum da wanda zai kirani dashi.? Ban ɗauka mota zamu shiga ba, sai gani nayi ya zagaya ya buɗe mani murfin gaba yana mai faɗin "Gate in dear" Banyi musu ba, zagaya wa nayi na shiga, saidai kaf hankalina baya jikina, student fa nata kallon mu. Saidai naga shi kaman ma bai damu ba, shima zagaya wa yayi ya shiga, yana mai yima motar key yayi ribos ya juya yana mai ficewa a makarantar. Lumshe idanu nayi, sanyin motar da ƙamshin shi na rasa ni a hankali Samun kaina nayi da cewa "Yaya Ina yini? Ya hanya?" Mun ɗauki hanya, bai juyo ya kalle ni ba, sai gani nayi ya kawo hannu da niyyar murɗe mani baki. A hankali na sanya hannu na, ina mai sauke nashi ƙasa "Am sorry" na faɗa cen ƙasn maƙoshi. Shima ɗan murmushi ta saki, "Kin faye tsoro fa my ƙanwa" Kaina na sauke ƙasa, ina. Ai sauke ƴar ɓoyayyar ajiyar zuciya, ganin mun doshi hanyar barin garin ma kwata kwata. Da mamaki nake kallon shi, shima kallon nawa yayi, wanda saida ya jaza man faɗuwar gaba, idanun nashi na rikita ni, aduk lokacin da suka sarƙe da nawa. "Mamaki kike yi ko? To sai doki zanyi" Ya faɗa cikin dakewa, kaman ba wasa yake yi ba, hakan ne ya sanya ni sakin ƴar dariya mai sauti. "Kin ce ma Umma bakya lafiya, sai gashi ni banga haka ba" Ya faɗa yana mai juyowa ya kalle i sosai. "Jiya ne nayi zazzaɓi, Amman na warke, nasha magani an mani allura" Nima na faɗa cikin wata irin dakiya. Gyaɗa kanshi yayi, yan mai maida hankalin shi kan tuƙin da yake yi. Mu yo tafiya mai nisa, yayin da shiru ya ziyarci motar, sai ƙira'a da ya sanya tana tashi a hankali, har bansan lokacin da na jingina kaina da makarin kujerar ba ina mai bin karatun a hankali a hankali. Shima ta gefen ido yake daɗa kallo na, na masifar burge shi, bansan yanda akayi ba, sai gani nayi munyi parking. "Muje ko?" ya faɗa mani, yana mai sanya hannu ya buɗe man murfin motar ta ciki. Hakan ya sanya hannun shi shafar jikin nawa, tsikar jikina ce ta tashi, ba Arziƙi nayi saurin ficewa ina rufo ƙofar. Shima fita yayi yana mai rufe ƙofar. "Wow masha Allah" Abunda na faɗa kenan a cikin zuciya ta, wurin ya matuƙar ƙawata ni, ciyawa ta fito tayi shar kaman grass carfet, sai korayen flowers da ja, masu matuƙar kyau da ƙamshi, wurin akwai ni'ima sosai, daga gefe wani ɗan rafi ne cike da ruwa, bado da kainuwa sun fito su yi fafut, harda wata farar flower mai adon yellow a jikin ta. "Here we can go" Ya faɗa yana mai juna mani cen gefe ƙarƙashin wasu irin flowers masu tsawo, suna zubo da wasu irin ƴan ƙananan flawowi. Kujeru ne guda biyu, irin na gida wanda akayi da zallar cement da duwatsu. A baya na shiga binshi har muka isa inda suke. Shine ya nuna mani inda zan zauna, Nifa kaina ya kulle, na mamaki nake bi shi da kallo. A zamanin nan da babu tsaro, shine zamu zo wurin nan mu kaɗai mu zauna? Duk da dai wurin yana da matuƙar kyau, kaman wurin shaƙatawa yake. Saida na zauna sannan shima ya zauna, yana mai faɗin "Huhhh Finaly gani ga Madam ɗita" Sauke kaina nayi ƙasa, wata irin kunya ce ta kama ni. "Kinyi matuƙar kyau my Suhan, kaman muyi ta zama a haka nake ji" Ya faɗa cikin wani yanayi na sauƙi da dakewa. "Uhmmm" Abunda na iya cewa kenan ina mai wasa da yatsun hannuwan nawa. "Ki saki jikin ki Suhan, babu Abunda zanyi maki, kawai dai ina so mu saba ne, nan da wata ɗaya ne" Ya faɗa sosai cikin son haɗa ido dani. A hankali na ɗago idanun na ina mai kallon shi. Sai kuma yaga ina ɗan waiwayawa alamun a tsorace nake. Baice komai ba, naga ya jawo wayar shi, bansan me yake yi ba sai naga yana magana, kaman video call yake yi. Sai kuma ya nuni mani fuskar wayar. Wasu mutane nagani tsaitsaye riƙe da bindigogi,alamun masu tsaron lafiyar mu ne. To yaushe suka zo nan? "kada ki damu, duka nan akwai tsaro sosai, fiye da yanda kike tunani. Sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya. Ko ba komai na samu natsuwa. Ƙureni ya cigaba da yi da kallo. A hankali naji ya sanya hannuwan shi duka ya kamo nawa. Ɗan firgita nayi ina mai son janye hannun. Bai bani damar haka ba, sai ma ƙara matse hannuwan da naji yayi. Da kallo nake mashi alamu da babu kyau fa. Shima kallon na sani ya shiga bina dashi, yana mai ɗan haɗe fuska kaɗan. "Kinsan me?" ya faɗa yana mai sakin hannuwan nawa. Girgiza mashi kai na shiga yi, ikon Allah yau nake kallo, wai wannan Ya Ameen ne da kanshi? Katse mani tunani yayi da cewa "Shekarun cen baya, wata ƴar yarinya ce kyakkyawa, bana gajiya da ɗaukar ta, bana gajiya da wasa da ita, haka bana gajiya da kallon ta, itama bata gajiya da zama a tare dani, har barci takeyi a ɗaki na, muna zuwa da ita unguwa, har wajen wasanni ina kai ta, a hankali ta fara girma, sai kuma Maman ta ta fara hanani ɗaukar ta bansan dalili ba, duk da haka bana gajiya da siyo mata sweet da biscuit, haka yasa idan ban siya mata ba a rana tana kuka sosai, kwatsam tafiya ta kama mu zuwa wata ƙasa, nan na barta cike da kewa, cike da tsantsar ƙauna, cike da muradn dama ace da ita muka tafi, cike da alhinin rabuwa da ita. Saidai ko kafin in dawo ta girma, ko kafin in dawo ta zama budurwa hakan yasa na fara ja baya da ita, hakan ya sanya na fara jin ina ma ace bata girma ba, na cigaba da wasa da ita, kyakkyawa mai gashi, ga wayau, ga yarinta a tattare da ita. Hmmmm. Kinsan wacece wannan?" A ƙasa ƙasa nake kallon shi, labarin ya ƙayatar dani, a take Naji ina mai son yarinyar yanda yake fasalta ta, sai kuma na ɗna ji wani abu, ashe ma ya taɓa son wata acen baya?dukda yarinya ce, amman shaƙuwar tasu ta ɗan taɓa mani zuciya. Girgiza kai na shiga yi a hankali a hankali. Da ɗan yatsan shi manuni ya shiga nuna ni, sai kuma ya sake kamo hannuwa na dukan su, yan mai ɗora su zuwa saitin inda zuciyar shi take. "kece Suhan, kece wannan yarinyar, na raineki da hannuna Suhan, nayi bacci tare dake, munyi wasa tare dake, kin man fitsari a bisa jikina Suhan, na maki wanki na kaiki makaranta na ɗauko ki suna, kinyi bacci bisa ka faɗa ta, kinyi bacci bisa ƙirjina Suhan, kinyi bacci bisa cinya ta. A karo na biyu ina fatan ace wannan rayuwar ta dawo, kin mani kina yarinya, ki taimaka kiyi mani ina babba, wanda na mallaki hankalin kaina, wanda zaki samu lada Suhan" Dukan da zuciya ta keyi bai musaltuwa, da zai kula zai fahimci ma kaman nayi suman zaune ne, na kasa cire hannuna daga cikin nashi, haka kuma ina iya jiyo bugawr zuciyar tashi. A hankali ya saki hannuna yana mai miƙewa. Da kallo na shiga binshi har ya isa zuwa ga motar tashi. Wani abu ya ɗauko cikin mota ya dawo ya zauna. Hak dama ya Ameen ɗin yake? Hak Soyayyar take wai? Ni kaina yanzu ba zan iya fasalta yanda nake ji ba, wani irin yanayi nake ciki, ga sanyi da ƙamshin wurin na baibaya ta, ga kuma wata irin kunya dake addaba ta, har na kasa ma haɗa idanu dani. Zobe da sarƙa ya fiddo daga cikin ƴar cover ɗin tasu. Sai ya ajiye sauran bisa cinyar shi. A hankali ya ɗago su cikin haɗin hannun shi mai matuƙar kyau, Nidai haka nake zaune kaman mutum mutumi, na kasa taɓuka komai, saidai in saki ɓoyayyar ajiyar zuciya. Sarƙa ce da zobe na Gold masu masifar kyau da tsada. Tunani na ya katse, daidai lokacin da naji yananmai cewa "Idan har kin yarda da Soyayya ta Suhan ki bani dama in sanya maki sarƙa da zoben nan da hannuwa na, ba zan takura maki ba, saidai zanyi matuƙar farin ciki idan har na sameki a matsayin abokiyar rayuwar tawa" A hankali na ɗago fararen idanu na, ina mai ɗora su bisa kyakkayawar fuskar tashi dake mani kwarjini a koda yyaushe. Shi ɗinne dai, Ya Ameen ne kaman yand ana sani. Fuskar shi cike da annuri dake fidda zallar soyayya, idanun nan nashi har wani walƙiya sukeyi kaman wanda aka ɗiga ma zaiba. A hankali na shiga ɗaga hannun nawa ina mai miƙa mashi cikin wani irin yanayi da ni kaina ba zan iya cewa gashi ba.. ...... _Hadda na gobe_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'ar zama tsakanin sujadar farko da ta biyu.* رَبِّ اغْفِـرْ لِي ، رَبِّ اغْفِـرْ لِي . *Rabbigh-fir lee, rabbigh-fir lee.* *Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ya Ubangijina! Ka gafarta mini.* اللّهُـمَّ اغْفِـرْ لِي، وَارْحَمْنِي، وَاهْدِنِي، وَاجْبُرْنِي، وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي وَارْفَعْنِي . *Allahummagh-fir lee, warhamnee, wahdinee, wajburnee, wa'afinee, warzuknee warfa'nee.* *Ya Allah! Ka gafarta mini, ka ji kai na, ka shirye ni, ka wadata ni, ka ba ni lafiya da tsira daga musifu, ka azurta ni, ka daukaka ni.* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~53~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Har ya kawo hannun shi cikin wani irin yanayi dake nuna zallar shauƙi a saman fuskar shi, sai kuma na janye nawa a hankali ina mai cewa "Yaya ina jin tsoro fa" Ajiyar zuciya ya saki a hankali yana mai faɗin "Tsoron me wify?" "Mom" na faɗa a hankali Huh. Ya sake dauke ajiyar zuciya a hankali, yana mai rumtse zoben da sarƙar a cikin tafukan hannayen shi. Tsaf ya taso a hankali daga inda yake zaune yana fuskanta ta. Sai kuma ya dawo bisa kujerar da nake zaune, dayake tana da ɗan tsawo da faɗi, hakan ce ta sanya ni ja baya a hankali ina mai lumshe idanu na, jin ƙamshin turaren shi a kusa dani. "Suhan tsoron me kike ji? Bayan gani a tare dake?" Sauke kaina ƙasa nayi, ina mai fara wasa da Zara zaran yatsun hannun nawa. Har yanzu idanun shi a bisa kaina suke, ya gaza koda ɗauke wa. Kallon ne yayi mani yawa, hakan ne ta sanya ni ɗagowa a hankali, ina mai ɗora idanun nawa a saman tashi fuskar. "Yaya Mom ba zata yarda ba, ina tsoron hukuncin ta..." "Common Suhan, kin faye tsoro, zanyi mata bayani, insha Allahu zata fahimta, beside ki ƙyale maganar mom komai yana a hannun Dad, he'll handle the issue" Ya faɗa cikin ɗan marairaice fuska. Sai naga ya sake yi mani kyau a idanu na, a hankali na sauke idanun nawa bisa hannun, sai kuma na fara murza yatsu na, hannuwan suna a dunƙule, ina mai ɗago su na wara mashi yatsun hannun. Wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki, zamowa yayi daga inda yake zaune, ya zuƙunna bisa ƙafafun shi, yana mai kamo ɗan yatsa na na kusa da ƙaramin ya shiga zura mani zoben da yake da matuƙar kyau da walwali. Sai kuma ya riƙe hannun sosai, bayan ya gama sanya zoben ya ƙure shi da kallo. Ji yake kaman ya sunbace shi, saidai yana gudun Abunda ka iya jeea ya dawo. Ko ba komai yardar da yarinyar tayi mashi, akan cewa ba zai iya cutar da ita ba, bai kamata ace ya dasa wani tsoro ko shakku acikin ranta ba. A hankali ya miƙe, yana mai tallafo damatsan hannuwa na duka ya shiga miƙar dani tsaye. Ba musu na miƙe nima, har gyalena yana zamewa daga jikina. Ɗan durƙusawa nayi da niyyar ɗaukowa, ya riga ni kai hannu, sai kuma ya tattara shi ya ajiye bisa kujerar, yana mai warware sarƙar dake cikin hannuwan shi. Nidai da idanu kawai nake bin shi, wai Ya Ameen ne haka tsaye gabana, yana mai marmari da muradin soyayyar tawa, wani irin yanayi ne na tsinci kaina ciki, masalan yanda da muka kaɗai ce daga ni sai shi a wurin. Ban aune ba sai ji nayi ya wara duka hannuwan nashi gabaki ɗaya, yana mai zagaye ni dasu, ya shiga ɗaura mani kwaɗon sarƙar a dogon wuyan nawa da yake fari tas cike da gashi ya kwakkwanta. A hankali ya sakeni, sai kuma ya ja baya yana mai ƙare mani kallo, ba Arziƙi na kuma sunkuyar da kai ƙasa. "Wow my beautifull wife" Nisawa yayi yana mai yin taku biyu inda nake tsaye, sai jinai ya tallafo duka fuska ta, daf da tashi. *"You are highly Welcome in to my life Mrs Al'ameen Almustapha Dambulan"* Ya faɗa cikin wata irin murna, mai nuni da tsantar jin daɗi wadda take cike da wani irin sauƙi na soyayya. Duk abun nan fuskar tashi na maƙale da ɗan murmushi da gefen fuskar, da har saida kumatun shi suka loɓa. Sakin fuskar tawa yayi, jan hannu na ya shiga yi a hankali, bayan ya ɗauko gyalen ya yafa mani. Inda ɗan ƙaramin rafin nan yake ya shiga jana. Haka na shiga bin shi, ina mai ƙare ma ƙeya da bayan shi kallo, wanda ko salon takun tafiyar tashi ma abun kallo ne. Daf da ruwan yaja ya tsaya, yana mai sakin hannun nawa. Sai kuma naga ya zuƙunna ya zaro wata irin flower mai ban sha'awa da ƙamshi guda uku, ya haɗe su wuri guda. Miƙewa yayi yana mai ɗan kai ta zuwa hancin shi ya sun suna, yana mai wani lumshe kyawawan idanun nashi, masu ɗauke da Zara-zaran gashin ido. Sai kuma naga yayo saitin hancin nawa da ita. Ɗan kautar da kaina nayi gefe, nifa duk kunya ta cika ni, gani nakeyi kaman a mafarki. Masalan ma yanda wurin ya ƙawatu da furanni da kuma shi kanshi ya Ameen ɗin da ya kusa kasheni da mamaki. Wane irin salon soyayya ne haka? Wannan ai sai yasa in tsaya wasa da karatun nawa. "Bana son wannan Kunyar fa, Shiyasa nake ce maki baƙauya" Ya faɗa yana mai yawatawa da idanun shi bisa fuskar tawa. Ɗan murmushi na saki, ina mai ɗan ja baya, saboda yanda muke tsaye dashi daf da daf, kusa da kusa, har hucin numfashin shi ina ji, sai jikina yake ƙara yin sanyi ga kuma yawan faɗuwar gaba da nakeyi. Lallai matuƙa Ya Ameen ɗin ya shayar dani matuƙar mamaki, mutumen da ada ko gaida shi nayi, sai dai ya amsa kawai a gajarce ya wuce, ko kuma ya ɗaga maka hannu, duk ranar da baya jin ƴan magana? "Say something mana, bana son shirun nan Suhan, sai inga kaman baki yadda dani ba" "A'a Yaya" Na faɗa a hankali. Duk kunya ta cika ni. "To muje in zagaya dake" Ya faɗa yana mai wucewa gaba, cikin salon takun tafiyar shi. A hankali na shiga bin shi, ashe wajen yana da girma da faɗi har haka? Gaskiya wurin ya bani sha'awa matuƙa, wani wurin ma ko ciyawun babu, saidai flowers da suka zuzzubo suka rufe ƙasar dake shimfiɗe wurin. Ya Ameen ya zage fa surutu, saidai duk Abunda zai faɗa cikin irin halin shi yake faɗa, kai da gani kasan surutu ba halin shi bane, illa iyaka ƙoƙarin da yakeyi na in saki jikina dashi. Mun ɗan yi yawo ba laifi, har na fara gajiya. Lura da yayi na fara gajiya ne ya sanya shi cewa mu zauna in huta. Bisa koren ciyawa muka zauna, ina mai tattare ƙafafu na duka, shima kusa dani ya zauna yana mai faɗin. "Ko kin gaji ne mu tafi?" Da kai na ɗan amsa mashi, ina mai faɗin "Ina gudu ne dare yayi, gashi munyi nisa da makaranta" "Kada ki damu, insha Allahu makaranta zaki kwana" Ban fahimci me yake nufi ba, illa iyaka dai naga yayi shiru, yana mai jawo wayar shi ya shiga lallatsawa. Sai kuma naga ya ɗaga ta yana ta ɗaukar mu hotuna da muke zaune kusa da juna haka. Hannuwa na duka na sanya ina mai kare fuska ta, cikin shagwaɓa nake cewa "Kai Yaya?" Ɗan murmushi ya saka yana mai faɗin "Bacci zai dinga taya ni, kafin kizo" Da sauri na kalle shi, sai kuma na kauda kai cike da kunya, Amman shi naga ma ko a jikin shi, hidimar shi kawai yakeyi, saida yayi mai isar shi, sana Naji yana faɗin "To tashi muje ko? Na fara jin yunwa, gashi kuma wife ɗin tawa bata iya tarbar baƙi ba, koda kuwa da abun sha ne" Sai a lokacin kuma Naji wata Kunyar ta sake kama ni, a haka na shiga bi shi har gaban motar, saida ya buɗe mani na shiga na zauna, sannan naga shima ya zagaya ya shiga. Kaman kar na bar wurin haka nake ji. Da kallo na dinga bin wurin, har muka ɓace daga wurin muka hau titi. Ba zan iya fassara halin da nake ciki ba a yanzu, kasancewa ta atare da ya Ameen na ɗan wani lokaci ya mantr dani wasu damuwoyi na, ashe haka Ya Ameen ɗin yake? Rashin sani ya sanya nake mashi fassara kala kala a cikin zuciyar tawa. Na mai girman kai, mai ji da kanshi, mai ɗagawa da miskilanci. Ashe sai in baka zauna dashi bane yake haka. A hankali na shiga wara idanun nawa, ganin mun dawo cikin garin zariyn. Amma ga mamaki na, maimakon mu nufi makaranta, sai naga mun wuce cikin gari. Wani irin restaurant ne naga munyi parking a gaban shi. Wannan karon ma shine ya buɗe mani, Nidai har yanzu da mamaki nake kallon shi, kaman wata sarauniya haka ya maida ni. A hankali na shiga bin bayan shi, wata ƙofa mai kyau naga mun nufa, a saman ta an rubuta VIP. Ɗamin ya matuƙar ƙayatuwa, kaman kana gidan ka, kai wani ko a gidan shi ba zai samu haka ba. Fali ne babba, yana ɗauke da set ɗin kujeru masu kyau, irin na gidan alfarma. Tsakiyar su da wani irin centre table. Suna da Stools guda huɗu gefe da gefen kujern. Tiles ne malale a tsakiyar falon, sai wani irin chinese carpet da ya kusa cinye rabin falon. Ƙatuwar tv na bisa tv stand da akayi da POP akayi ma wani irin ado da fitilu masu haske sosai kowanne launi. Sai daga cen gefe ne dining table ne mai kyau, na zallar glass mai ɗaukar idanu, saman shi cike yake da abinciccika kala kala. Wurin dai daga i shirya shi akayi na musamman. Gefen dining table ɗin sink ne na wanke hannu, da towels na tsane hannu. Kai tsaye kujera yaja mani yana mai faɗin "Have a sit wife" haka na zauna ina mai ɗan bin shi da kallo. Yaushe duk yasanya aka harhaɗa waɗannan abubuwan? Dare fa nayi, Amman hankalin shi kwance kaman ma ba yau zai tafi ba. Shima kujera yaja yan mai zama inda zai iya fuskanta ta. "who will serve us?" ya faɗa cikin ƴar zaulaya, yana mai sakin wani ɗan guntun murmushi. A hankali na miƙe ina mai kai hannu saman serving spoon ɗin, cikin rashin sa'a shima ya kai hannu, hannuna ne ya sauka bisan nashi, kaman wadda aka jona ma shork haka nayi maza na janye hannun. "Ni na isa? Zauna princess ne kike so in zuba maki" A hankali na koma na zauna, ina mai cewa "Abunda zaka ci yaya, ni bana jin yunwa sosai" "Sure?" ya faɗa yana mai ɗan kanne mani idanu ɗaya. Ɗaga mashi kai na shiga yi, nima ina mai ɗan kallon shi da murmushi, duk na takura, wallahi ji nake kaman ba Suhan ɗin Umma ba. Abincin ya shiga zuba mani, ɗan daidai daidai, sai kuma shima ya zuba ma kanshi. "Ko in haɗa mana?" Ya faɗa cikin wani irin salo na tambaya. Girgiza kai na shiga yi a hankali, ina mia jawo gefen gyalena na rufe fuska ta. "Hmm alright" ya faɗa cikin wani irin yanayi mia nuni da watarana ma a baki zan baki. Lemon 5alive shima ya zuba mani cikin wani cup dogo mai garai garai. Duk na takura, yayin da shima ya shiga cin abincin shi, hankalin shi kwance. Akwai akai yana mai duba agogon hannun nashi. Tsam ya miƙe yana goge baki da tissue, yana mai faɗin "Kici abincin nan kafin inyo salla in dawo, in ba haka ba, ɗura zan mani" Ya faɗa yana mai zagaye ni ya fice daga falon, cikin sauri, kaman ya soma makara masallacin. Da ɗan kallo na shiga binshi, wannan kuwa anya ba zanyi fama dashi ba? Duk lokacin da akace an ɗaura mani aure dashi. Ganin ya fita ne, ya sanya ni fara cin abincin, yayi mani daɗi, saidai duk da haka ba zan iya sakin jiki inci abinci ba, a rana ta uku da sanin shi a matsayin masoyi. Har ya dawo ina mai ɗan jujjuya cokali. Da kallon bakiciba ko? Ya shiga bina. Da sauri nace "Allah kuwa Yaya naci sosai" "Ok" Ya faɗa yana mai zama, sai kuma ya ɗauki ruwa ya ɗan kurɓa haka yana mai faɗin "Muje ko?" Da kallo nabi kayan abincin, nan fa duk ya biya, gashi sun zama wastage, in banda abun Ya Ameen wannan kayan abincin ai ko mutum goma zasu iya ci su ƙoshi har su rage. A mota ne yake tambaya ta wai ko akwai Abunda nake buƙata? Ɗan girgiza mashi kai nayi, ina mai cewa "Babu yaya" Duk da haka saida ya tsaya wani shopping complex, saidai naga ana jijjibga abubuwa a mota. Bamu sha wahala ba wajen shiga makarantar, tin dai daya nuna ma masu gadi Id card ɗinshi, sai naga ma har wani sara mashi suke yi. Hankali na ya ɗan tashi ganin irin kayan da ya jijjibgo mani,to duka ma yaushe ne zamu samun hutun semester? Bai wuce sati uku nan gaba fa. Godiya yai mashi sosai, har saida ya nuna mani ɓacin rai, sannan yace "Akwai biscuit da Sweet a ciki, harda springles ma, irin waɗanda kike ci da kina kid" Dariya ya bani har saida na dara. Jingina yayi jikin motar, yana mai harɗe hanjuwa duka a ƙirji, cikin hasken soler ɗin dake yi hake iya kallon fuskar shi. "Suhan zan koma masauki na, amman insha Allahu zuwa gobe zan wuce. Kada dai ki manta zuwa jibi ne ƙa'idar lokaci na ta cika" Ya faɗa yana mai tsattsare ni da idanu. "Himm" kawai nace ina mai sauke kaina ƙasa. Sai kuma naga ya sake buɗe motar ya cire wata farar leda ya ya miƙo mani. Wannan kyauta ce daga hannun Mijin ki, bana so kuna kallo na a wani mutum daban, Suhan ni ne mijinki da izinin Allah, don haka duk Abunda kike buƙata feel free ki tambaye ni. insha Allahu babu Abunda zai gagara, maganar Mom ki ajiye ta gefe, kada ki sake damuwar kanki akan al'amarin, insha Allahu komai mai zuwa ne dasauƙi" Nidai a ƙasa ƙasa nake kallon shi. Yau ɗin ta daban ce a tsarin rayuwar tawa. Godiya na shiga yi mashi a sanyaye cikin jin kunya. "Ki kira frienss ɗinki su tayaki ɗibar kayan. And Bilal yace in gaida mashi ke, yayi wata ƴar tafiya ne, da tare zamu zo" "Ina amsawa". Na faɗa cikin sakin murmushi, ko ba komai Bilal ɗin ya kula damu sosai lokacin da babu Ya Ameen ɗin, har ma munyi sabon da ko Ya Ameen ban saki jiki dashi haka ba, bansan kuma dalili ba. Komawa yayi cikin mota yana mai faɗin "I am going to miss u Wify, zamuyi waya" Ina ji ina kallo yaja motar yayi ribos ya fice. Ajiyar zuciya mai ƙarfi na saki, ina maida kallo na bisa kayan daya jibge mani harda su Lemuna na kwali manya manya, da kayan ƙwalama irin na ƴan makaranta. Number ɗin Raihana na kira, ai kuwa sai gasu ita da khadee. Cikin mamakin yawan kayan suka shiga taya ni kwasa, har muka shige dasu duka ɗaki. Kowa mamakin kayan yakeyi, masalan ɗana faɗa masu Ya Ameen ne ya siya mani, kuma tare muka fita. Sun tayani murna matuƙa, masalan Raihana, domin khadee na lura har yanzu akwai wani miki dake yawo cikin ranta, duk kuwa da tana ƙoƙarin karewa kada in gani. Ina kallon raihana na zungurar ta, itakuma sai ta saki yaƙen dole. To nima kam ta bani tausayi, ko ba komai dai son maso wani ƙoshin wahala ne. Saida nayi wanka, sannan na rama duk sallolin da ake bina. Ga mamaki na kwanciya nayi, wai ina mai jiran kiran nashi, domin inji wai yanda ya isa, ni kaina nayi mamakin kaina sosai da sosai. Ɗana kulle idanu sai in hango shi lokacin da yake ɗaukar mu selfie ko kuma in hango lokacin da ya saka man zobe da sarƙa. A hankali na ɗago yatsan nawa ina mai ƙare mashi kallo, lokaci guda kuma ina mai shafi sarƙar wuyan tawa da na kasa cire wa, har wanka da ita nayi. Wani irin yanayi ne yake ziyarta ta, ashe ya Ameen ya daɗe yana dakin soyayya ta. Tun ma kafin in mallaki hankalin kaina, tin ma kafin in san wacece ni, tin ma kafin shima ɗin ya san mecece soyayya. Allah sarki, Soyayya daban ce, Amman in ba haka ba, ina ni ina Ya Ameen ɗin? To ai ko abokin shi Bilal yafi ƙarfi na, balle shi sunkutukum *yariman Matasan Arewan* *Ayi manage wlh banda isasshen charge* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ Addu'ar Wanda Ya Fitinu da Shakka a cikin Imani - Ya nemi tsari da Allah. - Ya bar abin da yake sa shi shakka. Ya ce: أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ. A'uzu billahi mina shaytanir rajeem. آمَنْتُ بِاللهِ وَرَسُولِهِ. Amantu billahi wa rusulhi. Na yi imani da Allah da Manzanninsa. Ya karanta fadin madaukaki: هُوَ اْلأَوَّلُ وَاْلآخِرُ وَالظَّاهِر وَالْبَاطِنُ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ. Huwallahu wal akhiru waz-zahiru walbatinu wa huwa bikulli shay'in alim. Shi ne na farko, Shi ne na karshe, Shi ne Bayyananne, Shi ne Boyayye, kuma Shi Masani ne da komai. *Page ~54~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Mafarkai na dinga yi a daren iri iri, wasu dai ba zan iya fasalta yanda suke ba, Amman mafi yawan wanda Ya Ameen yake ciki, sun zauna mani daram a cikin zuciyar tawa. Ni kunya ma nake ji in na tuna wai yau nice da yin mafarkin Ya Ameen ɗin. Kiran wayar Afnan ne ya shigo tin dasafe a cikin wayar. Ƙorafi take mani wai na manta da ita, haƙuri na dinga bata, ina mai cewa yanayin karatu ne, saidai duk yanda ta dinga zulaya ta, kasa biye mata nayi, ita kanta Kunyar ta nake ji, in na tuna wai yayan ta zan aura, saidai jin bata yi mani maganar bane ya sanya ni share wa, ina tunanin ƙila basu kai ga jin maganar ba. Shaida mani tayi yau ne zasu wuce, har ta haɗa ni da Aunty Feena muka gaisa, duk da ba wani sakin jiki tsakani na da ita, Amman ita sai na fahimci kaman ta ɗan san wani abu. Bini bini na kan saki murmushi, ko a wajen ɗaukar karatu, har malamr saida ta kai ga yi mani magana. Aiko hankalin kowa ya dawo kaina, hakan ne ya sanya ni natsuwa da ƙoƙarin fidda komai a raina. A hanya ta ta komawa ɗaki ne muka haɗe da Sir Salim da abokin shi malam Musa. Yanda naga mun gaisa da malam Musa ɗinne ya sanya ni gane cewa baisan rabuwar mu da Sir Salim ɗin ba, har zaulayata yakeyi yana cewa amaryar mu. Shi dai Sir Salim saidai ya ɗan kauda kai, ga yadda ma na kula shine kaman baya son kallo na, duk sai naji ya bani tausayi. A haka na wuce sukuku, wani irin abu yana mani yawo cikin jiki,wanda na Gaza tantance ko na menene. So nake in kira ya Ameen ɗin, inji ko ya wuce? Saidai ina gudun yace har na fara sonshi ne, ko yayi tunanin wani abu daban. Sharewa nayi, saidai fa, akai akai na kan kai kallo na kan wayar, ko yaya naga tayi haske sai na ɗauko na duba, ina zaton ko shine ya turo mani saƙo. Kai daga ƙarshe dai kasa daurewa nayi saida na jawo wayar tawa na rubuta mashi saƙo kamar haka. _"Aslm Alkm Yaya, Ya hanya ka isa lafiya?"_ Saida naga saƙon ya shiga, sannan na sauke wayar ina mai sakin ajiyar zuciya a hankali a hankali. Ko tashi banyi ba daga wajen da nake zaune, naga saƙo ya shigo. Shine ya maido mani da amsa. _" On my way dear, call u latter"_ Ɗan murmushi na saki, ko me ya tsaida shi har kawo kaman yanzu da ƙarfe huɗu take neman yi? Sharewa nayi, ina mai miƙewa na shiga tattara kaya na, domin yin wanki. Gabaki ɗaya Abunda Ya Ameen ya siya mani, a fili na ajiye shi, mu duka zamuyi amfani dashi, saboda abubuwan sun mani yawa, ba zan iya cinye su ba kafin mu samu hutu, nan da sati biyu, tinda na rago mana lokacin jarabawar. ******** Wanka kawai yayi yayi sallah, sannan ya zauna haɗi da jawo wayar shi domin kiran Bilal, sai ga kiran Bilal ɗinma ya shigo. "Aslm alkm" Ya Ameen ɗin ya faɗa, yana mai ɗan zamewa kaɗan ya kwanta cikin yanayi na gajiya. "Wslm Ya dai malam? Kaman kayi wani uban aiki?" Bilal ɗin ya furta cikin salo na ɗan zaulaya. "Mtsew, kaidai bari wlh, driving nayi mai nisa, gashi na dawo a gajiye, ko wanka da salla ma daƙyar nayi su, ya hanya?" Ya sake faɗa a hankali cikin salon maganar shi da gajiya duk ta kama shi. "Alhmdllh friend, na iso lafiya, harma mun zauna dasu yau, saidai Abunda ke faruwa, ina tunanin fa sai kazo gaskiya, akwai abubuwa da dole sai CEO ne zaiyi signing kuma akwai muhimman abubuwa da zaku tattauna da turawan nan dole" A hankali ya tashi zaune yana faɗin. "Friend kadai san halin da ake ciki, ko na taho hankali na zai rabu ne biyu, dole wani abun sai ina kusa..." "It will not take much time friend, u have to come, kasan yanda suke da tsari sosai gaskiya" Ɗan ƙaramin tsoki ya sake ja,yana mai idasa zamewa ya kwanta sosai bisa gadon. "Friend zan duba in gani, zuwa yaushe ne Meeting ɗin?" "Eah sunce suna jira suji lokacin da zaka basu" "Nan da kwana uku" Ya faɗa straight ba tare da ya tsaya wani tunani ba. "OK Friend zan sanar dasu, kasan duk abunda zan iya yi, na riga na kammala su, ka bari idan na iso kai sai ka taho, zamu taho da Abie ne, yace yana so yazo yaga su Mom, i'll take All the responsible there, idan na dont worry" "Noo Bilal, kada ku taho da Abie, tell him ni na hana, saboda ko na zo, ni ba zama zanyi ba, ɗana gama Abunda nakeyi zan juyo, idan kun taho dashi wanene zai zauna?" "Ok Ameen Amman ka bari mu taho tare dashi, idan yaga su Mom ɗin sai ku taho tare dashi, kasan fa ya daɗe ƙasar nan, u have to allow him" A gajarce yace "OK Friend See u later" ya datse wayar. Da kallo Bilal ɗin yabi wayar, Ooh Ameen, halin shi na nan ba zai cenza ba, ko ya tsaya ma su idasa maganar da ya kamata suyi. Shi kam yana matuƙar buƙatar yaga lokacin da aminin nashi zai cenza. Ɗan sauke kafaɗar shi yayi a hankali, yana mai furta "Allah ya shirya mana kai" a fili. Sh kau ya Ameen ajiye wayar yayi, yana mai lumshe ido a hankali cikin matuƙar gajiya, sai kuma ya saki murmushi tunowa da text ɗinda tayi mashi ɗazu, kenan ta fara damuwa da lamarin shi? Saidai kuma fa, dama cen ita gwanar yin text ce, bata iya kiran mutum, saidai ta iya yi ma mutum text. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai sake rubuta mata wani text ɗin, sanin da yayi cewa bacci bayan la'asar ɗin ba abu ne mai kyau ba, ya sanya shi miƙewa dole ya koma perlon nashi cikin rashin kuzari, daga shi sai amless da thre queter. Yana so ya shiga sashen Mom ɗin tashi amman yana gudun Abunda zai iya zuwa ya dawo, duk da ya san rashin zuwa ɗinma wani ƙarin laifin ne. Dad kawai ya kira, ya sanar dashi ya dawo lafiya, dari kawai Dad ɗin yayi, yana mai yi mashi sannu da zuwa, ya zuwa yanzu baya buƙatar a sanar dashi cewa Suhan ɗin ita ce farin cikin yaron nashi, kula maganar gaskiya yanzu yana matuƙar sonta, yara nawa ne aka kawo mashi talla, ko kuma suka nemi kafa kansu a cikin zuciyar tashi Amman duk yayi biris dasu? Dama ya san lokacin yana zuwa, duk complain ɗin da Hajiya Kubra na mashi saboda rashin kula matan, dama ya kan ce mata ta ƙara haƙuri, lokaci ne bai zo ba, ko kum matar tashi ce bata bayyana ba, ashe acikin rashin sani ma tana a cikin gidan ba tare da sun sani ba. Bayan sun gama wayar ne ya nemi layin Afnan bai samu ba, so yake ya sanya ta kawo mashi abinci, sai kuma ya jaraba ta Aunt Feena, itama bata shiga, ɗan tsoki yayi yana mai ƙarasawa kusa da telephone ɗin dake ajiye gefe bisa stool, ya kira landline ɗin cikin gidan. Maree na perlon tana goge goge, kiran ya shigo, matsawa tayi tana mai ɗagawa tare da yin sallama, duk da sallamr bata cika ba. "Afnan ki kawo mani abinci marar nauyi please" ya faɗa a gaggauce saboda tsaye yake bisa ƙafafun shi. Har zai ajiye sai kuma ya jiyo ana cewa "Ranka ya daɗe su Afnan basa nan sun koma, Amman bari inzo in kawo maka" Ɗan dakatawa yayi yana mai sauraren ta, sai bayan data kammala ne cikin shaƙe murya sannan yace mata "ki bar shi kawai" ya faɗa a gajarce yana mai ajiye kan wayar, lokaci guda kuma yana mai sakin ƙaramin tsoki. Dole dai shiga cikin gidan ya kama shi, baya so su haɗu da Mom ɗin tashi, Amman ya zaiyi? Dole ne ya shiga gidan saboda baya da ra'ayn cin abincin waje kaf a cikin rayuwar shi, saidai in baya da yanda zaiyi ne, wannan ce ta sanya shi koyon girki kala kala, ko domin ya huce ma kanshi takaici, komin ita girkin mace saidai ya cita gyara, Amman ba kaman yanda mafi yawan matan ba jagwalgwalo kawai suke yi. Ɗakin ya koma yana mai cire amless ɗin, ya zura jallabiya, ƙafafun shi sanye cikin takalman pajamas farare da surmin ruwan omo mai cizawa, ya nufi Sashen Mom ɗin tashi. A falo ya tadda Maree ɗin da Nihal kuma zaune bisa kujera tana kallo, lokaci guda kuma tana mai latsa wayar dake hannun ta. Maree ɗin na daga cen ɓangaren dinning tana ta faman gogewa, sai haɗa gumi takeyi, duk da al wai sanyin ac kaɗan kaɗan a sashen. "Ke me kike yi kuma a gida har yanzu?" Ya faɗa yana mai ɗauke idanun shi daga kan Maree ɗin da tin da taga shigowar shi, ta saki tsumman tana kallon shi,sannan ya sauke su bisa fuskar Nihal ɗin. A hankali ta zumɓyra baki, cikin kaffa kaffa kada ya kula ta shiga cewa " Ba Baby ne yace in taho guda ba?" "Baby kuma? Wanene baby kuma?" ya faɗa cikin ɗan faɗa haka, yana mai gyara tsayuwar shi bisa kanta. Miƙewa tayi tsaye ta fara diddira ƙafafu. "yaya cewa yayi in taho gida, wai in koyi cock da wanke dishes, da mopping da shara" Sai a lokacin ya fahimci me take nufi. Hmmm Kowa ya san za'a rina. "Shine kuma su Mom basu maida ki ba?" Ya faɗa a ɗan tsawace. Ba Nihal ɗin ba har Maree da take cen gefe saida ta razana. Ɗan ja baya tayi, saboda ta san Halin Ya Ameen ɗin, baya shiga sha'anin da ba nashi ba, Amman kuma duk lokacin da ya shiga ɗin basa ji da daɗi. " ku ba kuna gani cewa mace ta zauna ta latsa waya kaman shine burgewa ba? Ku hau motar da kuke so, kuje inda kuke so kuma a lokacin da kuka ga dama, Mom tana kallon ku ta zura maku idanu, ko hakan aka tsaya ya kamata ku hankalta, masalan ke da kece gaba wajen raina mutane, ai sai kije Suhan ɗin da kuka raina kuke ɗaukar ta ƴar ƙauye bagidajiya ta koya maki" Ya faɗa yana mai zagaye ta ya wuce. Aikuwa kuka ta saki, sai kuma ta nufi ɗakin ta tana mai raira wani kukan, Ya Ameen baiyi ba a rayuwa, gashi ya katsa ta a gaban Maree, kuma yana haɗa ta da waɗancen kwaɗayayyun wai har ma yana cewa taje ta koya mata. Kitchen kawai ya nufa kai tsaye, abinci ake girkawa, saidai sanin da yayi cewa gashi dai Nihal bata iya girki ba, harma miji ya koro ta, to tabbas Maree ce ke girkin, shi kau ko yunwa zata kashe shi, baya jin cewa zai iya cin abincin nata. Domin da yaci abincin Maree gara ya je eatery yaci, duk kuwa da yanda ya tsane shi. Ga alama Mom bata gidan ma gabaki ɗaya, ɗan girgiza kanshi yayi yan mai nufar sashen Umma domin ya san ko ba komai ba zai rasa wani abun ci ba. Saida yayi sallama ta kai Ukku sannan Umman ta fito daga cikin ɗakin, hannun ta ɗauke da counter, da gani dai lazimi take yi. Cikin sakin fuska ta shiga cewa "A'ah Muhammadu kai ne?" "Eh Umma nine" ya faɗa yana mai ɗan rissinar da kai alamun girmamawa ya shiga gaida ta. Amsawa tayi cikin ɗan jin nauyin shi, duk da ta kula boko ta ratsa shi, shi baya ma ko nuna mata sarakuta sosai, to dama ƴan boko haka suke, sun saba da irin wannan rashin Kunyar. "Mom yanzu na dawo na gaji, nace ko zan samu Abunda zanci anan, cen naje Mom ɗin bata nan" Ya faɗa kai tsaye a hankali ba tare da ya ko tuna ita ɗinfa surukar shi bace. "Eh sosai ma, ina zuwa" ta faɗa tana mai miƙewa daga zaman da tayi bisa kujera ta nufi kitchen. Da kallo yake sake bin sashen, kullum kaman ba'a rayuwa ciki, tsaf, ko ina a goge ƙal, duk da Tasan bata da wata mai aiki da zata iya taimaka mata, har yanzu bai ji an sake yin rabon masu aikin ba, amman zai jira dawowar Dad ɗin duk da dai dama shine mai alhakin kula da masu aikin. Hannun ta ɗauke da ɗan kwando mai matuƙar kyau na saki. Jug ne ciki mai garai garai, yana iya hangen abunda ke ciki. Sai plate lulluɓe da poil paper. Gabanshi ta dire kwandon tana mai faɗin "Gashi, in kuma da wani abu da kake buƙata to ko a waya ne sai ka kirani" Itama ta faɗa, tana mai san kauda wannan Kunyar ta sarakuwa, duk da Tasan cewa hakan abu ne mai matuƙar wahala, masalan ma gasu Fulani. A hankali ya miƙe yana mai saɓar kwandon yake faɗin "A'a Ummata, wannan ma ya isa, sai da safe nagode" Da "To" ta bishi da kallo, tana mai alfahari da samun miji kaman Al'ameen ɗin da Suhanan tayi. ****** Yana komawa ɗakin ana kiran sallar magrib, don haka alwala kawai yayi ya wuce masallaci, bayan ya maida Jug ɗin cikin fridge tinda ya buɗa yaga kunun aya ne ciki. Ba al'adr shi bace da yaci ya kwanta, hakan tasa yana dawowa masallaci ya zaro plate ɗin ya nufi kitchen. Meat pie ne guda biyu, sai samosa da shawarma house made. Cikin micro wave ya sanya su haɗu da ɗumama su, sannan ya ɗauko Jug ɗin kunun ayan yana mai zaro tissue daga cikin ɗan kwalin nata. Perlour ya dawo ya zauna, gami da kamo tashar NTA News. Gutsirar farko da yayi saida ya lumshe baki, gabaki ɗaya ɗanɗanon meat pie ɗin ya gauraye bakin shi. Hakan ce ta sanya shi tsiyaya kunun ayar ya kai bakin shi, yana mai sake lumshe idanu. Bai taɓa shan kunu aya ba sai yau, shi ƙyamar shi yakeyi, masalan ma da yake yawan ganin shi wajen sabga, sai yake ɗauka anayi ne kawai saboda ba'a iya sayen lemo ya wadata. Sai ƙamshi kunun ayan yakeyi, ya sha kayan ƙamshi da kwakwa da dabino. A hankali ya jawo wayar shi, ai dole ne ma ya kira ta, dole ne ma ya sanar da ita wannan delicious ɗin da Umma ta haɗe shi dashi a daren yau. Ina kallo wayar na ringing na kasa ɗauka, waini irin jan ajin nan, ko text ɗinshi na ɗazu da nagani, ban maida mashi reply ba, ina gudu yayi mani dariya, ko yace har na fara kewar shi ne. Saida ta kusa katse wa sana na ɗaga ina mai sallama a hankali. "Baby na ya kike?" ya faɗa cikin wani irin yanayi, yana mai sakin ɗan murmushi gefe guda yana taunar meat pie. "Lafiya ƙlau ya hanya?" "Sau nawa zaki tambayi hanya ne wai baby na?, ni gani ma har na soma hutawa, albishirinki?" "Goro" Na faɗa murya cen ciki. "Yau dai ni ne na maye gurbin wannan shagwaɓar taki. Yau ni ne na zama ɗan gatan Umma, dinner ma ita ta bani yau" Ya faɗa cikin zaulaya, yana mai sakin ƴar ƙaramar dariya. "Uhmm" kawai na iya cewa, ba wai don ban yarda ba, sai dai ina mamakin ne wane irin mutum ne ya Ameen? Ya saki jiki da Ummata har haka? Ashe har yana iya zuwa wajen ta ya amso wani abu? Itama Umman ta bani mamakin yanda ta saki jiki a gidan take gudanar da harkokin ta hankali kwance, ba tare da shakkar komi ba. Ƙit, Naji ƙarar katsewar wayar, wai ashe yana ta magana na zurfafa a cikin tunani. Video call ya kira, a hankali na ɗaga ina mai sakin ƴar dariya, haɗu da rufe gefen fuska ta da gyalen doguwar rigar da take jikina. "Wow My Sunlight, kinyi matuƙar kyau, You are so much beautifull girl that i ever met" ya fɗa yana mai kuma sakin dariya, haɗi da kanne mani ido guda. Ƙara sanya ni jin kunya yayi. Ba ce mashi komai ba, sai a ɗago mani cup ɗin kunun ayan yayi, yana mai nuna mani plate ɗin snacks ɗin. "uhmm ɗan gayu, gaskiya ni ban yarda ba, dawowa zanyi, no one can took my plate" na faɗa ina mai ɗan narkewa alamun shagwaɓa. Hakan da nayi ta matuƙar burge shi, da daddaɗar fira ya shiga jana, har na fara sakin jiki a hankali a hankali dashi, bai ankara ba ya cinye komai tas, kunun ayan dai ne ya rage, duk da shima yana yi yana ƙara tsiyayawa. Sai gani nayi ta ɗago empty ɗin plate yana mai sakin dariya. "Alhmdllh saura na gobe" Ya faɗa yana mai sake kashe mani ido ɗaya, sannan ya zame ya ɗan kwanta bisa kujera yana mai sakin miƙa a hankali. Kauda idanu na nayi, domin duk wata halitta ta ƙirar jikin shi saida ta bayyana, Amman naga shi ko a jikin shi, "Daga yau abinci na ya koma sashen Umma, zan dinga zuwa ina cin nawa ana haɗa mani da naki" Ya faɗa kai tsaye cikin kuma ko in kula. "Allah ni ka bari Yaya, ina jin kunya fa" Na faɗa ina mai turo baki gaba. "Zaki bar tura baki gaba, duk lokacin da na kama shi..." Sauke kaina nayi ƙasa ba Arziƙi, duk da earpiece ne a kunne ne, sai naga kaman su Khadeeja sunji abunda ya faɗa. Cikin jin kunya nace "Sai anjima Yaya" "Ni ban gaji da kallon ki ba, ina assuming ma ace kina kusa ne dani yanda naci na ƙoshin nan" Ya faɗa yana mai sakin dariya, har saida wushiryar shi ta bayyana. cikin ɗan zaro ido nace "Me zan maka?" "Tausa" ya faɗa kai tsaye yana mai ɗan karya kai. Sannan ya lumshe ido a hankali, hakan da yayi baƙaramin kyau ya ƙara ba, gefen fuskar nake hangowa da sajen da ya kwanta ku, yana shan gyara abunshi. "Uhmm ai ban iya ba" Na faɗa nima ina mai sake kauda kai. "Zan koya maki ai" Shima ya bani amsa, idanun shi na a lumshe still. "ai bana fahimta" Na faɗa a hankali. "Ki gaya ma wani, ba dai Al'ameen ba" Shima ya bani amsa, har yanzu fa bai buɗe idanun shi ba. "To Yaya, kaima ɗin zan faɗa maka tinda ba ajinmu ɗaya da kai ba" A hankali ya shiga wara idanun shi a kaina, sun ɗan cenza kala zuwa jaja haka, bansan dalili ba. Sai kuma ya sake ƙanƙance su. "Haihuwar ki ne kawai ba'a yi ba gabana, kin manta labarin da na baki jiya?" "Uhmm" kawai na iya faɗa, sai kuma wata Kunyar shi ta kama ni, masalan da naga kaman ya cenza a lokaci ɗaya. Sai kuma gabana ya fara halbawa, nake faɗin "Yaya zanyi salla" "Ba inda zaki, kin manta ni liman ne? Akwai sauran kusan minti ashirin nan gaba" A hankali na ɗaga idanu na, ina mai kallon agogo. "Ƙibar kallon clorck, kawai ki yarda" A hankali nace "Eh Hakane Yaya, saidai mu muna rigan ku yin salla.." "What So ever, kada fa kika ince yau a haka zamu kwana" Ya faɗa kai tsaye, nasan zai iya cewa hakan, tinda shi datar ma ba wani abu bace a wurin shi, kuma yanzu ma nasan da ta gida yake using. "Yaya kwana fa kace?" Na faɗa a hankali ina mai ɗan zaro idanu waje. Baice komai ba, sai ma maida idanun shi yayi ya sake kulle wa. Munkai tsawon lokaci a haka, ba abunda nake ji sai bugawr zuciyar shi, da kuma saukar numfashn shi a hankali, ba don in akula da ba bacci yakeyi ba, da sai ince ni ya maida sakarai da tabar ni riƙe da waya a hannu, ina ta hask mashi fuskar tawa. Kiran sallah da aka ƙwala ne ya sanya shi buɗe idanun nashi a hankali, wani irin feeling yake ji, kaman tana kusa dashi. "Take care I love u" ya fɗa a hankali yana mai buɗe idanun nashi da suka ƙara rinewa. Sai kuma ya datse kiran Ƙit. Sakato nayi da waya a hannu na. Ko dai na bashi haushi ne? To me nayi mashi da ya sanya shi jin haushi? A hankali na rubuta saƙo na ban haƙuri na tura mashi ina mai miƙewa domin ɗura alwala, su Raihana har sun yo tasu, sun tada salla. Ko da ya kashe kiran, zuciyar shi ce keta bugawa, ya kamata yake controlling kanshi gaban yarinyar fa, da kunya ta kalle shi ta gano halin da yake ciki, alhalin bai kai ga auren ta ba. Yana kallo wayar tayi haske, alamun saƙo ya shigo, saidai baya da ƙarfin amsawa, a hankali ya miƙe yana mai jan ƙafar shi zuwa toilet ya sakar ma kanshi ruwa. Saida ya gama wanka ne, sannan ya ɗauro alwala ya fice zuwa masallaci. Duk da ya samu sauƙi sosai, amman yana daga cikin karo na barkatai da yake fuskantar yana tsananin son aure. ******* A hankali motar ta dinga gangarawa zuwa cikin gidan. Mudi ne ya fito da sauri yana mai buɗe ma Alhaji Mustapha ƙofar motar. Bai tsaya sauraren komai ba, ya nufi sashen Hajiya Kubran. Ba kowa a falon, hakan ne ya sanya shi haurawa saman nata. Nan ma bata nan, yana saukowa ne yaci karo da Nihal ɗin ta fito daga kitchen, jikin ta sanye da kayan bacci masu taushi. Da wani irin matsiyacin kallo yake binta. "Dady barka da dare" Ta faɗa tana mai ɗan raɓewa gefe ta takure. Da kallo mai cike da harara yake binta "Ina Mom ɗinku?" "Dad bata dawo ba" "Ke yanzu Abunda kika zaɓar ma kanki kenan ko? Ai sai kizo ki zauna kujeru ke da ita, ba abunda zance, har yanzu baku gama yin hankali ba ke da uwar taki" Ya faɗa yana mai zagaye ta ya fice, cike da ƙunar rai. Sashen shi ya wuce kai tsaye, dayake yau ba sashen Umman tawa yake ba, hakan ce ta sanya saida ya kammala wanka ya shirya bacci, sannan ya shiga sashen Umman tawa. Ya samu tarba irin wadda yake da buƙata, kasancewar ba ita ke da girki ba ya sanya bata tanada mashi komai ba, shima ɗin lura da tayi yunwar yake ji, ya sanya ta ɗumama mashi sauran Abunda ya rage a fridge irin wanda taba Al'ameen. Shima yaji matuƙar daɗin hakan, nan ne yake shaida mata cewa gobe zasu je Kankiya, Alhaji Tsoho na kiran su, Amman da Hajiya Kubra za'aje, ita ta bari zuwa wani lokaci sai suje ta gaida iyayen nashi, sum su ganta, dukda dai cewa kaka zuwaira dama ta santa. Da fatan dawowa lafiya ta bishi, har ta raka shi ƙofar futa. Sashen Hajiya Kubran ya koma. Ta dawo Amman tana wanka, gefen gado ya zamu ya zauna, yana mai ƙissima dalilin kiran da Alhajin nasu yayi mashi cikin gaugawa, kuma ya umurta da azo mashi da Hajiya Kubran. Ta ɗau lokaci, sannan ta fito tana goge jiki da towel. Har yanzu Hajiya Kubra tana da matuƙar kyaun ta, da jikin ta ɗan daidai dukda tana da ƙiba, Amman ba mai muni baceba, idan ka kalle ta ma ba za kace tana da kaman su Feena ba, tsabar hutu. Sai a lokacin ne ta kula da Alhajin mustapha & in da yake zaune, jikin shi da jallabiya fara, da hula irin ta larabawan Makka a kanshi. Kasancewar shi fari fat, sai yayi kama da larabawan. Har yanzu tana son Alhajin nata, saidai laifin shi a gareta yana da yawa, hakan ne ya sanya ta gimtse fuska kaɗan take faɗin "Alhaji Lafiya dai ko? Na ganka nan a zaune" "Da kallo yake binta, shima Sam fuskar tashi ba walwala. " Eh ai dole ki ganni na zaune, saboda Allah Kubra sai yaushe ne zaki cenza? Kin kasa tsayawa ki kula dani da yaran naki, yanzu a gaban idon ki ga Hajiya nan an koro maki ita, Amman abun bai ko dameki ba, sai ma sanya ƙafa da kikayi kika fice daga gidan, sai yanzu ne zaki dawo" "Alhaji to ya kake so inyi ne wai? Ya koro man ita ko ya ma kanshi? Sai me idan yce ta dawo? Ai bamu gaji da ita ba, shara da wanke wanke ne ba zata yi ba, ai ba wahala muka kai ta tayi ba, in banda ma Baida mutumci, yaushe ne za'a ce kaman Nihal muji ya koro ta daga ɗakin ta? Dama me take tsinana daga gareshi? Ina ce komai dama bama tsayawa jiran duka mazajen nasu, komi my ne mukeyi masu, koda suna gidan mazajen? Masu aikin ɗana ɗiba mata ma ya kore su? For God sake Alhaji ya kake so inyi to? Sata gaba zanyi in maida mashi ita in bashi haƙuri saboda na gaji da ita ne ko me?" Ta faɗa cikin masifa, tana mai zama bisa kujerar gaba mirror ta fara shafa tsadadden man nata na bacci. Ƙhtawa Alhaji Mustapha ɗin yayi. " Ba fa zan lamunta haka ba Hajiya, dole mu kira shi muji ta bakin shi, masu aiki sune zasuyi mata zaman auren? Duk kinbi kin sangarra yara, ke a ganin ki wannan shine so? Ba gara kuke yi masu ba, kuma ni a matsayi na na mahaifin su, bana jin idan zan zura maki idanu kina yin gaban kanki a cikin gidan nan, kema a ƙarƙashi na kike, ai dole ne kuma kiyi mani biyayya indai kina son zaman ki lafiya. Ba wannan ce ta kawo ni ba, ki shirya idan Allah ya kaimu zamuje kankiya Alhaji yayi kiranmu ni dake da Hajiya Zainab da Yaya Auwalu, saboda haka da wuri zamu tafi" Ya faɗ a yana mai miƙewa cikin tsananin ɓacin rai zai fice. Sai kuma ta sanya kukan kissa irin na gogaggun mata, wanda idanun su ya buɗe da naira. "Alhaji ba sai ka faɗa ba, nasan saboda kayi aure ne kake ta wulaƙanta ni haka, kuma nasan ba yin kanka bane, wallahi ba'a barka haka nan ba, duk yanda zanyi kuma sai nayi na ƙwato miji na" Cak ya tsaya, yanda take kuka, har ya fara jin tsoron wani yaji. Da baya ya dawo. Har yanzu yana son matar tashi, ko B komai ta bashi yara wanda sune farin cikin idanun nashi, kum dasu yake taƙama da alfahari, masalan ma Al'ameen. "Kubra ni ba wanda tayi mani wani abu da kuke tunani daban, halinka ne bana so tin cen dama kun sani, ni Allah bai yoni da son zuciya da son kaina ba, ba zan zuba idanu ina kallo ki zama kece mai gida ba, bayan gani da raina, duk Abunda naga ya dace akan yara na, ni shi zanyi, bana buƙatar shawarar ki ko amincewa ki, sannan da mun dawo daga kankiya, dole ne zan nemi yaron nan i ji dalilin maido Nihal gida da yayi, sannan kada ki daura ma kowa alhakin cenza maki da nayi, ki binciki kanki, gashi dai kin girma harda jikoki, Amman wani lokacin tunanin ki sai ya dinga komawa kaman na Afnan" Yana gama faɗar haka ya sanya kai ya fice daga ɗakin nata. Ko ba komai yau dai bai sanya ran zata je sashen nashi ba, dama tinda yayi aure, saidai taje kawai idan wani abu ya kai ta, Amman dai ba kwana ba, a cewar ta ba zata taɓa haɗa miji da ƴar aiki ba maciya amana. Wani kukan ta kuma fashewa dashi, tana mai jawo wayar ta ta kira number ɗin hajiya Sa'a. Yau ita Kubra ita ce Alhaji ke faɗa ma magana haka? Lallai kura tayi kafiya, ko ba komai itama indai malamai ne masu addu'a tasan inda zata bi ta same su. Hajiya Sa'ar na ɗauka, sai kuma ta ƙara fashewa da wani kukan tana zayyane mata abunda ke faruwa. *Yau Hajiya Kubra mai taƙama da kuɗi, wayewa da jin kai ita ce ke ma miji kuka, akan kishiya? Hmmm* _Duk ina kuɗin?_ _Duk ina dukiyar?_ _Duk ina jin kan?_ _Duk ina wayewa?_ _Duk ina izza da alfaharn?_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'ar Ziyarar Makabarta.* اَلسَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ المؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنّا إِنْ شَاءَ اللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، وَيَرْحَمُ اللهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ. *Assalamu 'alaykum ahlad-diyari minal-mu'mineena walmuslimeen, wa-inna in shaal-lahu bikum lahikoon,{wa yarhamu l-lahu-l- mustaqdimina minna wa-l-musta'khrina} nas-alul-laha lana walakumul-'afiyah.* *Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma'abota wadannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji kan wadanda suka gabata daga cikinmu da wadanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala'i gare mu da gare ku.* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~55~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Yayi matuƙar mamaki, lokacin da ya fito da safe ake shaida mashi tafiyar iyayen nashi zuwa kankiyar To saidai bai kawo komai a ran nashi ba, haka ya wuce kai tsaye zuwa cikin gidan. Nihal ce zaune a falo bisa sofa, hankalin ta kwance take ta latse latsen wayar ta, yayin da Maree ke gaban Tv stand tana goge goge. Zama yayi, yunwa yake ji, Amman yana gudun yace Nihal ta sama mashi wani abu, domin yasan ba iyawa tayi ba, shi kuma baya jin ma idan zai iya kai abincin Maree a bakin shi, totaly ma shi ƙyamar ta yakeyi baisan dalili ba. A hankali ya maida kallon shi kan Nihal ɗin da ta gyara zaman ta, cikin ɗan shakkun Yayan nata haka ta shiga gaida shi. Amsawa yayi a daƙile, yana jifan ta da wani irin kallo mai ma'anoni da dama. "Je ki matso mani Cofee" Abunda kawai ya faɗa kenan, yana mai ɗan zamewa bisa sofar ya jingina bayan shi jikin kujerar. Da saurin ta ta miƙe, zuwa ga dispenser ɗin da take ta gefen dining da yake cen area ɗinshi ajiye. A hankali Maree ta ajiye ƴar farar doster ɗin dake hannun ta, tana mai isowa inda yake zaune, daga ɗan nesa kaɗan ta zuƙunna tana mai cewa "Yaya ina kwana? Me za'a kawo maka?" Bai ko ɗago idanun shi da suke kulle ba ya kalle ta, sai cewa yayi "Kije kawai ki bar shi" Ko da ya faɗi haka kasa tashi tayi daga inda take zuƙunne, ganin idanun shi a kulle ne ya bata damar kuma ƙure shi da kallo ko motsi bata yi. Shi ya ma fita batun ta, saboda haka ya ɗauka tabar wurin ne, saidai yanda yaji idanu na yawo bisa jikin shi, kaman ana kallon shi, ya sanya shi buɗe idanun nashi a hankali, sai kuma ya shiga ɗagowa yana mai wara idanun shi akan Maree ɗin da yaga ta natsu ko numfashi bata sauke wa. "Ke Meye kike yi haka?" ya faɗa cikin daka mata tsawa. Cikin firgita da ƴar gigita ta ja baya, sannan ta miƙe tana ƴan kame kame, "Yaya jira nake ka faɗi Abunda za'a kawo maka" Ɗan zaro mata idanun shi yayi, saboda yasan ƙarya takeyi, cikin sakar mata wata uwar harara yace "Nace ki bar shi ko?" "To" ta faɗa tana mai wucewa da sauri zuwa inda take goge goge Da harara ya raka ta, yana mai jan ɗan ƙaramn tsoki, "Village girl" ya faɗa a hankali, daidai lokacin da Nihal ɗin ta iso ɗauke da Mug ɗin Cofee ɗin da yake ta faman tururi. Amsa yayi yana mai nuna mata gefen inda yake zaune, alamun ta zauna. Tasan ba zai tanka ba, hakan ne ya sanya ta kai zaune kaɗan cikin ɗan ɗosanawa. Ajiye Mug ɗin yayi bisa stool, sannan ya jawo wayar shi, yana mai latsa kiran wata number. Ta ɗaya ɓangaren kuma bugu uku tayi aka ɗaga. Cikin girmamawa Wancen ɗin ya shiga faɗin "Ranka shi daɗe barka da tashi, ya gida da aiki?" "Lafiya ƙlau Deen ya naka aiki?" shima Al'ameen ɗin ya faɗa babu yabo ba fallasa. Zaro idanu Nihal ɗin tayi, cikin kaɗuwa, gaban ta ne ya cigaba da faɗuwa, kadai ace Babyn ta ne Ya Ameen ɗin ya kira? "Lafiya ƙlau Big Bros" "Deen bansan me ke faruwa ba, na dai dawo naga Nihal a gida, shine take faɗa mana wai ai kai ne kace ta taho, shine dalilin kiran naka domin in yi comfirming sannan inji dalilin tahowar tata, kada ya kasance ace ba kai ne ka turo ta ɗin ba" Ya ƙarshe cike da takaici, ta ɓangaren guda yana mai sakar ma Nihal ɗin harara, wadda har tayi narai narau da idanu. Tasan halin Yayan nasu gabaki ɗaya, wannan shine ƙaramn aikin shi, ita dama bata jin Mom daga shi sai Dad take ji, Tasan ko Mom tayi shiru da maganar su fa ba zasu ƙyale bane. Gyara zaman shi Deen yayi bisa waiting chair, sannan ya shiga cewa "Eh kwarai kuwa yaya, nine nace ta taho gida, dalili kuwa shine, Nihal babu Abunda ta iya, na dangane da zaman aure, kai ko kaya ta cire anan zata bar su, saidai masu aiki ne zasu yi mata, hatta da ɗaki na sune take sanyawa suna shiga suna gyara mani har toilet, gashi ba wata kyakkyawar alaƙa tsakanin ta dasu, kullum sai zagi da hantara, komi sukayi mata bata godewa, girki wannan ko ruwan zafi ne za'a dafa bata san yanda zata yi shi yayi daɗi ba, saidai ta sanya ƴan aiki, na sallama su, saboda ta samu ta koya, shine take faɗa man ita fa ba zata iya ba, wannan ne dalilin da yasa na ce ta taho gida to, idan ta koya sai ta dawo, saboda Nidai na faɗa mata, ko da nake sonta, ba zan iya haƙurin zama da ita a haka ba, infact ma ace ko hidima ta data kamata ace tayi mani saidai ta sanya ƴan aiki suyi mani, na nema mata makaranta da zata je tayi course na shekara ɗaya, inda duk zata iya waɗannan ayyukan tace mani ita gaskiya ba zata iya zuwa ba, shine ya sanya nace ta thao gida domin asan halin da take ciki, na Ɗauka ma za'a kira ni tin jiya, gashi kuma ni yanzu ina airport, da sai inzo gidan ayi maganar gani gata" Tin da ya fara magana Ya Ameen & in bai katse shi ba, sai ma sipping cofee ɗin shi da yake tayi a hankali a hankali. Jin ya kai aya ne, ya sanya shi shima ajiye Mug ɗin, sannan ya maida hankalin shi kan Deen ɗin. "Is ok Deen kayi tafiyar ka, har zuwa lokacin da ka dawo, ai bamu san Abunda ke faruwa ba, da tun tuni mun ɗauki mataki, kayi haƙuri, Allah kuma ya tsare hanya, kada ka damu, insha Allahu duk waɗannan abubuwan za'ayi ƙoƙarin ganin ta iya ɗin" Ya faɗa cikin wani irin yanayi na takaicin zuci. "Shikenan Big Bros, na gode matuƙa Allah ya ƙara girma, don Allah ina gaida su Dad da Mom, a sake basu haƙuri, nasan na ɓata masu" "ah no non no, ba wata damuwa insha Allahu, Allah ya kiyaye hanya" Al'ameen ɗin ya faɗa yana cutting kiran. Duk abunda suke faɗa tana ji, domin a yanda free ya sanya. Har ta fara matar kwalla, wai yau ita ce Babyn ta yake faɗar haka a kanta, bayan babu ta inda ta gaza dashi, jikin ta da duk Abunda ta mallaka nashi ne, bata yi mashi shamaki duk lokacin da ya buƙata, to ai ita a zaton ta shine kawai zaman auren, in har zata biya mashi buƙatar shi, komai mai sauƙi ne. "Kinji Abunda ya faɗa ko? NIHAL nasha faɗa maku, wannan sangartakun da Mom keyi maku ba gata bane, kowanne namiji da halin shi, shi ya ma yi haƙurin zama dake kusan shekara har da wani abu, a haka Amman bai taɓa koro ki gida ba, yanzu wa gari ya waya? Mom ita ce zata maki zaman auren? Balle kice ta ɗiba maki masu aiki komi sune zasuyi maki? Deen fa ba yaro bane kaman ki da za'a ce bai mallaki hankalin kanshi ba, saboda haka bana son jin komai a bakin ki, idan zaki gyara ki gyara. Ya faɗa cike da takaici, kaman baya son maganar, ita kanta muryar tashi a hankali a hankali take fita, duk abun nan da ake Maree na daga cen gefe tana aikin, Amman a zahiri hankalin ta yana kan Ya Ameen ɗin, ta baza kunnuwa tana jin Abunda ake Miƙewa yayi,hannuwan shi duka zube cikin aljihn shi, ya fara taka wa da niyyar barin sashen. Sai kuma ya dakata yana mai waiwayowa, ya kalli Nihal ɗin da har ta fara shesshekar kula, ko ba komai tana son mijin ta, Babu bai kyauta mata ba, kuma wallahi ya bayar da ita, ita fa babu wahalar da zata yi saboda zama dashi, idan bai iyawa a haka ya rabu da ita kawai, wasu zasu kawo kansu, tinda Allah ya mallaka masu komai na rayuwa. Muryar shi ce ta katse mata tunanin da takeyi. "Ke Daga yau bana son sake ganin ki a sashen nan kinzo aiki, ki bari Nihal ce zata dinga yin komai a cikin gidan nan, harda girki ma duka" ya faɗa yana kai juna Maree da hannu. Ba Nihal ɗin ba da maganar tazo mata kaman saukar aradu, har Maree tasha mamaki. Aikin gidan nan? Ace Nihal ce zata yi? Lallai rayuwa mai juyi, wai kwaɗo ma daya faɗa ruwan zafi, cewa yayi "Uhmmm kaima ka cenza hali ne?" Kuka Nihal ɗin ta fasa, tana mai Miƙewa ta nufi ɗakin ta, take faɗin "Wallahi yaya ba zan iya ba, ni wallahi ba zan iya ba yaya" Bai jira komai ba ya juya ya idasa ficewa, yana mai cema Maree "Kinji dai na faɗa maki" Gyaɗa kanta tayi, tana mai ƙyaƙyata dariya, bayan ficewa tashi, ko ba komai zata samu sauƙi, saidai inda abun baiyi mata daɗi ba wuri ɗaya ne, ta yanda ba zata samu damar ganin Ya Ameen ɗin ba a kullum, sannan burin ta na ta samu wani abunda Tasan zai ci ta barbaɗa mashi magani ya ruguje. A haka itama tabar sashen tana mai ayyana in yasan wata ai bai san wata ba, ko ba komai idan ita an hana ta shiga, ai ga Mama talatun ita ba'a hana ta ba, ko ita zata aiwatar masu da komai. Cikin matuƙar ɓacin rai ya koma sashen nashi, gara yaje ya dafa ko noodles ce yaci, domin yana jin yunwa, gashi ba zai iya komawa wajen Umman yace ta bashi wani abu ba kuma yaci, kunya yake ji, ko jiya da ya faɗa domin ayi raha ne kawai ya faɗa. Kafin ya isa ga kitchen ɗin ne, ya latso number ɗinta. Saida ta kusa katse wa ne yaji ta ɗaga cikin murya mai kama da ta yanzu ta tashi bacci. Sallama nayi mashi cikin ƴar murya ta, ina mai gaida shi a lokaci ɗaya. "My Queen bacci ma kike yi kenan? Nine na tada ki?" ya faɗa yana mai idasa shige wa kitchen ɗin. Ɗan gyaɗa mashi kai nayi a hankali kaman yana gani na, yau bana da lecture ɗin safe, Shiyasa nayi kwanciya ta, ina ji su Khadee suka tattara suka tafi library, duk da suma basa da lecture, Amman cen suke zuwa yin karatu wani lokacin. "Eh yaya, bana da lecture ɗin safe" "Naji daɗi, ai hrt beat har na fara tunanin sama maki trnsfer saboda bana so wannan malamin tsohon saurayin ki, yana kalle mani ke" Ya faɗa cikin ɗan zaulaya, lokaci guda yana mai ɗauraye tukunya cikin sink. "Uhmm" kawai na iya ce mashi, domin dai ni ya bani mamaki, tin bayan rabuwa ta da Sir Salim ɗin, bai kuma yi mani magana akan shi ba, shima haka Sie Salim ɗin ke nunawa kaman babu wata alaƙa da ta taɓa shiga tsakani na dashi. "Yes dear kada kiyi mamaki, kinsan ina matuƙar kishin ki gaskiya, idan so samu na mane, ya kasance makarantar nan babu namiji ko ɗaya" Cikin mamakin shi na ɗan zaro idanu na waje, yanzu shi har ya iya yayi mani irin wannan kishin? Duka ma yaushe ne aka fara soyayyar da har za'a e irin wannan kishin ya fara shiga? Katse mani tunani yayi da cewa "My Suhan gani zan dafa indomie, kinsan ban iya ba, shine na kira ki ki faɗa mani yanda zanyi tayi daɗi, su Mom basa nan sun tafi kankiya" ya faɗa yana mai ɗan ƙumahe dariya. Nima dariyar nayi, kaman na taɓa ji fa Afnan tace man ya iya girki, to Amman ya na iya tinda yanzu yace mani bai iya ba? A hankali na shiga kwatanta mashi yanda zaiyi, sai kuma Naji ya kashe wayar, cen sai ga kiran video ya shigo, ooh ni ƴasu, shi dai ya yarda da video call, ko me yake ji idan yana kallo na? Gashi ni kuma ko fuska ban wanke ba, a hankali na sauka kan gadn ina mai jawi niƙab ɗina na ɗaura sannan na amsa kiran. Cikin ɗan zaro ido shima yake faɗin "Ne zan gani haka? Wa kike ɓoye ma fuska? Abeg ki cire shi tin muna mu biyu" ya daɗa yana mai ɗan haɗe idanu sama da ƙasa, saboda in gane yaji haushi. "Yaya dama a haka nayi bacci" Na faɗa a hankali, saida ya kauda fuskar wayar yayi dariya kaɗan, sannan ya maido fuskar tashi yana faɗin. "Idan ba zaki cire ba, sai in kashe waya ta, ba kuma zan sake kira ba, har sai na dawo" A hankali na zare niƙab ɗin, ina mai faɗin "yaya tafiya zaka yi ne?" "Eh dear, wani ɗan aiki ne ya taso mani, Amman kar ki damu kwana biyu kawai zanyi in dawo, nima bana so ina nisa dake, nafi so har sai an ɗaura mana aure sannan, kinga yanzu da kina kusa ba sai na shiga kitchen ba" ya faɗa yana mai ajiye wayar gefe sai tin inda zan dinga kallon shi, ya shiga juye indomie ɗin, sannan ya ɗauko kwai guda biyu ya shiga kaɗawa. Nidai kallon shi kawai nakeyi cikin wani yanayi, ya saki jiki dani sosai kaman ba shi ba, kuma duk Abunda yakeyi cikin kwarewa yakeyi, gashi dai komai a nutse aka yin shi, kitchen yake Amman kaman yana cikin ɗaki, saboda tsafta da kyaun kitchen ɗin. Har ya gama yana ɗan hana da fira haka jefi jefi. Sai kuma ya kinkimi wayar da abincin ya nufi bisa dining, acen muka cigaba da fira haka a hankali a hankali yana zaulaya ta wai tayi daɗi nazo ya bani a baki.. ****** Kaduna suka sauka, don haka driver ya kwashe su sai Katsinan Dikko ɗaki kara, kunya garemu ba dai tsoro ba. Kowa part ɗinshi ya wuce, tin cikin jirgi tsakanin Hajiya Kubran da Hajiya Zianab ɗin saidai sama sama, KO alhaji Auwalu tin da ta gaida shi bata sake tanka mashi ba, Alhaji Mustapha yana kula da ita, saidai kawai ya girgiza kai. To itama Hajiya Zainab ɗin wannan karon ɗaurewar tayi, ta kula lallaɓa ta da akeyi ne ya sanya take ganin kaman biyayya gareta dole ne, ko kuma tana ganin zata iya taka su a duk lokacin da taga dama ta wuce, ta shirya nuna mata ba fa haka abun yake ba, kawai wani lokaci Albarkaci mijin nata mutumen kirki take ci, tinda bata neman komai a wurin ta, ai tana ganin ba dole bane ace sai ta mu'amalance ta. Kafin suje an shirya masu abinci mai rai da lafiya, kowa sashen shi aka kai mashi, duk da Hajiya Kubra har yanzu akwai abubuwa cunkushe a cikin ranta, tin da aka faɗa mata tafiyar take ƙissima akwai abunda ya shafe ta a cikin al'amarin, saidai ma ko menene ta shirya jin shi daga bakin surukan nata. Bayan sallar la'asar ne, rana tayi sanyin lokacin, duk dai da babu zafi daman ko ina Ac na aiki, wannan aikin Alhaji Mustapha ne, a cewar shi dole ne suma tsofaffin su dara a lokacin da Allah ya ara masu rayuwa, ina amfanin ka samu iyayen ka na cikin wahala? Su Alhaji Mustapha ɗin ne suka fara shiga Falon Mahaifin nashi, Alhaji Isuhu farin tsoho, mai tarin kwarjini da hajba, ko wanne gashi na jikin shi ya rikiɗe ya koma hurhura. A ƙasa suka samu suka zauna, yana daga bisa kujerar ta alfarma wadda aka ƙawata kaman a gidan sarakuna. Nuni yayi masu da su koma bisa kujera su zauna, magana ce mai muhimmanci ta tara su anan, yana so su fara tattauna wa ne, kafin ace matan nasu sun shigo. "Dalin da yasa na tara ku anan shine, kai Mustapha maganar auren yaron wurin naka ce data taso, Naji dukkanin Abunda ke faruwa, alal haƙiƙa mu duka harda ita mahaifiyar taku, mun goyi da bayan ayi auren, saidai kasancewar itama mahaifiyar yaro tana da haƙƙi a kanshi ne, ya kamata itama a bata dama ta faɗi ra'ayn ta, a kuma nemi amincewar ta, cikin ruwan sanyi ba tare da tursasawa ba, kaman yanda Naji kana ƙoƙarin yi" Dukansu kansu yana ƙasa,ba wanda ko yace uffan, har mahaifin nasu ya kammala maganar shi, na daga cikin irin tarbiyyar da suka samu kenan, mahaifin nasu duk da yake ya matuƙar tsufa, yana iya zartar da hukunci akan iyalan nashi da ma nasu baki ɗaya. Alhaji Auwalu ne ya ɗago cikin girmamawa yake ceman mahaifin nasu "to alhaji, gaskiya abunda ya kamata kenan ayi tun tuni, a nemi yardar ta da sanya albarkar ta acikin al'amarin, muddin har muna neman zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin su" Jinjina kai tsohon yayi, cikin matuƙar gamsuwa, a kullu yaumin yana alfahari da yaran nashi, ko da suka zama wani abu a rayuwa, suna matuƙar kiyayewa, suna bin unurnin su, sannan ba zasu taɓa yin wani abu ba, batare da sun nemi shawara da yardar iyayen nasu ba. Ko auren alhaji mustapha da umman ba abunda basu sani ba akai, kuma sune ma suka bada goyon bayan su ɗari bisa ɗari saboda Kaka zuwaira ba abunda bata faɗa ma tsohon mijin nata ba, zaman da tayi lokacin bikin su Hafsat ɗin. Umurni Alhaji Isuhun yayi da ace matan su shigo. Hadda Kaka zuwaira aka shigo ɗin, nayi mamakin da naga bata wajen da su Alhaji Mustapha ɗin suka tattauna, ashe Alhaji Isuhun ne yace ta dakata su gana da yaran nashi sannan, har yanzu akwai biyayya mai ƙarfi da ƙauna da girmama na gaba tsakanin tsofaffin (Abunda zamanin yanzu babu kenan, so da dama ma wasu matan na jin matsayin su ɗaya da mazajen nasu, masalan ma ace an manyanta a tare) Kujera suka samu suka zauna, Amman Hajiya Zainab saida ta kai ƙasa zata zauna ne Alhaji Isuhun ya umurce ta data tashi ta koma kan kujerar kaman yanda ƴar uwar ta tayi. Bayan yayi gyaran murya ne, sun gaida shi ya amsa, cike da manyance ya fara magana. "Maƙasudin tara ku anan shine, maganar auren yaron nan ne Muhammadu Al'ameen, Ke Kubra duk munji meke faruwa ta ɓangaren naki, saidai akwai ƴan shawarwari da nake so na baki, a matsayi na na mahaifin mijin ki gashi nan zaune, ina so ki sani su ƴaƴa amana ne Allah ya ɗora mana bisa kanmu, kuma akwai ranar da za'a tambaye mu a isa amanar da aka bamu, ina so ki sani, shi yaron nan Muhammadu yaro ne da kaf zuri'ar mu take alfahari dashi, zan iya ce maki babu yaro mai hangen nesa, mai jin ƙan talakawa, ƴan uwan shi, da ma na ƙasa dashi kaman shi, saboda haka ya kamata ace muma ya bujiro mana wata buƙata da bata fi ƙarfin mu ba, ace mun magance mashi ita, aure ne yace yana so yayi, kuma ya bayyana wadda yake so ya aura, ga mahaifiyar ku nan zaune, ita ce ta bada shaidar halin kirki irin na mahaifiyar yarinyar da ma ita kanta yarinyar, saboda haka ni a madadin shi Muhammadun nake roƙon ki da ki janye maganar ƙiyayyar da kike nuna ma yarinya, ki amince su auri juna, ina gudun lokacin da zai iya bijire maki ne, sanin kanki ne tinda kika haifi yaron nan, baki taɓa buƙatar shi da yayi maki wani abu ya gaza ba. Ga mahaifa shi nan zaune maza, sun sha alwashn yin auren ko da kuwa ace baki yarda ba, nine nace masu ba haka akeyi ba, a matsayin ki na mahaifiyar shi kema kina da haƙƙin a tuntuɓe ki kuma a samu amincewar ki, ina mai roƙon ki da ki amince ma auren, ki sanya masu albarka, kuma ki ajiye duk wasu makaman yaƙin ki dashi, ki sani shine ɗanɗan ki babba namiji, zaki ji daɗi ace yau duniya ma gabaki ɗaya tana alfahari da yaron naki ba ma nigeria kaɗai ba, kina so ya samu koma baya akan al'amurran shi? Ta dalilin ƙin amince m auren nashi da kikayi shi kuma ya nace sai yayi? Ta tabbata yana son yarinyar nan, itama kuma tana sonshi, tana da tarbiyya daidai gwargwado kusan ma muce a gaban ki ta taso, to akwai buƙatar sanin wani abu kuma bayan wannan?" Ya ƙarshe yana mai kallon Hajiya Kubran d aka ta yaje ƙasa, kwarjinin tsohon da yanda yake zaro magana sun cika ta. Ga Hajiya Zainab a kusa da ita, tinda Alhaji Isuhun ya fara magana take gyaɗa kai. Zama dai ne na manya, idan kafa da yanda ake maganar zaka sha mamaki, kuma abun zai ƙawatar da kai. Shiru ne ya biyo baya. Kaka zuwaira ce ta muskuta, tana mai gyara zamanta, sannan ta cigaba da cewa "Hajiya Haƙuri zakiyi, ƙiba yaron nan dama, ni dama tun bikin waɗannan yaran su takwara ta, na fahimci yaran suna matuƙar son junan su, kuma ma ba haka ba, tin kafin nan, ina ce a gaban ki ya shaida mana cewa ita yake so zai aura? An dakatar dashi ne ada cen baya saboda dalilan da kika kawo, a yanzu ba wannan dalilin ga Mustapha nan, shine uwar su shine uban su, muma mun amince masu ya auri ita Maryamar balle ɗiyar ta, don haka muna mai roƙon ki, ba wai don wani abu ba, saboda gudun bijirewar shi Ameenun gareki, ki bar shi ya aure ta, ki sanya ma abun albarka, saboda baki damar ki kema ta uwa, ya sanya muka kira ku nan, wannan shine" Alhaji Mustapha da Alhaji Auwalu, gabaki ɗayan sai jinjina kai suke yi, gaskiya Mahaifiyar su ta faɗa, saidai su dukansu suna mamakin taurin kai irin na Hajiya Kubran. Nisawa Hajiya kubran tayi, cikin isar ta da har ta zamar mata jiki, ta fara cewa "Shikenan baba Alhaji, naji buƙatar ku kuma na amince, Amman ina so shi Al'ameen ɗin ya sani, akwai wasu sharuɗɗa dan zan kafa mashi, muddin ya amince, to nima na amince a ɗaura auren su, kaman yanda kuka buƙata, saidai fa bijire ma sharuɗɗn nawa, daidai yake da sake ƙin amincewar tawa" Da mamaki su dukansu suke kallon su, ba ma kaman Hajiya Zainab da take mamakin wai Hajiya Kubra na da lafiya kuwa? Sharuɗɗa take kafa ma surukn nata? Ɗan murmushi tsohon ya saki yana mai faɗin "shikenan Kubra, faɗi sharuɗɗan naki muji, saidai muna fata ba zasuyi matuƙar wahala ga shi yaron nami ba" Saida ta ɗanyi jim, tana mai ɗagawa ta kalli mijin nata, sannan tace "sharaɗi na farko, zai ajiye matar tashi a cikin gidan mu ne, bana da buƙatar ya gina mata guda a waje, sharaɗi na biyu kuma nan gaba zan bashi wata matar da zai aura, idan har ya amince to nima na amince da buƙatar tashi, Allah ya basu zaman lafiya" Gabaki ɗayan su sunyi mamakin wannan sharaɗn nata, Alhaji Mustapha ne ya buɗe baki zaiyi magana, sai Alhaji Isuhun ya dakatar dashi. "Ba komai Kubra, hakan ma yayi, Allah ya sanya ma abun albarka, kuma ya basu zaman lafiya, muna fatan zaki cigaba da taya shi addu'a, a matsayin ki n a mahaifiyar shi, domin cin nasara a Rayuwar shi?" Jinjina kai ta shiga yi, fuskar nan tata tam, kaman bata taɓa dariya ba. Sun sake tattauna abubuwa, sannan suka sallama matan, suka koma sashen nasu, yayin da su huɗn suka cigaba da tattauna wa. Ita kuwa Hajiya Zainab, tana shiga sashen ta, ta kasa ƙarasawa ciki, me hakan ke nufi? Ko dai Kubran tana d a wata manufa ne ta buƙatar a ajiye Suhan ɗin cikin gidan? Kai anya kuwa hakan zai yuwu? Zama gida ɗaya a ƙarƙashin inuwar aure ita da Umman tata? Ita kuwa Hajiya Kubra tana shiga sashen nata, wayar Hajiya Sa'a ta kira. Tana ɗauka bata ko yi sallama ba ta shiga cewa "Hajiya Sa'a, na amince kaman yanda mukayi dake, yanzu aiki ya rage naki, ina so yaji duk duniya ba wadda ya tsana kaman ita, ina so yaji cewa ko a ƙafa aka ɗaura mashi ita zai iya kwance ta, ina so taji duk duniya ba wadda baya son gani sai ita, ina so yaji tana wari, ina so yaji baƙiƙƙin duk lokacin da ya kusanto ta, sannan ina so yaji baya iya bijire ma buƙata ta, aduk lokacin d ana buƙaci wani abu, idan kikayi mani haka, zan baki mamaki, zan mallaka maki Abunda baki taɓa tsammata ba, har karshen Rayuwar ki" "A gama Hajiya ta, duk yanda kika buƙata hakan za'ayi, yanzu dawowar ki kawia nake tsimaye, komai ya tafi daidai insha Allahu" Katse wayar Hajiya Kubra tayi, tana mai sakin wani irin huci kaman wadda tayi gudun fanfalaƙi. *Haba Alhaji Isuhu, Hajiya Zuwaira, Alhaji Auwalu da baƙar daga Hajiya Zainab, in kunsan wata ai baku san wata ba* Ta faɗa tana mai yaye gyalen ta, ta wurga shi bisa sofa ta zauna bakin gadon a hankali, jin sawun takun shigowar Alhaji Mustapha. ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Addu'ar Cin Abinci* *Idan mutum zai ci abinci sai ya ce;* بِسْمِ اللهِ. *Bismi l-lahi.* *Da sunan Allah* *Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna)* بِسْمِ اللهِ فِي أَوَّلِهِ وَآخِرِهِ. *Bismi l-lahi fi awwalihi wa akhirihi.* *Da sunan Allah a farkonsa da karshensa.* *Wanda Allah ya azurta shi da abinci ya ci, to ya ce;* اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَأَطْعِمْنا خَيْراً مِنْهُ. *Allahumma barik lana feehi wa-at'imna khayran minh.* *Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma Ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri.* *Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce;* اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَزِدْنا مِنْهُ. *Allahumma barik lana feehi wazidna minh.* *Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka kara mana ita (madarar).* *Page ~56~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Bai ko kalli inda take ba, ya wuce kai tsaye zuwa gaban wardroop gami da buɗe ta, ya zare babbar rigar shi ya raya ta ta ciki, sannan ya juyo yana mai ɓalle links ɗin hannun shi yake ce mata... "Ki shirya da wuri zamu wuce gobe" "Amman Alhaj...." da hannu ya dakatar da ita. "Ya isa Kubra, kinyi abunda ranki ke so, to nikam bana son jin wani abu daga bakin ki, sharaɗi ne kun kafa, kuma su Alhaji sun yarda so what else kuma? Aure ne dai sai anyi shi, ko da izinin ki ko ba da izinin ki ba, kuma inaso ki sani, yardar ki da kika ga an nema domin bana da yadda zanyi ne, magabata na ne, ba don haka ba ko sauraren ki ba zan tsaya yi ba" Yana gama faɗar hakan ya zare rigar dake jikin shi ya shige toilet ya barta nan sake da baki. Ka faɗa ta ɗaga, cikin zuciyar ta take cewa. "Yaro dai nawa ne, in kai Van isa hana ka aure ba, ai shi ina da hanyoyin da zan bi a kanshi, me ake da irin talaka ma a rayuwa?" **************** Da wuri suka shirya kuwa. Sunyi sallama da iyayen su, sun kuma ƙara jan hankalin su, akan kada su biye ma mace hidimar auren nan ya kawo matsala. Hajiya Zainab da Hajiya Kubra sama sama ake tsakani, don ma Hajiya Zainab ɗin wayayya ce, Sam bata bari mazajen nasu suka fahimci akwai wani ƙulalla tsakanin ta da Kubran ba. Har suka iso Kaduna, daga nan ne sukayi talking flight direct to Abuja. Mudi driver ne yaje ya ɗauko su, Hajiya zainab kuwa kai tsaye tace a wuce da ita gidan Alhaji Mustapha ɗin zata je wajen Umman Suhan. Ba wanda yayi musu tsakanin mazajen nasu, ko ba komai sun san Abunda zai kai ta, kuma suma suna da buƙatar hakan, itama Umman Suhan ɗin ai uwa ce, ya kamata ko me ake ciki ta sani itama. Hajiya Kubra kuwa ta shaƙa, gani takeyi don Hajiya Zainab ɗin taci mata fuska ne ya sanya ta faɗi haka, koma menene zata yi maganin su ne su duka ta ruwan sanyi. Wajen ƙarfe sha biyu suka isa gidan, fuuu hajiya kubra ta fito daga cikin motar ta nufi part ɗinta, da kallo suka bita su duka Alhaji Mustapha na girgiza kai cikin takaici na halin Kubra da yake fama dashi ba tin yanzu ba. Haƙuri Alhaji Auwalu ya shiga bashi, yana mai faɗa mashi su fa mata duk inda suke mata ne, saidai wata tafi wata, haƙuri kawai zaiyi, Amman shi kanshi ai yasan dole ya gamu da hakan. Kai tsaye Hajiya Zainab part ɗin Umman ta nufa. Falon ba kowa sai tashin ƙamshi yakeyi. Ga ƙira'a mai daɗin sauraro a hankali tana tashi Sallama take ta yi, Amman ba wanda yaji. Hakan ne ya sanya ta nufar ɗakin Umman kai tsaye. Knocking ta shiga yi, daga ciki umman taji ana bubbugawa, ta taso daga gaban mirror da take shafa kwallo, already ta riga ta gama shiryawa tsaf, Alhajin ta kawai take jira, tin lokacin da ya shaida mata sun taso, ko ba komai yanzu ta shirya tsaf wajen amsar mijin nata. Buɗe kofar tayi tana mai sakin murmushi. "A'a Yaya ce? Sannun ku da zuwa, ki shigo daga ciki mana" ta faɗa tana mai kamo hannun Hajiya Zainab ɗin suka koma cikin ɗakin. Bisa Sofa kwaya ɗaya dake ɗakin Hajiya Zainab ɗin ta zauna. Gaisawa suka shiga yi a mutum ce, kowa na ganin ƙimar kowa, Ta fannin Hajiya Zainab halayya da sanyin halin Umman uwa uba fara'r ta, da girmama mutanen ta na ƙara mata ƙaunar matar, tana so Al'ameen yayi dacen suruka kaman Umman, Tasan in hakan ya faru baya da matsala ko alama, ko ɗan dake cikin ta bata jin idan zata hana shi nema mashi tsatson Umman. "Ina su Alhajin ne? Kaddai ace wucewa sukayi, gashi na shirya maku abinci, kada a barni dashi in rasa ya zanyi dashi". Umman ta faɗa fuskar ta a sake cike da annuri. "Aiko suna waje, ki kira su, kada su kuma fita, don ni ba tafiyar mu ɗaya dasu ba, ni daganan gida zan nufa direct" Waya ta jawo gami da rubuta ma Dad ɗin saƙo. Suna tsaye da Alhaji Auwaln suna sake tattauna yanda komai zai tafi, sia ga saƙon ya shigo. Da fara'a yake kallon yayan nashi. "To yaya kaji wani abu kuma, wai Maryama ce take cewa kar ka tafi don Allah abincin mu na nan yana jiran mu" ya faɗa fuskar shi ƙumshe da fara'a. "a'a kuma? To ayi haka? Gaskiya kuma fa ina buƙatar abincin nan, to ka faɗa mata akai mana sashen ka, don Nidai ba zan iya zama part ɗinta inci abinci ba, kasan har yanzu mu Fulani ne" alhaji Auwalun ya faɗa shima cike da fara'a. "To bari in sanar da ita." Kiranta yayi ya sanar da ita akai masu abincin cen part ɗinshi. Cema Hajiya Zainab ɗin tayi ta jira ta don Allah ta miƙa ma su Alhaji Abinci, Hajiya zainab ɗin ke ce mata. "Ki kirawo wani cikin mazan cen dake bakin gaye ya kai masu mana, naga kayan da yawa " A'a yaya Allah na tuba, ai ba komai, yanzu zan gama haɗa masu, ina zuwa" ta faɗa tana mai miƙeea ta fice. Da kallo ta bita, lallai idan hajiya kubra batayi sa'a ba, tana kallo Maryamar zata ƙwace mata miji a hannu. Yanzu ne Alhaji Mustapha yasan yayi aure... Saida ta gama shirya komai a dining sannan ta leƙa Falon ta gaida Alhaji Auwalun cikin girmamawa, haɗi da yi masu ya hanya. Sannan ta koma sashen nata. Ta fannin Hajiya Kubra, koda ta shiga part ɗin nata kuma, kai tsaye saman ta ta haye, Nihal na ta mata magana ko sauraren ta ma batayi ba. Ta window take kallon yanda amman ke zurga zurga da kuloli zuwa sashen Alhaji Mustapha ɗin, dama kuma taga shigar su sashen da Alhaji Auwalun, watau dama ai Tasan duk wani munafunci Auwalun ne ke haɗa shi, to tinda haka ne, in sun san wata ba su san wata ba, Maryamar da suke rawar ƙafa kanta, sai ta rasa sukuni a cikin gidan. Komawa tayi sashen nata, ta yadda Hajiya Zainab ɗin har ta dawo falo. A nan ta kawo mata abincin. Taci sosai kuma taji daɗin shi, saida ta kammala ne sannan ta gyara zaman ta tana mai fuskantar Umman. "Watau Umman Suhan, nasan da kin ganni zaki kawo ma ranki cewa maganar yaran nan ne, gaskiya ne haka ne, nasan kinsan inda muka je, kuma ke ɗin ba wadda za'a ɓiye ma komai bace, zuwa yanzu dai daga Suhan har Al'ameen yaran ki ne, kuma ke nasan kinsan daraja da ƙimar yaran naki, roƙo ne nake tafe dashi, don Allah Umman Suhan ki bamu goyon baya, ba muna ƙoƙarin jefa yar uwar Suhan a wani hali bane ko don son zuciyar mu, ko domin yaron mu ne ke sonta ba, sai don kinsan ko wanene Al'ameen da kuma dukkan abun da ke faruwa a ƙasa...... " nan ta kashe duk yanda sukayi a kankiya, harda sharuɗɗan Hajiya Kubra ta faɗa ma Umman. Shiru ne ya biyo baya, sai cen kuma Umman ta nisa. " Yaya ai wannan ba wani abu bane, shi dama namiji ai mijin mace huɗu ne, ni insha Allahu ba zaku samu wata matsala da ni ba, saidai maganar zaman nasu ne anan gidan...." "Ba komai Umman a Suhan, ayi kaman yanda tace ɗin, ba tsoro bane, alƙawalin ne aka ɗaukar mata, kuma SU alhaji na kankiya ne suka gindaya wannan sharuɗɗan, Suhan ki yi mana addu'a, da Izinin Allah komai mai wucewa ne, ina so Idan alhaji yazo maki da maganar ki mara mashi baya, tabbas lokaci na zuwa da Kubra zata yi nadamr duk waɗannan abubuwan da take aikatawa" Sake nisawa Umman tayi, ba damuwa Yaya, insha Allahu ba abunda zai faru, saidai nima ina da wata magana fa idan ba zaku damu ba, saidai ina so ne muyi ta mu duka huɗun, ina nufin gaban ki da Shi Alhaji Yaya ɗin" "Ba damuwa Umman Suhana, bari su gama cin abincin, sai muje cen ku same su" Nan suka cigaba da tattaunawa, har zuwa wani lokaci da suka tabbatar da sun gama ne suka miƙe zuwa sashen Alhaji Mustapha ɗin, ko da suka fito zasu shiga sashen Alhaji Mustapha Umman bata rufe sashen nata ba, sai Hajiya Zainab ɗince ke ce mata kul ɗinta da barin sashen ta buɗe, duk inda zata ta tabbatar da tana rufewa, tinda tasan gidan yana cike da magautan ta. ****** To zaune dai yake Office, sai faman juya kujera yakeyi shi kaɗai, Ac ɗin dake Office ɗinma ya dame shi sosai, Amman ya kasa koda miƙewa ne ya kashe. Ya rasa me ke mashi daɗi, so ma yake ya kira Suhan ɗin Amman kuma ya gaza, gashi Bilal ya kira shi tin cikin dare akan cewa sun taho da abie, kuma yaso yaje ya ɗauko su, saidai tau jiki da jini shi kanshi jin shi yakeyi sai a hankali. Mudi driver ya kira, yana mai shaida mashi yaje Airport ya ɗauko su Bilal ɗin, ya wuto dasu kai tsaye Office ɗin, domin ya samu su sake tattaunawa akan abubuwan dake ƙasa, acen birnin New York ɗin da yake amurkan. Cikin awa guda kuwa sai gasu sun iso. Da murna Abie ya nufi yayan nashi yana mai rungume shi, da kallon mamaki yake bin Abie ɗin da ya zama cikakken saurayi abun shi, kaman ba shi ba, ga jiki irin na turawa, ko ina ɓul-ɓul. Saida Bilal ya bashi hannu suka yi musabaha ne, sannan ya koma bisa Sofa ya baje yana faɗin "wash friend, wlh akwai tafiya kam sosai, kusan awa 12 a jirgi" Ɗan hararar shi Al'ameen yayi yana mai faɗin "Kaji shi kaman yau ka fara tafiya america" Mudi ya ba saƙon yayo masu take away. Sannan ya maida kallon shi kan tilon ƙanen nashi "Ya Abie, how far? Ya gajiya?" Cike da shagwaɓa irin na ƴaƴan masu kuɗin abie & in ke cewa "Wallahi Big bros akwai ta, ni fa na ƙagara naga Su Dad da Mom, anya ba wucewa zamuyi da Mudi ba, idan kun gama kun same ni a gida" Kafaɗa Al'ameen ya sauke, yana mai faɗin "To ka kira Mudin ka faɗa mashi ban da kai zaiyo, nima banda ni, sai ko dai Bilal" Da harara Bilal ɗin ke binshi, sai kuma yace "Kajika, kana gauro ɗinne zaka ce band kai, sai dai ko ni? Ka manta ina da mata ne?" "To ina matar take?" cewar Al'ameen yana mai maida kanshi bisa makarin kujerar ya kwantas, lokaci guda yana mai jujjuya kujerar a hankali a hankali. "Oooh haka ne fa, mtseww wlh friend har na fara gajiya da rashin ta a gidan" "Kai ka sani, ka ƙara mana" "aidai gara ni, kai kuwa da ko ɓalli baka da ita fa?" "Me kake tauna na baka na zuba, ƙila dai baka lissafi, nima saura kwanaki ne ai" Da mamaki Abie ke kallon shi, ɗan wari idanu yayi. "Wow yaya ne kake cewa? Kana nufin you are on a date?" Ɗan murmushi ya sakar ma Abie ɗin yana faɗin "Yeah Lil Bro, ka kusa yin aunty, Amman ita bata son hayaniya da surutu fa" "Bro nima ai bana da surutu, ko kuwa Yaya?" Ya maida tambayar kan Bilal. "Really my Bro, ai shi ya ma fika surutu" Ɗan harara wasa Al'ameen yayi, "zama da kai ne shegen kaya" "ko kuma soyayya ba" cewar Bilal ɗin. Su duka murmushi suka sanya, yayin da shi kuma gogan naka ya murmusa, ko ba komai sun tuno mashi da sahibil ƙalbin shi. "wao wat a suprise Yaya? Wacece wannan a ina kuma take?" A hankali ya ɗago yana mai kallon Abie ɗin. "zaka ganta soon bros, me kake ma sauri ne?" Ɗan murmushi Bilal ɗin ya saki. "Lallai ta ciri tura yaya, ashe a ƙasar nan matar taka take, ni da na ɗauka baka son ƴar nigeria ne" Bai tanka mashi ba, sai ma sake sakin murmushi da yayi, da ido Bilal ɗin yayi ma Abie nuni da ya bar maganar. Ɗan ɗaga gira yayi, yana mai ɓame bakin shi, da yin alamu za hannu (Zip). Dariya suka sake saki su biyun, daidai shigowar mudi ɗin ɗauke da take away. Yana ajiye ma Bilal ɗin, Abie ya miƙe yana mai yi masu sallama, yabi mudi ɗin a baya, *********** Zama sukayi Umman na mai sake gaida su, cikin fara'a suka shiga amsa mata, ko ba komai tayi abun da Kubra bata taɓa yi ba tinda mustapha ya aure ta, sun dawo daga tafiya su tadda abinci ready? Wanda kuma ita ce ta girka masu shi? Cikin nuna farin cikin su ALHAJI Auwalun ya shiga yi mata godiyar abinci, ita ma har ya bata kunya. Hajiya zainab ɗin ce ta shiga shaida masu dalilin shigowar su wajen nasu. Dumansu natsuwr su suka maida kan Umman. A hankali ta fara magana, bayan ta sauke kanta ƙasa. "Alhaji nima nace ina da magana, Suhan yarinya ce da tun da ta taso take mani maganar mahaifin ta, da maganar dangin mahaifin ta, da maganar ni kaina dangi na, Amman ko sau ɗaya ban taɓa faɗa mata wani abu ba, daya dangance mu, tayi magiyar har ta gaji, tasha gorin cewa bata da mahaifi, to yanzu lokaci yayi da bama ita kaɗai ba, ku dukan ku zaku san labarin namu, kuma ba yanzu ne zan faɗa ba, har sai munyi wata tafiya mun dawo, ina SO alhaji tafiyar nan ta zama sirri tsakanin iya mu nan, ko su yaran bana so su sani, nayi hakan ne ba domin komai ba, sai don ba yadda za'ayi in iya aurar da Suhan ba tare da sanin mahaifa na ba, ba tare da amincewar su ba, duk da nasan ba wai zasu hana bane, shi kanshi yaron (Al'ameen) domin shi da mahaifiyar shi su samu natsuwar cewa Suhan na da mahaifi, kuma tana da usili mai kyau, kaman yanda nima nake dashi" Ba Alhaji Mustapha ba, har Hajiya Zainab da Alhaji Auwalu ba wanda biyo mamaki ba, dukan su zuba mata idanu sukayi. Ikon Allah, ashe akwai ranar da zata zo Maryamar tayi maganar mahaifarta da kanta. Kusan zamu iya cewa Alhaji mustapha yafi kowa murna da zancen. Cikin mamaki suka shiga jera mata tambayoyi, saidai babu wadda ta amsa, kawai dai ta nemi da su sanya lokaci wanda zata yi masu jagora zuwa ga mahaifar tata, wadda ita da kanta ne ta sanya ƙafar ta tabar ta, shekara ashirin da huɗu da suka wuce. Su ji daɗi, sun yi matuƙar godiya gareta, hankalin su ya kuma kwanciya da auren, sun sanya ranar Juma'a mai zuwa za'ayi tafiyar, don haka Alhaji Mustapha ɗinne zai shirya komai kafin zuwan lokacin. A haka su Alhaji Auwalu sukabmiƙe, gami da yi masu sallama suka nufi nasu gidan, to ko dai a mota tattaunawr da suka shiga yi kenan, Alhaji Auwalun ne ke cewa, shi yana ji a jikin shi, Maryamar duk inda ta fito, ta fito ne daga babban gida, natsuwar ta, da kuma yanayin yanda take mu'ammala da mutane ne ya nuna hakan. Shima Alhaji Mustapha ɗin bai kuma tada mata maganar ba, sai ma waya daya ɗauko yana neman Layin Al'ameen gami da shaida mashi ya same shi gida. Nan ne ya kuma cigaba da lala shin Umman, gami da bata baki, akan ta daure ta jure taba yaran goyon baya su samu Abunda suke so, sharuɗɗan Hajiya Kubran ba abun dubawa bane, muddin dai aka ɗaura auren. Ita kuma tayi hakan ne domin ta tseratar da yarinyar tata daga gorin dangin mijin nata, ko ba komai gorin asali ba ƙaramn gori bane, lokaci ne yazo da zasu gane cewa Suhan ɗin ba abar wulaƙanta wa bace, itama da kalar nata asalin. *********** Saida Bilal ya gama cin abincin, sannan Ya Ameen ɗin ya ɗauko shi zuwa gidan nashi, domin yayi wanka ya huta. Sun rabu akan cewa da ya tashi daga bacci zai neme shi, domin su fara shirye shiryen wucewar Al'ameen ɗin zuwa gobe. Gida yayi ma tsinke, zuciyar shi na daɗa bugawa, domin baisan abunda zai je ya taras ba, masalan wannan tafiyar da sukayi, zuciyar shi na raya mashi cewa ta shafe shi, gashi tin ranar da suka haɗu da Mom ta ɓalla mashi harara rabon da ya sanya ta a idon shi kenan. Part ɗin Dad ɗin nashi yayi ma tsinke. A perlour ya tadda shi, zaune yake bisa Sofa yana kallon tashar aljazeera, shi kaɗai a Falon sai tulin jaridun da suka fito yau wanda bai gama dubawa ba, dama haka akeyi mashi, kullum sai an kawo mashi jaridun da suka fita a ranar ta duba su. A ladabce ya ida ga Dad ɗin nashi dake zaune, ƙafafun shi gabaki ɗaya bisa doguwar kujerar ya kishingiɗa. Dad ɗin nashi mutum ne dake cike da kamala da kwarjini, ƙasa ya samu gefen shi ya zauna, yana mai tanƙwashe ƙafafun shi yake faɗin "Dad barka da rana, an dawo lafiya ya hanya?" Da murmushi Alhaji Mustapha ɗin ya miƙe zaune, yana mai zuro ƙafafun shi daga bisa kujerar, ya daidaita zaman nashi, yana mai shafo kwantaccen sumar kan yaron nashi yake cewa "lafiya Lau Son, ya aiki? Ya rana kuma?" "Duk lafiya lau Dad, ya kuka baro su Alhaji da Hajiya?" "Duk suna gaida ku Son" "To masha Allahu Dad, Allah ya huta gajiya" "Ameen Son, na kira ka ne nan saboda ina so ne mu tattauna wata muhimmiyar magana, nasan kasan munyi tafiya, kuma wata ƙila ka iya gane dalilin maganar auren ka ce ta kaimu cen kankiya ɗin, to Alhamdulillah munje lafiya mun dawo lafiya, kuma na dawo maka ɗauke da magana a bakina, saidai ina so ka natsu tsaf ka fahimta, nasan kana son yarinyar nan Suhan ko ba haka ba?" Gyaɗa kai Al'ameen ɗin yayi, yana mai sake sun ne kai ƙasa, wai yau shine Dad ɗinshi ke cewa yana son wata da bakin shi. Katse mashi tunanin yayi ta hanyar cigaba da cewa." Abunda ya kaimu kankiya kenan, su Alhaji suka buƙaci ganin mu, to cikin ikon Allah ita mahaifiyar taka ta amince da auren naka" Cikin tsanann mamakin farin ciki ya ɗago yana mai kallon Dad ɗin nashi, sai kuma ya saki murmushi, har kumatun shi suka loɓa. Sai kuma ya sake sauke kai ƙasa, zuciyar shi na ƙara hur a mashi wutar son Suhan ɗin, yanzu ne ma da Dad ɗin nashi ke sanar dashi amincewar Mom ɗin, sai yaji ya sake samun natsuwa da soyayyar, wai dama she Abunda ke dakushe mashi kafin soyayyar tashi ga Suhan ɗin, rashin amincewar Mom ɗinne. "Saidai kuma fa, akwai wani hanzari ba gudu ba, ita ma Mom ɗin taka, ta kafa sharuɗɗan guda biyu, a bisa amincewar tata" Cikin mamaki ya kuma ɗagowa ya kai duban shi kan fuskar Dad & in, da take ba yabo ba fallasa. "Dady sharaɗi kuma?" Ya faɗa annurn dake fuskar shi na ƙoƙarin gushewa. "Kwantar da hankalin ka Son, ni a gani na, a ɗaura auren shine mafi muhimmanci kafin wannan. Sharaɗi na farko shine, zaka zauna da matar cikin gidan nan, ina nufin ba zaku bar gidan nan ba kauda a Suhan ɗin ko bayan anyi auren, sharaɗi na biyu kuma shine, duk lokacin da taga wata wadda ta kwanta mata arai zata kawo maka ita ka aura, waɗannan sune sharuɗɗan Mom ɗin taka a gareka, idan ka amince to.. " Baisan lokacin da ya miƙe tsaye ba, sai kuma ya koma ya zauna" Dad zama da mata ta acikin gidan nan? Matar ma wadda kowa yayi yaƙi in mom bata sonta? Aure kuma Dad? Mata biyu ni a shekarun nan nawa Dad?" Duk ya shiga jera ma Dad ɗin tambayoyi, fuskar shi a matuƙar haɗe, wadda ke bayyana tarin rikici da ɓacin ran da suka same shi a nan take. Hannun shi Dad & in ya kamo, yana mai ɗago shi ya zaunar dashi bisa kujerar da yake zaune, kaman wani abokin shi. A ƙoƙarin shi na kwantar mashi da hankali ya shiga cewa "Son kwantar da hankalin ka, babu abun ɗaga hankali ciki, sanin kanka ne cewa idna har baka yarda ba, ba zaka taɓa samun kwanciyar hankali ba a gidan nan naka, muddin matar taka zata haɗu da mom ɗinka, mafi a'ala dai ka yarda da dukkan sharuɗɗan nata. Zam dai ka zauna na wani ɗan lokaci, kafin komai ya daidaita, Amman maganar auren ne nima har yanzu nake nazari akai, Amman dai ka fara ce mata ka amince ɗin, daga baya ko me kenan sai ayi shi" Sai yanzu ya samu kwanciyar hankali, koma minene zai ce ya amince ne kawai ko domin ƙiyayyar mom ga Suhan ɗin ta ragu, sannan ko domin kada wata fitinar ta kuma ɓullowa. Gyaɗa kai ya shiga yi, yana mai cewa "To Dady ba damuwa, insha Allahu hakan za'ayi, zan same ta da maganar dady, nagode Allah ya ƙara girma" Ba damuwa Son, insha Allahu zan tsaya tsayin daka akan ganin komai ya yuwu, tinda ka amince zuwa gobe za'a fara gyaran sashen naka, sai ka bada plan ɗin yanda kake so a tsara maka, kuma maganar kaya duk ni ne zan zuba maku da kaina, babu Abunda nake buƙata daga gare ku, saidai cen tsakanin ka da yarinyar, ina nufin lefe da abun da ba'a rasa ba, sadaki kuma babanka yace shine zai bada" Cikin farin ciki ya kuma shiga gyaɗa kai, ko ba komai mahaifin nashi, na ƙoƙari wajen ganin ya faranta mashi rai, yana sonshi yana ƙaunar shi, haka kuma yana girmama duk wani ra'ayi nashi da bai saɓa ma shari'a ba. Shiru ne ya biyo baya, sai kuma suka shiga tattauna harkokin kasuwancin su, anan ne yake shaida mashi cewa zaiyi tafiya ma zuwa New York ɗin zuwa gobe idan Allah ya kaimu, saboda zasu tattauna da wasu kanfanoni akan zuba hannun jari. Al'ameen ɗinne ya kuma gyara zama. "Dad maganar Nihal, na kira shi mijin nata jiya, to mun tattauna dai......." Ya kashe duk yanda sukayi da Nureen ɗin ya faɗa ma Dad ɗin. "Na sani Al'ameen, ban yi maganar bane saboda ina so ne su gane kuskuren su, kuma na gansu da duk hukuncin daka yanke kuma ina mai goyon bayan ka, zuwa anjima ma zan shiga in jaddada masu hukuncin naka, dole ne su gane kuskure nasu, Amman tinda kai ka riga ka kira shi kunyi magana shikenan hakan yayi, kada ka kuma tanka masu akan maganar har sai lokacin da ka lura ita ɗin ta cenza ta gyara, saboda don tana ɗiyar mu, ba shi ke nuna cewa zamu goyon ma rashin gaskiya baya ba" Jinjina kai Al'ameen ɗin ya shiga yi, yana mai faɗin "Haka ne Dad, bari inje in samu Mom ɗin, insha Allahu duk yanda mukayi da ita, zanzo in sanar maka" Da kallo ya bishi yana ta faman murmushi har ya fice. Samun natsuwar yaron nashi shine auren, insha Allahu duk yanda zaiyi yaga anyi auren zai bi, domin ganin yaron nashi ya samu natsuwa... ~Our-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'a Idan Ya yi Buda Baki a Gidan Mutane* أَفْطَرَ عِنْدَكُمْ الصَّائِمُونَ وَأَكَلَ طَعَامَكُمُ اْلأَبْرَارِ، وَصَلَّتْ عَلَيْكُمُ الْمَلاَئِكَةِ. *Aftara 'indakumus-sa-imoon, wa-akala ta'amakumul-abrar, wasallat 'alaykumul-mala-ikah.* *Allah Ya sa masu azumi su yi buda baki a wajenku, kuma Allah ya s anagartattun bayi su ci abincinku, kuma Allah Ya sa Mala'iku su yi muku addu'a.* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~57~* *Godiya mai ɗinbin yawa zuwa gareki ƙawata _Salamatu_ haƙiƙa kin nuna mani ƙauna, kin nuna kuna tare dani da kuma ~SuhAmeen~ godiya marar adadi, wannan Page ɗin naki ne, kyauta halak malak, na gode da wannan ƙauna da kike nuna mani, Allah ya barmu tare.* *Jinjina gareki ƴar uwa ta, Jiddon Dady, kina ƙara ƙarfafa mani guiwa da kuma shawarwarn ki, haƙiƙa nafi kowa dace da samun ƴar uwa kuma ƙanwa a duk faɗin duniyar nan, ba zan iya misalta ƙauna ta gareki ba, har kullum kina cikin zuciyar tilon ƴar uwan ki Oum-Deedat. Fatan zaki dawwama cikin aminci, da ƙauna daga angon ki, mai gidan ki Yusuf Tijjani Baffa (Dady) gaisuwa zuwa gareku baki ɗaya* _@One lurv marubuciyar ( *Ƙareenaty* ) da Fatima batula marubuciyar ( *Ni da Malama ta*) gaisuwa zuwa gareku. in kuka ɗauke Umar babu wanda ke nuna ma littafi na ƙauna, duk cikin forum ɗinmu kaman ku, ina yinku irin over ɗinnan, a cigaba da zazzaga mana zallah fasaha._ ~Hehehe @Batula ina so ki sani, yanzu ne ma na fara karanta *Ni da malama ta* yanda kike zazzaga fasaha ai ba zan taɓa son in dena karantawa ba, kada a shani masilla~ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° A falo ya tada ta zaune, Abie na kwance gefen ta, kanshi bisa dukkanin cinyoyin ta. Da sallama ya ƙarasa ɗauke a bakin shi, zuwa kujerar da take kusa da su. Zama yayi, yana mai gaida ta, da dukkanin kulawa da fara'a sosai ɗauke a fuskar ta, ta shiga amsawa. Gama wayar ta kenan da Hajiya Sa'a, ta tabbatar mata da an kammala komai, duk da sharaɗin da boka ya gindaya masu mai matuƙar ƙarfi, cewa an kammala komai da zaran an ɗaura auren zaiji duk duniya ba wadda ya tsana irin matar tashi, to saidai fa, muddin suka yadda ya santa a ɗiya mace, lokacin ne fa komai zai warware. Son da yake mata ma zai daɗa linka na da. A haka suka amince, masalan Hajiya Kubran da idon ta ya riga ya makance, ƙiyayyar da tsanar ce kawai ke cin ta, ita a ganin ta, tinda kusa da ita zasu zauna, zata yi duk yanda zata yi ta hana shi tarawa da Suhan ɗin, masalan ma gashi ance zai tsane ta, dama dalilin ta kenan na cewa a zauna gidan kenan, saboda ta sanya ma duk wani motsi nasu idanu, ita fa ba zata taɓa sake jiki tana ji tana kallo ta haɗa iri da waɗannan baƙaƙen talakawan ba. "Son an dawo lafiya? Ya gajiya?" Ta faɗa, tana mai kallon yaron nata cike da annashuwa, gani takeyi kaman burin ta ya gama kammala, ita har ta ƙagara ma a ɗaura auren, ko zai fara tsanar tata, kuma lokaci ne yanzu da zata sauya salo, zata nuna ma kowa ta amince da auren, kuma tana ƙaunar Suhan ɗin 100%. Yayi mamakin sakewar ta gareshi, dukda haka dai sai ya basar, yana mai cewa "yes Mom, gajiya akwai ta" Ya faɗa yana ɗan zamewa bisa kujerar. "Ko zaka ci abinci ne? Sai Nihal ta kawo maka" "wa yayi girkin?" ya faɗa yana mai ɗagowa ya dubeta. "Eh to wai Nihal tace ita ce tayi, ai kai ne kace ta dinga yi" "Uhmm" kawai yace, domin yasan ƙarya Nihal ɗin takeyi, ba zata iya cika sharuɗɗan shi ba. "No Mom, ta bar shi kawai, kinsan ba iyawa tayi ba, zan samu abun da zan ci a ɗaki na" Ya faɗa yana mai ɗan gyara zama ya fuskance ta. Ɗan ɗaure fuska tayi, domin Nihal ɗin ta faɗa mata komai, to ita ma ɗin duk da bata ji daɗin hukuncin Al'ameen ɗin ba, zata so ace Nihal ɗin ta koma gidan mijin nata, kaman ita Hajiya Kubra bai kyautu ace an koro mata ɗiyar tata gida ba, Amman yanzu ba ta Nihal ɗin takeyi ba, so take ta gama da matsalar Al'ameen ɗin tukunna. "Kai malam sai ka ɗaga man Mom ko? Kazo ka wani hahhaye ta" Ya faɗa a hankali, cikin salon maganar shi, mai cike da sanyi. "A'a ƙyale mani auta na, yaushe rabon da in ganshi?" "ita Afnan ɗin kin bada ta ne? Da kike kiran shi auta, wannan gotai gotai ɗin dashi, kalle shi fa, ya kusa tsawo na" "Mom ƙyale shi, na dawo fa kenan ai, so yake ya takura ni" Abie ɗin ya faɗa cike da shagwaɓa. Murmushi ya saki, yayin da shi kuma gogan ya ɗan lumshe ido yana mai kauda kai gefe. Saida ya tattaro dukkan natsuwa da dakiya ya ɗora ma kanshi sannan ya fara cewa "Mom daga wajen Dad nake, munyi magana dashi sosai, ya faɗa man dukkanin sharuɗɗan ki, insha Allahu na amince, kuma zaki sameni mai yi maki biyayya a koda yaushe" "Dama zaka ce haka mana, Soyayya ta rufe maka ido, to ai ni ba zan zuba maka idanu ba haka kaman baka da gata, ka rasa wadda zaka aura sai takalan masu aiki na" ta faɗa cikin zuciyar ta, a zahiri kuma murmushi tayi sannan tace. "Ba damuwa Son, feel free, nice na amince maka da kaina, da fatan dokokn basuyi maka tsari ba, bana so ne kayi nisa kusa dani, Shiyasa nace a taimaka a zauna kusa dani ɗin, na gane cewa yarinyar tana da natsuwa kuma kan sonta, ni kuma kasan ina ƙaunar dukkanin abubuwan da kake so" Da matuƙar mamaki yake kallon ta. Anya kuwa mom ce? What bring this suddent change? Shima ɗan zura mata idanu yayi, Un blievable, ace kaman mom ce yau ta tausasa murya tana mashi magana haka akan auren nashi, bai ƙara shan mamaki ba, saida tace mashi "ya inlaw ɗin tawa? Fatan dai tana lafiya?" "Lafiya Lau Mom, tana gaida ku" Ya faɗa a hankali cen Ƙasan maƙoshin, na farko kenan a tarihn rayuwar shi, tin tasowar shi daya ji tana tambayar lafiyar Suhan ɗin. Abie ne da yake kwance, Baisan wainar da ake toyawa ba, tashi zaune yayi yana mai cewa "Mom yaya yaƙi faɗa man wacece groom ɗin tashi har yanzu fa" Kallon ta ta maida kan Abie, "Kada ka damu Son ai ka santa ma, Suhan ce ta gidan nan" "what? Mom Suhan wadda na sani? Ita yaya zai aura?" Ya faɗa yana mai ɗan zaro idanu cikin kaɗuwa. Hankalin shi Al'ameen ɗin ya maida kan Abie, kada dai ace shima baya goyon bayan abun kaman saudat da Nihal. "Yes for Sure Son, kaga tuwon mu manmu" Ga mamakin Al'ameen wani irin ƙayataccen murmushi ya saki, yana mai tashi ya koma bisa kujerar da Ya Ameen ɗin yake kai, rungumo shi yayi yana mai cewa "Congrat Yaya, Allah ya sanya alkhairi, ai Suhan tayi, tana da kirki da natsuwa, ta cencenci a aure ta" Su duka da kallon mamaki suke binshi, daga mom ɗin har Al'ameen ɗin. Shima murmushi Al'ameen ɗin ya saki jin abinda yace, sai kuma ya maida kallon shi kan Hajiya Kubran da take hakimce, fuskar ba yabo ba fallasa. Miƙewa yayi yana mai cewa "Thanks Bro, bari in wuce daƙi, ina so ne in huta, gobe insha Allahu da wuri nake so in wuce, alabasshi kai ka tafi daga baya" "Ina zuwa ne Son?" Mom ɗin ta faɗa, har yanzu fuskar ta ba yabo ba fallasa. "Mom New York nake so naje zuwa gobe akwai ayyukan da suka taso mana ne acen, kuma dole sai nine zan yi su, maganar zuba hannun jari ne a cen kamfanonin nasu" "OK to babu damuwa, inda ka dawo sai muyi maganar yanda abubuwa zasu kasance Son, kada ka damu ni na amince Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa, sannan nima ina so ne muyi maganar ƙara share ɗin da zanyi a nnpc tower, ko zuwa bayan hidimar ne" "OK Mom see u later" Ya faɗa yana mai wucewa zuwa sashen nashi, bai san me ke damun mom ɗin tashi ba, da take ta ɗaukar maƙudan kuɗaɗen ta tana zuba hannun jari a kamfanin man fetur da iskar gas ɗin ba, duk dai da cewa lafiya lau tana ganin profit nata, saidai fa shi ba wai ya natsu bane sosai da har kar, kasancewr haka take abun wani lokaci ba lauyoyi, duk da dai shi yana rubuta komai da sanya hannun waɗanda kuɗin nata ke shiga hannun su. yayin da Abie ma ya miƙe ya nufi ɗakin shi, yana mai faɗin "Mom bari inje in watsa ruwa nima" Da kallo ta bisu dukan su, har suka ɓace ma ganin ta. Zuciyar ta na ayyana mata abubuwa iri iri, watau yanzu aka fara wasan. ******** Umma ce zaune bakin gadon nata. Tunani ne kala kala cikin ran nata, saidai ita tana ganin wannan ne kawai abun da ya dace tayi, a tsawon shekarn da ta ɗauka, daidai da rana ɗaya bata taɓa tunanin komawa mahaifar tata ba, saidai bata da zaɓi ne, wannan karon ta shirya tsab, koda kuwa cewa daidai yake da rasa rayuwar ta, ba zata taɓa bari yarinyar tata tayi zaman ƙunci a gidan miji ba, ta dalilin rashin sanin asalin ta. Saidai ta ina zata fara? Ita ɗin da kowa yake tunanin ta mutu, ita ɗin da kowa yake ma kallon maragayiya tsawon shekaru masu yawa. "Hmm" ta faɗa tana mai nisa wa, sannan ta zakuɗa zaman nata, tana mai cewa "komai yazo ƙarshe, Mamana lokaci yayi da kema zaki dara, cikin dangin ki da ƴan uwan ki" Wayar ta dake gefe ajiye ce ta ɗauki tsuwwa, alamun kira ya shigo. Ganin baƙuwar number sai baisa tayi saurin ɗagawa ba, har ta katse, kiran ya kuma shigowa. A hankali ta ɗaga, cikin manyance da dattako take amsa sallamar da akayi mata. Muryar mace ce, cike take da annashuwa da fara'a. A haka suka shiga gaisawa, saidai tin kafin ma Umman ta tambaya matar tayi saurin cewa "nasan baki gane ni ba, nice Hajiya Khaltum, Ammin Salim, malamin su Suhan" Fara'a umman ta faɗaɗa, kunya na mai kama ta "Allah sarki Ammi, ya gida ya kwana biyu, nima ina ta so ince Suhan ta bani number ɗin in kira wallahi na shafa'a, da fatan dai kowa na lafiya?" "Lafiya Lau Umma, dama cewa nayi bari in kira mu gaisa, tin bayan da abun nan ya faru bamu sake jin juna ba, Salim ne ke sanar dani an sanya ranar Suhan ɗin, shine nace bari in sanar dake, Suhan har yanzu ɗiya ta ce, saboda haka nake so ki amince ko zuwa sati guda ne kafin bikin in aiko da mai yi mata gyaran jiki irin namu na nan barno, sannan don Allah ki sanya ta, ta lissafo mani dukkanin abubuwan da take buƙata, da suka danganci kayan kitchen, insha Allahu duk na ɗauki nauyi, bana so kice a'a don Allah, alkhairi ne nayi niyyar yi, ko da ace ba Salim zata aura ba, ai shima namiji ne, nasan in nace tayo da kaina ba zata yo ba, kuma nasan idan na sanya Salim yayi mata maganar ba yi zaiyi ba, yace Kunyar yi mata magana yake ji, Shiyasa nace bari in biyo ta ɓangaren ki Umma, don Allah ki taimaka" Mamaki ma ya hana Umma magana, iko sai Allah, har cikin zuciyar ta, tana jin ciwon rashin suruka da Suhan tayi irin Ammi ɗin, lallai wannan ƙauna daga Allah ne, babu Abunda zata iya cewa saidai godiya, da fatan Allah ya ƙara yalwata masu Arziƙi su. Ta ɗaure ta da dukkanin jijiyoyin jikin ta, don haka ne ta shiga zuba mata godiya, "Ah haba ba wani abun godiya a ciki, ai har yanzu Suhan ɗiya ta ce" Ammin ta faɗa har yanzu cikin fara'a take. Kaman Umman tace mata zasu shigo garin nasu, sai kuma ta share, tinda tafiyar ba tata bace ita ɗaya ai bai kamata ta ɓata masu lokaci ba, alabasshi bayan biki zata shirya da kanta zuwa wajen Ammi ɗin, takanas domin godiya da ƙauna da ɗawainiya, ko ba komai duk wanda yaso ɗanka ai kai yake so. Haka sukayi sallama cikin mutun ta juna, kowa na girmama kowa, lallai Ammi ɗin ta cika mace, har ma tafi, duk wadda ya samu Ammi a matsayin Uwa, ko kuma a suruka, ya cencenci jinjina, Ammi ɗin irin matan nan ce da za'a iya cewa basu ɗauki duniya da zafi ba, kuɗi ilimi duk basu isa su sanya ta jin kanta a matsayin ita ɗin wata bace. Number ta Umman ta kira, bayan mun gaisa ne take sanar dani yan da sukayi da Ammi. Nima kunya ma sai ta kama ni, rabona da Ammin tin ranar rabuwar mu da Sir Salim ɗin. Allah sarki Ammi, kenan ita bata yi fushi ba? Kenan ta fahimce mu? Gyaɗa kai kawai na shiga yi, ina yi ma Umman godiya, sannan ta gargaɗe ni da in lissafa kaɗan, domin anan Alhaji ne yace zaiyi komai, kada yaga kaman mun raina abunda yayi mana ne ɗin. Taso tayi mani maganar zama na gidan tare dasu sai ta share, koma miye Hajiya Kubran ke shiryawa, da izinin Allah zai koma alkhairi ne, in ma domin ta ƙuntata mani ne, Allah yana kallon zukatan kowa, bama nufin su da sharri, insha Allahu ba zasu iya cutar damu ɗin ba. Kiran na Umma na katse wa kiran Ya Ameen ya shigo. Bansan na saki murmushi ba, har saida ta kusa katse wa sannan na ɗaga, wai ni irin jan ajin nan na mata. Duk da yanzu na yarda ma kaina cewa ashe tsundum na faɗa soyayyar Ya Ameen ɗin, ashe da cen wauta nakeyi ba soyayya nakeyi da Sir Salim ba? Wasan yara ne nake mashi. Ashe haka soyayyar take? Akai akai ni kaɗai na kan saki murmushi, wani lokacin har ƴar dariya nakeyi, idan na dinga tunano lokutta mabanbanta, lokacin da na suma a lambu ya ɗauko ni, da lokacin da naji wani abu na bina a bayan gida na faɗa mashi, da lokacin da ya shigo ɗakin ya tadda ni ina neman warin ɗan kunne na. Da lokacin da Umma bata lafiya naje na ruƙunƙume shi. To dama wai cen ina sonshi ne? Ko kuma yanzu ne na fara, yanda nake ji a kanshi zuwa yanzu kaman na shekaru ina sonshi. Na saki jiki dashi, dan dai ina jin kunyar shi yanzu sosai, wasu kalmomn da yake faɗa lokutta da dama, sai inga kaman ba shine ba, sai inga kaman ba daga bakin shi maganar ke futowa ba. Sallama yakeyi, yayin da ni kuma na faɗa shauƙin tunanin soyayya. "My wife kina ji na kuwa?" Ya faɗa a hankali. Kaman ince ka kira ni video yaya, sai kuma na share, ya zuwa yanzu ba abunda nake marari da muradin gani kaman Fuskar Yayan nawa, kuma mai shirin zama miji na nan gaba, zuwa lokaci ƙanƙani. "Eh yaya, ina jinka, ina yini ya gida?" "Lafiya lau ya karatu my sweet?" ya faɗa, yana mai mirginawa ya kuma matse filon dake hannun shi rungume. "Alhamdulillah, gashi zamu fara exam, nan da sati mai zamu iya gamawa" na faɗa nima a hankali, cikin muryar da budurwa kan yi ga saurayin ta, ni kaina har mamakin kaina nakeyi, yanda na cenza lokaci guda, nice wai har nake sirara murya ta, ga ya Ameen ɗin, harda kashe murya duk domin yaji daɗi, lallai ma ni Suhan. "Wow my hrt, Allah ya bada Sa'a, kiyi karatu sosai kinji dear" "OK dear insha Allah" Ɗan murmushi ya saki, jin har ta fara cenza mashi suna, hmm Suhan ma kenan, nan gaba yana da tabbacin sai ta rasa sunan ma da zata kira shi dashi, domin duk ta riga ta faɗe su a gareshi. "Albishir na kira ki in maki my Janam" Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "To Yaya ina sauraren ka" "Menene tukuici na?". Ya faɗa kai tsaye, cikin sake sakin murmushi. "Me kake so?" "a'a dear kada ki ce haka, ba zaki iya bani ba" "ka wuce komai a wuri na yaya" na faɗa ina mai kallon zoben da shine ya saka mani da kanshi a ɗan yasan nawa. "OK shikenan tinda kince haka, I want deep Kiss" Ɗan zaro ido nayi, ina mai ɗauke wayar daga kunne na. Ƙit naji ya katse, sai gashi kuma ya sake kira ta video. Duk da ina son ganin nashi, Amman Kunyar shi ta baibaye ni, haka na ɗaga a hankali ina mai sanya hannu na na rufe fuskar tawa. " Look at ne dear, ke kika ce fa zaki iya, oya ina sauraren ki kiyi mani" Ya faɗa yana mai lumshe idon shi da suke ɗauke da Zara zaran gashin ido. Maimakon Kiss ɗin da yace in mashi, sai ma ƙura ma fuskar tashi idanu da nayi. Lips ɗinnan nashi pink mai duhu duhu kaman maroon, sai walƙiya suke kaman ya shafa masu lip balm, gashi bakin nashi ɗan tsut dashi. Wanda kwantaccen gashin baki ya zagaye, sai ya ƙara ma fuskar kyau. Masha Allah, gaskiya Ya Ameen ƙarshe ne, komai nashi daban yake, jibi don Allah kaman shi ya halitta kanshi, ina da tabbacin cewa duk gidan shine ya ɗebo kyaun Alhaji Mustapha da Hajiya Kubra. Bai ce komai ba, har yanzu kuma idanun nashi a lumshe suke, sai ɗan murmushin gefen baki da yake saki akai akai, ya sani sarai kallon shi nake, Amman da zai buɗe idon, sai fa in basar ko? Harma ina iya cewa meye abun kallo a ciki ko? A hankali ya buɗe idanun nashi, aiko ta kama ni, idanu na ƙur akan fuskar tashi. Maimakon in janye idanun nawa, sai na gyara zama. Bansan lokacin da nace "yaya u are so much handsome" "like u my beautefull wife" Ya faɗa shima yana mai wani ƙanƙan ce idanu. "Hmm more than me Yaya" "Ban son wayau, ina jiran alƙawari na kafin na faɗa" Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "OK dear later" "promise?" "Yeah promise" "ok" ya faɗa yana mai tashi zaune, ya tattara dukkan natsuwar shi a kaina. "Mom fa ta yarda da auren mu" bansan lokacin da na ɗago daga jinginn da nake ba, ina mai zaro idanu. "wow are u sure Yaya?" "Yep dear, don haka sai ki shirya zama surukar Mom, da na dawo daga tafiya zanzo mu tsara yadda komai zai kasance" Wani murmushi na saki, ina mai sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali. Shima ya kula da yanda nake murna, Allah sarki Suhan, ashe dama tana sonshi, tsoron Mom ne ya cika mata zuciya. Mamaki nakeyi yanda akayi ta amince lokaci guda, ko me ya faru kuma? Gashi Umma bata sanar dani komi dake faruwa a gidan, iyaka dai kawai fira ce tsakanin mu, da Abunda ya dangance mu. "To Allah ya kaimu yaya" na faɗa nima ina mai sauke kai ƙasa, sai yanzu Kunyar murnar da nayi ta shiga kama ni, kaddai ace yayi tunanin dama cen ina sonshi. Aiko abun da nake gudu ne ya faru. "Yaushe kika fara sona har haka?" Tambayar da ya jefa mani kenan. Saurin kauda kaina nayi gefe, ina mai ɗan firgita hka, yanda maganar ta dakar mani zuciya. "kwana uku da suka wuce" na faɗa ina mai ƙara sauke kai ƙasa cikin kunya. Sai kuma na kife kan wayar a cinya ta. "Banson ƙarya, wannan soyayyar tafi shekaru" na jiyo shi ta cikin earpiece yana faɗa, duk da bana kallon shi Murmushi nake saki, lallai soyayya daban ce, masalan da ya Ameen ɗin. Ba zan kuma cutar kaina ba, kaman yanda Raihana ta bani shawara, ni ɗin wadda Allah ya zaɓa ya mallaka mani zuciyar Ya Ameen ce cikin mata fiye da dubu, ba buƙatar in tsaya ɓata lokaci, ya Ameen ba irin mazan da ake sake dasu bane, Soyayya nake fatan mu shimfiɗa fiye da tunanin kowa, wani abun ma sai munyi aure, domin yanzu haka na shiga wani group na WhatsApp na matan aure ne zalla, ni kaina basu san bana da aure ba, a matar aure na shiga, suna koyar da abubuwa iri iri, ina ta ɗaukar darasi kuma, da burin dukkanin abubuwan da ake faɗa zan jaraba su akan Ya Ameen ɗin, domin na lura shi salon tashi soyayyar ta miskilai daban take da kowacce, gashi komai zaiyi cikin jan aji da ya ga yake yin shi, na daga abubuwan dake ƙara ma mata sonshi kenan, bayan kyawu da kuɗi da nasaba da Allah ya mallaka mashi. Haka muka cigaba da waya tsawon lokaci, bana so ko network yayi rawa, shima ta ɓangaren shi, zamewa yayi yana mai kwantawa, rigingine, ya tada kanshi da hannun shi guda ɗaya, yana ta zuba mani kalamai, wasu ma ban taɓa tunanin zai iya furta mani su ba, masalan ma yau da yaga nafi sakin jiki dashi a kn kowacce rana, yana da tabbacin cewa ya dasa soyayyar shi mai girma a cikin zuciyar tawa, to nima yanzu bana da haufin son da yake yi mani ɗin, idan nayi la'akari da yanda kowa ke faɗar yanda nake da kyau da natsuwa, na cencenci a soni ɗin fiye da kima. A haka har Bilal yayi sallama ɗakin. Kai tsaye bisa gadon da Ya Ameen ɗin yake kwance yayi ma tsinke, ɗan duka ya kai mashi ta baya yana faɗin "to fafarawo baban soyayya" Ɗan juyowa yayi ya kalle shi, shi fa bai ma ko ji shigowar tashi ba. Sallama yayi mani yana mai katse wayar cikin dan tsoki, yasan yazo kenan zai fara takura mashi, kaman shi wani ne yaje ya takura mashi lokacin soyayyar tashi da Ummin. Duk da bilal ɗin ya kula yaji haushi katse mashi firar tashi da yayi, saidai ya sani ba wai zai tanka mashi bane, to mutumen da magana ke ma wahala, shi yana ma mamakin yanda suke kwashe tsawon awanni suna magana da Suhanan a wayar, ko me yake faɗa mata? Oho wa ma ya sani ko ita ce keyi mashi firar? Domin dai shi yasan abokin nashi bai kware ba ta wannan fannin. Haka ya samu daƙyar suka shiga aikin da ya kawo shi, so yake ya bashi komai in details, ta yadda ba zai kuma neman shi ba, koda ya isa cen ɗin. Yana kula dashi kuma wani lokacin sai yayi ɗan kasaƙe, sai kuma ya saki murmushi yana mai sosai gefen girar nashi da biron dake hannun shi. Kaman wanda ya zauce a soyayya. ********** Haka rayuwa ta cigaba da juyawa, daƙiƙu na shuɗewa, awanni da kuma kwanaki, cikin kwana uku ne muka fara Jarabawa, haka kuma cikin kwana ukun ne ya kasance kwanan ya Ameen ɗin biyu ke nan cur da tafiya, saidai ya lura abun mai yawa ne, zai iya ma ɗaukar shi kusan sati ba tare da ya juyo ba. Shiyasa yanzu ko waya bamu cika yi ba, wani lokacin ma sai rana ta ƙare bamuyi waya ba, tinda awannin daren mu, sune awannin ranar su su acen A haka ne kuma ranar tafiyar su Umman tazo. Tafiya ce da aka shirya ta cikin sirri, su huɗu ne zasuyi tafiyar, sai driver da yake cikon na biyar. Tin a daren ranar Umman ta sanar ma da Dad ɗin garin da zasu je, nan yake tambayar ta zadai ta iya gane wurin ko? A hankali ta shiga jinjina mashi kai, zuciyar ta cike da tarabbabi da wasi wasi. Hajiya Kubra bata wani damu ba, duk da ba wai tasan da tafiyar bane, hasali ma tana cen hulɗoɗin ta, tin dai da su Hajiya Sa'ar suka tabbatar mata cewa komai zai tafi yanda aka tsara. Koda taga ana gyaran sashen Ya Ameen ɗin, bata damu ba, bata kuma tambayi Alhajin ba, kawai dai tasan cewa kurkuku ne ake gina ma Suhan ɗin ba tare da sanin kowa ba in banda ita. Ba'a rushe tsarin gidan ba, saboda yace a bar shi haka, shima ai ba zaman shi ne dindindin a gidan ba, kawai zai biyayya ne ya zauna, kaman yanda Mom ɗin ta buƙata, shima na wani lokaci ne. ******* Tafiya miƙaƙƙa. Alhaji Auwalu, Alhaji Mustapha, Hajiya Zainab da Umman. Firar su suke gwanin ban shawa'awa, Amman banda Umman, da kaf hankalin ta ya riga ya tafi a kan yadda zata je ta tadda wurin. Wace irin tarba zasu samu? A matsayin ta na matatta a wajen su? Salla kawai suka tsaya sukayi, dayake lafiyayyar mota ce, kuma ta samu tuƙin driver ɗin Alhajin sai gasu dan danan sun isa zuwa jihar ta Adamawa. Da kallo Umman ke bin garin, an samu ci gaba iri daban daban, komai ya cenza, saidai hanyar zuwa gidan nasu har yanzu tana nan yanda take, saidai ƙara faɗaɗa ta ne da akayi da titi mai matuƙar kyau da ban sha'awa. Sun wuce ya kai gate uku, ko wanne gate sai na tsaida su, lura da irin motar, da kuma manyan mutanen da ke cikin ta, ya sanya ko binciken su sosai ba'a tsayawa yi, kasancewr an san baƙi ne daga wani garin. Gate na huɗu, shine ya sada su da ainahin harabar masarautr. Babbar masarauta ce, mai daɗaɗɗen tarihi. Inda aka tanada musamman domin ajiye mitoci, nan driver ɗin yayi parking, kowa mamaki ya cika mashi zuciya, saidai babu wanda ya tanka cikin su. Haka Umman ta wuce gaba suna biye da ita, kowa kallon mamaki takeyi. Babbar masarauta ce, mai haɗe da gini irin na da, saidai an ƙawata shi da zamani, ma'ana an zamanantar dashi, ta hanyar abubuwan ƙawa irin na gine gine. Fadawa ne birjik ke kai da komo a cikin gidan, suna hango shigowar motar wasu daga cikin su duka rugo zuwa inda su Alhaji Mustaphan suke. *"Hayya dai Hayya dai, ranku ya daɗe, baƙin sarki, barkan ku da zuwa masarautar mai martaba sarki Muhammadu Bello Barkindo lamiɗo, muna maku maraba da zuwa a madadin sarki"* Wani bafade da yake ta muzurai, hannun shi riƙe da wata zabgegiyar Bulalar dorina, irin ta bugun dawakai. Wani tanƙamemen falo ne aka shigar dasu, sarkin zagi ne yazo ya kwashi gaisuwa, duk da dai ba wai an shaida su bane, Amman yanda aka gansu cike da kwarjini da kamala, ya sanya aka san baƙin sarki ne, gashi kuma sarki baya so ana banzatar mashi da baƙo koda baya nan. "Hutawar ku lafiya ranku shi daɗe, yanzun nan za'a nemo maku iso wajen sarki mai ɗinbin daraja da alfarma, an gaida baƙin sarki da suke tafe da tarin albarka da alkhairi" Su dai sai faman murmushi suke yi, har yanzu dai suna tare da ɗinbin mamaki, gashi kuma Umman ta ƙi cewa komai. Nan da nan aka ciccika masu gaban su da kayan itatuwa. Falo ne mai matuƙar girma da kyawu, ba kowa cikin shi, sai kilisai da aka shisshinfiɗa, da kuma tumtum irin na tada hannuwa dashi, sai mafitai masu kyau da ban sha'awa da aka ajiye gefe gefen falon, duk da akwai yalwar central Ac dake ta faman yin aiki. Mamakin su ɗaya, meye haɗin Umman Suhan ɗin da masarautar? Gashi kuma ga dukkan alamu ba wanda ya ko gane ta cikin fadawan, da ma ma'aikatan bayin gidan da aka aiko suka ajiye abubuwan ci ɗin. Basu fi minti sha biyar ba, sai ga wannan bafaden ya dawo cikin sauri, yana ta faman saɓa babbar riga. "Barkanku da hutawa baƙin sarki, sarki ya ce a yi maki iso zuwa fadar tashi yana mai fitowa ba da jimawa ba" A hankali suka miƙe, suna mai bin bayan shi, ta wani ɗan cirridor suka bi, sai gasu sun bayyana a wani tafkeken fili da babu Abunda ke cikin shi banda rairayi mai kyau, da kuma itatuwa tsanwaye shar shar dasu. Fada ce babba, wadda ta amsa sunan ta fada, kai lallai sarauta daban ce, masalan ma yadda wannan masarautar da kai da ga ganin ta, kasan ana shimfiɗa mulki mai cike da kyawu ta tsafta. Komai na fadar kalar jaaa ne sosai mai cizawa, kujeru ne irin na sarauta masu ado da ruwan gold suka zagaye faɗar dashi, anyi ma faɗar ado kala kala, har ma kusan muce sunyi yawa, duk da fadar ta matuƙar ƙayatar da su dukan su. Kai daga ganin faɗar ka tabbatar da an narkar da dukiya wurin. Babban sarki ne, da dukkanin faɗin nahiyar tamu ake ji dashi sosai. Su dai sai bin Umma da kallo suke, wadda ta sadda kanta ƙasa, ba zaka ma iya tantance halin da take ciki ba. Zaman su keda wuya, suka jiyo tahowar sarki, tare da masu yi mashi kirayi, da kuma gyara mashi alkyabba da hanya. *"Gaba salamun baya salamun sarki ɗan sarki, ƙanen sarki jikan sarki, iyayen sarakunan mu masu daraja na nan gaba, an gaida ɗan gidan mai martaba Barkindo lamiɗo, sarari, gyara kintsi, hadari sa gaban ka inda kake so, ɗan toron giwa, kai sarki jikan sarki, kakan ka sarki, an gaishe ka, gyara kintsi, gaba dai gaba dai"* Su Dad suna gani haka suka miƙe tsaye cikin girmamawa, komi kuɗin ka, komi matsayin ka, sarauta daban ce, sarki daban ne, masalan ma sarki kaman wannan da yake da ɗinbin daraja da kuma wuƙar yanka. Sai bayan da suka gyara mashi zama ne, ya zauna sosai, cike da izzar mulki da taƙama. Sannan suka matsa cike da girmamawa, suna mai naɗe hannayen babbar rigar su, suka koma gefe suka zauna. Suna mai duƙawa sosai suka shiga kai gaisuwa Yayin da ya daidaita zaman shi bisa kujerar shi yake kallon su Alhaji Mustapha Dambulan ɗin. Murmushi irin na sarakai ya saki, lokacin da suke miƙa mashi gaisuwa, cike da girmamwawa, sarkin zagi ne ke amsawa "Sarkii Yaaaaa Amssaaa maku" kaman yanda yafi kowa halshe a faɗar, itama Hajiya Zainab gaisuwar ta kai har ƙasa, tana mai girmamawa ga sarkin. "An gaishe ku baƙin ariziƙi baƙin alkhairi, sarki ya amsa baƙuncin ku, maraba da zuwa babbar mmasarauta mai tarihi da ɗinbin daraja" Mai makon Umman ta zuƙunna ta kai gaisuwar itama, sai ta wuce kai tsaye zuwa inda sarkin yake zaune, ya zuƙunna tana mai sakin wani irin kuka. "Hattara dai Hajiya, Sarki baya ɗaukar wargi da wasa, Hattara ya ke wannan baƙuwa" Da mamaki mai martaba sarki Bello ke kallon ta, har yanzu bata ɗago fuskar ta ba, ta sanya hannuwan ta dukan su tana mai kamo dukkanin kafaɗun shi, take faɗin "BAFFAAA" sannan ta ɗago fuskar ta cike da hawaye wasu na korar wasu. Cikin kaɗuwa da furgici mai martaba ke kallon ta, sai kuma ya miƙe cike da mamaki da al'ajabi yake mai faɗin *MARYAMA???* _Waih Allah kuyi haƙuri da wannan, gaskiya typing akwai wahala._ Masu son suga auren Ya Ameen da Suhan su bini a hankali, komai ɗan a hankali ne ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'a Yayin Da Aka ga Tumu,(Hurai-Sabon Amfanin Gona* اَللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِي ثَمَرِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مَدِينَتِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي صَاعِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مُدِّنَا. *Allahumma barik lana fee thamarina, wabarik lana fee madeenatina, wabarik lana fee sa'ina wabarik lana fee muddina.* *Ya Allah! Ka albarka ce mu a cikin kayan gonarmu, ka albarkan ce mu a garinmu, Ka albarkance mu a kwanon awonmu, Ka albarkan ce mua mudun awonmu.* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~58~* *Masoyan Ya Ameen da Suhan masu azarɓaɓin suga auren Ya Ameen da Suhan, ina mai baku haƙuri, ku bi Oum-Deedat a sannu, bana so in saurin kammalawa ne, ba tare da saƙon da nake so in isar ya isa ba, kuyi haƙuri ku bini a sannu, shi aure fa ba daga sama ake yin shi ba, sai an bi wasu matakai, idan kuma kuna so in dunƙule maku komai ne a Page ɗaya, to shikenan ni kun ma sauƙaƙa mani, saidai ku sani fa, da zaku bi a sannu ɗin abun sai yafi ƙayatar daku fiye da tunanin ku, na barku lafiya, ku cigaba da yi mani addu'a Allah ya biya mana buƙatun mu na Alkhairi. Na gode Love u All my Fans especially Salamatu Auntyn Ya Ameen Suhan* _Naja'atu Bala bakori, kema naga gift ɗinki nagode Allah yabar ƙauna, Suhan da Ya Ameen suna matuƙar godiya, sunce suna yinki suna Over and Over. Allah ya bar ƙawa ce na amana_ *_Not Edited_* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° A hankali mai martaba ya koma ya zauna, yana mai haɗiyr miyau na tsabar mamaki. Tabbas gimbiya Maryama ce zuƙunne gaban nashi tana mai kuka riris. Da hannu ya yafito sarkin fada. Cike da girmamawa ya taso ya zube gaban mai martaba yana jinjina gareshi tare da mashi kirari. "A kira mani jakadiya" Abunda ya iya faɗa kenan, cikin muryar su irin ta sarakai masu ji da sarautar su. "An gama rana ya daɗe, ɗan sarki jikan sarki, gaishe ka sarki mai adalci" Abunda sarkin fada yake faɗa kenan, har ya miƙe ya kwasa da gudu, zuwa wata ƴar ƙaramar ƙofa da take cen gefe, wadda sai an duƙa ne ma za'a iya shigewa. Su dai su Dad da kallo kawai suke bin kowa dake fadar, ga Umma da take duƙe tana kuka duk da dai cewa yanzu ta rage sautin muryar tata. Duk da dogarawan dake tsaye ta bayan shi suna mashi fifita, ga sanyin Ac bai hana mai martaba tsiyayar da zufa ba, gani yake kaman almara. Shigowar jakadiya ce taja hankalin kowa dake fadar. Da saurin ta, ta isa gaban sarkin itama, tana mai zubewa ta kwashi gaisuwa, tare da yi mashi kirari na ban mamaki. "A shiga da su gimbiya Maryama cikin gida ta ƙofar baya, a kaisu ɗakin Fulani, sannan a haɗa ma baƙi abinci yanzun nan" Mai martaba ya faɗa ba tare da ko ya kalli jakadiyar ba, cikin isa. "An gama tanka hsi daɗe" Jakadiyar ta faɗa tana mai ƙara rissinawa ta kwashi gaisuwa. A hankali Umma da Hajiya zainab suka miƙe, wadda tsabar mamaki ya cika ta, to in ta tabbata Umma gimbiya ce a masarautar me ya ja mata zuwa gidan Hajiya Kubra tsawon shekaru tana aikin bauta da ƙasƙanci? Me yaja mata ɓoye ma ɗiyar ta ainahin asalin ta, muddin wannan asalin mai cike da girma da ɗauka ka shine nata? A haka suka duƙa ta ƙaramar ƙofar suka shige cikin gidan. Jakadiya wadda ta kasance babbar haɗimar sarki ce, hatta da matan sarki, idan zasu gana da sarki ita ce take masu iso, kuma ta basu lokaci. A hankali take tafiya tana waiwayen fuskar Umma, wadda ko cikin duhu ba zata taɓa mance ta ba. Babban gida ne da ya gaji da haɗuwa, bayi ne mata da maza ta ko ina, an ƙawata gidan sosai kaman ba gobe, duk inda suka ratsa, zuƙunnawa ake ana kwasar gaisuwa, saboda ansan duk wanda aka biyo dashi wannan hanyar, ba ƙaramin baƙo bane, ko ƴan gida. Wasu mata suka ci karo dasu su biyu suna tsaye suna zantawa, bayan sun bi su Umma da kallo ne, suka gaishe su, suna masu jinjina kai da taɓe baki. "Ke Haule, wannan fa kaman nasan fuskar nan" Cewar ɗaya daga cikin su, tana mai yafito gudar da hannu, wadda ta bisu da kallo. "Nima fa haka nake gani gaje, anya duk dai yanda akayi waɗannan sun haɗa jiɓi da masarautar nan" Ta maida mata da amsa, bayan ta sauke ajiyar zuciya, tana mai maido kallon ta gareta. "Uhmm koma dai miye maji ma gani, kin san fa gulma kawai nake jira, inje in fesa ma uwar gijiya ta, kinsan waccen jakadiyar da mugun baƙin hali take, yanzu ba zata bari muji komai ba, balle naga ɗakin Fulani suka dosa. Su Yi tafiya mai tsawo, sannan suka iso wani babban part, da ya jiƙu da kyau, saida suka ratsa falo biyu ne, sannan jakadiyar tace masu su zauna tana zuwa. Har ta juya ta tafi, sai kuma ta dawo ta zuƙunna gaban Umma. "Ranki shi daɗe, kada kice wani abu wallahi, sai naga kaman Sarauniya Maryama ta nan gidan ko?" ta faɗa tana mai saddar da kai ƙasa, cikin tarabbabi. "Eh nice Ramma" Abunda Umma ta faɗa kenan, har yanzu hawaye tsilla tsilla suna bin fuskar ta, tana sanya hannu tana sharewa, tin da suka fito daga fada take kallon gidan, kaman bata yi rayuwa ciki ba, kaman bata zama haske fitilar gidan ba, kaman ba anan aka haife ta ba. Cikin tsabar firgici jakadiya ta ɗago kai tana kallon Umma, sai kuma ta hau salati tana mai tafa hannuwa. "Oh ni rammanatu, Sarauniya Merama? Kece nan? Iko Sai Allah" ta faɗa cikin mamaki, tana mai miƙewa ta wuce zuwa wata ƴar ƙofa da sauri. Ita ko Hajiya Zainab da kallo take bin falon. Duka falunan da suka biyo ta ciki, wannan ya fisu kyau da haɗuwa, falo ne kaman ba na ginin sarauta ba, Sam babu wani abu na da dake falin, in ka ɗauke zanen bangon. Sai kuma kilisai da tuntuna da kumbuna da suke saƙo da saƙo na falon. Bayi ne suka dinga shigowa da ɗaiɗaya suna kwasar gaisuwa, duk da wasunsu basu san Umma ba, Amman ga kama nan irin ta ahalin gidan. Ai tini masarauta ta ɗauka ga sarauniya Merama nan ta dawo. An jima, cen sai ga jakadiya ta fito tana faɗin "Hutawar ku lafiya Sarauniya, Fulani tace a sanar daku tana mai isko ku yanzun nan" Da kai kawai Umma ta amsa mata, ita kuwa Hajiya zainab sai zare idanu takeyi, har yanzu ta gaza cewa komai, kallon Umma takeyi, kai Haba no wonder halin Umma sak irin na sarakai ne, Meyasa bata taɓa lura ba sai yanzu? Sarauniya Merama? Me ya haɗa ta da sarautar ta har ake ta faɗa mata wannan suna? Fitowar Fulani ne, ya maida hankalin su gabaki ɗaya kanta, snaye take da wani ɗan yen leshi, ta ɗora alkyabba sama sai walwali takeyi. Bayan ta amintattun bayin ta ne, suna mai gyara mata zaman alkyabbar haɗi da yi mata kirari. Kujerar da ke fuskantar su Umman ta zauna. Fuskar ta cike take da mamaki. Duk abun nan fuskar Umma na duƙe, har yanzu ta gaza gazgata zancen da jakadiyar tazo mata dashi, duk da Tasan cewa ba zata yi mata ƙarya ba. "Gimbiya Merama!" Ta faɗa a hankali, cike da isa. Yau ne Hajiya Zainab taga tsabar isa, ashe da cen Hajiya Kubra ba komai take yi ba. A hankali Umma ta ɗaga fuskar ta, cike da wani irin yanayi ta shiga amsawa. "Na'am Mama" Waro idanu Fulani tayi cikin kaɗuwa, sai kuma ta juya ta kalli bayin nata, alamun su fita su bata wuri. Duƙar da kansu suka shiga yi, alamun girmamawa, sannan suka zagaye ta suka fice, suna masu jan ƙofar falon. Miƙewa Fulani tayi, tana mai isowa gaban Umma ta sanya Hannu ta tallafo hannuwan Umma gabaki ɗayn su tana mai miƙar da ita tsaye. Sai kuma ta rungume ta, aiko me Umma zata yi banda kuka, ashe akwai wannan ranar da zata kawo kanta da kanta cikin gidan mahaifin nata? Ita kanta Fulani wadda ta manyanta sosai, kukan ta saki tana mai ƙara rungume Umma. "Da gaske kece kuwa gimbiya? Da gaske kina da rai duk tsawon wannan zamanin? Ina kika shiga ne haka gimbiya? Ina abun da kika haifa?" ta faɗ a tana mai sakin Umma ta shiga binta da kallo. Hajiya zainab dai ta zama hoto, zaune take kawai, Amman jin ta takeyi wani gingirim. Sun zame mata kaman faifan sidi da take kallo a allon talabijin. " Mama labari ne mai tsawo, yanzu ma tare muke da miji na, da kuma yayan shi da matar shi gata nan zaune" Umman ta faɗa tana mai juyawa ta shiga nuna Hajiya Zainab dake zaune. "Mijin ki kuma Merama? Yaushe kika yi wani aure?" Sadda kai Umman tayi ƙasa, ganin hakan da Fulani tayi ne, ya sanya ta shaida cewa ba zata bata labarin yanzu ba. Sakin Umman tayi, tana mai wucewa gaban landline da yake ajiye ta latsa kira. " Kizo yanzu" Abun da ta faɗa kenan tana mai datse kiran, sai kuma ta koma ta zauna bisa kujerar da ta taso akai. Bata kuma cewa komai ba. Amman har yanzu fuskar nan cike take da tsoro da firgici, da kuma mamaki. Gani take kaman ba Meramar bace, gani take kaman fatalwa ne tayo masu. Kai sarauta shegiyar aba ce. Da gudu wata haɗima ta shigo, sanye da kaya irin na bayi, ta zube gaban Fulani, tana mai kwasar gaisuwa haɗi da kuma kirara ta. "Aje a buɗe ɗakin sarauniya Merama yanzun nan, a ƙara gyara shi, zata shiga" Abun da Fulann ta faɗa kenan, har yanzu fuskar ta na kan Umma wadda ta kuma sadda kai ƙasa tana matsar kwalla. Da sauri ta juya tana kuma waiwayawa ta kalli ɓangaren da su Umman suke zaune. Mamaki takeyi, ashe dai da gaske ne zancen da taji anayi a cikin gida? Da gaske sarauniya Merama ce ta dawo? To ba ance ta mutu ba? "To Ranki ya daɗe, Amman dai ɗakin a gyare yake, kullum sai an gyara kaman yanda aka saba" "To kuje da su, a basu cikakkiyar kulawa, a kai abinci masu rai da lafiya, a fiddo masu kaya, idan sun gama sai ku dawo dasu nan zuwa fada ta" Ta faɗa cike da isa da taƙama, irin ta jinin saraki. Da gani dai ita ce uwar gidan sarki. "An gama uwar gijiya ta, gamawr ki lafiya Uwargida ga Mai martaba" ta faɗa tana daɗa russunawa ta sake kwasar gaisuwa, sannan ta miƙe ta nufi hanyar fita. Da hannu Fulani ta nuna ma su Hajiya Zainab akan su bi haɗimar tata, tana mai ɗan sakar masu murmushi. Haka su Umma suka sake miƙewa suka bi bayan haɗimar, har yanzu dai Hajiya Zainab bakin ta sake yake galala. ********* Da idanu mai martaba yayi ma fadawn nashi da sauran hakimman alama da su basu wuri. Dukansu su saida suka kuma duƙawa suka kwashi gaisuwa cikin girmamawa sannan suka fice. Alhaji Auwalu mamaki kawia yakeyi, ina ne nan kuma Maryama ta kawo su? Gashi kuma yaji har sarkin ma da kanshi yake ce mata Sarauniya. Bayan kowa ya fice ne daga fadar, ya rage daga mai martaba sai Alhaji Auwalu da Alhaji Mustapha. Gyaran murya sarki ya kuma yi. Cikin muryar shi mai kama da ta riƙaƙƙun sarakuna ya shiga cewa. "duk da ban kai ga sanin haƙiƙanin matsayin ku ba ga ita Merama, Amman ku ba baƙi bane a gare mu, a koda yaushe ayyukan Alkhairan ku suna iske mu, bayan haka ma, ko wancen ɗaurin auren yaran naka da akayi saida muka halarta, nasan kun san haka?" Da kai suka shiga jinjinawa, ko ba komai sarki ba baƙon Alhaji Mustapha bane, hasali ma, yana daga cikin waɗanda suka assasa sarautar da aka ba Al'ameen shi da sarkin Katsinan. Muryar mai martaban ce ta katse masu tunanin da suka shiga. " Alhaji duk da bansan musabbabin zuwan naku ba, zamu iya cewa, wannan zuwan naku yafi komi daɗi a gare mu, mun samu ɗiya gare mu a tare da ku, duk da munyi matuƙar mamakin kasancewr ta a raye, tsawon wannan lokacin ta bar gida, ta barmu cike da jimami da alhini, wanda mu duka cikin. U babu wanda yasan dalilin tafiyar tata, ciki kuwa harda mahaifin ta, watau tsohon sarki Allah yayi mashi rahama" Ba Alhaji Mustapha ba, har Alhaji Auwalu babu wanda bai kaɗu da jin maganar da mai martaba ɗin ya faɗa ba. "kwarai kuwa, Merama ita ce ɗiya ɗaya tilo da Allah ya ba ɗan uwan nawa, kuma yayana, to saidai kasancewr ni ba anan ƙasar nake ba, ya sanya duk bansan abun da ke faruwa ba, hasali ma sai dawowa nayi aka sanar dani mutuwar tata, to kenan akwai wata ƙullalliya a ƙasa, dawowar tata, ya sanya ni matuƙar tunani, ina fatan dai dawowar tata ya kasance ta dawo kenan har abada" Jinjina kai ALHAJI Auwalu ya shiga yi. Sai kuma ya shiga cewa "Kwarai kuma Ranka shi daɗe, haƙiƙa Maryama ta kasance a gidan ƙanina na tsawon shekaru, duk abun nan ba tare da ta taɓa bayyana mana ko ita ɗin wacece ba, kuma mun sha tambayar ta, Amman sai ta ɓoye mana, yanzu ma babban dalilin zuwan namu shine yarinyar ta, da yaron namu yake so da aure, shine tace ba zata iya aurar da ita ba, ba tare da sanin ku ba, kuma Shi alhaji Mustapha ɗin shine yake matsayin mijin ta a yanzu, ta aure shi ne watanni ƙalilan baya da suka wuce, yanzu haka a gidan nashi take zaune" Mai martaba yana jin shi kuma yana sauraren shi. Gyaɗa kai yayi cikin gamsuwa, sai kuma ya shiga cewa "Masha Allahu, haƙiƙa Naji daɗi da kasancewr Merama a wuri da bana da haufin shi, kenan ma ko ɗaurin auren yaran naku da muka je Merama na cikin gidan ba tare da sanin mu ba, ikon Allah" Su duka gyaɗa kai sukayi. Su a da kyakkaywar fahimta da mai martaba, ko ba komai Alhajin Mustapha ba ɓoyayyen mutum bane, ga dukkanin manyan ƙasar, hasalima appointment ɗin da shugaban ƙas aya bashi da kamfanin da yake dasu ne, ya sanya yayi fice kowa ya sanshi. "Naji kunce Yaron wajen naku ke son ita yarinyar Merama, ina fatan dai ace Muhammadu Al'ameen kuke nufi?" Da murmushi Alhaji Mustapha ya shiga gyaɗa kai. "Madalla da jin wannan zancen, ba abunda zamu ce, sai Allah ya sanya alkhairi, kuma shi Muhammadu Aminu ba ɓoyayye bane a wajen mu, ayyukan Alkhairan shi basa da iyaka, hatta da ƴan gudun Hijirar mu baya barin su hakanan, duk wata akwai Abunda yake tura masu ta asusun ƙungiyar tasu, bayan zuwa da yakeyi yana duba su, haƙiƙa wannan masarauta tayi matuƙar farin ciki da samun irin wannan suruki, kuma kaima ina jinjina maka Alhaji a bisa amincewa da auren Merama da kayi da kuma bata kariya na tsawon wannan lokaci, a domin haka ne, zaku je kuci abinci ku huta, zuwa anjima sai mu sake tattauna wa, muna maku maraba da zuwa masarautar Barkindo Lamiɗo" Da matuƙar murna da farin cikin wannan karamci da suka samu, suka shiga miƙewa. Mai martaba da kanshi ya miƙe yana mai basu hannu suka sake gaisawa, sannan yayi masu jagora zuwa babban falon da aka shirya masu kayan abinci cima kala da kala. Zuciyar Alhaji Mustapha cike take taf da fari cikin kasnacewar shigowar Ahalin shi, cikin wanna zuri'a da suke da tarin karamci da mutumci, uwa uba sanin darajar ɗan adam. ****** Cike da ruwan hawaye a idanun ta take bin ɗakin da kallo. Sai kuma ta fashe da kuka, tunowa da tayi Wancen lokacin zaman ta a ɗakin nan.sai gashi yanzu an cenza mashi fasali da komai, duk da babu wanda ke rayuwa a cikin shi, har yanzu ana kiran ɗakin da mallakn ta. Mahaifiya da mahaifin ta take tunowa, wai yau sai gashi ta dawo a matsayin baƙuwa, sai ga ƙanen mahaifin nata a bisa karagrr mulkin mahaifin nata, sai ga Mama a matsayin Fulani, matsayin da Mahaifiyar ta take ada cen baya kafin rasuwar ta. Hajiya Zainab ce tavkamo ta, ta shiga zaunar da ita a bakin tafkeken gadon da ya sha shimfiɗu iri iri. Bayan haɗimar ta russuna cike da biyayya take sanar dasu. Idan zasuyi wanka ne, yanzu zata kawo masu suturun da zasu sanya a jikin nasu. Da to Hajiya Zainab ta bita, sake russunawa tayi, sannan ta fice tana mai waiwayen Umma da take ta sharar kwalla. Ba musu Hajiya Zainab ta shiga tanƙamemen banɗakin da ya gaji da haɗuwa ta gama biyan buƙatar ta duka harda wanka da alwala, sannan ta fito ta tadda Umma har yanzu zaune inda ta barta, ta rafka uban tagumi. Kaya na ajiye gefe, saƙi ne irin na sarakai da ya sha adon fulawoyi masu ɗauke da ƴan kananan madubai sai walwali suke yi, sannan alkyabba gefe da takalma irin na sarakuna. Da hannu Umman ta nuna ma Hajiya Zainab nata kayan. Sunyi kyau, kusan ma ince sun dame wanda seke jikin su a kyau da tsada. Gefe kuma wani ƙaton kit ne cike da kayan shafa. Da ƙauye hajiya Zainab ta lallaɓa Umma akan tayi wankan itama, ita ko ta ɓangaren ta, duk wani motsi da tayi, sake tuna mata da waccen rayuwar tata yakeyi. Har gobe tana danasanin kasancewr ta jini sarakai, jinin sarauta da babu Abunda take cikin rayuwar tasu da ya wuce tarin ƙalubale, akan sarauta za'a iya hallaka ka, to me akeyi kuwa da irin wannan rayuwar. Ba zata taɓa mance Abunda kunnuwn ta suka juye mata ba, ba kuma zata taɓa manta wani dare da yake cike da Ruɗani ba, wanda shine musabbabi ko kuma ince mafarin juyi da birkicewar rayuwar tata ba, tin tasowar ta a rayuwar ta ba. Itama tayi wanka ta shirya, hajiya zainab ce take taya ta shiryawr, tinda komai takeyi a kasalance take yin shi, tabbas labarin mutuwar tata ya zagaya ko ina a faɗin masarautar. Kaman yanda yanzun ma labarin sake bayyanr tata ya ratsa dukkanin lungu da saƙo na masarautar. Saida sukayi salla, dayake ƙasau ce sukayi, bayan sun gama ne, suka kuma dawowa falon, inda suka tadda kuloli sun fi a ƙirga kowanne shaƙe yake da abinci kala kala. Iya ganin ka iya ci ka, ga kayan itatuwa babu abun da babu a wurin. Da ƙyar Umman ta yayyabiɗa, yayin da Hajiya zainab ɓarayi baƙunta ba, kasancewr su su biyu ya sanya ta kwasar garar ta. Duk da har yanzu tana kula da yanda hankalin Umman yake tashe. Hakan kuwa yana da nasaba da tuna rayuwar ta ta baya da tayi, sai taji Umman ta ƙara birge ta, ita kanta ta kula tin lokacin da ta gane cewa ita ɗin sarauniya ce mai cikakken gata, kallon da take mata ada na matar ƙanin. Uji ya sauya, sai take ganin ita kanta har wani girmamawa take mata cikin kalaman ta, duk da Umman ta nuna mata bata so, saidai sarauta daban take a duk inda take, ita kanta tako ƙafar tata cikin gidan, sai ya zamana cewa kaman ta rikiɗe ta sake komawa sarauniyr a idanun kowa. Haka suka gama cin abincin suka miƙe suna mai komawa kan kujeru irin na sarautar suka zauna, jiran wannan haɗimar tazo ta maida su ga faɗar Fulanin. Ada falon ba wani babba bane sosai, irin ginin nan ne bada, ginin ƙasa da zane zane da yake shimfiɗe da jajayen kilisai da wasu irin barguna an lilliƙa ma bangon, saɓa in yanzu da yake ginin zamani cike da ƙawa da kyau, irin na sarakan yanzu, hatta da ƙofofin gidan abun kalli ne, kai daga gani naira tayi aiki a wurin. Basu daɗi da zama ba, sai ga haɗimar ta kuma dawowa. Cike da girmamawa take sanar dasu akan su dawo ta maida su ga Fulanin, kaman yanda ta bata umurni. Haka suka kuma miƙewa suka bi bayan haɗimar, har zuwa wani ɓangare na gidan inda Fulani take hakimce cen ƙuryar faɗar an ƙawata ta da kumbuna da kwallaye, irin dai faɗar da, sai hakan ya kuma Sanyawa tayi kyau fadar. Zaune take ta kishingiɗa bisa wani tun tun, ga wasu bayi bayan ta na mata firfita cike da biyayya. Wasu mata ne zaune suma cikin shiga irin ta manyan mata, gefe da gefen ta, watau dai sun sanya ta tsakiya, da gani dai suma matan sarki ne. Bayi ne zazzane ana ta fadanci, kowa ya natsu wata zabiya na ta zuba ma Fulanin kirari, ita ko sai faman murmushi takeyi. Shigarsu ce taja hankalin kowa zuwa kansu, nan fa bayan nan duk suka mimmiƙe suna masu sadda kai ga su Umman cike da girmamawa. Da hannu Fulani tayi ma Umma nuni da wata shimfiɗe da ta cika da ƙawa, alamun dai nan ne zata zauna. Hannun Hajiya Zainab taja suka nufi shimfidar suka zauna su biyu. Suna mai tankwashe ƙafafu su kaman yanda sauran matan sarkin sukayi. Bayin nan ne ɗaiɗaya da ɗaiɗaya suka dinga miƙewa suna zuwa gaban su suna kwasar gaisuwa, daga haka har suka gama, sai kuma suka sanya layi suna mai ficewa daga fadar cike da biyayya. Bayan fitar su ne, Fulani ta kuma tashi zaune, tana mai gyaran Murya. Cike da taƙama ta fara magana. "Waɗannan sune sauran matan mai martaba, kaman yanda yake cewa baki sa su ba, domin sai daga bayan hawan shi ne karaga ya kuma ƙara su, wanna sunan ta Sarauniya Indo, wannan kuma sarauniya Khairiyya" ta faɗa tana mai nuna su da dukkanin hannuwan ta, su kuma sai sakin murmushi suke yi cike da wani irin ya ayi da zaka iya tantance me ke cikin zukatn su. Sai kuma ta juya ga sauran matan, tana mai nuna Umma. "Wannan ita ce Gimbiya Merama, kaman yanda kuka samu tarihin ta, nasan duk cikin ku tin kafin ma auren ku da mai martaba saida kuka samu tarihin Gimbiya, saboda haka ne nake mai sanar daku cewa Wannan dai ita ce Gimbiya mai cikakken iko a wannan masarauta" Dukansu da kai suka gaisa, ba wadda ta iya buɗa baki tayi magana. Haka itama Umman, sai sarautar tata ta asali ta motsa. Fulani ce ta cigaba ta cewa "Yanzu muna jiran iso ne a wurin mai martaba, ya aiko jakadiya a sanar damu cewa duk mu shirya zai aiko mu same su ƙaramar fada" Jinjina kai suka shiga yi, ita dai Hajiya Zainab iyakar ta kallo, yau Allah ya haɗa ta da inda ake zuba tsabar mulki, watau magana ma basa iya yi ma junan nasu. Zaman shiru ne ya biyo baya a faɗar, inda kowa da abun da yake saƙawa a cikin zuciyar shi, yayin da duk da ita umma tana cikin wani irin hali na alhinin rashin mahaifin ta, da bayan barin ta gidan Allah yayi mashi wa'adi, Amman hakan bai hana ta sakin murmushi ba, kasancewr ta yau a cikin ahalin nata. Saidai duk zuba ido da tayi bata ga ta inda matar waziri da ahalin wazirin suka ɓullo ba, haka kuma ko a faɗa bata ganshi ba, indai ba shima ɗin Allah yayi mashi rasuwa ba, batare da ta sani ba, i ko haka ne, duk wata hujjar da ta kama ta rushe kenan. Suna haka ne, jakadiya ta shigo, sanar dasu tayi ison mai martabar. Fulani ce ta fara miƙewa, jakadiya ta gyara mata alkyabbar ta, sai kuma ta wuce gaba, yayin da sauran matan suma suka miƙe, hadda su Umma suka mara mata baya. Sashen mai martaba suka nufa, duk i da suka ratsa bayi ne ke aikace aikace, ta cikin barga suka bi, inda suka ga dawaki masu jini a jika sun cika sunyi ɓulɓul sai harbin iska suke yi. Sashen mai martaba, kusan mucr yafi ko ina ƙawatuwa, tun daga waje zaka shaida haka, wasu irin ƙofifi ne na zallar glass tar, kana iya hangen abun da ke ciki. Haka suka rinƙa ratsa wasu irin fadoji masu matuƙar kyau, har zuwa isar su ƙaramar faɗar da tafi ko ina kyau da tsaruwa. A bisa kujeru suka tadda su alhaji Mustapha ɗin, yayin da mai martaba ke zaune gefen su, shima bisa kujerar irin ta sarauta. Kujerun da suke mallakin matar sarki kowacce ta ja ta zauna, yayin da Umma da Hajiya Zainab ɗin suka zauna ƙasa daga gefe. "Aa taso ki dawo nan Gimbiya Merama" Cewr mai martaba yana nuna mata gefen shi daga ƙasa. Ba musu Umman ta miƙe ta koma inda ya nuna mata. Jakadiya ce ta russuna cike da girmamawa, sannan ta sanya ƙafa ta bar fadar, tana mai ja masu ƙofar. Saida mai martaba yayi gyaran murya sannan ya buɗe taro da addu'a. Bai jira komai ba ya fara jawabi. "Gimbiya duk da kasancewr yanzu kuke tafe da ke da mai gidan naki da kuma dangin shi, hakan ba zai hana in nuna maki tsantsar ɓacin rai na ba, wanda ke kanki kin sani tafiyar taki ba ƙaramin ruɗu ta saka masarautar nan ba, duk da cewa bamu san babban dalilin ki na tafiyar ba, hakan kuma yanzu ba dalilin nake so inji ba, duk munyi maganganu da mai gidan naki sosai kuma na fahimta, saidai ina so in riƙe shi wata alfarma ne, duk da kasancewar ita mai sunan Fulani shi Alhaji ne ya riƙe ta, har girman nata, kuma ya shaida mana cewa yanzu haka dalilin auren nata ne da yaron wajen nashi Muhammadu ya tafo ku ƙafa da ƙafa, kenan ma da ba zaki dawo ba, da haka ne nake riƙon shi alfarma da ya maido ma masarauta da sarauniyar ta, watau ita Hauwa'un, ayi hidimar bikin nata anan, kuma a ɗauke ta anan zuwa gidan mijin nata, ba ƙwace zamuyi mashi ba, alfarma zaiyi mana, daga yanzu duk wani abu da fannin amarya keyi mune zamuyi mata. Yanzu nasan akwai hidindimu masu ƙarfi dake tafe, Shiyasa ba zamu riƙe ku ba, Amman duk kanku muna so ku sani masarauta tayi matuƙar farin ciki da kasancewar ku waɗanda suka riƙe mata gimbiyar ta har kawo yanzu, ita da abun da ta haifa, zamu samu lokaci mu tattauna dalilin barin naki guda ke Gimbiya Merama, Amman ba yanzu ne lokacin ba, tinda hidimar aure ta taso, ba zamu ce a ɗaga ba, saidai za'a maido mana amarya da mahaifiyar amarya zuwa nan, inda duk wani shagali na fannin amarya zamu gabatar dashi anan, kafin mu baku amarya" Ya ƙarashe yana mai sakin ɗan murmushi haka kaɗan. Suma su Dad murmushi suke yi. "Ranka ya daɗe ai wannan ba wani abu bane, ba damuwa ko ɗaya acikin hakan, insha Allahu yarinya daga makaranta ma nan za'a zarto da ita, kafin ta dawo ita mahaifiyar tata zata fara yo gaba, duk Abunda kasan ana gabatarwa na al'ada insha Allahu za'a zo nan a gabatar dashi, godiya mukeyi Allah ya ƙara ɗaukaka" cewr Alhaji Auwalu ya har yanzu fa kallon Umma yakeyi cike da mamaki, lallai ta cencenci yabo da jinjina da ta kasance a matsayin mai aiki a gidan ƙanen nashi na tsawon lokaci. Sun kuma tattaunawa, sannan mai martaba ya gabatar da matan nashi garesu suka sake sabuwar gaisuwa. Nan fa aka buɗe babin fira kaman ba'a masarauta ake ba, inda shima mai martabar ya kuma sakin jiki yana sake gaya masu halin da ƴan gudun Hijira ke ciki. Wajen ƙarfe biyar ne sukayi haramar tafiya, ba yanda mai martaba baiyi dasu ba akan su tsaya su kwana suka ƙiya, a ceear su basu shiryo ma kwanan ba, amman yanzu ai ya zama gidan su har sai an gaji dasu. Shi kanshi mai martaba ya jinjina dattakon su Alhaji Mustapha ɗin, duk da kasancewar su ba baƙin shi ba, hasali ma suna yawan haɗuwa, duk lokacin da wani abu ya taso, dama tin cen yana jinjina Alkhairin mutumen da yaron nashi, hidima suke yi ma ƙasar su da ƙarfin su da dukiyar su kaman basa so, lallai sun cencenci yabawa da kardamawa, ya kuma yi alƙawarn yin bikin tarbar Gimbiya Merama da mijin nata, kafin lokacin tattaunawar yanda za'ayi da sarautar ya taso. (Uhmmmm to ko me yake nufi da hakan kuma?) Saida sukayi ma bayin sarki da fadawa alkhairi mai yawa, mai martaba da kanshi ya rako su har zuwa motar tasu yana mai ɗaga masu hannu, da jin Meramar a jikin shi kaman kar ta tafi, ganin ta da yayi ne ya tuno mashi da ɗan uwan nashi har matse kwalla sai da yayi. Wannan babban abun alkhairi ne ya same shi da ahalin nashi baki ɗaya, kasancewar Allah bai bashi haihuwa ba sai guda ɗaya, itama t a kasance mace ce, kuma ba yanda zata yi ta gaji sarautar tashi tinda dama tin cen asali Meramar ce zata kasance sarauniya ko kuma mijin nata.... Amman ga yanda rayuwa ta juye dasu, saboda haka yayi alƙawarn amsar ɗiyar ɗan uwan nashi da hannu bibbiyu... Haka suka ɗauki hanya, daga Hajiya Zainab har Umma ba mai ta ƙawa, akai akai Umma ke share kwalla ta, ita bata ma san baffan ta ne a kan karagar mulkin nata ba sai yanzu, koma dai minene lokacin da Suhan zata san ko wacece ita ya ƙarato. Alhaji Mustapha da Yaya Auwalu ne kawai ke firar ƙaramin su, sai driver daya tattake yana ta zuba uban gudu, gashi dama ya nake cikin shi nak da irin cimar gidan sarauta, da har sai kaji ba wurin zubawa. Cikin dare sosai suka dawo, saida suka biya suka sauke su Hajiya Zainab ɗin sannan suka juya zuwa nasu gidan. yayin da Hajiya Zainab ɗin tayi alƙawarin shigowa gobe su sake tattauna wa da umman. Hatta mai gadi yayi mamakin ganin su cikin daren, dama ita Hajiya Kubra koda ta tambaya ina suke aka ce mata sunyi tafiya, taɓe baki tayi, tana mai cewa "zaki ƙaraci abubuwan ki ko guda nawa ne, lokaci na baki, daga ke har talakr ɗiyar ki" Dama Umma ce keda duty, saida ta sake haɗa masu ruwa sukayi wanka, sannan suka kwanta cike da gajiya, ko Abunda zasu ci basu tsaya nema ba. Alhaji Mustapha yayi matuƙar murna da sanin asalin Amaryar tashi, yayin da Umma ta kwana tunane tunanen abubuwa, lallai akwai sauran riba a kaba, tinda ko eulgin waziri ita bata gani ba, kuma a duk furar da sukayi da Baffa mai martaba bata ji ya ambaci sunan wazirin ba. ****** Ya Ameen bai kira ni ba tsawon kwana uku kenan, kuma ko na kira bana samu, na rasa dalili, Amman na bar hakan ne a cewar ayyuka ne sukayi mashi yawa. Gashi har mun kusa gama exam ɗin. Nayi mamakin da Umma tace mani ko na gama Exam in zauna a makarantar har zuwa lokacin da zata buƙaci tahowar tawa, na rasa dalili, kuma ita bata yi mani wani jawabi ba. Haka na share na cigaba da zana Jarabawa ta, ranar cikon kwana na huɗun ne, sai ga kiran Ya Ameen ya shigo waya ta. Cike da ɗoki na Ɗauka, Amman sai na saisaita murya ta kada ya gane cewa ina kewar shi, duk a ƙoƙari na na kare kambu na a matsayi na na mace. Duk dai da haka saida ya gane nayi kewar tashi, ƙorafi zan fara mashi, ya katse ni da bani haƙuri yana mai sanar dani ayyuka ne sukayi yawa, ashe ba kamfani ɗaya bane ke son ƙulla harkar kasuwanci dashi ba. "Sai yaushe ne zaka taho?" na faɗa cike da shagwaɓa, ina mai tura baki gaba. "Kinga my Amarya, kwantar da hankalin ki, yanzu haka ma gani a airport lokacin tashin jirgi kawai nake jira, saidai zuwa nan da wa biyu ne, nayi lattin samun ticket, kinga ba zan ƙara so ba sai goben ku kenan, tinda mu yanzu nan rana ce, kinga kuma ku dare yayi nisa yanzu. Da kai na shiga amsawa cikin shagwaɓa, ina kallon khady sai mktse moste takeyi, ga dukkan alamu idanun ta biyu, ita da har ga Allah son Ya Ameen ɗin takeyi, ya zuwa yanzu fa ta fara bani haushi, tinda nima na gane cewa tsundum fa na faɗa tarko. "Zan kama bakin nan naki ne" Ya faɗa shima yan mai kwaikwayar murya ta. Maida bakin nayi, ina mai lumshe idanu, jin daɗin muryar shi da nakeyi, har cikin kwalwa ta, ji nakeyi kaman yana busa mani sarewa a kunne, dama ashe haka amon muryar Ya Ameen take da masifar daɗi, ban kuma tantancewa ba, har sai da na fara soyayya dashi sana. Komi yayi burgeni yakeyi, salon shi, kai hatta da wannan miskancin dake bani haushi a da yanzu ya koma burgeni yakeyi. "Saura kwana nawa?" Ya tambaye ni, cike da zaulaya, cikin wani irin amon murya da ya sanya na faɗa wani shauƙi. "Sixten" Na faɗa a hankali. "Wow ashe amaryar tawa tana ƙilgawa, kin ƙagara ko baby ta?" Ya kuma faɗa cikin wata zaulayr. "Uhmmm Uhmmm ni Allah yaya ba haka bane, ina dai ƙilgawa ne saboda na kusa gama exam" "Ba wani baby, kina ƙilfa ra ar shigar ki ɗakin Ameen dai ne kawai, Dont worry, dama ina so ne ki faɗa mani abubuwan da kike so a zuba maki a lefe, Aunt Feena ce zata haɗo maki acen, ko kuma zan bata numb ki sai ta tuntuɓe ki" Da sauri nace "Nooo Yaya, kar ka bata, ba ma sai an tambaye ni ba, ni ai kai nake so, ba kayan ba, don haka duk abunda ta sanya duk ɗaya ne, i only want u" "Wow dear, are u sure?" Cike da kunya nace "yes Yaya very much sure ma" na ƙarashe a hankali ina mai noƙe kai cikin fillow, sai yanzu Kunyar abun da na faɗa ta kama ni. "To ai shikenan, saidai akwai abubuwan da dole sai kin faɗi size ko zaki faɗa mani yanzu, tinda ita kunya kike ji? Ni kau kinsan komai nawa ne" Kaman in nutse haka na dinga ji. "Ba zan iya faɗa ba yaya, i'll text u later" Na kuma faɗa cikin kunya. "Okay baby, bari in barki ki kwanta, zamuyi waya in na sauka, i kissed u, sleep tight" Ya faɗa a hankali, yana mai sakin ƙaramin Kiss ya huro mani iskar cikin kunne. Noƙewa nayi a hankali, kasala na saukar mani, murya cen ciki na shiga cewa "Okay Yaya Safe journey" Ƙit na katse wayar, ina mai sauke ajiyar zuciya jeri jeri. Khady ce ta miƙe zaune ta kunna hasken ɗakin, snanna ta maido kallon ta gareni. "Suhan ina mai maki murna matuƙa, ki riƙe Dambulan da amana, shi ɗin kalar namijin da kowa ke buƙatar samu ne" Tana gama faɗar haka ta kashe kwan ɗakin ta koma ta kwanta. Ashe duk firar da muke idanun ta biyu, dama nayi tunanin hakan, wayyo Allah so shegen abu, gashi ta kasa bacci, jin wanda take ƙauna shi kuma ya mutu akan ƙawar ta, har yana faɗa mata daɗaɗan kalaman da idan ya faɗa sai ta rintse idanu wa, ji take kaman ita yake gayamawa, Dambulan da babu wanda zaiyi tunanin zai iya tsayawa ba soyayya muhimmanci haka, sai gashi shine yake faɗar wasu kalaman masu matuƙar sanyaya zuciya. Ji nayi kaman in mata kuka, Amman in na tuno da Ya Ameen fa take so, sai inji wani haushn ta, ɗan ƙaramin tsaki naja, ina. Ai wulla mata harara daga bayan ta, cikin zuciya ta nake faɗin "wahalla kawai, Ya Ameen na Suhan ne ita ɗaya, ko baki raya ni murna ba, babu Abunda za'a fasa" (Uhhmmmmm Suhan kenan, lallai kin fara yin nisa) Shima yana kashe wayar ya rubuta saƙo ma Aunt Feena akan cewa ta siya duk Abunda taga ya dace kawai, saidai ta zaɓi mashi classic kaya, saboda Amaryar tashi daban take. Shi kanshi mamakin kanshi yakeyi, wai Suhan ce yanzu saura kwana sha shidda auren nashi da ita, shi kanshi ya san yayi dace, aure irin na soyayya, tinda yan da tabbacin cewa, ya zuwa yanzu Suhan ɗin ta dumbula cikin narkon soyayyar shi, tinda gashi har tana faɗin wai *Shi kaɗai take so* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'a Ga Wanda Yayi sabon Aure* بارَكَ اللَّهُ لَكَ، وَبَارَكَ عَلَيْكَ، وَجَمَعَ بَيْنَكُمَا فِي خَيْرٍ. Barakal-lahu lak, wabaraka 'alayk, wajama'a baynakuma fee khayr. Allah Ya sanya albarka a gareka, yayi maka albarka kum aya hada tsakaninku da alheri. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~59~* *Fans Naji daɗin comment ɗinku haƙiƙa, ashe Gimbiya Umma ma tana da masoya har haka?* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Washe gari tin da safe sai ga kira daga masarauta, mai martaba ne da kanshi, yana tambayar lafiyar Umma, da bincikar ko dia za'a kawo mata haɗimai ne masu tsaron lafiyar ta, da yi mata hidindumu? Dayake Dad suka kira, sai ya miƙa ma Umma wayar, cike da girmamawa take gaida mai martaba Baffan nata. Sannan take sanar dashi cewa babu komai, suna da ma'aikata isassu, koda za'a kawo a bari sai daga baya. Bayan sun gama magana ne, sai ya buƙaci da taba mai gidan nata. Sake damƙa amanar Umma yayi ga Dad ɗin, duk da yasan ba za'a samu wata matsala ba, tinda ko da cen lafiya lau suke zaune, saidai haƙƙin fada ne akan tasan halin da gimbiyr tata take ciki a kulli yaum. Mai martaba ɗinne ya kuma buƙatar da suna so a gaggauta kawo masu amarya, kuma basa buƙatar komai da ya danganci lefe, saboda masarauta ita ke yi ma duk wadda ta fito daga tsatson ta komai. To sha'ani ne na masarauta, shima Dad ɗin bai ja ba, gudun saɓa ma sarkin, sai ma cewa yayi insha Allahu ba da jimawa ba za'a hannanta masu amaryar. Cike da girmamawa sukayi sallama, yana mai buƙatar sanar da Al'ameen da Mom ɗin tashi, akan cewa su adana lefen su, har sai yarinyar tazo gidan sannan a bata. Duk da shi fa har yanzu ba wai ya yarda bane akan cewa har cikin zuciyar hajiya Kubran ta yarda. Miƙeea yayi yana mai nufar sashen Hajiya Kubran, baya da tabbacin cewa ya zuwa yanzu ma bata fice daga gidan ba. ********* Wajen ƙarfe tara ya kira ni tare da shaida mani saukar tashi, da yaso ya wuto nan waje na kai tsaye, Amman sai aka kira shi akan cewa order ɗin kayan da za'a sanya a sashen namu sun iso. Hakan ce ta sanya shi wucewa gidan kai tsaye. Dayake part ɗin an gyara shi fiye da tunanin mutum, duk da ba'a rushe shi ba, ɗaki ɗayan nan dai har yanzu shine, sai kitchen da babban falo. Saidai an sake kankare plaster ɗin anyi wata, hatta da fentin da akayi ma part ɗin abun kallo ne. Shi kanshi daya gani saida abun ya burge shi, haƙiƙa Bilal aboki ne kuma amini ne, shine ya tsaya akan aikin kan jiki kan ƙarfi, dukkan Abunda yasan zai burge Al'ameen da Suhan ɗin shi ya sanya aka zuba. Umma tana kallon ana aikin, saidai tayi murmushi, zuciyar ta na ayyana mata, yarinyar tata ta kusa samun ƴancin kanta, da yin rayuwa kaman kowa. ******** Duk abunda ke faruwa ma'aikatan gidan basu sani ba, saidai labari ya bazu ko'ina akan auren da Umma tayi ma Alhaji, ko Mama talatin yanzu ba wani samun abun gulmar take ba, Maree dake shiga itama yanzu an hana ta, Nihal ɗince ke jagwalgwala masu komai, kusan ma ince sun koma yin order, domin ko ta girka basa iya ci, haka gyaran sashen da ka shiga zaka dinga ganin ƙura, Amman duk da haka Hajiya Kubran bama wani ganewa takeyi ba, saboda ba wannan ce a gaban ta ba. Saidai kowa ya kula da sauyn da aka samu cikin gidan, to Umma ce dai, itama ba inda take zuwa, ko fitowa bata cika yi ba, in ba sashen Alhaji zata ba. Dole ne kuma suka koma girmama ta, yayin da bata nuna masu komai, alheri akai akai takan sanya Alhaji yayi masu, saboda halin girma irin nata, ba kowa ne ma ta riƙe arai ba, masalan Mama talatun da tasan cewa ba ƙaunar ta da ɗiyar ta takeyi ba. Maree kam tana cen ta haukace, kullum maganar ta Ya Ameen, masalan da taga ana gyaran sashen tana raya ma kanta ko ba daɗe ko ba jima ita ce za'a shigar sashen duk yanda zata yi zata yi, domin ganin ta karkato da hankalin Alhaji ƙarami a kanta. ******* Kai tsaye gidan Hajiya Zainab ya wuce, to ita ɗin ma bata shaida mashi sunyi tafiyar ba, shaida mata yayi isowar kayan, da kuma buƙatar ko zata samu waɗanda zasu je su shirya part ɗin. Daga nan ya wuto gida kai tsaye, to a gidan ma ne ya sake yadda Bilal, yana tsaye jingine da mota yana amsa waya da Ummin. Yayin da ma'aikatan kanfanin da zasu haɗa kayan ke ya faman kwasar kayan zuwa cikin sashen. Tsayiwar shi ya sake daidaitawa, bayan yayi parking ya fito, hannuwan shi duka ya zube cikin aljihun suit ɗin da take jikin shi, da ta kasance kalar ash mai haske. Yayi matuƙar kyau, ya sake fari, fatar ta sake murjewa, kai da ka kalle shi ba sai an gaya maka hutu ya zauna a jikin shi ba. Sashen yake kallo, yana raya abubuwa da dama acikin zuciyar shi, shi dai ba wai dan yaso zaman bane, saidai baya so wata fitinar ta kuma ɓullowa ne. Saida Bilal ɗin ya datse kiran sannan ya juya ta inda yake tsaye yana faɗin "My Man you Welcome, maimakon ka faɗa mani inje in ɗauko ka?" "ah no, ai wannan aikin da kake yi, yafi ɗaukonin, dama mota ta a airport na ajiye ta Wancen karon, ko da nayi landing kawai sai na Ɗauka" ya faɗa yana mai sake maida kallon shi kan sashen da ake ta faman shigar da kaya. "Aiki yayi kyau Friend, nagode da samun amini kaman ka" ya faɗa yana mai nuna sashen da hannu haka kaɗan. Ka faɗar shi Bilal ya dafa. "Kafi gaban komai my man, ina fatan mission ya kammala?" "Alhamdullahi, saidai sun ɗan riƙe ni da yawa" "ai tinda an samu Abunda ake so, ba wani damuwa ina ganin" Bilal ɗin ya faɗa shima yana mai maida kallon shi kan kayan. "Ina fatan akwai komai cikin kayan, domin ba zasu koma ba, sai sun gama haɗa komai" cewr Bilal ɗin. "Eh komai akwai cikin package ɗin, Abunda basu kammala ba ma Mama Zainab zata zo da mutane sai su ƙara sa su" "OK tau shikenan, ya kamata kaje kayi wanka hakanan, sai ka huta" "Ok Mom na gida kuwa?" "eh tana ciki ita da Dad" "OK" kawai ya faɗa, yana mai juyawa ya nufi part ɗin Mom ɗin baki ɗaya. ******* "Dama ai dole suce kada akai lefe, su san basa da Abunda zasu bada tukuici mana, inma ƴan uwan gaske ɗin ne" Mom ɗin ta raya cikin ranta, a zahiri kuma tayi murmushi tana mai faɗin "Shikenan ma, sun hutar damu, dama Feena ta kira ni akan cewa end of this Week zata shigo da kayan, shine nayi tunanin ko sunday ne sai aje akai" "A'a ba sai an kai ko ina ba, ni zan fita sai na dawo" ya faɗa yana mai Miƙewa daga bisa sofar. Shigoway Ya Ameen ce ta dakatar dashi daga tafiyar d aya yi niyya. "A'a Son kai ne da safen nan?" Cewr Dad iɗn, yana mai sakar ma yaron nashi murmushi, ko ba komai ya tabbatar da Yaron nashi zaici aure inda ya dace dashi, babban gida masu dattako, Amman duk da haka mahaifiyar tashi bata sani ba, sai hauka takeyi. "Dad Good morning, baka fita ba?" "Yanzu dai nake Da niyya Son, ya aiki ya hanya?" "Alhmdllh Dad, muna kyautata zaton za'a samu Abunda ake so wajen turawn nan" "Tau mSha Allah, dama yanzu nake maganar ka da Mom ɗinka" "To Dad, Mom Good Morning" ya faɗa a hankali yana mai maida kallon shi kan Mom ɗin. Murmushi ta saki a hankali, tana mai miƙewa itama, "Son You are Welcome" Ta faɗa itama, tana mai ɗan taka wa kaɗan zuwa wajen yaron nata, fuskar ta ɗauke da murmushi kaɗan. "Batun lefe ne mukeyi, su ƴan uwan matar taka sunce basa buƙatar komai, shine muka yanke shawara da Dad ɗinka akan a bar shi, alabasshi idan tazo sai a bata daga baya" Da mamaki kaɗan a saman fuskar tashi, ya juya yana mai kallon Dad ɗin nashi, wane ƴan uwan matar shi kuma? Suhan dai it ace matar tashi, kuma yasan basa da wasu ƴan uwan idan ba su ba. Gyaɗa mashi kai Dad yayi, yana mashi alama da ya biyo shi waje, da idanu. "OK Mom hakan yayi, zanje in watsa ruwa" "OK to a fito lafiya, kayan ka na guest room na sanya aka mayar maka, kafin a gama gyaran" Itama ta faɗa, tana mai nuna mashi makullin part ɗin da hannu. Bai ce komai ba, ya shiga taka wa a hankali, yana mai ɗaukar keys ɗin sannan ya fice. Ko da ya fito har Bilal yabar wurin, hakan ce ta sanya shi bai tsaya sauraran komai ba, ya wuce zuwa guest room ɗin kai tsaye, yana mai ɗan kallon sashen su Suhan ɗin, yana mai raya ma ranshi dama ace tana gidan yanzu ta fito ya ganta. Daf da zai shiga part ɗinne ya hango fitowar Alhajin, kai tsaye shima wajen kayan y nufa yana masu magana, su kuma suna ta faman gaida shi. Kai tsaye ya juya zuw aga Dad ɗin nashi. "Kaje ka huta, zamuyi magana da daddare" Abunda Dad ɗin ya faɗ a mashi kenan, domin yana iya hango tarin gajiya akan fuskar yaron nashi. ****** "kin tabbata da kammaluwar komai?, domin fa kinsan idan akwai Abunda na tsana a rayuwa ta bai wuce yarinyar da maman ta ba" "Haba hajiya ta, ai baki da matsala, gani ga laila ma, tare muka sake komawa, kuma malam ɗin ya sake jaddada mana cewa indai aka bi sharuɗɗan da ya gindaya mana, aiki ziyi kyau fiye da yanda muke tsammani, kedai kawai kiyi ƙoƙarin ganin bai kusance ta ba, domin ana ɗaura auren nan fa, zaiji babu wadda ya tsana irin ta, ita dai Uwar ce malam yace muyi haƙurin ganin an gama da lamarin ɗiyar, saboda ita akwai wani al'amari mai girma tattare da ita" Gyaɗa kia ta shiga yi cikin gamsuwa, "Ba matsala indai dan wannan ne, cin amanar da suka yi mani, ba zan taɓa kyale su su tafi hakanan ba, sai sunyi nadamar shiga rayuwa ta da sukayi" Ta faɗa cikin kaushin murya, tana mai sauke wayar daga kunnen ta. " Zasuyi danasani." ******** Kullum ya ganta babu Abunda ke faɗo mashi cikin rai, illa iyaka yaga cewa ya same ta. Shifa Maree ce kaɗai wadda yake ganin dacewar shi da ita. Ada kua baya jin hakan a ranshi, ko shi gani yake ya wuce da iyawar ta, Amman dai koma minene zai je ya samu alhaji da maganar akan cewa yana so a aura mashi maree, wallahi idan bai aure ta ba, yana jin za'a samu matsala, ya tabbata ba zata ƙi shi ba, masalan ma idna akayi la'akari da cewa shi ɗan aiki ne itama ƴar aiki ce. ********* Sai bayan daya kammala komai ne, sannan ya kira ta, duk da bacci da yake ji, Amman yana tunanin idna ba muryar ta yaji ba, baccin ma gagarar shi zaiyi. Sun daɗe kuwa suna waya, kalami yake zuba mata masu narkar da zuciya, shida baiƙi ma ace gobe a ɗaura auren nan ba , yana ganin wutar shi da cen baya, da ya tsaya ruwan ido, ashe ga wadda ta dace dashi ma tana rayuwa a cikin gidan ba tare da sanin shi ba. Mun jima sosai a waya, kiran Umma da nagani yana shigowa wayar tawa ne ya sanya ni ce mashi yayi haƙuri zan sake kiran shi. Shaida mani ta shiga yi, da zaran na kammala Jarabawa ta gobe, in shirya za'a zo a ɗauke ni, dukkan abubuwan da nasan zan buƙata in ɗauka, domin ba lallai in koma makarantar ba saida aure na akai. Kunya Naji ta kama ni. Nan na kashe ina mai amsa mata, sannan na kira shi, nake faɗa mashi Amman Umman tace driver ne zai zo ya ɗaukeni da kanshi. Faɗa ya kama yi, wia minene amfanin shi, shine zai zo da kanshi ya ɗaukeni, tinda ai yana gari. Shifa ba zai lamunci yawan shiga motar driver ba, kai infact ma da munyi auren zai koya mani mota, yana matuƙar kishi na, ace kullum duk inda zani ina tare da wani ƙato, gara ya koya mani in dinga jan kaina. Ya zuwa yanzu, na sakankance ma soyayyar da Ya Ameen ɗin yake yi mani, ashe dama haka yake, da nayi mashi gurguwar fahimta, sai nake ganin ko Afnan yanzu bata kaishi daɗin zama ba. Har addu'a nake yi, bayan auren namu, in samu zaman lafiya, da kwatankwacin ƙaunar da yake nuna mani yanzu, domin ni kaina na sani, a yadda nake ba kowa ɗinnan ba, ace na samu miji kaman ya Ameen tabbas nayi ma mata zarra, bana kuma tunanin idan akwai wadda zata iya kamo ni nan kusa. Haka mukayi sallama dashi, kaman kar mu rabu, kowa na begen juna, duk da har yanzu ina jin kunyar shi, domin wani abu ɗin idan ya faɗa sai na sauke kaina ƙasa tsabar kunya kaman yana gaba na. Umman na sake kira na shaida mata yanda mukayi da ya Ameen ɗin. Cewa tayi to ba damuwa, ai sai a gaya mashi inda zai kai ni, domin dai dama shi ɗin ba baƙon wurin bane. Kai A ya ɗaure, tambayar ta na shiga yi akan cewa ban gane ba, kaman ya inda zai kai ni. Cewa tayi in bari goben na gani. Nidai haka na kashe wayar tawa, to me Umman ke nufi? Ni fa wannan hali na Umma na damu na, ita bata taɓa fitowa fili ta sanar da kai komai, tafi so komai ka gani da idon ka, inma ka tambaye ta, ba zata taɓa faɗa maka ba. Haka na kwana cikin zulumi sosai, koda ya kira da daddare yaji kaman bana lafiya, ba irin tambayar da baiyi mani ba, Amman na shaida mashi cewa babu komai. Haka mukayi firar dai ba wani annashuwa, duk yanda yayi ya shawo kaina kasawa yayi, saidai ya haƙura ya ƙyale ni, shima ran nashi babu daɗi. Washegari na shiga tattara kaya na, shaida ma su Raihana nayi komai da ake ciki, sunyi alƙawarin halartar biki na ɗin, da cewr idan lokacin yayi in turo masu da katin ko ta waya ne, zasu kira ni. Cikin wata irin rantsattsar mota ya iso makarantar tamu, misalin ƙarfe sha biyu, shi kaina da kallon mamaki ya shiga bina, jin inda akace ya kai ni, kuma Dad ne ya shaida mashi da kanshi, duk da yace zasuyi magana jiya Dad ɗin bai dawo da wuri ba, yana cen harkoki sun riƙe shi, shirya ɗaurin aure yake yi mai cike da ƙawatarwa, saboda ko ba komai tuwon girma miyar shi nama. Da kanshi ya dinga kwasar kaya na yana zubawa but, mutane sai mamaki suke yi, wasu na cewa Al'ameen Dambulan ne, wasu kuma na cewa bashi bane, saida Khadeeja ta shaida masu cewa shine, nan fa wasu suka fara ɗaukar shi hoto da waya ba tare da ya kula ma dasu ba. Nidai da kallo nake binshi, yayi matuƙar kyau cikin manyan kaya, shadda ruwan ƙasa, da hula tangaran da takalma half cover sai kalli suke yi. Khadeeja kasa tsayawa tayi wurin, haka ta juya zuwa ɗakin namu, zuciyar ta cike da ƙuna da suya, tabbas so daban ne, watau kuma son maso wani ƙoshin wahala ne, ita tana ganin son da Suhan keyi ma Al'ameen ko rabi rabin nata bata yi mashi, da ace ita ce Allah zai mallaka ma Al'ameen ɗin da ta kusa kashe shi da soyayyar ta. Haka ya zagaya yana mai buɗe mani sit ɗin gaba, ba gaddamanna shiga, har yanzu ba walwala sosai a tare dani, saidai ganin shin da nayi ya mantar dani kusan komai. Haka muka bar makarantar, tuƙi yake cikin gwanancewa, rabin hankalin shi duk yana kaina. Hannun shi guda ɗaya ya sanya ya riƙe steary ɗin, yayin da gudan yayi amfani dashi wajen kamo nawa, "Me ke damun ki ne dear? Ko zullumin auren ne har kin fara?" Ya faɗa a hankali, cikin salon muryar shi, mai sanyaya mani jiki. Ban ƙoƙarin ƙwace hannun nawa ba, saidai ina jin taushi da ɗumin hannun nashi har cikin kwalwa ta. Ba ce dashi komai ba. Shima bai sake cewa komai ba, sai ma tuƙin shi da yake hankali kwance, har yanzu bai saki hannun nawa ba. Yatsan da zoben da ya saka mani yake murzawa a hankali. "Thanks dear" "For what?" na bashi amsa a hankali. "Keeping my promise" "Uhmm" Na sake faɗa ina mai ɗan ƙoƙarin zare hannu na daga cikin nashi. Sai kuma na ƙware da miyau ɗin da ya tsinke mani yana ta gudu cikin baki na. Tari na fara yi, yayin da cikin ƴar ruɗewa ya saki kan motar yana mai tallafi dukkanin kaina, ya shiga hura mani iskar bakin shi a saman fuska ta. Ganin kan motar ya fara yawo ne, ya sanya ni sake sakin ƙara, ganin gadan gadan motar ta nufi wani rami daki gefen titn. Wata ƙarar na sake saki. Cike da firgita nake faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya tuƙi fa kake yi." Cikin gwanancewa ya riƙo kan motar, yan amai murza ta ya sauka daga kan titn ta ɓarayin da babu ramin yayi parking. Cikin daji ne, hakan ya sanya ni sake kallon shi, idanuna har sun kaɗa sunyi ja. Gorar Sona ya ɗauko daga cikin ɗan fridge ɗin motar, ya ɓalle murfin yana mai kara mani a baki. "sha ruwa my matsoraciya , ashe haka kike da tsoro? Ya faɗa yana mai kallo na da ɗan murmushi. Ban musu ba na amsa ina mai tuttula ruwan a baki na, sai kuma na sauke ajiyar zuciya ina mai faɗin" huh" sannan na runtse idanuna, ina mai rufe fuska ta da tafukan hannaye na. "Kina tsoron ki mutu baki ganki a ɗaki na ba ne?" Ya faɗa a hankali yana mai ɗan keanto da fuskar shi saitin tawa, domin ya kalli cikin idanun nawa sosai. Ba ce mashi komai ba, illa "Yaya Please mu bar wurin nan, Allah ina tsoron daji" na faɗa cikin tuno da Abunda ya faru dani ranar da zamu haɗu da Sir Salim. Shima bai ce komai ba, ganin bana cikin natsuwa ya sanya shi sake tada motar ya hau titi. Mu biyu muke ta tafiyar mu cikin mota a nutse, duk da uban gudun da yake shararawa, bamu tsaya ko ina ba, kasancewar Naji yana faɗin tafiyar da nisa. Kaman in tambaye shi, sai kuma na ƙyale shi, so nake inga inda za'a kai in kaman yanda Umman ta faɗa. Snacks ya ɗauko mani a bayan motar, haɗi da lemo, yace inci, saboda ba zamu tsaya ba. Kaɗan naci na ajiye, duk Kunyar shi ta cika ni, gani nake ba zan iya sakin ciki in i wani abu a gaban shi ba. Soyayya yake zuba mani mai tsabta, ji nake kaman ina a aljanna ne, ga sanyi dake ratsa ni a hankali a hankali, ga ƙamshi sosai cikin motar, da kuma wanda ke tasowa daga jikin mamallakin motar. Ko salla bamu tsaya ba, a cewar shi ai ƙasau zamuyi. Ba zan iya cewa ga sunan garin da muka isa ba, saboda ko a mafarki ban taɓa ganin garin ba, saidai abunda na kula dashi shine ƴan garin suna da matuƙar kyau, kuma kowa hidimar shi yakeyi ba ruwan shi da kowa. Titin da muka ɗauka, shi yafi komai burge ni, da mamaki nake kallon Ya Ameen ɗin, shima ka faɗa ya ɗaga mani cikin wani salo yake cewa "Ohh nima haka akece mani in kawo ki nan" Gate kusan nawa muka wuce, sai nake ganin kaman masarauta ce inda muke nufa, domin na fara ganin wasu mutane masu kama da dogara wa, kuma duk Gate ɗin da muka wuce sune ke tsaron Gate ɗin. Na yarda shima Baisan komai a kai ba. Ban ƙara mamaki ba, saida naga mun shiga wata damfareriyar masarauta mai matuƙar kyau da ƙawatuwa tin daga waje. Inda aka tanada wajen yin parking nan naga mun dosa. Saida mukayi parking ne ya fito, ya zagayo yana mai ɓalle mani murfin motar. Wasu gungun mata ne sanye da wani irin kaya iri guda mai kalar ruwan omo, sai maza masu sanye da kalar kayan suma. Sannan dogarawa da kuma wasu gungun dattaw amasu ɗauke da rawani a saman kansu da babbar riga. Tako wa muka fara yi a hankali muna nufar inda mutanen nan ke nufi mu suma. Suna ƙarasowa naji an yafa mani wani abu tin daga kaina har ƙasa, ina dubawa naga Alkyabba ce, kallo na na maida kan Ya Ameen da yaje ta faman gaisawa da mutane, kaman dama cen ya sansu, ko ma ya sansu ɗinne oho? "Ranki ta daɗe, barka da ƙarasowa" Naji suna ta faɗa, lokaci guda kuma wata tana mai kamo hannuwa na ta nufi wani sashen na gidan dani. Da kallo nake waiwayar Ya Ameen da naga suma mazan suna ta mashi biyayya, sun nufi wani sashe dashi na gidan. Inda aka shigar dani dai kaman fada, a yanda na lura. Wata mata ce dattijuwa ta taso da kanta ta tare ni, tana mai rungume ni tsam cikin jikin ta, mun daɗe a haka, sannan ya sake ji tana mai cewa "A kai ta ɗakin Gimbiya Merama domin ta huta tayi wanka" Haka suka kuma hana zuwa wani ɗaki mai masifar kyau, an gaya ko ina sai ƙamshi yakeyi, tunani nake ta faman yi, nan ina ne aka kawo ni? Me ya Ameen da Umma suke nufi ne to? Wasu haɗimai ne suka kuma shigowa da tulinbkaya a hannun su, sai kuma akwatuna na nakaya, suna fita wasu suka shigo ɗauke da wasu irin manya manyan ƙwarya cike da kayan marmari a cikin su. Wata baiwa ce ta ƙara so inda nake zaune turus duk mamaki. "Ranki ya daɗe, an kammala haɗa ruwan wankan, ki taso muje in nuna maki" Ba ce ƙala ba, na miƙe ina mai nufar inda take bi, wani ɗan saƙo ne a cikin ɗakin. Muna binshi muka isa wani haɗaɗɗen toilet, an haɗa ruwan wanka cikin baho sai tashin ƙamshi suke yi da tururi. "Kiyi wanka Ranki ya daɗe, Fulani na nan shigowa da kanta zuwa gareki" Da mamaki nake binta da kallo. "Nan ina ne wai?" Abunda na ita furta mata kenan. "Masarutar Mai martaba Muhammadu Bello Barkindo Lamiɗo" Abunda ta iya faɗa mani kenan ta juya tana mia russunawa gareni ta fice. Na gaji sosai, haka na shiga kwaɓe kayan nayi wankan, sai tashin ƙamshi nakeyi, ina fitowa na tadda kaya ajiye saman gado, da kuma kayan shafa masu masifar kyau jere bisa mirror ɗin dake ɗakin. Komai akwai a kayan da aka ajiye mani, hatta da eaner wears akwai. Haka na koma banɗakin na saka kayan. Kaya ne irin na sarauta sosai, sarauta ma kaman ta Fulani, domin kayan saƙi ne irin na kayan Fulani, saidai waɗannan an zamanantar dasu, sai walwali sukeyi. Gaban mirror ɗin na koma ina mai shafa mai, sannan na koma bisa gado na zauna, ina mai ɗaukar Apple ɗaya na fara ci. Wayata da ke ajiye gefe na ɗauko ina mai latsa number ɗin Ya Ameen. Saida ta kusa katse wa ne ya ɗaga. "Am sorry ina wanka ne wify" "Yaya ina ne ka kawo ni nan?" "Ina na kawo mu dai zaki ce?" Ya faɗa shima da ɗan murmushi. "Eh Yaya" Kina Jihar Adamawa my Wife, ki kwantar da hankalin ki, zasuyi mana bayani, kina gidan girma ne anan" Ya faɗa yana mai goge jikin shi da ƙaramin towel dake saman kanshi. "Yaya Nifa tsoro nake ji" Bai kia ga bani amsa ba, naga haɗimai na shigowa tare da wata mata, suna mai sunkuyawa gareta cike da girmamawa. Nuni tayi masu da hannu akan su fita. Ba musu suka fice sun amai nuna biyayya gareta. Samun wajen zama tayi ta zauna. "Maraba da Gimbiya mau Sunan mai babban ɗaki, ɗiya ga Gimbiya Gimbiya Merama hasken masarautar Adamawa" Duk cikin kalaman ta ban iya tsintar ɗaya ba na fahimta. Da kallo nake kuma binta, saidai na Gaza cewa komai sai "Ina yini?" "Barka da wannan lokacin Gimbiya Suhan, nasan zakiyi mamakin ganin ki anan wajen, ki kwantar da hankalin ki, ke ba baƙuwa bace a nan gidan, duk da nasan ba lallai ki fahimci komai a sannu ba, Amman ina so ki sani, ya zama wajibi ki saki jikin ki damu, nan shine inda zaki zauna har zuwa lokacin ɗaurin auren naki" Toh fa! Nan zan zauna kuma? A hankali na ɗaga kai ina mai kuma kallon ta. "Nan shine gidan su Mahaifiyar ki Gimbiya Merama kaltingo" Waro idanu na kuma yi. Tau fa, sunan Umman tawa Maryama shine ta koma Merama kaltingo? Ganin mamaki shimfiɗe a saman fuska ta, ya sanya ta sakin wani ɗan murmushi. "Kada ki damu jiƙa ta, ki saki jiki ki huta, yanzu za'a shigo maki da abinci, kici sosai kafin mai martaba ya shirya ganawa daku, keda angon naki" Abud ata faɗa kenan, ta miƙe a hankali, tana mai tattare Alkyabba sannan ta fice daga ɗakin. Da kallo na shiga binta, kwanya ta gabaki ɗaya ta cushe. Nan ne Gidan su Umma kuma? Haba tayaya za'a ce haka? Bayan nasan Umma ta ƴar aiki ce a gidan su Suhan? Tayaya za'a ce ƴar sarki ce taje tana aikin bauta a wani gida, Ummata da gatan ta, ba zata taɓa iya tsallake wannan daular taje tayi zaman ƙas-ƙanci ba. Wayata na jawo ina mai latsa number ɗin umman. Biyu biyu ma nake gani, jin kaina nake kaman zai tarwatse, sai numfashi nake fiddawa akai akai, na ras ama tunanin da zanyi. Na kira ya kai sau goma Amman bata ɗaga ba. A hankali na miƙe daga zaunn, na fara safa da marwa cikin tanƙamemen ɗakin, wand a ake ta faman bi da kallo, hannuwa na goye bisa bayan nawa. Wai wace irin rayuwa ce nakeyi haka NI Suhan? Da farko ƴar aiki? Sai ƴar makaranta? Sai wadda aka sama biki da namiji ɗaya tamkar da dubu? Sai kuma wai Gimbiya Suhan ɗiyar Gimbiya Merama? Wasu mata ne nagani sun kuma shigowa ɗauke da kayan abinci. Basu ce ƙala ba, illa sunkuya mani da sukayi, suka shiga her kayan abincin gabana. Suna ficewa na sake ɗauko wayar na kira Layin yaya. Yana ganin kiran ya saki murmushi yana mai amsawa. Shi fa duk a zaton shi, Dad ne ya sanya a kawo ni nan, saboda wani dalili nashi. "my Wife" Abunda ya iya faɗa kenan. "Yaya ban fahimce su ba Sam, suna faɗ aman wasu maganganu masu rikitarwa, kayi mani bayani yaya, me ka sani game d anan gidan?" "Look sweet janam, ki kwantar da hankalin ki, yanzu zamu gana da mai martaba, shine zaiyi mana dukkanin cikakken bayani, ance yanzu za'a mana iso wajen shi,kici abinci please" Yana gama faɗar haka ya datse kiran. Bazan iya cin komai ba. Jina nake kaman wata mahaikaciya. Bayan kaman rabin awa ne, har na kammala salla ta, sai ga wasu bayi sun shigo, cike da girmamawa suke faɗin "ran gimbiya ya daɗe, mai martaba na son ganin ki" Ban masu musu ba na miƙe, ina mai yafa gyale na, dakatar dani suka yi, suna mai yafa mani Alkyabba. Babban gida ne masha Allahu, ya gaji da haɗuwa, kaman ba masarauta ba da aka sani da ginin ƙasa. Duk inda muka gitta kallo na ake tayi. Oho masu, koma dai minene na ƙagara inje wajen mai martaba en domin ya fidda ni a duhu. Wata ƙaramar fada ce aka shiga dani, jakadiya ce tayi mani iso har cikin faɗar, sannan ta kwashi gaisuwa tana mai juyawa. A cen na tadda Ya Ameen zaune tankwashe da ƙafafu, jikin shi sanye da wata shaddar an mata ɗinki da aikin sarauta ko ina a jikin ta, yayi matuƙar kyau, Amman dayake hankali na ya kasu gida biyu, sai ban damu da kyaun da yayi ba. Wuri na samu gefe ina mai zama, cike da girmamawa na ce ma mai martaba "ina yini?" "Barka da wannan lokaci mai babban ɗaki" Shima mai babban ɗakin ya kira ni. A hankali na ɗaga kaina, ina mai duban shi, ya man kwarjini sosai. Sadda kaina ƙasa nayi, daidai lokacin da na tsinkayo muryar shi yana mai faɗin "Barka da dawowa gida Gimbiya Suhan ɗiya ga Gimbiya Merama hasken masarauta" Cikin ɗan zaro idanu na kuma ɗagowa nima ina mai kallon shi. Murmushi ya saki, sannan ya nisa ya cigaba da cewa "Nasan baki sani ba, nasan mahaifiyar ki bata sanar dake komai ba, kaman yanda ta shaida mana, saidai muna so ki sani, nan da kika gani gidan su mahaifiyar ki ne, watau umman ki, kuma zaki cigaba da zama tare damu ne har zuwa lokacin ɗaurin auren naku" Ai fitsari ne kawai ban saki ba, Amman shima kaɗan ya rage, a tare muka zaro idanu da ya Ameen ɗin da shima tinda mai martaba ya fara magana yake sauraron shi. "Nan kuma gidan su Umma kuma? Dama Umma ƴar sarauta ce? Amman taje tana aiki a gidan nasu tsawon lokaci? Me yaja mata? Menene dalilin ta nayin hakan? Gimbiya Merama? Shine sunan da duk lokacin daya kawo ziyara masarautar yake ji suna yawan ambata, dayake duk idan zai je IDPs camp sai ya fara kawo gaisuwa masarautar kafin nan yake wucewa, wannan ce ta sanya sun sanshi sosai matuƙa, kuma masarauta tana yaba mashi haɗi da jinjina ma namijin ƙoƙarin shi. "Tanka ya daɗe Ummata ta faɗa mani bama da kowa, bama da dangi duka sun mutu" Ya tsinkayo muryar ta, tana faɗa cikin rawar murya, kaman zata saki kuka. "Ta shaida maki haka ne, a bisa wani dalilin ta, wanda sai nan gaba ne zamu ji shi muma, Amman ki sani Umman ki kuwa ita ke da kowa, ita ke da gata, ita ke da asali, sannan kema kina da asali mai kyau, kuma mu nan da kika gani duk ƴan uwan ku ne, domin haka ki saki jikin ki damu, nan gidan ku ne" Ba ni ba har Ya Ameen ya matuƙar kaɗuw ada jin wannan kalaman da suke fita daga bakin Mai Martaba, daga ni har shi ɗin kowa da abun da yake saƙawa a ranshi. A hankali na ɗago ina mai maida kallo na saman fuskar Ya Ameen ɗin. Girgiza mani kai ya shiga yi kada inyi kuka , ganin kwallar da ta taru a idanun nawa, wanda na Gaza riƙe su,sia faman shatata sukeyi. Ya ba zanyi kuka ba? Tsawon wannan lokaci ina tambayar Ummana akan asalin namu da dangin namu, bata taɓa shaida mani ba, sai yau kwatsam ace in tsinci kaina cikin su? Wani irin kuka na ɓalle dashi, ko a haka ya Ameen ya barni ya gama mani komai, ya yarda zai aure ni ba tare da sanin ko ni ɗin wacece ba, ba tare da sanin cikakken asali na ba, ba tare da yarda da huɗubar mahaifiyar shi a kaina ba, ya tallafi rayuwa ta, ya tallafi ta mahaifiyar ta, ya tsaya akan karatu na, ya tsaya akan lafiyar Umma ta, yau sai gashi shine da kanshi ya ɗauko ni yana mai sada ni da dangi na, zuri'a ta alhali na, irin wannan family mai ɗinbin daraja. Nikau da me zan saka ma Ya Ameen dashi wanda ya wuce soyayyar da nake mashi a yanzu. Ba wanda yayi yunƙurin hana ni, kaman yanda suke iya hangen irin raɗaɗin da zuciya ta keyi mani, da irin halin da nake ciki saman fuskar tawa..... Shi kau Ya Ameen runtse idanun nashi yayi, yana mai sauraren kukan nawa dake ta ratsa mashi zuciya,sai yanzu Kunyar Abunda Mom ɗinshi keyi ya shiga bashi matuƙar kunya, a hankali ya shiga jinjina kanshi yana mai hamdala da jin wannan kalaman daga bakin mai martaba, lallai Allah gafurun raheem ne, mai samrr da akwai daga babu, mai samar da babu daga akwai, ya fidda matacce daga rayayye, ya fiddabrayayye daga matacce, mai amshe kuɗi dukiya mulki ya ba wanda baya dashi, mai ba wanda baya da komai mulki da dukiya, mai maida sarki bawa, ya kuma mayar da bawa sarki, wanda bashi da abokin tarayya sai shi kaɗai, azzawajalla..... *Kuyi manage, walh bana da chaji* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'ar Saduwa Da Iyali: بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا. Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana. Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~60~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Kuka na nake saki bil haƙƙi da gaskiya. Mai martaba da kanshi ya taso zuwa gareni, haɗi da sanya hannuwan shi ya ɗago ni yana mai rungume ni cikin jikin shi, tabbas ko ba'a faɗa ba, irin kukan da nake yi, yasan rayuwa tayi walagigi dani, ko ba komai ya sha alwashn duk wanda yake da sanya hannu a wannan manaƙarƙashiyar ba zai taɓa ƙyale shi ya tafi hakanan ba. Rarrashi na ya shiga yi, har yanzu ya Ameen na durƙushe saman ƙafafun shi, dana buɗe idanu shi nake hange yayi kasaƙe yana kallo na, wuyan shi a karye, dukkanin natsuwar shi ya ɗora ta a kaina. Mahaifiyar shi, ita kaɗai yake hangowa, irin Kunyar da zata kwasa, muddin taji wannan al'amari, saidai koma minene shi yayi imanin farin cikin da yayi ya zarce kaso ɗari cikin ɗari. A hankali na tsagaita da kukan nawa, har bisa kujera mai martaba ya kai ni yana mai zaunar dani. Da hannu yayi ma Al'ameen alamu da shima ya koma bisa kujerar ya zauna. Nayi mamakin ganin ya doso inda nake zaune ɗin. Daf dani ya zauna, yana mai riƙo hannu na wanda yake kusa dashi, cikin nashi, yana mai ɗora su bisa kujerar ta yanda mai martaba da yake gefen mu zaune ba zai iya gani ba. A hankali ya shiga murza yatsun nawa, alamun lallashi. Ni kau sai faman jan majina nakeyi. Farin ciki da wani irin yanayi sun haɗu sun tattare mani wuri guda. Sake bani haƙuri mai martaba yayi, sannan ya miƙe yana mai faɗin "Ku sake tattaunawa, domin dai ita mai babban ɗaki ba zata koma cen ba kuma, har sai an ɗaura auren. Da kallo muka bishi, muna mai faɗin" a fito lafiya" Yana ganin shigewar shi yayi saurin juyowa gareni, yana mai zamowa daga bisa kujerar da yake zaune bisa ƙafafun shi ya durƙuso sosai. Dukkanin hannuwan shi yayi amfani dasu wajen taffo fuskar tawa. "Kukan na menene uhumm? Ke da zakiyi farin ciki?" Ya faɗa a tausashe, cikin alamun lallashi da tausaya wa. Wasu hawayen ne suka sake malalo mani "Yaya menene dalilin Umma nayin haka? Ashe muna da asali Umma take ta faman ɓoye mani tuni?" Da wani irin yanayi yake kallo na. "Suhaaann" Ya ambaci sunan nawa bisa laɓɓan shi, kaman bai taɓa furta sunan ba a yanda Naji haruffan sun zauna a bakin nashi, kuma yana furta su yadda ya dace. "muyi ma Umma uziri, haƙiƙa dole akwai wani abu dake faruwa, koma muce ya faru ɗin, zamu so jin ta bakin ta, kaman yanda Mai martaba ya faɗa, saidai ba a wannan lokacin ba, sanin kanki ne, idan akace yanzu ne za'ayi maganar, to fa wani abu na iya ɓullowa da ka iya kawo cikas a auren namu, muyi haƙurin bayan ɗaurin aure, ke kuma na yarda na amince ki cigaba da zama anan, saidai ina so kafin in wuce gobe mu tattauna abubuwan da kike da buƙata, da kuma yanda hidimar bikin zata kasance, kuma zuwa gobe ina so kafin in wuce ki raka ni sansanin ƴan gudun hijira, domin in bayyana ki garesu, a matsayin wadda zan aura, kaman yanda suka zame mani dangi" Da jajayen idanu na nake kallon shi. Wane irin mutum ne ya Ameen ɗin? Haƙiƙa ko tantama babu nasan nayi dacen samun abokin rayuwa, ina mai gode ma Allah akan wannan baiwa da yayi mani, ni Suhan ashe da gata na? Ashe zan mori rayuwa da jin daɗin rayuwa anan gaba? Hannuwa na na sanya ina mai sauke hannuwan nashi daga tallaffo fuskar tawa, mai makon in saki hannun, sai na sake runtse su cikin nawa. "Yanda kace haka za'ayi Yaya, ina mai alfahari da samun ka da nayi a matsayin miji na, kuma uban ƴaƴa na, ina mai godiya ga Allah da ya nuna mani wannan ranar, haƙiƙa rayuwar da nayi a cen baya ta zame mani darasi, na koyi abubuwa da yawa daga ciki, na gode da jajircewa da kayi a kaina, ba dare ba rana, ka soni duk kuwa da cewa kasan ko ni ɗin wacece sannan.... " " Shiiiiit" ya faɗa yana mai zare hannun shi guda ɗaya ya ɗora shi saman bakin shi, alamun inyi shiru. "Suhan kece rayuwa ta, na daɗe ina dakon sonki ba tare da na sani ba, ki taimaka ki tallafi rayuwar bawan Allah Al'ameen" Murmushi nayi, yanda ya furta kalaman yana wani karyar da wuya, sai ya bani dariya. Ganin na murmusa ne ya sanya shi sakin wata wawuyar ajiyar zuciya. Miƙewa yayi tsaye, yana mai kamo hannuwa na nima na miƙe,, da yatsa yake ɗauke mani sauran hawayen da suka idasa gangarowa, wanda ya zuwa yanzu na tabbata na farin ciki ne. "Muje ko? Ki samu ki kwanta ki huta, da wuri nake son wucewa, akwai abubuwan da nake son aiwatarwa acen goben, sai ki shirya da wuri, sannan zan rubuto maki programme ɗin da za'ayi, sai ki duba ki gani idan yayi, kinji sweet heart" A hankali muka shiga taka wa, har ƴar ƙofar da zata sada ni da cikin gidan, inda ya ja ya tsaya yana mai kallo na cike da ƙauna, sadda kaina ƙasa nayi, har yanzu duk da nasan ko ni wacece ɗin, sai nake ganin kaman Ya Ameen ɗin yafi ƙarfi na, shi mutum ne mai kwarjini da cika fuska, ko kyawo da gayun shi zasu sanya ka kasa samun natsuwa in yana wuri. A hankali ya sake dukkan hannuwan nawa, yana mai furta "Good night dear, sleep tight janam" A hankali ya shiga steeping back, yana mai ƙallo na cikin shauƙin ƙauna, ni kuma sai na kasa sauke hannuwan nawa ƙasa, ji nake kaman sun fara maraicn tafukan hannayen nashi masu taushi. "Yaya programme ɗaya ya isa please, dinner kawai za'ayi please" na furta cen Ƙasan maƙoshin. Cak yaja ya tsaya, sai kuma ya kafe ni da idanu. "Hakan yayi maki?" "eh" na faɗa ina mai ɗaga kai sama a hankali. Hannuwan shi ya ware, sannan ya ɗan sara mani "Consider it done ran gimbiya ta ya daɗe" Murmushi na sakar mashi mai ƙayatar wa, ina mai faɗin "tare da kai *Yariman Matasan Arewa* " Ai sai naga ya saki murmushi yana mai sake kallo na cike da shauƙin farin ciki. "Dama kina sane ko murna ma bakiyi mani ba?" Ya faɗa shima yana mai sake takowa zuwa gareni. Daf dani ya kuma ja ya tsaya, daidai lokacin da nima na wara kwayar idanu na cikin tashi na shiga cewa "ai ba kai ne ka sanar dani ba, Kaga baka buƙatar murna ta" sannan na kaɗa kwayar idanun tayi wani far haka. "ah haha" ya saki wata irin dariya mai ƙayatarwa, har dukkanin kuma tun shi suka loɓa ciki. Da gani na so kashe shi da farin da nayi da ida nu na A hankali ya cije lips ɗin shi da suke Light pink. Kasaƙe nayi ina mai kallon shi yana ta sakin dariya. Ya ƙayatar dani, komai Ya Ameen yayi kyau yake mashi, shi mutum ne mai salo ba tare ma da yasan yana yi ba. "Lokacin ai kina Suhan ƙanwa ta" "A'a Yaya, lokacin ina..." Katse ni yayi cikin kamo hannuwa na still "Suhan please ki dena tuna rayuwar ki ta baya a gidan namu, sanin kanki ne cewa ina baki kariya da dukkan iyawa ta, tun a lokacin bana so ko hakki ya tsire ki, saboda yanda nake jin zafi a lokacin, saidai na kasa yarda ma kaina cewa soyayya ce, saboda nayi imanin soyayya ƙarya ce, ashe bansan kuskure ne nake tafkawa ba, ba yanda Bilal baiyi ba wajen fahimtar dani, saidai na Gaza gazgata shi, yau gani gaban ki ni Muhammad Al'ameen Almustapha Dambulan da ƙoƙunan bara ta, a taimaka a cika man su taf da soyayya, nayi alƙawarin sake inganta rayuwar taki iyakar iyawa ta" Ɗan murmushi na saki, ina mai faɗin "Soyayya dai ka samu, saura mai soyayyar" nima na furta a hankali, cike da wani yanayi na soyayya, gani nake kaman ba Ya Ameen ba, ashe miskilai haka suke muddin suka faɗa tarkon so? Hannun nawa ya kai zuwa bakin shi, yana mai sumbatar su a hankali, ya daɗe bai ɗago da fuskar shi ba daga sumbatar, sai kuma ya saki a hankali yana mai faɗin "I am going to miss you dear, take care" yana gama faɗin haka ya juya cike da murmushi cikin salon tafiyar shi, har zuwa ƙofar da zata sada shi da ɓangaren da aka sauke shi ɗin. Da kallo na raka bayan nashi, har zuwa bakin ƙofa da ya tsaya ya buɗe kofar yana mai waiwayowa ya bani wani irin peck sannan ya shige yana mai ɗaga mani hannu. Da kallo na shiga bin hannun nawa da ya sumbata, wanda na Gaza sauke su ƙasa, sai kuma na saki dariya, ina mai ɗan girgiza kaina a hankali na duƙa na shige cikin gidan. Ina fita naga wasu bayi sun kai su biyar, da sauri suka ƙaraso gareni, suna mai faɗin "ran Gimbiya ya daɗe, uwargijiyar mu Fulani ce tace mu raka ki ɗakin ki, kuma mu zauna tare dake har zuwa wani lokaci" Da kallo nake bi su ɗaya bayan ɗaya "Oh ni Hauwa'u, wai yau nice ake ma biyayya da durƙusa mani, yau nice tare da masu mani hidima, bayan ada nice mai yi ma wasu, rayuwa kenan na baya ya koma gaba" na furta a cikin zuciyar tawa. A zahiri kuma Fuska na saki ina mai cewa "to muje ko?" Na wuce gaba suna biye dani, saidai da suka lura ban san kan gidan bane, ya sanya wata wucewa gaba su kuma sauran suna biye dani a baya, suna gyara mani zaman alkyabba ta. Ko da muka isa ɗakin, na tadda har an sake gyara ko ina tsaf, an kuma haɗa mani ruwan wanka masu masifar ƙamshi, ce mani sukayi zasu zauna falo su jira ni, idan ina buƙatar wani abu inyi magana. Ko da na fito wankan, na tadda har an kwashe kayan da na cire an ajiye mani wasu na bacci. Ban ɓata lokaci ba na sanya, ina mai hayewa gado, sai bacci, dama ga gajiya na kwaso da yawa, zuciya ta cike da saƙe saƙe. Washegari tun da asuba suka shigo suka tashe ni inyi sallah, tin dai da nayi sallar na koma na kwanta ba'a kuma tashi na ba, sai da na gaji na tashi, a ɗan firgice nake, saboda na shafa'a shaf da yaya yace in shirya da wuri. An kuma haɗa mani ruwan wanka na shiga nayi, su ɗin dai ne suka kuma fiddo mani wasu kayan, ba irin na jiya bane, suma yau hadda alkyabba, su suka taimaka mani na shirya, abincin da suka shigo mani dashi ma sama sama naci shi, ina mai cewa su kai ni wajen Fulani in gaida ta, sannan su kai ni Fada wajen mai martaba. Haka kuwa akayi, saida na gaida Fulani, cike da ƙauna ta amsa mani, tana hakimce komai haɗimai ne keyi mata, matar ta burgeni matuƙa, tana yi mani kama da wata wadda na sani, Amman na Gaza gane ko wacece ita. Haka aka kakkaini sauran sashen matan sarkin, duk mun gaisa ba yabo ba fallasa, sannan ne jakadiya tayi mani iso zuwa faɗar sarkin, inda duk an taru ana ta fadanci. Daga nesa na durƙusa ina mai bada gaisuwa, kowa sai kallo na yake cike da al'ajabi, masalan da mai martaba ya sanar dasu ko ni ɗin wacece. Nan fa suka yi ta sanya mani albarka, da tofa albarkacin bakin su. Ban ma kula da Ya Ameen dake zaune gefen sarkin ba, cikin shiga ta sarauta, kaman wani ɗanɗan sarki, sai naga ya mani kyau, ya kuwa tsare ni da idanu, yana ta faman yi mani murmushi ta ƙasan fuska. Ba wanda ya kula da Abunda yakeyi. Sallama mukayi da mai martaba akan cewa zamuje mu dawo, sanin ko ina zamu ɗinne ya sanya shi sanya mana albarka, sannan ya bada mota biyu ta dogarai cewa a raka mu zuwa wurin, sannan ya haɗa mu da wasu hakimai guda biyu, manyan mutane. Ni da Ya Ameen a motar shi muke ciki, wani dogari ne ke tuƙawa, sai mota biyu bayan tamu, da ta hakimmai, sai ta dogara wa, yayin da wata ke gaban mu ta dogarawa. "kinyi kyau wife" abunda ya faɗa kenan, bayan ya daidaita zaman shi cikin motar. "Thanks and barka da safiya Yarima" na faɗa ina mai sauke kai ƙasa Da mamaki yake kallo na, kenan har na fara iya kalaman masarauta? "Da fatan kin tashi lafiya Gimbiya ta?" A hankali na ɗaga mashi kai ina mai cewa "kaman yanda yarima na yake" Murmushi ya saki, yana mai cewa "Yariman ki yana cikin ƙoshin lafiya, masalan da ya tsinci kanshi a gidan su gimbiyar tashi" Jinjina kai na kuma yi, ina mai sakin ɗan murmushi, a hankali na ɗauke kaina ina mai maida shi bisa titi, yanayin garin nake kallo cike da ban sha'awa, shima a hankali ya shiga nuna mani wurare, kaman dama cen nan ne garin nasu. Mun ɗan yi tafiya mai nisa naga mun iso wani tafkeken gareji, sojoji ne da ƴan sanda, tare da wasu irin kaki da na rasa gane su, ganin ko daga ina ake ne ya sanya suka wangale mana gate muka shige. Kai tsaye Office ɗin shugaban su muka nufa, bayan Ya Ameen ya buɗe mani ƙofa na fito, da wani dogari ne zai buɗe mani, sai Ya Ameen ɗin ya hana ta hanyar dakatar dashi da hannu. Babban Office ne mai kyau, cike da girmamawa aka karɓemu hannu bibbiyu, a take aka cika mana gaban mu da abubuwan sha, ba wanda yabi ta kansu, dayake yarima ba baƙon su bane, su kansu sunyi murna da zuwan nashi, domin sun san duk lokacin da ya kai irin wannan ziyarar ta bazata, asusun nasu na lamusar wani kaso mai tsoka a cikin dukiyar *Yariman Matasan* Bayan ƴan gaishe gaishe, cike da mutuntawa, masalan ma da muke tafe da manyan mutane da zasuyi sa'anni da su Dad, a gaggauce ya gabatar masu dani. Nan suka shiga yi mana murna, hadda kawo mani wasu ƴan kyaututtuka, a lokacin ne yake mai buƙatar su da su sanar dashi buƙatocin su. Bayan sun gama tattauna wa ne, a take yayi masu trnsfer na dukiya mai yawa, ko ni da naji saida na girgiza, ashe Ya Ameen yana da ɗinbin dukiyar da har zai iya sa daukar da wannan kaso ɗin a ciki ba tare da ya ko girgiza ba. Sannan ya buƙaci da akai mu wajen ƴan gudun hijirar. Nan fa aka fara bada sanarwar su fiffito ga *yarima nan ya zo duba su* aiko sai gasu suna fiffitowa ta ko ina. Tuni aka zagaye mu, da muke tsaye cikin wata rumfa, domin Yariman yace ba zama zaiyi ba yana sauri ne zai wuce. Daddaɓe shi sukayi suna ta kai mashi gaisuwa cike da jin daɗi, yayin da ya shiga ɗaɗɗaga yaran dake so ya ɗaga su, da gani ya sabar masu da hakan, da alamu baya ƙyamatar su, suma sun fahimci hakan, da kallo nake binshi da nake tsaye cen baya, sun matuƙar burge ni, masalan Yariman nawa da yake da zuciya ta kwarai irin wadda ake so dukkan musulmi mawadaci ya samu. Nan fa suka shiga kai mashi koken su, duk da sun san cewa ko ba komai zasu kwashi tsawon kwana goma suna cin abinci mai rai da lafiya, harda shanu ake yankawa, duk lokacin da Yariman ya kawo masu ziyara. Kuɗi ya koma mota ya fiddo ƴan bandir bandir ɗin dubu dubu, nan ya shiga rarraba masu, sosai sukayi murna da jin daɗi, hatta da tsofaffin da suke kwance basa lafiya sai da ya shisshiga ya gansu, suma ya masu alheri mai yawa, sannan ya buƙaci da a kira likita zasuyi magana dashi. Koda likita yazo sun tattauna abubuwa masu yawa, ciki harda kai marasa lafiyar zuwa asibiti mai kyau, da kuma zasu ɓullo da har kar samar da magunguna kyauta ga mazauna sansanin, muddin rashin lafiyar bata yi tsanani ba. Sannan yana so zai gina masu asibiti mai rai da lafiya, zai ɗauki ma'aikatan da zai dinga biyan su albashi cikin aljihun shi, tare da kawo waɗanda zasu dinga koya masu sana'o in hannu ga masu buƙata, domin dogaro da kansu. Aikau kaman su rungume shi, saboda tsabar murna, wasunsu kuka suke yi, Abunda nima ya ƙaryar mani da zuciya kenan na shiga rera nawa kukan, Allah na gode maka, Allah na tuba, rayuwar da nayi sai nake ganin babu wanda ya kai ni shan wahala, ashe akwai waɗanda suka fini, wasu an kashe masu mazaje, wasu sun rasa ƴaƴan su, wasu sun rasa iyayen su. Kuka nake rerawa mai cin zuciya. A hankali ya shiga takowa zuwa inda nake tsaye, ba wanda ya kula da kukan da nake ta faman yi ma, su kansu fadawan hankalin su ya ɗauku wajen rage cunkoson mutanen dake son kai hannun su ga jikin Ya Ameen ɗin da har suna mai neman kada shi, jikin shi kuwa yayi futi futu, masalan ma ƙafufun nashi dake sanye cikin takalma masu lanƙwasar kalar na sarauta. Amman haka yake daurewa yana ta sakin murmushi yana raba masu kuɗi. Tabbas zuciyar Ya Ameen mai kyau ce, yana da imani sosai, ga tausayn na ƙasa dashi, tin fara soyayya ta dashi, ban ci karo da Abunda ya ƙara sanya ni alfaharn samun shi a matsayin mijin nawa ba kaman yau. Tausayin su ne ya kama ni, ashe ni ina cikin aljanna ne, ko ba komai zanyi aikin da za'a biya ni, kuma a cida ni, zan ɗinka ma kaina sutura, su kau wasunsu yagaggun kaya ne jikin su, wasu ma kusan kana kallon tsuraicin su, ga rashin ruwa, wasun su yunwa duk ta busar dasu, ga ƙazantar makewayi, "Ya Allah Na tuba Allah ka yafe mani" Abunda nake furtawa kenan, har zuwa lokacin da naji ya rungume ni yana lallashi na, ai sai na sake sakin wani marayan kukan, "ya Ameen sun bani tausayi, don Allah ka cigaba da taimaka masu" Abunda nake furtawa kenan cikin kukan nawa. Gyaɗa mani kai ya shiga yi, yana mai ɗan bubbuga baya na, cikin shigar lallashi."I promise u my wife" Tsaye sukayi suna mai kallon mu. Ganin hakan ne ya sanya shi bayyana masu cewa nice wadda zai aura. Nan fa wuri ya sake ɓarkewa da hayaniya, ƙoƙarin ƙarasowa suke inda nake tsaye su taɓa ni. Ban hana su ba, kaman yanda shima bai hana su ba. Wata yarinya ce ta ruga sosai zuwa jiki na, tana mai faɗin *Inna jaki tafi dani gidan ki?* Tausayi ta bani, zuƙunnawa nayi sosai na ɗago ta zuwa saman kafaɗa ta, ba zata wuce shekara uku da rabi ba. "Ina maman ki?" Na tambaye ta. "Bana da Mama" Ta furta cikin maganar da bata ida kwarewa ba. Da kallo na bi sauran matan dake tsaye gefe, gyaɗa man kai sukayi suna kai shaida mani wani hari da aka kai ƙauyen su Bomb ya tashi da Mamar tata, ita kaɗai ta tsira a gidan. Kayan dake jikin yarinyar sun yi dauɗa duƙun duƙun, ga zarni haɗi da wani irin wari dake tashi daga jikin yarinyar, kaman zanyi amai, haka na daure na rungume ta ina mai sake sakin wani kukan. "ya sunan ki?" "yaaagana" Ta furta itama a hankali, tana ta zaro idanu, ganin bata san me nake ma kuka ba, lokaci guda ta shiga ƙoƙarin sauka tana faɗin "kiyi haƙili Inna bansan zakiyi kuka ba, nima kullum sai nayi, saboda Mamana bata nan ba mai bani haƙuli" Ai bansan lokacin da na kuma rungume ta ba tsam tsam a jiki na, har yanzu kuka nakeyi, Amman mara sauti, kuma har yanzu ɗin ya Ameen yana tallafe dani a jikin shi. Ajiye ta nayi ina mai zaro kuɗi a jikka ta, na shiga cewa "Wa zan ba amana, kullum a siya mata wani abu mai ɗan daɗi taci?" Nan fa aka fara turereniyar cewa "Ni, ni ni zaki ba hajiya" Wata mata dake tsaye cen baya, duk abun nan da akeyi bata ko motsa ba, tayi shiru, ga dukkan alamu akwai Abunda ke damun ta sosai. Ita na yafito da hannu. Damƙa mata kuɗin nayi ina mai cewa "gashi ki ajiye mata, don Allah ki kula da ita sosai kafin in dawo" Sannan na zuƙunna na riƙo hannun ta ina mai Damƙa ta ga matar nake ce ma Yaganar "ga Maman ki nan daga yau, zata dinga kula dake, zan dawo in tafi dake kinji?" Cikin murna da tsalle take ta cewa "yaaaa nima znaci bickin kaman su Baba gana" A hankali Ya Ameen ya janye ni, ganin ina shirin sakin wani kukan, nan mukayi masu sallama muka baro su cike da farin cikin kuɗin da Ya Ameen ya basu, ya sanar dasu cewa su kiraye shi nan da kwana biyu, domin cika masu alƙawurran daya ɗaukar masu. Ko a cikin mota kukan nake yi, tabbas yau zuciya ta ta sosu, imani da tsoron Allah ya ƙara kama ni, ban taɓa sanin haka sansanin ƴan gudun Hijira yake ba sai yau, duk da gwamnati na iya nata ƙoƙarin, Amman wasu ne suke samun na abinci a wurin, suna sama da faɗi da kusan duk wani taimakon da zai je masu, masalan na ƙungiyoyi masu zaman kansu. Lallashi na ya shiga yi, yana faɗin in da yasan haka zan kasance da bai je dani wurin ba. Nan nake roƙon shi da ya taimaka ya ƙara sama masu da ruwan sha ɗana amfani, ya ƙara masu yawan makewayi. Da kai ya shiga amsa mani, cikin shigar lallashi Haka muka koma masarauta, duk yanda yaso ganin walwala ta, saidai kaɗan. Mai martaba ya yaba mashi, ya jinjina mashi, fada tayi alfahari da samun suruki kaman shi, masalan da labarin abun alherin da yaje yayi masu ya iso kunnen mai martabar tun ma kafin mu dawo. Haka mukayi sallama dashi yana mai ƙara bani haƙuri, Baisan haka nake da kararriyar zuciya ba, da bai je dani ba, kuma tabbas yasan hakan ne, duk wanda yaje wurin nan sai imani ya kama shi, ko shi lokacin farko farkon da ya fara zuwa, gagara bacci yake yi, hakan ce ta sanya kusan lokaci lokaci yana hanyar zuwa wajen nasu, hakan ce ma ta sanya sukayi sabo har haka dashi. Duk da naji ba daɗi tafiyar tashi, Amman bana da yanda zanyi, idan da rabo dai yau saura kwana sha biyar komai ya kammala. Ko yaya Ummata take? Ina buƙatar fa in kira ta, domin jin lafiyar ta, haka na juya cikin gidan, baya na haɗiman da suke mani hidima ne biye dani. ********* Umma na zaune a falon nata ita da Hajiya Zainab suna kuma tattauna yanda abubuwa zasu kasance, basa so ko alama hidimar bikin nan a samu matsala, masalan ta ɓangaren hajiya Kubran, ita da so tayi ma ba zata yi taron komai ba, kawai zata tattara ta tafi gidan nasu kaman yanda Mai martaba sarki baffan nata ya buƙata. Hajiya Zainab ɗince ke ce mata aiinsha Allahu ba abunda zai faru ma, masalan yanzu da kowa idan yaji ita ɗin wacece dole ne a jinjina mata, kuma itama Hajiya Kubran matsalar asali ne ta fake dashi tana ta wannan hakan, to yanzu zata fasu kowa ma yaji. Umman saidai tayi murmushi, ta lura tin lokacin da suka fahimci ita ɗin wacece, wani girma na musamman suke bata, harda Dad kuwa, shi da yake ma mai gidan ta, shi kau ta ɓangaren shi wani girma da ƙimar ta yake gani, Sam ya kula abun duniya baya gaban ta, domin idan da yana gaban ta, ba zata taɓa tsallake masarautr tasu da take da ɗinbin girma da kuɗi ba. Suna tsaka da tattaunawa ne, mama Talatu tayi sallama. Karo na farko kenan da ta taɓa shigowa sashen Umman, domin suna jin tsoron Hajiya Kubra ta ga shigar tasu ta kore su, masalan Mama saude da take so ta shisshigi ma Umman, domin yanzu ta kula Alhaji yana matuƙar jin maganar ta. Gefe ta samu ta raɓe ƙasa, kaman yanda take yi sashen Mom. Da hannu Umma ta nuna mata bisa kujerar dake gefen ta. "Haba Talatu meye na zama ƙasa kuma? Ki zauna saman kujera mana" umman ta faɗa cike da girma. A hankali ta ɗan ɗosana. "dama masu haɗa kaya ne suka ce a sanar naku an kammala" Ta faɗa tana ɗan bin sashen da kallo haka kaɗan, cikin ran ta Allah kaɗai yasan me take rayawaa. "Kije ina zuwa" cewr Hajiya Zainab, domin ta kula Mama talatun munafuka ce, bata so take shiga hidimar Umman, domin yanzu ita ba sa'ar su bace, dama cen tsautsayi ne ya kai ta shiga cikin su munafukai suna ƙuntata mata. A hankali ta miƙe tana faɗin "to Hajiya a fito lafiya" Da kallo su duka suka bita, nisa wa Hajiya Zainab tayi, "umman Suhana sai fa kin kiyaye mutanen nan, kin san fa irin zaman da kika yi dasu, kuma ni nasan har yanzu akwai wani abu a cikin zuciyar tasu" "Ba komai Hajiya, ni da zuciya ɗaya nake zaune dasu, Allah na nan, kuma ba abunda suka isa suyi mana" ta faɗa itama cike da ƙwarin guiwa tana ɗan nurmusawa. Hajiya zainab ɗince ta miƙe tana faɗin bari inje wajen mutanen cen, domin Bilal ya fita tin ɗazu, kinga kuma ya kamata ace an sallama su kinsan nan da sati ɗaya ƴan kankiya zasu iso, to suma Alhaji ya bada kuɗin gyaran sashen nasu" Da to Umma ta bita, tana maida hankalin ta kan wayar ta da ta ɗauki tauwwa. Hajiya Khaltum ce. A hankali Umman ta ɗauka tana mai sakin murmushi. "Ran Hajiya ya daɗe" cewr Umma tana mai sakin dariya. "Wannan taku ce Umman Suhan, ya guda ya hidima?" "Duk lafiya lau wallahi, ya yara ya jama'a da su Eesher?" "Duk suna nan lafiya lau Umma, na kira ne akan maganar da mukayi dake, lokaci yayi da ya kamata in turo mai gyaran jiki ga amarya fa" Ɗan murmushi Umma taja tana mai cewa "Hajiya na maki laifi fa, gaskiya ai mamana ɗin ma tana nan garin ku, ba zata dawo nan ba ma sai an ɗaura aure" Hajiya Khaltum cikin mamaki take faɗin "kaddai kice Adamawa?" "Eh Hajiya nan Adamawa dai" Ɗan murmushi Hajiya Khaltum ta saki, tana mai cewa "shikenan kinga ma ta kwana gidan sauƙi, ki kwatanta mani kawai gobe sai muje da mai gyaran da kaina, kuma insha Allahu zuwa gobe kayan zasu iso, indai kina gida" "Ina gida Hajiya nagode Allah ya bada ladar zumunci, babu Abunda zan ce maki saidai Allah ya biya ki abinda kike mana, nagode, insha Allahu zan maki text ɗin address ɗin inda take ɗin" "To ba damuwa, ai ba godiya tsakanin mu Umma, kun wuce nan, Allah ya basu zaman lafiya" cewr Ammi. "Ameen Ameen, shima Salim Allah ya bashi wadda ta fi Suhan komai a rayuwa" cewr Umman itama, da Ameen Ammi ɗin ta bita tana mai cewa to shikenan sai na saƙon. Tana kashe wayar kira na ya shiga wayar. To na gaji, daga kwanciya sai wanka da cin abinci da sallah, komai yi mani akeyi, latsa waya shine babban aiki na, gashi Ya Ameen hidindumu sunyi mashi yawa, inma kinga ya kira ni, ko ni na kira na samu to dare ne. Gaida ta na shiga yi, ina mai tambayar ta lafiyar ta. Cikin murmushi take amsawa, tambaya ta take ya sabon wuri? Shiru nayi bance ƙala ba, na ma rasa ta inda zan fara, ce man tayi "kinga Mamana nasan dama zaki kira, saboda haka nake so da ki adana tambayoyn ki, yanzu ba lokacin su bane ya zuwa yanzu dai na san kin gansu da cewa kina da asali da kuma gata, saboda haka ki cigaba da yi mana biyayya Allah yayi maki albarka" Da Ameen na amsa, murya a dusashe, ban ɗauka haka zata ce mani ba, har yanzu ina cikin ɗan duhu fa, ban gama tantance komai ba. Abunda nayi ƙoƙari dai shine ganin na saki jiki da haɗiman dake man hidima, inda su kuma basa samun damar yin hakan, saboda tsari irin na gidan sarautar, ko su Fulani sau ɗaya nake ganin su idan naje gaishe su da safe, mai martaba ma haka. Saidai babu abunda na nema na rasa, komai akwai shi enough ba matsala, kawai dai kaɗaici ke dake damu na, gashi a gidan babu wata yarinya mace tsara ta. Su Raihana na kira na lallaɓa su akan cewa su taimaka su taho da wuri, saboda wannan amaryar dai ita kaɗai ce kullum a ɗaki, sai Afnan da kan kira ni akai akai tana zaulaya ta wai amaryar Yaya. Umman ce ta sanar dani cewa wai Ammi na nan tafe gobe inda nake da mai gyaran jiki. Nayi mamaki, gaskiya kirkin Ammi har yayi yawa, ace yaron nata ma bai samu auren nawa ba, Amman tsaye take kyam akan hidimar tawa, kaman dama cen ta samu ne. Al'ajabi na shiga yi Umman na taya ni, sai sanya ma Ammin albarka take yi, nima ina jin daɗin hakan, wata irin ƙima da darajar Ammi da Sir Salim nake gani a idanun nawa. Da "to" na amsa mata tana mai kashe wayar tace in da wani abu in kira ta. ******* Fulani ce ta shigo tana mai shaida mani cewa an shirya yin kamu ranar Alhamis saura kwana biyu ɗaurin aure, saboda haka sai in shaida ma angon nawa domin ya sanya shi cikin programme, saboda suma duk zasu taho cen ne ayi kamun. Kiran Ya Ameen ɗin nayi bai ɗaga ba, hakan ce ta sanya na tura mashi saƙon text,bai bani amsa ba, sai cen da marece ga kiran nashi yana bani haƙuri, ayyuka ne suka taso shi gaba, ga shirye shiryen ɗaurin aure, anan ma ne yake shaida mani wai ba za'a kawo mani lefe ba, ga Abunda masarauta tace. Da "to" na bishi ina mai sake jinjina ma ƙoƙarin da yake yi, da murmushi akan fuskar shi yake sanar dani cewa "babu Abunda ba zan iya yi a kanki ba mai kuka ta" Nima dariyar nayi ina mai cewa "na gode ma Allah, ko nayi ina da mai share man hawaye na, ya kuma lallashe ni" Yaji daɗin maganar tawa kuwa. Nan ya biye mani muka yi ta fira cike da shauƙin so da kuma ƙaunar juna. Washegari sai ga Ammi, nayi mamakin yanda kai tsaye na ganta cikin gidan, har ɗaki nawa ita da Fulani, sai a lokacin ne na fuskanci inda kaman da nake gani a fuskar Fulani ta fito. Itama da mamaki sosai tazo ta kama ni tana mai rungume ni, duk ƙoƙarin da nake na zamewa daga jikin nata kuwa in durƙusa, ta riƙe ni gam a jikin nata, tana ta salati da tasbihi ga Allah. Tun jiya da Umma ta mata text ɗin address ɗin ta kira ta domin taji haƙiƙanin gaskiyar Abunda ya kai Suhan masarautar su ɗin. Saidai bata samu ba, haka yau tin da wuri take doka ma Umman kiran, Amman still bata samu ba. "Suhan ashe ke tamu ce? Ashe ke jini na ce Suhan? Gaske Naji ƙaunar da nake maki har cikin jinin jiki na" ta shiga furta wa, tana mai zaunar dani gefen gadon, itama Ammin ta zauna. Su kau haɗiman da suka rako su, ganin hakan sai suka sulale suka fice, domin doka ce cewa ba zasu taɓa tsayawa ayi maganar da ta shafi masarautar gaban su ba. Kaina a ƙasa na shiga gaida ta. Waya Ammi ta ɗauka tana mai kiran Salim, nan ta shiga shaida mashi Abunda ke faruwa, da alaƙar shi da Suhan ɗin, yana cikin raɗaɗin rabuwa da Suhan ɗin, ce mata yayi kawai sai yazo, ya datse wayar yana mai runtse idanu. Fulani ce ta samu bisa sofar dake ɗakin ƙwaya ɗaya ta zauna, itama mamaki takeyi inda har Khaltum ƙanwar tata ta san mu haka. Nan Ammi ta shiga shaida ma Addar tata yanda akayi ta santa, da kuma irin abubuwan da suka faru. Gyaɗa kai ta shiga yi cike da sarauta, "Khaltum ashe kin daɗe da sanin hasken masarauta Gimbiya Merama, Amman dayake ba zumunci yanzu sai ba ku gane juna ba, baku san ku ƴan uwa bane" "gaskiya ne Adda Fulani, saboda haka ayi haƙuri, Nidai nazo da mai gyaran jiki, wadda zata fara yi mata kuma daga yau, saboda haka sai a shigo da ita, domin muji yanda abubuwan zasu kasance" "Haka ne Khaltum" "Gajee" Fulani ta kwala ma wata haɗima kira, ɗaya daga cikin masu kula dani. "Na'am ranki ya daɗe" ya faɗa tana mai shigowa da gudu ta gurfana gaban ta" "Aje maza a shigo da mai gyaran amarya" Fulanin ta faɗa cike da isa. "an gama rani shi daɗe" Ta faɗa tana mai miƙewa ta sunkuya mata, muma ta juyo ta sunkuya mana, sannan ta fice. Nidai zaune nake, na kasa sakin jiki na sosai, ga Ammi ga Fulani, firar su suke yi a hankali irin ta ƴan uwa. Gaje ce ta shigo da mai gayarn jiki. Su duka durƙusawa suka yi, suka sake kwasar gaisuwa ga Fulanin, sannan gaje ta miƙe ta fice. "Muna so ne za'ayi mata na musamman, saboda haka kada ki damu da Abunda za'a baki ko na nawa ne ayi mata" cewr Ammi dake zaune gefe na riƙe da hannuwan nawa har yanzu. "To Hajiya yanda kika ce haka za'ayi, saidai dole ne gimbiya ta kiyaye shiga rana har sai ranar da aka kammala" "Ba damuwa, dama babu inda take zuwa" cewar Fulani dake hakimce bisa kujera. Sake gurfanawa tayi, tana faɗin "An gama Ranki ya daɗe" Fulani ce ta miƙe tana mai cewa "Hajiya Khaltum idan kin gama, ina mai jiran ki a sashen nawa" Tana gama faɗar haka ta sanya kai ta fice, fuskar ta cike da fara'a. Na kula mutumci da kirkin Su Ammi a jinin su yake, to ni kam ina mamaki ta ina suka haɗa alaƙa da su Umma? Koma dai minene nan gaba zamu ji. Kasa sakin jiki nayi, nan mai gyaran jikin aka nuna mata toilet ta shiga ta fara haɗa abubuwan ta, nan fa ɗakin ya ɗauki ƙamshi na musamman, har baka gajiya da shaƙa. Ammi bata bar gida ba sai kusan dare, har bayan da aka gama man dilka da halawar sana, ɗaki guda aka ba mai gyaran jikin zata zauna nan har a kammala. Da kanta Ammi ta dinga yaba ƙyauna, har yanzu tana jin babu daɗi rashin samu na da Salim ɗin baiyi ba, kuma gashi lamarin Ma'u maimakon abu yayi baya sai gaba yake ci gaba, yanzu ta kai da ko kwanciya da ita Salim ɗin yazo yayi sai ta barbaɗa ma ƙawayen ta, ga ƴan shige shige da gulmace gulmace da muguwar ƙazanta. Naji daɗin kasancewa da Ammi, duk da duk yanda naso in saki jiki da ita na gaza, duk da ina mata kallo ne kaman na Umma ta. ******* Kwanaki na ɗauka ana mulke mani jikin nawa, yanzu ko ni bana gajiya da shaƙar ƙamshin jiki na, duk da ina jin jiki wajen dirzar mani jiki da ake ta yi. Cikin kwanakn su Raihana suka iso, su kansu sunyi matuƙar mamakin ganin gidan namu, dama dai ban taɓa ce masu komai dangane da ko ni ɗin wacece ba, dama haka ake son mutum da kama bakin shi, domin yana iya sakin jiki yayi ta bada labari abubuwa suzo su cenza, daga baya ayi tunanin ƙarya yake yi ba haka bane. Naji daɗin zuwan nasu, dasu aka haɗa aka cigaba da gyara mana jikin. Ya zuwa yanzu bana da matsalar kaɗaici, matsala ta ɗaya, rashin kasancewa da Yayan da bana samun yi sosai ko a waya, to shima dai ɗin abubuwa sun mashi yawa, ga tarin masoya da abokai da suke ta ɓullowa jin hidimar tashi ta kankama. Ya zuwa yanzu fata ta tayi wani irin sulɓi da kyau, ga wani sheƙi da walwali da take yi, hatta man da nake shafawa wani haɗi ne na musamman, kowa ya ganni sai ya yaba, akai akai Ammi ke zuwa ta duba ni, tare da tambayar ko bana da wata matsala, su kansu su Raihana sunyi mamakin cewa wai ita ce mahaifiyar Sir Salim, ashe ma duk abun nan muna da alaƙa da su ta sosai. Itama sakin jiki take suyi ta fira, wani lokaci har da Aseeya ƙanwar Sir Salim ɗin sukan taho, wadda ta shige cikin mu mun zama kaman ƙawaye. Tin ranar da Ammi tace kayan zasu isa, suka isa ɗin, sunyi mamakin kayan ita da Hajiya zainab, masalan da Umman ta sanar da ita wacece Hajiya Khaltum ɗin a wurin ta, domin Ammi ta ce ba zata kira Umma akan alaƙar dake tsakanin su ba, jira take sai tazo kwatsam su haɗu suyi ta mamaki. Hajiya Zainab ce ta kwashi kayan zuwa sashen nawa, wanda aka haɗa har ya gaji da haɗuwa, shi kanshi Ya Ameen tinda aka gama tsara sashen bai shige shi ba, dayake makullan na hannun Hajiya Zainab ɗin, sai yabar mata, ko da suna so su ƙara zuba wani abu ciki daga baya. Hafsat da tazo taga sashen ihun murna ta saka, ya zuwa yanzu cikin nata kaman zai faɗo, sai nishi take daƙyar take ɗaga ƙafa, domin ya wuce watan haihuwa tuni, so suke suyi mata aiki, daga ita har sadeeq ɗin sun hana, cewa sukayi a bari idan lokacin haihuwar yazo ba abunda zai hana a haihun. Tana yawan kira na, akai akai mu kan yi waya, da cewa tayi itama zata zo, sai da akayi da ƙyal aka bata haƙuri akan kada taje cen ta haihu masu, ba don ranta yaso ba, tana ji tana gani Umman tawa ta shiga harhaɗa kayan da zata tafi dasu cen. Saura sati ɗaya biki ƴan kankiya suka iso, kaf gidan babu wanda bai girgiza ba ganin ɓangaren da aka tanada ma amarya, ya zuwa yanzu dai maganar kamun da za'ayi a ɓangaren amarya ya yaɗu, saidai babu wanda yasan inda za'aje ayi shi ɗin. Su ma dangin Maman Hajiya Kubran sun iso, sai zuba isa da habaici suke yi, to dayake ba wanda ke ta su, umma dai in dan ita suke yi, saura kwana biyu ma tabar masu gidan, sai suyi ma wanda zasu yi mawa. Haka kuma isowar ƴan kankiyr ne ya shaida ma sauran ma aikatn ɗin wadda Al'ameen zai aura, ai Maree suma tayi, saida aka yayyafa mata ruwa, koda ta farfaɗo sai ta saki kuka mai haɗe da ihu, tana ta shiga Ukku ta lalace ita Al'ameen zaiyi ma haka? Ganin asirin su zai fallasa ne ya sanya Mama talatun cewa ai aljannu ne suka kama Maree ɗin, ba wai don sun yarda bane, sai dai ya zuwa yanzu kowa ya gane nufin Maree da Mama Talatu da tuni aka daɗe da gano cewa ita ce mahaifiyar ta, na son mallakar gidan, kuma ya zuwa yanzu kowa ya gane cewa Mama Talatu da Mama saude sune munafukai gidan, kuma Al'ameen ya san duk wani abu dake faruwa, domin kuwa ya sanya Mudee yana mashi CID a cikin gidan, kuma duk Abunda ke faruwa yana sanar dashi ɗin. Aiko gida ya kacame, ko ina ka gani sai hada hada ake yi, dangin Hajiya Kubra suka buƙaci da abasu makullan sashen Al'ameen ɗin zasu duba, Hajiya Zainab ta hana su, tace masu bata san inda ta saka ba, dole haka suka yi ta gaye gayen magana suka haƙura, duk da jin kansu da suke su wasu ne a gidan. Cikin kwana biyun ne Alhaji ya bada motar da za'a kai Umma Adamawr, Hajiya Zainab ce ta raka ta, kwana ɗaya tayo ta baro Ummar cen ta dawo, tayi mamakin yanda ta tadda ana ta shiri masarauta, kowa ka gani cikin farin ciki, domin tin bayan hawan mai martaba ɗin ba'a ƙara wani shagali ba a masarautar da ya wuce na salla, kasancewr Allah bai bashi haihuwa ba. Cikin ƴan tarbar Umman harda Ammi, su duka sunyi mamaki, masalan da Ammi ta shaida ma Umma yanda suke, ai sai aka buɗe sabon ba in fira da ƙaunar juna, Aseeya ƙanwar Sir Salim ta dawo nan gidan har sai an gama hidimar bikin, itama kullum mitar ta, cewa take dama Yayan natane zai kwashe ni gabaki ɗaya, su Raihana ne ke ce mata, dan bata ga wanda zan aura bane Shiyasa take cewa haka, har take ganin ƙarkon yayan nata. Ranar da su Umma suka tafi, ranar Su Afnan suka iso, har kuka tayi jin cewa wai ina cen kuma yau Umma suka tafi. Shagwaɓa take ta zuba ma yayan nata, wanda daƙyar ya ratso ya shigo gidan shi da Bilal, akan cewa sai ya sanya an kai ta, ba yanda ya iya, haka ya tada mota aka tafi kai ta inda muke ɗin, to itama dai da kallo take bina, ganin a inda nake da kuma yanda na koma. "Allah yaso ba muyi asara ba" Abunda ta fara furta wa kenan tana mai ruƙunƙume ni. Tayi mamaki, kuma dama haka lamarin Allah yake, zata so taga yanda Mom ɗinta zata yi, duk ranar da aka shaida mata ni ɗin wacece. Nan fa hidima ta kaure, kusan kullum sai an yanka shanaye, kai hadda raƙumma aka yanka, kaji kuwa kullum ne, hidima ake sosai, ya zuwa yanzu ko ina labarin auren namu ya bazu, kafafen yaɗa labari sai sanarwa suke yi. Ko da Hajiya Kubra taga iyayen kayan da Aunt Feena ta haɗo, faɗa ta hau yi, wai akan me za'a banzatar da kuɗi haka? Akan wadda hatta da kayan ɗaki uban ango ne ya sanya mana, saboda tsabar faƙiranci da talauci. Ƴan uwan nata na zuga ta, to basu da yanda zasu yi, dandai ƴan kankiya sunga kayan, Amman da rage su zata yi, ko gwala gwalai da aka zubo ciki sunfi saiti goma, ita babbar matsalar ta da zai kasance cewa ba wani abu zasu samu ba in return. Haka suna ji suna gani Alhaji Mustapha ya sanya aka kai kayan lefen sashen amaryar aka kulle. Tinda dai ance ba za'a kai ba sai an kawo ni ɗin. Yanda tafiya kamun zai kasance ake tsarawa, ƴan uwan Hajiya Kubra cewa sukayi ba zasu je ba, sai dakyal ne suka zaɓi mata Ukku shima dan kar ace abun nasu yayi yawa ne, da Hajiya Laila da Hajiya Sa'a mutum biyar kenan, dama su su Nihal ba'a tsara dasu ba, saboda ansan cewa ba zasu je ɗin bane ba ma, suma daga cikin ƴan kankiya mutum biyar, duka mutum goma kenan. Hidimar da akeyi gidan da shagali da akeyi, kaman ba kuɗi ake kashewa ba, dan dai Alhaji Mustapha hannun Hajiya Zainab ya hannanta komai, saboda yasan idan ya bar Hajiya Kubra akan hidimar za'a ga ba daidai bane. Sashen Umma kuwa saidai aka kulle shi. ******** "Laila na fara nadamar amince ma auren nan da nayi fa, kada ina ji ina gani wankin hula ya kai ni dare, yanzu fa kina gani sai in kwana in yini ban sanya Al'ameen a ido na ba fa, tin ma yanzu kenan?" Hajiya Kubra ta faɗa, tana zaune gefen gado ita da sa'a Hajiya Laila kaɗai ne a ɗakin. "Kada kice haka Hajiya ta, komai zai tafi yanda aka tsara, ai ki ƙyale su, wannan dariyar da suke yi zata zame masu kuka ne, ba ita Maryamar ta tafi ba? To ki zuba idanu ki gani, ita da gidan nan sai a lahira, kuma itama yarinyar da za'a kawo da ƙafafn ta zata kwashi takalman ta a sukwane ta bar maki gidan ki" Cewar laila ɗin wadda ta dafo kafaɗar Ƙawar tata cikin wani irin yanayi na jimami da ƙuncin zuciya. "Laila girma na da aji na ya zube, muddin na bari akayi auren Al'ameen da yarinyar nan, kowa yasan Al'ameen ba ƙaramn mutum bane, duniya ma ta shaida haka, ace babu wadda zai aura sai maƙasƙanciyar ƴar aiki? Beside ma fa ni na tsani yarinyar wallahi, ganin ta nakeyi kaman aljana ma ni, wani lokaci fa idan ina kallon ta sai inji gaba na yana faɗuwa" "Kada ki bamu kunya mana Hajiya Kubra, ki daure ki cije ayi abun nan lafiya, kada ace kece kike ɓullo da wani tashin hankalin kuma" cewar Sa'a dake gefe, wadda ta taso itama zuwa ga Hajiya Kubra ɗin. "Sa'a ku tabbatar duk Abunda aka shirya ya kammala, ku tabbatar yarinyar nan bata samu wuri a zuciyar Al'ameen ba, ku ruguza abun ku wargaza komai, gaba na yana ta faɗuwa, masalan kwanan nan, gani nake kaman wani gagarumin abu na shirin faruwa, ku taimaka mani ku san yanda zakuyi" Hajiya Kubra ɗin ta faɗa cike da zullumi. "Hajiya Kubra ki kwantar da hankalin ki, ina mai tabbatar maki da cewa da zaran an ɗaura auren Suhan da Al'ameen ba zai kuma kallon ta a matsayin ɗiya mace ba, zata dinga warin jaɓa, zata zama kaman mujiya a cikin tsuntsaye a idanun shi, idan ta doshe shi, zai ga kaman baƙin maciji mai tattare da dafi ne ya fasa kai ya nufo shi, zai ƙuntata mata, zai tsane ta, zata yi nadamar Auren yaron namu da tayi"........ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'a idan aka ga wani wanda wata masifa ta fada masa:* الْحَمْدُ للهِ الَّذِي عَافَانِي مِمَّا ابْتَلاَكَ بِهِ، وَفَضَّلَنِي عَلَى كَثِيرٍ مِمَّنْ خَلَقَ تَفْضِيلاً . Alhamdu lillahil-lazee 'afanee mimmab-talaka bih, wafaddalanee 'ala katheerin mimman khalaqa tafdeela. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda Ya amintar da ni daga abin da Ya jarrabce ka da shi (na masifa), kuma Ya fifita ni a kan da yawa daga cikin wadanda Ya halicce su fifitawa. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *_Bana da bakin da zan iya gode maku, ashe haka ban fi ƙarfin ta yake da masoya da fans? Haƙiƙa ina mai alfahari da ku masoyana na haƙiƙa. To kuna ina? Duk ku fito mu ɗinguma zuwa gidan mai martaba domin gabatar da shagalin wannan gagarumin aure, yau dai Allah yayi. Saboda haka ne duk nake maku fatan alkhairi_* *Salamatu Abj, and Mrs Daura Kd, aga saƙonƙu kuma na gode wannan ya nuna mani iya wuya kuna tare da ni, to babu Abunda zan iya cewa anan illa Allah ya haɗa mu gabaki ɗaya a aljanna firdausi ya raya mana zuri'ar mu, ya barmu da mazajen mu tare da ƙunrsu gabaki ɗaya. Nagode matuƙa* *Ina kike Jiddon Dady? Sarkin hanzari, ai kin riga ma kowa isa, Salamatu mai masaukin baƙi, da fatan dai kin shirya tarbar ɗinbin tawagar BANFI ƘARFIN TA BA FANS da ƴan GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION domin yau fa kina ga gaggaruman baƙi* *Page ~61~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° "Ki kwantar da hankalin ki, ki dai yi masu ta ƴan duniya Hajiya ta, da idanun ki zaki ga Abunda zai wakana, duk ki sanya masu ido". Cewar Hajiya Laila da take zaune gefen Hajiya Kubra ɗin. Ita dai sai faman ƙutawa take yi, hankalin ta a matuƙar tashe, masalan da take ta amsa waya, ta ƙawayen ta da matan manya akan cewa zasu shigo hidimar insha Allahu. To da wane ido zata kalle su ta faɗa masu surukar tata ɗiyar mai aikin ta ce? Kai wannan abun kunya da zubda girma da yawa yake, ita bata hango wani dalilin da ya sanya Alhaji yace dole sai anyi auren ba, ko kuma shi Al'ameen ɗin mai ya gani jikin yarinyar ba. ****'****** Zuwa yanzu dai ni kaina nasan saidai maƙiyi yace ban yi kyau ba, ko ban haɗu ba, koda yaushe muna tare da Ya Ameen a waya yanzu, saidai suga ina ta sakin murmushi dayake yanzu earpiece nake sanyawa a kunnen nawa, ita kanta mai gyaran jikin nawa kullum faɗa take yi tana so taga angon nawa, dayake ita ce mai gyaran jiki, ƙunshi da kuma kwalliya, Ammi ce ma take faɗa mani wai da ita zamu tafi Abujan har ranar walima duk ita ce zata gyara amaryn. Hidimar biki ake ta yi fafa, duk yawan mutanen da suke zuwa gidan nan, haɗimai ne ke masu hidima, nan su khadeeja da Raihana aka baje ƙafa, har yanzu mamakin daraja irin ta su Suhan ɗin suke yi, ga tsabar mulki da ake zubawa a masarauta, komai a tsare ake yin shi. Ana haka ne sai ga Jidda ƙanwar Oum-Deedat ta isa, ai tsalle Afnan tayi ta rungume ta, murna take ta yi sosai, Ƙawar ta ce sosai a instagram haka ma Ƙawar Asiya ce ƙanwar Sir Salim a school, ai sai suka haɗe, hidimar biki ake ta yi sosai, domin shi Dady ɗin ne ma dakanta ya kawo ta, tare da damƙa mata dukkanin abubuwan da yasan zata buƙata yana mai sanar da ita cewa sai ranar ɗaurin aure zai dawo tare da su Ya Ameen dayake abokai ne, don dai sunyi nisa ne, kuma kowa na cen hidimar shi tayi mashi yawa ne ya sanya basu cika samun haɗuwa ba. Ƙawayen amarya su biyar hadda amarya su shidda kenan, tin zuwan Umman aka cenza masu ɗaki, wani sashe ne aka buɗe masu su duka babban falo ne da manyan ɗakuna guda biyu a ciki, Shiyasa suke gabatar da komai nasu a cikin tsari. Ranar Laraba ne aka yi ma amarya ƙunshi, wohoho, ai ko ni da nake mai ɗaukar rahoto saidai nayi kasaƙe da alƙali na da tawada da ɗan littafi na a hannu. Amarya ta haɗe ita haɗuwa, duk inda ta juya walwali da sheƙi takeyi, ga wani ƙamshi na musamman dake tashi, ga ƙunshi da tasha na zallar Ja, abun ka da fara ai nan da nan sai ta fara haskawa, kowa sai Sam barka yakeyi. Yanzu ba'a cika barin ma a ganta ba, indai ba ƙawayen nata ba, ɓoyon amarua akeyi, ba za'a fiddo ta ba har sai ranar kamu, Abunda ke ƙara ɗaure mani kai kenan, idan na tuna ni Suhan wadda ada bata a kowa yau nice na zama haka. Umma da Ammi kuwa sun ɗinke, komai a tare suke yi, shawara da komai, yayin da Fulani take taya su aiwatar da dukkanin tsare tsaren da za'ayi, mai martaba ne ya bata umurni hakan. ************** Ta ɓangaren dangin ango kuwa, suma ba'a bar su a baya ba, komai na tafiya yadda ake so, bisa jagorancin Hajiya Zainab, domin ita Hajiya Kubra da dangin ta, sun ware kansu, sai yanzu ne ƴan kankiya ɗin suka shaida cewa lallai fa Hajiya Kubran har yanzu tana kan bakan ta, koda tace ta amince kawai magana ce take yi. To saidai babu wanda yabi ta kanta, wannan kau umurni ne daga Alhaji Isuhu ɗan tsohon, wanda tin kafin su taho dama saida ya ja masu kunne sosai, shi dai yana so ne a yi komai lafiya a gama lafiya. Yanzu har abinci da eatery ɗin da Hajiya Kubran ta bada Order ɗin a dinga kawo masu kullum har zuwa a fara hidimar bikin. Ba wanda ya kula da hakan, domin kowa ya sani cewa sonsomin tashin hankali ne take nema, kuma a matsayin ta na uwar miji ba za'a biye mata ba azo aji kunya. A ranar Laraba ɗinne kuma motar laxirious mai ɗauke da tambarn Dambulan ta ɗaga zuwa Adamawa ɗin, mutane goma sha biyu ne a cikin ta. Hajiya Sa'a, Hajiya Laila, Aunt Feena, sai wasu da suke ƙannen Hajiya Kubra ɗin guda biyu da ɗiyar su mai suna Rauda. Ta ɓangaren Alhaji Mustapha kuwa Goggo Fatima, sai Ƴan biyu Aunt Hassana da Hussaina, da kuma yaran nasu ƴan mata guda biyu suma sai Mama Talatu. Itama ance aje da ita ne saboda ta samu ta kakkama masu wasu aikace aikacen. Dayake fa har yanzu basu san kan dawon garin ba, su Hajiya Sa'a kuwa harda guzuri Hajiya Kubra ta basu, wai bata so suje susha wahala, ita wlh da sun biye mata ma fa, ba zasu wani je ba, yanzu haka ma ko inda za'a ajiye su su kwanta basu, ƙila saidai a kaisu sansann ƴan gudun Hijira wai su kwana, saboda tsabar talauci. Cikin motar ma da ake tafiya, haka kowa ya kama kanshi, masalan ƴan kankiyr da suka lura dangin Hajiya Kubran kowa na jin kanshi, sai basu biye masu ba aka cigaba da tafiya haka, Hajiya Zainab zata je, Amman sai zuwa gobe ɗin in sha Allahu zata bi tawagar anguna. Makilli part ɗin nasu ya amsa daga hannun Hajiya Zainab, a hankali yake taka wa yana mai bin ko ina da kallo na sashen, lallai aure na rahama ne, sashen nashi da ɗaya duniya kaman bai taɓa zama ciki ba, kaman ba part ɗin nashi ba, gashi dai har yanzu ba'a cenza tsarin ginin ba, parlour ɗaya ne babba da single bedroom da kitchen, sai toilet a cikin ɗakin, Amman ko ina an ƙawata shi, hatta da plaster ɗin saida aka kankare ta aka yi wata mai kama da ta duwatsu, shi kanshi sashen ya matuƙar ƙayatar dashi. Kitchen ya nufa a hankali, yana tafe yana sakin dariya shi kaɗai, a tsakiyar kitchen ɗin yaja ya tsaya, hannayen shi duka rungume a ƙirjin shi, komai n a kitchen ɗin ya tsaru, gashi ba wasu tarkace, Amman kai kace a ƙasar Turai ne, juyowa yayi ya fito a hankali yana mai shafa dining table ɗin dake ajiye ta gefen kitching ɗin da glass kawai ya raba su da kitchen ɗin, komai dake falon kana iya hange daga kitchen ɗin saboda zallar glass ne kawai abunda ya katange kitchen da falon, hakan ya sanya indai ba cottons aka saki ba daga cikin kitchen ɗin kana hangen falo, sai ya ƙara ƙawata falon, ga wasu irin kujeru da aka sanya set ɗya ane, Amman kayan set biyu ne a cikin shi, kaman na gidan sarauta, lallai baiga laifin Dad ba, da irin waɗannan kayan da ya sanya aka zuba masu, ai tuwon girma miyar shi nama. Bedroom ya nufa kai tsaye, a hankali ya murza handle ɗin, yana mai tura ƙofar cikin sanɗa, kaman wanda wani abu zai kama. Makunnin ƙwan ɗakin ya kunna, ai sai ɗakin ya ɗauki walwali cikin wasu irin launika shi ba shuɗi ba, shi ba fari ba, haka shi ba bula ba, shi ba ja ba, kaman dai raimbow haka hasken kwan ɗakin yake, kayan dake ɗakin ƴan uban su, kalar upwhite hadda gadon shi ya ƙara jan hankalin shi, kuma ya ƙara ƙawata ɗakin. A hankali ya doshi gadon da aka lailaye shi da zanen gado mai kalar purple da sirkin baƙi baƙi da fari fari haka a jiki, kai kace wani ne zai kwanta saman shi a lokacin. Ɗosanawa yayi gefe, yana mai miƙa hannuwan shi duka da suke farare samɓal cike da garvasa ya fara shago saman gadon, fuskar nan tashi cike take da murmushi, wai nan da kwana huɗu fa matar tashi na a bisa gadon ko? Kwance ko zaune wama ya sani? Kuka take ko dariya, wama ya sani? Kawai dai Abunda zuciyar shi ke hararo mashi irin zallar ƙaunar da zai nuna mata a ranar. Hakan ce ta sanya shi sakin dariya mai sauti shi kaɗai, yana yi yana ɗan girgiza kai, alamar abun ya mashi daɗi kenan, toilet ya nufa, nan ma an cenza komai, an jera komai kaman yanda ya buƙata. Ɗakin ya dawo, yana mai jawo akwatunan da aka jera su reras kusa da gadon da suke kalar purple mai kyau, da upwhite jikin su, kaman dai kalar fentin dake ɗakin. A hankali ya shiga buɗewa yana dudduba kayan, kaya sunyi ba ƙarya fa, komai classic one ne aka sanya, kayan baccin ya ɗago yana mai imagining kayan a jikin mamallakiyar su, shi kaɗai yake sakin murmushi, haka ya rufe ya maida su kaman yanda ya tada su. Ji yake kaman kar ya bar sashen, Suhan ta daban ce shi yayi imani, komai da take burge shi yake yi, yanzu ne ya tabbatar da cewa ai ko Bilal ma ba wata soyayya ya iya ba, ko yake yi ba, tinda har zai iya rabuwa da matar tashi yayi nisa da ita, na tsawon wani lokaci, abunda shi zuciyar shi ke raya mashi ba zai taɓa iya yi ba kenan. Haka ya kullo sashen ya nufi part ɗin ƴan kankiyr, inda acen ne ya tada Hajiya Zainab ɗin ɗakin Kaka Zuwaira tana mata wasu aikace aikacen. Aiko da wa Allah ya haɗ alaka Zuwairn ba dashi ba, nan fa ta shiga caccakar shi, wai ango har ya fara kyallin goshi, ita fa gaskiya ba zata yarda ba, domin ta lura wannan amaryar ita aka yi wa. Murmushi kawai yake yi, kaɗan ya biye mata ya fice saboda Hajiya Zainab tana wurin, kuma ko ba komai yana matuƙar ganin girma da ƙimar matar. Saboda shi kanshi ya sani ita da mijin nata ba ƙaramin taimaka mashi tayi ba wajen auren nashi. Kafin ya fita saida ya sake jaddada mata cewa ta shirya da wuri zasu wuce a goben, saboda yanayi na hanya, da to ta bishi rana mai ƙara yi mashi fatan alkhairi. Ta ɓangaren Maree kuwa kaman zata yi hauka, komai ta kwance mata, wai yanzu ace yarinyar da ta tsana ita ce zata hau shinfiɗar ya Ameen ɗin a matsayin matar tashi, to ko bai ci abincin da tabbarbaɗa mashi magani bane ba kwanaki? Ga Iro da yake matsa ma rayuwar tata, ba daman ya ganta sai yayi kaman zai rungume ta, kuma ko gaban wanene, ya zauce akan soyayyar ta, iako sauran ma'aikata me zasuyi masu in ba dariya b? Ga mama Talatun tabi ƴan zuwa gidan su amarya balle ta samu wadda zata rage damuwar ta wurin ta, su kuma sauran ƴan aikin sanin rashin Kunyar tata ne ya sanya su duka babu wani mai sake mata jiki, ko kuma ya jawo ta jiki, sanin mugun baƙin halin ta, da na uwar ta. *********** Su dukansu babu wanda baiyi mamakin ganin sun doshi babbar masarutar garin ba, masalan dangin Hajiya Kubra ɗin da su Hajiya Sa'a, to ko dama cen ita Maryama baiwa ce a gidan Sarauta? Kafin ta gudu daga nan ta koma cen gidan Alhaji Mustapha ɗin? Kowa Al'ajabi takeyi, suna mai bin fadawa da suke ta wucewa da haɗimai a mota, ga dawakai ko ta ina sai harbin iska suke yi. A harabar gidan suka yi parking, dama tin da suka shaida tahowar tasu, aka fara sanarwa a masarutar akan cewa ga dangin ango nan sun taho, har kawo isowar tasu, haka suka tadda haɗimai da jakadiya na jiran su, ai tin fitowar su a mota ake masu busa da kirari, hajiya sa'a da hajiya Laila har gama hanya suke yi, ga wasu furanni masu kyau da ƙamshin da ake watsa masu, an shimfiɗa masu jan kilishi suna tattakawa a bisa shi, sai kirara su akeyi ana masu barka da isowa. Su dai sai zare idanu suke yi, da kallon mamaki suke kallon ko ina, abun fa da mamaki, kaman a mafarki suke jin shi. Suke kuma ganin shi, har zuwa lokacin da akayi masu masauki a wani tanƙamemen sashe dake cen ɓangaren guda na masarutar. Dayake Umma ta san komai, sai aka bambanta masu ɗaki, ƴan kankiya ɗakin su daban, haka ƴan uwan Hajiya Kubran ma, saidai duk part ɗaya, ne ma'ana falon guda ɗaya ne, cike da kayan alatu na more rayuwa. Suna shiga Hajiya Laa taja ta tsaya, tin bayan da haɗiman da suka yi masu rakiya suka fice domin kawo masu kayan abinci, kafin su gama a masu rakiya zuwa wajen fulani. "ke Sa'a wai ko dai mafarki nake yi ne? Nan ina ne mudi ya kawo mu? Anya kuwa nan ne inda amaryar da Maryama suke? Ni dai banga alama ba gaskiya" Hajiya Sa'a ɗince ta amshe zancen da cewa "To nima dai wallahi Laila Abunda zance kenan, tun da naga mun doso wurin nan gabana ke faɗuwa, ya kamata mu kira Kubra mu snaar mata fa, anya ba wasan kwaikwayo ne aka shirya mana ba? Kinsan fa yaron nan babu Abunda ba zai iya yi ba" Cewar Sa'a ɗin da ta nemi gefen sofa ta zauna. Aunt Feena ce ta shiga girgiza kai, Sauke Nasreem tayi tana mai cewa "a'a Aunty, gaskiya kada a kira Mom yanzu, a bari dai sai mu ga kamun ludayin abun, ni fitsari ma ya cika mani mara, bari in rage shi. Ta faɗa tana mai nufar toilet ɗin da yake ta gefen ta. Rauda ce ta faɗa saman makeken gadon tana mai faɗin" wash ni na ma gaji wallahi, ga yunwa ina ji, wai ba'a fito mana da kayan mu bane daga boot? " Mahaifiyar ta, wadda ta kasance dangin maman Hajiya kubran ce ta ɓalla mata harara," Ke baki ga inda muka zo bane? Kina nufin zaki rasa abin ci a irin wannan gidan?" ta faɗa tana mai bin sashen da kallo, su kau su Hajiya Sa'a sun kasa ma ko zama, balle su ji daɗi. Aunt Feena na shigewa toilet ɗin ta zaro wayar ta, gami da danna ma Ya Ameen kira, lokacin yana cikin abokan shi, su Bilal suna gaba gaba wajen tsara yanda hidindimun zasu kasance, masalan dinner da take tasu, bayan an kawo amarya. Zare jiki yayi yana mai shigewa ɗakin da yake mallakin Bilal ɗin. "Big sis ya hanya, kun isa lafiya ko?" "Kai ba wannan ba, nan ina ne mudi ya kawo mu? Anya kuwa gidan su Suhan ne?" ta katse mashi maganar da yake yi. Dariya ya saki a hankali yana mai cewa "to your suprise big sis, to ina ne haka mudi ya kai ku?" ya faɗa shima cikin murmushi. "Nan fa wata masarauta babba ce aka kawo mu, kuma kowa da ɗakin su aka bashi Al'ameen, gaskiya ina ji Mudi fa bai san inda ya kamata ya kawo mu ba, kuma shima nan da gani wata hidimar suke yi, ƙila Shiyasa sukayi tunanin mu ma baƙin su ne" Shima datsar numfashn ta yayi yana mai sakin dariya mai sauti, "Aunty Feena cool your mind, nan dai da kika gani shine gidan su Mahaifiyar Suhan, kuma gidan kakannin Suhan in fact, kawai ki yi kallo, kuma please kada ki yarda su kira Umma for now" Jinjina kai ta shiga yi, kaman yana gaban ta, sai kuma tace "zan sake kira dai angon Suhana" Shima to yace yana mai datse kiran, ya kuma sakin murmushi yana mai runtse wayar ta shi cikin tafukan hannayen shi yake faɗin "yyeeess" Tana fitowa ta sake tadda su dai yanda ta bar su, Amman yanzu an cika masu gaban nasu da kayan ciye ciye, babu Abunda babu a wurin, Amman sun kasa taɓawa , mamaki kawai suke yi, har yanzu a tsorace suke, basu san wa zasu kira tayi masu bayani ba, Hajiya Kubra ce, kuma itama in sun kira ta, ba lallai ne ta san meke faruwa ba, tinda basu ga alamun ta sani ɗin ba, da ko da guzuri ma ba zata haɗo su ba. Ta ɓangaren ƴan kankiya ɗin ma hakan ce, saidai su sun kira Hajiya Zainab, ta jaddada masu komai, aiko nan suka hau murna, yaron nasu yayi da en mata, ta ɓangare guda kuma jinjina abun suke yi, yanzu ace har Alhaji Mustapha ya san da hakan Amman bai faɗa masu ba, ai da ko wani abu ne sun riƙo saboda dai ayi abu duk a mutunce. Mama Talatu kuwa kaman zata yi bindiga, duk ta ruɗe, har saida suka kula suka yi mata magana, suna mai cewa ta saki jikin ta, nan duk ɗaya suke kaman cen, basa da maraba, su kansu mamaki suke yi, har yanzu ba wai dan a bakin Zainab suka ji ba da ba zasu taɓa yarda ba, saboda har yanzu basu ga wasu masu kama da su Umman Suhanan ba. Shaida masu akayi akan su ci abinci su huta, za'a masu iso wajen Fulani, amarya dai ce ba zasu samu ganin ta ba, sai zuwa goben wajen kamu, domin ya zuwa yanzu ma an ɗauke ta an maida ta sahen Mai martaba ita kaɗai, ko su Afnan da Jiddan saidai su kira ta ta waya. Komai suke yi jiki a matuƙar sanyaye suke yin shi, masalan su Hajiya Sa'a, Aunt Feena tana kiran Afnan a waya sai gata da gudun ta, ɗakin ƴan kankiya ta fara shiga, su dayake iyayen ta ne, ta shaida masu gaskiyar komai, inda tsabar mamaki ta sake cika su, mama Talatu har ƙwarewa take yi da abinci, Amman duk da haka babu wanda ya kawo komai a cikin ranshi. Ɗakin su Aunt Feena ta nufa, Amman koda suka tambaye ta, dayake Afnan taƙadarar kanta ce, ga wayau, sai bata faɗa masu komai ba, kawai dai ce masu tayi, itama har yanzu bata gama fahimtar komai ba, kawai dai Abunda ta Sani Suhan da amman ta suna gidan, kuma suma kaman yanda suka ga komai a girmamance, haka suma ake masu, tin zuwan nata gidan. Nan fa suka sake shiga komar mamaki, har yanzu an rasa mai kuzarn ma kiran wani domin yaji tabbaci. Haɗiman da aka tura masu, saidai sallamr su sukayi, domin duk wannan jin kan ga dukkan alamu sun zo inda aka linka su komai, saboda har yanzu ma basu ga wata mace da ta amsa sunan matar gidan ba, wai kuji ma sai an masu iso wajen Fulanin sana su ganta. *********** Hidima ta rincaɓe, gashi Hajiya Kubra tana ta jiran kiran su laila ɗin, Amman har yanzu ba wanda ya kira ta, cikin ikon Allah kuma a kira su dukansu bata samu ba, sai zuciyar ta, ta raya mata cewa sun shige ƙauye inda babu network, hakan ta sanya ta dinga sakin tsoki, ita fa bata tunanin idan zata iya Daurewa hidimar nan a gama ta lafiya, ga baƙi ko ta ina ɓullo wa suke yi masalan yau ɗin, da gidan har ya ɗinke da jama'a kuma manyan mutane. Sai lokacin ne ta fara fitowa, mulki da iko take bazawa, Hajiya Zainab na ganin haka ta ja baya da lamarin, duk wani abu da zai kawo fitina, indai ta fannin ta ne insha Allahu ba za'a same shi ba, masalan Saƙon alhaji Isuhu da ya iso kunnen ta ɗin na cewa su bi komai a hankali,a samu a gama lafiya. Hafsat ma ta tare a gidan, bacci kawia ke maida ta gida, to shima sadeeq ɗin yana wajen anguna kullum suna tsare tsaren su, masalan ma hadda suka shirya takar ango idan an kawo amarya. Butsu butsu Hafsat ɗin ta kira ni a waya, ni kau ina cikin wani ɗaki da zan iya kiran shi aljannr duniya, sai zare idanu nakeyi, ni ɗaya tsinken ragi, ya zuwa yanzu ma an gama mani gyaran jikin, kuma ko kwalliya ba'a mani, ance har sai ranar kamun, ba'a barin kowa ta shiga inda nake, daga Fulani sai Ummana, ko sauran matan sarkin basa shiga, bansan dalilin hakan ba, na bar ma raina dai cewa domin gidan masarauta ba gaskiya mutanen suka cika ba. Ya Ameen ma daƙyar muke samu muna waya, shine dai baya da time, Amman ni yanzu ai ba abunda nake daga inci sai in kwanta, kayan gyaran cen ciki kuwa har na gaji da sha, daga na gargajiya har na turawa, mamaki ma nakeyi idan jakadiya ta matsa mani akan cewa insha, sai kunya ma ta kama ni, idan na tuna cewa wai wannan gyaran da akeyi mani duk dan saboda Ya Ameen ɗinne, to ni tayaya ma zan iya kwanciya gado ɗya dashi ne ma wai? Na ƙara mujeea na ciko nayi ɓulɓul, ni kaina yanzu dukkan abunda zan aiwatar cikin aji nake yinshi, ga wata sarauta da take yawo a bisa kaina, masalan yanzu da na gane lallai na cika gimbiyr fa, inda ace tin tashi na na tsinci kaina acikin irin wannan Rayuwar Allah kaɗai ne ya san irin shuhurar da zanyi. Yanzu ko Hajiya Kubran zata yarda ta amshe ni a matsayin suruka? Idan ta fuskanci ko wacece ni? Koda yake ya zuwa yanzu ma bana tunanin idan bata san koni wacece ɗin ba. Kaya na ne aka shiga shigo mani dasu, ɗinkakku, dama tin zuwa na gidan mai ɗinkin yazo jakadiya ta auna ni, ta kai mashi awon. Kaya ne na ji da gani na faɗa, laces ne ma ya masu kyau da tsada, da material masu masifar kyau, sai atamfofi manya da zan iya cewa babu ta ƙasa da dubu hamsin a ciki. Kowanne set sun zauna ɗas a jiki na. Kusan kala talatin ne, sai set ɗin takalma kala sha biyar ko wanne da jakar shi mai kyalkyali irin ta amare da ɗaukar ido, kowanne kaya da sarƙa da ƴan kunnen su, sai alkyabbu masu kyau set biyar, da gyaluluwa su ma masu kyau, sai hijabai biyar suma. Akwati set ne mai guda goma. Kayan kwalliya su kansu akwati biyu ne, sai eaner wears suma masu yawa, kefe dai kawai za'a ce mai kyau, wadda sai ƴar wane da wance. Abunda ke bani mamaki, har yanzu banga wani daga dangin mahaifin nawa ba, ko mutum guda, duk da dai ina ji ana ta faɗa cewa ya rasu, to ko baya da dangi ne? Kuma har yanzu an ƙi barin wata ƙofa da wata magana zata iya tasowa balle har inji. Duk da irin gatan da nake samu hakan na ƙara ɗaga mani hankali, kadai ace akwai wani abu ne da ake rufa mani, domin sanin kaina ne nasan cewa dangin mahaifin nawa sune dangi, duk da suma nan ɗin dangi na ne, Amman ba kaman ace dangin mahaifin nawa ba, to ko ya zan ji duk lokacin da aka nuna mani wani aka ce yana ɗaya daga cikin dangin mahaifin nawa? ****** Sai zuwa dare ne duk suka gama hidindumn su, suka huta, tare da yin wanka sukayi salla. Sai da aka tabbatas sun gama dukkanin Abunda zasuyi ɗin ne Jakadiyar ta isa sashen haɗi da kuma gaida su, sannan ta yi masu jagora zuwa sahen Fulanin, dama ita Afnan tini dai ta koma ɓangaren amaren inda taja su Huda da sauran ƴan matan da aka zo dasu daga kankiya. Yanzu ƴan matan amarya sun zama su takwas kenan. ******* A sashen Fulanin aka shigar dasu, falo na uku aka zaunar dasu, yayin da jakadiyar ta shige cen ƙaramar fadar Fulanin domin ta nemi izinin shiga dasu. Da kallo suke bin sashen Fulanin, ikon Allah, an narka dukiya kaman ba'a so, duk da cewa cen gidan Hajiya Kubran shima ƙarshe ne wajen haɗuwa, Amman sai suke ganin kaman nan yafi cen, su dukansu mamaki suke yi, har fitowar jakadiyan tana mai russuna masu take basu izinin shiga. A hankali suke taka wa har zuwa cikin ƴar fadar, cen ƙurya suka hango Mama Fulani zaune da wata mata gefen ta, sai wasu mata biyu suma zaune bisa tasu shinfiɗar ta kikisai, fadar ta matuƙar haɗu, kaman ba a nigeria ba, komai na fadar kalar ja ne da royal golden. Gefe inda akayi masu shimfiɗa ta wani ƙaton darduma suka samu suka zauna, yanzu fa duk sun zama ɗaya, bama ka banbance dangin Hajiya Kubran da na Alhaji Mustapha ɗin, domin duk wannan girman kai ɗin sun fara ajiye shi, domin sarauta daban take. Gaisuwa suka fara yi, cike da girmamawa, cike da izza fulani ke amsawa haɗi da sake yi masu barka da zuwa, yayin da ta basu damar su gaida Uwar amaryar da take zaune gefen su, duk da dama ita ɗin tasu ce. Da tsabar mamaki suke kallon Umma, wadda ta ɗago tana mai haske su da murmushi cikin fararen haƙoran ta. "Barkan ku da isowa" Abunda Umman ta faɗa kenan, fuskar ta ƙunshe da murmushi irin na sarakai. Ai cikin rawar baki suka shiga amsawa, Hajiya Sa'a sai zungurar Hajiya Laila take yi, itama sai zungurar ta take yi alamun ta bari. Yanzu Maryama ce ta koma haka? Abunda kowa ke rayawa kenan a cikin zuciyar shi. Sauran matan sarki ma sun masu maraba da zuwa, inda Fani ta gabatar masu da su, Umma ce kawai bata ambaci yadda suke da ita ba, hakan ne ya ƙara ɗaure masu kai, masalan kamar da ta faɗa na cewa "Muna mai maku matuƙar murna da yaron naku zai auri ƴar gimbiyar masarutar tamu, hakan abun alfahari ne ga kowa, kuma muma muna mai jin daɗi da murnar samun suruki da mukayi na yaron naku abun alfaharn duk wani matashi dake faɗin ƙasar, da fatan zaku koma sahen naku ku sake hutawa, har zuwa gobe inda za'a gabatar da kamun wanda masarauta ce ta shiya shi, domin taya waɗannan ma'ayrata murnar auren nasu" Baki a sake suke kallon ta, ita dai Umma ba abunda ta iya faɗa, sai faman murmushi da take doka wa, kaman ma da biyu taje yinshi. Kuma tsaf ta kula da diriricewar da mutanen nata sukayi. Nan wajen ya ɗauki shiru, inda sai daga bisani ne Umman ta gabatar ma Fulani da Goggo Fatimar da ƙannan Alhaji Mustapha ɗin a matsayin ƴan uwan mijin nata, su kuma su Hajiya Sa'a ta gabatar dasu daga fannin Uwar ango. Hajiya Laila ce tayi ta maza wajen bada saƙon gaisuwar da ta ƙirƙira ta ƙarya wai mahaifiyar Ango ce ta bayar a ba dangin amaryar. Cike da kambama wa jakadiyar ke amsawa, tana ta sakin guɗa haɗi da dariya. Duk abun nan su Fulani basu san ko su wanene su Hajiya Sa'a ba, su kansu ƴan kankiya sun mamakin yanda su Hajiya Laila ɗin suka saki baki suna dariya, cike da girmamawa da russunar da kai. Jakadiya aka buƙaci da ta masu jagora zuwa sahen nasu, sannan idan da wani abu da suke buƙata suyi magana. Haka suka miƙe jiki ba ƙwari suka bi bayan jakadiyar, har yanzu fa gani suke kaman mafarki, yanzu sun ƙara tabbatar ma kansu da cewa ko wanene Umman Suhan ɗin a masarutar ba ƙaramin matsayi gareta ba, tinda har zata iya zama bisa shinfiɗar Fulanin da daga gani akwai cikakken iko a tattare da ita, domin wani lokacin ko magana bata yi, saidai tayi nuni da hannu. Ko bayan da suka koma ɗakin fa, ƙasa zama su Hajiya Laila ɗin suka yi, wayar Hajiya Kubra suka kira bata shiga ba, sai suka kira ta Layin su Nihal, to suma ɗin shaida masu sukayi ta shiga sashen Dad, dole suka haƙura da fesa mata gulmar ba wai dan sun so bane, sun bar ma ra su sai zuwa gobe zata ji komai. Lalai akwai buƙatar a duba lamarin nan, duk yanda suke tunani ba haka bane, yaron ƴar gidan girma ce zai aura, kuma akwai yuwuwar ma a mallaka masu wani gagarumin abu a matsayin kayan dangin miji da ake bayarwa. Su kau ƴan kankiya godiya ga Allah suke yi, suna raya ma zuciyar su cewa zasu ga kakar rashin Kunyar hajiya kubra ɗin, kuma suna nan sun baza idanu suga ko guda nawa ce rashin Kunyar tata. Mama Talatu kuwa har zawo saida tayi komawr su ɗakin, duk Abunda aka kawo ɗaya bayan ɗaya saida ta taɓa shi, ga zullumi da fargaba, duk ranar da Abunda tayi ma Umman ya fasu tasan ta kaɗe har buzun ta, lallai mutum ba abun raina wa bane, sai gashi a yanda take gani ma yanzu kaman Umman ta zarta Hajiya Kubran a komai a yanda ta lura. ********* Da safe misalin ƙarfe tara tawagar anguna suka ɗauki hanya, harda Hajiya Zainab, kai da gani kasan tafiya ce ta girma, motoci Ukku ne sabbi fal, tear leader wanda Al'ameen ne ya siye su kawai domin hidimar bikin tashi, tafiya suke a nutse, dayake manyan motoci ne masu masifar tsada, ko rami suka faɗa ba lallai ma ka fahimta ba, wasu irin murtukan murtukan tayoyi gare su, baƙaƙe ne fal, wadda ango da Bilal da Yusuf (dady) mijin Jiddo da Abie ke ciki ce fara, sai wadda Sadeeq da surukar tashi Hajiya Zainab da wani abokin ango guda ɗaya, wanda ya kasance bature ne, hidimar bikin Al'ameen ɗin ce kawai ta kawo shi. Sai wata guda ɗaya kuma da wasu abokan angon ne ciki suma, kowa ka kalla ka tabbatar yana cikin farin ciki. Ta ɓangaren masarauta ma haka, sai hada hada akeyi ana gyara lambu inda kayi ma deciration, da gani a ciki ne za'a gabatar da kamun amaryar, wanda za'a gabatar a yau da marece. Ni kau tin da safe ake ta ɓulɓul mani wani irin ruwan turare, sai sake murje mani jiki ake da wani irin mai fari tas, Abunda ban kula dashi ba shine, domin ina cikin ɗaki ne, wannan abun da ake sanya mani wanda zai sanya fatata ta ƙara sheƙi ne, kuma ƙamshin ya zauna a jiki na, har zuwa nan da wata guda. Kayan aseobe ne da akayi su kala ɗaya, jan saƙi ne akayi ma dangin amaryar, su kuma dangin ango akayi masu kalar bula mai cizawa. Haka aka bibbi ɗakuna ana ta rarraba ankon kamu ɗin, su kansu sunyi mamakin ganin an kawo masu kayan da zasu sanya wai, dayake rigar bubu ce, ba ruwana da kana da jiki ko baka da shi, zaka iya sanya ta normal, sai zane da za'a ɗora sama, da kuma wani dogo da za'a rataya a kafaɗa. Gaskiya saƙin yayi kyau matuƙa, su kuma ƙawayen amarya nasu silver ne duka, Asiya ce ta kira masu mai make'up, ita kuwa jiddo dayake ta iya, sai cewa tayi a barta tayi abunta yanda tasan dady na buƙata, domin shi bai cika son heavy make-up ba. Ana cikin haka ne sai ga tawagar ƴar golden pen ta dira cikin motar su da akayi ma tambari da *Golden Pen Writers Association* Umar ɗalha ne mai tuƙa motar, su Mazadu (Idan ke rabo na ce), One Lurv (Ƙarenaty), Umme yusuf (ummu Salma) Fatima Batula (ni da maka ta) Lipton girl (Matar ka ko Matata) Summe B. ( Aminta) Harira ƴar fillo (Jinnul Aashque) Ummyti (Shine Silah & Biyayya ce) Mamie (Ilham) mariam qurrah (Miye mafita) Queen indo (ƴan uku) ds suna nan dai da yawa, dayake su 25 ne sai aka basu babban part guda ɗaya, Umar ɗin dai ne aka ware aka kai shi ɓangaren maza, suma sunyi nasu ankon, saidai su wani material ne mai sulbi wai walwali yake yi, kalar sararn samaniya da gyale pink mai haske, suma ai nan da nan aka kai masu abinci da kayan ciye ciye, gida fa ya cika maƙil duk inda ka duba babu Abunda zaka gani sai tarin jama'a ana ta hidima. Ai sai wurin ƙarfe biyu tawagar ango ta iso. Ai ana fara sanarwr anguna sun iso, gida ya kuma hautsinewa, dama dai ni ina cen sashen mai martaba bansan wainar da ake toyawa ba, mai gayan jiki sai lindar mani jiki take yi, har na gaji, nayi jajawur kuwa tsabar dirza. Afnan ce tayo mani text "Habibinki ya iso fa" Murmushi na saki ina gama karantawa, wannan ai ya wuce habibi yanzu, ya zama bugawr zuciya ta, ji nake ma kaman in kwasa inje in gano shi in dawo, nayi kewaye fuskar tashi da taje cike da kwarjini da kyawu da haiba. Mai gyaran jiki ce ta shiga yi mani dariya, tana mai faɗin wannan angon dai nasan duk abun shi bai kai amaryar tamu ba. Da "Uhmm" kawai na bita, saboda bansan me zan faɗa mata ba kuma, ta bari idan anje wajen kamu ɗin ta gane ma idanun ta. Nan da nan aka buɗe masu sashen da aka tanadar ma anguna. Shima ango ɗaki guda aka ware mashi shi kaɗai, ashe shima da guzuri shi yake tafe, komai nashi a kammala na kayan da zai sanya, Amman duk da haka ba'a bar shi ba, ai tuni sarkin gida ya shiga cikin kirari zuwa ɗakin na Ya Ameen ya isar mashi da kayan da zai sanya, ai kaman an auna shi haka kayan suka zauna mashi a jiki das. Goldeen colour ne, yaji ne ɗan uban su, ya sha aikin masarauta mai ruwan cofee, har da hular da zai kafa da takalman da zai sanya, duka haɗe suke cikin wata ƴar jaka mai kyau, kai hatta da single da boxer akwai a ciki. Murmushi yake saki, tin da yake bai taɓa tunanin hidimar bikin nashi zata kasance a haka ba, domin shi da a tunanin shi ba ma a ƙasar za'ayi shagalin bikin nashi ba, sai gashi da gani ko a ƙasar wajen ma aka je ba lallai ya ƙayatar ɗin ba ma kaman hakan. ********** Zuwa ƙarfe biyar an gama tsara komai, kowa yaci abinci yayi salla da wanka. Nan fa aka fara fitowa zuwa cikin lambun, inda za'a gabatar da kamun, kowa ka gani yaci kwalliya yayi kyau, abun gwanin ban sha'awa, ga gudajen talabijin suna ta fama haɗa kayan ɗaukar su, harda su Arewa 24 da sauran manyan tashoshi. Wuri ne da aka ƙawata da kyale kyale irin na kamun sarauta.komai ka gani wurin nan sabo ne dal kujeru ne ne jere reras kowanne da table a tsakiyar shi, an ɗiɗɗora mashi mafittai masu kyau irin na gidan sarauta da wasu irin lemuna da cups masu kyau. An tsara wajen iya taruwa, ga wani irin ƙyakƙyali dake zubkwa daga sama, wanda masu decoration ɗinne suka rarrataye jakunkunan kyalkyalin. Duk da yamma ce, rana bata kai ga faɗuwa ba, saida aka kunna fitilu da kyandura masu matuƙar kyau da haske, ga kuma wasu irin electric buners manya, an zuzzuba ruwan turaren ƙamshi ciki sai tafasa suke, suracin ne ke fidda wani sassanyan ƙamshi. Wuri da ya ƙawatu, a hankali wasu mutane da aka ɗauko musamman domin su shirya wurin, watau organizers suka fara tsara yanda mutanen ke zama. Su mama Fulani ma sun ƙaraso wurin, Umma ta dai cewa tayi ba zata je ba, da kyal aka lallaɓa ta ta fito ita da Mama Fulani, da sauran matan sarki, rumfa ɗaya aka ware masu, sai rumfar dangin ango daban, tana fuskantar ta su Umman. Sai ta mutanen masarautar wadda ke fuskantar wurin zaman amaren. Kujeru goma gefen amarya, goma gefen ango, watau wajen zaman abokai da ƙawayen amaryar kenan Gefe guda an jera kayan ciye ciye sosai da sosai, da plates masu yawa manya, sai Abunda mutum yaga dama zai ce a zuba mashi, duk da babu wanda yake tare da yunwa, Amman wannan na musamman ne. Bayan kowa ya zazzauna ne mai gabatar da taro ya fara buɗe taro da bayani, haɗi da yin kirari ga masarauta da mai martaba da baya wurin, sannan Mama Fulani, da sauran matan sarki, Sannan Umma a matsayin ta na Uwa ga amarya, kuma hasken masarauta, kaman yanda aka bashi a rubuce. da kuma dangin ango da suke halarce a wurin. Dogon jawabi yayi na godiya, inda ya ke faɗin suna dakon shigowar ango da tawagar shi. Nan kowa ya zuba ma hanyar da aka ƙawata da furanni, inda ta nan ne amare da anguna zasu fito. Tafe suke cikin shadda dakakkiya, saƙar kamfanin gizna, sai ɗaukar idanu suke yi, kalar ruwan toka mai haske, ɗinkin nasu irin ɗaya ne, watau Abuja stile. Daga tsakiyar su ango ne wanda yake tafe cikin wani irin taku irin na gidan sarakai, dama Ya Ameen da ƙwambo, balle yau da take rana ta musamman. Ranar da ta buɗe babin samun Suhan ɗin tashi. Sun matuƙar burge kowa, balle ango da yake ta sakin murmushi, yasha naɗi irin na sarakai, tafe yake wani da ke ta bayan shi yana gyara mashi zaman babbar rigar tashi da akayi da kaftani mai ruwan ya ɗin nashi, shima cofee ne da aikin zaren golden a jikin shi. Ya burge kowa dake wurin. Wajen zaman shi aka nufa dashi, inda aka gyara mashi ya zauna, daga inda yake zaune, zai iya hangen Umma surukar tashi da fuskar tata ba yabo ba fallasa, su kau su Hajiya Laila sai washe baki suke, suma cikin ankon da aka basu wanda masarauta ta ɗinka ma kowa. Nan aka cigaba da gabatar da shirye shirye, inda mai gabatarwar yake ta jaddada a fito da amarya. Wata haɗima ce ta ƙaraso inda yake tsaye da loudspeaker riƙe, ta sunkuya tana mashi magana a hankali. Inda ya shiga jinjina kai yana sakin dariya, sai kuma ya cigaba da cewa *Ah Jama'a muna mai ƙara baku haƙuri da jinkiri fitowar amarya, saƙo ne daga uwargidn sarki akan cewa amarya ba zata fito ba, har sai ango ya biya sisin gwal ɗin duk takon nata ɗaya* Nan fa wuri ya kaure da hayaniya, masu dariya nayi, masu ƙananan surutu nayi, su kau su Bilal sai faman murmushi suke yi, da suke zaune ta gefen ango daga ɗan nesa da kujerar alfarma irin ta sarakan nashi. Tsit wuri yayi, duk hankalin su ya koma kan Ya Ameen da yake zaune cikin naɗi, da sarauta irin tashi, hatta zaman da yayi abun kallo ne. Da hannu ya ya fito wani bafade da yake gefen shi tsaye yana mashi firgita da maficin bindin ɗawisu. Raɗa shima yayi mashi, inda wannan bafaden ya naɗe babbar riga ya sake rugawa wajen mai gabatar da taron watau *Mc Malam Ibrahim shahrokhan* Yana gama faɗa mashi, sai ya kuma sakin dariya shima yana hura loudspeaker ɗin dake hannun shi still. *"Ah Jama'a saƙo daga bakin Yariman Matasan Arewan kuma angon Gimbiya Suhana insha Allahu, cewa a faɗa maku ya bada sisin gwal ɗari biyu"* Ai da nan wuri ya kaure da sowa da tafi. Wata zabiya ce ta ɗauri guɗa, "Ayurriririeie" Gimbiya tayi kasuwa, gimbiya tayi goshi, gimbiya tayi sa'a. Allah ya fito mana da gimbiyar tamu lafiya. Sai kuma aka ga wani ƙyakƙyali ya kuma fashewa ya shiga sheƙo ma mutane daga sama. Ƙamshin da ya ziyarci hancin kowa, shine ya tabbatar ma mutane cewa Gimbiya Suhana tana tafe. Nan fa hankalin kowa ya koma kai. Tafe suke sanye cikin asoebe ɗin su sun sanya ta tsakiya, a hankali suke ɗan rausayawa cikin ki ɗan da aka saki mai ɗaukar hankali na welcoming ɗin amarya. Gefen ta na dama Afnan ce sai raihana da Hafsat sai Huda, gefen ta na hagu kuma Jiddon dady c, sai Asiya ƙanwar Sir Salim, sai ƴan matan nan guda biyu ƴaƴan su Aunt Hussaina na kankiya. Daga gaban su kuma wasu ƴan yara ne darare masu kyau da gashi suke tafe suna watsa masu wata irin flowers suna fesa masu wani irin ruwan turare mai ƙanshi, inda ya karaɗe ilahirin wurin da ƙamshi. A hankali ya saki wata irin ajiyar zuciya, lokaci guda yana mai sakin sanyayyen murmushi hango fitowar tata da yayi. Itama sanye take cikin doguwr rigar wani irin codelace mai masifar kyau da walwali, jikin shi duk duwatsu ne suna ta ɗaukar hasken fitilun da ke wurin. Alkyabbar dake jikin ta golden ce, yayin da Kace ɗin ya kasance Cofee. Ta sha make up sosai, kaman ba Suhana ba, hancin nan ya ƙara tsawo, gashin idanun ta kuwa dama ba'a sanya masu komai ba, sai kaɗawa suke yi cikin duhn mascara ɗin da suka sha. Kai tsaye kujerar da ta kasance 2seater wadda ya Ameen ke kai ana zarce da ita, saida ƙawayen nata suka gyara mata zaman nata, sannan suka koma bisa kujerun nasu suma suka zazzauna, waɗanda kuma aka ga sun rage aka kauda su wurin. A hankali ya kuma sakin ajiyar zuciya, shaƙar daddaɗan ƙamshin ta da yayi, yana mai ɗago hannun shi da yake dunƙule cikin na juna da kamo hannun nata guda ɗaya ya runtse. A hankali itama ta ɗago tana mai ɗora fararen idanun nata da suka sha kalli raɗau akan tashi fuskar. A tare suka saƙar ma juna ɗan murmushi mai ƙayatarwa, inda ya ɗan ranƙwafa kusa da ita yana mai faɗin "you look so cute my groom i missed u aloot" Wani murmushi na kuma saki ina mai yi mashi fari da idanu haka kaɗan, sai kuma nace "ai Ka fini yin kyau my yarima" Bamuyi aune ba sai muka ji Mc na faɗin "Gaskiya fa daga i amarya da angon nan suna matuƙar ƙaunar junan su, duba kuga yadda yake faɗa mata magana mai daɗi ita kuma sai faman doka mashi murmushi take yi" Ɗan zabura nayi a hankali, kunya tana mai baibayeni. Saje runtse hannuwan nawa yayi a hankali yake faɗin "ki natsu Suhaann" Natsuwar nayi dole, ina mai sauke kaina ƙasa cike da kunya, masalan da na hango har Fulani na murmusawa take yi, umma ta dai ce ta kauda kai gefe. Nan ya cigaba da gabatar da shirye shirye, har aka zo kan inda abokin ango zai bada tarihn ango. Ban fa Bilal ya miƙe cikin ƙwarin guiwa ya fara gabatar da tarihn angon. Kowa murmushi yake yi, nan fa mutane da dama suka ƙara yaba dacen da amaryar tayi, Khadeeja kuwa ina kallon ta saidai ta sauke kai ƙasa tana wasa sa yatsun hannun ta, ita kuwa Jiddo dake pecing ɗin Dady ɗin nata, sai signal take saƙar mashi da idanu ɗaya suna sakin murmushi. Kowa ya yaba ma Ya Ameen, ya jinjina mashi, masalan taimakon marasa ƙarfi, da kuma gajiyayyu da yakeyi, ga tallafawa marasa da ayyukan yi, da kuma taimaka ma ƴan gudun Hijira, wanda akwai wasu daga cen sansann manyan su da suka zo suka wakilce su, to suma sun amshi loudspeaker sun ƙara yaba mashi haɗi da jinjina mashi, haka shugaban kamfanonin ya Ameen ɗin da Alhaji Mustapha. Nan kowa ya koma ya zauna, inda wuri ya ɗauki tafi da sowa, haƙiƙa a wurin ba wanda ya Ameen bai burge ba. Ɗaga idanu kawai nayi na HANGI Sir Salim a cikin abokan ango, ya ɗan rame kaɗan. Saƙar mani murmushi ƙarfin hali yayi, yana mai ɗan mani jinjina kaɗan haka da hannuwan nashi. Ita kuwa Asiya sai taɓo Afnan da take gefen ta zaune tayi ta shiga nuna mata Sir Salim ɗin. "Yayana ne dear Afnan baby" ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya. Kallon shi tayi da murmushi, sai kuma ta ɗan ɗaga mashi hannu alamar Hi! Shima murmushi ya sakar masu, masalan ma Asiya da take ƙanwar shi. Hannu ya ɗaga mata itama, yana mai kafe ta da idanu, hangen tsabar kamar da takeyi da Al'ameen dambulan yayi, sai kuma ya ɗauke kia shima yana mai hangen Ammin shi da take cikin rumfar su Mama Fulanin kusa da Hajiya Zainab da Umman Suhan, matar da yaji yana ƙauna kaman mahaifiyar shi, kuma har yanzu a haka yake jinta, duk kuwa da cewa ya gano shaƙiƙiyar alaƙar dake tsakanin su. Har ta ɗauke kai sai kuma ta maida idanun ta bisa fuskar tashi da yake kallon Ammin tashi. "Hmmm" ta sauke ajiyar zuciya, tana mai taɓo Asiya. "yayan ki mai kyau Asiya, haske kawai zaki nuna mashi" "Ai kema Ya Ameen ya fiki kyau, ƙila hakan ne ma ya sanya yayi mana ƙwace" itama ta bata amsa tana mai kanne mata ido ɗaya. Ɗan murmushi gefen baki tayi sai kuma tace "Ya Ameen daban yake ko a cikin mu, kinga wacce?" ta faɗa tana mai nuna Aunty Feena da take zaune cikin tasu rumfar riƙe da Nasreem da akayi mata kwalliya sosai. "wow masha Allah, wacece waccen ɗin?" "Ita ce babbar yayar mu, ita Ya Ameen ke bi mawa" Ɗan warobidanu Aiya tayi itama. "Masha Allah Afnan, lallai kuna da kyau sosai, kaman ku kukayi kanku, ki dubi don Allah kaman ba yayar Ya Ameen ba" Asiya ta faɗa itama tana mai sakin murmushi, duk abun nan a hankali a hankali suke magana. "aikuwa dai, sai ma munje gida zaki ga sauran" "TO Allah ya kaimu lafiya, Afnan gaskiya har Naji kun burge ni wallahi, Allah dai yasa zaki amince da Yayan nawa, Amman fa yana da mata" Da kallo Afnan ta bita, sai kuma ta kaɗa kai a hankali "nima ina da saurayi na, ba'a nan ƙasar yake ba" Ɗan gimtse baki Asiyar tayi, sai tace "Ai na sani kyakkyawa kaman ki masha Allahu ai ba za'a ce babu saurayi ba, saidai muma wannan karon zamu yi mashi ƙwace ne kaman yanda kuka yi mana kuma muka haƙura" Ƴar dariya Afnan ta saki, tana mai maida hankalin ta kan Mc,da yake bada sanar war cewa Amarya zata je da ango wajen dangin ta ya nemi albarka, haka shima ango zai je da amarya wajen iyayen nashi su sanya masu Albarka, daga haka sai a bada damar ciye ciye. A hankali ya miƙe yana mai riƙe da hannun ta har yanzu. Suna burge kowa matuƙa, Rumfar ƴan kankiya da su Hajiya Sa'a da Hajiya Laila ɗin ya nufa da ita riƙe a hannun shi kai tsaye. Sai tafi da sowa akeyi, wani ɗan sauti na tashi a hankali wanda yake ƙara ma masoya shauƙi. A gaban su ya durƙusa da ita, yana mai duƙar da kanshi ƙasa garesu, nima yanda yayi haka nayi, Goggo Fatima ce ta miƙe haɗi da ɗago ni ta rungume tana mai cewa *"Barka da shigowa family ɗinmu gimbiya Suhan, ɗita ga hasken masarauta"* nan kowa ya kuma sakin wani tafin. A hankali a hankali suka shiga miƙewa suna rungume ni. Haa har suka gama, Aunt Feena kam harda peck ta mani a goshi tana mai faɗin "barka dai ƙanwa ta" Abun ya burge kowa. Inda muka kuma juyawa zuwa runfar su Umman tawa. Bayan ya gaishe su ne cikin girmamawa, sai kuma mama Fulani ta miƙe tana mai kamo hannuwan mu ta haɗe wuri guda "ga Amana nan mun baka Yarima" jinjina kai yake cikin gamsuwa. Da girmamawa. Inda aka buƙaci da mu koma wurin zaman namu za'a fara ciye ciye ne, inda ango ne zai ba amaryar tashi tuffa a baki. Cike da kunya nake amsa, Nidai jina nakeyi kaman ba ni ba, shi kau sia wani kashe mani idnau yake yi. Nan fa aka fara ciye ciye, inda Mama Fulani da Umma suka miƙe suka koma cikin gida, yayin da aka cigaba da gabatar da sha'ani. Wayar Hajiya Laila ce tayi tsuwwa, tana ɗago wayar taga Hajiya Kubra ce. Miƙewa tayi tsam tana mai barin wurin saboda ƙarar kiɗa a hankali a hankali da hayaniyr mutane, kuma bata so aji Abunda zata faɗa. "Hello laila kina ji na? Me kuke haka ne har yanzu baku dawo ba wai? Ku yanzu har jin daɗin sakin jiki zakuyi ku zauna a ƙauyen nan?" "Hajiya Kubra bana jinki, idan kina ke kaɗai please ki kunna data, zan nuna maki wannan ƙauyen ki gane ma idanun ki" Hajiya Laila ɗin ta faɗa tana mai katse kiran wayar ta kira Hajiya Kubra video. Kai tsaye batare da tace mata komai ba ta shiga hasko mata inda ake ta hidimar shagalin kamu ɗin, ga mutane cen suna ta cin dukkan abubuwan da suke so, wasu kuma ƙawayen amaryar suna tare da abokan ango suna magana, wajen sai haske yake da walwali cikin fitilu masu launi daban daban, kasancewr duhu ya fara ratsawa. "Laila menene haka? Yanzu haka yaron nan yaje ynaa masu ɓarin kuɗi? Haka ya kashe kuɗi da yawa, Shiyasa bai bari na sani ba? Wallahi zai dawo ya same ni, sai na mugun saɓa mashi" "Kubra wai wace magana ce kike faɗa haka? To ko Sisin Al'ameen babu a wannan hidimar, ina so ki sani Suhana da Maryama dai jinin sarauta ne, tinda kin gane ma idanun ki, to tabbas ki tsaya ki cenza tunani, domin dai abun ba haka yake ba yanda muke tunani, kuma da wuri zamu dawo gobe domin muje a warware Abunda akayi ma yaran, saboda Al'ameen ya shigo babban gida, gudan sarauta, inaso ki sani yanzu wannan Suhanan da kika sani ƴar aiki ta tashi ta koma Gimbiya Suhana, idan inda kike akwai tv to ki kunna zaki samu sauran ƙarin bayani, ki natsu fa, Amman Abunda nake gaya maki tabbas haka yake" ta faɗa tana mai sake jaddada ma Hajiya Kubran, sannan ta katse kiran. Ai faɗuwa ne kawai Hajiya Kubra ba tayi ba, dakyal ta daddafa ta isa ga gadon nata, dama Allah ya so ta, ita kaɗai ce cikin ɗakin sai saudat da Nihal. "mom Mom lafiya me ya same ki? Mai Ya Ameen ɗin yayi" Abunda suke faɗ ake an suna mai rige rigen isa gareta suka kama ta suka riƙe. "Ƙarya ne, ƙarya ne ni Kubra za'a shirya ma wasan kwaikwayo? Ni za'a raina ma hankali? Ni za'a maida mara wayau? Laila duk ina wayewar taku? Ni da zaku kawo ma labarin gazawr su, ni zaku kawo ma labarin ƙoƙarin su? Ba zan taɓa yadda ba wallahi, wannan ma abun plan ne aka shirya mani, in haifi yaro da ciki na, Amman ya nuna yafi ni wayau" Sambatu take ta yi da ƙarfi. Su kau su Nihal sai faman tambayar ta suke ko lafiya "Ke kunna mani Tv dannubankinnake ki kamo mani arewa 24" Abunda ta faɗa kenan tana mai daka ma Nihal ɗin tsawa. Jiki na rawa ta ɗauko remote ta shiga kunna tv ɗin, hankalin ta tashe itama, sun rasa dalilin rikicewar Mom ɗin tasu haka suddently. Tar Abunda ake haskawa ya shiga karaɗe ilahirin allon Tv ɗin. Kaman a gaban su ake gudanar da komai, me ke shirin faruwa, suma basu kuma ruɗewa ba, saida aka kuma dallo fuskar Ya Ameen ɗin da Suhan yana gaya mata wata magana tana sakin murmushi, har rungumk ta yake yi kaɗan zuwa jikin shi, yana mai bata wani abu a baki itama tana riƙe hannun shin tana bashi. Side lamo dake ajiye bisa side drower ta ɗauka tana mai wurga ma Tv ɗin. Kashe ta Saudat kashe ta, ni za'a raina ma hankali, Al'ameen ne haka tare da waccen maƙasƙanciyar ƴar aikin haka? Har yana rungume ta? Su Laila sun tabbata marasa hankali da suka yadda suka zauna wajen wannan wasan kwaikwayn nasu. Aiko tini scream ɗin tv ɗin yayi raga raga, sia Sambatu taje yi tana ihu, daga ita sai Su Nihal cikin ɗaki, suma hankalin su a tashe suka shiga kiran Layin Dad. A ci sa'a baiyi nisa ba, sai gashi ya hauro saman nata, mutane sai gaishe shi suke yi. "Lafiya kuwa Kubra, kina lafiya haka? Me ke samun ki?" "Alhaji ni za'a raina ma hankali? Ni za'a shirya ma wasan kwaikwayo, da za'a wani ce Suhan da Umman ta ƴan gidan sarauta ne? Ka dubi fa yanda yaron nan yaje yana kashe masu kuɗi har haka..." Dakata Kubra, labarin da kika samu gaskiya ne, haka ne, ina ce su ƴan rahotn naki sune suka sanar dake komai? To ba wasan kwaikwayo ko ƙanzon kurege a ciki, su ɗin jinin sarauta ne gaba da baya, kuma ina so ki sani idan zaki hankalta sai ki hankalta ki san kuma ne kike yi, idan ba so kike ki bar abun faɗa ba a taron bikin yaron naki, aure kau babu fashi insha Allahu ko da yardar ki kuma ko babu, don haka shawara ta rage taki.. " Yana gama faɗar haka ya juya cike da ƙaunar zuciya ya fice daga ɗakin, yana mai gangara wa down stair yana zancen zuci. Baiga ranar da Kubra zata hankalta ba. Ita kuwa kuka ta fashe dashi, tana mai huci kaman kububuwa, lallai wannan rainin wayau da yawa yake, ku ji fa wai Alhaji ne ke sanar da ita cewa abun da laila ta gaya mata gaskiya ne. Mu kau bayan an gama ci an gama sha, sai aka sakar mana kiɗi har da Hamisu breaker da Umar M shareef saida suka zo suka taya mu chashewa, a hankali muke taka wa lokacin da aka bada fili ga ango da amarya. Liƙen kuɗi dai mun sha shi, wannan karon harda Sir Salim da yayi matuƙar ƙoƙari waje danne zuciyar tashi. Haka aka gama hidimar kamu ɗin, inda ya ƙawata kowa, jikkar surviniers ce aka ajiye kowa a gefen shi. Turare ne mai kyau da ƙamshi da kwalin tissue da hanky, babu photon mu a jiki, saidai sunan mu kawai, wannan kuma aikin Ammi ne, inda ta sanya Sir Salim ɗin yayi mani a matsayin gudunmuwa. Ko bayan da aka watse ni ɗakin da aka fiddo ni cen aka maida ni, haka aka kwana ana maganar kamun nan, inda ko shi ya Ameen da kyal muka samu muka ɗan yi waya dashi, saboda irin gajiyar da nayi ga bacci ina ji. Washe gari da suka tashi komawa, masarauta ce tace ba zasu tafin ba, ai su jira kawai ayi ɗaurin aure a basu amarya, haka kuwa akayi ranar Juma'a ɗin aka sanya ni a lalle. Ɗan bala'i hajiya kubra ko kiran su Hajiya Sa'a bata sake yi ba. Hakan bai masu daɗi ba, kuma ko sun kira ta bata ɗagawa, ranar kuma ko falo bata sauko ba, tana ɗaki tana ruwan masifa, inda bata bari kowa ya fahimci halin da take ciki ba. Shi kau malamin nasu, koda Su Hajiya Sa'a Suka kira shi, cewa yayi aikin gama ya gama, saidai Abunda ba'a rasa ba, Amman don tsabar ta fa sai ya tsane ta, kawai dai suyi ƙoƙarin ganin ya kusance ta, muddin suna so abun ya karye. Haka suka dinga sa ƙawa da warwarewa, wannan karon kuwa suna ji suna gani ba zasu bari Kubra ta rasa damar ta na samun jikoki wanda suka fito daga wannan babban tsatson ba, ba zasu bari ƙiyayyar ta sanya idon ta ya kulle ba, su sun ma yi mamakin da har yanzu bata gazgata abunda taji an faɗa mata ɗin ba.ko da yake ba zata gane bane, tinda ba wai gani tayi da idanun nata ba. ******* Ranar Asabar ɗin kafin kace me gari ya cika da baƙi, jini ya kaje ji ko ta ina tana tashi, ɗaurin auren fa ya karaɗe lungu da saƙon ƙasar, mutane ko ta ina ɓulɓulwa suke yi, ranar ne fa jikin Hajiya Kubra ya fara sanyi, ganin sanarwar ɗaurin auren da kafafen yaɗa labarin keyi, akan cewa lallai ɗiyar masarautar *Mai martaba Muhammadu Bello Barkindo Lamiɗo ce* Jiki a mace take aiwatar da komai, har kai lokacin da tawagar iyayen angon ta ɗauki hanyar tafiya, baƙi kuwa ko ta ina ɓulɓulwa suke, matan manya ne cike da sashen Hajiya Kubran da Sashen ƴan kankiyar, abinci kuwa sai shiga da fita dashi ake yi. Inda hankalin ta ta ɗan kwanta da taji duk wanda ya shigo yi mata murna sai yace yana taya ta murna da haɗa iri da masarautar da tayi, kenan ajin nata da take gudu ya zube bai zube ba? Dayake ƴar duniya ce sai ta saki jiki, ta haɗe cikin wani arnen lace, kai kace dama cen ta yarda da auren ne, sai washe baki take, inda ake ta zuba mata ruwan kuɗin gudunmuwa tana karɓa, domin wasu kuɗin ma cikin farar ledar su ake bata su haka, saidai ta wurga su cikin wata ƙatuwr sip dake ajiye gefen nata. Ta sha gwala-gwalai, ko su ƴan kankiyar sunyi mamakin yanda ta saki jikin ta, sai shiga da fita takeyi, har sashen nasu yau ba zasu iya ƙilga shigar ta nawa ba, Amman idan ta tuno da Abunda suka ƙulla, har yanzu zuciyar ta ba wai ta amince bane ko bata amince ba, bata kuma sani ba, tayi nadama ko ɓarayi ba, har sai ta tabbatar da zahiri. Haka masu kirari suka cika ƙofar gidan, maroƙa da mawaƙa, duk da wai ba'anan ma ne za'a ɗaura auren ba. Da misalin ƙarfe ɗaya da rabi dubban mutane suka shaida ɗaurin auren *Gimbiya Hauwa'u Muhammad da kuma Angon ta Yarima Al'ameen Almustapha Dambulan* akan sadaki naira dubu ɗari. Inda aka kuma bayar da dukiyar aure naira miliyan ɗaya, wannan kyauta ce daga asusun Alhaji Auwalu Yusuf uban ango, zuwa ga amarya Gimbiyar tasu. Ɗaurin aure yayi mutane, kowa ka gani sai washe baki yake, a faɗa aka ɗaura auren, inda aka zarce da shagalin cin abinci kai tsaye. Ba'a so a ɓata lokaci, saboda yanayin hanya, duk da yau dai kam an zuba jami'an tsaro kala da kala a hanyar, saboda kai kawo ɗin ƴan ɗaurin auren da wasu ma daga nesn duniya suka fara isowa tin jiya saboda yarima na matasa ne. Umma kam uwar amarya ba'a cewa komai, sai walwali take yi, haɗimi na ta faman hidima, su Hajiya Zainab da Ammi ne kan gaba gaba wajen aiwatar da komai. Inda mama Fulani ta sakar masu ragamr komai, duk da ba da Umma za'a tafi ba, Amman daga Hajiya Zainab har Ammi sunce ba za'a tafi kai amaryar ba tare dasu ba, wannan karon dai kam harda Fulani, da kuma matar shugaban ƙasa cikin waɗanda zasu yi ma amarya rakiya zuwa ɗakin ta. Nasha Kuka yau bansan dalili ba kuma, haka ak fiddo ni, fuskabjabge da hawaye zuwa wajen mai martabar, faɗa sukayi mani sosai da sosai, inda aka maida ji wajen Umma da su Fulani da su Hajiya Zainab da Ammi. Nan ma dasawa suka yi, inda su mai martaba suka tsaya. Nan fa aka fara hada hadar haɗa motoci na tafiya kai amarya. Inda Su ya Ameen da wuri suka wuce domin haɗa takar angon da zasu yi ta yamma liƙis, lokacin amary ta iso. Tin cikin mota kan nashi ke mashi ɗan ciwo haka kaɗan kaɗan, ba suyi mamakin ganin ya kama bacci ba a motar, sanin irin gajiyar da ke jikin shi da sukayi. Su Yi tafiya mai nisa ne ya farka yana mai tambayar Bilal wai har yanzu basu isa ba? Bilal ne ke sanar dashi ai sun kusa, suma amarn sun yi waya cewa gasu nan sun taso. Ɗan tsaki taja yana mai cewa "Bulal hawan da bar na fa bana tunanin zai yuwu gaskiya, ni fa hidimar nan ta ishe ni, ba za'a iya barin ta ba wai?" Da mamaki Bilal ɗin ke kallon shi, kaman ba shine ya matsa akan su tafi su shirya komai ɗin ba kan lokaci, saboda yana so ya burge amaryar idan an iso da ita, gashi kuma sun haɗa gagarumar dinner ɗin da daddare. " Me kake nufi ne wai Friend? Naga sia wasu abubuwa kake yi, kaman ya abar hawan?" "Eah a bar shi kawai fa, ni har dinner ɗin ma bana tunanin zan iya halarta, kai in short ma fa, ni na fara tunanin menene dalilin da ya sanya ni amince ma auren yarinyar fa da nayi" Burki Bulal ɗin yaci da ƙarfi, har abokan tafiyar nashi suma suna yin larking, Allah Allah suke yi dai ba wani abu ne ya samu motar da angon yake ciki ba. Da matuƙar mamaki Bilal ɗin ke kallon Al'Ameen. "Ban fa fahimce ka ba fa malam, me kalaman ka ke nufi ne Al'ameen? Kaman ya? Anya kuwa lafiyar ka ƙlau? Kasan me kake faɗa kuwa?" Da masifa cike yake kallon Bilal, malam me ya hana kai ka aure ta? Me ya hana? Auren nan sai nake ganin kaman tursasa mani akayi nayi shi, ni fa Sam yarinyar ta fita a kaina, gaskiya bana tunanin idan zan iya jure ma zama da ita" Ganin kaman abokin nashi ya zare be, ya sanya ce ma sauran abokan angon su koma motoci su, ba matsala yanzu zasu gyara Suma dai basu kai ga fahimtar inda kalaman abokin nasu ya suka dosa ba, suka koma mota jiki ba kwari, inda sukayi ma motoci key suka sake ɗaukar hanya. Shima Bilal tada motar yayi yana mai girgiza kai yake faɗin "you are not fine gaskiya friend, baka da lafiya ga dukkan alamu, Allah dai yasa ba stress bane ya kama ka." "Ba wani Stress Bilal, I AM Al'ameen Dambulan, and I am fine is u can see" "Girgiza kai Bilal yake" Kafin ka ɓata mani rai, zaifi kyau kayi shiru kawai friend, hawa ba fashi kaman yanda dinner ma haka babu fashi insha Allahu, yanzu haka ma nayi waya an gama shirya komai, kawai isar tamu ake jira. Cikin serious tone Al'ameen ya shiga kallon ya Bilal, sai kuma ya fara magana cikin ɗaga murya *"NACE BA ZANJE BA KUMA KAI BAKA ISABKA SANYA NI INYI ABUNDA BANYI NIYYA BA BILAL, U KNOW WHO I AM, BANA MAGANA BIYI, DON HAKA SAI KUJE KU KUYI TA YI, AURE DAI NE NA FAƊA DA BABBAR MURYA CEWAR NAYI NADAMAR YINSHI SAI KUMA YAYA???"* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Zikiri in an zauna a wani Majalisi Ibn Umar ya ce; an kasance ana kirgawa ga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a majalisi guda kafin ya tashi, yana cewa sau dari. رَبِّ اغْفِرْ لِي، وَتُبْ عَلَيَّ، إِنَّكَ أَنْتَ التَّوَّابُ الغَفُورُ. Rabbigh-fir lee watub 'alay, innaka antat-tawwabul-ghafoor. Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ka yi tuba a gare ni. Lallai Kai ne Mai yawan karbar tuba, Mai yawan gafara. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~62~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Ai sai jikin shi yayi sanyi kuma ya shiga bin Al'ameen ɗin da kallo, wanda idanun shi kulle yake ta surfa bala'i. Bai kuma ce mashi ƙala ba har saida yayi ya gama, ya koma yana mai jingina da ma karin kujera cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya kaman wanda yayi uban gudu. Maida hankalin shi yayi akan tuƙin da yake yi, bayan ya janye idanun nashi da suka fara cenza kala daga kan abokin nashi. Allah ma yaso suhuɗu ne kawai cikin motar, shi da Al'ameen a gaba, sai Abir da Sadeeq ɗin Hafsat a baya. Motar ta ɗauki tsit na wani lokaci. Sai cen ne Bilal ɗin ya kuma nisawa yana mai cewa "Friend you am very sure you are not in your mind, defenetly akwai Abunda ke damun ka, ni dai nasan baka shan komai balle ince ko ka kurɓa ne..." "Wuta nasha, Kaga Malam kada ka sake man maganar da ta shafi yarinyar nan, kada ka tunzura ni, ince a maida ta gida" "What?" Bilal ya tambaya cikin wani irin mamaki. Anya kan abokin nashi ɗaya kuwa? Ta baya yana iya hangen jerin motocin abokan nashi na ta sharara uban gudu, saboda su isa da wuri a fara shirya Abunda za'ayi. Girgiza kai kawai yayi, haƙƙun Al'ameen fa na neman dagula komai, to indai ba aljani bane suka kama abokin nashi ba, shi bai san ma me zai kira hakan ba. Abie dake baya shi kanshi kulle yake, yana ce ai Yayan nashi ne ya nasta akan sai ya auri yarinyar, a yanda yake samun labari, to in ko haka ne lallai ba banza ba, ruwa baya tsami banza, bai san halin da Mom ke ciki ba game da auren, hakan ya sanya sai bai tanka ba, kawai ya ɗauko wayar shi ya shiga rubuta ma Mom saƙon halin da ake ciki. Shima Sadeeq mamaki yake yi sosai, to ai in yanda Hafsat ke faɗa mashi gaskiya ne, bai ga dalilin Al'ameen na yin hakan ba, Al'ameen da yake mai halin dattako irin na manya. Aiko sai ga kiran Mom ya shigo wayar Al'ameen ɗin. A hankali ya ɗaga wayar, yana mai lumshe idanu, bai ga dalilin bijire ma Mom akan maganar auren ba, gashi tin kafin aje ko ina yarinyar ta fita a ranshi, ko sunan ta ma baya son a ambata mashi. "Idan kun iso ka shigo ina neman ka da gaggawa" Mo ɗin ta faɗa cikin ɗaga murya da tashin hankali sosai. Tana jin zata iya saɓa ma Al'ameen muddin yace zai kawo tangarɗa ga kasancewarta Surukar masarautar da take da tarin girma da ɗauka ka. "OK Mom" Abunda ya iya faɗa kenan, ya zare wayar a kunnen shi, yana mai sauke wata ajiyar zuciyar, ya tabbata kiran Mom ba zai wuce ƙila ya rabu da yarinyar ba, inko haka ne, babu Abunda zai hana shi yi mata biyayya a wannan karon, Sam basu dace da Suhan ɗin ba, shi bai san ma menena yaja ra'ayin shi akanta ba. Cikin tashin hankali Mom ta sauke wayar a kunnen ta, sai kuma jikin ta ya ɗauki ɓari, kadai ace aikin Malamin su Hajiya Sa'a ne yayi aiki. Cikin rawar hannu ta shiga latso number ɗin Hajiya Laila, tana mai gangarowa daga saman ta, ta ratso ta cikin jama'a manyan mata da ake zazzaune a fali nata suna ta zuba isa. Part ɗin Alhaji ta nufa kai tsaye, tana mai buɗewa ta shige. "Hello Laila, kuna ina ne? Kun kusa ƙarasawa ne?" "Uwar ango kenan, eh bai fi saura awa guda ba, mu ƙara so, Lafiya dai ko?" "Ina fa Lafiya Sa'a, aikin malamin nan wlh ya fara aiki akan Son, please ya za'ayi, ki sake kiran shi fa akan ya warware komai, yanzu na gane kuskure na, bana so wani abu ya kuma ɓullowa, tinda na gwada ma kowa na amince sai a cigaba da tafiya haka, ni yanzu ko da KUNYAR alhaji ma aka barni ai na sha ta." Ɗan waiwayawa Hajiya Sa' a tayi, ba ita kaɗai bace cikin motar, infact ma harda Ammin Sir Salim. " Kinga Hajiya Kubra, ki bari idan mun ƙaraso ma tattauna, yanzu muna bisa hanya ne" Jin haka daHajiya Kubran tayi ne, ya sanya ta gane cewa ba Hajiya Laila ɗin kaɗai bace a motar. "To shikenan Allah ya kawo ku lafiya" Ta faɗa tana mai katse kiran, sai kuma ta koma bisa sofa ta zauna, tana mai maida numfashi, zaman ba zai yuwu ba, ta miƙe ta shiga kai komo. Sanin da tayi ya zuwa yanzu ana cen ana neman ta ne, ya sanya ta fitowa jiki babu ƙwari ta koma sashen nata, saida ta biya sashen su Kaka zuwaira tayi masu ɗan yaƙe haka tana mai sanar dasu kusan ƙarasowar amaren. Da wani irin kallo suka bita, "uhmm to Allah ya ƙaraso dasu lafiya" da Abunda ƴan kankiyr suka bita kenan, suna mai jinjina hali irin na Hajiya Kubran, ta raina ma kowa wayau, gani take ita kaɗai ce ƴar bokon da zata yi masu wani ilaye duk cikin su babu wanda bai san bata son auren ba, yanzu haka wani munafuncn ne ta kuma ɓullowa dashi, tinda ko da safe tana ta ruwan bala'i da masifa, dandai basu kula ta bane. ****** Ni kau ina ƙumshe cikin alkyabbar da aka yafa mani, zufa nake ta haɗawa, duk kuwa da Ac ɗin dake busowa ta cikin motar, har ƙarƙashin kujeru, ma'ana wajen ƙafafun mu. Nasihar Su Umma kawai nake tunowa. Tabbas Umma tayi gaskiya, yanzu ba da bane, duk Abunda na gani wannan haƙurin da na saba shi zan cigaba da yi, domin yanzu ne ma zanyi haƙuri, saboda na kuma komawa ƙarƙashin inuwar mulkn ta. Gabana ke tsananta faɗuwa bansan dalili ba, ko zullumin shiga gidan ne nake? Tinda indai ta Ya Ameen ne bana jin shi, ya zuwa yanzu na gama gazgata irin ɗinbin son da yake mani, nima da wanda nake mashi. Na sha alwashin bashi dukkanin wata kulawa da soyayya ta, domin Ya Ameen ya wuce cencentar hakan a wuri na. Lafiyayyar rayuwa aure nayi niyyar shimgiɗa mana, mai cike da ƙauna, da zallar soyayya ta kula da tattashi. To inko haka ne, menene dalilin da yasa zan zullumin wani abu. Ba Hajiya Kubra na aura ba, ba kuma da ita zanyi Rayuwar aure ba, balle su wata Nihal cen da Saudat. Addu'a na cigaba da yi ɗauke a baki na, domin dai duk yanda naso in kauda wani zullumi, har yanzu zuciya ta ci gaba take yi da bugawa. Zna iya hangen motoci reras a gaban mu da bayan mu, wai duk ni za'a je kaiwa ɗakin nawa, to wannan wane irin gata ne kuma ban samu ba? Murmushi na saki, ina mai sake tunowa da cewa nan da zuwa gobe fa mun zama abu ɗaya da Ya Ameen ɗin. Hakan ta sanya ni sauke hamdala da wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, ina tuno moment da wasu kalamai da yake faɗa mani, masu cike da alƙawurran zaman lafiya da ƙaunar juna. ******* A Masarauta kuwa ya rage daga Umma sai sauran matan sarki da haɗimmai. Har yanzu akwai ɗinbin jama'a, ana ta cigaba da shagulgulan biki, duk kuwa da cewa an tafi kai amarya, Amman duk da haka wasu mutanen ne ke sake ɓulɓulowa. Manyan Motoci ne guda biyu ƙirar 4matic, baƙaƙe sal, suke tafe cikin masarautar har suka samu wurin da suka yi parking. Da kallon mamaki yake bin cikin masarautar, da gani dai wani abu ne yake faruwa, kaman wata hidimar akeyi, to Amman in haka ne kuwa shi yayi mamakin da babu wanda ya sanar mashi, ko kuma iyaln nashi, tin da ya shigo garin yaga alamun ana hidima, jama'a sia hada hada akeyi, ga manyan motoci da suke ta shiga da fita, a hanya ne ma yaci karo da motocin shugaban ƙasa sun riga sun wuce, hakan ce bai samu damar tsayawa ya kai gaisuwa ba. Fada ya nufa kai tsaye, to babu kowa dai ciki, da gani tau ba'a zaman fadancin ne, kai tsaye ya wuce zuwa babban falon sarki na cikin gida, haɗimmai da fadawa sai zubewa suke suna kai gaisuwa, yana mai ɗaga masu hannu cikin isa da taƙama. Shigar tashi ne ya sanya kowa miƙewa, banda Mai martaba, to shima dai duk manyantakar shi saida ya isa gaban mai martaba ɗin, yana mai duƙawa ya shiga kwasar gaisuwa. Cikin sannu da sauka mai martaba ke mashi magana, inda ya shiga bashi haƙuri akan abubuwa sun faru da yawa masarautar ba tare da an sanar mashi ba, hakan ya faru ne akan abubuwa sun zo ne a ƙurarren lokaci. Har yanzu dai bai gane inda kalaman sarkin suka nufa ba, matsa mashi akayi gefen sarkin ya zauna. Inda mai martaba ya sallami sauran fadawan dake wurin, saboda yana so yayi bayani, kuma ba hurumn su bane. Saida duk suka kwashi gaisuwa suka fita, sannan ne mai martaba ya gyara zaman shi a hankali yana mai fuskantar waziri. "Mai girma waziri, muna maka maraba da sauka, kuma muna mai baka haƙuri a bisa rashin shaida maka dawowr hasken masarautar, hakan ya faru ne kaman yanda na shaida maka cewa abubuwa ne suka zo a bisa ƙurarren lokaci, idan zaka iya lura ma tau masarauta tana cikin hidima ne, a bisa auren yarinyar hasken masarauta da akayi, watau Gimbiya Merama" Duk wannan bayanin yana yi mashi ne a rausashe, saboda ko ba komai Wazirin yayi sa'a da mahaifin shi. Cikin tsabar kaɗuwa da ɗimbin mamaki Wazirin ya ɗago yana maibkallon mai martaba ɗin. "Allah yaja zamanin ka, kace fa Merama ta dawo?" Gyaɗa mashi kai mai martaba ya shiga yi. Nisawa yayi yana mai cewa "amma Allah ya taimake ka, ka taɓa ganin inda matacce ya dawo? Sanin kowa ne anan cewa Gimbiya Merama ta daɗe da shuɗewa tsawon shekaru, to kuma tayaya za'a ce wata ta bijiro da sunan ta? Anya kuwa mai martaba wannan maganar ba abun dubawa bace?" Ɗan murmushi mai martaba ya saki, na daga cikin abunda ya sanya bai cika saka waziri a hidimar tashi ba kenan, shi tsoho ne gaddamamme, ga nuna isa da iko, wani lokacin har sarkin ma yana nuna mashi cewa shine gaba dashi tinda yayi sa'a da mahaifin nashi, kuma shine ma yayi ma mahaifin Sarkin waziri a zamanin shi, tin tsohon mai martaba ma yana raye. "Wannan magan taka haka take waziri, Amman al'amari ne da yake buƙatar dubawa a tsanaki, Amman Gimbiya Merama don ita, ita ce fa, saboda haka ne, muke so idan an gama shagalin bikin nan zamu zauna da ita mu tattauna, yanzu haka tana cikin gidan nan" Shima cikin wata kaɗuwr ya shiga cewa "ba komai Mai martaba, Allah ya sanya muji alkhairi, Amman abun da mamaki da ɗaure kai kam, ni zan shiga cikin gida saboda in samu in ɗan huta, a tashi lafiya" ya faɗa yana mai kuma russunawar ya miƙe gami da ficewa. Da kallo kowa ya shiga bin shi a fadar, wannan fa fararren abu bane, hasali ma kowa ya saba da hakan, shi fa duk Abunda za'a kawo maganar shi sia ya ja da ita, gashi da mugun son kanshi, shi yau bai ƙi ace an naɗa shi sarautar ba ma gabaki ɗaya kuma kowa ya san haka. Cikin gida kuwa tin da labarin dawowr Wazirin ta karaɗe, abun ka da gidan sarauta,labarin yaje har kunnen Umma, tin a lokacin ne aka rasa gane kanta, daga baya ma ɗakin ta cen ƙurya ta shige, tana mai cewa ayi mata haƙuri kanta na mata ciwo, Amman a zahirin gaskiya koda ta shige kuka ta shiga saki mai cin rai, gani take kaman mahaifin nata ma zai dawo, duniya babu gaskiya, zata ga da wane ido waziri zai iya kallon ta ya gaya mata wata magana, tinda ta samu labarin abokin cin mushen nashi ya daɗe da gushewa, sai shi kaɗai aka bari yana watayawa a duniyar, ba tare da abunda yake so ya samu ya samu ɗin ba kuma. ******* Suna isa ya ɓalle murfin motar yana mai ficewa, ko parking Bilal ɗin bai gama yi ba. Kai tsaye cikin gida ya nufa, babbar rigar ma yana tafe yana zare ta, har ya gama, daga shi sai fara ƙal ɗin shadda wadda rigar take iya cinya da wandon kayan. Shaddr ta haɗu, ta ji ɗinki sai walwali take yi. Mutane sai magana suke mashi "ango kasha ƙamshi, ran ango ya daɗe, masalan ma abokan wasan su na kankiya. Ba wadda ya tsaya kulawa balle ya bata amsa, fuskar nan tashi haɗe kaman an aiko mashi da saƙon mutuwa, duk da haka bai gusar da kyau da walwali da yake yi ba. Ga gyaran fuska da tasha abun sai wanda ya gani. Haka ya tsara falon, babu wadda ya gaida cikin matan dake zaune falon. Hayewa yayi sama, yana mai tura ƙofar ɗakin mom ɗin, tana zaune ita da wasu manyan mata da suka taho ƙafa da ƙafa tin daga Katsina yi mata murna, da taya ta murnar cewa ta samu suruka ƴar gidan manya. Kaman zaki saidai ta ganshi cikin ɗakin nata tsulum, matan da basu san meke faruwa bane, suma shiga washe baki suna faɗin "a'aha ai gama angon nan ya ƙaraso, ango ya hidima?" Ba wadda ya kalla still cikin su. "Mom gani kince kina nema na?" Itama miƙewa tayi cike da kaɗuwa da ruɗu tace "Eh kaje sahen Dad ɗinka ka jira ji, ina zuwa yanzu bari in sallama baƙi, aunties ɗinka ne, baka san su ba? Ka gaida su mana" Ɗan waiwayowa yayi, yana mai gaishe su, har yanzu fuskar nan haɗe, su kuwa washe baki suka shiga sake yi, kaf cikin su ba wacce bata yi ma ɗiyar tata sha'awr Al'ameen ɗin ba, saboda babu wadda ba zata so ya zama aurukin ta ba. Kuma sun ɗauka hidimar biki ce da jama'a suka hana shi walwala. Juyawa yayi ba tare da ya ko jira amsawr su ba ya fice, gangara wa yake daga bisa matakalar benen da uku uku. Nan d anan ya fice daga dakin kaman kububuwa, to suma sauran matan da kallo suka kuma bin shi, suna ayyana ma ransu cewa anya kuwa lafiya? Part ɗin Dad ɗin yayi ma tsinke, yana mai zare farar rigar shadda ɗin, ya rage daga shi sai farar singlet da dogon wandon shaddar. Kan Sofa ya zauna, yana mai ɗaukar remote ɗin Central Ac dake ajiye bisa stool ya shiga ƙara mata gudu. Ji yake duk duniya ta mashi zafi, babu Abunda ke mashi daɗi, kaman ba shi ba, kaman ba Al'ameen da yake awanni da suka wuce cikin farin ciki ba. Zamewa yayi ya kwanta samɓal, yana mai ɗora hannun shi ɗaya bisa fuskar shi, ɗaya kuma ya daɗe saitin zuciyar shi da yake ji tana habawa da matsanancin duka kaman zata tsago ƙirjin nashi ta fito. Shigowar Mom ce tayi sanadiyyar tashin shi zaune. Da sauri ta ƙaraso kusa dashi ta zauna, tana mai ɗan rungumo shi zuwa jikin ta. "Son baka lafiya ne?mr ke damun ka?" "Mom lafiya ta lau, saidai kawia ina so a fasa wannan auren ne, kije ki sallama kowa mom a shirye nake da inyi maki biyayya kaman yanda kika buƙata a cen baya" A zabure ta tashi tana mai matsawa daga inda take zaune riƙe dashi. Zuciyar ta na ta habawa "son kada kaja in kwaɗa maka mari fa, kada ka ja in maka mummunr magana wallahi, wane irin a fasa bayan an riga an ɗaura? Ya ne banyi dakai ba akan a faɗa ka kafe, sai yanzu da na riga na yarda har na tara mutane kace wani a fasa? Daga ina wannan tunanin yake?" Itama ta faɗa cike da nadamar, tana cewa aikin su ne ke aiki a jikin yaron nata. "Mom nine nace ina son ta, nine kuma yanzu nace bana son ta, Mom ki kira Dad a warware wallahi na fasa, bana jin son yarinyar ko ɗaya a zuciya ta yanzu" Cikin rawar hannu ta shiga latsa number ɗin Bilal, tare da ce mashi ya shigo sashen Dad ɗin, aiko sai ga Bilal a sukwane, domin suna cen har sun fara cenza kayan yin hawan takar angon, dawakan ma har an shisshirya su. Da sauri ta ƙara sa inda Bilal ɗin ke shigowa ta riƙo hannun shi "Bilal abokin ka baya lafiya, kayi mashi addu'a please, wallahi ina tunanin aljannu sun kama man shi" Cikin sauri ya ƙara sa ga Al'ameen ɗin da yake zaune dafe da kai, tallafe da fuska wadda har ta kaɗa tayi jajawur. Da sassarfa ya ƙara sa wurin shi yana faɗin "Friend what happened? Talk to me now" Zare tagumin yayi yana mai miƙe wa tsaye ya fuskanci Hajiya Kubra da Bilal, sannan ya shiga faɗin "Friend nothing to say, i have already said it! Ba zanyi ba na fasa, ai sai kuyi tayi, Mom ce da kanta tace bata so, and kuma na mata biyayya, ku kira Dad kawai kada su ƙaraso da ita nan gidan" Yana gama faɗin haka ya saɓi rigar shi ya zura, yana mai zagaye su ya wuce. Da kallo galala suka bishi. Bilal ne ya juya ga Mom da tsantsr tashin hankali yake bayyane a fuskar ta. "Mom kiyi haƙuri, ina jin akwai Abunda ke damun shi ne, zan san yadda zanyi dashi, Amman fa bana tunanin zai cigaba da bada goyon baya bikin nan ya cigaba kaman yanda aka faro shi, Mom ki natsu kada mutane su fahimci halin da ake ciki fa,i'ill tackle the isue" Shima yana gama faɗin haka ya sanya kai ya fice daga palon, barin Hajiya Kubra yayi da tsantsar tashin hankali, yana tafe yana girgiza kai, wannan duk sharrin Mom ne, gashi kuma ta fara gurbar Abunda ta shuka, shi bai san ma dalilin ta na yarda da auren har haka ba, balle dan Al'ameen yace baya yi har zata ɗaga hankalin ta haka, koda yake abun a bayyane yake, cewa yanzu ta san ko wacece Suhan ɗin, ba zata taɓa yarda wannan damar ta kufce mata ba, tinda B a shi kaɗai ba, har abokin nashi da kowa ma yasan dalilin ƙin auren nata, inko haka ne ta tabbata mai son abun duniya, wanda nata ya rufe mata ido kuma tana hangen na wasu, shi tun da yake duniya ma bai taɓa cin karo da mace kaman Mom ba, ga zafin nema, ga wulaƙanta wanda basu da shi, idan ba zai manta ba, friend ɗin nashi ya sha mashi complain akan halin Mom ɗin tashi, cikin halin damuwa, har yana faɗin da akwai yanda zaiyi ya cenza ma Mom halin ta da yayi, shi dai baya jin daɗin Abunda take yi. To sai gashi yanzu abun ya rikiɗe zai fara affecting ɗin Abokin nashi, ba zai taɓa sanya sanya ba, har wankin hula ya kai su dare, shi ya sani, jikin shi na bashi da hannun Mom a faruwr komai, saidai yaci alwashin tsayawa ga abokin nashi har ya samu Abunda yake so, Mom ba zata taɓa zama tarnaƙi na farin cikin ɗan nata ba kuma abokin nashi. Da haka ya ƙara sa inda auran abokan suke ana ta faman shiryawa, mai naɗi suka taho dashi sukutum daga masarauta saboda ya naɗa masu rawani na hawan da bar da za'ayi. Ce ma abokan yayi su cigaba da shiri kawai, Angon baya da lafiya, Amman insha Allahu zai sha magani, idan ya samu sauƙi zai fito. Da to suka bishi, basu kawo ma ransu komai ba, kawai dai Abie da Sadiƙ ne kawai zasu iya cewa sun fahimci me ke faruwa, shi kau Sadiƙ baya fata Hafsat ɗin taji wani abu, saboda halin da take ciki na tsohon cikin da har yanzu bata haife shi ba, domin dakyal take taka wa, tin da suka ƙaraso ma ta kasa fitowa, saidai shi ne ya shiga ya ganta kwance ɗakin Kaka Zuwaira, har tana mata faɗan shegen taurin kai ne ya sanya ta fitowa tana cikin wannan halin, ita fa sai taga ma kaman sonsomin naƙuda a tare da ita, Amman hafsat ɗin ta kafe cewa ita bata jin wani ciwo daban, idan ka ɗauke na yau da kullum irin wanda take ji. Yana fita daga part ɗin Mota kawai ya faɗa, driving yake Amman Baisan inda zai nufa ba, idan ya tuna wai shine yau ake ɗaura ma aure, sai yaji wani irin daɗi, Amman cen Ƙasan ra shi haushn kowa ma yake ji, masalan da yaga garin ya ɗinke ana ta hada-hada, sai cin karo da mutane yake haye cikin kayan hawa bisa dawakai, da yaga haka yake ɗauke kanshi, ba sai an faɗa ba, hawan da bar nashi zashi. Kai tsaye guest House nashi ya nufa, bai nufi na Dad ba, domin yanzu yana cen cike suna cin abinci shi da baƙin shi. Ko da ya shiga ɗakin, bai ko tsaya cire rigar ba, haka ya faɗa saman gadon yana mai sauke ajiyar zuciya kaman yayi gudu. Kan shi ke matuƙar sara mashi, shi baya ma jin idan nan da gobe zai iya barin gidan. Ya gode ma Allah da babu wanda yasan inda yake. Ya kai kusan minti talatin, sannan ya tashi yana mai faɗa wa toilet ya sakar ma kanshi ruwa masu sanyi, sai a lokacin ne kuma yaji wata ƴar natsuwa tana kama shi, saida ya gama wankan ne ya fito ɗaure da tawul, *innalillahi wa inna ilaihi raji'un* kawai yake maimaitawa, da *la'ilaha illa anta su hana ka inni kuntu minazzalimin* a hankali yaji wata natsuwa na saukar mashi. Kaya marasa nauyi ya sanya, daga cikin kayan shi da suke ajiye guest House ɗin, a hankali ya miƙe yana mai fita cikin lambu domin ya samu fresh air. Bia daɗe da zama ba yaji an dafa kafaɗr shi ta baya. Bilal ne cikin dakakkiyar shadda ƴar ubansu, ruwan omo mai haske, yayi kyau har ya gaji, abun ka da fari shima, fuskar nan sai fara'a yake saki. Hannun shi ɗauke da wata jikka ta kwali mai kyau, tana da ɗan girma. Runtse idanun shi yayi yana mai dafa goshi. "Bilal ya akayi kasan ina nan?" Ba Abunda ya kamata mu tattauna ba kenan Friend, please ka tashi ka shirya, dont ruine your happiness Al'ameen today is a very special day, ta kamata ace kana farin ciki ne, Suhan ce fa, yarinyar da kullum kake kwana da buri da muradn son mallakar ta, yanzu gashi ta zama mallakn ka, ya kake neman watsa mana ƙasa a ido ne? Idan Dad yaji abunda ake ciki, kafi kowa sanin sai ya saɓa mana mu duka, don Allah kada kayi gaddama Friend, idan har na isa ina da wani matsayi a wurin ka, ka tashi kawai ka shirya please kada kayi gaddama fit my sake" Jikin shi yayi sanyi, hannu na rawa ya sanya ya amshi jikkar da Bilal ke miƙa mashi, ba tare da yace komai ba ya miƙe ya nufi cikin gidan. Waya Bilal ya ɗauka yana mai cewa mai shirya Ya ameen ɗin da suke tare dashi ya bar shi a mota ya shigo. Dama Mudi driver ne ya faɗa mashi inda yake, domin tin da yabar gidan yana zaune yana kallon shi, ganin kaman baya cikin walwala ne ya sanya shi tashi ya bishi, kada wani abu ya kuma samun shi. An shirya shi kuwa yayi masifar kyau, cikin shadda ƴar ubansu mai kalar bula mai cizawa sosai, sai aka ɗora mashi babbar riga fara ƙar,mai aiki da farin zare, rawann shi bula ne shima mai cizawa, nan da nan sai ya haska kayan, suka zauna das a jikin shi, dayake babbar rigar fitted ce, sai yayi tsam tsam dashi, gwanin kyau. Duk yanda Bilal yaso yayi dariya, ƙiyawa yayi, fuskar nan murtuk, shi fa ba zai gane bane wai, Amman gani yake Bilal ɗin na neman takura mashi, har ya fara bashi haushi. San baiso cigaba da hidimar bikin ba, saidai domin baya da yanda zaiyi ne. Haka Bilal ya tasa ƙeyar shi har cikin mota, a bakin ƙofar gidan suka tadda mitoci burjik, ga dawakai, ga mutane haye bisa dawakan, ga maroka da makaɗa da mawaƙa kala kala, da gani ma kaman amaryar ce ta iso. Ai hango Ya Ameen da mawaƙa da maroƙa sukayi, tafe cikin takun shi kalar na sarakai, duk da fuskar a ɗaure take, Amman ba kowa ne zai gane haka ba, saboda an rufe rabin fuskar. Nan fa mabusa suka fara busa algaitr su cikin gwanancewa, abun ya matuƙar burge kusan kowa dake wurin. Cikin gidan suke ƙoƙarin shiga, sai ga Motar amarya ta doso, ai tuni aka wanfale mata gate, mutane sukayi caaa aka ta. Basu jira komai ba suka kutsa suma, domin shiga a fito da dokin ango. Daidai lokacin da aka buɗe ma amarya ƙofar mota ta fito, sai kuma aka shinfiɗa mata wani jan carpet mai tsawo wanda zata bi ta kanshi ita da Mama Fulani kai tsaye har sashen Hajiya Kubra. Bai ko kalli inda suke ba, duk kuwa da maganganun da yake ji suna tashi akan cewa marya tasha kyau masha Allahu. Ban fa akayi Caaa a kansu, ga masu busa suna tafe suna bin su a baya, a hankali suke taka wa ita da Mama Fulani da Ammin Sir Salim da suke riƙe da ita, kanta yabe da Alkyabba mai ruwan azurfa da take ta walwali. Cikin ikon Allah muka haɗa idanu dashi ta cikin Alkyabba ta, inda ya ɗan juyo a hankali yana kallo na, shima saboda Aunty Hassana da ta riƙo shi tana mai cewa "Ja'irin ango kalli amaryar ka" Murmushi na ɗan sakar mashi, duk da ba lallai ya iya gani ba, zuciya ta tana mai yaba kyaun da yayi, daidai lokacin da naga an ƙaraso da wani jibge gen doki da ya sha kayan alatu sai kyalkyali yake yana harbin iska. Gyara mashi akayi, ana mai taimaka mashi domin hawa. Har ya hau dokin idanu na suna kanshi, inda har ɗan waiwayawa nake ina kallon shi, Ya Ameen ya dace, dukkan abunda ya sanya a jikin shi kyau yake mashi. Ganin bai kula ni ba, sai na barna raina cewa saboda yawan jama'a ne, kuma duk ga masu hawan cen ƙofar gida suna jiran fitowar shi. Ɗaya daga cikin fadawan shi ne ya kama mashi dokin suka nufi fita, Bilal yana bayan shi shim haye bisa nashi dokin da ya kasance baƙi. Bakin ƙofar sashen Hajiya Kubra aka tsaya dani, Fulani ce ke cewa inyi addu'a sosai. Nan kuwa na shiga kwararo ta, harda wadda Umma ta bani ta neman tsari daga dukkan wani abun ƙi da ka iya tasowa, da kuma neman tsari daga sharrin Hajiya Kubra, wadda bansan a yadda zata karɓe ni ba. Ina hangen sashen Ummata a kulle, wani irin kwalla ce Naji tana neman zubo mani, ina son Ummana, saboda farin ciki na, zata iya haƙura da nata, mace mai kawaici da dattako, saboda nice za'a aura, hakan ne ya sanya ta barin gidan mijin nata, duk dan dai wai tayi mani kara. Haka suka sanya Ya Ameen a tsakiya suna mai taka wa a hankali gefen shi Bilal da Abie ne, sai ta bayan shi Sadiƙ da Baffan Jiddo. Komai dai a tsare, ga mabusa ga mawaƙa. Takar ango fa ta ƙayatar, Amman ta ɓangaren Ya Ameen shi dai tafe ake kawai, duk kuɗin da mutane ke watsawa ma bai kula ba, irin kirarin da ake zuba mashi ma, duk ba ta wannan yake ba. Baisan dalili ba, koda ya ganta bai ji komai a ra shi ba, ji yake kaman yaje ya jata ya fidda ta, duk kuwa da wata zuciyar tana mai ƙarfafa mashi guiwa da sanar dashi cewa Suhan ce fa Janam ɗinka. Saida na gama kwararo addu'o i na ne na shafe a jiki na, sannan Mama Fulani ta fara ja na a hankali zuwa cikin sashen. Su Kuwa Hajiya Sa'a da Hajiya Laila, tin shigowar su gidan suka kwasa suna ɓatare suka nufi sahen Mom ɗin kafin amarya ta ƙaraso. Cikin Mamaki suke sauraren Abunda Hajiya Kubra ke faɗa masu, sannan cikin wani tashin hankalin take cewa su taimaka su kira mata Malam akan a warware aikin nan, taga alama yaron nan zai iya bata kunya fa sosai. Su a cikin jaddadawa suke sake faɗa mata Abunda Malam ɗin yace, sannan suka shiga shaida mata cewa kawai dai abu ɗaya zata yi shine tayi ƙoƙarin Ganin Al'ameen ɗin ya kusanci Amaryar tashi, wannan kawai shine. Suna haka ne suka ji guɗa na tashi da kirari ga amarya da Mama Fulani, hakan ke alamta masu cewa sun ƙaraso kenan. Cikin zabura suka shiga ƙara gyara ɗakin, inda Hajiya Kubra tana mai ɗauko turaruma ta sake fesa ma jikin ta, haɗi da sake murza hoda, sannan ta ƙara yawan gwala gwalan dake hannun da wuyan nata. Sannan ta koma gefen gado ta zauna, ba don komai tayi hakan ba kuwa illa domin azo a tadda ta a Hajiya Kubra da kowa ke magana akai, da labarin shaharar tata babu inda bai karaɗe ba a ilahir in ƙasar, duk da ta san cewa su ɗin ba ɓoyayyu bane *Dambulan Family* domin su Hajiya Laila ɗin sun faɗa mata cewa matar Mai martaba Sarki ce tafe da kanta zata kawo mata amarya, sannan ta bata amanar ta. Wasu haɗimai ne jakadiya, da gudu suka fara taka matakalar benen suna mai kirara Mama Fulanin sosai. Inda su Hajiya Sa'a suka buɗe ƙofar ɗakin suna mai fitowa suka tarbi Su Mama Fulanin da Ammi da suke riƙe da amarya cikin taku na a hankali. Ja gba suka yi masu har zuwa cikin ɗakin Hajiya Kubran da tasha kayan alatu, sai ɗaukar idanu yake yi, ga wani sanyin ni'ima dake tashi a ciki. Miƙewa tayi tsaye cikin fara'a take faɗin "Lale Lale maraba da isowar ku ranki shi daɗe, da fatan kun iso lafiya." Murmyshi Ammi da Mama Fulani suka sakar mata, Hajiya Kubra ba baƙuwr su bace a sunan, saidai basu taɓa katarin haɗuwa da juna ba, duk kuwa da cewa ayyukan Alkhairin da yaron nata keyi a masarautar tasu. Ga mamaki na, sai ga Hajiya Kubra ma ƙarasowa inda muke tsaye Su Mama Fulani na sakin ƴar dariya cikin isa irin ta mulki, rungume ni tayi tsam a jikin ta, tana mai faɗin "maraba da zuwan ɗiyata cikin wannan family namu, da fatan zaki ji daɗin zama damu, duk kuwa da cewa ke ɗin dama ba baƙuwa bace, Amman wannan zuwan ya sha banban da kowanne" A hankali na shiga ƙoƙarin zame jiki na, zuciya ta kuwa sai bugawa take fat! Fat! Ya Allah ka sanya ba wani makircin bane daga wajen surukar tawa. Zamewa ƙasa nayi ina mai ƙoƙarin gaida ta. Tayi saurin sanya hannu ta ɗago ni, tana mai sake rungume ni ta nufi fegen gadon nata dani, duk yanda tayi akan in zauna gefen gadon na ƙiya, ƙasa na zauna ina mai lanƙwashe ƙafafu na. Su kuwa SU Ammi bisa Sofar mai cin mutum biyu suka koma suka zauna ana sake gaggaisawa, inda sauran tawagar ƴan rakiyr amarya suka yi mazauni a falo, wasu kuma a sashen Kaka Zuwaira. Amana ta sosai su Mama Fulani suka ba Monɗin, inda ga mamaki na Naji tana amsawa, haɗi da ɗaukar masu alƙawurra masu yawa aka cewa zasuyi alfahari da kasancewa ta a cikin family ɗin nasu. Inda nima suka ja mani kunne akan inyi biyayya, haka dangin Hajiya Kubran suka dinga zuwa suna rungume ni sosai, kaman babu wani abu a cikin zuvmciyar su, inda ni kuma nasan ba hakan bane, wani salon makircin ne, wanda ba Allah su Ammin su fahimta ba, saida aka kai ni sashen kaka Zuwaira, nan fa ta sanya ni gaba da zaulaya, to koma dai miye sun ji matuƙar daɗi su mama Fulanin, domin a yanda suka lura shine daga dangin Mom ɗin har na Dad babu wanda basuyi maraba dani ba. Daga ƙarshe ne aka mani rakiya zuwa sashen nawa. Nan ma saida suka sanya na tsaya nayi addu'a sosai kafin aka shigar dani, tare da rakiyar mutane da yawa, kama daga dangin su Hajiya Kubran da kuma na Alhaji Mustapha ɗin, sai dangin Umma da aka taho dasu daga masarauta, harda su Ammi, wadda har yanzu cikin zuciyar ta tana mai jin ba daɗi kasancewar basu same ni ɗin ba. Sun kuma mani faɗa, inda aka masu rakiya daga sashen nawa zuwa sahen baƙi da ak buɗe masu, wanda babu Abunda babu cikin shi shima. Nan fa aka shiga kai masu kayan abinci da kayan tarba cikin girma, wanda duk a ranar Hajiya Kubra ta tanade su, bayan ta samu tabbacin matsayin nawa a yanzu. Hafsat ma dakyal ta shigo tana mai sakin guɗa ita da Afnan, inda suke ta faɗin *Yau alƙawali ya cika, anyi aure tsakanin Gimbiya Suhan da Yarima Al'ameen Dambulan, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya Matar babban yaya* Nidai sake sunne kaina nayi ƙasa ina mai sakin murmushin dole, ko ba komai bansan irin farin cikin da nake ciki ba, yau kasancewa ta mata ga Yariman Matasan da bhrin kusan ko wacce budurwa ne samun nashi. Afnan ɗince mai kuma cewa *"Mai kwalliyr Dinner tana a side tana jiran lokaci yayi, wannan ni ita ce gudunmuwa ta, har kayan da zaku sanya keda Yaya ni ce nan na tanadar maku, ku kasance cikin farinciki"* Su kau su Ya Ameen daga wajen Takar angon, kai tsaye wajen reception suka wuce, inda Sadeeq ne da Baffan jiddo suka haɗa masu a matsayin gudunmuwa, domin sun ba Ya Ameen ɗin ya ƙi amsa tin tini, yana mai cewa ya ɗauke ma kowa. Ƴan *Banfi ƙarfin ta ba fans* kuwa suna gina Aunty Salamatu inda ita ce tayi masu masauki, kuma ta tanada masu dukkan abunda zasu buƙata, daga nan har a gama hidimar biki, jira kawai suke lokaci ya ƙara sa su ɗinguma zuwa ga Sharatoon Hotel ɗin, inda za'a gabatar da Ɗinne ɗin da Bilal ne ya ɗauki nauyi shi kaɗai. ******* Jakadiya ce ta nemi ison shiga ɗakin Hajiya Kubran, tana mai sanar mata kiran da uwar gijigar tata ke mata, watau Mama Fulani. Bata ɓata lokaci ba, inda ta samu rakiyar Amina mata, da wasu daga cikin ƙannen ta ɗin. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke a gaban kowa, inda siada hankalin kow aya koma kanta, sanar mata da akayi cewa *Yau ba wanda zai kwana ɗakin amarya, ango ne zai shiga ɗakin amarya, domin suna son tafiya da kyallen budurcn na amarya a gobe zuwa fadar masarautar* Wanna shine dalilin karewar aikin da Malam yayi, abinda hajiya kubra ke nanatawa kenan a cikin zuciyar ta, inda a zahiri ta saki dariya mai cike da kunya, wai a matsayin ta na suruka take faɗin cewa "Kai ai da ba sai kun kira ni ba, duk yanda kuka shirya ai yayi....." ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'a ga Wanda Ya Ce Maka; Allah Ya Gafarta Maka وَلَكَ. Wa laka. Tare da kai. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~63~* *Page ɗinku ne Lubabatu & Salma madu funtua. Haƙiƙa Naji daɗin ziyarar da kuka kawo mani ƙafa da ƙafa, dalilin da yasa na mallaka maku wannan Page mai ɗinbin...... Ina sonku kaman yanda kuke sona. Allahu ya bar ƙauna, zumunci da zaman tare. Nagode nagode nagode. Haƙiƙa kun cika masoyan asali. Oum-Deedat tace tana sonku over. Allah ya kaimu lokacin mu kwaso shoki.* *@Salamatu Moh'd Abj, ina cigiyar ki, Naji ki shiru, please ki fito ko comment zai ƙara bada kala. Allah dai yasa lafiya* *Oum-Deedat tayi ƙawa fa, mrs Daura har ba zan iya fasalta wannan ƙauna da kike ma su Ya Ameen ba, da ita kanta Oum Deedat. Hakan ne ya sanya domin ke kaɗai nayi wannan typing ɗin yau. Ki binjimi karatu lafiya, ina gaida Al'ameen* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Ta kuwa rasa ta yanda ma zata iya tun ƙarar shi da maganar, gashi marece yayi jama'a sai ƙara hauhawar shiga gidan bikin suke yi, ko ina gidan a cike yake duk kuwa da irin girman da gidan ke dashi. Bayan ta koma sashen ta ne, sai ta faɗa toilet tare da latsa number ɗin Al'ameen ɗin. Har ta katse bai ɗaga ba. Sai ta cenza akalar kiran ga Bilal. Bayan ya ɗaga ne, sai kuma ta shiga tambayar shi abokin nashi cikin hikima. Jikin ta fa har ɓari yake yi. Ba zata taɓa sake da wannan damar ba, idan har komai ya zama normal ta tabbata zata yi ma ƙawayen ta zarra Fintinkau, ace Son ɗin nata ne ke auren ƴar gidan babbar masarauta irin wannan. Shaida mata yayi da cewa sun gama takar angon, gasu ma a guest house suna cin tea break, da sun gama kuma zasu fara shirin ɗinner ɗin, zai aiko da abie da guest pass ma guda hamsin, dangin ta 25 haka dangin Alhaji Mustapha ma guda 25 sai ƙawayen amarya guda 10 da na dangin amarya guda 20 suma. Duka ya kama mutane 80 kenan, saboda abun a tsare yake. Basa so mutane su wuce 150 saboda komai iyakar na hakan aka tanada. Ba Abunda take son ji ba kenan. Amsa mashi tayi, ba tare ma data fahimci me yake faɗa ba. *"Ina Abokin ka?"* Tambayar da ta jefa mashi kenan. "Mom yana lafiya, gashi cen a ɗaki yana hutawa, saidai fa har yanzu ba lafiya sosai mom kiyi mashi addu'a, saboda ya kafe ma akan cewa ba fa zai je dinner ɗin nan ba ma" Aiko sai gaban ta ya shiga faɗuwa "Bilal please ka kai mashi wayar, ni yaƙi ɗaga tawa, Kaga mutanen nan manyan mutane ne suma, bana so yazo ya bamu kunya fa" Ta faɗa cikin rawar murya, tana mai ƙaro ƙarfin ac ɗin da take cikin toilet ɗin, kaman ba wurin kashi ba. Koda yake naga ai har a kitchen ma akwai ta. Tinda basa da aiki sai na shan ac kullum. Bai yi musu ba ya miƙe, yana mai ajiye spoon nashi ya nufi ɗakin. Tadda shi yayi ya fito daga wani wankan, Baisan meke damun abokin nashi ba da yake ta faman wanka yau. Daga shi sai tawul ɗaure a ƙugun shi, farar fatar shi ta sake bayyana asalin kwantaccen gashin da yake lulluɓe da fatar tashi. "Mom" Bilal ya faɗa yana mai miƙa mashi wayar. Baiyi musu ba ya amsa, dan dama dai yana wanka ne lokacin da wayar tata ta shigar mashi. "Hello Son ya kake ne? Kana dai lafiya ko ya gajiya?" "lafiya ta lau Mom" ya bata amsa a gajarce. Lokacin da yaje bin Bilal da kallo da ya juya ya fice daga ɗakin, domin komawa wajen abokan nasu. "yauwa Son, please idan kana da time kazo ina neman ka, kafin dare yayi" "Mom kin san fa gidan nan cike yake da mata" ya taro numfashn ta. "Na sani Son, please ka shigo ko ta ƙofar baya ne, akwai magana mai muhimmanci da nake son muyi dakai. Mu haɗu a lambu, idan ka taho u shud call me," "OK sai nazo" kawai ya iya ce mata yana mai datse kiran ya faɗa saman gadon a rigingine. Shi yau ji yake duk duniyar ta mashi zafi, duk irin tunanin da yake wajen ganin ya zaƙulo dalilin damuwar ya kasa. Yana haka ne Bilal ɗin ya sake shigowa. Yana mai faɗin "Friend guys ɗin nan fa zasu je su shirya, ya kamata kaima ka yi maza ka gama Abunda zakayi saboda a fara shirya maka wajen dinner ɗinnan fa, ka sani domin dole ne zaka je dinner ɗinnan, saboda ita ce kawai Abunda ka amsa a matsayin gudunmuwa ta a bikin nan, so Kaga dole ne kaje indai ba so kake inji haushi ba, na kira amarn ma akan cewa su shirya, ga guest pass cen ma na a Bilal ya kai ma mom" Da kallo yake bin Bilal ɗin, yau Bilal ya takura ma Rayuwar shi iya matuƙa, ji yake kaman ya yada shi ya huta. Ajiyar zuciya ya saki, yana mai miƙewa ya shiga zura jallabiya. "Bari inje wajen Mom tana kira na" "OK to sai ka dawo, Amman a haka zaka ratsa mutane da jallabiya a jikin ka kaman ba ango ba? Ko so kake sai kowa ya fahimci halin da kake ciki?" Bai ko kalle shi ba, ya sanya hannu tana mai ɗaukar firar ruwan dake saman wani ɗan ƙaramin fridge ya shiga kwankwala ko a cup bai tsaya zubawa ba. Yana gama shanye ruwan yayi wurgi da bottle ɗin cikin side ddustbin. Yana mai zarar key ɗin motar shi zuwa hanyar ficewa. Nannauyar ajiyar zuciya Bilal ya saki, ko ba komai yaji daɗin shan ruwan da yayi. Malamin su mai masu karatu bayan magariba shi yaje ma da matsalar dake faruwa da Al'ameen ɗin. Bai dai shaida mashi komai ba, duk kuwa da shi malamin ya gane aikin sihiri na tasiri a jikin Muhammadun (Dayake haka suke faɗa mashi) ruwa ya buƙata da Bilal ɗin ya kawo, inda ya koma mota ya ɗauko gorar swan ƴar madaidaiciya. Addu'a sosai yayi a cikin ruwan, yana mai tofawa. Sai da ya gama ya maida ma Bilal da ruwan yana mai cewa, "Duk yanda za'ayi, kayi ƙoƙarin ganin Muhammadun ya sha wannan ruwan, zuciyar shi zata yi matuƙar sanyi, ƙunci da yake ciki zai yaye insha Allahu, ko ba komai ba zai taɓa bayyana wani abu ba cikin jama'a da sunan zai dagula hidimar bikin." Haka yayi ma malam ɗin godiya, inda ya kawo wani abu ya bashi, saidai malam fir yaƙi amsa, yace ai aikin Allah ne yayi ba wai na kuɗi ba, kuma babu Abunda ba zai iya yi ma Muhammadu ba, saboda irin taimakon shi ga al' ummar musulmi baki ɗaya. Haka ya dawo da ruwan a hannu yana ta ɓoyewa, ya ɗauka Al'ameen zai tsaya cin snack ɗin da lemon da suka sha, to da anan ne zai ƙoƙarin bashi ruwan ya sha ba tare da ya sani ba. Ganin bai tsaya bane ya sanya ya ɗora su bisa fridge, yayi ma mamaki da Al'ameen ɗin ya sha Hu, duk kuwa da kasancewr su ba sanyi, kuma robar a buɗe take, wanda ga al'adr shi baya shan ruwan da wani ya buɗe. To saidai ganin hakan ne ya sanya shi gane har yanzu zuciyar abokin nashi na cike da ƙunci, koma dai minene yana fatan ace shan wannan ruwan addu'ar ya kawo mashi masalaha. Abokin NASHI Al'ameen ya cencenci koma minene daga gareshi, tinda shi ya fi kowa sani, har yanzu da BAZAR shi yake rawa. Shiyasa lokacin da soyayyar Suhan ta fara bijiro mashi, yayi ƙoƙarin yaƙar abun, saboda ba zai taɓa iya cin amanar abotakar su ba, wadda tin basu kai ga mallakar hankalin kansu ba suke yin ta. ******** Hajiya Laila wallahi ba zan iya misalta yanda nake ji ba yanzu a cikin zuciya ta, bansan dai dalilin da yasa nake matuƙar jin Nauyin yaron nan ba, kaman shi ne ya haife ni, ba nice na haife shi ba. Na rasa ta ina zan fara sanar dashi wannan al'amari, saboda ba hurumi na bane, ni kuma ba zan iya zuwa in tunkaro Hajiya Zainab ba, ko yayyen mahaifin nashi, su kuma dangi na gabaki ɗayansu shakkar shi suke ji, shine dalilin da yasa na kirawo ku nan kafin yazo, ku bani shawara" Hajiya Kubran ta faɗa, cike da wani irin yanayi da zaka kasa fassara shi, dagani dai nadama tayi mata ɗaurin huhun goro. Hajiya Laila ce da take zaune kusa da Hajiya kubran ta nisa, sannan ta shiga cewa "Ni fa dama Allah ya gani ba da son raina akayi wannan aika aikar ba, ina ganin tinda yaron nan ya nace da sai ki bar shi, wannan aure fa daga gani bamu san Abunda Allah yayi ba akan shi, kina gani fa, Wancen aikin da Malam yayi akan su ita Umman Suhan ɗin akan su bar gidan, aikin nan yayi kyau, kuma munga sakamako, Amman da suka tashi dawowa sai suka dawo da ƙarfin su, baki bari yaron naki ya auri yarinyar ba, sai gashi mijin naki ya auri uwar, ko anan ya isa mu gane ishara ce ta Allah". Hajiya Sa'a ma da take gefe, ma'ana dai sun sanya Hajiya Kubra a tsakiya, kowacce cikin maɗaukakin gayu cikin ɗanyun laces da gwal-gwalai. Itama nisawa tayi ta amshe zancen da cewa "Nima tuni na daɗe ina wannan nazarin, kamata yayi mu ƙyale su, tinda suna son juna, Amman Hajiya Laila kece kika matsa akan lallai ayi aikin da yaron nan zaiji ya tsani yarinyar nan, kina gani jiya fa kaman yanzu yaran nan suna cikin nishaɗi, Amman wayewr gari aka ɗaura aure muka gane kan yaron nan, gashi ya ɗaga maki hankali kema duk kin ruɗe, mai kyakkyawar fahimta dole ya gane bakya cikin natsuwa. Hajiya Kubra ce ta sake nisawa, cikin wata irin jin kunya, da zamu ce bata taɓa jin irin ta ba. "Ni fa ban san abun nan haka yake ba, duk son zuciya ta ne yaja mani, saboda bana so Sam ace ana yayata ni a cikin ƙawaye cewa yaro na ya auri ƴar aikin mu, shine kawai dalili, Amman ko ita Maryama ina cike da kunya da nadamar duk ranar da zata dawo gidan nan, domin a rayuwa na cutar dasu, na wulaƙanta su, kuma wlh duk ina sane, saboda son zuciya ta, Amman yanzu ba wannan ba, duk ma Abunda zai faru daga baya ne. Ku bani shawarar ya zanyi da Al'ameen, kun sanshi sarai wani irin murɗaɗɗen mutum ne, shine ma dalili na na cewa yazo ya same ni nan. Kunga kuma har yanzu bai kira ba. "Ni fa dama ina mamakin yanda kika ɗauki karan tsana kika ɗora ma matar na da yarinyar tata, naga ba sashen kike zuwa ba, Amman duk wani motsin su akan idon ki yake, nayi mamaki da bakiyi ma sauran ma'aikatan sai su..." Hajiya Sa'a ta faɗa itama "Sa'a kema dai kin faɗa, hakanan na ji na tsane su wlh, kuma tabbas bana zuwa sashen masu aiki, saidai ina da masu kawo mani dukkanin rahoto, Talatu da Sayde, saidai Talatu ita ce kan gaba, saboda ita ce shugaba, ban sani bama dukkanin abubuwan da take zuwa tana faɗa man ɗin, ko don inji na tsane su ne? Mu bar wannan maganar ba lokacin ta bane Sa'a ku bani shawara, duk yanda za'ayi ina so yaron nan ya tara da yarinyar nan cikin daren nan, ta yanda komai zia warware cikin sauƙi, daga yanzu ba zan kuma cutar Suhan ba, saboda nasan idan nayi haka ko ma sarautar ma ba zata ƙyale ni ba. Nayi nadama da wuri Laila ku bani shawara." " Al'ameen da take tsaye ta bayan su, duk Abunda suke faɗa ya gama ji, a hankali a hankali ya shiga takawa cikin wani irin rawar jiki, wurin yake ƙoƙarin bari, ko don kada ya faɗi a wajen. Baisan lokacin da ya kai kanshi bakin mota ba. Jikin shi kyarma kawai yake yi, tuni fuskar tashi ta rine da kwanciyar jini, haka idanun shi, baisan halin da yake ciki ba, a haka ya shiga jan motar cikin tuƙin ganganci. Har yanzu zuciyar shi ta kasa gasgata Abunda yaji, to da wani ne yazo ya faɗa mashi wannan maganar, Allah ne kaɗai zai iya raba su dashi a ranar nan. Haka ya shiga cikin gidan yana mai haɗa hanya, kaman wanda tasha giya kwalba goma. Da sauri Bilal ya miƙe yana mai taro shi suka zube kan kujera. "Friend gaya mani me ya faru kuma? Kaje gidan ne? Me ya faru ko in kira Mom ɗin?" Bai iya cewa ƙala ba, sai wasu irin hawaye masu ɗumi dake shatata a idanun nashi. Dakatar da Bilal yayi da hannu, da ya zaro waya yana mai ƙoƙarin kiran Mom. *"Dont call her"* Ya faɗa a tsawace, wani irin miyau na feshi daga bakin shi, mai kumfa kumfa. Ruɗewa Bilal & in yayi, zai iya cewa bai taɓa ganin abokin nashi cikin wannan halin ba. To me yake faruwa ne? "To ka faɗ aman Friend lafiya? Ka tada mani hankali fa, idan ba zaka faɗa ba, i'll call her defenetly" Shima ya faɗa cikin fushi, kukan da yaga Al'ameen ɗin nayi ya ɗaga mashi hankali. Tun hawaye na zuba, har ya fara sakin sauti, yana mai dafe da kanshi da yake ji kaman zai tsage mashi biyu. Da dukkanin hannuwan shi yayi amfani wajen kamo Al'ameen ɗin da ya kuma sake miƙewa ya nufi zuwa bedroom ɗin. Fizgewa yayi, yana mai wucewa yana haɗa hanya. Baiyi fushi ba, a zafafe shima ya miƙe ya bishi "Please Friend kada ka ɓata mana wannan ranar, ka sanar dani me ke faruwa don Allah, tin kafin nima ka sanya ni kukan, ba tare da sanin me ke faruwa ba" Ya faɗa yana mai zaunawa shima Ƙasan carpet, kaman yanda yaga Al'ameen ɗin yayi. A hankali ya fara rage sautin kukan nashi. "Bilal dukkan abunda ke faruwa dani Mom ce sila, Mom tana da masani ya, Mom ce dalilin tsanar Suhan da nayi, Mom ce da ƙawayen ta, Dalilin barin Su Suhan gidan namu Wancen karon, Mom ta azabar da su Suhan da Umma, a lokacin zaman su gidan namu, duk ba tare da ni ko Dad mun sani ba, Bilal ka faɗa man wace irin uwa ce Allah ya bani? Wane irin hali Mom ta jefa kanta na bin bokaye da sunan malamai? Me Mom zata tsinta a yin hakan da tayi? Me Mom ta nema ta rasa a rayuwar ta? Me su Suhan da Umman ta suka tsare ma Mom? Sai gashi yau da bakin ta duk tana faɗar waɗannan abubuwan. Da wanne ido zan kalli Suhan da Umman ta duk ranar da suka ji hakan? Shin bata tunanin su samu saɓani da ƙawayen nata su fita waje su tona mata asiri.? Bilal ka faɗa mani ya zanyi? Bilal ba abunda na nema na rasa wanda Allah bai mallaka mani ba, Amman ya jarabce ni da samun Uwa mai halin Mom. Bilal ina nadamar tsanar da na nuna ma Suhan a yau. Duk da ba wai ina jin son ta ya dawo mani bane ɗari bisa ɗari. Dole in danne zuciya ta, Bilal ka bani shawar wai ya zanyi ne?" Ya faɗa yana mai sake sakin wnai kukan. Shi kanshi Bilal idanun nashi sun kaɗa sunyi jawur. Dole dama zuciyar shi na raya mashi cewa harda sa hannun Mom a duk Abunda take faruwa, ya sakankance da lamarin Mom tin wata rana da ya same ta tana waya akan irin hakan, saidai bai fahimci komai ba, haka ya juya ya fita, ba tare da ya bata damar ganin shi ba, balle ta kawo ma ranta cewa ko yaji Abunda take faɗa a wayar. To ya zasuyi, uwa uwa ce, dole su jure, dole su danne, saidai suna gudun ranar jin kunya, kuma sun sani dole ne tana nan zuwa. Miƙewa Bilal yayi ya nufi fridge yana mai ɗauko gorar ruwa ya sake dawowa, inda Al'ameen ɗin yake zaune. Miƙa mashi yayi, bai wata wata ba ya sanya hannu ya amsa, yana mai ɓalle murfin ya sake kafa kai. Cikin matuƙar rausayawa yake kallon abokin nashi, ikon Allah kenan, yanzu dai gashi babu Abunda Allah bai mallaka ma Al'ameen ɗin ba kaman yanda yace kuɗi, gidaje, motoci, kmafanoni, ilimi, kyau, asali, nasaba, farin jini da sarauta, Amman shi kuma ta nan tashi jarabawar take, kowa dole ne Allah ya jarabce shi, wallahi kabar ganin mutum a cikin sutura, wani mai kuɗin ma da zai buɗe maka cikin shi, to tabbas sai ka fahimci ashe kai ne Allah yake so, kai ne Allah ke ma sutura, ashe shi kura ce lulluɓe da fatar akuya, Abunda da yawa mu Talakawa bama kawo ma ranmu kenan, muna ɗuaka idan Allah ya bamu kuɗi shikenan ba wata Jarabawa da zata iya biyowa baya. Gefe ya koma ya zauna yana mai kallon abokin nashi da ya haɗa kai da guiwa yana mai sakin ajiyar zuciya a hankali a hankali. Suna haka ne kiran Mom ya sake shigowa wayar tashi. Kai hannu yayi da niyyar latse kiran, Bilal yayi saurin ɗauke wayar ya amsa. "Mom Al'ameen yana wanka ne, kuma mun fara shiri, please kiyi haƙuri ko zuwa gobe ne sai kuyi maganar, saboda ya faɗa mani cewa kina neman sa, bama so ne mu makara" ya faɗa mata haka, yana mai katse kiran ba tare ma daya jira cewr ta ba, yasan hakan da suka yi mata bai kyautu ba, saidai basa da zaɓi ne baya ga hakan, dole duk wani abu da zai haɗa Al'ameen da Mom ɗin a yanzu su kauce mashi, ko don halin da Aminun nashi ke ciki. Kai gidan ma baya fatan ace ya taka yau, so yake ace har sai kowa ya watse, domin baya so zuciya ta kwashi abokin nashi ya aikata ba daidai ba cikin mutane yanda zuciyar na tashi take haka. Yana katse wayar, Al'ameen ya miƙa mashi hannu alamun ya bashi, ba musu ya miƙa mashi. Kashe ta yayi gabaki ɗaya, inda ya wurga ta cen bisa gado, domin ko alamu ma baya fata da burin sauraren Mom ɗin tashi a yau. Ita kuwa ta ɓangaren ta mamaki take yi, duka yaushe yace mata yana wanka, kuma har ya sake komawa wani? Wai me ke faruwa ne? "Hidima ce tayi mashi yawa Hajiya kibi a hankali" Cewr Hajiya Sa'a. Ajiyar zuciya ta sauke, dole akwai buƙatar ta kira alhaji, domin ta faɗ ama shi buƙatar masarautr, shi sai ya kira shi da kanshi yayi mashi bayani, tinda dai shi yake namiji, ba kaman ita ba da take mace. Ko da ta kira Alhajin yana cikin mutane, sai dai ya bata uzirin zai kira ta daga baya. Dole jiki ba kwari ta miƙe tana mai komawa ciki, inda ta sanya aka ƙra haɗa wasu kayan ciye ciyen zuwa wajensu Mama Fulani. Tare da guest Pass ɗinsu, kaman yanda Bilal ya kawo mata. Ai tuni gida ta ƙara harmutsewa ƴan zuwa dinner. Inda har motocin kwasar Mutane sun fara yin oarking a harabr gidan, domin basa fatan ace anyi African time saboda an gaji kowa ya kwanta da wuri ya huta. ******** Ni kau tin magariba aka sanya nayi wanka, sai bin ko'ina na ɗakin da kallo nake yi a sace, hatta da ruwan wankan da aka sanya nayi wankan dasu daban suke, wani irin ƙamshin daɗi ne yake fita daga cikin su. Sannan aka sake turara ni, har da na tsugunne. Domin Mama Fulani ta aiko da mai gyaran jikin, kuma ta faɗa mata cewa yau ne ango zai shiga ɗaki, ba kowa ya sani ba, Shiyasa take ta sake haɗe ni da wasu irin sirruka, tana yi tana sakin dariyar da ita ce kaɗai ta san ma'anr ta. Hatta da gashin kaina ba'a bar shi ba. Gashi kuwa indai ba na kaina ba, duk jiki na babu inda yake. Haka aka dinga bani wasu irin turaruka ina murje ma jikin, har da na matsawa, duk da ba wai shiga yake ba, haka ake sanya ni ina shafawa gefe gefe. Kai har dai na gaji, dan dai bana da yadda zanyi ne, tunani nake tinda ba yau ne ango zai shigo ɗaki ba, menene na yi mani wannan fi'ilin. Nan fa ko ina ya ɗau ƙamshi, har falo kana iya jiyo ƙamshin. Dama sashen bama da yawa ciki. Su Afnan ne da Jidda sai Asiya, Hafsat, khadeeja Raihana da Huda, sauran duk sun koma sashen su. Sai haɗimai guda biyu da suke zaune falo suna jiran ace suyi wani abu. Ƙamshin jikin nawa duk da yana da yawa sosai, amman hakan baisa yake hawan kai ba. Tana gama gyara ni, sai ta miƙa mani wani turare, tace in tabbata yau da gobe idan zan kwanta na shafa a jiki na. Wannan wani sirri ne da sai nayi mata godiya. Haka ta fice, inda mai kwalliyr da Afnan ta ɗauko tazo ta fara aikin ta. Cikin ƙanƙanen lokaci kamanni na suka cenza, na koma kaman wadda aka ɓanɓaro daga inji. Tuni na ɗau sheƙi da walwali. Wata irin doguwar wedding gown ce mai kakar Royal blue akan kawo mani har ƙasa tana jan ƙasa, sai wani irin head da mai kwalliyr ta tsaya ta zubda zallar fasaha ta wajen ɗaura mani shi, shi kuma fari ne tar, har yana ɗaukar idanu. Sai wasu irin flowers da zan riƙe a hannu na, da ƴar post ɗin takalman mai kalar fara tar da duwatsun bula sai walwali take. Hatta da sarƙar wuya na abun kallo ce. Tuni suka ɗau sowa da tafi. Inda su kuma suka shirya cikin riga da skirt na english wears kalar baƙin skirt da ruwan miyon goro ta riga, sai hula da suka kakkafa pecing cap itama baƙa, inda kowacce ta saki gashi ta hudar bayan hular. Sunyi kyau sosai suma kaman zasu bar ƙasar. Muna cikin wannan shirin ne, inda har yanzu an ƙi bari na hakanan in huta, sai ƙalailaicewa ake yi. Saƙon anguna ya iske mu akan cewa ƴan matan amarya su fito, Amman banda amarya, ango ne da kanshi zai zo ya tafi da ita. A barta ita da wata Ƙawar ta guda. Nan aka fara muhawarar da wa za'a barta. Hafsat dai ita aka zaɓa akan ta zauna jiran yayan nasu. Inda kowacce Ƙawar amarya da abokin ango guda cikin motar shi. Nan fa duk motar da ka buɗe ka shiga, ita ce ta abokin angon da zaku zauna wuri guda gashi har a gama dinner ɗin. Hafsat wadda bata sanya irin kayan sauran ƙawayen ba, wata doguwar riga ce jikin ta, kalar Orange da baƙin head, sai rigar taba cikin damar zama daram. Ita dama ai tana mamakin ace wai wani naƙuda take yi, gashi har zata je pherty ɗin hankali kwance, inda Sadeq ya shaida mata tare da Al'ameen zasu zo da Bilal. Cikin sa'a Jidda na buɗe motar da taji zuciyar ta ta aminta da Yusuf (Dady) ɗinta na ciki. Tana shiga ta sakar mashi murmushi, inda ya kashe mata ido guda shima yana mai faɗin, "Ai ni wata budurwa nake jira ta faɗo nan my jiddo, kinga ƙawa ce sai yayi daɗi ko?" Ɗan haɗe fuska tayi, itama cikin wata irin shagwaɓa tace "ai nice budurwar ko kuwa baby?" Jinjina mata kai ya shiga yi, cikin wata irin ƙauna da sauƙi, to dama su ɗin har yanzu amare ne, hakan ya sanya na bar su, ina mai nufar motar da naga Afnan ta buɗe ta shiga. Cikin sa'a ya ɗago kanshi, domin ganin wacece ta shigo. Hasken fatar tata, na ɗaya daga cikin Abunda ya shaida mashi ita. Ko ba'a faɗa ba, tabbas wannan jinin su Al'ameen ce, watau gayen da ya ƙwace mashi Suhan. Sai yaji ba daɗi sosai, yanzu ba komai ne da ya shafi Al'ameen take so ya ganshi kusa dashi ba, dan dai baya da yadda zaiyi ne, har yanzu kishin Suhan ɗin na sukar mashi zuciya. Saidai gaida shin da tayi ne cikin fara'a ya sanya ya ɗan kalle ta kaɗan yana mai amsawa, sai kuma ya sanya hannu yana kunna ƙira'a a motar, inda motar ta ɗauki shiru banda tashin ƙira'a, yana jiran a basu umurnn fara tafiya. Tini dangin Dad da Mom sunyi gaba, inda har sun zazzauna ana jiran ƙarasowar kowa. A haka aka bada umurnn fara tafiya, key suka fara yi ma motar suna mai fara barin harabr gidan, a hankali, inda suka saki fitilu ɗaiɗai na gefen bayan motar. Abun dai gwanin ban sha'awa. Inda ko da suka ƙarasa, bayan sun firfito daga motocin nasu ba'a bari sun shiga ba, aka tsaida su a wani reception cewa su jira ƙarasowar ango da amarya, inda zasu samu masu masu rakiya. *********** Da ƙyar Bilal ya shawo kanshi wajen shiryawa, Afnan ita ce ta zaɓa ma Yayan nata kayan Sanyawa, hakan ce ta sanya shi sawa ba tare da musun komai ba, Afnan ɗin daban take cikin ƴan uwan Ya Ameen, kusan ma zamu iya cewa yafi shaƙuwa da ita akan kowa dake cikin gidan. Ango yasha kyau, kaman ba shine yake kuka ba ɗazu, inda da ƙyal Bilal ya lallashe shi akan ya saki fuskar shi ko yaya ne. Motar da suka taho cikin ta ɗaukar amarya, yau ne aka fara hawan ta, renge rover 2020 inda ake jira ayi lunching ɗinta, Amman saboda wannan ranar Ya Ameen ya siyo ta, sai gashi cewa ranar bata zo mashi a yanda ya zata ba. Da gani Ya Ameen bai da wata motar da yake matuƙar so da ta wuce ƙirar kamfanin. Bai fito daga cikin motar ba. Inda Sadeeq yayi ma Hafsat waya akan cewa amarya ta fito. Yana mai komawa cikin motar shi da take fake gefe guda, inda a cikin ta ne zasu tafi shi da Hafsat ɗin, domin yan so ya kasance duk wani motsin ta a kan idon shi ne. Tana tafe Hafsat ɗin na gyara mata rigar ta dake sharar ƙasa, don ma interluck ne. Idanu ya zuba mata, yana ta gaban mota zaune. Ba Al'ameen ba, hatta Bilal ta burge shi. Kwakkwaran motsi ba mai yi, tunowa da yayi ko wacece Suhan ɗin a yanzu ya sanya shi ɗauke ido, yana mai sauke su bisa steary. Tayi mashi matuƙar kyau, wani irin mikin shauƙin sonta ne ke taso mashi cen Ƙasan rai, inda wani gululun abu ke tasowa yana danne wannan shauƙin. Bilal ne ya buɗe baki zai ce wani abu, yaga ya ɓalle marfin motar a hankali yake takawa zuwa gare ta. Ganin hakan da Hafsat tayi sai ya sanya ta cenza akalar tafiyar ta, itama tana mai nufar motar mijin nata dakyal inda yake zaman jiran ta. Hannu kawai naga ya miƙe mani, alamun in kama, ba wata wata na sanya hannu ina mai maƙale nashi. Wani irin shork ne ya fizge mu mu duka, saida muka ɗan zabura, inda a hankali na ɗaga fuska ta zuwa saman tashi. Fuskar shi ba yabo ba fallasa, saidai irin fara'a da murmushn da na zaci samu ban same shi ba. Sauke kaina ƙasa nayi, ina mai fara takawa, kaman yanda naga shima yayi. Saida ya buɗe mani ƙofar bayan motar na zauna, sannan ya gyara mani rigar, yana mai zagayawa shima ya buɗe ya shigo. Bilal yayi gyaran murya, dake ma Al'ameen nuni da kada ya saida hali, sannan yayi ma mota key, inda su sadeeq ɗin suka shiga binsu a baya. Muna hanya ne wayar Dad & in ta shigo. Ba tare da ya kawo komai a ranahi ba ya ɗaga, yana mai gaida Dad ɗin. Shima saboda yasan yana cikin hidima sai a gaggauce yace mashi idan sun gama komin dare ya same shi sashen nashi.. Da to ya amsa, yana mai yin shutdown ɗin wayar baki ɗaya. Saidai har yanzu bai ɗago idanu ya kalle ni ba, nima kuma irin Kunyar nan ta hana ni kallon nashi har zuwa lokacin da muka ƙarasa. Motar amarya na tsayawa, ƙawayen ta suka yi caaaa, inda suka kama tasu, suma anguna suka kama nasu. Saida aka daidaita ma kowa tsayuwar shi, sannan aka bada izinin mu fara takawa a hankali zuwa cikin hall ɗin, inda aka sakar mana waƙa a hankali take tashi cike da nishaɗantarwa. Hannu na yana cikin nashi maƙale, kai idan ka gan mu zaka ce ba'a taɓa yin masoya kaman mu ba. Saidai yanzu saɓanin ɗazu, murmushi yake saki a hankali a ƙoƙarin shi na kawar da duk wata damuwa dake ranshi, kaman yanda Bilal ɗin ya shawarce shi. Hakan sai ya ƙawatar da kowa. Kowa ya miƙe yana mai sakin tafi, inda sauran ƙawayen nawa suke rausayawa a hankali su da abokan angon. Kai tsaye wajen da ka tanadar mana domin zaman namu aka nufa damu. Har yanzu dai ina maƙale a jikin shi, kaman wani zai ƙwace mashi ni. Sai ma yaba iyayen nashi dake zaune wurin kunya, masalan Kaka zuwaira da ta matsa sai taje wurin saboda tsufa. Daƙuwa ta dunƙula tana mai sakar shi. "Kuji ja'iri, yana ta mamutse ta tin kafin ya shiga ɗakin, o'kho yaran yanzu ba kuna garesu ba" Dariya ta ba kowa, inda suka lura ma Al'ameen ɗin bai san tana yi ba. Duk da wajen zama na musamman aka tanadar mata itama. Bamu daɗe da zama ba, sauran abokai da ƙawayen suma suka koma inda aka tanadar masu suka zazzauna. Sir Salim baya da yanda zaiyi, dole hakanan ya zauna tare da Afnan, inda itama duk ta takura, gani take kaman baya da sakin jiki da mutane, ita kuwa Asiya sai daɗi take ji tana sakar mashi signal da ido, akan ga kamu nan tayi mashi. Dama ita ce ta tura Afnan ɗin zuwa ga motar Sir Salim ɗin tin da ta gane ta. Ba tare da Afnan ɗin ta sani ba. Wata waƙar aka kuma saki, sannan ne malam Ibrahim shahrukhan Mc ɗin da tayi masu jiya, nan ma shine zaiyi masu. Ya fara gabatar da shirye shirye, inda aka fara jejjera kayan ciye ciye bisa teburan da suke gaban kowa. Kirari ne muka ji an ɗauka, inda wasu fadawa da haɗimai ke tafe suna zubga guɗa, sai Mama Fulani da Ammi da suke take ma baya. Suma haka aka shigo dasu zuwa wajen da aka tanada masu domin zaman nasu. Nan fa shagali ya kankama, inda aka shiga gunguro wani irin ƙaton cake da yake ɗauke da photon amarya da ango cikin shigar dinner ɗin. Har an samu mai photon da ya ɗauka ya kai aka maƙala. Da na kalli ya Ameen sai yayi mani wata ƴar dariya da na Gaza tantancewa, mai kama da yaƙe. Ba haka na zaci gani ba ayau tattare dashi, to me ke faruwa ne? Kada dai ace nayi garaje nayi shisshigi. Irin rawar ƙafar da nago kan nuna ma amaryar shi wajen irin wannan pherty ɗin, ni sai ban ganta ba Sam. Inda Bilal da kallo yake bin Aminun nashi, hakan ne ma ya sanya wani abun yake maintaining nashi. Nan fa aka buƙaci amarya da ango da suzo su yanka cake, sannan su ci da kansu a gaban bainar jama'a. A hankali muka miƙe, har ina mai kusan faɗuwa, shine ma ya taro ni, yana mai ƙure ni da idanu. A wajen mutane sai hakan ya burge su, suna tunanin zallar ƙauna ce, Amman tsakani na dashi sai ma ɗaure fuska da yayi. Haka ya sake gyara roƙon da yayi mani muka nufi wajen cake ɗin. Sai da aka ƙilga uku, sannan wuƙar da take riƙe a hannu na, shi kuma hannun Ya Ameen yake bisan nawa, ta lume cikin cake ɗin, inda aka saki tafi da sowa, ana mai sake sakin wani kuɗi daban na waƙar auren tamu, wadda bansan lokacin da akayi ta ba, ban kuma san wanene ya bada ayi ɗin ba. A hankali na fara ɗebowa ina mai nufar bakin shi. Riƙe hannu na yayi, ƴan ami yi mani wani irin kallo, inda ya taimaka mani wajen Sanyawa a wabkin nashi, sai kuma ya sake riƙe hannun nawa ya nufo baki na dashi. Hakan ya sake burge mutane. Inda aka bada damar a sanya ma amarya da ango kiɗa su ɗan tattaka. An ba masu liƙo dama. Waiyo Allah na. Ai sai ga ruwan kuɗi har da daloli na tashi. Mama Fulani ma saida ta fito ta sakar mana ruwan kuɗi, kai hatta da kaka zuwaira saida ta tako a hankali zuwa wajen namu, ita kam ƴan naira biyar biyar da ba'a san inda ta samo su ba ta liƙa mana. Hakan yayi ma mutane daɗi, ko ba komai ya nuna tsohuwar bata da wani abu dake nuni da fahari ko ɗagawar cewa yaran nata su ɗin wasu ne, tinda kowa ya sani ko daloli taso liƙawa, za'a kawo mata su ta liƙa. Ana cikin shagali ne, sia ga wani group ya shigo hall ɗin, inda yaja hankalin kowa dake wurin. Dukan su mata ne inda ɗaya ne kawai cikin su yake namiji. Sanye suke da wata irin doguwar riga kaman za'a ƙulke su ciki sai ɗamarar rigar, inda ta bayyana matuƙa da kyawun rigar. Ko wacce ɗamara an rubuta *Banfi ƙarfin ta ba fans* inda aka sakar masu sautin su daban, kaman dai sai da suka zaɓo waƙar, domin waƙar taken ƙungiyar tasu ne, da kuma ambatar suna yen nasu da ɗaiɗai da ɗaiɗai. Nan fa suma suka ƙaraso cikin fili suna mai takawa a hankali cikin wani salo. Ruwan liƙo suka fara saki suna mai takawa sosai. Ah cen na hango su Salamatu mrs Daura, khaddeja, ummi zainab naja'atu da (kuyi haƙuri sauran da ban ambata ba, saboda yanayin rubutu mai yawa, gashi na gaji wlh) Sun burge kowa dake wurin. Masalan ango da amarya, da Sam basu san tayay akayi suka masu pass ba, ashe Salamatu ce da mrs Daura suka kira Bilal anan ne da suk samu, shima ba mai yawa ba sosai, Shiyasa ma basu je ba dayawa. Haka dai aka shiga ciye ciye, da shaye shaye, kowa dake wurin ya ga su sosai. Har aka tashi ba wata walwala sosai daga ya Ameen ɗin. Jikina yayi sanyi matuƙa, inda har su Hafsat suka so su fahimta. To ita daga cen dai sadeeq gida ya wuce da ita, saboda ya kura jikin nata baya mata daɗi, daurewa kawai take yi. Ta so matuƙa tayi magana da Suhan ɗin, inda ita fa taji ƙishin ƙishin ɗin wani abu har ma ta fara tausaya ma Ƙawar tata. Haka aka maida mu gida, inda ban sake saka ya Ameen a idanu na ba, haka muka koma, inda naga kowa ya dare ya barni. Afnan kawai ta tsaya, itama wai ceman take yi sashen su zata koma. Saboda babu wanda zai taya ni kwana. Jin haka na fara sakin kwalla, duk da dai na san cewa ba yanda za'ayi ango ya shigo yau gida cike da jama'a. Riƙe ta nayi ina mai cewa "please Afnan ki taya ni kwana don Allah wlh tsoro nake ji" girgiza kai take tana mai ƙunshe dariya. Inda ta tsaya ta gyaggyara mani komai. Tace bari ta shiga kitchen, ban sani ba ina daga ɗaki ashe ficewa tayi ta ja man ƙofar ta baya. Sai da naga bata dawo ba tsawon lokaci ne ya sanya ni miƙewa na leƙa kitchen ɗin. Bata ciki. Hakan ya sanar mani da cewa ta fice kenan. Jiki a matuƙar sanyaye na koma ɗakin, ina mai zare riga ta da duk ta dame ni da nauyi, wanka na shiga, na tara ruwan zafi sosai na gasa jiki na, har yanzu fa damuwar da nagani kwance bisa fuskar Ya Ameen ta dameni. Ko dai issue ɗin Mom ne? Ko dai ta sake bijiro mana da wata damuwar ne? Koma dai minene ni dai tattashin mijina zanyi in lallashe shi, in ma tar dashi daga duk wata damuwa da yake ciki. Ita kuma Mom duk yanda taso zaman namu haka zai kasance, domin yanzu fa nasan ƴan in kaina, da da yanzu ba ɗaya bane, idan har na juri wani abun, wani fa ba wai zan jura bane, ah to. Da haka na gama cuɗar jikin nawa, ina mai fitowa na tsane jiki na da kaina, da hand dryer. Mai na shaf mai sauƙin zafi, sannan na murje jikina da turaren da aka bani na kwanciya, wanda mai gyaran jikin tace in murza. Ban shafa komai ba, nayi oarking kaina ina mai zumbula hijab na tada salla. Bayan na gama ne, sai kuma Naji kaman ina jin yunwa. Kitchen na leƙa ba komai naci. Sai lemuna. Haka na ɗaga freah mulk na ƙwanƙwala, ina mai komawa toilet na sake yin brush, na jefa mint a baki na, bayan na fesa mouth fresh na koma gado na naɗe cike da tsoro, inda na rurrufe ko ina na saki sanyin ac a hankali. Yayi mamakin Abunda Dad ya sanar dashi, hakan ce ta sanya don dai baya da yanda zaiyi ne, dole ya nufo sashen nasu, addu'a ma yake yi Allah yasa ya zuwa yanzu tayi bacci. A haka ya tura ƙofar ɗakin a hankali yaji ta a kulle. Da makullan hannun shi yayi amfani wajen buɗewa, hra yanzu yana tunanin ta yanda zai iya bijiro ma da Suhan ɗin wani al'amari, shi fa Al'adar nan ɓarayi mashi ba, idan yaji ba zai iya ba, tattara masu ɗiyar su da zanen gadon da aka shimfiɗa mata zaiyi ya basu abun su gobe su koma da ita.... Wata zuciyar na ingiza shi, wata na kwaɓar shi. Da haka dai na sulale ɗauke da biri na. Hannu na duk tayi kanta, Alƙur'ani kau kuyi haƙuri sai gobe kuma..... *Masu son jin ehen an sha daku yau, su Salamatu sai a tanada ruwa ko a zubda cikin ɗayan biyu* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Abin Da Allah Yake Tsara Mutum Daga Dujal Saboda Shi. Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahfi, za a kiyaye shi daga Dujal. Sannan kuma mutum ya rika neman tsari daga fitinar Dujal a karshen tahiyar karshe ta kowace sallah. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~64~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° A hankali yake takawa zuwa nufar ɗakin, yayin da wani sashen na zuciyar shi ke cike da wani irin yanayi. Yana ji a zuciyar tashi wannan shine kawai mafitar Abunda zaiyi, wanda zai iya saka ma Suhan ɗin, a bisa dukkanin haƙurin zama da sukayi, duk kuwa da irin tsangwamar da suka sha daga wajen Mom ɗin tashi. A hankali ya tura ƙofar ɗakin da take saye. Abunka da ƙofofin zamani. Har ya shiga zuwa tsakiyar ɗakin da ya wadatu da hasken fararen gloves. Da kallo ya shiga bin ɗakin, iya kyau ya ƙara mashi kyau, komai na ajiye a inda ya dace, sai ma wani sassanyan ƙamshin dake tashi daga ɗakin. Ga mamakin kanshi wani irin murmushi ya saki iya gefen bak,yana mai maida kallon shi bisa gadon da ya sha farin bedsheet mai masifar kyau. An mashi tsani tsabi da golden, sai yarfin purple Tsakiyar gadon ya hango ta dunƙule, ita ba'a kwance ba, ita ba'a zaune ba, ma'ana dai ta ɗan kishingiɗa kenan. Wani irin tausayi yaji ta bashi, a hakan wai ake so ya cutar da ita, to cutar wa mana, domin shi fa baya jin idan a wannan halin da yake ciki zai iya aiwatar da wani abu daban. A hankali ya shiga nutsa ƙafar shi cikin chinese ɗin da yake da mugun taushi, wanda ya malale gaban gadon har zuwa gefen shi. Sannu kan hankali yake taka wa kaman mai sanɗa, har ya isa ga gadon yana mai ɗan ranƙwafawa ya ɗauko blancket mai taushi na zanen gadon da yake naɗe ajiye gefe. Warware shi ya shiga yi, cikin kulawa da takatsan-tsan gudun kada ta tashi, a ƙoƙarin shi na lulluɓe ta. Saidai kuma taushi da sanyin da bargon ya ɗauka, yana sauka bisa jikin ta, ta wani irin zabura tana faɗin "Wanene nan? Don Allah kayi haƙuri DON Allah" Ajiyar zuciya ya saki, lokacin da yaji ta kai mashi wawura, yana mai mannewa a jikin shi, a ƙoƙarin ta na kare kanta, har bata ma san ta rungume shi ba. Jin saukar hannuwan ta gabaki ɗaya ta zagaye su dashi, shi ya sakar mashi da jiki gabaki ɗaya, ya idasa silalewa da ita gabaki ɗaya zuwa kan gadon, har yana ɗan danne ta. "Suhan nine fa, ki natsu please" Idanun ta har yanzu na a kulle, amman jiyo ƙamshin turaren da take yi kusa da hancin ta nashi, hakan ce ta sanya ta yin lamo tana sauke ajiyar zuciya, kunya duk tabi ta cika ta, duk kuwa da nauyin shi da take ji a jikin nata, kasancewr ya danne ta sosai. A hankali ta shiga ture shi gefe, tana saɓule jikin ta daga nashi. Baiyi ƙoƙarin hana ta ba, saboda shi kaɗai yasan halin da yake ciki. Gefe ta koma tana mai sauke numfashi. "Yaya har ka bani tsoro fa wallahi, me kazo yi nan ɗakin yanzu?" Da idanun shi da suka fara birki cewa yake kallon ta. "Ni da ɗaki na sai ayi mani shamaki dashi? Ko kin manta a inda kike hala?" Ya bata amsa yana mai kakkafe ta da idanu. Ban samu zarafn ce mashi komai ba, illa iyaka sauke kaina da na kuma yi a hankali, ina mai sanya hannuwa na duka na shiga kare dukkanin jiki na, da kayan baccin suka bi lafiyayyar fata ta suka yi luf abunsu. "Anyway, haɗa mani ruwan wanka please masu zafi sosai" Cikin kwallo ido nake kallon shi, idan wani ya shigo yanzu fa? Wannan rashin kunya fa? To garajn me yake yi? "Please Suhan" Ya faɗa cikin wata irin murya, mai nuni da akwai Abunda ke damun shi, ko dai gajiya, ko kuma wani abun daban, domin da kyar muryar tashi ke fita. A hankali na zurk ƙafafu na, da niyyar in miƙe tsaye, har yanzu jiki na nake karewa da dukkanin hannaye na. Kaman wata munafuka haka na fara takawa na nufi hanyar toilet ɗin. Bansan lokacin da ya miƙe tsaye ba, sai kawai Naji ya jawo ni zuwa jikin shi, yana mai sauke ajiyar zuciya wata na korar wata. Saman gadon muka ƙara zubewa. Jagula ji yake son ran shi. Komai yake a zafafe. Ni kau hawaye nake saki sosai, ina ta kakkare kaina. Ture ni yayi daga bisa jikin shi, yana mai tashi ya faɗa toilet. Gefe na koma ina sauke numfashi,anya wannan kau Ya Ameen ne? Wasu abubuwa yake mani, wanda Sam babu soyayya a cikin su, to dama haka auren yake? Kafin a aure ka ne za'a nuna maka soyayya? Hijab da na gabatar da salla na ɗauko na zumbula, ina mai ficewa zuwa kitchen, ko zan samo mashi abun sha. Har ya zu ina jin wata irin wutar soyayyar shi na daɗa ruruwa cikin zuciyar tawa. Haiyasa bang a laifin Abunda yayi mani ba, tinda da auren shi a kaina yanzu. Saidai zuciya ta babu daɗi, ganin shi da nayi cikin wani yanayi, wanda na kula tin wajen dinner yake haka. To dama haka abun yake daga ɗaura aure sai miji ya cenza? Hollandia na ɗauko mashi mai sanyi, haɗe da ruwa da cup. Sum sum na dawo ɗakin, ina mai ajiye mashi bisa side drower, sai kuma na koma nazauna bakin gadon ina mai kallon side ɗin da ƙofar toilet ɗin yake. Buɗe ƙofar yayi ya fito. Ɗaure yake da ƙaramin tawul a ƙygun shi iya cinya, sai ƙarami yana mai tsane kanshi dashi. Saurin kauda kaina nayi ga barin kallon nashi, ko ina na jikin shi gashi ne kwance laya laya, masalan ma yanzu da yayo wanka, gashin a jiƙe yake. Bansan lokacin da na haye gadon ba, ina mai jan bargo gabaki ɗaya har kaina, na shiga baccin ƙarya, ni Sam wlh ko da tunani, ban taɓa kawo ma raina cewa Ya Ameen zai shigo ɗakin yau ba. Saidai nafi tunanin wankan kawai yazo yi ya fita, tinda ba haka ango ke shigo ma amaryar shi ba a daren farko, wasu ma abokai ne ke rakiya, masalan shi na ɗauka ai ko Bilal ne zai rako shi, ganin yanda suke. Duk abunda take yana kallon ta ta gefen ido, shima dariya ta bashi, sai kawai ya saki murmushi, yana mai nufar wata ƴar locar dake ajiye gefen sip ɗin ɗakin. Buɗewa yayi ya shiga zaro mayukan shi na bacci, haɗi da fara ƙar ɗin jallabiya, sai abun taje kai Shiryawr shi yake a hankali, har da murza turaruka masu taushin ƙamshin irin na maza. Ni kau da nake ƙumshe cikin bargo, a hankali na leƙo da idanu na ƙwaya ɗaya tal, domin ganin Abunda yake da naji shi shiru, ko motsin kirki baya yi. Shagala nayi da kallon shi, yanda yake komai nashi. Har zuwa lokacin da ya miƙe yana mai sakin tawul ɗin da yake ƙygun nashi ɗaure. Ai bansan lokacin da nayi maza na rufe idon ba, ina mai faɗin Innalillahi a zuciya. Ashe namiji baya da kunya har haka? Ya san ina ɗakin fa, to tayaya zai iya cire kayan shi duka bayan yasan ina wurin? Tini zufa ta fara keto mani, wani irin tsoro ya shige ni, tin ma kafin ace komai na fara matar kwalla, har na fara tausaya ma kaina, gamuwa ta da Ya Ameen ɗin, ganin irin ƙirar jikin shi da Allah yayi mashi irin ta zaratan maza masu ƙarfi. Har saida ya gama komai, ya sake kwasar towels ɗin ya nufi toilet ya shanya su. Sannan ya fito ya fice daga ɗakin. Kitchen ya shiga ya kashe komai, sannan ya dawo falo ya kulle ko ina, ya kashe komai, hadda hasken ɗakin. Ɗakin ya dawo, yana mai zama gefen gadon sannan ya ɗauko madarar da na ajiye mashi gefen gadon. Bai ko sanya cup ba, ya ɗaga ta ya kafa kai ya ƙwanƙwala sosai. Sanyin ta na ratsa shi, wata irin ajiyar zuciya yake saukewa. Bai ajiye ba saida ya sha fin rabi. Hamdala yayi, yana mai rufe murfin ya maida inda take ajiye. Ɗan kwantowa yayi ta gefen inda nake kwance. Sai kuma ya sanya hannu yana mai yaye bargon. Ni kuma jin hakan sai na kuma rintse idanu na, ina mai tuno karon mu dashi a ɗazu, da kuma ganin shi da nayi ba kaya. Ai sai na daddage nima na danne bargon, ni a tunani na ba zai iya ƙwace bargon ba. Ganin yana ta kokowa dani naƙi saki. Sai ya cicciɓo ni baki ɗaya, saidai kawai Naji ni a hannun shi ina yawo ni da bargon. Ƙoƙarin direwa nake, ina mai faɗin "Please Ya Ameen ka bari, Afnan da na nan zuwa mu kwana tare" "Ita tace maki haka?" ya faɗa yana mai dire ni, sannan ya yaye bargon gabaki ɗaya ya dunƙule shi, sannan ya wurga shi cen ƙarshen gadon. Tsuru nayi a tsaye, kare da ƙirji na, jiki na sai ɓari yake. Gyaɗa mashi kai na shiga yi, duk na wani firgice, hatta da gashin dake kaina ya warwatse kaman wata sabuwar kamu. Ganin na ruɗe da yawa ne, ya sanya shi sakar mani wani tattausan murmushi. Duk Daurewa yake yi, domin ji yake idan yanzu akace ya rabu dani, babu abunda zai hana. Saidai baisan me ke jan hankalin nashi zuwa gareni ba. A hankali ya sanya hannun shi ya shiga tattare mani gashin zuwa baya, sai kuma ya ɗan rungumo ni zuwa jikin shi, yana mai fara kitse mani gashin. Lamo nayi jikin shi ina mai shaƙar daddaɗan ƙamshin shi,da har ya riga ya kama lallausar fatar tashi. Nidai ban ɗauka ya iya kitso ba, sai ji nayi har ya soke mani gashin cikin tsakiyar kaina, inda ya bar wasu tsilla tsilla suna reto daga gaba. Ɗagowa yayi yana mai ɗora kyawawan idanun shi bisa kyakkyawr fuskar tawa. "Wife cool down, ba abunda zanyi maki, naga kin tsorata da yawa, ko kin manta wanene Ya Ameen ɗin ki?" A hankali na samu kaina da maida kan nawa bisa faffaɗan ƙirjin nashi, shima baiyi ƙasa a guiwa ba, ya sanya hannun shi yana mai zagaye ni dasu, tsam zuwa jikin nashi, kaman za'a ƙwace mashi ni. Mun kai minti biyar a haka, jin ɗumin jikin nake har cikin kwalwa ta. Hakan ya sanya na gagara tsayuwar, yaga na fara neman sulale wa, duk kuwa da babu abunda yake mani. Ban aune ba naji ya ɗaga ni ɗaf bisa ƙafafuwa na, bai dire ko ina bai sai bisa faffaɗan gadon, jikina. A u sauran lakka, saboda haka ina jinshi yana mani abubuwan da na Gaza hana shi, kuma ni ban biye mashi ba. Ban da tabbacin cewa daɗin hakan nake ji ko akasin hakan. Kawai dai Abunda na sani, wata wutar ƙaunar shi ce da take daɗa ruruwa a cikin zuciyar tawa. Ni Suhan nice wia da Ya Ameen a cikin irin wannan yanayin yana nuna mani zallar ƙauna. Tin bana biye wa har na ɗan fara maida raddi, sai kuma naji yin hakan da nayi ya ƙara ruɗar dashi. Sai kuma na koma ture shi, ina mai sakin kuka, jin abun na neman wuce gona da iri. Ina za'a haɗa ƙarfin namiji da mace? Sai ya kasance kaman ina ture dutsi, masalan ma da ya kama..... Yana mai aikata su son ran shi. Wani irin ƙarfi ne ya zo mani, jin ya nufi wata duniyar daban, ai bansan na wuntsilar dashi gefe ba, ina mai sakin kuka marar sauti, gudun kada in ɓare baki mutanen gidan su ji, ga ni a gidan surukai. Dunƙukewa yayi gefe, yana mai dafe marar shi da hannu, sai kuma naga ya kawai miƙe ya nufi toilet. Ruwa masu sanyi ya sukar ma kanshi. Ya daɗe bai fito ba, inda ni kuma nake dunƙule tsakiyar gadon da duk ya yamutse Koda ya fito bai bi ta kaina ba, ya buɗe sip ta ɗauko wani blancket sannan ya matso gaban gadon ya ɗauko fillow guda ɗaya, yana mai ficewa zuwa falo. Kuka na nake bil haƙƙi da gaskiya, ni kaina nasna bam kyauta ba, Amman menene dalili na nayin hakan? Nasan bai aikata saɓo ba, saidai bana tunanin zan barshi cimma burin shi ayau, saboda da jama'a har yanzu a gidan, ko ba komai idan wasu suka fahimci wani abu, ai Sam ba zan ji daɗi ba. Kuma zan sha kunya. Saukowa nayi a hankali ina mai nufar ƙofar na buɗe a hankali ya tura. Hango shi nayi kwance bisa 3seater ya lulluɓe kanshi dukan shi. Bana fatan mu kwana a hakan, duk wani abu da zai ɓata ranshi bana so. A hankali na koma cikin ɗakin, na shiga gyara gadon. Sannan na koma falon ina mai nufar inda yake kwance. So nake na lallashi shi ya koma ɗakin ya kwana bisa gadon, ba za ji daɗi ace wai ya kwana a bisa kujera ba, ko don gudun kada wuyan shi yayi ciwo. Bama fata Rayuwar auren namu da naci ma buri ta fara a haka. A hankali na durƙusa kan ƙafafu na, ina mai yaye bargon. Sai naji ya ja bargon da ƙarfi, yana mai sakin tsaki a hankali. "Leave me go on your own" Abunda ya faɗa kenan muryar shi na wani irin cracking. "yaya please kayi haƙuri, ka taimake ni, kada ka kwana anan bisa kujera please, idan kayi haka ba zan yafe ma kaina ba" Wani tsokin ya sake saki, yana mai juya mani baya. A hankali na rungume shi dukan shi, ina mai sakin wani irin marauan kuka cikin shigar shagwaɓa. Duk da naji jikin nashi da ɗan zafi, sai ban kawo komai a raina ba, ban kuma tashi ba, inda yayi mani shiru, yayi banza dani. Lallashin duniyar nan da nayi yayi mani banza, har saida na gaji da durƙuson. Na zame na zauna, ina mai ɗora kaina a bisa bayan nashi. Shiru mukayi mu duka, inda har barci ya fara kwasa ta ga gajiya. Cen cikin ɗan barcin da ya kwashe ni, Naji ana zame ni daga jikin shi. Sai kuma ya ɗauke ni cak, kamar ƴar baby. Ban niyyar hana shi ba, domin ni a tunani na ya haƙura. Saman gadon kawai ya dire ni, ko ƙofa da ƙafa ya tura ta, ko datsewa ma bata gama yi ba, ya rufu a kaina. Ya Ameen ya cenza yau gabaki ɗaya, ya zame mani kaman wani zaki, kaman zakanyar da tayi wata da watanni bata ci abinci ba. Yanda yake so yake dani, inda ni kuma sakin kuka kawai nake yi. Daurewa nake bana mai sauti. Amman lokacin da nayi shi duka cikin jikina, lokacin ne na saki wata razananniyar ƙara mai sauti. Inda bai ma san me nake ba, bai a kula da yanayin da nake ciki ba. Cizo yakushi mari duka ba wanda bai sha ba, Amman Sam bai a san ina yi ba, ya Ameen ya shiga wata duniyar da babu komai cikin ta banda jin daɗi. Wata irin wutar ƙaunar ta ce ke ruruwa a cikin zuciyar tashi, sai ya ji shi kaman ya farka daga wani nannauyan barci ne. Sai yake jin shi kaman a mafarki. Allah kenan, yau Suhan ce a bisa gadon shi, yake more duk wasu albarka tu da Allah ya mallaka mata. Ita ɗin ta daban ce, komai nata na daban ne. Ta cencenci komai, ko ma fiye da komai. Sambatu yake ta yi mani kala kala, inda har yanzu ya gagara ɗaga ni, jikin shi kuwa ya haɗa zufa, kaman wanda yayi gudun kilomitre ɗari. Tin ina dukan da ƙarfi, ina kare kaina. Har saida na datsa mashi cizo a damatsan hannu, wanda saida Naji alamun jini jini a baki na, sannan na saki. Har yanzu dai abu ɗaya yake yi, har saida yaji alamun kaman ko ina na jiki na ya saki. Sannan ya mirgina ya sauka gefe yana mai sauke numfashi. Ni kau kukan ma yanzu bana iyawa, hawayen ma sun ƙafe, ji na nake kaman ba ni ba, bana raba ɗayan biyun idan ba sai an mani ɗinki ba, yayi fata fata da rayuwa ta, soyayyar na ma fasa banayi, son nashi ma na dena, ba don dare yayi ba, da sashen Ummata zan tafiya ta. Bansan ma meyaja ra'ayi na akan auren ba, dama wannan ita ce soyayyar? Dama haka maza suke basa da imani, duk yanda suke iƙirarin suna sonka. Yanda Ya Ameen yake miakili, ban tinanin zai kula da wani abu nawa ba, balle har ya fidda maitar shi a fili, kuma a ranar daren da aka kawonin, ba zai bari ba ma ko wanda suka kawo ji Su Mama Fulani da Ammi su bar gidan ba. Ba ƙaramin cuta ta yayi ba, ba ƙaramin bani kunya yayi ba. Rintse idanu na nayi ga barin kallon shi, inda nake kwance lamo. Lannun shi ya ɗora saman kaina a hankali yana shafawa, yana mai sosa mani kaɗan kaɗan kaman mai kankare dundruf. Mai makon hakan ya burge ni, sai ma haushi da ya kuma bani, bama ma da ƙarfin da zan iya buge hannun. Mun kai minti goma a haka, shi yana faman sauke numfashi, inda wani irin daddaɗan barci ke fizgar shi, ni kuma tsananin azaba da raɗaɗi sun hana ni koda runtse idon, domin su kansu idanun wani irin zogi suke mani. A hankali naga ya miƙe, yana mai ranƙwafowa ta inda nake yashe, Kiss mai sauti ya sakar mani a goshi zuwa saman lips ɗina da suka sha murza kaman za'a cire su. Ba laifin shi bane, ƙamshin dake jikin ta, ɓoyayyar soyayyar ta, na daga cikin Abunda suka ja ra'ayin shi, yaji Sam baya ma da ƙarfin da zai iya controlling kanshi. Toilet ya wuce, yana mai haɗa ruwan wanka ya shiga watsawa. Murmushi yake saki a hankali a hankali, tino moment ɗin da suke ciki na wasu ƴan daƙiƙu shudaɗɗu yanzun nan. Haka mata suke? Ko kuwa Suhan ɗin tashi ce daban? Ina wannan tsanar tata da yaji? Gaskiya ne tsafi gaskiyar mai shi ne, yanzu ko baya tunanin idan ko Ƙuda zai iya bari ya raɓar mashi mata. Ya tabbata zafin na yau ne, zumar ta ma yanzu ya fara lasa, dama tunin duniya da zuciyar tashi ke raya mashi cewa Suhan ɗin ta daban ce. Haka ya gama wankan, yana ta wasa da ruwa cikin farin ciki, har watsi da ruwa yake yana ƴan tsalle tsalle shi kaɗai cikin toilet. Sai ya kalli kanshi cikin madubi, sai yayi tsalle haɗi da sakin dariya mai ɗan sauti yana faɗin Wooh sai mu *SuhAmeen* A haka ya gama wankan, ya sake tara wasu yayi na tsarki. Sannan ya tara wasu masu detol a ciki da wasu sinadaran na dusashe ciwo. Inda ya barni nan ya tadda ni. Wasu irin hawaye duk sun bushe a saman fuskar tawa. Ko yatsa na bana iya motsawa, ina tunani faruwr komai, shigar abun jiki na, shine Abunda yafi ɗaga man hankali, shikenan ni Suhan na rabu da budurci na, rabuwa ta har abada kenan? Yana kai hannu kaina nayi ta maza na buge hannun, bai daddara ba ya kuma kaiwa. "Please my happiness, kada kiyi man haka, let me help u don Allah" "Bana so" Na faɗa ina mai kuma bige hannun "Kina so, ki daure Wife, am your Al'ameen kinsan irin son da nake maki? Please dear Janam comon" Shiru nayi, sai kuma naga idan bai taimaka man ba, ai zan iya kwana cikin najasa. A hankali na kai hannun nawa ina mai kamo nashi na fara ƙoƙarin miƙewa. Ai sai wani irin jini ya ɓalle ya fara shatata bisa gadon har ƙasa saman tiles ba tare da na kula ba ma. Har saida muka fara nisa, ina maƙale a ka faɗar tashi. Sai naji kaman wani abu na bina kuma. Ƙara na saki, ganin uban jinin da ke bina, ga wani irin zogi da tsami da wurin ya fara. "please Suhan, muje mana, zan gyara please kiyi shiru ba komai fa, wannan jinin da kike gani shi ake son gani" ya faɗa yana mai sake jana zuwa toilet ɗin. Ba musu ko wani abu, ya shiga zare mani kayan bacci da ya ɗage su sama tun ɗazu. Ban musu ba, to wanda yayi mani wannan abun ina kuma sauran wani abu? Ya taimaka man sosai wajen gasa jiki na. Ko a hakan ma ƙoƙarin cigaba yayi. Saida na sakar mashi wani kukan cikin shagwaɓa. Saida yaga haka sannan ya ƙyale ni, yana zaulaya ta, sannan ya fice daga toilet ɗin. Shi kanshi ya ruɗe da ganin yawan jinin. Hakan ya yayo zanen gadon ya shiga goge jinin dake Ƙasan tiles ɗin. Yayi niyyar wanke jinin, saboda hakan ba wai addini bane, kuma shi baya jin idan zai iya fallasa ma wani Sirrin su. Kenan da matar tashi ta kasance ba masu jini bace ba fa? Duk da ba wai kowa ne ysan da cewa ba kowacce mace bace mai yin jinin. Saidai wata zuciyar na kwaɓar shi. Gudun ja ma Suhan ɗin matsala, tinda Al'ada ce ta masarauta, kuma masarauta babba kaman wannan, sannan yasan cewa su Mama fulani Abunda suka tsaya jira kenan. Haka ya buɗe wardroop ɗinshi ya zazzage wasu kaya dake cikin wata leda mai kauri, ya ɗauko ledar, ya dunƙule zanen gadon ya tura ciki. Ya ɗauko wani zanen gadon ya shimfiɗa, yana yi yana sakin dariya, shi kaɗai. Haka ya koma toilet ɗin ya tadda ni zaune cikin ruwan zafi, bayan na gama tsarkake jiki na, ruwan zafin na ratsa ni, ina mai wani irin lumshe idanu. Kawai saidai ji nayi an kwaƙume ni, ana sakar mani wani irin Kiss ta ko ina. Kare jikina na shiga yi, cike da kunya, ina mai faɗin "Ka bari yaya, Kunyar ka fa nake ji" "Ni fa mijin ki ne, ko kin manta, amarya ta, yau ne fa aka ɗaura" Cikin wata Kunyar na shiga kara kaina zuwa jikin nashi, inda ya fidda kunya ya shigo cikin bahon gabaki ɗaya. Tin bana sakin jiki, har na saki jiki ba kaɗan ba, yana mani wasu abubuwan ina zuba mashi shagwaɓa. A haka ya naɗo mu cikin shawul ɗaya, har bakin gadon, yana mai jawo mai ya shiga bin ko ina na jiki ma yana shafa mani, kunya ma nuna wa yayi wai baya so, to dole ce dai kunya, a haka na dinga bin shi, duk da har yanzu ban manta Abunda yayi mani ba, Amman ƙaunar shi na hana ni ganin laifin hakan. Da kanshi ya zura mani rigar bacci mai sauƙin nauyi, inda rabin bayan ta yake a kwashe, shi kuma dogon wando kawai ya sanya, ya rungume ni gami da ja mana bargo, yana mai raɗa mani *"Sleep Tight My Sweet Suger"* Gani da yayi bacci yana neman sake kwashe ni, saboda wankan da nayi, sai gajiyar take sauka a hankali, ga mai na gajiya da ya mani massaging a jiki. Lunshe idanu na nayi a hankali ina mai cewa "Same dear" sannan na saki wani irin murmushi, lokacin da nake iya jiyo saukar numfashn shi da laɓɓan shi bisa wuyan nawa. Ya riga ni yin bacci, ajiyar zuciya yake saukewa kaman baida nauyin komai a tare dashi. Ni kau gajiya da sauran raɗaɗi su suka taru suka hana ni baccin ma. Saidai in saki ajiyar zuciya a hankali da murmushi jin wai yau ni Suhan nice kwance cikin bargo guda da Ya Ameen ɗin kuma a gado ɗaya..... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> Addu'a Ga Wanda ya ba da Bashi idan aka zo biyan sa bashin: بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي أَهْلِكَ وَمَاِلكَ. إِنَّمَا جَزَاءُ السَّلَفِ الْحَمْدُ وَاْلأَدَاءُ. Barakal lahu laka fi ahlika wa malika, Innama jaza'us salafil hamdu wal'ada. Allah ya yi maka albarka a cikin iyalinka da dukiyarka. Hakika sakamakon bashi shi ne godiya da biya. *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~65~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Ya riga ni tashi, saboda haka yana buɗe idanun shi suka sauka a bisa kaina, wanda na riga na kwakwume hsi kaman zai gudu ya barni, a haka nake ta sakin bacci na, akai akai na kan saki ajiyar zuciya, ƙura mata idanu yayi cikin haken side lamp, fuskar nan tayi fayau ba ɗigon kwalliya ko wani abu, saidai gashi da ya barbazo mata. A hankali ya sanya yatsu ya shiga kauda mani siraran gashin da suka duddunƙule saboda shan ruwa da sukayi jiya. Sai da ya sakar mata wani side peck, sannan ya shiga raba jikin ta da nashi a hankali, yana mai sake ja mata bargo. Toilet ya wuce kai tsaye, ruwa ya sake haɗawa masu zafi yayi wanka, har yanzu yana iya jiyo ƴar gajiya tattare dashi, a hankali yake sakin murmushi, hamdala yake tayi ga Allah, daya mallaka mashi burin rayuwar tashi, yana mai ƙara gode ma Umma da tayi tsayin daka tare da taimakon Allah, Suhan ɗin ta zama cikakkiyar mace, mai tarin ni'ima da ɗanɗano. Sai da ya gama nashi wankan ne, sannan ya sake haɗa mani wasu ruwan, masu ɗan zafi suma. Dawowa yayi bakin gadkn, inda nake kwance har yanzu inda ya barni, duk da baccin Naji kaman ya rage armashi. Hannun shi dake da sauran ruwa dasu yayi amfani wajen shafa fuska ta a hankali, Miƙa na shiga yi, bakina ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, hakan ya ƙara mashi daɗi, ganin har yanzu ban buɗe ido ba, ga alama baccin bai isheni ba, dama yana iya jiyo ta ce cikin bacci tana ta mutsuniya, alamun bata samu bacci da wuri ba, to saidai ba zai iya barin ta haka ba, sallar asuba abu ce mai tarin falala,beside ma yana sane da cewa ko Sallar da ma'aurata keyi a daren da zasu tare su ba suyi ba, baisan dalili ba, wani irin abu ne yaji yananfizgar shi ga Suhan ɗin, wanda har ya kasa jure ma roƙon ubangijn nashi a kanta. Bakinshi ya kai a hankali kan laɓɓanta, masu ɗan duhu, sai ƙyalli suke yi suna ɗaukar ido. Jin sanyin laɓɓan nashi ne ya sanya ni saurin wara idanu na. Ai sai idanun mu suka sarƙe cikin na juna, fuskar shi na saman tawa, kaman zasu haɗe. Murmushi ya sakar mani, nima banyi sanya ba, na shiga sakar mashi kalar nawa, Amman cikin shagwaɓa. Miƙa nayi a hankali, daidai lokacin da ya tallafi ni gabaki ɗaya a ƙoƙarin shi na miƙr dani tsaye. Wani irin raɗaɗi Naji da har saida na ɗan runtse idanu na, yana kula da hakan, wani tausayi na yaji ya tsira mashi, ko ba komai dai yasan shine sila. Ga Suhan ɗin wadda har yanzu akwai sauran ɗanyantaka a jikin ta, tinda shi zai iya cewa ma duk cikin ƴan matan dake kawo mashi hari babu mai ƙarantar shekarun ta. Wasu ma har masters sun gama. Wasu ma Dr. ne. "Ko sai na ɗauke ki ne baby ta?" Ya faɗa a hankali, Bakinshi daidai kunne na. Sake riƙe shi nayi, ina mai girgiza mashi kai, "To bari in raka ki dai duk da haka" shima ya faɗa, yana mai ɗaga ni cak ya ɗora ƙafafu na bisa fararen ƙafafn nashi sal,da suke ɗauke da taushi da gargasa kwance bisa yatsun. A haka ya fara tafiya dani, kaman masu wasan yara, ni kuma sai sakin dariya nake a hankali, wia ashe haka Rayuwar auren take? Ashe haka soyayyar ma gabaki ɗaya take?, watau komin yanda kake soyayya da mutum idan baka aure shi ba aikin banza ne. Sai gashi ni daga daren da muka fara haɗuwa dashi bayan auren, zuwa yanzu ya saƙa mani abubuwa a zuciya waɗanda ba zan iya mantawa bane. A haka har muka isa Toilet ɗin, sai dariya nake yi, shima yana biye mani, har ɗan cakulkuli yake mani, sai nayi kaman zan faɗo sai ya taro ni, ni kuma cike na ke da kunya, sai sussunnewa nake, shi kau ko a jikin shi hidimar gaban shi kawai yake. Sia nake mamakin Ya Ameen, ashe wai yana iya dariya har haka, ya saki jiki dani kaman wadda muka shekara ɗari. Dire ni yayi a Toilet ɗin, yana mai faɗin "shiga kiyi wanka, zanyi alwala ne" Da kallo nake binshi, wai yana nufin inyi wankan, shi kuma yana kallo na yana alwala. To ta ina ma hakan zata yuwu? Ango daren farko, ko alwala dubu zaiyi, indai gaban amaryar shi ne tana wanka ai sai ta warware, bayan haka ma, ni ina zan iya wani yin wanka gaban shi? Ko jiya ma dan ina cikin wani hali ne, bana da yanda zanyi. Bai kula ni ba, ya shiga yin alwalar shi cikin sinc, yana yi yana sakin murmushi. Har ya gama. Sannan ya juyo yan amai yarfa mani sauran ruwan, saida na ɗan firgita, saboda ko alama ban san ina tsaye na shagala da kallon shi ba. YA Ameen daban ne, kome yake cikin natsuwa da ƙwarewa, ga aji kaman mace, kalar tashi soyayyar daban take a cikin zuciya ta, ko hakan yana da nasaba da babu wanda na taɓa tsayawa na kula da sunanan soyayya in bashi ba? Ficewa yayi daga Toilet ɗin, saida naga fitar shi ne, na danna ƙofar ina mai zura key, yana jiyo ta, sai ma murmushi daya sauke, yana mai zura Jalla biyar shi, ya shiga murza mai mai sauƙin zafi. Salla ya tada, daidai lokacin da yaji saukar ruwa, alamun ta fara wankan. Ya daɗe yana sallar, haka na fito ina ta sanɗa, wai kada ya ganni ɗaure da towel. Nima Jallabiya na sanya mai taushi har ƙasa, saidai rober ce, na murza mai kaɗan haɗi da turaren jiki, sai humra, sannan na zura hijab ɗita, nima na shimfiɗa darduma daga bayan shi, sannan na tada tawa sallar. Sai da muka kammala ne, sannan ya umurce ni da in tashi mu gabatar da sallar godiya ga mahaliccin mu. Kunya ce ta kama ni, sallar da ake kafin a san juna, shine mu sai bayan da muka san junan ne sannan zamuyi. Haka na sake miƙewa a hankali, yana mai shiga janmu sallar har muka kammala cikin natsuwa, sannan ne ya juyo zuwa gareni, tambayoyi ya shiga yi mani a hankali ina bashi amsa, inda yaga ban sani ba sai ya sanar dani, na ƙaru da abubuwa da yawa, anan ne na fahimci irin tarin ilimin da Ya Ameen yake dashi. Alfahari na shiga yi da samun miji kaman shi, bayan duk wahalhalun da na shiga a baya saboda tarayya dashi, duk da a lokacin taimako ne ma ba wata soyayya ba. Sai gashi ashe shi ɗin rabo na ne, ashe mallaki na ne, wannan kyakkawar halittar da take zaune ɗauke da alƙur"ani gaba na, tana rera karatu mai cike da natsuwa da ƙira'a mai daɗin sauraro kaman limamin Makka. Kaina ya dafa ya shiga kwararo addu'a, a kunyace nake amsawa da ameen, inda daga baya muka shafa mu duka, sannan ya miƙe yana mai naɗe dardumar shi ya maida ta mazaunin ta, sannan ya maƙala counter ɗinshi a yatsa, yana mai cewa dani "Zan tafi masallaci, idan kinyi salla ki koma ki kwanta baby, ki huta sosai, Allah yasa kada a tada ki har sai kin gaji dan kanki, jiya kin wahala baby, ina fatan zaki yafe mani, soyayyar ki ce ta jawo hakan, Amman kaina bisa wuya, ga keda cen idan Afnan tazo ki bata ta kai ma Mama Zainab, I love u much sweet heart, haskn zuciyar Al'ameen" Yana gama faɗar haka ya durƙuso da guiwoyin shi har ƙasa, sannan ya manna man peck a goshi, ya miƙe yana mai ficewa ya ja mani ƙofar ɗakin. Am spechless yau, komi Ya Ameen yayi mamakin shi nake, kaman ba shi ba dagaske, ina fatan ace ko mafarki nake kada in farka, indai har wannan ce irin ƙaunar da zan dinga samu daga wajen su, wanda ƴan mata da dama ke fatan ace dama su ne. Ina jiyo tashin sautin ƙira'r shi, cikin salo da gwanancewa yake jan sallar, a masallacin dake ƙofar gida, wanda dama ya kan ja akai akai idan yana nan, su kansu mutane sunyi mamakin ganin shi, hakan na ƙara dasa ganin girma da ƙimar shi a idanun ɗauka in mutanen. Ga kalaman shi na ƙarshe na gane ba zai dawo ba, hakan ta sanya bayan na gama sallar tawa, sai na miƙe, ina mai naɗe dardumar, sannan na hau gran gadon, kada ma wani ya shigo ya fahimci wani abu ya faru. Sannan na kwanta, ina mai duƙunƙunewa, jiki na yana kewa nashi jikin da yake ɗauke da ɗumi da ƙamshi mai daɗin shaƙa. Shi kuwa daga masallaci ɗakin Abie ya koma ya kwanta, Abie sai ƙunshe dariya yake, saidai sanin halin Yayan nashi ya sanya ya basar, kenan Yayan nashi wajen amaryar shi ya kwana, tinda lokacin da ya fito daga sashen ne suka haɗu, sannan suka rankaya zuwa masallacin, ko da suka haɗu da Dad, bai bari sun haɗa idanu ba, go gaida shin da yayi, idanun shi na ƙasa, inda Dad ɗin ke ta sakin murmushi, ko ba komai ya zuwa yanzu yasan yaron nashi ya girma. ******* Ban farka ba, sai da naji kaman motsin mutane a sahen nawa, a hankali na sauko ina mai fitowa falon. Haɗimmai ne ke ta aikin gyara ko'ina, duk da dama ba wai wata dauɗa yayi ba. Ganin na fito ne ya sanya gabaki ɗyaansu kwasiwa da gudu, suka zube suka shiga gaida ni, cewa nayi su tashi bana son wannan durƙuson, sannan na shiga amsawa, ɗaya daga cikin su ce ta matso inda nake tsaye, ta shiga miƙa mani wata kyakkyawr jikka, tana mai faɗin "Ranki shi daɗe, ɗiya ga Hasken masarauta, wannan kaya ne daga Mama Fulani, tace a sada ki dasu, domin kuwa sune wanda zaki sanya ayau, za'a gabatar da walima kafin su wuce, da wuri za'ayi walimar da haka suke fatan zaki shirya da wuri, mai kwalliya zata shigo yanzu tayi maki" Da hannu nayi mata alamu da ta kai su ciki, ba musu ta wuce kai tsaye zuwa cikin ɗakin. Inda wata kuma ta sake matsowa tana mai faɗin, "Ranki shi daɗe, ga kayan abincin safe cen an jera, saƙo ne daga Hajiya Babba, tace mu tabbatar Kinci abinci" Idan na fahimce ta, Mom kenan take nufi, Hmmm ni bansan me zan kira wannan al'amari ba, wai ban sani ba, ko dai tana yin na ganin ido ne? Kai tsaye na koma Toilet na sake yo brush, sannan na fito falon na zauna, ina cin abincin kaɗan kaɗan, har yanzu banga giccin wata daga cikin ƙawayen nawa ba, koda kuwa Afnan ce da take ƴar gida. Dan dai nasan hafsat bata isa shigowa ba yanzu. Kaɗan na tsakura na basu izinin fita dashi. Sannan na shiga ɗakin da har an riga an gyara, an wanke hada Toilet. Wanka na kuma yowa, su dai haɗimman duk suna falo suna jiran in basu umurni, saboda haka ina gama zura kayan da suke na zakkar sarauta, an masu dishe dishe da ruwan gold, ga sarƙoƙi har ciki da ƴan kunne, harda abun maƙalewa a hanci da gashi, kaman wata ba'indiya. Sannan ne na basu izinin kiran mai kwalliyar. Ana man kwalliyar, ina iya jiyo hayaniyr mutane daga harabr gidan, mai kwalliyar ce ke faɗa mani, wai abu da masu abun su, dan banga yanda ake ta shisshirya ma wannan walimr bane, dangin nawa fa, tafe suke cike da kayan Arziƙi, sannan ga surukan nawa ma sun rufa sun tada kai. Ganin kaman tana da surutu ne ya sanya ni yi mata shiru, saidai zuciya ta wata iri, ina gudun ace Hajiya Kubra salo ne ta cenza, bana fatan ace a zama na da Ya Ameen wani abu ya kawo tarnaƙi, da har zai iya shiga tsakanin mu da farin cikin mu. Na shirya tarar miji na, na shirya mallaka mashi kaina, har sai na wuce a kira ni baiwa, a shirye nake da aiwatar mashi da duk abunda yake so, muddin hakan zai faranta mashi, kuma bai saɓa ma shari'a ba. Ya Ameen namiji ne da kowacce mace ke da burin mallakar irin shi. Abun hannun shi, kyaun shi, ajin shi ko ilimn shi, bai sa shi jin kanshi shi ɗin wani ne ba, kuma masalan yanda na kula da yana da matuƙar zuciyar taimako, wanda hakan na tabbata ya gaje shi ne wajen mahaifin shi da ya kasance miji ga Umman tawa, kuma mutumen kirkn da tin dana taso na buɗi ido a duniyar nan nake ma kallon mahaifi. Domin babu irin Abunda baiyi mani ba a faɗin duniyar nan. Haka aka gama shirya mani, tini amarya ta ɗauki walwali da kalli. Ko ina na jiki na haskawa yake yi. Mai kwalliyar ce ta kwashe kayan, tana mai faɗin ƙawayen amarya na cen na jiran ta, sunce ba zasu fito ba sai sun gama shiryawa. Bayan ta fice ne, suma sauran haɗimman na sallame su, ina mai ce masu suma suje suyi wanka. Window na ɗaga ina iya hangen duk Abunda ke faruwa a harabar gidan, idan ba zan iya mantawa ba, wannan fa sashen Ya Ameen ne, kuma ga alamu babu abunda aka cenza, saidai gyarawa da aka kuma yi, na tini abubuwa ma bambanta da suka taɓa faruwa dani anan, ciki kuwa hadda kama ni da Ya Ameen ya taɓa yi dumu dumu ina binciken ɗan kunne a ɗakin nashi. Ashe ma zai zama mallaki na, ɗakin da mai ɗakin, Allah kenan, mai juya al'amari yayi yanda yaso dashi. Ina iya hangen yanda ake ta kai komo, ana ta shige da fice, wasu sun shirya wasu kuma basu shirya ba, ko ina ma'aikata ne da haɗimmai bayin gidan sarki da suke tare da su Ammi. Allah sarki, ammi mutumniyar kirki ce, kaman yanda na kula halin su ɗaya da mama Fulanin da ta kasance Yaya gareta. An kakkafa rumfuna, an ƙawata ko ina, sai shiga ake d a manyan kuloli da kayan lashe lashe, ina iy a hango ƴan uwan Hajiya Kubra gaba gaba, akan yanda za'a haɗa wurin walimr, a hankali na saki ajiyar zuciya, ina mai komawa na zauna bakin gadon. Abubuwa da dama ne ke kai komo. Ka in kace me sashen nawa ya fara cika da mutane, kama daga ƴan kankiyar da kuma sauran mutane, wanda basu samu ganin amarya jiya ba. Gida fa ya cika yayi maƙil. Sai hayaniyr Jama'a da kake jiyowa. Ina zaune ne tsiru bakin gadon, sai ga su Afnan ɗin sun shigo cikin kwalliya mai ɗaukar hankali, kowacce ta sanya kalar kayan ta daban, Amman na kasa tantance wadda tafi kyau, dan dai suturar da Afnan da Jidda suka sanya sunfi ja sauran tsada. Nan suka shiga rungume ni suna zaulaya ta wai matar Yallaɓai. Fara'ata ta yawaita, jin ƙawaye na wasu kuma ƴan uwa na kusa dani, nan suka buɗe babin fira, kowacce sai ƙunshe dariya takeyi. Har ƙarfe 11:30 ne sannan akace kowa ta fito za'a fara gabatar da walima. Inda akace ni amarya su barni, su mama Fulani da Ammi ne da kansu zasu shigo su fitar dani. Ina jiyo ƙarar loudspeaker ɗin Mc, ya fara gabatar da shirye shirye. Ina zaune sai ga Su Mama Fulani da Ammi. Da murmushi nake gaishe su cikin jin kunya, suma suna murmushin suke amsawa, kowaccensu saida ta rungume ni, Ammi tana jima kaman wadda ta haifa a cikin ta, sannan suka kamo hannu na, suna mai jana a hankali zuwa harabar gidan inda aka ƙawata har an fara gabatar da walima. Subhanallah! Tsayawa faɗar yanda aka ƙawata wurin ma ɓata baki ne, kowa ka gani cikin fara'a da walwala, in ka ɗauke Saudat, Nihal sai Mama Talatu da Maree da suke gefe raɓe, suna kallon dukkan abunda ke faruwa. Wajen Mom aka nufa dani, ana mai umurta ta da in gaidata. Bata jira komai ba ta miƙe tana mai sakin maɗaukakin murmushi ta rungume ni tsam, a jikinta. Wnai iri Naji banbaraƙwai, WAI hajiya kubra ce take mani haka? Wai shin ko dai dan gaban su Mama Fulani ne? Haka na zame jiki na na durƙusa ƙasa, ina mai gaishe su, ta cikin alkyabbar da aka yada mani. Haka ƴan uwanta, da manyan mata, matan manya suka dinga tasowa suna rungume ni da ɗaiɗaya, sai murmushi suke, suna masu yaba kyau na, da dace da Al'ameen yayi. Nan na tabbatar da Cewa Ya Ameen ɗan so ne. Kowa murna yaje da ganin matar shi, inda wasu ke faɗin sun dace, wasu kuma ta ciki na ciki, domin daga cikin waɗanda suka zo, harda iyayen yaran da suke cewa suna sonshi, shi kuma yana watsa masu ƙasa a ido. Daganan aka kaini wajen Su kaka zuwaira. Nan ma naga zallar ƙauna, lallai Ya Ameen na tabbata daban yake ko a cikin zuri'r su, kowa sonshi yake da ji dashi, ƴan kankiya kam sai Sam barka, domin duk a cikin su, kowa da zuciya ɗaya yake ƙaunar mu ni kaina na tabbata. Daga nan ne aka koma dani rumfar su Mama Fulani aka zaunar dani, kafin a gama a miƙa amana ta ga Hajiya Kubran. Walima ake gabatarwa mai daɗi, da ƙayatarwa, inda aka shiga gabatar da kayan ƙore ga Uwar ango da dangin ango. Kowa yayi mamakin iyayen abubuwan da aka basu, wannan ce ta sanya Hajiya Kubra ƙara tsinkewa da Al'amarin na masarautar, duk da kayan da aka bayar, ana cikin walima sai ga ƙatuwar mota daga masarauta inji mai martaba, wai aba ango, wannan tukuicin shi ne, harda motar da ta kasance sabuwa dal kuwa. Nan wuri ya ɗau sowa da tafi, walima ta ƙayatar da kowa. Nan su Mama Fulani suka miƙa ni ga Mom, suna masu jaddada amanar ta garesu, duk da su ɗin sun lura cewa Soyayyar da take nuna ma Suhan ɗin kaman ta abun duniyar da ta kula suna dashi ne, duk kuwa da cewa suma kowa ya sansu a faɗin Nigeria cewa indai kuɗi ne sunyi ƙarin suna akan hakan. Sai da aka sake raka ni sashe na, sannan suka ƙara man faɗa da jan kunne akan in zauna da kowa lafiya, da dangin miji na da ƴan uwan shi, sannan suka fara haramr tafiya, kaman inyi kuka, gashi harda su Asiya da sauran haɗiman guda biyu kawai aka bar mani wai su dinga taya ni aiki, Nidai cewa nayi a tafi dasu zan iya yin aiki na da kaina, to da nayi ma wanda ba gode bare na gode, balle wannan da yake na lada, kuma aikin ma a gidan Ya Ameen muji gareni a yanzu? Sai gashi ba Afnan ce tayi mani maganar ledar da ya Ameen ya bari ba, wanda ni bansan menene ciki ba, Hafsat ce ta leƙo tana tambaya ta, nuna mata inda take ajiye nayi, naga dai ta ɗauko ta buɗe tana ƙunshe dariya. A haka ta fice, saboda ɗakin cike yake da mutane. Ko bayan tafiyar Su Ammin shagali aka cigaba dayi sosai, inda Mom ta aiko aka maida ni sashen ta, yanda duk wanda yazo zaiga amarya ba tare da an ɓata man sashen ba a cewar ta. Ina ta shan amaki fa, Hajiya Kubra da ƴan uwanta da ƙawayen nata sun koma kaman ba su ba, sia kaffa kaffa suke dani, inda Nihal da Saudat suke ji kaman su fashe, masalan ma da suka ga cenzawar da Mom tayi a lokaci guda, sai suka yi shigewar su ɗaki ma ba tare da sun sake fitowa ba, to koma dai minene dan kansu domin Nidai ya zuwa yanzu na san kaina, kuma nasha gaban su Fintinkau, saboda ina auren Yayan nasu. ********** Komawra su mama Fulani suka tadda sabuwar dambarwar data so ruɗa su a masarautar tasu. Umma ce ta tubure akan cewa lallai Baba waziri yana da masaniya akan faruwar komai, saboda haka ne take so ayi zama domin ya warware mata dalilin mutuwar mijin nata da yake da masaniya akai, da kuma inda dukiyar ta data ɗiyar ta ta shiga, da kuma dalilin su na aikata mata wannan ɗanyen aikin, ta dena shiru, dawowa tashi ce ta sake tada mata mikin da ta daɗe tana binnewa a cikin zuciyar ta, inda yanzu bata iya jurar ganin wanda yake da hannu cikin rusa mata farin cikin ta, Rayuwar ta, shima yana cikin farin ciki da walwala. Kuka kawai take, Abunda ya tada hankalin mai martaba kenan, waziri na neman barin gidan, mai martaba ya hana a bar shi ya fita, a cewar shi Umman tayi haƙuri har sauran baƙin dake gidan su idasa tafiya, Abunda ya kuma ɗaga mata hankali kenan, gani take kaman ko da yaushe za'a iya wayar gari ba waziri ba labarin shi.... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'ar Tsoron Shirka: اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ أَنْ أُشْرِكَ بِكَ وَأَنَا أَعْلَمْ، وَأَسْتَغْفِرُكَ لِمَا لاَ أَعْلَمُ. Allahumma innee a'oozu bika an oshrika bika wa-ana a'lam, wa-astaghfiruka lima la a'lam. Ya Allah! Ina neman tsari da Kai da na yi shirka da Kai alhali ina sani, kuma ina neman gafararka ga wanda ban sani ba. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Wannan Page ɗin naki ne @Salamatu kiyi yanda kike so dashi, kuma ki gaida mana da Ya Ameen kice muna mashi Allah ya huta gajiya* *Dama rayuwa ta gaji haka, sai Kaga wani cen daban wanda baka haɗa komai dashi ba, shine masoyn naka, mai bibiyar ka, Amman wanda kake ganin ɗan uwa ka ne, abokin ka ne, maƙwafcinka ne, ko kuma abokin wasan ka, shi kam baya bibiyar ka, balle ma idan kayi posting ɗan sharhin nan yayi maka, wanda ni kau a gani na ba haka zaman tare yace ba, idan kana son mutum kana son Abunda yake yi, ka faɗa mashi, ka ƙarfafa mashi guiwa, ta hakan ne kaɗai zaka gane cewa mutum ya san dakai kuma shi ɗin naka ne. Hmmm Allah dai ya kyauta wlh* *Page ~66~* Walima tayi kyau sosai kam, ni dai ina cen zaune ɗakin da Mom ta sanya aka buɗe mana ni da ƙawaye na, afnan kau sai shige da fice take yi, komai ake buƙata ita ce mai kawo mana shi. Kyaututtuka dai na sha su daga hannun manya, idan Mom taga kyauta ce mai muhimmanci Afnan take ba ta kai mani sashe na ta kulle mani. Kwata-kwata ban ko ga giccin Ya Ameen ba, ko da wasa, tin dai asuba daya fice. Mai video coverage yana ta faman aikin yi, yayin da gidajen tv suma suna ta naɗar abubuwa masu amfani. Hayaniya naji ta kaure sosai a cikin harabar gidan, wai ashe anguna ne suka shigo gaida iyayen su. Da kuma yi masu Allah ya sanya alkhairi. Sashen Kaka zuwaira suka fara shiga, aiko sun sha zaulaya kaman me? Da zasu fice ne take cewa dasu wai suje su kawo mata amaryar a ɗauke su photon tarihi. To koda suka shigo sashen Mom ɗinma sun gaggaisa sosai, inda suka buƙaci amarya ta fito za'ayi hotunan tarihi, na wannan babbar ranar. Haka aka sanya aka sake gyaggyara mani, kaina a lulluɓe aka fito dani, duk kowa ya fito kuwa ana ta son ɗaukar photo da amarya. Bamu tsammani ba sai ga Dad da Alhaji Auwalu. Suma nan suka shiga akayi ta haskawa dasu, masalan da ƴan uwansu da kuma surukar tasu. Duk abunnan da akeyi su Nihal na ciki basu fito ba, baƙin ciki da kishi kaman ya kashe su. Nihal hada hawaye tayi na baƙin ciki, saudat ce mai bata baki, akan cewa ai dole ne ma su san abun yi. Dole aka sanya ni buɗe fuska ta saboda photon, Masha Allah, shine kalmar da kusan kowa ke faɗi, shi kau gogan naka sai tsura mani idanu yakeyi, duk motsi na yana kan idon shi, har tsarguwa nayi saboda kaf iyayen namu suna wurin. Yayi matuƙar kyau cikin dakakkiyar shadda kalar sararn samaniya, sai ɗaukar idanu take yi, ɗinkin Abuja style. Da mun haɗa idanu sai ya kashe mani ido guda, ta cikin farin glass ɗin da yake manne a saman kyakkyawr fuskar tashi, wanda ya taimaka wajen ƙara ƙawata fuskar. Idan aka jera mu kuwa waje guda domin ɗaukar hoton, sai ya ɗan ranƙwafo yace mani "Baby na ya jikin naki?" ko kuma ya kamo hannu na tsaf cikin nashi, kuma idanun kowa a kanmu suke, hakan ya sake tabbatar ma mutane irin zallar ƙaunar dake tsakanin mu, wadda ba'a san tun lokacin da ta fara ba. duk sai kunya ta kama ni, Naji na ƙagara mu bar wurin,tin kafin ya aikata Abunda zan ji kunya sosai, tinda na lura kaf natsuwar shi tana a kaina ne. Anyi shagali sosai, inda anguna suka fice, duk da haka saida ya kira Afnan gefe, wai idan ta sake ko Ƙuda ya taɓa mashi ni sai yaci ƙaniyar ta, kuma ba zai siya mata motar da take so ba. Aiko dariya ta fara yi, tana ihun tsallen murna, ta daɗe tana mashi magiyr motar nan, sai gashi yanzu ta dalilin Aunt Suhanan zata samu. Aiko ta dawo ta fara kaffa kaffa dani, da anyi magana tace ai ango ne ya bata amana ta. Don haka yanzu ita ce matsayin angon. Sai a sanya dariya, kowa na mamakin irin ƙauna da shaƙuwar dake tsakani na da Afnan ɗin, duk kuwa da cewa ma girme mata, ba za'a taɓa cewa tsara ta bace. A hankali mutane suka fara raguwa, sai bayan magariba ne Mom ta sanya aka maida ni sashen na. Inda aka hana kowa zuwa banda ƙawaye, wai a cewar su a bar su su gyara mani sashe na. Mom ce tace Maree taje ta taya su. Aiko jiki ba ƙwari ta bisu, dalili kuwa shine tana son ma ta shiga sashen da ake ta zuzutawar cewa yafi ko ina kyau a gidan, oh wai yarinyar da suka raina ma wayau yau ita ce Allah ya maida haka. Ni kam tinda ta shigo tana ta wani kalle kalle da raɓe raɓe, sai Naji na tsargu ban yarda da shigowr tata ba, Afnan nayi ma magana cewa tace nace ta bar shi kawai nagode, saboda ko alama ba zan iya lamuntr barin nata ta shigar mani ɗakin mijina sirri na ba. Aiko da saƙon ya iske ta, kaman ta fasa kuka, taso ko da kaɗan ne, ta gano wata mafaka da zata iya samu, wadda zata yi amfani da ita ko da nan gaba ne. Ta yanda ko wata ajiyar tayi ba zan iya gano ta ba kai tsaye. Haka ta fito zuwa ɗakin nasu, kuka ta dasa ma Mama Talatu, laifin ta take gani, ita ce ta kasa bata abunda take nema, ta kasa yin wani kwakkwaran aikin da zai warware wannan al'amarin. Aiko zagi mama talatun ta hau ta dashi kaman zata bugeta, har tana ce mata, ita fa ta zubda makaman yaƙinta ne, saboda yanzu ta gano cewa Umman mace ce ce mai ɗinbin darajar da idan tayi wasa da ita, zata iya sanyawa a ɗaure su har igiya tayi rara, sannan taja hankalin ta akan cewa itama ta kiyaye, in kuma zata je tyai wani abu da zai sanya a kore su a gidan ne, to ta sani daga ra ar ne fa zata gane cewa tayi wauta, domin cewa zata yi ba ita ce ta haife ta ba, itama tsintar ta tayi, domin ba zata ka. U ta ba, tsawon lokaci tana zaune a gidan cikin rufin asiri kwatsam tazo tayi mata sanadin inda take raɓe ba. Maree kam kukan ta take, koma fahimtar Abunda mama Talatun ke cewa bata yi, ta ƙudurce abubuwa masu yawa a cikin ranta. Sam ba zata lamunci ganin burin Rayuwar tata tare da wata cen ba. ********* Da kyar su Mai martaba da Mama Fulani suka shawo kan Umma ta yarda ta haƙura, zuwa bayan hidima, taji ɗan sauƙi, masalan da Mama Fulani ta sanar da ita irin tarba da masauƙin da suka samu, abun sai Sam barka, har suka baro gidan basu ci karo da wani abu da bai kwanta masu ba, sun sake tabbatar da cewa tabbar MUHAMMADU Al'ameen yarimn matasan gadon alkhairi yayi, domin ko kafin su taho siada Alhaji Mustapha ya cika su da sha tara ta Arziƙi, yana ta masu godiya, tare da miƙa saƙon gaisuwa zuwa ga Baffa mai martaba, da cewar sai sun shigo shi da zuri'r tashi kaf bayan biki godiya. Umma taji daɗin hakan, ta sake alfahari da samun miji kaman Dad ɗin, saidai Abunda ke ɗaure mata kai, cenzawar, da kuma amincewr auren da Hajiya Kubra tayi lokaci guda, saidai ma ko menene tana fatan ya kasance cewa har cikin zuciyar ta ne. ******** Sai bayan isha'i ne suka kammala gyaran ko ina, tsaf kaman ba'a taɓa shiga sashen ba. Su raihana ne ke sanar dani cewa gobe zasu koma makaranta, duk Abunda ake yi jikin khade a sanyaye yake, duk kuwa da cewa tayi sabon saurayi itama mai ji da kyau da naira cikin abokan Ya Ameen ɗin. Basu bar ɓangaren ba, siada suka jiyk maganar ya Ameen cikin gida, Afnan ce ta janye su, tana mai faɗin "Uhmm kuzo mu bar sashen nan, tin kafin oga ango yazo yayi mana mazurai" dariya suka sanya, suna sake jaddada mani cewa da wuri suke son wucewa, saboda jibi an gaya masu suna da assesment. Ganin hakan ne ya sanya ni tashi domin rage kayan jiki na, dama na gaji ga kuma nauyi da kayan ke dashi, kallo na nakai kan Kyaututtukan da na samu, harda makullan mota, da kuna gwala-gwalai, sai kuɗi cash ƴan bandur bandur ɗin 1k da kuma check, wanda bansan me ke rubuce jiki ba, dama jira nake sai ya shigo sannan in nuna mashi. lallai kyautar manya, tabbas wlh wata ma ta riya ce, to in ba haka ba, daga auren yaron su sai su dage suyi ta zuba mani kyauta haka? In ma sunyi don a maida masu ne, to wannan tsakanin su da Mom da Dad ne tinda domin su sukayi Toilet na shiga na watsa ruwa, ina fitowa Naji waya ta ta ɗauki ruri. _Hayateee_ shine sunan da na yi saving Number ɗinshi, domin ya zuwa yanzu na yarda cewa shine rayuwa ta. Ɗagawa nayi cikin siririyar murya ta, ina mai amsa Sallamar da yayi mani, jin muryar shi wani iri ne ya sanya jiki na yin sanyi. Shaida mani yayi cewa Hafsat ce ba lafiya, gata nan za'a shiga da ita teater, domin sun shaida masu cewa ba zata iya haihuwa da kanta ba. Salati na sanya, ina mai kai zaune cikin tashin hankali. "Ina Sadeeq?" tambayar da na fara yi mashi kenan, domin nasan duk inda yake yana cikin tashin hankali. "Wallahi baby yana cen yana kuka, bakiga tashin hankali ba, sunce yaro har ya shekara, dama tini suka so suyi tin kafin abun yayi worst haka, sune suka ƙiya" Nima ai sai Naji kukan ya taho mani, kuka nake yi sosai, ina ce mashi yazo ya ɗaukeni inje in gano Hafsat, kada ta mutu bamu gana ba. Lallashi na ya fara yi, sai kuma lokacin yayi danasanin kira na, ya manta halin ruɗu da firici na. Yanzu zan tashi hankali na, gashi kuma shi baya jin idan zai iya bari na fitowa a yanzu, dandai kawai sanin yanda nake da ita ne ya sanya shi sanar dani. Hankalin kowa fa a tashe yake. Hajiya Zainab dai zaune kawai take tana ta faman addu'a ga ɗiyar tata, domin halin da aka shiga da ita ba'a cewa komai. An kusan awa sannan aka fito da baby girl samɓaleliya da ita jawur. Saidai jikin nan duk yayi saɓa, yarinyar ido tar sai kallon kowa take yi, caaa akayi ma likitnn da ya fito da jaririyar ana tambayar shi jikin Uwar, bai ce komai ba ya juya ya koma yana girgiza kai. Sai kuma aka saka kuka sosai wurin ya amsa da koke koke, shi dai Sadeeq zubewa yayi wurin saida aka kwashe shi. Bilal ma idanun shi jawur, tunowa da yayi da tashi matar da take cikin hali irin na Hafsat ɗin, Amman bai sanar da kowa ba, so yake har sai an haihu ɗin sannan, masalan ma da yake shi ba ƙasar bane. Dfik dauriyar Hajiya Zainab saida ta koka, nima ya zuwa lokacin nasha kuka na na ƙoshi, ƙasa Daurewa nayi, da gudu na fito na samu mudi zaune shima jugum, saboda da shine aka kai Hafsat asibitin. Umurtar shi nayi da ya kaini nima, musu yaso yayi mani na shiga yi mashi magiya. Kwatsam saidai suka ganni wurin da gudu, ina ta faman kuka, kukan dana tadda wurin anayi ne ya sanya ni durƙushewa nima, ina mia sake sakin wani kukan. Kowa yayi mamaki, da sauri Ya Ameen ya isa inda nake durƙushn, Amman sai ya kasa ɗago nin zuwa jikin nashi, Goggo Aisha ce ta matsr dashi da hannu, tana mai ɗago ni itama ta rungume ni sosai, tana mai goge kwlalar ta itama, Hafsat yarinya ce mai shiga rai, duk hidimar bikin nan ta daure ayi ta da ita, ashe ma ba zata ga ko Abunda ta haifa ba. Abubuwa nake tunowa dangane da ita sosai, yanda take ƙarfafa mani guiwa, yanda idan na shiga ƙuncin hali ita ce mai lallashi na, yanda tayi tsaye kai da fata wajen ganin na samu mallakin zuciyar tawa, sai gashi ashe ko Rayuwar auren tawa ba zata gnai ba, tayo shahada, rai yayi halin sa, naso saka ma Hafsat da Alkhairin da ba zata iya taɓa mantawa ba. A hankali na zame jiki na zuwa ga Hajiya Zainab da take zaune kurum kaman mutum mutumi. Miƙewa tayi itama tana mai rungume ni, kaf wurin kowa ya tausaya mani, ganin yanda nake da Hafsat ɗin, duk a cikin zuri'r su daga ita sai afnan ne mukayi muguwar shaƙuwar da za'a iya cewa kaman ƴan uwa a suke. Dangin Sadeeq ɗin wasu suna nan tsattsaye suna ta aikin lallashin mu, wasu kuma suna cen wajen Sadeeq ɗin da har yau baisan wa ke kanshi ba. Haka aka gunguro gadon da Hafsat ke kwance, an lulluɓe ta dukan ta, fuskar ce kawai buɗe, tayi kyau, tayi haske tayi fayau, kaman ma murmushi take yi, hannuwan ta duka bisa ƙirjin ta, kaman ka kira ta, ta amsa. Da sauri na fara taka wa zuwa bin gadon, Ya Ameen ne ya sanya hannun shi ya riƙo ni , ganin nafi kowa ruɗewa a wajen, bansan lokacin ɗana faɗa daman jikin shi ba, ina mai sake sakin wani tsumammen kuka. Bai ƙasa a guiwa ba, wajen rungume ni da dukkanin hannayn shi ba, shi kanshi hawayen ne ke tsiyaya ta cikin farin glass ɗin nashi, kuma na, shine Abunda ke ƙara ruɗa shi, a kunne ya faɗa mani "Hafsat ta tafi Suhan, ba kuka take buƙata ba, addu'a ita ta kama ce ta a yanzu" "Babyn Yaya, ina babyn take?" Abunda na samu kaina da furtawa kenan. Wata mata ce cikin dangin Sadeeq ɗin ta matso kusa damu, haɗi da miƙo mani jaririyar naɗe a shawul, sai mamurar hannu take, alamun nono take so, idanun ta a buɗe rangaram, kaman tayi watanni. Rungume ta nayi, ina mai sake sakin kuka, yarinyar kaf kamannin Hafsat ta kwaso, sai Hasken Sadeeq ɗin. Muna a haka ne, sai ga su Mom da Afnan, kai harda su Raihana da Khadeeja, Jiddon Dady da shi kanshi dady ɗin. Nan fa aka buɗe sabon ba in kuka, saboda ɗan zaman da sukayi tare da Hafsat ɗin har sun saba da ita, masalan ma ganin yanda kullum tana zaune wuri ɗaya turus da uban ciki a gaba, sai ka ganta tayi shiruuu, kaman mai tunanin wani abu, cen kuma sai Kaga tana walwala kaman ba ita ba. Fitowar likitocin da nurses ɗinne yaja hankalin mutane. Raba jikin shi da nawa yayi a hankali yana mai furta mani "Am coming dear" bayan su yabi zuwa office ɗin nasu. Ko zama baiyi ba suka miƙa mashi hannu, fuskar su a washe. "Congratulation ranka ya daɗe, anyi Masarar ceto Hafsat Auwal, yanzu haka tana hutawa ne, saboda haka wannan koke koke da ake tayi please a dena, idan son samu ne ma, mutum ɗaya za'a bari wadda zata kula da baby, zuwa gobe idan Allah ya kaimu sai ku dawo kuga jikin nata" Bai ko zauna ɗin ba, sia yayo kwana. Kaman zai taka rawa haka take ji, matar tashi yake tunowa, wane irin farin ciki zata yi? Hajiya Zainab fa? Itama wane irin fari ciki zata yi? Hafsat ma da rai? Bata mutu ba? Alhamdulillah, shine Abunda yake furtawa har ya ƙara sa inda suke tsaye cirko cirko. "Alhamdulillah, Mama ki dena kuka, Hafsat na nan da ranta, bacci ne take yi, ba mutuwa tayi ba" shima ya faɗa yana mai ramawa zuwa wajen da Hajiya Zainab ɗin ke zaune ya kamo hannun ta. Ajiyar zuciya kowa ya saki, ai sai kuma aka hau murna, rungume jaririyar nayi ina mai sakar mata kisses, banyi niyyar bayar da ita ba, niyya ta ni ce wadda zan riƙe babyn Hafsat ɗin, nice ya cencenta da in riƙe ta. Wani irin kukan murna na saki mai haɗe da dariya, ai sai kuma aka fara ma juna murna da barka. Shima fuskar shi washe fal da murmushi yake kallo na. Ɗakin da ka kwantar da Sadeeq ɗin ya zarce kawai ya shiga labarta masu wannan abun farin ciki, ya tadda Sadeeq ɗin ya farfaɗo ana ta bashi baki. Ai baisan ya rungume Al'ameen ɗin ba, ba zai taɓa mantawa da wannan albishir ɗin ba ɗaya fito daga bakin Yayan nasu ba. Durowa yayi daga bisa gadon yana mai nufo ɗakin da aka kwantar da Hafsat, dakatar dashi akayi, cewar likitocin sun hana sunce a bari ta huta, ai bai ko tsaya jiran cewar su ba, ya danna kai ɗakin, nima ban jira komai ba na rufa mashi baya, tadda shi nayi rungume da ita, sai kisses yake sakar mata, miƙa mashi ɗiyar nayi, ya haɗa su ya rungume. Ya Ameen ne ya shigo, gami na tsaye ina goge kwlala da hijab, ya sanya shi kamo ni zuwa jikin nashi, ban gaddama ba nima na faɗa, ina mai sakar mashi wani irin siririn murmushi, a hankali ya kia bakin nashi saman goshi na, yana mai using da hannun shi ya shiga goge mani sauran kwallar data taru, yana yi yana girgiza mani kai,alamun in bar kuka, ɗan duka na kai manƙirjin nashi, ina mai kwantar da kaina, ya sanya hannun shi ya sake lafar da kan nawa. Mun jima haka, kai kace ba zamu so rabuwa ba. Sai cen ne muka fito Ya Ameen & in ke shaida masu kowa gida zashi zuwa gobe idan ta farko sai a dawo a ga jikin. Ban aka fara raguwa, inda Mom ce tace zata zauna da Hafsat ɗin, kowa yayi mamaki, har ƴaƴan nata, har shi kanshi Ya Ameen ɗin. Haka muka baro wurin zuwa gida, ba yanda ba'a yi da ita ba, tace da safe zata koma gidan, shima saboda tana da sauran baƙi ne. Ko a motar ma da hannu ɗaya yake driving, ɗayan yana cikin nawa yana murza shi a hankali. Afnan dake baya tana lura da hakan, saidai bata ce komai ba, sai murmushi da take saki, ita dama ai ta daɗe da hango tarin Ƙaunar Suhan ɗin a idanun yayan nata, to saidai ganin bai furta ba ya sanya ta ɗauka ko haukan yarintar ta ne. Bilal ma gida ya wuce, yana mai danna ma cen ɓangaren su Ummin tashi waya domin jin ya jikin. Shaida mashi sukayi da sauƙi, har yanzu dai ba'a sauka ɗin ba. Yayi niyyar tafiya gobe da safe suka dakatar dashi da cewa jikin ai da sauƙi sosai, idan akwai buƙatar su kira shi ɗin zasu kira shi. Afnan da su khadee sashen su suka nufa kai tsaye, inda ni da Ya Ameen kuma muka shiga sashen Kaka zuwaira, domin sanar da ita halin da ake ciki. Itama tayi murna da jin jikin da sauƙi, nan ta ƙara jan hankalin mu akan mu zauna lafiya mu mugunta juna, san na tayi mana adduo'i sosai, tare da fatan samun zuria ɗayyiba. Tin a gaban kaka zuwaira ɗin ya kamo hannu na da zamu fice, daƙuwa ta Di ga dunƙula mashi, shi kau yana ta murmushi yake cewa "To kin gani dai ni ita na zaɓa, ke kuwa ki koma ma tsohon mijin ki, kinyi kwantai" ba ita ba har ni saida nayi murmushi cikin jin kunya. Haka na shiga bin shi har zuwa sahen namu. Yana buɗe ƙofar muka shiga, kawai sai Naji caraf ya ɗage ni zuwa sama ya shiga juyi dani sosai, kaman masu rawa. Dariya nake ƙyalƙyala wa cikin jin kunya da murna. Shi kanshi ya lura da yanda nake cikin annashuwa, kuma ko raba ɗayan biyu baya yi akan cewa labarin samun Rayuwar Hafsat ne da nayi. Bai dire ni ko ina ba sai saman gado. A hakan ma bai kyale ni ba, sai kawai Naji ya zare hijab ɗin yana mai bina bisa ga don ya danne, nauyin shi kaf ya sakar mani. Ni kau sai nishi nake ina mutsu mutsu. Wai dam a haka Ya Ameen ɗin yake? To menene dalilin da ya sanya da ake kiran shi miskili ne? Ganin na gaji har na fara tsuwwar wahala ne ya sanya ni ɗaga ni, yana mai gyara rigar shi ya shiga kashe mani ido ɗaya da na kula kaman al'adar shi ce ta zaulaya. Toilet ya wuce kai tsaye, yayin da ni kuma na miƙe zaune ina ta maida numfashin wahala. Ɗakin ya dawo hannun shi duk ruwa, kallon shi nake ƙasa ƙasa, sai kawai naji ya yarda mani sauran ruwan dake hannun shi. Ajiyar zuciya na sauke ina mai ɗan zabura, ba tare da wata damuwa ba ya shiga kwaɓe kayan dake jikin shi. Ganin haka na zabura zan fice zuwa falo ga sanya hannun shi suka ya maida ni kan gadon. "Ba inda zaki baby zauna nan, ni fa mijin ki ne" Abunda ya faɗa kenan, yana mai zame dogon wandon dake jikin shi, ya rage daga shi sai boxer, tunowa da nayi abunda yayi mani jiya ne ya sanya ni sauke kaina ƙasa cikin tsabar tsorata, Ganin hakan da yayi ne ya sanya shi takowa zuwa gaban gadon. Durƙusawa yayi guiwoyin shi ƙasa, ya ranƙwafo sosai ta yadda zan iya ganin shi. "Ni dake mun zama ɗaya Hayateee tin jiya, na yarda kece rabin rayuwa ta, idan babu ke bansan irin halin da zan iya shiga ba, kiyi mani alƙawarin ƙauna da kulawa fiye da yanda zan baki dear promise me" ya faɗa yana mai miƙo mani hannun shi alamun idan na yarda in kama. Kaina a ƙasa still na miƙa mashi hannun, runtse su yayi wuri guda, zan iya jiyo tashin dake shimfiɗa a tafin nashi hannun, nan ma ajiyar zuciya na sauke a hankali. Lokacin da ya miƙe zuwa zaune bisa gadon, yayi amfani da dukkanin hannayn shi wajen kwanto da kaina zuwa bisa cinyar tashi. Baya da riga, illa kwantaccen gashin ƙurjin shi da yake Zara Zara baƙi siɗik bisa murzazzar farar fatar da gani hutu ya daɗe da ratsa ta. Ru tae idanu na nayi gam, Kunyar shi nake ji har zuwa tafin ƙafar tawa, ba zan iya jurar kallon shi a haka ba, wani irin kwarjini yake yi mani, har yanzu ina iya jiyo wannan abun dake tunatas dani Ya Ameen ba sa'an aure na bane, duk kuwa da cewa yanzu na gane ko ni ɗin wacece. Hannuwa na duka ya kamo tana mai ɗora su bisa ƙurjin nashi daidai saitin zuciyar shi. Fatar hannu na, da fatar ƙurjin suka haɗu suka bani wani irin shork. Kaman yau ne rana ta farko da na fara taɓa jikin nashi. "tin ranar da na fara sonki Suhan, tin ra ar ɗana buɗi ido na ganki, nan ɗina bai dena bugawa ba, da sonki nake kwana dashi nake tashi, hankali natsuwa tarbiyyar ki, kawaici haƙuri da kuma kamala sune suka haɗu suka yi tasiri a kaina, *Ina SONKI Suhana ki daure ki soni ki ƙaunci Muhammad Al'ameen ko zai samu salama a cikin zuciyar shi* Kalaman shi sun mani nauyi, sunyi matuƙar tasiri a cikin zuciya ta, lallai dole in sauke kunya dole ne in ba mijina dukka in kulawa ta, Ya Ameen ya cencenci fiye da haka a wuri na, har ina jiyo tarin ƙaunar da nake mashi kaman tafi ma wadda yake mani. Wayar shi ce tayi ruri. Bai tashi ba ya sanya hannu ya ɗauko ta. Sunan friend ya gani yana yawo a scream ɗin. Ɗagawa yayi yana mai mamaki, duka yanzu fa suka rabu. "Bello Friend how far?" Sai kuma Naji yayi shiru, cen kuma sai Naji yace "Kai A big congrat to you Friend kace mun zama Dad, to Allah ya raya Allah ya ɗayyaba, ina maka murna, ga Wife nan ma tace ayi maka murna, sai ka shigo ɗin" yana gama faɗar haka ya datse kiran, ko bai sanar dani ba, kalaman shi sun shaida mani cewa Ummin Ya Bilal ɗince ta haihu. Da murmushi yake shaida mani. Nima cikin jin daɗi nake mashi barka, ko ba komai yau zamu kwana cikin farin ciki marasa misaltuwa. Komai yai ji shi nake daidai zam. Kalaman ya Ameen ɗinne suka saka kunya kama ni, shaida mani da yake yi cewa "Mu zamu fi su ƙoƙari Sweet heart, mu ƴan uku zaki haifa mana kinji?" ya faɗa yana mai kashe mani ido guda kaman yanda ya saba. Bansan na ru gume shi ba, na shiga cusa kaina cikin jikin nashi, shima murmushi ya saki, yana mai miƙewa a hankali ya jawo filo yayi mani matashi dashi kaman yanda nake a bisa cinyar tashi. Wanka ya shiga, ya daɗe a ciki, sannan ya fito ɗaure da towel a ƙugu. Nidai sai kallon rashin Kunyar Ya Ameen nake yi. Ikon Allah, wai ashe shi ɗin miji na ne,namiji mai kyau asali tare da cikar haiba. Katse mani tunanin yayi da cewa ga ruwan wanka na cen, bam cire kayan ba haka na tashi na nufi Toilet ɗin, da kallo ya bita, yana sakin murmushi a hankali. Kunyar ta na ƙara burge shi, ko ba komai hakan na nuna mashi cewa bata rayu da maza ba hakan ne ya sanya bata saba dasu ba. Ko da na fito wankan baya cikin ɗakin, sai nayi tunanin ko yana falo. Mai da turaruka masu taushi na shafa, haka na sake yin using wannan turaren, ba tare da na san ma wai menene amfanin shi ba. Ina zura doguwar rigar bacci iya cinya be ya shigo. Saurin ida Sanyawa nayi, ina mai juyowa ta inda yake tsaye da ƙaton tray cike da kayan ciye ciye. Takawa nayi zuwa inda yake tsaye haɗi da karɓar tray ɗin, ina mashi sannu. Cen gaban gado bisa chinese carpet na ajiye. Ina ɗagowa Najini bisa ƙurjin mutum. "Kin yi kyau Wife, dole in bada tukuicin wannan kyau ɗin." Sunsunar jiki na ya shiga yi ta ko ina yana kai hancin shi, yamutsa ni yake sosai, daƙyar na kwaci kaina ina maida numfashi, idanun shi har sun kaɗa sunyi ɗan ja, zama yayi gefen gadon shima yana mai bina da mayataccen kallo. Ganin hakan da nayi ne gabana ya shiga faɗuwa, ba dai yanda yayi mani jiya haka zai maimaita yau ba? Ai sai tsoro ya shige ni, jikina ya fara rawa, ganin hakan da yayi ne ya sanya shi sauka ƙasa yana mai faɗin "Dear yi wa nake ji sosai, serve me please" Nima haka na zauna jiki babu kwari, na shiga zuba mashi fresh milk da naman gasassun kaji da tsiren da na gani, daga gani yanzu ya fita yaje ya siyo su. Sai chips da na zuba mashi kaɗan, ni kaina yunwr nake ji, Amman kunya ba zata barni in wani ci abincin ba sosai, shi yake bani da kanshi, yayin da kaina yake bisa ƙurjin shi lafe, duk yanda naso in kwaci kaina ya hana, duk yabo ya kanainaye ni, na kasa koda kwakkwaran motsi. Da kanshi ya kashe kayan zuwa kitchen. Ya dawo ya same ni kwance bisa gado na duƙunƙune sai muzurai nake. Murmushi kawai yayi, yana mai ƙudurta cewa ba abunda zaiyi mata, ai sai kuma ta warke sosai. Saida ya kashe ko ina ya kulle. Sannan ya dawo yana mai zare jallabiyar ya rataya ta cikin sip, sannan ya zare singlet ɗin itama, ya rage daga shi sai boxer, a haka ya hauro bisa gadon ya same ni, zuciya ta kaman zata tsaho ƙirji na ta fito. Ga mamaki na, rungume ni yayi yana mai faɗa mani wasu kalamai masu nauyi da suka girmi kwalwa ta, saida ya gama yamutsa ni sosai son ranshi, sannan ya kuma rungume ji yana mai tofa mana addu'ar barci. Daren ranar dai haka nayi shi cike da jin daɗi, bacci na nake cikin natsuwa kwanciyar hankali da annashuwa, kusan ma zan iya cewa tin da uwata ta haife ni a duniya, yau ne ranar farko da nayi bacci mai daɗin wannan. Har bana so ko alama inji jiki na zai rabu da nashi jikin da nake iya jiyo wani irin ɗumi da ƙamshi mai daɗi yana tasowa daga cikin fatar tashi...... °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'ar Kin shu'umci اَللَّهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلاَّ طَيْرُكَ، وَلاَ خَيْرَ إِلاَّ خَيْرُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ. Allahumma la tayra illa tayruk, wala khayra illa khayruk, wala ilaha ghayruk. Ya Allah! Babu shu'umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~67~* *Congatulation Sis Batula na kammala littafin ki _Ni da Malama ta_ Allah ubangiji yasa an kammala a sa'a. Saƙon da yake ciki muna fatan ya amfanar, kura kuran dake ciki kuma Allah ya yafe mana baki ɗaya. Allah ya baki ikon fara wani a sa'a. Ya kuma baki ikon rubuta mai amfani Batula. Ina yinki Over, ke da ɗaukacin Sisters na Golden Pen, Allah ya ƙara haɗa kawunan mu, ya tsole idanun maƙiya a kanmu. Ya ɗaukaka mu ya bamu ikon rubuta abu mai amfani, ba abunda zuciyar mu ta raya mana ba, wanda zai sanadin ɓata tarbiyyar wasu. Ameen Thumma Ameen* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Haka muka kwana tare dashi yana nuna mani zallar ƙauna, duk da babu Abunda yayi mani, Amman hakan bai hana shi yamutsa ni ba, son ran shi. Kunya yake sakar mani, hakan ce ta sanya saidai in sun ne kaina cikin jikin nashi, inda wata irin wutar ƙaunar junan mu ke ruruwa a zukatan namu. Godiya ga Allah na sha ta kuwa, saboda sai yanzun ne nake gane cewa ashe Abunda Ya Ameen ɗin yayi mani ba'a kiran shi da komai sai ƙauna. Nayi imani da irin son da take mani, ko kwayar idanun shi na kalla ina iya hango tsantsar ƙaunar tawa tana yawo. Shi yayi mana komai da safe, ko abincin cikin gida bai jira aka kawo mana ba, shi ya shiga kitchen da kanshi ya sama mana Abunda zamu ci, sannan ya koma bedroom ɗin yana mai taso ni bayan ya haɗa mani ruwan wanka. Komai yake cikin natsuwa da aji yake yi, Ya Ameen daban yake a ko yaushe ba zan gaji da faɗa ba, saidai har yanzu zan iya hango jini na miskilanci yana yawo a cikin jinin jikin sa. Domin idan yana abu shi kaɗai, sai kaga kaman bai taɓa rayuwa da wani ba a rayuwar shi, saidai in ya tuno some moment ya kan saki murmushi sosai. Nayi mamakin dana fito daga wankan na tadda ya ajiye mani kayan da zan saka, oho, kenan shi ne ya zaɓa mani da kanshi. Yana zaune bakin gadon da system a gaban shi, hannun shi riƙe da waya yana amsa kiran Bilal da yake sanar mashi shi fa yanzu jirgin nasu zai ɗaga, zai je ya duba mai jego ne da baby Boy ɗin da aka haifa mashi. Jikin nashi sanye da baƙar body hug wadda ta dace da kalar fatar jikin nashi.sai dogon wando har ƙasa na blue ɗin jeans. Ƙafar shi ba takalmi saidai baƙar safa. Yayi masifar kyau, ga gashin nan nashi da yasha gyara yayi kwance luf abun shi sai sheƙi da salƙi yake yi. A hankali na kai zaune bisa stool ɗin ina mai idasa goge kaina dana wanke da wani irin shampoo mai ƙanshi da ni ban ma taɓa ganin shi ba. Lokaci guda ina mai satar kallon shi ta ƙasa ƙasa, domin yayi mani masifar kyau. Peck naji an kai mani ta side ɗin kumatu na nadama. Da mamaki cike da kunya na ɗan waiwaya ina kallon shi cikin ido, sai kuma na sauke kaina ƙasa ina mai sakin wani irin ƙayataccen murmushi. Bansan lokacin da ya taso ba Abunda ya ƙara burge shi dani kenan, ya idasa takowa zuwa gareni yana mai datse kiran, sannan ya ɗora wayar zuwa bisa mirror ɗin a hankali. Miƙewa tsaye nayi, domin duk na takura, ina ma tunanin yanda zan iya cenza kaya, sannan in shafa mai a gaban shi. Bansan lokacin da ya zauna bisa stool ɗin da na tashi kai ba, sai ji nayi kawai ya jawo ni zuwa bisa cinyar shi. Banyi musu ba, domin ni kaina ya zuwa yanzu na tabbatar ma kaina cewa bana gajiya da shaƙar ƙamshin jikin shi mai daɗi, sannan da fatar shi mai ɗauke da wani irin sinadarin taushi. A hankali ya shiga warware mani towel ɗin da yake ɗaure a ƙirjin nawa. Saurin kai hannu nayi na kare, bai ce komai ba, sai a murmushn gefen baki daya saki, irin wanda yake yi idan abu ya burge shi. Bai nuna ma ya kula da abunda nayi ba, ya kai hannu yana mai jawo man da zan shafa ya shiga matsawa a hannu. Da kanshi ya shiga bin ko'ina na jiki na da man yana shafa mani, lokaci guda kuma yana matsa turaren jiki shima yana cakuɗawa,cikin tafukan hannun nashi masu matuƙar taushi. Kunya duk ta gama kashe ni, haka nake ta sunne kai yana bin ko ina da hannun nashi yana ɗan shasshafa wa da mammatsawa. Ganin zai kama wata tashar ya sanya ni Miƙewa da sauri na zari kayan, wuf na faɗa toilet. Miƙewa yayi yana mai sakin murmushi har fararen haƙoranshi na bayyana. Ɗan rungume hannun shi yayi yana daga tsaye, inda nabi na wuce yake kallo. sai kuma ya taka yana mai isa ga gadon ya ɗaukai system tashi da Phone tashi dake kan mirror ya fice zuwa falo. Sai da na leƙo na tabbatar baya ɗakin sannan na fito. Ina mai idasa shafar, sannan na ƙara gyaggyara ɗakin. Baisan lokacin da ya miƙe yana mai wara mani dukkanin hannun shi ba. A hankali nake takawa, cike da kwarkwasa da wata irin tafiyar da bansan lokacin da na koye ta ba,zuwa cikin ƙirjin nashi, bai wata wata ba ya maida hannun ya rungume ni tsam cikin jikin nashi, yana mai sunsunar kaina da na maƙale gashin sannan na ɗaura bandaner. Munkai minti biyu a haka muna mai amsa saƙon zukatan namu. Ƙarar kwankwaso ƙofa ne ya farkar damu daga duniyar soyayyar da muka Lula. Sai da ya kaini bisa dining ya zaunar dani sannan ya isa zuwa ga ƙofar yana mai buɗewa a hankali. Da kallo na raka shi. Hatta da tafiyar Ya Ameen abar kallo ce, ba tin yanzu na gane hakan ba. Kayan jikin shi sun amshe shi, su ne ma suka taimaka wajen fiddo da asalin kyawun halittar shi Nihal ce ɗauke da wani ƙaton kwando, daƙyar take ɗauke dashi, sai nishi take saki, da gani dai yayi mata nauyi. Fuskar shi ba wata walwala sosai yake amsa gaisuwar da tayi mashi. Ƙoƙarin shiga take ya dakatar da ita da cewa "Menene nan?" "Yaya break fast ɗinku ne, Mom ce tace a kawo maku" "Wanene ya dafa?" "Ni ce Yaya" Ɗan murmushi ya saki, yana mai gyara tsayuwar shi. "Ba zata ci wannan jagwalgwalon naki ba, ki ajiye ki shiga ki gaida ta, ki mayar da abincin na sama mana Abunda zamu ci" Cikin kwalalo idanu take kallon shi, jim kalaman da ya yaɓa mata, to saidai wargi ma wuri yakeyi. Jiki a sanyaye, zuciyar ta na azalzala tace "To yaya" tana mai ajiye basket ɗin ta raɓe shi ta shige ciki. Sakin ƙofar yayi ya biyo bayan ta, sanin ko wacece Nihal ɗin, tsaye ya tadda ta nesa kaɗan dani, tana mai cewa "Good Morning" Murmushi na saki, ina mai Miƙewa a hankali na shiga taka wa zuwa inda take. Batayi tsammani ba sai ji kawai tayi na rungumo ta zuwa jikin nawa ina mai cewa "Morning Sis Nihal ya gajiya?" ɗan sansaraƙwai tayi tana mai sakin dariyar yake. A hankali na raba jikin namu ina mai cewa "Ki zauna mana" Ya Ameen ɗinne ya katse mana maganar da cewa "No taje ta mayar da wancen abincin, zamu ci abinci ne" ya faɗa yana mai jawo mani kujera. Murmushi na saki wanda nasan sai ya tafasa mata zuciya sannan nace "Ayya Sis Nihal ai da baki wahalar da kanki ba, Yayan naki ai ya sama mana Abunda zamu ci, kinsan he's caring husband" Maganar tawa tayi mashi daɗi kuwa, hakan ya sanya shi kamo ni yana mai zaunar dani bisa kujerar, sannan shima yaja ya zauna, yana mai ce mata "ki kulle ƙofar idan kin fita" ya faɗa yana mai haɗe fuska alamun baya son wargi. Jiki a sanyaye ta juya tana mai nufar ƙofa tanayi tana waiwayen mu, har tana tuntuɓe da room Base. Shi kau Gogan har ya ja plate ya fara zuba mani abincin. Har ta fice kaman zata saka kuka, dole ne ta faɗa ma Mom Abunda ke faruwa, idan ba suyi sa'a ba wannan ƴar duniyar yarinyar zata raba su da ɗan uwan nasu, dubi fa yanda yake faɗa mata magana, wai harma da sanar da ita ba zata ci jagwalgwalo ba, kenan ma ita ce mai yin jagwalgwalon. Bata san sanda kwalla ta shiga ziraro mata ba, tayi saurin gogewa saboda wurin masu aiki duk sun fito birjik kowa na aikin gaban shi. Sannan bata son a raina ta ko misƙala zarratin Yana bani abincin yana mani fira, ba yanda banyi ba dashi ko loma ɗaya ce ya kai bakin shi Amman ya ƙiya, ni fa nayi mamakin da irin wannan ƙauna da Ya Ameen ke nuna mani, sai tarairaya ta yake yi kaman kwai, kaman wata jaririya. Wanda kuwa idan wani yaji a waje zai iya buga ƙasa yace ba Ya Ameen bane, wannan miskilin. "Bilal ya wuce yanzun nan" Ya faɗa daidai lokacin da na ɗebo abinci ina mai nufar bakin nashi. Bai musu ba ya sanya hannu ya riƙe nawa, yana mai idasa kai cokaln baki. Murmushi na saki ina mai cewa "Ah su Dad Bilal sarkin azarɓaɓi, kenan har ya wuce, to Allah ya raya, ina son a bani number ɗin Ummin ma inyi mata barka kafin muje" Ɗan haɗe fuska yayi kaɗan yana mai kallo na cikin ido "Kije ina?" ya tambaye ni sound so serious. "cen ƙasar mana dear, ko ba zanje ba?" gyaɗa kai ya shiga yi, sannan yace "thanks God tinda gashi kin ba kanki amsa. Duka kwanan ki nawa sweet heart?" A hankali na ajiye cokali ina mai sauke kaina ƙasa. Sai kuma na ɗago ina mai sakin fuska ta. "Shikenan Dear, Allah ya bata lafiya, idan ta dawo naje, Amman please ka sanya a turo mana pic ɗin baby" ɗan murmushi ya sake saki "Done Baby, zaki ganshi yau kuwa insha Allah" ya faɗa yana mai zaro tissue ya goge bakin shi, sannan ya miƙe yana mai ranƙwafowa ya sakar mani side peck. "Take care baby, zanje hospital wajen Hafsat" Nima Miƙewa nayi ina mai ce mashi "Ba tare zamu je ba baby?" ɗan dakata wa yayi daga niyyar wucewa da yayi, sai kuma ya juyo yana kallo na. "Ya Salam Suhan, yaushe duka yau kwanan ki uku fa, jiya ma ai bansan zaki fitan ba, kinga tinda ta samu sauƙi ko me kenan idan na isa zan kira ki video sai kiga jikin nata, baby ɗinma zan sake ɗauko maki pic ɗin nata ki sake ganin ta da kyau" ya faɗa a tausashe, jin hakan da nayi ya sanya ni matsawa kusa dashi sosai, ina mai ɗan ɗaga ƙafa ta nima na mayar mashi da peck ɗin, sannan nace "OK dear a dawo lafiya, a gaida masu jikin, sannan na manta in sanar maka su khadeeja yau ne zasu koma school fa" Da dukkanin hannuwan shi yayi using wajen Kamo ƙugu na, "Thanks for your understanding baby, akwai kuɗi cikin drower, ki sallame su baby, ba zan samu ganin su ba, may be kafin in dawo sun wuce, ki gaishe mani dasu please" Har bakin ƙofa na raka shi ina mai mashi a dawo lafiya, cikin salo da kwarkwasa, wadda ta tafi da imanin shi har yana tuƙi yana sakin murmushi a hankali a hankali, bayan ya shiga sashen Mom ɗin tashi ya gaishe ta. Dayake tin da safe ta dawo gidan saboda sauran baƙi da ƴan uwanta dake cikin gidan. Komawa nayi bakin taga na tsaye, duka hannaye na a rungume. Abubuwa da dama ne ke kai komo a zuciyar tawa, oh ni Suhan yau gani a gidan Alhaji Almustapha Dambulan, a matsayin surukar shi, surukar Mom sannan mata Ga Muhammad Al'ameen Almustapha Dambulan. Rayuwa kenan, Allah mai juya al'amura, a hankali na maida kallo na kan sashen Umma da yake kulle, nan shine inda Ummata zata rayuwa har ƙarshen Rayuwar tata a matsayin matar gidan, kallo na ma ɗauke ina mai maida shi kan hanyar da zata sada ni da sashen namu na masu aiki ada. Ƙure ta da idanu nayi ina mai sakin ɗan murmushi, sai naji ina mai son ziyartar wajen domin ganin yanda ya koma, ko su wanene kuma yanzu a ciki ɗakin namu ni da Umma ta? Ma'aikata kowa sai aikin gaban shi yake yi, gidan ya wani cenza, kullum sake sabunta shi akeyi, ga wasu kayan gyara da ake daɗa sassanyawa. Hango zugar ƴan mata na nayi suna mai nufo sashen nawa. Ƙure Khadee da idanu nayi, har yanzu jikin ta a sanyaye yake, yau gata a gidan su Dambulan ɗin, wanda ko a mafarki bata taɓa tunani ba, saidai ba'a matsayin ta na matar gida ba, a matsayin ta na Ƙawar matar gida. A haka suka iso bakin ƙofar ɗakin, ko kafin su kwankwaso na buɗe masu, ina mai maƙalƙake raihana, haɗi da sakin uhun murnar ganin su. Toshe mani baki sukayi suma suna dariya, raihanan ce mai cewa "hala dai kin manta ke ɗin amarya ce, ko har yanzu ba'a girma bane?" Ta faɗa cikin zaulaya. Harda Afnan suke, dan haka na janye su zuwa cikin falon.abincin da ya ragu nake ƙoƙarin sauko masu dashi ƙasa, suka dakatar dani tare da sanar dani sunci abinci. Afnan ce ta toshe baki tana mai cewa "Aikau yau kunci daɗi, dan abincin su Aunt Nihal ba kaman shi a daɗi nan gidan, wai dan ma ba ita kaɗai tayi ba, har Su Aunt Feena saida suka sanya masu hannu" Da harara nake kallon ta ta wasa, domin nasan sharri ne take ma Nihal ɗin da take a yayar ta. Nan muka taɓa fira, har na miƙe na ɗauki masu kuɗi masu yawa cikin kuɗin da suke ajiye cikin locker ɗin da bansan lokacin da ya zuba su ba, na dai ga suna da yawa sosai. Godiya suka shiga yi, suna kai tambayar ango, nake shaida masu ya fice zuwa asibiti gano jikin Hafsat. Saida suka sanar dani ai Afnan zata raka su su sake ganin jikin nata kafin su wuce. Bansan dalili ba sai Naji banji daɗi ba, naso su wuce, domin ya zuwa yanzu fa wlh na fara jin kishin Ya Ameen a cikin zuciyar tawa, Sam bana ma ko son su haɗu da khadeejan, Shiyasa ma ko da ya faɗa man ba zasu haɗu ba, banji komai ba. Afnan ce ta katse mana firar da cewa "amm Aunty Suhameen please nace wannan yayan naku faaa." Ɗan ƙanƙance idanu nayi ina kallon ta, sai kuma nace "Yayan mu da, Afnan wane yayan kenan?" Raihana ɗince tayi hanzarin tarar numfashi na da cewa "Sir Salim mana, ai jiya kwana mukayi ana mana firar shi, ke har waya fa naji suna yi" murmushi na saki mai sauti. Ina mai cewa "Ah ƙanwata, har ƙwallo ta faɗa cikin raga kenan?" Rufe gefen fuskar ta tayi wai ita kunya, sai kuma ta buɗe da sauri tana mai cewa "Ah dama cewa nayi Ammin shi da ƙanwar shi naga suna da kirki, Asiyar ma fa har kira na tayi jiya tana mani ban gajiya, while nice ma ya kamata inyi mata" Cinyar ta na dafa ina mai ce mata "Kinga Afnan, Sir Salim is a nice man, na maki sha'awar shi, and AMMIN shi bata da wata matsalar kome, idan har kun daidaita kanku, babu Abunda zance sai Allah ya sanya alkhairi, ki bari hidimar bikin nan ta kwaranye zan ma Umma magana, and shi ba Yayana bane ba ma, Uncle ɗina ne. Saidai ina fatan dai kinsan yana da mata ɗaya da yara biyu. U deserved each other Afnan Congratulation" Sai kuma maganar tawa ta bata kunya, ta shiga rufe fuska tana kyalkyala dariya. Afnan yarinya ce mai hankali da kunya, na tabbata zata iya daure duk wata matsala da zata iya samu da Ma'u, tinda har tana son Sir Salim ɗin. Basu wani daɗe ba suka miƙe, gami da yi mani sallama. Har bakin ƙofa na raka su, tinda ba zan iya fita ba a yanzu. Afnan ce ke sanar dani cewa Mudi driver ne zai je ya kaisu asibitin daga nan su wuce inda zasu hau mota. Sashen ya rage tsit, sai ni ɗaya, saidai waɗanda idan zasu wuce su sake biyo wa suga amarya, inda nake zaune cen ƙuryar ɗaki kada kuma ace nayi rashin kunya an tadda ni falo. Yinin ranar Nihal a ƙuntace tayi shi, ko da ta sanar da Aunt Feena Abunda Yayan nasu yayi mata, dariya ta dinga yi mata tana mai ce mata indai bata son ta dinga kwasar wannan haushin to lallai saidai ta laluba Nureen domin yazo a gyara auren nan nata, Amman idan ba haka ba, wlh ta bani da Al' Ameen a cikin gidan, masalan ma yanzu da gidan yake zaune dindindin. Butsu Butsu ya kan kira ni a waya, yana mai bani haƙuri wai yasan gidan da mata, Shiyasa bai dawo ba, Amman soon zan ganshi insha Allahu. Addu'a nayi mashi ina mai tuna mashi da alƙawari na na kira mun Hafsat, ce mani yayi in bari yayi alƙawarn da marece idan ya koma ba zai manta ba. ******** Kwance yake shame shame bisa gadon, ɗakin yayi ƙura matuƙa, Amman gajiyar da ya kwaso sai bata bar shi ya ko iya kakkaɓe gadon ba, hakanan ya raɓa ya kwanta. Cen cikin bacci yaji ana ta daga mashi tsawa, a hankali ya buɗe idon nashi yana mai ɗora su saman fuskar ta. "Ma'u" Ya furta a hankali. Sai kuma ya tashi zaune, jikin shi Sam babu ƙarfi ko kuzari duk ya bi ya gaji. "Salim ka tashi magana zamuyi dakai, wacece wannan yarinyar da naga kana kallo a cikin video ɗin bikin nan? Kuma naga kaine ka kai ta wajen dinner ɗin, sannan na ganku tare da ita" Ta faɗa muryar ta a sama, ta fanni guda kuma hannun ta ɗauke da ludayin miya sai yayyarfa shi take yi cikin ɗakin. A hankali ya sanya hannu yana mai kare fuskar shi, gudun kada ta watso mashi man miya. "Ma'u wace yarinya kenan kike nufi haka?" shima ya faɗa yana mai miƙewa tsaye. "Ban sani ba Abban Eesher, kana nufin ka ce mani baka gane me nake nufi ba? To kalli nan" ta faɗa tana mai haska mashi fuskar wayar shi dake hannun ta. Photon Afnan ne tsaye tana murmushi cikin garden ɗin gidan su. "Eh na gani menene kuma?" "So nake nasan ita ɗin wacece?" "Afnan" ya bata amsa kai tsaye. Ya fara gajiya da halin ma'u, ko ba komai shima lokaci yayi da ya kamata ya nuna mata cewa shine ke auren ta fa, ba ita ce ke auren shi ba, kuma ko ba komai shine namiji, shine sama da ita. "Oho koma wacece, ba sunan ta nake son ji ba,tinda an riga an sanar dani sunan nata. menene alaƙar ka da ita?" "Ƙanwar Al'ameen mijin Suhan, kuma ita ce wadda nake so yanzu zan aura, su wanda suka sanar dake sunan basu sanar maki da alaƙar tamu ba?" Sai kuma ta saki shewa tana kai bubbuga baki "ehooo ka daiji kunya wallahi, watau ka bibiyi ita Suhan ɗin ka gane ba ajinka bace, yaudarar ka kawai tayi, tuni tana da wanda ya fika, shine yanzu ka koma ma wata cen wai ita ƙanwar shi, to wallahi ka sani, kayi kaɗan Abban Essher, wlh mu zuba mu gani cikin gidan nan shelege ka fasa ɗan halak sai yanka" Da idanu kawai yake binta, jin Abunda ta faɗa ne ya shiga gyara tsayuwar shi yana mai faɗin "To wanene shegen Ma'u? Ina ce dai ba dani kike ba? Ki shiga hankalin ki wlh kada ki kuskura ki kai ni ƙarshe, don zan saɓa maki ne, dama Ammi ce ke dakatar dani daga yi maki wasu abubuwan, to yanzu ko sani ma ba zata yi ba, sai na aikata sannan taji labari, Haba na gaji hakanan, ki rabu dani in sarara mana Ma'u, yanzu don Allah dubeki, yanzu ƙarfe kusan biyar Amman har yanzu kayan bacci ne jikin ki, kanki ba ko ɗan kwali, dubi ɗakin mijin ki? Yanzu tsakani da Allah sai kuma kice in zauna dake ke kaɗai a haka? Da yarinta ta da ƙuruciya ta?" " Oho maka ka auro ɗari ma in zaka iya, Amman wlh ka sani ka siya tashin hankali da tijara da kuɗin ka, shanyayye kawai , komai kace Ammi, eh ita Ammi ai dangin mijin ta basu sako ta gaba ba, shine take neman ni ta sako ni gaba ta shiga rayuwa ta da ƙudundune, dama nasan duk Abunda kake yi wlh ita ce ke zuga ka. Amman ka sani....... " kalaman ta ne suka maƙake jin gaggauran marin da ya sake nata a fuska tafi biyu. Ba arzuƙi ta idasa maƙale sauran kalaman bakin nata. Sai kuma ta durƙushe tana mai sakin kuka, inda ta saki ludayin miyar saman gadon. Girgiza kanshi kawai yayi yana mai zarrar rigar shi ya sanya ya bar mata gidan. Kai tsaye gidan Ammi ya nufa, ɗakin da yake mallakn shi tuni shi ya shiga, ruwan sanyi kawai ya sakar ma kanshi, yana mai fitowa ya zura Jallabiya, sannan ya nufi sashen Ammin. Kafin ya idasa shiga wayar shi da ya fizge hannun Ma'u ta ɗauki ruri. Sunan Afnan ya gani jikin wayar yana yawo. Dakatawa yayi daga shiga, inda ya samu wata kujerar rober inda malamin su Esher yake zama in zai masu lesson Waya yake yi da ita cikin kwanciyar hankali da annashuwa, kafin kace me ta matar dashi damuwar shi, inda take labarta mashi haihuwa biyu da akayi masu masu muhimmanci. Yana cikin wayar da ita ne yaran nashi suka dawo daga islamiyya. Nan ya haɗa ta dasu cikin waya suna ta mata soki burutsu, daga ƙarshe ya ɗauki excuse nata akan zai shiga ya gana da Ammin shi, inda take bashi sallahun gaisuwa. Koda suka shiga yaran ne suka fara labarta ma Ammin labarin New aunty ɗinsu. Da kallon tuhuma Ammin ke bin yaron nata. Baiyi ƙasa guiwa ba, wajen fesa ma Ammi tsakanin shi da Afnan ɗin, taji daɗi matuƙa, ko ba komai ta tabbata samun suriki daga tsatsn Alhaji Mustapha abun alfahari ne, kuma ko ba komai tin wajen bikin ta kula da hankali da natsuwar yarinya, kuma dama tayi ma Salim sha'awar ta, to saidai rashin sanin takamaimai ko tana da tsayayye ya sanya ta share. Kuma bata da ra'ayin nema ma Salim aure, tafi son ya gani da kanshi yace yana so sannan Cikin jin daɗi take gyaɗa mashi kai, daga baya ta bishi da addu'ar nasara da dacewa, sannan ta sanar mashi zata smau Umman Suhan da maganar kafin ta koma, saidai tana mai roƙon shi da ya dakata har sai an warware wata dambarwa da take neman kunno kai ga zuri'ar tata. Ta kula yana cikin wani yanayi, auren yake so ruwa a jallo. To saidai shi komai ɗan a hankali ne, har kullum tana ma yaron nata addu'ar zaɓin alkhairi a Rayuwar shi, da kuma tsaro da kariya daga wajen mahaliccinmu baki ɗaya. Nan ya kai har dare suna ta wasanni da yaran nashi, Abunda ke ƙara ɗebe masu kewa kenan, har zuwa lokacin da Abban nashi ya dawo. Sun daɗe suna tattauna abubuwa masu mihimmanci, kafin daga bisani yayi masu sallama yana mai nufar gidan nashi zuciyar shi cike da ɗarɗar da zullumi. Kaman yanda ya tsammata haka ya taras, maimakon gyara ɗakin, sai a idasa tarwatsa shi da tayi, duk ta barbazo mashi da kaya masu amfani ta farfasa mashi bed lamp da sauran kwayayen dake cikin ɗakin nashi. Kayan shi masu muhimmanci duk tabi ta yayyaga su. Gefen gadon ya zauna yana mai dafe kai. MA'U kenan, shi ya rasa me ke damun ma'u, Sam bata cencenci irin matar da ya dace ya zauna da ita ba. Miƙe wa yayi a hankali yana mai lelleƙa sauran ɗakunan, duk bata nan, kuma suma duk tayi mashi ɓannar da tasan sai ya kashe kuɗi sosai kafin ya samu ya gyara. Ɗakin nashi ya koma yana mai girgiza kai, watau bata gidan ma kenan, saboda ta zagar Mashi ammi ya mare ta shine tayi yaji. Ko ma menene kanta tayi mawa, aure dai sai ya ƙara, bai ga abun zama da ita ba, tana kuɗɗar mace. Saida ya gyara ɗakin sosai sannan ya samu ya iya kwanciya. Ya daɗe yana juye juye, sai daga bisani ne ya kira Afnan, inda ya ɗan samu sauƙi, daren dai da ƙyar ya samu bacci yayi awon gaba dashi, shima ɗin dan dai ɓarawo ne. ******* Ya Ameen ya kira ni video, inda na ga jikin Hafsat yayi sauƙi sosai, har ma tana iya dariya, ga babyn ta rungume a hannun ta tana bata nono. Abun sai yayi mani daɗi ya ƙayatar dani kuma, Allah ya sani ina son Hafsat, ko ba komai yanayin yanda take ƙauna ta itama ba duka kowa ba, bayan mun gama ne Ya Ameen ɗin ya amsa yana mai ficewa mota ya koma ya zauna, yana mai sanar dani cewa wai gashi nan tafe gidan, me na tanadar mashi. Kai tsaye nace "soyayya ta My hubby, bayan ita ko kana neman wani abu ne bayan ita?" shima murmushi ya saki yana mai ce mani "Promise?" ɗan sadda kaina nayi ƙasa ina mai cewa "Yeah promise dear" "Me zan taho maki dashi?" "Anything dear Janam" saida ya ɗan ƙura mani idanu, jin na kira shi da sunan da shima yake kira na. "Kisha kurumin ki, abu mai daɗi zan taho maki dashi, har sai kin manta kanki, zan kawo maki sweet heart" Ɗan waro idanu nayi, "Dear in manta kaina fa kace? As how?". Saida ya kashe mani ido ɗaya , sannan ya juya fuskar wayar zuwa wani wuri yana mai kai hannu da niyyar shafawa, ai ganin inda ya dosa ne ya sanya ni saurin datse kiran, ina mai kyalkyala dariya. Hoo Ya Ameen wai ina yake kai Kunyar shi ne irin haka? Wallahi idan wani a waje ka faɗamawa ba zai ce Ya Ameen zai iya aikata hakan ba. Duk da na kashe wayar kunya bata barni ba, ina kallon kiran shi na kasa ɗagawa, sai kuma jikina yayi sanyi, kenan yana nufin yau ba zai barni in zauna lafiya ba? Shima ta cen ɓangaren shi, dariyar ya saki yana mai cewa "Baby magana zakiyi" sai kuma ya saki murmushi mai burgewa, yana mai tada motar ya nufo gidan kai tsaye..... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'ar Shiga Wata Karkara ko Wani Gari أَللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ وَمَا أَظْلَلَنَ، وَرَبَّ اْلأَرَاضِينَ السَّبْعِ وَمَا أقْلَلْنَ، وَرَبَّ الشَّيَاطِينِ وَمَا أَضْلَلْنَ، وَرَبَّ الرِّيَاحِ وَمَا ذَرَيْنَ، أَسْأَلُكَ خَيْرَ هَذِهِ الْقَرْيَةِ وَخَيْرَ أَهْلِهَا، وَخَيْرَ مَا فِيهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهاَ وَشَرِّ أَهْلِهَا، وَشَرِّ مَا فِيهَا. Allahumma rabbas-samawatis-sab'i wama azlaln, warabbal-aradeenas-sab'i wama aklaln, warabbash-shayateeni wama adlaln, warabbar-riyahi wama zarayn, as-aluka khayra hathihil-qaryah, wakhayra ahlilha wakhayra ma feeha, wa-a'oozu bika min sharriha washarri ahliha, washarri ma feeha. Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai da abin da suka rufe, kuma Ubangijin kassai bakwai da abin da suke duake da shi, kuma Ubangijin shaidanu da wadanda suka batar, kuma Ubangijin iska da abin da ta yayyada! Ina rokon Ka alherin wannan alkarya, da alherin mutanen da ke cikinta, da alherin abin da ke cikinta. Kuma ina neman tsari da Kai daga sharrinta, da sharrin mutanenta, da sharrin abin da ke cikinta. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page sadaukarwa ga duk masoyan Oum-Deedat. Na gode da adduo'i, da waɗanda suka iso gareni da wanda ma ban sansu ba, Oum-Deedat tace tana amsawa, kuma tace Ameen, sannan tace Allah ya bar ƙauna da zumunci. Jiki yayi sauƙi sai ƙarashe. Saboda jin daɗin adduo'in ne ma ya sanya na ƙoƙarta na baku wannan Page ɗin, gashi nan kuyi dumu dumu a cikin sa Nogede Allah yabar zaman amana* *Page ~68~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Bai iso gidan ba, saida ya biya ta wani babban super market yayo mana siyayya sosai. Har ƙofar part ɗin namu yayi parking, dirin mota kawai naji na miƙe daga zaunen da nake da littafin ishmawi a hannu na, wanda nake karantawa, ina mai ƙara missing Ummata, domin ita ce mai ƙara mani karatun a koda yaushe. Ni na buɗe mashi ƙofar da yake ta faman kiciniya da ledojin dake hannun shi. Yana shigowa kuwa ya dire ledojin yana mai cafe ni ya fara juyi dani. Ɗage ƙafa ta nayi ina mai wara hannuwa na nake kyalkyala dariya cikin sauƙin soyayya. Direni yayi yana mai tallafo kaina da dukkan hannuwan shi. "Sweet Heart ya gidan ya kaɗaici?" Murmushi nayi ina mai cewa "Dear ina tare da tunanin ka a zuciya bana tare da kaɗaici" shima murmushin ya mayar mani, yana mai shafo gefen fuska ta. Yake cewa "I missed u aloot wify, muje mu jera kayan nan ko?, sai kiga abubuwan da za'a sake nemowa" "Done dear" Abunda na faɗa kenan, ina mai sunkuyawa na sunkuci wasu ledojin, yayin da shima ya kwashi wasu a hannun shi. Ina gaba yana biye dani a baya har zuwa cikin kitchen ɗin. Nayi mamakin yanda akayi har ya iya wannan soyayyar kaman mace, duk abubuwan da yasan za'a buƙata ya siyo shi saidai Abunda babu. Hatta da kaji da dangin su kifi da jan nama, wanda akayi packaging nashi cikin farar santana, saida ya siyo. Shi ne ya koma motar yana kwaso sauran kayan ina jera su inda ya dace. Hatta da lemuna wanda ma ban taɓa gani ba, duk da dai dama akwai wasu a cikin fridge ɗin dana tadda. Muna gamawa ya kamo hannuwa na zuwa falo. Saman cinyar shi yake ƙoƙarin zaunar dani na ƙiya, ina mai sulalewa ƙasa na shiga zare mashi takalman da safar. Sai kuma na kwashe su zan wuce dasu ma'ajin su a bedroom. Caraf Naji ya sake ɗauke nj, ga alamu dai Ya Ameen yana jin ƙarfi a jikin shi, in ba haka ba, duk da nake ba siririya ba, hakan baisa yaji wahalar ɗaga ni. Har cikin bedroom ɗin ya ajiye ni jikin shoes rag ɗin. Da kanshi ya zari takalman yana mai jawo rag ɗin ya saka su ciki ya maida ya rufe. Sai kuma naji ya shiga jana zuwa bakin gadon. Zama yayi yana mai langwaɓe kai. "Sauran kayan baby" ɗan waro idanu nayi. Kayan ma nice zan cire mashi? Langwaɓe kai ya kuma yi, yana mai yamutsa fuska wai shi nan shagwaɓa. Kallon shi kawai nakeyi, mamaki nake cikin zuciya ta, anya kuwa ya Ameen ne? A hankali na duƙa ina mai tallafo fuskar shi da tafukan hannayn nawa, wani irin abu na fizga ta zuwa gareshi, gani nake kaman almara, wai Ya Ameen ne nan zaune gabana yana zuba mani shagwaɓa, ya ajiye girman kan, sarautar, kuɗi da izzar. "Dear ya gajiya?" Abunda na samu kaina da cewa kenan. "Akwai ta kam wify, ina son massage please" Gyaɗa mashi kai nayi, ina mai zare hannun daga fuskar tashi zuwa ƙirjin shi na shiga ɓalle mashi maɓallan rigar. Sannan ya ɗaga hannun na shiga zare mashi bady Hug ɗin. Kwantawa yayi plat, ƙafafn shi na ƙasa, na haye bisa gadon na fara mammatsa mashi jikin kanshi na bisa cinya ta. Lumshe idanu yake cikin wani irin yanayi. Har barci ya fara fizgar shi, gashi kuma ga alama yana buƙatar watsa ruwa. A hankali na shiga sauke kanshi saman fillow ɗin dana jawo. Yana ji na baiyi yunƙurin hana ni ba. Saidai murmushi da yake saki. Har na idasa sauka na nufi hanyar toilet. Sai da na haɗa ruwan sannan na dawo ina mai tada shi a hankali. Fizgata yayi na faɗa bisa gadon, inda ya birki ta ni zuwa ƙasa ya shiga nuna mani ƙauna. Daƙyar na kwaci kaina ina mai maida numfashi. Shima a hankali ya miƙe, yana mai cusa hannayn shi cikin sumar dake kwance luf saman kanshi, har yanzu idanun shi a lumshe suke. Ganin ya fara ƙoƙarin zame dogon wandon ne ya sanya ni saurin ficewa. Cikin abubuwan daya shigo dasu masu sauƙin sarrafawa na ɗauko gami da sama mashi abu mai sauƙi da nasan ba zai ƙi ci ba. Ya daɗe yana cuɗa jikin shi, da yake jin ƙamshin ruwan daban. Ga alamu ta zuba turarukan wanka da baisan da irin su ba. Ina kitchen har ya fito ya dawo ɗakin, saida ya gama muttsuka mai mai sauƙin zafi, sannan ya zuro gajeren wando mai ruwan na sojoji, sai amless fara mara nauyi sosai. Fitowar shi tayi daidai da gama ɗora abincin bisa dining. Tsaye nayi ina mai ƙare mashi kallo, cikin jin nauyi. Ya kula da hakan. Shiyasa ya nufi inda nake direct, yana kai cewa "Wife Sannu da aiki, me kike haka naji ki shiru, ina cen ina ta jiran kizo ki cuɗa ni" ya faɗa yana mai kashe ido ɗaya. Sauke kaina ƙasa nayi ina mai cewa "Yaya abinci na sama maka, nasan maybe baka ci komai ba" "Kaman kuwa kin sani, sauko mani dashi ƙasa, zanfi jin daɗin zama, u know i missed your food sosai" Sai ma ya bani kunya, mutumen da ina kallon shi ko abincin na girka bai cika ci ba sosai, yafi cin na Umma ko da cen ma. Tsakiyar falon na jera mashi abincin inda yake zaune da remote na Ac yana daidaita sanyin. Sai da na kammala ajiye mashi komai na zuba mashi sannan nima na koma gefe inda zai iya gani na na zauna. Ƙura mani idanu yayi. "ba zan iya ci da kaina ba fa" ya faɗa still yana wani lanƙwashe wuya irin na ɗazu. Dariya ma ya bani, murmusawa nayi ina mai cewa "Baby as u wish" Ba musu ya shiga amsar abincin da nake bashi a baki har ya ƙoshi, yaci abincin sosai har ya fara bani tausayi, ganin yanda yaji yunwa har haka. Shima haka ya shiga cida ni bayan na gama bashi, cikin kunya nake amsa. Har muka kammala cin abincin. Miƙewa yayi yana mai nufar ɗaki ya ɗauko wayar shi da system tashi. Sai da ya daidaita zaman shi bisa sofa, sannan ya jawo ni kusa dashi, ban musu ba na lafe, dama kuma na riga na maida kayan abincin kitchen. "Baby ina so ne muyi wata shawara dama, tin ɗazu sai kuma na bari mu natsu sana" Ɗan ɗago wa nayi ina mai kallon fuskar shi, bakin nan gum kaman gidan tsutsa, gashi da haske kaman ya shafa pink balm. Bance komai ba, sai natsuwa da na sake yi, bayan na maida kan nawa bisa kafaɗar shi. "Bilal nake san ba gudunmuwa, saidai nasan ba lallai ya amsa ba, shine nake so ki faɗa mani me ya kamata nayi mashi? Kinsan mun zama iyaye fa" Ina daga kwancn naji gabana ya buga dam. Yanzu ni daga aurena da ya Ameen kwana uku har na isa ya sanya ni cikin hidimar shi da Ya Bilal? "Banji kince komai ba baby" "Yaya a gani na kafi ni sanin Yaya Bilal, duk abunda ya dace dashi ka fini sani, kada in faɗi Abunda ba lallai ya so shi ba, Amman da a gani na ka bashi kuɗin kawai zaifi ko kaba Ummin, alabasshi nasan zata faɗa mashi" "Good idea Wify, Shiyasa na nemi shawarar ki, hakan za'ayi, let me check ai kaman ina da Acc number ɗinta" Ya faɗa yan mai shafo gefen fuska ta, sai kuma ya shiga katse latse, ya kuwa ci sa'a ya samu. A take ya mata trnsfer, fuskar System ɗin ya juyo mani ina mai kallo. Ina daga kwancn na waro idanu, ganin irin gudunmuwar da ya bata. Saidai sanin irin alhern Ya Ameen ɗin, sai baisa nayi mamaki ba sosai. Godiya na shiga zuba mashi kaman ni ya mawa. Saboda ba zan taɓa iya mance Alkhairin Ya Bilal ba a gare mu. Ya mayi gurbin Ya Ameen a daidai lokacin da muke da buƙatar shi, ya ƙaunace mu, ya kuma so mu ya tausaya mana fiye da tunanin wani. Yaji daɗi, inda ya rufe laptop ɗin yana mai zamewa shima ya kishingiɗa. Har yanzu ina bisa kafaɗar shi koma ƙirjin shi zance. Da gashin kaina yake wasa yana mai shafawa da yamutsa wa a hankali. Sanar mani ya shiga yi da daddare in shirya zamu shiga sashen Mom da su kaka Zuwaira. Naji daɗi, ko ba komai zan ɗan miƙe ƙafa, saidai gabana na yawaita faɗuwa, cin karo da Mom ɗin da zan yi. Masalan da na tuna Abunda Ya Ameen ya ma Nihal ɗazu da safe, ƙila kuma ta faɗa ma Mom ɗin. A zahiri yaga ina ta murna, sai yaji daɗi, ko ba komai hakan ya nuna mashi cewa na amshi dangin nashi da hannu bibbiyu. Bai daɗe ba aka kira sallar magrib. Miƙewa yayi cikin hanzari, yana mai ɗaura alwala, sannan ya fice jikin shi sanye da Jallabiya, yana mai cewa nima in miƙe inyi salla, duk da yasan zanyi, saidai dan sauke nauyin daya rataya akan shi wajen ganin na inganta ibadar tawa. Bai shigo gidan ba saida akayi isha'i, inda ya tsaya karatu ne, duk da mutane sun yi mamakin ganin shi wajen karatun shi da yake da amarya ƴar kwana uku, to saidai sanin wanene Al'ameen ɗin game da riƙon addinin shi ya sanya malaman basu yi mashi magana ba, kuma ko ba komai sunsan amaryar a cikin gidan su take, may be bata tare da kaɗaici ne. Ni kuma hakan ya bani damar sake gyaggyara ko ina na wanke komai na maida shi muhalln shi, na kunna burner ta ruwan turare, tini ta shiga turare ko ina da turirin ruwan ƙamshin. Baya buƙatar wanka, hakan ya sanya na fiddo mashi wasu manyan kaya, sanin cewa ya faɗaman zamu shiga wajen iyayen nashi. Ina saka kaya masu yalwa sai gashi ya shigo ɗakin, ina ƙoƙarin wucewa toilet sai Naji ya riƙo ni gam, yana mai idasa zura mani rigar da nake ta kiciniya, sannan ya rungume ni a ƙirjin shi, ya shiga zage mani zip ɗin zuwa sama. Kasaƙe nayi ina kallon shi. Hure mani idanun yayi, "Baby wannan kallon fa haka? Ko an sauya maki ni ne?" Baya naja ina mai murmusawa, na shiga taka wa ina mai nufar inda hijab ɗita take ajiye. Hijab ɗin ma shi ya amsa yana mai zura mani ita. Sai kunya nake ji. Wannan soyayya da ban taɓa tunanin irin taba, sai gashi yanzu ina samun ta daga wajen Ya Ameen ɗin da ko a mafarki ban taɓa tunanin samun shi ba. Ya kamata dai in cire wannan Kunyar da nake fama da ita, na kula ga alama zata iya kawo mani cikas, ga yan da na kula Ya Ameen baya buƙatar Kunyar a tattare dani. Nice na taimaka mashi ya sanya kayan shima. Da kaina na fesa mashi turare, ina mai zaulaya shi da saura hula. Harara wasa yake mani yana mai cewa "haka kawai kaman mai zuwa wajen surukai" Ba ce komai ba sai murmushin da nayi, i a mai dayawa acikin raina cewa "ai surukar ma tana nan dawowa. na wuce zuwa kitchen. Poil paper dana naɗe na ɗauko cikin wata farar leda mai kyau. Baisan menene ciki ba, haka miskilancn bai bari ya tambaya ba, haka ya kullo sashen muka jera cikin duhu da hasken fitilun da suka ƙawata gidan har zuwa sahen Kaka Zuwaira. Mun tadda ta cikin annashuwa sosai, wasu daga cikin jikokin ta, da dawowr su kenan daga asibiti wajen Hafsat suna ta bata labarin yanda Hafsat ɗin ke samun sauƙi sosai, da baby mai kama da Hafsat ɗin, sai murmushi take. Shigarmu ya sanya su gaishe mu, sannan suka miƙe suna mai ficewa. Da kallo na shiga binsu, ina jin gara haka a cikin zuciya ta, domin duk kansu ƴan mata ne, a yanzu kuma bana buƙatar dukkan abunda zai iya haɗa huɗɗar mijina da ƴan mata, in ka ɗauke su afnan da nasan cewa ba abunda zai iya shiga tsakanin su da miji na. Sai da muka gaishe ta cikin girmamawa, sannan ta tashi zaune tana mai amsawa, tana zaulaya ta wai kaɗaici. Nan suka shiga fira da Ya Ameen, abun gwanin burgewa, har nake jin nima ina ma ace ina da kaka irin haka, wadda zamu na yin wasa tsakanin mu. Har take faɗa mashi ta ƙagara ta koma taga tsohon mijin nata, sai kawai gashi an haihu, dan ma Hafsat ɗin na raguwa wai Shiyasa ta kasa haihuwar dakanta. YA Ameen ne ya shiga tare ma Hafsat ɗin, Nidai saidai inyi murmushi, haƙiƙa Ya Ameen na son Hafsat sosai, bansan wannan ƙauna da take tsakanin su ba, Amman zan so watarana inji ta, tinda na kula in ka ɗauke Afnan ita ce ta biyu da ya kan nuna tsantsar kulawr shi a kanta. Haka muka miƙe ina mai ajiye mata ledar da nake ta maƙalo maƙalo da ita. Godiya ta shiga zubawa kaman na bata wata duniya. Shi kanshi Ya Ameen yaji daɗin hakan duk da bai san menene a ciki ba. Haka muka fito zuwa sahen Mom inda har yanzu gabana bai bar duka ba. ********* Kai tsaye take takawa har zuwa cikin ɗakin Mama Fulanin da ya kasance bata da shamaki dashi, ba nan ba, duk wani sashe na gidan hatta da ɗakin baffan nata ba sai an nema mata iso take shiga ba. Mama Fulanin tayi mamakin ganin ta a daidai wannan lokacin da tuni sawu ya ɗauke, kowa ya nabba'a, masalan yanayin damuna da iskar hadari ta fara kaɗawa. Ba tare da ta kawo ma ranta komai ba da take kishingiɗe bisa lallausar shimfiɗr ta tana jan lazimi a hankali, idanun ta a lumshe. Kai zaune Umma tayi tana mai gaishe ta cike da girmamawa, ko ba komai ita ɗin tana mata kallo ne na mahaifiyar a gareta, duk kuwa da cewa ko kusa bata isa haihuwar Umman ba. Zaune Mama Fulanin ta tashi, tana mai sakar ma Umman tawa murmushi take ce mata "A'a Gimbiya kece tafe yanzu cikin daren nan? Allah dai yasa lafiya, ko da wani abu ne da kike buƙata ba bayi a kusa yasa kika fito da kanki?" Duk wannan tambayoyn tana yi ma Umman ne wadda ta daidaita zaman ta bisa wata shimfiɗa da take gefen tata. Girgiza mata kai Umma tayi. Itama fuskar ba yabo ba fallasa tace" Fulani barka da hutawa, Allah dai yasa ban katse maki lazimn ki ba" "Ba damuwa Hasken masarauta, ina sauraren ki, me ke tafe dake a daidai wannan lokacin?" Muskutawa Umma tayi, sannan tayi gyaran murya "Dama maganar komawa ɗaki na ne, munyi magana da shi Alhaji Mustapha yake sanar dani cewa zai zo mu wuce tare dashi, saboda mun samu ƙaruwa ɗiyar Hajiya Zainab ta haihu, kuma aiki akayi mata, shine nake so inje in ga jikin nata. saidai kafin mu wuce ɗin zai taho da abokiyar ita zaman tawa, watau surukar mai sunan mai babban ɗaki, domin masarauta ta santa, ita ɗin ma tasan masarauta. To shine bana iya yi mashi musu, nace ki sanar da mai martaba, ita waccen maganar za'a iya barin ta, idan muka samu lokaci zamu iya dawowa domin ta" Kallon ta takeyi sosai, sai kuma ta jinjina kai bayan ta tsahirta. "Kina ganin ba matsala hakan? Domin ya zuwa yanzu fa kinsan cewa idanun kowa da hankalin kowa na akan waziri, kuma ita kanta masarauta ta ƙagu taji Abunda ke wakana, tinda ya zuwa yanzu ta bayyana cewa waziri ya san komai da yake faruwa, saidai in kina ganin hakan yayi maki, ba damuwa zan samu shi mai martaba da batun, zuwa gobe insha Allahu sai asan abun yi" Itama ta faɗa da ɗan murmushi kaɗan a saman fuskar ta. Jinjina kai Umma keyi, kafin ta miƙe a hankali tana mai cewa "Shikenan sai naji daga gareki ɗin. A huta lafiya" da kallo Mama Fulanin ke binta tana mai girgiza kanta a hankali, abubuwa da dama ke kai komo a cikin ranta, tabbas Rayuwar sarauta ta wani fannin bata yi ba. Watau rayuwa ce mai cike da sarƙaƙiya, gami da cukurkuɗa, wanda idan mutum bai yi sa'a ba hakan na iya kaishi ga ma hallaka. "Allah ya bamu Alkhairin sa ya kuma tashe mu lafiya" mama Fulanin ta furta, daidai lokacin da Umman ke barin falon nata da ya gaji da haɗuwa. ********* Yanda Mom ta kama ni ta rungume, tini jiki na yahau rawa, ban saba hakan ba, ban kuma tsammaci hakan ba, shi kuwa gogan naka na gefe yaja ya tsaya, hannayen shi zube cikin aljihun dogon wandon nashi. Ba ƙaramin daɗi yaji ba, ba ƙaramin murna yayi da hakan ba, duk da har yanzu Abunda yaji daga bakin Mom ɗin tashi yana mashi kai komo, kuma yasha alwashin ɗaukar dukkanin matakin da ya dace, mom ɗince kawai yake jin zai iya ɗaga ma ƙafa, Amman ba ita ba, dukkanin wanda keda hannu cikin Abunda ya faru dashi da Suhan baya jin idan zai iya ƙyale shi. Sauran mutanen dake falon sai murmushi suke yi, rabi da kwatan su duk sun zubda makaman yaƙin su, masalan ma da suka ga uban abubuwan arziƙin da aka basu daga masarauta. Ƙoƙarin zaunar dani take yi gefen ta, na zame ƙasa na zauna fuska da idanu na duƙe ƙasa nake sakin ɗan murmushi a hankali. Addu'a suke binmu da ita, wadda tuni kaina ya kulle, anya kuwa ƴan uwan Hajiya Kubra ne hakan? Ikon Allah, son abun duniya ƙirƙiri, watau kai idan baka dashi kai da banza duk ɗaya ne. Ayan da Nasreem da suke ta wasan su gefe, Da gudu suka nufo inda nake zaune suna mai faɗa mani, Ayan ne dayake yafi Nasreem wayau sosai yake ce ma Nasreem ɗin "Laa My Lil look at my Uncle Bride. Is she beautiful?" gyaɗa kai Nasreem ɗin tayi tana mai ɗago da fuska ta wai ita ala dole sai ta ganni sosai. Kowa dariya ya sanya ganin shirmen yaran. Shi kuwa Ya Ameen da ya samu kujera mai zaman mutum ɗaya ya kame, ko dariya baya yi saidai murmushi a hankali a hankali, ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai naga ya koma mani kaman Ya Ameen ɗin da na sani da cen baya. Su Aunt Feena na asibiti ita da Afnan, basu dawo ba, hakan ta sanya sai ba wanda kusan na sani ciki. Zaune nake Amman duk a takure nake, muryar Mom ɗince ta katse mani tunanin da nake yi "Son akwai ajiya dana ba Afnan tayi maku a part ɗin naku, gifts ne da Suhana ɗin ta samu lokacin bikin naku, ka bar mata abun ta, idan da wani abu da take so tayi dasu" Gyaɗa kai ya shiga yi, ba baƙon abu bane samun kyaututtuka irin haka duk lokacin da suka yi hidima irin haka a gidan. To su ɗinma masu yi ne. Masalan Ya Ameen ɗin, tinda ita Hajiya kubran idan ta bada kusan zamu ce biki ne. Dama kusan haka hidimar manyan take. In ansan ma kai baka yi sosai, to fa ba'a sakin jiki ayi maka sosai. Ganin kaman a takure nake ne ya sanya shi cewa "Mom bari mu wuce na gaji sosai ina so in huta ne" ya faɗa yana mai miƙewa. Sai kuma na Gaza tashi, ina kallon shi yana mani kallon ki tashi ko inzo in kamo ki. Fir naƙi motsawa, su kau sai murmushi suke saki abun su. Alamun dai mun burge su. Dama Nihal tin da muka shiga ta miƙe ta nufi ɗakin ta tana zumɓura baki, Ya Ameen na kallon ta, kuma ya ƙudurce gyara mata zama acikin gidan dalilin matar tashi. Ganin ya fara takowa yana nufar inda nake zaunen, ya sanya ni nayi zumbur na miƙe ina mai zazzare idanu a ƙasa. Sai kuma ya saki murmushi yana mai dakatawa. Idanu Hajiya Kubra ta zuba mana, zuciyar ta na raya mata wannan irin ƙaunar haka yaushe ta fara? Nisawa tayi a hankali tana mai miƙewa ta haye sama. Sai naji nauyin dake wurin ya ragu.duk yanda yaso mu jera ƙiyawa nayi, saidai ya wuce gaba ina biye dashi a baya. Muna fita kuwa ya cafko hannu na gami da ɗan matsawa har saida na saki wata ƴar ƙarar shagwaɓa, ina mai ɗora kaina bisa ka faɗar shi nake diddira ƙafafu ƙasa. Sai ya biye mani yana mai saƙalo hannun shi na dama a ta bayana ya kamo ƙugu na da kyau. A haka har muka isa ga part ɗin namu. Muna gaf da shiga kuwa yaso cafe ni. Yana mai faɗin "Menene kika kaima waccen tsohuwar?" Aiko na zare hannun ina mai rugawa ciki da gudu. Shima rufa mani baya yayi, yana mai maida ƙofar ya kulle ya bini har cikin ɗakin, inda na zube bisa gadon ina maida numfashi. Maree dake tsaye bayan wata flower, tin fitowar mu a sashen namu take nan tsaye tana kallon mu. Har shigar mu wajen Kaka zuwaira, da fitowar mu zuwa part ɗin Mom ɗin. Ƙwafa tayi tana mai ayyana wani mugun ƙudiri a cikin ranta, wanda take son aiwatar da shi nan kwana kusa, bata so tayi gaggawa ne saboda bata so a gane tana da hannu a ciki. ******* Ba zan iya fasalta yanda nasha wahala ba, saidai bata kai ta Wancen karon ba gaskiya, baccin mu muka kwasa, bayan komai ya kammala yana rungume dani. Yanda ta faru jiya hakan ce ma ta kuma faruwa ayau. Saidai ba Nihal bace ta kawo abinci yau wata ƴar budurwa ce. Ganin ya tsaya yana magana da ita daga bakin ƙofa ne ya sanya ni ƙarasawa, saidai kafin in isa har ya sallame ta ya maida ƙofar ya rufe. "Zo muje sarkin kishi" ya faɗa cikin zaulaya yana mai kamo hannuwa na zuwa ga dining ɗin. "Abunda ake so, abu mai daraja shi ake kishi har a kimlace shi" Na samu kaina ina mai maida mashi amsa nima cikin shagwaɓa da salo na Abunda na faɗa har cikin zuciya ta. Lakace mani hanci yayi yana mai faɗin "Shiyasa nima nake kishin wannan abar tawa" Shagwaɓe fuska nayi "Nice ma Aba?" "Yes dear you are mu property" shima ya faɗa yana mai sagalo mani ƙugu. Ɗaf Naji ni a sama ina ta juyi. Kyalkyala dariya na shiga yi. Sai kuma Naji kaman juwa tana neman ɗiba ta. Maƙalƙale shi nayi ina mai sakin ɗan ihu kaɗan. Bisa kujera muka zube mu duka. Yana dariya yana faɗin "Waih dama haka kike da nauyi haka. Wannan ai kin kai 100kg" ina maida numfashi, har yanzu hannuwa na saƙale da wuyan shi fuskar mu Ɗaf da ta juna nake cewa "ban kaika ba ai Yaya, tinda kai kana iya ɗauka ta, ni ko bana iyawa" Dariya ya saki cikin salo na miskilanci, sannan ya shafi ɗan shaffafen ciki na yace "Amman nan zaki iya ɗaukar ƴan huɗu ko?" Bansan lokacin da na zaro idanu ba ina mai faɗin "What?" "Yep saboda nayi ajiya nan ciki kwana uku kenan" shima ya faɗa cike da tabbacin abunda ya faɗa" "You are not a doctor ai" nima na faɗa ina mai ƙoƙarin tashi zaune. Sai kuma ya sakar mani nauyin ƙirjin shi. Nishi na fara yi ina mai bashi haƙuri. "Ko shi doctor ɗin komin abun shi ai sai an yi ne zai faɗa ko? Kinga kuwa baikai wanda yayi ɗin ba sani. In kuma kina tababa ki bari in nuna maki zahiri" Tureshi nayi sosai, tsabar kunya kaman in shige ƙasa. Kai jama'a Ya Ameen na da abun mamaki, wai har yaushe ne ace kaman ya Ameen ya rutsa ni da maganganu irin haka?abun kunya. Mutumen da nake ma kallon da ko yatsa aka saka mashi a baki ba zai ciza ba. Nifa da har na fara tunanin kodai baya da lafiya ne, ganin irin yawa yawan ƴan matan dake rububin shi, Amman yana ƙinsu, ko kallo ma basu ishe shi ba. Ashe ni yake tattala ma kanshi, ashe komai ni ya tanadarmawa saboda jin daɗi na. "To Naji Naji Yaya, babies suna jin yunwa yanzu dai" nima na faɗa a hankali ina mai ɗaga hannu sama, alamun nayi giving up. "Da wuri haka? Har kin bada kai?" Shima ya faɗa yana mai ɗaga ni. Sai kuma ya kamo hannu na muka nufi wajen cin abincin. "Eh Janam ba komai dai" nima na mayar mashi cikin raha Yau dai ban bari ya bani ba a baki. Nice ma nayi ta mazar bashin. Naga kaman yana sauri ne, yanayi yana duba agogo. Yayi kyau sosai cikin suit ash colour da ƴar ciki fara ƙar, sai blue ɗin tight. Ƙafar shi sanye da takalma sau ciki, wanda duk nice na zaɓa mashi su cikin jerin kayan nashi. Bamu gama cin abincin ba, wayar shi dake bisa kujera ajiye ta ɗauki tsuwwa. Ɗan tsaki ya saki yana mai cewa "zance fa bana ma fitar, wai basu san amarya ke gareni ba?" zan miƙe in ɗauko mashi ya dakatar dani yana mai cewa "Ƙyale su mu gama dear Meeting ne kuma naga har yanzu da sauran time, gashi Bilal baya nan balle ince su fara" zama nayi ina mai kallon shi. Bai saba da hakan ba ga dukkan alamu, ina gudun ace daga yin auren shi zai fara samun matsala da ma'aikatan shi. Wayar ce ta katse mani tunani, ban jira cewar shi ba, na miƙe ina mai isa gareta da niyyar ɗaukowa. Ganin sunan Sweet Mom na yawo jiki, ya sanya ni ɗaga ƙafa da sauri ina mai isa inda yake zaune yana goge baki da tissue, idanun shi duka zube a kaina. Saida yayi mani murmushi sannan ya amsa yana mai shafo fuska ta cikin jin daɗin hakan. Bai jira komai ba shima ya ɗaga yana mai sallama. Ban iya jin Abunda Mom ɗin ta faɗa ba, sai cen kuma naga ya miƙe da sauri tana mai faɗin "Garin ya haka Mom? Yanzu ina Barrister Kabeer ɗin?"....... "OK OK am coming Now, ya jira ni ina zuwa" Cikin ɗan hanzari haka naga ya juyo zuwa gareni yana mai faɗin "Take care baby, sai na dawo" bai jira cewa ta ba, ya zari brief Case tashi dake ajiye bisa sofa a falo ya fice sauri sauri. Ba zan ita fahimtar abu guda ba, saidai na jiyo lokacin da yake faɗar "Mom why? Why? Why Mom? Baki jin shawara ne tin farko, sai da nace kada kiyi Mom" Abunda na iya ji kenan, lokacin da na bishi da ɗan sauri na ina mashi a dawo lafiya, bai iya amsa mani da komai ba, illa lakato mani hanci da yayi, yana mai manna mani Light Kiss a saman goshi ya fice. Da kallo na bishi ban rufe ƙofar ba, gabana na dukan tara tara, me ke shirin faruwa kuma? Me Mom ɗin tayi? Me ya faru? Ganin ya nufi hanyar part ɗin mom ɗin, ta sanya jikina yin sanyi, sai kuma na saki ƙofar ina mai komawa saman Sofa na zauna. Ina mai jan "La haula Wala ƙuwata illa billah"... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'ar Shiga Kasuwa لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ ولَهُ الْحَمْدُ، يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ حَيٌّ لاَ يَمُوتُ، بِيَدِهِ الْخَيْرُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. La ilaha illal-lah, wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, yuhyee wayumeetu wahuwa hayyun la yamoot, biyadihil-khayru wahuwa 'ala kulli shayin kadeer. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai; babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne (Shi kadai), kuma yabo ma nasa ne (Shi kadai); yana tayarwa yana matarwa, kuma shi ne rayayye wanda ba ya mutuwa dukkan alheri a hannunsa yake, kuma Shi Mai iko ne a kan komai. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~69~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° ...... Hannu kawai ya iya miƙa ma Barrister Kb da yake zaune shi kaɗai falon, sai Mom da take tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana ganin shigowar shi tayi saurin juyawa tana haye upstair zuwa saman ta. Bai jira komai ba shima ya mara mata baya. Ko tsakiyar falon nata na sama bata kai ba ta ja wata irin turjiya,tana mai juyowa ga Ya Ameen ɗin da yake nufar inda take. "Son kaji wata maganar banza wai? Tayaya za'a ce kuɗin da na bayar ba'a san ma hannun wanda suka nufa ba? Ba zan taɓa lamuntr wannan rainin hankalin ba wlh, Haba! Ina it cant be" ta faɗa cikin ɗaga murya sosai, fuskar nan har ta rine tayo jawur abun ka ga fara. "Mom calm down please, sit down lets talk, ki mani bayani me yake faruwa ne? Kuma yaushe kika bayar da kuɗin?" shima ya faɗa yana mai kamo hannuwan ta zuwa saman sofa. Kasa zama tayi sai da kyar. "Barrister ne yazo mani da wani zancen banza yanzu, tayaya nayi signing yayi shima kuma kuɗi sun fita a cikin account ɗina har maƙudan kuɗi irin haka miliyoyi, yanzu kuma Naji shiru ba'a sake tuntuɓata da maganar ba, shine yau sai ga Barrister ɗin zamu sake documenting ɗin komai nawa yake faɗa mani baya da record ɗin share ta" "Mom kina da shares sosai, please mom kiyi haƙuri muyi maganar nan a tsanake.wace share kike nufi?" Wani irin kallo take mashi, kaman zata make shi, sai kuma ta miƙe zufa na mai karyo mata. Shima miƙewar yayi, ba tare da yace mata komai ba ya fice yana mai gangarawa zuwa babban falon inda Barrister yake. Sake gaisawa sukayi, Ya Ameen ɗin yana mai neman kujera kusa da ta Barrister Kb ya zauna. "Barrister Mom ta kasa man bayanin takamaimai me ke faruwa, shine nace bari in same ka, ko zan iya sanin wace share take nufi?" Gyara zama Barrister yayi, yana mai gyara murya a hankali ya fara yi ma Ya Ameen bayanin me ke faruwa. "wato ranka ya daɗe, kwanaki ne lokacin kana america, Hajiya Tayi kira na zuwa Office ɗinta, to acen ne da na isa na tadda ta da wasu mutane manya suna tattaunawa, ta bani izinin in jira ta a falo. Sun daɗe suna tattaunawar kafin tayi kira na. Ina shiga ta bani wasu files tace nayi signing nasu a take. Ban ƙwauron baki ba wajen tambayar ta na menene? Kuma naga cewa kai baka nan, kuma nasan duk wani abu da yake mallakn Hajiya sai ka sanya hannu ma akai kafin ni in sanya, sai ta katse ni wajen cewa in sanya kawai shine dalilin da yasa ta kirani ba shawara ta kirani muyi ba, ganin cewa tana da gaskiya, iyaka ta documenting koda wani abu yaka taso, sai na sanya, tin a lokacin naso in kira ka, sai ta ja mani kunne akan kada in faɗa maka. Sai daga baya ne take sanar dani share ne ta zuba a kamfanin matatar man petur, to nasna dama tana da share, kuma profit nata yana shiga as normal kaman yanda ka sani, bana da masaniyar dalilin da yasa take son sake zuba maƙudan kuɗi har fiye ma da waɗancen. Ban kira ka bane saboda cika umurnin ta" Shiru ne ya biyo baya, yayin da Al'ameen ya koma a hankali yana mai jingina bayan shi jikin ma karin Sofa, jinjina kai yake yi a sannu, hannuwan shi duka suna a saman bakin shi. Ba zan iya tantance halin da yake ciki ba. Ɗagowa yayi yana mai kallon Barrister "Ehen KB ina jinka, sai kuma akayi yaya?" ya faɗa fuskar nan tashi murtuk, kaman bai taɓa dariya ba. "To ranka ya daɗe, tin kwanaki naso in same ta, akan cewa kuɗi fa sun fita tuni, Amman yanzu za'ayi wajen wata uku har yanzu ba wani labari, ba uwar kuɗin kuma ba ribar, sai ɗazun nan na same ta akan batun, shine take ta faɗa, ai tinda na sanya hannu ya kamata in dinga bibiyar al'amarin tinda ita ayyuka sunyi mata yawa..... " "Kasan mutanen ne? Ko kuwa kai ne ka kawo mata su? Kuma kuɗin zasu kai adadin million mawa? Sannan Alhaji Yasan da maganar ?" Ya Ameen ɗin ya katse Barrister ɗin. Nisawa yayi shima cike da tashin hankali "Wallahi yallaɓai ban san su ba Sam, hasali ma ranar na fara ganin su, kuma Alhaji bai san da maganar ba, tace idan ya sani ko kai ka sani ba zaku barta ba, kuma kuɗi ne masu yawa...." ya faɗa yana mai miƙa ma Al'ameen wata takarda fara ƙal mai ɗauke da signing saidai photo copy ce. Amsa Ya Ameen yayi yana mai dubawa. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, dole Mom ta girgiza, yawan kuɗin zai iya cewa sun kai rabin dukiyar da ta mallaka koma fi. "Wannan ai photo copy ce, ina original ɗin?" Ya Ameen ya maida mashi da tambaya bayan gama nazarin File ɗin. "Yallaɓai nima haka ta bani shi, tace na sanya a takardun kaɗarorinta dake hannu na" "Barrister ta yaya zakuyi agrement da mutane su baku photo copy kuma ku amsa ku bar su da original? Kaman yanzu ne kuka fara huɗɗar kasuwanci?" ya faɗa ɓacin rai bayyane a saman fuskar shi. Tini jikin Barrister ya fara ɓari "Yallaɓai ka sani, Hajiya bata bani dama ko izinin shiga wannan harkar ba sosai, hasali ma daga ranar ban kuma sanya ta a idanu na ba, saidai muyi waya. yanzu ita zamu so muji daga bakin ta su waɗannan mutanen su wanene? Saboda ina gudun ace damfara ta shiga al'amarin, kuma idan har hakan ta kasanc dole mu maka su kotu" "Bar maganar kotu tukunna dai Barrister..." ya faɗa yana mai miƙewa cikin tsananin ɓacin rai ya fara haurawa sama, matattakala uku uku yake tsallakewa, kaman guguwa sai gashi har ya isa ga bakin ƙofar. Tadda ta yayi tana ta kai komo, ta rasa inda zata zauna, hannuwan nata riƙe da wayar tata. Tana ganin shi da File a hannu ta zaburo zuwa inda yake. Kaman ba Hajiya Kubra da kuka sani ba, yau Sam babu izza ko ji dakai ko isa a tattare da ita, duk ta wani yamutse ta fita kamannin ta. "Mom bam gane wannan File ɗin ba, kiyi mani bayanin shi, yaushe kika bayar da kuɗin nan ban sani ba? Kuma su wanene kika ba?" "Son gaskiya ban sansu ba nima, Amman Alhaji Yaro ne ya haɗa ni dasu kuma shine ya zama grantor ɗin har aka kammala komai, shima kuma tin ɗazu nake kiran shi wayar tashi bata shiga Sam" "Mom Alhaji yaro fa kika ce? Yanzu Fisabilillahi Mom sau nawa Dad na faɗa maki akan ki rabu da wannan alhaji yaron? Cutar ki yake yi, damfarar ki yake yi, ke gani kike kaman saboda Allah yake tare dake, saboda matarshi na Ƙawar ki, Mom yanzu har wani ne zaki sanya ya maki grantor gani ga Dad, idan har bama nan ba zaki iya haƙuri mu dawo ba ko ki kira ni, kinsan ko daga ina nake ni mai amsa kira ki ne.... " " Dakata Al'ameen yi mani shiru dan ubanka" ta dakatar dashi cike da tsawa. "Kasan da wa kake magana kuwa? Ni kake faɗa wa haka? Na kira ka ne domin kayi mani faɗa? Kuɗi dai nawa ne, kuma na san Alhaji Yaro ba zai ci amana ta ba, ita kanta Hajiya Laila ɗin tun ɗazu nake kiran ta bata ɗaga ba, daga ƙarshe ma akace mani wayar tata kulle take..." Girgiza kai Al'ameen keyi, yana mai ƙure Mom ɗin tashi da kallo, ba zata taɓa cenzawar ba, idanun ta sun rufe, sai surfa mashi bala'i take, kaman shine ya salwantar mata da dukiya, kuma ai dole ne ta girgiza, irin wannan kuɗin ko shine ya rasa su dole ya girgiza balle ita, wadda yasan dukiyar tata bata ma kai ko rabin tashi ba. Juyawa a hankali yayi ya fara taka wa da niyyar barin falon. Dakatar dashi tayi cikin tawa "Ina kuma zaka? Nace ina zaka? Au shikenan ka kyale ni insan yadda zanyi ko? Dama nasan za'ayi haka, ta tabbata tin bataje ko ina ba, an shanye ka duka kwana huɗu da yin auren naka har ka cenza hali, ka zama gakanan dai sai Abunda mace tace maka, to kadai sani dan ubanka nice na ɗauki cikinka na haifeka, na rene ka, ba Maryama ba, dan haka dole duk wata matsala ta ka saurare ta, maganar Dad ɗinku kuma ba ruwan shi cikin wannan maganar, sanin kanka ne tin da yayi aure bai sake bani wata kulawa ko jiɓintar al'amari na ba, ka taka a hankali kada in saɓa maka. Ka jira ni in ɗauko gyale yanzun nan ka kaini gidan Hajiya Laila ɗin" Cak yake tsaye, idanun shi a kulle, maganganun Mom ɗin tashi suna ratsa mashi zuciya, cije lips nashi yayi kaman zai fasa su, hannuwan shi duka cikin gashin kanshi yana yamutsawa, bai motsa ba har saida yaji shigewar ta ɗaki. A hankali ya shiga taka wa ya gangara ya sauka. Idanun shi sun koma kaman garwashi. Me ya kawo maganar matarshi ko Umma acikin zancen nan Fisabilillahi, shi dama ya sani, baya tunanin idan har Mom ɗin tashi zata yi taubatun nasuha. Al'amarin Mom ɗin tashi yana bashi mamaki, ace bata jin shawara, bata jin bari, bata jin maganar kowa? Ba wanda ya isa yace ga yanda zata yi? Yanzu haka wannan asarar da tayi tana iya naƙalta hakan ga Suhan ko Umman. Har baisan ya isa ga kujerar da ya tashi ba. Ganin shi da Barrister ɗin yayi haka ya sanya gaban shi tsananta duka, tuni jikin shi ya ɗauki rawa, baya so ko alama wani al'amari na kuɗi ya haɗa shi da Hajiya Kubran, saida yafi kowa sanin wacece ita, tinda mahaifin shi shine ya kasance Lauyan mahaifin nata tin da daɗewa, tsufa ne da ajiye aiki ya sanya shi amsa daga inda ya tsaya. Bai ce da Barrister ɗin komai ba, ya zauna yana mai jingina kanshi ga kujerar, wani irin sa rawa yake jin kanshi na mashi, waɗannan sune ƙalubaln da yasan dole zai fuskanta ga auren nan, wannan asarar da Mom tayi sai ta shafi kowa shi ya sani, shine ma kuma kan gaba, idan ma har hakan bata taɓo da iyalin nashi ba. Yana jin wayar shi na tsuwwa alamun ana kiran shi. Da ƙyal ya ɗago wayar da idanun shi wanda yake buɗe su da kyar. Manager ɗinshi ne. Yasan zancen. A hankali ya ɗaga yana mai umurtarsu da su ɗaga Meeting ɗinnan zuwa wani lokaci. Ba tare da ya jira cewr su ba ya katse wayar, yana mai tura ta cikin aljihun cikin suit tashi. Haka Mom ɗin data yabiɗo wani gyale da zamu iya kiranshi da babu ta iso wurin. Takun tafiyar ta, daidai yake da bugawr zuciyar shi. Da sauri barrister ya miƙe, yana mai nufar ta da niyyar mata magana, da hannu ta dakatar dashi tana mai cewa "Ya isa Barrister kaje kawai sai na nemeka" jin hakan da yayi ne ya sanya shi saurin ficewa, kaman zai kifa. Ko kallon inda Al'ameen yake batayi ba, ta zagaye kujerar da yake kai tana mai ficewa. Shima ganin haka ya miƙe yana mai bin baya ta jiki a saɓule, da yana da yadda zaiyi ya ɗebe dukkan wani hali mara kyau na Mom ɗinshi ya cenza mata da yayi, da ya siya ko nawa ne, Sam halayn Mom ɗin nashi suna daga cikin Abunda ke ci mashi tuwo a ƙwarya, duk irin son da yake mata, Amman hakan baya Sanyawa yana kallon gaskiya ƙiri-ƙiri ya take ta. Motar shi suka nufa kai tsaye wadda ke ajiye gefen part ɗin namu. Da kallon wulaƙanci tabi sashn, yau fa an taɓo mom, gani take ta rasa gashi su kuma wasu a lokacin ne suka samu. Al'ameen wanda yana kallon ta ya shiga girgiza kai gami da yi ma. Motar key, ya juya mata ita daidai yanda zata iya shiga. Ni dake tsaye bakin taga gabana ya ruguje ya faɗi, ganin yanda yaja motar da matsiyacin gudu, kaman zai tashi, duk lokacin da naga yana irin wannan gudun nasan akwai wani abu a ƙasa. A hankali na sulale zuwa ƙasa saman guiwoyina. Ya Salam nake furta wa, me ke shirin faruwa ne? Fuskar Ya Ameen haka babu annashuwa ako annuri? Kai kace bai taɓa dariya ba? Kaman ba shine ɗazu muke raha da annashuwa ba? Na kai minti goma anan ban iya miƙe wa ba, ina buƙatar Umma ta a kusa dani, ina son mai share mani hawaye na, ƙalubale ne ni kaina nasan sai na fuskance shi, dama zuciya ta tana ta sanar dani cewa Mom ba don Allah take ta mani wannan rungumr ba, tabbas akwai wani abu a ƙasa. "Innalillahi" nake ta maimaitawa, Ya Allah kayi mani tsari da dukkan wani abun ƙi na fili da na ɓoye. Tin daga bakin Gate mai gadi ke sanar masu ai su Hajiyar basa nan, sun ma bar ƙasar, bai ma san ina suka tafi ba, Amman sun sanar mashi da cewa zasu daɗe dai. Shima sun sallama shi, yanzu haka shirin barin gidan yake. Kasa tada Motar yayi, yayin da ta shiga surfa bala'i tana yi tana yarfa hannuwa, ji take kaman tayi ta gaggaura ma Al'ameen ɗin mari. Gani take kaman bai damu da Abunda ya same ta ba. Da har zai iya ƙakubalantar ta. Gidan Hajiya Sa'a tace ya kai ta, ba musu ya juya kan motar, wannan shine ƙarshen mai aiki ba shawara. Ƙala bai ce mata ba, duk surfe surfen zagin cin amanar da Hajiya Laila da Alhaji Yaro sukayi mata. Bai barta ita kaɗai ta shiga gidan ba ya bita a baya. Saidai daf da zasu shiga ta juyo tana mai yi mashi wani irin kallo. Dole ya dakata daga bakin ƙofar yayin da ita kuma ta idasa shigeewa, ta sani sarai muddin ya bita zai iya hana ta Abunda tayi niyya. Zaro wayar shi yayi daga aljihu yana mai komawa mota ya kira Dad. Bugu uku ya ɗaga yana mai amsa sallamr da yayi, ko gaishe shi bai tsaya yi ba, ya shiga zayyane mashi Abunda ke faruwa, cikin matuƙar ɓacin rai Alhaji Mustapha ɗin ke ce ma Al'ameen "Bai kamata ka barta ita ɗaya ba Son, kasan zata iya aikata komai tinda ita bata jin shawara. Maza ka shiga gidan, nima ina zuwa yanzun mu haɗu gida nan ba da jimawa ba insha Allah" Bai jira komai ba ya ɓalle murfin motar ya nufi cikin gidan, saidai daf da zai shiga ne, Abunda yaji Hajiya Sa'ar na faɗama Mom ɗin tashi, shi yayi sanadiyyar kusan faɗuwr shi. Dakyal yaja ƙafa ya isa ga wata flower concrete dake ajiye ya ɗosana, yana mai dafe kanshi. "Kunya ta wuce wadda kika ji? Kina Kunyar ace surukar ki ta kasance mai aiki? Sai gashi daga yarinyar har uwar ta sun shiga gidanki sun kanƙane sunyi babakere sun maida ke ƴar kallo, duk ajin naki duk jin kan, menene nan baki sa munyi maki ba, waɗanne irin malamai ne bamu bi maki ba? Me kika taɓa bamu? Shikenan daga Laila taja rabon ta kuma sai kice an ci amanar ki? Cin amana ta ina? Cin amana ya wuci ƴar aiki ta zama surukar ki? Ƴar aiki ta zama kishiyarki? Sai gashi kina ji kina kallo yanzu sune abun so sune abun tattashi. Sun fiki, sun wuce da iyawar ki? Miji ma Kanshi Kubra baki san yanda zaki tsaya ki tattali abunki ba, kina ji kina gani ga yarinyar ki nan Nihal da kika ɗora ma son duniya ga yaran naki, miji ya koro ta, kuma ya ƙi waiwayar ta, da irin wannan zaman Wallahi gara zamna zawarcin da kike goran ta mani, ko ke da kike da da'awar kina da auren menene baki aikatawa? Kin manta? In kin manta in tuna maki, Kubra zina ce kawai ba zan iya shadar kinyi ba ko bakiyi ba, Amman ita ɗinma ba zan iya tantancewa ba, irin yadda maza ke kai komo Office naki. Ke kin ɗauka kuɗi ko dukiya sune rayuwa, kina ma kowa kallon ƙasƙantacce kuma bawa, baki san kece ƙasƙantacciyar ba, kuma baiwa. Saboda daga ranar da kika wayo gari baki da komai wallahi kare ma sai ya fiki kyaun kallo da farin jini irin yadda kike wulaƙanta ƴan adam. Asara ma wallahi baki fara ta ba Kubra, har sai kin gane abubuwan da kika aikata kinyi kuskure, ko alhakin BAIWAR Allah Umman Suhan da Suhan ɗin kaɗai ma ba zai barki ba, alhakin waɗanda kika cuta kika ƙwace ma gidaje, kika amshe ma jari kika maka koti aka kulle su, da waɗanda kika sanya aka kai kurkuku ba tare da alhakin su ba. Kubra ai kin daɗe kina aikata manyan laifukan da dama tuni ya kamata Allah ya nuna maki kuskuren ki, shine yanzu daga an ɗan taɓa ki zaki zo kina ma mutane kumfar baka. To ina so ki Sani Laila sun bar ƙasar nan ita da Mijin ta Alhaji Yaro, kuma bana ma tunanin idan zaki sake sanya ta a idanun kki....... Sa'a ni kike faɗa ma magana haka? Ni zaku ci ma amana? Wallahi ki sani sai na tona maki asiri dukkan abubuwan da kike yi a cikin garin nan, da irin yaran samarin da kike bi kina amfana dasu kina basu kuɗi, da irin cutar ƙanjamau ɗin da kike tare da ita shekara da shekaru, wallahi sai kin rasa mai raɓar ma inda kike, kuma ki sani Laila taci kuɗi na ta gudu Amman bata sha ba, sai na siyar da dukkan wata kadara tata, ke hatta da gidan da take ciki sai na siyar dashi wallahi. Kuma ba zan kyale taba, dukkan inda ta shiga a faɗin duniyar nan sai na nemo ta indai kuɗi suna da amfani..." Shewa Hajiya Sa'a ta sanya," Ke shashashar ina ce? Har yanzu kina nan da sauran toshewar basirar ki? Kuɗi kuma ai saidai ki roƙi yaron ki ko kuma wanda kike kira da sunan mijin ki su taimaka maki yanzu, kada fa ki manta Sa'a akwai abubuwan naki da suke hannun Laila, to ki sani duk ta tattara su ta fece dasu, dan haka ki fice mani daga gida, bana da lokacin kuma sauraron ki, kuma kuje duk Abunda zakiyi kiyi, gidan da su Hajiya Laila suke ciki kuwa na haya ne, dan haka tuni sunyi handing Over na gida ga mai gidan, idan zaki iya siyarwa kije ki siyar, ni wallahi yaran ki ma nake tausaya mawa da kika kasance uwa garesu, ai gara ni da ban haihu ba ke fa?.... Wata irin kururuwa Hajiya Kubra tayi tana mai nufar Hajiya Sa'a da take dake tsaye wuri ɗaya cikin shirin ko ta kwana. Da gudu Al'ameen da yake zaune a birkice jin irin maganganun da mahaifiyar shi da ƙawarta ke yaɓa ma junn su. Salati kawai yake ja da wasu addu'o in da suka sauwaƙa a bakin shi. Hawaye kawai ke malala daga idanun shi. Duk yaushe Mom ɗinshi ta aikata waɗannan abubuwan bai sani ba? Duk tausayn talakawan gidan su? Ashe ita Mom ba haka take ba? Prison? Wasu suna zaune Prison ta dalilin ta. Wasu sun rasa dukiyar su da gidajen su rufin asirin su ta dalilin ta? Maza? Maza ke kai komo a wajen huɗɗoɗin nata??? Tight ɗin dake ɗaure a wuyan shima tuni ya fincike shi ya wurgar, ji yake kaman ya dinga haɗa kanshi da bango tsabar tsananin ɓacin rai da firgita. Cikin hanzari ya kamo Mom ɗin tashi da take nufar Hajiya Sa'a. Yau ba jin kai ba izza, so take su daku koda zata ji sauƙi.... Jan ta ya shiga yi yana mai son ya fitar da ita daga cikin gidan. Cijewa take tayi tana ƙunduma ma sa'a ashar da zagi, wadda take tsaye sai faman jijjiga jiki da ƙafafu take yi. Da zata iya kallon fuskar Al'ameen a wannan lokacin da zata iya cewa tinda take a duniya bata taɓa cin karo da irin yanda ya koma ba, ya sauya, halittar shi gabaki ɗaya ta birkice. Ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, balle ita da bata da ma jiki sosai wanda har Al'ameen zai iya kasa janta. Tuni ta wurgar da ɗan gyalen. Mota ya saka ta yana mai danna luck. Ya zagaya ya shiga shima yayi ma motar key. Mari take sauke mashi ta ko'ina Amman bai ko kalle ta ba, balle ya kula ta, kukan baƙin ciki ta fashe dashi, gani take shine dalilin hana ta cimma sa'ar ko zata ji sauƙi, yayin da ya kuma rintse idanu yana jin kukan har cikin kwalwar shi. Yasan tayi asarar da zata iya sanya ta kuka fiye ma da hakan, Amman koma menene ya faru da ita, ita ce ta ja ma kanta, mom ita ce ummul aba'isin faruwr komai. A farfajiyar gida suka tadda Dad, shima ya cika ya tumbatsa. Ba don kada ace yaci amana daga auren shi ya saki matar sa ba, da ace basa da zuri'a a tsakanin su, da babu Abunda zai hana shi rabuwa da Kubra yau, jarabarta ta ishe shi, rashin jin maganar ta yayi yawa. To saidai gidan har yanzu da ɗan sauran baƙi. Hakan ce ta sanya shi cewa Al'ameen ɗin daya kamo ta cewa ya sake ta. Ya wuce ya tafi wajen matarshi. Ita kuma ta biyo shi sashen shi. Ba yanda ta iya, dole ta shiga bin shi, masu aiki sai kallon su suke, yayin da shi kuma Al'ameen ya nufi nashi sashen. Bisa Sofar da na koma na zauna, nan ya tadda ni. Da sauri na na ƙara sa gareshi ina mai bin jikin nashi da kallo. Bai wata wata ba ya jawo ni ya rungume ji tsam sosai a ƙirjin shi kaman zai tsaga ni biyu. Yanda Naji zuciyar shi tana bugawa da sauri da sauri. Hakan ya sanya nayi ƙoƙarin zare jikina da nashi na jashi zuwa bisa kujera. Zaunar dashi nayi na shiga zare mashi takalman. Ɗagoni yayi yana mai runtse hannaye na cikin nashi, sai kuma Naji yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri. Da gudu na nufi kitchen na ɗauko mashi ruwa masu sanyi. Tsiyaya mashi nayi, ba musu ya amsa ya kwankwale. Sai kuma naga jikin shi ya ɗauki kyarma. Kafin kace me zazzaɓi ya lulluɓe shi. Sai rawar sanyi yake. Nan inda yake ya zame ya kwanta, duniyar gabaki ɗaya ta ishe shi. Jin shi yake kaman ba shi ba, bai taɓa nadamar kasancewar shi tsatsn Mom ba sai yau. Mahaifiyar shi shi Al'ameen Almustapa dambulan ce sanadkyyar shiga ƙuncin wasu, ita ce da bin bokaye, da duk wasu sauran abubuwan da yaji da kunnen shi ba faɗa mashi akayi ba. Ɗaki na koma na ɗauko blanket ina mai lulluɓa mashi. Amman ya jawo ni zuwa jikin nashi, har yanzu idanun shi a kulle suke sai fuskar shi da take jawur, har yanzu bai ce mani komai ba, ganin hakan ne ya sanya nagane tsakanin shine da Mom. Sai ban mashi musu ba, ko ba komai lallashi ya kamata in mashi, wannan shine amfanin auren. Nima luf nayi a jikin nashi muna masu sauke ajiyar zuciya, a hankali a hankali Naji ya fara sakin numfashi alamun kaman bacci ya fara fizgar shi..... ******' Barrister Kb ya nisa daga koro ma mahaifin nashi Alhaji Baban bayanin halin da ake ciki. Dattijon da yake kishingiɗe a farfajiyar inda yake shan iskar ne ya muskuta yana mai tashi zaune. Sai kuma ya murmusa cike da dattako da dattijantaka "Kabeeru kada hakan ya ɗaga maka hankali, ni na sani ko badaɗe ko bajima wannan ranar sai tazo, kaima na barka ne kana ma Kubra aiki saboda wani dalili, kaman yanda nima saboda wani dalilin ne ya sanya nayi ma mahaifin nata aiki har mutuwar shi. Lokaci ne yayi da zata girbi abunda mahaifinta ya shuka, kada ka samu wata damuwa, muddin akace maka dukiya ba halattatta bace ga mutum, to ka tabbata komin yanda take da albarka sai ta lalace... " Da matsanancin mamaki Barrister Kabeer ya ɗago yana mai kallon mamaki ga mahaifin nashi, cikin son jin ƙarin bayani irin nasu na lauyoyi. " A'a kada ka damu kabeeru ba daɗewa zaka ji komai, komai zai bayyana kanshi, Amman ka sani kaf gabaki ɗaya a cikin ƴaƴan ta babu wanda nake tausaya mawa kaman Yaron nan nata Al'ameen, domin kuwa muddin komai ya bayyana, to fa yana cikin tsaka mai wuya...." ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Addu'ar Matafiya ga mazaunin Gida. أَسْتَوْدِعُكُمُ اللَّهَ الَّذِي لاَ تَضِيعُ وَدائِعُهُ. Astawdi'ukumul-lah, allazee la tadee'u wada-I'uh. Ina sanya ku a cikin kiyayewar Allah, wanda abin da aka sa a cikin kiyayewarsa ba ya tozarta. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~70~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Jiki a saɓule Barrister ya baro wajen mahaifin nashi, duk yanda yaso yaji wani abu dangane da maganar da mahaifin nashi yayi ya ƙi bashi ƙofa, kawai Abunda yake sanar dashi cewa shine, "Ya bari idan lokacin sanin hakan yayi zai sani, kawai dai abunda yake son sanar dashi shine duk wani rintsi da Al'ameen zai shiga kada ya sake ya bar shi. Ya tallafa mashi a kowanne situation". Bai jima ba yana baccin ya farka da matsanancin firgita. Salati yake ja, yayin da yake ta faman haɗa zufa,alamun zazzaɓn ya sauka. Ni kau dama ina gefe zaune jugum, duk wani motsin shi akan idanu na ne. Saurin tasowa nayi ina mai tallafo shi, ganin kaman jiwa na son hajijiya dashi. Hannuwan shi dafe da kanshi, idanun shi a runtse suke har yanzu. Wani irin tausayn shi Naji ya tsirga mani, shi kuma kalar tashi jarabawar kenan. Miƙewa naga yana son yi, saboda a haka ne na tallafa mashi ya miƙe, ina riƙe dashi har muka shiga uwar ɗaka. Gefen gado na samu na zaunar dashi, danma Ya Ameen mai ƙarfin hali ne, dan dai kawai damuwar da yake fama dashi. Toilet na wuce na haɗa mashi ruwa masu ɗan zafi, nice na taimaka mashi har zuwa cikin Toilet ɗin, da so yayi ya lankwashe bai iya wankan, ni kuwa kunya na damu na, duk da naso na taimaka ɗin, gashi tarin tambayoyi ne birjik a cikin raina. Komawa nayi na shirya mashi abinci, saidai koda ya fito ya shirya bai nemi abincin ba. Kawai ce mani yayi "Dear ki shirya zaki raka ni wani waje" duk da na kula har yanzu yana cikin damuwa, haka nima na shirya, so nake in bashi baki, saidai bansan me zance mashi ba, kada yaga kaman ina son shiga lamarin shi da mahaifiyar shi ne. Abincin da na shirya saidai na kira Idi yazo ya karɓa, haka muka shiga mota muka bar gidan, jigum jigum damu cikin mota, saidai hannu na ɗaya da yake cikin nashi yana murzawa a hankali a hankali. Wayar shi ce tayi ƙara, ba ɓata lokaci ya ɗaga, saidai ga alamu kaman Dad ne, yanda yake amsa wayar cikin tsantsr biyayya. "To Dady"... "To Dady shikenan, insha Allah" Juyowa yayi kalle ni da ɗan murmushi kaman ba abunda yake damunshi "Are u ready janam?" Nima murmushn na sakar mashi, cikin jin daɗin yanda ya fara warwarewa "Ready for what dear?" Maida hankalin shi yayi kan tuƙi yana mai sakin murmushi a hankali cikin ƙarfin hali. "U'll see wify" Mun ɗanyi tafiya mai ɗan nisa, daidai lokacin da naga mun shiga ta wani tafkeken gate daga sama an rubuta *Sharaton Hotel* Da mamaki nake kallon shi, hotel kuma? Me ya kawo mu hotel? Kaman ya san me nake saƙawa a cikin zuciya ta, sai gani nayi ya sanya hannun shi manuni akan laɓɓan shi, alamun inyi shiru, ba ariziƙi na haɗiye tambayoyn nawa, na shiga bin shi a baya. Reception ya tsaya ya amshi makulli, yayin da ya kama hannu na mukayi sama. Bin shi nake kaman raƙumi da akala, har zuwa bakin ɗakin da aka rubuta VIP Room 12. Makullin ya sanya ya buɗe, muka shiga a tare bakin mu ɗauke da sallama, ko ina tsaf yake. Ƙaton falo ne da yasha kujeru na alatu, duk da baikai namu na gida ba, Amman shima ba laifi ya tsaru kam, bisa kujera na ajiye jikka ta, ina mai zama a hankali, bakina ɗauke da sallama. Shi kau wucewa yayi kai tsaye, cikin salon tafiyar shi zuwa cikin bedroom ɗin, bai jima ba ya fito yana mai ƙure fuska ta da kallo, wadda mamaki ya cika ta. "Dear dama aikin jarida kika karanta" ya faɗa yana mai sakar mani murmushi. Nima Miƙewa nayi ina mai murmushi. Cikin raina nake saƙawa, kenan anan ne zamuyi namu honey moon ɗin?. Daidai lokacin da ya ƙara so gareni yana mai kamo dukkan hannuwa na. "Sweet heart ya zuwa yanzu nasan kin fahimta, ke ɗin ba irin wadda za'a ɓoye ma komai bace, kefe cikon rayuwa ta, saboda haka babu abunda zan ɓoye maki, zamu zauna ne anan zuwa wani ɗan lokaci, duk da nasan zaki so jin dalili, Amman ki kwantar da hankalin ki, Dad ne ya bani umurnin hakan, saboda yana son kashe wata wuta ne dake neman kunno kai, wanda zata iya kasancewa har ke sai ta shafa, duk da dama ni ina ciki already, dangane da Mom ne, please ina so ki taya ni da addu'a komai ya koma normal" Wani irin bugawa gabana yayi dam, saida na kusa faɗuwa, taro ni yayi da sauri, idanun shi ɗauke da alamun me ke faruwa? Wayancewa nayi ina mai cewa "Ah no dear, ba komai, to fatan dai abun baiyi tsanani ba?" "No dear Janam, komai ma ya kusa zama normal insha Allah" ya faɗa cikin son kauda tashin hankalin da ya hango cikin kwayar idanun ta, duk da ta nuna tana son ɓoyewa. "Muje ciki ko? Sai ki duba komai, zuwa anjima sai mu fita mu nemo kayan sanyawa ko? Daga yau har ranar da zamu bar wurin nan za'a dinga a kawo mana abinci ne, so bama da matsalar good, saidai wasu abubuwan. Gyaɗa mashi kai na shiga yi, ina mai bin bayan shi jiki a sanyaye har zuwa bedroom ɗin, da yake ɗauke da gado six by six, sai side drowers guda biyu ko wacce ɗauke da dum Light, sai mirror mara girma sosai da wardroop ta bango, Amman an mata design da irin katakn gadon, sai cuttons masu kyau sosai, ɗakin ba tarkace sosai Amman yayi kyau sosai. Akwai Ac ƴar ƙarama daga cen sama, sai window guda biyu da idan ka leƙa zaka iya hangen fili fayal mai ɗauke da flowoyi masu ban sha'awa. Bakin window ɗin na tsaya, ina mai kallon wurin ya burge ni sosai, duk da irin tarin damuwa da zuciya ta take cunkushe, ya Rab wannan wace irin rayuwa ne? Mutum da gidan su, Amman saidai ya koma ya kama hotel, gudun matsaltsalu irin na mahaifiyar shi, wannan wace irin uwa ce? Yau da auren yaron ki kwana biyar Amman ba zaki iya barin shi ya huta ba, koda na sati ɗaya ne, bayan da yardar ki da amincewr ki akayi auren nan... Har ya fito Toilet ɗin ina nan tsaye rungume da hannuwa. Da ka kalle ni zaka san ina cikin wani irin yanayi, ummata kawai nake son gani, ina matuƙar kewarta. Ji nayi an rungumo ni ta baya, yayin da akayi caraf dani sai bisa gado. Cikin son mantr dani damuwa ta ya shiga yi mani wasanni harda su cakulkuli. Dariya nake yi sosai, ko ba komai Naji daɗi, hakan ke nuna mani ya damu da damuwa ta. Muna cikin haka wayar shi ta ɗauki ƙara, kaman ba zai ɗaga ba, sai kuma ya ɗaga yana mai amsawa shima cikin murmushi sosai. "Ya dai angon jego? Kana lafiya? Shikenan daga tafiya sai muji shiru? To ya masu jikin ya baby?" Banji me yace mashi ba, sai naga ya ɗan ɓata fuska yana mai cewa "Ka dai san bana son haka ko? Ba Ummin wayar" gaisawa sukayi sosai cikin mutunta juna, ikon Allah Ya Ameen in ba zama kayi dashi ba, ba zaka taɓa iya fridicting halayn shi ba, domin sai kayi mashi tunani baibai. Saidai ban sani ba ko albarkacn aure ne ya sanya shi sauya wa. Miƙo mani wayar yayi, yana mai cewa "Ummin Bilal ce" nima cikin farin ciki na amsa ina mai gaida ta tare da tambayar baby, godiya ta shiga zabga mani, kaman nice na bata gudunmuwar, ni kam sai murmushi nake yi ina mai cewa ba komai. Bilal ɗin taba, shima cikin mutum ta juna da girmamawa muka gaisa sosai, har yana zaulaya ta, Nidai saboda kunya saidai na miƙa ma Ya Ameen wayar kawai, Miƙewa naga yayi ya fice suna waya da Bilal ɗin da shima ya riga ya fice daga ɗakin, inda Ummin take. Da kallo na bishi, lallai yana ɓoye mani ne, Amman akwai wani al'amari mai tsananin girma daya taso tsakanin shi da Mom, koma dai menene ina fatan ace bai shafe ni ba, kuma koma menene ina fatan ace yazo da sauƙi, saboda ina matuƙar tausaya ma Ya Ameen, mutum ne mai kiyayewa, Sam baya son hayaniya ko wahala a rayuwar shi, yanzu zaka ga duk ya ruɗe ko ya burkice. Ya daɗe sosai sannan ya dawo ɗakin, kayan jikin shi ya rage, yana mai kwanciya bisa gadon ya ɗora kanshi bisa cinyoyii na da nake zaune, wani irin labari yake bani mai daɗi sosai na lokacin ƙuruciyar Afnan, nasha dariya sosai, yayin da hannu na yake tsakiyar sunan kanshi ina shasshafa mashi a hankali. ******* Tashin hankali sosai ba irin wanda Dad bai gani ba, saida Mom ta zama kaman wata ƙaramar mahaukaci ya, sosai take ta surfa ruwan bala'i da ɗure ɗuren ashar wa Hajiya Laila da Hajiya Sa'a, harda Alhaji yaro. Tana faɗin kaf duniya bata ga wanda ya isa ya dakatar da ita daga kulle su ba, shi kuwa Dad zaman shi kawai yayi yana mai tsura mata idanu, har tayi ta gaji ta gama dan kanta, Abunda ya kula wanda bai gane kanshi ba, danganta faruwr hakan da auren Umma da Suhan a cikin gidan da akayi, wai sune masu farar ƙafa, daga zuwan su su ja mata asara ta miliyoyin kuɗaɗe,idna shi bata isa ta sanya ko ta hana shi ba, ai ta isa da ɗanɗan ta, dole ne yarinyar nan tabar gidan nan ayau yau ɗin nan, ba ƴan jarida ba, ko su wanene sun daɗe basu ji ba, ita akan dukiyar ta babu irin Abunda ba zata iya aikatawa ba. Sanin da Dad yayi ƙarami ne a cikin aikinta, ya sanya shi dole tura ma Al'ameen saƙo akan su bar gidan, ganin irin halin da ta shiga yanzu, ba zata iya lankwasuwa ba, ba kuma zata tsaya sauraren shi ba. Har tayi ta gaji ta koma ta zauna, sai kuma ta sake saka mashi kuka, akan wai ba zai taimake ta ba, yana ji yana gani zata yi asara wadda ita kanta bata san a daɗin ta ba. Sai da yaji tayi shiru ne ya nisa yana mai cewa "Kalle ni nan Kubra, kin gama? Nace kin gama? Ina so ki faɗa mani, lokacin da zaki sanya kuɗaɗen ki, cikin ni da shi Al'ameen ɗin wa kika tuntuɓa? Nace wa kika tuntuɓa? Ba gaban kanki kika yi ba? Sai yanzu ne da wankin hula ya kaiki dare shi ne kuma kika dawo kina son kuce mani in sanya baki acikin al'amarin? Ko ki juya al'amarin ya koma wani abu daban? To ina so ki sani, Al'ameen ma baya gidan nan gabaki ɗaya, kuma wallahi muddin kika kira shi kika tada mashi hankali, ko abun nan ya shafi matarshi ban yarje maki ba, kuma zaki gamu da fushi na fiye da yanda kike tsammani. Yaron nan tinda ya taso a rayuwar shi kuke cuta mashi tare da iƙirarin kinfi sonshi duk a cikin ƴaƴanki, Amman baki bari zuciyar shi ta natsu ba, haka ake soyayya? Ke haka naki iyayen suka yi maki? Ko kina so in tuna maki? Ko akul ɗinki wallahi njai wnai sabon abu, damfara ce an riga anyi maki, saidai kiyi haƙuri, ni dai Mustapha Dambulan ba zan iya sanya baki na acikin wannan Case naki ba, saboda a lokacin da zaki ƙulla rufa mana kikayi baki nemi shawarar mu ba, ina ce tun lokacin da kuɗaɗen naki hannun shi Ameenun suke, kika amshi kayan ki, a cewar ki yaji da nashi ayyukan, kin manta da kwazo da jajircewa irin ta yaron naki, sai yanzu kuma kinje kinyi Abunda kika ga dama kizo ki ɗaga man hankali ni da yaro na muna zaman zaman mu? Ke ko kunya ma baki ji ace yaro daga aure duka ƴan kwanaki ace ya fara shiga tashin hankali, ita surukar taki ace ta fara shiga tasku irin na uwar miji? Ke haka Hajiya keyi maki? To ina so ki sani, daga yanzu ma ban yadda ba kika sake taka ƙafar ki waje da sunan zakuje aiki ko Office, sannan na gane ki da saka Al'ameen a cikin maganar ki, kuma muddin kika bari wannan abun ya shafi zaman auren Al'ameen kema a iya bakin naki auren.... Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fice, bai ko sake waiwayarta ba, iya matuƙa ɓacin rai ya shige shi. Lokaci yayi da shima zai tsaya tsayin daka ya ka da gidan shi, aikin ambasador ne yayi deciding zai ajiye, turka turkar dake cikin gidan, ko kuma yace wadda Kubra zata iya kawowa yana tunanin zata yi silar dagula komai, zata yi silar wanzuwa wani al'amari mai girma, haka kuma zata yi silar da duniya zata yo caaa akansu. Ya snata sarai ba jin magana take yi ba, hakan ce ta sanya shi dole kiran Al'ameen ɗin a daidai lokacin da suke hanya. ******** Zaune take gaban mai martaba, inda ƙafafun ta suke tanƙwashe, shima mai martabr a ƙasa yake zaune, bisa shimfiɗun shi masu matuƙar kyau ta taushi. Daga gefen shi cen Mama Fulani ce itama zaune, da gani dai wani muhimmin abubuwa suke tattauna wa. mma kam da aka tado mata tsohon miki hawaye kawai take gogewa, kaman yanda mai martaba ya umurce ta, ba zata taɓa barin gidan ba, muddin ba yinta akayi ta ƙare ba, ƴan kwanakin nan kuwa mafalkin tsohon mai martaba mahaifinta kawai take yi, tare da marigayin mijin nata da ya daɗe da rasuwa. Abunda ke ƙara bata mamaki, yawan mafarki su a tare da take yawan yi, bayan tasan cewa ko alama mutuwar tasu bata shafi juna ba, hasali ma mijin nata ya daɗe da rasuwa kafin mahaifin nata. Sai kuma gabanta da yake yawan faɗuwa akai akai, Suhan kawai take tunawa, ko a wanne hali take ciki? Ta santa da kawaici, koda wani abu zai faru da ita, ko zai same ta, ba zata taɓa bari ta sani ba, gudun tashin hankalin ta, wanda tasan irin ciwon da take fama dashi. Aikuwa sai gashi wasa wasa Umma na neman kwanciya, ganin hakan ne ya sanya dole mai martaba ya Umurta da akira mashi Dad ɗin miji ga Gimbiya Meramar. Hankalin Dad ya tashi sosai, jin cewa mai martaba na neman shi shi da Yaya Auwalu, da kuma abokiyar zaman gimbiyar, kai har a da duk wani da yake ganin ya zuwa yanzu ya dace kowa yasan matsayin Umman a gidan, da ma ma sarautar baki ɗaya. Zullumin shi kawai ta yanda zai ce ma Hajiya Kubra ka neman da ake masu, domin yasan ga halin da ake ciki, duk da haka a haka yayi ta mazan shiga sashn nata. Nihal da Saudat ce kawai zaune a falo, ƴan sauran ƴan uwan Hajiya Kubran da suka rage, kaf sun tattara jiya sun idasa tafiya, to shi dama burin shi kenan, ya kasance cewa ba wani a gidan wanda zai iya fidda Sirrin halin da ake ciki a wajen gidan. "Dad barka da shigowa" suka haɗa baki wajen cewa, fuska ba annuri Sam ya kalle su ba tare da ya amsa ba yace "Ina Mom ɗinku?" "tana sama" Saudat ta bashi amsa, domin dama ita Nihal yanzu tin da abun nan ya faru bata kuma ganin dariyar Dad ɗin nata ba, wajen Mom ne kawai take samun sauƙi, ya zuwa yanzu komai ya fita a kanta, so take kawai ta ganta gidan babyn ta, wannan zama ya isheta, ita mai aure ita ba mai aure ba, Amman jin kanta ya hana har yanzu ko sau ɗaya ne ta kira shi, ko da ba zata bashi haƙuri ba taji matsayin ta, kuma har yanzu ba wani daga cikin dangin shi da suka zo gidan. Har yayi gaba zai gaye saman, sai kuma ya dakata, yana mai juyowa ya kalli Saudat ɗin, da duk sunyi tsuru, domin ya zuwa yanzu kowa ya fuskanci halin da ake ciki, hatta da ƴan aiki, aiko sun samu Sana'a sai ƴan gulmace gulmace suke yi, suna cewa alhakin waɗanda take wulaƙanta wa ne ya fara kama ta. "Ke me kike yi anan?" ya jefa ma Saudat ɗin tambaya, fuskar shi a matuƙar ɗaure. Cikin in'ina tace "Dad ba komai wajen Nihal da Mom nazo" Aiko kaman ta watsa mashi ruwan zafi, take ya hau balbaleta da faɗa, har yana cewa ita yaƙi zaman auren shine kema abun ke burge ki ko? Kike so kema sai kin zama irin ta, to maza ki haɗa inaki inaki ki wuce gida, kada in sake ganin ƙafar ki cikin gidan nan kwana kusa, daga ku har Mom ɗin taku da take ɗaure maku gindin rashin mutumci, zan saɓa maku ne, kada ki sak eki bari in sauko in tadda ki. Yana gama faɗin haka ya sanya kai ya fice, ita kuwa Nihal har ta fara sharar kwalla, Dad ɗinsu ya sauya hali yanzu, Sam baya so su kaman da, tin dai da ya ƙara aure, shikenan suka zama kaman ba ƴaƴan shi ba, an raba su dashi, irin jansu a jikin nan da yake yi ma yana jin damuwr su yanzu ya bari jiki na rawa Saudat ta zari mayafn ta ta fice har tana waiwayen Nihal da duk tausayn ta ya gama kama ta. Har ta isa gaban motar ta, tana tunani, yanda Rayuwar gidan su ta sauya cikin ƙanƙanen lokaci, mom ta zama kaman ba ita ba, yanzu duk isar nan da mulkn da take zubawa cikin gidan babu shi, hatta da ƴan aiki yanzu sun samu sake, haka zaka ratsa gidan ba tare da wani ma ɗan aiki ya gaishe ka ba, watau suna jin kansu a sama kenan tinda har ɗaya daga cikin su ta samu saken auren mai gidan.... ********** Bakin gado ya tadda ta tana waya, ganin shigowar shi baisa ta katse ba. "Kana jima Barrister lallai kazo yanzu ina son ganin ka" Abunda ta faɗa kenan ta katse wayar tana mai kallon alhaji Mustapha da yake tsaye bakin ƙofa, haushn shi take ji, gani take kaman yana adawa da ci gabanta, in ba haka ba, yaushe zai hana ta fita neman haƙƙin ta. Shima bakin gadon ya samu ya zauna, har ga Allah yana jin tausayn ta a yanzu, duk ta birkuce ta fita kamannn ta, har ta zurma lokaci guda, to asara ce tayi ta nama ƙarama ba, saidai koma minene tarin kanta ne yaja mata. "Hajiya kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki, ki dena tada ma kanki hankali sosai akan Abunda bai kai ya kawo ba, wannan ƙadai bai isa yayi ruining farin cikin ki ba, insha Allahu komai zai tafi normal kaman yanda kike fata, dukiyar ki zata dawo maki, bana tunanin idan Alhaji Yaro zai iya cutar dake, bayan duk amanar da kika bashi, shi da matar shi..." Har ya kai aya bata ce dashi komai ba, saida ya dire ne sannan ta samu damar magana. "Alhaji ka sani ba ƙaramar asara nayi ba, kuma kai shaida ne cewa akasinaka samu, ban taɓa tunanin cin amana haka ba daga wajen Laila da Alhaji Yaro, kuma bayan haka, yanzu Alhaji sabo da Allah ka kyauta mani kenan? Ka sanya yaron nan ya bar gidan nan. Shi da matar tashi? Dama wace ala cika, raini ne sun riga sun yi mani, sai kuma yanzu gashi kana neman ja mani wani, ka sani cewa yaron nan shine kawai wanda nasan zai tsaya mnai wajen kwato mani haƙƙi na, Alhaji don Allah kace ya dawo, ni ko na kira shi ma bata shiga" Itama ta faɗa cikin wani irin yanayi, kaman dai ta saduda, Amman har yanzu idan ka kalli kwayar idanun ta, zaka iya hango tashin hankali tsantsa a cikin su, Hajiya Kubra kenan, damusa mai kwanciyar ɗaukar rai. Sai da ya gama kallon ta da nazari ta, sannan ya nisa, sai da sharaɗi guda ɗaya, muddin kika cika shi, to tabbas zaki samu Al'ameen da matarshi sun dawo gidan nan." Ba tare da wani dogon nazari ba tace" Na yarda Alhaji" ɗan murmushi yayi, "Tun ma baki ji sharaɗin ba?" itama gyaɗ a mashi kai ta sake yi cikin amincewa Muskutawa yayi, cikin jin girman Abunda zai faɗa mata, domin yasan a wannan yanayi da ake ciki, bai zama lallai ta iya yarda ba, masalan ma na zafin Umman Suhan da ya lura da ta fara ji" Sharaɗin shine zamu je Adamawa tare dake, watau ina nufin Mahaifar Su Umman Suuhana, idan har kin yarda kin amince kin bini, to fa lallai zamu dawo mu tadda su Al'ameen da matar tashi a cikin gidan, kuma tabbas ba zan hana shi shiga cikin lamurran karɓo maki dukiyar ki ba, kuma sanin kanki ne cewa tabbas idan lamarin ya koma hannun shi, to fa sai inda ƙarfin shi ya ƙare... " Cikin wata irin tsabar kaɗuwa ta ɗago a matuƙar firgice tana kallon shi, cikin rawar murya da rawar baki tace" To Alhaji na yarda na amince, indai har wannan zai sanya ka kyale Al'ameen ya kwato mani haƙƙi na, ba damuwa zamu iya zuwa, ko yaushe kake so" Shima murmushi yayi, da mamakin jin furucn nata, lallai Hajiya Ku ra bata haɗa kuɗi da kowa da komai ba, ita su ne mutumcin ta, kuma bata yadda a ƙasa ba, mahaifinta ma tin a wancen lokacin haka yake, saboda kaf duk garin na Katsina babu wanda bai san da zaman Alhaji Ibrahim kwangila ba. Miƙewa yayi shima cikin jinjina kai yana faɗin "Sai ki fara shiri, idan Allah ya kaimu zamu yi sakon tafiya ne" Da kallo ta raka shi, gabaki ɗaya Alhaji Mustaphan nata ya rikiɗe ya koma kaman ba shi ba, sai da yaje gab da fita ne, tayi ta mazan sake cewa "To Alhaji wai ya maganar Nihal ne? Naga har yanzu yaron nan bai zo ba fa, bai kuma aiko ba, ya kamata asan halin da ake ciki fa, na gaji da zaman nata a haka wallahi, gashi har an fara yada mani magana akan hakan" A hankali ya juyo yana mai ƙare mata kallo, sai kuma ya girgiza kai,yana mai juyawa ya sanya kai yana mai ficewa tare da ce mata "Ba yanzu ba....." ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Yin Kabbara Da Tasbihi Yayin Da Ake Cikin Tafiya Allahu akbar. اَللهُ أَكْبَرْ Subhanallah. سُبْحَانَ اللهِ >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~71~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Tafiya yake a hankali, zuciyar shi gabaki ɗayanta a cunkushe take, fuskar nan tashi sam babu walwala, duk kuwa da ƙoƙarin da nayi wajen ganin ya saki ran shi kafin ya fita ɗin, dama tinda yaga wayar dady ɗin nashi saida gaban shi ya faɗi, har kawo lokacin da ya ɗaga yake sanar mashi cewa ya same shi guest house ɗinshi dake bayan gari. Yasan maganar, kuma yasan kan zancen, wannan ce ta sanya har yanzu ba zai iya tantance a matsayin da yake kai ba, ya sani sarai Mom ba zata lamunta hakan ba, Amman da ba abunda zai tsaida shi a ƙasar, balle dukkan Abunda zai faru ya faru yana nan, har ya juye zuwa kanshi, to saidai baya jin zai iya barin amaryar tashi da har yanzu basu rufa sati guda ba ma cur a tare, wanda zai iya cewa har yanzu bai san daɗin angonci ba saidai ƙalilan, yana matuƙar ganin ƙoƙarin Suhan, duk da ta fahimci Abunda ke faruwa, Amman Sam bata bayyana mashi fushin ta ba, in banda ɗan tashin hankali ƙalilan da yake iya hangowa a kwayar idanun nata, duk kuwa da ƙoƙarin ɓoye mashi da take yi. Da haka ya isa ga guest house ɗin, inda mai gadi ya buɗe mashi gate ɗin, a wajen parking ya tadda motar Dad, alamun da ke nuna mashi Dad ɗin nashi na jiran shi kuwa. Kallon agogon rolers da yake hannun shi yayi, lokaci guda yana mai ayyanawa a ran shi dare yayi, dole yayi maza ya kammala abunda yake ya koma ga Suhan ɗin da ya baro ta cikin tsoron rashin sabo, masalan a ɗakin hotel ita kaɗai, girgiza kai ya shiga yi a hankali, irin ƙaddarar tashi kenan. Da salon tafiyar shi cikin ɗan hanzari ya tattaka zuwa cikin babban falon da ya ƙunshi kujeru da dama, mai ɗauke da manyan ɗakuna da suka taimaka wajen ƙara ma ginin guest house ɗin girma. A ƙaramin falon dake cen ciki ya tadda Dad ɗin nashi, zaune yake cikin kamala da dattako kaman ko da yaushe, jarida ce ta daily trust a hannun shi yana dubawa, gefe guda kuma Mug ne mai ɗauke da cufee da ƴar ƙaramar buta mai kyau fara tas da ita. Gefen Dad ɗin ya samu ƙasa ya zuƙunna yana mai tankwa she ƙafa, gaida Dad ɗin nashi ya shiga yi, daga yanayin da Dad ɗin ke kallon shi, ya karanci tsantsrr damuwa dake yawo cikin zuciyar tashi. Cikin sakin fuska ya amsa, ko ba komai yana buƙatar ya kawo wani yanki na sassauci a cikin zuciyar Son ɗin nashi, tausayi yake bashi matuƙa ainun, saboda hakan ne ma ya yanke hukuncin Abunda yake ganin shine zai kawo masalaha ga al'amarin. Gyara zama yayi, yana mai nuna ma Al'ameen kujerar da take kusa da tashi, alamun ya dawo bisa ya zauna, ba musu ya miƙe ya koma bisa sofar. Da hannu yayi mashi alamun da ya zuba Cofee ɗin shima, jim yayi kaman ba zai zuba ba, sai kuma ya miƙa hannu yana mai tsiyaya kaɗan. Har yanzu Dad nazarn shi yake yi. Gyaran murya yayi, yana mai kallon Yaron nashi cikin wani irin yanayi ya fara magana. "Al'ameen dalilin da ya sanya nayi kiran ka anan shine, sanin kanka ne cewa ya zuwa yanzu Abunda ke faruwa a cikin gidan namu ya fara zaga kunnen mutane, saboda haka ne bana so hankalin ƴan jarida ya dawo kanmu, ka ganta nan? (Ya nuna mashi jaridar dake hannun shi) jarida ce ta gobe wadda zata fita, ka duba title ɗin dake sama me Kaga an rubuta?" Ya faɗa yana mai miƙa mashi jaridar. *WATA DAMBARWA NA NEMAN KUNNO KAI A GIDAN AMBASSADOR ALMUSTAPHA YUSUF DAMBULAN, SAKAMAKON DAMFARAR MATARSHI MAI SUNA DR. HAJIYA KUBRA DA WANI MUTUMI MAI SUNA ALHAJI YARO DA YA KASANCE MIJI GA AMINIYAR TA HAJIYA LAILA MAMUDA, DAMFARA KUMA DA ZAMU IYA CEWA TA MILIYOYIN KUDAƊE, WANDA HAKAN NA IYA KAWO RUƊANI DA FARUWAR WANI MUHIMMIN AL'AMARI* A matuƙar ruɗe Ya Ameen ya ɗaga yana kallon Dad ɗin nashi. Duniya kenan kana bacci ana maka munshari. Watau wannan maganar har ta iya fita waje kenan? To wanene ya fidda ta? Ko dai Hajiya Sa'a ce? Bai iya cewa komai ba, sai bin takardar yake da kallo, kaman tsohon makahon da idanun shi suka buɗe a lokaci guda. "Kada ka tashi hankalin ka, Abunda nake jiye ma Mom ɗinka kenan tun tuni, wannan al'amari kuma na iya kawo mana naƙasu da koma baya ta fannin kasuwancin mu, masalan ma kai da yanzu idanun kowa suke kan ka, saboda ɗaukaka da Allah yayi maka. Wannan ne dalilin da ya sanya na nemeka nan domin in sanar dakai Abunda nake so kayi, domin idan muka daka ta mahaifiyar ka, ba za'a taɓa samun masalaha ba" Jinjina kai yake yi cikin tashin hankali, me mom ɗinshi take so ta zama ne? Wai shin yin kuɗi ko Arziƙi kansu farau ne? Bai taɓa danasanin arziƙin da yake dashi ba sai yau, bai taɓa danasanin haihuwar shi gidan da suka rufa suka tada kai da Arziƙi ba sai yau, yana ji ace dama gidan da kullum rana ta Allah sai an fita an nemo za'a kawo masu suci, suyi makaranta ta gwamnati, su kwana a saman katifa ko tabarma, aka haifeshi yana jin da hakan da sai yafi zama mashi mafi alkhairi da kwanciyar hankali. Maganar Dad ɗinne ta katse mashi tunanin da yake yi, "Idan Allah ya kaimu gobe ka ɗauko Matarka ku dawo gida, ni da Mahaifiyarka da Alhaji Yaya zamuje cen garin su Umman ita matar taka, mai martaba sarki na neman ganin mu, saidai ina so kafin mu dawo duk yanda zakayi ka nemo dukkan info akan Alhaji Yaro, da dukkanin harƙallolin da Mom ɗinka keyi ba tare da mun sani ba, wannan kuma zai faru ne tare da taimakon Barrister Kabeer, saboda haka dole ne ka ɗaura ɗamba, ka ƙarfafa zuciyar ka, ni na sani zaka iya cin karo da abubuwa da zasu iya dagula maka lissafi, saboda kasan Halin Hajiya sarai, ba jin magana take yi ba a lokutta da dama, dole ka aro jarumta ka sanya ma ranka, dole ka ƙarfafa ma kanka guiwa, insha Allahu zamu kawo ƙarshen wannan al'amari cikin sauƙi, nima kuma idan na dawo da izinin Allah zan taimaka maka ɗin. Don haka yanzu ka tashi kaje wajen Matarka, zuwa da safe kuma ku koma gida, saidai kafin safen ya kamata kayi nazari ta yanda zaka ɓullo ma wannan al'amari cikin sauƙi ba tare da kaja hankalin ƴan jarida ba, ko gidajen redio" Sai da ya nisa sosai, sannan yayi ma Dad ɗin nashi sallama, da kallo ya bishi, yana mai kallon Mug ɗin Cofee ɗin da ya ajiye ƙasa, wanda bai ma san ya sauke shi ba, ko sau ɗaya kuma bai kai shi bakin shi ba. Har ya fice daga cikin falon, sannan ya sauke numfashi yana mai cewa "Hakanan zaka ci gaba da haƙuri da mahaifiyar ka, abubuwa da dama da take aikatawa bata yar a ƙasa bane" ******* Har bacci ya fara fizga ta lokacin da naji shigowar shi, saida ya kulle ko ina sannan ya nufo ɗakin, lokacin har na sauko daga bisa gadon, jiki na sanye da pajamas masu taushi tare da salƙi, kaina sanye da hula mai taushin gashin mage, na cusa dukkanin gashi na da yake tsefe ciki, sai nayi kyau, koni lokacin da nayi wankan na gama shiryarwar kasa dena kallon kaina a madubi nayi, duk da fuska ta babu komai saman ta in ka ɗauke face cream da glow dake sama. Bakin ƙofa muka ci karo dashi, yana ƙoƙarin shigowa ni kuma ina ƙoƙarin fita, saman ƙirjinshi na faɗa ban sani ba, saidai Naji ya sanya dukkan hannuwan shi ya zagayo bayana dasu, ya rungume ni tsaf a cikin faffaɗan ƙirjin shi. Luf nayi, ina mai amsar saƙon zuciyar tashi. Saidai yanayin yanda Naji tana bugawa da sauri da sauri ne ya sanya ji ɗagowa cikin hanzari ina mai kallon fuskar tashi. Idanun nashi a kulle suke ruf, sai zara zaran gashin idanun shi da nake iya hangowa, haɗe da girar shi mai kyawon yanayi. "Yayana kana lafiya kuwa?" Abunda na iya cewa kenan, har yanzu ina cikin jikin shi sosai. A hankali ya buɗe idanun nashi yana mai ɗora su saman fuska ta, sai kuma ya shiga zame hular kaina a hankali zuwa rabin kan nawa, yana mai ɗora bakin shi bisa fore head ɗina ya shiga sakar mani wani irin Kiss. Nidai har yanzu tsaye nake, hannun shi guda tallafe da ƙugi na, a haka na shiga jan shi, zuwa bakin gado. Safar shi na shiga saɓule mashi, tun da ya riga ya cire takalman already. Bai hana ni ba, sai kallo na da yake yi, wata irin ƙaunar shi na ratsa ni, a yanda nake ji a yanzu, ba zan taɓa iya rayuwa ba tare dashi ba. Toilet na wuce nan haɗa mashi ruwa, yau kam saidai ni na taimaka mashi wajen wankan, ina lura dashi yanda jikin shi yake sanyaye, kuma yana yawan tafiya tunani. Hakan ce ta sanya koda muka kwanta saidai ya rungume ni yana mai sakin ajiyar zuciya akai akai. Inda ni kuma Naji daɗin jikin nashi, tuni bacci ya kwashe ni, yayin da shi kuma ya zurfafa a cikin tunani, dole ne yace ma Bilal ya dawo, ba zai iya shi kaɗai ba, matsalar Mom zata iya tarwatsa mashi kwanya tuni. Yana buƙatar mataimaki, kuma baya so damuwar shi ta shafi Suhan ɗin, Shiyasa dole ne duk yanda zaiyi ya kauce mata wajen faɗa wa cikin damuwar itama zaiyi. Da safe bayan mun gama komai na Al'ada ne yake ce mani in shirya kaya zamu koma gida, kaman yanda bai man wani cikakken bayani ba, nima hakan ban tambaye shi ba na shiga haɗa kayan, hakan da nayi ya matuƙar burge shi, kuma hakan na nuna mashi ba zan taɓa bijire ma umurnn shi ba, sannan ni ɗin ba mai shiga al'amarin da aka juna ba'a so da in shiga ɗin ba. Ya santa da sanyin hali, hakan ne ya sanya dole ne duk yanda zaiyi wajen ganin ya bata kariya daga dukkan wani abu zaiyi, baya jin zai iya lamuntar damuwa da halin da yake ciki ya shafi matar tashi. Bai same ta da sauƙi ba, haka kuma dukkan wani al'amari da ya shafe shi baya jin shi da sauƙi. Har muka isa gidan motar tsit, ba mai cewa komai, sai naga yau ya koma man kaman Ya Ameen ɗin da na sani da cen baya, muskili mara walwala da fara'a. Nasan damuwar shi, kuma ina ganin ƙoƙarin shi matuƙa, hakan ce ta sanya nima sai ban nuna mashi nasan yawan damuwar da yake ciki ba, gudun kada yace ina shiga sha'anin shi shi da Mom ɗin tashi. Yayi mamakin da akace mashi su Dad ɗin sun wuce, Nihal ce ke sanar dashi hakan, lokacin da muka shiga cikin gidan, bata tanka mani ba, haka nima ban tanka mata ba, nasha alwashin matuƙar gyara mata zama cikin ruwan sanyi, shi bai ma ko kula da rashin gaida ni ɗin ba, ya sanya kai riƙe da hannu na muka fice daga sashen. Da kallo ta bimu tana mai taɓe baki cikin ƙaunar zuciya, cikin ranta take rayawa an gama da yayan nata, saidai duk yanda zata yi ta ƙarƙashin ƙasa itama sai tabi domin cusguna ma zaman nawa da yayan nata a cikin gidan, muddin tana cikin gidan (Nace ai sai kiyi ta zama, ki kalli Abunda zai kashe ki da rayuwar ki) Koda muka shiga sashen namu bai zauna ba, na kula yana cikin sauri ne, sai ban tsaida shi ba, na raka shi har ƙofa ina mai yi mashi a dawo lafiya, saida ya bani peck a goshi sannan ya fice. A sanyaye na koma cikin gidan, wannan wace irin rayuwa ce? Dama haka Rayuwar masu kuɗin take? Ashe hakanan talaka ke sha'awr Rayuwar masu kuɗi, ashe matsaltsalun su sunfi na talakawa yawa, takalma ne zai kwana Baida ko sisi yayi bacci hadda munshari, Amman mai kuɗin da yake da biliyoyi ya kasa bacci, kaman yanda Ya Ameen yayi a daren yau ɗin. Kitchen na wuce bayan na gama gyara ko ina, dole in sama mashi Abunda zai ci, wanda zai iya sanyaya mashi rai kafin ya dawo, duk da nasan maganin masalar tashi saidai Allah. ******* Kai tsaye office ɗin Br. Kb ya wuce, shi kanshi Br ɗin yayi mamakin jin cewa wai Ya Ameen ɗin ne da kanshi yazo wajen nashi, ba ɓata lokaci ya sanya aka shiga dashi har cen ciki. Miƙewa yayi da niyyar kawo mashi abun sha ya dakatar dashi. Bayan sun gaisa ne ya buƙaci da ya kawo mashi files na dukkanin ƙaddarorin Mom ɗin tashi, da dukkanin wata takarda dake ɗauke da shaidar zuba hannun jari ta, da kuma sauran duk wani abu daya shefi Mom ɗin tashi. Yayi mamakin ganin himilin tarin takaddu sosai a gaban shi. Haka ya dinga bun su ɗaya bayan ɗaya yana dubawa. Ba zan iya fasalta halin da ya shiga ba, da yana da hali kaf, gabaki ɗaya dukiyar Mom sai ya amshe ta daga hannun ta, ko za'a samu zaman lafiya, da zata iya zaman aure, kaman yanda ko wacce mace keyi, Dad ba abunda ya rage ta dashi, saidai har ta kai ga tana yin wasu huɗɗoɗi da kuɗaɗennnata da bata iya sanya wani daga cikin su saidai shi Brst ɗin, shima dan ya dama dole ne, gudun irin hakan. Zuciyar shi sai Fat-Fat take kaman zata tsago ƙirjin shi ta fito. Ba Arziƙi ya nemi Layin Bilal. Daga yanda yaji maganar aminin nashi ya san ba lafiya, Shiyasa tun kafin ma ya faɗ a mashi dalilin kiran ya shiga sanar mashi cewa gashi nan a airport zai taso. Kashe wayar yayi ba tare da ya ce komai ba, ya rufe folders ɗin, yana mai maidawa bisa table ɗin barrister ɗin da ya koma shima ya zauna yayi relax yana ta Kallon al'ameen da sai ka rantse da Allah bai taɓa dariya ba, idanun shi sun kaɗa sunyi jawur dasu. A hankali ya ɗago yana kallon barrister ɗin, inda a hankali ya buɗe baki, muryar shi na cracking ya shiga cewa "Ina so in gana da Baba Alhaji" "OK yallaɓai zamu iya zuwa yanzu" Abunda Barrister ya faɗa kenan yana mai Miƙewa ya shiga tattara folders ɗin ya zuba cikin wata safe lucker ya kulle da ɗan makulli. A motar Ya Ameen suke tafe, yayin da Barrister ɗin yake zaune gefen Ya Ameen, shi kuwa mutumen zaune kawai yake, inda tuƙin ma da hannu ɗaya yake yin shi, ya muskuta sosai inda hannun shi guda da yake bisa ƙofar motar ya dafe baki ɗaya dashi, Allah kaɗai yasan ne ke yawo a cikin zuciyar tashi. Mafita ɗaya ke gareshi, kuma ya tabbata da izinin Allah zai same ta a wajen Baba Alhajin, ba zai taɓa barin wata ƙofa ta tozarta da zata iya shafar ahalin nashi ba. Kusan duk inda suka gitta sai Kaga matasa na ɗaga masu hannu, sun gane motar, Amman Sam shi hankalin shi baya kansu, dalili da hakan ne ma ya kira manager ɗin shi tun da safe yake shaida mashi yaba dukkanin ma'aikatan leave na kwana biyu, akwai muhimman ayyukan da suka taso mashi, inda dukkanin kanfanonin nashi na gida da na wajen ya bada izinin a kukkulle su gabaki ɗaya, zuwa dare zai gana da shuwagabanin nashi na kanfanonin. Amman ya bar hakan ne har sai Bilal ya dawo, inda shine zai aiwatar da kaso 80 a cikin ɗari na ganawar. Ko da suka isa gidan, shaida masu akayi da Baba Alhajin ya tafi asibiti ganin likita ido, wanda yake fama dashi shekara da shekaru. Dan dole suka dakata a babban falon baƙin, inda barrister ya fiddo system ɗin da yake recording komai na Hajiya Kubran tun daga amsar aikin da yayi nata, daga hannun mahaifin nashi. Sosai ya natsu tsaf yana kallon komai, akwai abubuwa da dama da bai fahimta ba, yana so ne har sai Baba Alhajin ya ƙara so, inda yake sa ran jin cikakken ƙarin bayani daga gareshi.... ********** Tafiya ce da zamu iya kiran ta da zaman shiru, idan ka ɗauke Alhaji Mustapha da kwalli kwal ɗin yayan nashi dake gareshi kaf faɗin duniya, sune kawai suke ƴar firar su jefi jefi. Har yanzu zuciyar Hajiya Kubra na gargaɗar ta dalilin da ya sanya ta yarda ta biyo su wannan tafiyar, saidai shara ɗin da mijin nata ya gindaya mata, shine kawai Abunda ya katange ta daga cewa ba zata je ɗin ba, zuciyar ta na raya mata har yanzu wani ɓari na zuciyar bai yadda da Abunda aka faɗa mata ba, na cewa Umman ƴar sarauta ce gaba da baya, kuma masu Arziƙi ne, anya ba wata ƙullalla akayi mata ba? To ita yanzu tace taje ina? "Gidan su kishiya" wata zuciyar ta raya mata, ɗan ƙaramin tsaki taja wanda ita kaɗai ce zata iya jin Abunda tayi, wayar ta ta fiddo tana lallatsawa. Har suka shiga cikin garin tana nazari, ji take kaman tace su ajiye ta ta koma, gabanta na matsanancn faɗuwa, har kai lokacin da suka fara ratsa tangama tangaman gate ɗin tanƙamemiyar masarautr. Duk gate ɗin da suka bi sai driver ya tsaya da motar, kafin a lura da wanda suke ciki a basu izini wucewa. Sun samu tarba sosai, tun fitowar su daga mota zuciyar Hajiya Kubra ta tsinke, anya ko gaskiya ne Abunda take ji? Kai da sakyal, anya wadda take matsayin ɗiya ga wagga babbar masarauta zata iya tafiya tayi zaman bauta na kusan tsawon shekara ashirin, bayan ma kafin tazo gidan ga dukkan alamu ta daɗe a wani wajen? Jikinta da komai nata baya nuna cewa ita ɗin wata ce, kawai dai kawaici da rashin hayaniyarta ne zasu iya shida maka da cewa ita ɗin ba ta son hayaniya, ba daga nan ba, babu shaida ko kama. Da wannan tunanin suka ƙarasa fadar , inda suka tadda an cika maƙil ana fadan ci. Cikin girmamawa suka gaisa da kowa, ita dai Hajiya Kubra na zaune lankwashe da ƙafa, kaman yanda suka ga kowa nayi, sarauta ai tafi kuɗi, duk da kuɗin ma na siyan sarautar. "Wannan da nake gani kaman Kubra ɗiyar Ibrahim ko?" Cewr Waziri da yake zaune a gefen sarkin, duk da yanzu baya da wata faɗa aji, kowa ya san matsayin da ya ajiye shi, Amman hakan bai hana aka tilasta shi fitowa majalisar sarki ba. Cikin mamaki ta ɗago kanta tana mai ƙare ma tsohon kallo, kafin ta buɗa baki tace "Eh nice kuwa Baba" "Ikon Allah yanzu baki gane ni ba Kubra? Ba mamaki, ai shekarun da yawa" Shima Abunda ya faɗa kenan cike da jimami, lokaci guda kuma gaban shi na sake tsinkewa yana faɗuwa. Ba wanda baiyi mamaki ba, masalan ma Dad da mai Martaba, ikon Allah, shin ko ina kuma Waziri ya san matar da kallon shi ɗaya da ita ya kama sunan ta? Ba tare da sake cewa komai ba, aka sa sarkin zagi yayi kiran jakadiyan. Cikin gida aka sanya suka shiga da ita, yayin da suke ratsa farfajiyar gidan take bin ko ina da ido da kallo. Har ɗakin Mama Fulani, inda akayi masu iso suka shiga. Tasha tarba ta ban mamaki, duk da cewa dama ansan da zuwan nata, ɗaki guda aka ware mata a cikin sashen Mama Fulanin, inda aka cika mata gaba da kayan ciye ciye, ji take kaman ba ita ba, a yanda su Hajiya Sa'a suka bata labari ma, ai gani take yi kaman yafi hakan. To ina ita Maryamar take? Tana cikin tunani ne Muryar Umman ta karaɗe ɗakin da Sallama. Cikin mamaki ta ɗago tana kallon Umman da kuyangi ke biye da ita a baya, suna mai gyara mata zaman alkyabbar tata. Umurni tayi masu da su basu wuri, zata gana da Uwargidan tata. Sai da suka fice ne sannan Umman ta maida kallon ta kan Mom ɗin, cikin salo irin na sarakai ta buɗe baki ta fara cewa "Barkanku da isowa, ya hanya? Fatan kun iso cikin aminci?" Sakin baki Mom tayi tana kallon ta, anya Maryama ƴar aikin ta wadda ke durƙusa wa a gaban ta ce wannan yanzu zaune a bisa kujera a gabanta kaman yanda itama take? Anya ita ce cikin wannan daula da tsantsar sarauta wadda zata iya cewa bata taɓa ganin irin ta ba? Saurin kumtsa ta kanta tayi, wanda Umman na lura da ita, murmusawa tayi, lokaci guda kuma ta shiga cewa "Lafiya Lau ya muka same ku?" "Alhamdulillahi, muna cikin Salama" Itama Umman tabbata amsa, tana mai Miƙewa ta shiga taka wa tana faɗin "Na barki lafiya, kici abinci ki huta zuwa anjima" Bata jira komai ba, ta idasa ficewa. Mom ji take yi kaman tayi hauka, komai ya idasa dagule mata, wani irin baƙin ciki tare da tsantsar hassada ne ƙarara ke cin zuciyar ta, ga asara ga ci gaban Umma da ta gani, ita dama tun cen ta tsani wani ya fita, ta fi so kullum ta kasance ita ce sama a kowa, Shiyasa tun tana yarinya kafin ma tabar ƙasar zuwa karatu kowa ke shan wahalar ta, duk wanda yake ƙasa da ita baya taɓa hutawa indai tana ƙasar. Ba yanda ta iya, ko abincin ma bata ci na wani kirki ba, bata jin idan zata iya daure ma zama gidan, ita fa tana jin idan dai har nan zasu kwana ita zata iya tafiya ta kyale su, tinda bata ga wani amfanin zuwan ba, to Amman saidai wani abu guda. Wanene wannan wanda ya santa har haka. Lokaci guda, kallo guda ya kama suna ta harda na mahaifin ta? A garin da bata san kowa ba, bata ma taɓa tunanin zata zo shi ba? Koma dai minene zata zuba idanu taga shin shi ɗin wanene haka??? ****** Na kira Layin shi sau kusan uku bai ɗaga ba, hakan ce ta sanya na tsara text massage na tura mashi . *_"Amincin Allah ya tabbata a gareka mijina, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, ina nan ina keearka, na ƙagara ka dawo inyi tozali da wannan kyakkyawr fuskar taka da kan ƙasa saka ni cikin kogin nishaɗi, na tanadar maka abubuwan da kafi so a Rayuwar ka, ina zaman jiranka habibi na, Allah ya dawo man dakai lafiya. Ina ƙaunar ka, Muah"_* Ashe ban sani ba, wayar ma tana cikin mota ya manta da ita, wajen rawar jikin ganin Baba Alhaji, ko yanzu da suke zaune suna dudduba abubuwa sosai a laptop ɗin barrister hankalin shi ya ɗauku, yama manta shaf da wayar a babin rayuwar shi, ashe bayan kasuwancin da Mom ɗin keyi, akwai wasu ɓoyayyun kasuwanci da mahaifin nata yake yi, wanda bata bar shi ba, ta ɗora daga inda ya tsaya, kuma ba tare da sanin mijin nata ko ƴaƴan nata ba. Ganin hakan ne ya sanya ni ɗan kwanciya ina mai lallasa waya ta, pictures ɗin da muka ɗauka, da na biki da aka tuttura mani nake kallo. Allah sarki Afnan da Hafsat, aseeya, Jiddo Raihana, Khadeeja. duk nayi kewar su, haka na fara binsu ɗaya bayan ɗaya ina kiran su. Raihana ce ma ke shaida man wai an fara lectures, yaushe zan dawo? Nake sanar mata cewa zan tuntuɓi Yayan nawa idan ya dawo. Zaulaya ta suka shiga yi, wai har yanzu amarcn bai ƙare ba, ni kuma na maida masu da cewa yanzu ma aka fara. Munsha fira dasu sosai, inda na kira Jiddo da aseeya suma muka sha firar mu gwanin ban sha'awa. Afnan kuwa ɗana kira ta, Firar Sir Salim kawai take mani, inda ta haɗa ni da Aunt Feena harma da su Ayan da Nasreem muka gaisa sosai cikin sakin jiki da jin daɗi. Faɗa man take wai Uncle ɗina ya iya soyayya, ita fa har ta ƙagara ta ganta a ɗakin shi, ni kunya ma ta bani, na dinga kyalkyala mata dariya. Ko da na kira Hafsat video ita mukayi, Munsha fira, har tana nuna mani samɓaleliyar yarinyar ta mai kyau, ga wayau kaman anyi suna, dayake an sallamo ta tana gida, suna kuma an ɗaga sai nan da sati biyu, Abunda ya sanya ƴan kankiyr tattara wa suka koma kenan, suna mai cewa idan an tashi sunan sun zaɓi wasu su wakilci su, ai ba sun tare anan ba, Kaka zuwaira ma ta tafi jiya bama nan, bamuyi sallama ba, banji daɗi ba, ina son tsohuwar ta shiga raina sosai, naso nayi mata abun alkhairi sosai. Wannan ce ta sanya na rage kaɗaici, duk da nake zaune ni kaɗai kwallin kwal. Wata ƴar matashiyar yarinya ce tayi sallama sashen namu, daga bedroom na fito ina mai amsa mata, ba zata wuce shekara sha biyu ba, itama ɗiyar wata sabuwar mai aiki ce da aka ɗauka, wai zata dinga taya Umma ta aikace aikace, duk da Ummata ta nuna bata ra'ayi, har yanzu dai shi Dad yana nan kan ba kanshi. Bayan ta gaishe ni ne har ƙasa take sanar dani "wai inzo inji Aunty Nihal don Allah" Nayi mamaki, Nihal kuma? To kiran me take mani? Yanzu fa ba da bane da zata kira ni naje, Amman koma menene ya kamata inje ɗin saboda inyi ma abun tufkar hanci. Ce mata nayi tace mata ina zuwa, inda na ɗauko samosa guda biyu cikin wadda nayi ma Ya Ameen na bata, saboda na fita haƙƙin ta, ko ba komai nasan taji ƙamshi. Fita tayi tana ta murna, inda na koma na ɗauko gyale na nabi bayan yarinyar. Har bedroom ɗin Nihal ɗin na shiga, tana cikin bargo naɗe tana latsa waya. Sallama kawai da nayi ta amsa da kyar, tana mai ɗagowa ta kalle ni cikin yamutsa fuska. *"Banana shake nake so ki haɗo mani"* Abunda ta iya cewa kenan ta maida kanta ga wayar tata tana cigaba da latsawa. Tsaye nayi ina kallon ta, ta raina ni ma wallahi, kenan da yarinyar tace don Allah, ita ce ta tausasa kenan? Haba no wander Nidai nayi mamaki wai Nihal tace mani don Allah, saidai in da wata manufar. Ɗagowa tayi tana mai watsa mani wani matsiyacin kallon. "Bakiji me nace bane? Ko ba hali ne?" Ga yara tsayuwa ta nayi, ina mai sakin wani killer smile. Lokaci guda na shiga cewa. "Ke baki san inda kitchen ɗin yake bane? Ko na fiki sanin hanyar? Wannan na daga cikin Abunda yake son kashe maki aure, kada ki manta ni fa yanzu yayar ki ce, ba da bane, na ɗauka ma kin kira ni ne akan na taimaka na baki shawarar yanda ake zaman aure da kula da miji? to ki sani a yanzu saidai ni in sanya kiyi mani, idan kin ƙiya kuma in sanya Yayanki ya sanya kiyi don dole" A zabura take kallo na, idan ranta yayi dubu to ya ɓaci, Suhan ce ke tsaye haka kanta tana watsa mata wannan kalaman masu kama da tafasasshen ruwan zafi? Ita har tayi ƙimar da zata iya koya mata zaman aure? Yaushe ma ta fara zaman aure? Ganin zata buɗe baki ta sake gaya man wata maganar na dakatar da ita cikin ɗaga hannu "Enough is Enough malama, ki kiyaye ko dan gaba, idan ba haka ba Rayuwar ki zata iya ɓaci". Ina gama faɗin haka na sanya kai na fice, ina mai ƙutawa da kyaci. Ta bala'n ɓata man rai, Amman idan nayi la'akari da kalaman da na faɗa mata, sai inga ai gara ma da akayi hakan, ko ba komai zata dinga yin shakkar shiga gona ta Ina ficewa ta sauko daga bisa gadon cike da bala'i. Dole ne ma wannan matsiyaci yar yarinyar ta fice ta bar masu gida, ita ce zata zo har ɗaki ta yaɓa mara magana kuma ta fice lafiya lau? A karo na farko kenan da ta karya billen ta ta shiga kiran Layin Nureen ɗin. Saida tayi mashi missed call goma kafin ya ɗauka. Murya cen ƙasa ya shiga ce mata. "Hello please who is on the line?" Cikin kwallo idanu ta shiga cewa Baby baka gane mai magana bane? Kayi deleting ɗin number ɗita ne? "Owh Nihal akwai matsala ne?" Kuka ta fashe mashi dashi "Baby kazo ka ɗauke ni please, yanzu na iya komai kuma zan dinga yi maka komai please" "Hold on Nihal, yanzu am very busy we'll talk later on" yana gama faɗin haka ya katse kiran. Cikin kuka ta cire wayar a kunnen ta, tana bin wayar da kallo, kaman mai neman gano fuskar babyn nata. Sudat ta kira, ita ce abokiyar yinta, domin tasan ta kira Aunt Feena ƙaniyar ta zata ci sosai, to balle oga uban gayya Ya Ameen da baya ɗaukar wargi ko kaɗan. Saida tayi kukan ta mai isar ta Saudat ɗin na bata haƙuri, sannan ta faɗa mata Abunda Suhan da Nureen suka yi mata, itama bata ji daɗi ba, Amman tace ta shirya tazo gidan ta same ta zasu san abun yi, ita tana tsoron tazo su haɗe da Dad. "Aunt Saudat Mom fa bata nan, wai sun tafi gidan su Umman Suhan ita da su Dad da Uncle Alhaji" Cikin tsananin mamaki da ɓacin rai Saudat ɗin ke cewa "Me suka je yi ne, ita mom me ya kai ta? Ta sani fa sarai mutanen nan ba ƙaunar mu suke yi ba, ki duba kiga yanda suka raba mu da Dad, Amman shine ta kama ta bisu" cewa saudat. Cikin mamaki Nihal ɗin ke cewa "Ke Aunt Saudat baki san meke faruwa ba wai?" "Me ya faru ne Nihal tell me now" itama ta faɗa cike da yatsina. "Uhmm ke dai bari inzo kawai maganar bata yuwuwa a waya, Amman saidai nazo kawai, Mom na cikin wani hali ashe baki ji ba" saurin katse wayar tayi tana mai tashi ta zari yalolon gyalen ta, haɗi da ɗaukar makulli motar ta ta fice. Ni kuwa jin zuciya ta sakayuu nake yi, ko ba komai nima na fara rama wani kaso daga cikin irin wulaƙancn da na fuskanta daga wajen Nihal, bana ƙullatar su, saidai ya zuwa yanzu ba zan iya jure wulaƙanci irin wanda na Ɗauka ada cen baya ba, lokacin da ina ƙarƙashin su. ****** Sun jima sosai suna aiki, sannan sai ga Baba Alhaji ya dawo, tun da yaga Al'ameen fuskar shi ta yalwanta da murmushi, yayi tsammanin ganin wani daga cikin gidan dama, saidai bai tsammaci ganin Al'ameen ba, ya ɗauka ko Alhaji Mustapha ɗin dama ko ita kanta Hajiya Kubra ɗin. Bai ɓoye mamakin shi ba yake tambayar shi Dad ɗin nashi bayan sun gama gaisawa a mutumce. Ba tare da kawo komai a ran shi ba, ya shiga shaida mashi inda suka tafi tare har da Mom ɗin tashi. Ƴar fara'r dake kan fuskar shi ce ta ragu,yana gyaɗa kai a hankali, sai kuma ya gyara zama yana mai fuskantar a Al'ameen ɗin, tare da son jin dalilin zuwan nashi. Bayan ya gama zayyana mashi komai, sannan ya buƙaci jin ƙarin bayanin wasu bayanai da kaf duniya daga wajen Baba Alhajin ne kawai yake sa ran jin su. To saidai kalaman da Baba Alhajin ya faɗa mashi su ne suka sabbaba ɗaukewar numfashin shi, tare da bugawar zuciyar shi na wucin gadi. Da kyar ya lalubo numfashin nashi, yana mai ƙura ma Baba Alhaji idanun da ya zuwa yanzu idan ka kalle shi zaka iya cewa garwashin wuta ne aka ɗebo aka watsa mashi a ciki. Idanun nashi har sun fara tara kwalla, ji yake kaman kanshi zai tarwatse, me kalaman Baba Alhajin suke nufi? *"Al'ameen ina so ka natsu ka saurare ni, kuma ka fuskanci inda na dosa, a zahirn gaskiya batun da kazo mani dashi na son sanin wasu muhimman bayanai da kake son sani daga gareni, dangane da harƙallolin mahaifiyarka da kuma ita kanta asalin dukiyar, duk da ka tabbatar da cewa gadarta tayi daga wajen mahaifin nata marigayi, abu ne mai wuyar gaske, da zaka ji shawara ta ma, da sai nace kabar batun nan kawai zaifi, kada kaje ka bankaɗo wani sirri, wani ƙulli, wani mugun dakwaye mai warin gaske, da zai yi silar tarwatsewar farin cikin ku gabaki ɗayan gidan ku, da kuka daɗe kuna ginawa kuma kuna rayuwa acikin shi tsawon shekara da shekaru"* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~72~* *Ina fatan za'ayi haƙuri da ji na shiru da akeyi kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon ayyuka da suka sha man kai, haɗi da hidindumun wannan rayuwar da basu ƙarewa. Allah yayi mana muwafaƙa, ina jin daɗin Addu'oin ku, Oum Deedat tana yi ku over. A cigaba da gashi...* Falalar Salati Ga Annabi, Tsira da Amincin Allah Su Tabbata A gare shi Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Wanda ya yi salati daya a gare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi". Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Ka da ku mai da kabarina idi, ku yi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko a ina kuka kasance. Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba. Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce, Allah yana da wadansu Mala'iku matafiya a bayan kasa, suna isar mini da sallama daga al'ummata. Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa". °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Ya kai kusan minti biyar kanshi na a duke, jujjuya maganar Baba Alhaji yake yi a tsanake, ya gaza tsintar ma'anar ko kalma ɗaya, wannan wane irin ƙullin dakwaye ne haka mai mugun wari? Me Mom ɗinshi ta aikata ne har haka? Jin kanshi yake kaman zai tarwatse, ni kaina da nake laɓe ina kallon su, ba zan iya tantance irin yanayin da ya shiga ba. A hankali ya shiga ɗago kan nashi, yana mai ɗora idanun shi tsaf bisa fuskar Baba Alhajin da yake zaune, wani irin tausayin Al'ameen ɗin na kuma kama shi. Baki ya buɗe da niyyar cewa wani abu, Baba Alhaji yayi saurin dakatar dashi, ta hanyar ɗaga mashi hannu. "A'a Muhammadu Ameen, kada kace komai, na sani kai yaro ne mai biyayya, saboda haka ne ma tun haihuwar ka nake maka kallon Kabeeru gashi nan zaune, banso kaji wani abu daga baki na ba, sannan nayi murna da ka sanar dani cewa Alhaji Mustapha watau mahaifin ka, da Hajiya Kubra, mahaifiya gareka sun nufi garin Adamawa. Saidai zan so ka ƙkara sanya ma zuciyar ka hakuri da juriya kaman yanda na faɗa tun farko, abubuwa na ban mamaki da al'ajabi, ban haushi da tausayi zasu faru, Amman ina so ka sani har gobe ita ɗin mahaifiyarka ce, biyayya gareta dole ne kuma tilas ne, kaine kawai zaka zame mata ƙarshen ƙwarin guiwar ta, a yayin da kowa zai iya juya baya gareta, kada ka sake ka barta, kada ka sake ka nisance ta, ka kasance tare da ita a koda yaushe. Idan kuma har kaga na sanar dakai wani abu, to cikin ɗayan biyu, imma dai su mahaifan naka ne suka so ka san hakan, imma an kira wo mu ne ni dakai zuwa ga masarautar" Baba Alhajin ya ƙkarashe maganar tashi yana mai nisawa, tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tashin hankali!!! Da sauri ya dafe kanshi dake jujjuya mashi, ji yake kaman ana hajijiya dashi, me Mom take aikatawa har haka da Baba Alhaji yake iƙirarin kowa zai iya juya mata baya??? Baisan lokacin da ya tashi tsaye ba, ba tare da yace da Baba Alhajin komai ba ya nufi ƙofa, cikin sauri Baba Alhaji yace ma Barrister Kabeer "Maza kaje ka kai shi gida Kabeeru, sannan ka ce ma da matarshi ta kula dashi sosai, dole ne nasan wannan ranar zata zo, saidai koma menene ina fatan yazo da sauƙi" Da hanzari Barrister ya mike har yana sassarfa. Bayan Al'ameen yabi, ba tare da yace da Baba Alhajin komai ba shima. Cen ya hango shi yana tafiya yana haɗa hanya, kaman zai kife, da saurin shi ya ƙara sa yana mai ce mashi "Yallaɓai kawo makullin motar ko?" Miƙa mashi yayi ba tare da ya ce dashi uffan ba, yayin da ya kama shi yana mai zagayawa kujerar mai zaman banza, ya buɗe ya zaunar dashi, ya koma driver seat ya zauna, yana mai yi ma motar key. Gudu yake sosai har kawo lokacin da ya isa ga ƙkofar gidan, da gudu Idi ya buɗe mashi gate ya shige. Ya Ameen kasa fitowa yayi, gani yake kaman dama kowa yasan laifin mahaifiyar shi, kowa kallon su kawai yake a ɗage, zaune yake kawai kaman mutum mutumi. Barrister wajen da Idi da Iro suke zaune ya nufa, yana mai cewa dasu suzo su taimaka mashi. Da hanzarin su suka taso, inda har Ya Ameen ya ɓalle murfin motar ya zuro ƙafafun shi. Sallame Sallah ta kenan, ina zaune wurin dai kawai ina ta addu'oi na sosai na neman zaman lafiya da miji na, da sauran duk wanda Allah ya haɗa ni zama dashi. Naji ana ta ƙiƙirniyar shigowa, da sauri na miƙe ina mai shafa addu'ar, hannu na ɗauke da casbaha ina ja. Falo nayo, cikin salon tafiya ta, fuska ta ɗauke da maɗaukakin murmushi, so kawai nake nayi arba da gwarzon nawa, abun so na da alfahari na. Daga baƙin ƙofa ƙafa ta ta ƙage, na kasa cira ta in cigaba da tafiya, hangowa da nayi an shigo da Ya Ameen a rirriƙe, duk da yana iya takawa da ƙafafun shi. Har kai lokacin da suka zaunar dashi bakin sofa, suna mai gaishe ni suka juya suka fice, in ka ɗauke Barrister shima da ya zauna wata kujera mai kallon ta Ya Ameen. Da addu'a ta da komai na samu na cira ƙafa ta, ina mai takawa cikin sauri na nufi inda Ya Ameen yake zaune dafe da kai sosai. Gaban shi na zube ina mai cewa "Ya Ameen lafiya kuwa!? Me ya same ka!? Kayi man magana mana please, " Barrister me ya samu Yayana don Allah!?" na faɗa ina mai maida akalar tambayar ga Barrister da yake zaune, idanu na har sun kawo ruwa, gab suke da zubowa. Zaman shi Barrister ya gyara, yana mai fuskanta ta. "Nooo Suhan, ba wani abu bane babba, kin dai san yanayin jikin nashi, so dole ne ki kula dashi sosai, kada ki tada hankalin ki, saboda muna so dole ne sai kin taimaka wajen kwantar mashi da hankali, yana tattare da damuwa ne, shine kawai, Amman kiyi ƙoƙarin ganin kin samo kanshi please" shima ya faɗa cikin son kauda mani zargin wani abu, saboda baya da masaniyar ko nasan abunda ke faruwa. Ni kuwa har kwalla ta ta fara gangarowa, na juya ina mai kallon Ya Ameen da ya wara idanun shi a kaina, yana mai girgiza man kai a hankali, alamun kada nayi kuka. Hannun shi ya miko gareni, alamun in taso kusa dashi, ba musu na kama hannun ina mai miƙewa zuwa bisa kujerar kusa dashi, ganin hakan da Barrister yayi, ya sanya shi miƙewa yana mai faɗin "Na barku lafiya amarya, idan da wani abu please kiyi gaggawar sanar dani, ko wani na kusa" ya faɗa yana mai takowa zuwa gaban Ya Ameen ya miƙa mashi hannu sukayi musabaha. Da kyar Ya Ameen ya iya buɗe baki yana mai cewa dashi "Nagode Barrister, zamuyi magana zuwa anjima" "Take care" Abunda Barrister kawai ya faɗa kenan yana mai juyawa ya fice. Da yatsan shi yayi amfani wajen ɗauke man wani sabon kwallar da suka gangaro. "Kukan na menene wify?" Ya faɗa cikin ƙarfin hali, a ƙoƙarin shi na son kauda mani tawa damuwar Kaina na kwantar zuwa bisa kafaɗar shi, ina mai sakin shagwaɓa a hankali nake cewa "to ba kai bane?" murmushi yayi shima kaɗan yana mai shafo gefen fuska ta. "Nine me?" ya bani amsa shima, "Kaine mana, kasan baka lafiya ka fita a haka, gashi tun ɗazu nake jiran ka dawo kaci abinci, na kira ka kuma baka ɗauka ba, na maka massage ba reply, Haba dear" na kuma ƙarashewa cikin wata shagwaɓar. Ƙoƙarin zare man hijab ɗin dake jiki na yayi, yana mai sakin murmushinƙkarfin hali a hankali a hankali. "Ya isa hakanan to, ba gani na dawo ba? Dan dai salon shagwaɓa da sakata kawai, ga wata hijab da kika ƙaƙaba a cikin gida, kaman...." shima ya faɗa yana mai kashe man ido guda. Taimaka mashi nayi wajen zare hijab ɗin, ina mai cewa "Tun da na gama salla ne ai dear sai ban cire ba" nima na faɗa cikin jin daɗin yanda naga ya ɗan saki jiki, alamun sauƙi na samuwa. Shi kuwa Ya Ameen ta ɓangaren shi, ƙarfin hali kawai yake, gudun jefa ni cikin wata damuwar, tinda gashi har kwalla na fara, daga ganin shi cikin wani yanayi, ya kula ma dai kwallar bata yi mata wahala, kaman wata ruwa-ruwa. "A taimaka man da ruwan wanka, daga nan sai inyi alwala, idan na gabatar da sallar sai...." "Kaci abinci ko dear, nasan dai kana jin yunwa" na katse shi nima cikin murmushi, haɗi da jan dogon sirirn hancin shi, ina mai miƙewa na ɗauki hijab ɗita, na wuce kai tsaye zuwa bedroom, cikin murmushin da nasan yafi ƙauna daga gareni. A bakin ƙofa na tsinci cesbaha ta, ashe nan na yarda ita. Duƙawa nayi na ɗauka ina mai murmusawa na wuce zuwa cikin ɗakin. Ta bayan ta yake binta da kallo, komai nata a nutse yake, shi ya ma manta da wata aba wai ita yunwa, ƙalubalen da yake gaban shi, ya tabbata da baya da aure zai iya yin tsawon kwanaki, ba tare da ya kai ko spoon ɗaya a bakin nashi ba. A hankali ya miƙe zuwa waje, ɗauko wayar shi yake so yayi, sai yanzu ne ya tuna da wayar na cikin mota ashe. Da gudu su Iro suka taso suna masu yi mashi ya jiki,hannu kawai ya iya ɗaga masu ya buɗe murfin motar ya zura kanshi ciki da niyyar ɗauko wayar. Har ya ɗauko ya fito ya kulle motar, sai a lokacin ne ya kula da Iro da yake tsaye ta bayan shi. "Lafiya dai ko? Malam Iro?" Abunda ya Ameen ɗin ya iya cewa dashi kenan kawai. Shi kuwa Iro duƙar da kai yayo yana mai sosa ƙyeya da hannu, alamun kunya. Murmushi Ya Ameen ya saki, cikin kulawa ya shiga ce mashi. "Malam Iro kayi magana mana, daga ni fa sai kai ne a wurin, kunya ta kake ji? Ina fatan ba dai wata matsala ko? Idan da matsala, kayi haƙuri idan zan fito anjima sai in ganka" Sake duƙar da kai Iro yayi yana murmushi "Ranka ya daɗe ba wata matsala bace, kawai dai ina so ne muyi maganar Maree ne dakai, gaskiya ina neman da a bani auren ta, kaf duk duniyar nan babu wadda nake so da aure in ba ita ba" Maganar Iron ta bashi mamaki, har saida ya bayyana a fuskar shi, lokaci guda kuma ya shiga murmusawa. Ya Ameen kenan, mutum mai farin hali, farar zuciya, da farar fata. Komai nashi shi daban ne. "Malam Iro kenan, to ai ina ganin ba ni ne ya kamata ka samu da wannan maganar ba, ita yarinyar da mahaifiyar ta zaka samu, idan sun amince ne, sai ka neme mu daga baya, abu yayi kyau ina taya ka murna sosai fa" Ya ƙarashe yana mai dafo kafaɗar Iron, sannan ya ja shi suka fara takawa. Abunda ke burge kaf ma'aikatan gidan kenan dangane da Ya Ameen ɗin, shi mutum ne mai sauƙin halin da yake zaune da kowa lafiya, idan har Kaga fushin shi, to fa ka aikata abunda yake ba daidai bane. Cikin jin kunya Iron ya shiga cewa "To Yallaɓai, insha Allah zan tuntuɓe ta, wallahi na kasa ne tun tuni, Kunyar ta nake ji Shiyasa" Dariya sosai yaba Ya Ameen, har saida fararen haƙoran shi suka bayyana. Ikon Allah kenan, wai Maree da take hauka kanshi, ita ce yau Iro shi kuma ke cewa yana so. "Ya kamata ka ƙoƙarta malam Iro" ya faɗa shima yana mai zaro kuɗi daga cikin aljihun shi, ya damƙa su ga hannun Iron, kuɗi ne masu yawa "Ga wannan ba yawa kuyi haƙuri, kaje ku raba kai da Idi ko?" ya faɗa yana mai sakin hannun. Cikin tsantsar murna da farin ciki Iron ya shiga godiya, kaman zai duƙa ma, Ya Ameen ɗinne yayi saurin taro shi. "Ba damuwa kaji ka ƙoƙarta dai, ina sauraren ka" shima ya faɗa yana mai jufar cikin sashen nasu. Ni kau ina fitowa falon na tadda ba kowa ciki, kitchen na leƙa nan ma bai nan, ƙofar sashen namu na nufa, aiko na hango shi cen tsaye da Iro bakin mota, sai kuma naga ya saƙalo kafaɗar Iron sun shiga takowa. Murmushi nake sosai, watau Ya Ameen baya ƙyamar talaka, baya ƙyamatar masu aiki, jibi yanda ya haɗo jiki da Iro don Allah kaman wani abokin shi. Tun kafin ya ƙaraso inda nake tsaye, yake sakar man wani irin killer smile, nima murmushin nake mashi, inda ya shiga wara man hannayen shi alamun in taho. Ganin ana iya hangen mu, sai na shiga noƙe mashi kafaɗa alamun a'ah, turus yayi inda yake tsaye, shima yana mai noƙe man kafaɗar alamun a'ah shima sai na taho. Wayar shi ce dake hannun shi ta ɗauki ringing. Bilal ne. A hankali ya ɗaga, yana mai cigaba da takowa suka fara magana da Bilal ɗin. Sanar mashi yake ya iso yaje ya ɗauko shi. Inda shi kuma ya shiga sanar mashi cewa wanka zaiyi yanzu, idan zai iya jira. Bilal ɗinne yace bari ya hawo taxi kawai. Yana ƙarasowa inda nake tsaye ya damƙo hannu na yana mai jana, haɗi da ce man "Muje ki taya ni wankan Mrs Al'ameen Dambulan" Bance mashi ƙala ba, na shiga bin shi, har saida muka isa wajen hanyar kutchen, na zare hannun nawa, na kwasa da gudu zuwa cikin kitchen ɗin ina mashi gwalo. Biyo ni yayi da gudu shima, saidai kafin ya ƙaraso na maida ƙofar na kulle, na jingina baya na da ƙofar ina mai sulalewa nake sakin dariya sosai. Shima dariya take sosai, watau so take ta mantar dashi damuwarshi, abunda bata sani ba, damuwa ce wadda ba yanda zaiyi ya iya mantawa da ita, har sai komai ya warware. Shi abunda yafi komai ɗaga mashi hankali ma shine, kalaman Baba Alhaji da yake cewa wai tafiyar Mom da Dad ɗin nashi, zasuyi sababin faruwar abubuwan ban haushi ɗana al'ajabi. To meye alaƙar Mom da masarautar Adamawan? Wanda zai iya iƙirarin cewa Mom ɗin tashi bata taɓa taka garin ba? Duk yawa ce yawancen ta bata taɓa yin cen ba, duk kuwa da cewa tasha faɗa mashi cewa tana so taje, lokutta da dama idan yana bata kabarin ƴan gudun hijiran dake wurin. Murya sosai ya ɗaga yana mai ce mani "Kina nufin wayau kika yi mani ko? Zamu haɗu ne ai" ya faɗa yana mai wucewa kai tsaye zuwa ɗakin. Ya daɗe yana cuɗa jikin shi, ba don komai ba sai don tunani da ya tsunduma, bai ankara ba sai yaji ruwan zafin dana daidaita mashi sun ƙare, saidai na sanyi suka fara zubowa. Ba arziƙi ya ɗauraye jikin shi ya fito, bisa gado ya tadda kayan da na fddo mashi na sanyawa. Saida ya gama shiryawa ya fito,yayi kyau sosai, tun da kaya ne masu sauƙin nauyi, da kuma kyau. Already ya tadda har na haɗa table. Ko zama baiyi ba Bilal yayi sallama. Da sauri suka nufi juna suna masu rungume juna, soyayyar su daga Allah ne, ji suke kaman sun shekara ɗari basu ga juna ba Ina fitowa daga kitchen ɗin na tadda su zaune bisa table ɗin, kowa yayi ready ɗin plate ɗinshi, da gani shima Bilal yunwar yake ji. Da murmushi na ƙaraso ina mai gaida Yaya Bilal ɗin, ina mai tambayar shi ya bomboy da mai jego. Shima Ya Ameen ɗan zaulayar shi yake cikin wasa wai angon jego, gashi nan ai sai ƙarni yake yi. Dukan mu dariya mukayi, inda suka natsu suna mai cin abincin su, jefi jefi suna fira gwanin sha'awa. Ni kuwa ɗaki na wuce, naje na sake gyaggyara komai. Ina mai ɗauko wayata na cigaba da karatun littafi na *Aminta* na Sumayya Babayo. Littafin ya tafi da imani na, gani nake yi kaman gaske ne, labarin ya tsaru ya ƙayatar dani, da zan iya samun number ɗin marubuciyar, to da ina jin babu abunda zai hana ni kiran ta. Ina zaune bisa stool ne Ya Ameen ya shigo dafe da ciki. Ina ganin shi haka ne, na fashe da dariya, nasan zaulaya yazo yi, ni kaina lamarin Ya Ameen na bani mamaki. Kaman mai iskokai. Yanzu zaka ganshi a birkice, yanzu zaka ganshi a daidai. Duk da nasan ƙoƙarin shi na kada in sanya damuwar shi a raina. Bai sani ba, duk wani motsi nashi a ankare nake dashi, ko bai faɗa man ba, nasan musabbabin damuwar, masalan ma ɗana ganshi da Barrister ɗazu. Wannan ce ta sanya nibduƙuda yi mashi addu'a ba dare ba rana, ita ce kawai irin gudunmuwar da zan iya bashi, kaf faɗin rayuwar tawa, sai kuma ƙoƙarin kwantar mashi hankali da nake yi. Baice ƙala ba, ya iso inda nake, yana mai tsayawa kusa dani sai kuma ya buɗe baki da kyar yace mani "Akwai chewing gum a gidan nan kuwa?" Dariya na kuma yi, ina mai miƙewa na sauke hannun shi ƙasa, na ɗaga rigar tashi, cikin kuma ya ɗan ɗago ba laifi, gaskiya yaci abinci, wanda kuma ni haka nake so. Girgiza kai na shiga yi, sai kuma nace "Babu Yaya, saidai idan in aika a nemo maka" girgiza kai ya shiga yi, sai kuma ya gyara tsayuwar shi, yana mai faɗin "Fita zamuyi ni da Bilal, sanyo hijab ɗinki mu ajiye ki wajen Hafsat" Ai sai na shiga tsalle, cikin jin daɗi nake cewa "da gaske yaya?" Kano hannu na yayi da sauri "Ke! Akwai babies ɗina fa a nan ciki, kada ki ja mani asara" ya faɗa yana mai shafo ciki na. Ku ya ya bani sosai,duka ma yaushe akayi daren, balle gari ya way? Ai ko kula shi banyi ba, cike da kunya na zare hannun ina mai wucewa na zura hijab ɗita. Da kallo yake bina cikin sha'awa. Komai nayi burge shi yake, yana son gani na cikin walwala a cikin gida nashi, baya so nake zaman kaɗaici, kuma yasan idan ya fita zai jima, shiyasa yake so ya ajiye ni gidan su Hafsat, idan zai dawo kuma sai ya biya ya ɗauko ni mu dawo gida. Hannu na ya kama, yana mai juyawa muka fice, saida muka kukkule ko ina, sannan muka fice, Ya Ameen da Bilal na gaba, ni ina baya, da wai Ya Bilal ɗin baya zai shiga, nice sai da na kusan nuna ɓacin rai sannan ya barni na zauna baya, Haba ai da kunya wallahi, ina ma zan iya, kenan na raba ƙaunar dake tsakani ta tun yarinta. ******* Su ma saida suka shiga suka ga Hafsat da babyn ta mai kyau, sannan suka wuce. Hajiya Zainab ce naji tana ta zuba ma Ya Ameen godiya sosai, da alama wani alkhairin yayi masu, to dama halin shi ne baya gajiya, Shiyasa komai zai zo mashi a rayuwa yake zo mashi da sauƙi, saboda Allah baya ƙyale irin su su wulaƙanta,ko ba komai kullum cikin addu'oi yake, da kuma fatan alkhairi daga mabanbantan ba kuna. Fatan mu dai Allah ya amsa bakin nasu. Nan fa muka dasa babin fira da Hafsat, gidan fa ba laifi masha Allah, hada ƴan uwan sadeeq ɗin suna gidan, mutane wayayyu, ga ilimi sosai gasu basa da wulaƙanci. Duk da suma kaf ƴan uwan Hafsat ɗin haka suke, hatta da matar Aleeyu itama tana gidan, da goyon ta kuwa ya ɗan tasa mai sunan Alhaji Isuhu suna ce mashi Junior Alhaji. ****** Cikin tsantsar rashin hankali Saudat ke kallon Nihal. "Me? Nilah kinsan me kike cewa kuwa? Ina Aunty Laila ɗin yanzu?" Kafaɗa Nihal ta sauke, "Oho masu, wama ya sani? Ni fa banga abun tada hankalin Mom akai ba, ko Ya Ameen wallahi yana iya maida mata asarar ta, ni ba wannan ce ta dameni ba, kawai ya kamata su tsaya ayi maganar baby, don wallahi ni fa na fara gaza haƙuri, aunty Saudat baki ga irin wulaƙancn da Baby yayi mani ba ɗazu, kaman fa bai ma sanni ba" ta ƙarashe cikin damuwa. "Ke dalla wuce nan, ke wace irin yarinya ce wai? To bari kiji, wallahi kina da kyau da ilimi da dukiyar da ko yanzu kika rabu da Nureen zaki samu wani wanda ya fishi, ni kinma bani haushi, da har zaki tsaya wani namiji na ɓata maki rai a banza, ni kin ganni nan? Wallahi bana jiran komai daga hotty, Shiyasa na zauna lafiya, in ma kewa ce, akwai da dama waɗanda suke ɗebe man ita, Shiyasa yanzu na dena wahalar da kaina ma wajen bin shi wata ƙasar" Da mamaki Nihal ke kallon Saudat. "Me? Aunty Saudat ɗebe kewa fa kika ce? Da auren naki? Subhanallah, gaskiya ni bazan iya ba, Baby kawai nake so, da shi kaɗai zan iya rayuwa" Itama cikin jin haushn maganar Nihal tace "Ke daɗi na dake baki idasa wayewa ba, hakanan kike ganin kanki a wayayya, shiyasa gashi kina zaune wata banzar villager tana gaya maki magana, yarinyar da take matsayin ƴar aikin mu har yanzu..." "Aunty Saudat lallai na kula kin manta waye Big Bro, yanzu kinga yadda wannan yarinyar ta ƙara wayewa ta Faso gari? Yaya fa ya kama mata kan steary ɗin. Shiyasa take juya motar yanda take so, kuma yanzu hankalin Mom ba a kanta yake ba, amman ina mai tausaya mata duk ranar da Mom ta waiwayo ta" ta katse Saudat ɗin daga maganar da take yi. "Kice sun mallake gida, sun mallake Dad da Ya Ameen ai sun gama da gida kenan" itama Saudat ɗin ta bata amsa, cikin zaro idanu, da jinjina maganar da take ji daga bakin Nihal ɗin. Gyaɗa mata kai Nihal ɗin tayi, tana mai cigaba da latsa waya, tana mai taɓe baki. "Akwai dabara" cewar Saudat ɗin. Da mamaki Nihal ɗin ta ajiye wayar ta juya tana mai kallon ta. "Dabara fa kika ce Aunt Saudat, wace iri kenan?" "Matso kiji" cewar Saudat. Kunnen Nihal ɗin ta kama ta raɗa mata wani abu. Dariya suka sanya su duka, suna mai tafawa suka kashe sosai "Idan mukayi haka kina ganin ba za'a gano mu ba? Kinsan fa Yaya Akan wannan shegiyar Yarinyar" "Dole duk yanda zakiyi kiyi Nihal, kina ganin yanda kika ce ta yaɓa maki magana fa ɗazu, to wallahi idan ba haka kika yi ba, ba zata shafa maki lafiya ba, kuma taga makwancin ki kenan" cewar Saudat, tana mai ɗaukar cup ɗin da yake cike da mixed fruit ta kurɓa. "Haka za'ayi My Aunt, bari kiga in miƙe in koma gidan da wuri, domin in fara shirye shirye" Har bakin mota Saudat ta raka ta, tana mai sake faɗa mata yanda zata tsara abunda suka ƙulla game da Suhan ɗin ya tafi daidai... (Nace ta Allah ba taku ba, mutanen kawai) ************* Wayar ta kawai take lallatsawa, Allah kaɗai yasan ko me take y. Jir a kawia take wani ya shigo ta sanarmashibcewa tana son ganin mai gidan nata, saboda ta kikkira wayar shi bata shiga. Ikon Allah yau take ta kallo, jin kanta take kaman a akurki, gaskiya ita bata ga dalilin zuwa a ajiye ta anan ba. Tana cikin wannan tunanin ne, sai ga wata haɗima ta shigo, tana mai russuna mata, take sanar da ita saƙon mama Fulani. Bayan ta ta shiga bi har babban falon Mama Fulanin, har ciki tayi mata rakiya, inda ta tadda sauran matan sarkin. Sai Umma da take gefe zaune. Zama ne irin na sarauta, kowa na jin kanshi a sama, Amman duk da haka idan suka haɗu da Mama Fulanin dole suke yin laushi. Gefe bisa wata shinfiɗa akayi mata masauki, ita dai sai ikon Allah take kallo, komai na sarauta daban ne. Mama Fulani ce ta muskuta a hankali tana mai gyara muryar ta, sannan ta fara magana. "Barkan ki da zuwa masarautar Mai Martaba, Muhammadu Barkindo Lamiɗo, haƙiƙa wannan masarauta taji daɗin wannan ziyarar taku, a matsayin ku na surukai ga mai sunan mai babban ɗaki, haka kuma iyaye ga mai sunan mai babban ɗaki, kuma abokan zaman hasken masarauta, waɗanda kuma suka jajirce wajen ba ma hasken masarauta kariya, a lokacin da take ba'a ƙarƙashin kulawar masarauta ba. Haƙiƙa masarauta ta jinjina ma wannan namijin ƙoƙarin naku, kuma kunzo a daidai, sakamakon kira da kuka amsa na mai martaba, da haka ne nake sanar maki da cewa, zuwa anjima kaɗan zamu amsa kira daga wajen mai martaba ɗin, inda za'a tattauna abubuwa masu muhimmanci, muna fatan zaki bamu haɗin kai? ". Kaman mutum mutumi Mom ke kallon su, ikon Allah, wannan tsara magana haka har ina? Lallai sarauta daban ce. Murmusawa tayi cikin wayancewa ta shiga faɗin" Insha Allah babu wata damuwa, Haba ai wannan ba wani abu bane, nan ɗin fa kaman gidan mu ne" Mama Fulani taji daɗin maganar tata, inda itama ta murmusa tana mai jinjina kai, sannan ta fara gabatar mata da sauran matan sarkin. Inda suka sake gaggaisawa cikin mutumci. A sace take kallon Umma ta gefen ido, inda take kishingiɗe gefe tana mai jan casbaha, har yanzu ibadar ta tana nan, ga rashin son magana, kaman yanda ta santa da. Har kai lokacin da jakadiya ta shigo, bakinta ɗauke da saƙon sarki, cewa an ɗaga taron tattaunawar har zuwa gobe da safe, inda ta kuma shaida mata cewa sarki yana ganawa da baƙin shi ne. Hakan ce ta sanya, saidai aka maida Mom ɗin ɗakin da aka bata, tare da wadata ta da dukkan abubuwan da aka san zata buƙata, aka kuma bar mata haɗimai guda biyu, ko zata buƙaci wani abu. ********* Yana zaune bisa carpet ɗin da yake malale tsakiyar falon, ya barbaza litattafai, fuskar shi sanye cikin farin gasa na ƙara gani, yayi kyau sosai, hankalin shi kwance, tun da ma'u tabar gidan, sai ya jishi tsit, kuma har kawo yau ɗin nan bai nemeta ba, itama bata neme shi ba, ba yanda Ammi batayi ba akan yaje wajen matar tashi. Amman abu ɗaya yake sanar mata a kullum. "Bai kore ta ba, da kanta ta bar gidan, saboda haka da kanta zata dawo idna taso" Bubbuga ƙofar falon yaji da ƙarfi cikin tashin hankali, kaman za'a ɓalle ƙofar falon. A hankali ya zare glass ɗin, yana mai miƙewa ya nufi ƙofar, ya murza key a hankali ya buɗe. Tsaye suke su uku, bayan su wasu maza ne manya sosai dasu, majiya ƙarfi, girgiza da jijjiga jiki suke yi, cikin wani irin yanayi, da zai nuna maka cewa basu zo da lalama ba. Ya sansu farin sani. Dukan su ukun yayyen Ma'u ne. Sam basa da hali, abubuwa da yawa da Ma'un kan aikata, aikin zugarsu ne, basu ɗauki kowa da daraja ba, hakan ce ta sanya gabaki ɗayansu zawarci suke, in ka ɗauke guda ɗaya da ta mallake mijin da ƙarfi da yaji. To haka suka so Ma'un tayi a gidan Sir Salim ɗin, shi kuma ya nuna mata cewa shi namiji ne, ba zai taɓa bada wannan ƙofar ba. "Malam Salim munzo kwasar kaya ne" Cewar ɗaya daga cikin su, tana magana tana wani girgiza jiki. Gyara tsayuwar shi yayi, yana mai faɗin "Kaya kuma Yaya Luba? Wane irin kaya kenan?" "Kayan Ma'u mana" Itama ta bashi amsa, cikin tarar numfashin shi. Shiru yayi bai ce komai ba, fuskar nan tashi murtuk, dole ne yayi ma abun tufkar hanci, saboda ya kula lamarin yazo da matuƙar rainin hankali. "Ta kwashe kayan sawarta ai, ko bata faɗa maku ba?" Shima ya faɗa, yana mai ƙoƙarin maida ƙofar ya rufe. "Kaga malam ba magana muka zo mu maida ba, kayan ɗakin ta muka zo kwasa, ai kasan me muke nufi, dan haka ka bamu hanya kawai" Ita ƴar zaƙal ɗin da ya kira da Yaya Luba, ta sake faɗa, tana mai sanya hannu ta tokare ƙofar, daga kulle tan da yake neman yi. Fasa kullewa yayi, yana mai buɗe ƙofar sosai. Sai kuma ya tako sosai zuwa gaban su, bai ƙasa a guiwa ba, ya shiga cewa" To Yaya Luba ina jin dai kun manta cewa kayan dake gidan nan kaf nawa ne, ko kun manta lokacin da kuka sanya ta ta saida kaf kayan da aka kawo mata? Kuka ce mijin ta ai yana da kuɗi ya zuba wasu? Na kuma zuba, ban saurare ku ba? Yanzu shine zaku wani zo mani da masu kwasar kaya? Ku kwashi me? Ina mai gargaɗin ku, duk wanda ya sake ya shigar mani gida wallahi sai na kulle shi, har igiya tayi rara. Kuje ku sanar da ita Ma'un cewa tazo da kanta, idan har bata da kunya. Ba nine nace ta tafi ba, don haka ba zance ta dawo kuma ba, taje tayi ta zama, gidan ma yafi daɗi a haka, saboda haka idan ta gaji da yawo da igiyar aure na akanta ta dawo. Aure ne kuma ku sanar da ita yanzu ma na ɗaura ɗamba, ba fashi insha Allah." Yana gama faɗin hakan ya juya ya shige, yayin da ya bar masu ƙofar buɗe. Zage zage suka fara yana jiyo su, kaf ɗinsu ba ƴaƴan Arziƙi bane, saboda haka shi ba zai biye masu ba, idan sun cika marasa kunya su shigo ya gani. Dole suka tattara suka wuce, suna mai gunguni da ɗure ɗuren ashar, har da babbar motar su ta kwasar kaya kuwa suka zo. Murmushi ya sauke, yana mai faɗin "Ku ƙarata dai, cen ga su gada inji zomo" ya ƙarashe yana mai jawo wayar shi domin kiran Afnan. ********** Ba ƙaramin tashin hankali Bilal ya shiga ba, jin abunda ke faruwa da iyalin na abokin nashi, har yanzu ya kasa cewa komai, kallon abokin nashi kawai yake, da yake zaune. Fuskar nan tashi jawur. "Friend u have to go there for sure, baka san ne zai faru ba, but idan zaka bi shawara na, da safe kayi sammakon tafiya, ba abu ne da za'a tsaya sanya ba, baka san me zai faru ba, saboda haka kayi gaugawar zuwa ga mahaifan ka, ka dakatar da faruwar komai.... " " Bilal is too late to cry" Ya Ameen ya datse shi daga maganganun da yake faɗa mashi, murya a sama. Shiru ya kuma yi, ya zaiyi da abokin nashi, dole ne yayi comvincing ɗin abokin nashi, dole ne fa yaje gidan suruka nashi, jikin shi na bashi wani abu mummuna na iya faruwa. Nisawa yayi, yana mai son cewa wani abu, Al'ameen ɗin ya dakatar dashi. "Ka shirya kawai, sai mu tafi tare" Ya Ameen ɗin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye ya zari makullan motar shi. Har bakin gate ya rako shi, inda motar shi take fake gefe, mai gadi na kula mashi da ita. Sallama sukayi, akan cewa goben tun da sassafe Ya Ameen ɗin zai je ya ɗauki Bilal ɗin. Ya amince da zuwa ɗin, baya so ko kusa wani abu ya shafi iyayen nashi. Sai da ya biya ya ɗauke ni, inda nake jin kaman kar in tafi, masalan idan na rungume baby ɗin nan, ina ji dama ace tawa ce. Dole na masu sallama, akan cewa zan kuma komawa. Ita dai Hajiya Zainab da kallo take bin mu, tana yaba ma ƙoƙari na, sannan tana sake yi ma Ya Ameen murna, na samu na da yayi a matsayin abokiyar rayuwa. Yayi ƙoƙari sosai wajen daidaita kanshi, inda tun daren ya sanar mani zaiyi tafiya, in shirya mashi jikka. Tun cikin daren na shirya mashi jikka, ina ta mashi shagwaɓar wai zai barni ni kaɗai, sanar mani yayi cewa in shirya in sake komawa gidan su Hafsat ɗin, wata ƙila tafiyar zata iya kamawa ya kwana, hakan ce ta sanya ni sanya mashi kaya kala ɗaya sababbi,saboda bansan tafiyar ko ta mecece ba. ********* Har bakin mota na raka shi, ina mai zuba mashi shagwaɓa, lallashi na yake yi sosai, shi kuma sai wani lallashi na yake, har narke man yake, wai zai ajiye jikkar ya zauna gida, Tunda bana so ya tafin. Ganin hakan ne nayi mashi a dawo lafiya, yana mai tallafe da ƙugu na, yake manna mani wani irin peck a goshi, wanda har cikin zuciya ta yake man daɗi, duk lokacin da yake mani. Addu'oin tsari na shiga jero mashi, har kawo lokacin da motar ta ɓace ma gani na, ma'ana ya fice, zuciyar shi ba yabo ba fallasa, saboda irin waƙi'ar da yasan yake fuskanta. Ni kau da sauri na na koma ciki, ina mai murna da farin cikin komawa ta gidan su Hafsat ɗin, inda zan yini acen. Ko ba komai yau nasan bani ba kaɗaici, inda nake jin har na fara kewar mijin nawa kuma abun alfahari na, watau Ya Ameen. Sai da ya biya ya ɗauki Bilal, da ya riga ya shirya tun tuni, dama shi kaɗai yake zaman jira, inda ya bar ma mai gadon nashi dukkan abunda yasan zai nema. To shima mai gadin da fatan dawowa lafiya ya bisu, yana mai jinjina wannan irin ƙauna da soyayya da take tsakanin abokan guda biyu, saboda yanzu ba ko ina ake samun amini irin hakan ba. Zuciyar kowa ta lalace babu kyau, ta yanda mutum ba zai iya zama da ɗan uwansa, amininsa, ko abokin sa da zuciya ɗaya ba. Sharara gudu yake yi sosai, so yake ya isa da wuri, zuciyar shi ta gama tsinkewa, shirun da yaji, sai gaban shi ke tsananta faɗuwa, to menene ke shirun faruwa ne?. Irin mugun gudun da Bilal ɗin yaga Al'ameen ɗin na shararawa ne, ya sanya shi amsar tuƙin dole, gudun kada yaje ya jefa rayuwar tasu cikin wani hali, saboda gaugawa, garin neman gira a rasa ido. Jefi jefi ya kan juyo ya kalle shi bayan amsar tuƙin. Kwantar mashi da hankali kawai yake yi, cikin natsuwa da tausasan lafuzza. Yana yi yana nusasshe shi matsayin Uwa akan yaron ta. Da wacece Mahaifiya wurin ɗanta, duk kuwa da cewa ya sani. ********** Ƙarar wayar ta da taji ne alamun saƙo ya shigo, tsoki taja tana mai juyawa, yanzu haka kamfanin layi ne, basu ji worning ɗin da taje tayi masu ba kenan? Ba zasu bar damunta da ture ture ba kenan? Komawa tayi ta sake ƙudundunewa cikin blanket. Wasu ƙarakin ta kuma ji har sau uku, tsokin ta kuma ja tana mai miƙewa zaune, ta sanya hannun ta da suka sha faratan roba, an bisu kaf an fante su kala daban daban, ta zaro wayar daga bisa side bed. Murza idanu take a hankali, saboda ta fahimci inda saƙon ya dosa. Katin gayyatar ɗaurin aure ne. Amman sunan wa take gani jiki haka? Nureen ɗinta? Tare da wata? Kai kodai wasu ne masu suna irin nasu? Cikin sauri ta zuro da ƙafafun ta daga bisa gadon, *"WHAT?"* kalmar da ta saki kenan cikin tsabar tashin hankali. Sai kuma ta saki kuka tana mai dafe da ƙirji. Ganin hotunan mijin ta tare da wata tsaleliyar yarinya. Yana riƙe da ƙugun ta, fuskar shi daf da tata, kaman zai kai bakin shi saman nata. Subhanallah! "Wallahi Baby ne, Baby ne, na shiga uku ni Nihal, cin amanar da Nureen zaiyi mani kenan? Ina zaune a gidan namu ya ƙara aure?" sai kuma ta sake fashewa da kuka. "Na bani, na bani" Abunda take ta faɗa kenan, cikin wani irin kuka mai sauti ta fara neman layin Mom, bata shiga kwata kwata, sai ta cenza akalar kiran zuwa ga Aunt Feena, still itama bata shiga. Bata tsaya komai ba ta zari makullan motar ta, ko gyale da takalma babu, jikin ta sanye da rigar bacci fara mai taushi, sauƙin ta ma har ƙasa take. Da gudu ta fice tana kai rusa kuka zuwa ga motar tata, kaman zata kashe ma mai gadi kunne da horn, haka take matsar shi, inda ko gama buɗe gate ɗin baiyi ba ta fice, har tana mai bugun kyauren gate ɗin da ƙarfi, bata tsaya kulawa ko yanda gaban motar tata yayi ba, ta yanki hanya da matsancin gudu, kaman mahaukaciya. ************ Yau ba zaman fada, mai martaba ya bama kowa hutu, a cewarshi zai gana da baƙin nashi ne. Hakan ce ta sanya komai an shirya shi yadda ya kamata. Wajen ƙarfe goman sha ɗaya na safe ne saƙon sarki ya iso kunnen Mama Fulanin daga bakin jakadiyan, cewa su hallara babban falon sarkin na cikin gida, inda za'ayi ganawar da ta shafi ahalin gidan. Yau sarki da kowa da kowa ke son jin tarihin Gimbiya Merama, mijin ta, da kuma dalilin barin ta masarauta. Wanda kowa ya zaƙu yaji ainahin abunda ke faruwa. Kowa ya hallara, ciki kuwa harda Mama Fulani, da sauran matan sarkin, sai Umma da Hajiya Kubra da suka gaisa ba yabo ba fallasa bayan sun haɗu, sai mai martaba, Dad da Alhaji Auwalu, sai Waziri, da Magajin gari. An natsu sosai, inda kowa ya kai gaisuwa ga sarki, bayan ya amsa ne, sai kuma aka shiga gaishe gaishe tsakanin su. Har yanzu waziri na zaune fuska turɓune, Hajiya Kubra kawai yake kallo. Itama daga nata ɓangaren, data ɗaga idanu sai su haɗe cikin kallon juna, ido cikin ido. Gabanta ne ya shiga tsananta faɗuwa. Gani take kaman tasan fuskar, saidai Amman ta ina??. Mai martaba ne yayi gyaran murya, dalilin da ya sanya kowa ya sake natsuwa kenan. "Assalamu Alaikum". Ya faɗa shima cikin muryar shi irin ta sarakai.bayan kowa ya amsa ne, sai kuma ya nisa cikin jawabi kamar haka. "Nasan kowa yasan dalilin taruwarmu anan, ba komai bane sai dan jin wani ɓoyayyen al'amari, da masarautar Mai Martaba Barkindo Lamiɗo ta daɗe tana muradin jinshi. Tun gabanin rasuwar Sarki mai cikakken Iko. Watau shi Yayana kenan. A dalili da hakan ne ya sanya muka gayyato shi mai gida ga Gimbiya Merama, watau Hasken masarauta, kuma ɗiya ga sarki mai rasuwa, sannan da yayan shi gashi nan zaune, sai kuma ita abokiyar zaman Gimbiyar tamu, watau Hajiya Kubra. Dalili da hakan ne ba ɓata lokaci, muke so tare da umurnin Sarki, ni Baffan Gimbiya, nake umurtarta da ta bayyana mana komai, wanda muke zaune cikin duhu shekara da shekaru. Bama so ta ɓoye mana dukkan wani abu dake faruwa, masarauta a shirye take da tayi ma labarin nata duba na tsanaki, tare da yanke hukunci akai" Cikin tsabar mamaki Hajiya Kubra ke kallon Umma. Ta tabbata dai ita ɗin ɗiyar sarki ce, to ko in haka ne, menene dalilin zaman ta a gidan nata tsawon shekara da shekaru tana mata bauta. Tana jure wulaƙanci daga gareta? Kuma ba tare da ta taɓa nuna ta gaza ba, ko ta gajiya? Hasali ma kullum ɗin ita mai biyayya ce, saboda tasan kashi tis'in da tara na abubuwan da mama uwani da mama Talatu ke kawo mata gulmar Umman a kansu bata aikata ba, kawai dai tsanar matar da ɗiyar ta ne suka rufe mata idanu, wanda tasan ko ita Surukar tata, watau Suhan bata san da wannan ɓoyayyen Sirrin ba. Muryar Umma ce ta fargar da Mom ɗin daga duniyar tunanin da ta shiga. "Humm, ranka ya daɗe Baffa na, insha Allahu nayi alƙawarin bayar da cikakken dalili na na barin wannan masarauta, a matsayi na ta ɗiya ɗaya tilo ga mahaifin nawa watau shi mai martaba mai rasuwa. Zan so kowa dake nan ciki ya bani natsuwar shi. Da farko dai zan fara gode ma shi mai gida na, watau Alhaji Almustapha Yusuf Dambulan, wanda nasan shi ɗin ba baƙo bane anan wurin, dama faɗin nigeria gabaki ɗaya, sannan zan maida godiyr tawa ga Hajiya Kubra Nura, wanda aka fi sanin Baban nata da Suna Alhaji Ibrahim, nasan zata yi mamakin inda nasan wannan daɗaɗɗen labarin, wanda ba kowa ne yasan dashi ba, anan ciki mu Uku ne rak kawai muka san da hakan, ni, ita, da kuma Baba waziri gashi nan zaune" (ta faɗa tana mai nuna waziri) wanda dalilin hakan ne ya sanya na bar mahaifa ta, mahaifar mahaifi na, na kwammace inje cen inyi wata rayuwa daban. Saboda na kula cewa ita sarautar kanta matsala ce. Rayuwa ta da ta abunda ke ciki na tana cikin barazana. Wannan ne dalili na na komawa wani ƙauye cen da nisa cikin garin Jigawa, inda daga baya na koma Abuja gidan Hajiya Kubran da zama, tinda ina ganin cen ne kawai wajen tsira na, dalili kuwa, ita bata sanni ba, bata san komai daya dangance ni ba, haka kuma bata san komai nawa ba, ba tare da tasan ni ɗin na santa ba, kuma rayuwa ta tana da alaƙa da tata rayuwar ta fannin mahaifin nata ba" Cikin tsabar kaɗuwa, furgita da gigita Hajiya Kubra ta ɗago tana kallon Umman, wanda idanun ta suka kawo ruwa sosai, har sun fara zirara bisa farar alkyabbar dake sanye a jikin ta. Ba Hajiya Kubra ba, hatta da shi kanshi mai martaba ɗin, Dad, Mama Fulani, Alhaji Auwalu, da sauran matan sarkin, saida suka gigita da jin abunda yake fita daga bakin Gimbiya Meramar Shi kau Waziri, ƙasa kawai yayi da kanshi, yana mai jinjina kai, cikin nadama da tarin kunya, domin wannan ita ce ake kira da ranar nadama da tarin shan kunya. Nura ya mutu ya huta, ya mutu ya bar shi zaune cikin faɗin duniyar da babu komai cikin ta, in banda tarin son zuciya ga masu son zuciyar, nadama ga waɗanda suka aikata abun nadamar, danasani haɗi da tsantsar kunya. Wannan wace irin baƙar rana ce? Rana ce da yasan zata zo, koda kuwa bayan babu rayuwar shi, saidai idan tazo babu rayuwar tashi, abubuwa zasu cigaba da zama ne a dunƙule, kuma babu ranar warwarewar su, tunda shi dai ya zuwa yanzu ba zaice zai iya faɗar ga inda Barrister ya shiga ba. Shesshekar Kukan Umma kawai kake ji. Inda Mama Fulani ke bata haƙuri ƙasa ƙasa, shi kau Dad kallon Umman kawai yake yi, gani yake gabaki ɗaya yau ta cenza, kaman ba ita ba, ashe rayuwar ta rayuwa ce mai cike da tarin ƙalubale da abubuwa mabanbanta, wanda suka nesanta ta da farin cikin ta? A hankali Mom ta runtse idanun ta, tana mai sake buɗe su. Alhaji Nura, Alhaji Ibrahim. Suna biyu ne, ɗauke cikin gangar jiki ɗaya, wanda kuma yake matsayin mahaifi gareta. Saidai shi ɗin wanene? Me ya aikata a lokacin rayuwar tashi? Tasan wasu Amman bata san wasu ba. Me yasa bata bincika ba? Me yasa tabi son zuciyar ta? Son zuciyar mahaifin ta? Shin ita kanta ɗin ma wai wacece? Menene alakar tarihin rayuwar Maryama da tata rayuwar??? Muryar Umman ce ta sake katse mata zurfaffen tunanin da ta shiga. "Hajiya Kubra ki sani, na zauna gidan naki ne tsawon shekaru, ba don komai ba, sai dan in tattara hujjoji, yayin da nake ta kallon ki cikin fuska biyu, fuska ta farko a matsayin ki na ɗiyar wanda ya jefa rayuwa ta da ta ɗiya ta a cikin walagigi, fuska ta biyu a matsayin ki na wadda ke rayuwa tunƙhakaho da tutiya da dukiyar da asalin ta take mallakin ɗiya ta Suhan da kuma ni Gimbiya Merama Hasken Masarautar Mai Martaba Barkindo Lamiɗo...". Sallamar Ya Ameen da Bilal ce ta katse maganar da Umma tawa take yi, wanda ƙaraf sai a kunnen Ya Ameen. Wanda sai da yayi taga-taga kaman zai faɗi, jin kalaman da Umman kuma surukar tashi take faɗa. Bilal ne yayi saurin taro shi, inda ya dakatar dashi, gami da dagewa ya fara takawa cike da wata irin zumma ya isa ga inda sauran iyayen nashi suke zazzane, idanun shi jawur, ya kafe mahaifiyar tashi dasu... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~73~* _2020_ *Fatan za'ayi mani uziri jina kwana biyu. Dan Allah ina barar addu'a daga bakunan ku masu albarka. Allah ya cika man buri na, ya bani Abunda nake nema duniya da lahira Ameen* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° A hankali ya shiga janye idanun nashi daga kan mahaifiyar tashi. Gaisuwa ya kai wajen mai martaba, yayin da shima Bilal ɗin haka. Saida mai martaba ya amsa, sannan suka shiga gaida mutanen dake wurin. Maganar ƙarshe ta Umma, ita ke tayi mashi yawo a cikin zuciya, tun daga shigowar tashi har kawo yanzu. Me kenan? Dad ne ya katse mashi tunanin ta hanyar cewa su jira su a waje, inda Umma tayi hanzarin tarar numfashn shi, gami da cewa su zauna, abu ne da ya shafe shi shima. Ganin haka sai Bilal ya miƙe da niyyar ficewa, Al'ameen ɗinne ya riƙo hannun shi, yayin da Bilal ɗin ya shiga girgiza mashi kai, ko ba'a ce ba ai shi kanshi ya san ya kamata ya fita ɗin, Tunda wannan issue ne na cikin gida. Saboda haka ya saɓule hannun shi cikin na Ya Ameen ɗin ya fice zuwa Babban Falo. A hankali mai martaba ya maida kallon shi kan Umman, tare da yin gyaran murya, sannan ya shiga cewa "Ke muke saurare Merama" A hankali ta sauke kanta ƙasa, ƙissima abubuwa da dama ta shiga yi. Tayaya zata fara? Ta ina ma. Kauda duk wani tunani da kunya tayi gefe, tana mai muskutawa ta shiga faɗin. "Al'ameen shine dalili na na ƙin amince ma auren shi da Suhan, dalili na kuwa shine, nasan wannan ranar tana tafe, ko ba komai uwa uwa ce, bana son wani tarnaƙi da zaiyi silar farin cikin ɗiya ta a karo na biyu. Saidai yanda na kula suna son juna, bana da zaɓi, sai naci gaba da addu'ar koma minene zai zo, yazo da sauƙi, Alhaji Mustapha yana ɗaya daga cikin mutanen da bazan taɓa mantawa ba a rayuwa ta. Shine mutum na biyu daya karɓi rayuwa ta a yanda take, ba tare da musgunawa ko ƙuntatawa ba, ba tare da yayi la'akari da ɗiyar da nake ɗauke da ita ba, ba tare da ya matsa man da in sanar dasu ainahin asalin labari na ba, ko kuma daga inda nake. Hajiya Kubra ina so ki sani, mutane biyu da suke da alaƙa dake, sune Abunda ya hana ni bayyana komai tun da daɗewa, lokacin da kika so ruguza komai da hannun ki, kika so tursasani fallasa Sirrin da na daɗe ina bunnewa, ta hanyar gallaza mana ni da ɗiya ta, dalili da haka ne ya sanya na tsallake na bar maki gidan, duk da cewa a ranar ne burin ɗiya ta na farko yake daf da cika, watau ranar da zata tafi makaranta, wanda ɗanki ne yayi mata komai ba tare da sanin ki ba, saidai da sanin shi Alhaji gashi nan a zaune." Ta faɗa tana mai nuna Alhaji Mustapha da Hannu a karo na biyu. Hajiya Kubra da take zaune kawai kaman mutum mutumi, zufa ce ke karyo mata a cikin jiki, ta jiƙe tayi sharkaf, duk da sanyin Ac ɗin dake tashi a falon.kazalika shima Alhaji Mustapha da Alhaji Alwalu sun natsu tsaf, suna jin wani zance mai kama da almara, kenan Maryama tana sane da duk abubuwan da Hajiya Kubra keyi mata? Kuma tana jin zafi, Amman soyayyarta ga ɗiyar ta ne ya hana ta bayyanawa? Gyaɗa kai Mai Martaba keyi a hankali, yana nazarn kalaman Umman daki da ɗaki. Shi kuwa Al'ameen har yanzu idanun shi na bisa fuskar Umman da Sam baya ganin laifin ta, duk Abunda ta faɗa anyi ne. Irin Abunda yake gudar ma mahaifiyar tashi tun farko kenan, yau ga irin ta, yau ga ranar abubuwan da mahaifiyar shi ta aikata. Da wanne ido zai kalli Suhan muddin tasan Abunda ke faruwa? "Alaƙa ta da Baba waziri, mijina, mahaifina da shi kanshi mahaifin naki kuwa ta samo asali ne daga.... Masarautar Mai Martaba Muhammadu Bello Barkindo Lamiɗo, Babbar masarauta ce da take da daɗaɗɗen tarihi. Masarauta ce mai cike da izzar mulki, dukiya da kuma taƙama. Mai Martaba Muhammadu Bello, shine asalin mahaifi na, sarautar kuma ya gaje ta ne a hannun mahaifin shi, wanda shi kaɗai Allah ya mallaka ma mahaifin nashi. Ba'a sha wata wahala ba akayi ma mahaifi na naɗi bayan rasuwar mahaifin shi. Kasancewar shi ɗa ɗaya tilo a wajen mahaifin nashi, dukda matar kakan nawa watau shi sarkin tana da ɗa ɗaya wanda tazo dashi daga wani gidan, watau Baffa na gashi nan zaune, wanda yake matsayin sarki a yanzu. Kaman yanda nima nake ɗiya ɗaya tilo a wajen nawa mahaifin watau mai martaba Muhammadu Bello. Na taso cikin gata da kulawa sosai da sosai, yayin da ban taɓa neman wani abu a rayuwa ta na rasa ba. Sauran Matan sarki suna sona da ƙauna ta, inda ko shekara sha biyu ban rufa ba, mahaifiya ta ta kwanta dama, wannan shine dalilin da ya sanya soyayyar da mahaifina yake nuna mani ta ƙaru, inda riƙo na ya koma hannun mai babban ɗaki, watau mahaifiyar mahaifi na kenan. Kaman yanda mahaifina yake sona yake ƙauna ta, haka itama take nuna man soyayya da kulawa. Inda suma matan sarkin suke nuna mani soyayya sosai, saidai ashe ban sani ba, ta ciki na ciki, kowacce daga cikin su so take taga baya na, Amman ba tare da ta bari ɗayar ta sani ba. Ana cikin haka ne Allah yayi auren Baffa na da Mama Fulani a lokacin wadda take ɗiya ga ƙanwar mahaifiya ta, inda ya ɗauke ta suka tafi turai domin ƙaro karatu, sai suka ɗauki ƙanwar ita Mama Fulanin da take ƙarama mai suna Khaltum, duk da ta girme ni, Amman ita a ƙauye take zaune, suka tafi da ita. Wannan shine asalin barin Baffa na da nigeria, inda ya tafi yabar Yayan nashi yana mulkin masarautar. Nayi karatu sosai da sosai, inda nafi ba na Muhammadiyya ƙarfi. Saboda ina kammala makarantar sakandire na dakata daga katarun, mahaifi na ba yanda baiyi ba akan in cigaba na nuna ni aure nake so. Dayake Soyayya ta ƙullu tsakani na da Muhammadu, watau ɗanɗan Yayan Mahaifin ki. (Hajiya Kubra). Ankai ruwa rana sosai, akan me zan auri wanda ba jinin sarauta ba? Kenan duk lokacin da mahaifina ya mutu sarauta ta tashi daga hannun jinin sarauta ne? Duk da ƴaƴan sarakuna da dama suna kawo man ta yin soyayyar su, Amman naƙi kula su, saboda nafi son mahaifin Suhan watau Muhammadu Alhaji Ibrahim wanda asalin Sunan shi yake Alhaji Nura, mutumin Kaduna ne. Su biyu ne a wajen mahaifin su, watau Kakan ƴata Suhan kenan. Shi da Yayan shi Alhaji Isma'il kasancewar su ba uwa ɗaya ba, sai Alhaji Isma'il da yake shine babba yaja Alhaji Nura a jikin shi. Duk da iyayen su mata suna kishi sosai, daga baya ne Allah ya karɓi ran mahaifiyar Alhaji Nura, sai riƙon shi ya koma hannun mahaifiyar Alhaji Isma'il, inda mahaifin su ya roƙi ita mahaifiyar isma'il da ta riƙe nura kaman ita ce ta haife shi. Dayake ita bata cika zafin kishin ba, sai ta tallafi nura kaman yanda take ma isma'il. Kwanci tashi asarar mai rai, sai Allah ya buɗa ma isma'il sosai da sosai. Har ya kan ja ƙanen shi cikin kasuwancin nashi, saidai duk kuɗaɗen da yake bashi, sai ya tasa a gaba ya cinye su, haka zai sake dawowa wajen isma'il ya ƙara bashi wasu. Ana haka ne mahaifin nasu ya kwanta ciwon Ajali. Bayan rasuwar tashi ne aka raba masu gado. Inda aka hannanta dukiyar Nura hannun isma'il. Amman nura ya buga ƙasa shi Sam, saidai a bashi dukiyar shi, ai shima ya iya kasuwancin. Isma' il da ya ƙiya, Amman sai mahaifiyar shi taga nura ya fara wasu take take, sai ta sanya yaron nata ya miƙa ma ƙanen nashi dukiyar. Duk da haka dukkan abubuwan da ya saba yi ma isma'il bai dena ba. Hatta da hidimar karatun nashi. Har ƙasar waje ya fidda shi yayi karatu sosai. Inda acen ne ya haɗu da Baba Waziri, duk da ya girme mashi. Amman haka suka cigaba da abota. Har Allah yasa Baba Waziri ya gama ya dawo masarauta. Inda yazo ya gaji mahaifin shi da ya rasu. Bayan wasu shekaru shima Nura ya gama, dawowar shi gida ne ya tadda yayan nashi yayi aure, har ma Ya haihu da matar yaro namiji kyakkyawa dashi, ga shiga rai. Sai ya cenza taku. Ya fara jan yaron nan a jiki. Kunsan mai ɗan wawa, nan da nan sai matar isma'il ta saki jiki da Nura ƙanen mijin nata, har ma suka taɓa ɗan wasa haka tsakanin ta dashi. Duk da Isma'il baya so, Amman hakanan mahaifiyar shi taja mashi kunne akan ya kauda kai, kada kuma Nuran yaga kaman suna ware shi ne saboda ba ita ce ta haife shi ba. Yaro yayi wayau sosai, inda zuwa lokacin Nura ya gama ƙarar da dukiyar gadon nashi kaf, yayin da shi kuma Isma'il Allah ya sanya ma tashi albarka. Kasuwancin shi yake sosai da sosai. Zama ne yake gudana a tsakanin ƴan uwan biyu, yayin da abinci da komai ake ba Nura a gidan Yayan nashi, yayin da sauran buƙatoci Isma'il yace ya janye, ko hakan zai sa Nuran ya hankalta. Saɓani na biyu daya biyo baya shine Nuran ya haɗu da wata yarinya bafulatana mai suna Bilkisu, ya nuna yana son ya aure ta, Isma'il ya ƙafe kai da fata akan ba ruwan shi a cikin wannan hidimar, saboda Nura dai ba aiki gareshi ba balle sana'ar da zai riƙe ɗiyar mutane da ita. Ba yanda Isma'il baiyi ba akan ya ƙyale masu yarinya amman ya ƙiya, hakan ce ta sanya shi zura mashi idanu, domin yaga gudun ruwan shi. Rana ta farko ta buɗewar makullan walagigi da rayuwar miji na, rayuwa ta data ɗiyata baki ɗaya. Ita ce ranar da Isma'il da mahaifiyar shi haɗi da Matar shi suka nufi garin Katsina domin biya masu kuɗaɗen Hajji, wanda yake fatan suje tare, inda suka yanke shawarar barin Muhammadu wajen Nura. A bisa hanyar su ta zuwa ne sukayi hatsari su duka, Allah ya karɓi abun shi a take. Muhammadu yayi kuka sosai, iya rayuwar shi, yayin da Nura ko a jikin shi. Haka aka kawo su gida akayi masu sutura, haɗi da miƙa su gidan su na gaskiya. Tun daganan rayuwar Muhammadu ta cenza, dan ma dukiya hukumar ta shiga ciki. Inda aka je kotu domin rabon gado. Acen ne aka tabbatar da cewa mahaifiyar ta Isma'il ita ce ta fara rasuwa, sai shi sannan matar tashi. Ya kasance gabaki ɗaya dukiya mallakin Muhammadu ce, saboda haka aka duba cencenta aka hannanta ma Nura kaf dukiyar Muhammadu a hannun shi, saboda shine ɗan uwan mahaifin shi, kuma shine wanda zai kula dashi. Da shedu da komai Nura yana kukan Munafunci na jin daɗi ya amshi dukiya, yana mai rungume Muhammadu a jikin shi, alamun yana tausaya ma yaron. Daga kotun ne Wani barrister da akayi komai kan idanun shi, ya samu damar biyo bayan nura, inda ya buƙaci ko zai zame mashi private lauya, ba tunanin komai Nura ya amince, domin a cewar shi, dole dama ya nemi lauya, saboda ba ƙananan kuɗaɗe bane Isma'il ɗin ya bari. Abu na farko daya fara yi shine aure, auren yarinyar da tsabar kyawun ta ya kwashi Nura, saboda haka ya cigaba da fantamawa yanda yake so. Inda ya tattara kayan shi kaf, ya koma garin Katsina da zama, inda ba wanda ya sanshi, haka shima babu wanda ya sani.acen ne ya sauya sunan shi zuwa Alhaji Ibrahim Saidai abotarsu da waziri da tana nan, yana kaima waziri ziyara, inda waziri ma kan kawo mashi. Bilkisu mace ce wadda zamu iya cewa kusan halin su ɗaya da Nura, dalili da yasa ma suka nace ma juna kenan. Bafulatani ne ta asali, inda iyayen ta suke da dukiya daidai gwargwado ta shanaye da kuma raƙumma jajaye. Saboda haka ne ma ya sanya suka tashi kansu a waye, inda basa hana yaran su karatu. Har waje suna iya fidda yaran nasu suyi karatu, saboda zamani da yazo da hakan. Saboda haka ne Sam Muhammadu baya jin daɗin riƙon ta, inda ita kuma kullum take yi ma Nura mitar riƙon da take yi ma Muhammadun. Hakan ne ya sanya ya tattara shi ya kai shi makarantar kwana ta gwamnati. Saboda baya jin zai iya kashe mashi naira akan karatun nashi, duk kuwa da cewa dukiyar tashi ce, Amman babu wanda ya sani, in ka ɗauke ita Bilkisun, sai Barrister da kuma Waziri. Yayin da ita kuma Bilkisun ya maida ta makaranta mafi tsada ta cigaba da karatu, inda kanta ya fashe ta kuma wayewa, dama gata bata da dangin miji, bata ma san me ake nufi da hakan ba. Hakan ya sanya ta cigaba da cin karen ta ba babbaka. Rayuwa ta cigaba da gwarawa a hankali a hankali, har Allah ya azurta Bilkisu da Haihuwar Kubra. Yarinyar da ta taso cikin gata da tsantsar kulawa. Wayewa da kuma wani dalili nasu cen ya sanya suka juya mahaifar Bilkisun, a cewar su Kubra kaɗai ta ishe su. Tun sanda Kubra ta taso, Nura bai sake bari Muhammadu ya taka gidan shi ba. Ko hutu akayi sai yace a kai Muhammadu gidan Barrister ɗinshi Tunda ya amince dashi, ko kuma akai shi cen Adamawa wajen Waziri. Hakan ce ta sanya Kubra da Muhammadu Sam basu san Juna ba. Saboda baya ma son tasan cewa ga yadda suke da Muhammadun, saboda yasan yanda Kubra take da tambayar tsiya. Ba shine yabar Muhammadu zuwa mashi gidan ba, har lokacin da ya tattara Kubra ya tura ta cen ƙasar waje karatu, inda ya barta gidan wani abokin kasuwancin shi. Shi kuma Muhammadu lokacin ya kammala karatun shi na secondry, har ya samu shiga Jami'a. Dan dole ba yanda Alhaji Nura ya iya, ya haƙura ya bar Muhammadu na zuwa mashi gida. Saboda a lokacin Muhammadu ya mallaki hankalin kanshi, kuma ya san cewa dukiyar Alhaji Nura tashi ce yake juya mashi. Saboda haka ne ya buƙaci da ya bashi wani abu ya fara ɗan juyawa saboda hidimar karatu. Inda Alhaji Nura, wanda aka fi sani da Alhaji Ibrahim a Katsinan ya nuna ma Muhammadun ɓacin ran shi, akan me zaice ya bashi kuɗi, ashe bai yadda da yanda yake riƙe da amanar shi ba. Duk wani abu da yake so yazo ya tambaye shi, shi zai bashi. Haka Muhammadu ya cigaba da gungurawa yana karatun shi. Saidai kafin ya kammala soyayya mai zurfi ta shiga tsakani na dashi. Dayake wani lokaci yana kaima Baba Waziri ziyara. An kai ruwa rana sosai. Kafin aka samu aka amince da auren namu. Inda shi Alhaji Nura ya ƙi amincewa ne, saboda cewa Muhammadu zaiyi aure gidan girma, dole nan gaba zai buƙaci dukiyar shi da yayi aure. Yayin da shi kuma waziri yake ganin cewa Muddin Muhammadu ya auri Gimbiya Merama to fa tabbas sarauta zata koma wajen Muhammadu ne ba shi ba,kaman yanda ya sanya rai. Dalili da yasa suka shiga suka fita, suka cigaba da ƙullu-ƙullen su kenan. To Amman dayake Mai Martaba mahaifi na, mutum ne mai sanyin hali, da hangn nesa, kuma baya son auren dole. Hakan ce ta sanya shi girmama ra'ayi na, gami da cewa ya amince in auri Muhammadu, kuma ko bayan ba rayuwar shi, Muhammadu ne mai gadon kujerar shi, saboda shine miji a gareni. Kaman yanda yake a al'ada ba'a ma mace naɗin sarauta. Nan fa hankalin matan sarki ya tashi, sai suka shiga nuna mani tsana ƙarara, duk da suna tsoron mai martaba, Amman babu wanda ya kula dasu. Saboda irin sarauta da mulki da ake gabatarwa a masarautr mai zafi. Duk wanda yayi ba daidai ba, a take hukunci ke hawan kanshi. Yayin da hatta da zaman fada dani mahaifina ke futa. Ba wanda ya damu, inda waziri a zahiri ya nuna yafi kowa murna. Shi kuma Mahaifina ya bani wani sashe a cikin gidan ta cen baya yace anan ne zan zauna. Saboda kada a gane halin da Muhammadu yake ciki wajen Alhaji Nura, ya sanya suka haɗo kayan aure na gani na faɗa suka kawo gidanmu. Duk da al'adar masarautar ba'a amsa,amman saboda farin ciki na haka aka amsa. Aka sha shagalin biki na kece raini. Inda dubban mutane suka shaida ɗaurin auren nawa. Zuwa lokacin Muhammadu ya kammala karatu har yayi bautar ƙasa, sai ya nemi Alhaji Nura akan ya bashi dukiyar shi. Ta yanda zai dogara da kanshi shima. Amman fir Alhaji Nura ya ƙiya, wai a cewar shi sai ya mallaki hankalin kanshi sannan, ko ya bari sai na haihu sana. Wanda a zuwa lokacin har ɗiyar shi Kubra ta daɗe da dawowa har ma ta auri Alhaji Mustapha Dambulan. Amman duk da hakan sau ɗaya Muhammadu ya taɓa haɗuwa da ita. Shima kallon da take mashi na ƙasƙanci ya sanya shi share ta. Tunda yasan da cewa tasan dukiyar da take tunƙaho da ita ta mahaifin ta tashi ce. Wannan tasa ko bikin ma bata je ba ita da Hajiya Bilkisu, watau mahaifiyar ta. Abunda yaja tsegunguma kenan, masalan gidan sarauta da abu kaɗan ake jira, balle ga yanda nake da matan sarki. Ganin hakan da Muhammadu yayi, sai ya koma ya nemi Barrister. Inda shi kuma ya kasance mutum mai gaskiya, dama duk wannan abu da akeyi yana biye da Alhaji Nura ne ta dalilin Muhammadun. Domin ya tattara duk wasu shedu a hannun shi. Koda gaba za'a neme su. Bai ɓoye mashi komai ba, ya shaida mashi cewa ya sake haƙuri. Alhaji Nura yayi kafuwar da karawa dashi sai Allah, haka kuma ya shiga siyasa, da huɗɗoɗi da manyan ƙasa, ta yanda ko yace ma zai ja dashi ba zai iya ba. Amman yana shawartar shi da ya jira lokaci tukunna. Matsalar da muka kuma fuskanta ita ce ta rashin haihuwa, tsawon shekara uku da aure ba haihuwa Sam, anyi maganin anyi karatun shiru, har hankalina ya fara tashi. Mai Martaba mahaifi na shine ke lallashi na. Tare da mai Babban ɗaki, wani lokacin ma haka Muhammadu zai tasa ni a gaba da lallashi. Har ya kan bani misali da cewa mahaifina shi kaɗai ne a wajen iyayen sa. Haka ma Kakana. Sannan shi kanshi ba wasu dangi ne dashi ba, ko shi ma shi kaɗai ne a wajen iyayen sa, kazalika nima. Da ban baki yake samu ya shawo kaina. Kwatsam ana haka sai ga ɓullar ciki a jikina. Murna kam kaman ba'a yi, inda har ƴar walima saida Mahaifina ya haɗa mana. Aka shiga tattashi na, tare da bani kulawa ta musamman. Masalan a wajen mai gidan nawa, soyayya da kulawa sosai yake bani. Inda duk inda kabi maganar cikin dake jiki na akeyi. Ranar wata laraba, ba zan taɓa mantawa ba, na farka cikin dare da wani irin matsanancin ciwon ciki. Nasha wahala. Inda muna isa asibiti cikin ya ɓare, nayi kuka nayi kuka sosai, ban sani ba ko shikenan Allah ya nufeni da samu. Bamu kawo komai a ranmu ba, akayi man wankin ciki muka dawo gida. In taƙaice maku dai. Cikin shekarar saida nayi ɓarin ciki har uku. Abun ka da masarauta. Masu magani kala kala, kullum zarya suke a masarautar mu, gashi tsufa ya riski Abbana Mai Martaba. Kowa da Abunda yake cewa. Wasu suce sammu ne akayi mani. Wasu suce aljannu ne ake Sanyawa suna ɓarar man da cikin. Wasu suce ai wani abu ne ake sanya man a abinci. Dayake mu musulmi ne. Sai duk bamu yarda da hakan ba, kawai dai kun yarda da ƙaddara, ganin babu wanda bama zaune dashi lafiya. Kuma ko ba haka bama, yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, wajibi ne ga musulmi kuma mumini. Ana cikin haka ne. Aka sanar mana da haihuwar Hajiya Kubra, inda ta haifi Saudat, ba yanda banyi da Muhammadu ba akan ya barni inje, Amman fir ya ƙiya, dama su basu taɓa tako inda muke ba, a cewar shi wai alaƙa tayi tsanani dashi da Baffan shi Alhaji Nura akan lallai sai ya bashi dukiyar shi. Inda shi kuma ya nuna mashi akan hakan zai iya aikata mashi komai. Naso ya barni in sanar ma da mahaifi na Mai Martaba, Amman ya hana, a cewar shi lokaci zai zo wanda zai sani. Haka aka gama shagalin suna bamu je ba. Saidai yayi mashi barka ta waya. Ɓullar ciki na huɗu, shine Abunda yaja hankalin kaf mutanen dake rayuwa tare damu. Inda aka shiga bani wata kulawar ta musamman. Tare da mani saukar Alƙur'ani. Sannan aka maida ni cikin gida ɗakin Mai Babban ɗaki. Haka ciki yayi ta rayuwa a jiki na. Ko haɗimai ba'a bari su shiga inda nake. Jakadiyan ce kawai aka amince ma da hakan. Kullum ina cikin karatun Alƙur'ani da sauran addu'o'i. Ciki na ya kai wata na biyar har yanzu ba abunda ya same shi. Hakan ya sanya masu murna sukayi masu baƙin ciki suka yi. Har Allah ya sanya cikin ya shiga wata na shidda. To daganan ne fa sai ciki yaƙi gaba yaƙi baya. Har watan haihuwa ya shiga, ashe mu bamu sani ba ciki ya kwanta ne, watan haihuwa ya fice, ciki har ya shekara shiru, har ya zarta. Nan fa hankali ya tashi, kullum zarya ake asibiti, suna sanar da cewa ciki fa ba lafiya, kuma muddin aka sake akayi mani aiki za'a iya rasa ni. Hakan ce ta tada hankalin Mai Babban ɗaki tace a maido ni gida. Insha Allah za'a cigaba da yin na gidan. *Allah Baya Barin Wani Dan Wani Yaji Daɗi...* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'a Idan Ya Sauka A wani masauki a Halin Tafiya ko waninta.* أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ. A'oothu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaq. Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta. >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~74~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Ranar wata Lahadi wadda ba zan taɓa mantawa ba. Rana ce da ta kasance rana mafi muni a rayuwa ta. Da misalin ƙarfe shidan asuba ne, Muhammadu ya shigo man bayan ya dawo daga sallar asubahi, yana ta sauri da ujila. Na ɓaɓɓaka da kyar daga bisa sallayar da nake kai ina lazimi bayan idar da Sallar asubar da nayi. "Mai gida lafiya kuwa na ganka tun da dugu-dugun safiyar nan? Ina Mai babban ɗakin take da ta barka ka shigo yanzu?" na faɗa ina mai waige waigen ganin ina kakar tawa take. Hannuwa na ya kamo sosai cikin kulawa, yana mai shafo cikin nawa da dukkan hannuwan shi, sannan ya zuƙunna sosai yana mai ɗora bakin shi bisa cikin ya sumbace shi sosai, yana mai tallafo shi, yake magana da cikin kaman yana magana da mutum. "Fatan kana lafiya yaro na?nayi kewarka, nasan kaima kayi kewa ta ko? To Allah yayi maka albarka, ya kawo man kai lafiya" Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, sai kuma ya kama hannu na zuwa bakin gadon nawa ya shiga zaunar dani. Shima gefen gadon ya koma ya zauna, yana mai kallo na cikin kulawa. "Gimbiya ta, nasan zakiyi mamakin shigowa ta a yanzu, watau wata tafiya ce mai muhimmanci ta taso mani yanzu yanzun nan, cikin dare naga saƙon cewa ana son gani na wajen interview ɗin aikin da nake nema da misalin ƙarfe tara..." Ya nisa yana mai ƙure ni da kallo. " Saboda haka ne na shigo in ganki, sai kuma aka ci sa'a mai babban ɗaki bata hana ni ba, kaman yanda take yi kullum.. Naji daɗi, saboda haka ne ma ɗiyar mu ta biyu sunan ta zan sanya, saboda bata hana ni ganin abar sona ba daga ƙarshe" Ya ƙarashe yana mai tallafo fuska ta. Nima murmushi na sakar mashi "Naji daɗi maigida, Allah ya bada Sa'a ya kuma sanya a samu abunda aka je nema, Amman don Allah kada ka tafi baka ci wani abu ba" Shima murmushi ya sakar mani yana mai miƙewa; "Insha Allah Matata rabin raina. Ina ƙaunar ki da dukkanin rayuwa ta. Ina fatan Allah ya sauke man ke lafiya" Har bakin ƙofa na raka shi, ina mai murmushi, duk da yanda yau Naji ciki na yana juyawa, Amman daurewa nake kada in tada mashi hankali , gudun kada yaje ya kasa natsuwa ya bayar da abunda ake so. Har ya fita sai kuma ya kuma dawowa, ya tadda ni ina naɗe abun sallar. Banji shigowar shi ba, sai hannun shi naji bisa jiki na, yana mai cewa "Allah nake roƙo da kafin in dawo saƙon haihuwar ki ya iske ni, da zan fi kowa farin ciki da jin daɗi" Murmushi na saki nima, ina mai cewa "Ameen maigida. Ya kamata ka tafi kada ka makara fa" Tsayuwar shi ya gyara yana mai kallo na cikin ido. Sai kuma ya nisa yana mai cewa; "Tun ɗazu da na shafa cikin nan sai naji kaman yana motsi, abunda muka rabu daji tsawon watanni, wannan shi ya sanya na kasa tafiya, sai nake ganin kaman yau zai shaƙi iskan duniyar nan ne, kaman yau ne Allah zai cika mana burin mu, na ganin gudan jinin mu, ina fatan ace ya biyo kyau da halaye da komai nagari kaman ke matata, zanyi farin ciki.. " Numfashin shi na tara, idanu na har sun fara tara kwalla, ga ciwon mara dake katsa mani. Amman saboda ƙarfin hali sai na saki murmushi, ina mai shafo cikin nima da hannun sa yake sama. " Insha Allah kafin ka dawo Abunda ke cikin nan ya riga ka isowa, kuma ba dani zaiyi kama ba, da kai zaiyi kama, kyau kyawawan ɗabi'u haƙuri da kauda kai da komai da kai zai kama sarkina na nan gaba" Share man ƴar kwallar data ziraro mani yayi, yana mai girgiza man kai yake cewa; "Kukan na menene? Kodai in zauna ne kada in tafi." girgiza mashi kai nayi nima, ina mai matse baki nake danne kwallar tawa. "Allah ya tsare ya kiyaye hanya mijina farin ciki na, kafin ka dawo insha Allah zaka tadda kyakkyawar tarba daga gudan jinin mu a yau insha Allah" Murmushi ya saki, yana mai zagaye ni ya fara tafiya, sai kuma ya tsaya cak. Inda yake tsaye na isa, ina mai zagayawa ta inda zan iya hangen kyakkyawar fuskar shi mai kama da ta Suhan sak. Abun mamaki, hawaye na gani kwance male male a fuskar shi. Cikin zaro idanu na shiga cewa "Lafiya kuwa mai gida?" Girgiza kai yayi, yana mai share kwallar. Sai kuma ya shiga cewa "Ina son in ga gudan jinin mu Gimbiya, saidai wata zuciyar na shaida mani kaman zaman shi a cikin cikin shine zai fi mashi kwanciyar hankali da mu baki ɗaya, ina mai tausaya ma rayuwar abunda zamu haifa, duniyar nan babu komai cikin ta da ya wuce tashin hankali, son kai, son zuciya da kuma gurɓacewar rayuwa... " Saurin rufe mashi baki nayi da tafukan hannaye na, sai kuma na rungume shi ina mai sakin kuka. " Babu abunda zai samu ɗanɗan mu mai gida na, ina cikin wani hali, numfashi ma da kyar nake yin shi, yana tokare mani zuciya, yana mani nauyi, kayi man addu'a in haihu lafiya maigida" Shima cikin ƙarfin hali ya shiga shafo saman kaina, yana mai faɗin "Insha Allah Maryam insha Allah" A haka dai da kyar na samu ya tafi, na koma bakin gado na zauna ina mai share hawaye na, zuciya ta babu daɗi Sam, ji nake kaman mutuwa zanyi, kaman nayi sallama kenan da mijina, ko wajen haihuwa ne zan mutu, kaman ba zan ga abunda zan haifa ba ma. Mai babban ɗaki ce ta shigo, ganin fitar shi. Hankalin ta ya tashi sosai ganin halin da nake ciki. Lallashi na ta shiga yi, har ta samu nayi shiru. Wajen ƙarfe goma ne Mai Martaba Abbana ya shigo duba ni, kaman yanda yake yi kullum kafin ya zauna fada. Shima lallashi na ya shiga yi, nan ne mai babban ɗaki ke mashi albishir da cewa yau cikina ya fara motsawa. Yaji daɗi sosai, inda ya ƙara buƙata da a cigaba da bani tsaro da kulawa kaman yanda aka saba. Har fira saida yayi mani, kafin ya tashi ya fita. Ina mai jin daɗin yanda Abbana ke nuna mani soyayya da kulawa, kullum abunda ya kan kirani dashi shine "Hasken Fuska ta, Hasken Masarauta" wanda hakan ta sanya har sunan ya bini, kowa da Gimbiya Merama Hasken Masarauta yake kira na. Duk abun nan da akeyi gabana bai dena faɗuwa ba. Butsu butsu na duba lokaci, ganin har yamma tayi Muhammadu bai dawo ba. Gashi a lokacin babu wayar tafi da gidanka sosai. Muhammadun yana da ita, Amman ni bana da ita, saidai land line, wanda itama tana cen sashen mu balle in kira shi inji. Wajen ƙarfe shidan yamma ne naga jakadiyan ta shigo da gudu kiran mai babban ɗaki, haka tabi bayan ta duk kuwa da cewa tsufa ya kama ta sosai, ga kuma matsalar ƙafa. Sun kwashe wajen awa bata dawo ba, har akayi kiran sallar magariba. Na tashi da kyar na gabatar da salla ta. Sannan na koma na zauna ina mai jar carbi. Har akayi isha'i mai babban ɗaki bata dawo ba. Dan ma na samu amintattun haɗiman mai babban ɗakin suna taya ni fira, saboda kaɗaici, kada in zauna hakanan. Har na fara bacci bisa kilishi, inda nake kishingiɗe, sai Naji muryar mai babban ɗaki bisa kaina, tare da ta Abba na. Miƙewa nayi zaune, ina mai jan hijab ɗita na gyara ta sosai, ina mai cewa "Abbana kaine da daddaren nan?" Gyaɗa man kai kawai yayi, yana mai zama kusa dani, ban kawo ma raina komai ba, saboda sau tari Abbana ya kan yi mani hakan. Kukan da mai babban ɗaki ke riƙewa ne ya shiga ƙwace mata. Ai sai nayi saurin ɗaga kai na kalleta. Da sauri ta wuce zuwa ɗakin ta, tana mai girgiza kai. Sai kuma hankalina ya tashi, na maida kallo na kan Abbana domin son jin dalilin kukan tsohuwar. "Dukkan mai rai mamaci ne, sannan Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi, saboda haka ne nake mai baki haƙuri Maryam..." "Abba lafiya kuwa? Wani ne ya mutu? Ina Muhammadu yake?" nima na faɗa cikin tashin hankali ina mai yunƙurawa zan tashi tsaye. Hannu na Abbana ya damƙa, yana mai maida ni ya zaunar. "Shine Abunda nake so in faɗa maki yanzu Maryam. Muhammadu babu Abunda yake buƙata daga wajen ki yanzu dai addu'a. Kiyi mashi addu'a kuma ki sanyaya zuciyar ki, dukkan mai rai sai ya ɗanɗana mutuwa, haƙiƙa kinyi rashin Maryam, ko nace munyi dashi, to saidai Allah yafi mu sanshi, saboda haka yau Allah ya karɓi ran mijin ki Muhammadu, don Allah kada ki tada hankalin ki, kin dai ga a halin da kike ciki a yanzu" Tun ina jin abunda Abbana ke faɗa, har na koma saidai sama sama nake ji shi, ɗif naji jina da gani na ya ɗauke, banda ƴar ajiyar zuciya da na sauke a hankali. Sai kuma jiki na ya saki gabaki ɗaya na sheme nan saman cinyar Abbana. Salati ya saka, yana mai kwala ma mai babban ɗaki kira. Da sauri ta fito tana kai kallon ta gareni. Sai kuma itama ta saki salatin. Masalan da suka ga yanda cikina ke motsi yana kai komo kaman zai ɓallo ya fito. Da sauri ta shiga kiran bayin nata, inda suka rugo da gudu zuwa gare mu suna masu sadda kai ƙasa, saboda kasancewr Mai Martaba a wajen. Firfita da ruwa aka shiga yi mani, sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali, ina mai fara surutai. "Bai mutu ba, tayaya ma za'a ce man ya mutu? Ai ɗazu muka rabu dashi, yace man zai dawo kada kuyi mashi ƙarya, ba'a wasa da mutuwa, Abba ka faɗa masu su bar kuka, Muhammadu na yana nan da ran shi, wallahi zai dawo" na dinga surutai ina jijjiga jikin Abbana da nake kwance bisa jikin nashi. Kuka da salati wajen ya kaure dashi, duk dariyar Abbana shima saida ya share kwalla, duk da kasancewr Shi Sarki, kuma a gaban bayin shi. Da kyar aka shiga ɗaki dani, ina fizgewa ina jijjiga sosai, baki na har kumfa yake fuddawa, na zare na zama kaman wata mahaukaciya, har saida takai anyi danasanin faɗa mun, saidai da Abunda ya zama dole ne. Ɗakin da aka saka ni domin bani baki, sai da na bubbuge duk wanda suke riƙe dani, wai ni a sake ni zanje in gano Muhammadu na. Da naga dai da gaske ake ya mutum. Kuka na saki ina mai zubewa ƙasa sosai. Kuka nake baji ba gani, faɗi nake a barni in ganshi, me ya same shi? Me ya kashe shi?. Babu wanda ban sanya kuka ba a ɗakin. A daddafe aka kwana haka dani zur, ko runtsawa babu wanda yayi. Bayan an gama shirya shine da safe, aka buƙaci da abarni in ganshi. Ko dana shiga wani sabon babin kukan na buɗe, duk da nasan babu kyau kuka irin haka ga mamaci, saidai ba zan iya jurewa bane, Muhammadu ya gama man komai. Kwance yake damɓal cikin makara, sanye da fari tar ɗin likaffani, sai fuskar shi kawai da aka buɗe, jikin shi ko ina kaca kaca da jini, kaman kayi mashi magana ya amsa, fuskar nan tashi tayi tar da ita, ya ƙara kyau, yayi fari tas dashi, kaman ma yana murmushi. Saman shi na faɗa ina mai runtse idanu na, "Gashi nan yana kyaftawa, wallahi bai mutu ba zai tashi, ku ciro shi daga cikin makaran nan, ku dena kashe mani miji" Abunda nake faɗa kenan cikin gunjin kuka, janye ni akayi da kyar, ana mai cewa addu'a zanyi mashi. Ina ji ina kallo aka ɗauki gawar miji na aka fita da ita, jini har tsiyaya yake, duk kuwa da cewa an shirya shi sosai. Da gudu nabi bayan su da suka ɗauki makarar, riƙe su na shiga yi gam, ina mai jawo su zuwa baya, lallai ni su sauke man miji. Kada suje su binne shi cikin ƙasa da ran shi, zai tashi, zafin ciwo ne kawai yasa suke ganin kaman ya mutu. Ɓanɓare ni aka shiga yi, ina kuka ina ginji ina komai aka janye ni daga wurin. Inda ina ji ina gani ina kuma kallo aka fita da gawar mijin nawa, kuma mahaifi ga Suhan. Ɗiya ta guda ɗaya tilo da na mallaka. Kuma mata ga Muhammadu Al'ameen Zubewa nayi ƙasa sosai nana wurin har kaina yana mai buguea sosai. Daganan ban sake sanin inda kaina yake ba. Suma nayi? Me nayi Allah ne kawai masani. Ban tashi gane halin da nake ciki ba, saida akayi kwana biyu, daganan ne na tabbatar ma kaina shikenan Muhammadu ya tafi, yayi tafiyar da ba zai taɓa dawowa ba har abada, gashi ban haihun ba, balle ma yaga Abunda yake faɗar yana mai tausaya mashi. Kuka kuwa nasha shi. Har saida ruwan hawaye na ya ƙafe, saidai zafi da idanun suke man da wani irin raɗaɗi, kaman nayi kwalli da barkono. Idanun ko buɗewa basa yi. Abunda ya sake ba kowa mamaki shine, duk abun nan da akeyi wai Alhaji Nura, da iyalan shi basu zo ba, saidai aikowa akayi wai a faɗa mana suna nasu zaman makokin a cen Katsinan. Nan da nan fa gida ya ɗauka, masu gulma nayi, masu zunɗe nayi, masu tausaya man sunayi. Wasu ma cewa suke ai Allah ya ƙara man, kafewa da nayi da na cewa na sai na aure shi, gashi nan ina ta fama da matsaltsalu. A haka daddafe akayi kwana uku, kowa ya kama gaban shi, aka barni cikin kewa da jimami, duk da mai Babban ɗaki, da kuma Abbana suna iya ƙoƙarin su akaina. Ga ciki na daya sake komawa ya kwanta, babu motsi ko wani abu da zai nuna maka abunda ke ciki na yana raye. Ba ci, ba sha, ba bacci. A haka rayuwar ke gungurawa har zuwa wani ɗan taƙaitaccen lokaci. Kullum tsakani na da Muhammadu Addu'a ne. Ina tunano rayuwar shi, da irin haƙurin da yayi, na shi fa tun da Allah yasa ya taso bai taɓa jin daɗin rayuwar shi ba, har sai bayan aurena dashi. Sai gashi ya tafi ya bar masu duniyar. Da babu Abunda ke cikin ta, banda rigingimu da tashin hankali. Kwanakin takaba ta suka ƙare, har yanzu ban koma daidai ba. Ga mafarkai masu muni da nake yawan yi. Saboda hakan ne ma aka barni yanzu nake ɗan zazzagawa da tada jini na. Saboda yanzu idan ka kalle ni, ba zaka kuma kallo na ba, na fita hayyaci na. Nayi baƙi na rame. Sashen Baba waziri na nufa domin gaishe shi, bayan na fito daga cikin gida wajen matan sarki. Tun kafin in ƙarasa naji kaman ana magana ƙasa ƙasa a ɗakin shi. Nayi mamaki da matan shi basu shaida man yana da baƙi ba, hakan ce ta sanya ni sallamar kuyangar da ta rako ni, na zauna falon zaman jiran fitowar shi. Dayake falon babu kowa, sai hakan ya bani damar jin sautn maganar da akeyi a cikin ɗakin tana tashi a hankali a hankali. Muryar wani wanda ban sani bace naji tana tashi a hankali, cikin dariya da annashuwa. "Mai girma waziri ai ka kwantar da hankalin ka, insha Allah wannan kujerar kaman ka hauta ne ka gama, ni kuma wannan dukiyar ta riga ta zama tawa ta gama, domin bana jin idan akwai wani wanda yasan da cewa dukiyar Muhammadu na wuri na, kaf faɗin gidan nan. Saboda haka ne, ni kayi man daidai, banga laifin ka ba, na shirya mutuwar Muhammadu da kayi, duk da yana ɗanɗan ɗan uwa na. Sai magana ta biyu, yanzu ya kake ganin ya kamata ayi da Maryama da abunda yake cikin ta? Sanin kanka ne cewa koda ka hau kujerar nan, watarana dole dai sarauta ta koma ma abunda Maryama ta haifa, kuma kaga dole ne in miƙa mashi dukiyar shi. Duk da cewa shima uban nasa ba yanda baiyi ba akan ya amsa na hana shi... " Ɓaɓɓakewa akayi da dariya sosai sannan aka tafa hannuwa. Muryar Baba Waziri najiyo yana cewa;" Ai ka bari kawai Nura, au Alhaji Ibrahim, na manta da ashe ka daɗe da cenza suna ko? To Alhaji Ibrahim ina so ka sani, komai nake yi fa da tako nake yi, ai yanzu na kammala nata shirin itama Maryamar, da ita da abunda ke cikin ta duka ba zasu kai labari ba, jira kawai nake yi ta fara naƙuda, kaman yanda na shaida maka, komai zai tafi daidai. Ina nan da kai zaka ji an fasa kukan mutuwa biyu, nata da kuma na abunda ke cikin ta..... " Ai ban jira naji me zai idasa cewa ba na miƙe, jiki na yana ɓari, bakina yana kyarma. Ƙafa cikin sauri na baro falon, kaman zan kife, inayi ina waiwaye baya, kada ace sunjini ko sun ganni. Baki na toshe da hannuwa na. Saboda tsabar tsorata da nayi har wani sauti sauti nake saki. Ita kanta mai babban ɗaki tayi mamakin gani na hakan. Hankali na fa in yayi dubu ya tashi, sai kuka nake, haka tayi tambayar duniya ta gaji, har taji haushi ta shiga cewa zata gaya ma Mai Martaba ne ai, ƙila shi zanji maganar shi, tunda tana ɗauka ko mikin mutuwar Muhammadu ce ta taso mani. Wadda ke kwana dani ma haka fir yau nace saidai ta kwana falo. Domin akwai abunda nake saƙawa sosai cikin zuciya ta. Mai babban ɗaki tayi faɗan tayi faɗan har ta gaji ta sanya mani idanu. Domin lallaɓa ni da akeyi, saboda abunda ke ciki na. Ni kau cikin daren na haɗa kaya na tsaf, kala biyu ne sai na jiki na. Sai hijabina dana ɗauka, da kayan jariri guda biyu, sai zanen goyo da tawul dana ɗauka, hadda reza da zare, duk na haɗa na ɓoye. Sai ƴan kuɗaɗe da na ɗiba, cikin wanda Muhammadu yake bani lokacin da Yana raye. Daren kwana nayi salla, da kuma roƙon yafiya, da gafarar abunda nake shirin aikatawa. Ya zama dole in tsira da rayuwa ta, da na abunda yake ciki na, shi kaɗai ne jinin Muhammadu wanda zan kalla inji daɗi. Asubar farko kuwa Allah ya bani sa'a na fice daga gidan, nasha wahala sosai kafin in samu in fita, saida nayi ta laɓe laɓe, na bi ta ƙofar baya na fice, lokacin da aka shiga masallaci sallar asuba. Nasan ban aikata daidai ba. Ina tausayn Abbana da mai babban ɗaki, saidai su kaɗai ne wanda suka rage mani a duniyar nan wanda zan ce na ƙuntatamawa, kuma na tafi ne ba'a son raina ba. Tafiyar da ta zame mani danasani kenan a rayuwa ta. Saidai fitar da nayi ba tare da sanin inda na dosa ba, ban taɓa kawo ma raina cewa zan kuma waiwayar gida ba. Na yafe rayuwar gidan sarauta. Na bar masu dukiyar mulkin, da komai da komai. Ɗanɗana gudan jinin Muhammadu shi kaɗai nake so a raye. Dukiya mulki basa gabana. Na gane babu abunda ke cikin shi, in ka ɗauke tsantsr tashin hankali da son zuciya da yake cikin shi.... *Umma* ta dakata da maganar tata da take yi, cikin wani irin tsumammen kuka, kanta a ƙasa. Sosai mikin mutuwar tsohon mijin nata ta taso mata sosai. Shima kuwa mai martaba da kanshi sai share kwalla yakeyi, cikin tausaya ma ɗiyar tashi. Mama Fulani ma kuka take yi, jin halin da ɗiyar ƴar uwar tasu ta shiga, suma sauran matan sarkin gabaki ɗaya haka. Waziri kuwa tuni jikin shi ya hau kyarma, bai taɓa tunanin ɗanyen aikin da suka aikata zaiyi munin haka ba, bai taɓa tunanin wannan ranar tana zuwa ba. Sai gashi shi kaɗai yana mai girbe abunda su biyu ne suka shuka shi. Hajiya Kubra kuwa hawaye ne ke zirara daga idanun ta, tayi tsamo tsamo. Tana yi tana fyace majina. Sosai labarin ke Dakar mata zuciya, kunya, danasani ƙyeya, shine abunda take ji yana ɗawainiya da ita. Bata taɓa sanin ɗanyen aikin da mahaifinta ya aikata ba, bata kuma taɓa ɗauka halin rashin imann mahaifin nata ya kai haka ba. Haka kuma mahaifiyar tata bata taɓa bata labarin abunda ya wakana ba ko bayan mutuwar mahaifin nata, kuma itama bata taɓa tambaya game da ɗan uwan nata Muhammadu ba, dama tun cen iyayen nata sun riga sun dasa mata tsamar shi a zuciyar ta, in ba yanzu ba ma, bata taɓa kawo ma ranta cewa ta tambaya ko yana raye ko baya raye ba, kawia abunda ta barma ranta shine. Mahaifin nata baya da kowa baya ga ita. Kaman yanda tun bayan mutuwar mahaifin nata babu wanda ya ɓulla yace shi ɗan uwan mahaifinta ne, ashe ma bata sani ba Muhammadu ya riga mahaifinta mutuwa, kuma mahaifin nata yana da hannu a mutuwar ɗan uwan nata, kuma ɗanɗa ga ɗan uwan nashi tilo. Al'ameen kuwa zaune kawai yake kaman mutum mutumi. Idanun shi zan iya cewa sun fi garwashi ja. Shi kanshi baisan a wane hali yake ba. Illa iyaka dai har yanzu ya kasa koda motsa yatsan shi ne. Jira kawai yake Umma ta ɗora daga inda ta tsaya, domin a yanzu ba zai iya cewa ga matsayar da yake kai ba. Har sai yaji ƙarshen ta'asar da Baban Mahaifiyar tashi ya tafka. A ga jali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai sauke kanshi ƙasa, inda yayi amfani da yatsan shi, wajen ɗauke guntun hawayen da yake neman gangaro mashi. Wani irin son Suhan, kewarta da tausayin ta yana mai ratsa mashi zuciya, ashe haka tasha gwagwarmayar rayuwa?tazobkuma ta ɗora wata a gidan nasu. Duk ta dalilin mahaifiyar shi da mahaifin ta? Da wanne ido zai kalle ta. Son zuciyar na kakan nashi har ya kai haka?. A hankali ya runtse idanun shi, yana mai hango fuskar Suhan, yake ayyano kamannin mahaifin nata a cikin fuskar tata. Tasha faɗa mashi cewa Umman ta tace mata ita marainiya ce, saidai zata so ace ko hoton Abban ta ne Umman ta ta nuna mata. Bata taɓa sanin sarƙaƙiyar labarin ta, na mahaifinta ba da mutuwar mahaifin nata da take da alaƙa da shi kakan nashi ba. *Duk ranar da ta san hakan da wane irin ido zata kalli mahaifiyar shi dashi kanshi? Kuma ya alaƙarshi da ita zata cigaba da kasancewa? Kuma ya al'amarin auren nasu? Shin zata yadda ma tacigaba da zama dashi a hakan kuwa? Duk da tasan cewa kaf wahalhalun da suka sha, da mutuwar maiahin nata, suna da alaƙa da Hajiya Kubra da mahaifin ta?* _Hmmm Muje Zuwa Fans_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~75~* *Abin Da Ake Fada don kawar da kaidin shaidanu Masu Taurin Kai.* أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ. A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman. Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama! *Ban manta dake ba ƙawata, koda yaushe ina faɗin _Ilove u wujiga wujiga, haƙiƙa Alkhairin ki gareni ba zai kisaltu ba, saidai kawai ince Allah ya barki tare da baban Al'ameen ya raya mana Ameen kuma ya shirya mana shi. Kiji daɗin ki ki walwala ki shana duniyar taku ce. Lahirar ma haka insha Allahu Mrs Daura* i͠n͠a͠ k͠i͠k͠e͠ ƴa͠r͠ d͠a͠r͠u͠ t͠a͠ s͠u͠m͠i͠e͠e͠ b͠. (a͠m͠i͠n͠t͠a͠ & m͠i͠j͠i͠n͠ b͠a͠h͠a͠u͠s͠h͠i͠y͠a͠) w͠r͠i͠t͠e͠r͠. h͠a͠ƙi͠ƙa͠ g͠o͠y͠o͠n͠ b͠a͠y͠a͠n͠ k͠i͠ d͠a͠ s͠o͠n͠ i͠n͠y͠i͠ m͠a͠ f͠a͠n͠s͠ t͠y͠p͠i͠n͠g͠ y͠a͠n͠a͠ d͠a͠g͠a͠ c͠i͠k͠i͠n͠ a͠b͠u͠n͠d͠a͠ k͠e͠ ƙa͠r͠a͠ m͠a͠k͠i͠ ƙi͠m͠a͠ a͠ i͠d͠o͠ n͠a͠. a͠l͠l͠a͠h͠ y͠a͠ b͠a͠r͠k͠i͠ d͠a͠ m͠a͠s͠u͠ ƙa͠u͠n͠a͠r͠ k͠i͠. m͠a͠ƙi͠y͠a͠n͠k͠i͠ k͠u͠m͠a͠ a͠l͠l͠a͠h͠ y͠a͠s͠a͠ s͠a͠i͠d͠a͠i͠ s͠u͠ d͠i͠n͠g͠a͠ h͠a͠n͠g͠o͠ b͠a͠y͠a͠n͠ k͠i͠. a͠i͠ i͠n͠a͠ y͠i͠n͠k͠i͠ t͠a͠ w͠a͠j͠e͠n͠a͠ °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Rage sautin kukan Umma tayi, tana mai share hawayen da suke kwance male-male a kan fuskar ta. Lokaci guda ta ja majina a hankali, tana mai muskutawa. Lokaci guda kuma falon ya ɗauki tsit. Kowa da Abunda yake saƙawa a cikin zuciyar shi. Ci gaba tayi da cewa; "Tafiya nake cikin hasken alfijir daya keto, wanda da kyar nake lalubawa ina jefa ƙafa ta duk inda ya samu, lokaci guda kuma ga wani irin juyi da yunƙuri da naji cikin nayi, wanda na daɗe rabon da inji ya motsa, tun rasuwar Muhammadu. Haka naci gaba da tafiya har haske ya fara bayyana, rana ta soma ɓullowa. In naji cikin ya katsa mani sai in samu wuri in duƙa inta nishi da murƙususu har dai in samu ya lafa, sannan in tashi in dasa tafiyar tawa. Kuka nake sosai, ina tunanin halin da zan jefa rayuwa ta ciki data mahaifa na. Abbana ni kaɗai ya mallaka, tabbas nasan wani mummunan abu zai iya samun shi, muddin aka neme ni aka rasa, sai dai na zaɓi hakan ne, kasancewar domin in tsira da rayuwa ta, data abunda yake cikin ciki na, wanda ko iskar duniyar ma bai kai ga shaƙa ba, Amman ana so aga bayan shi kan abun duniya da ya kasance mai wucewa ne. Koma menene na haƙura dashi. Da kyar na samu na siya ruwan leda da ake ƙuƙƙullawa a tasha nayi alwala, na koma ƙarƙashin wata runfa ta mai siyar da abinci a cikin tasha na tayar da salla. Mai abincin dai sai kallo na take yi. Kayan dake jikina da komai nawa bai yi kama dana mai bara ba, sai dai a yanayin da ta ganni turtse-turtse da ciki tasan ba lafiya ba. Abincin da ban taɓa cin irin shi ba tun da uwar data haife ni, yau shi na siya naci da kuɗi na. Ba daɗi Sam hakanan na gama turawa na bata kuɗin ta, sannan na tashi na ƙara gaba. Cikin tasha na shiga sosai, ina jin ana ta ambatar garuruwa, Amman sam banji an ambaci sunan garin da ya kamata ace naje ba, wanda yake cikin lungu, inda ba lallai bane ko sun biyo ni su cim mani da wuri. Garin Jigawa, shine sunan da naji ya kwanta mani arai. Ko ba komai zuciya ta na raya mani idan naje cen zan tsira da rayuwa ta, ba ɓata lokaci ko shawara na faɗa motar, ina mai samun kujerar can baya na zauna. Motar ta daɗe bata cika ba, har na gaji da zama, ga ciwon mara sosai da yake murɗa ta. Har matar da take zaune kusa dani take ce mani "Baiwar Allah kodai naƙuda kike yi ne?" saidai in girgiza mata kai. Haka motar nan ta tashi, ina ji ina gani na bar gari na, mahaifa ta, mahaifar iyaye na, inda nake da gata da galihu. Tunda motar nan ta tashi nake kuka mai cin rai, ina kallon matar nan saidai ta kalleni ta girgiza kai. Har kai lokacin da muka isa. Gari ne mai yalwa da ni'ima sosai. Hakan ta sanya saida nayi salla. Sannan na siya bredi da lemo na sake ci Wata motar na kuma shiga, inda Naji suna ambata sunan wani ƙauye da yanzu na manta sunan. Ba tare da sanin inda na dosa ba na kuma shiga motar. Kuɗin da suka buƙata na ciro na basu. Gashi dai marece ya kawo jiki sosai da sosai. Gashi bansan inda zan nufa ba, wurin kwana ma kawai ya isheni tunani. Motar bata sauri, saboda haka ga wari ga tsami na tashi daga cikin motar. Hakan ya sanya zuciya ta tashi na dinga kwara amai a cikin motar, ga kuka inayi ga ciki yana ta motsi da son fitowa. Mun yi tafiya mai nisa sosai a cikin ƙauyuka motar ta lalace. Dole muka firfito ana dudduba motar. Muna wajen har magariba tayi, ba abunda nake tunani sai Abbana da Mai Babban ɗaki. Ina ji ina gani dole sallah ta gagareni a wannan lokacin. Gashi ƙarfina ya fara ƙarewa, masu surutu dai saiyi suke ina ji. Wai tayaya ma za'ayi nasan ina da tsohon ciki in tattagi tafiya irin wanna? Masalan ma da hanyar bata da kyau. Jin hakan da nayi ne ya sanya ni sake tsurewa, gashi naga sai sulalewa suke suna tafiyar su gami da yima driver ɗin Allah ya isa. Har yanzu kuma babu mota ko gida data doso hanyar da muke. Gashi naji suna faɗin cewa hanyar wai fashi da makami akeyi. Jin hakan nima na fara tattara kayana da kyar da niyyar barin waje. Matar da muka shigo mota ce da ita, ta ɗago ƙafa da kyar tana kai cimma ni, inda nake nufar wata hanya wadda bansan inda zata sada ni da ba. "Baiwar Allah ina zaki ne haka? Gashi kuma naga kina cikin halin rashin lafiya, sannan ga dare yayi, idan ba zaki damu ba ki biyo ni zuwa gida na mana cen gaba kaɗan, alabasshi da safe kya wuce, hanyar garin namu ce bata da kyau ko kaɗan" Da idanu nake binta, ban iya ce mata komai ba, ba yunwa ga ƙishi. Da kyar nayi mata murmushi ina mai cewa "Nagode baiwar Allah" Bayanta na shiga bi, inda ta kama mani jikkar kaya na. Gata da sauri, ni kuma ban iya sauri ba, uwa uba turtsetsen cikin da nake ɗaga ƙafa da kyar ina nishi. Sai tayi gaba sosai sai ta jirani in iske ta, da ƴar cocilar da take haskawa har muka isa cikin ƙauyen. Bamu wani yi tafiya mai yawa ba muka isa zuwa gidan da yake kaman shine nasu. Saboda kai tsaye naga ta cusa kanta zuwa cikin gidan. Ba kowa a tsakar gidan da yake ginin ƙasa da danni. Da sauri ta ɗauko mani kujera ƴar tsugunno ta ajiye mani gindin wani ɗaki. Da kyar na zauna. Kai daka kalle ni kasan bana cikin hayyaci na. Ɗakin da yake kusa da inda nake zaune nan ta shigar mani da kaya na. Tana mai fitowa da sauri kuma ta shige ɗan madafar da yake cen gefe ta hura wutar kara, sannan ta ɗora tukunyar ƙasa, duk ina hango ta, ta hasken farin watan da ya fara ɓullowa. Zaman kujerar fa ya gagareni, dole na sauke ƙasa ina mai miƙe ƙafafu na. Inda nake zaune ta dawo tana mai jawo kujerar ta kai zaune. Macece wadda zamu iya kiran ta da matashiya, duk da ta girme mani sosai, saidai ba zata haifeni ba, duk da a lokacin kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci tsantsar halin babu dake tattare da ita. "Sannu baiwar Allah, ni sai nake ganin ma kaman naƙuda kika fara tsai tsaye, gashi kuma ba ƴan uwan ki kusa, kodai delu unguwar zoma zan kira ta duba ko haihuwar ce?" Girgiza mata kai na shiga yi. "A'a Adda bama sai an kira ta ba, cikin nan yafi shekara haka ina fama dashi..." Katse ni tayi cikin firgita da kaɗuwa "Ke baiwar Allah, kinsan me kike cewa kuwa?" Katseta nima nayi ta hanyar ɗaga mata kai. Shiru tayi tana mai sake kalle ni tsaf, sai kuma ta nisa tana mai faɗin "Bari dai Malam ya shigo to muji idan da wani taimako da zai iya baki, kenan cikin kwantawa yayi, ikon Allah" Tana gama faɗin haka ta tashi ta shige madafar, tana ta aikace aikacen ta cikin ɗan hasken wata, har kai lokacin da ta gama girkin. Tuwo ne ta girka da miyar kuka. Nan ta zubo mana muka ci, tana ɗan yiman fira jefi jefi, har take tambaya ta inda na nufa, ganin nayi mata shiru ne ya sanya sai kuma jikin ta yayi sanyi. Kada fa ace tayi gangancin jawo ni gidan ta, ba tare da ta san koni ɗin wacece ba. Muna tsaka da cin abincin ne Malam ɗin ya shigo bisa ɗan keken shi. Shima ba tsoho bane kaman yanda na zata, dan a lokacin ba zai haura shekara arba'in ba. Jiki na rawa ta tsame hannun ta, tana mai miƙewa take mashi sannu da zuwa, kunsan mutanen da, har ƙasa ta duƙa tana gaishe shi, sannan ta wuce kai tsaye cikin ɗaki ta ɗauko kofin silver mai kyau ta ɗiba mashi ruwa a randa ta kai mashi ɗaki. Duk da ya kula da wata zaune, sai baiyi mata maganar ba har saida suka shiga ɗaki. Tarar numfashin shi tayi da cewa "Yauwa malam dama bari nayi kasha ruwan sannan,..." nan ta kwashe duk yanda mukayi har zamana a gidan ta faɗa mashi. Cikin tausaya wa yace mata ta gyara man ɗakin in kwana, zuwa safe saji koni ɗin wacece da kuma cikin dake jiki na. Nan ta dawo ta iskeni zaune. Nima na kasa ci gaba da cin abincin. Na tsame hannu na, har na siɗe shi tas na rafka uban tagumi. Ba sai na faɗi Abunda ke damuna, Tunda duk wanda yaji labari na yasan ina da dalilin damuwar. Taso ta fahimci wani abu, Amman sai ta share ta shige ɗakin tana mai gyara man, tare da umurtata da in shiga ciki in yi sallah sannan na kwanta. In taƙaice maku dai daren ranar ban samu runtsawa ko ɗaya ba. Tun da safe sai gata ɗauke da ƙwarya da ruwan ciki, miƙo man tayi tana mai shaida man ruwan addu'a ne inji malam. Cikin ɗan sakin fuska na amsa, ina mai godiya haɗu da gaishe ta. Tana gama amsawa ta fice, tana mai shaida man cewa lallai in tabbatar na shanye ruwan duka. Gari na idasa wayewa duka, sai gata ɗauke da kunun tsamiya da ƙosai kai zafi ta shigo, shima banƙi ci ba, saboda yanda nake jin yanayin jikin nawa da yunwa, duk da ciwon marar ya bari, saidai juyin da cikin ke tayi. Abun mamaki duka yinin ranar wannan matar bata tambaye ni komai game dani ba, haka bata sake man maganar tafiya ba, ashe wai sunyi magana da malam mijin ta yace su ɗaga man ƙafa, duba da yanayin da nake ciki. Haka kuwa akayi na share kusan sati a gidan, mutane ne masu girma da daraja sosai, saboda a zama na dasu banga wani abu da yaci karo da addini ba, ko kuma suyi Abunda zai dagula man lissafi, ita matar mai suna Hajjo ce ma ke yawan lallashi na, duk lokacin da ta kula na faɗa komar tunani. Ya zuwa yanzu har na ɗan sakin jiki dasu, daga ita har malam ɗin da nake mashi kallo kaman na mahaifi na. Duk da na lura kaman Allah bai basu haihuwa bane su, Shiyasa suke murna da ɗokin cikin dake jiki na, duk da basu san asalin cikin ba. Abun ka da ƙauye, sai gashi raɗe raɗi na yawo a ƙauyen cewa wai ni ƴar uwar matar malam ɗince naje nayo ciki, shine nazo nan zan haihu, akan hakan har mai garin saida ya sanya aka kira malam. Saidai bansan yanda sukayi ba, nidai kullum kuka, baci ba sha, duk na rame na ƙanjame. Su Malam ɗinne ke saka ni gaba da lallashi da komai, har yanzu cikin su babu wanda ya tada mani wata magana. A haka aka samu gulmace gulmacen yayi sauƙi, babu inda nake zuwa kullum ina gida, saidai na kan ɗan taya Hajjo aikace aikacen gida, duk da ba wai sabawa nayi ba, Amman ina ƙoƙarta wa a hakan inayi,kasancewar babu Abunda ban iya ba, Tunda ni ke girka ma Muhammadu abinci da hannu na lokacin da yana raye, har yake yaba mani kullum, wai gani gimbiya Amman abun duniya bai dameni ba, shi bai taɓa ganin gimbiya iri na ba. Nakan yi mamaki ince mashi "Ai aljanna nake so, ita kuma aikin ladar mace ga miji ba ruwan ta da sarauta" ya kan yi dariya shima ya rungume ni ya shiga taya ni aikin.a haka rayuwar cikin sashen mu take gudana, Allah sarki, ashe shi ɗin Allah yayi ba mai yawan kwana bane, sun kashe man shi, sun kashe shi yabar duniyar, ya barsu suci abunda zasu ci ciki. Duk lokacin da nayi irin wannan tunanin saidai Hajjo taga ina kuka, da kyar take samu ta lallashe ni. Sai danagaji da ɓoye ɓoye sannan na ɗan shaida masu malam ɗin halin da nake ciki, Amman na ɓoye masu ni ɗin wacece da kuma su wanene iyaye na. Hakan ce ta sanya su ƙara tausaya man, tare da Alƙawarina zama dani har sai komai ya kwaranye. Ranar wata Lahadi ina cikin bacci, sai naji kaman an tsunkuleni, firgigit nayi na tashi, sai ciwo kuma yace man salamu alaikum. Nishi da murƙususun da Hajjo ta jiyo ne, yasanya ta fitowa da sauri, aiko sai ta taraddani ba yanda nake ba. Da sauri ta zari hijab cikin dare taje ta kira delu unguwar zoma, saboda taga alamun haihuwa ce. Masha wahala sosai kafin in haifo yarona santalele namiji, murna kaman me, cen kuma sai ga mace ta biyo baya watau Suhan. Ansha murna sosai, inda aka gyara ni. Yara kyawawa dasu kaman su sukayi kansu, saidai namijin baya da lafiya sosai, ko numfashi da kyar yake yi. Kafin gari ya waye yaron ya koma. Nan aka gyara shi gami da shirya shi, zuwa safe aka binne shi a cen gefen gidan. Saboda irin kukan da nakeyi ya ɗaga ma kowa hankali, tun da na haihu banyi shiru ba, gashi dai na haihu lafiya, Amman sai komai ya dawo man sabo, ni gimbiya nice da haihuwa irin ta marasa galihu, gashi yau na haihu ba gaban Mai Babban ɗaki ba, Muhammadu baya raye, haka kuma Abbana baiga yaran ba. Duk wani abu da akeyi mai jego sunyi mani shi, saidai godiya tsakani na da mutanen nan. Mutane dai shigowa suke barka, duk da wasu da biyu suke zuwa suna gani na da jaririyar da ta rage mun. Haka akayi taron suna, inda ni da kaina na zaɓa ma yarinyar Sunan mai babban ɗaki, na cika ma Muhammadu burin shi, da wasiyyar da ya bar mani. Yarinya taci suna Hauwa'u, sunan Mamana kuma sunan mai Babban ɗaki kenan. Dalili da hakan ne ya sanya nake mata laƙabi da Suhana,ko kuma ince Mama a Haka rayuwar mu taci gaba da gungurawa, yau fari gobe baƙi, dole na fara ƴan aikace aikace, saboda in samu in samu Abunda zan kula da rayuwar yarinya ta, abun tausayi sai ga gimbiya da surfau, dakau da wankau, hakan bai dameni ba. Saboda har ga Allah nasan hakan ya fiye man in zauna inyi rayuwa a inda yake da haɗari. Allah ya sanya man ƙaunar yarinyar sosai a raina, gashi ta taso da kyau da wayau sosai abun ta, kowa so yake ya ɗauketa yayi mata wasa, ta saba da malam kaman shine mahaifin ta. Watarana ina wankin da aka kawo mani, Hajjo na madafa tana tuƙa tuwon dare, Suhana da malam na zaune a ƙarƙashin wata ƴar baranda da take ƙofar ɗakin malam, sauraren radio malam ɗin yake yi abun shi, wanda ya zame mashi al'ada. Akai akai yana yi ma Mamana wasa, ita kuwa sai ɓangala dariyar ta take ta faman yi. Kwatsam sai naji ana sanarwar rasuwar mahaifi na. Salati Naji malam ya sauke, yana mai tafa hannaye, kasa cigaba da wankin nayi, na zare hannu na ina mai miƙewa na isa inda malam yake zaune shi da Suhana, itama Hajjo da sauri ta fito jin salatin malam ɗin "Malam Lafiya kuwa? Me ya faru? Wanene ya mutu?" cewr Hajjo da take goge hannayen ta jikin zanen da take ɗaure dashi. "Bawan Allah! Allah kenan, sa'i yayi, ina sarkin da nake baki labari cewa ɗiyar sa ta ɓata? Wadda na taɓa shaida maki cewa an sanya cigiyr yarinyar tare da kyautar maƙudan kuɗi ga duk wanda ya gano ta? To ai shine tun lokacin sarkin Baida lafiya sai an kwantar sai an tayar, kinga dai har yanzu ba'a ga yarinyar ba, gashi har Ajali ya cimma shi, Allah ya jiƙan adalin sarki ya gafarta mashi, haƙiƙa anyi rashin sosai, saidai muce Allah ya kyautata makwanci... " Ai ban ƙara sa jin abunda malam ke faɗa ba, saidai suka ga na sulale ƙasa a some. Sai kuma suka yo kaina a sukwane, inda Hajjo ta shiga girgiza ni tana kiran sunana," Maryama! Maryama ki tashi subhanallah, me yake faruwa ne? Malam dama baka faɗi wannan tashin hankalin a gabanta ba, Kaga Maryama mutum ce mai rauni, na tabbata tausayi ne ya kama ta" Sakina tayi tana mai rugawa randa ta kamfato ruwa a kofin silver, tazo ta miƙa ma Malam suka shiga shafa man. Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sai kuma na saki kuka mai haɗe da sauti da kururuwa, ina ta surutai marasa kan gado. Basu fahimci komai ba, haka kuma basu tsinci ko kalma ɗaya danake faɗa ba, Hajjo ta janye ni zuwa cikin barandar, kan shimfiɗa malam ta shiga yi mani firgita da maficin da malam ya miƙo mata. Har yanzu hankalin su a tashe yake sosai. In taƙaice maku kusan kwana nayi kaman na zare na haukace, sai inyi kuka sai inyi dariya, abun duniya duk yabi ya damu su Malam, sai tofi malam ke man a ruwa Hajjo na ɗura mani, wani kuma a shafa man. Haka muka kwana muka yini, ko nono naƙi ba Mamana, juyin duniya na hana ta, haushinta ma nake ji, sai faɗi nake "Meyasa na zaɓi farin ciki na, rayuwa ta? Ta ɗiya ta, nayi wasarere da ta mahaifi na? Ta dalili na ya mutu, nice na kashe shi. Baƙin ciki na ne" Basu dai fahimta ba, duk sun ɗauka tsabar ruɗewa ne, har Hajjo ke cewa wai kodai iska ne suka kama ni? Malam ne ya kwaɓe ta da cewa "Ba wata iska bana son Jaye jaye Bahijja kawai ki taya ni muyi mata addu'a" Cikin ikon Allah washe gari na samu sauƙi sosai, saidai kuka da nake ta rizga, ina haɗa kaya na nake cewa ni tafiya zanyi. Sunyi lallashn duniyar wanda ba zasu fahimci me nake nufi ba, har yanzu ni kuma zuciya ta bata Aminta da in shaida masu meke faruwa ba. Da kyar suka shawo kaina na zauna, nima nayi tunanin zaman ne saboda kada in koma su ganni da ɗiya kuma su halaka mana rayuwa, anyi biyun babu kenan, gashi sun yi sanadiyyar mutuwar mijina, uba na, kuma suyi sanadiyyar mutuwa ta data ɗiya ɗaya tilo ɗana mallaka tare da Muhammadu. Addu'a sosai na dinga yi ma mahaifi na. Kullum ina ganin mutuwar shi kaman sanadi na ne, saidai ba yanda za'ayi na kuma dosar masarautar tamu, masalan ma yanzu da nasan burin waziri daf yake da cika, watau na hawan karagar mulkin mahaifi na, wanda yake yanzu mallaki na, mallakin Muhammadu da yanzu ya riga ya kushe. Wata zuciyar na tunzari ni, gami da ƙarfafa mani guiwa, Amman wata na kwaɓa ta, akan in ƙyale masu ko wanne irin mulki ne a duniya ake barin shi, gashi yanzu mahaifina ya tafi ya bar shi. An yi kusan wata muna haka, kullum tsakani na da Malam da Hajjo nasiha ce ta kuma ƙarfafa guiwa, duk da har yanzu basu san ne ke faruwa ba. Watarana da asuba na fito na shiga bayan gida saboda in kama ruwan alwala, sai naga kaman giccin mutum ta cikin hasken farin wata. Da sauri na fito ina mai komawa ɗaki inda Mamana take kwance, sai na tadda tana ta kuka sosai, kuma ba'a inda na ajiye ta take ba, bayan na fita ba barta ne tana bacci, da acibalbal ɗin dake hannu na na haska, banga komai ba, in baya ga cenjin wurin dana iske ta. Sai ban kawo ma raina komai ba, saboda yanzu tana rarrafe ne, sai nayi tunanin rarrafowa tayi da bata ganni ba. Gashi cikin duhu. Haka na lallashe ta, na koma nayo alwala nazo na tada sallah. Ban faɗa ma kowa ba, kuma akaci gaba dayin hakan har kusan kwana uku. Rannan sai nace sai naga me yake faruwa. Ina shiga bayan gida, sai na kashe fitilar nayi sanɗa na fito na nufi ɗakin. Garjejen ƙato naci karo dashi, ya fito hannun shi ɗauke da mamana, ya toshe mata baki sosai ko kukan da take yi ma ba'a ji. Yana gani na sai ya sake ta, ta faɗi ƙasa, ya bangaje ni har na faɗi nima ya ruga da gudu. Kukan da ta saki ne yaja hankalin su Malam suka fito suma a ruɗe, tadda ni sukayi a yashe ƙasa ina ta ƙoƙarin tashi na ɗauko Mamana, da gudu Hajjo ta ƙaraso tana mai ɗaga ni, yayin da Malam ya ɗauko Mamana. "lafiya Kuwa Maryama ko faɗuwa kikayi? Me yasa kike fitowa da ita a daidai wannan lokacin?" Hajjo ɗin ta faɗa tana mai dudduba jikina da ƴar acibalbal ɗin dake hannun ta. Gyaɗa mata kai kawai nayi, zuciya ta sai azalzala take yi, kaman zata tsago ƙirjina ta fito, na tsorata sosai, kenan sun gano inda nake zaune, to tayaya? Sun gano ina raye kenan? Sun gano na haihu kenan? To tayaya? Malam ne ya miƙo man Mamana ɗin yana mai cewa "ki dinga kula da ita sosai Maryama, ki dena barin ta tana kuka irin hakan" da "To" na bishi, ina mai karɓarta na shige da ita ɗakin, yayin da shi Malam ya wuce yin alwala, Hajjo kuma ta shige madafa. Ai ina shiga sai na hau tattara kayanmu, dole ne inbar garin nan, dole in tsira da rayuwa ta, waɗannan mutanen ba zasu taɓa bari in zauna lafiya ba, na bar masu komai da komai, yanzu na kula rayuwar tawa kawai suke nema. Saida na tattara komai sannan na adana shi. Cikin ikon Allah kuma Hajjo bata shiga ɗakin ba, balle taga kayan dana haɗa, ina jiran dare ya rufa in ci gaba. Tare muka ci tuwon dare muna ta fira, nayi ƙoƙarin sakin jikina ne a ranar saboda kada su fahimci wani abu, Amman Allah ne kaɗai yasan yanda nake ji a cikin zuciya ta. Har mukayi sallama na shige ɗaki ina kallon su Hajjo da tausayawa, saboda yanda suka kwallafa da rai ga Hauwa'u, komai suce Maijidda. Ƙarfe sha biyun dare ma batayi ba, na goya Mamana, na saɓi kaya na, wanda dama ba wasu yawa ne dasu ba, na fice daga gidan. Tafiya nake sosai, inda Allah ya taimake ni ma Mamana bata tashi ba, har yanzu bacci take yi. Nice ban isa hanya ba sai da safiya tantagarya. Fuska ta lulluɓe da liƙab, hakan ya sanya ba kowa ne ya shaida ni ba. Har na tare mota. Bansan ina ta nufa ba, Nidai kawai na shige, kada ma a biyo sahu na a cimmani. Sai daga baya na kula wai ashe garin Abuja ne muke nufa. Ikon Allah kenan, gashi bansan ina zan dosa ba, Tunda ban taɓa zuwa garin ba. Hawaye kuwa sai ambaliya suke mani ina gogewa ta cikin hijab, idan Mamana ta motsa sai in bata nono tasha, ga yunwa da nake fama da ita, gashi ba wani isassun kuɗi gareni ba. Har muka sauka a tasha inda kowa zai kama gaban shi, Allah ma yasa na harhaɗa kuɗin motar da kyar na biya, duk da haka saida wani bawan Allah ya cikasa mani. Yanda na kula gari ne wanda zan iya kiran shi da kowa harkar gaban shi kawai yake yi, saboda haka ne babu ma wanda ya damu dani ko sha'ani na. Abunda zan ci ma saida nayi kaman bara sannan na samu naci, na lallatsa na ba Mamana. Haka na naushi hanya a ƙasa, jami'an tsaron da nake haɗuwa dasu ne, dole ta sanya na yaye lulluɓin fuska ta. Lokacin akwai ƙarancin rashin gaskiya, hakan ya sanya ba'a damu sosai dani ba. Yanke shawara nayi ta shiga gida gida neman aiki, wani gidan ma daga waje mai gadi zaice man ba'a buƙata. Nayi nisa sosai a tafiya, har dare ya cim mani, ga yunwa ga gajiya ga mamana, sai kuka take mani, itama yunwar take ji, nonon babu ruwa, saidai tayi ta ja hakanan. Gidan da na yake shawarar da gashi zan haƙura in ban samu ba, babban gida ne Naji da gani sosai, a yanda na kula mai gadin nada sauƙin hali, tunda a tausashe yayi mani magana cewa "Masu gidan ma basa nan, Amman sun kusa dawowa, zan iya zama idan sun iso sai in masu magana" gefe daga ciki na samu na zauna, shine har ya bani wani ɗan buzu nashi na shimfiɗa Mamana sama, sannan ya bani abincin shi da baici ba, naci na ba Mamana, sannan ne fa nayi sallah gami da addu'o i na sosai, tare da nema na mahaifina gafara, haɗi da neman tsari daga dukkan azzalumi. Saboda gajiya danayi sosai, haka na dunƙule na kwanta bisa ɗan buzun da ya ara mani ni da Mamana, har bacci ya fara kwasa tane, sai kuma naji ƙarar horn na mota, aiko zumbur nayi na miƙe zaune, duk da ina ta cikin gidan ne, wanda zan iya kiran shi da aljannar duniya. Daf dani motar tayi parking, hakan ya sanya ni ɗauke mamana, na tashi da gudu, sai naga kaman motar zata take mu ne, saboda da alama matuƙin motar baisan da wanzuwa ta a gurinnba, duba da yanayin wurin bai kyautu ace mutum na zaune a wurin ba. Su biyu ne suka fito daga motar, sai yaran su guda uku, matar tana saɓe dana cikon huɗun a kafaɗar ta. Da gani dai sune mamallakin tanƙamemen gidan. Ƙarar da nayi ce ta ja hankalin su su duka, da sauri Alhajin ya iso inda nake tsaye ƙanƙame da Mamana a hannu, tsabar firgita duk na ƙanƙame Suhan kaman za'a ƙwace man ita. "Subhanallai baiwar Allah lafiya kuwa? Ba'a dai taka ki ba ko?" Abunda Alhajin ya ce man kenan cikin sake wa, da tsantsar kulawa. Ba kowa bane sai Alhaji Mustapha Dambulan, tare da matar tashi Hajiya Kubra, ɗiya ga Alhaji Nura/Ibrahim, wanda idan baku manta ba, ni ban santa ba, haka itama bata sanni ba. Sai yaran su Nafisa, da Al'ameen, sai Saudat tana goyon Nihal a lokacin, wanda zata iya kai shekara ɗaya ma. Dukansu idanu suka zuba man, suna sauraren abunda zance. Kasa bashi amsa nayi sai dai girgiza mashi kai dana hau yi, kwalla na shatata a idanu na, saboda saura kaɗan driver ɗin ya taka mu. Shi kuwa dreban sai bani haƙuri yake yi. Hannu Alhajin ya kai da niyyar amsar Mamana, Hajiya Kubran ta dakatar dashi ta hanyar cewa "Haba Alhaji, wacece nan wai? Da kake ƙoƙarin amsar mata yarinya? Me tazo yi anan ne me ya kawo ta?" Maganar kubran tayi tasiri wajen Alhajin, saboda haka ne ya sauke hannun shi ƙasa, yana mai zuba man idanu yaji me zance. Cikin in'ina na shiga cewa "Dama uhm, dama aiki nazo a taimaka man dashi don Allah" "Aiki! Wanne irin aiki kuma haka? Cewar Hajiya Kubra, da take cen daga baya tsaye, har yanzu ba zan iya shaida fuskar taba, haka itama. "Wanke wanke, shara ko wanki da guga, insha Allahu duk wanda ya samu zanyi Hajiya" Da sauri ta dakatar dani ta hanyar cewa "A'a bama dashi gaskiya, muna da ma'aikata, kuma sun ishe mu hakanan, mu da bama zaune muke ba, dindindin.." Alhaji Mustapha ne ya dakatar da ita, ta hanyar ce mata "A'a Kubra barta dai, kai Nuhu! Zo ka kira mani Talatu" ya faɗa yana kwala ma Nuhu kira, wani mutum da yake cen zaune suna fira da mai gadi. Da gudu ya amsa, yana mai nufar wani ɓangaren na gidan. Sai gasu sun dawo su biyu, shi da wata mata wadda zan iya kiran ta da cewa Zatayi tsarar Hajiya Kubran. "Kuje da wannan matar ciki, a sama mata ɗaki ta kwanta kafin safe, sannan a bata abinci" Abunda ya faɗa kenan, yana mai kama hannun Al'ameen suka nufi cikin gidan. Dan dole Hajiya Kubra ta mara mashi baya, tana tafe tana mita. Bansan dai ya suka ƙare ba, Nidai nabi matar cikin sashen da da gani na masu aiki ne, har wani ɗaki inda babu komai cikin shi sai katifa, Saurin sauke mamana nayi, wanda duk ta galabaita, tayi laushi sosai, sai fidda numfashi take tayi a hankali a hankali. Kafin in farga matar nan ta kawo man abinci ta ajiye ta juya tayi ficewarta. Haka dai na kwana, inda Allah ya taimake ni, a ɗakin akwai banɗaki da toilet. Harda water heater, saboda haka ne nayi ma Mamana wanka, nima nayi. Daren ranar dai na kwana cikin sauƙi zance, Tunda zuciya ta na shaida man insha Allah nazo maɓoya. Washegari kuma sai ga Alhajin da kanshi ya aiko kira na. Ban ajiye Mamana ba na tafi da ita a hannu. Ba ƙyama ba komai ya sanya hannu ya amshe ta, yana mai mata wasa na shiga gaishe shi. Cikin sakin fuska sosai yake amsa mani. Ba tare da ya buƙaci jin komai ba, ya shiga shaida man ya amince da in zauna inyi aiki, Amman duba da yanayin ina da goyo ba za'a bani mai wahala ba, Allah dai ya sanya na iya girki, domin zan shiga cikin gida ne in dinga masu girki duk lokacin da Allah ya sanya suna nan. Na iya na tabbatar mashi, miƙo man Mamana yayi, yana mai zaro kuɗi masu ɗan dama ya bani, sannan yaja kunne na da dukkan Abunda zan gani daga matar gidan na kauda kai, duk Abunda zata man in haƙura, Talatu zata shiga dani ciki ta koya man komai. Aiko nayi murna, koda na koma ciki har sallah nayi ta godiya ga Mahalicci na. Talatu ta gwaggwada man komai, saboda haka na kama aiki na ka'in da na'in. Duk wani abu da zai sa ace nayi ba daidai ba na guje shi. Sai gashi cikin ikon Allah na zauna da kowa lafiya, duk kuwa da cewa ina ganin wasu abubuwa da ba daidai ba daga wajen Talatun. Abunda na kula dashi shine mutanen cikin gidan ba kullum suke nan ba, hasali ma kaman idan anyi hutu ne suke zuwa nan, saidai naji raɗe raɗin cewa a Katsina suke zaune. Ba zan taɓa manta garin ba, ko ba komai dai Muhammadu ya taɓa mu'amalantar garin, duk da dai cewa ga yanda abubuwa suka kasance, ba wai yaji daɗin mutanen gidansun bane. Abu na farko daya fara tsorata ni shine sunan Kubra da nake yawan ji Alhajin na ambata. Indai ba zan manta ba, Muhammadu ya sanar dani yana da wata ƴar uwa Kubra, sai kuma gashi ance ita ɗin ƴar Katsina ce. Nan fa na tsure, kullum gani nake kaman in bar gidan, kada ya kasance cewa tazo ta gano ko ni ɗin wacece ta shaida ma mahaifin ta yayi nasara a kaina. Ashe ina tunanin na tsira ma hallaka na kawo kaina. Amman yanda Alhajin gidan yake da kirki da ƙwafƙwaf akai komai ya sanya ni zama, aman har yanzu na kasa sakin jiki. Koda aka tashi tafiya Katsina ni cewa nayi ba zanje ba yarinya ta tana mura, sai aka ci sa'a Alhaji Mustapha ɗin ya fahimce ni, duk da wasu abubuwa da nake fuskanta daga wajen matar gidan. Haka naci gaba da zama, ina kula da Mamana, yarinya mai wayau, kyau, farin jini. Uwa uba kuma ta taso mai natsuwa da hankali, duk abunda na hana ta ba zata kuma aikata shi ba. Ya zuwa yanzu na idasa tabbatar mana kaina cewa lallai Hajiya Kubra matar gidan da nake zaune, itace ɗiya ga Alhaji Nura. Ka duba dan Allah, san kai ƙiri ƙiri, kullum kuma ina zaune ne ina tunanin dukkan Abunda take taƙama dashi fa, ko mahaifinta ke taƙama dashi mallaki na ne ni da yarinya ta Suhan, marainiyar Allah wadda babu Abunda ta sani a rayuwar ta. Cikin tsakanin ne wani tashin hankali ya samu zuri'r gidan da nake zaune, watau Mutuwar Alhaji Nura data same mu kwatsam rana tsaka, shi da mahaifiyar Hajiya Kubran watau Bilkisu, ta sanadiyyar hatsarin jirgi wanda ya rutsa dasu. Aikuwa hankali ya tashi, yayin da zuciya ta ta tsinke nayi ta kuka. Me mutane ke nema da wannan rayuwar ne? Abunda yake toƙabo dashi yake nema yaki halak, yaki haram gashi ya tara kuma ya tafi ya barta. Ina ji ina kallo aka share makoki aka miƙa ma hajiya kubra dukiya. Yayin da bayan mutuwar mahaifin nata da wani lokaci suka tattara suka dawo Abuja da zama baki ɗaya, lokacin ne ta haifi Abie, daganan kuma sai Afnan. Daganan sai haihuwar ta tsaya mata. Ba zan manta ba, watarana da yamma Hajiya Kubra tayi baƙo, sai aka umurceni da in kai mashi abun motsa baki. Hantata ta kaɗa lokacin da muka haɗu da Baba Barrister, dama shi na sanshi wajen Alhaji Nura ɗin tun gidan mu. Shima hankalin shi ya tashi da gani na. Sai ya basar har suka gama abunda zasu yi yabar gidan, ashe ya sanya ma ran shi cewa zai neme ni. Sai watarana zanje kasuwa muka haɗu dashi a hanya, nan ne yake shaida man cewa sarauta dai ba'a ba Baba waziri ba, Baffana ne ya dawo daga ƙasar waje aka bashi, dama ƙanwar Matarshi mama Fulani tayi aure tuni, acen ta samu mijin, sai daga baya ne suka tattaro su kansu suka dawo. Inda manyan majalisar mahaifina sukayi ma Baffana naɗin riƙon ƙwarya kafin bayyana ta. Saboda ba tabbacin cewa cikin da na tafi dashi ban haife shi ba. Nan ne ya nuna mani lallai zai ɗaga Wancen case ɗin domin a dawo man da dukiya ta kuma zai tsaya man, zai tattara dukkan wasu bayanai da yake tare dasu, kuma yana da tabbacin zai samu nasara. Nice na roƙeshi akan cewa na haƙura, bana buƙatar komai, kuma yayi ma Allah yabar maganar hakanan, inci gaba da zama a talauce na cikin rufin asiri. Ba don yaso ba dole ya ƙyale ni, inda daga baya ya wakilta yaron shi ya cigaba da yima Hajiya Kubra aiki watau Barrister Kb. Duk na sani kuma ina kallon ta, dukkan wani abu da take yi akan ido na ne. Maganar ƙin amince ma auren Suhan da Al'ameen ya samo Asali ne da wannan ranar, ba zan so ace komai yazo ya tonu ba ba tare da sanin wacece Hajiya Kubra ba Wajen Suhan. Saboda tun Suhan na yarinya Allah ya sanya ma Al'ameen ƙaunar ta, tun kafin su tattara su koma ƙasar waje yake zuwa yayi ma Suhan wasa, ya ɗauke ta ya giya ta. Hakan ce ta sanya naso yanke alaƙa shaƙuwar tasu tun kafin komai yayi nisa, domin nasan tabbas indai da rai da rayuwa wannan ranar tana zuwa. Ban tsaya hakanan ba, na ɗan bibiyi rayuwar gidan su Hajjo, inda na gane cewa bayan tafiya ta wanda suke neman rayuwa ta basu tsaya hakanan ba, domin su Alhaji Nuran sun masu alƙawarin maƙudan kuɗaɗe idan har suka samu nasara a kaina. Ashe bayan na tafi bansan inda suka samo gawarwaki ba, suka shirya ta sosai ta uwa da ɗiya, suka zo suka kaima Malam da Hajjo suna kuka, suka shaida masu mota ce tayi haɗari da wannan matar da ɗiyar ta, har an shirya su za'ayi masu sutura sai aka samu wanda yasan daga inda take. Malam yaso a warware a sake man sutura, inda suka babbake suka hana. Ba dan malam yaso ba haka aka sallaci gawargwaki aka bizne ta. Hajjo tasha kuka sosai, har malam saida yayi kuka ba kaɗan ba, inda su kuma waɗancen mutanen suka koma wajen su Alhaji Nura suka ce sun gama komai. Da suka bincika suka ga lallai hakan ne, sai suka basu kuɗin su suka sallama su. Wannan ne dalilin da ya sanya ko lokacin da na koma da Suhan basu yarda ina raye ba. To kunsan nace maku basu san komai ba, hakan ce ta sanya nima ban sanar dasu komai ɗinba, kawai dai nace bani baceba suka yi ma sutura. Akwai akai Barrister na tuntuɓa ta akan idan na cenza shawara in tuntuɓe shi, shi zai tsaya ya amsa man haƙƙi na, nice na kan ce mashi yabar maganar kawai ni yanzu duk ba ta wannan nake ba. Nayi hakan ne saboda zaman daraja da mutunci da mukeyi da Alhaji Mustapha, yasan haƙƙin na ƙasa dashi, sai nake jin ba zan iya tozarta iyalan shi ba, ba zan iya zama silar kunnowar wata masifa da zata iya wargaza zaman shi da matar tashi ba. Saidai Abunda Hajiya Kubra tayi mana, wanda yasanya har nayi sha'awr barin gidan, shine dalilina na amince ma Auren Alhaji Mustapha, wanda ada naƙi amincewa, sai naga wannan ai dama ce da zan nuna ma Hajiya Kubra kuskuren ta, na cewa kowanne ɗan adam da ka gani yana da rana. Kuma na tabbata Alhaji Mustapha yana da adalcin da zai tsaya man wajen ganin na amshi haƙƙi na, tunda gabaki ɗaya duk kauda mata kai da nake yi bata sani ba. Na janye ƙudiri na ne ta dalilin auren Suhan, Saboda Al'ameen ya wuce matsayin suruki a wuri na, haƙiƙa yayi mana halaccin da zan iya cewa kaf gidan nan babu wanda yayi mana shi hatta dashi mahaifin nashi da yake zaune anan, watau Alhaji Mustapha. Bana da ƙuduri na amsar dukiya ta a yanzu, kuma har gaba ma bana jin zan iya amsar ta na bar mata, saidai ta Suhan ce ba zan iya cewa komai ba, yanzu hukunci ya rage gareta kuma. Sannan maganar zama da Al'ameen ba zan shiga ba. Idan har taji zata iya zama da Al'ameen da Hajiya Kubra a matsayin Suruka toh! Falillahil hamd, idan ba zata iya zama da ita ba, ina so wannan masarauta tayi ma yarinya adalci, ko yaya ne ta ɗanɗana zaƙin ƴanci a bakin ta a karo na farko.... Kuka ne ya sarƙe ta yaci ƙarfin ta, wanda da sauri ta miƙe tana mai nufar babban ɗakin da yake cikin falon. Saboda wani irin kuka ne wanda ya tado mata da miki da tabo wanda har yanzu yaƙi warkewa a rayuwar ta. Babu wanda keyin ƙwaƙƙwaran motsi a cikin falon.gabaki ɗaya sun jikin su yayi sanyi. Kukan Hajiya Kubra ne kawai yake tashi a hankali a hankali. Har yanzu babu wanda yayi yunƙurin ma ce mata wani abu. Labari ne wanda kowa yaji shi kaman almara, tayaya ɗan adam kuma musulmi zai iya aikata hakan? Dolene masarauta ta hukunta waziri ta yanda zai zama izina ga ƴan baya. Su kansu Alhaji Mustapha da Alhaji Auwalu zaune kawai suke gingirim. Kunya ce ma duk tabi ta dabaibaye su, masalan Alhaji Mustapha ɗin. Tayaya ma za'ayi ace surukim shine ya aikata wannan ɗanyen aikin? Wane irin haƙuri Maryama take dashi. Da har ta iya jure wannan al'amari? Ashe haka rayuwar ta take cike da miki da tabo? Zurum suka ga Al'ameen ya miƙe, yana mai nufar ƙofar da zata sada shi da waje, ba tare da yace ma kowa komai ba. Kaman Alhaji Mustapha ɗin zai tsayar dashi, Alhaji Auwalu da Mai martaba suka mashi alamu da ya ƙyale shi. Dole yana buƙatar shan iska, yana buƙatar hutu, yana buƙatar kaɗaicewa. Da kyar ya kai kanshi wajen, tun daga nesa Bilal dake zaune yana latsa waya saman mota ya hango shi. Durowa yayi da sauri, yana mai ƙarasawa ta inda yake dosar shi. Da hannu yayi mashi alamun da ya dakata. Ba musu Bilal yaci burki, hankalin shi a tashe, domin ya sani duk lokacin da yaga aminin nashi a cikin irin wannan halin, toh fa ba lafiya. Zagaye shi yayi, kai tsaye ga motar ya isa, cikin takun shi da zamu iya cewa haɗa hanya kawai yake yi. Ba wata wata ya faɗa motar gami da yi mata key ya kwanane ta da gudun tsiya kaman zai take Bilal ɗin da yake tsaye, wanda saida yayi ɗan tsalle gefe. Da kallo ya cigaba da bin motar, inda har saida ta ɓace ma ganin shi, lokaci guda ya sauke ajiyar zuciya yana mai furta *Oh ko me ke faruwa kuma?* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassanu (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~76~* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *Ina fatan za'a dinga yi an afuwa jina da ake shiru kwana biyu. A dai yita haƙuri damu hakanan don Allah* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Zamu iya cewa tuƙi kawai yake yi da hannu guda, ɗayan hannun kuma yana cikin sumar kanshi, wadda take kwance saman kyakkyawar fatar kan tashi, tasha gyara sai salƙi take yi kaman ta larabawa. Shi kanshi har yanzu zuciyar shi bata idasa tantance ina hannun nashi ke juya steary ɗin motar ba. Gabaki ɗaya ji yake kaman bashi ba, kaman ba Al'ameen dambulan da ya kasance cikin natsuwa ƴan shekaru da suka wuce ba. *"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi museebatii Haza wa aklifnee khairan minha"* kawai yake furtawa cikin zuciyar shi. Domin shi kanshi wannan al'amari ya girmi tunanin shi da hankalin shi, ba zai taɓa yadda da wannan labarin ba, da ace ba daga bakin Umman yaji shi ba. Wane irin zalunci ne haka? Wane irin haƙuri Umman Suhan, kuma suruka a gareshi take dashi har haka? Dole ne tayi ciwon zuciya, dole ne abubuwa suyi mata haka, ashe tana da hujjn ce mashi da take *Watarana sai labari* ashe a haka labarin zai zo? Ashe a haka labarin ya kasance?. Da wane irin ido take kalilan Mom ɗinshi dashi? Gashi kuma har ta iya ɗaukar ɗiya ta bashi? Har ta iya haɗa zuri'a da kakan nashi watau Alhaji Nura. Wace irin salihar baiwa ce wannan? Yana fatan ace matar tashi ta ɗauko koda ace kashi hamsin ne na daga cikin kyawawan Halin baiwar Allah Umma, wanda yana kyautata zaton hakan a gareta. Ta daɗe tana cutu wa, ta rasa mijin ta, uban ƴarta sannan mahaifinta da kuma dukiyar ta da duk Abunda ta mallaka, kuma tana zaune a ƙarƙashin gallazawar ɗiyar azzalumi, kuma tana mata bauta ba dare ba rana, sannan tana kiyaye duk wata doka da ƙa'ida da zata gindaya mata, duk da tasan cewa duk tutiyarta da tunƙahon ta mallakn tane. Shiyasa ake cewa karka raina mutum, bakasan wanene shi ba, baka san kuma me zai zama nan gaba ba, kuma baka san kaina ya rayuwar taka zata ƙare ba. Yau wa gari ya waya? me tsanar da Mom ɗinshi tayi ma Umma ta tsinana mata? Yau da ace Uwa ba Uwa bace, babu Abunda zai sanya shi waiwayawa ya kalli Mom ɗinshi, da zai tsayin daka wajen ganin an hukunta Mom da halayen ta, da kuma duk wata tutiya da gadara tata. Lumshe idanun shi yayi, yana jin wani irin tuƙuƙin baƙin ciki na kwarara a cikin ƙahon zuciyar tashi. Baƙin wani tafkeken ruwa yaja burki ya tsaya, da kyar yayi controlling kanshi wajen tsayawar, dan saura kaɗan motar tashi ta sukkuta cikin tafkeken dam ɗin. A sukwane ya fito daga motar, har yanzu hannun shi guda yana cikin kan nashi, da gudan hannun yayi amfani wajen dafe ƙugun shi. Tafiya ya shiga yi yana bin gefen ruwan, zuciyar musulumci ce kawai ta hana shi wuntsilawa cikin ruwan, ko zai huta da wannan halin dayake ciki. Idanun shi kuma sun koma kaman garwashi, tsabar tashin hankali, da yanda yake jin bugawar zuciyar shi na daɗa ƙaruwa, abunka da farin mutum, fuskar nan kaman an gaggaura mashi mari, masalan kan tsinin karan hancin shi, wanda yake kaman ya taɓo leɓon bakin shi na sama. numfashin shi har wani ja yake yi, da kyar yake fizgar shi. Sanyi da iskar bakin ruwan na kaɗa mashi kayan jikin shi, da duk wani gashi da yake kwance a jikin nashi. Amman hakan bai hana shi jin kaman yana cikin wuta ne ba. Ya rasa tunanin ne zaiyi, a hankali kwallar da yake ta faman danne wa ta shiga silalowa tana gangarowa daga ramin idanun nashi, sai yanzu ne ya ɗanji sa'ida ta fara shigar shi, zubar ruwan hawayen sai yake jin ya tafi da kaso ashirin cikin ɗari na tsantsar ɓacin ran da yake fama dashi. Bai hana kanshi ba, illa dai iyaka kawai ya zaro hancky daga cikin aljihun wandon nashi ya shiga matse idanun nashi, baya fatan ma ruwan hawayen ya dakata da zuba, ko hakan zai sa yaji sauƙin zuciyar shi. Ajiyar zuciya yake saukewa akai akai, lokaci guda kuma yana mai kai zaune bisa farin rairayin yashin da yake wurin, wanda gaɓar ruwa ta ɗan jiƙa, sai ƙamshin ƙasa ke tashi a hankali a hankali. Ta ina zai kamo ne? Ta ina zai fara ne? Wai shin a wanne irin hali halayen mahaifiyar tashi ke neman jefa Rayuwar shi ne, data Dad ɗinshi? Ƙarar wayar shi ce tayi sanadiyyar sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi, daga zurfaffan tunanin da ya shiga, lokaci guda yana mai ɗan firgita. Kiran ta ne ke shigowa cikin wayar tashi, wani sautin busar sarewa ne mai matuƙar taushin saurare ne ke tashi, mai sanyaya zuciya ma'abociyar so da bege. Wanda ya sanya aka buga mashi shi kawai saboda ita. A duk lokacin da kewarta ke addabar zuciyar shi, ya kan yi amfani dashi ne wajen kauda damuwar da kewar tata ke haifar mashi, ba zai iya ɗagawa ba, kaman yanda ya kasa kuma datse kiran, da idanu yake bin secream ɗin wayar da kallo, wanda har saida ta katse wani kiran ya kuma shigowa ba ɓata lokaci. Nan ma Gaza ɗagawa yayi, me zaice da ita? Tun yanzu wata irin kunya ce ke saukar mashi a cikin zuciya, kai kace ma tana gaban shi, a halin da ake ciki ma bai san da kalaman da zai furta ya kira ta da sunan da ya saba kiran nata ba na wify. Saida wayar ta saurara da tsuwwa ne, sannan ya iya sauke hannun shi, yana mai janye ƙwayar idanun nashi daga kan fuskar wayar. Toh amma me? Ya kyauta kenan? Idan fa bai manta ba, Tunda ya iso bai kira ta ba, balle ya shaida mata ya iso lafiya. Yana niyyar ajiye wayar bisa cinyar shine, ƙarar saƙo ya ziyarci kunnen shi, alamun saƙo ne ya shigo wayar tashi. Bai ɓata lokaci ba saboda zuciyar shi tana raya mashi ita ce. Ita ɗin dai ce, kaman yanda ya zata. Har kullum kalaman ta masu taushi ne a gareshi, kalaman nata sune tsani dake daɗa tabbatar mashi da irin soyayyar shi dake cikin birnin zuciyar tata. _Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah. Hubby da fatan kun isa lafiya? Ya hanya ya kuka iske su Mom ɗin? Duk ina gaishe da kowa, a gaida Ya Bilal shima da Dad_ _Ma'assalam ina kewar ka mijina, Ka huta lafiya, i kissed u.. Muahh_ Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, lokaci guda kuma yana manna fuskar wayar zuwa cikin ƙurjin shi. Ji yake ina ma ita ce? ina ma tana kusa? Ya rungume ta cikin faffaɗan ƙurjin nashi ko yin hakan zai samu sauƙi. Fuskar ta ce mai yalwace da sassanyan kwantaccen murmushi a koda yaushe yake tunowa, Suhan daban take a cikin zuciyar shi, ya daɗe yana dakon wani maƙoƙo a zuciyar shi, ashe bai sani ba tsantsar sonta ne ke kai komo a zuciyar tashi. Kaso talatin yake jin wucewr shi a cikin zuciyar tashi, koda Suhan take a matsayin matar shi, sannan Mom take a matsayin mahaifiyar shi. Hakan ba zai sa ya kasa mata adalci ba, duk da yasan ba lallai ta gujeshi ba, saidai shi adalci wani abu ne, kuma hakan ne zai daɗa tabbatar mata da cewa shi mai iya tsaya mata ne duk rintsi duk wuya. Miƙewa yayi a hankali, yana mai soka wayar aljihu ba tare da ya fita daga imbox nashi ba, kakkaɓe hannun shi yayi, lokaci guda yana mai kai kallon shi tsakiyar ruwan, inda masu kamun kifi ke ta sha'anin su. Babu damuwar komai tattare dasu. Motar ya koma ya zauna, har yanzu fuskar nan tashi kaman bai taɓa dariya ba, to dama wace Allah cika, shigowar Suhan rayuwar shi ce ta sauya abubuwa da dama, idan har ba zan manta ba kenan. So yake mata mai tsabta, ba jikin ta ba, ba kyawun ta ba. Saidai so ne na tsakani da Allah, wanda zamu iya cewa yayi ƙaranci a wannan zamanin. Ya maimaita karanta saƙon ta yafi sau shurin masaki, yana ji a cikin zuciyar shi cewa bai fa kyauta mata ba, me ya hana shi ɗaga wayar ta? Baisan lokacin da ya samu kanshi yana mai danna keyboard ɗin wayar ba, ya shiga maida mata amsar saƙon nata, yana fatan ace ta ji daga gareshi, koda zuciyar ta da hankalin ta zasu kwanta. _Wslm Janam, ina cikin ƙoshin lafiya, haka hanya ma lafiya, kuma kowa ma lafiya, ina kewarki nima. Will call u later. I Love u with all my heart. Take care with my love, i kissed u too_ Turawa yayi cikin sauri, yana mai fatan ace ta karanta saƙon nashi a cikin lokacin, saboda ta samu sauƙin tunani. Bai sauke fuskar wayar ba, saida yaga alamun saƙon ya isa ga wadda yaso. Sannan ya sauke wayar ƙasa, yana mai yima motar tashi key ya bar wurin cikin salon shi mai ɗaukar hankali. *Toh Ya Ameen ko ina kuma aka nufa?* ********************** Fitowa yayi cikin sauri, agogon rolex ce a hannun shi na dama, wanda yake ta ƙoƙarin ɗaura ta a hannun hagun, saura kaɗan suci karo dashi yayi saurin ja baya... "Ke Lafiya kuwa?" ya faɗa cikin basarwa, yana wani yamutsa fuska kaman yaga kashi. kwallar da take danne wa ne suka shiga zubo mata, ai sai ta idasa sakin kukan mai sauti sosai, lokaci guda kuma ta nufeshi da niyyar faɗa mashi a jiki. Sake ja baya yayi, aiko santsin tiles ya kwashe ta, ƙasa tayi ba shiri, inda kanta ya bugu da side na wall da yake hanyar da zata sada ka da bedroom ɗin nashi. Kukan take yi sosai, duk da yanda wajen yayi ja, har ma ya soma ɗagawa, hakan bai dame ta ba, ta sake Miƙewa cikin kuka take cewa "Baby ni kake gudu? Ni kake ƙyama baka iya haɗa jiki dani? Please ne nayi maka har haka? Kasan yanda nake sonka? Please kada ka bari sonka ya kashe ni, ka janye maganan auren, wallahi na gyara, na iya komai yanzu har ma...." "Khhh!!" ya dakatar da ita cikin wata irin tsawa, sai kuma ya shiga kaɗa hannu. "Ina fatan kinsan waɗannan kalaman naki basu da muhalli a cikin zuciya ta? Ai kaman yanda nace ne kije sai kin iya komai zan nemeki, yanzun ma bata canza zani ba, still ina nan kan baka na, kije ɗin sai nazo, Allah dai yasa har yanzu ma Mom ɗinki ba gatan take nuna maki ba, ta hanyar sanya ƴan aiki suyi maku komai. Kaiih koda ma ace hakan ne, ki sani aure ba fashi, insha Allah gobe za'a ɗaura, kuma a gobe amaryata zata tare nan gidan, ina fatan kin fahimta, sannan ki sani koda ace zaki dawo gidan nan, sai bayan amaryata ta tare, ta yanda kinga ko bakiyi mani komai ba, ina da wadda zata yi mani" Tuni ta nemi kukan nata ta rasa, bata ma san lokacin data haɗiye kukan ba, ta shiga bin Nureen ɗin da kallo. Kaman bashi ba, kaman ba Babyn taba, mai sonta, mai lallashi ta, mai zagewa yayi mata komai ba, mai yi mata daɗin bakin cewa zai zauna da ita a duk yanda take. Toh inko haka ne, ina daɗin wannan gatan? Gashi tana ji tana gani, mijin nata da yafi soyuwa a rayuwar ta na neman suɓuce mata. Wani uban ihu ta sake ƙwalawa, cikin shagwaɓa irin tasu ta sangartattun ƴaƴan masu kuɗi. Da sauri ya toshe kunnen shi, yana mai juyawa ya fice daga apartment ɗin. Itama batayi ƙasa a guiwa ba ta shiga bin bayan shi, har wani diddira ƙafafu, take so take ta jawo hankalin shi da kukan da tasan yafi tsana daga gareta a baya. Saidai ina ta makaro, yanzu zuciyar Baby tayi tsuntsuwa ta sauka kan wata bishiyar da take sabon toho. Tana ji tana gani ya shige mota, yana mai kullo ƙofar kaman da gayya, a gaban idanun ta yayi ma motar tashi key, yana mai jan ta a tsiyace bayan mai gadi ya buɗe mashi gate, saidai ya barta da ƙura. Zubewa tayi anan ƙasa rana mai rusa kukan nadama, nadamar da tasan bata da wani amfani, Mom bata kyauta ma rayuwar ta ba, ina amfanin gata da soyayyar data nun ambata, yanzu tana ji tana gani gashi gidan ta ya gagareta, wai itace yau da ɗaukar ƙafa ta maido kanta gidan miji, ba tare da yaje bikonta ba ko sau ɗaya, ba tare kuma da ya tura wani nashi ba. Jiki ba ƙwari ta tashi ta faɗa motar tata. Kai tsaye gidan Saudat ta nufa, dayake babu mai gadi yanzu gidan, saidai tayi parking motar ta ƙofar gida, tana mai faɗa wa gidan Saudat ɗin hankalin ta a matuƙar tashe, gefe guda kuma ga uban kuka da take rusawa. Saidai me. Abunda ta gani ya matuƙar tayar mata da hankali, ya girgiza ta, ƙafar ta ce ta ƙafe guri guda, ta kasa gaba ta kasa baya, wace irin rayuwa Saudat ta zaɓa ma kanta? Ashe ita halin da take ciki nafila ne? Lallai Saudat ta ɗaura ɗammarar kai kanta wuta. Kenan ma bayan maza har mata take bi? Wa'iyazubillahi, wannan wace irin rayuwa ce? Mom bata ɗorar dasu madaidaiciyar hanya ba, duk kuwa da yanda Dad yaso suyi zurfi a ilimi addini, ita da Saudat ɗin dai basu same shi ba, itama ta sani, domin ko acen ƙasar da sukayi rayuwa, a gaban Dad zasu shirya zuwa ɗaukar islamic lectures ɗin, Amman da Dad yabar gidan Mom ɗin ke kiran su su dawo gida, ko kuma ta tura masu kuɗi a account su tafi wajen shaƙatawar su. Ai sai ta kuma sakin wani kukan cikin takaici, zuciyar ta kaman zata fashe, inda ita kuma Saudat da abokiyar shashancin nata suka yi saurin Miƙewa daga bisa gadon. Saidai ganin Nihal ce, sai Saudat ɗin ta sauke ajiyar zuciya, tana mai jawo suturar ta ta maƙala, sannan ta nufo inda Nihal ɗin ke ƙame. Saidai me kafin ta idaso Nihal ɗin ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. *"Shame in you Saudat"* Abunda ta iya faɗa kenan ta juya da gudu, tana mai ƙara ma kukan nata farashi. Ita kuwa Saudat kafaɗa ta sauke, tana mai furta "On Your Own sis, Nidai ina da duniya a hannu, ba zan ƙi shanawa ba" _Toh Saudat saidai mu biki da addu'a yanzu kam. Ai kin ma ce ma Nihal ɗin bani wuri. Toh Allah dai ya shirya mana zu'ri'a ya ƙare mu daga shiga wuta. Ameen_ ************************ "Ammi wallahi zaman gidan ne a haka ya isheni, Shiyasa yanzu kika ga ma ban cika dawowa week end ba sosai, gidan ba daɗi, babu kowa Ammi, ba wata matar balle ince zan amshi su Eesher, please Ammi ki sanar da Abbi akan maganar auren nan, Kada kice nayi rashin kunya please" Sir Salim ɗin ya furta hakan, yana mai tasowa ya dawo bisa kujerar da Ammin tashi take, yana mai saƙalo ta da dukkanin hannayen shi cikin salon shafwaɓa. Ɗna duka ta kai mishi tana mai cewa "Baka da kunya Son, to ai nima na ƙagara a gama komai kam naga alama Ma'u ba dawowa Zatayi ba, ni kuma na gaji da ganin yaro na a matsayin gwauro" dariya suka sanya dukan su, yana mai manna mata peck a gefen kumatu. "I love u Ammi na, ba kaman ki a duk duniyar nan, nafi kowa dacen uwa, kuma ina ma Afnan murna ta samun suruka kaman ki, am.. Ammi tama ce in gaishe mata dake wallahi na manta ne.." ya ƙarashe cikin in'ina cikin jin kunya. "Aiko ina amsawa sosai ma, ka manta Afnan yanzu nima ɗiyata ce, ai ka bari zuwa da daddare insha Allahu zan samu Abbin naka da maganar, Kaga zuwa idan Allah ya kaimu, sai a shirya aje da maganar cen Abujan ko?" Itama cikin tsantsar soyayya da kulawa take daɗin hakan ga yaron nata. Aiko sake rungumo ta yayi tana mai sake manna mata wan peck ɗin. Saidai lokacin yaran nashi suka shigo. Da gudu Eesher ɗin ta nufo mahaifin nata, baiyi wata wata ba ya miƙe yana mai cafe ta ya shiga wulla ta sama. Ita kuwa sai kyalkyala dariya take yi cikin jin daɗin kewar mahaifin nata da tayi. Sama ya haye da ita kai tsaye, yana mata cakulkuli tana ta ƙanƙame shi. Da kallon aha'awa Ammin tabishi, tana mai sakin murmushi take jero mashi addu'oin Sa'ar rayuwa, natsuwa da kwanciyar hankali, tare da kauda dukkan idanun maƙiya, da kuma duk wani wanda zai kawo ma rayuwar tashi tarnaƙi da cikas. _Haka ake so dukkan uwa ta gari ta kasance akan yaran nata, kyakkyawar fata da addu'a, babu shamaki kaman yankan wuƙa addu'ar mahaifa ke karɓuwa wajen Mahaliccin mu. Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da yaran namu a bisa tafarki madaidaici_ ************** Bai tsaya ko ina ba sai sansanin ƴan gudun Hijiran, babu wanda ya gane motar tashi, hakan ne ya sanya masu tsaron wajen suka taso domin bincikar motar, wanda kai tsaye suke ganin ta doshi gate ɗin wurin. Saidai ganin shine da kanshi, ya sanya su washe baki, suka shiga sara mashi, sannan suka buɗe mashi gate ɗin ya kutsa hancin motar tashi. Direct Office ɗin shugaban ya wuce, saidai kowa ya kalle shi yau yasan baya cikin natsuwar shi, duba da yanda ma'aikatn wurin suke ta washe mashi baki suna gaishe shi, Amman shi saidai ya ɗaga masu hannu kawai ya wuce. Ko a Office ɗin shugaban nasu ba wata firar kirki sukayi ba, tun bayan gaisuwa, buƙata yayi da akaishi sansani inda yara suke wasa. Su kansu ma'aikatn sunyi mamaki, ganin yau Yallaɓai ɗin nasu babu wata walwala da annashuwa, maimakon ma yanda ake raha da wasa da dariya dashi, sai gashi da buƙatar da bai taɓa zuwa masu da ita ba. Baya suka rufa mashi, inda tun daga nesa da yaran suka hango shi suka shiga rugowa da gudu, suna mai mashi dafifi suka ɗane shi. Shima ɗaga su ya shiga yi ɗaya bayan ɗaya, ba wata ƙyama ko hantara,duk kuwa da cewa kaf ɗinsu sun ɓata jikinsu da ƙasa, wasu kuma majina ce yayyaɓe a hancin su, inda ƙudaje suka yi ma hancin nasu dafifi suna kwasar garar gishiri. yaba kowa mamaki a wajen, kaman ba shi bane yanzu kai fuskar shanu. Gabaki ɗayansu fata suke ace sune matsayi irin na Al'ameen ɗin, gabaki ɗaya fata suke ace dama sune shi a rayuwa, da sun gama morewa, basa tunanin da akwai wata damuwa da zata iya tasowa ta zama tarnaƙi, ko tayi masu shamaki da farin ciki mai ɗorewa na har abada. Roƙo yayi da duk su koma bakin aikinsu su bar shi da yaran na ƴan mintuna. Ba haufin komai ko ɗarɗar da wani abu suka jaye suka bar shi da yara. Inda shi kuma ya koma ya zauna a bisa dandagaryar ƙasa, inda sauran yaran suka zazzauna suka baibaye shi suma. Labari suka shiga bashi kala kala, tun baya dariya har ya koma yana murmusawa yana kyakyata dariya, lokaci guda kuma yana jin ina ma ace shine su, ina ma ace cikinsu yake? Ina ma ace baida gata da galihun da zai ke fuskantar wannan matsalar? Duk da suma sun tsinci kansu cikin wata rayuwa marar daɗi, saidai gabaki ɗayansu yana kyautata ma kanshi cewa zasu zama wani abu nan gaba, da har ƙasar tashi Zatayi alfahari dasu. Ba kaman shi ba, da duk wanda yaji labarin tarihin kakan nashi da na mahaifiyar shi sai ya tsine mashi, ya la'ance shi... Sai ya samu kanshi da zurarar hawayen da shi kanshi ba zai iya tantance na menene ba. Na godiya ga Allah ne daya sanya ya kasance ɗa a gurin Dad ɗin nashi, wanda duk duniya ta shaide shi da halin kirki nagari, ko kuma kasancewar shi ɗa a gurin Hajiya Kubra Nura. Wanda babu Abunda suka sani illa san zuciya, san kansu da son abun duniya, wanda basu damu da rayuwa da jin daɗin kowa ba sai nasu... ************ Mai martaba ne ya nisa, cikin isa da magana irin tasu ta sarakai, gefe Umma ce wanda bansan lokacin da ta dawo ta zauna ba, saidai ya zuwa yanzu kukan nata ya tsagaita, Mom ce ke magana, wanda ba zan iya cewa ga Abunda ta faɗa ba, a lokacin da bana nan. "Ya zama wajibi masarauta ta hukunta dukkan wanda yake da hannu a cikin wannan ɗanyen aiki, ya zama wajibi ga masarauta da tabi ma waɗanda aka zalunta haƙƙin su, sannan ya zama wajibi masarauta ta miƙa ma mai girma Gimbiya Merama sarautar ta. Saidai kafin nan, ni mai Martaba ina mai bada umurni da a tafi da Baba waziri gidan ajiya na masarauta, kafin ta yanke hukuncin da ya dace dashi. Haka kuma masarauta tana mai bada umurni da a kawo mata Baba Barrister, Alhaji yaro, Hajiya Laila da Hajiya Sa'a sannan a haɗo mata da Talatu mai aiki., to Amman ta ina za'a samu Alhaji yaro shi da iyalan shi? " *"Nine zan kawo shi da hannu na"* Muryar Ya Ameen ce ta karaɗe ilahirin falon lokaci guda yana mai takowa cike da wata irin dariya, dakiya tare da ƙwarin guiwa... Yayin da lokaci guda kuma hakan yaja hankalin kowa dake falon aka juya ana mai kallon shi, haɗi da tsura mashi idanu, sanin da kowa yayi cewa baya wajen har kai lokacin da Mom ɗinshi ta bada labarin kaf rayuwarta bayan rasuwar mahaifin nata, saidai kaman yanda Umma ta ɓoye gallazawar da tayi mata, haka itama ta ɓoye saboda wani dalili nata, wanda ba zamu iya fahimta ba a yanzu. ~Oum-Deedat ce~ [1/19, 7:59 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~77~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Idanun kowa na bisa fuskar tashi da take ɗaure tamau, har yanzu kowa ya gaza janye idanun nashi daga bisa fuskar tashi, har kai lokacin da ya ratsa ta tsakiyar falon yana mai nufar rantsattsiyar sofar da Mai martaba yake kai zaune, inda yasha naɗi, ga kwarjini cike da haiba. Daidai saitin ƙafafun shi yayi ma kanshi matsuguni, yana mai kai duka tafukan hannayen shi bisa ƙafar mai martabar da take sanye cikin takalma samfarin na sarakuna da suke ji da kansu, wanda akayi masu ado da gashin ɗawisu mai ƙyalƙyali. "Baba ina mai baɗa haƙuri a bisa laifukan da mahaifin na Mom ɗita ya aikata gabanin rasuwar shi, hakan kuma ba wai yana nufin bana goyon bayan wannan masarauta mai ɗinbin daraja bane da ta janye duk wani hukunci data gindaya a kan duk wani mai laifi, kuma ina roƙon wannan masarauta da ta bani dama in nemo Alhaji Yaro da iyalin nashi, duk inda suka shiga kuwa a faɗin ƙasar nan, sannan alfarma ta biyu da nake nema a wajen Umman tamu shine, ta janye maganar ta ta cewa ta yafe duk wani abu da yake haƙƙin ta ne, haƙiƙa ba kowa sai ya faɗa ba, ita ɗin ta kasance mai kawaici, kauda kai ga dukkan wasu al'amura da suka faru a yayin zaman ta gidan namu, da wannan nake cewa a bayyana ma Suhan dukkan abubuwan da suka faru daga farko har ƙarshe, a shirye nake da amsar duk wani hukunci da ta yanke kaina, sakamakon laifin Mom ɗita da kuma kakan nawa. Duk da har cikin raina ban shirya ma barinta ba, ban shirya ma rabuwa da ita ba, hasali ma ita ce rayuwa ta, rasa ta gareni, ba ƙaramin al'amari bane, saidai kuma hakan ba wai yana nufin tauye mata haƙƙi bane, ko kuma tursasata ta akan cewa lallai sai ta zauna da Mom ɗita a matsayin suruka bane" ya ƙarashe cikin wani yanayi da zai fahimtar da kowa cewa yana cikin ƙanar zuciya, masalan duk wanda ya kalli idanun shi, da har wani lumshewa suke yi, tsabar raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyar shi. Kaf falon babu wanda tausayin shi bai ratsa mashi zuciya ba, ita kuwa Mom jin abunda Son ɗin nata ya faɗa, sai ta kuma rushewa da kuka, wannan wace irin rana ce? Wace irin rana ce da tazo mata a haggunce? Kaman ita Hajiya Kubra har za'a zaunar da ita ana mata tonon silili haka? Kuma a gidan su kishiya? har yaron nata yana goyon bayansu yana wani cewa zai amshi duk dukiyar tata da ta mallaka kuma ya damƙa ta a hannun kishiyar tata da matar tashi? Bai tashi nemo Alhaji yaron da tasha fama dashi ada cen baya ba akan hakan sai yanzu??? Maganar Mai martaba ce ta dawo da ita daga dogon tunanin data zurfafa, har yanzu idanun nata na bisa fuskar yaron nata da yake durƙushe bisa ƙafafun nashi daya tanƙwashe su, yayi kaman zaman sallah, yayin da hannun mai martaba ɗin yake bisa sumar kan tashi da take kwance luf. "Masha Allahu, Jazakumullahu khairan. Allah ya saka maka da alkhairi a bisa wannan ƙudiri naka, kuma muna mai yi maka fatan alkhairi, da fatan gamawa da duniya da kuma iyayen ka lafiya, sai magana ta biyu, Masarauta ta amince ta baka damar zuwa ko ina a faɗin duniyar nan domin kawo mata babban maciyi amana mai ɗinbin laifi kuma. Sai magana ta uku maganar dukiya kuma ta rage tsakanin Hajiya Kubra da Gimbiya Merama, sai kuma Suhan, a saboda haka ne ya sanya mukace idan har sunce sun yafe to babu dalilin a matsa kan sai an ƙwace dukiya daga hannun mahaifiyar ka, komi zamu bishi kan ƙa'ida ne daki daki kaman yanda shari'a ta tanadar. Saboda haka ne nake bama kowa umurni da cewa yaje ya huta, sannan lallai azo ma masarauta da Baba Alhaji Barrister da kuma shi kanshi Barrister Kabirun, domin muji iya adadin kuɗaɗen da suke rubuce a wajen shi. Haka kuma idan ba Al'ameen da Bilal ba, masarauta bata bama kowa damar tafiya ba, har sai an warware wannan ƙullin da yake tsakani, da fatan kowa zai huta lafiya" Mai martaba na gama faɗin hakan, ya miƙe yana mai gyara zaman alkyabbar da take kanshi, sannan ya nufi hanyar da zata sada shi da ɗakin hutawar shi na musamman. Sai kuma zaman shiru ya biyo baya, inda kowa yake zaune jigum yana saƙa abunda yake kai kawo cikin zuciyar shi. A hankali Al'ameen ya miƙe, yana mai taka wa zuwa inda Umman Suhan ɗin take zaune, sai kuma ya durƙusa kusa da ita, yana mai kamo hannayen ta, wanda suke rumtse cikin na juna. "Umma ina alfahari dake, sannan da kasancewa ta suruki a wajen ki, haƙiƙa kin mana abunda ba kowacce uwa bace zata iya yima ɗanɗan ta ba, dan Allah ina mai roƙon ki da ki kwantar da hankalin ki, kinsan kina fama da lalura ta ciwon zuciya, kada ki sanya damuwa mai yawa a cikin ranki, wanda hakan zai iya shafar lafiyar ki Umma. Insha Allahu wannan al'amarn zai warware cikin sauƙi, kinsha faɗa mun cewa *watarana sai labari* Umma gashi yau labarin yazo wanda yazo mana cike da ɗin in kunya da danasani a gareki, a karo na biyu ina mai sake jaddada ban haƙuri a gareki, a madadin mahaifiyar tawa, da kuma kakana wanda yake kwance cikin ƙasa a halin yanzu, ba wai nace ki yafe masu bane, saidai bana so kina dinga tuna abunda ya faru a baya, Abunda ya faru ya riga ya wuce amma, don Allah ki sake kwantar da hankalin ki, kinji Ummanmu" Murmushi Umma ta sakar mashi a hankali, cike da so da ƙauna, itama ta runtse hannayen nashi cikin nata, jinshi takeyi kaman Suhan, soyayya da kulawar da yake ba ɗiyar tata kaɗai ta isheta a rayuwar ta, ko ba komai tasan indai Suhan na tare da Al'ameen bata da sauran damuwa ko fargabar hakan, saboda hakan ne ma ya sanya ta furta yafiya ga mahaifiyar tashi, bata fatan wannan al'amari ya shafi rayuwar auren yarinyar tata. "Allah yayi maka albarka ɗana, ya baka Abunda kake so duniya da lahira, Suhan kuma amana ce a gareka, ina mai alfahari nima da samun suruki kaman kai, hakan kuma ina mai jinjina ma ƙoƙarin ka, dauriyar ka, da kuma taimakonka ga na ƙasa dakai da biyayyar ka, hakan kaɗai ya isa ya sanya ka cimma dukkan ƙudurorinka, babu wata uwa da zata same ka a matsayi ɗa, ta gaza gode ma Allah a bisa baiwar da yayi mata, Allah nake roƙo kaima da ya baka masu yi maka, ya baka zuri'a ta gari. Cikin jin daɗi, karo na farko kenan da haƙoran nashi suka washe, fuskar shi ta cika da murmushi mai ƙayatarwa , wanda hakan yayi sanadiyyar loɓawar gefe da gefen fuskar tashi, wushiryar shi ta bayyana, inda kyawon fuskar tashi ya daɗa bayyana a fili. Addu'o in nata da maganganun nata, sun sake sama mata wani matsayi a cikin zuciyar shi, ina ma mahaifiyar tashi Zatayi koyi da irin halayen Umman? Ina ma... To saidai kash, izza, taƙama da isa, wanda zamu iya cewa tayi gadon hakan ne a wajen mahaifin ta, ba zasu iya bari ta zama irin Umman ba, wanda babu komai a cikin zuciyar ta, daga addini sai soyayya, jin ƙai da tausayi a ciki, Sam bata jin kanta a matsayin wata, da tuni ba zatayi ma mahaifiyarshi bautar da tayi mata ba. Baisan lokacin da ya wara hannu ba, yana mai rungumo Umman, soyayyar ta yake ji har cikin zuciyar shi, ta maye mashi gurbin rashin dacen uwa da yayi, hakan kuma sai yake jinta kaman Mom ɗin tashi wadda ta tsugunna ta haife shi, Wani irin ƙayataccen murmushi Alhaji Mustapha Dambulan ya saki, yana mai godiya ga Allah, ko Al'ameen kaɗai Allah ya bashi, ya tabbata ya gama dacen haihuwa, cikin tsantsar shauƙi yake kallon yaron nashi da yake durƙushe bisa guiwoyin nashi, yana mai rungume da surukar tashi, wadda yake jinta kaman mahaifiyar shi. Ji yake ina ma Umma ce ya fara haɗuwa da ita a zahiri, da babu abunda zai sanya shi ƙara wani auren, saidai ina ƙaddara ta riga fata, da bai auri Hajiya Kubran ba kuma da ba zai samu yaro Kaman Al'ameen ba, wanda bama shi ba, hatta da ƙasar baki ɗaya take ji dashi, da kuma alfahari dashi. Sakin Umman yayi yana mai sake bata kyautar murmushin nan nashi mai tsada, yana mai miƙewa ya isa inda iyayen nashi maza suke zaune, suma duƙawa yayi cike da girmamawa da ladabi ya gaishe su, albarka sosai suka saka mashi, inda yake sanar da Dad ɗin nashi cewa shi da Bilal ɗin yau zasu koma, Amman zuwa gobe yake son wucewa zuwa ga neman Alhaji Yaron. Addu'a sosai sukayi mashi, suna masu ƙara bashi ƙwarin guiwa. A hakan ya miƙe yana mai ficewa daga falon, abun mamaki ko inda Hajiya Kubran take bai kalla ba, baya ma son ko kallon nata yayi, domin baisan da wanne irin idanu zai kalleta ɗin ba, so yake ta gane kuskuren ta, so yake ta nemi yafiyar Umma, so yake ta nemi yafiya a madadin mahaifin nata, na halin da ya jefa rayuwar Umman da kuma Suhan ɗin tashi tun ma tana cikin ciki, amman yasan ba zata iya ba, Mom ɗin tashi ba irin mutanen da suke saduda lokaci guda bane su yarda makaman yaƙin su, shi kuma yasha alwashi cewa ba zai taɓa goyon bayan rashin gaskiya ba, ba zai taɓa sanya son zuciya ko son kai a cikin wannan al'amari ba, Mom ɗinshi tayi kuskure, wanda kuma dole ne ta gane cewa tayi ɗin. Har kai lokacin da yabar falon ya kula duk kukan da takeyi ba kukan nadama da danasani bane, kuka ne na son zuciya son kai, kukan za'a rabata da dukiyar ta, wanda take jin kaman za'a rabata da rayuwarta ne. Addu'a kan yanayi kuma zai cigaba da yi mata, yana so ta gyara rayuwar tata, ta daidaita akan hanya madaidaiciya, ta zama kaman kowacce uwa ta kirki akan ƴaƴan nata, ta zama kaman kowacce mata ta kirki a wajen mijin nata, ta zama kaman ko wacce suruka ta kirki a wajen dangin Dad ɗin nashi, idan tayi haka saɓon Allah ne kawai ba zaiyi ba akan ya kyautata mata, idan tayi hakan ko wuta tace ya faɗa, shi yana da yaƙinin faɗawa cikin ta, indai hakan zai faranta ran shi, saboda sanin kanshi ne cewa Mom ɗin tashi tana sonshi da ƙaunar shi, saidai wani lokaci son zuciyar tata ne yake danne dukkan wani abu na daidai daya kamata ace ta aikata, kuma ba wai dan bata sani bane. Bilal yayi mamakin sake ganin shi ya fito cikin ƙanƙanin lokaci, sannan yayi mamakin daya shaida mashi cewa yanzu yanzu ne zasu juya. Mamakin shi guda yanzu cikin wannan sanyin marecen zasu ɗauki hanyar Abuja? Saidai yanda yaga yanayin abokin nashi, sai bai tsaya gaddama mashi ba, ya shiga motar yana mai yi mata key, shima zagayawa yayi ya shiga ya zauna. Inda Bilal ɗin ya juya kan mitar suna masu ficewa daga harabar tamfatsetsiyar masarautar. A hanya ne ya shaida ma Bilal ɗin ƙudirin shi na zuwa neman Alhaji Yaro, Bilal ɗin baiyi mamaki ba, dan dama yasan issue ɗin, saidai ya jaddada ma Al'ameen cewa wannan tafiyar tasu ce baki ɗaya, kuma insha Allahu duk yanda zasuyi, zasuyi domin ganin cewa mai laifin yazo hannun su. Domin ba ƙaramar cin amana bace ta maƙudan kuɗaɗe da yayi ma Hajiya Kubran ba. Kamo hannun shi Al'ameen ɗin yayi, karo na farko da Al'ameen ya buɗe baki yana zuba ma Bilal ɗin godiya, gami da alfahari da kasancewar shi amini na amana a gareshi, ya daɗa tabbatar ma kanshi cewa samun Aboki kuma amini kaman Bilal ɗin a wannan lokacin da amana da yarda tayi wahala abu ne mai wuya. Bilal ɗin bai barshi hakanan ba, ya cigaba da jan shi da fira,har saida ya tabbatar ya ɗan saki jiki, a ƙoƙarin shi na son kauda duk wani tunani daga zuciyar abokin nashi, har lokacin da yaga Al'ameen ɗin ya jawo waya yana mai shaida ma Suhan ɗin cewa insha Allah komin dare yau zasu iso, ɗin haka ta shirya masu abubuwan buƙata. *******************' Ni kau ta ɓangaren na yini nayi yau babu daɗi, jikina nake ji kaman ba nawa ba, ga yawan faɗuwar gaba, wadda yau yini nayi da ita, dalili kenan da ya sanya nayi kira ga Mijin nawa, farin ciki na kuma saidai bai amsa ba, hakan ne ya daɗa tayar man da hankali na rubuta mashi saƙo, saidai saƙon bai daɗe da shiga ba sai ga reply nashi, inda sai lokacin na ɗan samu sauƙin zuciya ta. Miƙewa nayi ina mai harhaɗa kaya na, so nake zuwa dare in kira Ya Ameen ɗin na shaida mashi maganar komawa ta makaranta, tun da sanyin safiya Khadeeja ta kirani a waya tana shaida man lallai in dawo school in ba so nake in samu matsa ba, masalan ma yanzu da muka shiga aji na huɗun, inda karatun ya ɗauko zafi, sa'a ake nema tsakanin ɗaliban da malaman. *************** Ina kwance ne falon nawa, wanda na gyara shi tsaf na ƙalƙale shi, sanye nake da ƙananan kaya riga da wando iya guiwa, sai gashin kaina dana gyara, na tufke shi tsakiyar kaina, na bar sauran nata reto da lilo a baya. Kaina babu ɗan kwali, sai wata vandaner mai kyau wanda iya kaina kawai ta zagaye man, littafin *Menene Riba ta?* nake karantawa, inda nake jin irin zallar fasahar da marubutan suke zubawa cikin labarin, wanda yanzu yake faruwa sosai, wasu marubutan sun ɗauka rubuta batsa a littafi, ko fayyace rayuwar daren na'aurata shine ilimantarwa da faɗakantarwa. Na jinjina masu, kuma littafin yayi ma'ana, inda suka fiddo da aibun da kuma kuskuren aikata hakan a fili. Na natsu tsaf ina kwashe duk wani saƙo na littafin naji ƙugin mota da ƙarfi. Da sauri na miƙe har ina neman zamewa zuwa ƙasa, yanda naji an banki wani abu da ƙarfi. Ta taga na leƙa zuwa farfajiyar gidan, Nihal ce na hango da mugun gudu ta shige sashen su, tana mai rusa kuka, ƙafarta ko takalmi babu, haka jikin ta ko gyale ma babu. Ƙarar da naji kuwa ashe motar Ya Ameen ce da take fake gefe ta kaima karo, har bayan motar ya taɓu sosai, glassan motar ta baya sun farfashe suma. Hankali na ne ya tashi sosai, me ke faruwa ne? Gashi munyi waya da ya Ameen ya shaida man yana hanya. Ai da gudu na koma bisa sofa inda wayata take ajiye, na ɗauko ta da sauri gami da danna kiran Ya Ameen. Har ta gama ringing bai ɗaga ba, sai hankalina ya kuma tashi, yanzu duniyar nan babu gaskiya cikin ta, haka hanyar ma ana fama da wannan mamuguntan ƴan kidnapping ɗin. Ban tsaya wata wata ba, na ruga ɗaki na zura doguwar hijab ɗita ta sallah har ƙasa. Ban ko tsaya kulle sashen nawa ba, yanayin yanda hankalina yake tashe. Kai tsaye sashen Mom ɗin na nufa, har ina ɗan haɗawa da gudu. Kai tsaye ɗakin Nihal ɗin na ma tsinke. Cen bisa gado na hango ta lafe sai shesshekar kuka take yi, wajen gadon na matsa ina mai cewa "Nihal Lafiya kuwa? Me ya faru ne? Pls kiyi man bayani mana" nima cikin tashin hankali nake maganar. Da sauri ta taso zuwa gareni, sai kuma naji ta rungume ni tsam a ƙirjinta, tana mai sake fasa kukan. "Aunty Suhan ki taimake ni don Allah, ba wanda zai tsaya saurara ta yanzu nasan sai ke, kiyi ma Ya Ameen magana ya kira baby, wai aure zai ƙara please aunty Suhan" Maganar tata ta bani mamaki kwarai da gaske, yai ni Nihal ke kira da aunty? Ni take cewa inma Ya Ameen magana akan wata buƙata tata? Ashe ma tasan ina da wani matsayi a wajen shi, dama su baki ɗaya. A hankali nayi ƙoƙarin raba jikina da nata, abun ma da rainin hankali ciki. Jin ƙoƙarin da nake yine ya sanyata saurin sake ƙanƙame ni. "Please Aunty Suhan ki taimakeni, kada ku bari Baby ya ƙara aure, wallahi zan iya mutuwa in na ganshi da wata macen" Sai kuma naji jikina yayi sanyi, ko ba komai zata iya cin darajar Ya Ameen, ko ba komai ita ɗin ƙanwa ce gareshi, kuma ɗiya ga Alhaji Mustapha, ba zan taɓa iya ganin jinin Ya Ameen cikin wani hali ba, ba tare da na taimaka ɗin ba, muddin ina da yanda zanyi. Taci daraja ta Ya Ameen da Dad. Da ko kallo Nihal bata isheni ba, tom dandai babu kyau rama sharri da sharri. Bakin gadon na samu ina mai zaunar da ita. A hankali na shiga kwantar mata da hankali, ina nunnuna mata illolinta a wayance, da kuma dalilin halin data shiga, yau sai ga Nihal tayi kasaƙe tana saurare na, har ma da gyaɗa man kai, alamun maganganun nawa suna ratsa ta. Ni da kaina nace mata nayi alƙawarn koya mata dukkan wani abu datasan cewa bata iya ba, ba tare da ƙyara ko hantara ba. Nasha mamakin yanda Nihal ta sauke girman kai, izza da isa tana bani haƙuri har naji kunya, gashi dai a girme zata ɗan girme mani, sai ga Nihal yau Aunty sama Aunty ƙasa, harda rungume ni tana sabon kuka tana bani haƙuri, cewa wai tayi nadama, ashe fahimta ta ne batayi ba, ni ɗin ko a cikin mutane daban nake, kuma insha Allah ba zata sake hawa turbar Mom ɗinta ba, ita kanta ta sani ko Mom ba zata tsaya ta saurare ta ba, ta kuma fahimce ta kaman yanda nayi. Na daɗe sashen har kusan ƙarfe shiddan marece, ina ta kwantar mata da hankali, a ƴar firar da mukayi ne na fahimci gaskiya dole Nureen ya ɗaukar ma kanshi mataki, duk da ba wai yau nasan Nihal ba, Amman tare na da ita ban iya fahimtar yanda al'amurranta suke a dagule ba sai tau, kawai dai nasan komai bata iya yi da kanta sai nayi mata, ashe ni hakan gata ne a gareni, ashe ni hakan zai zame mani alkhairi a gaba, duk da a lokacin ina mai kallon wahala ne kawai nakeyi. Faɗa mata nayi cewa zanje sashe na inyi ma yayanta girkin tarba. Nacewa tayi akan sai ta bini, lallai ta hakan ne zata tabbatar da cewa na yafe mata, kuma a shirye nake da in taimaka mata. Sam batayi man maganar Saudat ba, duk da ita bansan irin rayuwar da take yi ba, Amman na tabbata kanwar duk ja ce, abunda yaci doma ba zai bar awai ba. Sai gashi mun zage a kitchen muna ta aikace aikace da Nihal, ni kallon ta ma nake tayi, wani lokaci har dariya ce take neman suɓuce man, ni kaina ban zata zan iya yafe ma Nihal haka cikin sauƙi ba, sai na fahimci hada tausayi data bani ne, da kuma darajar Yayanta data ci. Ni ke nunnuna mata komai, lallai Nihal za'a sha fama, a yanda na fahimta ruwan zafi kawai ta iya dafawa, sai kuma indomie, itama tsurar ta, daga mai sai magi sai kwai. Cikin lokaci ƙanƙai muka gama dukkan Abunda zamu gama. Ceman tayi zata koma ɗaki, saboda tasan bata iya haɗa ido da Ya Ameen, ita kanta tasan haushinta yake ji, sannan ta ƙara roƙo na da in sake ba Ya Ameen baki, akan ya duba al'amarn ta, ita kanta tasan muddin Ya Ameen ya sauko, to Dad ma zai saurare ta. Har bakin ƙofa na raka ta, inda saida ta sake bani haƙuri sannan tabar sashen nawa. Na lura cewa laushin nata na dole ne, duk da har cikin ranta ina ganin kaman tayi nadamar. To koma dai menene zan iya aiwatarwa ko domin Ya Ameen, idan nayi haka nasan ran shi zaiyi fari, duk da yana jin haushin ta, Amman ɗan uwa daban yake. Wanka na shige ina mai durje jikina sosai, ko bayan na fito daga wankan, na daɗe gaban dressing mirror ina ƙalƙale kaina sosai. Ni kaina nasan nayi kyau, doguwar riga ƴar kanti na saka, launin Ja mai haske, tsawon ta iya guiwa ne, anyi mata ado sosai, saidai hannun shimi gareta, hakan ya sanya ni ɗaukar ƴar falmara fara nai adon jajayen duwatsu na ɗora kai, sai fasion ƴan kunne dana manna ma kunnena na barima suma farare da ɗigon farin dutsi a tsakiya ja. Nayi matuƙar kyau sai tashin ƙamshi nakeyi, fata ta ta daɗa murjewa da kyau, haske na ya kuma fitowa. Fuskar sai tayi cas, sai walwali takeyi. Na ɓata lokaci sosai, inda Allah ya taimakeni na haɗo da alwala ta. Saboda haka zane kawai na ɗaura kai na tayar da sallah ta. Ina gamawa na kwance zanen na link gami da hijabin da sallayar. Gaban mirror na koma ina mai sake feshe jikina da turare mai sanyin ƙamshi. Ko kwalbar ban ajiye ba, na jiyo dirin mota. Ai da sauri na yaye labulen ɗakin ina hango farfajiyar. Motar ya Ameen ce, inda ina hango shi ya fito, haɗi da sakin wata ƴar ƙaramar miƙa alamun gajiya. Murmushi na saki, lokacin da na hango shi ya fara ta kowa cikin salon tafiyar shi mai ban sha'awa yana doso sashen namu. Sai na samu kaina da cenza tafiya, zuwa falon domin buɗe mashi. Aikuwa ina buɗewar na ganshi tsaye bakin ƙofa, dukkan hannuwan shi soke cikin aljihun wandon shi, ya wani karya kai alamun shagwaɓa da gajiya. Daga inda nake tsaye na haske shi da murmushi. hakan ce ta sanya shi takowa zuwa gareni, ja baya nayi kaɗan zan bashi hanya, naji wani irin sulɓi ya kwasheni, ai sai nayi baya suuuu zan faɗi, ban idasa kai ƙasa ba Naji ya fizgo ni zuwa jikinshi. Ai sai na maƙalƙale shi ina mai zare idanuwa. Mun kusan second ashirin a haka, idanu na cikin nashi, lokaci guda kuma na fara ƙoƙarin ɗago kaina inga abunda ya jani har haka, bayan nasan babu wani abu dana ajiye, ko kafin in shiga wanka, saida na daɗa gyara wurin. Ɓawon Ayaba ne barbaje a wajen. Cikin zaro idanu nake kallon wurin, tayaya akayi ɓawon ayabar da na zuba a dustbin, bayan na gama haɗa mashi banana shake ya fito yazo wajen? To wanene ya shigo man sashe bayan na shiga wanka?. Shima da alamu mamakin hakan yake yi, ɓawon Ayaba a bakin ƙofa? Me hakan ke nufi? Buɗe baki nayi da niyyar yin magana ya ɗora man hannu a baki, alamun inyi shiru, sannan ya raɗa man a kunne. Je ki sanya hijab, tare muke da Bilal, zan gyara wajen. Jikina a sanyaye na raba jikina da nashi, ina mai tsattsallakewa zuwa ɗakin namu cikin sauri, yayinda shi kuma ya wuce kai tsaye zuwa kitchen, ya ɗauko tsintsiya da abun kwashe sharar ya shiga tattara wurin. Daidai lokacin da Bilal yayi sallama yana mai turo ƙofar Falon. Dariya ya fashe dashi, yana mai cewa "Omo look at you Bro, kaine yau da shara? Daga isowar ka? Hahaha wani abun sai mata" Ganin yana neman yi mashi shaƙiyyanci ya sanya shi cemashi "ka tsaya gulma malam, idan ba zaka je kaci abinci ba" Wucewa Bilal ɗin yayi zuwa dining kai tsaye, yana ƙunshe dariya. Har ya gama yayi mopping ɗin wurin ban fito ba, ina cen ɗaki zaune bakin gado, tsoro fal a cikin raina, iko sai Allah, wanene yake neman ma ƙasa ta a cikin gidan nan? Wa na tsare ma wani abu? Mom bata nan, balle ince ko ita ce ta sanya wani, saboda ƙiyayyar da take man, kaina fa ya kulle, idanun na har sun kaɗa sun kawo ruwa. Gashi nidai ba zance Nihal bace tunda mun rabu lafiya da ita ta tafi... Katse man tunanin yayi, inda naji hannun shi cikin nawa yana mai cewa "Madam ya gida? Ya kaɗaici?" Murmushi na sakar mashi, wanda har saida ya sanya shi zama, yana mai zame hular dake kaina ya fara shafo sumar kaina, jin hakan sai na lafe bisa jikin shi, ina mai shafa gefen hannun nashi da nake kai a hankali. Yasan dole hankalina ya tashi, saboda haka ne ya shiga jana da fira da wasanni har na saki jiki, hijab na zura, ina mai bin bayan shi zuwa falon, inda dining yake. Bilal ya saki jiki ya kwashi girki son ranshi, sai zuba santi yake, ko bayan da muka isa wajen muka zauna, bai kulamu ba, har saida ya gama cin abincin shi, yana mai zuba ma matan da suka iya girki godiya, sannan ya miƙe gami da dafe ciki yayi hamdala yana mai cema Al'ameen sai zuwa safen sa haɗu. Sai lokacin ne muka gaisa, Ya Ameen dai cewa yayi ba inda zai raka shi, haka shima yace bai ce yana buƙata ba. Yana fita yaja mana ƙofar, inda duk muka bishi da kallo, muna masu taya shi dariyar. Nasha kula sosai a ranar, Ya Ameen daban yake ba zan gaji da faɗa ba, komai nashi cikin salo yake yinshi, saida yayi wanka ya gargama duk ayyukan shi, sannan muka kwanta. Kula da tattali ranar nasha su, sai nake jin ma duniyar kaman babu kowa cikunta sai mu kaɗai. Duk abun nan da akeyi ya kasa faɗa man komai na dangane da halin da ake ciki sai kallona yake da abun, ya gaza ta yanda zai ɓullo man da maganar. Yanke shawara yayi akan cewa zai bari sai ya nemo Alhaji Yaro, sannan zai sanar dani halin da ake ciki ɗin. Maganar makaranta nayi mashi, ce mani yayi yana sane, dan a halin da ake ciki ma wai ya nema mani transfer, kawai takadda yake jira, nan da kwana biyu zata iso, inda ya maidoni nan Abuja, anan ne zan idasa karatun nawa, wai a cewar shi baya son yin nisa dani. Naji daɗin hakan, lokaci yayi nima da zan roƙe shi ya koya man mota, Tunda ina da motar da na samu kyauta lokacin biki na, sai in dinga yin day kawai a kullun, ba sai na zauna Hostel ba da aure na. Cikin wayau na sako mashi maganar Nihal, ƙoƙarin dakatar dani yake yi, ban ƙara cewa komai ba, har saida ya kammala faɗace faɗacen shi, kunsan muskili bai iya zuciya ba, sai a lokacin ne nikuma cikin siyasa da kissa irin tamu ta mata na sanar dashi yanda mukayi da Nihal ɗin, harma ayyukan da ta tayani yau mukayi. Shiru yayi mani, kaman yayi bacci, har yanzu dai yana naniƙe dani, wani irin so na ne yake ji yana ratsa shi, yana mai ƙara gode ma Allah da mallaka ta a matsayin mata da yayi. In ba haka ba, inda wata ce yanda nasha wahalar Nihal, zan so ne ma ace rayuwar gidan tata ta lalace, sai gashi nice ma ke roƙon shi, akan cewa ya sanya baki a gyara komai. Saida ya rungume ni yana mai sanya mani albarka, sannan yace mani, in bari yaga kamun ludayin nata, idan yaga dagaske ta cenza, insha Allahu zai san yadda Zatayi ta koma gidan nata, Amman maganar ya hana Nureen ƙarin aure ma bata taso ba, tunda shi aure lokaci ne, kuma raine dashi, dan haka koma menene ya same ta ita ce ta ja ma kanta. Lamo nayi ina sauraren shi, inda yake sanar mani tafiyar da zaiyi goben shi da Bilal. Addu'a na dinga kwararo mashi, ina mai jaddada mashi matsayin Mom a gareshi, kwarai ya yaba a gareni, kuma ya ƙara tabbatar ma kanshi cewa koda abunda yake ta ɓoyo ya fallasa, shi yasan ba zan taɓa juya mashi baya ba. ******* Tun tana sa ran taji an fasa ihu daga sashen namu har dai taji tsit, kenan ɓawon ayabar da ta sanya bai yi amfani ba, duk wahalar da tasha kafin taga ta samu shiga kitchen ɗin nawa ta ɗebo ɓawon ayabar har ta kai da zuba mani, ba tare da kowa ya ganta ba, a duk tunanin ta, muddin santsin nan ya kwashe ni, ƙila ma ba karaya ɗaya ba, idan ta kai goma ƙila sai nayi ta. Saidai saɓanin yanda ta zata, sai ji tayi shiru, kuma a kan idanun ta Ya Ameen da Bilal suka dawo. Me hakan ke nufi kenan? Suna nufin sunga ɓawon ayabar ne, ko kuma ta faɗin ihun dai ne Allah bai sa taji ba? Koma dai menene zata bari zuwa safiya, domin taji abunda ya faru, Amman tana da tabbacin zuwa safiyar zata ga an cicciɓo Suhan ɗin zuwa asibitin ƙashi... Kaman yanda ta kwana sauraren farin saƙo a gareta, haka Ya Ameen ya kwana tunanin halin da yake fuskanta, da kuma dalilin zuwan ɓawon Ayaba sashen nashi, ya tabbata Suhan aka ƙulla ma hakan, sannan yayi imanin cewa koma wanene yayi hakan yana cikin gidan, sannan yasha alwashin koma wanene gamuwar tasu ba zatayi daɗi ba. ~Oum-Deedat ce~ [1/24, 10:00 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~Page 78~* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* Abin Da Ake Fada don kawar da kaidin shaidanu Masu Taurin Kai. أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ. A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman. Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama! >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~78~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Kusan zan iya cewa kwana yau Ya Ameen yayi bisa darduma. Ina kallon shi, tun ina binshi sallar har dai nima na ɓingire a wajen, saida ya kammala ne sannan ya ɗauke ni cak zuwa saman gadon. Ga mamaki na ma, koda ya tada ni sallar asuba tsab na ganshi. Tun daga fuskarshi da idanuna suka sauka akai, nake binshi da kallo. Da sauri na miƙe, a daidai wannan lokacin na saba ganinshi da farar jallabiya ko mai ruwan ƙasa, saɓanin yau da yake sanye cikin wani lallausan Yadi ɗan ubansu, kalar army Green mai duhu an mashi ɗinkin osinbajo, Ai da sauri na tashi zaune ina mai furta "Dear" a laɓɓan nawa. Shima wara kyawawan idanun shi yayi saman fuskar tawa, yana mai shafa ta da tafukan hannayen shi a hankali, lokaci guda kuma yana mai sake mani wani irin lallausan murmushi. "Nasan kin gaji my wife, gashi kuma lokacin sallah yayi, ki daure ki tashi kiyi sai ki koma" Abunda ya furta man kenan a hankali, har yanzu hannayen nashi na bisa fuska ta. Zuro ƙafafu na nayi daga bisa gadon, ina mai ture duvet ɗin gefe, sai kuma na miƙe, har yanzu da kallon tuhuma nake binshi. Ya kula da hakan, sai ya saki murmushi wanda ya ƙara ƙawata fuskar tashi da take fayau da ita, kaman wata ɗan daren sha huɗu. Buɗe baki nayi da niyyar cewa wani abu, muka ji ladan ya sake ƙwala kiran sallah, da sauri ya manna man side peck, yana mai cewa dani "Dear bari inje masallaci in dawo zamuyi magana" da "To" na bishi, zuciya ta cike da alfaharn samun namiji kaman Ya Ameen, ta fuska da dama ya haɗa dukkanin wasu abubuwa da ake buƙata wajen namiji, saidai ya zuwa yanzu ɗin zuciya ta ta fara karaya da wasu al'amuran, ko bai faɗa ba nasan yana cikin wani yanayi, akwai abunda yake ɓoye man, tau kwana yayi sallah, kuma ko daya koma ya ɗan kwanta, ina jin shi kasa bacci yayi, sai motse motse da yake ta faman yi, ƙarshe ma laptop ɗinshi ya tashi ya jawo ya cigaba da danne danne. Jiki a sanyaye nake aiwatar da komai, har kai lokacin da na kammala sallar, ina zaune kan sallayar ne ya shigo. Tun daga falo ƙamshin turaren shi yaman sallama. Miƙewa nayi ina mai naɗe sallayar. Ta bayyana naji an rungumo ni gabaki ɗaya na, hadda hijab ɗin da ban cire ba. "Good morning wify" Naji ya faɗa a hankali iya kunne na. Juyowa nayi ina mai sake shigewa cikin jikin shi. "Morning my Adorable Hubby" Mun kai minti biyu haka tsaye, kowa da abunda yake ƙissimawa, yayinda nidai ɗan murmushi nake saukewa. Ya Ameen komai nashi daban ne. Hannu na yaja zuwa bakin gadon ya zaunar dani. Shima zama yayi, yana mai zame baƙi siɗik ɗin takalmin shi cover shoe da suka ƙara taimakawa wajen fitar da ainahin Sirrin kyaun kwalliyar tashi, da gani dai ba sai na faɗa ba, kai kanka kasan sunci kuɗi. "Ya gajiya?" ya furta a hankali, idanu na cikin nashi. Gaza cigaba da kallon shi nayi, sauke kaina ƙasa nayi ina mai murza yatsun hannu na. Hannuwan ya kamo dukansu zuwa cikin nashi. "Am sory dear na Gaza samun wadataccen lokacin da zan kasance dake, please ki ƙara haƙuri wasu ƴan abubuwa ne just a little, Amman insha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe" ya faɗa a tausashe yana mai karya kai gefe. Gyaɗa mashi kai nayi, nasani dole akwai wani abu, saidai bana son saka kaina sosai a cikin irin hidimar mutane kaman su Ya Ameen, su sun saba, kuma na kula kaman yana da zurfn ciki, kada tun auren namu baije ko ina ba, yaga kaman ina mashi kutse ne a al'amurra. Saidai na sani mata da dama ire-iren irin wannan hidindumun na masu kuɗi, shi ke ci masu tuwo a ƙwarya, Kaga an wadata mace da komai, amman a gaza sama mata lokacin ta dana yaranta. Kanshi naji daidai saitin nawa, yana mai manna goshin shi bisa nawa, tsinin hancin shi yana mai gogar nawa, a hankali na lumshe idanu na, ina jin yanda zara zaran gashin idanun shi ke yawo bisa fuskar tawa, alamun dai ƙare mani kallo yake yi. Murmushi na saki a hankali. Buɗe baki nayi da niyyar ce mashi wani abu, naji yayi caraf da leɓen nawa, ban mashi musu ko gardama ba, na kula ɗabi'a da al'adar shi ce, saboda haka na bar shi yayi yanda yaso. Ganin kaman kayan nashi zasu yamutse ne, ya sanya ni ɗan matsawa baya, ina mai kwantar da kaina bisa faffaɗar kafaɗar tashi, numfashi nake saukewa a hankali, yayinda shima har yanzu idanun nashi suke lumshe, sai ya kwantar da kan shi bisa nawa kan. Munkai tsawon lokaci haka, wata irin ƙaunar Ya Ameen ce ke nusa ta, ya zuwa yanzu na fara jin cewa ba zan iya kaiwa ko ina ba, ba tare da mijin nawa ba. Ban sani ba, ada cen ashe ban mashi komai ba, na daga cikin irin ƙaunar da nake mashi a yanzu. Ko a mafarki ban taɓa kawo ma raina zan dace miji irin haka ba, mai sona, ƙauna ta, gani da tattalina ba. Ganin mun gama hutawa daga aikin saƙonnin da muka tura ma juna ne, ya sanya ni Miƙewa a hankali, ina cemashi "Zanje kitchen Yaya, ba zaka fita haka ba, baka ci komai ba" Baice man komai ba, saima Miƙewa da yayi shima, hannu na cikin nashi muka nufi kitchen ɗin. "Me za'a bani Dear Mrs Ameen?" ya faɗa cikin zaulaya shima. Murmushi nayi nima ina mai ce mashi "Oya guest mana" hannu ya ɗora daman bakin shi, alamun tunani, sai cen yace "Yes i got it" baya naja, ina mai jingina baya na da cabinet. "Uhm faɗi muji idan Miji zai iya karantar zuciyar matarshi" nima na faɗa cikin dariya mai ɗan sauti. "Cake and meant tea" ya faɗa yana mai karkaɗa hannu, shi ala dole hakane a cikin zuciyar tawa. Ai bansan lokacin da na ƙyalƙyale da dariya ba. Tsaye yayi tana mai ƙare ma fuska ta kallo, dariyar tawa sai ta bashi dariya shima, kuma ta birge shi. Akwai wani Sirrin kyau tattare da matar tashi, natsuwa da kuma sanyin halin ta, na daga cikin abunda ke ƙara jan hankalin shi zuwa ga Suhan ɗin. Mu biyu muke ta dariya a cikin kitchen, har ta kai ga bansan lokacin da na jini a cikin ƙirjin nashi ba. Rungume ni yayi tsam yana mai furta mani kalmomi masu daɗi na so da ƙauna. Abunda ya faɗa shi ɗin na mashi, yana ci tana man labari kala kala. Nidai kallon shi kawia nake yi, ashe haka Ya Ameen yake? Duk wannan miskilancin da take fama dashi da ina ya tafi? Muna cikin haka ne wayar shi ta ɗauki tsuwwa. Ya Bilal ne, saboda haka yace mashi ya shigo kawai ai bai kulle ƙofar ba, da sauri na kalle shi, ya gane abunda nake nufi, shigo man da ake yi, girgiza kai yayi alamun in kwantar da hankali na, yana mai nuna mani wata ƴar camera da take liƙe bakin ƙofar shigowar, wadda ni banma san da ita ba, duk zama na a sashen. "Ko wanene ma ya cigaba tara shi nake yi, zan juyo kanshi ne" ya faɗa yana mai ɗan haɗe murya, sai Naji ba daɗi, ashe shima abun ya mashi zafi, ai banga ya nuna bane jiya, ashe akwai tudun da ya dafa? To Amman in hakane, me yasa tun jiyan baiyi checking ba? Domin yaga ko wanene ya shigo ya man hakan? A hankali na sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, ashe ina cikin kulawar Ya Ameen aduk inda yake? Lallai dace ne babba samun miji ɗin kaman Ya Ameen Shigowar Bilal ɗince ta katse man tunanin da nake yi. Miƙewa nayi ina mai gaishe shi, cikin sakin fuska ya amsa mani, har zaulaya ta yake yi, wai da gayya muke mashi wani abun, dan munga Ummi bata nan, to ai shima ta kusa dawowa dai, domin ma yau ne ake taron sunan. Murna sosai har cikin raina, da anan ƙasar ne babu abunda zai hana ni leƙa ma Ummi, itama ta nuna mani so, ta jani a jiki sosai, tun kafin ma in zama yanda na zama. "Ya sunan baby ne Ya Bilal?" na furta hakan ina mai kallon fuskar Ya Ameen ɗin da zaƙuwa. Nuna mani Ya Ameen yayi, sai ban gane me yake nufi ba, na kalli Ya Ameen ɗin ina mai ɗan haɗe fuska. "Ka sani shine tun jiya baka gaya man ba?" na faɗa cikin ƴar shagwaɓa, shima kallona yake da murmushi, wannan shagwaɓa tawa ko ina na koyo ta? Sipping tea ɗinshi yake yi a hankali a hankali. "Kai a ina ka faɗa man malam? Salon kaja man wata rigimar ne?" ya faɗa yana mai maida duban shi zuwa inda Bilal yake tsiyaya tea a Mug. "Al'ameen" ya faɗa shima ba tare da ya kalli inda muke zaune ba. Babu wanda ya fahimta cikin mu. Shiru ne ya biyo baya, har kai lokacin da ya ɗago yana mai kallon mu cikin dariya "Yaro dai yaci sunan mijin ki, na mashi huɗuba da Al'ameen, ina fatan kuma Allah yasa yayi koyi da mai irin sunan" Ai ba Ya Ameen ba, har ni saida wuta ta ta ɗauke na tsawon wucin gadi. Wane irin aiki ne Ya Bilal? Ƙauna mai tsafta, ƙauna ta tsakani da Allah. Kawai gani nayi Ya Ameen ya dire Mug ɗin tea ɗin nashi, ya miƙe gami da dosar inda Bilal ɗin take zaune. Rungume shi yayi cikin wata irin ƙauna, amintaka da soyayya. Ni kaina Miƙewa nayi tsaye, ina mai haɗe hannu na dukansu, wani irin tsammm nake ji a jikina, bance ba za'a samu irin wannan abokantakar ba, saidai sai an bincika, sai an tona, ba duka ba. "Ka gama man komai friend, nagode nagode Allah ya barmu tare, ya kauda dukkan wani abu na ɓacin rai daka iya shiga tsakanin mu, sannan ina sanar maka, tun daga rana mai irin ta yau, duk wasu buƙatocin takwarana na ɗauke maka su, karatun shi, da dukkan abunda zai buƙata har auren shi, indai muna da rayuwa, Allah ya raya mana shi, ya shirya shi a bisa tafarkin addini madaidaici, sai ka buɗe mashi account dan Allah zan dinga saka mashi kuɗi, duk Abunda take buƙata a ɗauka ciki ayi mashi, wannan tukuici ne, kuma ba kai nayi mawa ba, yaro na nayi mawa, saboda haka kada in sake inji kace komai friend" Daga ni har Ya Bilal babu wanda kalaman Ya Ameen basu dakar ma zuciya ba. Sake rungume shi Bilal yayi, yana mai jaddada godiya gami da jin daɗi, yasan Ya Ameen, abunda yafi haka ma yana yi, kuma zai iya, wannan kaɗan ne daga cikin irin halayen shi kyawawa dake daɗa mashi kwarjini a idanun jama'a. Fatan alkhairi na shiga yi masu, har yanzu sun kasa sakin juna, kuma koda suka koma suka zauna, su dukansu murmushin jin daɗi da annashuwa suke saki. Lallai wannan ƙauna daga Allah ce, ni ba zan ma iya fasalta ta ba, ko in kawo misalin ta. Nima addu'oi na shiga zuba masu, su duka sunji daɗi, kuma sun barma ransu cewa ko gobe ba zan iya shiga tsakanin su bane, balle in kawo wata fitina daka iya raba wannan zumuncin tun na yarinta. A take Bilal ɗin ya kira Ummin, aiko bakaji yanda take murna ba, mai son ɗanka ai kai take so, sai ga kiran ta kuwa cikin wayar Ya Ameen, bayan sun gaisa ne take sake mashi godiya, nuna mata ɓacin rai yayi, yana mai miƙo man wayar, nima godiyar tayi mani, murmushi nake tayi ina zaulayar ta da cewa mijinta na nan yana gwaurantaka, tayi maza ta dawo. Ya Ameen ne ya duba agogon da take ɗaure bisa tsintsiyar hannun shi "friend muyi maza fa, tun cikin dare na kammala mana komai na daga abunda zamu buƙata, saboda haka ina so komai ya kammala cikin lokaci" Shima Bilal ɗin ajiye Mug ɗin yayi yana mai miƙewa tsaye. "OK am done" ya faɗa yana juyowa inda nake tsaye nima riƙe da ƴar brief case ta Ya Ameen. "Madam sai mun dawo ko? A gaida Hafsat fa da baby" ya faɗa shima cikin murmushi, yana mai nufar ƙofa ya fice. Jawo ni Ya Ameen yayi da sauri na faɗa jikin shi. Rungume ni yayi sosai. "Bilal ya sanya ni farin ciki Dear, kiyi mana addu'a please, I have no any than Bilal" ya faɗa a hankali Gyaɗa mashi kai nayi nima cikin yarda da abunda ya faɗa ɗin. "Na sani dear, ina maku addu'ar Allah ya sanya ma wannan tarayya taku albarka, har ƴaƴanmu" Ya kuwa ji daɗin me na faɗa ɗin, sake rungume ni yayi tsam, yana mai raɗa mani "Nace zamuyi magana ɗazu, Amman yanzu lokaci ya ƙure, please ki zauna kiyi tunani, bana son dukkan wani abu da zai sanya ki juya mani baya, sannan ina roƙon ki da kada ki hukunta wani da laifin wani, na sani dole ne komai zai bayyana, Amman ina so kiyi duba a tsanake, ko don irin soyayya ta a gareki.ki gaida man Hafsat nima, sannan nasan gobe ne suna itama, sai ki natsu tsab kiga me ya kamata ayi mata itama, harda Mama zainab ma. Sai na dawo, zamuyi waya" Abunda ya faɗa kenan, yana mai zare jikin shi da nawa, yaja ƴar ƙaramar jikkarshi ta goyo, wanda take da ƴan tayoyi, za'a ma iya janta ƙasa idan mutun ya gaji. Ƴan kala uku ne ciki, sai ƴan kayan buƙatocin shi. A sanyaye na bishi a baya har zuwa bakin ƙofa, jikkaar na miƙa mashi, ina mai yi mashi adawo lafiya. Har ya wuce sai kuma ya dawo, yana mai tallafo fuska ta ya bani prench Kiss a baki, a hankali ya buɗa bakinshi ya shiga cewa "Kiyi mani addu'a dear, wani aiki ne mai wahala ya taso mani, kuma ina so ki sani wannan fitar tawa ta shafe ki, saboda ke ne ma zan yita, duk abunda ya shafeki ni ya shafa, neman Alhaji yaro ba abu ne mai wahala ba, addu'ar ki a kullum ita nake buƙata" Yana gama faɗar haka ya juya cikin salon takun tafiyar shi. Gaza aiwatar da komai nayi, saidai binshi da idanu da na shiga yi, me wannan maganar tashi take nufi? Menene haɗi na da Alhaji Yaro? Me Ya Ameen yake nufi da kada in juya mashi baya? Wai shin me yake faruwa ne? Kaman ya kada in hukunta wani da laifin wani? Me ya zaunar da su Umma, Mom da Dad a Adamawan ne? Ina su Ya Ameen suka je jiya?. Dole akwai abunda ke faruwa, to Amman Meyasa Ya Ameen ke ɓoye mani?. Jiki a sanyaye na juya zuwa cikin falon. A saman Sofa nayi ma kaina mazauni, ina jin ƙugin tashin motar su, gami da ficewarsu gabaki ɗaya daga gidan, a hankali na lumshe idanu na, tabbas zuciya ta na shaida mani akwai wani abu dake shirin faruwa, bana so rayuwar aurena ta taɓu, bana son wani abu daka iya sake kawo ma auren nawa barazana ina son miji na, bana iya jure duk wani abu da zai kawo mana tangarɗa tsakani. Bansan lokacin da naji wasu irin hawaye masu ɗumi nabin fuska ta ba, duk dan ni yake yi, duk wannan jeka ka dawo ɗin kenan dan ni yake yi? Ya Ameen mutumen kirki ne, Allah ya bashi kyakkyawar zuciya, yana iya ƙoƙarin shi wajen ganin yayi kyakkyawar mu'amala da duk wanda Allah ya haɗa shi. Kuka nayi sosai ina mai share hawayen, fuska ta har tayi ja, tabbas nasan iyayen nawa wani abu ne mai muhimmanci suke ɓoye man, saidai koma menene alƙawari ne ba zan taɓa bari ya shafi auren nawa ba, wannan karon saidai ace nayi rashin kunya, koda kuwa ga Mom ɗinne, muddin dai naga tana neman kawo man matsala tsakani na da yaron nata kuwa. ******* Tun da suka ɗauki hanya ba wanda yace da kowa komai. Shi kanshi Bilal ya fahimci irin halin da abokin nashi yake ciki, to sai dai ya zaiyi? Shi kuma irin ƙaddarar tashi kenan sai haƙuri. Kai Tsaye Airport ɗin garin na Abj suka fara isa. Basu sha wahala ba wajen samun iso zuwa ga MD Office ɗin. Masalan ma dayake tun cikin dare Al'ameen ɗin yayi mashi mail. Cikin girmamawa shugaban yake masu barka da zuwa, kai tsaye bisa Sofar dake jere gefen Office ɗin yayi masu masauki. Bayan sun gama gaisawa ne ya sanya aka kawo masu tea na cardamon. Ba ɓata lokaci Ya Ameen ɗin ya gyara zaman shi, yana mai kora ma MD ɗin bayanin dalilin zuwan nashi, da kuma buƙatar tashi a garesu. Ɗan Jim MD ɗin yayi, kafin yayi gyaran murya "Watau ranka ya daɗe, kadai san dukkanin tsarin hakan, kuma dokar wurin bata bamu damar aikata abunda kazo mana da buƙata ba, domin yanayin tsaro da ake ciki" Tsabar haushi ma Al'ameen kasa ce mashi komai yayi, Saima ɗan komawa da yayi ya jingina bayanshi jikin makarin Sofar. Bilal ne ya amshi maganar da cewa "Eah yallaɓai mu kanmu munsan hakan yayi againsing low, to Amman babu yanda zamuyi ne, muna maka maganan miliyoyin kuɗi ne, wanda kuma muna tare da shaidar da zata tabbatar maka da cewa lallai mutumen nan ana neman shi ne wanted, so dan Allah ka taimaka mana, munsan kuna yi mana iyakar bakin ƙoƙarin ku, to Amman dan Allah ku ƙara, ko domin a ceto haƙƙin marainiya." Shiru MD yayi yana mai nazarin maganganun Bilal ɗin. Sai cen da jimawa sannan ya nisa" Ah to ko zan iya ganin shedar taku?" "Why not?" cewr Bilal ɗin, yana mai jawo laptop ɗin ta Al'ameen da take cikin brief case gefen Al'ameen ɗin ajiye. Saida yayi dogon latse-latse kafin ya fiddo ainahin abunda yake son ya nuna ɗin. Ya daɗe yana nazarin komai, kafin ya bada damar a kawo mashi wata ƴar ƙaramar i-pad dake ajiye cen gefen Office ɗin. Ciki yayi ta latse-latse, kafin ya saki ɗan murmushi, yana mai kallon fuskar Al'ameen ɗin, wanda ba zaka iya tantance halin da yake ciki ba. "Ina tunanin ai wannan ne ko?" ya faɗa yana mai nuna masu screan ɗin. Da sauri Ya Ameen ya kai idanun shi kan Alhaji yaro, wanda yake riƙe da jikkar trolley, gefen shi Hajiya Laila ce itama, jikin ta sanye da wani ɗanyen leshi, itama jikkar trolley ɗince riƙe a hannun ta tana ja. "Yes sune kuwa" Bilal yayi saurin cewa, tun ma kafin Al'ameen ya iya buɗe bakin shi. "Kuzo muje" MD ɗin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye zuwa ga ficewa daga Office ɗin. Sannu kan hankali suke binshi baya, har zuwa wani ɗan madaidaicin Office, inda anan ne za'a tantance Rana, Lokaci, da kuma ƙasar da Alhaji yaron ya nufa kai tsaye. Sun matuƙar sha wahala, inda Allah ma ya taimaka wai kusan zamu iya cewa Al'ameen ɗin sananne ne, kuma dama ko ba komai yana da parmanent viser a airport ɗin. Sannan yana da alfarma a ƙasar dama mahaifin nashi. Shi kanshi Bilal da idanu yake bin Al'ameen. Yau ya zama Al'ameen ɗin da ya sani ada cen, kafin Suhan ta shiga rayuwar shi, komai yake yi a ɗan zafafe yake yinshi, hatta da saurin aikin na ma'aikatan ya raina, da kanshi ya zagaya, yana mai amsar mouse ɗin computer ɗin. Ma'aikatan wurin kaf saida sukayi mamakin kwalwa irin ta Al'ameen ɗin, yanda yake sarrafa computer kaman shi ne ya ƙereta. Sansaraƙwai sukayi suna mai kallon shi, aiko cikin lokaci ƙanƙani ya samu dukkanin bayanan da yake son samu, da ƙasar da Ya tafi, da gidan daya sauka, kai hadda ma number ɗin taxi ɗin da ya hau lokacin da ya sauka. Da ƙarfi ya buga dex ɗin da computer ɗin take kai. "Yes I Got It" Abunda ya iya faɗa kenan, idanun shi da kalar fatar jikinshi gabaki ɗaya ta cenza kala zuwa ja. Saida wasu daga cikin Office ɗin suka tsorata, Amman an gaza samun wanda zaiyi wata kwakkwarar magana, tunda sunga MD ne da kanshi yazo dashi. A take ya bada umurnin da a sama mashi viser ta ƙasar shi da Bilal. Kusan zamu iya cewa kuɗi sune babban abun alfarma a ƙasar, cikin ƴan awanni sai ga ticket an kawo mashi har Office ɗin MD inda suke zaune suna sake tattaunawa. Ba ɓata lokaci, flight ɗin da zasu hau har yayi landing, saura ƴan mintoci su ɗaga zuwa ƙasar ta Turkey (Istambul) **** Nureen ne zaune cikin motar sa, ƙirar BMW 2019 model, gefen shi abokin shine mai suna Khalifa. Nuren ɗin ne ya kai kallon shi kan abokin nashi "Khalifa tell what should i do? Ina son Nihal na rasa ta yanda zan ɓullo mata, Kaga na jaraba wannan dubarar da ka bani ta ince mata zanyi aure, Amman naga shiru har yanzu tun da na barta gidan nan, babu wanda ya nemeni, ko ba komai dai yanzun nasan ta cenza, ya isa ace ta gyara, kasan fa Yayan nan nata Al'ameen da zuciya da kuma miskilanci, gashi shima Dad ɗinta har yanzu bai nemeni ba, na bincika ance ma basa garin shi da Mom ɗin tata" ya faɗa Sound tentionally. Kai daka kalleshi zaka fahimci irin yanayi na damuwar da yake ciki, matsalar mata ta cikin gida ba ƙaramin abu bane, yau da ace baya son Nihal ko aura mashi ita akayi, babu abunda zai hana shi rabuwa da ita ya nemi wata, matan nan ma yanda sukayi yawa a gari gashi da kuɗin shi. "Man kawai ka share, basu matsu bane kawai, duk lokacin da suka nemeka sai kaje, kayi ta zama a haka ka bari har sai sun nemeka" shima Khalifa ɗin ya faɗa cikin jin haushin abokin nashi. Kullum suka haɗu baida wata magana sai ta Nihal, Allah ma ya sani yana mugun son matar shi, har ƙasar ya bari ya gani ko zai manta da ita Amman ya kasa, kuma gashi har maganar da ake yanzu cikin dangin nashi babu wanda yasan halin da ake ciki, dama ya tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro. "Au haka ma zaka ce man? ina neman shawara Amman kana neman gaya man magana?" Nureen ɗin ya faɗa shima a zuciye. "To Man na faɗa maka yanda zakayi kaƙi ji, kawai ka tura mata text cewa nan da sati biyu ne bikin naka, an ɗaga Amman zaka bata zaɓi, kodai cikin sati biyun ko makaranta ce zata nema ta shiga, inda zata iya duk wasu aikace aikace na matar gida, ko kuma kayi auren ka kawai, ka tura mata da takadda, sai ta zaɓa, kana jiran amsar ta. Wallahi zaka ga reply nata cikin sauri. Kuma ka jaraba" "Ko?" Nureen ɗin ya tambaye shi. "Just try it Bro" cewar Khalifa. Ba musu Nureen ya jawo waya yana mai lallatsa keybord nata ya tura mata da saƙon waya. Ba ɓata lokaci sosai sai ga saƙon nata ya dawo. "Am happy Baby, One week ma is enough for me. I missed u dear Husby. I kissed u" Murmushi ya saki sosai, yana mai cewa "Bro look at her reply, itama tayi missing ɗina sosai, nagode maka, dan haka zanje kawai sai in sanya a fara gyara mata gidan zuwa nan da sati ɗayan. " Yanzu naji batu shege. Abokina, ai na gode ma Nihal ɗin nan, ta kusa zata man aboki" cewa Khalifa yana mai miƙa mashi hannu suka tafa, sannan Nureen ɗin yayi ma motar key suka bar wurin. ***** Da gudu ta shiga sashen nawa da murnar ihun ta. A zabure na fito daga cikin bedroom ɗin nawa domin ganin ko menene. Aikuwa ina fitowa ta rungume ni tana mai cewa Aunty Suhan ya amince, zan koma gida na, Aunty Suhan please ki fara man classes daga yau, wallahi ki nawa kike so zan baki, nidai ina so in iya. Please amaryar Yaya" Sai yanzu na fahimci inda zancen ta ya dosa. Ɗan janye ta a jikina nayi, nima ina mai sakar mata murmushi, cikin aji nace "Zaki iya biyana kin tabbata?" Gyaɗa man kai tayi da sauri cikin zaƙuwa da jin ko nawane zance ta biya. Ni mamaki ma ta bani, yau Nihal mai sanya ni inyi mata abu, babu gode balle na gode, yau ita ce ke cewa zata biya ni? Oh duniya kenan mai juyi juyi rawar ƴan mata, na gaba ya koma baya. A hankali na shiga takawa zuwa tsakiyar falon nawa, saida na daidaita zamana bisa Sofar, sannan na buɗe baki cikin wata irin magana mai cike da ƙwarin guiwar hankalin da nasha alwashn koya mata, nace zaki bada ten million!? (10m) Cikin zaro idanu da kaɗuwa take kallona, bata taɓa tunanin jin hakan daga bakina ba, yanda taga na amshe ta, na sakar mata fuska, na jata a jiki cikin kwana biyu nan, ta ɗauka ma kyauta zance zan koya mata, Amman sai taji saɓanin haka Ni kuwa a nawa ɓangaren, izza, tutiya da alfaharin dukiyar da tasha yiman a baya, sune suka sabbaba wannan abun da nake niyyar yi mata. Ko ba komai dole ne in fahimtar da ita kuskuren da tasha tafkawa a rayuwar tata. Baki a buɗe tace "Aunty Suhan Ten Million fa kika ce! ?" nima cikin san tabbatar mata da abunda nace ɗin na shiga gyaɗa mata kai *"Yes Ten Million Nihal"* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~79~* °^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^° Kusan zamu iya cewa sanyi ƙafafun nata sukayi. Da wani irin kallo Nihal ɗin ke bin Suhan, yanayin ta kaf ya cenza zuwa kalar tausayi. Duk da taɓa Suhan ɗin tausayi, Amman wannan ba shine zai hanata ta nun ambata matuƙar kuskurenta ba, masalan idan ta tuno irin yanda taci bala'in wahalar Nihal ɗin a rayuwa. Gyara tsayuwarta tayi, tana mai bin Nihal ɗin da kallo, cike da wani irin yanayi, gabaki ɗaya Suhan ɗin ta cenza, ta murje, fatar ta sai wani irin kalli da sheƙi takeyi, kai idan ka ganta ma zaka ɗauka dama cen cikin gata ta taso. Ta zama matar manya, hatta da jikin nata ya sake cikowa, duk da dama cen ita ɗin ba ramamma bace. "Kije kiyi shawara Nihal, duk abunda kika yanke zan saurare ki, and payment ɗin zaki iya yi throug Bank ko kuma cash, duk dai wanda yafi maki sauƙi, and i promise u sai kunzo kin mani godiya" tana gama faɗin hakan ta zagaye Nihal ɗin da take tsaye kaman an dasa ta. Kai tsaye cikin falon ta isa, tana mai zama saman Sofa, sannan ta jawo remote ta kunna tashar Zee world ta cigaba da kallon Saraƙat zaujen da take kallo a daidai lokacin. Murna ai sai ta koma ciki, tuni idanun Nihal suka kawo ruwa, ita yanzu ko yanka ta za'ayi ina zata samu waɗannan kuɗin? Ta tabbata ko Mom ɗinta ta tambaya ba lalle ta samu ba, masalan ma yanzu da take cikin irin wannan situation ɗin, na damfarar da Alhaji Yaro yayi mata. Dad kam dama ba'a maganar shi, shi ko kallon ta ma bayayi, toh balle uwa uba Ya Ameen, ta ina ma zata fara tambayar shi? indai ba sarƙoƙinta zata saida ba da motar ta? Amman kuma ai abun kunya ne ƙawayen ta suga tana siyar da ƙadarori, kuma aganta bata da mota, yanzu idan tayi saken rasa motar ta wanene zai siya mata wata? Ta tabbata ko da Nureen zai sai mata wata ba yanzu ba, sannan bama zata iya tunkarar Ya Ameen da zancen ba. Nisawa tayi, tana mai ɗan murmusawa, ga motocin Mom? Ai ko cikinsu sai ta ɗauki ɗaya kafin ta samu ta shawo kan Nureen ya sai mata wata, tunda duk abunda Zatayi danshi ne zatayi. Juyawa tayi, tana mai komawa cikin falon.kujerar dake kallon ta Suhan ɗin ta zauna. "Aunty naji na yarda zan bayar insha Allahu, dan Allah mu fara lesson ɗin kafin in haɗa kuɗin" Kallon ta Suhan tayi, tana mai murmusawa kaɗan. "Nihal pay before serve" Abunda ta iya ce mata kenan, tana mai maida hankalinta kan Tv ɗin. Jiki a sanyaye Nihal ɗin ta miƙe tana mai cewa "To Aunty insha Allahu zan kawo" Juyawa tayi tana mai ficewa daga falon. Dariya Suhan tayi bayan idasa ficewarta, "Humm Nihal kenan, ina so ne ki ɗauki darasi, ba komai ne kuɗi ke sama maka ba a rayuwa, kuma dan ka tsinci kanka a cikin waɗanda Allah yayi ma nasibi, ba shike nuna cewa kowanne talaka banza ne wulaƙantacce a wajenka ba, kuma shi ɗan adam daraja ne gareshi, dole ne watarana ka nemi wani abu wajen shi, idan ka riga ka mashi wulaƙanci tun farko fa? Kayi yaya?" Ɗan nisawa tayi tana mai cewa "Allah shi kyauta, ko kuɗin kika bayar zanyi maki ne kawai domin mijina, kuma ba wai wani amfani zanyi da kuɗin ba, aa darasi rayuwa kawai nake so ki ɗauka. Amman da ko kallo baki isheni ba, kije cen kiji da matsalar ki" ************* Suna sauka filin jirgin, hayar taxi suka ɗauka kawai, gami da shaida mashi inda zai kaisu. An kuwa ci sa'a tafiya ba nisa sai gasu cikin area ɗin. Unguwa ce da take tsit, baka jin komai sai kukan tsuntsaye, akwai yalwar itace, da wasu irin duwatsu masu tsawo, bayan duwatsun ruwa ne makeke, tsuntsaye sai shawagi suke sama, da manyan jirage da ƙanana na shaƙatawa. Ga wani irin sanyi, gabaki ɗaya ma area ɗin snow ce ke sauka a hankali. Bayan sun sallami taxi ɗin ne Ya Ameen ya sake duba number ɗin gidan. Da hannu yayi ma Bilal nuni, dama sun riga da sun tsara yanda komai zai tafi. A hankali suka shiga gangarawa zuwa gidan da ke maƙautaka da gidan, makulli Al'ameen yasa, gami da buɗe gidan suka shiga, dama tun jiya da daddare ya kammala komai na booking gidan, sannan suna sauka aka miƙa mashi ɗan makullun gidan. Gida ne ɗan madaidaici. Safe content ne, mai ɗauke da ɗan madaidaici falo, sai ɗakunan bacci guda biyu, da kuma Kitchen gefe, kowanne ɗaki yana da toilet da gadon barci, sai mirror ɗan madaidaici da kuma wardroop ta bango. Babu abunda babu a gidan, komai tsaf yake, kaman dai gidaje ne na haya, wanda ake bama baƙi da suka sauka ƙasar, kuma basa son zauna Hotel. Wasu irin manyan barguna ne cikin wardroop ɗin ɗakunan, saboda irin sanyin da ake tsalawa garin. Faɗawa bisa luntsuma luntsuman kujeru Bilal yayi, yana mai sauke ajiyar zuciya ta gajiya, lokaci guda kuma yana mai sakin miƙa gami da hamma. Ɗan guntun tsoki Ya Ameen yayi, yana mai wucewa kai tsaye zuwa cikin ɗakin, ba tare da yace mashi komai ba. Shima Bilal ɗin dariya ya sheƙe da ita, "Mutumena miskilancin ne ya tashi ko? Ka ji dashi kuwa, dan wallahi ni nan bakaji yanda na gaji ba" Al'ameen ɗin na jiyo shi, yayi mashi banza, yana mai idasa shigewa ɗakin. Kusan tsawon awa guda, sai ga Al'ameen ɗin ya fito, jikinshi ɗanye da kayan jeans set, kalar ruwan samaniya mai turuwa, ya ɗora baƙar rigar sanyi mai hula a bisa kai, ƙafafun nashi ƙunshe cikin sneckers suma kalar kayan, sai baƙar safa daya sanya ciki,ya ƙunshe fuskar shi cikin baƙin face mask saboda sanyi, kai idan ba mugun sani kayi mashi ba, ba zaka iya shaida shi ba. Dayake farar fata ne, sai kayan suka amshi jikinshi, kyaun shi ya sake fitowa fili, kwarjini da haibar shi suka sake bayyana. Hannayen shi soke cikin aljihun wandon nashi yake yima Bilal magana, wanda gajiya ta sanya har ya fara bacci. "Ka tashi ka shirya zamu fita" Cewar Ya Ameen ɗin, wanda yake tsaye har yanzu. A hankali Bilal ya shiga buɗe idanun nashi, saman fuskar Ya Ameen ya sauke idanun nashi, sai kuma ya tashi zaune yana mai fashewa da dariya. "Me zan gani haka Friend? Duk ɓadda kamar ce? Kaida har yanzu bamu da tabbacin suna cikin gidan ko basa nan?" Takawa Ya Ameen ɗin ya fara yi a hankali zuwa wajen ƙofar fita. Saida ya kusa ida ficewa ne, sannan ya dakata yana mai cema Bilal ɗin "Idan baka iya kama ɓarawo ba, ai shi sai ya kama ka, kuma tsuntsu mai wayau a wuya ake kama shi" Bai jira Cewar Bilal ɗin ba, ya idasa ficewa abunshi. Dariya Bilal ɗin ya saki, "Hoo mutumen gaskiya kam bahaushe ne kai gangaran, ko ina ya iya hausa har haka?" ya faɗa yana mai sakin dariya sosai, sannan ya miƙe zuwa cikin ɗakin. Yayi tafiya mai ɗan nisa, zuwa bayan manyan duwatsun. Bakin ruwan yayi ma kanshi wuri, har yanzu hannayen nashi suna cikin aljihun nashi. A hankali ya ciro hannayen, yana mai sauke hular rigar sanyin dake kan nashi. Sai kuma ya ɗaga ƙafa yana mai bin gefe da gefen ruwan. Wayar dake cikin aljihun shi ce ya zaro. Vedio Call ya danna mata, sa'a aka ci kuwa wayar tata na kusa da ita, haka kuma datar tata a kunne take. Ina zaune nayi nisa cikin kallon da nake yi, ya zuwa yanzu Kunal ya fara bani haushi, irin cin amanar da yake yima Mouli, abun har ya fara fita raina, ji nake idan dani ce fa? Ba zan taɓa iya sakakin barin mijina da wata wai ita ƙawata ba, kaman yanda Mouli tayi ma Nandini ba, sai gashi daga ƙarshe ya ci amanar ta, ya koma kuma yana neman Ƙawar tata. Ringing ɗin da yake mallaki Ya Ameen mai sanyin tashi ne naji yana kaɗawa a wayar tawa. Cikin zaƙuwa na kai hannu na ɗauka, tashin farko na haske shi da wani irin ƙayataccen murmushi, kafin in sake mashi sallama cikin wata irin murya, da ni kaina bansan lokacin da nake yinta ba. "Mrs Al'ameen Dambulan" Abunda ya furta kenan shima, fuskar shi ta wadata da murmushi, idanun nashi cike da kewata. Nima dariya na saki mai cike da wasu irin ma'anoni da dama, ina mai cewa "Yallaɓai barka da rana" "Barka dai Yallaɓiya ta, ya kewa, ya kuma kaɗaici? Ana nan ana kewa ta ko?" Sunne kaina nayi ƙasa, sai naji kunya ta kama ni. "Kaman ka sani Hubby, kewarka ita ce komai nawa, tun lokacin da ka tafi kabar amaryar taka" "Ɗan matse baki yayi a hankali, sai kuma ya shiga ɗan kaɗa kai a hankali a hankali," Na sani wify, nima nan hakan take gareni, sai nake ji dama tare dake na taho, Amman kada ki samu damuwa, da komai ya koma normal ba zan sake barinki ba, a koda yaushe zan ɗauko ki anan ɗina" ya faɗa yana mai nuni da ƙirjin nashi Wani irin daɗi naji ya ratsa ni, sai na sake murmushi,ina mai ƙure shi da kallo, ya zuwa yanzu ya ɗaga kanshi yana mai kallon ruwan da yake gefe, wanda igiyar ruwa keta kaɗawa, gashin kanshi sai iska ke kaɗa shi, sai naga ma ya cenza gabaki ɗaya, ya sake kyau, ga wurin da yake wajen gwanin ban sha'awa, ya saje, kaman dama ɗan cen ne. A hankali muka shiga fira mai kwantar da hankali, Saima na sanya hannu ina mai rage volume ɗin Tv ɗin sosai, nunnuna man ko ina ya shiga yi, hatta da irin yanda tsuntsaye ke shawagi, kaman dai ina wurin ne. Mun ɗan jima a haka, kowa kewar kowa yake, kalamai masu kwantar da hankali muke aike ma junan namu, ji nake kaman in tsuntsuwa in iske shi inda yake. Ashe na daɗe ina wauta? Ashe na daɗe ina jin son Ya Ameen a cikin raina? Sai yanzu dana kasance dashi ne, sai nake gane ashe ma tuni wannan shi ake kira da so , duk wani motsi nashi ina son kasancewa dashi, banƙi ba ace kullum numfashin shi, saman fuska ta yake sauke shi. Daga cen baya Bilal ke tahowa yana kwala mashi kira "Mr Fafarawo! Mrs Fafarawo!" Da ɗan sassarfa ya ƙarasa inda Ya ameen ɗin yake tsaye, sai haki yake saukewa. "Nasha neman ka, ashe kai kana ta nan kana cin soyayya?" ya faɗa yana mai manne ido guda, alamun zaulaya. "Baby zamuyi magana anjima, yanzu zamu je mu samu abunda zamu ci ne, ina jin yunwa, gashi ina kewar abincin ki" Ɗan zaro idanu nayi, "Dear yanzu fa ƙarfe huɗu anan, na kuma tabbata ku anan yanzu kusan bakwai tayi, please ka dena zama da yunwa, kuje ku samu wani abu kuci, kaci dani Baby, kasha man ice-cream kaji?" Murmushi ya saki, "OK Done wify, bye i love u" ya faɗa yana mai sakar man wani irin Kiss. Ina dariya na kashe wayar, so nake ma in tashi in tafi gidan su Hafsat, gobe suna gashi kuma har yanzu ban tafi ba, na ƙagara ma in fita, domin ya zuwa yanzu nasan ƴan Kankiya ma sun isa isowa. A hankali na sauke wayar ƙasa, wata irin kewar mijina nake yi, ba na gajiya da faɗar irin dacen miji da nayi, komai ya zama gwanin ban sha'awa. Ya Ameen namiji ne harma ya zarta, komai nashi a nutse, komai nashi daban ne, ina jin Bilal nata yi mashi tsiya, wai yaushe ya fara iya soyayya haka? Bai dai tanka shi ba, balle yace mashi wani abu. A haka na miƙe, ina mai isa bedroom ɗin, na ɗauko hijab da makulli, sai ƴar jikkata. Ƙasimu Driver ne na sanya ya kaini, wanda muka rabu da zummar cewa bayan isha'i yaje ya ɗauko ni zuwa gida. ******* Baba Alhaji ne ya sake russunawa gaban mai martaba, "Haƙiƙa ranka ya daɗe haka akayi, sannan duk ina da wasu hujjoji da zasu sake tabbatar ma mai martaba da abunda na faɗa ɗin, saboda haka ne nake so da a bani tsawon kwanaki bakwai, insha Allahu zan tattara sauran bayanan, kuma duk abunda ake buƙata za'a samu da izinin Allah" Gyaɗa kai mai martaba keyi cikin gamsuwa da bayanin Baba Alhajin. Cikin isa, da magana irin tasu ta saraki ya maida kallon shi kan Alhaji Mustapha da yake zaune bisa wata irin Sofa mai kyau, shi da Alhaji Auwalu ne bisa Sofar, yayin da gefe kuma Mama Fulani ce da Umma, sai kuma sauran matan sarkin bisa wata kujerar suma, sai Mom dake zaune bisa kujera mai cin mutum biyu. Yau babu irin tashin hankalin dake saman fuskar ta irin na jiya, saidai har yanzu fuskar babu koda ɗishin annuri ne a saman fuskar. Bana tunanin idan Hajiya Kubra zata iya bada haɗin kai irin yanda ake da buƙata. Maganar mai martaba sarki ce ta katse shirun da ya biyo baya, tun kammala jawabin Baba Alhaji. "Ah Alhaji Mustapha kaji abunda lauya ya faɗi, saboda haka ne mu ba zamu riƙe ku ba, zaka iya ɗaukar su matan naka ku koma gida, alabasshi zuwa sati guda ɗin da shi Barrister ya ɗiba, nasan zuwa lokacin shi Al'ameen ya samo shi Wancen mayaudarin Alhaji Yaro, saboda haka ne zamu san abun yi, masarauta tana yi maku fatan sauka gida lafiya" Abunda Mai martaba ya faɗi kenan, yana mai miƙewa, da kanshi ya tako har zuwa gaban Alhaji Mustapha da Alhaji Auwalu ya basu hannu sukayi musabaha. Kai tsaye cikin gidan ya nufa yana mai gyara alkyabbar dake jikin shi, wanda take ta faman ɗaukar ido da walwali. Kai Umma ta sauke ƙasa, a hankali Mama Fulani ta kamo hannuwan ta, gyaɗa mata kia take a hankali, haƙiƙa ita kanta tasan irin dattakon da Umman tayi, wanda wanna ba abun mamaki bane, duk wani jinin sarauta na asali, zai iya ma yin abunda yafi haka,masalan ita data kasance jinin mai martaba kai rasuwa. Wanda kowa ya sanshi wajen kawaici, dattako da halin girma. Idan ka kalli Hajiya Kubra kuwa, tabbas ba sai na faɗa maka ba, tana cikin wani irin yanayi na kaɗuwa, ga yanda take ganin Fuskar mai martaba zaiyi wuya ace yabar mata dukiyar nan, gashi da gani irin mutanen nan ne masu tsaida gaskiya, gashi dukkan hujjoji sun tabbatar da cewa lallai dukiyar ta, dukiya ce da take mallakin Suhan yanzu halak malak, idan ka cire wadda Umma tace ta yafe mata, kenan ba zata tsira da ko rabi ne a cikin dukiyar dake hannun nata ba kenan? Lallai ba zata iya bari wannan al'amari ya tafi a haka ba, zata san duk yanda zatayi ta mallaki dukiyar ta ita kaɗai, idan ma ta kama a kauda wani ne, tabbas zata kauda duk wanda yake neman shiga hurumin dukiyar tata, yanzu ita faɗan nata, ba da Umma Zatayi ba, da Masarauta Zatayi, wanda take iƙirarin yima kowa adalci, mai laifi kuma ya amshi hukunci. Cikin gida suka shiga, saida suka gama kintsa komai, sannan akayi masu rakiya zuwa bakin mota. Dole saida masarauta ta haɗa umma da kuyangi uku amuntattun dattijai, wanda zasu dinga tayata zama, da kuma kula da duk wani motsin ta, sannan ta haɗa ta da fadawa guda biyu, wanda idan ta kama koda driving ne zasu dinga yi mata. Sun baro masarauta cike da farin ciki, in ka ɗauke Mom, wanda zaune kawai take, har yanzu ta gagara cema kowa komai. Ta fannin Umma kuwa, wani irin annashuwa take ji tana shigar ta, ko ba komai yanzu komai ya bayyana, Hajiya kubran ta gane ko wacece ita, sannan ta gane matsayin ta a gareta yanzu, ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli yaci Riba, ba sauran taƙama ko ɗaga kai, sannan idan yanzu Suhan tace bata yarda ba, bata da yanda Zatayi da ita, dole ta miƙa mata haƙƙin ta, saidai bata fatan ace ankai ga hakan, saboda ko ba komai yanzu matsayin Uwa take gareta, na farko gata surukar ta, sannan gata abokiyar zaman Umman ta, sannan mata ga mijin Umman tata, ko dan haka za'a ɗaga ma Hajiya Kubran ƙafa, sannan tasan duk wani abu da tayiyyi mata a baya, sheri ne irin nasu Mama Talatu, wanda ko ita Umman a yanzu bata jin idan zata daure suci gaba da zama a cikin gidan nasu, bata son duk wani abu da zai shafi zaman gidan, saboda yanzu rayuwa take so su gudanar mai cike da tsafta, mai cike da addini, mai cike da soyayya da ƙaunar juna, tana fatan ace tayi sanadin kulluwar duk wata ɓaraka da ta riga ta shigo gidan, saboda haka, duk wani shige da fice, da motsin kowa a gidan tana ankare dashi, lokaci ne da zata fito ta shaida ma kowa da kuma duniya cewa itama fa mata ce kaman kowa, saboda haka duk wanda tasan zai iya zama barazana ga zaman lafiyar gidan, to fa a shirye take data ɗauki mataki akai, wana tana da tabbacin samun goyon baya, daga mai gidan har magajin gidan. Sun share awanni kafin su iso gidan. Kaman yanda suka zata ɗin dai ne, gidan tsit, in ka ɗauke mai gadi , sai iro da yake cen gefe yana yankar Flowers, sai masu aiki mata jefi jefi da sukan gitta. A harabar gidan sukayi parking, dukansu fitowa sukayi suna masu ɗauke da salati ga bakunan su, jin ƙarasowar su ne ya sanya sauran ma'aikatan firfitowa cike da farin ciki suna masu yi masu sannu da zuwa. Mom dai wucewa tayi kai tsaye zuwa sashe nata, yayin da take aike ma sashen Suhan da harara, kai kace Suhan ɗin ce a wajen. Ita ko Umma tsayawa tayi suna gaggaisawa da ma'aikatan gidan, masalan ma data kwana biyu bata cikin gidan, ya zuwa yanzu dai labari ya iske kowa na irin matsayin Umman, saboda haka ne, kowa sai yake kallon ta cike da kwarjini da haiba, gashi duk ta wani cenza, hutu da jin daɗi sun sake huda jikin ta, ta zama wata ƴar gayu, kaman ba Umma mai aiki da kuka sani cen baya ba. Mama Saude sai taɓo Mama Talatu take yi, inda ita kuma sai ta buge mata hannu, duk Umman na an kare dasu, murmushi ta saki tana mai cewa "Bari in ƙara sa ciki in ɗan watsa ruwa, ke GAJE muje ko sai a samu a ɗan gyaggyara man sashen" ta faɗa tana maida kallon ta kan haɗiman da ta taho dasu. Juyawa tayi zuwa sashen nata, ko ɓangaren sashen Suhan bata kalla ba, duk kuwa da yanda idanun nata ke son kaiwa wajen sai tayi maza ta janye kanta daga kallon sashen. Tana fatan ace ɗiyar tata tana ciki hankalinta a kwance, saidai tasan da kamar wuya kam, ko ba komai wannan issue ɗin kawai daya ɓullo ya isa ya wargaza dukkan wani farin ciki na Suhan ɗin. Shiyasa ma bata shaida mata ba da bakinta, ta ƙyale shi Al'ameen ɗin yayi amfani da baiwa da dubarar da Allah ya bashi wajen fayyace mata komai. Bata so ta saka kanta cikin rayuwar auren Suhan ɗin, masalan da ya kasance gida ɗaya suke zaman aure da ɗiyar tata. ******** Sun sha yawo sosai, dama shi Bilal wannan ne karon shi na farkon zuwa ƙasar, ƙasar ta matuƙar burge shi, Larabawa ne sosai, saidai al'adar su da ɗabi'ar su, suturar su tasha bamban da sauran Larabawa, idan Kaga yanda suke gudanar da al'amurran su, kai kace turawa ne. Saboda haka ne saida sukayi mai isar su yawon, sannan suka nemi abunda zasu ci suka koma gida. Bayan Sallar isha'i ne sosai, saboda haka suna gama abunda duk zasuyi, naga Ya Ameen ya fiddo waya yana magana cikin halshen turanci mai cike da gwanancewa,kai kace ba bahaushe bane. Wasu irin jibga jibgan riguna naga sun ɗora saman nasu kayan, sannan sukayi amfani da face mask baƙa, wadda ta rufe ko ina na fuskar su, in ka ɗauke idanun su, shi ya Ameen ma saida yayi amfani da baƙin Google ya rufe ƙwayar idanun nashi. Ƙarar motar da suka jiyo ce daga ƙofar gidan, ya sanya su hanzari ficewa cikin sanɗa, kaman wasu munafukai, cikin motar sukayi ma kansu mazauni, yayin da ɗaya daga cikin motar ya fice zuwa ƙofar gidan da Alhaji yaron yake ciki, hannun shi ɗauke da wani kwali. A cikin motar ne Al'ameen yabi dukkan hanyar da zai bi wajen ganin ya ɗauke ganin CCTV camera ɗin da take yankin, ta cikin Computer ɗinshi, ta yanda koda Anzo binciken wani abu ba lallai a gane ba. Sau biyu yana knocking, kaman babu kowa ciki, har ya haƙura zai juya, yaji alamun tafiya. Kwalin da yake ɗauke a hannun shi ne ya turo zuwa gaba. A hankali ta ɗaga ɗan abunda zata iya hango ko wanene a wajen, ganin mutum da kwalin burger a hannun shine ya sanya ta ja baya ta buɗe gidan. Shiga yayi ciki bai ce mata komai ba, yayin da ta saki kyauren tana mai binshi a baya. Saman dining tayi mashi nuni daya aza mata, sannan tace ya jira ta zuwa ga kawo mashi kuɗin. Tana fitowa kuwa ya buɗe wani ƙaton hanky yana mai rufe mata fuska, ƴar ƙara tayi kaɗan ta sulale a wajen, ƙarar dataja hankalin Alhaji Yaro kenan ya fito da sauri daga bedroom ɗin domin ganin ko me ke faruwa. Shima yana fitowa Irkan dake tsaye bayan kyaure ya rufe mashi hanci da wannan hancarchip ɗin. Ba ɓata lokaci shima ya sulale a wajen, da sauri Irkan ya latsa wani abu dake hannun shi, sai gasu duk sun shisshigo da sauri. Alhaji yaro ne ma yaso basu wahalar ɗauka, saboda irin yanda yake da tsayi da girma, bayan babbar motar duk suka kwakkwantar dasu, suna mai rufo masu gidan, sannan suka ja motar da matsananci gudu suka bar wajen... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~80~* *A cigaba da yi mani haƙuri dan Allah, uzirori ne ke riƙe ni, Amman insha Allahu mun dasa kenan, har sai mun ƙarƙare* *********** Ba ƙaramin mamaki Alhaji yaro yayi ba. Tun bayan daya fardaɗo yake bin ɗakin da suke ciki da kallo. Gefen shi Hajiya Laila ce tayi wurjan-jan, kuka kawai take yi. Tun ɗazu take dukan Alhaji Yaron da hannuwanta da aka ɗaure su, saidai ba'a matse su ba yanda zasu wahala. Da idanu yake binta, yana mata wani irin kallon wahala, da kuma tuhuma. "Nima ban sani ba, ban sansu ba, fuskokinsu duk a kulle, tun ɗazu suke shigowa su gani ko ka farfaɗo, ka tashi hakanan, kada su kashe mu" Ta faɗa cikin wani irin kuka. Ƙoƙarin tashi zaune yayi, amma ya kasa. Baisan ko awanni nawa ya kwashe cikin wannan halin na ɓacewar hankali ba. "Laila wanene yayi mana haka? Me mukayi ma wani? Su wanene su? " Ya maida mata shima, cikin wani irin kaɗuwa. Su dukansu sun girgiza da ganin halin da suke ciki. Ɗakin da aka ajiye su kanshi ma abun kallo ne. Domin kuwa yayi datti sosai, ga ƙura ko ina, sannan babu wani abu dake cikin ɗakin, koda kuwa tsinke ne, kaman ma a bayan gari suke. A hankali ya buɗe murfin ɗakin, yana mai shigowa, hannun shi ɗauke da wata ƴar roba ta take-away. Sai leda fara sol, zaka iya hango gorar ruwa ciki, da kuma lemon roba. Har yanzu fuskar tashi a rufe take, in ka ɗauke sumar kanshi da take kwance luf, iskar ƙofar da ya buɗe tana shigowa, tana ƙaɗa gashin nashi. Gefen su ya ajiye kayan dake hannun nashi, yana mai matsawa kusa da Alhaji yaron ya sanya hannu ya ɗago shi. Zaune sosai ya taimaka mashi ya tashi. Sannan ya koma bayan Hajiya Laila yana mai kwance mata ɗaurin da akayi ma hannun nata. Har yanzu kuka take yi. Saidai babu sauti, sai hawaye da majina da take sha akai akai. Ko kaɗan tausayin su bai kama shi ba, ba wai dan sun ma mahaifiyar shi haka ba, sai dan irin cin amana, da ha'incin da suka sanya a rayuwar tasu. Irin su ne ke ja ma ƙasar tashi ta nigeria zagi. Irin su ne ke sanyawa amana ko taimako yayi kaɗan. Robar abincin ɗaya ya matsar mata da ita zuwa gabanta. Aiko ba wata wata ta jawo abincin ta fara ci, kaman tsohuwar mayunwaciya. Miƙewa yayi tsaye, yana mai zura hannayen shi duka cikin aljihun wandon shi. Ƙissima yanda zaiyi masu kawai yake yi. Sai wata zuciyar take shawartar shi kawai da ya miƙa su ga hukumar ƙasar, ya zuwa yanzu babu abunda yake ji cikin zuciyar tashi, illa wani mugun tsanar su. Da hannu yayi alama. Sai ga wani murgujejen mutum fari sol dashi, ga alama shima ɗan ƙasar ne. Ya shigo ɗauke da wata irin kyakkyawar madaidaiciyar kujera. Gudan hannun nashi kuma bindiga ce, ƙirar pistol. Saida yayi alamun girmamawa gareshi, sannan ya ajiye kujerar, yana mai komawa gefe ya tsaya. Da hannu ya kuma yi mashi alama da ya kwance Alhaji Yaron. Kwance shi yayi, sannan ya matsar mashi da abincin gaban shi. Duk kansu zaune suke ƙasa gabanshi, suna masu cin abincin cikin ƙasƙanci. Zuciyar imani ce ma kawai ta sanya shi basu abincin. Dan da ya biye ma Bilal, da har su koma ƙasar tasu ba zasu basu abinci ba, saidai ruwa. Har yanzu basu tantance ko wanene ba, basu kuma san laifin su gareshi ba. Saidai ganin farar fatar tashi, sai basu ɗauka ma ɗan tasu ƙasar bane. Sun ɗauka ɗan ƙasar Turkey ɗin ne. "Bawan Allah dan Allah laifin ke mukayi maka haka? Ka tausaya mana, ka sake mu, ƴan uwanmu na cen na jiran mu" cewar Hajiya Lailan. Jin kalaman nata, baisan lokacin da ya murmusa ba, har sautin shi na ɗan fita. Lallai ma Hajiya Laila da rainin wayau take, kenan ma ya gane Sam har yanzu basu fahimci halin da ake ciki ba. A hankali ya sanya hannun shi, yana mai yaye lulluɓin fuskar tashi. Ai tuni Hajiya Laila ta kuma zaro idanu, tana mai ja da baya da baya. Bakin ta har rawa yake. Ba Hajiya Laila ba, har shi kanshi Alhaji yaron da yake namiji saida ya kaɗu, ganin ko wanene zaune a gaban su. "Al'aaammm.." Cikin rawar baki take son faɗar sunan nashi, Amman ta kasa, saboda irin yanda jikin ta ke rawa, bakin nata na karkarwa. Da hannu ta shiga nuna shi. "Son...!" ta sake ƙoƙarta wa ta faɗa, cikin matsanancin tashin hankali. Kallon da yake yi nata, shi ya sa baba wata irin kunya, haɗe da nadama ce suka taru suka lulluɓe ta a lokaci guda. Sai ta sadda kanta zuwa ƙasa kawai. Bata taɓa tunanin wannan ranar na zuwa ba. Bata taɓa hararo wai ita Laila akwai ranar da zata muzanta haka ba. Idanun nashi jawur, sai ya haɗu da farar fuskar tashi, suka bada wata irin kala. Ba sai na faɗa maka ba, ran shi a matuƙar ɓace yake. Da idanu kawai yake bin su da kallo. Tuni ai Alhaji yaro ya ture robar abincin daga gabanshi. Ji yake kaman ya tashi ya zura da gudu, saidai ina za shi? Ko waɗannan murtuka murtukan mutanen da suke tsaye suna gadin su, fuskar nan tasu ba alamun imani, sun isa su sanya su suyi biyayya. Kaɗa ƙafar shi yake yi a hankali. Na daga cikin al'adar shi, idan ran shi ya ɓacin irin haka, zai dinga girgiza ƙafa a hankali a hankali. Rasa ma me zai ce masu yayi, saidai kawai ya miƙe, yana mai dosar ƙofar fita. "You have to be ready, we must go back to nigeria" Abunda ya iya faɗa kenan, yana mai daf da ficewr.sannan ya sanya kai yana mai idasa ficewar. Kuka Hajiya Laila ta kuma saki.. "Duk laifinka ne Alhaji, kai ka kawo shawarar mu taho da kuɗin mutanen nan, na faɗa maka tana da hatsabibin yaro, kuma kaima ka sani, Amman kai ta zura ni cewa mu gudu kawai, duk yanda yake ba ko ina ya sani ba ai, yanzu gashi nan ka jawo mani abun kunya, abun faɗa, ace kaman yanda nake da Kubra naci amanar ta, sai gashi tun ba'aje ko ina ba, tun bamu mori kuɗin ba, yaron nan yazo ya kama mu, cikin ƙasƙanci da abun kunya, yanzu ka dubi halin da muke ciki dan Allah, could you imagine?.. " Cikin tsawa Alhaji Yaro ya dakatar da ita. " Is enough Laila, ya isa nace, bangane ni na zuga ki ba, tun yaushe muke neman wannan damar dake? Tun yaushe in da na biye maki zamuyi hakan? Sai kuma nace ki bari dukiyar tata ta ƙara yawa a hannun mu, ke kaɗai kika sha Kunyar ne? Nace ke kaɗai kike cikin halin? Malama in zaki man shiru kiyi kawai, mu nemi mafita, amman ba zan taɓa lamuntar cin zarafi da ƙanƙanci daga gurin yaron ciki na ba.. " " Kai kake ganin shi yaro, Al'ameen ya wuce inda duk kake tunani, na sani kuma kaima kanka nasan ka sani, wace irin mafita ke garemu? Ka duba fa waɗannan jibga jibgan mutanen? Kai in baka tsoron su, wallahi ni ina ji, idan kuma kaima ka kuskure, wallahi ɗauke ka zasuyi nan take, dan Allah Alhaji kada kayi wani gigi, na roƙeka" ta idasa cikin wani irin gunjin kukan. Dayake su masu tsaron nasu ba jin hausa suke yi ba, su dai kawai aikin su suke yi. Sai faman kaiwa da komowa suke yi. Duk da haka Alhaji yaron bai ji shawarar Lailan ba. Miƙewa yayi a sukwane, da niyyar ficewa. Bakin bindiga kawai suka sanya mashi a ƙyeya, sai gashi ya kuma sake baje wa nan gaban Hajiya Laila ɗin a some. Wani ihun kukan ta sake saki; "Na bani Alhaji, ka gani ko? Ka ga abunda nace maka ko? Basu da imani, sai su kashe ka, dan Allah Al'ameen kayi haƙuri ka sake mu, ka ƙyale mu, wallahi zamu mayar maku da dukiyar ku hankali kwance.." nan fa tayi ta sambatu, tana mai jawo gorar ruwan, ya shiga tuttula ma Alhaji Yaro, Amman inaaa. Ko motsawa ma baya yi... ************* Ina cen na shige cikin ƴan hidimar suna, aka sanar mana da isowar su Umma nawa. Ƙai tsaye gidan Alhaji Auwalun suka nufa. Bayan sun sun huta sunci abinci. Gida fa ya kacame kaman a ranar ake sunan, duk ƴan Kankiya sun iso, harda su Huda, har kaka zuwaira ma tace ba za'a barta a baya ba. Nan fa gida ya kuma rincaɓewa. Masalan ma yanzu da labari ya zaga ko ina cewa Umman tawa gimbiya ce. Sai kowa yake ƙoƙarin ya ganta su gaisa. Kai tsaye ɗakin Hajiya Zainab aka nufa dasu. Sai kowa ya kasance Umman tawa yake mararin gani. Irin yanda ake yi ma Hajiya Kubra ada, a matsayin ta na matar Alhaji Mustapha ɗin, kuma kasancewa ta mai kuɗi. Wannan karon duk sai taga ba haka ba. Suna zaune a ɗakin ne ana ta faman gaisa wa na shiga. Kai tsaye kusa da umma ta na nufa, ina mai rungume ta na yaushe gamo. Sai kuma naji kaman wani kuka yana neman taho mani, duk sai aka saka dariya, mun burge kowa, muma yanzu mun zama mutane, irin yanda Umman tawa ta saki jiki da kowa. Sai abun ya ƙara burge su. Ita kanta Hajiya Kubran sai ta koma tana yaƙe, mutane kaɗan kaɗan ne suke ta ita. Ɗan tureni Ummana tayi dgaa jikin ta, tana mai cewa "Ah ke me zan gani haka? Allah na tuba, gotai gotai ɗin me?" sai aka kuma saka dariyar. Har Kaka zuwairan na cewa; "Ah to kema kin faɗa gimbiya Maryam, gashi ta ƙwace man miji, yanzu kuma za tazo tana wata shagwaɓa, kaman ƴar jariri ya" Ƙasa na zame, kunya na mai lulkuɓeni, lokaci guda kuma ina maida kallon na ɓangaren da Hajiya Kubra ke hakimce gefe. "Ina yini Mom, ya hanya?" na faɗa cikin girmamawa. Sai ta ɗan saki fuska, ba yabo ba fallasa ta shiga amsa man, kowa yayi mamakin yanda tayi ɗin, tunda kowa ya san yanda take da al'amarin namu. Har tambaya ta takeyi, wai "Ya gida ya zaman kaɗai ci?" Ƙasa nayi da kai ina mai cewa "Lafiya lau Mom" Da kallo ta shiga bina. Sosai tayi mamakin cenzawar tawa. Sai yanzu ne take ta hango tsabar kamanceceniya ta da Mahaifin nawa Yayanta Muhammadu. Ko ba komai ni kaɗai ce a yanzu take kallo, wadda na fito daga ɓangaren mahaifin nata. Sauƙin tsanar tawa sai ya ragu a cikin zuciyar ta, duk dai da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba. Akwai takun saƙa tsakani. Sun jima sosai a gidan. Kafin Hajiya Kubran ta buƙaci tafiya, a cewarta zata je ta kwanta ta huta, sai kuma zuwa goben. Kaman tace in taho mu tafi, sai tayi wani tunani. Yanzu fa idan kowa yaji dukiyar mu ce a hannun ta, kowa zaice ba dan Allah tayi ba. Share wa tayi kawai, nan aka samu wanda suka raka ta mota ta tafi. Nidai ban gigin raka ta ba. Har yanzu bansan a halin da muke ciki ba, gashi kuma nasan cewa umma ta ba zata taɓa faɗa man halin da ake ciki ɗin ba. Isowar su Afnan ne ya ƙara ruɗa gidan, ka dangin Sadeeq ɗin da suke ta ɓulɓulowa ko ta ina. Bikin suna fa an shirya shi sosai, in baku manta ba, dangin sadeeq, dashi kanshi sadeeq ɗin masu hali ne sosai, Shiyasa a wannan karon ma sunyi bajinta, sunyi matuƙar ƙoƙari. Ko shanaye manya gida biyu suka kawo, da tulƙa tulƙan ragunan su guda biyu. Sai akwatuna na kayan barka set mai guda shidda. Biyu na mai jego, huɗu na jaririya. Babu abunda babu ciki. Komai yaji masha Allahu. Komai ake ciki, ni Hafsat ɗin ke sanyawa gaba gaba. Na zama wata *Cele* kasancewa ta mata a gurin ya Ameen ɗin. Wanda kowa ke matuƙar sonshi da ji dashi. Alkhairin nashi a cikin ahalin nashi, sai ya siya man soyayya fiye da tunani na. Na ɗauka idan akayi bikin namu, zan zama wata bare a cikin su. Sai gashi duk inda na gitta, Aunty Suhan kake ji kawai ana ambata. Ni kaina nasan na cenza, na ƙara wani irin haske, nayi mulmul, fata ta sai sheƙi take yi, ga wani irin kwarjini na ƙara yi. Ko Afnan saidai ta dinga bina da kallo tana zaulaya ta. Aunty Feena ma ta saki jiki dani sosai, Ayan da Nasreem sun ƙara girma. Dama Ayan ɗan wuri na, duk inda na gitta hannun shi na cikin nawa. Sai hakan ya ƙara yi masu daɗi, kunsan ance mai ɗa wawa. Umma ta ta ba Hajiya Zainab gudunmuwa sosai, yayi da ta keɓe gefe dani tana mai tambaya ta ni me zan bada? Dama na kwaso kuɗi wanda na samu gudunmuwar biki, Ya Ameen ɗin yace in ajiye waje na, ko zan buƙace su. Ba ma yanda banyi akan ya amsa ya ƙiya, saidai cewa yayi inshi bai ƙara man ba, ba zai amsa nawa ba. Shiyasa nace mata su zan bata, bansan ne zan siya mata ba. Taji daɗin hakan, inda tace ko Al'ameen ɗin kada in ma magana, kuma duk abunda nake so, kada in sake in tambayi mijin nawa, in tuntuɓe ta kai tsaye. Kusan dubu ɗari biyu na ware, kuɗin suna da yawa, dan haka nasan wannan ma sun isa, dama yau nayi niyyar bata. Sai kusan ƙarfe takwas na dare, Mudi driver yaje ya kwaso mu, ba yanda Hafsat batayi ba in kwana, ai nan ma duk gida be. Amman na ƙiya, na dai ce mata zan yi sammakon komawa gidan sunna, washegari. Ko a mota fira ake jefi jefi, Afnan kan saka ni, yayin da Aunty Feena saidai tayi murmushi. Nihal ma da ɗan dama, Amman tunda nace mata sai ta biyai kafin in koya mata wasu abubuwa, duk sai jikin ta yayi sanyi. Gashi inda Allah ya taimake ta, Nureen ɗin ya ɗan turo mata wani abu, wai tayi buƙatoci. Amman fa ta sani, ita da komawa, sai ta cika sharuɗɗan da ya gindaya mata. Dama ta ƙagara Mom ɗin tasu ta dawo taje ta same ta akan batun. Shiyasa ko Saudat bata faɗa mawa ba, tasan ba shawarar arziƙi zata bata ba. Ita duk sai taji ma Saudat ɗin ta sure mata. Irin manyan laifulan da idanun ta suka gane mata Saudat ɗin na aikatawa. Saida aka kai Saudat gida. Sama sama sukayi Sallama. Ita kanta Aunty Feena ta lura akwai abunda ke faruwa. Amman ta zura masu idanu ne, taga iya gudun ruwan su, dama tasan lokaci na zuwa, da kowaccen su zatayi nadamar abubuwan da ta aikata ɗin. Janye Afnan nayi zuwa sashen nawa, ita da Ayan. Munsha firar mu sosai. Nan fa aka zage ana bani labarin Sir Saleem. Tabbas naji matuƙar daɗi, daga Afnan ɗin, har Sir Saleem ɗin sun dace da juna. Tsoro na ɗaya cikin al'amarin watau Ma'u, domin na kula ita ɗin mahaukaciya ce a fannin Kishi. Sai dai ga alamu Saleem ɗin bai yi ma Afnan maganar ma'u ba. Dan duk cikin labarin banji tayi ma Suhan maganar Ma'un ba. Washegari da wuri wuri muka sake shiryawa, saidai kafin mu wuce, saida na leƙa sashen Mom ɗita. Ganin tare muke da Afnan, sai naga kaman bata saki jiki sosai ba, kuma gashi Alhaji Mustapha a sashen nata yake. Cewa tayi kawai mu wuce sai ta iso. Dan haka, ko da na isa bamu zauna ba. Mu kenan shige da fice. Yarinya taci Sunan Zainab. Ana ce mata Khairi. Suna ya ƙawatar.Hafsat taji daɗin kyautar da nayi mata ta kuɗi, duk da tasan cewa kyautar daga gareni take, tasan ta Ya Ameen sai ta wuce hakan. Hajiya Kubra ma tayi bazata. Itama ta kawo turamenta masu kyau sosai manya, da kayan jariri. Sai ɗan kunne Ƙarami na gwal wa jaririya. Nan fa aka shiga faɗa, da ƴan maganganu, dan a tarihi ba'a taɓa ganin tayi hakan ba, sai kowa ke ganin ko dan taga Alhajinbya ƙara aure ne, Shiyasa take son shiga dangi itama. Alhaji Mustapha ma yayi ƙoƙari sosai. Iyayen kaya da ya bada da duk wani abu da ake buƙata. Ya ɗauke masu shi na sunan. Suna fa yayi kyau ya ƙayatar. Kaya kala uku na sanya nima a ranar, duk inda na gitta saidai a bini da kallo, wanda basu idasa sani na ba a dangi, suka ƙara waye wa dani. Ita kanta Hajiya Kubran idanun ta na bisa ni. Mamaki take yi, wai nice na zama haka? Dama ita bata kushe ni ba ta hanyar kyau, Amman talauci da ƙanƙancin da nake ciki a lokacin su ta guda. Amman ko yanzu ai tasan tayi suruka, ga wata irin wayewa da na sake yi. Har su Khadeeja sun yi man kara sosai, suma sunzo sunan, duk da basu daɗe ba suka koma, tunda sun ji cewa na samu trnsfer. Sun matuƙar ji babu daɗi, har yanzu Khadeeja na tare da abokin Ya Ameen, wanda suka haɗu da bikin nawa. Taro ya tashi lafiya sai sam barka, Khairi tazo da goshi. Tayi matuƙar mutane, Hafsat ta samu alkhairi sosai, kasancewar ta mai zaune da mutane lafiya. Kowa nata ne, bata taɓa wulaƙanta ka dan baka dashi. Taro na watsewa muma muka tattara muka koma gida. Da niyyar zamuje mu huta kuma, sai an kwana biyu. Saboda aikin nama dai akwai ma'aikatan da zasu yi mata shi. Munsha albarka a wajen Kaka Zuwaira da Hajiya Zainab. Masalan ma ni, yanda suka ga inyi nan inyi nan, duk da nake ji na bana da lafiya, haka nayi ta daurewa, har dai Allah yasa aka gama lafiya. Duk inda nayi dama Kaka Zuwairan na hankalce sani. Inma taga na cika zirga zirga, ta kan ce wai inyi a hankali, gashi ni ba ni kaɗai ba. Abun na bani mamaki, saidai inyi murmushi kawai. To duka ma yaushe akayi auren? Auren da ko wata baiyi ba, Amman ace har na samu ciki? Kawai dai gajiya ce, saidai inyi murmushi cikin jin kunya kawai in wuce sum-sum. Kwana biyun nan da mukayi muna zirga zirga, sai na samu ƙarancin ganawa da Yayan nawa. Wani lokaci saidai in tadda missed call. Da na kira kuma zai hau ƙorafin bana da lokacin shi, ina cen tare da su Hafsat, muna ta luguden laɓɓa. Saidai inyi dariya. To sai ma nazo in na kira bana samu, saidai wani lokaci inga text ɗinshi, cewa yana lafiya. Bansan lokacin da zai dawo ba. Hakan yasa bayan na samu natsuwa na kira shi. Saidai bata shiga ba, saƙo na tura mashi. Amman shima sai na lura kaman bai shiga ba. Haka dai har aka kwana. Nan fa hankali na ya fara tashi, akai akai na kan kira, Amman dai a kashe. Kasa daurewa nayi na cenza akalar kiran zuwa ga lambar Bilal. Shima dai duk maganar ɗaya ce. Afnan ce ke kwantar mani da hankali, kan cewa insha Allahu ba abunda zai same sh, yana cikin ƙoshin lafiya. Duk da ita ma hankalin nata ya fara tashi. ******** Ta ɓangaren Ya Ameen kuwa, kwana uku ya ɗauka, kanshi yayi matuƙar zafi. Shirya yanda zasu fita da Alhaji Yaro, da Hajiya laila yake ta faman yi, ba tare da sun bashi wata matsala ba. Kuma gashi bugun da Erkan yayi ma Alhaji Yaro a ƙyeya, har ya samu rauni, saida ya kaishi asibiti aka duba shi, dalili da ya sanya kenan bai sake yunƙurin gudu ba. Suna cikin wani hali, dan ma babu wata izaya da ya ke yi masu. A inda suke dai, akwai toilet, zasu iya shiga su biya buƙata. Sannan ya sanya an kawo masu manyan barguna, kuma abinci ma yana basu. Saidai fa, nan da cen basa da damar motsawa. Ya amshe wayoyin su, basa da wata hanyar sadarwa. Sannan duk kuɗaɗen da suke Wancen gidan, ya sanya an kwaso mashi su. Haka kuma ya maida ma hukumar ƙasar makullan gidan. A cewarshi wanda suka amshi gidan sun koma ƙasar su, bayan ya sanya an kwaso masu kayan sanyawar su. Sai a kwana na huɗu ne abunda yake ysarawa ya kammala. Ko ya shiga ɗakin da suke ma, iyakar shi dasu kallo ne. Babu alamun tausayawa tattare da Ya Ameen ɗin wannan karon. Saboda haka ne, har suka samu suka nufi gida tare dasu, inda ya biya su Erkan kuɗi, zasu rako su har ƙasar ta Nigeria. Ko dan gudun yin gaddamar su. Suna zuwa gidan Nigeria kuma. Manyan motocin masarauta ne, cike da fadawa suka isa tarar su. Sun sha ɗinbin mamaki. Me kuma ya kawo masarauta ciki? Ai tuni Hajiya Laila ta sake tsurewa, ko ba komai tasan ƙarfi da ikon masarauta. Tuni ta sallama, ta tabbatar da cewa kashin su ma ya gama bushe wa. Amman tunda take bata taɓa ganin shegen yaro mai tauri kai, haɗi da fasahar Al'ameen ba. Kai shi kanshi ma ta daɗe tana ma Hajiya Kubra baƙin cikin kasancewar shi ɗan ta. Taso ina ma ace Al'ameen ɗin yaron ta ne. Da babu abunda zai hana ta sake buɗawa, haɗi da fantamawa. Ko da suka isa masarauta. Wata tarbar suka samu ta daban, kuma ta musamman. Sun sha matuƙar wahala. Amman sai mai Martaba yace masu, su koma gida, zai nemesu su duka. Saboda haka suna hutawa suka ci abinci, haɗi da cenza kaya suka ɗauko hanyar gida Abuja. Babu wanda yasan da zuwan su. Kawai sai dai dirin motar su akaji. Lokacin ina cikin ɗaki na kwance, bansan me ke man daɗi ba. Na kasa faɗa ma Umma ta, kunya ma nake ji. Gashi Afnan ce kawai da Nihal nake gani wani lokaci, tunda su Aunty Feena sun koma, wannan karon ba'a koma da Afnan ba, kasancewar zata fara service nata a nan Nigeria. Sai kuma Maree, wanda wani lokaci idan muka haɗu ko a hanya ne, sai tayi kaman ta bangaje ni, tana tafiya tana wani taunan chewing gum, haɗi da bubbuɗawa. Saidai in kauce in bata hanya, ni dariya ma take bani, har yanzu kenan son Ya Ameen ɗin take yi? Ikon Allah ni Suhan, ina ganin abu iri-iri. Gashi ni kuma sam bana son hayaniya, kuma ni yanzu ma yanda Allah ya ɗaukaka daraja ta, me ya kaini ga hayaniya da wani? Me na nema na rasa? Wani abun ma ai sai nasan asalin tarihin mahaifi na sannan. Kaman ance in tashi in leƙa ta window. Fuskarshi kawai na fara tozali da ita. Ya fito daga gidan gaba, yana jingine da motar, fuskar nan tashi wasai da ita, ga wata murje wa da fatar tashi ta sake yi. Hasken shi ya daɗa bayyana. Ɗan mitsitsin bakin nashi kaman an ɗisa mashi, leɓen shi na ƙasa na cikin bakin nashi, yana ɗan cizawa a hankali a hankali. A sannu yake bin ilahirin gidan da kallo, kaman wani baƙo. Ta inda zata ɓullo kawai yake jira. Yayin da Bilal yake ta cen baya, yana mai fiddo masu luggegs nasu a bayan seat. Hijabin sallah ta dake rataye a rag kawai na zara. Plat shoes kawai na soka a ƙafar tawa, ina mai nufar ƙofa. Tun daga nesa ya hango ta, cikin salon tafiyar ta mai jan hankali. Kaman tana rausaya, yanda kasan bishiyar dalbejiya cikin damuna. Tun daga nesa nake sakar mashi murmushi, da kallon nayi missing naka. Yayin da shi kuma ya shiga wara hannuwa, wai in tafi gareshi. Sam hankalin shi baya kan kowa sai ni, ni kaɗai yake iya hangowa. Duk da fuskar tawa ba kwalliya, Amman nayi matuƙar yi mashi kyau. Nima inda yake kawai nake dosa, saidai me, kafin in ƙarasa inda yake ɗin, sai hango Hajiya Kubra nayi ta nufi inda yake cikin wani irin farin ciki da annashuwa, domin labari ya iske su cewa, ya samo Hajiya Laila, da Alhaji Yaro. Rungume yaron nata tayi gaban ɗunbin jama'r dake wurin. Ba wannan ne karon ta na farko ga yin hakan ba. Saidai wannan ne yazo mashi wani iri a banbaraƙawai. Dan dole ya maida hannun nashi, shima yana mai rungumo ta kaɗan. Dalilin da ya sanya ni cin birki kenan, ba tare da na shirya ba. Har yanzu idanun shi kyar saman fuska ta. Da ido yake man alamun in ƙara so. Yayin da na shiga jan ƙafar tawa ina nufar inda yake. Saidai kuma wani abu da ya sake ba kowa mamaki, shine ganin hajiya Kubran ta sake jan hannun yaron nata sun nufi sashen nata. Da kallo kowa ya shiga binsu, har Umma ta da take tsaye bakin sashen nata, jin hayaniyar ƴan aiki, kowa ya fito yana masu sannu da zuwa. Ji nayi ƙafafu na sun gaza ɗauka ta. me zan gani haka? Wane irin abu ne hakan? Ita kuwa Maree dake tsaye gefe, wata irin dariya ce ta suɓuce mata, har tana ƙyaƙyatawa. Abun ya matuƙar yi mata daɗi, wannan game ɗin da aka bugata matuƙar burge ta ta. Somin taɓi ma kenan. Ba'a fara wasan ba. Yanzu ne za'a fara.... Ni kuma sai jin dariyar nayi har cikin tsakiyar kaina. To me hajiya kubra ke nufi? Me Maree ɗin ma take nufi? Jiki a sanyaye matuƙar sanyaye, na sake jan tsumman ƙafafu na ina mai juyawa zuwa sashen nawa. Tuni wani irin kuka mai cin rai ya taso mani.... _Oum-Deedat ce_ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~81~* Daf da zasu idasa taka ƴar matattakalar da zata sada su da cikin gidan ne yaja ya toge. A hankali Mom ɗin tashi ta juyo tana mai binshi da idanu, shima idanun nashi ƙyam cikin nata, sai yanzu ne ranshi ke raya mashi menene hakan kenan? Juyawa yayi a sukwane, yana mai nufar sashen nashi, inda yake iya hango Suhan ɗin ta ƙarasa shige wa da gudu. Ta bayan ta ya rungomo ta. Tana tsaye cikin kitchen, jikin cabinet ta juya ma ƙofa baya. Bata san lokacin da ta sauke wata bayyanannar ajiyar zuciya ba, lokaci Guda kuma tana ƙoƙarin goge ruwan hawayen da suka ziraro mata. Bata so ya gani kada ya kawo ma ranshi wani abu, Amman har ga Allah yanda mom ɗin tayi, sai ya sanya ta ƙara tsorata da al'amarin mom ɗin. Ta bisa kafaɗar ta ya saƙalo kanshi, yana mai shaƙo daɗaɗɗen ƙamshin nata mai idasa rikita mashi ƙwalwa. Sun Kai kusan minti biyu a hakan, idanun su a lumshe. Har yanzu tana matse cikin jikin nashi, hannayen nashi kuma suna zagaye bisa ɗan shafaffen cikinta, wata irin kewar juna suke ji tana taso masu, daga cen ƙasan zukatan nasu. A hankali ya juyo da ita sasai zuwa cikin ƙirjin shi, yana mai sanya hannu ya kwantar da kan ta saman faffaɗan ƙirjin nashi,har numfashin su na gauraya. Lamo tayi, tana mai jiyo sautin bugawar zuciyar tashi da sauri da sauri. Jin motsi a falo shi ya fargar dasu daga duniyar soyayyar da suka lula. Ɗan ja baya tayi kaɗan, tana mai sake mashi kyakkyawan murmushi. Lakato mata hanci yayi, yana mai murmusawa shima. Sai kuma ya gyara tsayuwar shi, har yanzu hannayenta cikin nashi. "I missed you Sweet Janam" ya furta murya cen ƙasa ƙasa, cikin wani irin shauƙi. "I missed u too Yayana" ita ma ta furta cike da ɗan zaulaya haka. Sannan ta zame hannayen nata daga cikin nashi, tana mai matsawa jikin fridge ta fiddo gorar ruwa da cup. Tana tsiyaya mashi yana amsa, saida ya ƙwalƙwale ne, sannan ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yana mai sake jawo ta zuwa jikin nashi, bayan ya ajiye cup ɗin bisa cabinet. Ƙoƙarin raba jikin ta da nashi take yi, jin yanda yake jagula ta, gami da sarrafa ta son ranshi. Ta sani sunyi kewar juna, amman sai zuciyar ta ke bata akwai wani a falon nasu. Shi kuma gogan da Sam ya manta ma da Bilal suke tare, har saida ta raɗa mashi a kunne "Ya Bilal fa?" sannan ne ya sake ta, yana maida numfashi, gami da gyara zaman necktail dake wuyan nashi. Hannun ta ya kama zuwa falon nasu. Su duka sororai sukayi, duk kunya kuma sai ta lulluɓe su, ganin Bilal ɗin zaune bisa sofa, sai latsa waya yake yi, yana murmushi. A kunyace na juya zuwa cikin kitchen ɗin. Kenan duk abunda muke yi yana jinmu, wata ƙila ma yana kallon mu. Saboda kitchen ɗin da falon farin glass ne kawai akayi amfani dashi wajen raba tsakani, saidai kuma golden cotton ɗin dake ta ciki, wanda idan aka zuge shi, tsaf za'a iya hangen tsarin kitchen ɗin. Ruwa na ɗauko, haɗi da lemo, sai snacks wanda bama rabuwa dashi kullum a fridge, microwaving nashi nayi masu, sannan na haɗa da kayan marmari, ina mai nufar falon. Ɗan tattaunawa suke a hankali a hankali. Ganin fitowa ta ne, ya sanya su yin shiru, tare da cenza akalar firar. "ƙanwa ta duk kin bi kin zauta man aboki, gashi har sambatun ki yake in yana bacci" Bilal ɗin ya faɗa, fuskar shi cike da murmushi, daidai lokacin da nake ajiye masu plates ɗin bisa stool. Nima faɗaɗa murmushi na nayi, tare da cewa "Ayya Yayana, nima ai har ƴar rashin lafiya nayi da baya nan" cike da jin kunya. Hannu ya sanya, tare da jawo ni zuwa jikin nashi sosai. Ban musa mashi ba na zauna gefen shi nima sosai. Duk Kunyar Bilal ta cika ni. Sai naga su dukan su basu wani damu da hakan ba, to an saba da ɗabi'ar turawa, su a garesu hakan wayewa ce sosai. "Baby naga kin ƙara wani irin haske da fresh! Uhm, faɗa man Sirrin" Ya Ameen ɗin ya faɗa a hankali, fuskar shi daidai kunne na. Ɗan zabura nayi, ina mai ɓoye fuska ta cikin jikin nashi. Shi dai Bilal sai dariya kawai yake yi, yanda yaga Al'ameen na cin soyayya, bai taɓa tunani ba, sai yake ganin kaman ba shi bane, kaman abokin nashi ba zai iya haka ba. Sun ɗan jima anan, har saida na sama masu abu mai sauƙi na daga abinci suka ci. Sannan Bilal yabar gidan. Cikin kwana biyun da ya share a gida, babu inda yake zuwa, daga masallaci sai sashen Mom da Umma. Komai a gida yake kammala abun shi. Da daddare na kan bi shi sashen Mom ɗinshi mu gaisa, gami da ƴar fira. Sai nake ganin kaman Mom ɗin na bina da wani irin kallo. Har yanzu dai ban saki jiki da ita ba sosai, idan muka je tare da Ya Ameen sashen, sai ta dinga janye shi da fira, dan ma Allah yasa Afnan na nan, wani lokaci kuma Nihal kan ɗan tsoma baki. Duk da shima sai na kula kaman akwai abunda yake tsakanin su, baya sakin jiki da ita kaman da. Amman banso hakan ba, sai nake ganin kaman nice na shiga tsakani, sai nake ganin kaman laifi na ne. Amman har yanzu na kasa yi ma Ya Ameen maganar. Har yanzu tsakani na da Umma ba wani sakin jiki sosai, bata so ma nake cika shiga sashen nata. Nima sai ban takura ɗin ba, nasan bata so wani abu ya faru ne, a ce da saka hannun ta ciki. Irin kulawar da Ya Ameen ke bani har ta wuce misali. Ya zuwa yanzu har makaranta munje an kammala komai, har na fara shiga aji. Dayake nuna shekarar ƙarshe ne, sai naga abun kaman wasa, gashi har mun fara shirye shiryen fita. ******* Zaune yake falo bisa sofa, gaban shi laptop ce tashi, sai kuma gefen shi ɗan dambun kaji ne cikin bowl fari, tare da ɗan cokali. Sai gorar ruwa da cup da suke gefen nashi. A hankali a hankali ya kan ɗan ɗago gami da ɗibar dambun ya kai bakin shi. Dambun ya mashi matuƙar daɗi, duk lokacin da bana nan, ina makaranta, dambun ne yake ɗebe mashi kewa, hakan ce ta sanya, bana yarda ya katse mun. Wani lokaci har Bilal ya kan zo yayi guzuri. Dayake Ummin shi ta kusa dawowa. Murɗa ƙofar falon aka yi tare da shigowa. Jin hakan ne ya sanya ni ajiye jera mana kaya cikin wardrooop tamu da nake yi, nayo falon domin ganin ko wanene. Tun dai da ya ɗago sau ɗaya ya kalle ta, sai ya maida kanshi ƙasa, ya zuwa aikin da yake yi mai muhimmanci. Wanda yake saka ran kamfanonin nashi zasu koma bakin aikin su cikin satin. Hakan ne ya sanya abubuwa yi mashi yawa, kusan zan iya cewa tare da Bilal suke yi. To Amman yau kasancewar Ummin Bilal ɗin zata dawo, sai kawai ya bashi hutu, tare da yi mashi tsiyar cewa wai yaje ya kula da sauran abubuwa. Dayake ana gyara gidan ne, tare da cenza fenti da sauran kayan dake cikin gidan. Jiki a sanyaye ta ƙarasa cikin falon ta zauna ɗan nesa kaɗan da Yayan nata. Fuska ta a sake kaman kullum, saidai babu alamun wasa a cikin ta, na ƙara so ina mai cewa "A'ah Nihal ce?". Ɗan gyaɗa kai tayi a hankali tana mai cewa "Eah nice Aunty" Ɗan ɗagowa ya sake yi yana mai kallon ta haka, sai kuma ya cigaba da abun da yake yi. "To sannu da zuwa, ya gida?" na tambaye ta, ina daga tsaye bayan kujerar Ya Ameen ɗin. "Lafiya lau" ta furta, har yanzu jikin ta a mace yake, zan iya karanto irin halin damuwar da ta shiga. Domin kuwa yanzu Nihal ta zama abun tausayi. "Yaya wurin ka nazo" ta furta a hankali, tana mai maida kallon ta bisa kan Ya Ameen ɗin. Da hannu yayi mata alama da ta cigaba yana jin ta. Ganin hakan ni kuma sai na juya zuwa bedroom ɗin, domin ƙara sa aikin da na fara. Saidai abunda kunne na yaji ta faɗa ne, ya sanya ni, ina shigewa ɗakin, na ɗan turo ƙofar a hankali. Saidai bana iya hangen ta, saidai Ya Ameen shima ya ɗan juya baya haka kaɗan, gefen fuskar shi kawai nake iya gani. "Yaya akan maganar Baby ne.. " sau kuma ta kasa idasa faɗar abunda tayi niyya. "Uhum ina jinki" ya faɗa shima, yana mai ɗan jawo wata ƴar joter da take ajiye gefen shi ya fara joting. Ɗan shiru ne ya biyo baya. Sai kuma cen tayi ƙarfin halin cewa. "Yaya ina son komawa gida na ne, Amman akwai matsala wallahi, dan Allah ka taimaka man." Ajiye abunda yake yi yayi gefe, yana mai ɗagowa sosai ya shiga kallon Nihal ɗin. Fuskar shi ɗaure tam, babu alamun wasa "Uhm ina jinki dai, matsala kaman ta me kenan?" Sauke kai tayi zuwa ƙasa, idanun Ya Ameen ɗin sun mata nauyi, dama tun cen, tun da daɗewa su kansu sunsan Ya Ameen ba irin wanda ake kawo ma wargi bane, sam baya ɗaukar wasa ko raini. "Eh Yaya! Naje na samu Mom da maganar, ta nuna mani cewa in rabu da batun komawa gidan Baby, tana jira ne ya kawo man takadda ta, gashi kuma Dad ko kallo na baya yi, bansan laifin da nayi mashi ba.." "Ya isa hakanan Nihal! Tunda ga abunda Mom tace, yanzu ni me kike so inyi maki? Duk abunda zan iya yi na riga nayi, sai Allah yasa ke ba mai jin magana bace, Mom ita ce duk abunda ta faɗa shine daidai, ita ke ɗaure maku gindin yin duk abunda kuka ga dama, to ba shikenan ba, sai kije kibi abunda tace maki ai, mahaifiyar ki ce, ta isa ta sanya ki kiyi, and tasan abunda yake daidai dake ai" Ya katse mata maganar tata a zafafe, yana mai maida kanshi bisa aikin shi. "Am really sorry Yaya, wallahi na gane nayi kuskure, Shiyasa ma na samu Aunty Suhan..." "What? Kika same ta akan me? Me zata iya yi maki? Look Nihal, dont deare involve my wife a cikin lamarin ki, babu abunda zata iya yi, bana son another problem kuma" Ya sake faɗa cike da faɗa, har yana rufe laptop ɗin tashi ba tare da ya sani ba. A tsorace Nihal ɗin ta shiga kaɗa mashi hannu, "Nooo yaya, wallahi i wosn't involve her, taimako kawai na nema wajen ta, Baby yace zai maida ni, Amman sai na koyi ayyukan gida da Cooking, shine kwanaki na same ta akan ta taimaka ta koya man..." sai kuma tayi shiru. Bayan shi ya maida jikin sofar, yana mai karewa, tare da jingina sosai, lokaci guda kuma ya ɗan shiga cusa hannayen shi cikin gashin kanshi mai tsananin baƙi da salƙi. "Nihal!" ya kira ta cikin wata irin murya, wadda har ni da nake tsaye bayan ƙofa sai da na razana. "Matsalar ki matsalar ki ce, bata shafi Matata ba, this time around ba zan iya ɗaukar duk wani abu da zai shafi Matata ba, she is my wife now, not your servant, enough is enough" Ya faɗa cikin murya mai amsa amo, lokaci guda yana mai miƙewa ya zari wayar shi dake ajiye gefe. Da sauri Nihal ɗin ta miƙe, tana mai faɗa wa jikin shi, sai kuma ta saki tsumammen kuka. "Yaya please dan Allah! Nasan a baya na aikata ba daidai ba, nasan ban saurare ka ba, banji maganar ka ba, Amman wallahi ba zan taɓa maimaita kuskure na ba, dan Allah Yaya ka saurare ni" Yana tsaye, shi bai wuce ba, shi bai zauna ba, har yanzu kuma tana maƙale a jikin nashi tana sakin kuka sosai. Shi ɗin mutum ne mai tausayi, mai yawan imani, kukan mace karya mashi guiwa yake yi, baya son yaga mace na kuka, saboda sai yake ganin kaman gazawar namiji ne ke sabbaba mace kuka. Shi kuma baya son gazawa, baya son duk abunda zai sa yaji kaman ya gaza. A hankali ya kama ta, tare da zaunar da ita a gefen shi. Saidai har yanzu fuskar nan tashi tam take. "Tell me Nihal me Suhan ɗin zata yi maki? Kuma ya kukayi da ita" Cikin kuka ta shiga zayyane ma Ya Ameen yanda mukayi da ita. Ni dai har yanzu ina tsaye ta cikin ɗaki ina hangen su. Ɗan tsagaita kukan tayi, tana mai cewa "Please Yaya, ka roƙar mani ita, kuɗin da ta sanya mani sunyi yawa, wallahi bana da such amount a yanzu, koda zan saida mota ta ne, ba zasu kai ba kuɗi, please ka taimaka ka sanya baki tayi mani discount" Ɗan gyara zaman shi yayi, har yanzu idanun shi na kanta. Shi kanshi yana Nihal ɗin ta cenza. Yarinyar da ada idanun ta suke tsai tsaye, ga rashin kunya, ga izza, da jin ita ɗin wata ce? sai gata yau a gaban shi durƙushe tana mai neman taimakn Suhan? Ikon Allah kenan "Is ok, ya isa hakanan, yanzu nawa ke gareki a hannu?" ya furta shima a hankali, yana mai kamo mata dukkanin hannuwn nata. Ɗan uwa kenan mai daɗi. "Five Million" ta furta a hankali. Girgiza kai ya shiga yi. "Noo Nihal, mai buƙatar ten Million ba zaka bashi five ya karɓa ba, kuma kinga kasuwanci ne, and haƙƙin ta ne, bana tunanin idan kuma zata yarda, domin ko da kuɗi ne, ta cencenci fiye da hakan, domin ta bauta maku a lokacin da baku san amfanin hakan ba, lokacin da kuka kulle idanun ku ga sanin darajar ɗan adam, Abunda tun tuni nake so ku gane kenan, ko kare ma yana da rana, balle ɗan adam Kaman Suhan. Gyaɗa kanta ta shiga yi, wasu hawayen na ƙara zirarowa "Yaya i swear su kaɗai gareni, suma sai na cikasa da kuɗin gold ɗina ne zasu kai hakan ma" ta faɗa a hankali. Kalon ta ya shiga yi, iyakar gaskiyar ta take faɗa, sai kuma ya ɗan saki murmushi "Go and ask Mom, nasan zata baki, duk abunda kuke nema ai tana yi maku" ya furta cikin wata irin magana. Irin na ai ita ce gatan naku da kuke gani ko? "Noo Yaya, ita na fara tambaya, sai ta hauni da faɗan wai banga halin da take ciki ba.? ko naira ba zata iya ba ni ba, Shiyasa na same ka akan batun." "Owh sai yanzu ne nake da rana? Ko sai yanzu ita Suhan ɗin take da rana a gare ku? Dont tell me nonsence Nihal. Kinga zaki ɓata man lokaci please, and ina so ki sani, zuri'r gidana nan kaf, bamu gaji siyar da abu ba, saidai mu bayar, saboda haka ko da wasa, kar in sake inji kin fita waje da niyyar siyar da wani abu" Kuka ta sake fashewa dashi "please yaya ka taimake ni in koma gida na, na gaji da zama hakanan, Baby fa kwanaki har aure yace zai ƙara, please yaya borrow me some, if you are willing to healp please Yaya" ta ƙarshe tana mai sake sakar wani kukan a hankali. Ɗan jinjina kai yayi. Sai kuma ya miƙe, yana mai cewa " OK je ki kawo abunda kike dashi, ni zan cika maki, Amman fa ki sani bashi ne. Sannan kuma da sharaɗi. Sharaɗin kuma shine... Har abada ba zan kuma sake jin wata matsala daga gareki ba, zaki maida hankali ki koya, sannan ba zaki dinga biye ma Mom akan aikata son zuciyar ta ba" (Ya faɗi haka ne saboda kada taje ta aikata wnai abun kuma daban, domin samo kuɗin, tunda ya snai d a gaske bata dasu ɗin) Cikin murna itama ta miƙe, sai kuma ta maƙalƙale shi tana murna. "Na yarda Yaya, i accepted" tana faɗa, tana ɗaga hannu sama, alamun ta yarda kashi ɗari bisa ɗari. Baya yaja, yana mai soka duka hannuwan shi cikin aljihun wandon shi. Murmushi yake ɗan yi. Ya gama da matsalar Nihal, an wuce wajen kuma, dama Aunt Feena baya da matsala da ita, haka ma Afnan da Abie, yanzu saura Saudat kawai da Mom ta rage mashi.. Da gudu ta fice tana tsallen murna kaman wata baby, to dama sakatattun yara ai haka suke, akwai sakarci sosai a rayuwar tasu. Waya ya jawo, yana mai kiran waya, bansan wa ya kira ba, sai ji nayi yana cewa ya kawo mashi Million biyar yanzun nan. A hankali na saki ƙofar, ina mai dosar gado na na faɗa, bansan dalilin kuka na ba, Amman nafi yarda da cewa wannan shi ake kira da kukan murna. Ya Ameen miji ne, na kuma tabbata a duk inda na samu kaina a yanzu, ba zai taɓa bari in wulaƙanta ba, zai tsaya man, zai jiɓinci al'amari na. Ko a haka aka tsaya Naji matuƙar daɗi. Ni kuwa dame zan saƙa ma Ya Ameen? Wanda nake cikin nawuyancin hali, ya tsamo ni, ya aure ni, ya mallaka man komai nashi, soyayyar shi, yardar shi da amincewar shi, kai har ma da zuciyar shi baki ɗaya. Bai shigo ɗakin ba, ya koma waje yana mai jiran wanda ya ba saƙo. Bansan yanda suke ciki ba. Nidai tashi nayi, ina mai goge dukkanin hawaye na. Ba kuka ya kamata inyi ba, murna da gode ma Allah shi ya kamata inyi, wata irin wutar ƙaunar Ya Ameen ɗin ce ke sake malala a cikin zuciya ta. Lallai Ya Ameen jan namiji ne da kowacce mace ke fata da burin mallaka, a matsayin abokin rayuwar ta, kuma uban ƴaƴan ta. A hankali na sanya hannu na, ina mai shafo ciki na, na kasa bayyana mashi ina ɗauke da cikin shi na ƴan satittika. Bansan wace irin murna zaiyi ba, amman kuma ni kaina na tabbatar da cewa a yanzu dai shine kawai sauran burin Ya Ameen ɗin da ya rage. Ko ba komai yau yanda ya faranta mani, ba tare da ya sani ba, naci alwashn sanar mashi da cewa ina ɗauke da cikin shi a jiki na, na tsawon sati shida ko ma fi. ************** Na faɗa maki ki fita hanyar yarinyar nan ko? Ke baki ga abunda ni na gani bane da idanu na. Ba ƙananan mutane bane wallahi, kuma kinsan Alhaji Ƙarami ba zai taɓa lamuntar taɓa mashi mata ba, saboda haka ki bari mubi a sannu, ta yanda ba za'a taɓa gane muna da hannu ciki ba... Da sauri Maree ɗin ta ka kai kallon ta kan Uwar ta ta. "Lallai ma Innarmu, wallahi da arziƙi ko da bala'i sai na ƙwato miji na. Irin asirin da tayi mashi ta ƙwace man shi, wallahi sai nayi wanda ya fishi, ko da kissa, ko da kisisina, ke ko da hakan zaiyi sanadiyyar wullawarta barzahu sai na ƙwato abu na. Abu ɗaya ne ya sanya ban zuba mata guba ba a abinci kwanaki, ina tsoron shima Al'ameen ɗin yaci in rasa shi ne. Amman ko yanzu wallahi ban ƙyale ta ba, sai na ɗau fansa, wallahi ko kashe ta ne.... " Bugun da aka kai ma bakin nata, shine dalilin ta na jan bakin nata ta tsuke lokaci guda. " Baki da hankali ne? Ke wace irin shegiyar yarinya ce ne wai? Wallahi nayi asarar haihuwar ki munafuka kawai, in banda sakarci, tayaya zaki zo kina faɗar wannan maganar anan? Idan wani ya jiki fa? Tunda kika ga na sare, ai kema sai ki haƙura, yanzu fa gida a hannun su yake, Alhaji Babba a hannun uwar ta, Alhaji Ƙarami a hannun ta.. Mariya ki rufa ma kanki asiri. Ki bari son shi ya kashe ki, kada kibja mana wani bala'in wallahi, kin dai sani yanda yake son yarinyar nan mai kama da aljannu, ko uwar shi bai haɗa ta da ita ba. Ki ƙyale su, kina zaman zaman ki zaki ji ance ya sake ta, ya kore ta a cikin gidan, nima ai ban zuba masu ido ba, akwai wani aiki da na ba Kawu na ƙauye ayi mani, da an gama ba ma sai kin ce ba, zaki ga abunda zai faru da ita. Ita dai Maryama mun ƙyale ta. Ba ta ita muke ba yanzu, Alhaji ƙaramin nake so yazo hannun mu, domin shine kan gidan a yanzu.. " Cewar Mama talatun, wanda take magana tana ɗan waige waige, gudun ace wani ya jisu. "Kutumar Ubaaa, ni kika buga haka Innarmu?" cewar Maree ɗin, tana mai hayayyaƙowa kaman zata rama. Dariyar shaiɗan ci Mama talatun tayi. " Ke shashasha ce, ni ba bugun ki nayi ba, bakin ki na buga, saboda baya da linzami, har yanzu baki biyo hali na ba, ai ta ƙarƙashin ƙasa ake komai, ke dai ki zuba mani ido, Amman Alhaji Ƙarami gaki cen a ɗakin shi, kinji na gaya maki" Sai yanzu ne Mareen ta saki dariya. Lokaci guda kuma suna masu taɓawa kaman wasu ƙawaye. Turo ƙofar da akayi gami da sallama, shi ya sanya suka ja bakin su suka ɗinke. Mama Uwani ce, take shaida ma Maree tazo tayo cefane inji Hajiya Babba. Ba musu ta miƙe, tana mai gyara kwalliyar fuskar ta, abun dariya sosai. Sannan ta yafa ɗan fingilin gyale, tana tafiya tana gantsaro gaba. A bakin gare ta haɗu dashi, jingine yake da mota, hannun shi wata ƴar jikka ce haka ta kwali mai kyau, shi da wani ne suna magana. "Ina yininku?" ta furta cikin shaƙe murya, sai wani karairaya take yi, dan ma babu ƙugun. Bai ko kalle ta ba, balle ta sanya ran zai amsa, sai wanda suke tare ne ya amsa mata, yana mai cewa "Oga ana gaishe ka" "Lafiya" kawai ya iya furta wa, yana mai ɗauke kanshi, ya zuwa buɗe motar ya ɗauko wani abu. Ƙafafu a sanyaye taka ta wuce, tana ji su Iro suna yi mata dariya da suke zaune bakin gate. Shi kanshi iron haushin yanda take nuna shige ma Alhaji ƙaramin yake ji. To koma dai kishi ne hakan? Oho! Gashi shi kuma ko kula shi bata yi. Yana nan dai yana sauraren Al'ameen ɗin, akan maganar Maree ɗin. Ƙutawa tayi a cikin zuciyar ta. Za kayi magana ne, sai ma an ganni a gaban motar taka, inji ta ƙaryar nuna ɗagin kai. Ko wa ma zai ɗaga ma kai? Shi da yake auren ƴar aikin gidan, wadda ko ni na fita gata, dan dai kawai tana da ɗan haske, wata ƙila ma mai ne take shafawa, Amman yana wani wulaƙanta mutum. Daga kai har ita zaku sani ne. A haka ta wuce su har tayi masu nisa, daidai lokacin da ya sallama mutumen, yana mai binta da kallo, haɗi da sakin wani guntun tsoki. Yarinyar Sam bata burge shi, zubin ƴan duniya gareta, gashi tana tafiya tana wani girgiza, haɗi da ban ƙaro ƙirji wai ita mace, wanda ko shi da yake namiji ya fita fasali mai kyau. ******* "Ammi na ji ki shiru ne da maganar tamu, Ammi ki taimaka man, nima ina son in ganni cikin iyali na Ammi, yarinyar nan tana sona fa, Ammi kada kiyi saken da zan sake rasa ta ita ma" Sir Saleem ɗin ya furta cikin marairaicewa, Shiyasa ma wannan karon sai bai dawo ba, yayi zaman shi a cen zariyan, saboda ko ya dawo gidan baya jinshi da daɗi, ga kuma ƴan uwan Ma'u dake karakaina gidan, kuma cikin salon cin mutumci. Wanda ya zuwa yanzu so suke yaje yayo bikon Ma'un kuma. Yaƙi zuwa ne, domin yana so ya nuna masu kuskuren su, sannan yana so Ma'un ta sake ƙara hankali, duk da har yanzu zuciyar shi na raya mashi cewa Ma'aun ba wai tayi sanyi bane. "Kayi haƙuri Son, insha Allahu komai yana tafiya daidai. Mai martaba ne da kanshi yace abar batun a hannun shi, daga kai har Afnan duk ƴaƴan shi ne, dan haka duk yanda za'ayi insha Allahu babu matsala, Shiyasa Kaga mun saurara tukunna, amman muna sane da kai Son" Ajiyar zuciya ya sauke, sai yanzu yaji sauƙi, ai tunda dai magana ta kai ƙoli, yasan ya samu Afnan ya gama. Jiki na ɓari ya katse kiran Ammin bayan sunyi sallama, yana mai kiran Afnan ɗin. ********* Ƙarar blander dake aiki ce na ji ta tsaya lokaci guda. Da sauri na waiwaya, har ina ɗan razana kaɗan. Sai kuma na saki murmushi, ganin gogan nawa tsaye, yana juye man markaɗaɗɗun kayan miyan cikin man da nake soyawa na miyar. Ɗan jingina nayi da cabinet, ina mai harɗe hannaye na, gami da langaɓar da kai cikin sigar shagwaɓa. "Allah kuwa ni yaya ka bani tsoro wallahi" na faɗa cikin sigar shagwaɓa. Saida ya tabbatar da ya gama juye wa, sannan ya wanke hannun shi jikin sinc, yana mai gogewa da kitchen napkin, sannan ya matso sosai zuwa inda naken, yana mai tallafo fuskar tawa. "Sorry my lolipop, taya ki zanyi fa" ya faɗa yana mai lalubar baki na a hankali. Kauda kai nayi gefe, ina ɗan dukan ƙirjin shi. Hannu ya sanya, yana mai lafar mani kai na bisa faffaɗan ƙirjin nashi. Mun natsu a haka, kowa na amsar saƙon juna. Babu abunda ke yawan saurin saukar mashi da natsuwa, irin jin Suhan ɗin a cikin ƙirjinshi, yana mai shaƙar daɗaɗɗen ƙamshin mayukan gashin nata. Ɗan ƙauri ƙarin da muka jiyo ne, ya sanya mu saurin raba jikin namu. Muna mai kai kallon mu wajen girkin namu. Dashishin farar shinkafar dake cikin stummer ɗinne ruwan ya ƙone, saurin saukewa nayi, yana mai taro man ruwa a famfo na sinc na ƙara zubawa. Shi ya cigaba da taimaka man, hatta da yanke yanken su Cabbage shi yayi mani. Muna girkin hana bani labaru daɗi, wasu har sia na dafe ciki saboda dariya, yayin da ya kan zuba mani ido wani lokaci yana kallo na ina dariya. Har cikin zuciyarshi yake jin daɗi hakan. Ya tabbatar ma kanshi cewa ina jin daɗin zaman nawa tare dashi. Na dafe ciki ina dariya, harda ƙyaƙyatawa ne, sai jin ya kamo mani duka hannuwa yayi. Ƙure ni da idanu yayi, ƙasa daure ma kallon nashi nayi na sadda kaina zuwa ƙasa. Idanun nashi na mani nauyi a kullum. Wani irin kallo yake yi mani, mai cike da tsantsar ƙauna. Ban taɓa tunanin Ya Ameen zai iya sakin jiki dani haka ba, na ɗauka ko da na aure shi, zamuyi zama ne kaman na ubangida da yaron sa, ban ɗauka soyayya ta ta kai har haka ba a cikin zuciyar shi. Katse mani tunanin yayi, yana mai nufar hannayen nawa dake cikin nashi hannuwn zuwa bisa ƙirjin shi, saitin zuciyar shi. *"I Love u Suhan... No words can explain how much u mean to me, please and please i beg u Suhan, for my sake, don ever leave me for any reason, u always means alot to me wife and always keep firgiven me ,please dear"* Ya furta cike da wani irin shauƙi. Ni kaina jiki na ya mace duka. A hankali na kai baki na bisa hannun nashi da ke dunƙule da nawa. Ina mai manna mashi wani irin peck mai sauti. Lokaci guda kuma na wara duka hannuwn nawa, ina mai shige wa cikin jikin shi tsaf. Ba wata wata shima ya maida hannuwan nawa cikin nashi, yana mai sake manne jikin nawa da nashi. A hankali ya shiga saddo da kanshi zuwa gareni, yana mai lalubar laɓɓan nawa. Wannan karon ban hana shi ba, kaman yanda sai lokacin da yaji ya gamasu, sannan ya sake ni, ya na mai maida numfashi, har yanzu idanun shi a lumshe suke. Saida muka kammala komai, sannan ya taya ni muka jera a saman dining, har yanzu komai take man a lallaɓe, cike da wata irin salon soyayya da ke ƙara ruɗa ni. Gani nake kaman ni kaɗai ce nayi Sa'ar miji a duniyar nan, gani nake kaman ni kaɗai ce macen da tayi saura a faɗin duniyar. A falo ta iske mu, zaune yake bisa sofa yana amsa wayar manager ɗinshi. Yayin da ni kuma nake kwance kusa dashi, kaina bisa cinyar tashi, ya zame hular dake bisa kaina, yana mai yamutsa dogon gashin kan nawa. Ni kuma hannu na riƙe da waya ina karanta mana wani littafi *Saif ko Maleek* kiran wayar manager ɗin ta shigo wayar shi. Gefe ta samu ta zauna, hannun ta ɗauke da wata leda. yayin da ni kuma ganin tan bai sanya na tashi ba. Duniya kenan, wai yau Nihal ce a ɗarare a sashe nawa. Wanda ada zanje ɗakin ta in ta sallama Amman sai taga daman amsawa, shima a gadarance, ko magana Zatayi man cikin isa da tsawa, ni kuma jiki na na ɓari, kaman zanyi mata sujjada. Saida ya kammala tsaf, shima akan komawar su aiki ne. Sannan ya juya ga Nihal ɗin, yana mai maida hankalin shi kanta. "Uhm Nihal kin dawo ne?" ya furta ciki ciki, kaman baya son maganar. "Um Yaya" ta furta itama a hankali. A hankali na zame kaina daga bisa cinyar tashi, ina mai miƙewa da niyyar wuce wa, domin dia ban nuna mashi naji maganganun su na ɗazu ba. Hannu ya sanya yana mai kamo nawa hannun cikin nashi, gami da maida ni ya zaunar gefen shi. "Zauna wife, maganar ta shafe ki ai, ko ma bata shafe ki ba, dani dake duk ɗaya ne, sit!" ya faɗa shima idanun shi cikin nawa. Ba musu na koma ma zauna nima, ina mai ɗan sakar mashi murmushi, gami da ɗan yin fari da idanu. Murmushin shima yayi, yana mai lakato man Kumatu. Gyara zaman nashi yayi, yana mai ɗaukar remote ya latse tv ɗin dake aiki, wanda ta kusa lamushe rabin bangon. Hankalin shi ya maido kaina. "Wife maganar ku ne ke da Nihal, akan koya mata abubuwan da zakiyi, na farko ina son sanar dake cewa, Naji daɗi, lallai zuciyar ki mai kyau ce wife, ina alfahari da samun ki a matsayin mata ta. Na biyu kuma ina mai neman alfarma a gareki, muddin kika ga bata maida hankali kan abunda zaki koya mata kada kiji nauyin sanar mani, sannan idan ba zata kwantar da hankalinta ta koya ba, gara tun wuri a barta kawai, sannan ina so ki sani, wannan kuɗi da kika nema naji daɗin hakan, wannan ke nuna mani cewa komai na duniyar nan yana da daraja, abunda su suka kasa fahimta kenan. Saboda haka ga kuɗin zata baki da hannunta" duk yana maganar ne a hankali cikin natsuwa mai tattare da haiba da kwarjini. Ya ƙara she yana mai yi ma Nihal ɗin nuni da gefen stool akan ta haɗo da sauran cikon da zai bata ɗin. Duka ta har haɗa su, sai ga uban tulun kuɗi a gaba na. Wanda hakan har saida ta sanya na kusa ruɗewa, ban taɓa gani ba, ko a mafarki. Saurin saisaita kaina nayi. Ina mai gyaɗa kai a hankali cikin basarwa na shiga cewa "Ba komai Yaya, komai nayi ma Nihal ban faɗi ba, domin ita ɗin kai ne, saboda haka kada ka samu damuwa, insha Allahu zuwa gobe zamu fara class da ita. Cikin lokaci ƙanƙani zan tabbatar da ta iya. Kuma wannan kuɗi da ta bayar, ina so ku sani ba ni ce zan amfani dasu ba. Ko naira bana so, bana da sha'awa a ciki. Dan haka na sadaukar ma da gidan Marayun da muka je dakai kwanaki, Naji kana son tallafa masu, dan haka nima wannan gudunmuwa ta ce zuwa gareka. Allah kuma ya taimaka, ya baka sa'a, sannan ya ci gaba da dafa maka akan dukkanin al'amurran ka ameen" Da sauri Nihal ɗin ta maida kallon ta zuwa gareni, cike da tsantsar mamaki da al'ajabi sosai take kallo na. Ikon Allah, wacece ma Suhan ne wai? Dama haka take? Dama mace mai ɗinbin alkhairi tattare da ita, suka dinga wulaƙanta ta ada cen baya? Saurin tasowa tayi zuwa garenin, tana mai rungume ni kai tsaye ta saki kuka. "Aunty ki yafe man, nayi nadama Yaya ka taya ni bata haƙuri, insha Allahu na ɗauke ta tamkar ƴar uwa ta a yanzu, Yaya Aunty Suhan mace ce ta gari kaman Umman ta, dan Allah Aunty ina mai roƙon ki da ki sake yafe mani a karo na barkatai" Nima rungume ta nayi sosai cikin jiki na. Ina mai goge ƙwallar da ta zubo mani. Ko a mafarki ban taɓa tunanin kaiwa haka ba, ko a mafarki ban taɓa tunanin zama yanda na zama ba a yanzu. Dole na gode ma Allah da wannan baiwa da yayi mani. A hankali na zame ta daga jikin nawa. Ina mai cewa "Ba komai Nihal, ke ɗin kaman ƴar uwa kike a gareni, insha Allahu babu abunda zai gagara inyi maki, ko domin miji na, ko domin uban ƴaƴa na, ko domin wanda ya bani farin ciki fiye da yanda na tsammata" Cike da so da sha'awa yake kallo na. Baima san me zaice mani ba. He's speachless dai a Yanzu. Har dare yayi Ya Ameen na yaba mani, yana mai faɗa man kalamai masu matuƙar daɗi, wanda saboda hakan ne ma naci alwashin sanar mashi da labarin cikin nawa, ko domin yanda naga yana cikin farin ciki da annashuwa. *_Oum-Deedat ce_* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~81~* Daf da zasu idasa taka ƴar matattakalar da zata sada su da cikin gidan ne yaja ya toge. A hankali Mom ɗin tashi ta juyo tana mai binshi da idanu, shima idanun nashi ƙyam cikin nata, sai yanzu ne ranshi ke raya mashi menene hakan kenan? Juyawa yayi a sukwane, yana mai nufar sashen nashi, inda yake iya hango Suhan ɗin ta ƙarasa shige wa da gudu. Ta bayan ta ya rungomo ta. Tana tsaye cikin kitchen, jikin cabinet ta juya ma ƙofa baya. Bata san lokacin da ta sauke wata bayyanannar ajiyar zuciya ba, lokaci Guda kuma tana ƙoƙarin goge ruwan hawayen da suka ziraro mata. Bata so ya gani kada ya kawo ma ranshi wani abu, Amman har ga Allah yanda mom ɗin tayi, sai ya sanya ta ƙara tsorata da al'amarin mom ɗin. Ta bisa kafaɗar ta ya saƙalo kanshi, yana mai shaƙo daɗaɗɗen ƙamshin nata mai idasa rikita mashi ƙwalwa. Sun Kai kusan minti biyu a hakan, idanun su a lumshe. Har yanzu tana matse cikin jikin nashi, hannayen nashi kuma suna zagaye bisa ɗan shafaffen cikinta, wata irin kewar juna suke ji tana taso masu, daga cen ƙasan zukatan nasu. A hankali ya juyo da ita sasai zuwa cikin ƙirjin shi, yana mai sanya hannu ya kwantar da kan ta saman faffaɗan ƙirjin nashi,har numfashin su na gauraya. Lamo tayi, tana mai jiyo sautin bugawar zuciyar tashi da sauri da sauri. Jin motsi a falo shi ya fargar dasu daga duniyar soyayyar da suka lula. Ɗan ja baya tayi kaɗan, tana mai sake mashi kyakkyawan murmushi. Lakato mata hanci yayi, yana mai murmusawa shima. Sai kuma ya gyara tsayuwar shi, har yanzu hannayenta cikin nashi. "I missed you Sweet Janam" ya furta murya cen ƙasa ƙasa, cikin wani irin shauƙi. "I missed u too Yayana" ita ma ta furta cike da ɗan zaulaya haka. Sannan ta zame hannayen nata daga cikin nashi, tana mai matsawa jikin fridge ta fiddo gorar ruwa da cup. Tana tsiyaya mashi yana amsa, saida ya ƙwalƙwale ne, sannan ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yana mai sake jawo ta zuwa jikin nashi, bayan ya ajiye cup ɗin bisa cabinet. Ƙoƙarin raba jikin ta da nashi take yi, jin yanda yake jagula ta, gami da sarrafa ta son ranshi. Ta sani sunyi kewar juna, amman sai zuciyar ta ke bata akwai wani a falon nasu. Shi kuma gogan da Sam ya manta ma da Bilal suke tare, har saida ta raɗa mashi a kunne "Ya Bilal fa?" sannan ne ya sake ta, yana maida numfashi, gami da gyara zaman necktail dake wuyan nashi. Hannun ta ya kama zuwa falon nasu. Su duka sororai sukayi, duk kunya kuma sai ta lulluɓe su, ganin Bilal ɗin zaune bisa sofa, sai latsa waya yake yi, yana murmushi. A kunyace na juya zuwa cikin kitchen ɗin. Kenan duk abunda muke yi yana jinmu, wata ƙila ma yana kallon mu. Saboda kitchen ɗin da falon farin glass ne kawai akayi amfani dashi wajen raba tsakani, saidai kuma golden cotton ɗin dake ta ciki, wanda idan aka zuge shi, tsaf za'a iya hangen tsarin kitchen ɗin. Ruwa na ɗauko, haɗi da lemo, sai snacks wanda bama rabuwa dashi kullum a fridge, microwaving nashi nayi masu, sannan na haɗa da kayan marmari, ina mai nufar falon. Ɗan tattaunawa suke a hankali a hankali. Ganin fitowa ta ne, ya sanya su yin shiru, tare da cenza akalar firar. "ƙanwa ta duk kin bi kin zauta man aboki, gashi har sambatun ki yake in yana bacci" Bilal ɗin ya faɗa, fuskar shi cike da murmushi, daidai lokacin da nake ajiye masu plates ɗin bisa stool. Nima faɗaɗa murmushi na nayi, tare da cewa "Ayya Yayana, nima ai har ƴar rashin lafiya nayi da baya nan" cike da jin kunya. Hannu ya sanya, tare da jawo ni zuwa jikin nashi sosai. Ban musa mashi ba na zauna gefen shi nima sosai. Duk Kunyar Bilal ta cika ni. Sai naga su dukan su basu wani damu da hakan ba, to an saba da ɗabi'ar turawa, su a garesu hakan wayewa ce sosai. "Baby naga kin ƙara wani irin haske da fresh! Uhm, faɗa man Sirrin" Ya Ameen ɗin ya faɗa a hankali, fuskar shi daidai kunne na. Ɗan zabura nayi, ina mai ɓoye fuska ta cikin jikin nashi. Shi dai Bilal sai dariya kawai yake yi, yanda yaga Al'ameen na cin soyayya, bai taɓa tunani ba, sai yake ganin kaman ba shi bane, kaman abokin nashi ba zai iya haka ba. Sun ɗan jima anan, har saida na sama masu abu mai sauƙi na daga abinci suka ci. Sannan Bilal yabar gidan. Cikin kwana biyun da ya share a gida, babu inda yake zuwa, daga masallaci sai sashen Mom da Umma. Komai a gida yake kammala abun shi. Da daddare na kan bi shi sashen Mom ɗinshi mu gaisa, gami da ƴar fira. Sai nake ganin kaman Mom ɗin na bina da wani irin kallo. Har yanzu dai ban saki jiki da ita ba sosai, idan muka je tare da Ya Ameen sashen, sai ta dinga janye shi da fira, dan ma Allah yasa Afnan na nan, wani lokaci kuma Nihal kan ɗan tsoma baki. Duk da shima sai na kula kaman akwai abunda yake tsakanin su, baya sakin jiki da ita kaman da. Amman banso hakan ba, sai nake ganin kaman nice na shiga tsakani, sai nake ganin kaman laifi na ne. Amman har yanzu na kasa yi ma Ya Ameen maganar. Har yanzu tsakani na da Umma ba wani sakin jiki sosai, bata so ma nake cika shiga sashen nata. Nima sai ban takura ɗin ba, nasan bata so wani abu ya faru ne, a ce da saka hannun ta ciki. Irin kulawar da Ya Ameen ke bani har ta wuce misali. Ya zuwa yanzu har makaranta munje an kammala komai, har na fara shiga aji. Dayake nuna shekarar ƙarshe ne, sai naga abun kaman wasa, gashi har mun fara shirye shiryen fita. ******* Zaune yake falo bisa sofa, gaban shi laptop ce tashi, sai kuma gefen shi ɗan dambun kaji ne cikin bowl fari, tare da ɗan cokali. Sai gorar ruwa da cup da suke gefen nashi. A hankali a hankali ya kan ɗan ɗago gami da ɗibar dambun ya kai bakin shi. Dambun ya mashi matuƙar daɗi, duk lokacin da bana nan, ina makaranta, dambun ne yake ɗebe mashi kewa, hakan ce ta sanya, bana yarda ya katse mun. Wani lokaci har Bilal ya kan zo yayi guzuri. Dayake Ummin shi ta kusa dawowa. Murɗa ƙofar falon aka yi tare da shigowa. Jin hakan ne ya sanya ni ajiye jera mana kaya cikin wardrooop tamu da nake yi, nayo falon domin ganin ko wanene. Tun dai da ya ɗago sau ɗaya ya kalle ta, sai ya maida kanshi ƙasa, ya zuwa aikin da yake yi mai muhimmanci. Wanda yake saka ran kamfanonin nashi zasu koma bakin aikin su cikin satin. Hakan ne ya sanya abubuwa yi mashi yawa, kusan zan iya cewa tare da Bilal suke yi. To Amman yau kasancewar Ummin Bilal ɗin zata dawo, sai kawai ya bashi hutu, tare da yi mashi tsiyar cewa wai yaje ya kula da sauran abubuwa. Dayake ana gyara gidan ne, tare da cenza fenti da sauran kayan dake cikin gidan. Jiki a sanyaye ta ƙarasa cikin falon ta zauna ɗan nesa kaɗan da Yayan nata. Fuska ta a sake kaman kullum, saidai babu alamun wasa a cikin ta, na ƙara so ina mai cewa "A'ah Nihal ce?". Ɗan gyaɗa kai tayi a hankali tana mai cewa "Eah nice Aunty" Ɗan ɗagowa ya sake yi yana mai kallon ta haka, sai kuma ya cigaba da abun da yake yi. "To sannu da zuwa, ya gida?" na tambaye ta, ina daga tsaye bayan kujerar Ya Ameen ɗin. "Lafiya lau" ta furta, har yanzu jikin ta a mace yake, zan iya karanto irin halin damuwar da ta shiga. Domin kuwa yanzu Nihal ta zama abun tausayi. "Yaya wurin ka nazo" ta furta a hankali, tana mai maida kallon ta bisa kan Ya Ameen ɗin. Da hannu yayi mata alama da ta cigaba yana jin ta. Ganin hakan ni kuma sai na juya zuwa bedroom ɗin, domin ƙara sa aikin da na fara. Saidai abunda kunne na yaji ta faɗa ne, ya sanya ni, ina shigewa ɗakin, na ɗan turo ƙofar a hankali. Saidai bana iya hangen ta, saidai Ya Ameen shima ya ɗan juya baya haka kaɗan, gefen fuskar shi kawai nake iya gani. "Yaya akan maganar Baby ne.. " sau kuma ta kasa idasa faɗar abunda tayi niyya. "Uhum ina jinki" ya faɗa shima, yana mai ɗan jawo wata ƴar joter da take ajiye gefen shi ya fara joting. Ɗan shiru ne ya biyo baya. Sai kuma cen tayi ƙarfin halin cewa. "Yaya ina son komawa gida na ne, Amman akwai matsala wallahi, dan Allah ka taimaka man." Ajiye abunda yake yi yayi gefe, yana mai ɗagowa sosai ya shiga kallon Nihal ɗin. Fuskar shi ɗaure tam, babu alamun wasa "Uhm ina jinki dai, matsala kaman ta me kenan?" Sauke kai tayi zuwa ƙasa, idanun Ya Ameen ɗin sun mata nauyi, dama tun cen, tun da daɗewa su kansu sunsan Ya Ameen ba irin wanda ake kawo ma wargi bane, sam baya ɗaukar wasa ko raini. "Eh Yaya! Naje na samu Mom da maganar, ta nuna mani cewa in rabu da batun komawa gidan Baby, tana jira ne ya kawo man takadda ta, gashi kuma Dad ko kallo na baya yi, bansan laifin da nayi mashi ba.." "Ya isa hakanan Nihal! Tunda ga abunda Mom tace, yanzu ni me kike so inyi maki? Duk abunda zan iya yi na riga nayi, sai Allah yasa ke ba mai jin magana bace, Mom ita ce duk abunda ta faɗa shine daidai, ita ke ɗaure maku gindin yin duk abunda kuka ga dama, to ba shikenan ba, sai kije kibi abunda tace maki ai, mahaifiyar ki ce, ta isa ta sanya ki kiyi, and tasan abunda yake daidai dake ai" Ya katse mata maganar tata a zafafe, yana mai maida kanshi bisa aikin shi. "Am really sorry Yaya, wallahi na gane nayi kuskure, Shiyasa ma na samu Aunty Suhan..." "What? Kika same ta akan me? Me zata iya yi maki? Look Nihal, dont deare involve my wife a cikin lamarin ki, babu abunda zata iya yi, bana son another problem kuma" Ya sake faɗa cike da faɗa, har yana rufe laptop ɗin tashi ba tare da ya sani ba. A tsorace Nihal ɗin ta shiga kaɗa mashi hannu, "Nooo yaya, wallahi i wosn't involve her, taimako kawai na nema wajen ta, Baby yace zai maida ni, Amman sai na koyi ayyukan gida da Cooking, shine kwanaki na same ta akan ta taimaka ta koya man..." sai kuma tayi shiru. Bayan shi ya maida jikin sofar, yana mai karewa, tare da jingina sosai, lokaci guda kuma ya ɗan shiga cusa hannayen shi cikin gashin kanshi mai tsananin baƙi da salƙi. "Nihal!" ya kira ta cikin wata irin murya, wadda har ni da nake tsaye bayan ƙofa sai da na razana. "Matsalar ki matsalar ki ce, bata shafi Matata ba, this time around ba zan iya ɗaukar duk wani abu da zai shafi Matata ba, she is my wife now, not your servant, enough is enough" Ya faɗa cikin murya mai amsa amo, lokaci guda yana mai miƙewa ya zari wayar shi dake ajiye gefe. Da sauri Nihal ɗin ta miƙe, tana mai faɗa wa jikin shi, sai kuma ta saki tsumammen kuka. "Yaya please dan Allah! Nasan a baya na aikata ba daidai ba, nasan ban saurare ka ba, banji maganar ka ba, Amman wallahi ba zan taɓa maimaita kuskure na ba, dan Allah Yaya ka saurare ni" Yana tsaye, shi bai wuce ba, shi bai zauna ba, har yanzu kuma tana maƙale a jikin nashi tana sakin kuka sosai. Shi ɗin mutum ne mai tausayi, mai yawan imani, kukan mace karya mashi guiwa yake yi, baya son yaga mace na kuka, saboda sai yake ganin kaman gazawar namiji ne ke sabbaba mace kuka. Shi kuma baya son gazawa, baya son duk abunda zai sa yaji kaman ya gaza. A hankali ya kama ta, tare da zaunar da ita a gefen shi. Saidai har yanzu fuskar nan tashi tam take. "Tell me Nihal me Suhan ɗin zata yi maki? Kuma ya kukayi da ita" Cikin kuka ta shiga zayyane ma Ya Ameen yanda mukayi da ita. Ni dai har yanzu ina tsaye ta cikin ɗaki ina hangen su. Ɗan tsagaita kukan tayi, tana mai cewa "Please Yaya, ka roƙar mani ita, kuɗin da ta sanya mani sunyi yawa, wallahi bana da such amount a yanzu, koda zan saida mota ta ne, ba zasu kai ba kuɗi, please ka taimaka ka sanya baki tayi mani discount" Ɗan gyara zaman shi yayi, har yanzu idanun shi na kanta. Shi kanshi yana Nihal ɗin ta cenza. Yarinyar da ada idanun ta suke tsai tsaye, ga rashin kunya, ga izza, da jin ita ɗin wata ce? sai gata yau a gaban shi durƙushe tana mai neman taimakn Suhan? Ikon Allah kenan "Is ok, ya isa hakanan, yanzu nawa ke gareki a hannu?" ya furta shima a hankali, yana mai kamo mata dukkanin hannuwn nata. Ɗan uwa kenan mai daɗi. "Five Million" ta furta a hankali. Girgiza kai ya shiga yi. "Noo Nihal, mai buƙatar ten Million ba zaka bashi five ya karɓa ba, kuma kinga kasuwanci ne, and haƙƙin ta ne, bana tunanin idan kuma zata yarda, domin ko da kuɗi ne, ta cencenci fiye da hakan, domin ta bauta maku a lokacin da baku san amfanin hakan ba, lokacin da kuka kulle idanun ku ga sanin darajar ɗan adam, Abunda tun tuni nake so ku gane kenan, ko kare ma yana da rana, balle ɗan adam Kaman Suhan. Gyaɗa kanta ta shiga yi, wasu hawayen na ƙara zirarowa "Yaya i swear su kaɗai gareni, suma sai na cikasa da kuɗin gold ɗina ne zasu kai hakan ma" ta faɗa a hankali. Kalon ta ya shiga yi, iyakar gaskiyar ta take faɗa, sai kuma ya ɗan saki murmushi "Go and ask Mom, nasan zata baki, duk abunda kuke nema ai tana yi maku" ya furta cikin wata irin magana. Irin na ai ita ce gatan naku da kuke gani ko? "Noo Yaya, ita na fara tambaya, sai ta hauni da faɗan wai banga halin da take ciki ba.? ko naira ba zata iya ba ni ba, Shiyasa na same ka akan batun." "Owh sai yanzu ne nake da rana? Ko sai yanzu ita Suhan ɗin take da rana a gare ku? Dont tell me nonsence Nihal. Kinga zaki ɓata man lokaci please, and ina so ki sani, zuri'r gidana nan kaf, bamu gaji siyar da abu ba, saidai mu bayar, saboda haka ko da wasa, kar in sake inji kin fita waje da niyyar siyar da wani abu" Kuka ta sake fashewa dashi "please yaya ka taimake ni in koma gida na, na gaji da zama hakanan, Baby fa kwanaki har aure yace zai ƙara, please yaya borrow me some, if you are willing to healp please Yaya" ta ƙarshe tana mai sake sakar wani kukan a hankali. Ɗan jinjina kai yayi. Sai kuma ya miƙe, yana mai cewa " OK je ki kawo abunda kike dashi, ni zan cika maki, Amman fa ki sani bashi ne. Sannan kuma da sharaɗi. Sharaɗin kuma shine... Har abada ba zan kuma sake jin wata matsala daga gareki ba, zaki maida hankali ki koya, sannan ba zaki dinga biye ma Mom akan aikata son zuciyar ta ba" (Ya faɗi haka ne saboda kada taje ta aikata wnai abun kuma daban, domin samo kuɗin, tunda ya snai d a gaske bata dasu ɗin) Cikin murna itama ta miƙe, sai kuma ta maƙalƙale shi tana murna. "Na yarda Yaya, i accepted" tana faɗa, tana ɗaga hannu sama, alamun ta yarda kashi ɗari bisa ɗari. Baya yaja, yana mai soka duka hannuwan shi cikin aljihun wandon shi. Murmushi yake ɗan yi. Ya gama da matsalar Nihal, an wuce wajen kuma, dama Aunt Feena baya da matsala da ita, haka ma Afnan da Abie, yanzu saura Saudat kawai da Mom ta rage mashi.. Da gudu ta fice tana tsallen murna kaman wata baby, to dama sakatattun yara ai haka suke, akwai sakarci sosai a rayuwar tasu. Waya ya jawo, yana mai kiran waya, bansan wa ya kira ba, sai ji nayi yana cewa ya kawo mashi Million biyar yanzun nan. A hankali na saki ƙofar, ina mai dosar gado na na faɗa, bansan dalilin kuka na ba, Amman nafi yarda da cewa wannan shi ake kira da kukan murna. Ya Ameen miji ne, na kuma tabbata a duk inda na samu kaina a yanzu, ba zai taɓa bari in wulaƙanta ba, zai tsaya man, zai jiɓinci al'amari na. Ko a haka aka tsaya Naji matuƙar daɗi. Ni kuwa dame zan saƙa ma Ya Ameen? Wanda nake cikin nawuyancin hali, ya tsamo ni, ya aure ni, ya mallaka man komai nashi, soyayyar shi, yardar shi da amincewar shi, kai har ma da zuciyar shi baki ɗaya. Bai shigo ɗakin ba, ya koma waje yana mai jiran wanda ya ba saƙo. Bansan yanda suke ciki ba. Nidai tashi nayi, ina mai goge dukkanin hawaye na. Ba kuka ya kamata inyi ba, murna da gode ma Allah shi ya kamata inyi, wata irin wutar ƙaunar Ya Ameen ɗin ce ke sake malala a cikin zuciya ta. Lallai Ya Ameen jan namiji ne da kowacce mace ke fata da burin mallaka, a matsayin abokin rayuwar ta, kuma uban ƴaƴan ta. A hankali na sanya hannu na, ina mai shafo ciki na, na kasa bayyana mashi ina ɗauke da cikin shi na ƴan satittika. Bansan wace irin murna zaiyi ba, amman kuma ni kaina na tabbatar da cewa a yanzu dai shine kawai sauran burin Ya Ameen ɗin da ya rage. Ko ba komai yau yanda ya faranta mani, ba tare da ya sani ba, naci alwashn sanar mashi da cewa ina ɗauke da cikin shi a jiki na, na tsawon sati shida ko ma fi. ************** Na faɗa maki ki fita hanyar yarinyar nan ko? Ke baki ga abunda ni na gani bane da idanu na. Ba ƙananan mutane bane wallahi, kuma kinsan Alhaji Ƙarami ba zai taɓa lamuntar taɓa mashi mata ba, saboda haka ki bari mubi a sannu, ta yanda ba za'a taɓa gane muna da hannu ciki ba... Da sauri Maree ɗin ta ka kai kallon ta kan Uwar ta ta. "Lallai ma Innarmu, wallahi da arziƙi ko da bala'i sai na ƙwato miji na. Irin asirin da tayi mashi ta ƙwace man shi, wallahi sai nayi wanda ya fishi, ko da kissa, ko da kisisina, ke ko da hakan zaiyi sanadiyyar wullawarta barzahu sai na ƙwato abu na. Abu ɗaya ne ya sanya ban zuba mata guba ba a abinci kwanaki, ina tsoron shima Al'ameen ɗin yaci in rasa shi ne. Amman ko yanzu wallahi ban ƙyale ta ba, sai na ɗau fansa, wallahi ko kashe ta ne.... " Bugun da aka kai ma bakin nata, shine dalilin ta na jan bakin nata ta tsuke lokaci guda. " Baki da hankali ne? Ke wace irin shegiyar yarinya ce ne wai? Wallahi nayi asarar haihuwar ki munafuka kawai, in banda sakarci, tayaya zaki zo kina faɗar wannan maganar anan? Idan wani ya jiki fa? Tunda kika ga na sare, ai kema sai ki haƙura, yanzu fa gida a hannun su yake, Alhaji Babba a hannun uwar ta, Alhaji Ƙarami a hannun ta.. Mariya ki rufa ma kanki asiri. Ki bari son shi ya kashe ki, kada kibja mana wani bala'in wallahi, kin dai sani yanda yake son yarinyar nan mai kama da aljannu, ko uwar shi bai haɗa ta da ita ba. Ki ƙyale su, kina zaman zaman ki zaki ji ance ya sake ta, ya kore ta a cikin gidan, nima ai ban zuba masu ido ba, akwai wani aiki da na ba Kawu na ƙauye ayi mani, da an gama ba ma sai kin ce ba, zaki ga abunda zai faru da ita. Ita dai Maryama mun ƙyale ta. Ba ta ita muke ba yanzu, Alhaji ƙaramin nake so yazo hannun mu, domin shine kan gidan a yanzu.. " Cewar Mama talatun, wanda take magana tana ɗan waige waige, gudun ace wani ya jisu. "Kutumar Ubaaa, ni kika buga haka Innarmu?" cewar Maree ɗin, tana mai hayayyaƙowa kaman zata rama. Dariyar shaiɗan ci Mama talatun tayi. " Ke shashasha ce, ni ba bugun ki nayi ba, bakin ki na buga, saboda baya da linzami, har yanzu baki biyo hali na ba, ai ta ƙarƙashin ƙasa ake komai, ke dai ki zuba mani ido, Amman Alhaji Ƙarami gaki cen a ɗakin shi, kinji na gaya maki" Sai yanzu ne Mareen ta saki dariya. Lokaci guda kuma suna masu taɓawa kaman wasu ƙawaye. Turo ƙofar da akayi gami da sallama, shi ya sanya suka ja bakin su suka ɗinke. Mama Uwani ce, take shaida ma Maree tazo tayo cefane inji Hajiya Babba. Ba musu ta miƙe, tana mai gyara kwalliyar fuskar ta, abun dariya sosai. Sannan ta yafa ɗan fingilin gyale, tana tafiya tana gantsaro gaba. A bakin gare ta haɗu dashi, jingine yake da mota, hannun shi wata ƴar jikka ce haka ta kwali mai kyau, shi da wani ne suna magana. "Ina yininku?" ta furta cikin shaƙe murya, sai wani karairaya take yi, dan ma babu ƙugun. Bai ko kalle ta ba, balle ta sanya ran zai amsa, sai wanda suke tare ne ya amsa mata, yana mai cewa "Oga ana gaishe ka" "Lafiya" kawai ya iya furta wa, yana mai ɗauke kanshi, ya zuwa buɗe motar ya ɗauko wani abu. Ƙafafu a sanyaye taka ta wuce, tana ji su Iro suna yi mata dariya da suke zaune bakin gate. Shi kanshi iron haushin yanda take nuna shige ma Alhaji ƙaramin yake ji. To koma dai kishi ne hakan? Oho! Gashi shi kuma ko kula shi bata yi. Yana nan dai yana sauraren Al'ameen ɗin, akan maganar Maree ɗin. Ƙutawa tayi a cikin zuciyar ta. Za kayi magana ne, sai ma an ganni a gaban motar taka, inji ta ƙaryar nuna ɗagin kai. Ko wa ma zai ɗaga ma kai? Shi da yake auren ƴar aikin gidan, wadda ko ni na fita gata, dan dai kawai tana da ɗan haske, wata ƙila ma mai ne take shafawa, Amman yana wani wulaƙanta mutum. Daga kai har ita zaku sani ne. A haka ta wuce su har tayi masu nisa, daidai lokacin da ya sallama mutumen, yana mai binta da kallo, haɗi da sakin wani guntun tsoki. Yarinyar Sam bata burge shi, zubin ƴan duniya gareta, gashi tana tafiya tana wani girgiza, haɗi da ban ƙaro ƙirji wai ita mace, wanda ko shi da yake namiji ya fita fasali mai kyau. ******* "Ammi na ji ki shiru ne da maganar tamu, Ammi ki taimaka man, nima ina son in ganni cikin iyali na Ammi, yarinyar nan tana sona fa, Ammi kada kiyi saken da zan sake rasa ta ita ma" Sir Saleem ɗin ya furta cikin marairaicewa, Shiyasa ma wannan karon sai bai dawo ba, yayi zaman shi a cen zariyan, saboda ko ya dawo gidan baya jinshi da daɗi, ga kuma ƴan uwan Ma'u dake karakaina gidan, kuma cikin salon cin mutumci. Wanda ya zuwa yanzu so suke yaje yayo bikon Ma'un kuma. Yaƙi zuwa ne, domin yana so ya nuna masu kuskuren su, sannan yana so Ma'un ta sake ƙara hankali, duk da har yanzu zuciyar shi na raya mashi cewa Ma'aun ba wai tayi sanyi bane. "Kayi haƙuri Son, insha Allahu komai yana tafiya daidai. Mai martaba ne da kanshi yace abar batun a hannun shi, daga kai har Afnan duk ƴaƴan shi ne, dan haka duk yanda za'ayi insha Allahu babu matsala, Shiyasa Kaga mun saurara tukunna, amman muna sane da kai Son" Ajiyar zuciya ya sauke, sai yanzu yaji sauƙi, ai tunda dai magana ta kai ƙoli, yasan ya samu Afnan ya gama. Jiki na ɓari ya katse kiran Ammin bayan sunyi sallama, yana mai kiran Afnan ɗin. ********* Ƙarar blander dake aiki ce na ji ta tsaya lokaci guda. Da sauri na waiwaya, har ina ɗan razana kaɗan. Sai kuma na saki murmushi, ganin gogan nawa tsaye, yana juye man markaɗaɗɗun kayan miyan cikin man da nake soyawa na miyar. Ɗan jingina nayi da cabinet, ina mai harɗe hannaye na, gami da langaɓar da kai cikin sigar shagwaɓa. "Allah kuwa ni yaya ka bani tsoro wallahi" na faɗa cikin sigar shagwaɓa. Saida ya tabbatar da ya gama juye wa, sannan ya wanke hannun shi jikin sinc, yana mai gogewa da kitchen napkin, sannan ya matso sosai zuwa inda naken, yana mai tallafo fuskar tawa. "Sorry my lolipop, taya ki zanyi fa" ya faɗa yana mai lalubar baki na a hankali. Kauda kai nayi gefe, ina ɗan dukan ƙirjin shi. Hannu ya sanya, yana mai lafar mani kai na bisa faffaɗan ƙirjin nashi. Mun natsu a haka, kowa na amsar saƙon juna. Babu abunda ke yawan saurin saukar mashi da natsuwa, irin jin Suhan ɗin a cikin ƙirjinshi, yana mai shaƙar daɗaɗɗen ƙamshin mayukan gashin nata. Ɗan ƙauri ƙarin da muka jiyo ne, ya sanya mu saurin raba jikin namu. Muna mai kai kallon mu wajen girkin namu. Dashishin farar shinkafar dake cikin stummer ɗinne ruwan ya ƙone, saurin saukewa nayi, yana mai taro man ruwa a famfo na sinc na ƙara zubawa. Shi ya cigaba da taimaka man, hatta da yanke yanken su Cabbage shi yayi mani. Muna girkin hana bani labaru daɗi, wasu har sia na dafe ciki saboda dariya, yayin da ya kan zuba mani ido wani lokaci yana kallo na ina dariya. Har cikin zuciyarshi yake jin daɗi hakan. Ya tabbatar ma kanshi cewa ina jin daɗin zaman nawa tare dashi. Na dafe ciki ina dariya, harda ƙyaƙyatawa ne, sai jin ya kamo mani duka hannuwa yayi. Ƙure ni da idanu yayi, ƙasa daure ma kallon nashi nayi na sadda kaina zuwa ƙasa. Idanun nashi na mani nauyi a kullum. Wani irin kallo yake yi mani, mai cike da tsantsar ƙauna. Ban taɓa tunanin Ya Ameen zai iya sakin jiki dani haka ba, na ɗauka ko da na aure shi, zamuyi zama ne kaman na ubangida da yaron sa, ban ɗauka soyayya ta ta kai har haka ba a cikin zuciyar shi. Katse mani tunanin yayi, yana mai nufar hannayen nawa dake cikin nashi hannuwn zuwa bisa ƙirjin shi, saitin zuciyar shi. *"I Love u Suhan... No words can explain how much u mean to me, please and please i beg u Suhan, for my sake, don ever leave me for any reason, u always means alot to me wife and always keep firgiven me ,please dear"* Ya furta cike da wani irin shauƙi. Ni kaina jiki na ya mace duka. A hankali na kai baki na bisa hannun nashi da ke dunƙule da nawa. Ina mai manna mashi wani irin peck mai sauti. Lokaci guda kuma na wara duka hannuwn nawa, ina mai shige wa cikin jikin shi tsaf. Ba wata wata shima ya maida hannuwan nawa cikin nashi, yana mai sake manne jikin nawa da nashi. A hankali ya shiga saddo da kanshi zuwa gareni, yana mai lalubar laɓɓan nawa. Wannan karon ban hana shi ba, kaman yanda sai lokacin da yaji ya gamasu, sannan ya sake ni, ya na mai maida numfashi, har yanzu idanun shi a lumshe suke. Saida muka kammala komai, sannan ya taya ni muka jera a saman dining, har yanzu komai take man a lallaɓe, cike da wata irin salon soyayya da ke ƙara ruɗa ni. Gani nake kaman ni kaɗai ce nayi Sa'ar miji a duniyar nan, gani nake kaman ni kaɗai ce macen da tayi saura a faɗin duniyar. A falo ta iske mu, zaune yake bisa sofa yana amsa wayar manager ɗinshi. Yayin da ni kuma nake kwance kusa dashi, kaina bisa cinyar tashi, ya zame hular dake bisa kaina, yana mai yamutsa dogon gashin kan nawa. Ni kuma hannu na riƙe da waya ina karanta mana wani littafi *Saif ko Maleek* kiran wayar manager ɗin ta shigo wayar shi. Gefe ta samu ta zauna, hannun ta ɗauke da wata leda. yayin da ni kuma ganin tan bai sanya na tashi ba. Duniya kenan, wai yau Nihal ce a ɗarare a sashe nawa. Wanda ada zanje ɗakin ta in ta sallama Amman sai taga daman amsawa, shima a gadarance, ko magana Zatayi man cikin isa da tsawa, ni kuma jiki na na ɓari, kaman zanyi mata sujjada. Saida ya kammala tsaf, shima akan komawar su aiki ne. Sannan ya juya ga Nihal ɗin, yana mai maida hankalin shi kanta. "Uhm Nihal kin dawo ne?" ya furta ciki ciki, kaman baya son maganar. "Um Yaya" ta furta itama a hankali. A hankali na zame kaina daga bisa cinyar tashi, ina mai miƙewa da niyyar wuce wa, domin dia ban nuna mashi naji maganganun su na ɗazu ba. Hannu ya sanya yana mai kamo nawa hannun cikin nashi, gami da maida ni ya zaunar gefen shi. "Zauna wife, maganar ta shafe ki ai, ko ma bata shafe ki ba, dani dake duk ɗaya ne, sit!" ya faɗa shima idanun shi cikin nawa. Ba musu na koma ma zauna nima, ina mai ɗan sakar mashi murmushi, gami da ɗan yin fari da idanu. Murmushin shima yayi, yana mai lakato man Kumatu. Gyara zaman nashi yayi, yana mai ɗaukar remote ya latse tv ɗin dake aiki, wanda ta kusa lamushe rabin bangon. Hankalin shi ya maido kaina. "Wife maganar ku ne ke da Nihal, akan koya mata abubuwan da zakiyi, na farko ina son sanar dake cewa, Naji daɗi, lallai zuciyar ki mai kyau ce wife, ina alfahari da samun ki a matsayin mata ta. Na biyu kuma ina mai neman alfarma a gareki, muddin kika ga bata maida hankali kan abunda zaki koya mata kada kiji nauyin sanar mani, sannan idan ba zata kwantar da hankalinta ta koya ba, gara tun wuri a barta kawai, sannan ina so ki sani, wannan kuɗi da kika nema naji daɗin hakan, wannan ke nuna mani cewa komai na duniyar nan yana da daraja, abunda su suka kasa fahimta kenan. Saboda haka ga kuɗin zata baki da hannunta" duk yana maganar ne a hankali cikin natsuwa mai tattare da haiba da kwarjini. Ya ƙara she yana mai yi ma Nihal ɗin nuni da gefen stool akan ta haɗo da sauran cikon da zai bata ɗin. Duka ta har haɗa su, sai ga uban tulun kuɗi a gaba na. Wanda hakan har saida ta sanya na kusa ruɗewa, ban taɓa gani ba, ko a mafarki. Saurin saisaita kaina nayi. Ina mai gyaɗa kai a hankali cikin basarwa na shiga cewa "Ba komai Yaya, komai nayi ma Nihal ban faɗi ba, domin ita ɗin kai ne, saboda haka kada ka samu damuwa, insha Allahu zuwa gobe zamu fara class da ita. Cikin lokaci ƙanƙani zan tabbatar da ta iya. Kuma wannan kuɗi da ta bayar, ina so ku sani ba ni ce zan amfani dasu ba. Ko naira bana so, bana da sha'awa a ciki. Dan haka na sadaukar ma da gidan Marayun da muka je dakai kwanaki, Naji kana son tallafa masu, dan haka nima wannan gudunmuwa ta ce zuwa gareka. Allah kuma ya taimaka, ya baka sa'a, sannan ya ci gaba da dafa maka akan dukkanin al'amurran ka ameen" Da sauri Nihal ɗin ta maida kallon ta zuwa gareni, cike da tsantsar mamaki da al'ajabi sosai take kallo na. Ikon Allah, wacece ma Suhan ne wai? Dama haka take? Dama mace mai ɗinbin alkhairi tattare da ita, suka dinga wulaƙanta ta ada cen baya? Saurin tasowa tayi zuwa garenin, tana mai rungume ni kai tsaye ta saki kuka. "Aunty ki yafe man, nayi nadama Yaya ka taya ni bata haƙuri, insha Allahu na ɗauke ta tamkar ƴar uwa ta a yanzu, Yaya Aunty Suhan mace ce ta gari kaman Umman ta, dan Allah Aunty ina mai roƙon ki da ki sake yafe mani a karo na barkatai" Nima rungume ta nayi sosai cikin jiki na. Ina mai goge ƙwallar da ta zubo mani. Ko a mafarki ban taɓa tunanin kaiwa haka ba, ko a mafarki ban taɓa tunanin zama yanda na zama ba a yanzu. Dole na gode ma Allah da wannan baiwa da yayi mani. A hankali na zame ta daga jikin nawa. Ina mai cewa "Ba komai Nihal, ke ɗin kaman ƴar uwa kike a gareni, insha Allahu babu abunda zai gagara inyi maki, ko domin miji na, ko domin uban ƴaƴa na, ko domin wanda ya bani farin ciki fiye da yanda na tsammata" Cike da so da sha'awa yake kallo na. Baima san me zaice mani ba. He's speachless dai a Yanzu. Har dare yayi Ya Ameen na yaba mani, yana mai faɗa man kalamai masu matuƙar daɗi, wanda saboda hakan ne ma naci alwashin sanar mashi da labarin cikin nawa, ko domin yanda naga yana cikin farin ciki da annashuwa. *_Oum-Deedat ce_* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~82~* Saida muka kammala komai na al'ada, sannan ne na samu na faɗa toilet ina mai sakar ma kaina ruwa. Wani farin ciki kawai nake ji yana shiga ta ta ko ina, in na tuno da albishir ɗin da nake shirin sanar ma Ya Ameen ɗin. Ina shiryawa ne nake hango shi ya ƙura man ido ta cikin madubi. Ɗan waiwayowa nayi ina mai sakar mashi murmushi, yayi mun kyau shima, kwance yake bisa ƙayataccen gadon, ya lulluɓe kusan rabin jikin shi da blanket purple, sai walwali yake cikin Hasken farin ƙwai, hannun shi riƙe da waya, alamun yana latsa wa, amman fuskar shi da hankalin shi tsaf a kaina. Shima lumshe man idanu yayi a hankali, yana mai jin wani irin yanayi a jikin shi, dalilin da ya sanya na idasa cusa gashin nawa cikin hular, ina mai taka wa a hankali na isa gaban gadon. Sai nake ganin kaman yana da ƴar damuwa, kawai yana ɓoye man ne. Hannayen shi duka na kamo cikin tafukan nawa hannayen, ina mai murza su a hankali. Sai ajiyar zuciya yake saukewa a hankali, inda ya sake janyo ni zuwa jikin nashi, na faɗa bisa gadon. Ban musa ba na lafe, kaman wata mage, shima sake gyarawa yayi sosai yanda zan ji daɗi, yana mai zame ƴar yalolon hular da take cike da sumar kan tawa. Shafawa yake a hankali a hankali. Mu duka munyi laƙwas, kowa na shaƙar ƙamshin kowa, wani irin yanayi ne a tattare damu. Samun Ya Ameen a gareni ba ƙaramin abu bane, gashi yau ni Suhan wai har da cikin Yayan namu a jiki na. "Kin yi kyau Baby na! Faɗa man menene Sirrin wai? Naga har wani shining kike yi" ya faɗa a hankali cikin kunne na. Ƴar naj i jiki na yayi man, lokaci guda ina mai sakin murmushi, na sunne kaina cikin ƙirjin nashi. "ko sirri ne? Ba za'a faɗa ma Yaya ba?" ya sake faɗa shima, cikin jin wani irin sauƙin kasancewar tamu haka. Ɗan girgiza kai nayi a hankali. "To a faɗa man, Sirrin Suhan ai na Al'ameen ne" ya jaddada man a cikin kunne. Naji daɗin kalaman shi, ko a mafarki ban taɓa tunanin zan samu daraja da ɗaukakar haɗa kaina da Ya Ameen ba. Sai gashi yau da bakin nashi ma yana haɗawa. A hankali na kamo hannayen nashi, ina mai ɗora su bisa shafaffen cikin nawa, wanda kai kace ma babu ƴan hanji a ciki. Shafawa ya shiga yi a hankali, yana mai wara idanun shi sosai a saman fuskar tawa. Soke kaina nayi cikin blanket, ina mai ɗan ɗaga kaina a hankali. Zumbur yayi daga bisa gadon, yana mai tallafo ni sosai. "What Suhan? Baby! Kina da baby nan ciki? Ciki na? Are u pregnant baby?" duk ya jero man waɗannan maganganun a lokaci guda. Gyaɗa kai nayi a hankali, har yanzu na gagara ɗora idanu na a kanshi, wata irin kunyar shi nake ji. Ai da ƙarfi naji ya sauke ajiyar zuciya, yana mai furta *"Alhamdulillah ya Allah"* *"Thanks you aloot aloot Baby, kin biya ni, kin gama man komai, am so proud of you Baby, you mean kina ɗauke da ciki na? My Kid? My happiness?"* Saukowa yayi sosai daga bisa gadon, ya shiga kai komo yana shafa kai, har yanzu fuskar shi a wasashe take sosai. Sai kuma na ga ya dawo da sauri zuwa bisa gadon ya ɗago ni sosai, yana mai rungume ni sosai, kaman zai mayar dani cikin ciki. Mun kai minti biyar a haka, sai numfashi nake ji yana saukewa a hankali a hankali *"Zan zama Dad very soon dear, me kike so? Me kike so in maki? Dama na faɗa maki ina da ajiya nan ciki, Dad zaiyi grandson haka ma Umma"* Ya faɗa cikin sauƙi sosai. Ni sai na zama ma kaman wata sauna, duk murnar cikin ce haka? Hada surutai? Da kallo nake binshi, nima murmushi kwance a saman fuska ta. Caraf! Naji ya ɗage ni zuwa sama, sai kuma ya fara juyi dani a hankali a hankali, maƙalƙale shi nayi sosai, ina mai sakin dariya mai sauti, bai damu da a jiyo mu ba, duk kuwa da cewa dare yayi. Saida ya kula da na fara jin juwa, sannan ya dire ni bakin gadon yana mai faɗin "Zauna a hankali Baby" Zama nayi, har yanzu hannaye na cikin nashi. Zamowa yayi zuwa ƙasa ya durƙusa sosai, yana mai kuma tallafo fuskar tawa. "Thank aloot dear, ban san kuma ne zance maki ba, kin gama bani komai a rayuwa ta, please ki kula man da kanki, ki kula man da baby na please and please Suhan" Gyaɗa mashi kai nake yi sosai, nima wani irin daɗi nake ji, zan so ace yaron ma yayi kama dashi, Ya Ameen komai da komai nashi burge ni yake yi, watau wannan miskilanci, rashin son hayaniyar da ada ya kan bani haushi, sai gashi yanzu su ne suka dawo suna burge ni, kusanta ta gare shi, sai na gane, ashe duk wani kallo da nake mashi a da, da kuma irin fassarar da na mashi, ashe duk ba haka yake ba, shi mutum ne dai da Allah yayi shi mara son hayaniya, ashe ba ɗagawa ko izza bace ke sanya shi hakan, shi mutum ne mai tausayin na ƙasa dashi, ko kuma wanda bai kaishi ba, shi mutum ne mai yawan kyauta, mai iya zama da mutane, mutum ne wanda babu ruwan shi da sha'anin wasu, mutum ne ba mai yawan abokai ba, balle yayi jaye jayen mutanen da ba su dace da rayuwar shi ba. Ɗan nisawa nayi, lokacin da naji laɓɓan shi saman baki na, har wata ajiyar zuciya na sauke, kafin in fara maida mashi da dukkanin saƙunan da yake aika man. Mun nutsa ne wayar shi ta ɗauki ruri. Duk da kasancewr dare ne, sai banyi mamaki ba, in nayi la'akari da cewa suna ƙoƙarin komawa bakin aiki ne, saboda a haka kusan zan iya cewa kullum a cikin amsa waya yake. Bilal ne, dan haka ya ɗan miƙe cikin dariya sosai, yana mai amsawa yake faɗin "Sai ka bani goro kafin na faɗa maka friend" Ta ɗaya ɓangaren Bilal cikin mamaki yace "Faɗi me kake so? I promise to give u friend" Dayake wayar a handsfree ya saka ta, ina iya jiyo abunda yake faɗa, juyowa yayi zuwa gareni, yana mai ɗan man alamu da waya akan me zaice? Me nake so? ɗan murmusawa nayi, ina mai son gyara wanciya ta, idanu na a kanshi. Da sauri ya maƙale wayar a kunnen shi da kafaɗa, yana mai matsowa inda nake cikin sauri ya shiga gyara man kwanciyar. Alamu ya kuma man da hannu, bayan ya miƙe tsaye, yana mai kashe man idanu. "Agwaluma" na furta a hankali, cikin jin kunya, duk da bansan lokacin da baki na ya faɗi hakan ba. *"Agwaguma"* ya faɗa shima cikin sauri. A lokaci guda muka tun tsire da dariya ni da Bilal ɗin. Watau agwalumar ma bai iya faɗa ba, ikon Allah. Ɗan ɗaure fuska yayi, lokacin da yaji Bilal na faɗin "Shege ai ba ma sai ka faɗa ba, to na gane, congrat friend, ashe girma kuma yazo? Yanzu zakayi hankali dan ubanka" Ɗan kallo na ya sata, ni kuma sai na ɗauke kai kaman banji ba, dai cen na ji ya bushe da dariya yana faɗin "Yanzu zaka kawo ta kuwa tunda kunyi mani wayau" Shima cikin farin ciki sosai Bilal ɗin ke ma Ya Ameen murna, saidai ya roƙi alfarmar a bari sai da safe zai kawo, yanzu kam dare yayi, har sha ɗaya ta wuce. Ina jin su suna waya, duk abunda Bilal ɗin ya faɗa, amsa mashi kawai yake yi, saboda a irin tsananin farin cikin da take ciki. Naga gata a cikin daren, komai nake kafa kafa yake dani, yanda kasan wata jariri ya, sai riritani yake yi. Hatta da sallr asuba da muka tashi, har toilet ɗin ya kaini. Kai ko bacci bai yarda inyi ni kaɗai ba, ba tare da ina cikin jikin shi ba, yana shafa cikin a hankali a hankali. Kafin kwana biyu kaf labarin cikin ya buɗe ko ina, nace ina ruwan ba sabun ba. Ni da ganɗoki mu je biki Sai kuma me, tun da maganar cikin ta fasu, sai jiki na ya fara ciwo, yau wannan gobe wancen, laulayi dai irin na masu yaron ciki, ina son Wancen, banson Wancen, duk abunda na ce ina so ya siyo mun shi mai yawa ya kawo, har asibiti muka je akace ba wata matsala bace, saidai in ɗan dinga hutawa. Umma na ba ƙaramin farin ciki tayi ba, saidai ta ɓoye ne saboda kawaici. Ƴan dubiya akai akai sukan zo, hatta da wasu daga cikin ƴan Kankiya saida suka zo. Kaka zuwaira kuwa kusan kullum sai ta kira ni, haka aunty Feena, haɗa ƙara bani wasu shawarwari. Dad ma sai gashi da kanshi sashe na, karon farko da ya tako sashen namu, kunya duk sai ta lulluɓe ni, dayake tare da Mom suka shigo, saidai na kula ta ɗan yi sanyi, tana son ba ni kulawa, saidai ban sani ba ko kunya ce ke hana ta. Labarin cikin ya yi ma wasu daɗi, saɓanin wasu kuma, saidai koma dai menene hakan mu a gare mu alkhairi ne. Abokan Ya Ameen wasu tun biki rabo na dasu, sai gasu suna tururuwar zuwa, oh ni Suhan, kenan duka binsu yayi yana shelanta ni, ciki kaman kanshi farau. Classes da zamu fara da Nihal ma, cewa yayi a dakata aga yanayin jikin, saidai ba ƙarya ba, wallahi ina ɗan shan wahala, ni kaɗai nasan yanda nake sha. Har Ammi ma saida ta kira ni, dayake Afnan ta tsegunta ma Sir Salim, shine shima fa ya kira ni. Ina ganin abubuwa iri iri, motsin kirki da nayi akan idanun shi ne, kullum sai an ba cikin nan Kiss ya kai sau ashirin, butsu butsu, ko fita yayi sai kiga ya dawo da wuri. Afnan kullum kusan tana sashen, ita da Nihal suke haɗuwa suna mna wasu aikace aikacen, da yace a kawo man masu taya ni, ni ce nace a'a bana so. Sai gashi Nihal da ada ni ce nake shiga in share mata ko ina a ɗakin ta, in dafa mata abunda take so, yau gashi har ɗaki har toilet Nihal ke gyara mun, the same wahalar da na kasance ina mata a da, ita take yi man, ko so take ta ƙara kakkaɓe laifin ta a gareni ne? Oho? Na kusan sati biyu a haka sannan na fara jin dama dama. Shima makaranta ne da zamu rubuta final exam, ya sanya na daure, na ƙarfafa jiki na na miƙe. Sai gashi kuma nan take dole, karatu muke yi sosai, at the same time kuma in na samu chance, mukan yi class da Nihal da Afnan, sai gashi Nihal na mamaki, da ta tambayi Afnan wai nawa na amsa, tace ko naira, ban ma yi maganar ta biya ni ba, jikin ta ya sake yin sanyi, kenan dai ta kula da biyu na karɓi kuɗin ta, to koma dai menene ta gode, tunda duk abunda muke yi tana ganewa sosai, sai gashi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci komai nata ya fara cenza wa, ta fara komawa ainahin Nihal ɗinta a baya, mace mai son gayu da kwalliya, gashi kuma Nureen akai akai ya kan kira ta a waya, ya ji daɗi da ta tabbatar mashi da cewa ta fara iya abubuwa da dama. Saudat ko tazo bata leƙowa, ko a sashen Mom muka haɗu da ita, saidai ta bini da wani kallon banza, haushin Nihal take ji, wai kaman Nihal ace ta saki kambun ta, tana bina sau da ƙafa, gashi ni kuma sai wani jansu a jiki nake yi, ina nuna kaman su ƙannai na ne na gaske. Zamu iya cewa Hajiya Kubra ta ji matuƙar daɗin hakan, ta ɗauka aure na da ɗan nata zai kawo cikas, ko naƙasu a zamantakewar gidan nata, ta ɗauka ci baya ne ace yaron nata ya auri yarinya ƴar aiki mara gata da galihu kama ta. Saidai bata nuna ba ko alama, kuma har yanzu ta kan ɗan fita ga harkokin ta, duk da har yanzu taji shiru daga masarauta, duk kuwa da cewa an kamo Hajiya Laila da Alhaji Yaro. So take Sa'a taji kunya, har lailan ma, tunda su dai mayaudara ne, maciya amana, ko da za'a raba ta da dukiyar, Amman ya kasance ta ga Hajiya Laila, Hajiya Sa'a da Alhaji yaro sun wulaƙanta, sun muzanta a duniya. ************* Kaman kullum, mun kammala duk girkin da muka yi a ranar, Nihal na kitchen tana gyarawa, Afnan kuma na zaune bisa Sofa kusa da ni, tana mammatsa man hannaye na, da ƙafafu na da suka ɗan yi fushi, saboda tsayuwa. Ya Ameen yayi sallama shi da wani Likitan shi mai suna Dr Aleeyu, Wanda ya kasance shi ke duba ni. sai Bilal da suke tare. Ɗan janye ƙafa ta nayi, da niyyar tashi, ina mai gyara zaman ɗan kwali na a bisa kaina. Itama Afnan niƙewa tayi. Da sauri ya sanya hannu yana mai dakatar da ita. "Noo Lil Sis, cigaba da matsa mata ƙafafun, hala aiki tayi mai yawa ko? Bata jin magana, Dr yace ta dinga samun hutu, Amman ta matsa ma kanta, sauƙin ma ɗaya da ta samu ta kammala jarabawar. Dr gata nan ka duba ta, sannan ka sake yi mata faɗa, ni bata jin magana ta" Zama Dr ɗin yayi gefe, yana mai murmushi yake faɗin "Madam ya gida? Ya je ya tattago ni, wai nazo na duba mashi ke, baki ɗan jin daɗi, gashi kin ƙi ki zauna ki huta, wai haka ne?" Ina kallon Ya Ameen da yake tsaye ta kusan bisa kaina , nake girgiza kai "Dr zaman ne ya isheni, shi yasa banson in zauna ɗin" Ɗan hararar wasa ya sakar mani, yana mai tarar numfashi na "Aleeyu kada ka yarda da maganar ta, ka duba ta sosai please" Cewar shi, yana mai komawa kusa da Bilal ya zauna. Sosai muka gaisa da Bilal, ina tambayar Umme, wanda har ta dawo, har ni ma tazo ta duba, da yaron ta danƙwalele kyakkyawa sosai mai sunan Ya Ameen. BP ɗina ya fara ɗauka, sannan nauyi na, sai kuma sauran aune aune. Ɗagowa yayi yana mai kallon Ya Ameen cikin ido. "Watau yallaɓai, akwai buƙatar a sake kula fa sosai, ita da baby duk lafiyar su lau, nan da wata guda ma zata iya fara zuwa awo, sai ka kai mana ita cen wajen mu, akwai ƙwararrun likitocin da zan sanya su bata kulawa ta musamman, wanda suke fannin masu ciki" Gyaɗa kai yayi sosai cikin gamsuwa, inda sai da ya sake kafa wasu dokokin sannan ya tafi. Tun da likita ya sake bada doka, sai ya kasance ko ƙwai baya shan kula da riritar da nake sha. Hatta da ruwan zafi a flaks shi ke dafawa yana zuba wa. Abinci kuma daga cikin gida, sashen Mom ake kawo man, shima Afnan ce ke yi. Sai Umma idan ta dafa abun marmari na gargajiya tana aiko Afnan ɗin dashi. Shima sai da Ya Ameen yayi ma Dad complain ɗin Mom yanzu bata kula ni sosai, sannan yayi mata magana, sai a lokacin ne ma aka samu ta shigo ta duba ni, duk da cewa cikin ranta tana tausaya man, domin ta san irin wahalar da nasha lokacin ina ciki, kuma tana fata ace ciki na, ba zaiyi daɗewar da ni nayi ba, duk da nima sherri ne irin na mahassada. Ya Ameen ya kan ɗauke ni wani lokaci mu zaga gari, wajejen shaƙatawa muke zuwa, idan ka gammu sai mun burge ka, duk hassadar ka, komai kaf kaf yake yi dani, gashi cikin ya fara ɗan tasawa kaɗan, ina ɗan jin motsi a hankali a hankali, wani lokaci idan yana motsi, Ya Ameen ɗinne kan ɗora hannun shi bisa cikin, yana yi yana murmushi, yana ma cikin magana, kaman yana sauraren shi. Wannan ciki fa ya ga gata over, komai nake so shi ake man, komai nake son ci shi ake bani. Aunty Feena ce kan kira akai akai tana ja mashi kunne, duk da ya kula Mom kawaici ne take mashi, ko kunya ce? Ko kuma ƙiyayyar tawa ce ta shafi cikin, saidai shi bai damu ba, a haka yake ci gaba da kulawa dani, tare da bani dukkanin wani jin daɗi na rayuwa. Kusan zan iya cewa yanzu bana da matsala, ta kowanne fanni lafiya lau, Afnan da Nihal sun maida hankali, duk abunda nake koya masu ɗauke wa suke yi. ********** Ranar wata Asabar ne, muna falo muna kallo, saidai rabin hankalin mu, yana ga kan yanke man farce da Ya Ameen ke yi, yana faɗin ya kamata a jira mai lalle tazo ta yi mani, ni dai sai dariya nake yi. Wayar shi ce tayi ƙara kaɗan, alamun saƙo ya shigo. Bai dakata daga yi man abunda yake yi ba, komai a nutse, cikin salon shauƙin ƙauna, motsi kaɗan nayi sai yace "Ya dai baby? Akwai wani abu ne? Ko baby na ne?" sai in girgiza mashi kai. Har sai da ya kammala, sannan ya ɗauko wayar yana dubawa. Da sauri naga ya miƙe, yana mai faɗin "Tafiya Adamawa ya kama mu yanzu, harda Umma da Mom da Dad, ina fatan zaki kula da kanki sosai har in dawo, zan turo Lil wajen ki Baby, please ki kula fa" Jinjina mashi kai nayi, hankali na ya tashi sosai da sosai, hakanan sai naji ba daɗi jiki na, kira daga masarauta kuma? Harda Mom kuma da Dad? To me ke faruwa? Cikin salon takun shi, da ɗan sauri ya nufi bed room. Sai gashi ya fito saɓe da ƴar jikka. Inda nake zaune ta dawo ya iske ni. Durƙusa wa yayi sosai, yana mai bani peck a goshi, sannan ya maida akalar Kiss ɗin zuwa ga cikin, yana mai shafawa yake faɗin "Baby na sai na dawo kaji? Kada kayi ma Mummyn ka rigima, Allah yayi maka albarka" Kaman cikin yaji abunda Ya Ameen ɗin ya faɗa, sai naji ya motsa yayi ɓul! Murmushin mu ne ya faɗaɗa, yana mai cewa "Kin gani ko baby? Yaji abunda na faɗa, sai na dawo kuyi mana addu'a" "Allah ya tsare, ya kiyaye hanya, ya sanya a dawo lafiya, a gaida mana kowa da kowa, har da Mama Fulani, da mai martaba" na samu kaina da faɗa a hankali cikin wani salo. Saida ya rungumo ni cikin jikin shi sosai na wani lokaci, sannan ya sake ni, yana mai matsawa jikin stool ya zari makullin mota, sannan ya juya ya fice. Har sai da ya kai bakin ƙofar fita, sannan na samu kaina da cewa "Ya Ameen" Cak ya ja ya tsaya, yana mai juyowa a hankali gareni. Tashi nayi a hankali, ina mai dafe da ƙugu, sannan na taka har kusa da inda yake tsaye. Sannan na kamo hannayen shi ina mai cewa "Ya Ameen ina so in tambaye ka, Amman please kayi alƙawarin faɗa man gaskiya" Kallo na yake da mamaki, sai jikin shi yayi sanyi kuma. Tallafo fuska ta yayi, yana mai cewa "Ask me dear" Sai dana ɗan yi jim, nauyi da girman maganar nake aunawa, saidai ya zama dole nayi mashi ita, "Uhm..." ya faɗa shima, yana mai bin fuska ta da waɗannan shanyayyun idanun nashi. "Ya Ameen please me ke faruwa ne? Menene alaƙar dake tsakanin Mom da Umma? Me yasa masarauta ke neman ku? Jiki na yayi sanyi, sai nake ji kaman ba lafiya ba, Ya Ameen zuciya ta na halbawa, bana son duk wata matsala da zata iya shiga yanzu tsakanin mu, sai nake ji kaman ban iya jurewa, Ya Ameen zuciya ta zafi take man, tsoro ne fal a cikin ta.. " Da idanu yake kallo na. Sai yaji kaman ƙasa ta tsage ya shige, sai yaji wata irin kasala ta lulluɓe shi, tausayi na ya tsira mashi sosai, me zai ce ma Suhan? Da wanne ido zaiyi nata bayanin halin da ake ciki? Kama ni yayi sosai, har zuwa bakin Sofa, sannan ya zaunar dani. Shima kusa dani ya zauna, yana mai kwantar man da kai na bisa kafaɗar shi. Hannaye na cikin nashi yana murzawa. "Suhan!" ya kira sunana a hankali cikin wani sauti. "Ba lafiya ba", haka zuciyata ke raya man, na daɗe rabon da naji irin wannan kiran daga bakin Ya Ameen. Ƙoƙarin ɗagawa nayi in kalle shi. Ya sake mayar man da kan bisa kafaɗar "Zan faɗa maki Baby, Amman sai mun dawo, and ki kwantar da hankalin ki please, no matter how ina tare dake, da unburn namu, i will never leave u in my entire Life. Ke ce rayuwa ta, ke ce farin cikin Al'ameen, wannan kuma shi ne burin Al'ameen" Ya faɗa daƙyar kuma a hankali, yana mai shafi saman cikin nawa. Maimakon inji hankali na ya kwanta da maganganun shi, sai naji hankali na ya kuma tashi, wai me ke faruwa ne? Gashi Umma bata faɗa man komai, ba kullun nake ganin ta ba ma, in dai ba ni na shiga sashen ba. Baki na buɗe da niyyar zan magana, ya sanya hannun shi, yana mai toshe man bakin, tare da ɗan girgiza man kai. "Kiyi mana addu'a mu is lafiya, da na dawo zaki ji komai ƙanwata" Ɗan Murmushin yaƙe na saki, ina mai ɗagawa daga bisa jikin shi. "Shikenan Yaya, sai kun dawo, Allah ya kiyaye mana ku a duk inda kuke" ya ji daɗin addu'ar, Shiyasa ya ɗaga yana mai sakar man murmushi mai kyau, tare da lakace man hanci "To kuma ko ke fa baby na? AMEEN Ameen to, ki kula man da kanki, da ajiya ta kuma" ya faɗa yana mai miƙewa. Har bakin ƙofa na raka shi. Saida ya fice sannan na koma ɗaki na kwanta, tunani fal a cikin zuciya ta, sai na samu kaina da zurarar da ruwan hawaye masu ɗumi, ban shirya duk wata matsala da zata ɓarko a tsakanina da miji na ba, ina mashi son da bazan iya kwatanta wa ba, ba zan iya rabuwa dashi ba, ko da kuwa za'a yanka ni ne. Balle ace matsala daga ɓangaren Umma. To ko dai faɗa suka yi? Shine ake neman sasanta su? Kai ai kuma da naji labari, ko na ga wata alama dake nuna hakan, kuma nasan Umma ta, ba mace bace mai irin halin faɗa ba. Kaman yanda yace, sai ga Afnan tazo man taya ni fira.nan fa muka shantake, muna kallo muna labari, zuwa cen kuma sai ga Nihal ita ma, nan fa labari ya sake ɓarkewa. Agwaluma ta nake sha a hankali, wadda akai akai Bulla ke kawo man ita. Na ja su sosai a jiki na, su ma sun saki jiki dani sosai, Nihal ko da yaushe so take tayi wani abu, da zai sa ta gane cewa na yafe mata har cikin raina. Haka na kwana tunane tunane da juye juye, kaman marar lafiya, sauƙi na ma butsu butsu ya kan kira ni a waya, duk da sai dare suka isa, amman mun raba dare muna fira, yana tambaya ta unborn nashi. Saidai na ce lafiya lau, yana mai ƙara ja man kunne da na kula, domin wannan cikin shi ne rayuwar shi a yanzu, sannan ya sanar da ni cewa duk abunda nake so, na kira Bilal, in ya kasance bana da ɗan aike, bai yarda in fita in yi driving da kaina ba (Dayake ya koya man mota cikin tsakanin, saboda zuwa makaranta) ************* A hankali sawun takon mutum ke bayyana, har zuwa lokacin da ƙafafun suka daidaita tsayuwar su cikin ƙayataccen falon. Ko numfashin kirki baya yi, yayin da aka duƙa a hankali a hankali, aka ajiye wani abu dake cikin baƙar keda, wanda ba zaka iya tantance ko menene ba. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin akayi a hankali, lokaci guda kuma, ana mai ɗaga ƙafafu cikin sauri aka fita daga sashen. Cikin bacci mai daɗi naji ana Ƙwanƙwasa man ƙofar ɗaki. A'ah me ke faruwa ne? Ashe ban rufe ƙofa ta ba jiya? Kai anya kuwa? Ni ce fa na rufe ta da hannu na, kafin na kwanta, lokacin da na raka su Afnan bakin ƙofa. To ko dai Ya Ameen ne ya dawo? Shi kaɗai ke da makullin sashen namu, sai kuma Mom wanda take dashi tun tuni. Gaba na ne ya tsananta faɗuwa, bansan dalili ba, saidai ya ta'allaƙa da jin ƙila ƙofa ta a buɗe ne. Doguwar rigar bacci ce jiki na, mai taushi da kuma haske, fara ce ƙar da ita, har wani santsi santsi take yi. Plat shoes ɗina na soso mai taushi na zura, ina mai jawo ƴar hula ta da ta zame saboda daɗin bacci. Kafa ta nayi a kaina sosai, na sauko daga bisa gadon, baki na ɗauke da salati. Nayi mamakin ganin har gari ya fara wayewa, kenan har anyi sallar asuba? Ikon Allah, wayyo! Daɗin ya Ameen kenan, da ba zai bari in dinga baccin Lalaci haka ba, duk da yake lallaɓa ni sosai a yanzu. Saboda haka ne na nufi ƙofa da ɗan hanzari na, zuciya ta wanke fes, tuno firar mu da ya Ameen da nayi jiya, wanda har saida bacci ya ɗauke ni muna fira dashi, kafin wayar ta sulale ya kashe daga cen ɓangaren. A hankali na murza handle ɗin ƙofar, bayan na sanya makullin na buɗe. Kai kawai na saka zuwa falo, sai faman murza idanu nake yi. Daga cen gefe na hangi wata baƙar leda a dunƙule, in ba idanu na bane suke man gizo, sai naga ledar kaman tana motsi. Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "Oh ko me ya kawo leda kuma nan? Ko dai ledar agwaluma ta ce na manta ban ɗauke ba? Gadan gadan na nufi wajen da ledar take, a hankali na zuƙunna ina mai kai hannu bisa ledar na yayo ta kai tsaye. Wani irin taushi da sulɓi da wani irin yanayi na ji cikin ledar, lokaci guda kuma abunda ke motsi a cikin ledar yayi ƙoƙarin fitowa da gudu. Wani irin razananne ihu na saki, ganin wani irin danƙareren ɓera, baƙi wuluk yayi tsallen burgu, har yana bige mani ƙafa ya nufi bedroom ɗina da gudun masifa. Ihuuu na sake kurmawa, cikin wata irin gigita, domin har faratan ƙafar shi sun yakushe ni a ƙafa, lokaci da kuma na sulale ƙasa a sume, a lokaci guda kuma cikin nawa yayi wani irin juyi da hautsinawa, sannan ya dunƙule waje guda ya cure, sai kuma naji ya wani irin saki, sakamakon razana da nayi, sai ga jini shaaa yana biyo tsakanin cinyoyi na da gudu wani na korar wani. Daidai lokacin da idanu na suka kai kan jini ne, wata irin gigita ta sake kama ni, saidai duk yanda naso inyi controlling kaina kasa iyawa nayi. Ruf! Idanun nawa suka idasa rufewa, daidai sa'ilin da Afnan da Nihal suke rige rigen shigowa sashen nawa... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~83~* ************************* Rige rigen kaiwa gare ta suka shiga yi, hankalin su idan yayi dubu ya tashi. Basu ƙara gigice wa ba, sai da suka ga yanda jini yake malala daga ƙarƙashin Suhan ɗin. Ihu sosai Afnan ta saki; "Innalillahi Aunty Suhan lafiya dai ko? Me ya faru?" take ta jero ma Suhan ɗin tambayoyi cikin kuka, ko kula ma bata yi ba, da yanda Suhan ɗin take kwance samɓal ba numfashi. "Kira Yaya, Afnan yi sauri" Cewar Nihal ɗin itama, da duk ta gigice, zube take kawai ƙasa kusa da kan Suhan ɗin, ta tallafo kan nata zuwa bisa cinyar tata, sai fiffita take yi mata da ƴar fingilar rigar baccin tata. "Aunty Nihal na baro waya ta ɗaki" Afnan ɗin ta faɗa da ƙarfi tana goge ƙwalla. "Nemo wayar ta maza Afnan bata numfashi fa..." Cewar Nihal ɗin. Ko bari Nihal ɗin ta ƙarasa maganar Afnan batayi ba, ta bazama da gudu bedroom na Suhan ɗin. Cen bisa gado ƙarƙashin fillow ta hango wayar, ai da sauri ta latsa tana mai kiran Yayan nata. Saidai duk kiran da tayi ta mashi ƙin shiga wayar tayi, da gudu ta fito falon tana faɗa ma Nihal ɗin taƙi shiga, kuka take yi sosai, ganin Suhan ɗin kwance kaman gawa. "Ɗauko ruwa Afnan, ɗauko ku zuba mata please" Da gudu Afnan ɗin ta juya zuwa kitchen. Bottle water ta ɗauko na Faro, tun kafin ta ƙara so ta ɓalle murfin. Sheƙa mata ruwana suka shiga yi, Amman ko gezau bata yi ba, gashi har kawo yanzu jinin da yake malala bai tsaya ba. Nan fa suka sake ruɗewa, sai koke koke suke cikin falon, har yanzu Suhan samɓal take, alamun babu rai a tattare da ita. Afnan ta kai gwauro ta kai kari, sun rasa me zasu yi, wayar Suhan na hannun ta, tana ta faman danna mashi kira, Amman taƙi shiga. Girgiza ta Nihal ɗin keyi, tana mai faɗin; "Aunty Suhan ki tashi DAN Allah, mun bani, ki tashi kar ki mutu, me ya faru dake? Wa yayi maki haka? Ki tashi..." "yauwa ta shiga" Cewar Afnan da ƙarfi, ai da sauri Nihal ɗin ta miƙe, tana mai matsawa da gudu gaban Afnan ta fizge wayar. "Assalamu Alaiki Ya Habibty, Good morning Sweet Janam, how is your night? missing me?" duk ya faɗa lokaci guda, yana mai sakin murmushi, dan ya shirya ma jin daɗaɗan amsar ta. Kukan da yaji an rushe dashi ne a cikin wayar, ya sanya shi hantsilowa daga bisa gadon ba shiri, yana mai cewa" What happened Suhan? Tell me now, ki dena kula, me akayi maki ne?" Saboda tsabar ruɗewa, ya ma kasa tsayawa ya tantance ba muryar Suhan ɗin bace. " Yaya Nihal ce! Aunty Suhan ɗin.." sai kuma ta kasa idasa wa. " Look Nihal tell me me ya faru? Ina Suhan ɗin? Me ya same ta? Ki faɗa man mana, ina sauraren ki ɗan Allah Nihal kiyi magana, me ya samu Matata? Ina take?" Ya jero mata tambayoyin lokaci guda, yana mai buɗe ƙofar ya fice zuwa falo da sauri "Yaya Aunty Suhan ce, bamu san me ya same ta ba, mun dai jiyo ihun ta, kafin muzo, sai muka tadda ta kwance ƙasa cikin falo jini na zuba a jikin ta, kuma bata numfashi tun ɗazu muke kiran....." "Enough! Ya isa nace Nihal, wa ya taɓa man mata? Me kuka yi mata? Tun ɗazu uban me kuke baku kaita asibiti ba? Sai ta mutu? Sai kun kashe man ita? Garin yaya ma akayi hakan ta faru? Bayan jiya lafiya lau muka kwanta, Nihal kiyi magana, tun kafin in saɓa maki" Jin tashin hankalin da take ciki, sai ya hana ta magana, kuka ne mai ƙarfi ya ƙwace mata, dasa guiwoyin ta tayi ƙasa, tana mai sakin tsumammen kuka. Shi kau gogan sai surfa bala'i yake yi, har ma ya buɗe falon ya fice harabar gidan bai sani ba. Da sauri Nihal ta ɗauki wayar daga ƙasa da Nihal ta sake ta. "Hello Yaya!" "Lil zaman me kuke yi da ita a gida haka? A cikin wannan situation ɗin? Sai ta mutu? Jini fa kuka ce yana zuba a jikin ta, saboda baku da hankali, shine kuka sanya mata ido, Afnan! Nace ku kira mudi ku kaita asibiti yanzu, bansan jin komai ku wuce nace!" ya ƙarshe cikin ƙaraji da ɗaga murya, barorin da ke kai komo cikin harabar gidan, suna ta kallon shi, saidai sanin ko shi ɗin wanene, saidai kawai su russunar da kansu zuwa ƙasa, cikin girmamawa da ladabi, sannan su wuce, bai ko kula su, bai ma san suna yi ba, inda motar shi kawai take ajiye ya zarce. Da gudu ya isa ga motar, yana mai zura makulli ya buɗe ya shiga, sai da yayi mata key ne, sannan ya tuna a inda yake, da kuma dalilin zuwan, bayan hakan ma, babu wanda yasan halin da ake ciki, balle ma asan tafiyar tashi. Zai iya tuƙi a haka kuwa? Cikin wannan halin da yake ciki? Kashe motar yayi, yana mai fitowa da sauri, ya nufi sashen da su Dad da Alhaji Auwalu suke ciki. Da ƙarfi yake knocking kaman wani zarrare, gani yake Dad ɗin nashi yayi nawar buɗewa, kaman ya ɓalle murfin sashen yake ji, sai sauke ajiyar zuciya da numfashi yake yi. "Ba dai ɓari Suhan tayi ba? Baby na! Shikenan na rasa baby na? Unborn ɗina? Meyasa na taho? Ƙila da ina nan, hakan ba zata faru da ita ba, zan bata cikakkiyar kulawa, kaman yanda ya dace. Wanene yayi maki haka Suhan? Me ya faru dake? Wa ke bibiyar rayuwar ki? Tabbas wanda ya saka ɓawon Ayaba a sahen nasu rana, shi ne ya sake harar Suhan ɗin, bayan anga baya nan, in ko haka ne, lallai ya taka babban kuskure, cikin nashi da yake ji dashi, kaman tsoka a miya? " Duk cikin zuciya yake wannan tunanin, yayin da ya goya dukkanin hannuwa nashi a baya, yake takawa daga kusurwa zuwa wata kusurwar dake harabar wajen Ƙarar buɗe ƙofa ne, ya sanya shi zabura, da sauri ya nufi ƙofar "Dad!" ya furta da ƙarfi, cikin wata irin murya, daga ji zaka iya fahimtar halin da yake ciki na tashin hankali "Son what happened lafiya dai ko? Irin wannan bubbuga ƙofa haka? Baka koma ka kwanta ba?" Cewar Dad ɗin, wanda yake tsaye da Jallabiya fara sol da kuma casbaha a hannu. "Dady Suhan ce, Suhan Dady, baby na Dady, Suhan bata lafiya, Dady tafiya zanyi yanzu please Dady allow me" Ya furta, zuciyar shi na mashi wani irin suya, idanun nashi kuwa kaman garwashin wuta. A hankali Dad ɗin ya kama mashi hannu, zuwa cikin sashen nasu, duk da shima hankalin shi yayi ƙololuwar tashi, irin wahalar da Suhan ɗin tasha, yanzu ace ba cikin, ai akwai damuwa, ba ga Suhan da Al'ameen kaɗai ba, ga kowa ma dake cikin gidan. Bakin kujera ya shiga zaunar dashi, kaman ba zai zauna ba, sai kuma ya zauna, yana mai kai hannu zuwa kwarmin idanun nashi, ya shiga goge wasu siraran ƙwalla. Da kallo Dad ke binshi, lallai Al'ameen ya ƙwallafa rai ga Suhan da abunda yake cikin ta. "Son ka natsu kayi bayani, me yake faruwa ne a cen gidan? Dama bata lafiya ne?" Girgiza kai ya shiga yi "Dad lafiyar ta lau, akwai dai abunda ke faruwa, ga su Nihal cen sun nufi kaita asibiti, Dad zan tafi, ba zan iya zama ba, bansan a halin da take ciki ba..." "Assalamu Alaikum" sallamar Alhaji Auwalu, ita tayi sanadiyyar maida kallon su gabaki ɗaya gareshi. Amsa mashi sallamar sukayi su duka, yayin da ya ƙara so ga ƙanen nashi, yana mai bashi hannu suka yi musabaha, sannan ya miƙa ma Al'ameen shima, yayin da shi kuma ya ƙara da gaishe shi. Murmushi yake yi mashi, tare da amsawa, duk da zai iya jiyo maganganun su, kafin ya ƙara sa fitowa. "Me ya faru ne Mustapha?" cewar alhaji Auwalun "Yarinyar nan ce Suhan ce bata da lafiya, bata jin daɗi, shine ya tada hankalin shi, akan lallai sai ya tafi, ni da gani nake, kaman ya haƙura kawai, tunda Bilal na cen, sai ya aiwatar da komai, a dai samu a ƙarƙare zancen nan yau. Girgiza kai Alhaji Auwalu ya shiga yi. "a'a ba za'a yi haka ba, kai Ameenu tashi kaje, Allah ya tsare hanya, je ka wajen matar ka, ya fi wannan muhimmanci, lafiyar ta ita ce, akan gaba, Allah ya tsare hanya" ya faɗa shima, cikin jimami da alhini. Zumbur ya miƙe, yana mai ɗaga ƙafa da sauri ya shiga takawa da niyyar barin ɗakin, ya manta ko sallama ma bai yi masu ba, har ya dakata, sai kuma ya shiga cusa kai zuwa ficewa waje. Wannan karon ma da gudu ya isa ga motar tashi, wanda ko parking daidai baiyi ba, ya faɗa yana mai yi mata key. Shi in ma ba dan Alhaji Auwalu da ya ambaci Bilal ba, ya ma manta dashi. Kira ya shiga jera ma su Nihal ɗin, yayin da su kuma suke cen suna taga tagar sanya ta mota, komai na jikin ta ya saki, ba numfashi a tattare da ita. Kuka kawai Nihal ke yi, tana faɗin ki tashi Suhan, na bani da Yaya idan kika mutu, dan Allah ki tashi. Kowa na gidan ya firfito, harda Mudin suka kakkama aka saka ta haka a motar, jini na yarara, tun daga sashen Suhan ɗin, har zuwa parking lots ɗin. Gudu suke sharara wa su biyu, yayin da mudi ya nufi asibiti, shi kuma Ya Ameen ya nufo Abuja. A kan hanyar shi ne ya latsa lambar Bilal, tayi ta ringing bai ɗaga ba, saboda haka ya tura mashi saƙo. Akwai akai ya kan daki kan motar; "Suhan, wa yayi maki haka ne? Wanene shi? Wanene ya ja man asarar ciki?" Babu mai bashi amsa, dalili kenan da ya sake take kan motar, wasu da yake wucewa a hanya, har sukan saki tsaki, ko ma su ambata zagi a gareshi, shi dai ba tasu yake yi ba, hankalin shi na kan ya isa yaga halin da matar tashi ke ciki. ********** Da gudu aka gungura ta bisa keken marasa lafiya, yayin da wasu likitocin suke aikin maƙala mata oxygen, wasu kuma suna ƙoƙarin ɗaura mata ruwa,sai dai ruwan ma baya shiga jikin nata. Kuka sosai suke yi su Afnan, duk sun fita hayyacin su. Tun dai da aka shiga da ita A&E Sam hankalin su bai kwanta ba, gani suke kaman za'a fito ace masu ba ta. Wayar Suhan ɗin ce ta ɗauki ruri Da sauri Afnan ɗin ta ɗaga, muryar Bilal ce, shima hankali tashe yake tambayar suna ina? Kwatancen asibitin Afnan ɗin tayi masu, ita Nihal ma ko magana baya iya yi tashin hankalin da za'a fuskanta kawai take zullumi, muddin Ya Ameen ya iso. Domin daga tasowar shi, kawo yanzu, yayi kira ya kusa hamsin. Ko minti goma cikakke ba'a yi ba, sai ga Bilal a ruɗe, saɓe da babyn shi a kafaɗa, Ummi na gefen shi, suna ta zuba uban sauri. Da Nihal suka fara cin karo, ta ci kuka ta ƙoshi, idanun nan sunyi luhu luhu, abun ka da fara. Kasa amsa masu tayi, sai cen ne suka hango Afnan, tana kai gwauro ta kai mari. Kusa da ita suka ƙara sa, ita ɗin ma dai hakan ce, fuskar nan zawur, kaman wadda aka daddala ma maruka. "Garin ya haka Afnan?" Cewar Bilal "Yaya wallahi muma. Bamu sani ba, a haka muka iske ta, Amman dai da gani wani abu ne ya razana ta, tunda sai da tayi ihu sosai, jikin nata kuma, ba alamun cewa faɗuwa tayi. Da sauri Bulla ɗin ya miƙa ma Umme da take tsaye gefe Lil Ameen, yana mai wucewa da sauri zuwa Office ɗin Dr ɗin direct. Ya ɗan jima Dr ɗin bai fito ba, sai daga baya ne ya fito, zufa sharkaf a jikin shi. Sai da ya cire hand gloves nashi, ya sanya sanitizer ya ɗauraye hannun shi, sannan ya koma ya zauna, yana mai kallon Bilal. "Ranka ya daɗe barka da zuwa, ya masu jiki kuma?" cewr Dr ɗin. "Lafiya lau Dr. Ya condition na Suhan Dr?" cewar Bilal ɗin. Ɗan girgiza kai Dr yayi, yana mai tattara natsuwar shi duka ga Bilal ɗin. "Haƙiƙanin gaskiya Yallaɓai ba zamu iya cewa komai ba tukunna, abokan aiki na, suna iya ƙoƙarin su, wajen ganin an ceto rayuwar ta, da ta abunda yake cikin cikinta, Amman dai maganar gaskiya, da akwai kamar wuya, idan zamu iya bada tabbacin zata tashi, domin kuwa ta samu heart attack ne lokaci guda, abunda kuma ba'a so ga mai ciki, wannan shi ne yayi sanadiyyar suman ta, wanda har kawo yanzu da nake maka magana bata farfaɗo ba" Idan hankalin Bilal ya kai million ya tashi, har baisan lokacin da ya miƙe ba, yana mai haɗa zufa. "Dr please, ku taimaka ku ceto rayuwar ta, kada ta mutu Dr. Dan Allah! Na san kuna iya ƙoƙarin ku, Amman ku ƙara" Cewar Bilal, wanda yake tsaye kan ƙafafun shi, ya ɗan ranƙwafa, zuwa ga Dr ɗin, ko zama ya gagare shi. "Ɗan murmushi Dr ɗin yayi; "Zamuyi iya ƙoƙarin mu insha Allahu kada ku samu damuwa, insha Allahu zata miƙe, Amman cikin biyu sai anyi ɗaya, ko dai ita, ko kuma abunda yake cikin cikin ta!" Da hanzari Bilal ya sauke kai ƙasa, yana mai hangen wayar shi dake cikin hannun shi tana sakin haske, alamun ana kira, kuma ya san Al'ameen ne, a yanda ya san halin shi, ba zai taɓa ita ɗauka ba, balle har ya sanar dashi halin da ake ciki, tuƙi yake yi, komai zai iya faruwa. Hannu Bilal ya miƙa ma Dr yana mai yi mashi godiya, tare da sake roƙon shi. A reception ya tadda su duka, hadda Umme da ke ta famn jinjiga Lil Ameen dake bisa kafaɗar ta, yayin da Nihal take zaune ta zuba uban tagumi, sai Afnan da take tsaye ita kuma ta haɗa kai da bango, sai shesshekar kuka take yi. Babu madadin Suhan a garesu, ba zasu taɓa samu ba, Suhan macen kirki ce, Ya Ameen na masifar ƙaunar ta, ta ina zasu fara rasa ta? Ya zasuyi? Wanne hali Umma da Yaa Ameen zasu shiga? Balle a gangaro zuwa kansu? Kukan nata ne ya cigaba da tsananta, yayin da Umme ta matsa kusa da ita, tana bata baki. A sanyaye Bilal ya wuce zuwa cen gefe ya samu kujera ya zauna, da idanu Umme ke tambayar shi, ɗan girgiza mata kai ya shiga yi, wanda karaf sai a idanun Nihal. Ai wani kuka ta kuma fasawa, tana mai cewa "Shikenan Suhan, kaddai ace kin tafi kin barmu, ya zanyi da Yaya? Taya zan fara sanar mashi babu hannu na a ciki?" Gabaki ɗaya mutanen da suke wajen suma zazzauna, sai suka kuma shiga kallon su, wasu na tausaya masu, wanda sun gane ga dukkan alamu, wadda ke cikin halin rashin lafiyar tana da muhimmanci a garesu. ************** Karaf! Gam! Ƙiiiiiiii...... Wata irin mahaukaciyar ƙara ce ta karaɗe ilahirin wurin. Da hanzarin tsiya ya take burki, yana mai fitowa a zuciye, a sukwane kuma yayo kan motar Ya Ameen ɗin, wanda shima dan dole ya ja burki ya take. "Malam kai mahaukacin ina ne haka? Lahira zaka ne da kake ta wannan uban gudun? Wai ku mutane Meyasa baku da hankali ne? Kenan da ka kashe mu fa? Kace ma iyalan mu me? Ko ɗan baka da iyalan kuma baka san darajar su ba? In baka da su ai na tabbata akwai iyaye ko? Ko suma asara suka yi ne na haihuwar ka? Tunda har zaka iya aikata abunda zaka ja masu zagi, yanzu gashi da ka bugar man mota ta lalace, wallahi sai ka biya ni, ba zan taɓa ɗaukar asara ba. Mutumen da ake ta rirriƙe shi, yana fuzgewa, tare da sakin baƙaƙen maganganu ga Ya Ameen ɗin, wanda ya haɗa kanshi da jikin motar ya lumshe idanun shi, ya san shi ke da laifi, shi ya buga ma wancen mutumen motar shi, saboda haka ne ya zauna cikin motar bai fita ba, yana mai sauraren kalaman mutumen nan, wanda yake ta danƙara mashi zagi, ba ma shi kaɗai ba, har da iyayen nashi. Sai rirriƙe mutumen ake yi, yana mai fuzgewa, gami da cewa "Wallahi ku sake ni, sai ya biya ni asara ta, in ba haka ba, in bugi kuɗi na wallahi, tun ɗazu yake mana overtaking, mun ƙyale shi, shine bai ishe shi ba, sai da yazo ya buga man mota, banza dashi kaman wani makaho, ya bar ganin yana cikin wannan motar, wallahi yanzu haka ma aro ta yayi, baisan darajar ta ba, shiyasa baya lallaɓa wa yake wulaƙantawa" Wani daga gefe ne yace mashi, "Haba kai kuwa Malam, ka duba duk zagin da kayi mashi, bai fito ba, saboda kada hayaniyar tayi yawa, ya dakata a cikin tashi motar, Amman kai sai zagin shi kake harda ma iyayen shi, wanda hakan ba shine masalaha ba" "Kai malam dakata, ba ruwanka, dan ba motar ka bace? Kasan ko nawa na siya mota ta? Hakanan wani banza yazo ya lalata mun? Nace ko ka cikasa man ne da zan siya motar? Balle kazo kana gaya man ƙarya da gaskiya? Irin ku ne masu neman na adawa a baki, ƙanzagi kake mashi dan ya ɗebi wani abu ya baka ko? Ku daga kunga mutum a jibgegiyar mota, sai kuyi tunanin duka kenan, yanzu haka ma holoƙo ne." yana yi yan fiffizgewa, tare da kunfar baka, kaman Zaizo kan motar Ya Ameen, ana rirriƙe shi. *"Ku ƙyale shi, yazo yayi abunda zaiyi, duk abunda yake ganin zai iya yazo yayi"* Cewar Ya Ameen, wanda ya fito a hankali, yana mai rufe motar tashi ya jingina da jikin motar, yana mai harɗe hannuwa a ƙirji. Duk da jallabiya ce a jikin nashi, kuma fuskar nan Sam babu annuri, gashi ta cenza kala zuwa ja, hakan bai hana shi yin wani irin kwarjini ba. Dafe baki wanda suka sanshi suka fara yi, daga ciki ma, har akwai ma'aikatan da suke ƙarƙashin kamfanin shi, wanda sun sanshi farin sani, yana masu alkhairai, tare da kyautatawa iyakar iyawar shi. Yanzu ma suna kan hanyar su ne ta komawa bakin aikin su. A hankali mutumen nan yayi shiru, yana mai fizge hannun shi daga cikin na waɗanda suka riƙe shi, sai kuma ya saddar da kai ƙasa, yana mai cewa "Yallaɓai dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban san kai bane, wallahi tallahi, dan Allah kayi haƙuri" Ɗan murmushi Al'ameen ya saki, sai yanzu ne ma ya gane mutumen, ya taɓa zuwa ya same shi, akan ya taimaka ya bashi aiki, kaf gidan su, a ƙarƙashin shi suke, Amman maimakon Ya Ameen ya bashi aiki, sai ya bashi maƙudan kuɗi, yace yaje ya ja jari, wanda zai riƙe kanshi da iyayen shi da ma iyalan shi, da duk wani dake ƙarƙashin shi, dalili kuwa shine ;idan aiki ya ɗauke shi, sai ƙarshen wata ne za'a biya shi, kafin nan matsaltsalun sun sake lunkuwa, Amman idan kasuwanci kake yi, kullum kana cikin juya kuɗi ne. A hankali ta shiga takawa zuwa gaban motar Ya Ameen ɗin. Mutane dai sai suka koma kallon su kuma, suna masu sakin maganganu ƙasa ƙasa, ai ga irin ta nan, wanda yaso wulaƙantawar ma, ya fishi a komai. Ƙoƙarin duƙawa yake yi, Ya Ameen ya dakatar dashi, yana mai cewa "Allah ya kiyaye gaba, nawa ne kuɗin gyaran ɓarnar da nayi ɗin?" Girgiza kai mutumen yayi, kanshi a ƙasa "Allah ya sauwaƙe Yallaɓai, Allah ya kyauta in karɓi ramuwa daga gareka, nayi danasani, saurin fushi shine sila, wallahi bansan kai bane, da ban fara ba ma, ko da kuwa damaged motar nan tayi, ba zan iya amsar ko sisin kwabo ba, daga hannun ka, dan Allah ka yafe man, na roƙe ka" Sake girgiza kai Ya Ameen yayi. "Ba komai na yafe maka, kaima kayi haƙuri, ina cikin wani uziri ne, Shiyasa na kasa controlling kaina. Amman komai ya wuce, Allah ya kiyaye hanya" Yana gama faɗar haka, ya miƙa mashi hannu suka yi musabaha, sannan ya faɗa motar tashi, yana mai yi mata key, dan dole ya shiga lallaɓawa a yanzu, saboda gudun sake samun wata matsalar, wadda har ta kan zama barazana ga saurin da yake yi. Bayan tafiyar shi ne, mutumen ya ba mutane dake wurin labarin Ya Ameen ɗin. Nan fa aka shiga shi mashi albarka, hadda waɗannan ma'aikatan nashi, suma suna sake faɗin kyawawan halayen nashi, da Alkhairin shi garesu, wanda shi baima gane su ba. Jiki a mace cike da kunya mutumen yaja motar shi, yana mai barin wajen, nadama cike da zuciyar shi, yasha alwashn nan gaba, ko da kashe shi za'a yi, ba zai ƙara gigin yanke hukunci cikin fushi ba. ********* Babu wanda ya san halin da cen gida ake ciki, dangane da Suhan, kuma su Alhaji Auwalu sun yanke shawarar ba zasu faɗa ma kowa ba, har sai an gama abunda ya kaisu, gudun sake ɗaga lokacin zaman. Sannan sunsan Umman Suhan ɗin ba zata iya jurewa ta zauna a wajen ba. Falon yayi tsit, baka jin komai sai ƙarar na'urar sanyaya ɗaki, kowa ya natsu, ya bada hankalin shi ga mai martaba. Wannan karon hada Baba Waziri aka zo, wanda ko haɗa idanu da Umma ya kasa, haka itama Hajiya Kubra, Amman akai akai, ta kan ɗaga idanu ta kalli baba waziri, wanda take ji, kaman hada shi cikin ummul'aba'isin jefa rayuwar ta, da ma dukiyar tata cikin garari., sannan sai Alhaji yaro da Hajiya Kaila, wanda suke cikin wani hali, tun lokacin da aka damƙo su aka gano da haɗin bakin Hajiya Sa'a itama aka je aka cafko ta. Mai martaba ne ya cigaba da magana "Nasan kowa ya san dalilin taruwarmu anan, saboda haka, ba amfanin sake maida hannun agogo baya, magana ce ta cikin gida, wanda ya zuwa yanzu mun gane ainahin me ke faruwa, kuma su wanene ke da laifi, dan haka ga Baba Alhaji Lauyer nan, zai sake mana bayanin ainahin dukiyar Muhammadu, da kuma ta ɗiyar shi Hauwa'u, sai kuma ta Ita kanta Gimbiya gata nan a zaune. Wanda kowa ya sani, waɗannan kuɗi su ne, Alhaji Nura ya cigaba da juyawa, har Allah yayi mashi cikawa, daga baya dukiya ta koma hannun Hajiya Kubra." Gyaɗa kai kowa ke yi cikin gamsuwa, in ka ɗauke Hajiya Kubra, wadda har yanzu kanta yake sadde ƙasa. Nan fa Baba Alhaji ya dinga bayanin komai dalla dalla, kuɗi ne zunzurutun, tare da takaddun maka makan filaye a Abuja, da kuma gidaje a Abuja, da kuma Katsina, haɗa wasu sauran garuruwan da suka haɗa da Kano da Kaduna, sai kuma Binin Sakoto, da kuma jihar Lagos. Sannan da zunzurutun shaguna maƙare da kaya, wanda zasu iya kai adadin shidda, a kasuwn wambai, kwari da kasuwar sabon gari. Sannan gwalagwalai da kuma zunzurutun kuɗi da zau iya kai kimanin million ɗari shidda, wanda a ciki ne Alhaji Yaro yayi nasarr damfarar ta kimanin kuɗi Million ɗari uku da talatin da uku. Sai kum shagon gyaran jiki, wanda ba da daɗewa ba Hajiya Kubran ta buɗe shi, shima dai duk cikin dukiyar su Suhan ɗin ne. Idan Kaga Alhaji Yaro da Hajiya Laila da Hajiya Sa'a, wanda tun farko ashe ma ita ce ta kitsa yanda komai zai faru, Ita kanta Hajiya Kubran ta sha mamaki, wai ganin mutanen da ta yarda dasu, ta basu amana, da duk wani Sirrin ta, ashe makasar ta suke nema. Kafin zuwan ranar zaman, saida masarauta ta sanya Alhaji yaro ya yi trnsfer na dukkanin kuɗaɗen dake cikin account nashi, wanda har ya shiga cikin su, ya fara ragargazar su, Shi kanshi Dad da Alhaji Auwalu sun sha mamakin yawan adadin kuɗin, dole ne Hajiya Kubra ta ruɗe, kuɗin da tayi sama da shekaru ashirin da biyar tana tarawa, tana juyawa, rana tsaka azo ace ba nata bane. Bayan kammala haɗa jimilla kuɗaɗe da dukiyoyi, mai martaba ne yayi gyaran murya, yana mai sake jaddada godiya ga Baba Alhaji, sannan ya sake sanarawar cewa Alhaji Yaro da Hajiya Sa'a da Hajiya Laila, sai Baba Wazirii, shi ba zai yanke hukunci ba, za'a shigar da magana babbar kotu, domin ta yanke duk hukuncin da ya dace a kansu. Sannan ya sake cewa "Muna fatan masarauta bata shiga haƙƙin kowa ba, abunda ke nan, kotu ita zata sanar da duk yanda ake ciki. Ko akwai mai magana ne?" Shiru ne ya biyo baya, yayin da kan Hajiya Kubra ke sadde, tana ta saƙa abubuwa a cikin zuciyar ta, Amman kai da ka kalle ta, kasan jikin ta yayi sanyi ƙlau, masalan da Umma ta sake jaddada cewa ko naira bata da muradin samu daga cikin wannan dukiyar, saura kuma abunda Suhan tace, saboda ba zata shiga haƙƙin ta ba, ta tauye ta wannan karon. Kowa yagamsu matuƙa da hukuncin Umma, ta ƙara ƙima sosai a idanun Alhaji Mustapha da ma shi kanshi Alhaji Auwaln, har Baba Alhaji ya jinjina halin girma da dattakon da Umman take dashi. "Idan babu mai magana, sai muyi addu'a, domin mu samu ku koma gida da wuri, kafin nan ni zan tattara komai, in miƙa ga hukuma, domin ta san abun yi." Cewar Mai martaba yana mai gyara zaman shi. *"Ina da magana Ranka shi daɗe"* Cewar Hajiya Kubra. Da sauri kowa ya ɗaga kai ya ɗora mata idanu, mamaki kowa ke yi, duk zaman da ake yi, bata cika magana ba, wannan izzar da take cikin jinin jikinta har yanzu tana nan, saidai ba kaman da ba. "Muna jinki Hajiya Kubra" Cewar mai martaba "Magana ce ta cikin gida, saboda haka nake so, dan Allah da a barta a cikin gida, ba sai an fidda ba, maganar dukiya, na amince zan ba Suhan dukiya ta, ni da ita duk ɗaya ne, ɗiya ta ce, suruka ta ce kuma, nayi nadamar dukkan abubuwan da na aikata, dama waɗannan (Ta Nuna su Hajiya Laila) suna daga cikin waɗanda suka ƙara tunzura ni, suna daga cikin waɗanda suka daɗa zuga ni, akan aiwatar da komai, na yafe ma Maryama, ina fatan itama ta yafe man, a shirye nake da muyi zaman lafiya, mu haɗa kan zuri'ar mu kuma, sannan na amince da Suhan a matsayin suruka, bana fata kuma a samu Abunda zai sake kawo saɓani a tsakanin mu, tunda waɗannan shaiɗanun zasu amsa hukuncin hukuma, sannan ina mai sake bada haƙuri, a madadin mahaifina da baya raye a wannan duniya, ya aikata kuskure sosai, ya aikata son zuciya, wanda ni ma kaina a bisa shi na ginu, kuma nake jin kaina na kai, nake jin babu wani in ba ni ba, nake jin ba wanda ya isa sai ni, ashe duk ba haka bane, son zuciya ne irin nawa, Alhaji ya sha faɗa, ya sha kwatanta mani, ba ma shi ba, har Al'ameen da yake yaro, ɗan ciki na, ya sha kwatanta man, Amman na kasa ji, na toshe kunne na, na runtse idanu na, huɗubar waɗannan matan na kai komo a cikin ƙwalwa ta, kun cuce ni Sa'a da Laila, sai Allah ya mana sakaya a tsakanin mu, ba ku ba, har Talatu ba zan yafe mata ba, ba kuma zan ƙyale ta ba, saboda a haka nayi nadamar abubuwa da yawa, ina fatan za'a yafe man, yanda xanji daɗin gyara kuskuren da na aikata a haya, Alhaji ka yafe man, Hajiya Maryama ki yafe mani dan Allah, ko dan Albarkacin zuri'ar da muka haɗa" Ta ƙarshe a hankali, nadama fal a cikin maganar ta. Babu wanda jikin shi baiyi sanyi ba, hajiya kubra, duk izzar ta, duk cikar matsayin ta, duk ji da kanta, yau ita ce ke ambata nadama, tau ita ce ke cewa zata mayar da maƙudan kuɗaɗen da duk ta mallaka, take kuma juyawa ga mai su. Ikon Allah kenan. Idanun Umma ne suka cika da ƙwalla, duk da haka murmushi ne fal a cikin ranta "Na yafe maki Kubra, na yafe maki, insha Allahu itama Suhan zata yafe maki, ai ɗiya ce a gareki, kina da cikakken iko a kanta, Allah ya yafe mana baki ɗaya, sannan ina da wata magana, ina so dukkan Abunda mahaifin Suhan ya bari, a lissafa, a bata iya kwatankwacin abunda mahaifin nata ya bari, sauran kuma na Hajiya ne, wahalar ta ce, kuma gumun ta ne, zata cigaba da juya kuɗaɗen ta, da kuma dukkanin dukiyar ta." Nan ma sai jikin kowa ya sake yin sanyi. Tabbas umma ƴar aljanna ce, mace ce har mace, ashe ma Hajiya Kubra tana tare da irin wannan matar mai ɗimbin daraja da sanin ya kamata a cikin gida? Ta kama wasu shashashai wanda babu abunda suka ajiye sai yaudara? An taru an yayyafe ma juna, inda aka sake iza ƙyeyar su Hajiya Laila da Hajiya Sa'a da Alhaji yaro zuwa cell, inda shi kuma Baba Wazuri aka mayar dashi inda ake tsaron shi, kafin ranar zama kotu tayi, tunda maganar dukiya an riga an kammala ta, take ma Baba alhaji yayi lissafi, kuɗi iya million ɗari huɗu da sha biyu kuɗin Suhan suka kama. A take kuma aka yi rubutu, sannan aka zuba kuɗaɗen a cikin account na daban, wanda yake da sunan gimbiya merama, kafin komai ya lafa asan yanda za'a yi dasu, ita kuma Hajiya Kubra aka bar mata sauran, da niyyar zata cigaba da juyawa, da tayi musu, tace a barta zata yi zaman aure kawai, tunda babu abunda Alhaji Mustapha ya rage ta dashi. Saida aka kai ruwa rana, kafin ta yarda ta amsa. Ba wanda ya kai Alhaji mustapha jin daɗi, ya kuma yardar ma kanshi da cewa lallai Hajiya Kubran ta gyaru, ta gane kuskuren ta, ta kuma ɗauri ɗambar gyarawa. Ana cikin haka ne, sai ga jakadiya, saƙo daga mama Fulani. Sai da jakadiya ta gama zayyana saƙon Mama Fulani, cikin wani irin yaren da masarauta ce kawai ta sanshi, babu wanda ya iya fahimta sai Umman Suhan. Wanda take sakin murmushi a kai akai. Ba'a ɗau lokaci ba, sai ga Mama Fulani, ƙarƙashin jagorancin jakadiyr, sun sake shigowa. Sai da ta zauna ne, aka sake gaggaisawa, duk an zama ɗaya, sannan mai martaba ya sake gyara murya. Wannan karon, har saida ya zame rawanin shi daga saman fuskar tashi, yana mai fuskantar su Alhaji Auwalu. "Sai magana ta biyu, maganar neman auren ɗiyar wajen ku Afnan, ga yaron wajen mu Saleem, tun tuni ke akwai maganar, Amman ganin halin da ake ciki, sai muka ce a dakata, to yanzu dai munzo da ƙoƙon bara a karo na biyu, bayan mun nema a na farko bamu samu ba, yanzu kuma kanmu a ƙasa, muna fatan za'a duba ƙoƙon barar tamu, a taimaka mana da iri fisabilillahi" Kaf Falon babu wanda baiyi dariya ba, mai martaba mutum ne mai barkwanci, ga Mama Fulani a zaune, wadda take matsayin Babbar uwar ango. Ba ɓata lokaci aka amince masu, domin kuwa kowa ya yaba da Sir Saleem, yaron akwai tarbiyya tare da kawaici, ya so Suhan, Amman daga baya Allah yayi ashe Afnan ɗin ce matar shi. Basu baro Adamawa ba, sai da aka tabbatar da cewa nan da wata shidda masu zuwa ne auren Afnan da Sir Saleem ɗin. An rabu cikin mutun ta juna, tare da daraja juna. Ko a bayan mota, Hajiya Kubra ke ta jan Umma da Labari, saidai bata saki jiki ba sosai, gudun sake samun wata matsalar, sannan gashi ita bata san dalili ba, hakanan sai take jin gaban ta na tsananta faɗuwa sosai ma. Yaƙe kawai take yi, yayin da su kuma Alhazawan suke saƙe saƙe a zuciya, gashi basu sanar ma da kowa ba halin da Suhan ɗin ke ciki, gudun tashin lalurar Umman, wanda kowa ya sani, tana ɗauke da ciwon zuciya mai tsanani ************ Wata irin tafiya yayi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci ya isa garin na Abuja, Suhan kawai yake son gani, da ita kawai yake son arba, baya so ace wani abu mummuna ya same shi. Amman zuciyar shi, na raya mashi cewa, ba zai iya haƙurin zuwa gareta ba, har sai ya isa gidan ya kunna cctv idanun shi sun gane mashi dalilin faruwar hakan,zucjyar shi ma raya mashi akwai wnai abu a ƙasa, lallai akwai wani abu. Jigum Jigum ya iske kowa, ko da yayi horn, ba wanda ma ya zaci shi ne, hankalin kowa ya sake tashi, ganin mai gidan nasu, ƙaramin alhaji afujajan. Ba wanda ya amsa ma gaisuwr da yake mashi. Kai tsaye sahen nasu ya nufa, tun daga bakin ƙofa ya fara cin karo da busasshen jini. Jinin matar tashi, jinin Suhan, babyn shi, ɗanɗan shi, gudan jinin shi. Bai tsaya ba, har kai inda Al'amarin ya faru, ji yayi ƙafafun shi basa iya ɗaukar shi, ai a sukwane, ya zame wurin, yana mai sakin kukan da ya kasa dannewa. Ya ilahirrahman! SUHAN ɓari tayi, cikin shi ya zube, ya rasa ɗan shi tilo, da idanun dake tsiyayar ruwan hawaye yake bin sashen wajen da kallo. Yanzu nan ɗanɗan shi ne kwance ko? Har wurin ya daskare ya bushe, menene dalili? Me ya jawo hakan? Ya jima a wajen, kafin ya iya tashi a hankali ya isa ga bedroom ɗin, ga gadon nan a yamutse alamun an kwana lafiya lau, ga sallaya a gefe, alamun har sallar asuba tayi, A hankali ya kai zaune gefen gadon, yana mai ɗauko fillo ya rungume tsam a ƙirjin shi, yana mai shaƙar ƙamshin ta, abubuwa da dama yake tunawa. Tayaya zai fuskanci Suhan? A wanne hali take ciki? Meyasa basu ɗaga wayar shi idan ya kira? Cikin hanzari ya miƙe, yana mai isa ga mini laptop ɗin da ya haɗa da cctv ɗin, wadda ke ajiye a ƴar corner ta ɗakin. Stool ya ja zuwa gaban system ɗin, lokaci guda kuma yana mai kunna wa daga ranar da yake tunanin an saka masu ɓawon Ayaba. Dafe baki yayi sosai, idanu a waje, kaman zasu faɗo, na farko dai Maree ce, sai na biyun, wanda aka ajiye mata ɓera, na jiya kenan, an lulluɓe fuska, Amman fa alama namiji ne, sannan ko ma wanenn ya san ta kan gidan, kuma ya san baya nan. Ya kasa gane ko wanene, dalilin da ya sanya ya kashe kenan, yana mai tashi a sukwane ya fice daga gidan. Direct asibitin ya nufa, Allah ne kawai ya kaishi lafiya, tun a gidan yaso ya fara cin uban Maree, saidai ba wannan ne a gaban shi ba, halin da matar shi take ciki, shi ne farko. Tun daga nesa suka hango shi, daga yanayin yanda aka shigo da gudun masifa, sun tabbatar ma kansu da cewa shi ne. Saboda haka jikin Nihal ya sake ruɗewa da ɓari, tuni zazzaɓi ya lulluɓe ta, tun ma kafin ya ƙara sa wajen da suke. Bai ko tsaya kula Bilal ɗin da ke mashi magana ba, ya nufi Office ɗin Dr ɗin. To me zai ce mashi ne? Bayan yana ta kiran shi, ya gaza ɗaga mashi wayar, balle ya sanar mashi da halin da ake ciki, ko ma wane ɓoyo yake yi, gashi ya iso da kanshi, gashi ya iso yaga Menene ke faruwa ne wai?, kuma ga dukkan alamu Suhan na cikin wani mawuyacin hali, duba da yanda ya gansu Jigum jigum Jikin shi har kyarma yake yi, ɓari kawai yake yi, duk ya firgice ya ruɗe, Ya Allah! Me ke faruwa ne? A wanne yanayi Suhan ɗinshi take ciki ne? Da ƙarfi ya sanya ƙafa ya tura ƙofar Office ɗin likitan, ta buɗe kuwa dukan ta. Da sauri Dr ya miƙe, yana mai zame glass na idanon shi, tare da tattara takardun da yake rubuce rubuce a jikin su. Jin yanda aka banko mashi ƙofa, kaman ba hankali. Ganin Al'ameen ne ya sanya shi zagayo wa da sauri, yana faɗin "Ranka shi daɗe barka da isowa, ya hanya?" "Ina Suhan take? Ina Matata? Me ya samu Matata? Ina kuka kai man ita? Kada kuce man wani abu ya same ta, ba zan iya jurewa ba, kada ka faɗa man wani abu daban Dr. Ina Suhan?" "Calm your Self Engr Al'ameen matar ka tana lafiya, ana ƙoƙarin ceto ta ne" "Ceto ta like how? Since when take anan? Kun kasa ceto ta, kun san irin jinin da ta zubda kuwa? Tell me whare is she? I'll trnsfer her to another hospital, tinda ku kun gaza, gaya man ina take?" Yana magana ne cikin tashin hankali da wani irin ƙaraji, Bilal dake bayan shi yana ta taɓo shi alamun ya yi shiru, ya kwantar da hankalin shi, Amman inaaa, baya ma ko sauraren shi. Su kuwa Nihal da Afnan kuka kawai suke yi, Umme ma ta yi kukan har ta yi shiru, ganin ƴan uwanta mata na yi. A hankali Dr ɗin ya buɗe baki ya ce "A&E" Ai bai jira Cewar komai ba, ya ɗaga ƙafafun shi cikin sauri ya nufi ɗakin, ko gani baya yi sosai. Yana banka ƙofar Ward ɗin, idanun shi suka sauka kan wani Dr, dake tsaye, riƙe da wani ɗan abu kaman dutsin guga a hannun shi, yayin da yake ta girgiza kai, kwance take samɓal saman wani farin gado, an ɗaga gadon sosai, jikinta jojjone da wasu irin na'uri barkatai, an lulluɓe rabin jikin nata da fari da blue ɗin yadi mai kyau, komai nata a samɓal taje, kwance take, bata da jaraba da gawa, gabaki ɗaya fuskar an toshe ta da wata farar roba, zaka iya hango yanda tayi fayau, ta cikin fararen ƙwayayen da aka haske ta dasu, raka am. suma sauran likitocin kai suke girgiza wa, gami da salati "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ɗaya daga cikin su ne, ya sanya hannu, gami da jawo farin ƙyallen dake lulluɓe a rabin jikin nata ya idasa lulluɓe mata fuska, yayin da gefe guda, na'urar dake nuna bugawar zuciya, da numfashin mutum ta tsaya cak! *"Kulli nafseen Za'iƙatul maut"* ɗaya daga cikin likitocin ya faɗa, yana mai zare face mask dake fuskar tashi, lokaci guda, da kuma farin gilashin dake manne a idanun nashi. *"She's gobe"* Abunda wani daga cikin Dr ɗin ke cewa kenan, yayin da wani daga cikin su ke cewa, "Anyi jinkirn kawo ta asibiti, gashi abun har ya ci tura, saidai haƙuri." Iyakar kalmomn da suka samu nasarar shiga kunnen shi kenan. Idanun shi ne suka firfito gabaki ɗaya zuwa waje, me suke nufi kada dai suce mashi Suhan ta mutu? *"SUHAANNNNNNN"* Ya furta da iya ƙarfin shi, Yana ɗaga ƙafa da niyyar ci gaba zuwa cikin ɗakin, numfashin nashi yayi wani irin mugun ja, lokaci guda ya sulale zuwa ƙasa kawai. Bilal da Umme dake bayan shi, suka ruga zuwa gareshi, yayin da Nihal da Afnan suka jiyo ƙarar Umme ɗin ta na cewa *"TA MUTU BILAL"* ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~84~* *_Insha Allahu mun kusa ƙarƙarewa, ayi haƙuri dai dani. Har na gaji da bayar da uziri, Amman na san wasu daga cikin ku zasu iya fahimta ta. Nagode_* ************ Karo na biyu kenan da yana yunƙurawa, cikin sauke ajiyar zuciya, saidai har yanzu idanun shi a kukkule suke. Sosai kan nashi ke juyawa, a hankali ya shiga buɗe bakin shi yana ambato sunan ta. Saidai ba kowa zai iya fahimtar halin da yake ciki ba, masalan da hankalin kowa yake matuƙar tashe, masu kuka na yi, masu share ƙwalla na yi. *"Suhannnn"* Ya furta da ƙarfi, cikin amon murya mai amsa kuwwa. Lokaci guda kowa ya kai kallon shi inda yake kwance bisa gadon marasa lafiyar. Shi ma hancin shi liƙe da oxygen ta take ƙara taimaka mashi, gefe guda kuma ruwa ne, wanda aka saukar mashi shi da ƙarfi. Yunƙurawa yayi da ƙarfi, yana mai sakko ƙafafn shi daga bisa gadon, lokaci guda kuma ya fizge ƙarin ruwan da kuma ƴar siririyar robar taimakon iskar. Da sauri Dad ya sanya hannu ya dafe mashi kafaɗa, ganin ya miƙe tsaye yana neman faɗuwa. Har yanzu idanun nashi basu gama buɗewa ba. "Calm down Son, Suhan na cikin ƙoshin lafiya" Dad ɗin ya faɗa, shima hankalin shi a matuƙar tashi. Maida shi yayi ya zaunar dashi bisa gadon, yana mai tallafo dukkanin fuskar tashi, wanda har ta cenza kamanni daga ta Al'ameen ɗin da aka sani. "Look at there Son, Suhan ɗin ka ce cikin ƙoshin lafiya, bacci take yi" Dad ɗin ya sake faɗa, yana mai nuni da cen gefen su sosai, inda aka yi ma wajen shamaki da farin glass tar, saidai zaka iya hango dukkan abunda ke gudan ɗakin. A hankali ya kai kallon nashi, inda Dad ɗin nashi ke nuna mashi, cikin son tabbatar da cewa ba mafarki yake ba, cikin son gasgata maganar Dad ɗin tashi, cikin son tabbatar ma kanshi cewa Suhan ɗinshi bata mutu ba. A hankali ya shiga jinjina kai, sai kuma wata ƴar siririyar fara'a ta ƙwace mashi gami da bayyana a saman fuskar tashi "Dad really Suhan ce? Dad tell me please bata mutu ba, Dady ka faɗa man, Suhan bata tafi ta barni ba" ya faɗa souded emotionally. Gyaɗa mashi kai Dad ya shiga yi, yana mai shafo yaloluwar sumar kan tashi, wadda take a harmutse, kaman anyi dambe cikin ta, duk dai da cewa baƙa take siɗik mai ɗaukar ido. Sai a lokacin yaji wasu irin siraran ruwan hawaye masu ɗumi sun taho mashi, bai damu da ya sanya hannu ya goge ba, ya shiga ƙoƙarin miƙewa. Ƙoƙarin dakatar dashi Dad yayi, ya sanya hannu ya dakatar da Dad ɗin, inda ya shiga takawa da sauri yana mai nufar glass ɗin. Da dukkan hannuwan shi yayi amfani, wajen dafe glass ɗin, yana mai ƙura mata ido. Kwance take sosai, komai nata a nutse, sauke numfashi take yi a hankali a hankali. Wannan karon babu komai a jikin ta, da ya danganci bata kariya. In ka ɗauke yaloluwar rigar ta da take ɗanye fa ita, ruwan bula mai cizawa. Ajiyar zuciya ya sauke, mai haɗe da ƴar dariya, daidai lokacin da ya dafe glass ɗin da hannun shi ɗaya, yana mai goge ƙwallar da gudan hannun. Ta bayan shi yaji an dafa shi, juyawar da zaiyi yayi arba da Mom. Hannun ta ɗauke da ƴar jikkar ta ƙarama, sai wayar ta dake tsuwwa alamun ana kiran ta, Amman sai ta sanya hannu ta kuma katse kiran. Rungumo shi tayi sosai zuwa cikin jikin nata. Baisan lokacin da ya saukar mata murmushi ba sosai, yana mai faɗa wa jikin nata ba yana sakin dariya, kaman wani ɗan farko, itama dariyar take yi. "Mom Suhan ta tashi, Mom ba zan iya rayuwa babu ita ba please" "Is ok Son, ba zata tafi ta barmu ba, mu duka muna son ta, and am happy da naga ku duka kun samu sauƙi" Ta mayar mashi da amsa cikin wata irin ƙauna. Hango Umma da yayi ta shigo hannun ta ɗauke da Food Basket ne ya sanya shi ɗan ja baya daga jikin mom ɗin. "Alhamdulillahi, Muhammadu ashe jiki yayi sauƙi, dan Allah ka kwantar da hankalin ka, babu abunda zai same ta, Beside ma ai ta tashi fa, yanzun ma bacci take ɗan yi ne, zuwa wani lokaci zaka ga ta farka" Ɗan duƙar da kai yayi ƙasa cikin jin kunya domin daga shi sai singlet da dogon wando a jikin shi, "Eah Umma, Alhamdulillah na samu sauƙi, to umma Allah ya tashe ta cikin ƙoshin lafiya" Ya faɗa shima cikin jin kunya, daidai lokacin da Dr ya shigo cikin sauri. Ɗan turus yayi, ganin marar lafiyan nashi da iyayen nashi tsai tsaye tsakiyar ɗaki, yayin da shi kuma gogan yake cen dafe da glass, kaman zai tsaga shi ya shige, Dad ne kawai yake zaune bisa wata farar sofa da take ajiye gefen ɗakin. "Ah ya dai yallaɓai? Ya akayi ka tashi kuma?" Ya faɗa yana ɗan murmushi, bai ma ko kula ba, yana cen hankalin shi na kanta. "Da sauƙi ne Dr. Ai ka san dama fargaba ce, gashi kuma ya sha hanya, hada gajiya" cewar Umma Sai lokacin hankalin shi ya dawo jikin shi. Ɗan juyo wa yayi, yana mai kallon Dr ɗin, sai kuma ya ɗan saukar mashi murmushi. "To ya jikin naka?" cewar Dr ɗin. "Dr. Ta samu sauƙi ko? Ya jikin nata? Baby..." sai kuma ya an kare da Umma na wajen, kada yayi abun kunya. Murmushi Dr ɗin ya saki, har Dad sai da ya murmusa, ita kuwa Umma saidai ta sauke kai ƙasa kawai, tana mai wuce wa ta nufi table ɗin da zata ajiye Basket ɗin. "Ranka ya daɗe, ta samu sauƙi sosai, yanzu kai ne ma muke so muga ka samu sauƙi, tunda ita yanzu Alhamdulillah, mun mata allurar bacci ne, da zaran ta farka zata warware insha Allah" ya faɗa, yana mai ɗan kamo Al'ameen ɗin ya taimaka mashi ya zauna. "Dont mind ne Dr. Am feeling beter now" Sai da ya auna fulse nashi, sannan yayi mashi awon BP, komai dai normal, sai ɗan abunda ba'a rasa ba. Ɗakin yayi tsit, in ka ɗauke Dr da ke ta faman bashi shawarwarin yanda zai sake kula da kanshi. Saboda akwai matsala indai yana irin wannan faɗuwar. Ta gefen ido ya hango kaman motsin ta. Zumbur yayi ya miƙe, yana mai dakatar da Dr daga sake jona mashi sauran ruwan nashi, wanda akayi ma allurai da zasu sake taimakawa wajen saukar da bugawar jinin nashi zuwa daidai. Bai jira cewr komai ba, ya shiga tankawa zuwa ficewa, zagayawa yayi zuwa cikin ɗakin nata. Lallai kuwa, motsi take yi, tana mai ƙoƙarin buɗe idanun nata. Dire guiwoyin nashi yayi zuwa ƙasa, yana mai tallafo hannuwan nata, wanda ta sake su, kaman zasu faɗo ƙasa. Rungume su yayi tsaf a ƙirjin nashi, yana mai shafo gaban goshin ta. "Wife wake up please" yake faɗa a hankali. Duk sai dai aka bishi da kallo, ko shi kanshi Dr ɗin saidai ya bishi da idanu, lokaci guda yana mai nisa wa, sannan ya miƙe, yana mai bin bayan Al'ameen ɗin, shi kanshi mamakin irin wannan ƙauna da ke tsakanin ma'auratan yake. Sama sama take ƙoƙarin buɗe idanun. Ya ɗauke ta tsawon lokaci kafin ta iya cin nasarar fara ganin hasken duniyar tamu. Juyawa kanta yake yi a hankali, wasu irin siraran hawaye ne suka fara kwaranya daga gurbin idanun nata. Tuni gashin idanun nata ya jiƙe, "Yaya! Yaya!!" Take furta wa a hankali, wanda ba kowa ne zai iya fahimtar abunda take faɗa ba. "Na'am Dear! Buɗe idanun ki please, gani nan kusa dake, Yayan ki ne, gani a kusa dake" ya furta, yana mai sake matsawa sosai, kaman zai haɗe jikin shi da nata. "Ah Yallaɓai please ka ɗan dakata da yi mata magana, har sai ta dawo hayyacin ta, saboda bama so hankalin ta ya rabu" Gyaɗa mashi kai Al'ameen ɗin ya shiga yi, kaman wani ƙaramin yaro, shi dai fata da burin shi, ace Suhan ɗin tashi ta tashi. Shi kanshi Dr ɗin da mamaki yake kallon Al'ameen. Kaman Yariman matasan, ace yana irin wannan abu akan nace? Lallai ya sara ma mata, mata iyayen giji, matan iyayen gida, mata mahaɗin rayuwa, mata sinadarin rayuwar namiji. Kanta ya rufu, yana mai tofa mata addu'oi sosai daga bakin shi. Cikin ikon Allah kuma sai juwar ta fara sakin ta. Damƙe hannun shi tayi sosai da ƙarfi *"Innalillahi Yayaaa gashi nan Yayaaaa ka taimake ni"* Ta furta da ƙarfi sosai. Duk da basu iya jiyo abunda take faɗa daga ɗakin nata, saidai yanda suka ga Dr ɗin ya zabura zuwa kanta, sannan shi kuma Ya Ameen ɗin yana rirriƙe da kafaɗun ta yana mata magana, ya sanya su zabura su duka, in ka ɗauke Umma da ta samu gefen sofar ta zauna. Daidai lokacin da Bilal ya shigo shi da Ummin shi ɗauke da warmers na abinci masu kyau, shi kuma hannun shi riƙe da flaks na ruwan lipton da ya sha kayan ƙamshi. A tare suka ɗunguma zuwa bakin ƙofar ɗakin, inda su Nihal da Afnan suke jigum jigum, sun sha kuka har sun gaji, dan kowa a tsammann shi an rasa Suhan ɗin,saidai basu shiga ba, kaman yanda yake sanin kowa ba'a shiga ɗakin, saidai za'a iya hango komai ta waje. Shima Ya Ameen dokar ce ya karya. *"Suhan gani nan tare da ke, babu komai ba abunda zai same ki, ina tare dake,"* ya furta a hankali daidai sai tin kunnen shi. Allura Dr ya matsa, tare da soka mata, ko minti biyu bata yi ba, ta sake komawa baccin. Sake durƙusawa yayi daf da kanta, yana mai shafo mata fuskar ta, yana mai sake tofa mata addu'oin. Sai ya ga tayi mashi kyau, tayi wani fayau da ita. Zuciyar shi ce ke mashi saƙe saƙe, ingiza shi take yi akan abubuwa da dama, saidai yanzu ta lafiyar Suhan ɗin yake yi. Miƙewa yayi da sauri, har yanzu idanun shi ma bisa kan ƴar kyakkyawar zagayayyar fuskar tata. Wanda gashin idanun nata suka jiƙe, sai suka sake miƙewa sosai, kaman zasu tsole idanu. Hannun likitan ya ja zuwa gefe "Dr Baby na! Pls ya condition nata yake please Dr, kada ka ɓoye man, ina tunanin ko zamu cenza mata asibiti ne? Zan fitar da ita Dr.." "Is Ok ranka ya daɗe, both Baby and Momma are in well condition, no need of referring her to another hospital, we are trying our best, insha Allah daga yanzu da ta tashi shikenan, zama a iya sallamar ta, kawai tsorata ne da tayi sosai, saboda a bazata komai ya zo mata Shiyasa, sai dai zamu kafa mata dokoki masu nauyi, wanda Insha Allah idan ta bi su, zata haife abunda yake cikin ta lafiya, duk da a yanzu ma da kyar muka shawo kan lamarin, babu wanda yayi tunanin ma cikin bai fita ba. " " Huh!!!" Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke, jin cewa Suhan na cikin ƙoshin lafiya, tare da cikin nata, Abunda bai taɓa tsammani ba, kuma ko yanzu baya tunanin idan zai iya ɗaga ma Maree da duk wanda yake da hannu wajen ganin ya salwantar masu da rayuka gida biyu da suke a matsayin su ne rayuwar tashi. Bai tsaya sake saurarar likitan ba, ya zagaye shi, yana mai ficewa daga ɗakin. Ko ta kan iyayen nashi dake tsaye bai bi ba, ya shige inda aka kwantar dashi, yana mai zarar rigar tashi, haɗi da makullin motar ya fice. Ganin hakan da Bilal yayi, cikin azama ya bi bayan shi, inda Alhaji Auwalu da Alhaji mustapha saidai suka bi shi da kallo kawai, suna masu girgiza kai. Sam Al'ameen ɗin ya kasa sama ma kanshi natsuwa, dama sun san halin shi, akwai ruɗewa duk idan irin hakan ta faru. Da sauri Mom ta ɗaga ƙafa zata bi bayan shi, tana mai faɗin *"Son.."* Dakatar da ita Alhaji Auwalu yayi "Ƙyale shi Hajiya, naga suna magana da likita, ƙila wani abu aka buƙata zai je ya kawo, kuma ga Bilal cen ya bishi, ku ƙyale shi, indai har hakan zai sanya ya samu natsuwa" Ja tayi ta tsaya, saidai har yanzu zuciyar ta na raya mata cewa ba lafiya ce ta fidda shi ba, zullumin ta ɗaya, yaje ya aikata wani abu da ba daidai ba, masalan a yanda yake ba cikin hayyacin shi ba sosai, tunda ta san halin shi sarai, daga yanzu har lokacin da Suhan ɗin zata samu sauƙi, ba zai taɓa sama ma kanshi natsuwa, ita kam ta sare da wannan al'amari, irin son da yaron nata ke ma Suhan ya shallake tunanin ta tuni. _Toh ko ina kuma su Ya Ameen aka nufa?_ ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Ya Allah muna neman tsari gare ka, daga dukkan wani abun ƙi, na fili da na ɓoye, ya Allah ka san halin da bayin ka suke ciki, kai mai taimako ne, kuma gareka kaɗai muke neman taimako, ya Allah ka yaye mana wannan annoba da ta addabi duniya baki ɗaya (Covid 19). Ya Allah wannan cuta da ke barazana gare mu, da dukkanin wani musulmi ya Allah ka yaye mana ita, Allah ka bamu ikon bauta maka kai kaɗai, ya Allah ka bamu ikon kiyaye dokokin ka, haƙiƙa wannan annoba ce, wanda a zahirn gaskiya take mana nuni da mu sake komawa ga Allah. Ya Ubangiji mun san mu masu laifi ne, masu saɓo ne, masu kuskure ne, sannan masu son zuciyar mu ne, ya Allah ka yafe mana, alfarmar annabi da Alƙur'ani, ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa kuma tsarkaka, ya Ubangiji domin son da kake yi ma Annabin mu, fiyayyen halitta baki ɗaya, ya ubangiji ka amshi tuban mu, ka yaye mana, ka fuwace ma dukkan wani musulmi na duniya baki ɗaya. Ameen* *Page ~85~* ************** Cikin sauri ya sha gaban motar shi da tashi motar, ya daɗe yana biye dashi, ganin kaman ma zagaye gari kawai yake ta faman yi, ya rasa wajen nufa takamaimai, sannan ga wani irin tuƙi na ganganci, kaman ma baya cikin hayyacin shi. Cikin sauri ya ɓalle nufin motar ya fito "Wai me kake yi haka ne Friend? Ya da hankalin ka, kana neman ka hallaka kanka? Wannan shine tunani? Kada fa ka manta yanzu haka Suhan tana cikin wani hali ne, kuma mu duka abun ya shafe mu, Meyasa kake ganganci da rayuwar ka har haka ne?" Bilal ɗin ya faɗa, yana mai dafa murfin motar Al'ameen ɗin. Bai ko kalli inda yake ba, har yanzu idanun shi a ƙulle suke, ya jingina kanshi da kujera. " Friend please dont lose your mind please, muje gida muyi magana dan Allah! Komai zai daidaita" Cikin azama ya ɓalle murfin motar tashi shima, yana mai fitowa a zuciye. "Me tayi masu? Wane laifi ta aikata masu da suke neman rayuwar ta? Wanene wanda har zai shigo cikin gida na ya nemi illata man mata? Garin ya Bilal? In zuba ido kenan? Yanzu da Allah bai tsare ba, kana ganin da yanzu a cikin wane hali take? Bilal ka sani fa, an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, i cant take it any more Friend, ka ƙyale ni zan ɗauki mummunan mataki, shin bana fita haƙƙin su ne? Duk mugun nufin da suka nufe mu dashi a baya bai isa ba? Sun laƙa mana sharrin zina, sun kai Mom wajen boka, duk dan kada in aure ta, sun ja mana laba'i iri iri, duk na kauda kai, na share ne dan bana son wata fitina, ba wai dan bana iya & sukar mataki a kansu ba, ai na ɗauka sun hankalta ne sun gyara, laifin Mom ne, ita ce ta basu dama, da sanin ta suke komai Bilal, please kada ka hana ni, na roƙe ka" Ya ƙarshe yana mai haɗe hannayen duka guda biyu waje guda, alamun roƙon Bilal ɗin yake. Lokaci guda kuma yana mai faɗawa jikin motar ya jingina bayan shi jikin motar, sai fidda zazzafan numfashi yake yi. Shi Bilal ma saidai da idanu ya shiga binshi,yanda yake ɗaɗɗaga hannu, yana nuna baya da gaba, kaman zai tashi sama dan masifa. Ikon Allah! Al'ameen dambulan kenan! Al'ameen na da haƙuri da kauda kai, duk abubuwan dake faruwa ya sani, saidai ya zaiyi? Wata irin mahaifiyar ce Allah ya haɗa shi da ita, mai son kanta, mai son zuciyar ta, ta kuma ci sa'a Al'ameen ɗin mai biyayya ne, mai kauda kai ne, saidai ya tabbata wannan abu zai zo da sarƙaƙiya, baya so Al'ameen ya aikata ma mahaifiyar shi wani abu da ba daidai ba, duk kuwa da ita ta jawo ma kanta, duk kuwa da cewa da sanya hannun ta, saidai uwa ai uwa ce a ko ina ne. Horn ɗin da yaji ana masu ne, alamun sun haɗa ƙaramin go slow ne ya sanya shi takawa da sauri ya nufi motar, yana mai janye ta gefe, ya sakar masu one way, domin kuwa har yanzu Al'ameen yana a jingine jikin tashi motar, ya haɗa dukkanin hannayen shi ya rungume, cike da Ƙunar zuciya. Wasu da dama gefe kallon Al'ameen ɗin suke yi, yayin da wasu ma har suna ɗaga mashi hannu, alamun sun gane shi, saidai shi ko hankalta da su ma baiyi ba Saida Bilal ya kulle tashi motar gefe, sannan ya dawo, yana mai cewa da Al'ameen ɗin ya shiga su tafi. Aminta ce ake yi domin Allah, kowa da ƙaunar gudan a cikin ran shi, sannan basa da nufin juna da komai, suna martaba juna, tare da ɗaukar shawarar juna. Ba musu ya zagaya a hankali yana mai shiga motar, saida Bilal ɗin ya ƙara Ƙarfin na'urar sanyaya motar, sannan ya tada motar suka hau hanya. Kai tsaye Office suka nufa, waje tsaf ko ina, ga ma'aikata sai kai komo suke a cikin Company ɗin. (Dayake an koma aiki) Saida ya ɗauko ruwan gora masu sanyi, sannan ya ɗauko cup cikin mug cove ta roba dake gefe mai kyau. Miƙa ma Al'ameen ɗin yayi, wanda ya samu gefen sofa ya ƙame. "Take it easy Friend, every thing will be solve very easily insha Allah" Ɗaga gorar ruwan yayi ya ƙwanƙwala, sannan ya sauke yana mai maida numfashi. So yake ya faɗa ma Bilal komai yayin da Bilal ɗin ma Abunda ke wakana yake son ji, tunda sun kwana biyu basu zauna ba. Tiryan tiryan ya shiga faɗa ma Bilal ɗin komai. Jinjina kai ya shiga yi, shi kanshi kanshi ya kulle sosai, masu aiki da wannan mugunta? Kuma da sanin Mom da sanya hannun ta, akan iyalan ɗanta? Wace irin mata ce wannan? "Friend kada ka ɗauki mataki cikin gaugawa, zaifi kyau a tuntuɓi Dad akan maganar nan, muji yanda zaice, kada muje mu aikata kuskure ko ba daidai ba" "Is ok Bilal! Ya isa yanzu ni ban kai matsayin da zan yanke ma kaina hukunci ba? Matata ce fa? Ko ka manta ne? Ba zan jira cewr wani ba, cikin hukuncin abunda ya kamata in ɗauka, idan zaka goya man baya fine, idan kuma ba zaka goya man baya ba, you can remove your Self from my everything" Ya kula har yanzu bai sauko ba, dole ya lallaɓa shi, dole ne ya mara mashi baya, saidai ba zai taɓa bari dokin zuciya ya sanya ya bar aminin nashi ya aikata abunda zaiyi danasani ba a gaba. "Noo friend ba haka nake nufi ba, ka fahimce ni da kyau, ka isa, har ma kayi yawa, kasan ko kai wanene, kuma kasan matsayin ka ga al'umma, da kowa da kowa ma, ba gasu kaɗai ba, mu kanmu da muke tare dakai mun san muhimmancin ka, idanun kowa yanzu a kanka yake, sannan hidimar ta haɗa da hannun Mom a ciki, abun yana buƙatar a samu natsuwa sannan, kafin mu aiwatar da komai, yanzu ina so ka kwantar da hankalin ka, kada ma ka bari wani ya gane kasan komai, mu jira muga yanayin jikin Madam sannan, kuma insha Allah ƙarshen komai yazo, tunda ka riga ka fahimci masu yi maka zagon ƙasa, ai dama kasan ance makashin ka, yana tare da kai" Sai yanzu ya ji sanyi ya fara ratsa shi, lallai amini na gari kaman Bilal abun alfahari ne ga kowa, samun kaman shi ba dai yanzu ba, sai an tona. Saida ya lallaɓa shi, har zuciyar tashi ta ɗan yi sanyi, sannan ya sanya shi ya shiga toilet ɗin Office ɗin ya watsa ruwa yaji sanyi sosai. Sannan suka wuce kasuwa domin samo abunda xa'a buƙata a asibitin. Saidai fa har yanzu zuciyar shi ma shaida mashi indai yaga Bilal zai ja mashi lokaci ƙyale shi zaiyi ya aikata duk abinda yaga ya dace. ************** Tulin kaya ne masu kyau ƴan uban su, komai yayi kyau masha Allah. Asiya ita ce gaba gaba wajen ɗaɗɗaga kayan tana mai hasaso Ƙawar tata cikin kayan, lalai kowa yayi imani sai yanzu ne Salim zaiyi aure, sai yanzu ne zai huta. Easher ce da take gefen Asiya, suna ta kallon kaya tare, ta maida kallon ta kan Ammi dake gefe bisa sofa ita da Abban Sir Salim. "Granny wannan kayan duka na Aunty na ne? Abbin mu yace aunty sabuwa zai kawo mana, wadda zata dinga mana wanka da dafa mana noodles" ta faɗa cikin murna, duk da take ƙarama Amman ranta fayau yake, dayake kullum sai Salim ya kira Afnan ya haɗa su a waya, suyi ta shirmen su. Murmushi Ammin tayi mai kyau. Sannan tace; "Ƴar Auntyn ta kenan, nan kusa ba da daɗewa ba, ashe yaji zakiyi mani? Ai gara ku tafi cen, domin ni na gaji da cinye man abinci dama da ake ta faman yi, gashi ayi ta ƙwace man mai gida" Duka dariya suka yi, hada Abban nasu, sannan suka cigaba da tattauna yanda abubuwa zasu kasance, tunda gobe ne ake sa ran zuwa kai kaya gidan su Afnan ɗin. Salim dai na gefe, sai sosa kai yake ta faman yi, butsu butsu sai Asiya ta ɗago ta kalle shi, shi kuma sai ya maka mata harara irin ke banson gulmar nan. Wannan Family suna cike da ƙaunar juna da zaman lafiya, abun gwanin ban sha'awa. Sallama akayi da ƙarfi daga bakin ƙofa, lokaci guda ana ƙwanƙwasawa da ƙarfi. Kafin kowa ya miƙe, Easher tayi zumbur ta miƙe ta nufi ƙofar domin buɗewa. Duk da haka Salim ɗin bai zauna ba ya nufi ƙofar shima. Da gudu ta ƙarasa tana mai buɗewa take faɗin "Yeeh na riga ka Abbi" dariya yayi yana mai cewa "sai a baki ƙwai Amman na jakki" Taɓe fuska tayi sosai, saboda ata fahimci me yake nufi, saboda haka ne tayi fushi ma kawai cikin wasa, tana mai juyawa ta koma cikin falon. Malam Yahuza ne mai gadin gidan Sir, Salim ɗin. Ko tsayawa su gaisa baiyi ba ya shiga faɗin "Maigida kayi mani aikin gafara, ga uwar ɗaki na cen da yayyen ta, sunzo da wasu masu babbar mota, hada maza majiya ƙarfi, suna ta kwasar kaya suna zubawa a mota, nayi mata magana sai cewa sukayi idan ban masu shiru ba zasu buge ni har lahira, su mazan da tazo dasu fa kenan, Shiyasa na garzayo in faɗa maka, tun ɗazu nake kiran ka bata shiga ba. Cikin mamaki da kaɗuwa Salim ɗin ke kallon Malam Yahuzan. "Kana nufin Ma'u?" "Eh ita ranka shi daɗe" shima ya bashi amsa. Cikin sauri ya sallame shi, yana mai komawa ciki domin kwasar wayoyin shi, da makullan motar. "Ina zaka?" Cewar Ammi "Ammi kina jin fa abunda malam Yahuza yace, ma'u bata da hankali Ammi, ki barni inje in nuna masu kuskuren su, duk sai na sanya an kulle man su" Girgiza kai Ammi ta shiga yi a hankali. "Ban baka irin wannan tarbiyyar ba Salim, ka ƙyale su duk abunda zasu yi, idan ma sun lalata gidan ne, ai sai a cenza wani, Amman yanzu ai ba girman mu bane, aga kaje kana faɗa da mata akan kayan gida" Ta faɗa cikin natsuwa da kamala. Kallon shi ya maida kan Abban shi. Ko da alama bai ɗauka Ammi zata hana shi ba, duba da irin kayan manyan kuɗi da ke cikin gidan. Jinjina mashi kai Abban nashi yayi, yana mai nuna mashi gamsuwa da maganar Ammin. Zaune ya kai cikin Ƙunar zuciya, yana mai cire hular kanshi ya ajiye gefe, daf yake da sahale ma kanshi da masifar ma'u, ya gaji, ya gaji, ba zai iya ba, daga wannan sai wannan. Ita ko Asiya tuni ta fara tattara kayan tana maida su cikin manyan akwatunan nasu. Dama ita da Ammi da Mama Fulani ne suka haɗu suka zaɓi kayan, sannan aka bada order nasu. Har cikin ranta tana mai tausaya ma Afnan, gata mara hayaniya, Hasalima kaf rayuwar ta a Turai tayi ta, bata san wani abu wai shi kishiya ba, bata taso ta san menene kishi ba, balle har tayi zaman kishi da Ma'u masifaffa, ita ko tana addu'a Allah ya kawo sanadin da wannan gayyar ta ma'u da yayanta zata watse, bata jin ta su Easher ita ta sani har ga Allah Afnan zata iya riƙe masu su kaman nata ƴaƴan. Duk da haka kasa zama yayi wajen, zuciyar shi na mashi suya, kwasar tarkacen shi yayi ya haye saman ɗakin Ammin. Bisa gadon ta ya kwanta, yana mai mirgina, zuciyar shi taf a cunkushe, da Ammi zata bari ba zai kwanta ba yau da sauran igiyar auren Ma'u a hannun shi, waya ya zaro gaki da danna ma Afnan kira, ko da hakan zai sanya yaji sanyi. Suma da wani irin kallon tausayawa suka bishi, lallai Salim na ganin Jarabawa, ai mata irin Ma'u babu abunda ke cikin aurenta sai masifa, ya ma yi ƙoƙari, da ƙarancin shekarun shi ace yana samun irin waɗannan matsaltsalun. Saidai suka bishi da addu'a. Yayin da Abban ya tashi yana mai ficewa zuwa fada domin tsara yanda za'a yi tafiyar gobe kai kayan auren Salim ɗin. ********* Da hannu ya dakatar da ita ga ƙoƙarin amsar kayan hannun nashi. Zagaye ta yayi ya wuce, har yanzu babu wata walwala tattare dashi. Cikin kasala da tsoro mai haɗe da fargaba ta bishi da kallo tayaya zata gamsar dashi babu hannun ta cikin al'amari? Kallon ta ta kai kan Afnan da take cen gefe, wayar ta take hankalin ta kwance, ko ba komai dama tasan Ya Ameen ba zaifi fushi da Lil ɗinshi ba. Itama kurar ta ce tayi kuka, da ta riga ta bari ya san cewa ta tsani Suhan ɗin a baya, duk da yanzu ba wannan a cikin ranta, saidai ita kanta ta sani da kanta ta ɗaure akuyar ta a rana a wajen shi. Zaune suka tadda ta, an cire mata komai na taimakon asibiti, saidai hannun ta da yake sanye da canula har yanzu. Tayi fayau da ita, tayi wani irin haske sosai, duk ta cenza, har ta faɗa sosai, sai wani irin hanci da ya fito sosai, gashin kanta duk ya kwakkwanto gefen fuskar ta, kaman an shafa mashi gel. Hafsat na daga tsaye tana jijjiga Babyn ta, yayin da Mom ke zaune bisa wata kujera matsakaiciya ta flastic, hannun ta na riƙe da wani bowl ɗan fari tana ba Suhan ɗin Shake. Kasa amsa take yi, sai Hafsat ɗin ta ɗanyi mata magana. Kunyar Mom ce duk ta cika ta, tana ganin ikon Allah. Tun da ta buɗe idanun ta take ganin Mom ɗin, har kawo yanzu ta kasa tafiya, ta gaza gane wannan al'amari. Dad da Umma basa nan, tun dai da suka ga ta farfaɗo, sai umma tace ba zata zauna ba, tunda ga Mom nan, ita zata wuce gida ne, tunda ba daɗewa suka samu saƙon waya daga fada cewa gobe ƴan kawo kayan aure zasu iso. Shine tace gara ta wuce taje ta fara shisshirya wani abu, ita da Hajiya Zainab. Bilal ne ya iya gaida mom da mai jiki, yayin da shi kuwa gogan ya wuce kai tsaye zuwa inda matar tashi take. Saida ya dire ledojin dake hannun shi kafin ya kai zaune gefen gadon, yana mai haske ta da murmushi. Itama. Cikin ƙarfin hali ta mayar mashi, har yanzu sai a hankali, daurewa kawai take yi. Ta mashi kyau ainun, dalili da ya sanya ya kamo hannun nata guda kenan da ke sanye da canula ya shiga murza mata a hankali, jin kaman wajen ya ɗan kumbura. Ganin haka ne Hafsat ta shiga gaishe shi, ɗan juyawa yayi a hankali yana amsawa,fami da tambayar ta Khairi, Hankalin shi kaf yana kan Suhan ɗin, ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin ta tashi. "Son Kaga ai jiki yayi kyau Alhamdulillah! Dr yace zuwa anjima zai yi discharge namu" ɗan ɗaga mata yayi da kai a hankali, bai kalli ko inda take ba,gani yake hidimar mom ɗin kaman akwai yaudara ciki Maimakon ya bata amsa, sai ya maida hankalin shi kan Suhan ɗin "Janam ina ke maki ciwo yanzu?" Girgiza kai tayi a hankali, alamun dasauƙi "Kina son wani abu ne yanzu?" Ɗan shiru tayi, sai kuma ta gyaɗa kai a hankali. "Tell me Habibty, yanzu zan kawo maki" "Alale" ta furta ciki ciki. Babu wanda ya iya fahimta, hakan ya sanya shi zakuɗawa sosai, har jikin su na gugar na juna. "Alale mai yaji Yaya" Ta sake furtawa. Kallon kallo suka shiga yi, ido cikin ido, Ikon Allah! kenan.. Yau Suhan ce da cewa tana son tuwo Da hanzari ya tashi zai fice, duk fa ya bi ya ruɗe, cikin su babu wanda yayi tunanin so zai iya zauta Al'ameen haka. Ashe shiru shiru irin su haka suke soyayya a makance? Da hanzari Bilal ya sha gaban shi. "Bari inje Umme ta sama mata yanzu, ka zauna ka huta, yanzu zan dawo" Gyaɗa mashi kai yayi, yana mai ɗan sanya hannu ya bugi gefen kafaɗar shi, alamu da ke nuna cewa ya burge shi kenan, duk lokacin da yayi mashi hakan. Inda ya tashi ya sake komawa ya zauna. Har kunya ma ya ba Hafsat, ko Kunyar Mom bai ji, sai wannan abu yake yi. Duk da itama ta sha kukan ta ta gode ma Allah, dan da kyar aka lallashe ta "Son gobe in Allah ya kaimu fa iyayen Salim zasu zo, ka tuntuɓi Dad ɗinku kaji idan da abunda ake buƙata daga gareka" Mom ɗin ta sake furtawa. Still har yanzu ya gagara kallon inda take, baya so yayi mata wani kallo ne na daban, har yanzu zuciyar shi na ruruta mashi wuta akan mom ɗin, da ɗanyen aikin da ta aikata. Ganin yanda yayi ne, ita kanta jikin ta yayi sanyi, Al'ameen ya fara kai maƙura, sai kuma take ganin ai bata cancanci haka ba, tunda ba gaddama duk abunda ake da buƙata tayi, kuma ta yarda da Suhan a matsayin surukar ta, to me ya sanya kuma yake yi mata haka? Miƙe wa tayi a hankali, tana mai cewa "Zo son ina son magana dakai" sannan ta fice daga ɗakin zuwa waje. Baiko alamun motsawa ba. A hankali Suhan ta zare hannun ta daga cikin nashi, tana mai mashi alamun da yaje. Miƙewa yayi ya bi bayan ta, ba don ya so ba, sai dan baya so ya bada wata ƙofa da Suhan ɗin zata iya samun damar cewa akwai ɓaraka tsakanin shi da Mom ɗin tashi, ko ɗan nan gaba, duk da yasan cewa ta san komai, Amman har yanzu ya tabbata bata san labarin alaƙar dake tsakanin su ba. Abunda ita kuma mom bata ganewa kenan. Shimfiɗar da Khairi Hafsat tayi, tana mai komawa inda Mom ta tashi ta zauna. Cikin taɓe baki tace "Koma dai menene insha Allah a kanki zai ƙare, ya Ameen mutum ne mai zuciyar zinari, insha Allah babu abunda zai samu iyalin shi. Ɗan kallon ta Suhan tayi, ita kuma sai ta sakar mata murmushi, har cikin zuciyar ta tana son Suhan, bata da kamar ta. Komawa tayi ta jingina bayan ta jikin makarin gadon, abubuwa ne dayake suke kai komo a zuciyar tata, ita kanta ba zata iya jin zata bar wannan al'amari ba, muddin ta gane mai hannu a neman rayuwar ta, bata jin idan ba zasuyi shari'a ba har igiya tayi rara. A hankali ta kai hannun ta kan saman cikin nata ta shiga shafawa, tana jin yanda yake ɗan ɓulla nata a hankali a hankali, tuni wata irin ƙauna gami da tausayawa ma cikin ya ziyarci zuciyar tata. ************* "Son me kake yi haka ne? Ina maka magana kana share ni? Gaban matar ka da Hafsat? Kana son bani kunya ne? Me...." "Mom please and please is ok hakanan dan Allah! Suhan Matata ce, baki sonta, na ji wannan, baki yarda da ita ba a matsayin suruka, shima na ji wannan kuma na yarda, Amman mom please yarinyar nan ni ne nace ina so ta, ni ne nace ina ƙaunar ta, haka kuma ni ne na aure ta, duk ba ita bace tayi hakan, mom please dan Allah ki ƙyale mu hakanan mu huta, mom banda ɗaukar zugar ƴan aiki, kin fifita su Maree da Talatu akan mu ni da Matata, munji wannan, sannan mun ɗauka, zamu bar gidan, zamu tafi muyi nisa dake, kiyi haƙuri, ki kuma yafe man, nasan na aikata maki ba daidai ba, da tun farko kika hana ni auren Suhan, Amman ba zan iya zuba idanu ina ji ina kallo inyi asarar ran Matata ba, umman ta tayi kawaici, ta kauda kai, ta jure, ita kaɗai ta mallaka, ba zata iya haƙurin rasa ta ba, kafin na aure ta, na mata alƙawarin kare ta, na mata alƙawarin zama da ita har abada. Mom me kike ganin zai faru idan nayi saken da aka kashe mun ita? Me ta aikata maku mom? Tun tana cikin ciki kuke neman rayuwar ta, ke da kakana, wane irin hali kike tsammani zata shiga idan taji? ..... " Wani irin kuka ne mai cin rai ya taho mashi, Amman yayi tirjiyar hana shi ya fito. Da sauri ya sauke hannu ƙasa " Is ok is ok mom naji, duk na yarda, i accepted it the way its come, ki yafe man idan nayi maki wani laifi, Amman nayi maki biyayya iya rayuwa ta, lokaci yayi da zan ɗauki matata mu bar maku ƙasar" "Keep quit Al'ameen!!!" ta buga mashi wata irin gugutacciyar tsawa. Sannan ta shiga nuna kanta da hannun ta "Ni? Ni? Ni kake gayawa haka? Kana cikin hankalin ka kuwa? Wai ka manta ni ce mahaifiyar ka? Zaka tafi? Zaka zaɓi mata akan ni? Ni kake cewa zan kashe Suhan?ka manta na riga da nasan ko wacece ita yanzu a gareni? Ni kake cewa na zaɓi ƴan aiki akan ka? Kasan irin son da nake maka kuwa? Duk cikin ƴaƴa..." "Noooo! Nooo mom kada ki faɗa man haka, kullum haka kike cewa, Amman banga alama ba Mom! Kiyi haƙuri in na ɓata maki rai, Amman zamu tafi defenetly, maganar auren Afnan kuma idan an gaya mana zamu zo, idan kuma ba'a gaya mana ba, zamu je cen Adamawa wajen su mai martaba shikenan kawai. Zan yi nesa da ke mom tunda kin nuna bakya son farin ciki na, bakya sona da duk wani abu da ni nake so. Allah ya sani nayi biyayya iyakar iyawa ta. Ki yafe man!" Yana gama faɗar haka ya juya a sukwane ya bar wajen, har yana haɗawa da ɗan gudu, tsabar yanda zuciyar shi ke tafarfasa Cikin ƙwalalo idanu take kallon shi. Anya Al'ameen ɗinta ne? Anya kuwa shine? Son da yake ma Suhan har ya kai haka? Me ta aikata ne har haka a rayuwar ta? Gashi ta fara cin karo da bijire wa daga ɗan da tafi so kaf a cikin ƴaƴan ta. Da sauri sauri gudu gudu ta shiga ɗaga ƙafar ta, tana mai nufar ta inda yabi, saidai kafin ta idasa isa, har ya tada motar tashi ya bar wajen. Sun haɗa kai su duka biyun, kuka suke sosai da sosai, duk abunda ya faru a saman kunnen su ne, ashe hada hannun mom? Ashe Maree ce da Mama Talatu? Ashe mom ce ta saka su? Sai gashi suma abun ya shafe su. Wace irin mace ce mom? Tana so ta shiga aljanna kuwa? Wane zance ne Yayan nasu take yi haka? Basu gane tun Suhan na ciki ake neman rayuwar ta ba ina Mom tasan Suhan? Tayaya kakan nasu ya san Umman Suhan? Wacece Suhan a wajen Mom? Menene alaƙar su? Wannan shine abunda ya sake dagula masu lissafi, dole ne su nemo amsar wannan tambayar Da sauri mom ta ƙara so garesu, a kiɗime take sosai da sosai, ya ilahirrahman, wace irin kunya ce yau tasha haka? Me ke shirin faruwa da ita? Kaddai ace abunda ta shuka da wanda mahaifin ta ya shuka ne zata girba. Ganin suna kuka suma, jikin ta ya sake ɗaukar ɓari, cikin sauri ta buɗe baki zata yi magana Nihal ɗin ta dakatar da ita. "Is ok Mom, munji komai kuma komai ya fito fili ya bayyana, bakya sonmu, son zuciyar ki shine gaba akan komai, ke kika haife mu, banso faɗin haka ba, saidai wannan ita ce kaɗai gaskiyar da zamu sanar dake. We love Suhan to the extent,sannan zamu bincika akan abunda muka ji daga bakin Yaya, sannan kada kiga laifin yaya, wannan shine kaɗai abunda ya kamata yayi" Tana gama faɗar haka suma suka juya suna masu barin inda take tsaye. Sa'ar ta ɗaya marece ne sosai babu kowa a wajen, daga ita sai su, da ba ƙaramar kunya zata sha ba, ƴaƴan cikin ta? Ƴaƴa uku a cikin shida duk sun juya mata baya? Hada Nihal yau? Me ke shirin faruwa da ita ne? To ina ga Nafisa da Abie kuma sunji? A halin da ake ciki ta tabbata yanzu Ƙila Saudat ce kawai za ta mara mata baya. A hankali ta ɗaga ƙafa tana mai isa bisa wata kujerar silver ta kai zaune. Gabaki ɗaya ƙwalwar ta ta cushe, ta rasa ma daga inda zata fara kamo zaren tunanin nata... *Danasani kala kala ne ya fara ziyarar ta,ko da wasa bata taɓa tunanin al'amarn zai dagule mata haka ba, wa zata nufa? Wa zata tunkara? Wanda duk ta yarda dasu sun ci amanar ta, da wa zata tattauna abunda ke damun ta? Lallai ita kanta ba zata bar Talatu ba, me ya kawo hannun Maree a cikin al'amarin kuma?* ~Oum-Deedat ce~ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *Page ~86~* *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* *Addu'ar wanda ya Razana a cikin barci, Da wanda Ya Kasa Barci.* أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ. A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon. Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin al'amurana). >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~86~* *Shin kun manta cewa kafin Allah ya saukar da cuta sai da ya saukar da maganin ta? Ko kun manta cewa dukkan tsanani yana tare da sauƙi? Shin kun manta cewa Allah yace ku roƙe ni zan amsa maku? Dan meyasa zamu ja bakin mu muyi shiru, wasu suna yayata zancen ƙarya akan wannan cuta, wasu kuma suna ƙaryatawa, yayin da wasu suka maida ta hanyar Sana'ar su... Duk haka ya dace muyi? Wannan shi zai fisshe mu? Shin an bamu shawarwarin da zamu bi domin mu kare kanmu, ko ba'a bamu ba? Shin munbi? Mun kiyaye doka? A haka ne muke so Allah ya dubi al'amarin mu? Bayan bamuyi abunda ya dace muyi ba? Wallahil azeem mu hankalta, Corona Virus (covid-19) gaskiya ce, ta kashe da dama, yayin da take wahalar da dadama, shin mu da Allah ya ba lafiya bai kamata ace mun gode ma Allah ba? Sannan mun dage da yi ma waɗanda suka kamu addu'a ba? Sannan mun roƙi Allah ya yafe mana.. Gaskiya akwai gyara acikin al'amarin mu baki ɗaya, ance muyi, mun ce bama yi, ance mu bari mu ce bama bari, shin jama'a bari fa ba shegiya bace, wallahi da ubanta, to bama so uban ya bayyana. Dan Allah jama'a mu hankalta, mu kiyaye, sannan muci gaba da Addu'a. Insha Allahu Allah zai amsa mana.* ******************* "Mom what is happening ne?" Muryar Saudat ɗin ta karaɗe ilahirin wajen, yayin da take tahowa da sauri zuwa ga Mom ɗin, domin ta haɗu da Nihal da Afnan a waje, ko kallon inda take ba suyi ba, abunda yasa ta gane da matsala kenan. Har ta kai inda Mom ɗin ke zaune dafe da kai, Mom bata ɗago ta kalle ta ba. Ajiye ƴar kyakkyawar jikkar tata tayi gefe, tana mai kai zaune kusa da Mom ɗin, da dukkanin hannun ta tayi amfani, wajen ɗago da fuskar mom ɗin. Cikin razana da yanayin da taga Mom ɗin tata ta miƙe da sauri "Mom me ya faru please, ki faɗa man, wani abu ya faru ne? Ina Ya Ameen? Me su Nihal suka fita yi? Mom kaddai kice man dan Suhan ta mutu ne ya sanya kike kuka.." Itama ta faɗa cikin damuwa sosai. Maganar Saudat ɗin ta ƙarshe ce, tayi sanadiyyar ɗagowar mom ɗin da sauri.. " Saudat! Kina da hankali kuwa? Wa yace maki ta mutu? Who told you? " mom ɗin ta faɗa itama cikin ɗaga murya. A hankali Saudat ɗin ta sauke kafaɗa, cikin alamun ko inkula tace "Ɗazu ne Afnan ta kira ni" Girgiza kai mom tayi, "Bata mutu ba Saudat, and it will never happen now insha Allahu" ta faɗa cikin wata damuwa "So what mom? Kada kice man kema kin biye ma yaya, wajen son yarinyar nan, mom ki kalla da cin amanar da sukayi mana, ta aure mana Yaya, and Maman ta ta aure mana Dad, mom ki kalla fa, wallahi na tsani ko buɗe ido inyi inga yarinyar nan, ta raba mu da brother namu, a kansu Dad ya juya mana baya, sannan suna ƙoƙarin ƙwace mana gida.... " " Ya isa hakanan Saudat, bana son jin duk wannan, ya riga ya wuce, and its enough..." mom ɗin ta faɗa a fusace, tana mai dakatar da Saudat ɗin da hannu, sannan ta miƙe ta zagaye ta zuwa cikin ward ɗin. Da kallon mamaki Saudat ta bi Mom ɗin tata Me ke shirin faruwa ne? Kaddai itama Mom ta yarda da yarinyar nan, kaman yanda Nihal tayi? Hannu ta sanya, gami da ɗaukar jikkar tata ta mara ma Mom ɗin baya, zuciyar ta cike da tarin tambayoyi. Zaune ta tadda Mom ɗin gaban gadon Suhan ɗin, yayin da ita kuma take kwance ba bacci take ba, Amman idanun ta a lumshe suke, Hafsat kuma tana goye da khairi, tana ta faman zagaya ɗakin. Su dukansu basa cikin natsuwar su, dukkan abubuwan da suka faru a cikin kunnen su ne, har kai lokacin da Mom ɗin ta shiga ɗakin inda Suhan ɗin take, dalili kenan da Suhan ɗin ta koma ta kwanta, tana mai share siraran ƙwallr da suka zubo mata. Me kalaman Al'ameen suke nufi akan Mom? Kenan Mom ta san wanene mahaifin ta? Kenan mom ta san ko wacece Umman ta? Itama Umma tasan Mom? Amman Meyasa Umma ta ɓoye mata? Wace alaƙa ko dangantaka ke tsakanin su? "Sannu fa! Ya mai jiki?" Saudat ɗin ta faɗa tana mai ƙarasawa cikin ɗakin, ko sallama bata iya yi ba. Ko kallon inda take Hafsat bata yi ba, balle ta sanya ran amsa mata. Taɓe bakin ta tayi, tana mai zama bisa sofar dake cikin ɗakin. Suna haka ne Bilal ya shigo hannun shi ɗauke da Warmer mai kyau, bayan shi Ummi ce, saɓe da Lil Ameen. Tun kafin ma a buɗe Warmer ɗin tayi zumbur ta miƙe zaune. Ya mai jiki suka sake yi ma Mom. Kadaran kadahan ta amsa, har yanzu zuciyar ta ba daɗi Ita ta amsa da niyyar ba Suhan ɗin, Hafsat ta hana, tana cewa ba komai, ta huta, ita zata bata. Kowa yayi mamakin yanda ta ci alalen sosai, sannan ta kuma shan ruwan lemon Cook, kafin ta sake gyara kwanciyar ta, tana mai fata da addu'ar a sallame su yau, domin ta ƙagara ta isa ga Umman ta, tare da tarin tambayoyin da suke cikin cikin ta. An jima kafin Bilal ɗin ya sake yi masu sallama, da niyyar zai fita, ko zuwa dare ne, zai dawo ya tafi da Ummin. Ita kanta Mom taji daɗin yanda Bilal ɗin yake tsaye kan al'amurran nasu, ta sani cewa ba yanzu ba, ko nan gaba da wuya yaron nata ya samu amini na ƙwarai kaman Bilal ɗin. *********** Aikace aikace suke ta faman yi sosai, jefi jefi sukan taɓa fira, jinin su ya haɗu sosai, saboda Allah suke ƙaunar junan nasu, aikin da za'a bayar a waje, tuni Umman ta kira Ya Ameen ta bashi ya kai. Duk da baya cikin natsuwa, Amman tayi hakan ne domin ta ɗan ɗauke mashi hankali, wajen ganin irin tunanin da ya saka kanshi ɗin. Ko da ya dawo sashen su kawai ya sake wucewa, cctv ɗin ya sake kunnawa, sosai ya natsu yana kallon camera ɗin, akwai abunda yake son kula dashi sosai, kuma ga dukkan alama, daf yake da ya cika burin nashi. Sai dare sannan likita ya sake shigowa duba ta, nan ne fa yake sanar masu da sallamar da akayi masu, tare da kafa tsauraran dokoki akan Suhan ɗin. Al'ameen yayi kane kane, duk Suhan ɗin na kula dashi akan rashin kula Mom ɗin, wadda ya zuwa yanzu kowa ya kulle ta, sai kaji kaman ka zubda mata ƙwalla. Ko Saudat da ta gaishe shi a zafafe ya juya yana mai ɓalla mata harara, yake cewa "Sai yanzu kika ga damar zuwa?" bata ce komai ba, ta sadda kanta ƙasa, ba laifin kowa bane sai na Mom da ta bari su Suhan ɗin suka shiga rayuwar su, tare da damalmala masu rayuwa irin hakan. Sai gashi yau Mom da kanta ita ce ke daka mata tsawa, wannan abu fa na ɗaure mata kai. Tattara kaya suka shiga yi, hada Afnan wadda ta dawo, Amman Nihal na gida tana gyara ma Suhan ɗin sashen nata. Haka fa suka tattaro suna mai dawowa gida, Saudat ma bata bi su ba, gidan ta kawai ta wuce, domin akwai ƙawayen ta da zasu zo taya ta kwana. Shi ma Bilal da Ummi sallama sukayi masu, tare da shaida masu zasu sake dawowa duba ta, da Hafsat suka wuce, zasu ajiye ta gida, dayake dare yayi. Kai tsaye Sashen Umma ya ja hannun ta a hankali suka nufa, ɗan ja tayi ta tirje, tana mai kallon shi cikin ido, sai kuma ta marairaice ido, domin ta san Umman ba zata barta ta zauna sashen nata ba, gara ma ta wuce ɓangaren ta kawai Ɗan girgiza nata kai ya shiga yi, cikin kulawa sosai, baya so ta koma sashen nasu, har sai ya kammala binciken shi, sannan yana so ta samu kulawa sosai, har lokacin da zata sake warwarewa. Ganin haka sai ta langaɓe kai sosai a jikin nashi, hannu ya sanya shima cikin kulawa kawai ya rungumo ta. Sashen Umman dai ya nufa da ita, Mom dake baya tana fitowa ta cikin mota, har ta buɗe baki da niyyar magana, sai kuma ta fasa, tana mai wucewa sashen nata. Saidai me kasa shiga tayi, tsaye tayi jim, ta rasa me ke mata daɗi yaron da ta fi so kaf a cikin ƴaƴan ta, yanzu shine suke haka dashi? Duk wa yaja? Duk laifin wanene? Meyasa bai yarda da ita ba? Meyasa har yake zargi da saka hannun ta a komai? Me Zatayi wanda zai wanke ta gare su baki ɗaya shi da Dad ɗinshi? Juyowa tayi kawai zuwa sashen Umman. Lokaci na farko kenan da ta taka ƙafar ta cikin sashen, bata ma san ya yake ba, bata ma san kalar tsarin shi ba,dan haka ko da ta shiga da idanu at shiga bin dashen, ya burge ta, ko'ina tsaf, ga kayan alatu irin na kwalliyr sarauta da aka yiyyi ma bangon ɗakin, ake nuna cikar ƙarfin sarautar su, dan hada tambarin masarautar ma. Kai tsaye ɗakin da ke jikin na Umman ya nufa da ita, inda yake mazaunin ta lokacin da tana budurwa. Umma dake kitchen taji alamun magana ƙasa ƙasa. Ɗauraye hannun ta tayi, tana mai cewa da Hajiya Zainab tana zuwa, kaman taji alamun motsi. Hango shi tayi maƙale da ita yana ƙoƙarin shigar da ita ɗakin, tsakiyar falo ta tsaya tana mamaki, toh fa, meye na kawo mata Suhan ɗin sashen ta? Saura Mom ɗinshi tace wani tuggu ne aka haɗa? Duk dai da ta kula kaman ta fara sauka, Amman ita ba zata taɓa sakin jiki da ita ba zuwa yanzu dai. Bayan shi tabi, bakin gado ta tadda shi, yana mai gyara mata kwanciyarta bisa gadon, ita sai taji kunya ma, yanda taga ɗiyar nata na daɗa langaɓewa, shi kuma sai lallashin ta take yi. Ƙarasawa tayi cikin ɗakin sosai tana mai ce mashi "Ah Muhammadu ku ne? An samu sallama kenan?" ɗagowa yayi daga ɗan lulluɓa ma ƙafafun ta wani yalolon blanket mai taushi, yana mai ce mata "Eah Umma, sunce ta huta ne sosai" "Amman maimakon ku wuce kawai ɓangaren ta, ta idasa hutawa acen, sai kuma ka kawo man ita nan? Ni me zan mata?" Daga bayan ta, taji muryar Hajiya Zainab na cewa "Aiko ke keda yanda zakiyi mata Umman Suhana, ki barta ta kwana biyu anan wajen ki, ta ƙara warwarewa ko zata koma cen ɗin, Meyasa kike haka ne?" Ɗan murmushi Umma ta saki, cikin manyace tana mai cewa "Ai Yaya da barin ta yayi cen, shi sai ya kula da ita sosai, sannan akwai ma'aikata da zasu iya taimaka mata.." "A'a Umma, duk ban yarda dasu ba" ya samu kanshi da saurin faɗa, a tare Duk suka maida kallon su gareshi, sai kuma ya saukar da kai ƙasa, baya so kuma ya dasa masu wani zargi a rai. Wayancewa yayi yana mai cewa "Ba Zasu iya kulawa da ita bane sosai, gashi ni kuma wani aiki ya taso man mai muhimmanci, Umma kiyi haƙuri ta zauna anan zuwa kwana biyu, zan zo na ɗauke ta" Ɗan jim Umman tayi, sai kuma tace mashi "Amman Muhammadu kasan bana son abunda zai kawo matsala tsakanin ka da Mom ɗinka ko? Ina gudun tace ba'a yi daidai ba, Shiyasa nafi so ku tafi, zaka iya ɗaukar ta, ka maida ta sashen Hajiya ɗin, alabasshi sai a kula da ita cen, ga Nihal ga Afnan, duk suna iya bakin ƙoƙarin su a kanta" "Kiyi haƙuri Umma, banyi maki musu ba, sanin kanki ne halin da ake ciki da Mom, bama so wani abu ya samu Suhan, ba zata iya sake wa a gaban Mom ba, tunda kin dai san ko me ke faruwa, ni dai zuciya ta tafi natsuwa da ta zauna anan ɗin" ya faɗa cikin damuwa. Ita dai Suhan idanun ta a lumshe tana mai jin duk abunda suke faɗi. "Ke tunda ya ce haka kiyi haƙuri mana, da nan da cen duk ɗaya ne, muje mu idasa aikace aikacen mu, dare yayi, gashi ina son tafiya, yara ba zasuyi bacci ba sai na koma, zo muje mu basu waje" cewar Hajiya Zainab Ɗan jinjina kai Umma tayi, tana mai cewa "Toh ai shikenan, an dai fi ƙarfi na ne" sannan ta shiga bin bayan Hajiya Zainab ɗin. Duk maganganun nasu a kunnen ta ne, tabbas ji tayi kaman ƙasa ta tsage ta shige take ji, Umman Suhan na da kyakkyawar zuciya, me ya ruɗe ta ne ada cen baya? Duk irin wulaƙancin da tasha yi masu, bata taɓa ɗaga ido ta kalle ta ba, balle ta maida mata, sai gashi ko yanzu da ta bayyana ko ita wacece binta take yi sau da ƙafa Jin sawun tafiyar su zasu fito ne, ya sanya ta ɗaga ƙafa zuwa cikin ɗakin. A bakin ƙofa suka haɗu, inda Umman ta sakar mata murmushi sosai, tana mai cewa "A'ah Hajiya da kanki kuma?" Itama murmushi tayi mata kadaran kadahan, tana mai cewa "Wallahi kuwa, ai tare muke dasu, nazo in sake ganin jikin nata ne" Sake juyawa sukayi duka cikin ɗakin, yayin da Umman ta jawo mata stool na mirror ta zauna, tana mai tambayar jikin Suhan ɗin. Bai kalli inda take ba ya tashi ya fice, Suhan ɗin na kula, yayin da su kuma su Umman basu kula da me ya faru ba. Su duka sunyi mamakin yanda Mom ɗin ke nuna kulawa kan Suhan, saidai ita kanta Umman har yanzu jinin ta kan akaifa yake da Mom ɗin, sanin halin mom ɗin da kuma ita ɗin ko wacece. Bata jima ba ta miƙe, cike da kulawa take faɗin "Ko kina da buƙatar wani abu?" ɗan murmushi Suhan ɗin tayi, tana mai girgiza kai. "Kiyi magana mana Suhan, kada kiji kunya, ni da Umman ki duk ɗaya muke, ke ɗiya ta ce" Ɗan sake girgiza kai tayi, tana mai cewa "A'a Mom babu komai Alhmdllh" "To ai shikenan, idan dai ta buƙaci wani abu, ko waya ne ayi mana, sai nasa Afnan ta kawo mata ko?" ta faɗa, tana mai maida kallon ta kan Umman. Hada ƙara gyara mata lulluɓin sannan suka fice, ikon Allah, kowa mamakin Mom yake yi, Amman ita kanta Suhan ta barma ranta da cewa akwai wani abu a ƙasa, Amman kafin ta yanke hukunci, sai ta tambayi Umma sana. Saida suka kammala sannan Hajiya Zainab ta tafi, ita kanta ta ƙudurce ma ranta, dole ne suyi ganawa da umman suhan anan ne zata iya fahimtar ƙudirin Hajiya Kubran. Ba ƙaramin daɗi Suhan taji ba, lokacin da aka sanar mata neman auren Afnan da za'a zo gobe, tayi murna sosai, sai da dare sosai sannan ya shigo, hannun shi ɗauke da uwar sayayya sosai, har Umman saida tayi mashi faɗa, ya zuwa yanzu ta tabbatar ma kanta ƙaunar dake tsakanin yaran nata, kuma abun alfaharn ta ne ace ɗiyar tata ta samu miji nagari irin Al'ameen yariman matasan. Washegari kuwa da aiki sosai aka tashi Komai Umma ce keyi, Hajiya Kubra saidai ta kalla, anyi shirin tarar baƙi sosai da sosai, gida fa ya cika da ƴan uwa, abunka ga babban gida, hatta ma'aikata kowa da abunda yake yi, an gyara gida, an ƙalƙale ko'ina. Su kuwa su Nihal da Afnan suna ɗakin Suhan ɗin, suna ta shan firar su, yanzu ta saki jiki da Nihal sosai kaman ba abunda ya faru, anan ne Nihal ɗin ke shaida mata cewa sati mai kamawa take sa ran komawa, domin haka Baby ɗinta ya faɗa mata. Godiya kam ta zuba ma Suhan ita, hada addu'a take yi wai Allah ya sanya Saudat itama ta gane gaskiya. Saidai Suhan tayi dariya sosai, su duka sunyi kwalliyar su daidai misali, duk da dai maza ne zasu kawo kayan, Amman ai an riga an zama ɗaya, duk Family ne, saboda Ammi ma cewa tayi sai tazo ta duba jikin Suhan ɗin, dan haka da ita aka taho. Ƙarfe ɗaya na rana baƙi suka iso, tare da tarin kayan Arziƙi, lallai su Ammi mutanen kirki ne, sai gashi Ammi, Umma, Hajiya Kubra, Hajiya Zainab, tare da Mama Fulani an zage ana ta fira sosai, cewa tayi a kira mata Afnan ɗin ta ƙara ganin ta, aiko ta kama ta ta rungume gaban kowa, albarka take saka mata, tare da bata amanar ɗan nata, ba wanda bai ji daɗi ba a wajen, masalan ma Mom, ai sai kuma kunya ta kama ta, gashi ita ta kasa yi ma ɗiyar tasu irin wannan ƙaunar amma gashi ita a gaban kowa take nunawa. Sunci sunsha sun yi hani'an, wanda duka ƙoƙarin Umma ne. Sai Sam barka ake yi, hada gogan naka aka amshi kayan, da cewa yayi ba zai tsaya ba, saida Suhan ɗin ta nuna mashi rashin jin daɗin ta sosai, sai gashi har Bilal ya kira suka gaggaisa a mutumce wallahi. Ƙarfe uku suka fara haramar juyawa, aiko kaman kar a rabu, saƙo daga mai martaba ya iske kowa, mutane ne dattijai, wanda suka san me suke yi sosai, ita kanta mom sai taji alfaharin kasancewar ɗiyar tata da Zatayi aure a cikin Family ɗin. Ko da zasu tafi Ammi kaman kar ta saki Afnan, duk kuwa da yanda take sunne kai ƙasa, shatara ta arziƙi sosai ta kawo ma Suhan da Afnan ɗin, har yanzu tana ƙaunar Suhan, tayi ma Salim sha'awar ta, Amman tunda basu samu ba, ga Afnan nan madadin Suhan ai. Bayan sun tafi ne aka bar baje kaya sashen Dad ɗin, inda anan ne aka karɓi kayan, Mom sai jin daɗi take yi, lallai ta tabbatar ma kanta taso tafka wauta a baya, abunda yaron nata ya sha nuna mata kenan ada cen baya, Amman ta kulle idanun ta, ta kasa ganewa. Gashi yanzu yaron nata yana fushi da ita sosai daga gaisuwa babu wani abu dake haɗa ta dashi, ko sashen ta ma ya dena shiga sam. Afnan dai guduwa tayi ɗaki, inda Suhan ma ta ɓaɓɓako da ƙyar zuwa sahen Dad ɗin, duk da tana jin kunya, Amman abu ne na murna, kuma kowa yau yana cikin ta. Ana haka ne sai ga Hafsat itama, tare suka zo da Ummin Bilal, dayake basa da nisa sosai, Kaya sunyi kyau masha Allah, har ma'aikata sai da akace su shigo su kalla, kai daga baya ma sashen Umma aka maida kayan, ba dan taso ba saidai dan Mom tace haka, ai ita ce Uwar amarya, dan haka wallahi ta bar mata hidimar, aiko an sake shan mamaki, harda Al'ameen da yake zaune gefe saman sofa yana ta faman latsa waya, rabin hankalin shi na kan matar tashi, da ta ƙara kyau tayi wani fayau da ita. Butsu Butsu sai sun haɗa idanu, ita kuma ta haske shi da murmushi, har lumshe idanu yake yi, kai ƙarshe ma har kiss yayi mata gami da hura mata iskar, ita kuma sai ta wani langaɓar da kai, tana dafe saitin zuciyar ta, baisan lokacin da ya saki dariya ba, nan fa hankalin kowa ya koma kanshi, sai ya wayance, yana mai duba wayar shi, alamun wai a cikin wayar ne aka bashi dariya. Alama yayi mata da idanu, na ta taso ta bishi, kaman ba zata ba, kunya take ji, kada kuma ace har ta fara bin miji daga dawowar su jiya. Ita ta fara fita, ba jimawa ya bi bayan ta, Hafsat na kula dasu, dariya tayi a zuciya, tana mai ƙara masu addu'ar ƙaunar juna. A sashen Umman ya tadda ta, ta sha kuwa matsa sosai, yayi missing matar tashi sosai, bata hana shi ba, saidai ta ƙoƙarin daidaita kanta, kada a wuce gona da iri, gashi tana kan bed rest ne. Ƙaunar juna sosai suke yi, bisa jikin shi tayi masauki, inda shi kuma ya shiga lallaɓa abar shi sosai, kalamai suke musaya masu kwantar da hankali, duk da kowa da abunda yake cikin ran shi, amman ya bar abun a zuciya, dama kawai suke so su samu, kuma ta kuwa zuwa. Hafsat ce ta fara rutsa su, aiko ya sha caccaka, duk da take ba abokiyar wasan shi ba, sai ga Al'ameen ya zage ya biye mata, har Suhan na shigar mashi, nan ko suka yi ta raha da jin daɗi, har Hafsat ɗin na mamakin Ya Ameen ɗin, soyayyar Suhan ta cenza shi totaly. Sun jima kafin ya fita ya barsu nan tare, shima saida yayi ma Hafsat kandakon cewa ta kula mashi da mata, ko ƙuda baya so ya taɓa ta. ***************** Cikin kwana biyu jiki na yayi sauƙi sosai, kulawa nake samu daga both side sosai, har mamaki nake yi, Dad da kanshi yake shigowa har ɗaki gaishe ni da jiki, har fira ya kan tsaya muyi a lokutta da dama, masalan ma idan Al'ameen na kusa. A tsakanin ne kuma maganar komawar Nihal ta taso, ba yanda banyi a barni inje raka ta ba, aka hana ni wai nabi dokar likita dai. Umma da Hajiya Zainab ne suka je suka maida ta, sai Afnan da Hafsat, tasha kuka kaman ba ita ba, Nihal tayi sauƙi sosai, duk wannan halin nata, kaman an wanke mata shi tas, ta canza sosai kaman ba ita ba, godiya dai na shata sosai da sosai, sai gashi washegari Nureen ɗin ya Kira ni yana man godiya sosai. Kusan zamu iya cewa yanzu kanmu ya haɗu, mom na ɗauke ta a matsayin uwa kuma suruka, so nake na mance komai, kuma ina so na mance ɗin, Amman har sai Naji alaƙar dake tsakanin mu, wadda har ta sanya Al'ameen juya ma mahaifiyar tashi baya, bana jin daɗi, Sam, nasha alwashin yi mashi magana. kaman kullum Zaune take falo, riƙe da ɗan ƙaramin littafi na husnil muslim tana karantawa, tayi zurfi sosai a karatun na fito daga ɗakin nawa. Sallama ta kawai ta amsa, tana mai maida kanta ga karatun addu'on nata. "Umma sannu da hutawa" na faɗa, ina mai zamewa ƙasa na zauna sosai, na miƙe ƙafa ta. "Yauwa" kawai ta iya ce man ta maida kanta ga littafin. "Umma magana nazo muyi fa" ɗagowa tayi cikin kulawa sosai, sai kuma tace "Ko dai jikin ne?" Ɗan girgiza mata kai nayi, ina mai jin nauyin maganar da zata fito daga baki na. Saidai ya zama dole ne a gare ni, indai ina so al'amura su tafi man kaman yanda ake so. "To menene? Ko ɗakin ki kike son komawa?" ta sake tambaya ta. Kunya ce ta lulluɓeni, ƙasa nayi da kaina, ina wasa da ƴar ƙulalan doguwar riga ta, da akayi mata ado da stone sunyi kyau sosai, kuma sun haska ni sosai, dayake kalar ja ce. "Umma kiyi haƙuri in magana ta ta ɓata maki rai, banyi da niyya ba, saidai naga kaman lokaci yayi, Umman Dan Allah ki sanar dani wanene mahaifi na, sannan kuma wace alaƙa ce tsakanin mu da Mom ɗin su Ya Ameen?" Cikin sauri Umma ta sake kafe ni da idanu, kaman zasu faɗi ƙasa, sai kuma ta nisa, tana mai ɗaukar remote na Ac ta ƙara Ƙarfin gudun ta, tayi mamaki sosai, take taji iska ta dena shigar ta, sai wani irin zufa da ta ringa tsiyayo mata ta ko'ina. Bata taɓa tsammanin zan zo mata da irin wannan maganar ba, bata taɓa kawo ma ranta cewa nasan akwai wata alaƙa dake tsakani ba. "Uhmm" ta kuma nisawa, sai ta ɗauke kanta ga barin kallo na. "Mamana menene dalilin ki na zuwa mani da wannan maganar? Shin ban hane ki ba? Na rage ki da wani abu? Ko Dad ɗin ku bai cancanci maye gurbin mahaifin ki ba?" ta faɗa a hankali cikin wani irin yanayi. "Umma kiyi haƙuri nace, haƙiƙa Dad ya cancanci fiye ma da Uba, to Amman kinsan tsakanin mahaifi da ɗa, please Umma ki taimaka ki fada man, ko zan samu sauƙi, ko zan ji sanyi, ko zan samu amsoshin da nake son inji daga gareki, *shin Muna da alaƙa ta jini ne da Mom?"* "Ya isa Mamana, ki dena man wannan maganar, Mom Mahaifiyar take a gareki, kuma Suruka, ki barshi kawai a haka, bansan jin komai daga haka" Ta faɗa cikin ɗaga murya, tana mai miƙewa zata bar wajen, bata so Sam wani abun kuma ya taso, duk yanda ta lanƙwasa zuciyar ta, ba lallai Suhan ɗin tayi hakan ba, ta sani, bata so wannan al'amari ya shafi auren ƴar tata, amman sai gashi yau da kanta tana so ta tono Sirrin da ta jima tana ɓoye mata. "Umma ya kamata ace ta sani tun tuni, ayau zata sani, kuma ni ne zan sanar da ita..." Muryar ya Ameen ta karaɗe illahirin wajen, yayin da Umma taji ƙafar ta ta ƙafe ta kasa cigaba da takawa, da sauri Umman ta juyo, tana mai ƙafe Ya Ameen ɗin da idanu. Nima da sauri na yunƙyra na tashi, mamaki fal a cikin raina, cikin hanzari ya ƙaraso inda nake tsaye, yana mai tallafa ta ya mayar dani ya zaunar dani, yana mai jinjina man kai, ganin irin kallon mamakin da nake binshi dashi _"Mom ƙanwa ce a wajen mahaifin ki, kuma ɗiya ga ƙanen mahaifin naki Suhan"_ Ya faɗa cike da tabbaci, yayin da Umma tayi saurin saka hannun ta ta dafe dukkanin bakin ta, saboda bata taɓa zaton ya Ameen zai iya tona ɗanyen dakwayen da suka lulluɓe ba, na aika aikar kakan nashi, ga mahaifin Suhan ɗin.. ~Oum-Deedat ce~ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~88~* *_#Stay Home_* *_#Stay Safe_* *_#Wash your hands_* *_#Avoide over crowded place_* *_#Stop spreding the dx_* ************* "Son me ke faruwa ne nan?" Muryar mom ce dake tafe cikin ɗan saurin ta, hannun ta riƙe da waya tana latsawa, da alama kira ta gama amsawa ta hango su tana daga sama. "Ehem Daughter me ya faru ne?!" ta sake maimaitawa, tana mai bin jikin Suhan ɗin da take tsaye bayan ya Ameen da kallo. Hannun ta cikin nashi runtse, yayin da Maree ɗin ke zuƙunne tana sakin kukan Munafunci. Kafin ma tayi yunƙurin bata amsa, tsulum Maree ɗin tayi tana mai miƙewa, cikin kuka take cewa "wallahi Hajiya ban kula da ita ba, wallahi Hajiya ban ganta ba, buge ta nayi ban gani ba.." "Ya isa Maree" Mom ta dakatar da ita, fuskar ta ɗauke da mamaki, ganin Al'ameen tsaye, Amman miskilanci ya hana shi tankawa, ga wani irin kallon Maree da yake mai cike da tsana. "Wai me ke faruwa ne, Son kayi man bayani mana" Mom ɗin ta cigaba da faɗi, tana mai dakatar da Maree da hannu, wadda ta sake yunƙurin buɗe baki. "Mom duk abunda ya faru akan ido na ne, da gangan ta ture man ita, and kuma har ta isa tsayawa tana gaya ma Suhan magana, kinji wasu dirty talks da take faɗa ma mata ta. Kaman wannan yarinyar? Har tana cewa nan ba gidan ubanta bane..." "What?" Mom ɗin ta faɗa da ɗan ƙarfi, tana mai zaro idanu, sai kuma ta koma da kallon ta kan Suhan ɗin, sauke kai nayi ƙasa, to me zance ni? Ita kanta mom ɗin ta sha faɗa man hakan ai a gaban su, May be ma anan taji. "Je ki kira man Talatu" cewar mom ɗin, tana haɗawa da tsawa sosai. Ai da gudun ta ta ruga sahen nasu, har yanzu kukan take yi, bata taɓa ɗauka ƙwabar ta zatayi ruwa haka ba. "Sannu Daughter, baki dai faɗi ba ko? Baki ji ciwo ba ko?" cewar mom ɗin da turanci, tana ɗan dudduba jikin Suhan, wadda Ya Ameen Ya maida ta zuwa jikin shi, duk kunya ma ta cika ta. Saidai ga alama Mom ɗin ma ko damuwa batayi ba. Kukan da taji ɗiyar tata tana yi ne ya sanya ta yo waje da sauri, zani a hannu, duk a zaton ta, cikin ƴan aiki ne wasu suka ɓata ma Maree ɗin. "Ke dalla yi man shiru, muje inji wane shegen ne ya taɓa ki a cikin gidan nan? Har zaki wani tsaya yin kuka, bayan kinsan ko ke wacece anan gidan" ta faɗa da ƙarfi, da Mama Saude take, dama jiya sun samu saɓani, akan abincin da Mama Sauden ta zuba masu, wai bai ishe su ba, ita kuma tace bata ƙarawa, dama haushin Talatun take ji, irin yanda take zuba masu mulki da isa, kaman itama ba matsayin ƴar aiki bace. But Mama Saude tayi itama, tana fitowa daga ɗaki, take sakin guɗa ƙarama. "Ahayye nanaye, Allah mun tuba, yo ai sai ki faɗa mana matsayin ta, wanda ya wuce ƴar aiki kaman mu? Kafin ma tazo ga aikin wace irin rayuwa ce batayi ba? Munafukai ku duka, uwa da ɗiya ba zuciyar arziƙi, kun ɓoye mana ku su wanene ada, to dai a sani, mun san shafe shafe mun san kala, ah to ehe! kuna fakewa da hajiya kuna aikata duk abunda kuka ga dama, mugun abunku zai koma kanku da yardar Allah!.. " " Kinga Saude ki fita a ido na, naga take taken ki fa, wallahi summa tallahi zanyi sanadin barin ki gidan nan, kinsan na isa, zan kuma iya.. "" Yo kin isa mana, kaina farau? Kafin ni ma'aikata nawa kika saka aka kora da munafuncin ki da tuggun ki? Sai dai ni na riga ki nace Allah, nan gani nan bari wallahi, duk abubuwan da kika saka muka aikata da wallahi nayi nadama, na gane kafurar zuciyar ki, kinso ki ingiza ni, Amman dayake na riga ki nace Allah, sai Allah ya fidda ni, ko akan Hajiya Maryama ya kamata ace kin ɗauki ishara, kin ɗauki darasi, gashi yanzu ta haye ta barki, a matsayin da ke kike hange, dayake ita mace ce mai gaskiya da haƙuri, ba ruwan ta da Munafunci irin na ki, ta aure Alhaji, ɗiyar ta ta aure alhaji Ƙarami, wand akuke ta mafarkar aura, saboda ku samu abun duniya, sai gashi wai saboda daƙiƙancin ku, gani kuke har wannan sandar ɗiyar taki zata iya sace zuciyar Alhaji Ƙarami, har ma ta aure shi, ku mallake gida, duk abunda kuke yi suna tafin hannu na, kuma lokacin da zaku shuke abunda kuka... Ehoo an dai ji kunya, ɗiyar cikin ki, ki zauna tana mulka, ki, kuma wai har kice so kike muyi maki biyayya, ki mulka mu kaman ƴaƴan cikin ki" Kuka Maree ta sake fasawa, jin muryar Mom tana ƙwalwa ma Talatun kira da ƙarfi, kaman tana dosa dashen nasu "Wayyo Allah na! Mama Hajiya Babba ce ke kiran ki fa, ni kin wani tsaya kuna faɗa kaman kaji" " Ke dan Ubanki ba zaki bari na ƙwatar maki ƴancin ki ba wajen wannan munafukar matar ba?" mama talatun ta sake daka ma Maree ɗin tsawa. "To ai wallahi sai ki tsaya kiyi ta yi ni zanje ince mata baki zuwa, baki san masifar da ta tunkaro mu ba ne, kizo muje kawai" ta faɗa cikin gatsali, tana jan hannun Mama talatun kaman ba mahaifiyar ta ba. "Ko inzo da kaina ne?" muryar Mom ta sake amsa amo cikin ɓacin rai. Da sauri Mama talatin tabi bayan ta, tana faɗin "Na shiga uku, yau kuma me kika jawo mana ni Talatu? Mariya baki jin magana dan ubanki, nace kar ki aikata komai, Amman saida kika je kika aikata, aiko dan Ubanki saidai ki bar gidan nan, ina zaman zama na, ina cin Arziƙi da daula ta, kika zo kika fara dagula man lissafi" "Ko ma me zakice saidai kice, wallahi indai na bar gidan nan kema sai kin barshi, ai ke kike bani goyon baya duk abunda nake, ba kece kike zuwa.." Wata irin wafta ta kai ma bakin, aiko taci sa'a ta samu bakin sosai, tuni ya dare, dama gashi ba cikakkar tsafta, jini yayi tsartuwa. Wani kukan ta sake saki, tana cewa" Kan bala'i.. Ni kika fasa ma baki? Ai wallahi duk Abunda kike yau sai na faɗa, kwarankwatsi dubu kuwa" daidai lokacin da suka idasa inda su Suhan ɗin suke tsaye. Da wani irin mugun kallo Mom ta bisu, ba tun yanzu ba, duk in Mom tayi ma mai aiki irin wannan kallon, sunsan da matsala, cikin Mama Talatu ne ya hautsina, daidai lokacin da taji muryar mom cikin ɓacin rai tana ce mata "Ke kika ba wannan yarinyar damar haɗa kafaɗa da zuri'a ta? Nace ke kika ce masu matsayin su ɗaya da ita anan gidan?" Mom ɗin ta faɗa, tana nuna Suhan da hannun ta kai ɗauke da waya. "Wah ni Hajiya? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Wallahi tallahi bansan me ta aikata ba, ina ja mata kunne hajiya wallahi sosai, dan Allah Hajiya kiyi haƙuri, ɗan yau ne ka haife shi baka haifi halin shi ba.." dakata Talatu, kina ja mata kunne akan me? Kinsan tana da shirin aikatawa kenan?" cewar Mom cikin wani ɓacin rai ɗin. "Wallahi tallahi Hajiya.." sai kuma ta saka kuka sosai, tana mai rufe Maree ɗin da duka, tana yi tana kuka sosai. Gyara tsayawa Ya Ameen yayi, yana mai soke hannayen shi duka cikin aljihun shi, yana mai watching wata drammer mai ban dariya. Saidai fuskar shi sam a turɓune take, babu ko alamun murmushi akai. "Ya isa, dakata dena dukan ta, ai ta aikata abunda take ganin daidai ne, kuma sanin kanki ne, daidai yake da taka doka ta anan gidan, ban haɗa yara na da kowa ba, *Suhan ƴa ta ce* kuma ba zan taɓa lamuntar duk wani abu da zai faru da ita ba, masalan ta ɓangaren ku, idan da kuna ganin ta kaman matsayin ku, dama tun cen ba ɗaya kuke ba, ke kanki kin sani, kinje kin ga asalin ta, nima kuskure na aikata, kuma na amshi kuskure na, kuma ina kan gyarawa, ba zan lamunci wani yazo ya ɓata mun lamari ba. Nan gida na ne, kuna zaune ne a ƙarƙashin na, kuna aikata abubuwa da ya kamata ace na kula tun tuni, duk wani mugun hali da mariya ta ɗauka, a wajen ki ta gada, dan haka ba zan iya ci gaba da zama daku ba a cikin gidan nan, kuyi hanzarin tattarawa ku fice man daga gida, tun kafin dare yayi maku" Mom ɗin ta faɗa cikin kakkausar murya, ba abunda ya Ameen yace, da idanu kawai yake binsu, Suhan ɗin ma haka, wadda yanzu Mom ta saka hannu tana mai janta zuwa nata jikin, Idi, da Mudi da Iro, duk suna daga nesa kaɗan suna kallo, masalan Iro wanda ya tattakura ya ɗora hannu bibbiyu a saman kai. Ji yake kaman ya idasa wajen ya ɓaɓɓalla ma Hajiya Mari, ganin yanda take ma Surukar shi, da kuma masoyiyar tashi. Da sauri Umma ta ƙaraso wajen, jikin ta sanye da Hijab mai tsawo, bayan ta kuma haɗiman ta ne, wanda suka sanar da ita abunda yake faruwa na cewa Hajiya Babba ce, da su Suhan a wajen, dalilin fitowar tata ma kenan, take faɗin "Lafiya dai ko? Hajiya me yake faruwa, tun ɗazu nake jiyo hayaniya haka?" ta maida akalar tambayar tata ga zuwa Mom. Cikin ɓacin rai ta sanya hannu ta nuna Maree, wadda har yanzu uwar ke dukan ta, tana yi tana fyace majina. "Mariya mana, wai ta ture Suhan, har ita wacece da zata haɗa kafaɗa da yara na? Bata kula ba ita kaɗai bace, Allah ya taƙaita abun ma, da ai ba haka ba" mom ɗin ta bata amsa cikin kulawa sosai, har yanzu fuskar ta da ɓacin rai. Ɗan murmushi Umma ta sake, sai kuma tace, "To ai Alhmdllh tunda ba abunda ya faru, ke Talatu bari dukan nata haka, ai tunda Allah ya tsare, sai a kiyaye gaba kuma" ta faɗa, tana mai juyawa zata bar wajen. Da gudu Mama Talatu ta sha gaban ta, tana mai zubewa ƙasa, Dan Allah Hajiya kiyi man rai, ki ba Hajiya Babba haƙuri, wallahi ba da saka hannu na ba ta aikata, yanzu da akace in bar gidan, ina zani? Wa ke gareni? Ina zan dosa da wannan budurwar ɗiyar haka?" Cikin mamaki Umma ta saka hannu, tana mai ɗago ta sama sosai take kallon ta." Wa yace ki bar gidan ne?" Ummn ta tambaya, tun ma kafin ta idasa, ta tari numfashin ta," Hajiya ce wallahi Maman Suhana, ban san mariya zata aikata wannan ɗanyen aikin ba... " Juyawa umman tayi sosai gaban Mom. Tana mai cewa "Ayya hajiya, Haba, wannan ai bai isa yasa ace su bar gidan ba, a gode ma Allah da ba abunda ya faru ma, sai a kiyaye gaba, kiyi masu haƙuri dan Allah komai ya wuce, itama Suhan ɗin sai ta kula nan gaba" Kallon ta Mom tayi, tana mai girgiza kai, "Ke zan ba haƙuri Gimbiya, lallai fa dole zasu bar gidan nan, na gaji, dama ya kamata ace tuni na sallame su ɗin, sun aikata abubuwa da hankali ba zai ɗauka ba, haɗa ita kanta talatun, to zaman me zan sake yi dasu kuma a gidan? Nan gaba ai sai su nemi rayuwar ɗiyar tawa" cewar Mom. Itama Umman girgiza kai ta shiga yi " Subhanallah! Hakan ma ba zata faru ba, in sha Allahu, ki dai yi masu haƙuri, ai ya riga ya wuce, kuma duk abinda mutum ya aikata, kanshi yake ƙarewa" itama Umman ta faɗa. *"Ai saidai kuma wani, dama tuni ta aikata, wannan ma Ƙarami ne"* muryar ya Ameen ta karaɗe wajen cikin kakkausar sauti, karo na farko kenan tun zuwan Umma wajen. Da sauri kowa ya kalle shi, mamaki cike fal a fuskar kowa. Wani irin ihun kukan Mama Talatun ta sake saki tana mai dafe kai, "Na shiga uku na lalace ni Talatu, mariya tur da haihuwar ki, wallahi haihuwar ki bata amfana man komai ba, haihuwar ki batayi man rana ba, da haihuwar ki gara ɓarin ki wallahi, Allah dai ya tsine...." "Ke Talatu, akul ɗinki da tsine ma ɗiyar ki, ko me ta aikata ki mata addu'a shine mafita" Umma ta sake tarar zancen daga bakin Mama Talatun. Dama tasan za'a rina, tasan za'a aikata, wannan ranar tana zuwa, irin tuggun da Talatu ta haɗa mata, ai Allah ma ba zai barta haka ba. "Son me ta aikata kuma wanda baka faɗa mana ba tuni?" cewar Mom, daidai lokacin da sauran ma'aikatan suka fito da gudun su, jin koke koke yayi yawa, da kuma hayaniya. Ganin me ke faruwa ne, ya sanya Mama Saude sakin dariya sosai, tana mai cewa "Kin gani ko Talatu? Kina ɗauka Allah na barci ne? Nace mugun abunki a kanki zai ƙare, ko haƙƙin wannan baiwar Allah ɗin ba zai ƙyale ki ba" ta ƙarshe tana mai nuna Umma. Nan wani sabon Al'amari ya sake faruwa, da mamaki kowa ke bin fuskar Sauden da kallo, me kenan? Me Saude ke nufi? "Ke saude me kike nufi kuma?" cewar Mom, da sauri kuwa saude ta amshe "Ai Hajiya, wannan da kike gani.." Ƙarar horn da ya cika bakin gate, shi yayi sanadiyyar dawowar kowa cikin hankalin shi, dama tuni Afnan tayo waje da gudu itama, tana tsaye kusa da Yayan nata. Abun fa kaman a mafarki, watau yau ranar tone tone ce. Motar Alhaji Mustapha Dambulan ce ta kunno kai. Ganin kowa tsai tsaye, ya sanya shi saurin fitowa, da sauri ya nufi inda suke cirko cirko, ga Maree da Mama Talatu durƙushe suna kuka bil haƙƙi da gaskiya. "Lafiya dai ko? Me yake faruwa ne anan haka?" shima kalmar da ya faɗa kenan, yana gyara zaman babbar rigar shi. "Mugun abun da suka daɗe suna aikatawa ne ya fito sarari yau kowa ya gani, Talatu kinji kunya, ashe mun daɗe kuna ƙulla mugun abu ban sani ba? Ashe duk gulmace gulmacen da kike kawo man ƙarya kike yi? ashe makasa ta kike nema ban sani ba?" Mom ta faɗa cikin kaushin murya, har wani haki take yi. Har yanzu Alhaji bai gane maganar da suke yi ba. Al'ameen ya kalla domin neman ƙarin bayani, ganin shi kaɗai ne namiji wajen, kuma yasan zai fi samun gamsasshen bayani a bakin shi, duk kuwa da cewa wani lokaci idan Mom ɗinshi na aikata ba daidai ba, ya kan tsawatar mata, sai gashi yau yana tsaye a wajen komai yake faruwa, ya saka masu ido, yana binsu da kallo. Shima fuskar tashi ko annuri kuma babu, ga matar shi rungume jikin Mom ɗin tashi. "Dad wannan yarinyar ce ta ture Suhan, sannan ta tsaya tana gaya mata maganganu marasa daɗin ji, wannan ya sanya Suhan ɗin ta mare ta, shine itama zata rama, Beside dama cen akwai wani abu da ya faru da ban faɗa ma kowa ba. *Mariya ita ce ta saka ma Suhan ɓawon Ayaba kwanaki ta kusa faɗuwa, sannan bana tababar da saka hannun ta, wajen faruwar abunda ya faru da Suhan kwanaki ma* " Salati da sallallami kowa ya saka, hada Mom kuwa, ita dai Umma dama ta san zasu iya aikatawa, sai abun bai bata mamaki ba, mamakin ta guda kawai, menene haɗin Suhan da mariyar da har zata iya aikata mata haka? Shi kau Alhaji Mustafha, gilashin idanun shi ya zare, yana mai bin yaron nashi da kallo, gyaɗa mashi kai yayi cikin tabbatarwa. Wuf Mama Talatun ta sake yi, tana mai ƙara rufe Maree da wani sabon dukan iya ƙarfin ta. "kin cuce ni, kin cuci rayuwa ta, rashin imani na baikai haka ba Mariya, na faɗa maki ki ƙyale yarinyar nan hakanan, ki ƙyale Alhaji Ƙarami tunda yayi aure, ita ce matar shi, ba zai so ki ba, ba zai aure ki ba, kika ƙi ji, kika ƙi gani, gashi yanzu abunda kika jawo mana, gara in kashe ki wallahi, da nasan haka zaki aikata mana, da tun da na haife ki na shaƙe ki kin mutu wallahi" ita kuwa Maree sai zunduma ihu take yi iya ƙarfin ta, tana faɗin "na shiga Uku na lalace, wallahi ina sonshi, ba zan iya rabuwa dashi ba, wallahi ba zan iya ƙyale shi ba ina kallon shi da wata, kin ƙi ki aura man shi, dole in ƙwaci abu na da kaina" Cikin wari idanu Ya Ameen ke kallon ta, me take nufi? Ba dai wannan kalaman a kanshi take sake su ba? Ko dai Iro wanda tuni ya same shi da maganar yana son Mariyar? Suhan kuma ƙasa ta sake yi da kai, ba tun ya zu ba tasan Maree na son Al'ameen, ba tun yanzu ba ta kula da take taken ta, saidai bata san abun har zai iya shafar lafiyar ta ba, a ƙoƙarin ƙwace shi da akeyi daga gare ta ba. "Ya Isa hakanan" cewar Alhaji Mustapha. "wannan ba maganar da za'a yi anan bace ba, zamu iya zuwa mu zauna ko? Ko zamu iya gano daga ina matsalar take" ya ƙarashe, yana mai wucewa ya nufi sashen shi. Alamun a ciki za'a zauna kenan. "Ku kikkira kowa ya same mu sashen Alhaji, banda mai gadi" cewar Mom ɗin, tana mai juyawa riƙe da hannun Suhan ta nufi sashen Alhajin, inda dama Umma tuni ta bishi a baya, saboda yau aikin ta ne, ita ce zata kula da Alhajin, saidai zuciyar ta fal da damuwa, Suhan kaɗai ta mallaka, ashe duk kawaicin da take masu, su hankalin su yana ga kan neman rayuwar ta, bata jin ko ita a wannan karon zata iya bada haƙuri, ga duk hukuncin da ya dace dasu. Matsawa yayi sosai, yana mai share ma Afnan ɗin hawayen ta, sosai take ƙwalla, jin irin abubuwan da suke faruwa. "is ok Lil, ya isa, kukan na menene?" ya faɗa, "Yaya kaji fa abunda take faɗi, wai kai take so? Yaya ashe duk abunda ya samu Aunt Suhan Maree ce?" ta faɗa mashi, wani sabon ƙwallr na gangaro mata. "Common dear, wipe your tears ki dena kuka saboda ita, she will collect her result today, i dont want see you crying autar Mom" shima ya faɗa mata, hada ɗan murmushi ƙarfin hali, yana son ƙanwar tashi sosai, yana jin ta a jinin jikin shi, komai zai iya yi saboda ita, balle tana daga cikin wadda ta fara buɗe mashi ƙofar son matar tashi Suhan. "Lets go inside dear" ya sake faɗa, yana mai jan hannun ta shima suka nufi sashen Dad ɗin, gabaki ɗaya zuciyar shi a cunkushe take. Idan ba gani yayi sun bar gidan ba, ba zai kuma samun kwanciyar hankali ba. Wayar shi ya lalubo a aljihu, yana mai lalubo video ɗin cctv ɗin da yayi trnsfer nashi zuwa wayar tashi, domin ya zame mashi shaidar abunda ya faɗa a gaban Dad ɗin nashi. Da ƙyar Mama Talatun ta ɓaɓɓaka, tana mai sake sakar ma Maree ɗin rankwashi sosai a saman kai, dama fuskar duk ba kyaun kallo ga baki ya kumbura suntum, dukan da tayi mata na farko, wani kukan ta sake saki, ko me za'a yi mata saidai ayi mata, Amman ayau dole a bata ya Ameen, ba zata iya haƙura dashi ba, miji na kere sa'a, miji ɗan uban su, ga kyau ga naira. Sauran ma'aikatan fa duka ciki ya ɗuri ruwa, ba'a taɓa yin irin wannan zaman da za'a yi ba yau, na ƴar turke, ƴar tone tone, dukkan wani wanda ya san ya taɓa ƙulla mugun abu a cikin gidan, yau ya tabbatar da cewa kashin shi ya bushe... ~Oum-Deedat ce~ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~89~* *Ina Barar Addu'a da bakunan ku masu albarka* _Allah ya cika man buri na indai da alkhairi, in kuma babu, Allah ya musanya man da wata hanyar, Allah ya zaunar da mu da ƙasar mu lafiya ya ƙara kare mu tare da kiyaye mu Ameen_ *_#Stay Home_* *_#Stay Safe_* *_#Wash your hands_* *_#Avoide over crowded place_* *_#Stop spreding the dx_* *Dan Allah a zauna gida, ayi addu'a Allah ya buɗo hanyoyn alkhairi, Allah yasa mu fi ƙarfin abin da zamu ci, zamu sha, zamu suturta da kuma muhalli. Ameen* ****************** Sama sama kake jin kukan Maree, har kai lokacin da kowa ya natsu ana son jin ta bakin Alhaji. Gyaran Murya Dad yayi, yana mai kallon Mom, "Hajiya ina so insan abunda yake faruwa a cikin gidan nan, tun daga farko, wanda ni kaina ban sani ba, ko kuma nace baki sanar dani shi ba tun tuni" Ya faɗa, yana mai tattara natsuwar shi a kan Mom ɗin. Zaune yake bisa kujera mai cin mutum biyu, gefen shi Mom ce zaune, yayin da nake ƙasa saman carpet zaune bisa ƙafafu na, har yanzu hannaye na cikin nata ta ƙi ko ta saki. Gefe kuma Umma ce bisa Kujera mai cin mutum ɗaya, yayin da shima Ya Ameen yake zaune bisa kai cin mutum ɗaya ɗin (One seater) Afnan na gefen shi bisa hannun kujerar zaune. Kaman an jera su suna neman gafara, haka sukayi layi zazzaune tanƙwashe da ƙafafu, ɗaukacin ma'aikatan gidan ne, wanda mata zasu iya kai su bakwai, sai maza uku hada mai gyara lambu da bargar dawakai. "Humm! Alhaji wannan duk ita ce silar faruwar komai, kaman yanda na faɗa maka a ɗazu, Talatu tun ba yanzu ba take kitsa Munafunci a cikin gidan nan, ba tun yanzu ba Talatu ke da mugun nufi a kaina da zuri'a ta ba, duk ban fahimta ba. Hasalima ita ce mace ta farko da ta fara saka man tsanar Maryama da ɗiyar da tazo da ita, hakanan kuma ita ce ta fara kawo man ƙananan gulma ce gulmace a zuwan duk dan son da take yi man, ita ce idanu na a cikin gidan nan, haka duk tsegumn da zai taso daga gareta ne. Ta ɓoye mana cewa mariya ɗiyar ta ce, sannan ita ce ta faɗa man cewa Maryama ta mallake Al'ameen sai abunda take so yake mata, sannan ta faɗa man tana son auren ɗa na su mallake shi suma, kuma ita ce ta taɓa faɗa man cewa yaro na Al'ameen da Suhan suna aikata masha'a a ɓangaren shi, Suhan ɗin ke kai mashi kanta wai.. dalilin da ta sanya na ƙara tsanar Suhan da Maryama kenan, ko menene ya faru dai ita ce sila" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" gabaki ɗaya falon aka saki salati a tare, wasu daga cikin ƴan aikin ma hada tafa hannuwa suke, suna mai riƙe baki alamun mamaki, yayin da ita ma ta fasa wani uban kuka tana salati, shi kuwa Ya Ameen kaman zai faɗo ƙasa saboda masifar ya da yaji hankalin shi ya kaɗu matuƙa... Shi? Shi akayi ma wannan sharrin? Shi akayi ma wannan ƙazafin? Shi aka laƙa ma sharrin zina? da jajayen idanun shi da suka kaɗa a lokacin kaman wuta ya shiga kallon mama Talatu da ta ɗora hannu bibbiyu saman kai tana faɗin "na shiga uku na lalace, wayyo ni Talatu da ganin wannan rana gara mutuwa ta, na bani na lalace, shikenan ni Talatu tawa tazo ƙarshe" "Yi mana shiru munafuka, yau ne asirin naki ya tonu, bayan nan ai kin faɗa man maganganu masu yawa sosai, nace ko ba kece kike gaya man cewa Maryama wajen boka take zuwa ba? Shin ba da sanin ki muka je wajen malamai aka yi ma su Maryama kurciya ba? Ke da su Sa'a da Hajiya Laila? " Wani salatin aka sake saki, yayi daidai lokacin da Suhan ta saki wani marayan kuka, tana yi tana girgiza kai, ita kuwa Umma sauke kai ƙasa tayi, cike da takaici, ita kanta Mom ɗin ai taji kunya ta fito bainar jama'a da ƴan aiki tana faɗin taje wajen boka saboda ƴar aiki, wanda babu Abunda suka iya yi daga ƙarshe kuma. Da hannu bibbiyu ya tallafa kanshi, ji yayi kaman zai faɗo daga kan kujerar, duka ƙafafun shi ya haɗe, yana jin wata irin jinjiga na taso mashi, tun daga cikin ɓargon shi, so yake ko ɗigon hawaye ne ya zubo mashi yaji sauƙi, fuskar shi ta yi ja sosai har kumbura tayi, kaman an ɓaɓɓalla mashi mari. Duka idanun shi a kulle suke. Mahaifiyar shi da zuwa wajen boka? Mahaifiyar shi da yi ma wani asiri? Shi Al'ameen? Ina ma ace baiga wannan rana ba? Wace irin kunya ce yake fuskanta haka? Da wanne ido zai kalli Surukar shi da matar tashi? Itama Afnan hawaye ta fara yi, Mom ɗinsu ta aikata abubuwa da dama, ba dan ta riga ta tuba ba, da zata iya cewa tana danasanin fitowa daga tsatson ta. "Ya isa hakanan hajiya, duk naji wannan, gaskiya ke Talatu kin aikata ba daidai ba, kuma babu..." "Alhaji ba iya abunda ta aikata kenan ba.. Nima ina da magana" muryar mama saude ta karaɗe ilahirin falon. Da sauri kowa ya maida kallon shi akan fuskar Sauden, ciki kuwa hada Mama Talatu. "Dan Allah Talatu ki rufa man asiri, ki bari inji da wannan abun Kunyar da na aikata tsawon rayuwa ta.." mama talatun ta faɗa, tana mai yarfa ma Saude hannuwa alamun roƙo. Ko kallon inda take bayati ba, ta shiga cewa "Ta sha alwashin sai Mariya ta auri Alhaji Ƙarami ko ta halin yaya, daga baya su kashe shi, su kashe ka, su kashe hajiya su ci dukiya, kuma sannan ta sha aika Mariya sashn alhaji Ƙarami da niyyar ko zata ribace shi ya aikata masha'a da ita, daga ƙarshe ta samu ciki tace shine, kuma ko a lokacin da take zuwa ɗin, tana da ƙaramin ciki, da sun samu nasarar Alhaji Ƙarami, babu Abunda zai hana suce cikin nashi ne, shine yake neman mariyr, kuma shine ya lalata mata rayuwa, da suka ga haƙan nasu bai cimma ruwa bashi, shine suka ɓarar da cikin. Bayan haka, Umman Suhana kiyi haƙuri, duk hana ki abinci da muke yi a cikin gidan nan, lokacin zaman ki tare damu, wallahi Talatu ce ke hanawa, kuma ta sha bada abu a saka maki cikin abinci, tace ai magani ne na zafi Hajiya ta bada tace a saka maku, saboda baku da lafiya, shiru shirun da ake ganin kike yi, ba na lafiya bane. Sannan tabbas Mariya ce ta saka ɓawon Ayaba a sashen Uwar ɗaki na Suhana. Akwai ranar da na taɓa tadda mariya waje ita da wani suna magana, sai na laɓe bayan flowers Naji tana cewa "Haka dai Hajiya Laila ta bata umurni, kuma zata cikashe mashi kuɗin shi, ya tabbata idan Baba mai gadi ya tafi masallaci ya shiga sashen Suhanan ya ajiye abun daidai inda ta umurce shi. Idan ya kammala aiki zata cikasa mashi kuɗin shi.." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" falon ya kuma sakin wani salati da ƙarfi. Warwas Talatu tayi a tsakiyar falon kaman matatta, da sauri Afnan ta ɗauko ruwa a fridge ta ƙwara mata, tashi tayi kaman mai aljannu, tana mai hawan Maree da duka "Dan uwar ki dan ubanki ni zaki tona ma asiri? Gara ke in tona maki tun kafin ke ki tona mani, dama dole ki gado mugun baƙin abu, tunda ubanki ya ɗirka man ciki, ban sake ganin shi ba, ko jin ɗuriyar shi, na gudo na barki, daga baya tausayi irin na ƴa da uwa na kasa barin ki, yanzu shine zaki zo ki nemi tona man asiri.. " " Ya isa Talatu" Alhaji ya faɗa cikin ɓacin rai, tun da nake da Alhaji ban taɓa ganin ɓacin ran shi irin yau ba. Muryar shi har wani amo take fidda wa mai cike da Zallan ɓacin rai. "Son zuciya son kai ya maki yawa, banga dalilin dukan nata ba Talatu" cewar Umma, a karo na farko da ta saka baki. Sannan ta cigaba da cewa "A zama na daku ba zan iya cewa komai ba, illa iyaka duk wadda tasan ta cutar dani, na barta da Mahalicci ta, haka kuma rayuwar ƴa ta da kuke nema, ta Allah ba taku ba, kuma shi Munafunci dodo ne, haka kuma ance in zaka gina ranun mugunta.. Yanzu gashi kin faɗa ciki, kinzo kina mana kuka da birgima, bayan duk nan cikin mu, ba wanda zaki iya ba tausayi." Umma ta ƙarashe itama cike da tsantsar ɓacin rai shimfiɗe a fuskar ta. Shiru falon yayi, sai kukan Maree da Mama Talatu inda sai ƴan ƙananan maganganu ke tashi, shi kanshi Alhajin ya koma ya jingina da kujera, ya ma rasa abun cewa. Duk kyawon halin ka, duk kyawon zuciyar ka, sai ka samu wani da ke neman ganin bayan ka. In ba haka ba, wace irin kyautatawa ke bai masu? Wace irin kulawa ce Al'ameen baya basu? Saboda su Sam yaƙi aiki ƙasar waje, saidai jefi jefi, saboda yaga ya kyautata ma na ƙasa dashi.. Sai gashi wai ace na ƙasa dashi ɗin ne ke haɗa masu tuggu da har suke son ganin bayan matar shi, ta hanyar haɗa baki da maƙiyan su da a yanzu suna gidan gyaran hali. "Ka dai ji ko Alhaji? Ka ji abunda duk suke aikatawa ko? Lokacin tonon asirin ta ne yayi, na gode ma Allah daya haska man na gane wacece ke Talatu, bama ke ba, duk wanda nake tare dasu da babu alkhairi a rayuwar su, Allah ya raba ni dasu, ina fatan kuma tuban da nayi ya zame man izina da ishara, kuma ya sanya shine silar daidaituwar al'amari na. Umman Suhana ki yafe man, na aikata ba daidos ba, na aikata kuskure, tare da jagorar wasu sheɗanu a cikin mutane. Amman yanzu na gane, ban ɗauke ki a matsayin kishiya ba, na ɗauke ki a matsayin ƙanwa ta, kuma ƴar uwa ta, mata a wajen Yayana Muhammadu, kuma mata a wajen miji na, insha Allahu sai kowa yayi mamaki na, tabbas na gane yanda rayuwa take, ashe masoyi ka zai iya komawa maƙiyin ka, haka kuma maƙiyin ka zai iya komawa masoyin ka, kada ka yarda da kowa ɗari bisa ɗari, kuma ka kyautata ma mutane zato, sannan addu'a ita ce makamin mumini, ita ce zata warware komai." Ta ƙarshe a sanyaye, fuskar ta fall da damuwa, ɗauke da tarin nadama Ɗan girgiza kai Umma tayi" Ba komai Yaya, ni dama ban riƙe ki ba, nasan ba yin kanki bane, Allah ya yafe mana baki ɗaya" Da yayi niyyar buɗe cctv video ɗin, sai ma yaga ai baya da amfani, baya da dalili ma, me zai nuna? Bayan ta tabbata sune ummul aba'isin faruwar komai? Da gefen ido yake kallon ta, yanda take ta share ƙwalla akai akai da bayan hannun ta. Ta bashi tausayi, ta ga rayuwa kala kala, ta ga iftila'i iri iri, tausayi take bashi, ji yake kaman yaje ya rungume abar shi, just to melt her anger. "To Alhmdllh muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan rana, a haƙiƙain gaskiya muna baki haƙuri Talatu, duk Abunda kuka aikata dan kanku, mu dai Allah ya sani mun zauna da ku har zuciyar mu, mun zauna daku da zuciya ɗaya, ashe ku daga gareku ba haka bane, bamu rage ku da komai ba, masalan ma shi yaro na Al'ameen, yana iya ƙoƙarinshi a kanku, ashe ku bayan mu kuke son gani? Ashe mu tarwatsewar mu kuke son gani? Ashe ku ba da zuciya ɗaya kuke zaune damu ba. Ashe dukiyar mu ta tsine maku ido? Ashe bayan mu kuke son gani ku mallake duk abunda yake halalin mu, mukayi aiki ba dare ba rana muka samu, wanda da shi ne muke duk iya ƙoƙarin mu, wajen ganin mun kyautata maku. To anan dai babu abunda zan iya cewa sai godiya, kuma kuje mun barku da halin ku, zaku samu daidai daku nan gaba, da wannan nake cewa ba zamu iya ci gaba da zama daku ba anan gidan, zaki tattara kayan ku ku tafi, yau yau ba sai gobe ba, yanzu yanzu ma, saboda har ga Allah idan akwai abunda na tsana a duk faɗin rayuwa ta shine cin amana, ku kuwa kun aikata babbar cin amana. Dan haka ba zamu iya cigaba daku ba" Wani kukan ta sake ɓarkewa dashi, tana mai sake shemewa ƙasa take roƙon Alhaji Mustapha ɗin cikin kuka "Alhaji kayi mana rai, kayi mana aikin gafara, na tuba, ba zamu sake aikatawaba, idan ma tafiyar ce na yarda ita Mariyar ta tafi, Amman ni a barni nan Alhaji shekara da shekaru ina tare daku nan, Amman rana tsaka kace in tafi, bansan ina zani ba, bana dakowa dangi na ƙauye duk na guje su, banda kowa ba zan iya tunkarar su ba" Hannu ya ɗaga mata, "ya isa, na gama yanke hukunci ku tashi kuje, sannan ke Saude kema ba zamu iya cigaba da zama dake ba, saidai zaki iya samun Al'ameen domin asan abunda za'a iya yi maki, alabasshi ko Sana'a ce zaki iya kamawa, saura gareku, ya ishe ku izina hakan, duk wanda ya kuskura ya sake aikata wani abu makamancin hakan ba iya sallama ba, hada abu marar daɗi da zai iya biyo wa baya, fatan zaku kiyaye" Alhajin ya sake faɗa, yana mai gyara zaman shi, tare da ɗaukar cup ɗin ruwa yayi sipping biyu. Jinjina kai Mom keyi, cike da gamsuwa da hukuncin Dad, dama itama shi ta zartar, na su bar masu gidan nasu, abun mamaki kuwa shine ko Umman batayi yunƙurin bada haƙuri ba, ita kanta zuciyar ta zata fi Aminta da hakan, muddin suna cikin gidan ba zata iya sake wa ba, masalan ga al'amarin ƴar ɗiyar tata, da tasha wahalar rayuwa. Idan har Dad ya yafe masu, shi baya jin zai iya, korar su kaɗai ba zai gamsar dashi ba. Karo na farko shari'a zata fara shiga tsakanin shi da ma'aikatan shi, kai harma da wani a rayuwar shi, in bayan da ka ɗauke wani matashn mai kuɗi shima da ya kunno kai, yana niyyar yaƙar Al'ameen ɗin, shima ya nemi rayuwar shi kaman me, kafin ya kai ma shari'a abun ta shiga tsakanin su, to shi Wancen ma ya haƙura ya janye, ya gane ba zai iya ƙarawa da Dambulan ɗin ba, ga komai ya zarce shi, ya kuma kere shi, dan dole yayi mubaya'a suke kasuwanci tare, yana siyan kaya daga kamfann Ya Ameen ɗin. Miƙewa yayi cikin azama da niyyar ficewa, baya ma so abun ya ɗau lokaci, gara tun da zafi zafi ya hukunta su, daidai da laifin da suka aikata. Kowa da kallo yake binshi, babu wanda yace mashi kanzil, har kai lokacin da ya kusa idasa ficewa, wanda nima da kallon na shiga binshi, tabbas ko da ganin fuskar shi yana cikin wani hali ne. Gam yaji an riƙo ƙafar tashi ta baya, juyawar da zaiyi ya haɗa idanu da Maree, durƙushe cikin kuka take cewa "dan Allah Alhaji Ƙarami kada ka barni, duk dan kai nake aikata hakan, sonka zai iya kashe ni, zan mutu muddin baka aureni ba, wallahi zan zauna dakai a duk halin da kake ciki, ni dai ina sonka, kana da kyau, kyawon hali kyawon zuciya, ga tausayin na ƙasa dakai, duk hanyar da zanbi in same ka, wallahi sai na bita, muddin zan cika buri na, barin gidan nan ba damuwata bane, damuwa ta rashin ganin ka da zan dena tunda har ƙarƙashin gada na kwana, Amman fa ka sani ba zan iya rabuwa da soyayyar ka ba, indai ina raye" Gudar ƙafar ya sanya ya halba ta gefe, har tana ƙume kai da bango. Juyowa yayi sosai yana mai fuskantar ta. "Ko da ace bana da mata ta nuna ma sa'a, koda ace bankai yanda nake ba, koda kuwa ace ni ɗin mummuna ne, bazan taɓa iya haɗa jiki na da naki ba, ba zan taɓa yafe ma kaina ba, duk lokacin da naji wani abu game dake, *Na tsane ki, bana ƙaunar ki, mai ƙaunar ki ma bana son ganin shi* rabuwa dani dole ne, ko akala aka saka aka ɗaure man ke, wallahil azeem sai na kunce ta. Ke idan har zuciya ta taji wani abu dangane dake, sai na saka hannu na ƙwaƙule ta na yarda. Kinyi kaɗan, baki kai ba, wadda ma ta fiki bata kai ba. Waccen ɗin dai, wadda kuka raina, wadda kuke son ganin baya, wadda kuka so jefa rayuwar ta da ta mahaifiyar ta a cikin wani hali, ni ita na gani, kuma ita nake so, mugun nufin ki a kaina, zai tabbata a gareki, ni Al'ameen Almustapha Dambulan, ba zan taɓa iya ƙyale ku ku tafi haka ba, dan haka ku jira me zai biyo baya, kuma ina gargaɗarki da sake riƙe mani jiki, saboda ni ba sa'an ki bane shashasha, wadda bata san ciwon kanta ba, kuɗɗa ballagazar mace" yana gama faɗin hakan ya sanya kai yana mai ficewa. Kuka sosai Mama Talatu keyi, tana bin ƙafafun su Mom da Umma tana riƙewa, babu abunda ya dame su da ita, itama Saude saida tayi kuka, tasan hakan zata faru da ita dama, tayi nadama tuni, taso kuma ta fallasa komai tuni, Amman wannan ranar take gudu. Sauƙin ta ma taji alhaji yace Alhaji Ƙarami zaiyi mata wani abu, kuma ta san ba zai barta da kaɗan ba. Alhaji ne ya sallami kowa, lokacin salla yayi, ko da akayi haka, sashen Mom ta wuce dani, tana ta lallashi na, wai kukan me nake ai komai ya wuce, indai ita ce, yanzu bana da matsala da ita. Jiki a sanyaye suka fice, suna ta rusa kuka, Iro ne ya biyo mariya daga baya, yana faɗin "e chilun ki maliya ta, ni ina sonki kuma zan aule ki a haka, ina matuƙar ƙaunal ki, ni ma ba zan zauna ba, zan biku kinji?" "Kai dan ubanka matsa ka bani waje, shege mahaukaci, ko maza sun ƙare duniya zan iya auren ma ne? Jibi yanda kake tashin ƙarin dauɗa fa, ka saka ido ka gani yanda zan dawo cikin gidan nan in baza haja ta, kowa ya kwasa.." Maganar ta ce ta maƙale a baki, jin ihu da jiniyar motar ƴan sanda tana mai danno kai a cikin gidan nasu. Da sauri duk muka sake firfito wa, hada Alhaji da yayo alwala zai fita masallaci, shi ko Ya Ameen yana jingine jikin wata motar shi, hannun shi riƙe da waya yake latsa wa. Kawai nuni yayi masu da su Maree da suke tsaye tsakiyar gidan. Diddirowa suka yi su biyar, suna masu kakkafa masu bindiga a kai, "Muje Malamai, you are under arrest, muna tuhumar ku da yunƙurin kashe wata, dan haka zaku amsa laifin ku a gaban alƙakili" cewar wani daga cikin ƴan sandan, da gani shine babba. Aiko sai suka zube ƙasa har Maree ɗin, da taji hanyar cikin ta ta kaɗa, cikin ya hautsina, kaman zata saki zawo. "Yallaɓai wallahi.." "yi mana shiru nace, duk Abunda kika faɗa man zai zama hujja a gaban alƙali ne" Take aka buga masu ankwa duka hannuwan, kuka kawai suke yi, wannan shine ƙarshen mai cin amana, munafuki magulmaci. Saida suka iza ƙyeyar su zuwa bayan motar, sannan suka sarm Al'ameen, shi kuma yayi masu nuni da suje zazo. Da gudun masifa suka fice daga gidan, ba abunda kake ji sai ihun Mama Talatu da mariya, abun gwanin ban kunya da kataici. Ace gida babba irin wanna ka fice daga cikin shi, cikin ƙasƙanci da wulaƙanci. Ɗan girgiza kai Alhaji yayi, bai so haka ba, saidai ya riga ya aikata, kuma ya sani, yanda ran yaron nashi ya ɓaci, muddin ya hana shi, ba za'a zauna lafiya ba, gara ya ƙyale su a hukun ta su, alabasshi gaba wani zai kiyaye. Sauran ƴan aikin kuwa duk jikin su yayi sanyi, sun ƙara tsorata, saidai sam basu ga laifin Al'ameen ba, hakan shine ya dace da mutane irin su Talatun masu baƙar zuciya. Ita kuwa Mama Saude sashen su ta wuce kai tsaye domin har haɗa kayan ta a tsanake. Muma jiki a sanyaye muka koma sashen Mom ɗin, jiki na duk ba lakka, ga wani ɗan kumburi da naga alamun kaman na fara, ciki na wata biyar kenan a yanzu, har ma yana niyyar shiga na shida. Fitar da baiyi ba kenan ya koma sashen namu yana jiran shigowa ta. Jin shiru ban shigo ba ne, ya sanya shi sake wanke, gami da sauya kaya marasa nauyi, ya kulle sashen ya fice zuwa wajen Bilal, daga cen zasu wuce division ɗin. Ni kuwa sai wajen ƙarfe biyar na koma sashen namu, alale Mom ta sanya aka siyo man mai daɗi, mai ƙwai da kifi da anta ciki, sai Alayyaho, gashi tayi saƙa sosai, ko acen saida na kwanta ɗakin Afnan nayi bacci, Afnan ɗin na matsa man ƙafafu na wanda sukayi man fushi, butsu butsu Mom kan leƙo taga ko ina cikin ƙoshin lafiya. Har abun ke ba Afnan mamaki, ta sake tabbatar ma da ka ta cewa Mom ɗin ta shiryu sosai, bayan faruwar abunda ya faru. Da taimakon Afnan ɗin na kammala komai, duk abunda na san zai nema saida na tanadar mashi. Na san yau baya cikin natsuwa, tun bayan shiga rayuwar tashi da nayi, komai ya sauya mashi, Sam idan Kaga ya Ameen kai kanka ka san ya cenza daga da. Ya Ameen mara hayaniya, ga natsuwa tattare dashi, Amman yanzu da ka kalle shi, ka san akwai wani al'amari tattare dashi, tausayi yake bani sosai matuƙa, duk hanyar da zanbi wajen ganin na daidaita mashi rayuwa ta koma kaman ta da zanbi. Bai dawo ba sai ƙarfe bakwai, ana yin sallar magrib sai gashi, kaman ma saida ya tsaya masallacin waje yayi sallah sannan. Nima sallame sallah ta kenan, ban ko miƙe ba daga kan dardumar, ya turo ƙofa, kai tsaye cikin ɗakin ya shigo, daidai lokacin da nake shafa addu'a na ɗan waiwaya haka ina mai cewa "Sannu da dawowa Yayan mu ya hanya?" ɗan murmushi ya sake mani, da gani na son kauda tunanin yana da damuwa ne. "Fine" ya faɗa a gajarce. Yana mai zama bakin gado. "Wash" ya sake faɗi alamun gajiya, yana mai kai kwance bisa gadon da na lailaye da zanen gado mai taushin gaske. Kusa dashi na ƙarasa, ina mai zame hijab ɗin na linke, na ajiye ta mazauni ta, bisa dardumar. Zama nayi sosai jikin shi, ina mai ɗan ƙwantawa na tada kaina da hannu na, fuska ta daf da tashi nake cewa Habibi gajiya ko?" na faɗa cikin kulawa. Ɗan lumshe idanun shi yayi, masu ɗauke da zara zaran gashin ido, sai kuma ya buɗe su, yana mai narke idanun cikin nawa yace " Yes Habibty, anything for me?" wani murmushn na sake ina mai cewa" Aloot dear" jawo ni yayi zuwa jikin shi sosai, yana mai cewa "Gist me mom baby" ya faɗa yana shafo cikin. "Aloot of your love, cant imagine baby" dariya yayi, har kumatun shi na lotsawa, fararen haƙoran shi da suke jere reras suka bayyana. "Mee to dear, muje ki sama man wani abu for now" a tare muka miƙe, ina cikin jikin shi, har dining. Shi kanshi yayi mamakin yanda na tsara abinci, duk da yanayin da nake ciki. Yaci sosai kaman ba shi ba, labari ya dinga bani akai akai, abincin ya mashi daɗi, masalan dayake abincin gargajiya ne mai sauƙin nauyi. Muna gamawa muka koma falo. Aiki ya fara cikin computer, kaina na saman cinyar shi, akai akai nakan shafo sajen shi mai ƙayatar dani. Har aka kira Isha, sannan muka miƙe, ko bayan da muka dawo daga sallar ma hakan ce dai ta sake faruwa, komawa mukayi yanda muke. Aiki yake sosai a computer yana yi yana ɗan bani labari. Har na miƙe na kawo mashi fresh milk. Ina jin daɗin zama da Ya Ameen, mutum ne mai sauƙi, fiye da yanda nayi tsammani, kowa na mashi kallon mai miskilanci, amman a zahirn gaskiya saidai in baka zauna dashi ba. Hannun shi naji saman fuska ta, yana mai shafowa yake faɗin "Baby na jiki shiru ko kinyi bacci ne? " ɗan zakuɗawa nayi, ina mai damƙe hannun sa sosai da ke kan ciki na. Nace "A'a Yaya" murmushi ya sakar man, tare da bani peck a goshi. Sannan ya cigaba da aikin sa. Bansan lokacin da nayi bacci ba, ina shaƙar ƙamshin sa mai daɗi, tun da na samu ciki nake jin marmarin ƙamshin, idan har zan rayu dashi, ko yunwa bana ji. Ko da ya gama aikin, baya son tada ni, gashi ƙafafun shi sunyi sanyi, Amman ko motsin kirki ya kasa yi, saboda yanda take dauke numfashi a hankali cike da gajiya. Ya daɗe nan a zaune yana saƙe saƙe, yayi mamaki yanda bai sha wahala ba a case ɗin su Maree cikin sauƙi aka tura su cell, tare da filling ɗin case ɗinsu, gobe za'a tura su ga kotu, a bisa tuhumar su da ake da ƙoƙari da haɗa baki wajen kashe Suhan. Wani irin abu mai ɗan ɗumi naji yana ɗigar man saman fuska, ɗan yamutsa fuska nayi, ina mai gyara kwanciya, still naji ya sake ɗigowa. Ɗan zabura nayi na tashi, cikin ɗan sauran hasken da bai wadata ba na ke kallon fuskar shi. Lallai kuwa Ya Ameen kuka yake yi, to me ya faru? Ko case ɗin ɗazu ne bai wuce ba? Baisan na tashi ba, saidai yaji fuska ta kwance a saman kafaɗar shi ina cewa "sorry dear" a hankali da jajayen idanun shi yake kallo na, tare da saurin goge ƙwallar, saidai na riga na gaji, hasalima ita ce ta tashe ni ɗin. Shafo gefen fuska ta yayi, a kasalance, ban jinkirta ba na cigaba da faɗin "Na nasan ni ce sila, nice dalilin faruwar komai, ina mai sake baka haƙuri, ban shigo rayuwar ka ba, sai domin son da nake maka, ban shiga rayuwar ka ba, dan in cenza komai, ban shiga rayuwar ka ba dan in haddasa fitina, kuma ban shiga rayuwar..." Saurin rufe man baki yayi da nashi, ban musa ba, domin a shirye nake da na lallashe shi ta kowanne hali. Saida ya gaji dan kanshi, sannan ya ƙyale ni. Yana mai goge man hawayen fuskar tawa nima. Saida ya gyara komai sannan ya kwanta kusa dani, rabin jiki na ma na a nashi, sannan ne yake faɗa man duk yanda sukayi da su Maree. Na sha mamakin da ya sanar mani har yaje bakin Maree wai bai mutu ba, ita fa sonshi take da aure, ko ni sai da nayi dariya, shima dariyar yayi, yana mai cewa "Ai ina jin fa yarinyar nan ba kanta ƙalau ba" ɗan jinjina kai nayi, wani irin kishi na taso man, ko ɗazu da ta riƙe mashi ƙafa, ji nayi kaman in zame daga roƙon da mom tayi man inje in faffalla mata maruka naji, ina kishin miji na, balle da Allah ya mallaka man Ya Ameen da nake ji kaman na fi kowacce mace sa'a da dace da miji na gari. ygyara kwanciya na sake yi, yayin da ya rungume ni na koma bacci na mai daɗi, tare da sauke ajiyar zuciya akai akai, ina ganin matsala ta tazo ƙarshe. Shi kuwa ta ɓangaren shi, bai shaida mata cewa zasuyi dakon mutumen da yazo ya sanya mata ɓera a ɗaki ba cikin daren, inda defenetly Maree ta shaida ma su jami'an tsaro ɗin cewa yau sukayi zai dawo ya ƙarasa aikin shi, da ta ji matsa. Ya san in ya faɗa mata babu bacci a tattare da ita. Ilai kuwa wajen ƙarfe biyu da wani abu ya fara jin motsi, alamun ana son shigowa ta wajen lambu, lamo yayi sosai, yana mai tabbatar da cewa ko wanene ma yake niyyar shigowa to fa gab yake. A hankali ya sauke kai na daga bisa ƙirjin shi, yana mai kara man fillow, tare da ƙara gudun Ac ɗin ɗakin yanda ba zatayi man illa ba, kuma zan ji daɗin baccin, sannan ya tashi yana mai buɗe ƙofar falon cikin sanɗa ya fice.......... ~Oum-Deedat ce~ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~90~* *Ina Barar Addu'a da bakunan ku masu albarka* _Allah ya cika man buri na indai da alkhairi, in kuma babu, Allah ya musanya man da wata hanyar, Allah ya zaunar da mu da ƙasar mu lafiya ya ƙara kare mu tare da kiyaye mu Ameen_ *_#Stay Home_* *_#Stay Safe_* *_#Wash your hands_* *_#Avoide over crowded place_* *_#Stop spreding the dx_* *Dan Allah a zauna gida, ayi addu'a Allah ya buɗo hanyoyn alkhairi, Allah yasa mu fi ƙarfin abin da zamu ci, zamu sha, zamu suturta da kuma muhalli. Ameen* ****************** Ko wayar shi bai ɗauka ba, duk wani abu da zai alamta cewa akwai matsala a gidan baya sonshi, yana so sai ya kammala koma menene sannan kowa ya ji, hakan ce ta sanya wata ƴar agogo ce kawai ɗaure a tsintsiyar hannun nashi, wadda tun kafin ya kwanta ya maƙala ta. Bai kulle ƙofar ta baya ba, kuskuren da ya tafka kenan, hankalin shi ya ɗauku da ya kammala aikin. Cikin duhun dare yake bi, ba zaka iya gane da mutum ba, saidai wajen yana da tsawo da kuma faɗi, dan haka daidai wani saƙo da zai iya sada ka da hanyar garden ɗin ya laɓe. Ya kusan minti biyar, daidai lokacin da yaji motsin ya lafa, cikin ɗan hasken da bai wadaci wajen ba, ya ɗaga hannun shi, yana mai nuni dashi cikin farin watan daya haske kusa da inda yake laɓe, ƙarfe uku ta kusa, ya raya a cikin ran shi. Ko ba komai ya zuwa yanzu ya tabbatar da cewa jami'an tsaron da ya saka suka lallaɓe a kusa da gidan yanzu haka suna bakin aikin su. Har saida ya fara gajiya da tsugunno, sannan ya lallaɓa ya ɓalle murfin da zai sada shi da lambun, yana mai bi ta ciki yana haskawa. ********** Na natsu sosai ina bacci na, naji motsi sosai kusa dani, ɗan miƙa na sauke, ina mai lalubo kusa dani, banji komai ba, illa filon da ya ƙara mani. Zumbur nayi ina mai tashi zaune, da ɗan sauran hasken dum Light nake iya hango mutum tsaye daga bakin ƙofa, saidai ban iya tantance koma wanene. "Yaya lafiya kuwa? Ko wani abu kake buƙata" na furta a hankali, cikin muryar bacci. Ba'a amsa man ba, sai ma takowa da aka shiga yi, zuwa inda nake bisa gadon. Ganin hakan sai na sauko da ƙafafu na zuwa ƙasa, duk a zato na, ƴan maganar ne basa kai. "Yaya na tashi fa, ko kana son wani abu ne?" na sake faɗa, ina mai haske ɗakin, ta hanyar kunna maƙyallin haske. Wata irin razana naji, tun daga ƙafafu na har ƙwalwar kaina. Baki na buɗe zan ƙwalla ƙara, mutumen da yake kaman basamude yayi saurin zaro wuƙa, yana mai nuna ni da ita. Bashi da kyaun kallo, a tsaye da jiki ya linka ya Ameen uku. "kina man ihu zan yanka ki" ya faɗa cikin kaushin murya, duka hannaye na na saka, ina mai daɗe baki na sosai, hawaye ne ke malala sosai a idanu na, girgiza akai na shiga yi, alamun ba zanyi ba, lokaci guda kuma ina mai haɗawa da ja baya. Shi kuma a lokacin yana doso ni, wuƙa tsirara a hannun shi, yana mai nuni dani. Ban tsaya ba, har saida naji na dangane da makarin gado, Hantsilawa nayi bisa gadon, duk da cikin dake jiki na, na ma manta da shi, ina Ya Ameen Ya tafi ne wai? Na shiga uku, wa ya buɗe mana ƙofa? Kaddai ace sunyi mashi wani abu. "Ina mijin ki ya tafi? Hahaha Naji daɗin hakan, abu yazo da sauƙi, yanzu zan gama dake da kuma wannan shegen cikin da ke jikin ki, ba tare da wani ya sani ba" ya faɗa shima, yana mai niyyar haurowa saman gadon. Dunƙulewa nayi sosai saman gadon, ya zuwa yanzu sautin tsoro da tsananin tashin hankali ya fara ƙwacewa daga baki na kaɗan kaɗan. "Zo nan" ya sake furta wa cikin ƴar tsawa. "Dannn Allllahh kaa... Yi hhhaƙuuri" na furta cikin giggiwa da tsoro sosai, murya ta na karkarwa. "Ba zaki taso ba? Sai na idasa haurowa saman gadon??" ya sake daka man tsawa. Sake dunƙulewa nayi, saura kaɗan na saki fitsari, gabaki ɗaya idanu na sunyo waje, na tabbata saura ƙiris na some. "Wato ke da mijin ki masu tarin kai ko? Zakiga sakamakon tarin kai, gabaki ɗayan ku sai na gama daku" ya sake faɗa cikin amon muryar shi mara daɗi. Ganin yanda yake doso ni, da wuƙa tsirara kawai na sadaƙas, runtse idanu na nayi gam da ƙarfi, ina mai tattakura na fasa ihun da nasan cewa hatta da mai gadi sai ya jiyo shi. Wani irin Dammm ya jiyo a cikin ƙirjin shi, sakamakon ihun ta da ya jiyo daga cen sashen nasu. Da gudun bala'i ya juyo, yana mai nufar dashen nasu, da ya hango ƙwan fitilar ɗakin nasu a kunne ƙau. Ai bai tsaya wata wata ba, ya afka cikin sashen, har yana nemna zamewa da santsin tiles, me kenan? Shi yana cen ya tafi neman mugun, ashe shi yana nan zai mashi ta'asa. Ɗakin ya faɗa kai tsaye, Allah ya soshi, ɗan ta'addan ya juya baya, aiko ya rarumo shi, duk da tsayi da girma da ya linka shi. Zubewa sukayi saman tiles, yayin dana sake tattakura na fasa kuka cikin ihun amo. Ai da gudu idi mai gadi, mudi driver da Iro suka yo fitar burgu zuwa sashen namu da suke jiyo ihun kukan. Faɗa ne sosai ya kaure tsakanin su, duka sosai ya Ameen yake kai mashi, duk a ƙoƙarin shi na son danne shi ya kama shi, amman shi duk idan ya kai ma Ya Ameen duka ɗaya, sai wajen ya fasa, gami da yin ja, yankar shi yake ƙoƙarin yi, Amman bai samu nasara ba, sai sau biyu, jini ne ya fara ɗibar ya Ameen, inda ina ganin hakan naji wani irin jiri na ɗiba ta, sake kwatsama ƙara nayi, ina mai cewa "Wai ba kowa ne a gidan? Azo a taimake mu, zai kashe mu" Amman duk da haka Ya Ameen ta maza take yi, yana sake kai mashi naushi. Dayake shi baƙi ne Wancen kakkaura, Ya Ameen Ya fishi jin jiki sosai, abunka da fari, har ƙarfin nashi ya fara ƙarewa. A wahalce ya latsa wani ɗan abu da ke liƙe da agogon da yake hannun nashi, cikin ɗakiƙa ɗaya ƴan sandan nan suka fara diddirowa ta saman katangar. Su ma su Mudi basu tsaya wata wata ba, suka afka sashen namu, masalan ma da suka ganshi a wangame, sun san da matsala kenan. Kokowa sosai suka tadda suna yi, duk ya yayyanki Ya Ameen, lallai wannan mutume da ƙarfin hali yake sosai, ni kuwa sai kuka nake na dunƙule saman gado, duk na yayyayo bargon da zanen gadon ma lulluɓe jiki na dashi. Afka mashi sukayi sosai da sosai. Abunka ga sarkin yawa, tuni suka kai shi ƙasa, Amman har yanzu ƙoƙari yake na ya kufce ya iso gareni. Da sauri Umma da Alhaji Mustapha suka yo waje, dama Umma na sashen shi, ita ma Mom haka, ita da Afnan, kowa hankalin shi a tashe, masalan da suka ga ƴan sanda rirriƙe da bindigu a cikin gidan, wasu kuma sun shige sashen namu. Ko da yaga bindiga, dole yayi surrender, tuni suka nannauahe shi, gami da buga mashi ankwa. Afnan har ta fara kuka haka ma sauran ma'aikatan gidan sunyo waje. Hankalin kowa ya matuƙar tashi. Masalan ma Umma. Addu'a take kaddai ace wani abu ne ya faru da ƴar tata. Ikon Allah Suhan dai na gani tashin hankali iri iri. Saida suka taso ƙyeyar shi zuwa waje ne, sannan kowa ya gane me ke faruwa, cikin tashin hankali kowa ke kallon mu. Masalan Alhaji Mustapha da bai kai ga ma fahimtar me ke faruwa ba. Ƴan sanda a gidan shi? Wanene wannan da aka kama sun fiddo shi daga sashen Yaran nashi? Ɗan naɗe Jallabiyar shi yayi, cikin son ƙarin bayani ya matsa kusa dasu. "Kai Lafiya kuwa cikin daren nan? Me ke faruwa..." maganar shi ce ta maƙale, ganin Mudi da Iro sun kamo Ya Ameen rana ranga , gani biye dasu ina rusa kuka. Faɗi nake "Ya kashe shi Dady ya kashe shi" Ai da gudu suka zabura inda muke, Mom ce ta rirriƙe shi cikin tashin hankali take faɗin "Son me ya faru? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, Son buɗe idanun ka me ya faru wai?" ta jefo man tambaya cikin tsananin tashin hankali. Da gudu nima na faɗa jikin ta ina mai cewa "Mummy nima bansan me ya faru ba, bansan waye shi ba, sashen mu ya shigo mummy" Da hannu Alhaji Mustapha yayi ma ƴan sandan alamu da su wuce da wannan mutumen, sannan ya tallafi Ya Ameen yana ce ma Mudee ya fiddo mota. Dishi dishi yake gani, kuka ya hango ta tana yi sosai, hannu ya miƙa mata alamun tazo gareshi, ba musu kuwa ta tako cikin sauri, tana mai damuƙar shi, duk jinin da yake jikin shi, haka ta rungume shi, ta ma mance su Umma na wajen, ga shi cikin jikin Dady. "Ya Ameen ka tashi, kada ka mutu dan Allah, jini a jikin ka, Ya Ameen dubi yanda yayi maka fa" na furta cikin ƙarajin kuka.. Umma ce ta matso tana mai zare ni a jikin shi, daidai lokacin da ake cusa shi cikin motar. Mom ma saida taso shiga Dad ya hana ta, daga shi sai Mudi da Iro suka nufi asibiti dashi, yayin da har ƴan sandan sun fice da ɗan ta'addan. Kuka nake sosai, na ƙi komawa sashen na, dan haka ne ma Mom tace Umma ta wuce dani ta lalasshe ni, Afnan ma binmu tayi. Kusan haka muka kwana a ranar, ba wanda ya rutsa, ni kuka kawai nake, duk yanda Umma da Afnan suka so su lallashi ni kasawa nayi, na tsorata, ga Ya Ameen cikin wani hali, ina ji ɗan ciki na yana dunƙulewa gami da warwarewa a lokaci guda. Ruwa kawai Umma ke ɗirka man tare da tofi da tayi man ciki, ko zuciya ta zata dangana. Tun da safe sai ga Dad, cewa yayi mu fito a kaimu asibitin, sallah kawai nayi, ko ruwan tea da Umma ta haɗa man na kasa kurɓa, matsa man tayi wai saboda abinda yake ciki na, aman na kasa sauraren ta. Ita kanta mamaki na take yi, son da ɗiyar tata ke yi ma mijin nata yana da yawa. Haka aka kwashe mu sai asibitin, jikin Ya Ameen ɗin da sauƙi, saidai yana bacci, inda duk aka nannaɗe yankan da bandage. Ya wahala sosai, duk dan ya ƙare ni, dan ya kuɓutar dani, kuka kawai nake, muna hango shi ta cikin glass, idanu na duk sun kumbura sunyi ja, sai raɗaɗi suke yi mani. Mom ma lallashi na take yi, ganin jikin da sauƙi, tun cikin daren Abie yace zai taho, dayake su cen safiya ce. Haka ma Aunt Feena, Amman sai Mom ta hana ta, a cewar ta, ya zatayi da karatun yaran? Dan mijin ta yana kauda mata kai kuma sai ta dinga tafiye tafiye, kullum tana hanya? Kusan zan iya cewa Salla kawai ke motsa ni daga jikin glass ɗin, ƙafafu na kuwa har sun kumbura saboda tsayawa. Ko da ya farka, ni ce ta farkon da ya fara miƙo ma hannu, ba'a hana ni shiga ba, saboda ya samu ƙwarin jiki sosai. Ko da na shiga kukan dai nake yi, shi ke share man hawayen yana girgiza man kai. Yayi wani fayau dashi, ya sha duka, duk fuskar tayi kwaɓa kwaɓa, wanda ko ga alama ba wanda zai tunanin akwai wani mahaluƙi da ya isa yi ma Ya Ameen haka, ganin ko shi ɗin wanene. Har abinci an samu yaci, ni ce na bashi, inda yake kauda kai, sai na saka loma ɗaya a baki na sannan shima ya amsa, da haka ya man wayau na ci sosai, shima ya ci sosai ɗin, bayan ganin jikin ya samu sauƙi ne, aka bamu sallama, da zummar cewa zai dinga zuwa ana duba ɗinkin yankan da akayi mashi a damtsen hannu, gefen cikin shi, da bayan shi, sai wajen cinyar shi da kusan ƙirjin shi. Har lokacin ban dena kuka sama sama ba, gani nake nice sila kawai, anya ba zan fita a rayuwar Ya Ameen ba? Ko da zata daidaita. Haka muka dawo gida, Amman tsoron sashen namu ya kama ni sosai, saida akayi ta man faɗa, hada Hajiya Zainab, wai wanene zai jinyar mijin nawa? Haka na koma, Amman da Afnan muke yini, dayake baya da ƙan jiki, sai gashi cikin kwana biyu ya soma warwarewa sosai, har fita yake ƙofar gida, shi da Bilal, da kullum yana hanyar zuwa gidan namu. Alhaji Mustapha da kanshi yayi handling case ɗin mutumen, wanda dai Maree ta turo ne, da taimakon Hajiya Laila, ba'a yi wata wata ba aka tura ƙyeyar shi zuwa gidan maza, ita kanta Hajiya laila ɗin da Alhaji yaro sun ja ma kansu, azaba da uƙuba kawai ake gana masu, ashe har suna gidan gyaran hali ma, halin nasu bai cenzu ba. Maree ma haka, ihu take sosai tana faɗin Ya Ameen, ba wanda ya kula ta, gani ake kaman ta zare, ita kanta saida aka maka ta gidan yarin, Mama Talatu ce aka saki, tare da cinta tarar kuɗi masu yawan gaske, ko kuma ɗauri na talala a wani mugun ƙauyen da ba wuta ba ruwa ba hanya, ga mugun talauci, idan ka ganta sai ta baka tausayi. Gashi tana ji tana gani aka iza ƙyeyar ɗiyar tata, wanda a yanzu mugun haushin ta take ji, gani take hada silar ta komai nata ya taɓarɓare da wuri, ba tare da sun cimma manufarsu ba. (Duk shekarun da suka ɗauka suna aikata mugun abu) ************** Shiri suke gadan gadan, masalan da hidima ta matso sosai, shi Sir Salim ma so yayi a baje gidan a cenza tsari, Abban shi ne ya hana, inda ita dai Ammi saidai ta dinga mashi dariya, wannan aure yanda yake ɗokin shi, gani take kaman bai taɓa aure ba, koda yake a wannan ne yake saka ran dacewa. Duk da haka dai, saida aka sake fentin gidan sosai, dayake babban falo ne sai kuma wasu falukan ciki, gami da manyan ɗakuna guda biyu, sai kitchen a ciki da toilet. Dan haka sashen amarya fa an gyara shi gani da zuba flowers wall sosai. Jeren kayan amarya kawai yake jira. Lefe na ji da gani suka haɗa tare da taimakon Ammi da Asiya, lallai suna ɗokin auren nan, gashi duka yanzu bai fi sati huɗu ba a fara hidima gadan gadan. Ammi ce ta tura mai gyaran jiki, wadda tayi ma Suhan, a cewar ta, ai Afnan ɗin ba Surukar ta bace, ɗiyar ta ce. Ba ji ba gani aka fara Gyaran Afnan, tini ta ɗau sheƙi, abunka ga amarya, dayake nima nan ina ɗan bata wasu tips, masalan da hankali na ya ɗan kwanta, ganin Ya Ameen Ya warware sosai. Hidimar biki ake sosai, siyayya ba kama hannun yaro, tun ana saura sati biyu su Umma suka je sukayi jeren su ɗan uban su, masalan da take ƴar gatan Yayanta, komai take so sai ya siya mata. Akai akai Nihal da saudat na zuwa, saidai harara ce kawai tsakani na da Saudat, Abunda ma ya bani mamaki, wani uban haske da naga tayi, watau bayan hasken ta, har shafe shafe ma ta fara ko? Mom kuma ta kasa ce mata komai har yanzu ɗabi'ar son yaran nata da rashin tsawata masu na cikin ranta, koda yake haka dama rayuwar wasu masu kuɗin ta gada. Nihal da yaron cikin ta, ni kuma nawa yayi wani uban tsini sosai, da ƙyar nake cira ƙafa, duk inda nayi sai an jini da kallo. Kowa mamakin cikin yake yi. Shi kanshi Ya Ameen kullum tausaya man yake yi. Yanzu banda matsala da kowa masha Allah, Mom ta zaman man back bone a cikin gidan, ko wani abu nake so, kafin ma in ma Ya Ameen magana, ita tayi mashi, kuma bana samun wata matsala, saidai ina da burin da Afnan tayi aure, zance mashi ya taimaka mu cenza gida, ina ɗan jin Kunyar Mom har yanzu. Nima ba'a barni a baya ba. Duk Abunda nasan Afnan zata nema na siya mata, Sir Salim ni yake kira yaji ko Afnan ɗin tana da wata buƙata, shi bata faɗa mashi, aiko zagewa nake in faɗa mashi, masalan ma yanzu da muka kasance ƴan uwa. Aunt Feena ta iso, dama Abie tun ciwon Ya Ameen Ya diro, haɗa tarkato ƴan kayan shi, yana mai cewa ya dawo kenan wai shima aure yake so. Dariya muka dinga yi mashi, lallai ma Abie, duka nawa yake balle yace aure yake so, ko ya Ameen da yaji zancen nashi, saida yayi dariya wa shirmen Abie ɗin, yana mai faɗin "Yaro ka gama shirmen naka, ana gama biki zaka tattara ka koma." Nima an gyarani, duk da kunsan mai ciki sai a hankali, ciki na ya shiga wata na takwas fa, komai na saka saidai kawai dan sitira baya man kyau sosai, saidai doguwar riga, Shiyasa ko kayan biki da na ɗinka duk dogayen riguna ne. An fara hidima sosai, hatta da su Mama Fulani nan suka taho gidan mu, ga ƴan kankiya, hidima fa tana kyau sosai, Mom duk ta cenza, kaman ba ita ba duk da hidimar bikin ta bar ma Umma da Hajiya Zainab, saidai kallo ita, Amman duk da haka ba wata matsala dake faruwa. Ƙawaye na ma duk sun ma kara, haka na Afnan ɗin itama. Ni ce Yayar Amarya, duk inda nake amarya na nan. Ranar Jumu'a ɗinbin mutane suka shaida ɗaurin auren Afnan ɗin da Sir Salim a gidan Alhaji Auwalu. Nan fa aka sake ɓarkewa da hidima. Amarya sai gobe ne za'a kaita. Dan haka aka sha shagali hankali kwance, hada su Kamu akayi da arecen a nan cikin gidan namu. Butsu Butsu Kaga Ya ameen Ya leƙo kira na. Har Kaka zauwaira na mashi tsiyar wai baya tausayi na, da na zauna zai zo sake kiran a, idan wani abu ne yaje yayi da kanshi mana. Dariya yake yi, yana mai cewa "Ke dai tsohuwa ladar auren da ke kika kasa samu ce, bakya so ta samu, taso muje kinji sweety na" ranƙwashi take kai mashi akai. Kowa na mamakin sauyawar Ya Ameen a yanzu, yaman sake da kowa ayi wasa da dariya, dukda yanayin nashi ne a haka, shi gani yake. yana iya ƙoƙarin shi. Washegari aka shirin kai amarya, Ya Ameen Ya so hana ni, saida Mom tayi mashi jan ido, ita kanta Umma wai cewa tayi "Me zata je yi da wannan cikin? Salon ta haife mana shi acen?" Mom ce tace ba komai, indai ta haihu lafiya ai Arziƙi ne, cen ma ai gida ne. Haka muka tarkata, dayake Cikin motar Ya Ameen sabuwa, haka aka saka amarya, nima haka na shiga gidan gaba, da Umma da Hajiya Zainab da Goggo Aisha da Goggo Fatima na baya, dayake sabuwar mota ce ya siya mai girma sosai da kyau, saboda hidimar Family irin hakan. Sauran motocin da dangin ango da suka kasance dangi na, haka aka ɗauki hanya, zarya fa tsakanin Abuja da Adamawa ai ta ga Family namu, yanzu duk an zama ɗaya, ita kuwa Mom gida ta zauna tarar sauran baƙin, da wanda basu samu zuwa kai amaryar ba. Gidan Afnan yayi matuƙar kyau, zullumi na ɗaya Ma'u, bana so Afnan ta shiga wani hali, tana da zuciyar zinari, mace ce mai kawaici, son mutane ga kirki. Addu'oi sosai wanda na koya a wajen umma ta na bata, kafin ta shiga gidan ta karanta. Mun ga gata kuwa, sai nan nan ake yi damu, abunka ga dangin sarauta, nan da muka tadda gida cike da hamshaƙai da manyan mata ƙawayen Ammi da sauran ƴan uwa. Umma fa Gimbiya tarba ta musamman akayi mata, duk ind ana wuce nuna ni ake yi, ga ɗiyar Gimbiya Hasken Masarauta, nan aka shiga magana caaa, caaa, wasu ma hada cewa ni ce nayi nasarar yin *Wuf* da zuciyar Yariman matasan arewar. Duk da Mama Fulani taso na bita cen masarautar, ƙiyawa nayi, ina mai ce mata sai dai gobe, dayake ai Kaka ta ce, janta nake yi sosai da sosai. Ango fa baki har kunne, ya ma manta da mun taɓa wata aba soyayya, dukda har yanzu yana girmama ni a cikin ran shi, ni yake faɗa ma wai na kula da Afnan ɗin, saidai inyi dariya, domin ji dai gani na kawai ake yi, hada ma wani Aunty yake ce man. Washegari akayi walima sosai mai kyau, sannan ne fa aka fara jidar mutane ana mayar dasu, wasu gidajen su, wasu masarauta. Ya rage daga mu, sai amarya, muma gyara mata gidan muke.Ya Ameen yana waje cikin mota, ya azalzale mu, wai mu fito mu wuce masarauta, cen zamu kwana sai gobe za'a ɗunguma kuma a juya gida. Zaune take saman gado, muna gefe ni da Nihal da Saudat da take ta cika tana batsewa, faɗa nake ɗan yi mata, da bata wasu shawarwarin, aka bugo ƙofa da ƙarfi, kaman za'a ɓalla ƙofar, cikin sauri muka juya, domin ganin ko wanene? *Ma'u ce tsaye ita da wasu zaratan mata sun ci ɗammara, sai faman jijjiga jiki suke yi, hannun su ɗauke da manyan itace, ko wa zasuyi ma rotse kuma?* da ganin fuskar su dai basu gaji mutumci ba. Gabana ne yayi muguwar faɗuwa, toh fa, abun da nake gudu yana shirin faruwa, gashi angon ma baya kusa, ga Afnan ita kaɗai zamu bari, tinda wancen uban azarɓaɓin ya dame ji, sai doko man waya yake yi. *Ina Munafukar take dan Ubanta?* cewar Ma' Un, wadda ke tsaye kaman tsohon kumurci, tana hurci kaman tana a filin daga ne, lokaci guda kuma tana mai kai kallon ta saman gadon inda Afnan take zaune fuskar ta lulluɓe da Mayafi na haɗaɗɗiyar lafaya, irin ta masarauta. *"Sai na ga uban da ya ɗaure maki gindi kika auri miji na, wallahi yau ko ni ko ke a cikin gidan nan, maza ku gama masu aiki kuna ɓata mana lokaci"* Ta sake faɗa cikin kaushin murya, tana mai nuna mu da muke tsaitsaye muna lallashin Afnan ɗin saboda kukan da take yi. ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ *Page ~91~* *Ya Ubangiji bamu da tsumi bamu da dubara, bama da wayau bama da fasaha, kai kaɗai ne Allah, kai kaɗai muke bautamawa, kai ke jin ƙan bayin ka, dan tsarkakan sunayen ka guda tis'in da tara, dan tsarkakken mulkin ka, domin fiyayyen halitta, kuma habibin ka, masoyi ka, kuma annabn ka, (Muhammadu SAW) ka yaye mana wannan cuta ta COVID-19 ya Allah ka dube mu da idon Rahma, ka yafe mana dukkanin laifukan da kukayi maka, mun ƙasƙantar da kanmu zuwa gareka, muna masu tuba da istigfar, Ya Allah mu masu laifi ne a gareka mun sani, mu masu saɓa dokar ka ne, ka jarabce mu, kuma mun amshi jarrabawa da hannu bibbiyu, kayi mana afuwa, kayi mana gafara, ka yaye mana wannan annoba da ka jarabce mu da ita. AMMEN YA RABBAL ALAMEEN, YA ZULJALALU WAL IKRAM, YA HAYYU YA ƘAYYUM, BIRAHMATIKA ASTAGISU.* ***************** Da sauri ya ƙara so wajen, ganin danƙareriyar motar Ya Ameen ɗin fake a gefen ƙofar gidan nashi. Cikin salon girmamawa tare da mutuntawa ya duƙa saitin ƙofar motar Ya Ameen ɗin yana ce mashi "Yallaɓai barka da warhaka, ya gajiya?" ɓalle murfin motar yayi, yana mai fitowa ya miƙa ma Sir Salim ɗin hannu, cikin sakewa sosai, fuskar shi ɗauke da fara'a sosai ƙwarai. "Ah barka da zuwa dai ango, kai za'a tambaya ya gajiya? Ya fama da jama'a kuma?" cewar Ya Ameen ɗin. Shima dariya ya shiga yi, ƙwarai ɗabi'u da halayen Al'ameen ke burge shi, wanda a yanzu ya zama Yaya za'a ce. "To Alhmdllh gata nan ana fama da ita dai, wai ba dai shanya ka sukayi anan ba?" Salim ɗin ya faɗa, yana ɗan waige waige, ganin wajen wayam ba kowa sai tsirarun motoci, wanda sauran ƙawayen amarya ne ke zance, dayake unguwar ba mai hayaniya bace. "Wallahi kuwa, Kaga tun ɗazu nake jira, ba dan madam na tare da su ba ma, wucewa ta zanyi, sun nemo mai maida su" Ya Ameen ɗin ya faɗa cikin ƙosawa, tare da jingina sosai jikin motar, da gani ya gaji sosai. "Ai kasan lamarin shiriritar mata, ƙila ma yanzu suna cen suna firar su" ɗan zaro idanu Ya Ameen ɗin yayi, yana mai cewa "ah haba? Aiko zasu sake kwana anan" ɗan murmushi Salim ɗin yayi, cikin zaulaya yake cewa "Haba Babban Yaya? Ka san fa yau ne ranar, a tausay man mana, ai ni da kaina zan mayar dasu ma ko ka tafi" bushewa sukayi da dariya su biyun, suna masu tafawa sosai, hada ɗan haɗa jiki Ya Ameen ɗin yayi da Salim. Maza kenan, kaman nema bai taɓa haɗa su ba, gashi yanzu sun sake kamar ba su ba, Shi kanshi Ya Ameen Ya tabbatar ma kanshi da cewa Afnan ta dace miji, Salim yana da natsuwa, ga kamala a tattare dashi, masalan ma da ya kasance ɗan uwa ga Suhan ɗin a yanzu. Kaman sun daɗe ƙwarai, kaman wasu abokai na haƙiƙa, nan fa suma suka sake, fira suke zubawa sosai da sosai, sai ga Sir Salim hada ɗora manyan ledojin da yayo siyayya dasu a saman mota. Sun nutsa da fira ne, Ya Ameen yace "Bro please kada mu ɓata lokaci anan, idan ka shiga ka turo man su, but please ƴar ƙanwar nan tawa dai please" dariya suka kuma bushewa da ita, suna masu ƙara tafawa sosai, cikin ƙaunar juna, Salim ɗin ya fahimci me Al'ameen ke nufi, Musabaha sukayi, sannan ya kwashi ledojin shi da niyyar wucewa ciki, sai kuma ya juyo sosai ga Ya Ameen ɗin. "Ah nace ba! dai ka shiga ka ga ɗakin amarya?" cewar Salim ɗin, ɗan jim Ya Ameen yayi, sai kuma ya girgiza kai, "Zan dawo ne ai kafin mu wuce Abuja ɗin." Girgiza kai Salim yayi, yana mai kamo hannun Ya Ameen da gudan hannun shi "Ya kamata dai muje ka duba Yaya, kasan fa ƙanwar nan taka ba zata ji daɗi ba" ya faɗa yana mai jan hannun Ya Ameen ɗin. Ba dan ya so ba, ya san yanzu haka Afnan kuka take yi, baya son ganin hawayen ta, abu ne da ya zama dole, zai iya ji kaman ya saka ta a mota ya mayar da ita gida, duk da yasan ba zata rasa komai ba anan. ********* Gadan gadan matan nan suka yo kanmu, yayin da wasu suka juya zuwa cikin falon Afnan ɗin. Ƙarar sautin rotsa tv ita ce ta saka mu wata irin zabura, ba ƙaƙautawa muka ji ana ta fasa abubuwa kaman mahaukata, yayin da sauran suka iso gaban mu suna masu mugun huci, wuntsilawa Saudat tayi zuwa bayana, yayin da Nihal ta ɗare bisa gadon cikin tsoro, ita kuwa Afnan saukowa tayi sosai bisa gadon, tana mai sanya hannu ta shiga ja na baya, saboda ka da a samu matsala, ni kuwa ƙafafu na sun kasa ko da motsawa ne. Tsabar tsoro da firgita, Sam babu imani a saman fuskar su. "Ke ce mai shegen shisshigin da kika yi giggiwar shigowa gidan ƴar uwar mu ko ɗan Ubanki?" cewar wata gansamemiya, da dukka ta kere su tsawo da kauri. Duk da kuka daya ƙwace ma Afnan, masalan jiyo irin ɓarnar da suke mata, wanda muna iya jiyo su har sun faɗa kitchen ɗinta. Buɗe baki tayi da ƙyar tana mai cewa" Ba ni ce na auri kaina ba, sannan ita wadda ta turo kun, meyasa bata zo nan da kanta ba? " Cewar Afnan ɗin, tana mai share hawayen fuskar ta, cikin son ƙarfafa ma kanta guiwa. *" Keeeeh! Ya isa, ba sa'insa muka zo yi daku ba, sawun ku a likkafa ku fice daga nan gidan, tun kafin lahira tayi baƙi, balle ke wannan mai tulelen cikin Munafukar Allah, sai wani zazzaro mana idanu kike yi, tare da wannan taron matsoratan banzan" , ta faɗa tana kai nuna su Nihal dake kan gadon. Ni kaina na sare, na ga bala'in ƙoƙarin Afnan ma, kenan zata iya ƙwatar ma kanta ƴanci? Sake buɗe baki tayi Zatayi magana, na sanya hannu na toshe mata baki, ina mai girgiza mata kai. "Kuzo mu tafi" abunda nace masu kenan, ina mai kaima Hijab ɗina raruma wadda ke ajiye saman gado, cike da kaɗuwa. "Aunty ina zamu je a haka? Ina Ya Ameen ne? Ba yana waje ba?" Cewar Saudat Ba ni ba, hatta da Afnan da Nihal saida suka juya suna mai kallon ta, Saudat ce haka yau? Ja'ira! ta ga gura'i, sai gashi da kiran Suhan Aunty. Ganin irin kallon da suke mata ne, ya sanya ta kauda kai cikin wayancewa, cikin wata kaɗuwar tace" ni dai wallahi ba inda zani, Aunty kira mana Yaya kawai" ta faɗa, tana mai sake haurawa cen ƙarshen gadon Ban ma yi wannan tunanin ba, cikin rawar hannu na lalubo waya ta a cikin jikka, ina mai latso number ɗin ya Ameen zan danna mashi kira, wani irin duka aka kai ma wayar dake hannun nawa, da ƙaton icce, sai gata ƙasa watsa watsa, da wuya ma idan zata tashi wannan wayar. Cikin wata kaɗuwar muka bi wayar da kallo, kaman fa wanda ake niyyar kashewa, duk munyi tsamo tsamo, Afnan ce ma kawai mai ɗan ƙarfin hali a cikin mu. Ihu sosai Saudat ta ƙwalla, karaf sai a kunnen su Ya Ameen da ke niyyar shigowa. Da ya Ameen da Salim ba'a san wanda yafi wani gudu ba, jin sautin ihu da kuma fashe fashen abubuwa na tashi daga cikin gidan. Turus suka ja suka yi cikin tsananin kaɗuwa, gami da bin ilahirin falon da kallo. dukka kamannin falon an cenza shi, ya zama kaman anyi yaƙi ko wani damben bala'i a ciki. Hatta da kujeru duk an birkice su, an farfasa kayan kallo, ga show glass mai masifar kyau, da zallan turaruka a ciki, duk an illata su, gabaki ɗaya falon fasassun kwalabe ne a ƙasa barbaje. *"MA'UUUU"* Cewar Sir Salim ɗin, yana mai rugawa zuwa ɗakin da yake mallakin Afnan ɗin. Ganin inda ya bi shima Ya Ameen Ya bishi cikin gudu gudu sauri sauri, Suhan kawai yake ji, wadda ke fama da turtsetsen ciki kaman zai ɓallo ƙasa, gashi da gani kuma babu lafiya a cikin gidan. "Keee" Salim ɗin ya daka ma matar da take tsaye gaban namu, ɗauke da mugun icce, gigita ciyar tsawa, yayin da sauran da suke ta fama farfasa komai na ɗakin suma suka dakata, jin sautin amon muryar namiji. "Wacece ke? Me kuka zo yi man a gida a daidai wannan lokacin? Wa ya saka ku?" duk Salim ɗin ya jefa mata waɗannan tambayoyin cikin tsawa sosai, jikin shi ma karkarwa ganin irin rashin hankalin da sukayi masu a wannan lokacin.. "Nice nan Baban Esher" Cewar Ma'u ɗin, wadda take shigowa, kallabin ta ɗaure a ƙugu, bayan ta waɗannan sauran zaratan matan ne rirriƙe da itace, kowacce ta ci ɗamara, sai haki suke yi, saboda aikin ɓarnar da sukayi. Da sauri duk muka juya muna masu kallon su cikin zaro idanu. Lallai ma, Ma'u ce, na shaida Fuskar ta, ai ba zan taɓa mantawa da ita ba. Kallon ta ta maido saman fuskar mu, "Munafukai masu mugun son abin duniya, ta Allah ba taku ba, nan gida na ne, babu shegiyar da ta isa na haɗa miji da ita.." "Ya Isheki Ma'u, me kika zo yi man a cikin gida, wannan haukan da kuke duk na menene?" Cewar Salim ɗin. Shi dai Ya Ameen sai kallon ikon Allah yake, nan ne inda zai bar ƙanwar tashi? Da irin wannan kishiyar? Lallai akwai damuwa. Zuƙunnawa yayi ƙasa, yana mai ɗauko waya ta da idanun shi suka sauka a kanta, ta yi watsa watsa kuwa, ya ci screen "Ba zanyi ba Salim, wallahi ba zanyi ba, wannan ma Ƙarami ne, Indai wannan ne hauka, yanzu ma na fara, sai ka sake ta, wato an hana ka waccen mujiyar, shine yanzu aka laƙa maka wata nunar ranar ko? Ana baƙin cikin zama na ni kaɗai ko? Ni za'a munafunta? Da kai da tsohuwar mahaifiyar ka...." tsalle guda kawai yayi, sai gashi gaban ta, yana mai sakar mata ɓarin makauniya a duka kumatun nata. Ihu ta sake ƙwallarawa, yayin da tayi wani kukan kura tana mai cewa" Ni zaka mara akan wannan banzar? Wallahi akan matar ka zan rama, wallahi sai na nakasa ta yau a cikin gidan nan, sai na nuna maku kalar tawa haukar" tana mai yo kan Afnan da sauri. Baya na na tura ta, ina mai tarar Ma'un cikin dakiƴar zuciya, ba zan iya bari tayi mata wani abu ba, wani mugun naushi ta kai mana mu duka ni da Afnan ɗin, yayin da Nihal ta wuntsilo daga saman Gadon, tana mai tare mu da muke shirin zubewa ƙasa, shi ma Ya Ameen da sauri ya isa garemun, taro mu yayi mu duka, muka zube a jikin shi, ina mai sakin sauti "Wash" Da ƙarfi Salim ɗin ya sake fuzgo Ma'un, yana mai sake ɗauke ta da wani gigitaccen mari. Zubewa tayi ƙasa tana mai sakin gunjin kuka, Amman duk da haka bata sare ba, ta sake yunƙurawa tana mai yo kanmu, wanda nake tallafe jikin Ya Ameen ɗin, ita kuma Afnan ɗin tana bayan shi a lafe. Fizgo ta ya kuma yi, ta ja turjiya da wata irin zamiya. Bai ƙasa a guiwa ba, ya ɗauke ta cakkk, yana mai nufar hanyar falo da ita, sai zillewa take, tare da faɗar baƙaƙen maganganu. Kuka sosai Afnan ke yi, bata san haka ba, Salim bai ɓoye mata komai ba, daga labarin Ma'u ɗin, amman bata ɗauka abun ya kai haka ba, tana sonshi, amman da wuya in zata iya jure ma zama a haka, watarana ai sai ta nemi kashe ta, daga ita sai ita cikin gidan. Bisa wata kujera da tayi saura basu tuntsirar ba ya wurgi da ita, har saida ta buge kai, sannan ya bita yana mai danne ta, tare da sakar mata nauyin shi sosai. Ihu take yi sosai da sosai, yayin da sauran matan ganin maza, sai jikin su ya fara yin sanyi, duk suka nemi ficewa. "Kada wadda ta motsa" Ya Ameen Ya faɗa cikin kaushin murya, idanun shi sunyi jawur. Cak suka ja suka tsaya, jikin su na karkarwa, tun da suka haɗa ido dashi suka fara ɓari, basu ga alamun shi ɗin ƙaramin mutum bane, tun daga shadda, zuwa wayar dake hannun shi, kalar fatar jikin shi, tare da diri na cikakken namiji da Allah ya bashi. Afnan ya sanya hannu yana mai jawo ta gare shi, rungume ta yau sosai, yana mai share hawayen fuskar ta, "Am Sorry Lil, ɗauko Hijab ɗinki mu tafi" ya faɗa cikin sigar lallashi, cike da tsantsar takaici a cikin muryar shi. Gyalen ta da ya faɗi ƙasa ta zuƙunna ta jawo, tana mai yafawa. Hannun ta ya kama da niyyar juyawa da ita su fice, ba zai iya barin ta ba, ba zai iya barin ƙanwar tashi da yafi ƙauna a kashe ta ba. Gaban shi na sha da sauri, fuska ta tam, babu alamun wasa, girgiza mashi kai na shiga yi. Ba'a haka, idan da wani gurmi ma sanyawa a bar gida, da tuni shi ma na bar nashi. Dakatawa yayi yana kallo na, nima cikin ido make kallon shi "Noo Dear, ba inda zata, nan gidan mijin ta ne, infact ma duka duka shekaranjiya aka kawo ta, bana goyon bayan mu tafi da ita, zamu yi sanadin auren ta, tana son mijin ta, yana sonta, and Salim na iya ƙoƙarin shi, babu inda zamu je da matar shi, bamu da ikon tafiya da ita yanzu, sai in har shi ne ya bada goyon baya, mu saka ido muga matakin da yake shirin ɗauka, you see a gaban idon ka, ba wai zuba idanu yayi ba" Magana ta ta dake shi dan haka ya saki hannun Afnan ɗin, yana mai juyawa ya kalle ta, yaga yanayin ta. Sauke kai ƙasa tayi, cikin rashin sanin madafa, sai dai ga alama itama bata son tafiyar, dan haka ne ya sake janta zuwa bakin gadon ya zaunar da ita. Duk muna tsai tsaye, wani irin ciwo da yunƙuri nake ji, saidai ina daurewa ne, kada na kuma tada masu da hankali. Durƙusawa yayi sosai a gaban ta, share mata hawayen fuskar ta yake, yana girgiza mata kai, Alamun ta bar kuka. Hannayen shi duka ta kama, tana mai runtse su Sosai. "Yaya i love him, i cant goo please" ta faɗa cikin rauni. Gyaɗa mata kai ya shiga yi, "Its Ok Lil, ba inda zaki, indai zaki iya zama a gidan mijin ki, and i cant let that Womens go freely, hear" ya faɗa cikin shigar lallashi. Itama gyaɗa mashi kai ɗin take yi. Duk komawa sukayi bakin gado suka zaune, lallai tau sun ga tashin hankali, ashe duk girman ka, duk yand aka ke jinka, wani cen da idanun shi suka rufe zai iya wilulaƙanta ka a idanun kowa? Ashe su ɗin ba wasu bane a rayuwa? Yau da babu Suhan ɗin ya zasuyi? Tsayuwar ta a wajen ta basu kariya fiye da yanda suke tunani. Yayin da ni kuma na shiga takawa a hankali ina mai kai komo cikin ɗakin, saboda mara ta dake tsunkulawa, akai akai shi kuma ya kan ɗago kai ya lallace ji haka, cikin tausaya wa, tare da ganin ƙarfin hali na tare da jajircewa ga ƴan uwan nashi. ************ "Ki natsu Ma'u, banson hauka, waccen fa Matata ce, ita kike zagi a gaba na? Ita zaki duka a gaba na? Amaryar tawa? Ina sonta ne Shiyasa na aure ta, and ita ce Matata for now" ya faɗa shima cike da ɓacin rai. Cak ta tsaya da kukan, tana mai ɗagowa ta kalle shi, "Kenan kana nufin kafi sonta da ni?" ta jefa mashi tambaya, "yes" ya bata amsa cikin tabbatarwa... Kururuwa ta sake sakawa, tana mai yunƙurawa zata nufi ɗakin, ya Gizgo ta, yana mai sake jefa ta saman kujerar, mistakenly ta taka wata ƙatuwar ƙwalba, ta shige ta kuwa sosai. Ihu da kururuwa ta sake saki, jini na malalowa kaman an yanka kaza. Bai ko kula ta ba, ya nufi ɗakin, a bakin ƙofa ya tadda matan, duk sunyi tsamo tsamo, tak suke jura su zura da gudun bala'i. Bai ɗauka zata iya tasowa ba, hakanan ta zare kwalbar, saboda masifar bala'i ta ɗangyaso hakanan zuwa bin bayan shi. Saidai yaji mugun duka daga ƙyeyar shi, (Gummm) da sauri ya juya, Ma'un ce riƙe da ƙaton icce, lokaci guda tana mai yoea hanyar cikin ɗakin da azama. Gara duk ta bisu ta kakkashe su, kowa ma ya rasa. Da sauri Ya Ameen Ya miƙe, ganin abunda ya faru, lallai matar nan bata da hankali, dole ya ɗauki mataki, hakanan Suhan ke hana shi, dole ne ya sanya a fidda matar nan a cikin gidan nan. Police yayi ma waya, take kuwa sai gasu, Salim ya bugu sosai ta ƙyeya, saboda haka dole saidai ya samu waje ya zauna, yana mai dafe ƙyeyar da jini ke kwarara. Saidai me, tana isa gaban Ya Ameen ta kasa taɓuka komai, hannun shi soke cikin aljihun wandon shaddar shi yake kallon ta, ƙafafun shi a ware alamun babu wasa a cikin idanun shi. Sai kuma ta saki kuka, "Allah ya isa tsakani na daku, kun cuce ni, kun raba ni da miji na, gashi kun kawo mashi ƴar uwar ku, saboda kuna ganin kuna da kuɗi, da yardar Allah wannan auren babu inda za shi, indai an yi shi ne dan aci amana ta" ta faɗa cikin gunjin kuka. Ɗan murmushi ya saki na takaici, baya son kukan mace, saidai kukan Afnan a yanzu shine kan gaba a komai, bata da hankali mahaukaciya ce, saboda haka ko ƙala bai ce mata ba, saidai ta coge a wajen tana sakin kukan daɗi zance, ana haka ne sai ga ƴan sanda sun shigo da saurin su kuwa, yana ji yana gani aka tasa ƙyeyar Ma'u da sauran barandan ta, zuwa Police station. Waya Ya Ameen Ya sanya na kira Umma na, ina mai faɗa mata dukkan abunda ke faruwa, tare da cewa bama so wani ya sani ne, dan haka ta turo haɗimai su gyara wajen kafin safe a sake danki. Ba jimawa aikuwa sai ga mota ɗauke da mata huɗu, shi kuma Ya Ameen Salim ya ɗauka zuwa asibiti aka yo mashi dressing, saida muka ga komai ya daidaita, sai wajen ƙarfe sha biyu muka baro gidan, jikin Nihal yayi sanyi sosai, haɗa ma Saudat, sunga tashin hankali, kowa da irin ƙaddarr shi, ita kuma Afnan tata ta kishiya mahaukaciya ce. Kuka Afnan tayi ta yi, saida muka yi ta lallashin ta, tare da taimakon Salim ɗin, wanda yake ƙarfafa ma kanshi guiwa, wajen ganin komai ya tafi normal,duk da haka saida Ya Ameen Ya skaa baki sosai, yana mai shaida mata cewa duk abunda take buƙata ta mashi magana. Tin cikin dare ya faɗa ma Ammi, dan haka tun da safe sai ga mata ta sake turowa, aka zo aka sake gyara ko'ina, tare da kiran wani Company na interiors suka zo suka yi repairing duk abunda aka lalata a gidan. Ran Ya Ameen Ya ɓaci sosai, Ya tausaya ma Salim sosai, rashin dace da mace ta gari ma wani babban bala'i ne, dan haka da kanshi ya je Police station ɗin ya saka aka sallama ma'u, domin dai har yanzu ita ɗin matar Salim ce, kuma akwai girmamawa a tsakanin su, ko ba komai shi surukin shi ne, kuma ɗan uwa ga matar shi, Amman sauran matan cewa yayi a riƙe su zuwa kwana uku sun ji jiki, sannan. Aiko Allah ya isa suka dinga da ƙara ma ma'u, domin kuwa basu biyo ta ba, saida tayi ma kowacce alƙawarin 20k cash, kafin suka yarda suka zo, duk da suke ƴan uwanta, ko ma ina zata same su ta basu? Sai gashi basu samu ko sisi ba, sun ƙare a cell. Ya so ya kai mu washegari mu dubo Afnan ɗin, ni ce na hana shi, ganin kada aga zaƙewar mu, masalan ma gashi Salim ɗin yana iya ƙoƙarin shi, sai ga Ammi ta kira tana bada haƙuri. Salim ta kira shima tana mashi faɗan rashin sanar da ita tun da wuri, bai yi wata shawara da kowa ba, takarda ya rubuta mata ta saki ɗaya, tare da gargaɗar ta cewa idan ta sake yunƙurin shiga hidimar iyalan shi, zai saka a kulle ta har igiya tayi rara. Aiko ihu suka dinga zundumawa ita da ƴan uwan nata, bata tashi nadama ba wai sai a lokacin, bai ko tsaya sauraren su ba, ya sanya kai yayi gaba, har yanzu ƙyeyar tashi a ɗinke take. Wai sai kuma Ammin Shi Abban shi suka hau mashi masifa, tayaya zaiyi wannan hukuncin ba tare da sanin su ba? Bai gudun zagin bakin mutane, zasu ce daga yin auren shi, ya saki uwargidan, mutane ba zasu tsaya la'akari da me ya faru da yayi sanadiyyar sakin ba. Shi ɗin dai ba wannan ne a gaban shi na, yana son samun sa'ida ne a cikin gidan nashi, hankalin shi yake so ya Ma'u tayi rashin miji ɗaya da ɗaya, tayi rashin suruka, bata yi wayau ba, dan haka yana komawa ya saka aka kwashe komai aka kai mata, duk da ba nata bane, Amman ya bata, kuma ko ba komai har yanzu da zuri'a tsakanin su. Dama ba wanda ya san anyi sai Umma ta, itama bata gaya ma kowa ba, wannan ai matsala ce ta ciki gida, so no need ace an faɗa ma wani. Cikin daren da aka tsara komawa washe gari, bamu kwana lafiya ba, naƙuda nake gadan gadan, ai fa ba zama, da an yi shiru da maganar aga yanda hali zai bada, saidai Ya Ameen da ke kai gwauro da mari, ya kasa haƙurin jurewa, tun cikin daren aka kira Mom, cewa tayi zata taho aka hana ta, inda washegari bai hana an maida ƴan biki ba, Amman Ya Ameen Ya ƙi tafiya, ba yanda ba'a yi dashi ba, shima Dad cewa yayi a ƙyale shi kusa da matar shi, ko ya taho ba zai iya aikata ma kowa komai ba. Haihuwa ta ƙi, wasa wasa sai gashi har wani daren yayi, ga bala'i kawai da nake sha, ta kai ko numfashi da ƙyar nake yi. Mai martaba ya kai ma koken shi, na hana a kaini asibiti da akayi, ana ta ɗura man jiƙe jiƙe, dayake al'adar tun kaka da kakannin ce hakan. NAn da nan kuwa mai martaba ya sanya aka fiddo mota. Ko da aka fiddo ni, sai gani akayi Ya Ameen na zurarar da hawaye sosai, kaman mace, ganin yanda na galabaita sosai. Na tantance matsayin uwa ga ƴaƴan ta a duniya, sunan Umma ta kawai nake kira da Ya Ameen, ina faɗin su yafe man, na sadaƙar da rayuwa gabaki ɗaya, gani nake kaman ba zanga abunda yake cikin ciki na ba. A haka aka nufi asibiti mai kyau dani, inda masarauta ke da File. Nan fa duk gari ya ɗauka ne cewa *Gimbiya Suhan zata haihu, mutane da dama ne ke taya ni addu'a da fatan sauka lafiya, saboda tsananin kirki da adalcin masarautar* Hankalin Umma ta idan yayi dubu ya tashi, daurewa kawai take gaban mutane, ko da aka ajiye ni gida, sai ta ji kaman ta faɗi cewa a taimaka a kaini asibiti, sai taga yanda Mama Fulani ke ƙoƙarin ta a kaina, bari dai ta kauda kai, tunda sai dai ta shige banɗaki ta ci kukan ta ta gode ma Allah, idan kuwa sujada tayi, ta kan yi kaman rabin awa tana kai koken ta ga Allah, bata fatan ace ta ɗago daga sujada ba'a zo ance mata gani cen na haihu ba. Bata manta wahalar da tasha lokacin haihuwa ta ba, faɗi take ta yafe man, "Ya Allah kada ka jarabbi yarinyar nan da shan wahala yayin haihuwa, kaman yanda nayi lokacin haihuwar ta, na yafe mata Ya Allah, ka bata ikon sauke abunda ke cikin ta lafiya" tana addu'a ruwan hawaye na malala a saman fuskar tata, saidai ta sanya ɗan farin hancky dake hannun ta ta share, ita kaɗai tasan yanda take ji cikin ranta, saboda haka ne ma ta sallama duk haɗiman wajen da take ɗin, gudun su ga uwar gijiyar su ta kuka, har kai lokacin da Nurse ta fito da gudun ta, tana mai dosar Office ɗin likita cikin tashin hankali... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ _Kaman yanda na alƙauranta, wannan page gabaki ɗayan shi ɗungurum sadaukarwa ne ga *MIJIN BAHAUSHIYA FANS GROUP* Haƙiƙa muna jin daɗin goyon bayan ku garemu, ga yanda kuke jajircewa wajen yi mana comment, da nuna mana cewa saƙonnin mu na isa gareky cikin sauƙi, ba abunda zamu ce, illa Allah ya barmu tare, ya ƙara danƙon ƙauna. Gashi nan kuyi waja waja dashi, ku ba wanda kuke so ya karanta, ku hana wanda bakwa so ya karabta, lol.. Naku ne, abu naku maganin a kwaɓe ku_ *Page ~92~* *Ya Ubangiji bamu da tsumi bamu da dubara, bama da wayau bama da fasaha, kai kaɗai ne Allah, kai kaɗai muke bautamawa, kai ke jin ƙan bayin ka, dan tsarkakan sunayen ka guda tis'in da tara, dan tsarkakken mulkin ka, domin fiyayyen halitta, kuma habibin ka, masoyi ka, kuma annabn ka, (Muhammadu SAW) ka yaye mana wannan cuta ta COVID-19 ya Allah ka dube mu da idon Rahma, ka yafe mana dukkanin laifukan da kukayi maka, mun ƙasƙantar da kanmu zuwa gareka, muna masu tuba da istigfar, Ya Allah mu masu laifi ne a gareka mun sani, mu masu saɓa dokar ka ne, ka jarabce mu, kuma mun amshi jarrabawa da hannu bibbiyu, kayi mana afuwa, kayi mana gafara, ka yaye mana wannan annoba da ka jarabce mu da ita. AMMEN YA RABBAL ALAMEEN, YA ZULJALALU WAL IKRAM, YA HAYYU YA ƘAYYUM, BIRAHMATIKA ASTAGISU.* ***************** Cikin matsanancin sauri Dr Aleeyu fito, yana mai ɗora farin medical glass a saman fuskar shi. Ta gaban su ya wuce, kai tsaye labour ward ɗin ya nufa, hankalin shi a matuƙar tashe, yarinyar na shan wahala. Gaban shi Al'ameen ya sha, fuskar shi tana haɗe, lokaci lokaci yana iya jiyo nishin ta, saboda bakin labour ward yayi ma kanshi masauki. Ya kasa tsaye ya kasa zaune, idanun mama Fulani tun ɗazu a saman kanshi,tana mai jinjina irin wannan kula ta yaro, tabbas ko ba'a faɗi ba, ta fahimci cewa Suhan ɗin tasu ta yi dace da miji na ƙwarai. "Dr matata.. Please Dr, do what you can as soon as possible, i dont want lose her, she's my life.." saurin girgiza mashi kai Dr yayi, "Insha Allahu ba abunda zai faru Yarima, muna iya ƙoƙarin mu, and insha Allahu she will get her self, just pray for her" yana gama faɗin gakan ya zagaye shi ya shige ɗakin. Shiru shiru ba Dr ba alamun shi. Ni kuwa ta ɓangare na, azabar ma ba zan iya misalta ta ba, cikin wata irin dakiya da na aro na yafa, duk da nishi da tsananin jinin da naga yana zuba a jiki na. Bansan lokacin da na kamo hannun Dr ɗin ba, "Dr ka kira man Umma ta, da miji na, nasan ba zan tashi ba, dan Allah su yafe man, Dr duk yanda zakayi ka cire abun da yake jiki na, kada ka bari Ya ameen ya rasa gudan jinin shi, koda ni ba zan tashi ba, ka faɗa ma abunda na haifa, na yafe mai, kuma zan tafi ina mai farinciki, kasancewar na bar wanda zai yi man addu'a.. Dr... " kuka ne ya ci ƙarfi na sosai, Fuskar Ya Ameen kawai nake kallo, irin yanda yake shiga tashin hankali idan bana da lafiya. Balle wannan haihuwa, ƙafa ɗaya a duniya ƙafa ɗaya a lahira. Sake gyaɗa man kai Dr yayi, yana mai matse wasu ruwan allurai a cikin drip ɗin da ya saka man tun shigowar shi. "Kiyi haƙuri kinji, ai kin sha wahala gaskiya, Amman zaki haihu da kanki insha Allah, ba ma sai an yanka ki ba" ya faɗa cikin tausaya, yana mai dawowa saitin inda cikin nawa yake, ya shiga mammatsa man a hankali a hankali" Wata irin jijjiga da girgiza na fara yi, haƙora na suna haɗewa, tare da bada wani sauti ƙas.. Ƙas, shi kanshi cikin nawa sama da ƙasa yake yi sosai, ganin hakan ne ya saka likita kiran abokan aikin shi suka rufu a kaina. Ni kuwa zufa har ƙarƙashin tafin ƙafa ta, wai nan ma sun ɗaɗɗaure ni sosai, ganin yanda nake jijjiga zan iya faɗowa daga bisa gadon, gashin kaina nake kama ina fizga, tsabar bala'i, bansan a inda kaina yake ba, abunda kawai nake iya jiyowa likitocin suna faɗa shine free eclampsia, na bani no suhan, ba dai ciwon tsinkau tsinkau ne yake shirin kama ni ba? Da sauri Dr ɗin ya bada umurnin shirya Emergency theater, tare da fita wajen Ya Ameen domin ya saka Hannu. Ƙinbl sakawa yayi, kamar ƙaramin yaro yake kuka, hatta da Dad lallashin shi yake yi, wanda ya iso tun jiya cikin daren, baya kallon kowa, hakan ne ya karya ma Ummata zuciya, ta saki kukan ta a fili, tana faɗin "Ya Allah ga yarinya ta nan, Ya Allah kada ka jarabe ni da abunda kasan ba zan iya ba, ita kaɗai ka bani, ita ce sanyin idaniya ta, ita kaɗai nake gani ina tuna muhammadu, ita kaɗai ce ta rage man a duniya, Ya Rabbi ka ɗauki rayuwa ta nima, idan har ka san ba zata tashi ba, babu amfanin zama na a wannan duniyar, ya Allah duk wanda nake so sai ya mutu, yarinyar nan ta sha wahalar rayuwa sosai, ya Allah ka barta hakanan ta huta, ka yaye mata, ka huwace mata, Ya Allah ni mai bauta ce a gare ka, ka kawo ma yarinyar nan sauƙi ya Allah, ka sanya ta haife cikin nan lafiya" Kuka sosai ake yi a wajen, masalan ma Nihal, Saudat ma kukan take yi, Ya Allah ashe haka haihuwar take? Me ya shiga kanta ne haka? Haka Yayan ta ke son matar shi? Bata taɓa ganin kukan Ya Ameen irin yau ba, sai gashi Dad ya rungume shi yana lallashin shi, kaman ƙaramin yaro. Kukan Umma ne ya sake ɗaga ma kowa hankali a wajen, duk kawaicin Umma, duk haƙurin ta, sai gashi ta zube ƙasa saman tiles tana kuka. Wane irin tashin hankali ne haka? Dad da kanshi ya sanya hannu, yana mai faɗin "Gara a yanka ta a cire koma menene a cikin, da muzo mu rasa su su duka" da sauri Dr ɗin ya koma ciki. Bansan inda kaina yake ba, duk na daddatse baki na, har jini ke fita, ga surutai ina ta yi, wanda duk ya fi alaƙa da Ya Ameen, sai kuma Afnan, wanda abunda ya faru da ita a daren ranar nan ya tsaya man a rai, haka aka fito dani bisa gado, sanye da kayan aiki, da gudu suka nufi gadon, yayin da nurses ɗin ke turawa, ba tare da sun tsaya sauraran su ba. "Ba zaku tsaya in gana da matata ba ne wai? Ko sai kun fiddo man da gawarta ne?" cewar Ya aameen ɗin yana mai daka masu tsawa sosai. Cak suka ja suka tsaya, ita kanta Umma rungume ni tayi gaban kowa, kuka take sosai, ta sadaƙas, ta barma ranta cewa ba zan fito ba. "Na yafe maki Mamana, na yafe maki, Allah ya baki sa'ar tashi, ya sauke ki lafiya, insha Allahu zaki haihu ki reni abunda kika haifa da kanki..." Da sauri Dr ya fito yana mai yi ma nurses ɗin faɗa, minti biyar aka ƙara nan gaba, za'a iya rasa ni da abunda ke cikin ciki na, ni kuwa Dariya ma nake, surutai nake yi, kaman ba nice ke naƙuda ba, sam hankali na baya jiki na, faɗi nake" Haha, yo kukan me kike? Menene? Me ya saka ki kuka wannan matar? Kai kuma wanene? Kalli fuskar shi.. Hahaha ni da bature kenan, malam ka sanni ne kake riƙe man hannu? Ina za su kaini? Ku sake ni in tashi ni, lafiya ta lau" surutai dai marasa kan gado. Hakan ya sake birkita kowa, kaman dai ƙwalwa ta ta juye, ji surutan da nake kaman mahaikaciya. Har bakin Theater yana riƙe da hannu na, daga nan ne aka dakatar dashi, bai ko saurare su ba, har ciki ya bisu, yayin da Umma ta dakata daga wajen, tana mai hango ni take man kallon ƙarshe Sai da ƙyar Dr ya lallaɓa Ya Ameen ya futa, duk da haka bakin ƙofar ya tsaye, hannayen shi saman fuskar shi, da ƙyar yake iya buɗe idanun shi saboda zogi da raɗaɗi da yake mashi. Cikin ikon Allah, ina shiga kuma sai faya ta fashe, ko kafin a cicciɓe ni zuwa saman gadon aikin, sai ga kan ɗa da ƙarfi ya fara ɓullowa, sosai Dr ɗin ke dariya, ya ji daɗi sosai, duk da mamakin da take yi, tabbas a wannan halin da nake ciki, ba kowacce mace ce take shiga cikin shi ta haihu lafiya ba, dan danan aka cenza man gado, kafin kace me sai ga sunkuceciyar yarinya ƙatuwa jawur da ita ta faɗo, ai kuwa tana faɗowa ta tsanyara kuka da dukkanin iya ƙarfin ta. Da ƙarfi ya bankaɗa ƙofar ɗakin ya shige, kai tsaye wajen gadon ta ya nufa da gudu, har an ɗago babyn an ɗora man saman ciki, inda baki na yayi laƙwas, kaman ba ni ce mai surutai ba. Wata Nurse zata yi mashi magana, dr yayi saurin girgiza mata kai, ya fahimci ko me kenan, za'a iya samun matsala dashi muddin aka hana shi, balle Jarumi fasihi haziƙi, kuma babban mutum kaman Al'ameen da duk faɗin ƙasar an san dashi, yau gashi a asibitin su, yana mai masu magiya akan matar shi.. Yana tsaye riƙe da hannu na ake gyara ni, duk da wani mugun bacci da ya kama ni ina haihuwar, kallo na kawai yake yi da babyn cike da sha'awa. Yarinya ƙatuwa har haka? Ai dole asha wahala,ni kuwa na nutsa sai baccin wahala nake, ina sauke numfashi ɗai-ɗaya Hankali kwance nake bacci, har an gyara ni da baby, an naɗe ta cikin wani farin tawul, mai sirkin ruwan samaniya mai haske, murmushi kawai take saki, har fuskar shi ta fara washewa. Dr ne ya miƙa mashi Babyn yana mai cewa "Congrat Ranka ya daɗe, ina goron Albishir ɗina?" Amsar ta yayi cike da fara'a da maɗaukakin farin ciki a saman fuskar tashi, yana mai rungume ta cikin ƙirjin shi, "You will travel to saudiyya insha Allahu Dr. Nagode nagode, Allah ya saka maka da alkhairi, kayi ƙoƙari sosai" Tsayuwa Dr ya gyara, cikin jin daɗi yace " Nima ina godiya, sannan ina ma yaro na kamun babyn nan, wadda ta ba mahaifiyar ta wahala, na san za'a so ta kaman nama tsoka ɗaya a miya" dariya suka yi su duka, yayin da Dr ya koma wajen wasu gyare gyare a ɗakin, shi kuma Ya Ameen sake ringume ɗiyar shi yayi, yana mai jin ƙaunar ta, ya zu nan fa tashi ce ko? waje ya dosa riƙe da babyn a hannun shi. Tin daga nesa suke hango shi riƙe da wani abu nannaɗe a tawul, kafin ma kowa ya isa inda yake Umman ta isa, tana mai cewa dashi "Ina Suhan? Tana raye?" gyaɗa mata kai yai cikin jin daɗi da murna, yana mai miƙa mata babyn. Amsa tayi, tana mai rungume ta cikin jikin ta tsam, tsam. Godiya ga Allah ta shiga yi, Suma su Mama Fulani duk wajen suka ƙarasa, suna masu amsar baby ɗin, zagaye ta akayi ana kallon ta, gwanin ban sha'awa, ɗiya kamar ƴar aljannu, hasken da kalar fata da komai na Ya Ameen ne, sak kaman an tsaga kara dashi. Lokaci guda ya ji ƙaunar yarinyar ya ɗarsu a zuciyar shi, duk da hankalin shi na kan Suhan ɗin, wanda Dr ya sake tabbatar mashi bata da wata damuwa yanzu, duk abunda ya kamata ayi mata anyi mata, da ta farfaɗo ne ma za'a iya basu sallama in ta huta. Ɗan rankwashi na wasa Umma ta kai mata a kai, tana mai cewa "Ke dai anyi ja'ira nan, sai da kika wahalar man da ƴa sannan ko?" Mama fulani ce ta janye ta tana mai cewa "Ba ruwan ƴata, ɗiyar ki dai ce raguwa, amman zaka haifi wannan ƴa masha Allah ka dinga raki?" duk dariya aka saka, shi kuwa Ya Ameen waje ya fice, saboda kunyar da yake ji, na irin kukan da ya dinga sha ɗazu akan Suhan ɗin, yanzu kowa ya gane cewa Suhan ɗin ita ce week point nashi. Kafin dare, sai gamu shar, har nabtashi an bani team mai kauri sosai nasha, Sallama aka rubuta mana, haka muka baro asibitin, tare da Jaddada ma Dr da Ya Ameen yayi akan zai koma su ga juna. Mom kau kaman tayi tsuntsuwa ta taho, har video call take kira a bata, sai gashi an shantake a masarauta. Ganin haka Umma tace a tattara ni a maida ni ɗaki na, suruka ta tana yin kara, gashi tana son ganin baby, amman Dad ya hana ta tahowa, kuma duk ƴan kankiya na cen suna jiran mu, shi kanshi Ya Ameen yayi murna, kafin mu taho saida Salim ya kawo Afnan taga baby dani, santi ta dinga yi, tana kama ƙafar babyn tana mata wasa, yarinya idanun ta tar take kallon kowa, ga hancin har baka ga dimple irin na Ya Ameen ko ya ta motsa sai ya lotsa, sannan ga na gemu, ni kaina cikin dare sai in tashi in ta kallon ta, idan naga kowa yayi bacci, masalan idan ina bata nono, wai yau ni ce ke da ɗiya tare da Ya Ameen, wanda ada nake ta tunanin cewa *Ya Fi Ƙarfi Na* wani shauƙin son miji na ke kama ni, masalan ma da yarinyar ta biyo shi sak, hadda kwantacciyar Sumar kan tashin. Duk a tunanin shi Sashe na za'a wuce dani, ya ƙagara ya keɓe ni da ɗiyar ya nuna mana zallar ƙauna, da yanda yayi missing ɗina, saidai saɓanin haka, sashen Mom yaga an wuce dani kai tsaye, duka ni da ɗiyar Mom ta rungume, bamu san ya akayi ba, sai gani mukayi tana hawaye, "Ashe da na mutu? Rabon wanann yarinyar sai ta taka duniya, ashe da rabon ta ya kashe ni, ki yafe man Suhan, ki yafe man dan Allah" abunda ta dinga faɗa kenan, har ta fara karya man guiwa nima na fara ƙwalla. Ya Ameen ficewa yayi zuwa namu sashen, duk baiji daɗi ba. Dayake tare da Nihal da Saudat muka taho wanda naga duk ta cenza, sai ta dinga ɗaukar baby tana mata wasa, tare da man wasu ƴan aikace aikacen cikin jin kunya. Suma gida suka wuce, da niyyar washe gari zasu dawo. A ranar sai ga Ummin Bilal, da shi kanshi Bilal ɗin, kai naga jama'a, naga mutane, ashe haka Ya Ameen ke da mutane? Ƴan kankiya ma duk suna nan suna jiran mu dama. Nan fa gida ya ɗin ke, duk inda ka yi labarin kyau da girman baby ake yi, lallai soyayyar Ya Ameen a cikin zukatan ƴan Family ɗin ce ta shafe ni, ni da ɗiya ta, kowa so take insan da ita, kai har maza ma, kowacce so take ta ƙulla alaƙa dani, to nima ina sonsu Kafin kwana uku sai gamu munyi shar, umma na Adamawa cen muka baro ta, Mai martaba ne yace ta tsaya yana son ganin ta, fna haka babu abunda nuka nema muka rasa. Hatta da kaka zuwaira, kullum sai ta digaro ta zo ta ganmu, ko ƙuda kuwa bata bari ya taɓa babyn. Kayan barka naji da gani Mom ta haɗo mana ni da baby, Ya Ameen ma ya kawo nashi, wanda zuwabyayi ya zauna dirshan su Nihal suka dinga zaɓar man suna tuntsura dariya, masalan idan yace kada a kashe shi fa, ganin irin expences ɗin kayan da suke ɗaukar man da baby, sai ga Bilal shima da wasu akwatuna, yarinya tayi goshi, ga wayau sosai, wani lokaci saboda ɗauka har cuwon jiki take yi. Saidai Nihal ta goya ta bayan an mata wanka, dayake kullum suna zuwa, yanzu har mamakin Saudat nake ta zama wata cool, magana ma a tausashe take yi man ita. Ya Ameen yana cen yana jin haushi, Mom ko sakewa bata bari yayi, da ya ɗauki Baby zatace dalla ajiye ta ka futa mara kunya mara ta ido, kawai, dole sum-sum yake yi ya fita. kafin suna naga mutane kala kala, tabbas na yarda cewa jama'a Allah ne ke ba mutane su. Alhamdulillah zan iya cewa yanzu bana da wata matsala gaskiya, Mom ta zame man Umma number 2, ban ɗauka tuban nata na gaske bane, sai gashi, yanda take so na da ririta ni, ko su Nihal bata ma haka. Aunty Feena ma bata koma ba, duk muna sashen Mom tare dasu. Ranar suna kwatsam muka ji Sunan ɗiya *Maryam* duk munyi mamaki, ni na ɗauka ma Sunan Mom za'a saka, ashe Mom ce ta tubure lallai sai sunan Umman, tace ita ta yafe, gaba a saka nata. Munyi kyau mun gaji da haɗuwa, abun mamaki ƙauye Ya Ameen yaje ya kwaso su Hajjo da malam, dasu aka sha suna, daga nan zasu wuce cen Adamawa wajen Mom anan ne muka ji irin abun Alkhairin da Ya Ameen yayi masu. Hada ni wajen yi mashi godiya, saidai ya rufe man baki kawai da nashi, da sauri na matsa, a ɗakin Mom nake, kuma ga ƴan suna suna shigowa akai akai, na kula Ya Ameen duk ya cenza, yanzu jin kan shi yake Daddy, komai na yi sai yace "Yanzu fa ni Dady ne Mummyn Umma" Haka taro ya watse, kowa ya hakarta, Ranar Sunan Umma ta dawo, ansha suna an gama lafiya, ni kaina ba zan iya cewa ga abun alkhairin da na samu ba, da wanda Baby ta samu, Mom ce tace a buɗe mata Account a sai mata hannun jari, haka kuwa akayi, sai gashi bayan suna muna ta baccin dole da na gajiya. Gida ya gama watsewa, kowa ya kama gaban shi, daga mu sai halin mu, anan ne fa Ya Ameen ya kulle ido, shi lallai saidai a mayar mashi da matar shi, Mom zata hana Dad ya ce akan me? A maida mashi ni cen mu ƙarata, yanzu haka ginin gida na inda zamu koma mu tare yayi nisa, nan dai cikin layin ne, saidai cen ƙarshen layin ne. Naji daɗi, ba wai dan bana son zama da iyaye na bane, saidai gaskiya akwai takura, baka sakewa ka nuna ma mijin ka ƙauna a ko'ina idan ba kai kaɗai bane a gidan. Ina da sati biyu aka maida ni sashen nawa, naga zallar ƙauna, ko ina an bibbishi shi da teddys da kayan wasan yara, kama daga su flowers da sauran su, ikon Allah, abu fa ya zo ga ma'iya, kukan aure da sallallami. Yarinyar da dududu 2wks har an fara mata kwashe kwashe. Zama ne muke cikin so da ƙaunar juna, mukan kwashe awa uku da ya Ameen cikin gidan nan yana ma yarinya wasa, tun bata fahimta, har ta fara fahimta, kullum cikin mata hotuna yake yana sanyawa a status da dp, IG da FB. Nan za'a yi ta liking ana mashi comment, kowa yaba kyaun ɗiyar yake, da wayon ta, da tsabar kamannin ta da mahaifin ta. Hankali na ya kwanta, har ƙiba ta na narka, in ba Feeding na Baby nake yi ba, to indai yana gidan za kaga yana ɗauke da ita, ko aiki yake latsa system ma da yake yi da ita a saɓe a kafaɗar shi, na rasa inda ya koyi reno, da nayi magana sai yace wai nima haka yayi man, har fitsari da kasho ya wanke man, kunya ce ke kama ni, saidai na shige kitchen ko ma share shi ina dariya. Har goyo Ya Ameen ya iya, sai ya goye ta tsaf, yarinya har ta saba dashi, da ta ganshi zakaga tana ɓangala dariya. Wata ranabkuma idan baya nan, yini take cikin gida wajen Mom, sai idan ta buƙaci nono ne ake dawo da ita. Ayyukan shi suna tafiya successfully, akwai albarkar iyaye a kanshi, masalan ma yanzu da Mom ta gane cewa Addu'ar iyaye akan yaran su kaman yankan wuƙa ne, sai gashi Mom na zama Umma na koya mata karatu sosai, suna shiga sashen juna, ko Hajiya Zainab ta ji daɗin hakan, balle da ta sake tara su ta sake yi masu faɗa, yanzu duk inda zasuje zaka gansu a tare, Umma ta ɗauki Ya Ameen kaman Ni, haka Mom ta ɗauke ni kaman Ya Ameen,kusan ma zan iya cewa, duk ƙaunar da take mashi rabi da kwata kan ni da ɗiya ta ya dawo, wanda muke mata laƙabi da *Janaa* Dole aka tarkata Abie da Bilal suka koma cen American, dan Ya Ameen yace shi ba inda zashi, indai ta kama yaje ya dawo zaije, wannan karon Bilal da Ummen shi suka tafi, da Lil Ameen, nayi kewar su sosai, saboda akai akai ya kan kawo su, ko ni Ya Ameen ya kaini. Wannan shine sirrin nasarar Ya Ameen. Ga komai nashi sai ƙara haɓɓaka yake yi. Abunda ya bamu ɗinbin mamaki shine; yaran da suka yi niyyar raping ɗina a sunkui, ashe wai Ya Ameen ya koma ya neme su, kuma dukkan su ya basu aiki watau ya gina gidan ruwa a nan sunkui ɗin ya basu halak malak suna juyawa da fiddama malam kason shi duk wata, duk bamu sani ba, har saida suka shigo mota suka zo har gida suna mai bani haƙuri, tare da ce man wallahi sun shiryu, dama dai hada ƙari da rashin aikin yi. Ana cikin haka ne, maganar murabus na mai martaba ya taso, ba yanda ba'ayi dashi ba, yace shi fa lallai yayi alƙawari cewa sai ya maida ma gimbiya Merama karagar ta, duk ranar da ta bayyana. Umma kuka ta dinga yi tana bashi haƙuri, a cewar ta babu abunda zatayi da ita, zaman ta gidan mijin ta shi ne kan gaba akan komai, ba wata sarauta ba a halin yanzu. Kafewa yayi Allan baram fa sai ya sauka, dan haka ne ma aka neme su cen masarautar. Umma Dady da Mom sai ya Ameen, sune wanda suka ɗunguma zuwa Adamawar domun suji yanda komai zai kasance..... ~Oum-Deedat ce~ https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/ 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹 🌺🌺🌺🌺🌺 *~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~* *~We are bearer's of so golden pen🖊~* *~we write assidiously perceive no pain~.* *~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~* *~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~* >>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>> *Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_ *Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_ *Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._ _The End_ *Kyautar Page ga ɗaukacin ƴan ƙungiyar golden pen writers association, tare da ƴan banfi ƙarfin ta ba Fans Group, Allah ya bar zumunci da ƙauna* *Page ~92~* *Happy Ramadan Kareem* ******************* Dayake gudu yake ta faman shararawa, sai gasu nan da nan sun isa ba ɓata lokaci. Sun tadda masarauta duk ana ta hada hada, ga gyare gyare sosai ana ta faman yi, duk da sunyi mamaki, haka aka sake masu jagora, kai tsaye akayi masu iso wajen mai martaba, to ƴan gida ne ison me suke jira ayi masu, ga maroƙa sosai suna ta yi masu busa, tare da kirari. Ba ɓata lokaci mai martaba ya sanya duk aka tara hakimman shi, kaman sun san da maganar, sai gasu, duk wanda ya shigo sai yayi ma su Umma jinjinar ban girma kafin ya zauna. Zuwa kaman minti goma, sai ga Mai martaba ya bayyana, cike da kwarjini ya shiga murmusawa ga manyan baƙin nashi, gefe guda kuma ƴaƴan shi, gasu kuma surukkan shi. Bayan an gyara mashi ya zauna ne, sannan aka buɗe taro da addu'a, kowa ya natsu yaji bayani daga bakin Babban sarki mai adalci. Gyaran murya yayi, yana mai bin fuskar kowa da kallo, ciki kuwa hada Ya Ameen da yayi wani irin durƙuso cikin girmamawa, ya sadda kanshi ƙasa, dayake yana zaune ne daga gefen mai martabar, dama haka ya saba mashi, duk indai zai zauna fada, to fa haka yake jawo shi kusa dashi sosai, natsuwa kyawon hali da ɗabi'ar yaron ke burge shi. "Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu, ba tare da ɓata lokaci ba, kowa dai ya san dalilin tara mu anan da nayi, ba tare da wani dogon jawabi ba, inaso ku sani, tabbas zan cika alƙawarin da na ɗauka, dangane da mayar da karagar mulkin ƙasar nan ga hannun mai ita, kowa ya sani cewa, ba wai dan na gaji sarauta bane ya saka aka bani, a'a saidai dan babu wani makusanci da ya kamata ace an ba, tun bayan rasuwar muhammadu, da ita kanta gimbiyar, watau Merama Hasken masarauta. To kaman yanda dai kuke gani, nan ita ce, kuma kowa ya sani cewa, ta bayyana ne a tattare da ita, akwai aure mai girma a kanta, aure wanda ya tabbatar da wanzuwar farin ciki a kan fuskar mu, haka kuma Allah yayi kata zaɓi kafi alkhairi a tare da ita. Haƙiƙa muna mai miƙa godiyar mu ga Allah subhanahu wata'ala, da kuma shi kanshi Alhaji Almustapha Dambulan, wanda ya kasance ba baƙo ba ne ga ɗaukacin mutanen da ke rayuwa a ƙasar nan, alkhairi shi ya iske kowa har inda yake, haka kuma yayi dace da yaro nutsattse, kuma ɗan halak, wanda hakan ne ya sanya muka shawarta bashi sarautan *Yariman Matasan Arewa* cencentar shi ce ta sanya haka, wanda tun bamu san ma zai iya zama ɗaya daga cikin mu ba. Ba tare da ɓata lokaci ba, ina mai sanar da murabus ɗina daga kan wannan karaga, daga rana mai irin ta yau, na miƙa sarauta ga Hannun mai ita, ina fatan zata amsa da hannu bibbiyu, ba tare da ta yi man gaddama ba, a bisa umurnin da muka bata" Ya ƙarashe fuskar shi yalwace da fara'a, yana mai bin kowa da idanu, ganin yanda zasu amshi batun. Ga mamakin su Ya Ameen, sai ya ga kowa ya yalwata fuskar shi da murmushi, suna mai gyaɗa kansu, alamun amincewa. Busa aka saki gabaki ɗaya gidan ya amsa, lokaci guda kuma duk wani haɗimi dake cikin gidan, tare da barori, suka durƙusa kansu a ƙasa, alamun yin mubaya'a, su kansu Hakimman ba'a barsu a baya ba, hakan ce ta kasance a fada. Da kallo duk su Ya Ameen ke binsu, lallai sarauta ma saidai a barta. Take wasu kuyangi suka shigo tare da jakadiya, hannayen su ɗauke da wasu manyan turay, cike da kayan alatu da ƙawa. Nan da nan aka zagaye Umma, wanda take zaune gefe naɗe da ƙafa, ita kanta fuskar ta ba yabo ba fallasa. Alkyabbu da kayan ƙawa da alatu aka naɗa mata, lokaci guda kuma fadawa na ɗaukar kirari, tare da take mata baya har zuwa gaban mai Martaba ta zuƙunna ya saka mata albarka ta hanyar dafa kanta, sannan ya muƙe a hankali, yana mai ɗaukar wata ƴar wuƙa cikin kuben ta, wanda wasu haɗiman ke riƙe da wani farin tray ƙarami mai kyau. Jinjina wannan wuƙar yanka yayi, lokaci guda yana mai miƙa ma Umma ita. Amsa tayi cike da girmamawa, tare da ɗan duƙawa, wata busar aka sake saki, tare da kirari daga sarkin zagi, nan da nan kowa dake gidan suka sake russunawa sosai, suna masu mubaya'a. A hankali ya shiga matsawa, yana mai nuna ma Umma kujerar sarautar domin ta zauna. Saida kowa ya miƙe domin nuna girmamawa. Zama tayi a hankaki cikin natsuwa, shi dai ya Ameen sai kallon ta yake yi, cikin murmushi sosai, abun ya burge shi sosai, kaman a film, ikon Allah kenan, wai *Maryama mai aiki ce ta koma sarauniya ayau* Har saida Umma ta daidaita zaman ta bisa karaga, sannan kowa dake fadar ya zauna, ciki kuwa hada mai gidan nata Alhaji Mustapha Dambulan, da ya nuna goyon bayan shi a gareta, fuskar shi cike da annuri, yana mai alfahari da samun Umman a matsayin mata.sannan haka ma Mom wadda ta zama ƴar kallo a wajen. Wata irin busa aka sake saki, tare da goga goge da busar sarewa mai daɗi, sai kuma masu bindigu suka ɗauka, ji kake daram, daram, sai kuma masu busar ƙahunna suma suka ɗauka "Buuuuu" Masu algaita ma suka ɗauka, gidan fa ya hautsine, kowa ka gani farinciki yake da murna. Da sannu aka dinga shiga ana kwasar gaisuwa ga Umman, wanda har yanzu fuskar sake take ga na ƙasan nata. Hatta da Su mama fulani da Ammi saida suka shiga suka kwashi gaisuwa, tare da nuna mubaya'a a gareta. Dama saida suka shirya komai kafin zuwan su Umman, yanzu dai karaga ta zama ta Umma, komai sai yanda tayi. Ba'a yi jinkirin komai ba, aka sake shirya wata liyafar, sarakuna da suka dinga halarta da ɗai ɗaya da ɗai ɗaya, live ake ɗaukar komai, Suhan da kowa da kowa dake babban falo gidan nasu hatta da masu aiki an basu izinin shiga, yanzu Mom nada kyakkyawar alaƙa da kowa da kowa, saboda haka ne ta kira, tare da umurnin kowa cewa yaje ya kalla. Suhan kukan murna da farinciki take yi, ina ma ace tana wajen? Ina ma ace gaban ta ake yin komai? Kowa na gidan murna yake yi, sun san cewa Allah ya kaisu inda basu taɓa tsammani ba. Anci an sha, an wadata, kowa na ta murna da farinciki, ranar har ƴan sansanin gudun hijira mutanen Ya Ameen saida suka shaida, nan take Ya Ameen ya bada gudunmuwar shi zuwa ga masarauta, tare da bada kuɗi masu tsoka ga sansanin. Abun da ya fi ɗaure ma kowa kai shine, bayan an kammala duk abunda za'a yi, kowa na shirin tafiya ne, Ummar ta buɗe baki gami da tsaida kowa. Sanarwar maida sarauta ga hannun mai gidan nata ta bayar, wanda ya ba kowa mamaki sosai, nan fa wuri ya sake kaurewa, tabbas Alhaji Almustapha ba ɓoyayye bane, zasu so kuma ace ya mulke su, adalcin da yake nunawa akan ma'aikatan shi, zasj so ace ya kwatanta shi a kansu. Kuka Mom ta dinga yi, lallai ta so ta tafka kuskure, sosai abunda tayi yake bata kunya, ta ɗauka kuɗi sune sai yanzu ta gane sarauta ma wani abu ce, ko baka da ko sisi dole ayi maka biyayya. Alhaji Mustapha ƙin amsa yai. A gaban kowa, nan fa aka fara bashi baki, ana nuna mashi alfanun hakan, dama girman masarauta kaman wannan bai kamata ace an barta a hannun mace ba, da Muhammadu na raye, tabbas ba abunda zai hana shi sarauta, amman dayake yanzu baya raye, Alhaji Mustapha ɗin dai shine daidai wanda ya kamata ya amsa, dama shi abunda ya hana shi amsa, sarauta na da tarin matsatsi da ƙalubale, yanda yake babban ɗan kasuwa, da siyasa yana ɗan taɓawa, ai zata zo mashi da wahala. Saidai ba yanda ya iya, haka aka sake yin naɗi wa Alhaji Almustapha, tare da naɗa Ya Ameen Yarima mai jiran gado, a matsayin shi na mai auren Suhan ɗin, ɗiya ga Ginbiya Meramar. Kuka sai ya ƙaru ga Suhan, yayin da wasu ke murna, kiran wasu ta ko'ina Alhaji Almustapha ɗin ya sha shi, nan aka gama daddale komai, tare da tabbatar da cewa dole gimbiya Merama zata koma cen da zama, yayin da Mom zata koma abujan, duk da ita ma tana da sashen ta anan gidan, ba nan zata dinga zama ba dindindin, saidai tazo. Cen baya aka gyara ma tsohon mai martaba ya koma da iyalan sa. Suma su Ya Ameen suna da Sashe, dayake gidan babban gida ne. Sai gashi har shugaban ƙasa da kanshi yazo ya kawo ma Alhaji Mustapha ɗin ziyara, tare da ba masarauta wani sabon grant, domin yanzu ta koma kaman sabuwa ne. Kwanan su Mom Ukku suka tarkata suka dawo, da niyyar sake shiryawa domin suje su ɗanyi ko wata biyu ne acen. Kowa nurna yake, hada ma'aikatan gidan duk za'a tafi. A gaban udon mom ake ba Umma cikakken girma, kowa ya sani sarauta tata ce, dan haka sai ya kasance ma cewa kaman ita ce uwargida ga sabon mai martaban, hakan baya ɓata ran Gidan mu ya zama settle, dan haka komai an saka, tarewa kawai yayi mana saura. Abunda ya bani mamaki irin yanda Saudat ta same ni, tare da neman yafiya ta, sannan ta faɗa man duka abubuwa marasa kyau da ta aikata, wanda har rashin lafiya saida ya kaita ga yi, daƙyar ta samu ta shawo kan ta, tare da faɗa man ta tuba har cikin ranta, naji daɗi sosai, ko hakan ma aka tsaya Allah ya nuna masu ni ba wulaƙantatta bace ba. Dan haka na ƙaravmata wasu addu'oi da zata dinga yi, domin neman yafiyar Allah, somin ta aikata abubuwa marasa kyau, da Alah ke fushi da duk mai aikata su. Ko Mama Saude da zata tafi kuka ta dinga yi tana neman yafiyar mu tare da faɗa mana abubuwa marasa kyau da suka dinga aikata mana. To sauƙinta ma Ya Ameen ɗina ya bata jari mai gwaɓi, yanda ba zata tagayyara ba. Muna ganin gata, ga soyayya, Janaa kuwa ta zama abun so da sha'awa ga kowa, ko yaushe kyaututtuka take samu, idan ka ganmu yanzu ba zaka ce mun taɓa fuskantar barazanar rayuwa ba. Yarinya tayi kyau da wayau sosai, kamannin ta da mahaifin ta sun ƙara fitowa sosai, gashi sai tace wai surutai take son yi, kullum tana fada wajen nai Martaba Dad, ta cika shi da surutun gwaranci kuwa. Haka muka cinye kwanakin mu muka juya, kaman kar mu dawozmunji daɗin zama sosai, daga mu har Ya Amewn wanda sarautar tayi mashi masifar kyau soaaizsai manin munje barga yana hawan doki da Jaana, itakuma tana ƙyalƙyala dariya. inda muna komawa zamu tare a sabon gidan mu. Mom ta nuna bata ji daɗi ba, amman ba yanda ta iya, yanzu gudun yin wani abu da zaisa a yi tunanin halin ta nada cen baya yana nan. Mun tare a babban gidan mu mai kyai sosai komai yaji, Ya Ameen yayi ƙoƙari kullum duk abunda zaiyi inji daɗi shi yake yi, baya abu baiyi shawara dani ba, hatta a harkar kasuwancin shi. Tare da taimakon Ummin Bilal, Hafsat da su Nihal da Saudat muka tare, saida suka kammala mana komai sannan suka bar gidan cike da jin daɗi, da yabon gidan a bakin su, domin dai dukkan su gida na ya shefe nasu kyau da komai da abubuwan ƙawa, domin dai har swimming pool ke akwai, haka kuma ɗaki guda aka fidda na Jaana, inda aka sake cika mata su da kayan wasa, yarinya mai shiga rai da kwanciya a zuciya. Tabbas ina ganin soyayya cike da ƙauna a tattare da Ya Ameen, kuɗi na da Umma ta damƙa su a hannu na, a cewar ta miji ma ya iya komai na kasuwanci, haka kuwa akayi, ni na danƙa kuɗin duka a hannun shi, zama mukayi ni dashi muka shawarta. Babban shago na kayan costimetics da botique na mata da ƙananan yara aka buɗe, inda aka zuba manyan laces da atamfofi na girma, sai jakunkuna da takalma da blawus na yara, sai vails da kuma ƴan kunne fation, hada golds, ya amsa sunan shi kuwa, *Janaaa Collection* muka sanya ma shagon, inda kai tsaye muke bada order daga waje, ake shigo mana da kaya, hada shaddoji masu masifar kyau ƴan mali da gizners. Nan da nan shago ya karɓu, hada aseobe muna fiddawa, irin na manya, da kuma ya ku bayi, sannan bama sanya farashi mai tsada sosai. Sauran kuma kuɗi na aka siya man ƙaddarori dasu. Shi kanshi Ya Ameen ya natsu yanzu sosai, gida ya zama kaman ba wani hayaniya da ya taɓa faruwa a cikin shi. Mom na cen daga ita sai ƴan aiki, inda akai akai take zuwa cen adamawar, Umma na Adamawa tare da mai martaba, inda muma muna gidan mu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Afnan ma ta shaida man Ma'u nabta bibiyar Sakim da tashin hankali, da yafa zata ɗaga mashi hankali ya idasa cikashe mata sakin gabaki ɗaya, banso hakan ba, saidai tace Ma'un na neman shi da sharri ne, dile ce ta sanya yayi hakan, ibda yanzu yaran gabaki ɗaya suna hannun ta, ta haɗa ta riƙe gwanin ban sha'awa, duk da tana zuwa aikin ta lafiya lau. Nayi ƙiba ta sosai, na zama babbar mace mai ji da aji, inda har ƙungiya ta taimaka ma marayu da marasa shi na buɗe, inda ni da Ya Ameen muke zuba abunda ya sauwaƙa, muna bi lunguna da saƙuna muna taimakon al'umma, har cen Adamawar ma bamu barta a baya ba. Su Wazeeri dai an yanke masu hukuncin kisa ta hanyar zama gidan yari har ƙarshen rayuwar su, haka ita ma Maree da ɗan ta'addan ta. Su kuwa su Hajiya Laila da Hajiya Sa'a da Alhaji Yaro, zaman gidan yari na shekara goma goma na cin amana, tare kuma da tarar kuɗi manya. Zan iya cewa yanzu hankalin mu ya kwanta sosai, tunda Ya Ameen ya ce ba zanyi aiki ba, bam matsa ba, dan ina gida irin nasu, ba abunda zanyi da wani aiki, duk da dai shi aiki security ne dashi. Ƙungiyar mu mai suna *Needies are all human being* sai gashi yanxu ta karɓu tayi suna, har kwantaragi gwamnati ke bamu, tunda ta san ba ƙwange ba coge, zai kai hannun masu buƙata, sannan wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu ma suna tallafawa, kai har ma da turawa, masu yaƙi da fatara da kuma talauci, ba inda bama taɓawa mu, hatta da yara ƴaƴan masu ƙaramin galihu muna sakawa makaranta, tare da ba iyayen su jari, ta yanda zasu tallafa ma ƴaƴan su yayin karatun. Wani lokaci na kan ɗan leƙa shago na, dayake wani amintaccen yaron Ya Ameen ke kula man dashi, Amman dayake ban cika zama ba, ina yawan zuwa seminer, da kuma taron ƙara ma juna sani, Jaana ma saidai mu kaita wajen Mom, har ta saba da ita ma, tun ban yaye ta ba, har na yaye ta. Zaman ta yafi yawa ma wajen Mom, amman ana kawo ta indai ina gari. Ya Ameen bai damu ba, mutum ne ɗan boko mai aƙidar boko, ya san amfanin nema na, ko domin gaba, bai taɓa nuna man damuwa ba, watarana ma, shi ke zama da kanshi ya koya man abunda ban iya ba. Zama ne muke na so da ƙaunar juna, tare da mutunta juna, duk inda na shiga sha'awa ta ake, hutu da natsuwa sun ratsa ni. ************** Ranar Asabar ya kasance ranar hutun ƙarshen mako, aiki ne ya kacame man sosai, dan ma Mom ta sama man ƴar matashiyar yarinya dake taya ni kula da Jaana, ganin irin yanayin da nake ciki, na shigar wani sabon cikin. Yanzu mukayi waya dashi yake sanar mani ya sauka a ƙasar tashi ta haihuwa, in bam manta ba, yau watan Ya Ameen biyu baya ƙasar, wani aiki ya riƙe shi mai muhimmanci, inda suke ta ƙoƙarin dawo da dukkan wasu harkokin su ƙasar tasu ta haihuwa gabaki ɗaya, basu samu nasarar kammala wannan aikin ba sai yanzu. A gurguje na shiga wanka, dama naci sa'a Aliya mai kula da ita, wanda ba zata wuce shekara sha uku ba, itama na saka ta makaranta ɗaya da Jaana, yanda ko acen zata dinga kula da ita, yarinya ce mai ƙwazo, ban saka ta komai, in banda wasa da Jaana, ita ke ɗauke mata hankali suyi ta wasannin su a lambu ko ɗakin su. Ta shirya ta sosai ta mata kwalliya, sannan na saka mata kaya masu kyau sosai, yau zata haɗu da cucu Abbin ta, kaman yanda take kiran shi. Shirya kaina nayi cikin wata jar jallabiya ƙirar ta larabawa mai haɗe da wando, rigar iyakar ta guiwa daga gaba, sai daga baya ne har tana jan ƙasa, tana da kyau sosai, gami da babban baƙin ɗakwali. Dan haka dashi nayi amfani na yane kaina, takalma masu tsawo nayi amfani dasu baƙaƙe suma, ƴan kamfanin bineina fesa turare ne naji dirin motar shi, inda Mudi Driver ya ɗauko shi, shi da Bilal, amman sun biya sun ajiye Bilal a gida. Kafin ma'in fita, Jaana tayo but ta fita da ɗan gudun ta, tana ɗaga hannuwa take faɗi "My Cucu Abbi welcome dear" caraf yayi da ita zuwa sama, sannan a hankali a hankali ya fara juyi da ita sosai, wara hannuwa tayi sosai tana ƙyalƙyala dariya, gashin ta na danyi mata calaber dashi, sannan na saka mata bids yana ta faman reto shima. Har saida ya gaji ya tsagaita da ita, yana mai sakin nishi tare da ɗan ƙaramin haki, sannan ya rungume ta tsam cikin ƙirjin shi, yana sakin wani irin murmushi mai ƙayatarwa. Luf tayi sosai a ƙirjin nashi, tana sakin ajiyar zuciya. Daga bakin ƙofa da nake tsaye, saidai na saki murmushi, ina mai relaxing a jikin ƙofar harɗe da hannuwa na, cikin so da ƙauna nake kallon su. A hankali na shiga takawa zuwa inda suke, ganin hankalin shi ma bai kai kaina ba. Ta baya na rungume su su duka, ina mai cewa "Ban yi fushi ba Habibi na, idanun ka sun kulle kan ɗiyar ka ko? Ka manta da ɗiyar Mom ko?" Dariya ya saki sosai, yana mai juyowa ya rungume ni tsam ni da Jaana ɗin, "Am really sorry dear, kinsan nayi missing naku ku duka, taya zan manta da hasken zuciya ta?" ɗan ɗagowa nayi ina kallon shi, cikin murmushi da ɗan farfar da ido na lakace mashi hanci, ina mai cewa "Ba wani nan, yanzu dai ka ajiye ta ka huta, muje" na faɗa ina mai nuni da hanya.. Hannu ma ya kamo, har yanzu Jaana na kwance a ƙirjin nashi, abun gwanin ban sha'awa. Bayan yayi wanka ne muka zauna dining table. Wasa yake ma Jaana, yana bata abinci, rabi da kwatan hankalin shi na kanta. Ɗan ƙwarewa nayi da gangan.. Saurin tasowa yayi zuwa inda nake, yana mai tallafo ni sosai zuwa jikin shi, luf nayi, yana shafa man baya a hankali. Ganin Jaana tana kallon mu, ya sanya na ƙwace kaina daga gareshi, yarinyar ta fara wayau, tana iya fahimtar wani abu. Saida muka kammala komai ne, sannan muka yi niyyar fita siyayya, daganan zamu je mu gaida Mom. Ko da muka je cewa tayi Aliya da Jaana ba zasu bimu mu koma ba, tayi hakan ne domin na sake da miji na, mun fahimce ta, shiyasa sai bamu ja ba, muka tattara muka koma gida, bayan mun ajiye mata nata siyayyar, tana ta shi mana Albarka sosai, kaman ta goya ni. Hakan yana yi ma Ya Ameen daɗi, shiyasa yanzu yake bin Mom sau da ƙafa, yanzu har cewa take ya rage wannan shegen kafiya da taurin kan nashi, gami da miakilanci Wai taga amfanin aure na dashi. Kwana biyun da ya Ameen yayi a gida, ya sangarta ni, hatta da girki wanke wanke da shara hada mopping shi yake yi iyaka dai a fita dani a siyo man shawarma da ice cream. Haka kuwa akayi yau, fitowar mu kenan daga shagon ice cream, ina daga gaba jingine da mota, yayin da yake fitowa hannun shi ɗauke da ƴar ledar ice cream. Gaban shi ta sha cikin yanga da kwarkwasa, "Hey Handsome Ameen" ta faɗa, tana mai far-far da idanu. Ɗan kallon ta yayi a fizge, fara ce sosai, saidai ƴar fingila ce bata da jiki sosai kaman bulala, amman da gani hutu ya ratsa ta. Zagaye ta yayi niyyar yi, ta saka hannun ta tana mai ɗan ja mashi hannu haka. A zuciye ya dawo baya yana mai zare farin glass ɗin idanun shi ya kalle ta. Sauke kai ƙasa tayi, saboda kwarjini da yayi, mata, ɗan tsoki yayi, yana mai zagaye ta ya wuce. Duk akan idanun Suhan, ɗan dariya ta saki, bata san yana kallon ta ba, amman ita kanta ta yarda da Ya Ameen ɗin, koda wata ya gani ya ce yana so a yanzu, zata ji kishi, amman ba tare da tayi na hauka ba. Saida ya buɗe mata gaban motar, sannan ya ja motar suka fice daga wajen. Tsantsar ƙaunar juna cikin zukatan su, shafo ɗan cikin ta yayi cikin ƙauna, yana mai cewa "Janaa Lil sis ya hutu?" murmuahi na saki, ina mai ɗora hannu na saman nashi, ƙwaunar shi ne ke kwarara a zuciya ta zuwa ƙalbi na. Kamo hannun nashi nayi ina mai sakar mashi kiss sosai, tare da rungumi shi, da kwanciya bisa kafaɗar shi, yana mai ƙarama motar tashi gudu zuwa gida.... Riri ta ni yake, haɗi da lallaɓa ni, saboda cikin dake jiki na, yana tausay man, baya mance wahalar da nasha a lokacin na Jaana, tabbas ya sani Allah ne ya jarabce ahi da so na, ahi kansho ya san *BAIFI ƘARFI NA BA* kaman yanda wasu ke faɗa ada. Matar tashi ɗaya ce cikin dubu, duk tunanin wani abu baya yi idan yana tare da ita. Ni kaina ririta abu na nakeyi sosai, ni kaina nasan Ya Ameen miji ne, a koda yaushe zuciyar shi a wanke take fes, koda yaushe baka raba shi da masu neman taimako, kuma daidai ƙarfin shi yana yi masu, gashi nima har na koya zama tare dashi. Babu abunda yake son ji da gani a yanzu sai ganin matar tashi ta sauka lafiya, dan haka duk wani abu na wahala ya hana ta. Da kanshi yake raka ni har zuwa bayan layi inyi exercise, kowa ya ganmu sai yayi sha'awar mu, masalan da kowa ya san cewa Ya Ameen ɗin matashi ne mai jini a jika. Hankalin ya Ameen ya kwanta sosai, yayi ƙiba shima ya murje gwanin ban sha'wa, ga wata ƙasumba ya ajiye, dariya nake yi mashi, ya zama wani alhaji cikin lokaci, amanar shi da Bilal har yanzu tana nan, Umme ta sake haihuwa ta haifi wani namijin aka saka mashi Khalil, Afnan ma ta haihu har munje suna an samu *Asiya* Sunan ƙanwar Salim ɗin, haka ma Saudat ta haihu itama. Fanuky namu ya cika da yara fa, gwanin ban sha'awa maslaan idan aka zauna meeting na wata shida shida da akeyi wanda ya Ameen yake jagoranta, dukda ba shine babba ba, saidai ba zance ya fi kowa kirki ba, aman mutum da matashi kaman Ya Ameen samun kaman shi sai an tona. _Alhamdulillahi, na gode ma Allah daya bani ikon kammala wannan littafi, kuskuren da nake ciki Allah ya yafe mani, Allah kuma ya baku ikon yin amfani da dukkan abubuwa na alkhairi da ƙaruwa dake ciki Ameen._ ~Oum-Deedat ce~