[27/3 22:42] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM .... Godiya ta tabbata ga Allah (SWT)me kowa me komi .. yanda na fara rubuta littafinan Allah ka bani ikon k'areshi lafiya ...tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabin mu (SAW) da sahabbasa da alayensan ... Allahouma Salli Ala Sayyidina Mohammadin was Salim... Ban yarda wani ko wata ya canza min littafina ba inhar bada izinina ba dan kotuce zata rabani da shi dan haka akiyaye🙏 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Ina mik'a gaisuwata ga yan kungiyar mu *STAR Writer's Ass ..* Allah ya k'ara had'a kanmu.love you All❤ 🅿 01__02 Tafe take tana rusa kuka kamar wanda aka ce parent d'inta sun rasu ..hannunta d'aya ta kare fuskarta da shi d'ayan hannun kuwa tana rike da wani fashen2 tulu koda na matso kusa da ita na k'are mata kallo senaga yarinyace qarama fara wacce baza tafi 11ans(11years)duda karanci shekarunta aman bai hana kyan ta fitowa ba tanada hancinta zarot ..bakinta dan madedeci pink ga magana masha Allah amma fa kayan jikintaa dakon2 dasu bakyan gani duk sun kod'e sun cicire ...riga da zanen da d'an kwalin duk daban2 tayi daurin nan irin namu na yan kauye wato ta zaro jelar dan kwalin ta gaban rigarta .....ganin irin shigar yasa nayi zaton tallaka wane amma me..😳 ganin gidan data take shirin shiga yasa nayi mamaki dan kaf kauyen manga gidan daya kaishi ba dan shafe da sumunti gidan yake kuma an kewayeshi da katanga sab'anin sauran gidajen da kusan duka buka ne... Ta jima tsaye baki kofar gidan ta kasa shiga se tayi kamar zata shiga se kuma ta dawo baya tayi haka yafi sau ukku daga karshe tayi shahada ta shige ganin haka nima na mara mata baya .. Wata bakar mata nagani zaune bisa kujerar nan tayani tsegumi se girgiza kafa take tayi d'aurin d'an kwali ture kaga tsiyar nan .. D'an nesa da ita yarinyar nan naga ta durkusa se kame2 take ta kasa magana ga hawaye na tsiyaya bisa ''joue''(cheek) d'inta ... Matar ta kalleta tace wai miyene kin wanizo kin sani gaba kamar ni d'in bakuwar ganin kice.....ina kuma ruwa dakikaje d'iba ne eee ta fad'i cikin tsawa.. Seda ta firgita yarinyar har tayi baya ta fad'i ragwaf baki na karkarwa tace kiyi hakuri Inna Murza wly mun d'ebo ruwan nida su Ma'u kawai sega su Murtala sunzo fice wa gani suna gigin tseda mu ne . da muka ki tsayawa se kawai suka biyo a guje ina cikin gudu nayi tuntub'e nafad'i tulun ya fashe kuma ma harda ciwo naji ta bud'e gwiwarta idan taji ciwon..tana nuna mata A maimakon taji tausayi yarinyar se wani uban ashar ta abka tace yoni ina ruwana dajin ciwonki .kuma kice de kin tafi wajen karuwan cin ki da samarinki de.. walahi baki isa tulun nawa zafi fasa sanan wani bani hakuri ... to walahi se kin biyani ko jikin ki ya fanshe ki yanzu nan dan bazan dauki asara ba.... Cigaba da kukan take tana bata hakuri amma ina Murza ita neman ma bugi take ..muciya naga ta d'auko tayi kanta .nanfa ta dinga jibgar yarinyar tun kana jin ihun ta har muryar ta dishe bata barta ba seda ta sumar da ita tayi jifa da muciyar taja kafafun yarintar takaita tsakiyar rana tayi shigewarta daki se mita da zagin yarinyar take ... Ba'ita ta farka ba se wajejan karfe biyu na rana shima sakamakon ruwan da Inna Murza ta sheka mata...firgit ta tashi se wuki2 da ido take .... Murza tace shegiya mai kama da aljana tashi ki fice kiwo sauran inkin tafi ki tsaya yawon karuwancin naki dakika saba ... sum2 ta d'au buta ta nufi rijiyar cikin gidan da niyar yin alwala tayi sallah ..ashe ma akwai rijiya cikin gidan dan tsabar mugunta irin na Inna Murza tace baza'a ja ruwan ba sede taje can cikin rijiyar garin ta d'auko mata.. Wata tsawa ta daka mata tace ke kina hauka ne uwar mi zakiyi min da butana iye.. Cike da tsoro tace Inna alwala zanyi inyi salla.. Shewa tayi tace gaji ladaniya to kokece tabarmar massalaci wacce kullum acikin mosque d'in take baza kiyi sallar ba kamar wacce tafi kowa addini .....maza aje ki fice.. Tace inna to bari nayi fitsari sena tafi ... Shiga kiyishi hakanan base kin kama ruwan ban ...shasha kawai .. Fitsarin da batayiba tace Inna abincina fa yunwa ake ji... Iye i lalle wuyanki yayi kwari kai tsaye tace to ban dafa dake ba Zata yi magana Murza tace.MAYSAM MAYSAM dige ki fita a idona in rufe tau..tayi shigewarta d'aki Bayanda MAYSAM d'in ta'iya dole ta d'au sandar kiwon ta kora shanun ta fice....Allah yaso ta cikin shanun akwai masu shayar wa bayan taje idan take kiwon se ta tatsi nonon tasha ta gama.cikin ta dan dama kullum hakace take faruwa idan anbata abincin safe tofa da ranan batada kwanon tuwo idan kuwa bata bata na safe ba to zata bata d'an tsakure da rana... Bayan tagama sha tayi alwala tayi sallah Wanan kenan... Fasma ce✍ [28/3 23:03] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 🅿 03__04 ```An karbo daga Anas dan maalik R A yace: Manzon Allah( S A W) yace''dukkan d'an adam mai kuskure ne,mafi alkhairin masu kuskure sune wad'anda suke tuba(idan sun aikata kuskuren kuma bazasu sake komawa ba)'' `` Bayan ta gama sallar nan ta zauna tana tunani rayuwarta ita bata san miyasa innarta bata sonta batason dommi yasa ta tsaneta ba ...kullum da iri cin zarafin data ke yimata sab'anin kowace UWA da take nunawa d'anta so da tattali ...ga kuma kalmar da take tsaya mata cikin brain wato Karuwa '' tarasa mi kalmar take nufi so tari Murza zatayi ta kiranta da sunan kuma ba damar tabbayarta ....tana nan har aka kira sallar Asr ,,,bayan tayi sallah ta d'an ringesa kafin a d'an jima ta koma gida...abunka da wanda ta gaji ga wahala da yunwa se kawai bacci me zurfi yayi awon gaba da ita ...ba'ita ta farka ba se gab da magarib ,,,da sauri ta tashi ta kora shanun ta kama hanyar gida tana addu'ar Allah yasa baba MUSA ya dawo ... Tun daga nesa ta hango Murza a bakin kofar gida tana dube2 da alama jiran isowarta take ,,,.. Dafe kirji tayi tace na shiga Ukku ni MAYSAM yanzu kuma ko wace azaba Murza zatayi mun..Murza na hangota ta juya cikin gida ... nan Maysam ta fara karkarwa tana matsar kollah ... Bayan ta d'aure shanun ta shiga gidan ai kuwa tun a bakin zaure taji saukar dorina a jikinta seda ta gantsare ta zube nan ta kama qafar ta tana bata hakuri ..... Hankad'ata tayi da qafa ta dinga zabga mata dorina tana fadin kaji shegiyar yarinya kina son d'auko muna magana a gari wato kiwon ma se kin tsaya wurin karuwanciki..... Fad'i take wly inna ba'inda natafi bacci ne kwashe ni..... Iye dan ubanki har kika samu lokacin bacci keda kika tafi kiwo kenan kice hakan kika bar min dabbobi da kishi dan bakin ciki ko.... Tace a'a inna wly ... Bata bari ta qarasa ba tayi ball da ita wani kara ta saki segata wanwas ta suma a wurin dama sauran yanwa ga duka ai abin yayi yawa(gaskiya na tausaya miki Maysam😭)... Ana kiran isha'i ta kuma shekamata ruwa a firgice ta tashi se kuma ta saki wani kuka me cin rai ... Amaimakon taji tausayin ta se kawai naga tana kasa gyad'arta tana qirgawa .bayan ta gama tace idan kin gama kukan munafuncin se kizo ki tafi dandanli kuma wly b'atan daya kikayi jikinki ze fanshe ki.. Ta goge hawayen tace dan Allah ki temakamun da abinci yunwa nakeji ... Kamar baza tace wani abuba se kuma tace ga zazafen safe can ki d'auka kice .. Hannu baka hannu kwarya take loma dan ba wani yawane dashi ba amman de ta done wasu kofofi cikin...ta d'au tiren tallar ta fita...... Wajejen goma na dare aka tashi a dandali ..itada kawarta Ma'u suka rako dayake makota ne a hanya tace dan Allah Ma'u ina sonyi miki wata tambayya.... Ma'u tace ina jikin Allah yasa na sani.... Maysam tace wai mi kalmar karuwa ke nufi? Waro ido Ma'u tayi dayake ta d'an girmeta kad'an tace kada ki bari wani a kauyen nan yaji wannan kalmar a bakin ki ... Miyasa don ni sunan da innata ta lakaba min kenan... Ma'u tasa hannuta ta rufe mata baki tace kul kada kibari wani ya san da maganar nan dan karuwa na nufin macen data bada kanta ga maza saboda kud'i wato ta meda yin Zina sana'arta ...ita kuwa zina anyi hani dayinta ga dukka musulmi mumuni dan ko kasanci da ita an hanemu bare yinta ....... Gyad'a kanta kawai tayi amma badan tagane duka abunda Ma'un ta fad'imata ba ...ganin Ma'u ta shiga yanayin damuwa yasan itama tashiga koda bata gane ma'anar kalmar ba amman tasan ba abu ne me kyau ake nufi da ita..... Bawanda ya sake cewa komi har suka zo kofar gida Ma'u ta kalli Maysam cike da tausayawa kawartata tace kiyi hakuri da abunda Murza take mike wata rana se labari...nan sukayi sallama kawa ta fice gidansu.... Zaune ta tarar da Murza nan ta biqa mata kud'in da ragowar gyadar...seda ta lissafa yafi sau ukku wai ko zataga b'ata amma taga sun cika cif2 ...ta harareta tare da yi mata rankwashi a ka tace Allah ya soki da kinci na jaki.... Sum2 ta d'au buta tayi alwala ta shige wata yar bukka kusa da kitchen da alama store ne dan ga kayan miya nan a ciki ..tattare wuri tayi ta kabarta sallah bayan ta gama ta b'ingire nan bacci ya kwasheta..... Kiran sallar farko akunnenta akayishi ta tashi ta sand'a tayi alwala ta koma bukkarta tayi sallah...ta salamce kena. Murza ta shiga kwalla mata kira ko azkar na safiyar bata samu damar yi ba ta fito a guje ta durkusa gaban ta tace ina kwana Inna .. Ya tsine fuska tayi tace da ban kwanaba kya ganin ..ni ba wannan na kira kiyi mun ba maza 2 d'au tulu ki tafi rijiyar cikin gari ki d'auko ruwa sauran ki tsaya yin abunda kika saba.... Tulu da guga ta d'auka amma me har ta kai kofa Murza tace dawo aje mun gugar inki tafi can wani ya baki ki d'iba.. Haka ta fita a ranta tace da rijiya a gida amma ace se an tafi wani wuri d'aukan ruwa ..dan kawai wai kada ruwan rijiyar ya kare...ko a ina ruwan rijiya ya tab'a qafewa..... Bata dawo gidan ba se bakwai ... Murza ta kalleta tace issashiya se yanzu kika gama tumb'elen ki ko nan da cikin gari ma sekinyi halin.... Batade ce komi ba ta sauye ruwan ta fara kiciniyar d'aura koko a ranta tace waye ze tafi daukar ruwa da asubar fari kuma kinsan da hakan kika hanani d'aukan goga ...bayan ta gama ta d'umama tuwo sannan ta share tsakar gidan tas ta had'a kayan wanke2 tayi... Ta zauna zaman jiran a bata kari amma Murza yi tayi ya bata san da halita a wurin ba ta bud'e baki da niyar yin masifa ta tsinkayi sallamar Malam Musa d'up tayi shiru ta fara washe baki tana laale Malam sannu da zuwa... Da gudu Maysam ta rumgume shi tace sannu da zuwa Abba..... Rumgume ta yayi shima ya shafa kanta yace yawwa yar Abba da fatan na same ku lafiya ..e tace ya jawo ta suka zauna bisa tabarma yace yar Abba mike damunki naga kinyi wani irin a kwana biyunan da bana nan.... Kasa magana tayi se hawaye da take gogewa ... Hankalinshi ya tashi yace yar Abba kiyi mini magana mana ... Karaf Murza tace ayya ai rashin lafiya tayi massasara ke damunta ...jiyan nan na kaita chemist aka bata magani gashi bata son cin abinci ko kad'an har balangon nake sayo mata amman bata iyaci se na matsa mata....ga jikinta wuni take da zazzab'i bata son ruwa ko kad'an ya tab'ata.shiyasa kaga jikinta da d'an datti...kuma kasan marar lfy ba'a matsa mishi diyawa seda lallab'a ...yanzu haka dramar setayi break ne muke nayi2 takici ..... Maysam batayi wani mamaki ba dan inda sabo ta saba da makircin Murza tayi fiye da hakama ... Malam Musa yace wayoo yar Abba ashe baki ji dad'i ba to Allah sawwake ya baki lfy.. Ameen tace da farar'arta dan ko ba komi zatayi hutun masifar Murza Kwana biyu... Suna had'a ido Murza ta buga mata harara ...ta sadda kanta a ranta tace sede harara dan yau ba wunin yunwa bare zuwa talla da kiwo... Nan ya bude tsarabar daya kawo musu fruits iri2 nan Maysam ta bud'e sauran qofofin cikinta ta dinga ci ba kyakyautawa...seda taji ba wuri tukon ta sarara...ga wasu d'inki atamfa daya basu kala uku2 ,,,.nan ta ja ruwa a rijiya ta feso wankanta wanda rabonta dashi tun bayan tafiyar Abbanta ..tasa kayanta ta fito tsaf da ita .Murza kamar ta had'e rai dan takaici ... Abinci rana ta d'aura musu abbanta na gefe se fira suke abunsu gwanin ban sha'awa...dan kuttu Murza kasa zaman wurin tayi ta koma d'aki ..haka tayi musu lunch tare sukaci .. A kwana biyun nan da Abba ya dawo har wata yar kiba da haske ta qara dama gata da tsapta masifar Murza ce ke sata zama da daud'a dan kuwa batada incin saka kaya masu kyau inde har Malam Musa baya nan... . Tofa kuji makirci irin na Murza... .. Love you all my fans ❤ Fasma ce✍ [29/3 23:52] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 🅿05__06 ```Daga Abdullahi dan Umar Allah ya yarda da shi yace:Manzon Allah (S A W) yace''mutum bazai gushe ba yana tambayar muta ne(roqo) har sai yazo ranar qiyama fuskarsa babu tsoka d'aya ta nama ,ruwayar Bukhari da Muslim ce_ ``` Washe gari Maysam cike da farin ciki ta tashi tayi shirinta na zuwa school tasa uniform d'inta ta fito tsaf da ita ...nan tsakar gida ta tarar da inna Murza da kuma malam Musa suna breakfast ta zauna itama ta gama cikinta lokacin da zata tafi Malam ya dari biyu na break ....ta ansa tanata godiya ... Wani kallo Murza tayi mata sena ga ta gyad'a mata kai ta fice a gidan ...(ko kallon miyake nufi oho) Haka Murza tayi wunin aiki a ranar se tsaki da gungunai take ... Ita kuwa Maysam a school d'inma principal hanata shiga aji yayi dan cewa yayi seta zo da parent d'inta yaji mike hanata zowa akai2 ... Da kyar ta samu ta shawo kanshi tana kuka ta d'an fad'i mishi abubuwa kad'an daga rayuwarta .... Nan ya tausaya mata tare alkawari tallafa mata tasamu ta gama primary tunda ma yarinyar Allah yayita da kaifin ilimi dan danan ta haddace duk abunda aka koya mata.... Qarfe biyu na rana suka sauko ta dawo gida Allah ya temaketa Malam yana gida nan ta shari girkin lunch ...qarfe hudu kuma ta tafi islamiyya .... Malam na fita sallar magrib Maysam na zaune tana biya karatunta se jin rankwashi aka tayi ...koba'a fad'a ba tasan inna ce ...tana d'ago idonta kuwa taga Murza se wani fuci take ta biko mata hannu tace ban ... dari biyu naga Maysam ta fitar daga bag d'inta ta bata ... Warcewa tayi tasake yi mata wani rankwashin tace nazata baki ganeba dana ganar dake yanzu munafuka kawai .. Itade ko A batace ba ta meda hankalinta kan abinda takeyi...a ranta kuwa kukan zuci take ace kud'in break d'inma se an anshe ... Bayan kwana biyar Malam Musa yayi shirin tafiya dayake kasuwoyin kauyika ya keci shiya sama be cika zama a gida ba... Kuka kuwa harda na banza Maysam tayi dan tasan tayi bye2 da jin dadi har seya dawo .. Nan ya rungumeta yana lallashi yace yar Abba kukan nan ya isa haka ... Murza se wani washe baki take tace ai kasan bata san rabuwa da kaine ... Maysam aranta tace dole inyi kuka dan nasan lokacin azabata da cin zarafi yayi.. Kudi ya fiddo ya bawa Murza sanna ya bawa Maysam kudin school dinta .. Ya tafi ya barsu nan Maysam na ta d'aga mishi hannu... Shigowar su keda wuya Murza tace munafuka annamimiya .. Kwace kud'in tayi tace tundade ba school din zaki ba ..aiki ya dawo sabo.. Haka rayuwa tayi ta tafiya kulum da irin sabuwar muguntar da inna Murza take fito mata dashi ..yau har zasu zana jarabawa shiga secondary Allah yasota Musa na gida dan haka bata samu wata matsalaba ...bayan yan watanni resulta kuwa na fitowa Allah ya temaketa taci fad'ar irin murnar datayi b'ata time ne .... Inna Murza na gefe se wani murmushi mugunta takeyi a ranta tace e kuma kin gama school daga haka..wannan d' inma dayaya na bari balle har na bari kishiga secondary ee bazama ta sab'u ba.... Bayan kwana biyu da faruwar hakan suna zaune bayan sun gama abincin dare Murza tace Malam dama ina son yimaka wata maganace game da karatun Maysam amma ina tsoron kace nayi mata shishigi.. Malam yace haba Murza wani irin shishigi keda y'arki ki fad'i kawai ina sauraronki.. Dam gaban Maysam ya bada ta kasa kunne tana jiran jin mi zata fad'i Kalar tausayi tayi tace dama cewa nayi be kamata taci gaba da karatunta ba dan kaga a al'adar garin nan yan mata basayin makaranta gabada primary kuma ka sani kowacce a d'akin mijinta take jinin farko (menstrue)dan abun kunya da tsangwama ne idan har yarinya ta farashi a gida.. Gaban Maysam cigaba da fat3 yayi tana jiran taji mi Malam ze fad'i.. D'an jim yayi yace nikaina abunda nake dubawa kenan dan d'azun nan Mai gari damuka gama yin sallah bayan yayi min barka nasararta se kuma yace d'anshi Murtala yaga y'ar wurina kuma yana so ..na de cemishi zanyi shawara da iyalina tukon..yakike gani kenan Wasu sirarrun hawayene suka zubowa Maysam tayi sauri ta gogesu a ranta tace aure kuma.. Wani malolon bakin ciki ya tokare mata wuya aman seta cije tace kawai ka bashi tunda Mai garin da kanshi ya nema kaga be dace ba ka hana d'anshi ko...ta kuma cewa kaga jiya2 nan aka saka ranar qawarta Ma'u ..a ranta kuwa cewa tayi yanzu de matsalar cigaban karatunta ce a gabana tunda nayi nasara daga baya kuma sena ji da auren dan walahi bazan barta ta aurin d'an me gari ba . Malam yace shikena Allah ya zab'a mafi alheri... Kasa2 Murza tace ba Ameen ba.. Ya kalli Maysam yace y'ar Abba kinji duka abunda mukace in har bakya son Murtalan ki fad'an bazan miki dole ba.. Kanta a kasa tace Abba zab'inku shine nawa kuma ai dama Uwaye ya dace su zab'awa yar su budurwa miji .. Allah yayimana zab'i mafi alheri Ameen y'ar Abba hakika ina alfahari dake Allah yayi miki albarka .. Ameen tace ta shige d'aki dan wani kuka yazo mata..a ranta tace yanzu a rasa wanda za'a had'ani dashi se marar mutunci nan meyiwa y'ay'an mutane fyad'e ..ta d'aga hannu sama tace Allah gani gareka kayi mini zab'i na alheri ..tana kuka ta shafa ..nan bacci ya kwasheta.... Tofa fans anya Murza zata bari ayi auren nan kuwa? Ina sonku masoyana irin dayawan nan❤ Fasma ce✍ [31/3 16:41] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 🅿 07__08 ```Mazon Allah (SAW) yace''lallai mamaci anayi masa azaba saboda kukan masu rai'' Ruwayar Bukhari da Muslim ce``` Washe gari da matse nanci ciwo kai ta tashi saboda kikan datayi dayake babu school tayi shara da wanke2 gidan tana kiciniyar d'ora break Malam da Murza suka fito da alama tafiyar kasuwancin shi zashi bata san lokacin da hawaye suka zubo mata a ranta tace yau kuma ko wata azabar zansha ....nan ya bawa Murza kud'in cefane ita kuwa Maysam dari biyar ya bata tunda yanzu ba school ..ko fita daga gidan beyiba Inna Murza ta kwace kud'i tayi shigewarta d'aki ashe Malam Musa ya gani dan yayi mantuwa ya dawo ....bece komi ba ya d'auki abunda ya manta ya sake yiwa Murza sallama sekuma yace Maysam ta biyoshi ze aiketa wani gu......Murza bata kawo komi a ranta ba.. Bayan sun fita ya kalleta yace yar Abba ki zanki hakuri da Innarki wata rana se labari ki qara hakuri da ita kinji ko...ina sane daduk abunda take miki dan qawarki Ma'u tana sanar dani komi yayi zafi maganinshi Allah dan baze yuyu na dinga tafiya dakene ba .. Wani hawaye taji ya zubo mata magana ma kasayi tayi se gyad'a kai kawai ta iya'yi ... Share mata hawayen yayi ya rumgumeta yana lallashi har ta fasa kukan ..ya ciro dubu biyu ya bata yace ki sayi duk abunda kike so kada ki bari innarki ta gani bare har ta kwace miki kinji kuma daga yanzu zan ringa baki kud'in da zakina kashewa ... To tace Abba na gode Allah ya kara bud'i ya bada sa'ar abunda aka tafi nema... Sosai yaji dadi addu'ar yace ameen yar Abba Allah ya albarkaci rayuwarki.... Ameen tace .. Nan ya tafi ya barta tana d'aga mishi hannu har ya bace ganinta...a bakin zaninta ta kulle kudin ta koma gida... Tana shiga taga inna da tulu a hannunta tasan mi hakan yake nufi dan haka da duka da niyar karb'ar tulun ai kuwa ta daka mata duddu tace shegiya annamimiya har da wani kukan munafurci dan Malan yayi zaton ina cin zarafin ki in bayanan ko..... Itade batace mata komi ba .. Dungura mata tulun tayi tace saura kitsaya inda kika saba tsayawa ..... Biyawa Ma'u tayi sukatafi tare ..a hanyarsu ta dawo ne suka gamu da Murtala shida abokanan shashacin shi.... Nan suka taresu har sun tatare zanin su zasu arce Murtala yace wly in kuka gudu kun jawowa kanku ..cak suka tsaya ... Ya matso daf da Maysam yace matana ya kike ...kin san banso kina daukan ruwan nan bara natayaki ..yayi niyar sauke tulu daga kanta nan taja baya da sauri ..ma'u tace wai miye hakane kun wanizo kun tsare mu a hanya har kana wani kiranta da matarka kota ina ma... Daka mata tsawa yayi yace ke kuwa asuwa ...kinci darajar kece yarinyar da abokina ze aura wly da yanzu na keta miki haddi...tsit kake ji Ma'u tayi... Suka kwashe da wata arniyar dariya ya sake matsowa daf da Maysam wadda ita alokacin tuni hawaye keta zuba....yace haba tawan nan yasa hannu ya share mata hawaye se kuma yayi niyar rumgumeta wai azuwan lallashi .. Efa nan ake yinta nan kokowa ta barke har rigarta ta cire daga gefen ai bata san lokacin da yarda tulun anan ta arce a 60.....zasu mara mata baya Murtala yace a'a ku barta ku muje idan zamu kawai .... Seda ta isa kofar gidan su tukon ta tsaya duk jikinta karkarwa yake ...se kuma ta sake fashewa da kuka ...ga abunda Murtala yaso yimata ga kuma tulun Inna ya fashe wanda jiya2 nan ta sayeshi ta jima nan tsaya sannan ta shiga gidan se rarab'ewa take.. Inna na ganinta ba tulu tayi dariyar mugunta dan ta fad'i gassasa yau.... Game hanunta tayi tace dan Allah inna kada ki dokeni walahi su Murtala ne nan ta kwashe yanda sukayi ta fad'i mata.. Wani ashar tayi ta rarumo icce ta fara buga mata tace kicede yau asirinku ya tunu keda shii wurin gudu kika barar mun da tulun ga sheda nan harda cirewar riga ..dukan ta take baji ba gani ai kuwa dubu biyun da Malan ya bata ta fad'i kasa .. Salati Murza ta shiga yi tace munafuka asirinki ya tunu ashe karuwancin naki me degree ne harda dubu biyu ...nan ta dauke kudin ..ta d'ago fuskarta za zazzabga mata mari ta kuma sa hannun a kwalmin idon ta dunga kyarkyarta saman idon har seda taga jini yana fita tace shegiya me kama da mayu wata ran sena fidda miki idon nan kowama ya huta ..sanan ta cigaba da duka har seda taga bata motsi tajata ta yar a tsayar rana..lokacin kiwo nayi ta sheka mata ruwa ta tashi tace maza tashi ki fice kiwo.. Tasan kotace zatayi sallah baza ta barta ba setace Inna abincin nafa? Abinci fa ai kedashi se gobe kuma tunda yau kinyi kari ... Haka ta fita gwani ban tausayi... Haka rayuwa tayi ta tafiya wanda kullum se Murza ta caje Maysam inde harta fita ...ga kuma takurar da Murtala ke mata kullum inde sa had'u to seya nemi tab'a jikinta...shiyasama bayan anyi auren Ma'u ta sati ta gayawa Malan itama gwara asaka nata auren dan saboda tsaro..😁 Haka kuwa akayi nan aka saka ranar goma ga sabon wata kenan nanda kwana goma... Iya tashin hankali Murza tashiga dan ga dukka alamu auren nan ba fashi gashi kuma da gani yarinyar zata huta idan ta auri d'an megari tunda ko kayen lefenta ya kere na kowace budurwa nanfa ta fara shige da fice ta ciru ta kullu dan ganin auren ya fasu .. Nan ta wanke qafa taje gidan me gari har d'akin uwar Murtala ta shiga dayake sunsa sirukarsuce sesuka mata tarba ta kirki ......bayan gaishe2 tace dama wata magana ce take tafe dani... Uwar Murtala ta gayra zama tace ina sauraronki.. Nan ina ta tsara karya da gaskiya ta fad'i mata wanda harda cewa ai yarinyar bin maza take yanda kasan kariya haka take bin maza .... Inna Murtala tayi jim ...can tace shikenan barin zan sanar dashi Murtala kinsan yaran yanzu se abunda suka sa gaba sukeyi.... Nan ta kakab'e zane ta fito...dede kwanar gidan ta gamu da Murtala ..nan ya gaydata gatse2 bata wani damuba tace yauwa d'an albarka daman akwai maganar dana keson muyi ...... yace to ki fad'a kawai danni sauri nake.. Yauwa dama ba wani abu bane gayamaka ne zanyi kasan de yarinyar nan karuwace ko...?. Ta 'aza zeyi mamaki seta ga ko aka sema cemata yayi toni ina ruwana... A ranta tace kaji shegen yaro amma inkasan wata bakasan wataba..tace ai ba wanna ne matsala taba ai yarinyar tana d'auke da cutar nan me kashe garkuwar jiki ... Wani uban ashar yayi yace ni za'a cuta a had'ani dame kanjamau...wly da sake.. Murza tayi wata dariyar cin nasara tace ai shi yasa nace gwara na fad'a maka tun wurin amma ka bari se ana jibi auren sekace ka fasa .. To kawai yace ya fice se banbami yake.. Zuciyarta fari tas ta tafi gida... Hakan kuwa akayi ana jibi d'aurin aure Murtala yace shifa ya fasa auren inkuwa har aka d'aura auren to a ranar ze saketa...nanfa yayi d'an jinjinb'in haukanshi har seda yaga an fasa zancen ... Maysam tayi farin cikin wanan abu dudda batasan miyasa yace ya fasa auren ba..shima Malan da fari abun ya b'ata mishi rai aman gani Maysam bata damuba yasa shima jin saukin abun Bayan sati da faruwar hakan ta dawo daga rafi taga su Murtala ...abin mamaki seta ga suna gudunta sab'anin da daze dunga famar fa'damata....daga d'an nesa da'ita suka tsaya Murtala yace karuwa Allah ya toni asirinki ashe kina dauke da cutar HIV kikaso na aureki danki gogan ko ..to ta Allah bata kiba... Nuna kanta tayi tace ni kuma... Kwarai ke Maysam har gida Innarki ta iskeni ta gayamun... Batace komi tayi ficewarta.. Ranar kwana tayi tana kuka bata san mita tsarewa Murza a rayuwa da bataso taga farin cikinta... haka rayuwa tayi ta tafiya inda yanzu har takai 13 years aman ba me zuwa wurinta da sunan saurayinta koda kuwa yazo to baya sake dawowa inkuwa kaga har ansa ranar aurenta to fa baqone shima kuma da zarar yaji labari zakaga ya d'auke kafarshi..anyi haka yafi sau biyar..dan haka ta daina sauraron duk wanda yazo mata da sunan saurayi duniya tayi mata zafi ga wata rama data 'karayi ga jaraba da wahalar Murza kullum qara gaba ke..duk gari ya d'auka karuwace kowa gudunta yake wurin Qawarta Ma'u kawai take samun sauki se kuma Malan.. ..shima Malan tausayin yarshi yake gashi babu damar ya tashiga cikin mutane ..dan zakaga mutane nata nunashi abunka da karamin gari... Duk cikinsu Murza ce kawai wanen abun yayiwa dadi dan karenta takeci babbabaka..mugunta duka muzguna kuwa da ana sabo dasu da yanzu Maysam ta saba Murza ayide a hankali duniya ce... Fasma ce✍ [1/4 23:26] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Jinjina da ban girma ga yan kungiyar mu na STAR Writer's Ass* 🖊🌟. **ina sonku sosai* *Queen Baby*👸 *Momyn Mufeedah* *Arfat Nurdeen* *dama sauran yan* *kungiyar Star Writes Ass gaba* *daya ❤..Allah ya* *qara had'a* *kanmu..Ameen* _Ban manta da ku ba_ _Maman Shuren_ .. _Aisha__ ___ Momyn Hajia_ _Momyn Waleed_ _Dizo_ _Zarbaby_ _Sambaby_ _Sarga_ _Dala_ Ya Yusuf.._ _kuna da yawa fa dan sena gama cika page_ _d'innan ban gama_ _zano kuba😁 sede_ _ince Allah ya qara donkon zumuncin_ 🤝... _Alherin Allah ya kaimaka Yayana na kaina Mujaheed_ .. __da kuma ma petite__ _sœur de valeur Balkissa_ _Wannan page d'in na kune kuyi_ _yanda kukeso dashi_ .. _ina sonku irin totaly d'in nan__ ❤😍 Dedicated to All my Fans❤ _ 🅿 09__10 ```Manzon Allah (SAW) ya ce ''Mafificin ayyuka shine sallah a farkon lokacinta'' Tirmizi ya rawaito``` Duk duniyar ma ta fice a ranta Yau kam da wani irin matsenecin zazzab'i da headche ta tashi ga rashin qarfin jiki sakamakon damuwa tsangwama da sukayi mata yawa da rashin cin abinci ko fita daga d'aki ta kasayi ga kuma yau Malan Musa bayanan .. Tun safe Murza ke bambami da zage2... Har goma na safe ta kasa fitowa .. Murza ta hasala ta shiga d'akin a shashame ta ganta kuma se karkarwa sanyi take .... A memakon taji tausayinta a'a sema Wata tsawa ta daka mata... har bata san lokacin da ta zabura ta zauna ba .... Murza tace dan ubanki wa kike son ya miki shara da wanke2 ne da kika wani shigo d'aki kika kwanta wani sabon salon munafincine kika koyo ..to maza2 tashi ki fice kafin raina ya b'ace na miki dukan tsiya anan... Haka ta fita da kyar tayi aikin zata zauna kenan Murza ta fito da wani uban wanki tace kada ma ki zauna zo maza ki wankesu kuma su fita tas ehe Ko rabin wankin bata yiba ta fara kakarin amai wanda babu komi ciki se yellown ruwa .saboda ba komi a cikin ... Wani salati da tafa hannu Murza ta shigayi tace yau ni mizan gani a gidan nan CIKIn shege kika yo Maysam dama nasan za'a rina to walahi baze yiyuba Malan yazo da sake da. baza ki haifa mana d'an shege a gidan nan ba . . Dafe kirji tayi tace na shiga ukku ni ..walahi Inna Murza bani da ciki.. Ba ukku kika shiga ba goma de Nan ta fad'ata da duka ..da kyar ta sarara mata .. Ranar wuni tayi tana fad'i kuma taki bata abinci bare har ta tausaya mata kan aikin gida Maysam kam duka karfinta ya qare banda kuka babu abunda takeyi... Bayan isha'i sega Malan yayi sallama . Murza bata bari ma sun gaisaba ta fara fad'i mishi qarya da gaskiya wai daman taga alamun batun yauba dan tana kyautata zaton ba wannan ne na farko ba...se yau da Allah ya toni asinrinta ne ...dama itama shegiyace gashi kuma zata haifi shege... Wani wawan mari ya zabga mata yace kada ki qara shegan tar min da d'iya...Hankali a tashe Malan yake tambayar ina Maysam d'in..... Bata bashi ansa ba se cewa tayi akan shegiya zaka mareni.. yo ba shegiyar bace..ai ba qarya nayi ba... Dede lokacin Maysam ta futo daga tolet .. Batasan lokacin da tasaki butar dake hannunta ba Har ze tanka mata amman gani Maysam yasa yayi shiru ...da sauri ya isa wurinta ya riqeta ganin tana famar fad'uwa ....nan ya kamata ya kaita bisa taburma dake shinfid'e anan tsakar gidan ... Yace tun yaushe ne baki da lafiya yar Abba.. Dakyar ta iya fad'in jiya ne kawai ..tace dama Abba ni banida Uba Shegiyace? Rufe mata baki yayi yace a'a Yar Abba ke ba shegiya bace ki bari zan miki bayanin komi idan mun dawo..daga asibiti.. Allah de ya baki lafiya... Nan ya d'ago ta ya saka mata hijab ya kamata suka fita zuwa chemist na nan cikin garin.. Nanfa Murza ta samu abun fa'din Koda suka tafi gwajin farko akace tana fama da ''paludisme''(malaria)....nan aka mata allura tareda qarin ruwa aka rurubuta musu magani suka dawo gidan..koda ya fad'ima Murza Malaria ce ..bata yarda ba tace kunde je ancire mata zaku wani zo kuce wai Malaria .. Girgiza kai kawai yayi ya shige d'aki... Washe garin kafin dare kaf kauyen ya d'auka Maysam tayi cikin shege kuma taje an zubar mata ..yaran garin har zowa suke suna kallanta... Bayan sati har bata iya fita saboda cecekuce mutanen garin da kuma jifan da yaran kauyen keyi mata.... Da dare bayan sun gama cin abinci tace Dan Allah Abba ka bani labarina ..shin da gaske ni shegiyace. ? Malam Musa Yace Yar Abba ki saurareni da kyau kiji mi zance miki.. 🌹🌹. 🌹🌹🌹 A ranar wata juma'a ce lokacin ban fara kasuwanci ba kiwo ne nakeyi ..a hanyata ta dawo daga kiyo da yamma nan ne Naganki kina yawo cikin jeji kina kuka banyi zaton mutun bace dan haka na fara karanto kowace aya data zo min baki..amma abin mamaki se qara tunkaroni kike lokacin baza ki fi shekaru ukku zuwa hud'u ba kusa dani kikazo kina fadin ruwa2 ..nan na baki kika sha na tambaye ki suna kikace MAYSAM sanna na tambayyi ina Parents d'inki amma shiru baki ansaba na sake tambayarki daga ina kike nanma ba ansa .na diba dama da hagu amma banga kowa ba gashi kuma babu wani gari ko kauye dake kusa da nan. .ganin haka yasa nayi ficewata na barki nan .ashe biyoni kikayi ban ganki ba seda na kusa shigowa gari .... Ganin haka yasa na d'auke amman adu'a ce cike a bakina ..daga nan ma gidan mahaifiyata na kaiki dan lokacin banida aure matata ta fari ta rasu wajen haihuwa... Hannu biyu 2 ta karb'eki nan ta raineki har Allah ya d'auki ranta lokacin kina da 8years.. To tun lokacin na d'auki aniyar barin garin dan daman ita kad'e ta rage min a dangina... Dan haka na tattaro na dawo garin nan ..ganin rikon d'iya mace se mace yasa nayi aure na auro Murza .....kuma a lokacin na fasa yawon kiwo na fara kasuwanci.. To kinji yanda abun yake...nan ya d'auko wata riga me shegen kyau da wasu takalma da warwaro na alfarma yace wannan sune kayan dana sameki dasu.. Sekuma wani zobe me kyau kamar diamon a samanshi daga ciki kuwa ,wasu harrufane'' MM'' .yace wannan kuma a wuyanki kamar sarqa na ganshi sena cire na adana miki har lokacin dazaki wayoo sena bakishi.. ta ansa ta saka a hanunta sosai zoben ya birgeta .. Nan tayi ta kukan Abba yana lallashi tace duda hakan Abba banida wanda suka fiku a fad'in duniyar nan😭😭 Murza tace to kinde ji da kunnenki ko .. Itade bata ce komi ba a ranta tace lallai biri yayi kama da mutum ashe ba bazan kike azabtar dani dan ba kekika haifeni ba.. Ranar kwanan kuka tayi.. Two days later Malan yayi tafiyarshi.... Maysam ta fito kiyo amma yau kwata2 hankalin ta baya jikinta tana tafiya amma tashiga duniyar tunani....tambayyoyi ne cike da kanta tana son sanin wani daliline ya rabota da iyayenta?miyasa basu neme taba?a ina suke yanzu??shin ko dagaske ni shegiyar ce? Wasu motoci sunfi goma na gani se gudu suke ...oda sukeyi mata amma ina batama jinsu tanacan tana tunanin ta irin gudun da suke yasa d'aya daga cikin motocin yayi qoqarin kauce mata amma inaa seda ya bugeta jikake kiiiiiiiiiiii... Tofa !Ku biyoni danji yanda zata kaya... Nice taku har kullum ...love you all❤😍 Fasma ce✍ [4/4 00:42] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to All my Fans❤💋 🅿 11__12 ```Manzon Allah (SAW) yace ''Idan mutum yayi kiran matarsa zuwa shinfid'arsa sai taki zuwa ya kwana yana fushi da ita to mala'iku zasuyi ta tsine mata har safiya '' Buhari da Muslim ne suka rawaito shi ``` Wasu motoci ne sunfi goma na gani se gudu suke .... Oda suke yi mata amma ina bata ma jinsu tana can tana tunanin ta .. Irin gudun da suke yasa d'aya daga cikin motocin wanda take tunkararta tayi qoqarin kauce mata amma inaaa seda ta bugeta jikake kiiiiiiiiii... Wani razananna ihu Maysam tayi segata a qasa ta fad'i a sume..... Cikin hanzari mutanen motocin suka fito kowa se rabka salati yake... Amma shi wanda yake cikin motar da'aka kad'eta be fitoba yade zaro qafarshi guda waje kuma da alamu baze fito ba...se direban ne ya fito da gudu... Wata kyakyawar mata fara me kimani shekaru 45 zuwa 50 ta fito daga d'aya daga cikin motocin ta iso har inda ACCIDENT d'in ya faru.se innalillahi ....takeyi...ganin yarinyar ta suma yasa ta bada umarnin susata mota su kaita hospital.....Sarauniya MARIYAMA kenan wacce ake cewa Fulani matar sarkin garin Damagaram wato ZINDER mace me tausayi ,,rikon amana ..hakuri .da kuma gaskiya ... mazan naga sun tunkari ta da niyar d'aukanta Cike da b'acin rai Fulani ta daka musu tsawa tace bakwa ganin mace ce da kuke famar d'aukan ta ....da sauri naga sun rusuna suna bata hakuri .. Se a lokacin na qare musu kallo kayan jikin su irin na dogarai sarauta ne ...... Wasu mata nagani su ukku masu kaya iri d'aya da alama kuyangu ne ...da sauri cike da zafin nama suka dauki Maysam suka sakata a mota suka fice daga garin ma gaba d'aya ba tare da sunyi abunda ya kawo su..... Direct masarautar su suka fice da ita dayake sunada clinik anan cikin masarautar dan haka emergency na clinik din aka kaita ...nan da nan Doctarori kwararru na clinik d'in suka ansheta dan ceto rayuwarta ..... Sunfi awa biyu tukon suka fito suna goge zufa...abin mamaki fulani na nan zaune tana jiransu ... Nan suka rusuna suna kwasar gaisuwa ... .. Damuwa qarara kwance a fuskarta tace Doc da fatan de bata mutu ba? Doc Mansur yace muje office de... Nan tabi bayanshi tare da kuyangu mata suna take mata baya .. Bayan su zauna Doc ya fidda lunette(gilashin). Yace sede kuyi hakuri yarinyar ta samu karaya a qafarta ... Innalillahi ......fulani tafurtawa..tace yanzu ta farfard'o .. Eh ta farfard'o da kyar sakamakon irin razanar da tayi amma kada ku damu ''elle est hors de danger''yanzu mun mata karin ruwa tare da allurar bacci koda zata farka se zuwa nan da 8hours kenan gobe da safe incha Allah... Nan tayi godiya ta fice cikin gida ... Bisa doguwar kujera ta falon yake a kwance ya malla'ka ''écouteur''(earpice).a kunnenshi.ya rufe ido kamar me bacci...dogo ne .fari ba irin sosai d'in nan ba ..yana da sumar gashi tare da saje yanada faffad'an kirji ...gashi da dongon hanci ..bakinshi kuwa irin kiss me baby nanne😜 lol ......Prince MURAD kenan Besan da zuwanta ba se jin kiran sunan shi da tayi .. Tashi yayi zaune yace na'am Momy .tareda fidda earpice d'in. Fulani tace yanzu abunda kayi ka kyauta kenan ? Kicin2da rai yayi..kallo daya yayi wa kuyangi eh kuwar har rigay2 futa suke dan sun gane ma'anar kalon yace to ni mi nayi ne Momy? Au baka ma san mikayi ba ..?..jinake motarkace kuma kana ciki kuka kad'e yar mutane amma ko ka leqo ..idan fa da ta mutu ..kuma a haka kace kai docteur ne .... Haba Momy jiya2 nanfa na dawo amma har kin fara gajiya dani ...kuma kun sani ba tun yau bana son zuwa hanyar qauyikan nan ..dan kullum inde nabi hanyar to se munyi ACCIDENT imma da mutum ko da dabba..amma kuka matsa keda me martaba da sena je Kuma fa kada ku manta a wannan hanyar ce mukayi ACCIDENT din da yayi sanadiyar rasa qanwata ,,jinina ..rabin raina ''ma raison de vivre''sega hawaye sharshar yana futa daga idonshi .. Fulani Tausayin d'anta ya ka mata ...ta dora kanshi bisa cinyarta tana goge mishi hawayen tace ya za'ayi na manta da tragic ACCIDENT d'innan wanda a SANADIN ACCIDENT d'in ne na rasa y'ata ....ga ciwon zuciya da Qanwata ta kamu dashi ...dama abubuwa da dama..sede muce Allah ya kai haske kabarinta.....ameen cewar Murad Tashi zaune ya kumayi yace amma ni Momy a kullum zuciya na na bani bata mutuba ....a kullum ina ji ajikina kamar tana raye a wani gurin ..shiyasa bazan tab'a yin aure ba ... Fulani tace haba wai bana hanaka fad'in kalman nan ba .......tun lokacin da abun ya faru kake fad'in haka..kuma kasan hakan baze ta tab'a yuyuwa ba..dan kuwa ko satin da ya huce seda me martaba yayi zancen aurenka tundade ka gama karuntun ka kuma har kana aiki... Haba Momy nifa bazan tab'a yiwa Angel kishiya ba ..ita kad'e ce a duniya kuma haka ma a aljanna.. Momy tace kajiye mun yaro da shirmen banza ..to ina Angel d'in take ne?..itada bata ma doron kasa amma har kana wani baza kamata kishiya ba.....to tun wuri ma ka fidda wannan daga kwakwaluwar ka... Bece komi ba ya tashi ze fita a palon yana fad'in bari na tafi mosque... Girgiza kai kawai tayi ta shige rooms dinta... Washe gari Maysam bata farfad'o ba se wajejen sha biyu na rana ..da Fulani tayi arba wanda.shigo warta kenan itada jakadiya .... Da sauri tayi yunqurin tashi amma seta ji wani zafin bala'i a qafarta se a lokacin ta tuna abunda ya faru .... Nan ta fara kuka qasa2.....jakadiya ta futa kiran docteur..... Fulani kuwa matsowa tayi kusa da ita tace sannu ya jikin..? Da kyar ta'ya furta da sauki.. Ita Fulani a tunanin ta kukan zafin da qafarta take ...ita kuwa anata b'angaren kukan had'uwar ta da Murza take..abunda ya fara fad'o mata a rai shine ko ina shanun data fito kiwo suke...... Fulani ta katse mata tunani da fad'i kiyi hakuri kiyi shiru kinji tsautsayine inya wuni baya kwana ......tace ya sunanki ne? MAYSAM kawai a takaice ta fad'a.. Fulani ta sake maimaita sunan tana shirin kara wata maganar ... sega Doc ya shigo nan kwashi gaisuwa wurin fulani ..sannan yayi yan gwaje2 shi yace alhadulillah komi normal se karyar qafar kawai ...amma a bata abinci taci yana fad'ar haka ya fita a d'akin ... Maysam tace karaya kuma na shiga ukku ni se kawai ta fara kuka..... Ta kalli Fulani tace dan Allah baku ga shanun dana 'e kiwonsu ba...? A'a fulani tace ..amma bari zan tura a gani ..yama sunan qauyen ku da a sanar da iyayenki kada suyi ta nemanki .... Nan ta fad'i sunan tare da suna Malam Musa amma addu'a ce fal ranta Allah yasa a samun shanun....(baiwar Allah a memakon kiyi add'ar samun saukin ki amma ke ta shanu Murza kike...😭..) Fulani tace a memakon kiyi ta lafiyar amman ki ta shanu kike Maysam tace shanun Murza ne.. Wacece kuma Murza? Innata ce cewar Maysam Bata qara cewa komi ba daga haka Bayan kwana biyu tana jiyya nanfa hankalinta ya koma gida Alla2 take a meda'ita gida .. Bayan docteur ya duba ta tace itafa qauyensu takeso a mayar da'ita . Yace ai ko a barki ki koma senan da one week ..nan fa ta shiga kukan ita dole a kaita gidan Suna haka sega Fulani da kuyangunta sun shigo tare da kulolin abinci... Fulani tace ya akayi ne take kuka ...nan docteur ya labarta mata ..tace jeka abunka zanji da ita ..nan ya fita kuyangu ma sukayi waje ... Fulani tace kiyi hakuri nan da satin nida kaina zan sa akaiki qauyen ku ..kuma na tura an sanar da innarki . cewa ACCIDENT kikayi kinanan Wani kukan ta saki jin Murzace aka sanarwa ba Abbata ba ..tace nide dan Allah ku barni ta tafi dan walahi inna Murza dukana zatayi.. Fulani takalleta da kyau tace duka kuma bayan an sanar da ita bakida lafiya.. Se alokacin ta tuna subul da baka datayi .. Fulani ta share mata hawayen dake zuba a idonta tace ko zaki iya bani labarin ki ....dan da alamu kina da damuwa gaki kuma yarinyar karama dake ... Ganin irin kirki da kulawar da fulani ke mata yasa Maysam bata labarin rayuwarta amma ta b'oye mata ita yar tsintuwace... Bakaramin tausaya wa fulani tayi mata ba har seda tayi kwalla bata sani ba ... Lalashinta tayi sosai harta saki ...ta bata abinci taci .Maysam a ranta tace kamar ba matar sarki ba ko kad'an bata da girman kai... Fulani tasa akayi mata gwanji HIV aka ga batada komi .....nan ta qara tabbatar da irin makirci na Murza Bayan sati kuwa.ta murmure tayi kyau har wani shining take ...sosai fulani ke bata kulawa gashi har sun dan shaku da buna dan kuwa tana zowa dubata a kullum... A b'angaren Murad kuwa ya koma England dan can yake aiki kuma a leqe bezo yaga yarinyar dasuka kad'e .. Fulani tayi fad'a har ta gaji ta kyaleshi 🌹🌹🌹🌹 A qauyen kuwa bayan kwana hud'u dayin Accident d'in Malan Musa ya dawo ya tarar da abun bakinciki dan kuwa.Murza ce mishi tayi Maysam ta gudu itada wani saurayin abokin karuwancinta ..kuma duka qauyen abunda.suke cewa kenan...alhalin Fulani ta turo dogarai an sanar da Murza da accident ne har aka bukaci ta biyo su amman taqi amman dan iya makirci ta shirya wannan qaryar.. Sosai hakalin Malan Musa ya tashi shide yasan qarya akeyiwa Maysam tsoranshi daya tana ina yanzu? Nan ya fara kewayen qauyika na kusa dasu amma ko mekama da ita be gani ba yau har tsawon sati kenan.. 🌹🌹🌹🌹 Maysam kuwa sauki ya fara samuwa nan tace itafa a meda ita gida ..fulani batayi gaddama ba nan aka sallameta tare da alkawali za' a ringa zuwa diba ta har ta warke ..jakadiya da kuyangu biyu aka bata yan rakiya tare da d'umbun alheri harda keken guragu aka bata.. Kafin su fice aka kaita wurin me martaba sarkin Damagaram Alh MUSTAPHA sari me gaskiya dantako da adalci..ta kwashi gaisuwa sanan suka kama hanya wanda harda kukan rabuwa da fulani tayi ..ita ma a b'angaren ta fulanin bata so rabuwa da'ita ba... Muje zuwa... Fasma ce✍ [5/4 18:23] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) S.W.A 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Sakon gaisuwa ta musamman zuwa ga y'an kungiyar mu Star writer's Ass hakika ina me farin cinkin kasan cewa cikin wannan kungiya* *Allah ya qara had'a kamu* ... *Alherin Allah ya kaimu ku a duk inda kuke* : *Queen baby* ( *in-law d'ina* 🙈) *Momyn Mufeeda* .. *Ummu* *Hadjara Arfat .. ina sokon sosai* 😍❤. _Allah ya bar zumunci_ 🤝 Dedicated to All my Fans❤💋 🅿 13__14 ```Manzon Allah (SAW) yace''Duk wanda baya tausayin mutane to shima Allah ba zaiyi masa Rahama ba'' Bukhari da Muslim suka rawaito shi``` . Tafiyar awa biyu ta kaisu kauyen . Maysam tunda suka tunkari unguwar su kirjinta yake ta fat2 tsoranta daya kar ace Malan Musa bayanan.. A kekenta na guragu kuyangun suka turota har tsakar gidan ...idan sukayi ta kwad'a sallama sega Musa ya fito daga bayi da buta a hunnu wanda besan lokacin data fad'i daga hunnunshi sakamakon tozali da yayi da Maysam .. Da sauri harda d'an gudun shi ya qaraso wanjenta ya rumgumeta yan shafa kanta yana fadin yar Abba kece?ina kika shiga tsawon lokacin nan ?kisan kuwa irin wahalar neman naki danayi? Itama qanqameshi tana kuka me game da dariya ..sun jima a haka sai da jakadiya tayi gyaran murya tukon ya san ashe da mutane a wajen. Sakinta yayi yana kallon su yace ku kwa daga ina bayin Allah ... Maysam tayi saurin cewa Abba ka bari ku gaisa mana .... Taburma ya dauko ya shinfid'a musu ...ya kawo musu ruwan sha .suka gaigaisa .... Jakadiya ce ta labarta mishi komi game da ACCIDENT d'in Sosai ya tausayawa yar tashi har da kwalla ashe tana can tana jiyya Murza da yan qauyen sharri ne kawai suka kulla mata daman ya san haka kawai Maysam baza ta bar gida ba ... Da zasu tafi Malam ya musu sha tara ta arziki duk da yasan sun fi qarfin abunda ya basu.... Murza na d'aka tana jin duk abunda suke fad'i a ranta tace ai walahi baza ki tab'a warkewa daga karayar nan ba ...gurguwa ma zan meda ke shegiya mayya ina jin dadi na rabu da ke ashe kika ce ina nan dawowa...tayi tsuka yafi a kirga ...(jifa se kace gurgunta mutum din a hanunta yake😏.) Wunin ranar har dare Maysam na bawa Musa labari irin kirkin da kulawar da Fulani ta bata ..shima ya labarta mata irin yawon neman daya yi mata... 🌹🌹 Haka rayuwa tayi ta tafiya yau har tsawon wata guda idan Maysam yanzu sauki ya fara samuwa sosai ta murmure abunta har wata qiba tayi tana jin dadi rayuwarta dan kuwa Musa yanzu baya zuwa ko'ina yana zaune yana jiyyar y'ar shi har ta warke ... Lokacin kuwa Murza had'e zuciya ne kawai batayi ba dan haushi taso yayi tafiyar kasuwancin shi dan ta samu damar idasa qafar Maysam.. ga aikin gida ita kad'e keyi Maysam na zaune sede a dafa a bata taci....😆 Zowan su jakadiya ma ukku dan duba lafiyar Maysam d'in.... 🌹🌹. 🌹🌹 Zaune yake a gaban me Martaba ya sadda kai kasa se bada hakuri yake Fulani na gefen me martaba gefen d'ayan kuwa wata matace wacce za suyi sa'anai da Fulanin kyakyawa ce itama hjy MADINA kenan matar sarki ta biyu kishiya ga uwar gida hjy Maryama (mahaifiyar Murad) amma se wani yatsina fuska take kamar wanda taga kashi a wurin ..qasa2 kuma inta faki idon sarki seta zabgawa Murad harara.. Fulani na ganin duk abunda take yi batade ce komi ba dan idan sabo ta saba da hakan... Sarki kuwa se fad'a yake yiwa Murad yace to walahi bari kaji na baka sati biyu ka fito da mata in kuwa bahaka ba zan aura maka wacce naga dama .. Shide Murad hakuri kawai yake badawa.. Caraf Madina tace a d'an qara mishi lokaci de d'an nawane se da lallab'a cike da kissa tayi maganar ... Murad beyi wani mamaki ba dan kuwa ta kware wajen makirci a gaban sarki zata nuna tafi kowa sonshi ... Sarki yayi murmushi yace ai d'an naki ne bayaji yaune ake mishi magana d'aya ... Ta qara cewa ayide mishi hakuri wannan gamun ze kawo ... Kasa cewa komi yayi dan takaici ... Bayan sun dawo bangaren Fulani nan ya dinga yiwa fulani kuka kamar qaramin yaro shifa bayason aure kuma bazeyi aure ba ...itade fulani lallashi take tare da yi mishi nasiha ranar a nan b'angaren ya kwana ...a zuwan washe gari ze koma wajen aikin shi.. 🌹🌹. 🌹🌹 Maysam kuwa sauki ya samu har tana d'an taka qafar ... Ganin haka Musa yace zeyi tafiya amma a ranar ze dawo ..Maysam bataso ba amma ba yanda ta iya ..haka yayi sabko ya tafi.. Ranar Murza har zubda ruwa a qasa tayi tasha ...ko awa guda da futa beyiba Murza kwallawa Maysam kiran wanda seda gabanta ya bada ras tasan kiran Murza babu alheri cikinsa ..haka ta turo keken ta fito tace gani inna. ... Wata dariyar mugunta tayi tace yau daga ni seke agidan nan(nace se kuma Allah ba) kiyi abunda na saki ki tsira ..bakiyishi dedeba jikin ki ya fanshe ki ... Itade kallonta take batace komi ba.. Murza tace kaf aikin gidan nan yau kece me yinshi daga sharar garken shanu zuwa ta tsakar gida ..wanke2 girki .wanki d'oko ruwa a rafi.... Batace komi ba hakanan ta lallab'a tayi shara da wanke2 ...tana cikin jan ruwan wanki gugan ya kubce ya fad'a rijiyar ... Wani uban dundun tayi mata wanda seda gantsare ta saki kukan wahala .. Murza tace to kuwa tunda kika bari gugan ya fad'a seki fice rijiyar cikin gari ki d'auko ruwan.. Ta d'auko tulun kenan bisa tsautsayi shima ya kubce ya fad'i a bunka da laka daidaya tayi anan.....daman me karaya inashi ina iya dauko ruwa inba muguntaba ... Murza bata tsaya b'ata lokaci ba ta fara jibgar ta daman da gangan tasata ..iya qarfinta take dukanta har Maysam ta fad'o daga keken aman wannan be sa Murza ta dena kishinta ba.. Cike da mugunta tasa qafa ta take qafar me karayar tana wani mummurza qafar har wani cije leb'e take irin na inkana yiwa wani mugunta .. Wani quwa Maysam tayi se kawai tayi suman wahala ...tajata rana ta yar anan..(Allah sarki Maysam😭.) Kan kace mi qafar har ta fara kumbura ... A dede wannan lokacin sega su jakadiya suna rafka sallama a gidan jin shiru yasa suka leko daga zauren gidan ..ganin Maysam a yashe tsakar rana ga kuma babu alamun rai a tare da ita da gudu suka qaraso cikin gidan suna salati ganin irin kumburin da qafar tayi yasa suka d'auketa dan kaita likita.. Eh kuwa sega Murza nan ta fito nanfa tace babu wanda ya'isa yatafi mata da y'a ta fara musu borin hauka tare da zage2 hakan ya tunzura jakadiya ta kwallawa sarkin hukunci kira dayake tare suka zo ... Murza na gani shirgegen qato fuskar nan murtuk ai da gudu ta shige daki ta kulle tana ihu b'arayi zasu sace Maysam wai anufinta ko makota zasuji ... A guje suke tafiya tun a hanya jakadiya ta sanarwa Fulani abunda ya faru nan fulani ta dinga kiran doctarori kan kace mi duk wani kwararen docteur na garin me d'orin karaya ya zo clinik jiran iso warsu kawai ake... Har suka iso Maysam bata farfad'o ba an shafa mata ruwa yafi a kilga aman shiru .... Suna isowa aka kaita emergency nanfa doctarori suka dukufa neman ceto rayuwarta.... Seda suka shafe awanni tukon suka fito fulani na nan tana jiran fitowarsu kamar wancen lokacin.... Bayan sun kwashi gaisuwa d'aya daga cikin doctarorin yace alhadulillah munyi nasara aman a gaskiya yarinyar nan ta wahala dayawa kuma karayar ta dawo sabuwa har ma tafi ta farkon dan haka tana bukatar hutu a 100% ...yanzu haka mun mata allurar bacci ...da zasu tafi akayi musu biya me tsoka .. 🌹🌹. 🌹🌹🌹 Malan Musa kuwa be dawo gida ba se can cikin dare dan haka besan abunda ke faruwa ba .se washe gari yaga bega wulgin Maysam ba har goma tayi ya kasa hakuri yace waini Murza ina Maysam ta shigane ... Kamar jira take ta saki kukan munafunci tace ai Maysam jiya b'arayi suka tafi da ita.. Cikin tsananin tashin hankali yace wani iri b'arayi ke dakata tun wuri kafin raina ya b'ace ki gayan inda kika kaimun diyata inba hakaba zan d'auki mummunan hukunci a kanki Ganin ya d'auki abun da zafi yasa tace wanda suka tab'a kad'e tane sukazo suka tafi da ita wai nan bama kula da ita.. Wani mari ya kifeta dashi yace walahi inde dasa hannunki se kin yabawa ayya zakinta ya fice daga gidan kamar ze tashi sama dan sauri ...dayake masarautar sananna ce kuma wancen lokacin sun sanar dashi dan haka mota me zuwa garin direct ya shiga ..bewani wahala ba aka kaishi har kofar masarautar .... A kofar clinik din ya gamu da jakadiya nan suka gaisa dayakesun shedi juna ..nan ta labarta mishi yanda suka tarar da Maysam da kuma dramar da sukayi da Murza ranshi ba qaramin b'aci yayi ba nan ya bata hakuri tayi mishi jagora har d'akin Maysam d'in ... Har lokacin bata farka ba nan ya samu wuri ya zauna yana kallonta tare da rafka tagumi.. Yana nan har fulani ta shigo nan ya kwashi gaisuwa ..suna cikin haka Maysam ta farka da wani irin ihu tana fad'in dan Allah inna kiyi hakuri ba da gagan bane..bazan qaraba Da sauri fulani ta isa kusa da ita ta riqe mata hannu ta kirayi sunanta Maysam Maysam...... Jin murya fulani yasa tayi shiru tana kallonta se kuma ta fashe da wani kukan me tsuma zuciya tace qafata zafi take mun .. Fulani ta shafa kanta tace yi shiru ze dena kiyi hakuri kinji.....garin yaya kika bari qafarki ta sake karyewa ne ... Tana hawaye ta labarta wa fulani duk abunda ya faru ta qara da cewa kuma fa a gaban Abba bata nuna ta tsanane aman da zarar baya nan seta yi ta muzguna mini....hakika Abbana yana sona bayason b'acin raina yana faranta min amman bansan miyasa Inna Murza ke yimini haka kodan ba'ita ta haifeni ba ne..har lokacin batasan Malan Musa na d'akin ba .... Fulani ta share mata hawaye tace kiyi hakuri insha Allah daga yanzu Murza bazata sake muzguna miki ba..kinjiko.. Gyad'a kanta tayi tace to ..se kuma tace dan Allah a sanarwa da Abbana kada yaje yayita nemana besan ina nan ba.... Batayi aune ba taji muryashi yana fad'in Yar Abba sannu da jiki Cike da jin dadi tace laaa Abba yaushe kazo ne... Be bata ansa ba se cewa yayi ashe haka Murza ke azab tar dake amman baki tab'a gayamun ba?mesa haka yar Abba kina cutar da kanki ... Sadda kai kasa tayi tace kayi hakuri Abba ina tsoran kada na gaya maka kuma daga baya Murza ta huce a kainane.. Ai kuwa ta yiwa kanta dan walahi sena d'au mummuna mataki a kanta yanda kika wahala itama seta sha.. Maysam tace a'a Abba ka kyaleta da halinta kuma ai ba'a meda sharri da sharri .... Duk wanda ya nufeka da sharri to kai ka saka mishi da alheri .. Nan ya rumgumeta yace shikenan y'ar Abba na hakura Allah ya isar miki ya albarkaci rayuwarki hakika ke y'a ta gari ce ina alfahari dake...ameen tace.. Ba karamin burge fulani sukayi ba bare ma Maysam gata yarinya karama aman da kaifin tunani har taji wani abu ya tsargu mata a rai.. Nan aka dinga bawa Maysam kulawa ta kirki komi se anyi mata kai hatta da cin abinci inde fulani na wurin to itada kanta zata bata wata irin shakuwace ta shiga tsakanin su ..kuyangi har mamakin wannan abu suke sunsa fulani da kirki ga tausayi amman abunda take yiwa Maysam abun azo a ganine musamman Maysam da take y'ar kauye.. Malan Musa ne zaune gaban sarki bayan ya kwashi gaisuwa ..sarki yayi gyaran murya yace to daman wata alfarma mukeso kayi mana .. da sauri ya d'ago kanshi ya kalli sarkin se kuma ya meda kanshi kasa yace alfarma fa kuma ma a wajena? Sarki yace ai muna nema alfarmar ka bar mana yar ka ne.. Shiru yayi bece komi ba a ranshi kuwa fad'i yake gaskiya bazan iya bar muku ita ba.. Gani shirun yayi yawa sarki yace dama jiya ne mukayi wata shawara da fulani kan inde bakayi wa yar ka mijiba to muna nemawa yarima Murad auren y'arka Maysam ...😳. To fa fans kun ji wata sabuwa kuma ..... Mu had'u a shafi na gaba insha Allah .. . Ina kaunar ku fans irin sosai d'in nan❤💋 Fasma ce✍ [6/4 23:05] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) S.W.A 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Saudat Farouq na gode sosai da kaunarki ..na ga mesage d'inki kuma in sha Allah zan gyara..Allah ya bar kauna..* ❤😘 Dedicated to All my Fans😍💋 🅿15__16 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce'' Muslim ne ya rawaito shi``` .* Malan Musa yace yarima Murad da Maysam? A gaskiya da wani ne dana bashi amman ai yarima ba sa'an auren Maysam bane.. Sarki yace haba Malan Musa dukan mu yan adam ne duk d'aya muke a wurin Allah babu wanda yafi wani babu fifiko se wanda yafi wani tsoran Allah ...hakane Allah ya bani mulki amman wannan ba yana nufin na fika sede ko in bakason had'a Zuri'arka da tawa ne Da sauri Musa yace wane ni nace bana son had'a Zuri'ata da taku ..tunda hakane ta b'angare na bashi ...bansan ko ita Maysam d'in zata aminci ba amma fa wani hanzari ba gudu ba ya kamata kusan labarin ita Maysam din .. Da sauri fulani tace a'a eh duk Maysam ta fad'a mana komi har irin sharri da akayi mata wanda tun wancen lokaci nasa aka mata duk wani gwaje2 daya dace kuma alhadulillah duk kariyar mutane ce .....kuma kada ka damu nida kaina zan sanarwa Maysam d'in Malan Musa a ranshi ya ce kenan ta sanar dasu y'ar tsintuwace ..amman duk da haka suka amince ..to shi inbe basu ba dami ze saka musu da irin son da suke nunawa yar lelen shi.. A fili kuwa se yace shikenan Allah ya zab'a mana abunda yafi alheri .. Daga haka ya koma clinik... Waziri kuwa wanda akayi abun a gabanshi ...yayi wa sarki da fulani kirari sannan yace ina neman alfarmar fad'in tsokacin bakina game da wannan had'in da ake son yi .. Fulani tace fad'i waziri an baka.. Ya kuwa gyara zama yace naga yarinyar nan ba jinin sarauta bace kuma a al'adar masarautar nan dan sarki se yar sarki hakama yar sarki se dan sarki ..amma agafarce ni idan na fad'i badede ba ... Sarki yace hakane al'ada kace ba addini ba dan haka na rigayi dana zab'awa yarima mata mu hali ,tarbiyya da addini muka bi ,,ina anfanin auren jinin sarautar da ba tada tarbiyya ..daga haka yayi shiru.. Waziri kam kamar ya mutu dan takaici shi yar shi ya so a aurawa yariman sega wata yar qauyen qayau zowar rana tsaka ta samu a bulus ..shida yayi shekara da shekaru yana jira. . ..fakar idon sarki waziri yayi yayi kwafa... Koda ya koma ya tarar da Maysam tana bacci abunta be tada ita ba ya zauna yana tuna magaganun da sarki...... Har fulani ta riskeshi nan ..bayan ya kwashi gaisuwa se kuma ya fita yana fad'in bari na dan zaga cikin gari .. Ko minti biyu ba'ayi ba Maysam ta farka .arba da fulani tayi a tare suka sakarwa junan su murmushi ..ga kuyangu wasu tsaye suna mata firfita dukda AC da ke kunne saura kuwa a zube gabanta ... Fulani tace ya karfin jiki? Alhadulillah cewar Maysam ... Fulani ta kuma cewa a zuba miki abicin kici ko? Gyad'a kai kawai tayi.. Nan kuyangi suka fara zuzzuba abinci kala2 .Maysam ta kalli fulani tace abincin nan yayi yawa fa Batace komi ba ta dauki plate guda me free rice da miyar zogale wacce tasha naman zabuwa ..spoon ta sa tace ci ko kuma sena baki a baki ne ... Dariya Maysam tayi tace a'a zan iya ..ansar plate d'in tayi ta faraci ko spon goma batayi ba tace ya ishe ta ... Fulani ta anshi plate d'in tare da cewa han na baki a baki tunda hakan kika fi so... Babu yanda ta'iya haka take ansar abincin dan tana jin nauyi cewa fulani a'a.... Seda taci rabin tukon fulani ta kyaleta ..tasha lemun abarba wanda yaji kayan kamshi..bayan ta gama ne fulani ta umarci kuyangi dasu basu wuri jiki na karkarwa suka fice kafin nan seda suka yanyaka fruit kamar pomme(apple) ..pastèque (watermelon) dade sauran su.. Fulani tayi gyaran murya tace Maysam ina son muyi wata magana amman bansan ya zaki dauki abunba.. Maysam ta dauki yanka d'aya na kankanar tace ba komi haba kawai ku fad'i ni na d'auke ki tamkar mahaifiya ta .. Sosai furuncin nan yayi wa fulani dadi har taji soyyayar yarinyar ta dad'a nimkuwa a zuciyar ta ...tace amince warki nake nema na ki auri d'ana yarima Murad .. Maysam wacce take shan kankana ai kuwa seta kware ta ringa tari ...da kyar ya tsaya tace yarima Murad fa?ni?gaskiya bazan iya se kuma ta rushe da kuka ta kasa qarasawa tana kunyar cewa bata son jinin fulani kuma ma a gabanta.. Fulani ma sega hawaye shar yana bin kuma tunta tace Maysam bazan miki dole ba kema y'a ce kina da inci ...yarima kad'e Allah ya bani ...ina son ganin jikokina kafin na mutu amma shi yarima aure baya gabanshi saboda wani kuduri nashi ..ina ganin ke kad'e ce zaki iya zama dashi har ki'iya samun soyyayarshi because na yaba da hankalin ki nutsuwarki uwa uba kuma da hakurin ki ...shiyasa nake neman alfarmarki .. Da sauri ta dago kanta ganin shar d'in hawaye a fuskar fulani da sauri tasa hannun ta ta goge mata t tana kuka tace kiyi hakuri na amince se kuma .. suka rumgume junan su fulani tace hakika ke y'a ta gari ce ..ina son ki dauke ni tamkar nina haifeki .tun lokacin da na fara ganin ki naji kin shiga raina time din daki ban labarinki na tausaya miki matuka ..ina son ki riqe amana ki kula mun da yarima .... Duk da bata san yanda ake wani kula da miji ba amma seta tsinci kan ta da fad'in insha Allah zan kula dashi kuma bazan tab'a cin amanar ki ba...se bayan ta fa'di kuma se taji kunya tasa hannuta ta rufe fuskar ta .......girgiza kai kawai fulani tayi tana dan murmushi... Se bayan sallar asar Malan Musa ya shiga d'akin tana lazumi daga zaune abisa gadon da alama yanzu ta idar da sallah....addu'a tayi ta shafa .. Ta juwo tace Abba sannu da zuwa .. Yauwa yar Abba ya jiki ..? Da sauki ta ansa .. Se kuma sukayi shiru har na tsawo yan mintuna .. Maysam tace Abba kaji abunda momy fulani tace mun d'azu.....? Ya san de be huce zancen auren ba amma seyace a'a se kin fad'a dan ya k'arda .. Nan ta labarta mishi komi tana jiran jin mizece ... Yace kwarai kuwa y'ar Abba ni suka fara tuntub'a kuma na amince ......dan mutanen nan suna kaunarki suna da kirki da karama ..kuma shi sarkin da kanshi ya nemi auren ki ....ba muda abunda zamu iya saka musu dashi ..kiyi hakuri ki karb'i rayuwa a duk yanda tazo miki. ....na tabbata bazasu cutar dake ba.... Kukan daya zo mata ta shafe tace shikenan Abba Allah yi mana zab'i na alheri.. Ameen ya ansa nan suka ci gaba da hirar su irinta d'a da uba.....har magarib .. Haka akayi ta kula da Maysam har na tsawon wata biyu .alhadulillah kuwa sauki ya samu har tana taka qafar .....nan suka fara shiryen2 komawa qauyen su ..wanda sati biyu ya rage a daura auren dan haka sarki ya nemi alfarma kuma Musa ya amince ... Abunka da gidan sarauta nan aka fara kuskus ... Waziri ne zaune gaban sarauniya Madina yace gaskiya nayi sakaci dayawa dana san haka zata faru baza 'aba y'ata yarima ba dana biyewa shawarar ki da dad'ewa... .shi 'isa yanzu nazo mu gama karfi da karfe dan mu cimma burin mu.. Wata dariya Madina ta kece da ita tace ai daman kwad'ayin ka yaja maka kayi ta jiran gawon shanu ...da kaso ai da yanzu kaine a kadagar Mulkin nan aman wai kai me y'a ..ai ga irin ta nan .. Waziri yace a bar tuna baya yanzu de na mika wuya... Da kyau cewar Madina ...yanzu de babu wani plan mu bari se ya dawo kasar... Nan suka ringa kuskus wanda bana iya jiwo komi.. 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 A b'angaren.Murad kuwa besan wainar da ake toyawa ba ..yana zaune a office dinshi kiran Me martaba yashigo ......se kawai ya tsinci kanshi da fad'uwar gaba ....haka ya daure ya d'au kiran....bayan ya kwashi gaisuwa Sarki yace ya zancen mu na zaka kawo mun wacce kake so gashi har time din ya shud'e aman bakace komi ba.. Sosai kai yayi kamar yana gaban shi yace ayi hakuri ban samu ba.. Alhadulillah to ni na samo maka kuma nan da two week ne dan haka seka fara shirin dawowa. Wani mummunar faduwar gaba yarima Murad yayi ..yace... Kash kuyi hakuri da wannan . Ina godiya da kaunar ku fans ...ina sonku irin sosai din nan❤💋 Fasma ce✍ [8/4 00:19] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _🏠Home of spécial &extraordinary writers_ ) S.W.A 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Jinjina ga MAMAN SHUREIM hakika kin cancanci* *yabo na ban girma ...Allah ya* *miki jagora a lamuran ki ....thanks for all .* . *wannan page d'in* *na kine ke kad'e Fasma tace kiyi* *yadda kike so* *da shi*.😍❤.. _Allah ya qara donkon zumunci🤝_ 🅿 17__18 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''Sallar jam'i tafi sallar mutum guda daya da daraja ishirin da bakwai'' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` . Wani mummunan fad'uwar gaba yarima Murad yayi dan danan zufa ta karyo mishi duk da AC da ke kunne yace Dady two week fa ?kamar zeyi kuka . Me martaba yace kwarai kuwa kuma bazan karb'i excuse d'in kin rashin zowanka ba dan haka sati me kamawa ina son ka tattaro ka dawo gida.... Beyi iya cewa komi ba se to in sha Allah zanzo.. Sarki yace yauwa Allah yayi ma albarka ... Ameen yace lokacin idonshi har sun kad'e sunyi ja kamar wuta .. Suna gama wayar da Sarki ya kuwa dannawa fulani kiran . Sallama kawai ya iya yi mata ya fashe mata da kuka..kamar wa'i qaramin yaro Bata hanashi ba seda yayi me isar shi sanan tace Murad .. Jin ta kirashi da sunanshi yasa ya nutsu ta wayar kamar yana gaban ta dan bata fiye kiranshi da sunan ba se de inhar maganar dazata fa'da tanada matuka mahimmaci Fulani tace Murad ina so kayi hakuri ka zama me biyyaya ga iyayen ka ..kasan baza mu tab'a zab'a maka abunda ze tab'a cutar da kai ba.......ina son ka zama me tawakali a rayuwarka .....kaza me karbar da kuma yin imani da kaddarar rayuwa au ta alheri wala ta sharri .... Na sani ba tun yauba kake kai bazaka tab'a yin aureba .....kasan kuwa aure sunna ce babba ....Manzon Allah SAW ya na ce wanda baya son sunnata to baya tare dani ...shin kana son kasance wa cikin mutanen da basa tare da Manzon tsirane...? Kamar yana gabanta yake girgiza kai ..yace Astagafirullah....Momy kiyi hakuri daga yau banza sake ba. .... shikenan Allah yayi mana zab'i na alheri.. Ameeen tace Allah ya maka albarka.....to baza ka tambayyi wacce yarinya ce ba? A'a Momy duk wacce kuka zab'a min tayi mini dan banida zab'in da ya huce naku.... Shikenan Son Amma ko sunan ta bazaka so sani ba? Bayason Fulani ta fuskancin wani abun kawai se yace ...ina so mana .. Sunnata MAYSAM seda gabanshi ya fad'i jin sunan aman ya dake yace ..shikenan Momy inada aiyuka anan Office ...next week ganinan zowa in sha Allah.. Cike da murna fulani tace Allah ya kawoka lafiya a ganinta ita ya sauko ya amince da auren daga nan bata san qarfin hali kawai yake yana danne zuciyarshi.. Ranar wuni yayi yana tuno zancen auren ..gaba daya ya kasa qarasa aikin dayake se gidanshi ya koma ...yana me bakin cikin wannan al'amari.. 🌹🌹🌹. 🌹🌹 A b'angaren su Malan Musa sun isa lafiya ...Murza se kaf2 da Maysam take tana tsoron Malan Musa yayi mata maganar karayar Maysam amma se taji shiru hakan yasa ta saki jikinta dan duk a ganinta Maysam bata gaya mishi yanda akayi.ba.. Ai kuwa Malan Musa na fita koda massalaci ne to fa seta san duk yanda zatayi ta muzgunawa Maysam koda rankwashine kuwa... Bayan kwana biyu da dawo warsu da dare tsakani magarib da isha'i suna zaune suna hira Malan Musa yace Murza dama akwai wata magana danakeson muyi. Gyara zama tayi tace ina jinka Allah yasa muji alheri .. Murmushi yayi ya ce alheri babba ma.... Ai kuwa cike da zumud'i tace har na qagauta ka fad'an mana Yauwa dama Maysam ta samu mijin aure ne . Wani turnikeken bakin ciki taji ya taso mata aman ta danne tace miji ..a ina dan ita jira take taji yace dan shaye2 ne ko kuma wani dan daba ko barawo wanda de Maysam zatasha wuya.. Ai kuwa yace Yarima MURAD dan Sarkin Mustapha me damagaram.. Kasa boye bakin cikinta tayi har seda tace na shiga ukku ni Murza Yarima Fa?dan sarki kake nufifa?se kuwa ta fashe da kukan bakin ciki.. Shi abun ma mamaki ya bashi..be iya cewa komi ba se girgiza kai dayayi a ranshi yace tsanar da take yimata har takai haka?to Allah ya shiryeki inme shiryiwa ce.. Kiraye2 sallah isha'i aka farayi ..Malan Musa bebi ta kanta ba ya fice mosque.. Tana gani fitarshi ta fad'a d'aki Maysam na sallah lokaci se jin saukar dorina tayi nan ta dinga jibgarta harta kaita kasa ..ita kukan azaba ita kukan bakin ciki.. Ta rasa miza tayi se kawai ta kama dantsen Maysam ta gantsara mata cizo har sau ukku har ta fitar mata da fata tace walahi baza ki tab'a auruwa ba ..senayi duk yanda zanyi na hana wannan ma.. Wani sabon kuka ya zo mata ta d'aga hannun da niyar kaymata mari taji Sallamar Malan Musa da sauri tace yi mun shiru munafuka sauran ki gwada wani alamu har malan ya fahimci nayi miki wanin abun (kuji fa keda yau har da cizo)... Maysam kam kwna kuka tayi da ga bisani ta dauro alwala ta rinda jero nafilfi tana roqon Allah ta mata zab'i na alheri Murza kuwa kwana tayi tana neman mafita shawara kawai ta yanke taje wurin boka ya hana auren tunda tasan sharri baze yiyu ba tunda sunga irin wahalar da tasha a hannuna..da wannan shawarar ta kwana Washe gari kuwa tayi waMalan Musa karyar zuwa gidan su ta kuwa fice han se wajen boka ''yankan wuka'' To fa Fans ya kuke gani zata kasance ?Murza zatayi nasarar hana auren nan? Yau ba yawa kuyi hakuri da wannan ..je vous aime tous❤😍 Fasma ce✍ [9/4 09:21] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( 🏠_Home of spécial &extraordinary writers_ ) S.W.A 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍💋 🅿. 19__20 Manzon Allah ( ```SAW) ya ce''babu wata musiba da zata sami musulmi sai Allah ya kankare masa wani zunubi shi da ita har ma qaya da zai taka ta sokeshi yaji zafi'' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.``` Zaune take gaban wani bakin mutum ba kyan gani shi kanshi abun tsoro ne ...dagashi se d'an pante irin na mutanen da d'in nan ..kan wannan gashi buzu2 duk ya cikukuye ..se wani uban ja da hakoran shi suke da..wai shi'' Boka yankan Wuka '' Murza kuwa ki kyenkyamin shi bata jiba ..ta zauna tana zayyano mishi duk irin abunda take bukata ..... Buga kasa yayi yayi wani d'an tsubuce2 shi ..ya jima... ya d'ago kanshi ya kalleta a ranshi yace idan na fad'amata gaskiya aikin nan baze yiwu ba tana iya zuwa wajen wani bokan yaci kud'intan a banza dan yaran da take son ayi mata aiki akansu sun riqe addini wani mugun abu baze iya kamasu ba Allah ya karesu .... Se kawai ya kece da wata arniyar dariya yace aikin da kike so ba baze yiwu ba aure ba fashi sede a saka tsanar ta a zuciyar shi bayan auren ya saketa... Jimm tayi tace babu abunda za'a iya yi baya ga wannan? Wannan shi kad'e ne taimakon da zan iya yi miki kuma ko kinje wani wuri kud'in ki ne kawai za'aci.. Shikenan amma asa harda dukanta ya ringa yi... Wata dariya ya sake yi se kuma ya daure fuska kamar bashi ba yace bakida matsala kud'inki dubu goma ne Kud'in kawai ta fiddo ta aje ..ya bata wani kulli magani yace a zuba a abinci ko ana sha a bawa yarinyar...amma ki tabbatar bata yi bismillah ba Se wani washe baki take ta ansa tana zuba godiya kamar kyauta ya bata .. Cike da farin cike ta dawo gida ...ta tarar Maysam ita kad'e a gidan.. Kusa da Maysam ta zauna da sauri tayi tsaye tana fad'in inna sannu da dawowa... Yawwa jeki tatso min nonon shanu ki kawo.. Batayi gaddama ba ta tafi amma a ranta fad'i take lafiya inna yau bata zagen ba bata rankwashen ba ..... Bayan ta kawo mata Murza tace zo zauna kusa dani ita de mamakin abun take .. Kulli maganin Murza ta fiddo tace yauwa ga magani nan na anso miki wurin inna ta ...na tsari ne da kuma mallakar miji .. Itade Maysam kallon ikon Allah take.. Zubawa tayi ta motsa shi tace ungo shanye shi duka Karb'a tayi dan ba yadda ta iya tana tsoran taci na jaki in bata shaba ... Bismillah tayi a hankali takai kwanan bakin ta ... Murza jitake yanzu ne zatayi bismillar se kawai da karfin tsiya ta kama tayi mata d'ure(ee kin makaro Inna Murza dan tayi bismillah tuntuni😜) Har kwarewa Maysam d'in tayi Amma ko ajikin Murza ita murna ma take burin ta ya cika... Ana sauran kwana goma Fulani ta turo jakadiya wacce zata koya mata tafiya dariya ,,magana da ka'idodin gidan sarautar kuyangi kuwa zasu ringa ringa bata labarai da ze sata nishad'i ..dade sauran su ..se kuma wasu mata guda biyu wanda aikin su kawai gyaran jiki ciki da waje... Kan kace mi Maysam har ta fara canza kala fatar nan tayi laushi ga wani d'an banzan kamshi da jikinta ke fitarwa..gashintama ya qara tsawo abunka da farar fata se ta qara yin haske kyawunta da yarintar ta suka qara fitowa .duk abunda ake koya mata kuwa dan dana ta haddace su .. Bakin ciki kamar ya kashe Murza dan ganin Maysam din ma wuya yake mata bare ma ta samu daman dukan ta sede ta shiga d'aki tayi ta rusa kuka (kujiye min wani karfin hali) Malan Musa kuwa yana iya qoqarin shi na gani ya fitar da y'ar shi kumya dukda Fulani tace ta dauke mishi nauyin komi ai diya za'a kowamata ba surika ba.. Yaji dad'in yanda suke nuna kaunar su ga Maysam amma ai wannan baya nufin ya nad'e hannuwa yaki yin komi ba.. 🌹🌹🌹🌹. Yarima Murad kuwa ana sauran satin ya diro ..sosai Fulani sukayi farin cikin ganinshi amma fa shi auren baya gaban shi ...har fulani na tambayarshi event nawa yake so ayi amma se cewa yayi baza'a yi ko daya ba ..a ranta tace be hakura ba kenan... Tundaga haka bata sake mishi maganar auren ba seta nemi babba abokinshi me sunan MAHMUD ta bashi katin auren ya rabawa sauran abokanan su..shi kanshi yayi mamakin dan ko cikin wasa Murad be fad'a mishi ba..nan ya fara raban katin har abokanan su da sukayi karatu tare seda ya kaimusu... Shi kam gogan aka ma be kawo ba kamar ba aurenshi ne za'ayi... Haka Mahmud ya tsara event kala biyu na gani na fad'a ....ranar auren da yamma ayi walima dan ga nan kuma a fice paty da dare.. Yau har gobe daurin aure duk inda ka gilma a masarauta zakaga ana ta shirye2.... Waziri naga ya shiga part d'in Madina na kuwa mara mishi baya..zama yayi ya kwashi gaisuwa tare da zuba mata kirari... Hannu ta d'aga dan danan kuyangun suka basu wuri... Waziri yace na zone naji a ina muka kwana da maganar mu wacen time d'in kince mu jirayi dawowarsa ..amma naji har yanzu shiru shine na biyo sau.. Dariya tayi ta dauki apple ta fara ci cike da isa tace kada ka damu gobe yi warhaka ana ta'aziyar yarima..(se kace ran a hannunta yake) Gyara zama yayi yace fahimtar dani yanda zan gane... Apple d'in ta aje tace kamar kullum danake sawa a fidda mishi Birkin motarshi to yanzu ma haka zansa 'ayi kasan kuwa duk ACCIDENT d'in da yakeyi nice nake haddasa shi amma d'an jaraban yaki mutuwa ..so d'aya nayi nasara shima ba wata ta 'azo a gani bace ... Idan kana tune shekaru tara zuwa goma da suka huce sunyi wani Accident a hanyar su na zuwa kai taimako kauyika.. Kwarai kuwa ni kuwa nake tune dashi wanda shine Sanadin da Murad yanzu kwata2 baya sakin fuskar shi bare har yayi dariya SANADIN ACCIDENT d'in ne ya fara yiwa mutane rashin mutun ci da wulakanci yade na shiga mutane..inde kaga dariyar to yana tare da makirar Uwarshi ne .... To ai nice nasa aka datse musu burkin dan suyi Accident su miuu baki daya amma cikin rashin sa'a yarinyar nan ita kade ta mace.... Ashe kin dade kina farautar ranshi.. Wata dariya tayi tace ai huce nan tun yana cikin mahaifiyar shi naso kashe shi aman dayake me taurin kaine kamar na uwarshi se yaki mutuwa.. Dariya shima yayi yace aikin ki yana kyau Allah nuna muna gobe ..za mu kwashi shokin mutuwar shegen nan.. Sosai ma kuwa ......nan ya fice cike da zumud'i.. Zaune yake a gaban fulani se kukan shagwab'a yake kamar yaron goye .. Fulani tace wai ni halan kuka baya maka wuyane ...daga zance shikenan se ka zauna ka azan kuka.. Matsowa yayi ya daura kanshi bisa cinyar ta yace Momy ba naki maganar ki bane ......ina tsoran wani abun ya kuma sake faruwa dani .........a duk sanda na dauki hanyar zuwa wani kyauye to kamar ina tarbar ajalina ne....a duk sanda na dauki hanyar se nayi Accident kuma ko ba'asa mu wanda ya mutu ba se ansamu rauni me tsanani ....ki duba fa na kwanan da nakayi har muka kad'e yarinyar nan harda karaya ....kaf motocin sun tsaya amma banda tawa ..ba kiga awata motar na dawoba ...lokacin dana tambayyi driver cewa yayi burkin ne ya cire alhali ana gobe tafiyar seda aka dubata komi normal haka kuma duk sauran Accident din ma matsalar burki ne...ina kyautata zaton wani ne yake son ganin bayana ... Da sauri ta rufe mishi baki tace zato bashi da kyau ka bari kasamu preuve tukon ka fad'i haka kada nasake jinka ..Mazon Allah SWA yace 'ku kiyayi zato ,lallai shi zato shine mafi karyar zance''ruwayar Bukhari da Muslim. Shikenan Momy Allah ya shige mana ga .. ameen.tace..idan zaku tafi ka shiga motar Dadyn ka ku tafi tare .shikenan rigima ta qare ko?... E yace,,se kuma yace waini Momy wace yarinya ce ma? Shafa kanshi tayi tace yarinyar daka kad'e ranar nan itace ..matar daza aura.. Whattttttt yar qauyen nan ..qazama da'ita ?haba Momy walahi kun kare dani.. Murmushi kawai tayi tace yaro2 ne koda d'an giwa ne... Washe gari takama samedi''saturday'' kuma ranar daurin aure tun shidda na safe aka kama hanya idan Murad ya shige motar Da Dadyn shi yake ..Waziri kamar ya hade zuciya ganin plan dinsu ya sha ruwa...aman se yayi kwafa yace ai da amariya zamu dawo dan haka a wata amotar zasu dawo ...se suyi Accident d'in ma tare su mutu kowa ya huta.. Takwas ma acan tayi musu nan aka yi musu tarba ta kirki inda kaf yan gari suka girgiza da wannan al'amari ga babu bakin magana ...... Tara(09) dede dubunen jama'a suka sheda auren Maysam Malan Musa tare da Murad Alh Mustapha ...masu murna nayi shide gogan fuskar nan ba annuri dan ma Mahmud na ta tausar shi.. Bare ma inya tuna wai shi akayi wa auren dole kuma da y'ar qauye ji yake kamar yayi fifike ya ganshi England wajen aikin shi... Haka yan bakin ciki ma nayi ..dan Murza rufe kanta a d'aki tayi ta tunga rafsa uban kuka......ho ho ho Murza se haushi .Maysam tayi miki nisa 😜😜. Mu had'u a shafi na gaba dan jin yanda zata kaya.. Fasma ✍ [14/4 23:40] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 (🏠 _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.A.W✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Ina me bawa fans d'ina hakuri na rashin jina kwana biyu hakan ya faru* *sakamakon wani* *uzuri daya taso mini da fata zaku fahimce ni .. ..ina sonku irin sosai* *d'in nan💋💋* *Gaisuwa da jinjina masu tarin yawa ga yan* *kungiyar mu na Star W.A...gaskiya ina* *alfahari da ku mussaman ma* *Momyn Mufeeda* 😍 *Ummu Usman* 😘 *Arafat* 💋 *Mimsqueen* ❤ *Queenbaby my in-law 👸(i miss* *you so much Allah de yasa you are fine..)* *Allah ya qara had'a kanmu gaba daya ina sonku irin* *totaly d'in nan..😍😘* Dedicated to all my fans. 🅿 21__22 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''an halicci zuciya tare da dabi'ar son duk wanda ya kyautata mata da kuma kin duk wanda ya munana mata '' Baihaki ne ya rawaito shi``` . Bayan d'aurin aure me martaba sarki da sauran tawagar suka dau hanyar komawa yayinda su yarima zasu jira su tafi da amariya ...jiyake kamar ya had'e zuciya ya mutu ga tsoro duk ya cikashi tunda su sarki suka tafi yana tsoran kada suyi ACCIDENT a hanyarsu ta komawa... Mahmud de se hakuri yake bashi yana sashi yana yin yaken dole duda ba wata dariya bace yake yade d'an saki fuskar ...zaune suke kasan wata bishiya me tarin ni'ima an cika musu gaba da kaya makulashe da fruits iri2..... Waziri kuwa dan munafunci se yaki bin su sarki wai acewar shi shi ze kula da yarima ba yanda sarkin dogarai beyi ba kan shi waziri ya tafi da sarkin shi se ya tafi dasu Yarima Murad d'in ..amma kimimi waziri yakiya .... Zowa yayi ya zauna a kusa da yariman ya d'anyi mishi kirari yace cikin wace motar zaka koma dan nasa a duba inkomi is mormal cewar Waziri kenan ... Seda ya d'an dau lokacin kamar ma baze amsa me ba se kuma yace cikin bakar Prado .... Da sauri waziri ya miki yana fad'in an gama ranka shi dade... Ya fice yana dariyar mugunta .. Seda ya faki idon jama'a yayi kamar yana duduba tane ashe daga nan ya datse burkin motar amma ba duka ba dan kada a gane a ranshi yace ai daga kai har amariyar taka a lahira zaku angonce har wata waka yake cike da nishadi ... Har hakurin yarima ya fara qarewa suna zaune kusan awa guda suna jira ... A cikin gidan kuwa Mlm ne yake tayi wa Maysam nasiha bisa zaman takewar aure ...yi nayi bari na bari ....yiwa miji biyyaya binshi sau da qafa kai da duk abunda ya shafi aure ..hakkishi shi da hakkita duka seda Mlm ya fad'ima Maysam .. Ita de banda kuka babu abunda take har shima seda ta sashi kwalla ..haka aka lulub'eta aka fito da ita ... Ganin haka yasa su yarima tasowa dan ya matsu ya bar kauyen nan kamar yayi fuffuke yake ji .. Already duka motocin an jere su a kofar gida... Mahmud ne ya nuna motar da za'a saka amariyar amma mi?kimimi Maysam taki shiga motar anyi2 aman taki ko motsawa daga kofar gidantakiyi wannan abu bakaramin b'atawa Murad rai yayi ba jiyake kamar yaje ya rufeta da duka tsaki kam yaja yafi a kirga.. Mlm Musa yazo ya kama hannun nata har zata shiga motar se kuma taja da baya mlm Musa yace haba Yar Abba ba ki gani kina b'ata musu lokaci ne... Bata ce komi ba se kawai ta fara tafiya kowa ya tsaya yana kallon ikon Allah... Motar dake gaba da wannan prado ce itama amma fara taje ta shige ta zauna abunta ta cigaba da kukanta.. Ran yarima Murad inyayi dubu ya b'ace idon shi har sun fara canza kala zuciyar nan se tafarfasa take .dan kuwa a motar daya kad'e ta ce ranar nan taje ta shiga .a ranshi yace mi take nufi yarinyar nan ne ai de bani takeso na isketa ba ..? Mahmud ya katse shi da fadin calme toi mana kowa yana kallonka kayi hakuri ka shiga waccar d'in mutafi dan kada mutane su fahimci cewa baka son auren kuma ma umarnin Momy ne cewa ku tafo cikin mota guda Ba yanda ya iya tunda yace umarnin Momy ne.. Zagayo wa sukayi shida Mahmud zasu duka dan gaisar da mlm da sauri ya rikesu yace a'a base kun kai kasa ba Nan ya d'an yi musu takaitacciya nasiha sanna yace ya damka mishi amanar yar shi .. Sosai jikin Murad yayi sanyi .. Murza na leke daga kofar gida se sharb'ar kuka take a rantan tace yanzu wannan kyakyawan ne mijin Maysam ga kudi ga sarauta ..kai walahi da sake wai ambawa me kaza kai.. Da gudu ta koma gida tana kukan bakin ciki da yawa sun tausaya mata dan a jiinsu kukan rabuwa da yarta ne takeyi.. Kamar da wasa ta yafo mayafinta wai itama rakiyar amariya zata babu wanda yai yunkuri hanata ta kuwa shige wata mota tayi kane2 a ranta tace ai se naga kwakwaf... Mlm musa girgiza kai kawai yayi ya kyale tane dan yasan yanzu Maysam tayi mata nisa baza ta tab'a gigin tab'ata ba dan kuwa kafin auren ma wuyar gani take mata duda suna gida guda tayita mitar har ta gaji.. A gefen waziri ma kamar yayi kuka dan takaici Maysam ta b'ata mishi show shi har ya hango yarima cikin makara a ranshi yace aman yarinyar. Nan tacika magulmaciya.kwafa yayi yace ai yanzu aka fara Wasan Koda ya tunkari motar yaji zuciyar na b'aci tuna abunda Maysam tayi mishi yanzu a zuciye ya bud'e ya shiga motar kamar wanda ya aka hankad'o shi se huci yake.. Yace ke d..... Kuyi hakuri da wannan... Ku biyo ni dan jin yanda zata kaya ..nice taku har kullum Fasma✍ [16/4 00:22] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( 🏠_Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 👏👏 *jinjina gareki Momyn Mufeeda ina tayaki murna* *kammala littafi ki* *na UWAR RIKO part one da kuma fara part two hakika kina nishad'antar* *damu da fadakardamu ...Allah ya qara* *miki basira nikin banikin ...ya qara miki hazaqa da zakin hannun* .... *Ina yinki irin sosai d'in nan ......* *Muna biye dake se mun jiki a* *part two 👍fans kada ku bari abaku labari ....je t'aime beaucoup ❤😘* *Fans din Sanadin Accident ban* *manta daku ba alherin Allah ya kaimuku a duk ina kuke ..ina jin* *dadi yanda kuke *bibiyar* *book d'in ..Allah ya bar kauna ...je vous aime tous* *irin totaly d'innan* ❤💋 Dedicated to all my Fans ..❤😘 🅿23__24 ```Mazon Allah (SAW)ya ce''Babu wani daga cikinku wanda aikinshi zai shigar dashi aljanna,haka nan babu wanda aikinshi zai tserar dashi daga azabar wuta ,har ni kaina sede don rahamar Allah'' Muslim ne ya rawaito shi. ``` Kamar wanda aka hankad'o shi ya fad'o cikin motar se huci yake beyi wata2 ba ya ware yatsun shi biyar da Allah yayi mishi ya zabga mata mari seda taga Star✨ ze qara mata Mahmud ya rike hannun ya ce haba Murad miye hakane ...jinake yanzu nan mahaifinta ya damka maka amanarta ..... Bece komi ba ya dunkule hannun tare da juya. Kai... Maysam kam tana lulub'e ciki mayafinta taci gaba da kukanta kasa2 Mahmud kuwa ya ba driver oder su tafi .. Sun kama hanya ko ida fita daga garin basuyi ba Murad ya ce arrête(tsaya)... Suna tsayawa Gaba daya motocin suka tsetsaya suma.. Da sauri dogarai suka kewaye motar yarima suna jiran suji dalilin tsayiwar ..yafi 5mn sannan ya bud'e motar ....nan ma ya dau kamar 2 mn da kyar kamar wanda bakinshi yake ciwo yace '' je besoin de laver mes mains ''(ina bukatar wanke hannu na) Kan kace mi tuni dogarai sun kawo ruwa. sabulu da 'eau de javel' da alama dama sun tanadi hakan nan ma yakai 5 mn yana wankewa tukon ya koma cikin motar ... Mahmud ya ce wai wani irin abune wannan muna tsaka da tafiya ka tsayar damu saboda wani wanki hannuka ... Wani kallo Murad yayi mishi yace bakaga hannuna ya taba jikin kazamar nan ba so ina tsoran daukan wata cuta ne... Bece komi ba se tsaki dayayi suka cigaba da tafiya.. Sunci rabin tafiyar amman Maysam bata dena kuka ba .. Wata sangamemiyar tsawa Murad yayi mata yace walahi ki rufe min wanan kazamin bakin naki ko na tattaka yanzu nan(jifa kaida ma baka ganta ba taya kasan bakinta kazami ne🤨)in bama iskanci ba ni banyi kuka ba da aka kakaba minke ..seke dan kin raina mu zaki tasamu gaba kina kuka ..to tun wuri kiyi muna shiru konayi waje dake yanzun nan dakikiya kawai.. Tsit kakeji tayi shiru kamar wanda ruwa ya cinyeta Mahmud ya girgiza kai kawai yayi a ranshi yace a dake ka a hanaka kuka kenan Har suka isa babu wanda ya sake yin magana .... Zo kaga yanda fulani ke shiga da fice tana bada oder yau sirikar ta zata zo shirye2 ake ainun .... Wajejen sha biyu na rana suka iso Madina dake lab'e tana jiran taga an fito da gawar su Murad amma se taga ya fito ya na tafiyar nan tashi ta kasaita ...dogarai da kuyangi se kwasar gaisuwa suke ... Kukane kawai ya rage mata tayi amma iya bacin rai tayi ..jitake kamar taje ta kasheshi ...a fusace ta koma d'aki tana huci tace walahi ya zamo dole kabar duniyar nan matukar ina numpashi to se na ga bayan ka...dana zauna in ga an nad'aka sarki na tashi a tutar babu gwara na kashe kai na.walahi...kafin hakan ta faru kuwa zan kawar dakai daga doran duniya...(ji wani jahilci.....Allah ka shirye mu) Tana cikin haka sega Waziri ya shigo shima fuskar nan ba annuri ...nan ya labarta mata duk yanda akayi ... Ta ciza yatsa tace ba komai kaje kawai zan san yanda zan b'ulowa abunn...kabarni dashi kawai...... Direct b'angaren Fulani a kayi da Maysam su Murza se kale2 take anshigo binni se wani washe baki take ta ma manta gidan Maysam tazo... Babu wani kyakyami fulani ta rungume Maysam... Itama kuwa batayi kasa a gwiwa ba ta kankanmeta tasaki wani sabon kuka... Rad'a naga fulani tayi mata se kuma tayi shiru tanagoge hawayen ta.har da yar dariya.. Murad daketa kallonsu tun d'azu a ranshi yace na kusa fasa hawa cinyar Momy tunda har ta rugume wanna kazamar(jifa kai ko kunya baka jiba wai ka hau cinyar Momy.😏) Tarba ta gani ta fa'da akayi musu ..Murza an samu kafar kaza se guiguiya take ..tana zuba santi...tama manta da bakin cikin da take Maysam kam d'aki na mussaman aka kaita ana bata kulawa ....itama yanzu har ta fara d'an sabawa da bawa kuyangi oder duda ita tafi sontayi komi da kanta .. Kamshi kam duk idan ta zauna se ta bar kanshi a wurin .. Kyau kam har wani yellow 2 tayi kyawunta da tsantsar yarintar ta ya fito shar da ita... Karfe hud'u dede aka fara walimar inda mutane da dama suka halarta ...anci ansha inda uban gayar da kyar aka shawo kanshi ya zo wanjen shima albarkacin abokanen shi na wajen aikinshi da sukazo .....amma fuskar nan a d'aure tam...haka aka gama gabani magrib sannan kuma bayan isha za'ayi paty... Zaune take se kuka take yi anyi2 tayi shiru takiya kuma taki shiga tayi wanka har ana kiran sallar isha'i. Dasuka ga abun banayi bane se suka kirawo fulani nan suka fita gaba d'aya aka barsu su biyu . .... Fulani tace Maysam2 Ta d'ago kai idanunta har sun fara yin ja saboda kuka Goge mata hawayen tayi se kuma ta rumgumeta ..tana d'an bubbuga bayanta tace haba Maysam kukan nan ya isa haka ko so kike ki jawowa kanki ciwon kaine?ko yunwa kike jine? Ta girgiza kai tace a'a Wani abun kike so ?ko kuma wani ya b'ata miki rai ne yanzu ya fuskanci hukun ci . Nan ma girgiza kai tayi alamar a'a To mi ya saki kukane wai.. Cike da yarinta tace ni bana son zuwa patyn nan ...ni walahi ina jin tsoran shi kada ...se kuma tayi shiru... Momy tace kada mi?fad'i mun mana ''ma fille'' ....mi Murad d'in yayi miki ne? Yo ba d'azu damuna zowa ne kawai.....se kuma ta sake yin shiru tace shikenan ma Momy manta kawai bari nayi wanka.. Kan tace wani abu tuni ta shige tolet dan kada tasata dole ta gaya mata.. Batace komi ba itama ta fice a d'akin a ranta tace lallai Yarima yayi sa'ar mata ..tun ba'aje ko ina ba har tasan ta rufe sirrisu duda karanci shekarunta,....kai alhadulillah ..cike da nishad'i ta shiga part d'in sarki dan yau ita ke da girki... Bayan ta fito aka fara cancad'a mata kwalliya ...wata dakyakiyar shadda fara ce dumki doguwar riga aka bata tasa aka kashe mata daurin dan kwali ...komi na jikin ta ''rouge'(ja) banda rigar kama daga d'an kunne takalmi etc...se dan mayafi me kama da net shima rouge ta yafa ...rigar dama daga sama ta dan matse se daga guiwar aka bude ta ....dukiyar fulanin da hips din nan sun fara fitowa dan bazaka bata su a shekarunta ba..... Tubarikallah masha Allah abunda yan cikin dakin suke fadi ...inde har baka yiwa Maysam farin sani to baza ka tab'a ganewa ita ce ...Fans naso kuganta kukanku da se kun saki baki da hanci ...kuyangi se zuba mata kirari suke Takwas saura suka fito ..lokacin kuwa su Murad sun jima suna jiran su....duda acikin masarautar ce za'ayi amman dayake abun nasune se amota za'a tafi .. Zo kuga bakin ciki kiriri wurin Murza dan har kasa hakuri tayi ta cewa Maysam wly ina bakin cikin wannan auren kuma se nayi duk yanda zanyi na raba auren nan shegiya Mayya me kama da aljannu ..waya sanima ko diyar sarkin wani aljanin ce...ta bankad'e ta ta fice.. Itade Maysam idon wannan shine bata ce da ita komi ba ...se addu'ar neman tsari datayi .. Ran Murad in yayi goma ya bace banda tsaki babu abunda yake dan ya tsani african time.... Gabanshi ne yayi wani mummunan faduwa sakamakon yin tozali dayayi da fuskar Maysam dake nufo so ...baki da hanci ya saki (kamar Halima da Samira sunga MIP😜 .)ya zubawa sarautar Allah ido banda wata barakallahou fi.........babu abunda yake ambato wani abu yaji ya d'asu me a zuciya kafin ya lalibo yaji miye Mahmud ya katse shi da fadin kallon ya isa haka kada idon su fad'o sanan yasa hannu ya rufe mishi baki... Wani haushi ya ji ...Mazgewa yayi ya buga tsaki Mtssss to uban mi zan kallan a jikin yar kauyen ne ... Shide Mahmud dariya yayi yace ashe shegen ka iya zab'e wannan kyau har haka gata kuma yarinya danya sharat haka ..amma kake wani basarwa kamar baka son auren.. B'ata fuska yayi yace ya ishe ka haka fa to.. Kafin yace wani abu su Maysam suka iso.. Mahmud ya fito ya bude mata baya inda Murad yake yace bismillah amarya Tana d'ari2 ta shiga motar ya rufe ya zagawo ya shiga danshi ze tuka su.. Wani ni'imtaccen kamki shi ya daki hanci Murad besan lokacin daya lumshe ido ba ..... Itama hakan ta kasance a ban'agarenta a hankali ta bude baki zata gaishe shi gudun kada tayi laifi amma mi? Wata jibgegiwar tsawa Murad ya daka mata yace d..... Wash kuyi manaje da wannan.. Fasma✍ [17/4 01:03] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *My queenbaby my lovely in-law wai ina kika shiga ne two days..Allah de yasa you are fine .* *and alherin Allah ya kaimiki a duk inda kike..i miss you so* *very very much💋reviens vite...je t'aime* ❤ Dedicated to my queenbaby😍💋💋 🅿25__26 Manzon Allah ( ```SAW) ya ce''Dayanku ba zaiyi imani ba har sai na kasance ni nafi soyuwa a gareshi daga dansa da mahafinsa da duk mutane baki daya'' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` . Wata jibgegiyar tsawa Murad ya daka mata seda ta gigice gaba daya ta qara tsorata dashi yace...ke dabbar inace da baza ki iya gaishe damu ba.... ohooo 😮ko mu kike jira mu gaishe kin ko ? Idiote kawai....... Jikinta har b'ari yake ta sauri tace ina wuninku Yaya.. Muryarta na dakar dodon kunnenshi besan lokacin da ya juyo da kallenshi gareta ba Aka koyi sa'a ta d'ago kai itama ...idonta cike da kwalla kad'an ya rage su zubo ... Habawa idon na sarkewa cikin juna gaba dayansu suka kasa d'auke idon kowa da abunda yake ayyana wa a zuciyarshi ..... Ita tana yaba irin kyan da Allah yayi mishi ne Shikam gogan gani yayi tana mishi kama da lovely sister dinshi data rasu a SANADIN ACCIDENT dasukayi da dad'ewa.....wata irin tsanar ta yaji yana shigarshi dan kuwa ta tuno mishi kahon zuciyar shi .........kawai beyi wata2 ba ya zabga mata wani kantameman mari seda gefen bakinta ya fashe yace ''que ça soit la première et la dernière fois(wannan ya zama kashedi na farko kuma na karshe) dazakiyi gigin qara saka idonki cikin nawa kai ko kallona na kamaki kinayi da wannan idon naki me kama dana mayu to walahi na lafira seya fiki jin dadi shasha kawai kina yar jinjirar ki amman har kin san ki kafe mutum da ido a ranshi yace walahi Momy ta gama dashi a rasa wacce za'a aura mishi se wannan yar shilar(ni kuwa nace dama na lahira inde dan aljanna ne ai dole ya fita jin dadi nesa ba kusa bama😏ehe ).. Batace komi ba se hawayen dake makalle su ka zubo shar2 ta dafe kuncinta dan marin ya shigeta sosai ... Se kuma ya ga rashin kyauta war hakan danshi be cika son dukan mata ba kai ko gani yayi wani yanayi to ze yi kokarin hanawa ..a ranshi yace to pourquoi na mareta ?mi tayi mun...wata zuciyar tace saboda tana famar tado maka da tsohon ciwon kane...... Ita kam kuka take me cin rai duda in silence takeyi.. Ganin sun kusa isowa yasa ya bata Mouchoir yace amshi maza goge mun hawayen nan sanan kuma kiyu mun shiru duk kin wani cikawa mutane kunne da kuka salon ayi zaton wani abun nayi miki.... Mahmud da bece komi ba tun d'azu yanata tukinshi yace M2 ya zaka daki yarinya sanan ka hanata kukan ai abun se yayi mata yawa ... Wata harara daya zabga mishi yasa shi yin shiru.... Maysam kuwa amsa tayi ta goge hawayen sanan ta gogoge jinin na gefen bakinta ..yar karamar bag dinta ta bude tasa mouchoir din kudun kada ta bashi tayi wani laifin a ranta tace shi kuma wannan haka kalar tashi muguntar take,? Babu wanda ya sake cewa komi har suka iso ... Har ze fita Mahmud yace na roke ka kushi ga tare kamar yanda ko wa yake yi ...fais ça pour moi Bece komi ba ya fita ..ganin haka yasa itama tafito...wani jan tapis me laushi da fleurs (flowers) ne shimfid'e tundaga dede motar har cikin hall d'in ... Jero wa yayi da ita suka fara tafiya ...da sauri Mahmud ya sha gaban su yace haba alfarma fa na nema kuma walahi su momy gaba daya suna ciki... Tsaki Murad yayi yace to ya kake so ayi ne dan raini kawai.. Dariya Mahmud yayi dan inda sabo ya saba yace hannun ka zaka zagayo ta baya ka rike kugunta ..itama kuma tayi hakanan se kuma ta kwantar da kanta bisa ka fad'arka shikenan fa Zo kaga yanda Murad ke mishi wani irin kallo kamar idon ze fad'o kasa ..sunfi 2mn amma ko alamun yi beyiba sema wani juyar da kai dayayi gefe Mahmud yace haba M2 kufa kad'e ake jira.. Tsaki ya kuma ja mtsss sannan ya sa hannun da niyar d'aurashi a kugun amma mi?yana d'ora hannun yayi maza ya dauke sakamakon wani shock électrique daya ji ..itama hakan ce ta kasance a b'angarenta har seda ta runtse idanu.... Shikam Murad abun ba karamin mamaki ya bashi ba dan kuwa wannan shock din idan ya tab'a late lovely sister d'in shi kade ne yake jin shi ..ya gane hakan ne dan betab'a sake jinshi ba tun bayan rasuwar ta kuma gashi docteur yasha tab'a mata dan yi musu magani amma bejishi ba.. Wani haushinta tare da tsanar ta yaji yana qara d'asuwa a zuciyarshi har wani zafi2 ta fara yi mishi... Kafin ya gama tunani kiran Momy ya shigo wayarshi yana dagawa ta fara balbaleshi da fad'a taya za'a tara mutane amma dan raini kuki shigowa banci tun dazu kuka zo...kan yace wani abu ta katse wayar... Bin wayar yayi da kallon se kuma yayi shahada ya daure ya mazge ..ya tattaro jarumtarshi ta last year lol ..ya riko kugun .. Mahmud yace amariyar mu ke muke jira fa.. Hannun na karkarwa tayi yanda Mahmud din yace takuwa kwantar da kanta bisa kafad'arshi sede dayake ya fita tsayi so duka tsawon nata bakin dede kafad'ar tashi ne ..nan suka fara tafiya a hankali kamar masu jin tausayi kasar.. Suna shigowa kowa ya zuba musu idanu hall din tak a cike yake da mutane wurin uwaye daba haka wajen matasa ma..ko wacce se wani gyara zaman dan kwalinta take ko zata sayu lol.... Dj ya saki kid'a Masu photo sukace kau ban guri ta ko ina flash kake gani...fulani naga tayi wa Maysam wani abu da hannu wanda bansan mi hakan yake nufiba ..amma ita wanda akayi wa senaga ta wani sunne kai tana dan murmushi kasa2 ...jin ta kara manna kanta bisa kafad'arshi ya sa yajiwo yana kallonta ..haba wannan position ba karamin burge mutane tayi ba .. A Wasu kujeru na alfarma masu ruwan zinare guda biyu jikin juna ne suka zauna ... Nan aka fara programme din da fari aka bada takaitancen tarihin soyaryarsu wanda duk Mahmud neya shirya kayanshi ........aka umarce su da su fito su taka rawa duda a tsaye suke dukan su amman zo kaga yanda ake b'arin kudi.... Daganan kuma akace su fito su yanka ''gâteau ( cake ) tare suka yanka se kuma shi ya fara bata ...dayake ya fita tsayi ..kumashi shi baze iya dukowa ba se kawai ya dan dagata kadan dede tsawonshi ta saka mishi ..tafi raf2👏 kake ji ta ko ina Can na hango yan Star Writer's Ass se wani washe baki suke ana korawa juice..ana kus2 kasa2 lol Samira.. Murjanah ..Dala.. Sarah ...Ummi .....Mzz beeberh ...se shoki ake kwasa ana korawa da juice😜.... Daga can bangaren na hango members na zuri'amu fans2 suma se ciye2 suke .... Anyi ciye2 da shaye2 amma fa na juice duk wanda yazu ya cika tumbinsa sanan duk wanda ze tafi to se anbashi wata sac me shake da alherai kan turarenki ..atampopi ..etc... Se wajejen goma na dare aka tashi wanda a lokaci Murad jiyake kamar yayi fufuke ya ganshi a gida.. To daza su dawo ma seda yaso yayi musu drama .....Maysam tazo kenan zata shiga motar ya kuwa daure fuska yace... Sorry fans Fasma ce✍ [21/4 00:16] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _🏡Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *ina me qara bawa fans ina hakuri na rashin jina kwana biyu ..dayawa* *daga cikin ku naga sakon ninku ..da addu 'oin ku na gode sosai Rabbi* *ya biya ku ...Allah ya qara donkon zumunci ....thanks ina bala'in sonku nima .......* 😍😍 *Welcome back my Queenbaby ...munyi kewarki matuka ......masoyan* *littafin MEERAH ku fito mu kwashi shoki lol* 💃🙈 *anty xaynab is back* ... *Allah ya qara miki basira da* *hazaka .... kinayi muna jin dadi ....fans kada* *ku bari a baku labari dan littafin* " *MEERAH."" na hazikarmarubuciya Xaynab dan* *a gaskiya ya had'u.......love you so much my in*- *law* 😘😍 Dedicated to all my fans❤😍 🅿 27--28 ```Manzon Allah (SAW) ya ce "fiyyayen musulmi shi ne wanda duk musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da hannunsa" Muslim ne ya rawaito shi``` . Da zasu dowo ma seda yaso yayi musu wata drama.....dan kuwa lokacin da Maysam tazo zata shiga motar..ya kuwa d''aure fuska yace ke...se kuma yayi shiru sakamakon ganin Momy da yayi se kawai ya shige motar fuskar nan ba annuri se wani muzzire yake ...ganin haka itama Maysam da ta shigo taja bakinta gum..... Koda suka iso da tayi niyyar fita da sauri ya riko hannunta duk da namijin kokari yakeyi dan ba qaramin dauriya yayiba jin wani irin shock na ratsashi.. Seda yaga shigar Fulani bangaren ta sannan ya jiyo da fuskar nan tashi da har ta canza kala yace dan tsabagen gulma da munafinci miye na wani biyoni dan shinshin daa shegen iyayi kika wani shigo mun mota kamar wata bita zai2 nan ya dinga mata fada ta inda ya shiga bata nan yake fita ba..ya qara da cewa kai ko magana inba nina baki iznin yimun ba kikayi hum yayi kwafa.. Itade idon wannan shine Abunda ya qara harzukashi kenan ya kuwa kaimata rankwashi seda kwalla ta cika mata ido.... Da sauri tace dan Allah Yaya kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba. Na tuba ka yafen.. Wata uwar harara ya ban kad'a mata yace kima qara kiga yanda zanyi da ke ..ya fice abunshi. Sum sum itama ta fito ta fice bangaren Fulani ..a ranta tace Allah abun godiya ... Washe gari wajejen goma na safe Murad ne zaune gaban me martaba ya wani sunne kai banyan ya kwashi gaisuwa ..me martaba yayi gyaran murya yace alhamdullilah Son Allah yanuna mana aurenka ina alfahari da kai nan ya d'anyi mishi nasiha sannan yace game da tarewar matar kace ....nida Fulani mun yake shawarar kawai ka tafi da matarka can England . Wata irin zufa Murad yaji tana karyo mishi kamar baze ce komi ba se kuma yace Ranka shi dade bawai naki bin shawararku bane amma ni aganina abarta nan se asakata makaranta tayi karatun nan Ganin ya fara yin nasara ya ci gaba da fad'in ..because a can karatun zeyi mata wahala dade anbari ta gama koda secondary ne seta ci gaba a can din... Ayi mini afuwa idan na fad'i badede ba Dan murmushi yayi yace shikenan to Allah yayi mana zabi na alheri Ameen yace sanna ya fice direct bangaren Fulani ya nufa..a ranshi yace alhamdullilah na rabu da alajakai ..amma inba abun su momy ba ina yar kauyen nan da zuwa England .... Kwance take ta d'aura kanta bisa cinyaryar Fulani se hira suke abunsu kamar uwa da y'arta gwanin sha'awa... Suna haka ya shigo palon ganin Maysam bisa cinyar Fulani ba karamin haushi yaji ba...ya qara daure fuska... ..gaidata kawai yayi yayi shiru se wani ku mbare2 yake... Da sauri Maysam tace ina kwana yaya ... Wani kallo yayi mata na irin zamu hadu dinna..ciki2 ya amsa a takaice da lafiya.. Momy ta gumtse dariyata tace wai ni son waya tabo min kaine se gumtse fuska kake.. da safiyar. Nan Kicin2 da fuska yayi yace haba Momyn ya zaki bari wannan tahau min cinyata Fulani tayi dan murmushi tace yo inba abunka ba yarima ai yanzu na yayeka ka huce hawa cinya..ka girma ai yanzu kam matarka ya maye gurbin ka ..kafin itama ta haihu ta barwa baby place ko?... Be iya cewa komi ba amma a ranshi yace wai baby ..bade da niba zakiyi ta jiran gawon shanu Kuwa . Maysam kam abun mamaki ma ya bata ta saki baki da hanci tana kallon wannan shiriritar kawar da zancen yayi da labarta mata duk yanda sukayi da sarki yanzu .. Dan jimmmm tayi kamar me tunani Da sauri yace kuma kinga in anan take zatafi sakewa tayi karatu da kyau .. Shikenan Allah yasa hakan yafi alheri cewar fulani... Maysam da tun dazu take jin duk hirar se wani washe baki take tana mirmushi kasa2 dan akwaita da son ecole Suna haka sega sarki ya aiko kiran Fulani ....nan ta barsu palon cikin su babu me magana ... Fitarta keda wuya ya ce kuwa ke zo nan.d.... Pls fans ku kara hakuri ina gani korafen2 ku Kwana biyun nan ne se a hankali. Ina de barar addu'arku ..... Kuna raina fans love you all😍❤❤ ✍Fasma ce [22/4 09:28] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans❤💋 🅿 29--30 ```Manzon Allah (SAW) ya ce "ya ku mutane ku tuba ga ubangijinku. Na rantse da Allah ni ina tuba ga Allah a rana sau dari " Muslim ne ya rawaito shi``` Fitar Fulani keda wuya yace kuwa da Maysam ke zonan wacce ita har ta kai kofar fita palon ganin fulani ta fita.. Jiki na b'ari ta zo ya durkusa gwiyoyin ta a kasa ta sada kai kasa tace gani Yaya ... K'ara murtuke fuska yayi beyi wata2 ba ya dadage iya karfin shi ya rankasheta a kai yace wannan na hawa cinyar Momy nane ...ya qara mata yace wannan na gaishe nine da kikayi dan nace kada ki sake kimun magana matukar bani na baki izni ba...ya qara mata yace wannan kuma na kallona da kikayi ne.... Ze qara mata da sauri tace dan Allah yaya kayi hakuri bazan qara ba...sega hawaye shar2 Wasu biyu masu shegen zafi ya sake yimata yace wa inan kuwa na jin dadi da kikayine dan za'a sakaki makaranta tare da ban hakuri da kikayi yanzu ya hankad'eta yayi ficewar shi ya barta nan se kwasar kuka take... Ta jima nan taga ba sarki se Allah ta lallashi kanta ta tashi ta shige room tana me ayyana abubuwa da dama... Sarki ma kuwa maganar karatun ce yayi wa Fulani ta ko yi na'am ganin irin farin cikin da Maysam tayi lokacin da yarima ya sanarwa musu yanzu... 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹 A b'angaren Murza kuwa Madina tasa aka yi mata kiranta ...tana dari2 tsoro duk ya cikata ta amsa kiran dan duk a ganin ta wuyyar da tabawa wa Maysam ne za 'a hukuntata Amma me jin irin mugun nufin Madina da waziri akan su Maysam din har bata san lokacin da wata bazawarar dariya ta kufce mata ba ta kuwa gyara zama tana sauraron su daga nan itama ta ta karkace kai ta sanar musu irin yanda take yiwa Maysam har zuwanta wurin boka seda ta sannar musu Madina tayi wani murmushi tace shikenan fad'uwa tazo dede da zama in lokaci tafiyarku kauye yayi zan turo miki da kudi kisa bokanki yayi mini wani aiki.... Murza se wani wangale baki take taji zancen kudi... Haka suka yi ta tsara makircinsu ... Murza jitake kamar ta zuba ruwa a kasa tasha jin za akashe mata Maysam ..sun jima sannan taron makircin ya qare kowa ya kama gaban sa ... Sha biyu na rana dede aka maida su Murza kauyensu cike da murna dan kuwa Madina ta saki mata kudi a zuwan ta kaiwa boka ayi mata aiki akan Marud da Maysam ...zuwansu keda wuya ta kuwa haura hann se wajen boka yankan wuka dayake bata tarar da Malan Musa ba..... Zaune take a gaban bokan se wani hangame baki take tana watsa wasu jan hakoranta...nan ta fad'imi shi yanda suka tsara na akashe su .. Buga kasa da tsubbace2 yayi kamar na wancan lokacin ... Ya dubeta yace wannan yara da taurin kai suke dan kuwa ajalinsu ba anan kusa ba yake abunda zan iya yi muku anan shine kawai rabashi da iyayenshi da matarshi kai dama masarautar baki daya duk da aikin ba karamin aiki bane dan se azubadda da jini ma.. Ko ajikinta Murza tace babu matsala a zubar ko na waye inde bukata zata biya ..nan ta zube mishi rafar kudi wanda ita kanta bata san adadinsu ba a ranta tace nikam kudi be daman ba inde Maysam zata dawama a wahala...se wani murmushi take... Wani magani ya bata cikin wani tsumma yace a turara a wurin da aka san ze ketara ..... Yana ketarawa yanda hayakin yabi iska haka shima in ya bar masarautar baze sake waywayen su ba har se in ku kuka bukaci dawowarshi........ Ta karbe magani ta fito har da yar rawarta ta kama hanyar gida..... ta shigo kauyen cike da murna dede wata kwana ai kuwa wata motar yan kasuwa ta shayo kwanar itama ai kuwa ta kwasheta jikake ragajaf ta zube kasa wanwar... Kuyi manage da wannan 😁😊 Fasma✍ [23/4 00:38] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _🏡Home of spécial &extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Ina maqiyan Murza ku fito wannan page* *din takuce .....ku fito ku kwashi shoki fa ....lol..* 😁😜 *Ban manta dake ba my dear Hadjara* ( *Arfat.)..ina godiya da qaunarki Allah* *ya bar qauna da dankon zumunci...ina yinki sosai ...* *littafinki "AMEMAH " yana wuta🔥gaskiya* *yana fadakardamu da nishadantar damu Allah ya* *qara basira da zakin hannu Fans kada kubari a baku labarin* *littafin Amemah dan gaskiya ya hadu sosai* ❤😍 Dedicated to all my fans ❤💋 🅿 31--32 ```Manzon Allah(SAW) ya ce "wanda duk ya yarda da cewa ALLAH shi ne Ubangiji,ya yarda musulunci shine addini,ya yarda MUHAMMADU(SAW) manzon ne to wannan ya dandani zakin imani " Muslim ne ya rawaito shi``` . Ta shigo kauyen cike da murna dede wata kwana ai kuwa wata motar yan kasuwa ta shayo kwanar itama ai kuwa ta kwasheta ji kake ragajaf ta zube nan kasa wanwar ... Ta kuwa bare baki iya karfinta ta saki wani runtamemen ihu sakamakon wani bala' in zafi da taji a kafafunta ...tuni ta sume dan zafi ..kan kace mi a ka kwasheta akayi likita baban gari dake kusa da su ..amma mi daga nan ma aka turasu babar likita ta birnin Damagaram har lokacin da suka isa bata farfado ba.. Nan likitoci suka bata taimakon gaggawa .....sukayi mata allurar bacci dayake dare yayi daman .. Dreban daya kade ta ne bayan sun koma kauye yaje ya sanarwa da Malam Musa ...be wani daga hankalinshi ba yade ce Allah yabata sauki.. Washe gari wajejen goma na safe ta farka da kadan2 take bude idon ta harta bude su ware ..dan motsa kafafunta tayi aman se taji kamar babu su ..dan danan gabanta ya bada fat .....da sauri ta yunkura zata tashi aman ta kasa ..se kawai ta fara ihu..... Sega infirmieres"likitoci " sun shigo da gudu da kyar suka samu tayi shiru tace miya kawoni nan ne. D'aya daga cikinsu tace ina kyautata zaton Accident ne kukayi wanda ya hadasa miki karaya har biyu a qafar dama se kuma qafar hagun da aka cire miki ita saboda gaba daya kashishuwan wajen sun ratatake babu damar dori dole seda aka cire ta Wani ihun kururuwa da ta saki se da ta firgita su ta dunga ihu da fuzge2 kamar sabon kamu... Wata nurse tace haba baiwar Allah kamata yayi kiyi hakuri kiyi hamdallah daba duka bane aka cire miki ko kuma ma da kika rayu baki maceba Haba ina Murza bata ma san tanayi ba ganin abun bana qarewa bane yasa suka mata allurar bacci tukon suka samu lfy.. Se sha biyu Musa yazo likitar ..nan docteur yayi mishi bayani halin da Murza ke ciki.. Banda girgiza kai babu abunda yake.... Ya na fitowa daga office din doctor direct chambre "daki"da Murza take ya shiga wanda yayi dede da farkawarta ... Ta bare baki zata fara kururuwa yace ke dakata bakida hankaline ?ko baki san nan likita bane da akwai marasa lfy?to walahi kiji da kyau inde kika ci gaba da wannan ihun naki to ina me tabbatar miki gidan Mahaukata zasu kaiki.. Tsit kakeji Murza tayi se wani mazurai take.. Nurse suka shigo duka dan duduba ta suka bata magani tasha ...(su Murza an zama me kafa daya😁😁....) Kafin sati ya zagayo har ta fara jin sauki .... Labari na kaiwa ga Maysam ta kuwa bi ta tada hankalinta ta ringa rokon Fulani ta barta taje ... Da fari Fulani ta kiye mata ganin duka ma yaushe akayi aure harda zata fara futa amma irin addabar tata da tayi setace shikenan jeki tambayo mijinki inhar ya barki sekizo mutafi tare dan ban yarda da Murza ba.. Jin haka yasa Maysam ta bata rai tace haba Momy (haka itama take kiran Fulani yanzu) miye na wani tambayyarshi kawai muyi ta fiyarmu..a zahiri kuwa tsoran zuwa idan yake take.. Fulani tayi dan murmushi tace baki san mace bata futa seda izinin mujinta ba?..duk macen da ta futa bada ixinin mujinta ba to tana cikin tsinuwar malaiku .ne har ta dawo Nan tayi tajan hankalinta.... Maysam tace shikenan bari na tambayoshi to ta fice daga palon Fulani kuwa a ranta ba karamin dadi taji ba ganin yanda Maysam din ta dauketa kamar mahaifiyar ta... Seda taje bangaren nashi tsoro ya kamata nan ta fara wasisin shiga..ta jima nan se kawai tayi shahada ta shiga.. Zaune yake bisa doguwar gujera a palon ya mak'ala ecouteur "earpiece "a kunne se wani karkada kafa yake... Tun lokacin data shigo fitinenen kanshinta ya sanar mishi da zuwanta amma se yayi kamar besan da shigo warta a.. Itama tunda ta shigo kallo daya ta mishi ta kauda kai .. Ta jima nan tsaya tana tsoran yi mishi magana tajawa kanta rankwashi dan bata manta dana waccen ranar ba.. Ta kusa rabin awa tsaye sekuma ta samu waje ta zauna a kasa ta sada kai Ganin haka yasa ya tashi ya zauna yace ke dabbar inace daba zakiyi sallama ba ...kuma ki wani zo kisani gaba bako gaisuwa ke gaki ishashi ko? ... Itade batace komi ba a ranta tace kai wannan mutumun komi zakayi baka yi mishi dede.. Shifa yace kada na sake gaisheshi ..amman yau kuma yana fada akan gaisuwar.. Abunda ya harzukashi menan jin tayi mishi shiru ya ce ke yaki nan na tatakaki.. Maysam da shegen tsoro har kwalla ta cika mata ido ta miki ta fara tafiya kamar hawainiya .. Wata sangamemiyar tsawa ya daka mata. Ai kuwa bata san lokacin daya gurfana a gabanshi ba. Yace.... Sorry fans nida kaina nasan yanxu banayin typing me yawa kuma ina ganin korafe2 ku banaki d'auka bane....de kuna muna uzuri ..am buzy kwana biyun nan ne.. Love you all fans irin sosai din nan 😍❤❤ Fasma✍ [23/4 23:03] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Fans na Sanadin* *Accident ina jin dadi yanda kuke nuna qaunar ku ga littafin nan ** *mussaman yan group din* *MEERAH FANS ZURI'ARMU FANS2* GENTLE LADIES* H FATIMA(A'S)H* *ETC .. *Ina godiya* *hakika ina alfahari daku ina jin dadin yanda kuke bibiyar book dina* *Allah ya bar zumunci* 😁🤝 je vous aime my fans❤😍😍 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿33--34 ```Manzon Allah (SAW) ya ce""Allah ta'ala yana da sunaye casa'in da tara,wato dari badaya,duk wanda ya haddace su, to lallai zai shiga Aljanna " Bukhari da Muslim se suka rawaito shi. ` Wata sangamemiyar tsawa ya daka mata ai kuwa bata san lokacin data gurfana a gaban shiba .. Yace ke wai mi kika d'auki kanki ne??ee..ya kuwa kai mata rankwashi a kai ze qara mata da sauri tace yi hakuri yaya kaifa kace kada na sake yi muka magana in har bakaine ka bada izinin haka..ba.. Wani kallo ya watsa mata yace ohoo😮 kuma shine kika zo kikayi mun kikam kamar wani dogari kin wani zura min ido kamar manya ya kuwa dungure mata kai yace to wai ma miya kawokine? Iye me kama da aljanu Baki na karkarwa muryarta har sarkewa take tace da......ma2 innata ce ba ta da lafiya shine Momy tace nazo na tambayeka zamu tafi ganinta.. Mi kikace???Momy komi ne?? ..ya sake rankwasheta ya kama kunnenta ya murd'e harda ciza leb'e yake dan mugunta seda ta saki d'an kara yace wannan Momy nace ni da sweetbaby na kadai in kika kuskura kika sake kiranta da Momy tooooo yayi kwafa tare da sake mata kunnen .. ....yace kuma ni ina ruwana da fitarki tunda ba d'aureki nayi ba??(umm umm Murad to🙃) Yaja dogon tsaki Mtsssss KE SORS DE MA MAISON VITE2 Qafafunta har hadewa suke wajen sauri ta fice a dakin seda ta fita ta sauke wata nauyenyar ajiyar zuciya tana luliya kunnen a ranta tace shi wanna wai hannunshi baya gajiya da mugunta ne..? Amma de kwanda shi da Murza .. Bayan fitarta ya lula kogin tunani yace kai ya zamo dolema na koma England wajen aikina dan kuwa inde har ina tare da yarinyar nan to kuwa seta saka tsohon ciyona tashi ..ba damar ya tabats se yaji mass shock koda kuwa mugunta ce ze mata da zarar fatar su ta hadu to se yaji..gwara ya tattara yanashi2 ya tafi kafin ta bullo mishi da wani aiki (umm su Murad manya😁😜) tare suka tafi da Fulani lokacin Murza anji jiki duk da taji sauki amma tayi yar rama... Irin yanda ta dinga tarerayar Maysam ke kace ta sadudane ita ko da ga ranta tana ta kisima abubuwa da dama ..dan har yanzu bata bar munmunan qudirinta akan Maysam ba.. Ita kuwa Maysam yarinta me dadi ganin yanda Murza take yimata yasa ta dan saki jikinta se dadi takeji wai yau ga Murza na mata magana me dadi ba hantara harda tafawa.. Itade Fulani kallonsu take amma bata yarda da tuban Murza ba..... Nan kuyangi suka shishigo da kayan marmari da abinci iri2 .. Murza har wani lashe lebe take dan kwadai taga abubuwa.. Basu jima sosai ba Fulani tace su tafi .. Maysam badan tasoba sedan batason yiwa Fulani gaddama.. Tundaga wanna lokacin kusan kullum se Maysam tazo ganin Murza i zuwa yanzu ta saki jikinta sosai da ita...ita kuwa Murza se dariyar mugunta take kasa2..tana fad'in shigo2 ba zurfi shegiya me kama da aljanu..ai sena rabaki da wannan mijin zakisan ni Murza yar bala'i ce( Allah de ya shirya) 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 A bangaren su Madina kuwa Lokacin da sukaji labarin Accident din da Murza tayi waziri ya garzayo a b'oye... Nan ta bashi kullin magani tare da gaya mishi yanda za'ayi dashi...suka kuwa sheke da dariya kamar ba a likita suke ba...nan ya sake zube mata wasu kudin tare da alkawarin zasu na kula da ita a boye har ta warke garau dan suci gaba da cin karen su ba babbaka.. Lokacin da waziri ya kaiwa Madina wannan labari ba karamar mjrna tayi ba harda d'an taka rawa tayi.. Nan suka tsara yanda zasu turara hayakin....waziri yace kinsan shegen nan.akwai shi da son zuwa lambu bayan la'asar ..kinga se a turara a hanyar.. Wani murmushi Fulani tayi tace aikin ka na kyau kaga yanzu karfe biyu kenan nanda awa biyu komi ya kammala...shege inbe mutu ba ma to mu kawar dashi daga masarautar..kaini dama haukatar dashi tasa akayi .. Waziri ya washe wasu hakoranshi yace ai yanzu aka fara mu gama da wannan se musan yanda zamuyi dashi nan gaba... Wajejen uku na rana waziri ya turara hayakin a kofar shiga lambu sannan ya kasa ya tsare ya hana kowa shiga. Ya zauna nan yana gadin wurin Har lokacin isowar yarima murad tareda dogarai da kuyangi ... Shikam waziri ya zube nan yana kwasar gaisuwa tare da zuba mishi kirarin da be kai zuciba... Hannu kawai yarima ya daga mishi ya sa kai ze shiga lambun To fa fans ya kuke ganin zata kaya??asirin nan ze kama Murad kuwa?? Fans ku kara hakuri dani ayukane sukayi mun yawa da zarar komi ya lafamin zaku ringa jina akai2 kuma mai yawa in sha Allah Nice taku har kullum👇 Fasma ce✍ [24/4 22:12] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 35--36 ```Manzon Allah (SAW) ya ce "lallai su malamai magadan sune Annabawa ,sun gadar da ilimi,duk wanda ya same shi ya samu babban rabo " Bukhari ne ya rawaito shi.``` Hannu kawai yarima ya d'aga mishi yasa kai ze shiga lambum... Amma me se kawai yaji kamar a mafarki ana kwala mishi kira seda gabanshi ya bada ras jin wata murya me shige data babysweet dinshi na kiranshi da Yaya da sauri2 cikin zafin nama ya juyo se kawai ya ga yar qauyen nan ce Maysam wani turnikeken bakin ciki yaji ya rufe ya kuwa d'aure fuska tumau ... Cikin sauri dogarai da kuyangi suka zube nan suna Allah ya huci zuciyar ka yarima dan sarki jikan sarki ...blabla dan kuwa ranshi yayi matukar baci Itama Maysam data kula da haka se taki isawa wajenshi ta zube daga inda take tana Allah ya huci zuciyar ka idan ranka ya bace.dama Fulani ce take neman ka yanzu.. Gadan2 ya nufota Ai kuwa tace kafa minaci ban baki ba ta zabga da gudu se bangaren Fulani .... Ranshi in yayi dubu ya bace kamarshi ace an aura mishi wannan yar shilar banda shirme kauyenci yarinta babu abunda ta iya shi walahi yaga ta kanshi banda auren dolen da aka yi mishi a memakon a samu babbar yarinya wacce tasan ciwon kanta koba komi zata iya fidda shi kumya cikin abokanan shi se kawai a aura mishi wannan aba... shifa yanda take gudu kamar ba Gimbiya matar yarima dan sarki ba ...mtss yaja dogon tsaki Harze shiga lambun se kuma ya tuna da tace Momy na nemanshi...se kawai ya juya ya nufi bangaren Fulani fuskar nan ba annuri.. Takaici be gama kasheshi ba seda ya tarar da Maysam tayi daidaya a cinyar Momy se kwasar firarsu suke kamar ba surukai ba ..kwafa yayi tare da zama gaishe da ita kawai yayi ya ci kip... Murmushi Fulani tayi tasan wannan bacin ran har da kishin Maysam data kwanta a cinyar sa..... Maysam kuwa da tun shigowarshi taki ta kalleshi ma bare taga irin mugun kallon dayake watsa mata.. Fulani tace Murad2 Da sauri ya d'ago kanshi yana kallonta Tace ya maganar karatun Maysam ne ??ka b'ullo da zancen kuma kayii shiru gashi har kana shiryen2 tafiya ... Dan sosa kai yayi yace tana nan Momy.. Nasan da haka inaso nasan wacce makarantar ka zab'a mata ne? ? Shifa beyi wannan tunanin ba ....yace Momy nace ba da wai a sakata a makarantar kwana .. Waro ido tayi tace ban gane makarantar kwana ba...kada ma ka tada zancen nan dan me martaba ma baze amince ba.. Maysam ma seda ta tashi ta zauna tana wuwurga ido amma jin abunda Fulani tace yasa tasaki ajiyar zuciya .. Murad ya marerece fuska yace haba Momy miye aibun makarantar kwana kuma fa ta nan kusa wato ta birnin MARADI za a sakata ......idan bata ganinku zata fi zagewa tayi karatu kuma makarantar ta Abba Mahmud ce .. Jim Fulani tayi kamar me tunani Da sauri yace kin kwantar da hankalin ni zan sanarwa da me martaba ... Nan ta dan saki sukaci gaba da hirar su .. Maysam de badan taso ba tade yi shirune kawai.. Yayi tsaye ya faki idon Momy ya zabga ma Maysam mugun kallo yace Momy a bawa yarinyar nan tea takawo min ina b'angare na...kan tace wani abu ya fice abunshi Seda cikinta ya bada kululu jin Fulani tace ta shiga cuisine ta d'ako tea ta kai mishi.. Ita baza ta iya yiwa Fulani gaddama ba bare tace a 'a bazata jeba ..ba yanda ta iya haka ta d'oko ta nufi bangaren gabanta na bada fat2.....a ranta tace yau kuma ko wace muguntar zan tarar duba da irin kallon kad'e dayake mun yau kam seta Allah... Ta jima nan tsaye taga tana b'atawa kanta lokaci se kawai tayi karfin hali ta shiga. .... 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹🌹 A bangaren waziri kuwa ba karamin bakin ciki yaji ba ga maganin duka ya turara wai dan ya kama Murad sosai har kwalla seda yayi saboda takaici Maysam kam ya tsine mata yafi cikin kwando .. Haka ya lallab'a jiki ba karfi ya tafi bangaren Madina wacce take jiranshi tun tuni tana so taji in maganin yaci... Nan ya labarta mata itama jitayi kamar ta mutu dan takaici tace wai wannan wace irin jarabace haka ..amma ba komi ka saci jiki yanzu ka tafi wajen Murza inda akwai ragowar maganin ta baka idan kuma babu to ta kwatanta maka wajen Boka se ka tafi ko zuwa gobe ne.... Nan waziri ya saci jiki se likitar da Murza take ya koyi sa'a Malam Musa baya nan... Murza kam har tafisu shiga damuwa .jin wannan zance ..ta shiga tsine ma Maysam tare da surha mata zagi da kyar . tayi mishi kwatance. wurin Bokan.. ya tafi da yar murnar shi... Je vous aime mes fans ❤❤😍 Fasma✍ [27/4 00:07] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Ban manta dake ba yayata takai na SARAH ina alfahari dake* *Allah ya bar kauna da zumunci ina yinki irin sosai dinnan* 😍❤❤💋 *Up up up STAR .W.A✨ ✍ hakika ina* *alfahari da ku yan kungiyar mu musamman ma* *Antyna Momyn Mufeedah* ..😍 *Hadjara (Arfat)* 💋 *Mimsqueen* ❤ *Ummu Usmane* 😘 *(i miss you keda* 👇) *My in-law Queenbaby* 👸 .. *Allah ya qara hada kammu ina kaunar irin totally dinnan* 😍😘😘. Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 37--38 ```Manzon Allah (SAW) ya ce "ya na daga alamar kyawun musulunci mutum ya bar bin duk wani abun da bai shafe shi ba " Tirmizi ne ya rawaito shi. ``` A bangaren Maysam kuwa tana shiga falon da sallama a bakinta amma setaji shiru wata hamdalah tayi tare dasakin murmushi jin dadin dabata taras dashiba isa dining tayi ta aje mishi tea din sum2 cikin sauri tayi hanyar futa amma mi se taji yace ke zo nan... Dan danan dariyar jin dadin data ke ta gushe ta tsaya cak ta kasa gaba kuma taka sa yin baya ... wata uwar tsawa ya daka mata dan tsoro bata san lokacin data zube nan ba dan kafafuwanta gaza daukar ta sukayi dan ta razana sosai ...da rarafe ta isa inda yake tuni har kwalla ta cika mata ido. Tayi kalar tausayi Se kawai yaga kamar sweetbaby shi idan tayi b'anna wato idan tayi laifi ko kuma idan taji tsoro .... Runtse idon shi yayi wata zuciyar tace ka tausaya mata mana ko dan tana kama da babynka... Wata zuciyar tace mishi a a kada ka raga mata ai dan tana kama da ita ne ma ya kamata ka bata wahala kamar yanda take ba zuciyarka duba da tun da tashigo rayuwarka ta tado maka da ciyon daya dade da warkewa ....beyi wata2 ba yabi umarnin zuciyarshi ya zare belt dinshi ya zula mata daya yace wannan na qara hawa cinyar Momy ne seda ta gantsere saboda zafi. Ya dadage iya karfinshi se qara mata ... Mi Maysam zatayi da gudu ta shige jikin shi ta cukukuye shi Wani mayan shock yaji gaba daya jikinshi ya saki yayi tagal2 suka zube bisa kujerar palon ... Maysam wacce tun dazu idonta ke rumtse se yanzu ta bude su jin sun zube .. Waro idon tayi ta kama bakinta ... Shi kuma gogan sandarewa yayi sakin baki da hanci yayi ya zuba mata ido bako kiftawa itama Maysam din kasa janye idanunta tayi dan ta tsorata jiran hukunci kawai take Sun jima a haka ita tana son tserewa amma gogan ya kasa ya tsare ya riketa da hannushi ...kuma ya fada kogin tunani..... Mutsu2 da take ya dawo dashi da sauri ya tureta taee da hankada ta lokaci guda kuma ya daka mata tsawa ta fice mishi a daki .. Gaba daya ya gigita ta ..tama rasa ina ne kofar fitar seda taga ya taso ya nufo ta cikin tsawa yake fadin "je dis sors de ma maison " da gudu ta fice kan kace mi har ta isa bangaren Fulani se haki take ..nan kofar palon ta tsaya tana meda numpashi seda taji normal tukon ta shiga "heureusement"(luckily) Fulani bata palon direct room din ta tashige a ranta tayi hamdalah da Allah ya kubutar da ita a hannunshi da taci na jaki yau ta shafa bayanta tace nasan kila da ya qara min wata da bayan nan ya gama moruwa..... A bangarenshi kuwa rasa abunda yake mishi dadi yayi kwata2 yarinyar nan ta haddasa mishi fadawa tunanin babynshi a ranshi yace kai dolema na kaita school gobe2 nan ko zanma dena ganinta kwata2...yaja dogon tsaki mtssss Washe garin kuwa suka kama hanyar Maradin dayake tun a daren ya sanarwa Fulani da me martaba a cewarshi wai an tsere mata a karatun dan haka gwara ta tafi kota cin munsu Tun adaren tashirya kayanta tsaf akwati ukku manya komi na bukata ta dauka wanda kuwa bata da se gobe yarima ya kaita shopping . A shopping dinma tsayawa tayi bata dauki komi ba seda taga Murad yayi mata jan ido tukon ta dauki mai da turaruka shima bawai dan batada suba aa kawai dande tsoran fadan yarima Shikuma wurin kayan ci ya tafi yasa yaran wurin suna jidowa kamar madara lipton Milo etc...komi a wadace ya saye dan Momy seda tayi mishi kashe kwakwara kafin su fito Haka ya biya kudin aka jida musu a motar da kuyangi duke suka fice se Maradi. Yana tuki a ranshi yace ya akayi bega yarinyar nan ta dauki pad..wata zuciyar tace mishi peut etre (may be) bata faraba ma..yace amma walahi angama dani (jifa to mi ruwanka ciki kawai iyayi😜) Juyowa yayi yana kallonta ..ita kam se sharara bacci take ..besan lokacin dayace bacci nayi miki kyau...se kuma yace to mi ruwana ciki..tsuka yaja ya cigaba da tukinshi...(kadeji da gulmarka ehe) Tafiyar awa ukku sukayi suka iso wani shago ya shiga ya sayo mata simkin pad din gabad'aya... Har llokacin bata farka ba.. Wani haushin ta ya karaji Tana baccita me dadi cike da mafarkai masu dadi taji saukar ruwan sanyi a fuskarta firgit ta bude ido kamar zatayi kuka amma ganin dodonta ne seta sadda kanta kasa.. Suna isa makarantar dayake abun na sune nan aka cicika komi ya zuba kudin shekarun shidda dazatayi wato secondary da kudin furniture dana uniform duka komi ya biya Har dakinta kuyangi sukakai mata kayanta ......daza su tafi da kyar suka rabu da kuyangin...barema da jakadiya rumgume ta tayi se rusa kuka take... Lallashin ta tayi tace kiyi hakuri naso zama nan kai hatta fulani taso a baki koda kuyanga dayane amma yarima yace aa a barki ai school kikazo ba hutu ba .shiyasa nakeso kidage kiyi karatunki banda wasa..kada kiyi kuka kijawa kanki ciwon kai dama gana safe dakikayi wajen rabuwa da fulani... Share hawayenta tayi tace shikenan zan baku mamaki in sha Allah .. Yarima murad seda ya biya gidansu Mahmud ya gaisar da iyayenshi sannan suka kama hanyar komawa 🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 A bangaren su waziri kuwa samako yayi ya nufi wurin boka amma har yamma be samu wajen ba ya gaji likis dole ya hakura ya dawo gida Ya labartawa Madina komi wani bacin rai taji tace mu bari har murza taji dan sauki se muje ta nuna muna amma kada ya fice satin nan dan asabar din nan ze koma England nan da 6 jours kenan...... Kuma wani babban bakin ciki yau yayi tafiya shida kucakar matarshi abunda ya kullar dani ma shine da kanshi ya jasu ashe dana sani da munyi anfani da wanna damar mu qara cire musu burki.. bansan da tafiyar ba seda zasu tafi shima a bakin jakadiyata naji koda na fito tuni har sun bar cikin fadar ..takaici kamar na mutu... Waziri ya jinjina kai yace ba komi zamuyi nasara nan gaba.. Love all fans😍❤ ce✍ Fasma [28/4 23:10] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 39--40 ```Manzon Allah (SAW) ya ce "Duk wanda yake so a bashi tsawon rai,a kara masa yalwar arziki,to yabi iyayensa kuma ya sadar da zumuntarsa " Imamu Ahmad ne ya rawaito shi.``` Waziri ya jinjina kai yace ba komi zamuyi nasara nan gaba..... Madina tace Allah ya kasan yaron ne taurin rai ne dashi (Hum to lokacin mutum beyi ba taya ze mutu inba jahilci ba irin naki😏hum) 🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 Maysam kam koda akayi mata interview se suka sakata a js2 a memakon js1 dayake Allah yayi ta brain ..basuba ni kaina taban mamaki amma wannan kadan ne daga ciki baiwar da Allah yake bawa tsirakun mutane... Dakin da aka kaita gado ukku ne a ranta tace kenan mu ukku ne a dakin nan kodan kayan dataga kusa da gadajen ya tambbatar mata da hakan... Nan ta zaune ta rafka tagumi tana tunanin rayuwarta .....tace ko yanzu Abbana miyake??ko yaci abinci??ko ya tafi kasuwa ...i miss you Abbana..... Se kuma tace Allah sarki inna Murza ko ya jikinta yanzu ??? Sekuma ta tsallako tunanin Fulani ai kuwa nan shar3 hawaye ya fara zarya a kumatun ta tace har na fara kewarki Momyna hakika kin cancaci yabo baki sanin ba amma kika sani a jikin ki har kika auran danki kwaya tal ..kin nunamin so, kauna inasonki sosai fulani Allah meyin yanda ya so *Sanadin Accident* na samu Momy na fita daga kangin wuyar Murza ....Allah ya saka miki da alheri...tana haka se kuma tunanin yarima Murad ya fado mata tace shin ko ya isa gida yanzu? ??ko ya ci abinci??ko miyake yanzu se kuma ta saki murmushi wanda ni kaina bansan ma anarshi ba .....se kuma naga ta tsuke fuska tace mi nawa nayin tunanin shi mtss banda mugunta da keta mi ya iya da wata fuskarshi me kyau ......yana wata tafiyar shi ta takama kodayake yarima ne dole yayi .........haka ta lalace tana ta tunanin ta data tuno wannan se ta tuno wacan.. Dafa tan da akayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunani ..... Firgit ta juyo taga waye... Wasu yan mata biyu ne baza su fuce sa aninta ba .. Wanda ta dafa ta ta sakar mata murmushi tace ya haka kedaya kuma kina tunani Itade da ido ta bisu Tace ""je suis Mariam Moctar ... D'ayar ma tace nikuma Mufeedah Muhammad ......kefa? ?? Suka fadi a tare jin bata ce musu kala ba Tace nikuma Maysam Musa by name.. Wani aji kike cewar Mufeedah ... Js2 ta fada a takaice... Waro ido sukayi a tare sukace ashe ma ajin mu daya ....sekuma suka shiga murna Nan sukayi dan sabo har suka qara gaya mata sharrudan makarantar da yanda suke gudanar da karatun daga takwas na safe zuwa daya na rana school ne daga ukku zuwa shida na yamma islamiyya ne..... Haka kuwa akayi ukku nayi suka saka uniform na islamiyya suka fuce harda Maysam din dayake kama daga furniture, uniform duka a school din ake baka.... 🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 A bangaren oga kuwa bayan ya koma gida gaba daya ya tsinci kanshi cikin kunci ..besan ya akayi ba amma kwata2 a ranar be runtsa bacci ba ya na rufe idanu se kawai yaga fuskar Maysam ..shi kade se juyi yake yana tuna scene dinsu na jiya ..yaja tsaki yafi cikin kwando ..ranar kam se barawan bacci ne ya saceshi abunda ya jima beyi ba kenan tunanin wani abu ya hanashi bacci shiyasa tsanar Maysam ta dada ruruwa a zuciyar shi... A bangaren Fulani ma se taga yau gidan yayi mata fadi da babu Maysam dukda basu wani jima tare ba kuma ga kuyangi dasu na debe mata kewa amma Maysam ta daban ce a wajenta.. Washe gari kam sukuku Murad ya tashi har seda Fulani ta tambayeshi ko lfynshi amma se ya fake da kanshi yake mishi dan ciwo..(hohho su Murad manya) Maysam kam cike da zumudi ta tashi tun wuri tayi shirin ta na school uniform din ba karamar karbarta yayiba rigace har guiwa da wando har kasa ruwan toka se dan baby hidjab fari tas ..nan ta fara bubude kayayakinta ..dan ta samu ta karya ..ita kanta ta yaba da sayayyar da Murad yayi mata dan kanyan sunyi yawa ma a cewarta .....can ta hango katan abu ta janyo shi taga an rubuta Pad sanitary .....ta dinga jujuyashi a ranta tace komiye wannan kuma oho ..haka ta mishi wuri ta aje sanna ta jere kayanta tsaf cikin wardrobe dayake ba wani girma ne dashi ba dan kahaka sauran kayan ta bardu nan cikin bags... Haka suka nufi aji su ukku bayan an tashi lokacin islamiyya nayi suka tafi tare kafin dare Maysam ta gaji likiis mi su Mariam zayi inba dariya Mufeedah tace zaki saba muma da farko haka mukaji... Bayan kwana biyu Maysam karatu ya fara zafi karatu take ainun basuda time idan ka gansu suna fira to lokacin baccine amman a yinin rana in basa aji to suna blibliotheque (library) ko kuma suna exercise itada su Mufeedah ...takan tuna Abbata da Fulani lokaci zuwa lokaci dan yanxu batada ma times din tunanin Yarima kuwa besan ganin dayake mata yana mata mugunta kad'e ma wata rahamace a zuciyarshi tun bayan tafiyar Maysam ciwon zuciyarshi yake famar tashi ..dole ya fara shirin koma wa England dan ganin doc dinshi a cewarshi gwara ya tafi tun kafin abun yayi nisa..hum😏 Ai kuwa su Madina najin tafiyar Murad ta tashi haka aka d'auki Murza da kafar karyaya aka nufi wurin boka da ita dad'insu d'aya Malan Musa ya tafi kauyensu d'auko musu wasu yan abubuwa se kawai sukayi anfani da damar suka kad'a han sewajen Boka yankan wuka🔪... To fa fans Kuyi hakuri da wannan ina sonku fans ❤❤❤ Fasma✍ [30/4 23:38] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ *Sede kash my fans dan ayau nake sa ran tsayar da wannan littafin saboda kusantarwar azumi ga kuma littafin da sauranshi ....ku kasance dani bayan Ramadan in sha Allah ...ku rike da kyau daga page 41--42 muka tsaya ...ina sonku fans dina irin totaly dinnan* ❤❤ 🅿 41--42 ```Manzon Allah (SAW) ya ce " Zaka sami mafi lalacewar mutane a ranar kiyama mutum mai fuska biyu, wato wanda yake zuwa wajen wadannan da fuska, kuma ya zowa wadannan da wata fuskar " Muslim ne ya rawaito shi. ``` Zaune suke Murza da Waziri gaban boka yanka wuka bayan sun zayyana mishi irin rashin sa ar da sukayi sannan suka bukaci da a sake basu wani wanda ya fi wanca dan waziri seda ya nemi a salwantar mishi da rayuwar Murad da Matar shi Maysam .. Boka ya sake jaddada musu rashin yuyuwar hakan tukon suka amshi irin na farkon ... Waziri yace in san samu ne kai koda yana kasar to ya qauracewa garin nan de har lokcin da time dim mutuwar shi yazo se kawai mu salwantar da ran nashi... Bokan ya basu maganin amma da sharadin insuka sake maganin nan me kamashi ba baze sake basu wani irinshi ba tunda sakakin su yayi yawa ..kuma ma ko.wancan lokacin da kyar suka samu ran da sukayi sacrifice dashi kuma ga wani ran mutum biyu yanzu da aljanin da ze muku aiiki zai asha ...... Waziri har wani shoki yake kwasa jin za amusu aikin da yarima ze bar masarautar ..makkudan kudi suka zube mishi shikuma la' anannan Allah ya basu maganin tare dayi mudu bayani kamar na wancan lokacin .... Cike da nishadi suka dawo gida inda aka dawo da Murza likita. Ta kalli waziri tace wani hanzari ba gudu idan shi yarima Murad ya bar kasar ya za'ayi da iya maysam din dan ganin tabar masarautar nan?? Wata dariya waziri yayi yace yo inba abinki ba ai da zarar ya tafi ya jima to ina kyautata zaton dole a raba auren tunda ba miji kinga seta kuma wurinki ko?? Ee fa hakane kai amma naji dadi haka sukayi ta saka warwarsu .Allah yasota dan har lokacin Musa be dawoba.. 🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 ' Murad kam abun duniya sun taru sunyi mishi yawa besan haka zuciyarshi take son ganin yarinyarnan ba da be turata makarantar nan ba gashi yanzu lokaci ya kure mishi ....dan haka se ya samu Mahmud da zancan amma ya boye mishi cewa rashin Maysam ne kawai ya fadimishi yana son komawa dan ciwanshi yana famar tashi sosai Mahmud ya tausaya wa abokin nashi yace amma ya akayi hakan ta faru bayan ka jima bakayi shiba har muna tammahanin ka rabu dashi?? Girgiza kai Murad yayi yace nikai na bansan ya akayi ba Kode yana da nasaba da aurenka Mahmud ya sake jefo mishi tambaya Seda gabanshi ya tsinke amma se mazge Nan ma yace aa Shikenan Allah ya sauwake amma yaushe ne tafiyan naka?? Gobe nakeson ficewa har na ciri ticket ammafa ko su me martaba ban sanar musu ba... Tab kanada aiki kaida Fulani yau kenan ,ka sani sarai batason zammanka acan dande kawai ba yanda ta iyane amma shine se ana gobe tafiyar zaka sanar mata. ...... Kaide bari aboki ni kaina tsoro ne yahanani fada amma zansan yanda zan bullo mata... Duna gama hirar ya nufi bangaren Fulani cike da zullumi ... Tana waya ya tadda ita koda ya kashe kunne se ya gane da Maysam take wayar kuma da alama kuka take Fulani na aikin lallashi... Tuni yaji ba dadi jikinshi ya sanyi shikam duk wani zafin ranshi da nuna shariyarshi akan abu baya iyayi akan abunda ya shafeta .. So tari beson don meyasa yakeson yi mata muguntar ma akan abunda be kai ya kawo ba ..da wanine kowata da tuni ya bada umarni an horar dashi ...... Karbar wayar yayi daga hannun Fulani ya kara a kunnenshi ... Kukan shagwaba kawai Maysam ke xubawa ita ta gaji tayi kewarsu iya gaskiya a medota gida... Kiran sunanta kade yayi yasa tayi tsit kamar ruwa ya cinyeta dan tagane me maganar .. Shiru ya biyo baya can yace waike wace irice baki iya gaisuwa bane mtsss yayi tsuka A memakon ta gaisheshi setace to ai baka bani umarnin magana bane.. Kut ya fada ni kike fadawa haka?? Shiru ta sake yi mishi A bunda ya kular dashi yaceto wly kiji da kyau keda dawowa gida se nan da shekara idan kunyi hutun karshe banyarda kidawo ba ehe ..kuma wly kika sake kika ki yin karatun yanda ya dace ummm ni kade nasa irin horan da zan baki dan bazanyi asarar kudi ba ke inbaki zo ta daya ba wly kada ma kisake ki dawo gidan nan kiyi zamaki can .. ... Mi Maysam zatayi inba kuka ba. Sosai ta cika mishi kunne da taratsi harseda ya kauda wayar daga kunnenshi ... Yana medawa kuwa ya zunkud'amata wata xungureriyar tsawa yace "Ferme moi ta bouche idiote" kawai a kanki aka fara school ne da zaki damu mutane ...dama shi tallak..... Da sauri Fulani ta wabce wayar ta shiga lallashi ganin ze baro mata aiki da kyar ta lallabata ta kashe wayar .. Ta kalleshi da niyar balbaleshi da fada amma ganin idon har sun kada sunyi ja saboda bacin rai yasa tasoma yi mishi nasiha da yayi hakuri da duniya wannan yawan fushin nashi baze kareshi da komi ba ...tace shin wai kai baka tawwakali ne ..??baka karban kaddara ne?? Da sauri ya dago kai yace inayi mana Momy.. Bana tunanin haka Dan da kanayi da kayi da dadewa...shekara nawa da rasuwarta amma ka kasa sakin ranka kayi rayuwarka yanda ya kamata ...addu arka take bukata amma bawai da dauki bakin hali ka saka a ranka ba.... A da bahaka kakeba kowa yana yabon halinka jama a na sonka dan kyautata musu da kakeyi amma yanzu gaba daya ka cusa musu tsoranka a xukatansu ....ma aikatan gidan nan kama daga bayi dogarai kowa yana tsoran hada hanya dakai...dan gudun horan ka me tsanani ..shin a haka kake ganin wata rana jama a zasu soka a matsayin sarkinsu... Ka canza halinka ka dawo yanda kake kamarda... Wani kukane yakubce mishi yakuwa zube kasa tare da daura kanshi bisa cinyarta ya dafe Dede saitin zuciyarshi yana fadin ki yafeni Momy ni kaina na kasa sarrafa zuciyana ne amma zanyi kokari ki tayani da addu a...zuciyar shi har wani zogi take mishi Farin ciki fal zuciyarta Ta shafa kanshi tace Allah ya shige mana gaba Ameen ya furta Ya jima haka sannan ya fara sauke ajiyar zuciya akai2 har ya dawo nml Nan ya sanarwa Fulani zancen tafiyarshi gobe..amma gamamakinshi se yaga bata nuna damuwar ta ba se nasiha data qara yi mishi ta dora dacewa yanzu de kai magidan ci ne dan haka zancen ka tafi kayi zamanka kamarda se lokacin dakoso zowa ma be taso ba .. haka suka yi ta hirarsu har lokacin sallar magarib yayi ya fice.. A bangaren Maysam kuwa ba karamin kuka tayi ba jin muryar fulani datayi se kuma gigan nata ya fado mata a rai nan ta lalaci cikin gogin tunanin shi...can kuma tayi kwafa kamar yana gabanta tace kadeji dashi mutum bashida aiki se zallar mugunta.haka tayi ta tunanin shi Wajejen goma na dare ya shiga wajen memartaba sanin adede wannan lokaci to babu kowa a fadar daga sarki se matanshi dan wannan lokacin iyalanshine Su biyu kawai ya tarar daga sarki se Madina ..zama yayi ya kwashi gaisuwa sannan ya sanar musu tafiyarshi sarki ya mishi fatan alheri tare da nasiha.." Madina ma cike da iya bariki take mishi nasiha wai annan itama ta iya makirci...amma idan zaka bude xuciyar farin ciki ne fal har shokyn dadi zuciyar keyi lol.. Nan yayi musu sallama ya fice... Zo kaga murna wajen Madina har ta kagu tabar wajen me martabar se kawai ta sulale se dariyar mugunta take.. Haka kuwa akayi seda suka bari dare ya raba waziri yayi turaren a dede kofar dakin Murad bayan sun tabbatar dayana ciki a cewar su yana fitowa se bin duniya... A bangaren Murad kuwa bayan yayi komi na al adarshi kamar yanda yasaba se hau gado amma me tunanin Maysam ya gama cika mishi zuciya daya rutse ido ze dinga jin kukanta na dazu..banda juyi babu abunda yake tsaki kam da ina kirgawa da rubutawa da nayi read more 3 lol.. Ganin babu bacci a idanunshi yasa ya doro alwala ya dinga jero nafilfili ...se wajejen 3 da rabi barawo ya saceshi wanda ya haddasa mishi makarar sallar asuba ..se karfe shida ya bude idonshi da gudu ya fada tolet yayi wanka tare da doro alwala yayi sallah..dayake tara jirginsu ze daga se ya fara shirye2n shi..7 da rabi ya gama tsaf ya jawo jakar kayanshi ya fito ... Yana ketara kofar dakin wata irin juya ta kwasheshi kan kace mi har ya kai kasa....ga wani irin ciwan kai daya far me da sauri ya fara ambaton sunan Allah kadan2 ciwon ya lafa komiya dawo nml amma me gaba daya yaji garin ya fice me a rai burinshi kawai yaji a wani gari ko wata kasa.. Da sauri yana kayanshi ya fice atsetse yayiwa Fulani bankwana a cewarshi yayi latti kada ya rasa jirgin A jikinta takeji kamar kar ya tafi..kamar ta hanashi tafiyar nan Yana shiga mota driver yaja suka fice a masarautar Madina da waziri dasuke tsaye suna kallon komi da alamade maganu yaci dan waziri ya ga har sanda ya tsallaka da yanda juya ta kwasheshi Madina ta shiga waka kamar haka Mun rabu dakai..... Mun yi nisa da kai abadan damu dakai se a lahira💃 Waziri yace wanna haka yake.... Nima bari nayi nan🏃‍♀ tunda de Murad ma ya tafi ya barmu.. 😭 Wasa soman tabi Kukasance da ni my fans bayan RAMADAN IN SHA ALLAH. Ina bala'in sonku irin dayawan nan ..❤💋😍.... Ina neman afuwarku wanda nayi wa laifi ina sane ko cikin rashi sani ya yafen ni na yafewa kowa ..se mun hadu bayan sallah.. HAPPY RAMADAN ALL. HEUREUX RAMADAN A TOUS FASMA CE✍ [22/6 17:40] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 **Dubun gaisuwa zuwa ga fans din wannan littafi hakika ina alfahari da ku da irin so da.kauna da kuke nunan .......* **Daya wa daga cikin ku naga sakon nin ku in sha Allah zakuga* *canji....ina love dinku irin totaly and completly din nan lol* ~Goron barka da sallah~ Inama kowa barka da sallah da fatan duk kunyi sallah lfy to Allah ya maimaita mana ..ya karb'i ibadun mu yasa munyi a dede ..Bonne fête du Ramadan a tous💋🌹 _Ina ma abota Son karanta novels masu ma'ana ,fad'akarwa nishada'ntar wa ,etc ...ina me farin ciki gaiyatar ku da ku biyo writers na kungiyar_ *STAR WRITER' ASS* ... _mun sake fito muku da news novels kamar su_ *NIDA KAWATA &UWAR RUKO part2* _na Momyn Mufeeda_ 😍, _Da kuma_ *KALAR TAWA UWAR & KARSHEN ALEWA KASA* _na Mimsqueen_ 💋 _Ga kuma_ *MEERAH* _na in law dina Xaynab(queenbaby👸)_ *AMEEMAH &DAJIN SOYYAYA* __na Hadjara (Arfat ba😘)_ _Se kuma_ *SALMAH* _na Usman(miss you a lot❣)_ __Fans Kada ku bari a baku labari dan gaskiya novels din sun had'u masu_ _iya magana sukace da abaka labari gwanda ka bada......._ *Ina alfahari da ku yan kungiyar Stars W.A...Allah ya kara hada kanmu irin éternity din nan_ 😁💞* _Je vous ai pas oubliées mes sis d'amour Maman Haneep..Maman Shurem...Zainab.Sarah...,Ramatou_ _and my namesake Fatima municipale... Ina kaunar ku irin sosai din nan..Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa.dama wa dinda ma ba ambata ba kuna raina_ Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 43__44 ``` Manzon Allah (SAW ) ya ce :''me yanke zumunta baya shiga Aljanna '' Bukhari ya rawaito shi ``` Yana shiga motar driver yaja suka fice daga masarauta direct aéroport (hilin jirgi)suka tafi zuwan shi keda wuya jirgin su ya daga kamar daman shi kade ake jira...Mahmud ma tsetseye sukayi sallama dashi anan har yake tambayarshi ko se yaushe ze dawo amma budar bakin shi ya ce ba rana ...... .. 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹 Madina da waziri da suke tsaye suna kallon komi da alama de maganin su ya ci dan waziri yaga har lokacin da Murad ya tsalaka da yanda juya ta kwasheshi... Madina ta kwashe da wata arniyar dariya ta shiga waka kamar haka mun rabu dakai... Munyi nisa dakai Abadan damun dakai se a lahira💃 Waziri yayi dariya yace wannan haka yake ...saura shegiyar figigiyar matarshi... Madina tace barni da karamar kwari wannan ai karamin aiki ne.... Rayuwa juyi2 yaude rayuwa ta juyo gare mu sauran kuma ogan ..shima ya kamata a fara planning din yanda za ayi mu kaudashii.fadar waziri..kenan Madina tayi yar dariya tace wannan ma barshi a hannuna lokaci kawai nake jira.....kaide ka zamo kullum cikin shiriii.. Ba damuwa ai ni akowani lokaci a shirye na ke ..keni ko yanzu hakama... Shikenan da zarar na shirya komi zakaji ni. ... Nan waziri ya daga waya ya kirayi Murza ya sanar mata ... Murza dake gadon asibiti tuni farin ciki ya cikata har bata san lokacin da wata makirar dariya ta subce mata wanda yayi Sanadin tashi M.Musa daga bacci ..ya kalleta ya girgiza kai .....Itamade kashe wayar tayi tare da yin kwafa A ranta kuwa fadi take dadi kasheni ..Maysam wannan karan sena zamo ajalin ki..(kuji fa🙄.) A bangaren fulani kuwa da sauri ta daga waya a nufin ta kirayi Murad kan ya fasa tafiyar amma ina baa ta shiga tayi kiran yafi a kirga dole ta hakura ta bishi da addu'a... Shikuwa Murad gaba daya ya rasa abunda yake mishi dadi nan ya jingina da kujerar jirgin ai kuwa se bacci yayi awon gaba dashi... Be farka ba seda suka isa birnin ENGLAND..shi kanshi yayi mamakin wannan bacci da yayi kuma ga wani irin ciwo da kanshi yake yi ..hakade ya lallab'a ya shiga taxi ya na isa gida yanemi magani yasha kuma wani sabon bacci ya sake daukeshi ...wunin ranar de a bacci ya kareshi ganin abun bana karewa bane yasa ya daga waya ya kirayi wani abokin aikinshi me sunan MARK kuma daman shike kula dashi idan ciwon zuciyan shi ya tashi..... Be wani dauki lokaci ba yazo tare da kayen aikin shi...yayi yan gwaje 2 shi .....can ya bashi maganun nuka ya sha .....ya kaleshi yace haba Murad kamar ba Docteur ba zaka bari ciwon ka ya tashi har haka koma ka sani sare irin conséquence din daze biyo baya in har ba'yi intervenir da gagawa ba.....idan ma wani abun ne yayi Sanadin tashinshi to ina baka shawarar idan akwai yuyuwar ka mallakeshi to kayi gaggawa inko ba hakaba ka dangana dashi amma fa zakasha wuya ko kuma ma yayi sanadiyar zama ajalinka... Murad yayi karfin halin yin dariya yace bazaka gane ba ..tunda de yanzu ganinan ai se kayi abunda ya dace.. A ranshi yace abun dama mallaki nane kawai de bazan so naci amanar my sweetbabyna ba(🙄kaide kasani iya kacinta de in lokacinka yayi ka mutu mu kuma musha gumba da nono atoo....,😎.) Ya rurubuta mishi magani .sanan yace tode a iya bincike na baccika bashida nasaba da ciwonka mayebe gajiyace ....daga nan ya mishi sallama akan ze tafi siyo maganin da kuma dan abinci dazeci Gyada kanshi yayi tare da mishi godiya ........ Washe gari kam ras ya tashi har ya tafi wurin aikin shi sede zuciyarshi bata dena yime zogi ba ..aiki ya tarar ba kadan ba.yinin ranar kaf a aiki yayishi se gab da magrib yakoma gida ...bayan yayi isha'i ya dauko wayarshi se alokacin ya ganta ashe a kashe take...yana kuwa kunnawa kiran fulani ya shigo .. Da sauri ya daga ya gaïda ta tare da jero mata ban hakuri .. Daga can fulani tayi dariya tace shikenan ya huce da fatan ka isa lafiya ... Nan suka dan taba hira tace wai ni shi ko ka sanar da Maysam tafiyarka ? Seda gabanshi ya fadi shi sunan ta kade ma in yaji se gabanshi ya fadi bare yaji muryarta ko kuma ya ganta...gaba daya se yaga kamar yar kanwarshi ya daure de yace to ai Momy batada waya .. Amma kasan baka kyauta ba ko ko batada waya ai seka biya ta Maradin kayi mata bankwana ko..to yanzu de ba wanan ba ka kirayi offishin makarantar sesu bata .. To kawai yace amma fa badan ze kira din ba....nan tayi mishi sallama tare da jaddada mishi ya kirayi Maysam din..kuma zata kira taji ko yayi .... Yayi kicin'2 da fuska shifa gani yake Momy ta takura mishi .... babu yanda ya iya bayan ya kirayi Mai martaba hakade ya kirayi makarantar dayake sun sanshi farin sani koda ya basu sani ya nemi zeyi magana da Maysam ba a wani bata lokaci ba aka kirata.... Tana ansar wayar bata tsaya taji me kiran ba tace ina wuni Momy ya gida? ya.. ....cak ya tseda ita yace ke wai bakida hankali ne bakiji me kiraba kawai ki kama zuba zance yaja tsuka..mtssss... Shiru tayi can tace kayi hakuri ban san kaine ba..ina wuni.. Se kuma jikinshi yayi sanyi yace lafiya ....yace da fatan de kina karatu dan walahi kinji na rantse idan har baki zo ta daya ba to kada ki kuskura ki dawo gida hutu ... Tace to..a ranta kuma tace daga kira se masifa Yace kuma badan kinga na koma ba kice zakiyi abunda kikaga dama zansa a dinga fadamin duk wani motsinki da kamaki da laifi daya sekin raina kanki Nan ma tace to(a ranta tace kenan ma baya kasar tayi kwafa) Nan de yayita banbaminshi Ita kuma komi se tace to ... Ya kari fadace2n shi ya kashe wayar ... Maysam ta koma aji amma tunanin fadan Murad ne fal ranta ....tace waishi baya gajiya da yiwa mutum fada ne ....komi shi se yayi fada da mugunta ciki........tana shiga aji ta tatara komi ta watsar tacigaba da karatun ta..... A bangaren Murad kuwa yana kashe wayar ya dafe zuciyarshi da hannu saboda wani irin zogi da take mishi ...ya daga waya ya kirayi docteur Mark tun yana daukan abun wasa har ya fara ganin dishi2 .kan kace mi tuni ya zube nan kasa .........Mark na shigowa ya tarar da shi cikin wannan halin dataimakon wani abokin aikinshi dayake su biyu sukazo...suka ciccibe shi sukasa a mota suka nufi hospital dashi ...kafin su isa tuni ya sume...direct emergency aka shiga dashi....... Ta fa fans muje zuwade.... Nikuwa nace amma su waziri sunyi aikin banza da suka tsaya a barin masarauta da ai se susa a shiga tsakaninshi da har mazauna a cikin masarautar tundade gashi ya bar garin amma kuma ya ci gaba da mu'amalal shi da parents dinshi..amma a ganina fa🙃🤔 Fasma ce🖊 [24/6 14:57] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 45__46 ```Manzon Allah (SAW)ya ce''duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce'' Muslim ne ya rawaito shi ``` Kafin su isa tuni har ya sume ...direct emercency a ka shi ga dashi .. Nan docteurs suka duqufa dan ceto rayuwarshi a bunka da turai kayan aiki birjik dan haka kan kace mi cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo normal ....amma fa idanun sa a rufe da alama bacci yake.....Be farka ba seda ya kwana yayi rabin wuni har wata rama yayi ta kwana daya .......Mark na zaune kusa da shi da yake shi ke jinyarshi ya ga bakin shi ya na dan motsawa kamar me sonyi magana ga kuma idon shi a rufe suke... Kusanto kunnenshi yayi dede bakin se yaji Murad na ambatan sunan Maysam.... Maysam... Cike da mamaki Mark ya dago kai yana kallon Murad dake kwance yace Maysam?to ko..... Kafin ya gama tunanin Murad ya fara bude idanunshi Tar ya bude shi se akan Mark ..yayi karfin halin yin dariya .. Mark ya kamashi ya kaishi tolet yayi wanka tare da doro alwala ..........yana zuwa ya saka jallabiya ya kabarta sallolin da ake binshi bayan ya gama Mark ya gabatar mishi da abinci ....kadan yaci shima dan ya samu ya kama karfin jikinshi .... yana tsakada ci . Mark ya kalleshi ya ce .....waccece Maysam ??? Tambayar a bazata tazo mishi dan kuwa har seda ya kware ..... Mark ya tsiyayi ruwa yabashi Da tarin ya lafa yace Maysam kuma ....''.non je ne la connaît pas ''...(ka ban santa ba) Mark yayi dariyar gefen baki yace shikenan idan baka santa ba amma ka sani sunan dakayi ta kira kenan ...... Ya mutsa fuska yayi yace nide ban santa ba ..ya kauda fuskar shi... Mark yace bazan tambayeka abunda ya tado maka ciwon ba amma abunda zance maka kayi gaggawar mallakar ko hakura dashi dan kuwa idan ka bari zuciyar ka ta sake bugawa kamar yanda tayi jiya tofa the best solution se amma ka opération kuma kasan irin ''risque''(hatsari) din dake cikin opération.... Gyad'a kai kawai yayi amma badan ze iyaba dan ko yanzu dayaji sunna ta seda yaji wani zogi a zuciyar shi ....shi yasa tsanar yarinyar yake kara yawa a zuciyarshi....... kwanan shi ukku aka sake shi ya dawo gida ....ran na hudun ma ya koma aikin shi duk duk dade be wani kama karfin jikinji kamar da ba... 🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹 .Abangaren Maysam kuwa karatu take ka'in da na'in ba kama hannu yaro ......dayake kuma ta hadu da masu son karatu Mufeedah da Mariyam ga kuma ilimi ..duk inda bata fahim ta ba suke ganar da ita daya ke su sunyi jss1 ..a duk inda ka gansu to fa zaka tarar suna biya karatun sune na bako ko na arabi........ Akulum kuma Maysam idan ta tuna cewa SANADIN ACCIDENT ne had'uwar su da Fulani har ta samu gatan zuwa école ga islamiyya taci me kyau ta sha me kyau sannan ta saka me kyau ga soyyayar uwa da Fulani ke nuna mata ...se kwai ta fashe da kuka tare yi wa Allah godiya .su Mufeedah de se suyi ta bata baki da hakuri dan su ji suke idan ta tuna rabuwa da yan gida ne take kukan......... Haka de rayuwa tayi ta tafiya yau da dadi gobe akasin haka inda yau har su Maysam suke zana exam na karshen shekara wato pass to jss1......sun dage karatu suke bana wasa ba ..sati suka jera sunayi se kuma sati me zuwa za'a fada musu résultat se kowa ya tafi gida hutun wata ukku......lfy lau suka gama question din kuma basu bata wahala ba ....tsoran ta daya kada tazo ba ta daya ba saboda har yanzu bata manta da sharadin Murad ba... A wannan lokacin kuwa Fulani har ta gaji da fadan rashin zuwan Murad tayi fadan tayi fushin ta gaji kullum maganarshi daya ce cewa zezo .....kai daga baya in ta kirashi da sun gaisa seyace mata yana dakin tiyata ko kuma aikin sun mishi yawa ze kirata da ga baya kuma ba kiran zeyi ba..tun abun baya damunta har yazo yanayi....se de kawai ta bishi da addu'a.. Shima anashi bangaren yana so yazo dan yayi missing dinsu barema Maysam zuciyarsa na matukar son ganinta amma besan miyasa baya son dawowa garin ba ba .....gashi har yau zuciyar na mishi zogi lokaci zuwa lokaci...... 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹 A bangaren Waziri kuwa duk ya bi ya fige ya rame saboda diyar shi MAHEEBATOU dake cikin mawuyacin halin sakamakon kama mahaifinta wato waziri cewa da sa hannushi akayi wa Murad asiri ya bar kasar ita kuma tunda ta taso ta mallaki hankalin kanta bata da wani buri da ya huce ta ganta a garakal mulki tanayin yanda taso kamar Madina dukda de tanada kuyangi har biyu amma ita tafi so ace gaba daya masarautar a hannunta take........lokacin kuwa hanya daya take ganin zata bi ta cika burinta hanyar kuwa itace ta auri Murad idan sarki ya mutu tana da yakinin yarima Murad shi ze gaje shi tunda shi kade ne danshi na miji ... Mahaifinta waziri ya daure mata gidin se abunda take so takeyi kasancewar ita daya Allah ya bashi bayan shekara da shekaru da yin aure shi yasa ya dauki karan so ya dora mata .duk abunda zatayi baya ganin laifinta ....koda ta sameshi ta sanar mishi burinta se ya goya mata baya ...a lokacin ya samu me martaba da yanaso akara hada zumunci wato a hada yarima Murad da diyarshi Maheeba aure ... Sarki ya sa aka kira Murad a lokacin sannan ya sanar masa idan har yana da ra ayin aurenta .. Bude bakin Murad yace a'aaa kiri2 yace shi baya sonta ...wannan magana tayi matukar batawa waziri rai amman ya danne zuciyarshi... Koda ya sanarwa da diyarshi yanda sukayi se kawai ta fashe mishi da kuka har dasu birgima ..... .....duk da haka seta fara shigewa tana nuna mishi so ...shi kuwa Murad be masan tana yiba duk inda yayi se taje ........ganin haka yasa ya tattara ya koma England da zama bayan ya sha fama da fulani..... Wannan tafiyar tashi gaba daya Maheebatou ta fice a hanyacinta dan a rayuwarta ba a saba ce mata a'aa ba dole tasa waziri ya turata kasar Mali karatu wajen dangi mahaiyarta da alkawarin idan ta dawo ze cika mata burinta ..... To fa ranar da tazo ne ta riski Maihaifinta na zancen asirin shida mahaifiyarta ...tun lokacin ba agane mata ba ..dan dama saboda cikar burinta ta dawo.... Ganin abun bana qarewa bane Waziri ya wanke kafarshi ya tafi ya sanarwa Madina halin dayake ciki ..amma Madina fir ta kiya ..babu irin rokon da beyi mata ba kan a karya asirin Murad ya dawo daga baya a san yanda za'ayi aman tace bata san zancen ba .. Rai a bace ya fito kamar wanda zetashi sama a ranshi yace baki san ko biye miki danake saboda Maheeba bane dan na samu na zama sarki sena barta ta taka wanda take so... Haka ya isa gida yanata banbami amman mi abunda ya tarar ya kara daga mishi hankali dan kuwa Maheeba numpashinta ya dawo sama2... Ba shiri ya fita ya kama hanyan se wurin BOKA gobe da nisa ... Makuddan kudi ya zube mishi nan yace yana son a karya asirin Murad ya dawo gida kuma idan ya dawo kawai a daura aurenshi da diyarshi Muheeba... 😳😳😳to fa fans kunji wata kuma..... Shin ya luke ganin zata kaya ne? Fasma ce🖊 [26/6 01:25] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿47__48 ```Manzon Allah (SAW) ya ce'' ciyarwar mutum ga iyalinsa sadaka ce'' Bukhari ya rawaito shi.``` Makuddan kudi ya zubewa Boka gobe da nisa yace yana son a karya asirin Murad ya dawo gida kuma idan ya dawo kawai a hada aurenshi da yarshi Muheeba... Boka Yayi wata mahaukaciyar dariya seda waziri ya tsorata can kuma ya daure fuska ya ce ina jin dadin aikin ka ......saboda akwai zubar da jini ... Waziri ya zaro ido yace jini kuma Ee na jarirai ma kuwa idan har a nason aikin yayi kyau ... Waziri yace ayi komi ma idan de har burin er leleta ze cika sannan kuma wani hanzari ba gudu ba ina son abani maganin da zata mallake shi se abunda tace za ayi nan ya sake zube mishi kudi .. Boka yayi dariya yace an gama ..yayi yan zubace2n shi ..ya dauko wani kullin magani yace wannan a abin ci kona sha za'a zuba mishi amma fa a bari har a daura aure ......sauran aiki mutanen mu zasu cika shi da zarar sun sha jinin jarirai komai ze wakana kaide kawai abunda zakayi shine ka cusawa Murad auren da zarar ya dawo .... cike da murna ya karbe maganin ..har ze tafi la'anan nan Boka yace kada ka tado zancen auren a kwanakin nan dan kauda duk wani kokwanyo na mutane ka barin a samun koda sati ne da dawowar shi sekace mishi kana so ya auri yar ka ...kafin nan mukuma zamu cusa masa kwar jinin ka da ba ze iya cewa a'a ba .. Cike da murna ya tafi gida jin harda shawara boka ya bashi .... Muheeba dake zaune se hirar su suke ita da mahaifiyar ta har da shewa ...ai kuwa ta najin sallamar mahaifinta ta koma ta kwanta ta fara numpashi sama2.......(tab 😳 a raina nace ashe gaba ma da gabanta makircin wani yafi na wani) Da sauri ya isa kusa da ita yace sannu Muheeba .....ki kwantar da hankalin ki wannan karon Murad na kine ...kinga wannan ya fiddo kullin magani yace na mallaka ne.. Caraf ta bude ido aman saboda makirci de taki tashi ta zauna tace Abba zan auri Yarima Murad na hau kadagar mulki ? ........ Waziri yayi dariya ya ce sosai sannan ki shirya wa zowar shi kwanan nan yana kuma zuwa se.aure kawai ... Ai bata san lokacin da ta tashi zaune ba ...tace wai Allah da gaske? Yace haba yar lele kin bazan miki wasa da irin wannan batu ba .... Nan murna ya cika ta har ta fara hangota tana ba kuyangi order se kawai ta fashe da dariyar farin ciki .. Ganin haka ya waziri fita ya nufi fada ciki da murna yasa yar leleshi farinciki.....🙄 Yana fita suka tafa itada mahaifiyarta tare da yin shewa tace kai mama kin iya hada plan da ba dan nabi shawarar ki nayi cutar karyan nan da baze je a karya a sirin ba ... Tace kede bari y'ata ai rayuwar ce seda haka ... Suka sake yin shewa tare da tabawa kamar ba uwa da diya ba .. 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 A bangaren Maysam kuwa yau aka basu vacation bayan an bawa kowa sakama konshi inda Mufeedah tayi ta daya Maysam ta biyu se kuma Mariam ta ukku sunsha kyautikika ..ita de Maysam gaba daya tayi sanyi ta san ba ita ba zuwa hutu gida duk wanda ka gani cike da dauki yau zata tafi gida banda Maysam ... Mariam aka fara zuwa dauka sanan motar su Mufeedah tazo ...tananan tsaye motocin fulani suka fara zowa daya na bin daya har goma dan kuwa fulani da kanta tazo daukarta ... ...... Maysam na hango fulani ta kuwa zanbad'a da gudu ta rungumeta .... Sun jima a rungumen fulani ta dagota tace Maysam ya banga kayan ki ba? Ta dago kai idanun ta har sun kawo ruwa tace Momy banyi ta daya ba ta biyu naci.. Fulani tayi murmushi tace kai amma kinyi kokari fa congrats dauther... Maysam tace Momy kin manta da sharadin Ya Murad ne.... Fulani tace sharadi kuma?dan ita har ga Allah ta manta Maysam tace yace idan har banzo ta daya ba to bazan zo vacation ba.. Fulani ta bata rai tace bari batun shi je ki hado kayanki mu tafi... Da sauri ta zube nan kasa tace Momy ki mun rai ki barni nan dan walahi ko kiranshi na karshe seda yayi mun warning... Sega hawaye shar2 .. Fulani ta dagota tace kada ki damu zanyi mishi bayani... Maysam tace kiyi hakuri Momy badan bazan iya bin umarnin ki bane a'a kin huce haka a wurina bana son shiga tsinuwar mala'iku ne dan cewa yayi bada izinin shi ba inde har banyi ta daya ba nazo hutu.....ko satin nan a islamiyya malam ya kara jaddada mana irin sab'awa iyaye ko miji bala'in dake faruwa da mutun .... Ran fulani ya kara baci a ranta tace ta yaya ma ze gindaya mata irin wannan sharadi kan wani banza dalilin shi da beda tushe ....nan ta zaro waya ta shiga neman layin shi amma a kashe...tayi kira yafi a kirga amman bata shiga...ta kalli Maysam tace shikenan amma bazan iyabarinki a school din nan ba koda kuwa da kuyangi..ki had'o kayan ki na kaiki bade shi garin ne yace bazaki bari ba? Ta ce eee Fulani ta bada order a ka debo kayanta aka saka a booth ...suka fice ... A motan kam fulani tasha surutu har suka iso wani tamtsamemen gida ....tun kofa gidan abun kallo ne bare cikin ba'ama zancen ...katon gidane na gani na fada duk da babu kowa ciki se me gadi da me bawa fleurs (flowers)ruwa amma fa ko ina tsap2 nan kuyangi suka fara goge2 masu shara nayi masu daura abinci ma nayi ..fulani da Maysam kuwa shopping suka tafi kafin su dawo komai is ready. Se biyar na yamma fulani suka fara shirin tafiya bayan a zube mata kuyangi bakwai dan yi mata komi se digorai biyar ... Tofa nan ake yinta dan kuwa Maysam kuka take shab'e2 fulani ma daurewa kawai take dan ji take kamar tayi mata kukan sede ga bayinta nan kusa ba dama ...da kyar ta samu ta lallaba ta tafi.... A mota kam fulani duniyar tunani ta fada tana yaba kaifin hankalin Maysam ,,gata karama da ita ta tuna lokacin da take ta fadan rashin samun Murad a waya ...cike da shagwaba Maysam tace kai Momy ki barshi haka mana may be yana wani aiki ne ......wannan kira haka se ya 'aza ko ba lafiya tayi dan murmushi... Madina da Murza kam basu san wainar da waziri yake tonawa ba se saukar Murad suka gani a masarauta... Madina kam bakin ciki ya kusan kasheta abunda bakinta ke fadi kawai ta yaya haka ta faru?...ras gabanta ya fadi data tuna da waziri tace kadade shi ya batan planning dina tayi dariyar gefen baki tace zan kuwa bincika...... Zo kaga Murna wajen fulani bakinta ya kasa rufuwa dan murna ....haka ma me martaba sarki ... Murad kam tunda yazo yake baza idanu yaga ta ina zega Maysam ama shiru kwanshi biyu yaga baze iya hakuriba ya tuntubi lfulani da zancen dan yasan de yanzu anyi hutu a ko'ina Kamar me ciwon baki ya tambayi fulani ina Maysam take yana wani babasarwa waishi a dole be damu da itaba.... Fulani tace tana Maradi mana.ya sake jefo mata tambayar basuyi hutu bane? Ta kalleshi tace sunyi mana tun satin jiya ... Da sauri ya kalleta yace to tana ina ne ? Fulani tace tana gidanka na Maradi tareda kuyanginta da dogarai .. Quoi(what)!!??ya fada cikin wata irin voice ta...... ... Ina sonku fans ❤❣😍 Fasma ce🖊 [27/6 22:01] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿49__50 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''hakika Allah ba ya kallon surorinku da dukiyoyin ku amma sede abinda ya ke kallo shine zukatanku da ayyukanku'' Muslim ya rawaito shi``` . Da sauri ya kalleta ya ce to tana ina ne? Fulani tace tana gidanka na Maradi tare da kuyanginta da dogaran ta.... Quoi(what)?ya fada cikin wata irin voice. ...se kuma ya sassauta murya tunawa dayayi da fa Fulani yake magana ya danne bacin ranshi baki na karkarwa yace Momy wanne daga cikin gidan ? Cike da nutsuwa ta kalle shi tace gidan ka dake unguwar ''sabon gari''wato babba gidanka ba.... Besan lokacin da ya waro ido ba yace haba Momy gidan nan fa na ginashi ne saboda sweetbaby.na ne sega hawaye shar2 kuma ai..... Kafin ya karasa ta tare shi da fadin wai anya Murad kana cikin hankalin kuwa ?yo inba haka ba taya zaka gina gida akan wacce bata ma doron duniya ... Rararafo wa yayi ya dora kanshi a cinyarta tare da dora hannushi dede zuciyarshi yace Momy har yanzu zuciya tace ta kasa yarda cewa sweetbaby na ta mutu a kullum gani nake kamar zata dawo gareni ko na ji ma kamar tana kusa dani..... Fulani ta shafa kanshi tare da goge mishi hawaye tace kaci gaba dayi mata addu'a dan shi take bukata daga gareka bawai ka dorawa laifin wani akan wani ba....... Bede ce komi ba se ajiar zuciya dayakeyi a jere ... Can kuma kamar wanda aka ciza ya tashi ya zauna cuwat yace Momy dawama kikace kin bar wacan abar..? Fulani ta gane sare amma seta mazge tace me wa kenan? Cike da shagwaba yace ita fa !! Fulani tana sonyin dariya amma ta danne tace idan baza ka fada min waba abar maganar tunda de ni ba yar modi bace bare nayi arwa...... Kamar zeyi kuka yace Maysam fa nake nufi...... Au wai da ita ....to tare da bayyinta take......... Ya dan sauya fuska yace ina de fatan dogarai masu tsaron mata aka bata ? Fulani kam se gimtse dariyar ta take tace ka taba ganin dogarai mata ne? Yayi dan shiru can yace to wai ma miyasa bata dawo gida hutu ba? Wanna karon fulani ji tayi kamar ta dokeshi a ranta tace ashe shi ya ma manta da sharadin shi ya bar baiwar Allah da wahala... Tade daure tace to batayi ta daya ba ta biyu tazo... Yayi fuskar tunani yace to mi alakar zowanta da ta biyu datayi..? Fulani tace iii lale fa dole ka tambayya to sharadin daka ginda ya mata ne kan in bata yi ta daya ba to kada tazo hutunnnn.. Shi se yanzu ya tuna ya dan shafa kanshi yace aii hakane ashe........yace Momy bari na dan zaga gari..... Tayi murmushi tace a dawo lfy ..... Har yakai kofar futa falon ya juyo yace kuma Momy dogarai nawane suke can din.... Fulani danta tsoratashi tace su goma kacal ne .... Bashiri yace goma fa? Tace to ko sunyi kadan ne a tura mata wasu? Zuciya na tafarfasa yace Momy goma ai sunyi yawa ina laifin biyu ko daya ma.... Murmushi kawai tayi ta shige room dinta ganin inta biye mishi seya kashe mata aiki da tambayoyi.. Fita shima yayi rai a jagule se yaji baze ma iya fita yawon ba ....lambu ya tafi wai ko zeji dan sassauci amma ina inya tuna maza goma ke can tare da Maysam se yaji wani zut a zuciyarshi gaba daya ya saka kanshi a damuwa ya kasa sukuni wani bangare na zuciyar yace wai mi kake yi hakane?to wai ina ruwana in maza dari ke tare da ita tundade ba santa kake ba....wata zuciyar ta kitsa mishi ai ba wani damuwa bane kayi da ita kawaide kana kare martabar aurenka ne haka yayi ta saka da warwarar shi ... Bayan sallar la'asr ya nemi izini ganin me martaba..... Bayan an bashi izinin shiga ya shiga ya zauna fulani da Madina na kusa dashi sun sakashi tsaka da alama de wata magane ce suke wacce ta shafi shagulgulan gidan... Bayan ya kwashi gaisuwa sekuma yayi shiru ganin haka Sarki yayi dariya yace da alama de akwai magana a bakin ka yarima MURAD me jiran gado...yayi y'ar dariya Wannan furuci ba karamin ta dawa Madina hankali yayi ba ta kasa boye kishinta har seda fuskarta ta nuna wanda fulani kade ta lura da hakan bata ce komi ba se girdiza kai da tayi dan inda sabo ta saba..... Shima yar dariyar yayi tare da dan sosa kai yace dama2 ina son zuwa Maradi ne yanzu se ya sadda kai....... Me martaba sanin matar shi Maysam nacan ya sa be wani tambaye shi daliliba sede yace baza kayi hakurin gobe ba tunda yamma ta farayi.. Caraf ya ce ai jirgi zanbi ne. Fulani bata san lokacin data dara ba Madina kam fadi take kuyi ku gama na dan lokaci ne...kamaci sa'a a jirgi ne da a mota ne da cire maka burki ka mutu kowama ya huta🙄 Sarki be sake cewa komi se addu'ar sauka lfy dayita jero mishi tareda sakon gaisuwa ga Maysam Nan yayi musu sallama ya fice fulani ma addu'ar tayita mishi .. Yana zuwa jirginsu ya daga se Maradi ... 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 A bangare Mubeeba kuwa dadi kasheta ne kawai beyi ma amma iya murna da nuna jin dadi tayi shi ..ita a yanzu hartaga ta zama matar yarima me jiran gado .....itada ummarta karansu suke ci ba babbaka waziri ma hankalin shi ya kwanta ganin yar shi ta ji sauki... Muheeba kuwa tuni ta fara cusa kanta wajen Murad duk da yana korarta tare da yi muta wulankanci amma kamar bada ita yakeba a cewarta ta bashi time ne kan ya shigo hannu ..... 🌹🌹. 🌹🌹🌹 Biyar da rabi ma acan tayi mishi ..yana sauka motoci suka zo daukarshi daya ke dogaran a sanar da su zuwanshi.direct gidan shi na sabon garin suka sauka... Tunda suka shigo unguwar gabanshi ya fara fat2 ai suna sshigowa gidan ma gaba daya ya dan rikice da kyar ya seseta kanshi ya fito direct hanyar falon ya nufa ya na zuwa yayi knoking .... Maysam dake zaune tana shan ace cream ga ta saka Tv gaba ...ga kuma biyu daga cikin kuyangi daya na matsa mata kafa dayar na bata labari me noshadantarwa da saka ban dariya..... Jin knoking yasa tace waye ne...setaji ba amsa.... Aka sakeyi da har daya daga kuyangi zata bude Maysam tace a'a' bari na bude da kaina... Da ace cream dinta a hannu ta bude kofar ...wa zata gani inba Murad ba wani waro ido tayi irin na kaga abun tsoron nan ...tace y.. Kuyi manage da wannan Ina kaunar ku fans ina jin dadin yanda kuke bibiyar novel din Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa ...ina sonku irin totaly din nan 😍❤❤ Muje zuwa 🏃‍♀ Fasma ce🖊 [28/6 23:23] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 51__52 ```Manzon Allah (SAW) yace''fiyyayen musulmi shine wanda duk musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da hannunsa'' Muslim ne ya rawaito shi``` Da ice cream dinta a hannu ta bude kofar ...wa zata gani inba Murad ba wani waro ido tayi irin na kaga abun tsoron nan tace yaya se kawai robar ice cream din ta fadi daga hannunta gabadaya ta bata mishi kafa ......... Kara zaro idanu tayi tace yaya kayi hakur........ Kafin ta gama fada ya sauke mata yatsunshi biyar a fuskarta ....har tayi taga2 kamar zata fadi ...se yayi saurin fizgota ta fada jikinshi ... Wani mayen electric shok yaji yabi jini da jijiyarshi kamar de na kowani lokacin idan har fatar jikinsu ta hade da sauri kuma ya hankada ta yace ''comment oses tu t'habiller de cette façon ? (Waya baki izinin yin wannan shigar .)..... Hannunta dafe bisa kumcinta tace Momy ce ta say mun da muka tafi shopping Wani marin ya sake sauke mata yace Momy ta ce ni kade sekuma sweetbaby na ....... Da gudu ta fice cikin room ta bar shi nan tsaye ...... Dadin ta daya da Kuyangi tun lokacin da sukaga Murad ne su ka ficewar su Shima hanyar stair yayi ya shige daya daga cikin dakin sama ....koda ya shiga dakin ya jingina da kofar ya rasa miyake mishi dadi zuciyar shi na wani irin zafi sai kawai hawaye ya fara zarya a fuskar shi wanda besan dalilin yinshi ba .....nan ya tsaya ya ringa tariyo scene din su ta yanzu da yanda take kuka wanda shi yafi kona mishi rai dan koba komi bayason ya ga mace na kuka bare shine sila ...wata zuciyar tace mize hana ka tafi ka lallasheta kada ma Allah ya kamaka da laifin cin zarafin ta, gashi kuma kaikade ta sani a garin..gata yarinya ...ya tuna nasihar Fulani cewa ya daure ya kulada Maysam ya ringa tausaya mata mareniya ce.....sanin irin zafin da mutum keji idan ya rasa wani nashi dukda yasan seyakai zuciyarshi nesa sannan ze iya kula da ita amma ze kwatanta ya gani.. Da sauri ya fita ya shiga dakin dayake tunanin tana ciki ... Yana shiga ya hangota kwace bisa gado se kwasar kuka take .... Gefen gadon ya zauna yace ke.... Da sauri ta tashi zaune tana kallonshi fuska cike da hawaye tace na'am.. Hannu ya biko mata yace zo ... Da sauri ta rarafa tazo d'orata bisa cinyarshi yayi yasa hannu ya goge mata hawaye yace kukan ya isa haka nan ... Can yace bakisan ke matar aure bace .... Cike da shagwaba tace na sani man... Yace to shine kike irin wannan shigar bayan da maza cikin gidan ..... Tace to ai naga basa shigowa ,ni kuma bawani futa nakeyi ba shiyasa ai ..... Ajiyar zuciya yayi yace shikenan kikiyaye kisan irin shigar da zakiyi ...ina fatan de ba haka kuke shigar nan ba a school.... Nan ma tace a'aa bayan mun yi hutu ne Momy ta say mun a matsayin gift dan nazo ta biyu ... Yace to nima ki shirya gobe na kaiki shopping ki zabi abunda kike so dan kin yi kokari amma fa kiyi kokari ki ringacin ta daya se kuma jibe mu huce can gida... Wata dariya ta kubce mata jin zasu taga Momyn ta fulani har yar karamar wushiryar ta tafito tare da fararen hakoran ta wanda kyawunta da tsantsar kamarta da Sweebabyn shi ta fito besan lokacin da ya rungumeta tsam a jikinshi dudda ya ji shok din amma wannan karon sema ya kara matseta a jikinshi har seda tayi yar kara tukon ya dan sassauta mata ... Ta raba jikinta da nashi tace yaya Jibifa kayanka sun bace bazaka canzasu bane? Ya kalla tare da mikewa da ita a hannushi yace mutafi to na fidda...Da ita suka shiga har dakin ya ajeta ya ce ina zuwa ya dauki kayanshi yashiga tolet seda yayi wanka tare da doro alwala jin an fara kiran sallar magrib........koda ya fito ta dan gogge wurin dayayi yar kura tana ta kiciniyar sake zanin gadon amma ta kasa shimfidar kasancewar yayi mata girma se turo baki take ...dariya yayi ya kama ya shimfida ya gyara tana kallonshi se dariya take mishi yana gamawa ya yi hanyar fita tare da fadin kiyi ki gama kiyi sallah ..tace to ... Shikam be dawo ba se bayan sallar isha'i ..a zaune ya isko ta ta saka tv gaba se kallon dessin animé take a ranshi yace i lalle yarinya ce ....direct dining yaje ya zauna kuyangi sun zube abinci iri2 table din a shake yake taf da abinci dana sha .....a raina nace mutum biyu kade fa kawai zasu ci abincin nan amma ko mutum goma aka bawa to na tabbata se sunci sunyi saura.....wani nacan kwana ma zeyi beci .ba.Allah de shi kyauta... Ganin bata alamun zowa yace ke zonan.kiyi serving dina inke bazaki ciba ......dan shi ko a gida baya barin kuyangi su zuba mishi sede Momy ko kuma in bata nan ya jira har lokacin dazata zo ..in kuma a England ne to wannan shi ze zuba abunshi.. Cike da shagwaba tare da turo baki dan bataso ya katse mata kallon ba ..... Tana zuwa ta bude ta zuba mishi ...ta kama hanyar komawa ...yace ke zonan ...ya zare mata ido yace zauna kici maza ...ganin ta saka abincin gaba ta kasaci yace ci mana... Dan kadan ta taba ta tashi ta koma fallon ..... Bayan ya gama shima falon ya zauna tare da canza tasha zuwa discovery ch .....tun tana kallo har bacci yayi awon ga da ita... Shima sha daya nayi ya kashe komi tare da daukanta ya nufi daki da ita... Asuba ta gari Maysam.. Kuyi hakuri da wannan walahi ina buzy ne..wannan ma dan naga coment dinku ne yasa nayi.... Love you all❤😍😘 Fasma🖊 [30/6 22:17] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ *Queenbaby ina kika shige ne kwana biyu keda Ummu Usman..?Allah de yasa all is fine....munyi* *missing dinku matuka ..😍😍pls come back soon...* *Dubun gaisuwa zuwa ga yan kungiyar mu na STAR ,W,Ass .hakika ina alfahari daku * Allah* *ya qara hada kammu* ... * *Ina yinki irin totaly din nan tawan Arfat ba ....ina jin dadin yanda kike kula dani da nunan kauna Rabbi ya kara dankon zumunci** ❤😍❤❤...... 🅿53__54 ``` Manzon Allah (SAW) yace''tsakanin mutum da shirka da kafirci shine barin sallah kawai'' Muslim ne ya rawaito shi.``` Da asuba ta rigaye shi tashi tayi mamakin ganinta a dakinshi ...direct tolet ta nufa ta doro alwala ta kabarta sahlan nafila dan har yanzu lokacin sallar asuba bai yiba ... buda idonshi yayi ya saukeshi akan ta tanata lazimintz yayi matukar mamakin ..jin an fara asalatu yasa shima ya doro alwalan yayi raka'atanil fajr ya na gamawa ya nufi masallaci don yin sallar asuba Itama tashi yayi tayi .. Bayan ya dawo ta duka har kasa ta gaidashi Ba yabo ba fallasa ya amsa ...nan ta fido alkur'ani ta fara tilawa tare da azkar ....shima zaman yayi sukayi tare sanan ya jata suka koma .gado dukda de kowa a sharenshi yake kwance . Bai bude ido ba se wajejan goma na rana ......beyi mamakin rashin ganinta ba ...wanka yayi ya fito cikin shirin shi .. Tana zaune ita kade ta saka tv gaba ya fito ....... Kare mata kallo yayi daga sama har kasa shigar riga da wando ne a jikinta na english wear ......kayan ba karamin kyau suka mata ba .....ga ba dan kwali a kanta kitson nan ne ''tsinar shimkafa'' akanta duk ya zubo bisa kafadinta .....da sauri ya dauke kanshi jin zuviyar shi ta fara sauya kid'a ... Direct dinning ya nufa ..ya zauna... Tana ganin haka ta bishi itama ... Arish da pepper soup ta zuba mishi da wainar shimkafa se ruwa tea .......ta sakashi gaba tana kallo .... Be dago kai ba ya fara ci tare da fadin ke har kinyi break dinne ..? Ina Maysam bata ma san yanayi ba ta tafi duniyar tunani ....a ranta tace ita bata taba ganin mutum me kyau irin yayanta Murad ba kamarsu daya da babanshi ....... Dago kan da zeyi jin bata amsa meba ai kuwa idonsu suka sarke jikin juna ...dama ya kurbi tea ne ai kuwa se ya sarke shi ya shiga tari ba shiri .........itam a kuma seta rikice gaba daya ruwa kawai ta iya bashi yasha tare da dan bubbuga bayanshi irin yanda taga anayi.... Da kyar tarin ya tsaya yace dama an zo ansaka mutum gaba ba dole ya sarke ba... Tayi dariya tace kasan mi yayana ..........? Ya gimtse fuska yace miye ne....? Se jikinta yayi sanyi tace a'a bakomi shikenan ma...... 'Dage kafad'u yayi irin ''je m'en fou''(i don't care)din nan.... ...a ranshi yace yarinyar nan sena dena sake mata fuska dan kada ma ta rena ni.irin wannan kallon .... Be gama tunanin ba ta tashi ta barshi nan ..... Ya bita da kallo tare da tabe baki yaci gaba da cin abincinshi amma jikinshi yayi sanyi.... Falo ta zauna se turo dan karamin bakinta take wai ita adole tayi fushi ...... Bayan ya gama ya dawo falon ya kalleta shi abun ma dariya ya bashi yanda take turo bakin ..... Cike da wayo yace to ni natafi shopping din ........tunda kinyi fushi ai seki zauna tsaran gida yayi hanyar fita a palon .... Da sauri ta mike tare da sakin fuskar tace kai yaya bafa fushi ne nayi ba... Ya juyo yace to ai naga se wani turo baki kike kamar shantu... Bubbuga kafa ta farayi akasa irin na shagwababun yaran nan ... Ba karamin birgeshi tayi ba dan haka sweetbabyn shi keyi ..... Tsayawa yayi yana kallonta ganin abun bana karewa bane yace to shikenan jeki ki shirya kizo mutafi ....kuma cinq(5)mn na baki... Da gudu ta fice dakin ....... Bata jima ba tafito cikin shirin ta na atampa riga da ''jupe''(sket) se dan gyale data yafa ....tana fito wa yayi mata nuni da hannu data je ta sako hijab...batayi musu ba ta koma ...hijab din ya fice gwiwar ta ..... Suna fitowa dogarai suka fara kwasar gaisuwa ansar key din yayi daga hannu driver ya shige itama tana ganin haka ta shiga ...suna gani ya shiga mota suma suka fara haramar shiga sauran motocin amma se ya daga musu hannu ya na nufin baya bukata ....... Ba karamin mamaki dogaran sukayi ba amma babu yanda suka iya haka suka dawo.. Har sun shiga mota yace ke wai bakida nikaf da safa ne? Girgiza mishi kai tayi...... Dan jim yayi sannan ya tada suka tafi ... Shopping mall ya kaita kayan kam babu irin wanda bata dauko ba kama daga lesh ,,,atampa ....daganan suka nufi bangaren turare da man shafawa ...ganin be dauki komi ba yasa ta dauki wasu mayun turare tare da mayyukan su da sabulunsu har kala biyar duk na maza se kuma irin set din na mata shima kala ukku... Bayan sun gama layin nikaf da safa ya nufa ..ya jibgo mata yana fadin ko a school ne to ki tattabatar kin saka safar nan ...ehe... Ita de to ne nata bayan sun gama ya kaita wurin wasan yara ... Yana daga gefe se wasannita take a ranshi yace wannan ba aure ba aka mun raino de aka ban ..... Kai ranar yakaita wurare daban2 ..se la'asr likis suka dawo ..bayan sunyi sallah direct dinnig suka nufa dan sun kwaso yunwa...... Set din turaren nan kala biyu ta doko ta bashi tace naga baka sai komi ba shi yasa na dokoma... ba karamin mamaki yayiba nan ya amsa tare da fadin ashe. de bakida rowa .. Dariya tayi tareda rufe fuskar ta.. Shima dan murmushin gefen baki yayi ... Washe gari kuwa sha daya na safe ma acan tayi musu inda suka bar dogarai da kuyangi zasu shigo motocin su dawo dan su jirgi suka biyo ,,,dukda yasha kauyanci wurin Maysam..dan ita jirgin ma se ranar tayi mishi kallon gaba da gaba ... murna wajen fulani ba'a ma zancan girke2 iri2 tasa aka yi musu ...sosai taji dadin yanda Murad ya rage hantarar Maysam a daya daga cikin dakunan fulani Maysam ta sauka yayinda Murad ke nashi bangaren ... Da dare bayan sun futa ta fito da turaren ruka ta bawa Fulani set biyun na mata da buyu na maza tace wannan naki ne keda dady ne (Sarki) se kuma wannan ta fiddo wasu set din iri daya guda biyu tace wannan kuma daya na Abbana ne dayan na inna Murza... Zo kaga Murna wajen Fulani kamar wacce batafi karfin kayan ba ..nan ta ringa saka mata albarka..dan gaskiya taji dadi kuma ta yaba da hankalinta.. Shima me martaba ba karamin nuna jin dadin shi yayi ba tare da saka mata albarka.... Lokacin da aka jewa da Malam Musa da wannan alheri har kukan murna da jin dadi yayi ya saka mata albarka yafi cikin kwando...sab'anin Murza da bakin ciki saura kiris ya kashe ta wunin ranar tayi shine tana tunanin yanda zatayi da Maysam tsaki tayishi yafi sau a kirga a ranta tace wannan yana nufin kenan tana can tanjin dadin rayuwarta ko....?can tace kai wly da sakema wai abawa me kaza kai .... Madina sosai ta sawa lamuran waziri ido ta baza bayinta ko ina dan ganin mi waziri ke barkatawa dan yanzu yama dena shigowa part dinta .. Aranta tace kowa yaci tuwo dani to miya yasha... 🌹🌹🌹. 🌹🌹 Su Murad kuwa Tunda sukazo tare suke yawo duk inda yayi tana binshi dare ne kawai ke rabasu ba karamar shakuwa da juna sukayi.ba....har Mahmud yana tsokanarshi da cewa kode ya fada tarkon son Maysam ne... Shikuwa se ya yatsine fuska yace ina abunso anan dan farin nata ko dan dogon hanci da karamin bakin ze jani...yaja tsuka ...yace yarinyar da ko kirgen dangi ma bata faraba ina abunso a jikinta ..... So daya ne nakeyiwa Sweetbaby na..wannan itama tanacin alfarma fulani ne yo banda wahalar raino ma ba abunda nake.... Mahmud ya sheke da dariya yace gaskiya nawan ka iya tsara mutum .fa.....da wani ne na tabbata ze kama zancen nan...amma yo ai ko irin kallon dakake binta dashi ko makaho ze gane bare aka zo ga zancen kishi ..... Murad yayi kicin2 da fuska yace a'aa ya ishe ka hakafa inayin haka ne dan kare martabar aure tunda de an rigaya an auramin ita babu yanda zanyi ne... 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 A bangaren Maheeba kuwa ba karamin tada hankalinta ba tayi dan ita se yanzu tasan Murad yanada mata duk da taga yarinya ce karama aman kyaunta ya tsora tata... Nan fa ta dagawa mahaifinta Waziri hankali .....babu yanda ya iya haka yayi shiri zuwa ga Murad da zancen....... Zaune yake shida Maysam datake kan cinyarshi se wasa take da sajen fuskarshi tana dariya yayinda shikuma yake daddana waya a lambu ga kayan marmari cike a gabansu ... Ganin waziri yasa Maysam sauka ta zauna a kasa kusa dashi...jin ta sauka yasa ya do kai ya kalleta seyabi inda take kallon ..tsinkayo waziri yayi yana magana da dogaran dake kofar shigowa lambu... Iso akayi wa waziri ...bayan ya kwashi gaisuwa se kuma yayi shiru ...Murad ma shiru yayi mishi dan yan Mulkin sun motsa .. Can Waziri yace ranka shi dade inason yin magana dakai ... Hannu ya daga alamun ya fadi yana saurarenshi ... Kallon wurin da Maysam waziri yayi ..cuwat ta mike zata basu waje..Murad ya dawo da ita kan cinyarshi .... Waziri a ranshi yace tirkashi wata zufa ta karyo mishi ..... Can yace dama zancen wajen y'ata ne....ina son ka aureta .... Ba Murad ba hatta Maysam da sauri ta dago ta kalleshi ...Murad ma kallon nashi yayi yace.... Wash kuyi manage da wannan... Bansan haka masoyan wannan book din keda yawa haka ba ...a gaskiya ina alfahari daku Rabbi ya bar kauna da zumuncin mussaman yan group din HAUSA YOUNG NOVEL na facebook ..ina jin dafin yanda kuke nuna kaunar ku ga book din nann...ban manta da kaiba Ahmed Gumel ...godiya me tarin yawa Alherin Allah ya kaimaka a duk inda kake......sauran groups ban manta dakuba kusan ina yinku irin dayawan nan 😍❤❤ ... Fasma ce🖊 [3/7 04:46] Fasma😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿55__56 ``` Manzon Allah (SAW) ya ce''me zuwa gyadar da marar lafiya ,ya kama wata hanya daga hanyoyin aljanna har yaje ya dawo'' Muslim ne ya rawaito shi``` . Ba Murad ba hatta Maysam da sauri ya kalleshi....Murad ma kallon nashi yayi se kuma ya kalli Maysam wacce tuni yanayin ta ya sauya...... Ido cikin ido ya kalli waziri yace ''non je n'en ai pas besoin''(a'a bana bukata) wannan bashi ne karo na farko ba dakazo min da zancen auren y'ar ka amma ina son wannan ya zama na karshe .....yace kanacin darajar tsufan kane da wani ne da nasa an hukuntashi. .ya cigaba da fadin idan dama wannan ce maganar dakazo muye to kana iya tafiya na sallame ka .... Waziri ba karamin mamaki yayi ba haka jiki ba kwari ya tashe ya zazzage wandonshi ya fice a ranshi kuwa fadi yake taya hakan ta kasance bayan boka ya jaddada mun yuyuwar hakan....har ya bar lambu yana tunanin wannan al'amarin .... Yana tafiya Murad ya kalli Maysam dake cinyar shi duk tayi wani kicin2 da fuska duk da karanci shekarun aman taji zafin furucin waziri.... Yace yade yar gidan Momy ke baki san fushi baya miki kyaune ba .yanda fa kika son kunun safe kirtup din nan to haka kike in kinyi fushi......... Babu komai ta ce mishi tare da yin haramar tashi daga cinyar dan inhar ta tsaya to zata iya fashewa kukan da ita kanta bata san dalili ba... Dawo da ita yayi ....yace ke bason iskanci to mi akayi miki ne daza kiyi tawani turowa mutane baki ya shantu.... Dama me nema se kawai ta fashe mishi da kuka tare da tashi da gudu ta barshi nan .... Shi abun ma mamaki ya bashi .... Tashi shima yayi ya mara mata bayan..... A palon fulani ya tarar da ita se kukan shagwaba take zubawa fulani kuma tayi2 ta fadi mata abunda ya sakata kuka amma taki fadi ,,,,se aikin rararshi take .... Bata san da shigowarshi ba se jin gaida fulani .data ji.. Tsit kakeji tayi ,,,tayi saurin tashi tare da fadin Momy bari na shiga ciki Tana shiga ba ko kunya Murad ya bita dakin ... Abun ba karamin mamaki da birgewa ya bawa fulani ta bisu da addu'a kara samun zaman lafiya tare da kara hada kansu .tayi dan murmushi.... Shi kuma ya na shiga yaganta a kwance bisa gado tana kuka ciki2...bisa daya daga cikin kujerun dakin ya zauna yace ke taso kizo nan ... Firgit ta tashi ta zauna tayi rau2 da ido ... Yace ke wai bada ke nake ne ba ''viens ici''(zonan) Jiki ba kwari ta taso tazo tana murza ido tace gani yaya... Daga zaunan ya dauketa ya dorata bisa cinyarshi ya goge mata hawayen ....yace wai mi yasaki kuka.. Shiru tayi mishi ... Can yace zaki sha chocolats ? Ta girgiza kai alamun a'a Yace to alewa fa? Nan ma tace a'a Ace cream fa? Naman ta girgiza kai... Yace to mikike so ? Ta ce ba komi .... Shikenan amman kukan nan ya isa haka kada ki jawa kanki ciwon kai... Ta ce to...... Algyabar ya fidda mata yace to maza je kiyi wanka dan kiji dadi jikin ko kinaso na miki ne? Kamar da wasa tace e'e... Be tsaya bata lokaci ba ya fidda mata kayan suka shiga tolet din ya wanko ta tas ya dado ta a towel ..... Koda ya fito ya lura duk kayan jikin shi sun bace da ruwa komawa yayi tolet din kafin yace ki tabbatar kin saka kayanki kafin na fito .sanan ki tafi dakina ki dokomin kaya comlet guda......dan baze iya fita da kaya a jike haka ba ..kuma shi baze bari har su bushe a jikinshi ba.... yana fitowa ya ganta kwance bisa gado bacci ya kwashe ta Abunka da sauran kuka.... Allah yasoshi akwai irin rigar wankan nan a tolet din kuma tanada tsayi dan har ta fice mishi guiwa ....... Abun takaici yama rasa yama zeyi ...shima gadon ya hau ya kwanta kan kace mi bacci yayi awon gaba da shi... Ta rigyashi tashi ya saka kayanta ta dau wayarshi ta fara game abunta dan ita tama manta da wani doko ishi kaya..... Tana tsaka dayi kiran Mahmud ya shigo batayi wani dogon tunani ba ta dauka tayi sallama tare da fadin ina kwana yaya Mahmud.... Cike da jin dadi ya amsa nan ta dunga zuba zance Hayaniyar ta tadashi daga baccin ...da sauri ya anshe wayar ya kara akunnen shi jin Mahmud se ya kashe wayar...ya zare bata ido yace waya baki izinin daukan wayata ne... Ganin ya fara hayayyakoo mata yasa tayi kalar tausayi tace kayi hakuri bazan kara ba.... Bece komi ba ya fara dube2 ko ze hango kayann...can yace ke ina kayan ne.... Wani waro ido tayi tare da fara yarfe hannu tace kayi hakuri na manta ne ... To kuma yanzu mikike jira ? Da sauri ta mike tayi hanyar fita ... Dakatar da ita yayi yace ke haka zaki fita .babu hijab.. Kallon jikinta tayi riga da jupe ne na atampa.... Da sauri ta dawo ta dauka ta fita tana gungunin shi wannan yaya cikin bangare dayan ma se mutun ya saka hijab... Bata ankara ba taji yace ke uban miye kike cewane?naji kamar kince yaya.... Jikinta har bari yake baki na karkarwa tace cewa fa kawai nayi kai yayan nan nawa akwaishi da kirki2... Murmushi kawai yayi dan yajita sarai....... Kayan ta kawo mishi se kuma ta tsaya ... Ya kalleta yace ke fice mun a daki ko kina tsaye zan sa ne... Turo dan karamin bakinta tayi tace to ni shine ka kalleni hakanan harda yi mun. Wanka ...to nima kawai ka saka ina nan ..kaga kenan mun joje ko... Wani kallon bakida wayo yayi mata yace ke ni sa'an wasan kine?ina wasa da kene? Dariya ta kyalkyale tace to shikenan ni na tafi ma.... Ta fice abunta tana fadin ma hadu ne the next time... Shikam yanzu mamakin kanshi yake yanda yake sake mata ...baya ma iya mata fada sosai....zuciyarshi tace kawai de kanayi ne saboda farin cikin fulani ne....se kawai yayi na'am da hakan....🙄 Yana gamawa direct inda yasan ze samu Mahmud yayi ....,ya koci sa'a yana nan..bayan sun dan gaigaisa irin ta abokai..se kawai Mahmud ya kwashe da dariya yace kai mutumen kana bada wuta fa.... Cike da rashin gano mafitar hakan yace kamar yafa? Mahmud yace a'a ba komi naga yar raino ce harta fara taya bacci ya fadi cike da zolaya.... Wani dogon tsuka mtsssss yaja yace kaifa dan iskane .....towai ma idan ma hakane miye na sawa mutum ido ne?gwauro da kai amma ka iya sa ido...dan Allah a daure ayi aure ko sa ido ze ragu... Kwashewa da dariya Mahmud yayi yace shikenan zance Maysam ta samo min yar reno kamarta kaga se mu gamu mu reno su ko..... Ganin abun ya fara zama iya shege yasa Murad fadin idan zaka fadan dalilin kiranka to ka fadan odan kuma ba haka kaga tafiyata... Gimtse dariyar shi Mahmud yayi yace shikenan ...nan suka firar su ...ganin haka yasa na fiyo ta marawa Waziri baya shima 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 A bangaren waziri kuwa kasa fadawa diyarshi abunda ya faru yayi ..se kawai yace ta shirya itada mahaifiyar ta su rakashi wani gu... Basuyi wani musu ba suka shirya han suka kama hanya ...suna tsaka da tafiya ya gaya musu komi har Maheeba zata fara bambami waziri yace a'a tsaya ai yanzu haka wajen boka zamu daku kuji mike faruwa da kunnenku... Ajiyar zuciya Maheeba tayi tace yauwa Sekayi Abbana....suka tafa itada uwarta.......🙄 Suna isa basu wani ji tsoro ba duk da cikin daji ne ga datti ga komi.... Suna zuwa kafin ma su zauna Boka ya sheke da wata karuwar dariya .....bayan sun zauna se kuma yace na san mike tafe daku ba sekunyi bayani ba Dan mutanen mu sun sanar damu komi....hahahahha.... Ya cigaba da fadin ku kwantar da hankalin ku ...yaron ya zo muna da taurin kai seda muka sha jinin jarirai ukku amma. Shiru...shiya sa zamu biyo mishi ta bayan fage Kude ku aje hankalinku gu daya ku saurara Sarki da kanshi ze yi maganar auren idan kana so kuma zama ka iya dan turzawa ka gani ....shi da kanshi zece se anyi aurennnn.... Maheeba tawani kwashi shoki daga nan zaunan tace se kayi Boka aikin ka yana kyau.waya ganni a garakal mulki...hhhhh.. Boka ya cigaba da fadin muna bukatar jarirai ukku daya fari,daya baki da kuma masara (yan japon,),,se kuma jinsi shanu suma haka ,,,rakumma kuma na saudia ... Caraf Mahaifiyar Muheeba ta carafke da fadin wannan ai se ku yankan wuka zade mu bada kudi se a tura akawo ...... Gyada kai Boka yayi se kuma yace wani hanzari ba gudu ba ... Dam gabansu ya bada... Yace se kunyi taka tsan2 kada ku bari asirin nan akar yashi ....da kuwa kai da ke ya nuna waziri da matarshi yace idan ya karye komi ze iya samun ku dan haka ku kiyaye....... Dariya naga sunyi sukace hakan bazama ta faru ba...nan suka zube mishi makkudan kudi suka tafi cike da farin ciki.da ...... A hanyar su ta dawowa ...Muheeba tace Abba ai mun mance da wannan matar tashi me kama da aljanu ai da mun gama ta da boka itama... Waziri yace ki kwantar da hankalin ki ki bar batun yarinya keda mulki ne ze kaiki mi gaminki da ita iya kacin ta de ki bata oder kuma dole tabi... Ee fa hakane Abba ....nan sukayi ta hirarakin su har suka iso.. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Fulani kuwa ganin Maysam tana son koyon girki yasa ta sakata a makarantar koyon girkin har na tsayon wata daya wanda zeyi dede karewarta dede fara Azumin Ramadan ..dan acewarta tana yiwa Maysam kwadayin ta samu ladan aure a wannan wata me albarka koda ko iya girkin ne da gyara gida zatayi..... Kan kace mi tuni ta fara kwarewa dayake akwai ta brain....tun tana taya fulani dan ita take shiga cuisine din da kanta ta dafawa sarki abinci inde har ita takeda girki a cewarta mulki baze hanata samun wannan ladan ba.. kai akazo wani sa'in ma Maysam ita take musu girkin .... Ana haka har watan azumin Ramadan ya kama..... I love you all❤ Fasma🖊 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 🎁🎁🎉 *Alhamdullilah* *Up...up...up my dear HAFSAH marubuciyar RASHIN GATA* *hakika muna nishandan tuwa da da book din nan Allah ya kara baseera je profite* *de l'occasion pour te souhaiter your Bouffday...* *Joyeux anniversaire yar uwa hakika ina tayaki murna you are plus 1 yanzu Allah ya bar* *mana ke cikin koshin lafiya da rufin asiri* ... *Duk da de am late to celebrate but i wish you* *tout le bonheur du*monde.....ni Fasma ina yinki irin sosai din nan hafsynmama ba* ❤❤😍😍🎁 🎉🎉 *Ohhhhh my lovely dauther RAHAMA happy birthday to you too ..today is your day ,,,am so* *happy today because tu grandis si vite ...alhadulillahplus* 1 *now you are 8years Allah ya raya mana ke ya albarkaci rayuwarki* ....🎁 🎁 _Hafsah &Rahama HBD que cette soit une année_ _de bonheur ,réussi, succès,, etc ina sonku irin totaty din nan_ ❤😍.....🎊* 🎉 *Wannan page din naku ne kuyi yanda kuke so da shi* 🎁...😍❤ * Dedicated to all my fans😍❤ 🅿57__58 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''ku kawata mazaunanku da yin salati gare ni ,lallai salatinku gareni haske ne a gare ku ranar Alkiyama'' Hakimu ya rawaito shi.``` Ana haka har watan azumin Ramadan ya kama.... Gaba daya Maysam ta koma bangaren Murad kwana kawai ke kawo ta bangaren fulani.... De temakon bayinta take yin komi ...shi har mamakinta yake dan kuwa yanzu ta koyi komi kama daga shimfidar gado komin girmanshi gyaran daki ,wanki tolet kam ko wata babbar se haka ... Tare suke shan ruwa suyi buda bakin su tare bayan sallar trawi kuma ta dawo ta tayashi hira ..kai atakaice de sun dan shaku ,,dukda har yanzu sweetbabyn shi na nan makale a zuciyar shi hasalima yanzu ya na jan Maysam jikin shi ne dan tana tsananin kama da ita ko shagwabar ma gani yake iri dayace kai wani zubin mantawa ma yake cewa wai Maysam ce a gabanshi dan jinshi yake kamar yana tare da sweetbaby .......shiyasa ma duk wata mugunta hanttara ya dena mata har Mahmud yana tsokar nar shi dan kuwa kusan duk futar da zeyi tare suke yi da Maysam idan Kuwa wajen abokanen shine to se ya barta a cikin mota ya kunna mata game ya bata ...... Azumi kam tun tana jin wuyar shi har ta saba yanzu dayake acan garinsu bawani yi take ba Murza bata ma barinta a cewar al'adar qauyen seka fara menstrue ko kuma anyi maka aure sanna zaka fara duk da de ita inde har Malan Musa na gari to kuwa ze tadda ita tayi...... A kwana a tashi ba wuya yau har azumi ya kai biyar ....bayan sallar la'asr Murad ya shigo gaida fulani bayan sun dan taba hira fulani ta kalleshi tace wai ya najika shiru har yanzu ne.... Ya dago kai yana kallonta da alamar tambayta kwance a fuskar sa yace wani abun ne akayi .... tabe baki Fulani tayi tace kana nufin baka san akan mi nake zance ba? Cike da shagwaba yace to ni ina zan sani ne ? Shikenan to zancen kai sucre(sugar)ne gidan sirrin kanka ne a bisa al'adar garin nan idan azumi ya kama to duk wani saurayi ko magidanci zeyi kokari ya kai sucre gidan surikin shi .... Gyada kai yayi yace shikenan zuwa gobe zan saka akai musu ..... Caraf fulani ta katse shi da fadin kai ya kamata ka kai da kanka dan hakan yana cikin al'adar kuma yana nuna ka mutunta su.... To fa nan ake yinta yayi kicin2 da fuska sannan yace Momy kisan fa bana son futa zuwa wani gari a mota gudun kada.... Daga mishi hannu tayi tace kada ma ka soma ka shirya ai Allah ne me karewa .....idan kanaso kada ka fadawa kowa se Abbanka ....ko Waziri da Dogarai se zuwa safe kawai zaka sanar musu da tafiyan .... In sha Allah babu abunda ze sameka se alheri kada ka damu Allah yana tare da kai ......muma kuma zamu tayaka da addu'a ..... Shikenan Momy Allah ya shige mana gaba ... Ameen ta amsa ..nan suka ci gaba da hirar su ... Har ya tashi ze fice tace kada fa ka manta Maysam gida biyu gareta wato can da nan gidan.. Waro ido yayi yace nan kuma .... Ee ta amsa ... To ai momy naga kunada shi isheshe ne mi kuma zakuyi da shi ... Dariya tayi tace al'adar kenan ..sannan inada tawa tsarabar da zan bayar zuwa safe kafin ka tafi ka turo a dauka...... Dariyar yayi shima yace ok Momy ki kwantar da hankalin ki inde sucre ne se kin ture..... Yana fita ya kirayi Mahmud yace su hadu yana son ganin shi.... Minti biyar ya dauki Mahmud ya iso ...nan Murad ya sanar mishi da komi..... Mahmud yace kwarai wannan haka yake. ..yanzu kawai ka bari zanyi wa wani magana zuwa dare se ya kawo.......kamar katon nawa ya kamata muyi oder... Murad yace kace kawai ya kawo 50. .....se na bawa Momy 25 ...can ma 25 ....ko ya kake gani.... Mahmud yayi dariya yace yayi tunda ko ankai za'a rarrabawa yan uwa da abokanan arziki.... Shikenan kawai kace ya kawo ..... Tun nan yayi kira ya sanar tare da jaddada yau yake son su..... Bayan sallah isha'i kuwa sega oder da sukayi abangaren Murad aka jibge su ..... Maysam na fenêtre(window)tana kallon ikon Allah tun abun yana bata mamaki har ya dawo bata tsoro....... Murad kuwa seda ya bari an tashi a fada sannan ya iske mahaifinshi bangarenshi ..nan ya sanar masa da komi ..ba karamin farin ciki yayi ba tare da saka mishi albarka sannan yace da safe a bude magazine a dauko bahun shinkafa 20 ..na makaroni ma haka......... Godiya yayi kamar shi akayi wa kyautar .. Yana komawa gida ya tarar da Maysam na tilawa qur'ani dan kuwa tun lokacin da wannan watan ya kama kullum cikin tilawar karatun ta take ...idan yana nan suyi tare ...ko tv sun dena kunnawa sede idan wa'azi ne zasu kalla Zama yayi shima yana sauraren zazzakar muryarta har wani lumshe ido yake.... Can ta rufe quranin ta kalleshi tace yaya wai wa incan sucre din hala sadaka za'ayi dasu ne...? Ba tare da ya bude idon shi ba yace na Abbanki ne gobe zan kai mishi ... Be shiryaba kawai se ji yayi ta haye bisa cinyarshi tare da zagayo hannuta a wuyanshi tace dan Allah zanje .... Girgiza mata kai yayi alamun a'a .. E kuwa nan ta fara zuba mishi shagwaba ... Bude idon dayake ya saukeshi cikin nata tarrrr...wani zut yaji zuciyar tayi da sauri ya rufesu ruf...yace shikenan ki shirya se mu tafi amman fa ki sani in baki fito da wuri ba zan tafiyata ne... Da sauri ta gyada mishi kai cike da murna ta rungume shi eeee se kayi yayana ina godiya Kara rumgumeta yayi yace se kinyi yar gidan Momy...nan sukaci gaba da tilawarsu har lokacin rakata bangaren fulani yayi .... Maysam kam tunda tayi sahur bata koma bacci ba guddin kada ya tafi ya barta... Lokacin da Madina ta samu labarin wannan tafiyar ba karamun bakin ciki ba dan lokaci ya kure mata bare ta cire musu burki kamar kullum ga Waziri ya juya mata baya....banda kai komo babu abunda take a dakin ...ta jiza yatsa wani zubin ta cije lebe... A bangaren waziri kuwa koda ya samu labari be wani tada hankalinshi ba dan su yanzu jiran Boka kawai suke yayi aikinshi ...dan ko rakiya beyi musu ba.. Fulani kuwa kamar yanda tace da safe zata bada ta ta gudunmuwar kuwa atamfuna , ,da shadda ,yadina ta bada kala biyar biyar ga Malam Musa da Murza dukda de badan halinta ba taci albarkar watan Ramadan ne...se kuma wasu atamfofin sun kai 20 tace a rabawa matan garin....nan ma Murad ya jerowa fulani godiya kamar shi aka bawa ko kuma dangi shi ...... Maysam se Murna ake yau za'aga Malan Musa ...haka suka kama hanya wacce ta dauke su awa daya da rabi kafin su isa ... Malam Musa besan da zuwansu ba yana kofar gidanshi se ganin motocin yayi ga yaran garin se ihu suke suna bin motocin...kafin ma su iso ya sheda motocin da sauri yayi tsaye yana jira yaga wanene yazo... Dogarai suka fara fitowa sunata gyara kimtsi da kyau ...... Mahmud ya fara fitowa se kuma Murad ...yana nan tsayen suka iso da ido Mahmud yayi mishi alamar dasu duka su gayshe shi ...wani kallon bakada wayo Murad yayi mishi... Shide Mahmud har kasa ya duka yana gaida Malam ganin hakane yasa shima fara dukawa da sauri Malam ya taro shi da fadin a'a ya isa haka ma ya rumgumeshi...nan Malan yace su shigo daga ciki...har ya juya ze shiga yaji an cukuiyeye shi daga baya..juyowar da zeyi yaga Maysam dinshi ce rumgumeta yayi shima yana dariyar farin cikin ganinta itama jitake kamar ta mutu dan murna.. Suna shiga yace ta shiga ta dauko tabarmi a dakinshi... Biyu sabbi fil ta doko ta shimfida se dariya take .. Bayan sun zazauna suka sake gaisheshi ..Maysam kam ta wani lafe kusada Malan ... Can sega Murza tana can yawonta taji labarin zuwan su Maysam aai kuwa ta kamo hanyar dawowa tunda taga motocin tasha jinin jikinta ..dan ita ji take koro Maysam din akayi kamar yanda suka tsara batasan komi waziri ya canzashi... Tana shigowa idonta ya saukan kan Maysam da inba farin sani kayi mata a da ba to kuwa baza ka ganeta ba.....wani abu taji ya tokare ma ta wuya bata gama wartsakewa ba taga ana jido kayyayeki...mutuwane kawai ya rage mata tayi..a lokacin saboda bakin ciki. Nan sukayi mishi bayani tare da sakon Fulani dana Sarki..zo kaga murna wajen Malan Musa har rasa inda ze sakasu yayi nan aka sanarwa da me gari...kan kace mi anyi bambami kowa yazo ...haka aka taro a kofar gidankamar wani taron aure dayake ba wani yawane dasu ba haka mazan garin sukayi layi kowa yazo se abashi bahun shimkafa dana makaroni ,suga simkin nan me 5 aciki da turmin atamfa....can na tsinkawo Murtala(da fatan de baku manta shiba)duk ya wani jeme ya manyata saboda wahala..dan kuwa yanzu haka matanshi biyu da yara ukku....layi yazo kanshi can ya tsinkayi Maysam dake kusa da Murad se dariya abunsu suke..wata kwala ta taru a idonshi a ranshi yace yanzufa da Maysam matatace,,,,🙄yace har yaude ina sonki Maysam dita(kuji fa🙄😏)haka jiki ba kwari ya amsa ya fice yana me dana sani....haka har aka gama me gari ma komi biyu2 ya dauka amman dukda haka komi seda yayi saura har Malan Musa yace asake rarabawa mutane. se Mahmud yace a'a kawai ya rikesu ai daman shi aka kawowa ganin damane yasa ya raba.. Bayan sunyi azahar suka kamo hanya kamin la'asr sun iso ....lfy Lau suka iso 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 Hakade rayauwa tayi ta tafiya yau har azumi saura kwana goma à de de wannan lokacin kuwa Murad ya kai Maysam yayi mata shopping bana wasa ba kama daga atampa..lesh,abaya...etc...iya Murna Maysam tayi tamishi godiya har ya gaji da amsawa .... Kwatsam ranar ana sallah saura kwana ukku ko hudu shida Maysam suna bangaren Fulani .suna ta hira can de fulani tace waini Murad ya akayi banga kayan sallar Maysam bane? gashi sallah na matsowa kada taje ta rasa dumki... Sosa kai yayi yace kai Momy duka ma yau ko sati ba'ayi ba nakaita ta shopping kuma fa duka komi na sai mata.. Fulani tace to ai wannan ra'ayin kanka ne ba kayan sallarta ba ne... Ya gaida kai kawai .. Tace yauwa kaga ni to... yanzu se ka kaita ta zaba da kanta . Maysam wacce tun dazu tana jinsu aman batace komi ba se yanzu tace kai Momy a barshi kawai sena bada wanda ya semin din dimkim.. Fulani tace bata san zancen ba ... Haka ya fito tana biye dashi a baya ,,,,.mota suka shiga..driver be zame ko ina bisa umarnin Murad ba se wurin da ake seda pant da breziya duk dade basu wani fara fitowa ba.. da kuma takalmi da jaka dan dama sune kawai be sai mata ba.... Itade idon wannan shine nan ya biya kudin aka zuba su a leda ya barsu nan dogaren dake kofar supermarché din su suka kwaso kayan aka laftasu a booth. Bayan sun dayo ne yace to gashi na se miki kayan sallarki yana fadan haka ya fice dan Mahmud ya dameshi fa kira... Kuyangin ta suka kwaso kayan suka kai bangaren Murad suka zubesu a dakin Maysam na nan bangarennn... Bayan sun fice ne ta fara duba kayan wata dariya naga tayi se kawai ta musu wuri a inda ya dace... Kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu hakan ta farune kasan cewa bana jin dadin jikina...kusan jiki da jini ...dayawa daga cikin ku na ga message dinsu kuma naji dadi da irin kulawar da kuke bani Allah ya bar qauna tare da kara donkon zumunci.. Love you all irin totaly din nan😍❤ Fasma🖊 : 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Ashe haka masoyan wannan book din kukeda yawa haka...kai amma naji dadi ina alfahari daku alherin Allah ya kaimuku a duk inda kuke wa inda na sani da wa inda ma ban sansu ba ... Allah ya bar kauna ya kara dankon zumunci...ina yinku irin sosai din nan ...* ❤❤😍 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿59__60 ```Manzon Allah(SAW) ya ce''ka bar duk abinda kaga ya shiga maka duhu ,ka kama abinda yake warai a wajenka Tirmizi ya rawaito shi.``` Bayan sun fice ne ta fara duba kayan wata dariya naga tayi se kawai ta musu wuri a inda ya dace... Yau da gobe se Allah yau har daren sallah gaba daya Maysam ta sauyawa bangaren Murad sanffari ..ta juya dakin shi kanshi ogan gyaran ya burge shi .... suna zaune bayan sallah isha'i shida Mahmud suna ta hira can yace inji de baka manta da alkawarin ka..... Murad yayi kasake yace ummm inajin na manta de dan tuna min man.... Tab ..to bari na tuna ma kace duk lokacin da kayi aure to ranar sallah zaka gayyaci goma daga cikin abokanan mu .... Se lokacin ya tuna yace kai amma kacika aboki na kwarai na gode kwarai kawai yanda za'ayi ka gayyaci wanda suka daci ni bari na sanarwa da Momy ...nan suka rabu....yana me jin dadi samun aboki irin Mahmud Yana shi gowa ya tarar da Maysam tayi daidaya a cinyar Fulani..se shagwaba take zubawa. Shigowar shi ma bata sa Maysam fasa abunda take.yi ba...ya zauna ya gayshe da fulani...Maysam ta dago da nufin gaidashi taga ya zabga mata harara ta turo dan karamin bakinta tace Momy kin gandhi ko... Kafin Momy tace wani abu....se kuma cuwat ta tashi taje tana famar hayewa cinyarshi ...... Be hanata ba ta kuwa haye ko kunyar fulani bata jiba ...shima kuwa ko aka se ma ya shiga yi mata rada a kunne ai kuwa se ga shi tana kyalkyalewa da dariya .....abun se ya burge fulani ta girgiza kai da taga abun bana karewa bane ta tashi zata bar musu wajen ...caraf Murad yace Momy wajenki fa nazo .. Fulani tayi dariya tace to ai naga tunda kazo ku manta dani ne ai... Dariya Maysam ta kyalkyale tace haba Momy mu mun isa ne .. kawai fa cewa yayi.wai... Da sauri ya rufe mata baki da hunnun shi..yace Momy daman gobe nake gayyatar abokane nane bayan a sauka a sallar Idi ..to shine nake son ayi musu wani abunn Fulani tace wai ni kake fadamawa ko kuma da matarka kake ne... Kicin2 yayi da rai.... Fulani tace to ai naga Martarka ta iya ne .... Yace Momy fa abinci mutum goma ne Maysam zata iya ... Dariya ta subcewa Maysam tace tab yo sosai ma zan iya ...kuma ma walahi tunda kace haka ni zanyi shi ko yayi dadi ko akasin haka tanayi tana murguda mishi dan karamin bakin ta ... Shi abun ma dariya ya bashi yace shikenan meda wukaken yar gidan Momyn ta ..amma fa idan beyiba nida kene a gidan nan... Itama ta cafke da fadin in kuma yayi fa nida kaine nima .. Fulani de banda dariya babu abunda take musu...nan sukaci gaba da hirar su gwanin ban sha'awa... Washe gari Sallah duk wanda kaga fuskarshi sake take da annuri Maysam tun asuba bata koma ba tana kitchen da kuyanginta se oder take basu kamar wata uwar mata ... Kan kace mi har sun gama sun jere komi bisa dinning table ...jus ma kala biyu tayi natural se kuma na gwangwani .....gida ya kaure da kamshi ni kai na ina mamakinta yanda take komi kamar ba yar sha hudu ba...tana jin alamar saukar idi ta shige tolet ta zabga wanka ta zauna nan ta fara kwaliya dankuwa an koya mata ado lokacin datake koyan girki...tana nan taji haya niyar su ...ya shigo da kanshi yace ta shirya ta fito yayi présenté(introducing)dinta ...to kawai tace da shi ...... Nima ina ganin futarshi na mara mishi baya ...samari ne zuka2 masha Allah .....Mahmud kawai na sheda sauran duk ban sansu ba ....suna nan sunata hira sun shafe 15 minutes shiru ba labarinta daya daga cikin su yace wai M² matar ka baza ta fito mu ganta ne ......dayake haka suke kiranshi tun suna secondry Shima abun ya bashi mamaki har ma zuciya ta fara daukanshi yana ganin kamar ta raina shine .... Dariya yak'e yayi yace bari na dubota .... Tashi yayi yana tafiyar nan tashi ta tamaka.da kasaita. Tunda ya hauro ya fara kiranta cikin fushi da karaji ....dama tana bakin kofar dakinta jin ze shigo itama se tayi kamar daman zata fito ne a dede bakin kofar sukayi karo ita tana famar fita shi kuwa ze shigo ... Wani waro ido naga Murad yayi ya nunata da yatsa yace miye hakane.?..... Se lokacin na kalleta wai fans kunsan miye a jikin ta... Hum ina kayan daya sayo mata wato pant da bresiya ,se takalmi da bag babu kaya jikinta se su ta kuwa ci uban ado .... Maysam ta jujuya tace mi kuma nayi naga kowa ranar sallah kayanshi na salla yake sakawa to miye na wani kallona ne harda tambaya...tana gama fadar haka ta raba ta jikin shi ta fita ... da gudu ya damko ta yace wai kina haukane zaki fita a haka... Tana kiciniyar kwace hannuta ita a dole seya saketa tace dan Allah barni na tafi na gaisa da bakin mana daga baya mayi magana...... Cimak ya dauketa ya shiga dakin ya meda kofa ya rufe harda sakata cike da bacin rai ya fara fada ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba kamar ze daketa yakeji... Aman mi maysam ko ajikinta se ma kara turo dan karamin bakinta take ..ta haye gado kwalla ta cika mata ido ....can kawai sega hawaye shar2... Nan da nan ya dakata da fadan zuciyarshi ta fara bugawa da sauri se kuma ta fara mishi zut2 beyi aune ba ya ji kwalla ta cika mishi ido shima .....da sauri ya haura gadon shima ya rumgumeta ya shiga lallashi da kyar ya samu ta tsayar da kukan yana sakinta ta juya mishi baya se turo baki take.... Juyo da ita yayi yace yar gidan Momy miyasa bakya jine wai .. Cike da shagwaba da yarinta tace to ni minayi ne?naga de kayan sallar daka siyo mun ne kuma kaida kanka kace sune kayan sallana se yanzu dan na saka kuma za'aga laifina... Goge mata hawayen yayi yace shikenan laifi nane ki saka wasu kayan zuwa gobe zan siyo miki kayan sallarki...cike da murna tace shikenan ta mike ta nufi wardrop dinta ...tana dubawa Murad yace zokiga wani abu ....bayan tazo ta tsaya gabanshi yace yanzu ke Maysam da na barki se ki fita a haka .... Tace e man ... Ya nuna kirjinta ta da ita yanzu ne ma ta fara kirgen su Murza da Malam Musa lol yace bakya ganin kin fara girma ne ... Se a lokaci ta kai idonta wajen hannu daya ta sa ta kare dayan kuma ta rufe idonta dashi wai taji kunya tana dariya kasa2 tace nima fa da gangan nayima haka shiyasa ma naki futa seda naji zaka shigo .... Shima dariyar yayi yace to kawo na saka miki kayan kinga mun bar baki a falo... Girgiza kai tayi tace nide a'a..stil bata fidda hannuwanta ba Leka fuskar tata yayi yace nine fa yayanki yanzu kuma kunyar yayan ake.... Se asan nan ta fiddhannunnu ta dauko wata narkekiyar shadda wacce tasha zubi tare da hijab kalar shaddar ta kawo mishi ..shi ya saka mata har hijab din ... Se kuma yace wai wannan adon da kikayi ina zaki dashi yana magana aman idonshi akan dan karamin bakinta..ya doko tissu ya fara goge mata girar datayi tas ya goge ta ...sannan ya fara kiciniyar Goge mata jan baki se mita yake nan fa ake yinta Maysam tace bata san yaren ba ta fara kuka ita ya bar mata adonta ..... .. Kawai kallon dan karamin bakin yake bata yi aune ba taji bakinshi cikin nata🙈 tsit kakeji tayi banda muzzurai ba abunda takei...nan fa Murad ya ci gaba da abunda yake inda tsayuwa ta nemi gagarar Maysam tana famar sume mishi cak ya daga ta ya cigaba..da abunda yake se wani lumshe idanu suke.. .seda ya tsotseshi tas tukon ya saketa se haki suke su duka ..zatayi magana yace shiit yajata suka fito palon kasa bakinta banda zafi babu abunda yake mata tana mamakin wannan abu a ranta tace komiye wannan kuma oho dukda abun yayi mata dadi amman tana ganin kazanta ne ai wannan.. Hannun sarke cikin na juna suka shigo falon ...nan fa aka fara kallon kallo har abun ya qullar da Murad yayi tsaki ciki2 ..har kasa ta duka tayi musu sallama tukon ta gaishe su zata qara yin wata maganar se kawai Murad ya tari numfashinta da fadin ya isa haka nan...ya jawo kayanshi bisa daya daga cikin kujerun ya zauna ..cinyarshi ya dorata ita kuwa se mutsun2 sauka take can de ya harare ta...tukon ta zauna abunta amma kanta a kasa saboda kunya.. Nan aka fara magana kasa2 ..Mahmud daya gaza hakuri yace to ai de zaka barta tayi serving din mu ko ... Wani kallo yayi mishi ....daga bisani kawai seya danna wani abun nan kusa dashi kan kace mi ukku daga cikin kuyangin suka shigo nan suka zube gaban yarima Murad suna kwasar gaisuwa ........sun kai 3minutes nan su basu tafi ba kuma shi bece su tafi ba....... Rada naga yayi wa Maysam ......bayan ya gama ne .....Maysam ta basu oder dasu kwaso abincin sukawo nan falon (to fa mulki ya motsa)..kan kace mi sun shimfida leda sun zube kulolin anan .....suna gamawa tace zaku iya tafiya.... Mahmud yace to tunda kin kora su se ki sauko ki zuzzuba mana cike da tsokana yayi maganar dan yasan gogan baze bari ba ..... Kamar yanda ya zata ne dan kuwa ita de har ta sauko Murad ya riketa tare da girgiza mata kai ..tasan mi hakan yake nufi ....ya kalli Mahmud yace ai idan sauran baki ne kai fa ...zaka iya serving dinsu ......amma kai ma kasan bazan bari mace ta shigo cikin ku tayi serving dinku kuma macen ma mat......maganar ta makale mishi jin yana shirin yin subutar baki ..... Gaba daya palon aka sa dariya .....nan Mahmud yayi serving dinsu efa nan suka fara santi shide yana zaune yana kallon su ...daya daga cikin su ya ce kai amma fa ka more fa irin wannan garar iya abinci.. Se yanzu ya sauke ajiyar zuciya dan shi duk atunanin shi abinci beyi ba ...kada aje yakiyin dadi ...se yaga kowa ya bude tumbinsa se durawa yake.....sosai yaji dadi a ranshi ....... ....Maysam kam tana samu ya saketa ta sulale daki ta hau buga game abunta.... Haka suka gama suka kara dan tataba hira.irin tasu ta abokai... Da zasu tafi ya kirawota sukayi mata sallama tare dayi mata godiya kudi suka aje mata kudi wai tukuicin dadin abincinta ne...tayi musu godiya tare da fatan sauka lafiya.. suna futa kowa ya shiga motarshi ya kama gabanshi... Se Mahmud da suna juyowa ya kwashe da dariya .... Murad ya kalleshi yace wai ya jikin naka ne? Mahmud dake dariya yace ba sauki ....yaci gaba da fadin wai dazun nan fa ka bani dariya yanda ka wani kasa ka tsare ka hana ta zuba mana abincin kamar ba bakin ka ba.. Bata fuska Murad yayi yace kajika da wani zance Matar t...se kuma yayi shiru... Mahmud yace karasa mana... Murad da abun ya kai mishi wuya yace kaga ya isheka haka kafa sa muna ido nida yar reno ta ehe.. Mahmud yace eee fa kace yar reno..to amman.. Da sauri ya daga mishi hannu yace ya isa mana ..ya fice bangaren shi.... Mahmud ma juyawa yayi ya fice gidansu ...yana me yiwa abokinshi dariya ganin da alama ya fara fadawa son yar renonshi ... Koda ya shigo a falon ya tarar da ita se buga game din take lokacin kuma har an kwashe an gyara wurin da sukaci abincin.....kudin da suka aje mata ya ga bata dauka ba ...ya doko ya zauna kusa da ita tare da amshe wayar ...dan karamin bakin ta turo .....yaiyai ta anshi kudin tace a'a ta bar mishi..........tace wai yaya dazu a daki me... Da sauri yace wai ke komi in baki sanshi ba se kin tambaya ne,,?(🙄jifa to ai ko kogi yana bukatar kari bare ma be koshi ba)kul kada kuma naji kin fadawa wani wannan abun ke koda kuwa Momy ce(to fa🤨)....gyaida kai kawai tayi ya jata zuwa bangaren sarki sukayi mushi barka da sallah nan waziri ya dinga mishi kallon zamu hadu....da ga nan bangaren fulani suka tafi inda suka rabshe se fira suke abunsu..... Washe gari kuwa ya kaita shopping ta zabi narka2n shadda da lesh .....suna dawo wa aka kaimata dumki... Kwanci tashi ba wuya yau har sauran sati su Maysam su koma school ...shirye2 take kawai .....kominta an tanadar mata na tafiya ...ranar kawai ake jira ...... Da yamma suna zaune itada Murad a bangaren shi suna kallon wani film ..can taji cikinta ya fara dan ciyo to dama tun safe tana ji amma ba sosai ba kuma yi yake se ya kwanta... Murad wanda yake lura da ita tun dazu yace wai ke lafiyar ki lau kuwa ..... Ita kam tama kasa magana Ido rufe ta kama mararta ....can daya kwanta tace mishi ba komai... A hakan ya barta ya ci gaba da kallonshi.... Ai kuwa can se ji yayi ta fado kasa tim tana murku susu har da kuka2 kasa2 ....da sauri ya isa wajen ta ya dagota yana fadin inna lillahi wa...yace ke wai mike damunki ne ...ina yake miki ciwo duk yabi ya rude.... Mararta kawai take nuna mishi amman ta kasa magana.... Yace mararki ke maki ciwo? Kai kawai ta iya daga mishi.. Iya tashin hakali ya shiga ..gashi likita amma ya rasa irin temakon da ze bata.... Love you all fans.... Fasma🖊 [24/07 à 12:28] Fasma: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Momyn Mufeeda ina kika shigane keda my in law xaynab two days shiru Allah de yasa lfy* ... **i miss you a lot 😒* Dedicated to all my fans😍❤ 🅿61__62 ```Manzon Allah (SAW)yace''babu wani musulmi da zai mutu ranar juma'a ko daren juma'a sai Allah ya kare shi daga azabar kabari'' Ahmad ne ya rawaito shi.``` Iya tashin hankali ,hankalin shi ya tashi ,gashi likita amma ya rasa irin temakon da ze bata... Can de ya dokota kamar yar jaririya ya nufi bathroom da ita.lokacin har jupe dinta ya fara ba cewa..wanka yayi mata tas ya dadota a towel ......kaya ya saka mata ,,,ya hado mata tea me kauri .....se da yayi mata jan ido sanna ta sha ...allura yayi mata ciwon ya ma hanata magana bare taki allurar.... Kan kace mi bacci yayi awon gaba da ita ...nauyenyar ajiyar zuciya ya sauke....yayi waje direct daya daga cikin motarshi ya nufa ......fadawan shi na ganin haka suka rogo da gudu amma seya daga musu hannu. .. Da sauri babba cikin su yace kayi hakuri yarima magajin sarki takawarka lfy se kayi dan sarki jikan sarki ...me martaba Sarki yace a dena barinka kana futa kai kade amma amin afuwa idan na batawa yarima me jiran gado rai ....... Cikin tsawa yace to nace bana so ko dole ne se kun biyo nin.....motar kawai ya shiga ya fice a gidan...nan fa wannan ya kalli wannan wannan ya kalli wacen kowa yana mamaki.... Bayan 15minutes se gashi ya shi ya dawo yana tafe yana maganar zuci shi daya ..shi da kanshi yasan ya canza ...besan mi yasa ya damu da yarinyar nan ne ..wannan rashin lfyr ma jiyake kamar shine bashida ita.......yanzu haka katon2 da pad ne ya je ya siyo mata ,...ya rasa mi yasa yake son shiga al'amarin yarinyar ba..wata zuciyar tace kawai dande Fulani na sonta ne ..kai kuma dan ka faran tawa Momyn ka kake yi mata haka.... Da wannan zuciyar din yayi na'am...budewa yayi ya dauko pad guda ...direct part dinshi ya huce...har lokacin bata tashi ba .........shikam gogan zaman gadi yayi ...foto kam ya matashi yafi a kirga Seda ta shafe awa guda tana bacci sa'anan ta farka ... Da addu'ar tashi daga bacci ta tashi a bakinta .....yanzu kam ciwon cikin ya lafa ... Kallonta yayi yace ya ciwon cikin ? Naji sauki kawai tace. Mishi .....tolet ta shiga ......minti biyu yayi yawa yaji ta kwalla wani ihu .... Beyi wata2 ba ya shiga tolet din ... A tsaye ya tarar da ita ido a rufe se tsala ihu take..... Da sauri ya isa kusa da ita jinjigata yake aman kamar me zugata...ganin abun bana karewa bane kawai se hade bakinsu ya shiga kissing dinta .... Ina Maysam .tsit ta dauke wuta .....seda yaji ta nutsu sannan ya saketa ya ce wai ke baki san girma yazo miki bane zakizo kina yiwa mutane ihu .. Kwalla har ta cika mata ido ta e yaya jini fa... Shifa abun ma kunyarta yake ji amman ita ko aka ......ya daure yace to ai girma ne yazo miki.ko.. Tayi kalar tunani tace girma kuma miye hakan.. Dafe kai yayi yace shikenan kiyi wanka kisaka wannan ki fito..sena fada miki... Amsa tayi tace na miye wannan kuma .. Ohhh ni wai hawon jini kike son samin ne komi... Turo dan bakinta tayi tace to ni nasan shi ne ..kawai danayi tambaya se kace zan. Samaka hawon jini bayan ma ni ya kamata infadi haka tundade gashi se zubar jinin nake... Shi maganganun nata ma dariya suka bashi ..amsa yayi ya makala mata jikin pant din..ya bata ..har ya kai kofa tace yaya wanka fa ai seka temaka kayi mun tundade bani da lfy .... Dariya yayi ya fice ya barta nan se mita da turo baki take ...tas tayi wanka ...ta saka pad din ...da towel ta fito se wani wara kafa take... Yana ganin taya faraa gimtse dariyar shi ..kaya ta saka riga da jupe(sket) da atampa ..ta koyi tsaye kamar dogari..... Kamota yayi ze dora ta cinyar shi ..'tayi saurin cewa jini fa yaya kada ya bata ka nima yau ina ga wunin tsaye zanyi dan kada na bata kayana .....se kuma tayi kalar tausayi tace pls yayana ka kaini asubiti su dubani kada jinina ya kare .....kana jin shi ko ....?se zobowa yake.. Ganin shirmen bana karewa bane ya dorata a cinyar yace ke wai baki san mentrue ne kika fara ba.... Wani waro ido tayi se kuwa ta fara famar sauka ta gudu dan kunya..a iya tunanin ta bata kawo wannan abun ba... Yana dariya ya rike ta gam yace seda kika gama rashin kunyar taki ne kuma yanzu zaki wani gudu... Hannu tasa ta rufe idonta tana dariya kasa ga kumya kamar kasa ta tsage ta shige..... Medo ta bisa cinyar yayi Yace nutsu muyi magana to ...... Kanta a sadde ta kasa dagowa ..yace ina fatan a makaranta an yi muku bayani akanshi ... Tace ummm. ..magana ma kam kunyar yi take yanzu.. Komi seta umm ko a'a.... Yace to ki bude kunuwanki da kyau ki jini....yace banda wasa da maza ko a school ne ..ke yanzu idan ma kika sake wani namijin ya taba koda hunnuki ne se ciki mu... Ai kafin ya gama cuwat ta tashi a kanshi tana yarfe hannu tare da zaro ido...tace shikenan yaya miyasa ka tabani yanzu shike nan na banu a garinan ..yanzu har nayi ciki tana tataba cikin se kawai ta fashe mishi da kuka.. Shikam yarinyar nan yarinta da wauwata sunyi mata yawa..dariya ce ta kwace mishi ita kuwa tayi kasake tana kallonshi ..yace to ai ni yayanki ne kuma miji..se kuma yayi shiru ...ya kuma cewa ai banda ni tunda ni kinga yayanki ne wasu mazan nake nufi... Ajiyar zuciya tayi ..wunin ranar maysam sokoko tayi shi ta kuma kiya Murad yama tabata .....taso gayawa Fulani amma kunya ta hanata se kawai ta share zancen..seda ta jera kwana biyar sannan ya tsaya mata tayi wankan tsarki..wanda yayi dede da gobe zata tafi karatun suna zaune a palo itada Murad tana zaune nesa dashi dan yanzu ta dena shige mishi ..yace ke dazu naga kamar kinyi salla ko .injin de kin iya wanka... Ee kawai tace dashi .. .....ba zato ba tsammani taji yace to tashi ki nuna mun yanda kikayi.. Kallon mamaki takeyi mishi .. Yace to miye na mamakin ba yau fa na fara ganin wankanki ba...dan haka tashi huce na gani... Tana tura baki kamar zatayi kuka ya tisa keyarta...tsaf tayi shi dede ko gyara beyi mata ba..... Washe gari jirgin yamma suka bi ita da shi wanda bayinta tun safe suka kai mata kayanta ...aka jere mata a dakinsu na hostel..... Duk da wannan gamin gogan so yayi ta koma gida da zama amma fulani tace bata san zancen ba ...tun farko mi yasa ka kaita makarantar kwana ..inka san daga bayan hanawa zakayi.... Babu yanda ya iya dole ya hakura ...suna sauka motoci suka zo daukan su .......daga nan ma gidanshi na sabon gari suka fice ..... Itade batayi magana ba duk da ta kagu taga kawayen wato Mufeeda da Mariam dan tayi missing din su..sosai..... Washe gari Dimanche ce .dan haka nan gida ya wuni yace se yamma ze koma ...duk tabi ta kagu ya fice ko taje taga amies(friends)dinta... Jirgin shida na yamma ze bi dan haka biyar nayi suka futo da zumar zata rakashi aéroport se driver ya kawota school din ...... Suna mota se shagwaba take zuba mishi ya kasa fitowa a motar har aka fara kiran yan tafiya... Da kyar ya lallaba ya tafi... Haka driver ya kawota school din Duk ranta ba dadi amma tana ganin su Mufee da manta da wata damuwa suka shiga murnar ganin juna..kusan kwanan hira sukayi.... Allah sarki Murad shikam kusan kwanan ido biyu yayi besan haka ya shaku da yarinyar nan se yanzu a ranshi yace gwanda na tafiyata wajen aiki ...da kyar dai bacci barawo ya saceshi... Maysam ma seda ta kwanta ya fado mata a rai se taji duk ba dadi..... Washe gari suka shiga classr(aji)dayake ba'a wasa tun ranar suka fara daukan lecture Murad kam yana gama break ya kirayi Mahmud... Bayan sun dan taba hira yace yauwa dama ina so kaje kamumun booking din ticket zuwa England .gobe nake son komawa... Mi Mahmud zeyi inba dariya ya kuwa kwashe da ita yace kai amma fa baka da ta ido ....ashe daman zaman taya matarka vacance ne kayi .kawai daga tafiyar ta jiya se yau kace wai zaka wani tafi ..ya kara wata dariya.. Takaici yama habashi magana kawai se ya kashe wayar yana fadin dan sa ido kawai....... Awa guda Mahmud ya dauka ya kawo mishi ticket din yana mishi tsiya shide be kulashi ba yayi fice warshi direct bangaren fulani yayi ....tana kishigide bayinta wasu na mata fifita ,wasu na matsa mata kafa..... Yana shigowa fulani ta sallamesu..zama yayi suka dan taba hira ..can ya sako zancen tafiyarshi.. Shiru tayi na dan lokaci...can kuma setace Allah kaimu goben..amma dan Allah kada kayi irin na wancen gamin nan tayi mishi nasiha....yayi tsammanin ko zata hana ma... Da dare ya sanarwa da Dadynshi ...shima fatan alheri yayi mishi tare da addu'oi... Washegari yayi tafiyarshi cike da kewar su fulani more exceptionnel Maysam... 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 Maheeba kuwa se jin tafiyar Murad tayi ba karamin tashin hankali ta shiga ba ..nan fa taga samu taga rashi...ta kuwa azawa Waziri rigimar se sun koma wurin Boka jin miya jinkirta wannan abun... Babu yanda ya iya haka suka shirya han se wajen Yankan wuka. ........ Tofa koya zata kaya kuma ?ku biyo ni dan jin cigaban..... Fans nasan kuna yi min uzuri amman ku kara akan nada ..kwana biyun nan se a hankali..need your prayer... Love yo all ❤❤😍😍 For correction or contribution +22799951593 Fasma🖊 [24/07 à 12:28] Fasma 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿63__64 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''Duk wanda karshen zancen sa ya zama La'ilaha illalahu ce lalle zai shiga aljanna'' Abu Dawuda ne ya rawaito shi.``` Babu yanda waziri ya iya haka suka shirya han se wajen boka yankan wuka.... Suna isa kafin ma su zauna boka ya kwashe da dariya ......bayan sun zauna yace base kunyi bayani ba nasan mike tafe da ku to ina so ku sani mu muna aiki da hatsabibun aljannai ne....... Caraf Muheeba ta amshe da fadin to mi alakar jinkirta bukartar mu da aljanai kuma... Wata dariyar ya sakeyi se da ta tsorata yace to ai saboda a watan Ramadan an daure su aman yanzu kam zasu iya yin komi(kuji wani jahilci kamar shi keda mulkin duniyar....,Allah ya kara karemu daga halaka ameen) ..yace.ku koma gida kawai kwanan nan zakuji bayani..nan suka shiga murna tare da godiya ...kudi suka sake zube mishi wai a sayawa aljanai jini dan su kara jin kafin jikinsu.(hum Allah de ya shirya .....kowa de yayi ta gari dan kansa koba haka ba my Arfat😉...) Nan suka dawo a karo na biyu zaman jiran asirinsu yaci..Muheeba kuwa har ta fara training din yanda zata dinga tsala rashin mutunci in ta hau garakal mulki ........ 🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 Madina kam sosai ta saka ido dan ko yanzu yan leken asirin ta sun kawo mata labarin waziri...ita kade tasan irin muguntar data shirya mishi lokaci2 Madina ke sakin murmushi ita kade... .... Wannan kenan Murza kam a can qauye abun ba sauki se abunda ya karu tana yar cokala gurguwar kafarnan ta zame ma yan garin annnamimiya se hada fadace2 tace ...Malam musa kam yanzu har kunyar fita yake cikin jama'a ..gashi kuma ya kasa sakinta ..shide addu'ar shi kullum Allah ya kara karesu shi da diyarshi Maysam daga sharri Murza gashi kumata ci alwashin se ta raba auren Maysam ko ba dade ko ba jima ... 🌹🌹. 🌹🌹 Satin Murad daya kacal ya ji duk garin ya ishe shi bashida wani buri daya huce ya ga ,Maysam kai shi ko baze ganta ba to ya ji koda muryarta ne. ..tun isarshi da kwana ukku zuciyarshi ta fara mishi zogi zut2 tun yana share abun har ya fara zama sérieux..... Ita kam tana can karatu suke ka'in da na'in itada kawayenta ba kama hannu yaro....... Yau kam tunda ya tashi ya shirya ya tafi office ya kasa yin komi gashide a office din amma ya kasa duba koda patient daya ne ...gashi rythme din zuciyar ya rage gudu ga wannan zut3 din ya dada da karuwa ba shiri ya daga waya ya danna number offishen makarantar... Suna tsaka da cours ya kira offishen wai yana son magana da Maysam ... Basuyi kasa a guiwa ba suka kirata tunda sunga lumbar ta Englace ... Tana zuwa tayi sallama a nutse tare da farin ina wuni Mom ,ya gida ,,kai amma nayi missing dinku ba kadan ba ,,ni fa.. Katse ta yayi da fadin to sarkin surutu ya isa kaka nine ba momyn ki ba. Wai ke inda aka kira bara ki tsaya kiji waye ne ba se ki hau zuba zance ne ...da Sauri tasa hannu a bakinta kamar yana ganinta tace yaya ''suis désolé (am sorry) baran kara ba...se kuma tace Bonjour comment vas tu?(ykk) da fatan ka isa lfy ... Tun lokacin zuciyar ta dan rage zut3 din har wata Yar dariya yayi seda taji sautin muryar ya ce lfy yar gidan Momyn ta da fatan kema hama ... Ya cigaba da fadin dama na kirane naji ko kina karatu yanda ya kamata ...(jifa taku irin nasu 😉...) Dariya tayi tace inayi fa ...to yaya se yaushe zaka dawo har na fara missing dinka.... Se kawai yaji zuciyan shi ya dawo normal har A ranshi yace ke yanzu ne kika fara ni kam na...se kuma ya Katse zancen zucin da fadin a fili really kinyi missing dina ...... Cike da jin dadi tace sosai ma pls wannan karon ka dawo da wuri... Cike da wayo da dabara yace to ko zaki dayo nan ne da karatunn.. Waro ido tayi se kuma tace a'a nide na fison nan din ...... Shikenan comme tu veux(as your wish) ..ze sake wata magana tayi sautin cewa kai yaya muna classe fa kasa ka kirawo gashi kasa nayi missing din karatuna...seda ga baya im mutum be yi karatuba kazo kayi tayi wa mutum fada bayan har da kai cikin masu hana mutum karatun...tana wani turo baki kamar shantu ...lol... Budar bakin shi se cewa yayi sede in dama mutum bashida niyyar karatun to inba haka ba yan mintuna ne zasu sa mutum kasa yin karatu.....''peu importe(any way) se anjima sanna ki meda hankalin ki akan karatu in kinyi ta daya ni kade na san kyautar da zan miki... Wata dariya tayi har seda yaji sautin ta a take zuciyar yaji tayi wasai babu wannan nauyi2 daya keji bare zut3 tace Allah yayana da gaske ta fada cikin zazzakar voice dinta.. Seda ya lumshe ido , ya bude su yace sosai yar gidan Momy kede kawai ki dage da karatu...... Shikenan yaya sena baka mamaki in sha Allah ... Nan sukayi sallama kamar karya kashe yake ji amman dole ne yasa ya kashen ... Dama yana office dinshi ne ga aiki baje gaban shi ya kasayi tun safe baya jin kwarin jikin shi se yanzu daya ji muryar Maysam amma fa zuciyar shi ta raya mishi da dan kawai sunyi sabo ne har ya dan damu da ita..(oho de ) Tafiya tayi tafiya yau har wata biyu cur da zuwan su Maheeba wajen boka ......ita kam duk tabi tawani tada hankalinta Mahaifiyar ta kullum na rarrashin ta..... Yaude kama almara da dare MaiMartaba Sarki da matanshin wato Fulani da Madina suna zaune a bangaren shi ..yayi gyaran murya ...tare da fadin ina son yi wata shawara ne.... Su duka suka nutsu ya ce mi ze hana ma hada aure tsakanin Yarima Murad da Muheeba diyar waziri.. Caraf Momy tace ee fa nima na so yi muka wannan maganar amman tunda yanzu kai kayi ni kam na amince ... Wani uban tsalle da Madina tayi se gata a tsaye cuwa su kan su seda suka tsorata tace wannan ai bama maganar daza a daga aji ce tun wuri ku sake tunani.. Tsawa sarki ya daka mata tare da fadin wannan na rigaya dana yanke shawara ko kiso ko kar kisio wannan ya rage naki.. Fuuu ta fice ta barsu nan ita kade se huci take tace ni Waziri zeyi wa haka ?ni zeci wa amana ?tab ....zamu gani ti Washe gare a fada ,,kama daga waziri sarkin fada ,sarkin dogarai..etc.duk sun hallara Sarki yace da waziri jiya mun tatauna bisa kan diyar ka Muheeba.. Da sauri ya rusuna tare da fadin Allah ya huci zuciyar Allah de yasa ba wani laifin tayi ba.. Ko daya se ma alheri ina de fan Mi ze hana mu kara qarfafa dangartarmu ne na mu hada y'ay'a mu aure wato Yarima Murad da yar wajrn ka inde ha ba'yi mata miji ba... Waziri kamar ya mutu dan dadi yace to ai ko anyi mata za'a iya tadashi barema kam ba 'amata ba.. Aa'a babu kyau nema aure cikin aure..shekenan tunda batada se a hada ai.. Da sauri waziri yace wani hanzari ba gudu ba shi Murad din yana da sha'awar karin auren ne(wai tirjin da boka yace yayi ne..) Sarki yace to ai base yana ra'ayi ba ..kuma dole ne ya yarda da auen.. Kowade na cikin Fada se mamakin wannan al'amarin yake..nan akayi addu'a aka rufe taron.. Muje zufa fans Fasma ce🖊 [24/07 à 12:28] Fasma: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 _Godiya me tarin yawa zuwa ga Fans din Sanadin Accident ..hakika ina jin dadin_ yanda _kuke bibiyar_ book din _Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa__ ...😍.. *Da yawa daga ciki naga sakon nin na shawarwarin ku . .. *in sha Allah* *Zan gyara .ku sha kuri minku kawai kude ku ci gaba da kasan cewa dani* *Fasma....kuna da yawa Fans bazan iya zano ku ba amma ai* *kusan ina yin ku irin totaly din nan😍😍❤* *MAMAN SS sakonki ya isa ga Maysam tace tana yinki* **irin sosai din nan lol❤...Amma fa Maheeba* *tace a gaya miki ta shirya tawagan yakin ta* ... *Nide🤐...ido ne nawa...😁🤣..na gode da kulawarki* *kwarai Allah ya bar zumunci* .. *_Ohh My Zarbaby tu me manque déjà ..wish you a good journey na gode da kaunarki Rabbi ya bar zumunci* ....😍😍😍. _ Dedicated to My ZARBABY😍❤ 🅿65__66 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''yana daga kyawun musulucin mutum ya bar duk wani abun da be shafe shi ba '' Tirmizi ya rawaito shi.``` Waziri ya sake cewa ai baza ayi haka ba abari ayi da yardar shi.. hannu sarki ya d'aga mishi ya ce na gama yanke magana ku fara shirye shirye kaway nan da wata d'aya daidai da congé Noël(chrismaty ) kenan .. nan waziri ya shiga godiya tare da mikewa ya fuce da shoki ya isa gida koda ya sanar wa da Muheeba wani wawan ihu ta kwasa har say da biron da nike rubutu ya subuce mini ya fad'i nan fa suka wuni cikin murna Muhiba kam harda fara yanda zatayi yafiya da kasaita take da wulakancin da zata ma mutane Shirye shirye kam ya kan kam yau har saura ''deux semaines''(sati 2) inda ango da Maysam basu ma san waynar da ake toyawa ba kay dama gari duka dan ko carte ba a bugu ba yan gidan su Muhiba da sarki kaday suke shirin su inda ita Muhiba har mai gayran jiki ta dauko dan a cewarta ta fi so ta fito yass da ita wai ita a nufinta tana so ta fi mai kama da aljanun nan kyau ni ko nace maysam ko batayi ado ba ta fi ki kyau ko ba ha ba fan???🤔🤔 Ana haka ne Sarki ya kirayi Murad bayan ya gaishe shi Se Sarki ya sako zancen auren shi da Muheeba yanda kasan wata saukar guduma haka yaji a kanshi a take ya dafe setin zuciyar yanainnalillahi..hi .......Sarki ya ci gaba da cewa kuma ina so satin me kamawa na ganka garin nan ... Da kyar ya iya hada kalmomin shima da kyar ya fara fadin pls Dady kar... Da sauri sarki ya katse tare da fadin inde har na isa da kai to ina so kayi mun biyaya..... Allah ya zaba muna abunda yafi alheri shikade Murad ya iya fadi..... Sarki na yanke kiran Murad ya yanke jiki ya fadi a sume..... Shigowar Mark kenan dan yayi ta kiranshi a waya baya dauka gashi yana son ansar wani doc me mahimaci shi ya sama ya tako ya zo gidan..... A sume sheme2 ya ganshi nan fa hankalin shi ya tashi bayan ya kirayi ambulance se kuma ya fara bashi ''premiers soins(first aid).... Da kyar ya samu ya farfado ambulance na zuwa aka fice da shi emergency.. kwanan shi daya yana jinya Allah ya tashi kafadarshi...tun agadon ya kirayi fulani .....tana dauka ya kuwa fashe mata da kuka kamar ba yarima Murad... Nan da nan jikin fulani yayi sanyi tasan abunda yake yiwa kuka nan ta lallasheshi tare da mishi nasiha kan yiwa iyaye biyyaya ..... Nan Murad ya ji zuciyar a kashi 100 ,,kashi 40 na damuwar dayake cikin sun ragu ...... Ita kam fulani bata san mi ya sa ma take goyon bayan auren nan ....barema yanzu dataji har kwanciya yayi a asibiti dan tasaan irin yanayin ciwon shi in ya tashi har fidda tsammanin shi ake ...gashi ita bakin ta yayi mata nauyi sosai baza ta iya cewa bata son ayi auren nan ......... Murad yace Momy Maysam fa?? Dan shiru tayi na yan dakika se kuma tace itama ba'asanar mata ba......dan bansan yanda zata dauki lamarin ba ...ina son yarinyar har cikin JININ JIKI NA na ke jinta dan bazan so taji wannan zancen daga bakina ba amma dayake kai mijinta ne se ka lallabe ta ka gaya mata... Momy kawai a barta base an sanar mata ba dan ni kai na baza....se kuma yayi shiru.. Nan sukayi sallama... Haka momy ta shiga saka da warwara ta rasa ya zatayi da Maysam.... Hakade ta daure ta kira offishen bayan an bawa maysam wayar ,nan fa maysam ta shiga zuba taji Momy se surutu take mata...can de ta tsageta tace Momy lfy najiki shiru yau ..,...? Fulani daurewa tayi ta sanawar da Maysam komi bayan tayi mata nasiha me ratsa zuciya .... Tunda Momy ta fara magana taji wani abu ya tokare mata wuya ,....da kyar ta tara nutsata ta nunawa fulani ba komai ai kuwa fulani na kashe wayar ta fara ganin dishi2 nan ta sulale itama kasa a sume....nan da nan akayi emergency na nan clinik din makarantar aka shiga bata temakon gagawa .... Murad kam suna gama waya da fulani ya dannawa Mahmud kira ..yana dauka ko gaisawa basuyi ba Murad ya fara magana cikin huchi yace wly kada ka sake ka bugo min katin auren nan kai kar ma ka fadawa kowa .....dan ni bani da tsarin auren mata biyu amma tunda su Dady sun rantse se sun min auren dole shikenan amman pls''je t'en supplie'' kada kayi komi ka barsu kawai in ya tambaya kace ee kayi ..haba da girma na da wayo na ace za'ayi mun auren dole har so biyu.... Ganin yana famar sauka daga kan layi yasa Mahmud taro shi da nasiha ...nan sukayi sallama tare da alkawarin baze yi shirye2n komi har se yazo... Suna gamawa ya danna wa offishen makaranta su Maysam kira amma mi se aka sanar dashi ai batada lafya ...dafe da zuciya yake tambayan mi ya sameta... Sukace ai tana emergency room basu fito da ita ba.... Nan fa ya lallaba batare da sanin Mark ba ya shige office din shi dayake a likitar daya ke aiki ake mishi traitement ..... Takardar neman hutu ya rubuta tare da cike kaf wani file dayansa za'a bukata bayan bayan nan.....direct da kanshi ya kai office din babba su ...dayake sun san yana da matsalar zuciya kuma abunda yake da bukata kawai gida ...ba tare da bata lokaci ba yayi mishi signé ya bashi dan su can suna tattala da taka tsan2 kan rayukan yan adam .kun de sani base na bata lokaci ba ...ko ba haka ba my Momyn Hajia😉... Direct aéroport ya fice amma cikin rashi sa'a be samu flight me tashi yau ba....shi so yayi ma ya dauki hayar jirgin gaba daya inde zasu kaishi se su ka nuna mishi ai abun ba daga nan take ba .....hanyar ce ke cike ga iska me karfi ...ga gajimarai .....Dole yayi hakuri ya dawo zuciyar shi kam banda lugundan zut3 babu abunda take moshi...kira kuwa yayi yafi a kirga amma maganar dayace tana emerjency..fada da masifa kam malaman makarantan sun shashi duk da sun sanar mishi yaune kawai amma se bala'i yake zuba a duk kiran da yayi..musu.. Kai bama su ba hatta Mahmud seda yasa shi zuwan Maradi babu shiri dan a yanda yake mishi magiyar yaje ya gani mi ya sameta ...har seda shi kanshi Mahmud din yaji tausayin shi....... Be tsaya nan ba nan ya kira fulani ya daga mata hankali ita ma ..ta kirayi makarantar suka jaddada mata ..direct ta nemi izini wajen mijinta sarki dare da fada mishi lalin da ake ciki...beyi wani gaddama ba ya sa aka shirya musu jirgi itada Mahmud daya zo sanar mata da ciwon Maysam din tare tafiyar Maradi .....abu nasu kan kace mi 10min har gasu a Maradi ..direct motocin dasukazo daukan su Clinik din makarantar suka fice... Har lokacin babu wani good news ... A bangaren Murad kuwa se hawaye yaji ya fara zarya a idon shi(haba kada ka bada maza man ....eh man😏🤨 )nan ya shiga tunani kada fa ya je ya rasata l Kamar yanda ya rasa SWEETBABYN shi...yana nan har aka kira magarib babu new .. Se bayan sallar isha'i daya sake gwada kira ya koyi sa'a ya na kira Mahmud yana dauka ya bawa Maysam dan ta farfado za a kaita dakin futu.......... Cike da zakuwa yace Mahmud how is she now..,? Muryar kawa taji se jin wani sanyi ya ratsa zuciyarta ita kanta tayi mamaki hakan ..tace yayana am fine now .. A tare suka sauke Wata sanyyayar da lallausar ajiyar zuciya ..kuma se suka saki yar dariya lokaci guda ...yace wai miya sameki ne.. Shiru tayi ..se can tace nima de ban sani ba kawai de s.... Momy ta karbe wayar tare da fadin haba Son ''elle as besoin de se reposer ...so ka bari in ta huta se kuyi maganar ...marerecewa yayi kamar tana ganin shi ya fara zubo mata shagwaba....ganin yana son rinja yarta yasa ya kashe wayar... Itama oganiyar bata so fulani ta katse su ba ........ Washe gari kam asubanci yayi ..karfe tare jirgin su ya keta hazo... Safe a good journey Murad.. Love you all..❤❤ Fasma🖊 [24/07 à 12:28] Fasma: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿67__68 ```Manzon Allah(SAW) yace''lallai Allah ta'ala ya haramta wa wuta cin naman wanda yake fadin ''La'ilaha illallahu''don Allah'' Muslim da Bukhari ne suka rawaito shi``` . Washe gari kam asubanci yayi ..karfe tara jirgin su ya daga se Niger......direct Maradi ya sauka .....Mahmud kawai ya san da zuwan shi shima se dan ya zo daukan shi ne..... Momy na break kawai se jin salamar Murad tayi ...ba karamin mamaki tayi ba .. Koda ya shigo direct bakin gadon da Maysam ke bacci yaje ya zauna abunshi ....kura mata ido yayi yana kalonta seya ga ta rame mishi......dukawa yayi yayi kissing din goshinta .... Mahmud da ya shigo yanzu ya duka ya gaida Momy ya tambayyi ya me jiki .......duka cike da mamaki take amsa mishi ta nuna mishi Murad ...... Mahmud dariya yayi yace to idan ka gama rashin kunyar seku gaisa da Momy..ko. Waro ido yayi yana kwallon wurin da Momy ke zaune dan fa shi har ga Allah be san tana dakin ba ...idon shi ya rufe kawai wajen son ganin Maysam... Se kuma ya zame ya zauna kusa da Momy yana aikawa da Mahmud sakon harara...... Mahmud yayi musu sallama ya fice abunshi yana meyi wa Murad gwalo.... Kicin2 yayi da fuska .......yana sosa kai yake gaida fulani ya kuwa sadda kai kasa..... Fulani har cikin ranta taji dadi ganin hankalinshi ya fara kwantawa da kuma karkata zuwa Maysam ..... Murmushi tayi ta shafa kanshi tace sannun Son kasha hanya fa ...ga break nan kayi dan da alama direct nan ka sauka..... Yana fa jin yunwar amma dan shagwaba ya saka kayan break din gabanshi amma yaki zubawa... Fulani ta gane shi sare ta kyaleshi ....tace zuba mana kaci... Shagwaba ya shiga zuba mata wai shi baze iya serving din kanshi ba........ Suna haka Maysam ta fara buda idannuta da addu'ar tashi daga bacci ta tashi ta sauke ido ta tar bisa fuskar Murad .... Itama bata wani lura da fulani ba tace yayana ....tana kokari saukowa... Da sauri ya isa bakin gadon suka rumgume juna ... Se Maysam ta fashe mishi da kuka .... Tashin hankali da sauri ya dora ta cinyar shi yana tambayar ta mi ya same duk ya wani kidime.... Cike da shagwaba tace ba kai bane.. Ni kuma ya nuna kanshi cike da tsoro dan shi besan miyayi mata ba...yace mi nayi to... Shirme irin na Maysam se cewa tayi bakai ne kayi tafiyar ka ba ni kuma nayi missing din ka.. Dariya yayi har da dan sauti yace to shikenan ai gani nazo ko .... Dogarai dake tsaron kofar dakin suka cika da mamaki jin dariyar Murad nan fa aka shiga kallon kallo dan su manta da suga murmushin shi tun kafin suyi wannan Accident din da SWEETBABYSHI ta rasu....wanda suka jima a masarautar kenan ....sabbi zuwa kam cewa ma suke baya dariya .. Dora kanta tayi bisa kafadarshi tare da fadin sannu da zuwa yaya... Karan hancinta ya ja yace yauwa yar gidan Momy... Tana dariya jin sunan daya kirata dashi ai kuwa daga idon da zatayi sukayi ido hudu da fulani .... Waro ido tayi sekuma cuwat ta yi tsaye ...ta sadda kai kasa ... Shi besan mi ya sata yin haka ba ...se ya fara kokarin meda ita bisa cinyar ... Nan fa ta fara tirje2 tana fadin kin ganshi ko Momy ...ni ka kyalleni.. Gumtse dariyar data taso mishi yayi ganin wai kunyar Momy takeji.. Sake mata hannu yayi ..da sauri taje kusa da Momy ta zauna kai a kasa ta kasa dagowa ..tace Momy ina kwana... Itama fulani dariyar tayi dan abun nata abun dariya ne..tace lfy lau ya kwarin jiki ... Murad ya ce daga baya kenan seda kika gama rashin kunyar taki zaki wani zo kisa jin kunya.. Shure2 kafa ta fara tana kukan shagwaba .. Fulani tace a'a kyaleta daga zowa kada ka takuran yarinya... Gwalo tashi ga yi mishi jin fulani ta goya mata baya ..yun kuri yayi kamar ze kamota .. Da sauri tayi hanyar tolet ta tana fadin momy barin wanka .. da sauri shima yake shirin mara mata bayan ..fulani da tayi kasake tana kallon shi ..wannan rashin ta idon har ina ....ganin fa da gaske shiga zeyi ya sa fulani tsayar dashi da fadin to barin in barmuku dakin nan ..tun kan abun yayi nisa.. Cike da shagwaba yake fadin haba Momy tayata ne fa zanyi ...saboda batada lfy ... Murmushi kawai tayi tare da girgiza kai ... Koma wa yayi ya zauna yana ta zuba wanda duk yawancin maganar Maysam ce.. Tajima ciki har Murad ya fara korafin da mitar cewa kada fa aje ko zamewa tayi ..ko .... Itade fulani najin shi bata tanka ba ... Tana fitowa daure da towel dinta da hidjab .....shi da kanshi ya shirya ita... Ya jayota ya zaunar suyi break tana kokarin serving dinsu ...Murad bako kunya ya rike hannun Maysam din yace bari na zuba mana ke da bakida lfy... Shiyayi serving din su kuma shike bata a baki .. Fulani a ranta tace ashe dama shakiyan cine ..zama ka iya serving din.. Ganin abun bana karewa bane se ta hau waya ..da sallama ta fara ..suka gaisa da alama de mace ce...sun dan taba hira take sanar mata da gata a likita ma matar Murad ce bata ji dadi ba .... Matar ta jajanta mata ...fulani tace yanaki jikin ...? Tace to alhadulillah Can kuma se ta bawa Murad wayar yana karawa bayan ya gaisheta ya shiga zuba mata shagwaba har tafi wacce yake yiwa fulani..najide ya kirata da Mom..... Ita kuwa Mom din ta lalace wajen lallashi ... Daga baya ya bawa Maysam wayar ya cemata Mom din SWEETBABY nace a... Hannu na karkarwa ta amsa tana nanata sunan cikin ranta dan ita jitake yana nufin yarinyar da ze aura ce SWEETBABYN..... Sallama tayi tare da gaisheta.. Muryarta kawai Mom taji amma seda gabanta yayi wata irin mummunan faduwa ..da kyar ta nutsu ta amsa mata ..tace ya jiki.... Tofa the same Maysam taji itama..da kyar tace naji sauki alhadulillah... Mom tace yaya sunanki ne.. Maysam sunana se kawai ta tsinci katan ta son yi kuka wanda bata san dalili ba.... Ganin haka yasa fulani karbar wayar ..itama muryar Mom din duk ta sauya ...nan sukayi sallama .. Murad ya goge mata hawayen da suka zubowa yace mi yasaki kuka.. .... Babu komi kawai tace dashi Wunin ranar anan sukayi shi...Maysam taji sauki sosai ganin Yayanta kusa da ita amma kasa zuciyar ta tana son sanin wacce ce Mom da Kuma Sweetbabyn nan.... Irin rigima ta Murad ta aka basu Sallama ya kuwa turbune sede Maysam Ta koma gidan su na nan Maradi .duk da daman wannan satin za a sake su hutun chirsmate(Noël).. Fulani ma turbune wa tayi ganin in ta biye mishi suka koma gidan kada soyyayar su yasa su manta ma da ta na school.....kuma gashi tayi2 su huce tare yaki yace se ya cinye satin shi anan ...haka Fulani ta koma dan cigaban shirye2 auren ... Murad na ganin tafiyar Fulani ya je ya doko Maysam suka ci gaba da rayuwar su irin ta yaya da kanwa masu ji da 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹 Abangaren Madina kuwa taci alwashin hana auren nan tunda har waziri yaci amanar ta ....jakadiyar ta tura musamma garin su Maysam wajen Murza kan tana son ganinta.. Murza ta kuwa yiwa Malam Musa karyar za'ayi wa Maysam kishiya zata tafi amatsayinta na uwa (ni kuwa nace kode UWAR RIKO ba ..littafin Momyn Mufeeda 😍) Bangaren fulani ta sauka dan kauda duk wani shakku ..lokacin Fulani na can Maradi ma...Murza..seta saci kafa ta faki idon mutane ta shiga bangaren Madina... Nan Madina ta kwashe duk irin cin amanar da waziri yayi musu... Murza har kukan bakin ciki tayi wai taga samu taga rashi ..ta kuwa share hayenta tace ki kwantar da hankalin ki akwai wani sabon Boka wai shi Matsafi aikin shi shi yakan Adda ne bama wuka ba... Madina tayi wata dariyar mugunta tace aikin ki yana kyau shiya sa nake son haraka da ke... Kudi ta zube mata tace kuma kice a kashe mana shi ma gaba daya ..in hakan bata samu ba ...to ayi muna irin na wacen ....a tura shi can kasar da baya dawo ba... Murza ta fice ..daga nan ma wurin bokan ta fice ...kai gaskiya fa wannan yafi wacen zaman hatsabibi da shu'umanci. ..... Bayani Murza tayi mishi bayani ta zube mishi kudi.tare da gaya mishi irin aikin da suke bukata... Wani kulli magani ya bata yace wannan a zuba akofar da shi Waziri ze tsallaka ..kuma yabata wani yace wannan kuma a zuba mishi a bun sha ....yana sha aiki ze ci dan daman kwarjini ne yake musu.. Ya basu wani yace wanan kuma a turarashi da zarar Murad ya shiki hayaki ..yanda hayaki yabi iska shima haka zeyi.....ya kwashe da dariyarr...yace ga dubara ta nunawa Waziri komi ya huce seta cuceshi daga nannnnnnnnnn..(jifa...Allah de shitya) Cike da Murna ta kawo wa Madina wannan labari ta bata magani ta komawarta kauye cike da kayan alheri da Madina ta bata...dan har lokacin Fulani bata dawo . ... 🌹🌹🌹. 🌹🌹 ba🌹🌹🌹🌹🌹🌹 A bangaren Murad kuwa saukar QURAN ya saka ana mishi anan Maradin tare da bada kudi makarantu da massalatai dan yi mishi addu'a ganin abun akwai tambaya ciki tunda ba tun yau ba ake son ya aureta amma daya nuna bayaso ba'a matsa mishi ba se yanzu rana tsaka a tilasta mishi...shiya sa yayi haka koma de minene to yazo mishi cikin sauki.... Haka Har suka cinye satin su kullum shida yar gidan Momy...wanda yayi saura kwana takwas auren shike kaita school ya medota ......Mufeeda da Mariam ma ba'a barsu a baya ba ..lelanta suke kamar mi..?da aka sake su ma hutu ma kamar su bita suke ji da kyar suka rabu.. Lokacin da zasu tafi so tayi taki binshi dan bazata iya jurar ganin auren shi ..amma matsa matan da yayi yasa ta biyo shi .dan dole... Koda suka zo ma beyi wani yunkurin yin komi ba....kuma da alama ma bashi da niyyar yi Murna kam ku san kashe Maheeba tayi ganin Murad yazo ita har ta ga an daura ..se wani d'ada'aga kai take wai ita a dole futur wife din yarima me jiran gado. A yaune kuma Madina take shirin aiwatar da kudirin ta.. Love all fans😍 Fasma ce🖊 [24/07 à 12:28] Fasma: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Ho.ho.ho MIMSQUEEN hamshakiyar shahararar marubuciyar ..ina murnar tayaki karasa littafin ''KARSHEN ALEWA KASA ''hakika kin nishadan tar damu kin fadakar damu ..Rabbi ya kara miki daukaka .da Baseera tare da zakin hannu ..sosai muka ji dadin littafin nan Readers kada kubari abaku labari ...zamuyi missing dinshi ..Amma abun murna da farin ciki shine muna nan tare dake a KALAR TAWA UWAR wanda shima ya dauko dadi and other dazasu biyo baya..muna biye dake ..love you irin totaly din nan.* 😍❤❤❤ Dedicated to all my fans😍❤ 🅿69__70 ```Manzon Allah (SAW) yace''kauracewar musulmi da dan uwansa musulmi kamar zubar da jininsa ne'' Ahmad ya rawaito shi``` . Hakan kuwa akayi Madina tasa akayi mata Kiran waziri ...dede kofar shiga falon ta kuwa barbada maganin ,,,,da farko yaso yaki zuwa amman ganin in betafi ba zata iya kulla mishi wani sharrin yasa ya tafi amma a ranshi fadi yake komi za'ayi sede ayi amma bazan biye mata ba kan auren nan ...tunda aka zuba maganin aka hana kowa shigowa bare fita ....bakam2 waziri ya shigo babu wata bismillah sallamar ma se da ya tsallaka har ya tura kanshi sanan yayi ta ...(a raina nace ai kuwa hakan be dace ba kana namiji ke koma macen ..wai se ka tura kai cikin falon mutum tukon zakayi sallama..kasan a wani hali zaka tarar dashi..ne... Ko dayake may be daga wazirin har Madina basu karanci hadisin ma'aiki SAW daya ke cewa''baya hallata ga musulmi ya leka gidan ko dakin wani ba tare da izini ba..Bukhari ya rawaiti shi.... ...kuma ai ita madina ta sake mishi fuska har haka) tunda ya shigo yaji jikin shi ya saki haka ya karaso ya zauna .. Madina ta shiga tsarashi cike da makirci da nuna cewa komi ya fice a wajenta har da nuna jin Dadin ta ga wanna auren koma ta na goyon bayan shi kan abunda yayi Wai shi me diya ..se kawai ya saki jiki da ita nan ya shiga ga zayyana mata yanda auran ze gudana ... Madina daga kasa se dariyar mugunta take mishi kai daga karshe ma tace ta dau nauyin kayan dakin amariya ... Abunda ya kara tunzura waziri da yarda da ita ....kamar gaske tasa aka kawo mishi lemo . abunka ga wanda murna ta cika shi ya ma manta da Madina ce matar Sarki ...Kawai be kawo komi ba ya bude cikinshi ya kwankwadi lemun shi .....yana gamawa sega kiran wayarshi ya shigo ...Maheeba ce da sauri wai yazo zasu kara tattauna wa ya fita tare da yi mata sallama ... Yana fita Madina tayi wata makirar dariya tace dani kake zancen ... 🌹🌹🌹 A bangaren su Fulani kuwa ita da Sarki suna zaune suna hirar su dan tunda akayi maganar auren Murad da Maheeba ya sa Madina ta dena shigowa .akai2 ...suna tsaka da hirar Fulani tace daman akwai wata magana dana ke son muyi akan auren nan ...a gaskiya yanzu bana goyon bayan auren nan kai hasali ma nifa ban masan yanda akayi na amince ba ba ...kuma ....jiya da dare kawai nayi wani mummunan mafarki kan auren nan ...nide gaskiya a fasa tunda de ko kati ba'a buga ba bare ace garin yasan mi ake ciki ...kuma ko jiya jiya nan da safe babu irin magiyar da be munba ...kasan kuwa har kwantar da shi akayi a england ciwonshi yayi wani mummunan tashi Allah de kawai yasa da sauran kwanakin shi nan gaba ...da yanzu mun ras ...se kawai ta kasa karasa kuka yaci karfinta .. Sarki ma hankalin shi ba karamin tashi yayi ba ..yace nima de kin sosa mun inda yake mun k'ayk'ay dan har ga Allah bazan ce ga yanda abu ya faru ba kawai de na tsinci kaina nane da amincewar auren ....amma yanzu kirawo mun shi a waya shi Murad din muji ta bakinshi... Kallon lokaci tayi taga goma har gifta amma dayake maganar me mahim manci ce yasa kawai ta danna mishi kiran ... Lokaci kuwa yana bangarenshi shi da Maysam se shagwaba take zuba mishi kan seya kaita shopping gobe Se burgima take ajikin shi duk ta yakuna mishi kaya.. .shi kuwa ya kyaleta ne dan yasan yanzu babu idan zashi dare ne ...kuma shi badan baze iya kaita bane a'a kawai futar ce ma baya son yi kwata2 dan baya son ya gamu da wani ma Wanda ya san zancen wannan aure ... Suna haka kiran ya shigo shiit yace da ita ya dau kiran da sauri ganin lokaci ya san ''quelque chose ne va pas'' lamo tayi a jikin shi tana jira ya gama ta cigaba daga inda ta tsaya.... Cike da ladabi ya dauka ya gaishe da fulanin.. Bayan ta amsa tace ya zo nan fada dadyshi yana son ganin shi .... Da sauri Maysam ta shiga ta dauko mishi wata riga .jin Sarki nason ganinshi ...kuma be kamata ya fita da rigar nan haka ba.. ..lokacin data dauko har yakai kofar fita dan sauri.. .. Itama Da sauri tace yaya tsaya.. Ya tsaya tare da juyowa yana fadin minene kuma cikin fada.... Turo baki tayi tace to ba riga na kawo maka ka sauya ba.. Shi se lokacin ya tuna da rigarshi ashe duk ta yakune se kuma jikin shi yayi sanyi gani tayi fushi...karba yayi ya saka ita kuwa ta anshi waccar din tayi shigewarta wai ita nan tayi fushi... Girgiza kai yayi ya fice dan lokacin bashi da time din biye mata... Su biyu ne palon kamar yanda ya zata nan ya kwashi gaisuwa wajen dady ... Sarki ya ansa cikin sakin fuska ...se kuma yace dama game da zancen auren ka ne yasa nayi kiran ka Kafin ma yaji mi za'ace ya shiga bawa Sarki hakuri kan shifa baya son auren nan hasalima auren dole ne ake shirin yi mishi har da yar kwallarshi.... Sarki yayi jim yana kallonshi..can yace to dama dan mujine ta bakin ka ..tunda baka so baza ayi ba ..kana iya tafiya... Nan kuma hankali shi ya tashi dan jiyake ko yayi fushi ne...ya shiga bada hakuri .. Sarki yace a'a daman muna da niyyar fasawa ..to mun tambayaka ne dan kada aje ko ka fara sonta... Da sauri ya kalle shi yace ..so..?fa Dady ai ni so daya kawai nayi Shima wa SWEETBABYNA. Fulani tayi dariya a ranta tace ita kuwa Maysam din fa...kayi ka gama mude idone namu .. Sarki yace to shikenan kana iya tafiya Allah yayi maka albarka . . Nan fa kawai ya rumgume Sarki yana zuba godiya harda kwalar murna ... Fulani ma ta shafi kanshi tace hankali ya kwanta ko.... Cike da farin ciki ya fice ... Sarki ya kalli fulani yace wai ashe har haka yake kin auren nan jibi fa ko lokacin auren shi da Maysam be nuna kin amincewarshi ba haka.. Fulani tace ashede da mun cutar da dan mu da kanmu ... Sarki yace Allah ya kara tsare mu tare da yi muna zabi na alheri aduk lamuran mu Ameen fulani ta amsa . Wani sauri ya ringa zunkudawa kamar wanda ze tashi sama .. Yana zuwa ya ma manta cewa Maysam tayi hushi dashi kawai tana zaune se ji tayi yayi sama da ita yana juyi .. Itade tana mamakin miyasa ka shi murna haka take .. Yana sauke ta yace ''devine quoi? ''(Ci aruwa?) Tana turo baki tayi kalar tunani ...tace na baka gari Yace to an fasa aurena da Maheeba .... Be gama fada bama tayi wani uban tsalle me game da ihu ta dare bisan shi tana me jin dadin wannan abun... Nan fa dadi kamar ya kashe su ...ya kirayi Mahmud ya sanar mishi ... Shima ba karamar murna yayi ba . Murad yace ki shirya gobe mufita yawo ba shopping kade ba .... E fa murna ta gamewa Maysam bibiyu ... Can yace ta tashi ya rakata bangaren fulani .. Nan Maysam tace bata san zancen ba ..kawai dan yayi mata wayo ne yayi tafiyarshi shi kade ya barta...🙄ji wani shirme.... Be hanata ba ... Ta shige dakinta na nan bangaren tayi wanka tasaka kayan baccin ta ..ta feshe jikinta da turare kamar yanda fulani ta koya mata ta nufi dakin Murad ...shi lokaci har ya kwanta tazo ta makalkale shi wai ita tsoro take ji be cema komi ba ya gyara mata kwanciya ...duk da har yau inde sun samu contact body tofa se yaji electric shok din nan sede yanzu ba sosai ba..... Cikin dare biyu na dare Murad ya raba jikin shi da shimfidar ya doro alwala ya shiga nafilfili da addu'oi da godewa Allah kan wannan sauyi lamari daya samu .yasan daman addu'a bata faduwa kasa ..ko ba dade ko bajima ... Wajejan uku na dare itama Maysam ganin shi yana salla yasa ta tashi ta doro alwala ta shiga nafila . Ba su suka kwanta ba se bayan sunyi sallar asuba tare da yin azkar dinsu ....ta kuwa kara shige mishi jiki..bacci me dadi ya a won gaba da su Wayewar gari lfy Maysam et Murad...❤ Ina masoyan Maysam ku fito mu ganku. To😏.. Mi ye makomar Waziri da iyanlanshi ?kuma Ina yinku irin totaly din nan 😍😘 More you comment, more i typing ..❤ Fasma ce🖊 [24/07 à 12:28]Fasma 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 🎂🎉joyeux anniversaire my sam ..wish you all the best ..que cette année soit une année de bonheur, réussit et plein de succès.. Today is your day so profite bien.because ça ne vient qu'une seule fois par an🎂🎂hbd *Ohhh Allah ashe haka masoyan Maysam kukeda yawa ...😍😍hakika ina alfahari da ku ..Maysam na meka dubun* *gaisuwa zuwa ga fans dinta tace tana yinku irin sosai din nan lol..Fans wly* *kuna da yawan bazan iya lissafo kuba dan se na cika page din nan .😁❤❤.amma fa sako daga MUHEEBA tace kada ku sake hanya ma ta gama ku* .. *Mussaman ma ke Maman SS 😁 ...Amma fa tace na gaishe mata da masoyan ta mussaman My* *Zee😎😎(Zaynab Idris ba😜) tace tana yinki* 😂.. _Welcom back Momyn Mufeeda Allah ya kara lafy ya sa zakkar jiki ce ._ 😍😍 *My in law(Xaynap queen),,my Arfat,and Ummu Usman ,i miss you a lot pls come back soon 😭😭* Dedicated to yo my SAMBABY😍❤ 🅿71__72 ```Manzon Allah (SAW) yace''wanda duk ya yi imani da Allah ,da ranar karshe to ya kyautata wa makocin sa .'' Mislim ne ya rawaitoshi... ``` [ Washe gari da wani farin ciki marar misal tuwa masarautar mussaman oga Murad da yar renon shi Maysam.. Abangaren fulani ma duk jitake kamar an sauke mata wani abu akanta.. ..wajejan goma na safe suka fito cikin shirun su na fita yawon ...lokacin da suka shiga gaida Fulani ba karamin kyau suka mata ba sunyi matukar burgeta sun kuma dace da junan su matuka kai yau har wata kama ma taga sun mata ...bayan sun gaisheta ne yake sanar mata za su fita cikin gari ... Fatan alheri kawai tayi musu har da tsokanar Maysam take ..ita kam bada dariya da sunne kai babu abunda take ..gwanin ban sha'awa ... Dede zasu shiga mota Muheeba ta tsinkaye su fito warta kenan ...da sassarfa ta iso tana fadin good Morning my future .... Daga Murad har Maysam Kallon mamaki suke mata bama kamar Maysam ba data ke ma Murad kallon tuhuma ganin haka yasa shi Wayencewa da fadin morning too kamar me ciwon baki (to fa mulkin ya motsa )a ranshi kam dariyar mugunta yake yi wa Muheeba dan yana da yakinin bata ji labarin fasa auren nan ba...... Maysam kam ta cika tayi fam .. Dogarai kam suna ganin Muheeba suka zube nan se kwasar gaisuwa suke .. Cike da mamaki yake kallonsu a ranshi yace yaushe har ta samu matsayin nan ... Koda ya kalleta seyaga ita kuma se wani sham kamshi take tana wani dadaga kai... Shi abun dariya ma ya bashi Da fari su biyu kawai ya so su fita amma gani irin kallon da Maysam take mishi ya sa driver jan su cikin wata mota kirar Prado 2018...gaba da bayan motar kuwa an rubuta Yarima Murad12 .. Dogarai ma suka shiga motocin su Gidan baya suka shige suka bar Muheeba nan sake da baki ..kwafa tayi tace oho de kuyi ku gama kafin na shigo ...tana wata tafiyar ta ta kasaita ta shige part dinsu wai ita a dole ga futur wife din YARIMA me jiran gado .. Duk inda ta gilma to se kuyangi su duka har kasa su kwashi gaisuwa in ba haka ba su fuskanci hukunci... Kaf gidan babu me sonta kai hatta kuyingin ta sun gaji da halinta kawai dan dole suke mata biyyaya A mota kam Maysam anci kip ta juyawa murad baya tana kallon waje ta glass banda turo baki babu abunda take.... Shi kuma duk ya wani rasa nutsuwar shi ...driver ya bawa oder inda ze kaisu se kuma ya danna wani buton nan kusa dashi a take wani bakin ''rideau''(labule) ya rufe duka glass din motar banda da nan tsakanin su da drivern .gaban motar ne kawai babu labulen Murad yace ke!! .. har cikin ranta taji kiran sede batan amsa ba kuma bata juyo ba .... Nan fa shima zuciya ta fara dibanshi ya shiga mata fada wai mi aka mata dazata saka mutane gaba tana hushi ...da karfi ya sa hannu ya kama dantsen ta ya jiyo ta yace ke wai yaushe reni ya fara shiga tsakanin mu dake ne da har ina miki magana ki ki amsawa .. Mi Maysam zatayi inba kuka ba daman jiran kiris take ta kuwa fashe mishi da kuka dan wurin jiyo tan karfi yasa mata abunka da jikin daya ji hutu gashi abun dama ba wani kiba ba....sosai taji zafi a damtsen...tana kuka take murza wurin tare da fadin kayi hakuri bazan karaba... To fa an taba zuciyar maza nan shima ta fara yi mushi zut .. shima daurewa kawai yayi amma fa ji yake kamar yayi kukan shima besan miyasa ba baya son kukan ta ko kadan. ..... Rungumeta yayi ya shiga lallashin ta. Ga electric shock na ratsashi aman ya daure yana mata massage din damtsen.. Tsit maysam tayi dan tunda ya rungumeta ta ji wani électric shock wanda bata taba jiba a da.. Kokarin kwace kanta take amma ba rikon ragon namiji yayi mata ba ...dole ta hakura ga zuciyar ta data sauya rythme fat2..... Jin ta nutsu .yasa ya kwantar da ita ya shiga kokarin kissing dinta wanda zuciyar shi take kitsa mishi kan tana son dan karamin bakin nan ..shiyasa ma yake biye mata .. Maysam na ganin haka ta kauda fuskar ta gefe. juyota yayi .yana kallonta Ta kuwa rumtse idonta kam Jin an tsaya yasa ya fasa dan yana da tabbacin sun iso wurin shopping din daya bada oder akawo su... Maysam kam hamdala tayi ganin ya fasa dan ita tana ganin kazantar yin hakan.... Haka suka wuni yana kaita wuri2 a takaice de yau Maysam ta gama wa garin kallo ....se daf da magarib suka dawo inda suka tarar da labarin abunda ya samu waziri ....... 🌹🌹🌹. 🌹 Wato bayan futar su da kamar awa guda SARKI yane mi Waziri tate da sauran yan fada.... Shi kam lokacin ji yake ko an bugo kati ne ma..da sassarfa ya amsa kiran.. Fada tayi tsit kaf makaraban fadar sunan nan zaune jiran jin abunda me martaba zece dasu ....da farko se da yayi mu su nasiha tare da jan hankali..can de ya sanar musu cewa an fasa auren nan ... Be gama rufe bakiba Waziri yayi cuwat tare da fadin to baka isa ba ....aure kamar an yi shi an gama.. Nan aka fara kallon2 .. Sarkin hukunci har yayi wata irin wawura ya iso gaban wazir jiran umarni kawai yake..ya zartar Fadawon gaba daya suka shiga bawa Sarki hakuri Gyara murya sarki yayi fadar tayi tsit banda waziri daya ke fadace2 kamar wani sabon kamu...se wani fizge2 yake.. Da karfin tsiya aka zaunarshi amma bakin nan ya kasa rufuwa ..... Shiru akayi ana sauraron shi ..wai kun san mi fans? Gaba daya sirri shi dana Madina ya shiga tonawa kaf duk abunda sukayi seda ya fada da irin makircin da sukayi ...kan kace mi fadar ta kacame da hayaniya.. Gyaran murya sarki ya karayi bacin rai karara a fuskar shi ya bada umarnin da aje a tsare waziri har se an yi bincike akanshi ...dan abun nashi ba sauki da alama ma ya fa haukace... Lokacin da labari ya isa ga muheeba sumanta biyu da kyar ta dawo normal ...ga rashin cikar buri .ga waziri ya haukace abun ya game mata biyu ..mahaifiyar ta ma banda jimami babu abunda take.. To fa Abangaren Madina kam dadi kasheta ne kawai beyi ba dan ita jitake aikin bokan su ne yaci ....ranar kam bayinta ma sun san tana cike da murna ,,...tace kowa yaci tuwo dani to miya yasha harni ze ci amana ta kadan ma ya gani.... Sede tashin hankalinta guda ..shine yanda waziri yake fallasa asirinsu amma dayake ta jima tana makirci babu wanda ya zargeta ...dan tana nuna tana son Murad a gaban mutane so babu wanda zeyi tunanin ta aikata hakan... Gashi kuma an sheda cewa waziri ya samu tabuwar hankali da wannan take kwantarwa da kanta hankali.. Murad kam beyi mamaki ba dan dama yasan akwai wata a kasa ..Sede yayi addu'ar Allah ya qara kare su daga sharrin masu sherri. Haka rayuwa tayi ta tafiya yau sati cur da faruwa wannan al'amari amman jikin waziri se gaba yake yi kai yaneu har da bugo ma ya fara .. Bayan bincike me zurfi da sarki yasa akayi mushi a ka gano irin makircin da waziri da iyanlanshi sukai amma abun bakin ciki ba'a gano nasu Madina ba ...haka aka yanke wa su Maheeba hukunci barin garin itada su waziri bayan an yi musu horo me tsanani itada Mahaifiyar ta... Haka suka fito daga masarautar da kullin kayan su Miheeba se waiwaye take tana ma masarautar kallon karshe..Mahaiyar Muheeba fadi take duk ke kika jawo muna da baki kwallafa rai ba da duk hakan bata faru ba ..dama boka yace kada mu bari asirin nan ya karye ka irin ta nan yanzu mahaifinki ya haukace.. Muheeba kam kukan ta na rashin aure nan ne takeyi aka ma bata kawo da rashin lfy waziri .....keken naped suka shiga ze kaisu aéroport su shiga jirgin zuwa ghana wajen dangi su...dan sun kwaso kudi.. Suna tsaka da tafiya ..abunka da mahaukaci ya faki idon su ya karkata musu sitiyarin ..naped dun ..jikake katsam..sun gamu da wata babbar motar .....😳😨😨 Kuyi manage da wannan .. Fans nasan kuna min uzuri aman ku kara akan nada ....ina yinku irin more totaly din nan..❤ Yawon comment yawan typing❤😎 Fasma ce🖊 [24/07 à 22:39] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 73__74 ```Manzon Allah (SAW) yace'kumya tana daga cikin imani' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. ``` Jikake kwatsam sun gamu da wata babbar mota ....... Me babbar motar ya kuwa tsere ya barsu nan ... Gaba dayan su a sume suke ...da kamar minti goma me a dedetan shi ya fara farfadowa cikin ikon Allah be ji wani ciwo sosai ba se dan gurje kafa dayayi ...Muheeba kam da wani irin taratsi ta farka ...ganin ta nan shaye a kasa komi ya dawo mata ...kuka ta shiga rerawa gashi tana son tashi amma ta kasa wani irin radadi takeji a kafarta da fuskar ta ...hannu ta kai ta shafa fuskar wani razannan ihu ta saka jin wani bala'in zafi ga kuma jini ya bata mata hannun.. Wannan ihun shi yayi sanadin farfadowar Mahaifiyar ta ........ Ita kam da alama bataji ciwo ba itama se karayar data samu a hannu ...rarafowa tayi kusa da Muheeba ..nan suka shiga rera kuka .....ganin duk glass ya yanyakewa Mufeedar fuska kuma da alama kuma ta samu karaya a kafar hagu.....me adedeta kam fada ya shiga yi musu sun san mahaukaci ne miyasa zasu shigar me a dedeta ..nan ya dinga bala'i kan se sun biyashi adedetar shi.dan baze dsuki asara ba.... Ganin abun bana karewa bane yasa suka bashi. kudi me yawa .dan sun kwaso kudi ..ba ko kunya ko tausayi ya karbe a bunshi ...da kyar ma ya dan ja adedetar ta bar titi ..yayi tafiyarshi... Can Muheeba ta lura da waziri fa baya numpashi iya karfinta ta ce Abbaaaaa ..tana kokarin jan kafar ta isa...Maihaifiyar tata ta daure da sauri ta isa kusa da shi tana fadin waziri2 amma ina baya ko motsi .....daya ke sun kusa eareport din shiya sama babu gida je nan kusa ...baya ta koma cikin gari dan neman temako.....cikin sa'a ta gamu da wani me adedeta ...shima da farko ya so kin daukar su amma seyaji tausayin su ga kuma kudi me yawa da zasu bashi in de har ya kaisu cikin gari... Da kyar ya iya saka waziri a motar ...suma suka lallaba suka shiga ... dede wata clinik ya kaisu yana ajesu yayi tafiyar shi dan ma kada ace se yaje police station yayi reporte. .. Dayake abun na masu kudine nan danan aka anshe su akayi emergency da su ...akayi musu dorin karaya da duk wanin abun da ya dace...tare dayi musu allurar bacci dan su sami hutu... Lokacin da suka farfado daki daya aka kaisu..bayan doctor ya shigo ya kara dubasu har ze fice Muheeba tace ya jikin Abbana... Seda ya share gumi tukon ya fara yi musu nasiha sanna ya sanar musu cewa waziri ya rigaye mu zuwa gidan gaskiya Allah yayi mishi cikawa se de kuyi mishi addu'a dan har an bunneshi .. Wani irin ihu Muheeba ta saka se kawai ta sume nan.. Tashin hankali mahaifiyar ta shiga ga Mutuwar miji ga diya ta sume se kawai ta shiga rera kuka itama.. Can zuwa dare ta farka babu wata addu'a sema kiran Abbata datakeyi ..nan mahaifiyar ta shiga lallashin ta .... Tana kuka take fadin duk nice sila da ban nuna ina soba da duk haka bata faru ba gashi yanzu SANADIN ACCIDENT na rasa Abbana wanda na fiso ...ga kafata ta karye ..kaico na ni Muheeba naga rayuwa . Mahaifiyar ta shiga lallashin ya itama tana me tausaya wayar tata.. 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 To fa a bangaren Madina da Murza ba karamar murna sukayi ba dan duk ji suke aikin bokansu ne yaci...Murza harda zuwa yi mishi godiya tare da kara mishi kudi daga Madina..se kuma suka fara shirye2 yanda za suyi asirin ya kama Murad.. A bangaren su kuwa rayuwar jin dadi suke ...yana kula da ita matuka wai saboda Fulani taji dadi yake yi a cewar zuciyarshi fa.... Tana cika sati ta fara shiryen2 komawa ecole ..wannan gamin ma seda ya rakata har Maradin . Lokacin da zuyi bankwana shi ze dawo dan so yake washe gari shima yayi ficewar shi England.... Suna mota a aereport se shagwaba take mishi ..shi kuma se lallaba ta yake kan ta yarda suyi tafiyar su England .... Da farko har ta amince amma jin wai in ta tafi baza ta cigaba da karatun ta yasa tace ta fasa zuwan ..wai rayuwar can da nan ba daya bace...itade jinshi kawai take...se turo dan karamin bakinta take ...dan tana son karatun ta..gashi a islamiyya ma sun yi nisa Batayi aune ba taji Oga Murad ya shiga kissing dinta .... Tureshi take amman kamar batayi .dan mayen electric shok din nan se ratsata yake..shima wannan karon dauriya kawai yakeyi .....tun tana jin dadin abun har yazo bakinta banda zafi babu abunda yake yi mata. . Kokarin tura hannushi yake cikin rigarta(ni kuwa nace to mi ka aje ne a wurin kaida kace babu su🙄...)... Rike hannun tayi tana girgiza mishi kai kukan ma ya kafe.. Amman shi kam se kara turashi yake ... Ganin ana shirye2 fara kiran ma su tafiya yasa da kyar ta rabashi da jikin ta se haki take tace nide gaskiya2 ...se kuma tayi shiru..dan azahirin gaskiya bazatace ga abunda take jiba Yana mede numpashi yace kede gaskiya mine? Cike da yarinta da tsoro tace nide bana son wannan abun muryarta har sarkewa take Kuri ya kafeta da ido yace miye din bakya so ... Tace kawai se ayi ta durawa mutum miyau gashi bakin ma se zafi yake mun... Jim yayi can ya kalleta yace bade ba kya so ba.. Ta gyada kai.. Yace shikenan bazan kara yi miki ba.. Cike da yarinta kuma ta fada kanshi tana Merci beaucoup yayana(thanks alot).. Goshinta ya ma kiss sanna ya fita ...ya nufi wurin da ake kiran passengers... Tana daga mishi hannu har jirginsu ya daga ...duk kuma se taji ba dadi Driver ya dawo da ita school dinsu . suka hade da kawayenta nan suka shiga revision'(review)din karatun su dan shugaban makarantar yace inde har sukayi kokari suka kawo maki excellent to ze yi musu tsallaken Ss2 direct kawai suje Ss3 ..dan haka sun dauri niyar yin karatu na ban mamaki .. Haka Murad ya dawo jiki ba kwari dan be ji dadin abunda Maysam tace mishi bs. ..... Tun nan aereport din ya ciri ticket zuwa England gobe... Yana zuwa ya sanarwa da fulani f......fatan alheri tayi mishi Zuws dare kuma Yana sanarwa da me martaba zancen tafiyar Madina ta shigo karaf se akkunan ta ... Wata dariyar mugunta tayi ta koma bangarenta... Jakadiyarta wacce tayarda da ita ta bawa magani a turara mishi..tace tayi maza ta tafi yanzu kan ya dawo daga wajen sarki Cikin sa'a kuwa bata sha wuyar shiga bangaren Murad ba. ..nan ta turara tafice abunta.. Yana shigowa ya shaki kamshi .nan ya fara jin kanshi yana juya mishi tare da wani irin ciwo..sunan Allah ya shiga kiran ..se yaji abun ya lafa amma mi se yaji duk garin ma ya ishe shi ...gaba daya Allah2 yake gari ya waye ya tafiyarshi ...baccin kirki ma beyiba Garin na wayewa dama jirgin 9h ne ze bi ..dan haka tun takwas ya shiga yayi wa Fulani da Sarki sallama ...ya fice cikin sauri.. Fulani kam wanna karon ma a jikinta taji kamar ta hanashi tafiya .amma se ta bishi da addu'ar Allah ya tsareshi ya kareshi da duk wani abun cutarwa daga mutum ko aljan.. Madina dadi kamar ta mutu ..se boka ta ke zumbudawa albarka...(hum🤨.).... Bayan sati da faruwar haka.. Da dare Sarki da matanshi suna hira dan kullum su se zuwa dare suke samun ganin shi. .. Fulani tace dama akwsi wsta shawara dana keson badawa .... Sarki yayi dan murmushi yace ai ke duk dhawarar da zaki bada me amfani ce dan haka kafin ma naji miye na amince ... Fulani ma dariyar marar sauti tayi dan tana jin dadi irin confidence da sarki ke yi mata.. Madina wacce ta kullu jin furucin sarki tayi kwafa tare da yi tsaki kasa2 a ranta tace shiyasa a kullum tsanarta tske kara ruruwa a zuciyata. Se shegen iya kissa dan inta na wuri sarki mantawa ma yake da akwai wani a wujen ko a'a..shiyasa take mata lakabin makirar mace..dan gani SWEETBABY ma renonta ce kafin Accident shi ya sama Murad ya Makalkale mata ya kasa yakiceta daga rayuwarshi..(jifa wani sharri🙄🙄) Sarki yace ina sauraronki Fulani tace dama cewa nayi in baka zabi wanda zaka sa a matsayin wazirin ka mi ze hana a nada Malam Musa mahaifin Maysam ... Sarki yace kamar kin shiga zuciyata kin gani nima haka nayi wannan tunanin .. Fulani tace to ai dama ni cikin zuciyarka nake shi yasa na gani . tanayi tana wani sakin sharme...a tare suka saki ma juna murmushi.. Kutttttt wani malolon bakin ciki ya ziyarci zuciyar Madina ..ta daure de tayi gyaran murya dan ta hago wanni abun .. Itama cike da irin tata kissar tace wannan shawara tayi ..ina goyon bayan hakann....... Washe gari kam Madina ta sanarwa da Murza cewa sun kusa dawo wa nan dan haka sesu ci karansu ba babbaka.. 3 jours(days)da yin maganar Sarki ya tura sakon san ganin Musa ... Babu bata lokaci ya ansa kiran ..Murza kan se murna ake za'a kaura birni.. Bayan ya iso sarki yayi mishi bayanin kiranshi ...da farko ya so ya kiya amma se yaji baze iya cewa sarki a'a ba dan haka ya amince..ba karamar murna sarki yayi ba.. Kafin sati ya zagayo har sn nadashi sun kauro masarautar.... To fa Murza a masarauta kusa da Madina ..se yaya kenan..🤔 Love you all irin more din nan😍😘❤ Fasma ce🖊 [26/07 à 00:21] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Alherin Allah ya kaiwa masoyan wannan book din a duk inda kuke ..hakika* *ina jin dadin comment din ku kuma yana bani kwarin guiwa ...daya wa naga sakon ninku..wasu* *suna cewa ina jan aji da rai ..to bahaka bane muma muna da uzuririka a gabanmu .....Allah* *ya bar kauna da zumunci ina yinku iri more totaly din nan*❤😍😍❤❤ *Pls masu juyamun littafi ku dena bana so . ...kun san kanku base na tona ku cikin jama'a ba so tun kafin abu yayi nisa ku fasa ....* Dedicated to all my fans😍❤ 🅿75__76 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''babu d'a'a(biyayya)ga kowa cikin sab'on Allah'' Bukhari da Muslim suka rawaito shi.``` Murad kam fushi ya dauka da Maysam ..ga zuciyar shi na azalzalarshi kan ya kira ta amman yayi biris da ita seda yaji ta fara mishi zut2 din nan sanna ya kira office din ..lokacin sun gama lecture kenan ... Da sallama ta amsa .. Tu nan yaji wani mayen sanyi yaji a zuciyarshi amma wani bangare yana tunatar dashi cewa yayi fa fushi da ita .. Dan haka Amsa sallamar yayi a dakile kamar ba shine ke daukin kiran ba. Cikin sanyi jiki ta gaishe shi tare da tambayar ya aiki. . Da kakkausar murya yake amsa mata fada2.. Maysam ta sake cewa yaya mi akayi ne ?ko nayi maka wani laifine,? Cike da kaguwa cikin fada yace au baki ma sani ba shikenan..yana fadar haka ya katse kiran.. Gaban Maysam ya bada dam ta fara tunani ...ji take kamar tayi kuka dan ita bata san lefin ta ba kuma gashi shi be fada mata ba... Har ta juya zata fita ya sake kiran dan zuciyar shi ta hanashi sukuni tana ayyana mishi cewa Maysam na can na kuka ..shiyasa ya kasa resister ya sake kira.. Tana dagawa taji shine yayi sallama bata jira taji me ze ce ba ta saka mishi kuka.... Tirkashi nan ya dafe setin zuciyarshi yana fadin why nayi mata fada gashi yanzu na sakata kuka..beyi aune ba yaji kwalla ta cika mishi ido..da kyar ya daure ya rarrashe ta ... Maysam tace shikenan amma yaushe zaka dawo nayi missing dinka fa.... Dan jim yayi dan shifa baya ma jin ze dawo kasar.. . Yace ni kaina bansan ranar dawowata ba kai inaga ma bazan kara dawowa ba ... Bata kawo komi ba dan ta zaci dan ya tsokane ta ne kawai dan lokacin daza suyi bankwana ya jaddada mata baze yi 3months ba ze dawo shi ya sama bata dau abun serious ba... Zata sake jefo mishi wata tambayyar ya katseta da fadin kin ga se anjima inada aiyuka ...be jira mi zata ceba ya katse kiran dan kwata2 ma baya son ta mishi zancen.......haka ta koma aji jiki ban kwari dasu Maheeba suka tambayeta ganin mood din ta ya sauya aman se cewa tayi ai bata jin dadi ne... Sarki kuwa ba karamin dadi yake jiba kasancewar Malam Musa wazirin shi ... Lokacin da labari ya isa kunnen Maysam harda kukan dadi tayi tace gashi yanzu SANADIN ACCIDENT ta samu gatan da ba kowa ke sa'an samun shi ba..da tana cikin 'KUNCIN RAYUWA(littafi na na gaba in sha Allah).na azabar Murza aman yanzu...ta samu Mahaifiya wato Fulani ..ga karatun boko da islamiyya. Gashi kuma yanzu anyi wa Abbata Waziri.ita kam in bata godewa Allah da wannan ni'imomin ba dayayi mata to mi zatayi ...har Fulani ta kiraya ta shiga yi mata godiya har seda ran fulani ya soma baci tukon ta dena.. Haka rayuwa tayi ta tafiya inda zuwan Murza ya kara sa zuciyar Madina kara yin baki yanzu bata da wani buri na taga Murad ya mutu...sabon boka ma yace mata hakan bame yiyuwa bane amma taki hakura kullum da irin plan din datake shiryawa.... Murza kam ta zama tabarya me baki biyu ko nace me fuska biyu ma ..dan yanzu tana yawon shiga bangaren fulani tana nuna mata ta shiryu ta dena abunda take alhali tsegumi ne ke kawota dan ta kai wa Madina rahoto. ..duk abunda ta gani ko taji a bangaren fulani to seta gayawa Madina shi. Amma har yanzu ba'ayi katari taji Fulani ta kirayi Murad a gabanta shi yasa suke kara jin dadi . Basu san duk safiya se Fulani ta kirashi a waya ba ...kuma kullum seta nemi ya dawo amma se ya fara kawo mata kabli da ba'adi ..kullum cikin yi mishi addu'a take . Ita kam Madina zuwan nan Murza yayi mata dadi tana samun information akai2.. 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 A banagaren su Muheeba kuwa bayan sun ji sauki amma fa fuskar ta bata dedetu ba duk tayi wani tabo2 babu kyan gani ... Kullum cikin kuka take ganin haka yasa Mahaifiyarta ta cira musu ticket zuwa wajen danginta na Ghana ..(safe journey du Muheeba Allah ya raka taki gona😎) A bangaren su Maysam kam itada kawayenta sun dage ba kama hannun yaro karatu suke sosai.... Cikin sa'a suka kawo makin da ake so dan haka shugaban makarantar ya ce vacation din 1 month ne kawai garesu dan wani lecture za'a fara yi musu dan kada susha wuya.... Har lokacin Murad be dawo ba kullum intayi mishi zancen se ya katseta da wani zancen ........yanzu kam ciwonshi har tashi yake kadan2 dan kuwa Maysam kuka take saka mishi kan se ya dawo tayi missing dinshi .. Shi kanshi baze ce ga taka meman abunda yake hana shi dawowa ba ...kullum cikin rarrashi yake ...Fulani ma kullum cikin bata hakuri yake.... A na sakin su Fulani tayi mata booking jirgi ta dawo gida... Ba karamar Murna sukayi ba itada M.Musa ba da suka juna ..rasa inda ze sakata yayi ..Murza na gefe se tabe baki take tana tsuka kasa2 amma da taga Maysam ta kallota se ta fake da dariyar yake wai ita a dole nan ta shiryu ta fara son Maysam..... Tun Maysam na dari2 da ita har ta saki jikinta kadan .. Lokacin da Maysam ta sanarwa da Fulani yanda sukayi da shugaban ba karamar murna tayi ba dan haka tana cika watan ta fara shirye2 komawa. .. To fa ranar wata samedi(Saturday )ana gobe komawar Maysam .....suna falon Fulani ,Maysam,Murza,da ita Kanta Fulanin ... Hira suke wacce duk ta karatun Maysam din ce . Murza se wani tarerayar Maysam din take amma fa k'asan zuciyar bakin cikine fal dan ji take kamar ta rufe Maysam din da duka ganin irin yanda take zuba shagwabarta a cinyar fulani ..ita kuma se lallaba ta take. ... Ganin abun bana karewa bane yasa fulani fadin bari de inkira mijin ki may be shi ya lallabaki ki barni na huta da shagwabar nan. Gaban Murza yayi wata irin mummunan faduwa ta shiga wuwurga ido .. Kamar wasa Fulani kuwa ta danna mishi kiran .. Murza ta kashe kunne kuwa. .. Bayan ya gaisheta ne ta sake tambayar shi yaushe ze dawo ..nan ya fara yi mata kame2 .. Fulani tace to ka bude kunnuwanka da kyau kaji ina son ganin ka a week din nan wannan umarni nake baka maza2 ka taho .... Cike da tashin hankali yace to Momy zan zo .. Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Maysam da ta fulani tace to se kazo Allah yayi maka albarka. Sabanin Murza datayi mutuwar zaune zuciyar ta cike da wasi2 a ranta tace daman suna waya ko kuma yau ne suka fara kawai. ..bata gama tsinkewa ba seda taji Fulani na fadin pls ka lallaba min yarinyar nan ysa duk ta hanani wali... Shata da baki Murza tayi ganin Maysam ta karbi wayar tayi cikin kuryar daki tana dariya kasa2 ...wani dunkulelen bakin ciki taji ya to kare mata wuya a ranta tace kada fa Yaron nan ya fara son aljanar yarinyar nan......babu me bata amsa dan haka ta danne bakin cikin ta gaban Fulani ta tashi tana fadin barin koma akwai wasu ayuka da zanyi ...nan tayi ma Fulani sallama ta fice .. Itade Fulani tana kallonta ne amma bawai ta yarda da tuban Murza ba.. Tana fita kuwa ta fada bangaren Madina ......😳😱 Kuyi hakuri da wannan... Fasma ce🖊 [27/07 à 14:25] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 👏👏 _jinjinar ban girma Momyn Mufeedah ,ina tayaki murnar kammala littafinki hakika kin fadadakar da nishadan tar damu Allah yasa sakon da kike son isarwa ya isa ,Allah ya bamu ikon yin aiki da shi ke kuma Allah ya biyaki da mafificin alherinsa ,ya yafe miki kurakuran dake ciki.._ _Up.up.up👏👏muna tare dake se mun jiki a sabon littafin ki..._ ❤ *congratulation my lovely sis SARAH hakika ina tayaki murna samun Bac din ki Allah ya riqa ya sa ki amfana da* *shi ....ina me kara jinjina miki .* 😍 *Ban manta dake ba kanwata ta kai na Balkissa kema ina taya ki murna samun Bepc ki matuka Allah ya rika ya sanya alheri*❤ ... *Kai da duk ma wanda suka zana jaraba wa ina muku murna tare da fatan alheri ..* *Wanda kuma ba su samu ba ne baissent pas les bras ,du courage and wish you bonne chance* .... _Ilou Ado Safaraou&Rabe Idi Salamatou Magaria ..les fausses jumelles ba ..ina jin dadin yanda kuke nuna kaunarku ga book din nan Allah ya bar kauna ❤😍Maysam tace ta gaishe ku_ 😁 Dedicated to SARAH&BALKISSA😍❤ 🅿77__78 ```Manzon Allah(SAW)ya ce''Musulmi dan uwan Musulmi ne ,kada ya cutar dashi. Muslim ne ya rawaito shi``` . Murza na fita ta fada bangaren Madina ..bakin ciki kam kamar ta mutu take ji ... Tana zuwa ta fara zayyanawa Madina komi har da yar kwalar ta bakin rai .. Wata zabura Madina tayi tace what?dama suna waya amma bamu sani ba ... Tirkashi zancen dawowar shi ma bata taso ba kawai abun yi yanzu base gobe ba ki tashi yanzu ki koma wurin yankan wuka ki sanar mishi ..se kuma ki ce mishi ayi mishi asirin da ze manta da zuri'a tashi ma gaba daya ya yanke alakarshi da su ... Murza bata yi kasa a gwiwa ba ta tashi ta fice bayan Madina ta cika mata jaka da makundan kudi... A bangaren Maysam kuwa shagwaba wacce tafi ta Fulani ma take zuba ma Murad .. Shi kuma se lallabata yake kan tazo mishi koda vacance din nan ne.. Se lokaci ta sanar dashi cewa ai wani lecture za suyi dan za ayi musu tsalaken ss2 .. Shima nan ya tayata murna tare da yi mata fatan samun nasara ... Hira tayi dadi har take tambayar shi sunan likitar dayake aiki a can ... Sedayayi murmushi yace to keda ba zowa zakiyi ba miye na wani tambayya... Kukan shagwaba ta sakamishi ..... Dolen shi shi ya gaya mata kai harda adress din gidan dayake..... Sun jima suna waya cike da jin dadi ga shi kuma yace zezo cikin sati se murna ta hade mata biyu... 🌹🌹🌹. 🌹🌹 Murza ce tayi wani zaman dirshen a gaban boka Yankan wuka tana gaya mishi duk irin makircin da suke so ayi musu tare da kara jadda da cewa arabashi da famylin ma gaba daya .. Boka ya sheke da dariyar jin dadi yace kai ina jin dadin aikin ki ...raba d'a da iyayenshi abune ne dayake bamu matukar wahalar aiki bare ma Uwa ...amma dole muke jajir cewa muga irin wanna danyan aiki ya yi tasiri badan komi ba se dan mun san yanke zumunta ma bashida kyau ,,bare yanke alaka tsakani da iyaye. ....(kuji wani shedanci 🤔) Dan haka muna bukatar kudi masu yawa dan asiya wa aljanan da zayi aiki jini ..,,kuma ma ba anan garin suke ba se an tafi wani gari wanda ake kira da''DOGON DOUTCHI''ake siyo su wato Aljana 'DOGUWA'....sune masu yin wannan aiki ba tare da an samu matsala ba....ya kwashe da wata dariyar hhhhhh... Murza se wani washe baki take tace kudi ba matsala bane inde bukata zata biya ...nan ta zube mishi su.. Cike da murna da kwarin guiwa ta koma gida dan Boka ya jaddada mata cewa baze taba dawowa ba..(jifa se kace shi keda ikon duniyar🙄🙄🙄..Allah de ya shirya in me shiryiwan ne) Lokacin da Madina taji bayanin boka ba karamar murna tayi ba tace Mulki ne de Murad baza ka taba hawanshi ba...saura shi kanshi sarkin ina nan zuwa lokaci kawai nake jira.... Wannan kenan 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 Washe gari Maysam tayi tafiyar ta Maradi karatu da zumar in Murad ya zo tasan de ze je ganinta tunda ya san tana school. Amman mi shiru kake ji kamar malan ya ci shirwa ...tun tana tammahani zowarshi har ta dena ...yau har watan su biyu .. Bayan ta dawo gida ne kafin su koma rentren Ss3 take yi wa Fulani mitar yayanta be zo ba .har yau Fulani ma dauriya kawai take yi...tana lallashin ta amma mamaki ne fal ranta ....da farko in tayi kira tana samun shi sede baya dagawa .,,kai daga baya ma wayar ta dena shiga.. Ta dau waya ta sake danna kiran shi amman kamar kullum bata shiga . Maysam kam zuciyar ta banda lugudan zut2 babu abunda take mata ..se kawai ta fashewa Fulani da kuka .. Da kyar itama ta nutsu ta shiga lallashinta .. Dama sati biyu ne zatayi ta koma school amma duk ta wani fige ta rame Fulani kam tana tausayin ta ..ganin abun na gaba yasa tace wa Sarki tana son zuwa England wurin Murad. Da kyar sarki ya lallabata da fadin bari Mahmud ya tafi ya gani.. Cikin satin Mahmud ya shirya ya daga se England ...lokacin da ya tafi akayi rashin sa'a Murad baya nan likitarsu ta tura su qarin karatu kasar Europe kan wata sabuwar cuta data shigowa kasar ..kuma formation din ze dauki 5_6 months.... Murad kam yana can yama manta da wasu wai su Fulani dan kuwa tun bayan kwana biyu dayin hirar shi da Maysam har ya fara shirye2 dawowa amma me kawai rana tsaka ya tsinci kanshi da son rashin dawowar . abun beyi nisa ba seda yaga Fulani tana kiran shi a waya amman ya kasa dauka...wani irin abu yake ji a zuciyar shi se kawai yama canza layi gaba daya ,,,kai da ga karshe ma dayaji tafiyar tura karin karatu se kawai ya saka sunan shi ama su son zuwa ..ya koyi sa'a aka tura sun.... haka nan Mahmud ya dawo ba dan ya so ba tun dade lfyr sa lau aiki ne kawai ya rikeshi...... To fa 🤔muje de zuwa Lokacin da Mahmud ya sanarwa da su Fulani se a sanan suka dan saki ransu .jin an turashi karatu ne .. Maysam ta koma Makaranta abunta . yanzu kam sun kara girma komi na cikar budurci ya bayyana a jikin su....se wani jiji da kai suke wai su yan matan Ss3 ...yanzu kam sun kara wayo Maysam yanzu bata da wani buri na ta ganta kusa da yayata Murad .. Ga karatu suke babu kama hannun yaro ... kullum su ke cinye ta daya ,biyu da ta ukku a ajin,,wannan abu ba karamar haushi yake bawa sauran dalibai ba dan ko wata competition se de a zaba cikin su ukku ...gaba daya kansu a hade sun shaku da junan su,,,class,diri ,kyau tsafta ,ilimi duk sun mallake su ..dan ko a islamiya ma kadan ya rage musu su sauke Alqur'ani....... Kullum zaka gansu cikin walwala da tsokanar junan ,,,har suke kiran kansu da tripleM.. . amman fa har zuwa lokacin su Mufeedah basu san cewa Maysam matar aure ce dan bata wani nuna musu alama ba...wani lokaci har sukan tsokane ta da fadin sun yi wa yayansu kamu .... Itade sede ta kallesu tayi dariya.. Bayan 6 months nan ma su fulani suka dinga diba hanyar ganin Murad amma ji kake shiru ...Fulani kullum cikin yi mishi addu'a take .. Maysam ma kam yanzu bata wani samun isheshen bacci,,,duk dare tana yawaita yin nafilfili da rokon Allah yayi musu zabi na alheri tare da karesu da duk wani me binsu da sharri mutum ko aljan.. Amma fa yanzu idonta ,kunnenta bakinta kai har ma gangar jikinta ba suda wani buri na su jisu tare da oga dan Murad ya rigaye ya koya ma ta sonshi ..dan haka ita da soyyayarshi ta girma cikin ranta ....mafi yawan cin lokaci zata dau photon shi ta saka gaba tana ta zance ita daya (umm su maysam an fada tarkon so ....sede lokaci ya kure miki😜.) . Tafiya tayi tafiya lokaci nata tafiya Bayan sunyi saukar Qur'ani da sati suka fara final exam .. Cikin ikon Allah suka gama lafiya suna jiran saka mako.. Gida ta dawo zaman jira..... Fulani na lura da ita tun dawowarta ta kaura bangaren Murad gashi da ka ganta kasan tana cikin damuwa ...fulani kam ba karami tausaya mata ba take..bz. Ana haka resulta din su Maysam ya fito ..gaba dayan sun ci harda mention exellente .. Zo kaga murna wajen su Harda wata yar kwarya kwarya walima suka shirya su ukkun ...acan gidan Maysam na Maradi akayi ta inda Mahmud ya taka rawar gani wurin yi musu komi dan ganin basu samu wata matsala ba..... Washe garin walimar su ukku suna ta hira Mariam tace yauwa dama akwai wata magana dana ke son yi muku.. Nan suka nutsu ta ce dama abbana nane yayi mun muji .. Wani ihu suka kwasa a tare suna fadi wai da gaske dan Allah .. Tace ee wly wani dan abokin shi ne sunan shi MA'ARUF. Kuma a England yake aiki docteur ne... murna fal ransu suka yi muta fatan alheri tare da fadin kice kawai da mun sha biki se England😁 .. Mufeedah ma tace kai nima fa Maysam yayan nan naki ya fara damuna ,,..bakiga jiya daya kaini Super market siyan kayan damuka sa ....ya wani tsareni da surutu kai daga karshe ma seda yayi mun wayo na bashi number ta .. Maysam ta kwashe da dariya tace kawai kada kija wani aji inya nuna yana so kawai ki amince Mahmud bashi da wata makusa ,kyau ne ,kudi ne,kamala ce, duk ya hada kawai ki yarda musha biki.kemz.. Cike da zolaya Mariam tace kai kede kawai dan yana yayankine kike wani yabonshi .. Dariya tayi tace haba ba wani nan .gaskiya de na fada.kuma ma abokin MIJINA NE A tare sukace miji😳😳😳... Tace ai koda na shigo makarantar nan da aurena ...kuma wannan wanda yazo lokacin da bani da lfy wato Yaya MURAD shine mijina...gidan nan ma nawa ne .. Mufeedah tace amman kin san baki kyauta ba ko ace ayanda muke ki kasa fada muna kina da aure... A tare sukace muna miki fatan alheri tare da zaman lfy me dorewa amman mu kinga tafiyar mu tunda de baki dauke mu ba da mahimmaci...suka tashi zasu tafi Da sauri tasha gaban su tana basu hakuri kan bata yi haka ba da wata manufa kawai de Allah ne beyi ba zasu ji ... Nan ta zaunar dasu ta basu tarihin rayuwar ta ...kan ta gama ,ita kuka su kuka ..nan suka rungume junan su ..sun jima a haka sannan Mahmud ya meda su gida ya kai Maysam airport ta dawo gida.. ,,,shugaban makaranta su Maysam ya kirayi iyayen su bayan yayi musu barka se kuma yayi musu proposing din a aje musu takardun su inda rabonsu gwamnati zata iya tura su kasar waje karatu... Da farko fulani bata amince ba amma ganin Maysam ta kwallafa rai yasa ta amince amma fa tace sede in England kusa da mijinta. Itade Maysam burin ta ta amincen ... Allah cikin ikonsa suka samu su duka ukkun kuma England duka aka tura su ....dadi kashe su ne kawai beyi ba ....zasu kara hadewa a makaranta daya.. Dan haka fulani tasake tutubar Mahmud da yasake koma wa England ya gani .ya kuma sanar mishi matarshi ta samu gwamnati ta turata England karatu.. Wannan karon Mahmud shi kanshi ya tsorata da lamarin ..dan Murad nunawa yayi da de duniya besan shi ba kwata2 ya manta dashi... haka Mahmud ya dawo zuciyarshi cunkushe da wasi2 iri2 .....shi be masan ta inda ze fara gayawa fulani cewa ga irin cin mutunci da Murad yayi mishi ba......dan haka tunda ya dawo ya shiga wasan buya da. Fulani.... Ranar wata litinin ana gobe tafiyar su Maysam England dan Mahmud ya cike mata takardun ta. Bangaren Abbanta ta nufa dan yi musu bankwana shida Murza sun jima Mallam Musa yana yi mata nasiha da kuma ta kare mutuncin ta da na aurenta ... duk sai jikinta yayi sanyi taji kamar ma ta daina tafiyar amman tuno wa da tayi yayan ta na can sai ta samu kwarin guiwa har zuciyarta tafara azzalzalata dan zumudi 😜 Dakin Murza ta nufa da niyar yimata ban kwana amma mi cak ta tsaya a dede kofar shiga palon banyi aune ba naga hawaye sun fara zarya a kumatunta cike da mamaki na matso na kara kunne na dan ji mi yasata kuka sai naji Murza tana waya tana fadin ee kadan ma suka gani wly ni nan zan zama ajalin Murad de Maysam (kuji fa da allah kamar ran a hannunta yake🙄) da ba ma rashin sa'a ba da yanzu sun dade da mutuwa ai..., ke nifa haukata shi naso ayi yabi duniya bama a raba shi ba da dangin ba fadar madina da ga bangaren layi , shewa Murza ta kwasa tace wannan shine target din mu na gaba sai kinyi uwar dakina shugaba Madina matar sarki shugaban masarauta gaba daya kai ko makirar Fulani ba ta isa ta taka miki birki ba dole ne ki taka wanda kikeso a garin nan dan duk wanda yayi miki kan kara za kiyi mishi ta itace abuga dake a barki anan waziri ma yayi nashi babin an shafe shi. Dafe kirjinta Maysam tayi cike da mamaki da kyar ta lallaba ta koma bangaren fulani dede zata shiga taji muryar Mahmud na fadiwa Fulani kaf abunda yafaru shida Murad, yakara da fadin amman fa ina ganin ba a hayyacin shi ba yake dan a gaskia wanan al'amari akwai ayar tambaya a ciki jim Fulani tayi tana jinjina maganar sai kawa Maysam ta fado ba ko sallama tana gwanjin kuka cinyar Fulani ta fada ta saki wani sabon kuka mai cin rai cike da tashin hankali fulani ke tambayarta miya faru .? kukan yakasa tsayawa ta shiga fadin Momy kada kiyi fushi da yayana ba laifin shi bane wly sune kuma sunce ma sai sunga bayan mu nida shi Cike da tsoro Fulani da Mahmud sukace suwa din? Yanzu nan naji Inna Murza tana waya da wata Madina matar sarki nan ta kwashe kaf abunda taji ta fada musu. Mahamud dey mamakine ya cika shi har yawun bakinshi ya kafe ya rasa mi zai fadi. Fulani batayi wani mamakiba dan dama bata yarda da tuban Murza ba kuma ta gane sare Madinar da take fadi sai tayi shiru. A fusace Mahmud ya tashi yana fadin kafin su kasheku ni bari nakashesu .. ,dakatar da shi fulani tayi da fadin zauna muyi magana Bayan ya zauna tayi mishi nasiha kan illar a bunda yake son aikata wa takara da fadin ''maintenant on a aucune preuve en notre disposition qui va prouver leur actes. . Mahmud ya ce''Mais Momy ,Maysam a tout entendu non?.'' Fulani ta sake fadin''Meme si elle a tout entendu c'est sa parole contre celle de Madina kuma ma babu wanda zai yarda saboda iya makircinta dan tana gwada kamar ta goya Murad gaban mutane in baka mantaba waziri ma fa yaka yafada amma babu wanda ya yarda .... Yanzu de mu fara da kubutar da Murad din daga baya se musan yanda zamu bullo musu....in su da adiri suka dogara to mu da Allah muka dogara Nan Mahmud ya bada shawarar ayi ta saukar qur'ani tare da zuwa makarantu su taya su da addu'a...ya kuma cewa muma kuma zamu rage bacci mu zanki rayashi da nafilfili da addu'a .. Sosai sukayi na'am da shawarar nan ..... Maysam tace Allah ya bamu nasara akansu..nima na samu Mijina ya dawo kusa dani..muyi.... Tsit tayi ganin irin kallon da suke mata .. Se lokaci ta tuna ashe fa a gaban Surikarta fulani take ..ai da gudu da shige kuryar daki tana dariya ga kunya kamar kasa ta nutse ta shige .. Dariya Mahmud ya shiga yi mata ... Fulani na fadin yaki dawo y'a ta ai bama yar haka dake... Amma ina Maysam ta ware .. .nan Mahmud yayi mata sallama tare da jaddada mata gobe2n nan zesaka a fara saukar alqur'ani..sanna ya fice. Fulani tabishi shi ma da addu’a dan a gaskiya samun aboki kamar Mahmud a yanzu se an tona.. A ranar su duka ukku baccin da sukayi kadan ne dan kwana sukayi suna rayashi da nafilfili da addu'a Allah ya basu nasara akan su Murza ya kubutar da Murad da ga sharrin su ... Love you all😍❤ Yawan comment dinku shi ze bani kwarin guiwar yin typing me yawa😅 Fasma ce🖊 [29/07 à 21:44] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *I miss you my Arfat and my in law Xaynabqueen ..wai ina kuka shige ne kwana biyu ...Allah de yasa you are fine* 😔😔😔😥 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿79__80 ```Manzon Allah(SAW) ya ce''wanda duk yayi imani da Allah da ranar lahira to ,ya fadi alheri ko kuma yayi shiru. Bukhari da Muslim suka rawaito shi..``` [29/07/18 à 18:40] Washe gari Maysam ta fito cikin shirin ta dan jirgin 10 na safe zasu bi . zuwa Niamey daga can kuma su daga zuwa England Da ka ganta kasan tana cikin damuwa .,,duk ma se take ji kamar ta fasa tafiyar nan duk jikinta yayi sanyi ...gashi wanda take zumundin son zuwa England dan shi ,din ma Murza sun mishi Asiri . Haka tayi break sokoko da ita duk Fulani na lura da ita ..dan haka seta ja ta jikin ta da nufin lallashi Ai kuwa kamar jira take ta kuwa fashe mata da kuka. Itama Fulani se zuciyar ta karaya duk se taji ba dadi ..... Haka tayi ta lallabata tare dayi mata nasiha me ratsa zuciya .. .. Da kyar tayi shiru har fulani na tsokanar ta da fadin ko se ta goyaki ta ne zatayi shiru.... Nan ta kyalkayale da dariya.. Fulani tayi mata jagora fardar sarki tayi mishi bankwana ..sosai ya yi mata nasiha shima .. Suna fitowa fulani ta. bata wata tsaleliyar waya ,,koda na leka na ga iphone,7,..zo kaga Murna wajen Maysam yau tayi waya ..dan dama Murad ne ya hana a bata ,to amma yanzu halin tafiya yayi sanadin an bata.. Fulani tace duk number kowa tana ciki na samiki.. Maysam ta kauda kai tare da fadin har ta yaya na ... Fulani tayi kamar bata gane ba tace ai ..na samiki har ta yayanki Mahmud... Tayi kicin2 ta fuska tace Momy ta mijina fa nake nufi ... Fulani tayi dariya tace tofa an zo wurin masu miji manyan to har ita na saka miki...kai har da photunan shi na tura miki dan daman sun cike mun waya.. Maysam tace kai Momy kin ceci zuciyana fa da yanzu zance a turo min dan ko bacci zanyi sena saka ka photon a .. ...se kuma tayi shiru da sauri tasa tafin hannuta tana kare fuskarta dan Seda tayi maganar taji kunya amman ta mazge dayi mata godiya...ita kanta bata san dan mi yasa ba bata iya controling din kanta wani lokacin.. A gurguje ta shiga bangaren Abbata tayi mushi sallama haka ta daure ta shiga Dakin Murza tayi mata sallamar. Kamar gaske tana wani dariyar yake wai ita dole yanzu son Maysam take ,,a zuciyarta kuwa fadi take ina nan kwanan nan zaki dawo gida kici Ubanki shegiya kullum se kara kyau take kamar yar sarkin aljanu.. Itama Maysam sakin jikinta tayi kamar ba'ta ji komi ba ..amma addu'a ce fal ranta .... Haka suka rabu da fulani duk kwalla ta cika mata ido inda Mahmud zeyi mata rakiya har AEROPORT DIORI HAMANI na birnin NIAMEY......acan suka hadu da sauran kawayenta Su Mufeedah suma sun iso duk da yan uwansu nan suka gaigaisa ....suna na zaune aka fara kiran passengers ..haka suma su Mufeeda suka rabu da familly , ,,Mahmud yana nan har jirgin ya daga .. Wata yar dantijuwa. na gani ita da mijinta wacce tun lokacin da ake kiran passegers naga ta tsurawa su Maysam ido bata ko kiftawa. mijinta na mata magana aman bata ma san yana yi ba . hankalinta rankatakwab yana. Wurin su Maysam din.....Mijin ta na mata korafin su huce tun dazu amman hankalinta baya ma wajenshi shima ya meda kallonshi ya ga miyene ya dauke mata hankali haka amma lokacin su Maysam tuni sun shige jirgin .... Suna nan har se da jirgi ya tashi naga ta sauke wata nauyayar ajiyar zuciyar... Da sauri mijin ya kalleta yace ya akayi ne ?ko jikin ne...? Girgiza mishi kai tayi kamar karamar yarinya tace a'a naga wata yarinya ne me kama da Baby na... Shima ajiyar zuciyar yayi ya ce ya kamata yanzu yaci ace kin sakawa zuciyar ki hakurin rashinya ta ....shekara nawa kuma kusan kullum se kinga me kama da ita .... Da sauri tace a'a wannan ta banbata da sauran wanda nake gani kullum.. Dan murmishi takaici yayi yace kamar kullum kenan haka kike cewa ...kiyi hakuri ki rumgumi kaddara ..idan har tana raye Allah ya bayyana mana ita .. Ameen ta amsa amma kam ta kwallafa rai a kan yarinyar dan ta so tayi mata magana kamar yanda take yi duk wacce taga tayi kama da Babyn ta.. Sun juya da niyar tafiya ..naji Mahmud ya ce Mom,da,Dad...😳😳parent din SWEETBABY ne.ashe.. Juyo wa sukayi suka ga Mahmud ne .. Nan ya gaishe su cike da.ladabi .. Suka amsa suna fara'a .. Mom tace que est ce que te venu faire ici. ? dan sosa kanshi yayi yace matar Murad ne na kawo zata fice England..... Dad yace a'aa Masha Allah.. Mom tace kash yau ma babu rabon zanga ta ashe ko dayake fulani taso ta turota kafin ta fice to se akayi rashin sa'a muna Paris.hakama lokacin da akayi aure bama kasar..da nasan yau ne tafiyar ma ai da tun jiya zamu dawo dan naga matar d'ana.. Su Dad sukayi yar dariya sukace ai gaba da yawa zaki ganta. Wata rana Itama dan murmushi tayi tace hakane to Allah ya nuna muna ya kuma sauke ta lfy . Suka ce ameen... Nan Mahmud ya yi musu sallama tare ya fice dan yana son a fara yi mishi saukar tun yau dan karfe da zafi2 ake dukanshi. Suma driver ya huce su gidan su. A raina na ce kenan de su anan Niamey suke. . Ko sarki fulani bata sarna mishi ba halin da Murad yake dan bata da wata sheda ..... To daman gata da temakon talakawa dan kowani wata biyu ko ukku se an kai tamako kauyika ko Mutuwar SWEETBABY ma suna hanyar kai temako wani kauyen ne sukayi shi. Wanna abu ba kamramin faranta ran sarki yake ba shiya sa ma kullum sonta yake kara shiga zuciyar shi sabanin Madina da ko yan Uwanta bata son temakawa bare wani .. Shiyasa ma yanzu da sarki yaga kusan kullum se an kai wa makarantu taimakon se beyi wani mamaki ba dan shi ya aza ta sauya takun ta ne na temakon.... Har ranar suna fada da dare su ukku yake tsokanar ta da fadin wai kode dan taji labarin zeyi ta ukku ne yasa take shiga da ficen nan dan addu'ar ta amsu ya fasa auren. .. Madina da bata san irin wannan wasan ba ta kuwa dafe kirji tace na shiga ukku . aure fa kace ka tsufan nan mi zakayi da wata macen.kuma shine ni ba'a gaya mun ba se yanzu tana wani kumbure2... Share zancenta sukayi sema Fulani da ta son tsokanarta kawai yake ta amshe karaf da fadin muna maraba da ita ...fatan zaman lafiya nake maka tanayi tana wani kashe me ido ..tace kuma ai har yanzu dan saurayi shatak yake ,,ni kam bana ganin tsufanshi..... Takaici ya kusan kashe Madina daga zaunen banda zabgawa fulani harara babu abunda take .. Sarki yace wannan haka yake nima kullum kamar yar sha bakwai nake ganin ki ...wai ma miye sirrin nan ne .um yan matana... Fulani tayi wani far da ido ta ce to kawo kunnenka kaji.. Babu gadama ya kuwa dan karkato kunnen shi yana dariya .. Cike da shaukin so da kaunar junan su ta kuso da bakinta zatayi me rada dan fa su sun manta da wata Madina na wurin...(kuji wani salon soyyayar tsofi ko🙈) Se ji sukayi Madina tayi tsaye tana fadin tsofe2 daku amman kuna wani abun kamar kananun yara ...wannan ai ko Murad baze yi abunda kukeyi ba tanayi tana dokawa fulani harara.... Fulani a ranta fadi take ...ke kike ganin mun tsufa amman ai ita soyyaya bata tsufa..(😳😳to fa kunji tsofafin ko?).... Fulani mikewa tayi tana fadin seda safen ku dan Madina keda girki yau.. Sarki yace zo ki fada mun mana kafin ki hucen ... Fulani na dariya kasa2 ta ce to ai ya fice sede wani jikon..kuma Kallon zamu hade naga yana jifanta dashi... Wanda ya kara harzuka zuciyar Madina ..ta shige kuryar daki fuuuu ..tana fadin jarabbabiya kawai.macce se jarabar iya kissa mtssss. (🤣🤣Madina kina sha'anin ki fa ) ..🌹🌹🌹🌹 🌹🌹 Su Maysam sun isa England lafiya ..daya ke gwamnati ce ta tura su kafin ma su isa har an turo musu bus din dazu dauke su dan ba su kade bane suka samu promotion din ba.... Direct babbar university England aka akaisu ..nan aka rarraba musu dakuna su anan cikin hostel din makarantar... Amman cikin rashi sa'a se ba a hadasu daki daya ba ...Mariam da Mufeedah da wata dakin su guda se kuma Maysam da wasu yan mata suma dakin su guda.. To fa nan ake yinta Maysam ganin an ware ta da su..da kyar da siddi suka shawo kan yan matar sukayi changé da Maysam.ta koma daki daya da su Mariam.dadi kamar ya kashe su ... Tun washe gari suka fara zuwa lecture dan har an fara da sati suka zo ..dan haka babu zancen hutu ma ... Class dinsu guda wato medecine dan sunce mutuwa ce kawai zata raba su ..komi nasu iri daya ne kai har dressing dinsu ma iri daya suke yi .kuma kullum zaka gansu da hidjab din su basa yarda su fito hakanan duk da suna garin turawa....., .suna taka tsantsan da rayuwar su ...sun meda hankalin su ga abunda ya kawo su.. Ba kadan ba suke birge ba mutane da basu sha'awa dan duk gani suke trijumelles ne(yan ukku)...... Yanzu har sun cinye 1 mois da zuwa ..suna ta karatun su cikin kwanciyar hankali banda Maysam data tsanan ta tunanin ta oga Murad ...shi yasa ma basa barinta ta zauna ita daya koda da second daya ne dan yanzu zata saka photon Murad a gaba tana ta tunanin shi..tun abun baya damunsu har yazo kuma yana yi dan sunsa miyasa Murad din be nema ta ba suma kullum cikin taya ta da addu'a suke... Yau ma kamar kullum su Mufeedah sun dan fita suka bar Maysam a daki tana dan exercice.. Amma mi ko minti daya basuyi ba da futa ta ture komi gefe ta fara sa'arta wato kallon photon.. Shigowar su kenan ...suka ji Maysam na fadin ita kade wly duk ranar da muka hade da kai ko to sena tsotse bakin nan tas ..dan gaskiya Allah yayi hallita a wurin nan ..dan lips din nan shine ake kira Kiss me babyn nan ..ita duk jitake a ranta tayi maganar Tana kallon photon tana doka murmushi. Mi su Mariam zasuyi in ba dariya ba suka kuwa tun tsire da ita har tasaki baki tana kallonsu dan bata san mi suke yiwa dariya ba Mufeedah ta matso tace inda muga irin lips din nan da ake ta wani yabawa haka... Wani waro ido tayi tace wai kuna nufin dama a fili nayi maganar nan ne.. Mariam tace a'aa a Mafarki ne.. Gaba dayan su suka saka dariya ...haka suka ci gaba da rayuwar su .cikin jin dadi. 🌹🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 A can gida kuwa sauka yi ake ba kakkau tawa .. Haka kawai ranar wata juma'a Murad tun safe ya tashi da wani matsene cin ciwon kai ..lokacin yana likita ne dan haka ya tattara ya dawo gida amma ciwon kamar karashi ake ... Ba bu zato yaji bakin shi yana abaton addu'a wanda rabon daya ce yayi addu'a kai koda bayan salla ne to ya manta... Kan kace mi bacci ya sure shi ..bashi ya farka ba se wajejen sha biyu da rabi na rana duk wani iri yake jinshi kamar wanda iska zata dauke shi yake ji fayau2 kawai....ganin lokacin sallar Juma'a yayi dan haka wanka yayi ya fice Masalaci duk da akwai yar tazara dashi da masallacin. Amman har yanzu kan be bar mishi ciwon ba... Tunda sheik din ya fara huduba jikin shi yayi sanyi duk se yake jinshi imcomplete kamar wanda ya rasa wani abu a rayuwar ya ke ji dan akan yin biyyaya ne ga uwaye...ake hudubar.. Haka jiki ban kwari har akayi sallar ..suna gamawa mutane suka fara tafiya dan ba wani yawa ne da su ba daman... Amma shi Murad nan ya tsinci kanshi da ya zauna ...yana yiwa fiyyenyen Halitta SALATI .. Mark dake share guda yana kallon shi duk mamaki ya cika shi ...duda yasan wannan al'adar shi da Murad ce in akayi Sallar juma'a nan zasu zauna suyita istigifari tare da salatin Nabiyi ..to aman fa shi Murad ya dade da fasata ..dan ana gama sallar yake tafiyar shi... Be gama tsinkewa ba seda yaga an tada sallar la'asar anyi shi da Murad din dan ba kullum ba yake ziwa masallacin ma agida yakeyin sallar shi... Shi kam Murad tun da ya fara yin Salatin ya ji zuiiyar shi ta nutsu ..wani rin nishadi yake ji yana bin duk illahari jikinshi Kasa hakuri Mark yayi ..bayan sun gama sallar ya matsa kusa da Murad din yayi mishi sallama nan suka gaisa ciki da fara 'a Murad din yake amsawa .. Mark de ya boye mamakin shi dan ba kamar kwanakin baya ba da sama2 suke gaisuwar ma.. Nan Mark cikin dakewa yace yau fa duk kawani sauya mun ... Murad yace mi ka gani ne..... Mark daman kamar jira yake nan ya kwashe komi ya fada mishi har da zuwan Mahmud din da yanda sukayi dashi ... Inna lillahi wa inna.ileyhi raji'un ... A bunda bakin Murad ke memetawa kenan ..... Be gama tsinkewa ba seda yaga babu numb familyn shi ko daya a wayar shi ... Mark yayi karfin halin fadin ai ka canza layi tun da dade wa.... Hawaye kawai ya shiga zarya a idon shi yama rasa abunyi ya kuma rasa miya sa shi yin haka gaba daya baya iya tuna komi...... Mark daya fara dan zargin wani abu se yaji tausayin shi ya kama shi dan shi dama yasan da walakin goro cikin miya ...Murad dayake tsananin son familyn shi aman farat daya ya yanke duk wani contact dinshi da su ... Nan Mark ya shiga yi mishi Nasiha tare da jan hankali kan ya rike addu'a don ita ce takobin mumuni.... Daga haka Mark ya bashi shawara ya kirayi su fulani yanzu .. Kallon agogon hannushi yayi ya ga hudu na yama kenan yanzu goma na dare ne a can .. Amma duk da haka ya danna number fulani dan ya haddace ta a zuciyar shi tun da dadewa... Lokacin fulani tana shirin fita zuwa wajen sarki..kiran ya shigo.. Ringing a na biyu ta daga duk cike da zumudi dan taga number england ta aza Maysam ce ta ari wayar kawayen ta kira...dan haka tana dagawa ta fara da fadin asallama yar gidan Momyn ta ..... Murad daga can a ranshi ya shiga dan tunani nan da nan zuciyar shi ta fara aikin zut2 dan tuno mata da Maysam...katse shi fulani tayi da fadin hello.. Cikin da sanyi jiki zuciya na mishi fat2 ya amsa sallamar tare da fadin Momy nine... Wani farin ciki marar misultuwa ya ratsa zuciyar fulani ...tace son kai ne... Cike da kwarin guiwa jin bata dau abun da zafi ba ya ce nine Momy ..dan Allah ku yafe mun wly basan miya sa man ba yana fadin yan kuka.. Godiya ta shiga yiwa Allah (SWT)daya kubutar mata da son dinta ....dama ai addu'a bata faduwa kasa . kuma ```Manzon Allah (SAW) ya ce'' idan zakayi roko ,to ka roki Allah ,kuma idan zaka nemi temako ,to kanemi temako a wurin Allah.(Tirmizi)``` sanin bayin kanshi bane yasa tace na yafe muka daman can ban rike ka ba ...nan ta shiga yi mishi nasiha da ya rike addu'oi dayin sallar nafila..dan ```Manzon Allah (SAW) ya ce''Addu'a itace ibadah (Tirmizi``` ) Sosai zuciyarshi tayi wasai ...sun jima suna wayar sanna ya kashe tare da fadin se zuwa safe ze kirayi Sarki dan har sha daya tayi...seda safe sukayi wa juna tare da gaya mata gashi nan cikin satin nan in Allah ya yarda.....cike da murna kamar karsu kashe wayar ..har ze kashe se kuma ya sake fadin Momy ina Yarinyar nan take .. Ganin dare yayi Fulanin kar sarki ya jita shiru dan ita keda duty yasa tace tana nan she is fine tana can tana wurin karatun ta... Bakinshi yayi nauyi tambayar a 'ina se kawai ya kashe kiran .. Fulani dan murmushi tayi tare da fadin ni kam ido ne nawa... Yana kashewa ya dannawa Mahmud kira ... Ringing biyu shima ya daga duk jiyake su Mufeedah ne shima... Amman mi se yaji muryar Abokinshi wanda ko cikin dubunan jama'a ze iya sheda ta.. Cike da zumudi yace M2 kai ne ko kuma kunuwana ne suke mini gizo... Murad yace nine aboki pls kayi hakuri da abunda.... Be gama ba Mahmud ya katse shi da fadin ai komi ya fice a kiyayi gaba de...shima de nasihar rike addu'oin tsari na safe da yamma yace ya rike kamar yanda fiyyenyen Hallita ya umarce mu da yin su...(suna nan cikin HUSNUL-MUSLIM).. Murad yace hakika ka cika aboki na kwarai Allah ya bar kauna da zumunci masu dorewa... Ameen ya amsa .. Se kuma Murad ya ce kenan de yar gidan Momy bata ci jarabawa ba ko kuma fasa yi musu tsallaken class din akayi ne dan na tambayi Momy tace tana can wurin karatun... Mahmud yace ita kuwa suka samu dan har da mention excellent SANADIN haka har gwanati ta tura su karatu England itada kawayen ta ... Yan zu haka suna can. enland... Tunda Mahmud ya fara bashi labari yake jin dadi har lokacin daya ce mishi wai sunan nan england sannan hankalin shi ya tashi wani irin bacin rai da kishi suka da baybaye shi wanda acewarshi martabar aurenshi yake karewa.. Cike da masifa irin tashi yace What?da Izinin wa?...waye yayi mata jagora batare da izini naba?ya ci gaba da fadin jinake na jima da gayamata cewa bazan barta tayi karatu anan ba......? Mahmud shima daya kai kololuwar bacin rai yace.. The more you comment ,the more i typing..😁😁. Bazan gajiya da fadi muku ina yinku irin totaly din nan❤❤ Fasma ce🖊 [31/07 à 23:35] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Alherin Allah ya kaimu muku a duk inda kuke aminan kwarai MOMYN HADJIA & MY AISHA (NANAS)ina jin dadin shawarwarinku da nuna kulawarku a gareni Allah ya bar kauna da zumunci me dorewa a gaskiya ina yin ku* 😍😘❤ __ban manta dake ba Garkuwa ina jin dadin yanda kike bibiyar littafin nan Rabbi ya bar zumunci......_ 😍❤❤❤ _Fans ban manta daku ba kusan ina yinku irin totaly din nan har kullum_ ❤😍 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 81__82 ``` ```Manzon Allah (SAW) yace''kowane abu me sa maye haramun ne. Muslim ya rawaito shi ``` [31/07/18 à 22:23] Mahmud ya kai kokokuwa bacin rai ..ya ce to Momy da Sarki suka bada izini.......... Jagora kuma da kake wani tada jijiyoyin wuya nina na mata shi ...,, Sanna da kake batun ai tasan bakada ra'ayin tayi karatu acan .to mu aljanu ne da zamiyi aruwar sanii komi kake nufi tunda de mu baka taba fada mana bz.....da kaji yanda yake maganar kasan cinkin bacin rai yake yin ta....... Se kuma jikin Murad din yayi sanyi yayi ajiyar zuciya yace sorry aboki ba haka nake nufi ba cikin sassauta murya yayi maganar Mahmud ya sauke ajiyar zuciya shima ya ce shikenan amma a tari gaba ...cike da tsokana ya ce kawai kishi ya wani rufe maka ido har baka san maganar dakake fadi ba.. Ya leman kuwa yace kishi fa?ni ba wani kishi kawai ina son kare martabar aure nane... Dariya Mahmud ya yi daman yayi zaton abunda ze fadi kenan .... Nan Mahmud ya gaya mishi komi game da makarantar har sunan ta ... Shi kanshi besan irin yana yin da yake ba yana de amsawa da to... Shi kuma Mhamud dan ya kara har zukashi ya ce ..bari na baka number ta dan kada kasha wuya. . Wani yawu me dacci ya hade yace Mahmud kun kashe ni yanzu har da waya kuka bata ..fadi yake kamar zeyi kuka .. Mahmud ya kwashe da dariya ..seda yayi me isar sa har Murad ya hasala dan haushi ....yace se anjima.. Da sauri Mahmud yace kenan de baka bukatar number ko...to seda safe... Da sauri yace bangane ba bana so ..?kaji na fada da bakina ne...kawai kaban in zaka ban kasa2 yake fadin kawai ana so a bata min yar renota a wani zo harda bata phone. To wai ma itada taje karatu miye na wani bata waya. Mahmud daya jishi yace da kuwa kasani iphone7 ce.. Kamar zeyi kuka yace wly kun gama dani ina yarinyar nan ina iphone7 miye laifin ki saimata touch ligth ma..... Mahmud daya samu abun tsokana yace kai har da fa Whatsapp ,twitter,facebook etc ..duk ta iya kai tama kware yanzuu...in fada maka kuwa Katse kiran kawai yaye ba tare da ya anshi numb wayar ma tuni zuciyar shi tashi bugon zut3. Banda huci babu abunda yake .Mark da ke kusa dashi ya dafa shi yace be carefuly .mana..bawani abun tada hankali bane kayi hakuri duk da banji miya ce ba amman ina so kabi komi a sannu.kada kayi saukin yanke hukunci cikin fushi daga baya kayi da na sani....nan yayi ta tausarshi har yaji sanyi a ranshi ...basu fita ba daga massalacin har seda suka gabatar da sallar isha'i sanna suka komo kowa ya nufi gidanshi .. ... Yana nan kwance bisa makalelen gadonshi har wajejen sha biyu na dare amma ya kasa bacci kai alamun jima be jiba kawai duk maganganun Mahmud ne ke masa yawo a kwakwaluwa ..kasa hakuri yayi ya kalli agogo yaga sha biyu har da minti 5. .dan haka ya danna mishi kira dan yanzu yana da yaki nin sun idar da sallar asuba acan.. Lokaci shi kuwa ya dawo daga masjid kenan yaga kiran Murad ..seda yayi murmushi dan yasan mussababin kiran ..... Yana dagawa yace kai wai har yanzu bakayi bacci bane ko kuma tunanin yar renon naka kake.... Seda ya ja tsaki yace ni ba wannan nakira ka fadamin ba ...number zaka bani ..kuma harry up ina da abunyi..yana wani basarwa wai dan kadama yaga damarshi.... Mahmud yace ka biya tukon.... Kamar ya shiga wayar yake ji yace wai kai wani irin dan rainin wayo ne ...yace ka fada ko nawane kasan de zan iya saye ko?... Yace amma de kasan number nan zatayi tsada ko ?dan kuwa me wayar.... Da sauri ya katse shi da fadin ''je t'en supplis''' kaban number nan ..wai mi natare maka ne a rayuwa da kake son yi mini katsa landa haka ne ..... Mi Mahmud zeyi inba dariya ba yace shikenan bari na turo maka.. No kawai ka gayan yanzuu.... Number ya bashi yana fadin ka gaida mun yar renon taka.. Katse kiran kawai yayi dan yaji haushi ba kanan ba .... Yana bashi ko save dinta beyi ba ya danna mata kira..... Haba yaya Murad sha biyun dare ne fa. ...ai lokacin Maysam ta kai goma ma na bacci.... Seda yayi mata missing call 5 bata dagaba ... Murad ba uzuri nan ya fara fadin zamu hade ne inba ma raini ba ina kira kiki wani dauka....tsaki daya ja yafi a kirga ..haka ya kwana da kyar barawon bacci ya kwashe shi... Washe gari Tun tashinta da asuba taga miss call 5 amman dataga sabuwar number se bata meda kiran ba kai daga karshe ma kashe wayar tayi dan yau wani pratical zasuyi kuma abayan gari sannan ba'a barin su suyi waya shi yasama basa fita da ita duk ranar da zasuyi... Murad kam yau har makara ma yayi salllar asuba seda gari yayi dan haske ya farka a gurguje yayi sallar yayi shirin fita . amman kafin nan ma ya mata kira yafi akirga yajita swich off....tun lokacin zuciyar ta fara lugude....ya na fita direct hanyar dazata kaishi makarantar yayi dan yau ko office baya jin ze iya tafiya..kira yayi ya sanar da Mark cewa baze samu damar zowa ba..... Cikeda zullumi ya isa makarantar ..be tsaya wata2 ba ya shige wurin shugaban makarantar ..dayake bawani boyayye bane dan haka tarba ta mussama shugaban yayi mishi. Nan yayi mishi bayanin abunda ya kawo shi. Babu mata lokaci shugaban ya fara bincike... Can yace ai kwarai a nan take karatu su biyar gwamnatin kasar Niger ta turo su...amma yanzu basa nan sun fita bayan gari yin wani pratical...kuma gobe ma can za su tafi... Ranshi in yayi million ya bace..amma se ya danne yayi mishi godiya tare da fice wa .....ranshi inba suya babu abunda yake ..a ranshi fadi yake dole ma ta bar makarantar nan ..... Su Maysam basu suka dawo ba se wajejan shida na yamma . duk sun galabaita...... Suna zuwa ta kunna wayarta da zumar yi wa fulani shagwabar wuyar dasu sha yau... Gefe daya kuma Mufeedah ce ke soyewar ita da Mahmud ....yanzu kam ba'ace wa komi dan sun shaku da soyyarsu.. Can yace wai ina kanwata ne. Gatan nan kusa dani kona bata ne.. Ee yace.. Bayan ta bata suka gaisa ..yace wai mijinki ya kiraye kuwa jiya.... Dafe kirji tayi ta wani waro ido kamar yana ganinta tace wayyo na shiga goma . kadade fa shine ya kirani jiya ....... Tace ya Mahmud kace tawa ta karemun dan naga number england ce sede ban kawo cewa shine ba shiyasa ma ban mede kiran ba... Mahmud yace ki kwantar da hankali ki ..nan ya bata labarin duk abunda ya faru jiyan. Wani uban tsale tayi ta dane bisa kan Mufeedah tare da wani ihun murna tace kai Alhamdullilah ..lallae Allah abun godiya ne. ... Cike da murna da zumudi har jitake kamar tayi fiffeke ta ganta kusa da yayanta.. Wayar ta bawa Mufeedah tashige bayi abunta ..se taji ma duk wata gajiyar da suka kwaso ta tafi ..fuskarta banda annurin murmushi babu abunda take. .. Suna zaune suna wani dan exercice su ukku.....lokacin har goma tayi dan haka suna gamawa kowayi shinfidar shi dan bawa gangar jiki hakkin ya... Lafiyar gado suka bi ....can se wayar Maysam ta shiga tsula kara... Da kamar bazata dagaba dan har bacci ya fara dibanta... Amman ganin number jiya ce yasa ta wartsake tana mutsitsike ido..tare da zubawa wayar kallo kurr Kasa dauka tayi se wani waro ido take kamar wanda tayiwa sarki karya..... Can de tayi shahada har ta kusan tsinkewa ta daga ... Da farko yayi niyyar yima mata masifa ..aaaman mi ..tana doka sallama yaji shi har cikin kokkon brain din shi. A take yaji ranshi yayi sanyi ...muryarta kade data daki dodon kunneshi seya ji ta mishi kwarjini ....yaji baze ma iya mata masifar ba.. Seda ya sauke ajiyar zuciya sannan ya amsa sallamar .. Tofa ita kam har seda ta wani lumshe ido jin muryar shi dan ta sheda Muryar.... Tace yaya ykk?ya two days?ya aiki?ya fama da jama'a? Wannan karon shima lumshe idanun yayi har besan lokacinda murmushi ya subuce mishi da fadin haba duk wannan question din wacce zan ansa ne ?dan ayanda take wata maganz kasa2 ko su Mariam da suke daki daya basu jiyo ta ba Kamar tana gabanshi ta wani turo baki tace duka..... Jin shiru yace ..to am fine ...komi Alhamduliilah... Tunda ya fara magana tayi shiru a ranta fadin take masha Allah ...yaya bade dadin Murya ba ....ko dayake ma ai daga bakin nan tafito wanda nakeji kamar na saka a biredi na cinye shi .... .(🙄to mikike jira🤨) Katse mata tunanin yayi da fadin haka mukayi da ke ne?jinake na dade da cewa bazakiyi karatu a England nan ba?kuma nace ba yanzu zaki fara aiki da waya ba amma sedakika amsa ko? to wly.. Da sauri tace haba yaya na ..yaushe rabon da ka ganni,ko kaji murya ta ma seyau dana ke daukin ka seka shiga yi muni fada...ta fada cike da kissar kamar zatayi kuka. ..ta cigaba da fadin kuma wly ni duk agajieye ma nake duk bacci ne tak ado na....pls yaya kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba...am so sorry.. Duk se yaji ba dadi ya tausaya mata yace shikenan bari na barki haka amma fa make sure zamu cigaba da maganar nan gobe.... Da sauri tace kada kashe wayar nan ni ban gaji da hirar ba... Yace to ai nima ban gajin ba se de zanje aiki gobe kuma kema gashi pratical zaku .... Har zasuyi sallama yace yauwa daman dan na fada miki yanzu kina da abokiyar zama dan nayi aure.da... Bata bari ya karasa ba ta kashe wayar tare da sakin wani kuka kasa..2... Yau itama kam bacci se barawo ne ya saceta ..dan maganar wai yayi aure se dawoma ta take..... To fa😳😳😱MURAD aure yayi kuma 🤔🤔😁😁 Kenan de Maysam anyi mata kishiya😅...kai abun nann yayi mun...🙊🙊🙊🙊 Ina yinku irin sosai din nan❤😍 Fasma ce 🖊(yar mutan Zinder😘) [01/08 à 23:12] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to my SAMBABY😍❤ 🅿83__84 ``` Manzon Allah (SAW) ya ce''kunya tana daga cikin imani'' Bukhari da Muslim suka rawaito shi``` [01/08 /18 à 22:58]A bangaren Murad shima beyi wani bacci ba. .nan zuciyar shi ta fara cewa why2 zaka fada mata nee.....ganin baze iya jurewa ba yasa ya danna mata kira amma har tagama ringing ba'a daga ba ...kai daga baya ma kashe wayar Maysam tayi ..duk se yaji babu dadi ..wata zuciyar tace mishi yo semi in ta kashe wayar ...ai k duk lefin kane dan kana sakar mata fuska ne har taga damar renakai . kawai abunyi anan ka shareta..kai mima ze hana ka tafiyar wajen su Momy .... Yana ta wasi2 ...can shi kade yace kai baze yiyu ba ..... Kiran sallar farko a kunnen shi ..tun da ya tashi yake ta danna mata kira amma har lokaci a kashe ..zuciyar shi ta raya mishi kawai ya iske ta school din mana..ya kuwa yi na'am da wannan shawarar.. Karfe bakwai da rabi ma acan tayi mishi ..amma cikin rashi sa'a har sun tafi daya iso ...ranshi in yayi dubu ya bace ..ya shiga motar shi yayi gida dan shiryowa office.....yana tafiya yana jan tsuka tare da buga sitiyarin motar shikade yake fadin zamu hade ne ...se kin san ni kika kashe wa waya... A bangaren Maysam kuwa tun tashita asuba su Mufeeda suka fahimci tana cikin damuwa ..kwata2 yau bata walwala.....komi cikin fada take yinshi Kuma gashi ta matsa musu kan su shirya yau bus din wuri zasu shiga ..ganin yanayinta yasa basuyi wata gadama ba suka shirya ...su aka fara kaiwa wajen dasuke pratical din..... Bayan sun iso ..suka jata can wani gu inda babu sauran dalibai ....tsakiya suka sakata a tare suka dora hannuwansu a kafadarta .... Suna kallonta Mariam tace what happen to you Maysam ?ko wani a cikin mu ya bata miki rai ne? Mufeedah tace haba Maysam kada ki dau halin da naki ba ...tun tasowar mu muna tattala junan mu ..pls muna me baki hakuri inhar mu muka miki wani abun...ki sani komi yayi zafi maganin shi Allah. .ki yawaita fadin innalillahi. Wa inna ileyhi raju'un ... Kuma ina me kara baki hakuri .. Da sauri Maysam ta rufe mata baki da hannun ta ..kamar me jira kawai ta fashe musu da kuka .. Cike da mamaki da tsoro suke kallonta ..a tare suke fadin inna lillahi.....miyayi zafi hakane wai Maysam tuni suma idon su har ya ciko da kwalla suka ce pls say something mana ..... Da kyar cikin gwanji kuka tace yaya Murad ne yayi mun kishiya.. . Duk se suka ji wani mugun tausayinta ya dirar musu se suka rumgumeta suna lallashi .. Mufeedah tace haba tripleM nasan kishi halas ne kuma mun san yanda kike son mijinki amma kiyi hakuri kuka bana naki bane. Lokaci yayi da zaki fuskanci miji ki ki bashi kulawar da gatan da kowani namiji ke samu..yanzu da da badaya bane ...kinsa ciwon kanki .... Mariam tace sanna shawara da zamu baki anan itace anan shine kiyi koyi da kishi irin na matan Manzon Allah(SAW) bawai kizo kiyi ta wani tada jijiyo yin wuya ba ki tada hankalinki ki tadawa mijinki shima .... Sanna kisani cewa su maza an halasta musu da su auri mata 4 in de har zasuyi adalci a tsakani ....Shi aure ana yinshi ne saboda asamun nutsuwa na sani kishi dole ne amma bana hauka ba. .... Mufeedah ta kara dace wa. Kuma shi namiji inde har yayi niyyar yin auren shi to kisani ba wai fadanki da maseefar ki ,ko fushinki ze sa ya fasa ba dan a lokacin giyar amariya na layi da ,,in kinga kinyi nasara da wa'inan to dama Allah can ya nufa ba matar shi bace..dan namiji in...ko kuma inkiyi wasa ma ya tsinke taki igiyar..dan dole se kin kauda idonki daga wani abun dan gujewa duk wata fitina.. Mariam tace ina me baki shawarar da kiyi zaman amana tsakanin ki da kishiyar ki ,,dan kuwa kota cuceki Allah baze barta ba ..... Mufeedah tace sanna ki kasance macen da akullum zata ringa tunatar da mijinta kan yayi kokari ya ringa kwatanta adalci ..bawai ki zamo wacce tana kallo mijin ta baya yin dede a tsakanin ku ba amma ki kasa tunatar da shi kai har ma wai ki zanki gani ko yafi sonki ko kuma kina takamar wai ke wace abace ..to kisani duk abunda kayiwa wani to kai ma kada ka cire tammahani wata rana se am maka. ..sanna ki sani fadar ma'aiki SAW ne ke cewa ```Duk wanda yake da mata biyu se ya karkata wajen daya ya bar dayar ,,to zai tashi ranar alkiyama barin jikinsa daya a karkace''(Ahmad)...``` Tace shin zakiso kiga yayaki a haka ne duk ikirarin dakike cewa kina sonshi? Nan sukayi ta tausarta har taji komi ya fice har da su dariya databawa suke..... Yau kam saukar wuri sukayi dan sha biyu ma a school tayi musu... Mufeedah tace Maysam na baki shawara mana .. Mize hana ki kaiwa yayanki ziyara office yau ..tunda kin ga yaushe rabonki dashi kawai ki mishi suprise yau.. Mariam ta ce brain dinki naja fa.. Maysam tace to karatun yau din fa? Mufeedah tace kuje ku biyu kawai ni se na tsaya na dau karatun in kun dawo sena koya muku... Haka kuwa akayi bayan sallar la'asar su biyu suka shiga taxi tare da gaya mishi adress din Likitar da Murad ke aiki.. Suna nan tsaye a harabar likitar dan basu san wa zasu tambaya ba ... Can suka tsikayo Doc Mark ...ganinshi da kayan doc yasa suka tsayar dashi... Sallama sukayi mishi sannan suka gaidashi. .cike da fara'a ya amsa sanna Maysam tace mishi Doc Murad muke nema... Kallonsu yayi da kyau yace yanzu kam ba lokacin visiting bane sede ku b secretair dinshi sunnan ku gobe se ku dawo... Har zasu ...se Mariam tace haba Maysam muda ba marasa lfy ba kawai kice ace mishi kanwarshi tazo na tabbata in yaji kece barin mu zeyi.. Ai Mark najin sunan yace kutsaya bade kece matarshi ba... Cike da kunya ta ga mishi kai .. Da sauri ya ce to muje na kaiku dan inyaji labarin kunzo nace se gobe nasan babu me rabani da shi se Allah..yana yi idonshi akan Mariyam kyar.. Itakuwa duk tabi ta tsargu da kallon Allah ma ya temaketa hijab dinta ya fice mata guiwa.... Yana gaba suna biye da shi har kusa da kofar office dinn.. Nan yace to ga office din nan.....Maysam tace mutafi Mariam... Murmushi tayi tace nifa ..kawai ki shiga ina jiranki anan salon in shiga ku manta dani....nan tasamu waje ta zauna Mark ma kuwa yace kwarai kuwa to ni bari na zauna na tayaki hira ko... Itade tayi mishi shiru ... Ganin maysam ta doshi office din yasa na matsa kusa da ita.. .. Kwankwasa kofar tayi ..amma shiru tasakeyi nan ma shiru kawai se ta murda ta shiga abunta A cikin bureau di kuwa lokacin Yana tattare kaya dan ya kasa sukuni kawai gwara yaje yaga maysam.... Jin an shigo yasa ya kalli kofar yaga waye ya shigo mishi bada izini ba.. Zumbur ya tashi tsaye ganin wata tsaleliyar budurwa mai kama da yar gidan momyn shi.sak..sake baki yayi yana kallonta se kuma yaga tayi mishi kama SWEETBABYN SHI.. Maysam kam da gudu tazo ta rungumeshi har saida suka fada kan kujerar dan babu zato ..tace yayana i miss you much cike da murna..... shi gogan ya zaci ma ko gizo ne take mishi harda dan mitsine kanshi yayi dan ya tabbatar ...shi kasa magana ma yayi , ganin bai ce mata komi bah kuma taga alamun mamakine ya cikashi Tana turo baki Tace haba yaya wai kai bakayi kewana bane da ko magana ma bazaka mun ba..kokari tashi tayi ... Ya kuwa kara matseta da kyar ya tattaro miyen bakinshi yace haba yar gidan momynta ni kuwa nayi missing dinki ba kadan ba.. Tunda yafara magana ta kafe bakin shi da ido (tofa Maysam gake ga bakin ci da biredin lol) ..shiru sukayi su duka kowa ya tsurawa bakin dan uwan shi ido...kowa yana zancen zuci Ita fadi take'' je t'en suppli embrasse moi'' yayana ..ohh ni ya Allah kasa yayi kissing dina yanzu.. Shima Murad anashi bangaren fadi yake miyasa bakya son inyi kissing dinki ..a gaskiya baki mun adalci ba ..ki barni kona second daya ne mana pls... Be ankara bah babu zato kawai saï ji yayi ta game bakinshi da nata wuri guda tana tsosar abunta kamar ta samu alewa dan zuciyar ta tabata wannan shawara cewa ga dama ta samu kada ta bari ta subce mata.... Murad kam duk da abunda yake so ne amman se yaki mayar mata da martani ... Can da taji ba ansa ta sakin bakin tana kallonshi.. Murad ya wani yamutsa fuska yace nide2 bana son wannan abun,kawai se ayi ta durawa mutum miyau gashi ma bakin ma se zafi yake mun.. Se lokacin ta tuna abunda ta taba fadi mishi wanccen lokacin a ranta tace ya rama kenan... A fili kuma se tace Shitttt tais toi et embrasse moi ( niko nace su Maysam yaushe kika kangare kika fitsare har haka...😳) Daurewa yayi duk da shock din dayakeji tun lokacin data rumgume shi amma ya fara mata wani salo na daban kissing din juna sukeyi har sai da taji abun yana so ya huce gona da iri sanna ta janye jikinta ta koma dayar Kujerar dake fuskantar shi ta zauna tana meda nufashi Shima kallona ta yakeyi Can Tace yaya ya kk?ya aiki E shi saï yanzu ma ya lura da kayan da ke jikinta after dresse ce baka tayi roling kanta da dan kwallin kayan kare mata kalo yayi yace ba tare da ya ansa mata ba yace tsaya ma bade da wa inan kayan kike fita ba? Duban kanta tayi tace haba yaya miye laifin kayan nan ? Besan lokacin da yace kin kasheni ...Kina Matar aure aman kifito bâ hijab da nikaf da safa?da kaji yanda yake maganar kasan ranshi ya fara baci .. Tayi rau2 da ido kamar zatayi kuka.. Kauda fuskarshi daga kallonta.. Dan ta kawar fa zancan tace Kash yaya na manta fah ba nikade bace tare da kawata Mariam nake..na barta waje ita da wani doc Ayya to tashi mutafi nima na tashi ai.... Har yakai bakin kofa ya juyo yace yauwa na manta ai de kinsan ba haka mukayi da ke ..ba ko?..seda nace ban lamunta ba da kiyi waya amman dan kin renani harda su facebook kike to bani ita nan ma... Marerecewa tayi tace haba wly Mahmud tsokanar ka kawai yakeyi ni babu wani su facebook din dana keyi ...tace kuma gama wayar ka duba ka gani. Se lokacin yayi ajiyar zuciya ..yace shikenan na yarda da ke ... Se kuma zancen makarantarki ..kisan de banida ra'ayi amma kika ketare dan tamakar ban isa da ke ba...to kuwa kima rubuta ki aje bab... Da sauri ta turashi tz gamashi da jikin kofar tasa hannunta ta dafe kofar.. shi kam ikon Allah yake kallo .. Tayi kalar tausayi ido cikin ido tace haba yayana kada kamun haka na kwallafa rai a karatun nan kuma wly saboda kaine kawai zanyi medecine fannin zuciya ..dan nasan irin kulawar da zanki baka nan gaba...kada ka hanani cika burina pls.. Tunda ta fara magana yaji tayi mishi kwarjini ..shi fa wani lokacin ma besan donmi yake kasa cemata a'a ba..kuma gashi ta cika shi da mamaki wai saboda shi to taya akayi tasan inada ciwon zuciya?ma Se kawai tsintar bakin shi yayi da fadin shikenan amma da sharadi... Na aminci kafinma naji miye sharadin.. Zaki dawo gidana dan kina matar aure zamman hostel be dace dake ba ..kai duk ma diya mace be dace ba in ba ya zamo dole ba kuma ma bare a kasar nan.. Seda ta bari ya gama tace ok yaya duk yanda kace haka za'ayi.. Ganin yanayin ta ya sauya yace miye kuma..? Maysam tace yaya kawaye na fa .tare muke tun muna can.kuma dayar ma budurwar Mahmud ce ... Ke bason wasa fa da gaske budurwarshi ? Wly yaya da gaske nake... Murad yace kice na samu abun tsokana..to yanzu de ba wanna ba se ku dawo ku duka ukku se ku zauna a bangarenki ....kuma yar uwar zamanki anata bangaren ko? Wani kallo take binshi dashi hawaye har sun fara mata zarya tace wai dan Allah kenan da gaske de kayi aure? Murad yace. Washhhh typing akwai wuya fa😥kuyi manage Fasma🖊(yar mutan Zinder) [03/08 à 23:18] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Allah abun godiya dama haka Fans din book din nan kukeda yawa ..kai amma na ji dadi sosai fa ina alfahari daku .ina ganin comment dinku...Allah ya bar kauna me dorewa ina yinku irin more totaly din nan*😍😍😍❤... _My Arfat ina kika shigene kwana biyu ....i miss you so mush...ke da my in Law xaynap queen_ 😥😍 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿85__86 ```Manzon Allah(SAW) yace ''wanda ya aibanta dan uwansa da wani aikin zunubi to ba zai mutu ba har sai ya aikata irinsa. Tirmizi ya rawaito shi``` . [03/08/18 à 23:01]Murad ya sa hannu ya goge mata hawayen dake diga daga idon ta yace haba yar gidan momy ina miki kallon jaruma kada kiba mata kunya mana ...kina yiwa kishiya kuka tun bakiga kishiyarba... Itade kallonshi take tama rasa mizatace. Ya sake cewa koda yake ma gwara kiyi kukan ki dan amariyata Allah ya zuba mata hallitar kyau gata fara ..hancin nan zurat dashi uwa uba kuma ga diri me dan banzan daukan hanka.. Da sauri ta rufe mishi baki da hannuta ta rumtse idonta se kuma ta fashe da wani sabon kuka tana fadin A'uzubillahi minna shayd'anin rajim Allahumma ajirni fi misibati wa....... Kallonta yake cike da tausayawa yace nine kuma shaidanin yau.. Ba tare data bude idonta ba tace pls bani hanya na futa .. Ze sake magana ..ta bude idonta wanda yayi ja tace pls in har ba sokake zuciyata ta buga lokaci guda ba to kaban hanya na futa... Ganin yanda idonta yayi wani ja besan lokacinda ya rumgumeta tsam a jikinshi yana fadin am so sorry i dn't mean to hurt you yana jin yanda zuciyarta ke bugawa da sauri2 ya kata matse ta sosai ..wasu ajiyar zuciya Maysam ta shiga saukewa a jere har de tajita ta dawo normal...raba jikinta da nashi tayi . tace pls mutafi Mariam na jirana ... Babu gadama ya bude mata dan yana gudun ya barko wani abun.. Zaune ta tarar da Mark se zuba zance yakewa Mariam ..ita kam tayi mishi shiruuuuu... Isowa tayi suka sake gaisawa tace da Mariyam su tafi... Mark yayi saurin cewa na gani fa pls ki ban numb kawarki tunda ita taki ta ban... Maysam tace aaa da garaje bada number ta dan an yi mata miji gaskiya Mark ya wani waro ido yace anyi mata beko ne? Maysam ta girgiza mishi kai . Yace Alhamdullilah tunda de haka ne ki bani kawai allura cikin ruwa me rabo ya dauka Maysam tace kasan de neman aure kan aure bashi da kyau ko? Kafin ya bata amsa Murad ya iso yana wani hade rai... .. Suka gaisa da Mariam Maysam na Ganin bakin Murad yana motsi da alamu wata magana zeyi ya sa ta tari numpashin shi da fadin am so happy yayana na yarda kai kaifi daya ne baka magana biyu na gode da barina da kai in cigaba da karatuna a hostel you are the best ta fadii tana dariyar yake ..and pls mutafi ka sauke mu kada magarib ta tarar damu anan.. Kamar bugun Wata guduma ,haka Murad yaji magagannu ta a ranshi yace mi yarinyar nan ke nufi ne?dago kai yayi ya kalleta ..,ta kuwa faki idon su Mariam ta zabga mishi harara.. Waro ido yayi yanamata kallon zamu hade ne.. Ita ma tamishi kallon se mi in mun hade dinn... Babu yanda ya iya haka ya kaisu ..a mota ma yi tayi kamar babu wani abun daya hadasu..se zuba zancen take tana dariya abunta Amma tana fakar idon su se ta zabga mishi harara...... 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹 A bangaren Madina kuwa da Murza basu san wainar da ake toya ba dadin rayuwar su suke ji karansu suke ci babu babbaka ..Murza an murje an wanku dan ko banza bata aikin komi kuyangi kemata ga ci da sha masu dadi .... Su Fulani kam suna nan suna shirya yanda zasuyi su tona asirin su Murza ...Mahmud yace mize hana musa ka camera a ko ina na gidan dan komi mutum ze fada ba llale bane a yarda amma in ka a zahiri dole koma waye yarda. Fulani tayi naam da shawarar nan sede matsalar anda zasu yi a saka a dakin madina ba tare da sun ankara ba ...dakin Murza bazasu sha wuya ba da kusan wuni wurin Madina take.... Dan haka suka yanke da asa a gidan Murza da gidan Murad duk da bayan nan ..dama nan bangaren fulani.. Sosai suke yin komi a tsanake cikin taka tsan2 da kada asamu matsala...Mahmud shike kan gaba..dan haka kullum Fulani cikin yi mishi addu'a take .. ... 🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Suna iso wa suka yi musu sallama suka shigewar su hostel abunsu Da kaga Murad kasan yana cikin damuwa haka ya juya suka koma shida Mark..shikam se zuba mishi zancen Mariam yake Su kam isowar su kenan aka fara kiran sallar ...bayan sun sauke farali ne Maysam ke sheda musu Murad ya yarda su koma su duka ukku can gidanshi da zama se yana kawosu duk safiya makarantar ... Ba karamar murna sukayi ba tare da cewa tayi mishi godiya kafin su mika tasu godiyar.... Wanka ta shiga tayi tare da doro alwala ..ana fara kiran sallar isha'i ta gabatar... Se kuma Mufeedah ta gabatar musu da abun ci data dafa musu ...amma Maysam kikam tace bata jin yunwa ..har suna tsokanar ta da mi yayan ya bata ne .... Itade dariya take musu aranta kuwa fadin take babu abunda ya bani se zallar bacin rai da kishi daya barni.dasu. Bayan sun gama Mufeedah ta fara koya musu lecture din yau da basuyi ba...suna tsaka da yi wayar Maysam ta shiga kara... Tana ganin kiran kuma tasan me kiran amma taki daga wa....har ta tsinke. ..se ana biyu ta daga ..tace salama aleikum yaya... Sallamar kawai ya amsa yace ki fito ina jiranki .a waje.be jira mizata ce ba ma ya kashe wayar shi... Haka ta tashi ta sauya kaya tare da daukan kayan data san tana anfani da su ta zuba a hand bag dinta.. Su Mufeedah kuwa sun zuba ido suna kallonta ...seda ta gama shirinta tsap tace to my tripleM ni na tafi seda safen ku. ... Mi zasuyi in ba dariya ba Mariyam tace to fa an zo wurin kawai kice de yau se kwana gidan yaya .. Maysam ta wani kada ido tace kwarai kam..to mi za'a fasa mutuwa ko ginin kabarin.. Mufeedah tace se kinyi kayan gidan Murad ..uwar gida ran gida alherin Allah ya kai mishi a duk inda yake..... Faddada murmushi ta tayi tace kai ki dau Mariam na baki ita kyauta..ladan ki..tace wanna haka yake fadi da karfi ki kara da ihu... Maysam har ta kai kofa tace pls ku shirya kayan mu duka gobe zamu koma din ....sannan pls ku dau lecture da kyau koda ban samu zuwa ba se ku koyamun ..kunsan mu matan aure se a hankali.. Mariam tace wai yaushe kika fitsare kanane abun naki ya fara ruko ido.. Mufeedah tace kede barta bamu iya mata jeki seda safen ..... Haka ta fice suna ta barkwan cinsu... Tana zuwa sallama kawai tayi mishi tayi wani kikam.. Amsa sallamar yayi yace ke shigo mutafi.gida.. Tana tsayen tace nifa babu inda zani ..kuje can kuyi zamku kaida amariyar ka na barmata kai..na hakura gaskiya..nifa ina ga ma fasa karatun nan zanyi na koma can gida.. Yar dariya yayi yace kai da kuwa kin bada mata inba abinki ba wa kika taba ganin ta barwa kishiya Miji ...harda barin karatun da kikaci buri akanshi... Shiru tayi mishi dan itama tirjine kawai bawai dan zata iya bar matan ba..ayanda take jinshi a kokon zuciyar nan tata ai sede amutu akanshi Murad ya sake fadin shigo mana..inada abunyi fa. Zaga yowa tayi ta shiga se wani turo baki gaba take... Hanyar gidan shi ya kama ...ganin taki sakin jikinta yasa ya kamo hannunta ya gama dashi yana tukin..yana fadin kai uar gidan Momy mi take bakine haka kikayi sauri girma ne... Wani mayan shok ya ziyarci Maysam tun lokacin daya dora hannunshi a nata... A ranta tace inda bari na gwada wani abu na gani.. .. Kamo hannunshi guda tayi ta shiga wasa dashi ...kawai beyi aune ba yaji tasa yatsarsa guda cikin bakinta.... Eee oga Murad kusan sakin sitiyarin yayi yace ke bakida hankali ne . Maysam tace to ni minayi ne kawai dama mutum ba wani iya tuki yayi ba. ...sallon a yarda mutum bayan ni din yarinya ce me tsada...a ranta kuwa cewa tayi ashe de da gaske ne wanan abun yana aiki .ai kuwa wly nima sena gana ma zuciyarka wuya kamar yanda kake yiwa tawa yanzu.. Murad kuwa cewa yayi ina tsada anan bayan amariya ta ma ta fiki tsada ..kinga kuwa koba kya nan ina da wata amariya me tsafta ,aji,etc. A ranshi kuwa fadi yake ee fa nina san irin tsadar ki....yar renota Itade shiru tayi mishi tana dariyar mugunta ita kade... Suna isowa suka firfito ..gaba ya shige tana gunguni tabi bayan shi ..har suka shigo falon Murad yace kin kyauta ci gaba da zagina.. Wani waro ido tayi tace zagi fa kawai cewa nayi nide kasan yanda zakayi da matarka dan kada ta bari mu hudu da ita..wly dan sak yarinya tayi mun sena kareraya ta .. Dama ya sako? bazata iya zaginshi ba kawai de yaji tana ambaton martarka shiyasa yayi mata haka ....yace kin ga nan ma bangarenta ne naki yana baya ..dan bata nan ne tayi tafiya se bayan kwana biyu zata dawo kinga seki zauna nan kan ta dawo kuma kafin nan an gyara miki naki bangaren kuma wanan umarni ne nake baki na ki zauna anan din dan bana son hayaniya...kuma ai dama taya ma za'ayi ki ganta matata ai me ganinta seni kade dan tsada gareta ga zubin zallar kyauu.... Tayi dariyar takaici tace really tana da kyau har hakane dakaketa yabonta ne.. Murad yace ai fadin irin zallar kyau nata ma bata baki ne.. Maysam a ranta tace bari kaji yanda nake jide daure fuska tayi tace ta kai SWEETBABYN KA kyau ne? Tofa kunji wata tsokana ko? Muje de zuwa Ina yin ku 😍❤❤❤ Fasma ce 🖊yar mutan zinder For comment or contribution :+22799951593 [05/08 à 13:49] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Love you my fans irin more din nan❤😍😍 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿87__88 ```Manzon Allah (SAW)yace''kada ku yawaita dariya domin yawaita dariya yana kashe zuciya Bukhari ya rawaito shi.``` [05/08/18 à 12:37] Cak ya tsaya daga murmushin ma daya ke ..wani kollo ya shiga watsa mata yace..'comment oses tu ki gamata da Babyna ?ita din banza ,,,yo ko kafar SWEETBABYNA ta isa ta kamane..ke ke...ke maganar ta makale mishi ya ma kasa fadar komi ..kadan2 ya tunkaro ta .yana nunata da yatsa yace wly ko sunan ta naji kin sake fadi na lahira ma se ya fiki jin dadi ... Maysam ta tsine fuska tana kalloshi se kuma tace ai kam yanzu na fara fadi sunan sweetba... Daga hannu yayi da niyyar wanka mata mari .. Wani kallo naga tayi mishi tare da marerecewa hakan yasa shi aje hannun shi babu shiri yace kinci darajar Momy wly fuuu..ya haye strain yana huci shikade a ranshi fadi yake yo koke da kike kama da aljanan baki kai ko rabin sweetbaby na ba...mtsssss Ta dan jima nan tsaye se kuma ta shiga nema kitchen da kyar ta samu inda yake. Komi na bukata akwai aciki kama daga..har zata dafa wani abunci dan wata bala'in yuwa takeji. ..se kuma tayi dariya tace baride na bashi wahala bade ni yayiwa kishiya ba ..to ai shima ze dandana yaji... Itama mara mishi baya tayi tana fadin wly dani kake zancen .. Dakin dake kallon wanda ya shiga itama ta shiga ..ganin daki tsaf dashi komi a gyare agoge tsaf..bude wardrop tayi taga kayan mace acikin wani abu yazo ya tsaya mata amakogaro tace kenan de da gaske bangaren matarshi ne ya kawoni dan tamakar banida galihu awajenshi... Duk seta ji bazata iya zama ma a dakin nan bare har ta kwana ciki .... Tana ta wanin ya mutsa fuska da kyar ta shiga tolet tayi wanka tare da doro alwala ..jakar ta ta dauko ta saka rigar bacci wacce da kadan ta fice guiwa ..tayi shafe2n ta ..sannan ta fice a dakin .... Direct dakin data ga ya shiga ta shiga babu ko sallama .. Shikam lokacin fitowarshi a wanka kenan daga shi se towel .... Maysam kallo daya ta mishi ta kauda kai direct gado ta hau ba tare datayi me magana ba... Shikam yanzu tsoro ma take bashi.. Shima shirin shi yayi tsaf ya kwanta a dayan bangaren....batare dayace ufan ba Can da kamar minti 20 cukin Maysam ya fara kukan yunwa kuuuu kuuu... Tun tana daurewa har ta kasa nan ta fara kiran yaya ...yaya.. Yana jinta yayi mata shiru... Tace pls yaya yunwa nakeji.... Nan ma shiru... Nan tashiga shure2 tana fadin ita yunwa takeji tama meda abun waka Yace ke wai bakiga dare yayi bane kije kichen ki dafa abunda kike so ki banni ni nayi bacci na Dan galgal ta zauna bisa gadon ta shiga rera mishi kuka ita yuwa takeji.kuma ai shawarma take son ci yanzu Ganin fa da gaske ba barinshi yayi bacci ba zatayi ya sa ya daka mata tsawa... A memakon taji tsoranshi se kawai ta koma ta kwanta tare da rushewa da wani sabon kuka tana fadin yanzu da Momy ce da ta san yanda tayi dani ...ke koda su Mufeedah ne da sun tashi komin dare su girka min amman abunda nake so kawai an kawoni ne daman dan a azabtardani da yunwa.. Dafe kanshi yayi ..yarinyar nan fa ta fara caza mishi kai ..yace wai ke bakya ganin dare yayi ne kibari har zuwa safe mana.. Maysam tace nide a'a wly yunwa nakeji kamar naci babu..da kasan baza na kulawa dani ba donmi ka kawoni.... ? Babu shiri ya zari jallabiyarshi tare da key ya fita..ai kuwa mi Maysam zatayi in ba binshi ba.ta zaro hijab ta kuwa goge hawayen da dama na rigimane kawai...be lura da ita ba seda yazo fita a fallon ...ze kulleta tace a'a tsayani mana mutafi tare... Kare mata kallo yayi hijab ne kawai ta dora a bisa rigar yace ke ina zaki kuma ....da. Wannan kayan kuma.... Kai tsaye tace rakiya kawai zanyi maka ... Be kara cewa komi ba ya shiga motar itama tashiga ya tada me gadi ya bude musu suka fice.... A wani restaurant yayi paking ..yana kokarin fito wa yaga itama zata fito da sauri ya koma ya zaune tare da kama hannunta yace ke bakida hankali ne zaki fita ahaka ? Turo dan bakin nan tayi tace wai komi se kace bani da hankali... Kallonta yayi yace to inba rashin hankali ba ya za'ayi ki fita da wanna shigar mtsss ya ja tsuka.. Maysam tace inde har baka so na fita to kiss me ...sena hakura nayi zama na a mota ...kai ko masu ficewa ma bazan kalla ba.. Waro ido yayi yace wai ke yaushi kika fitsare ne haka... Far tayi da ido batare da ta bashi amsa ba tace pls yunwar fa se karuwa take .kai kuma se wani bata min time kake..tayi tirjin kamar zata bude ta fita .. Da sauri ya jawota ya shiga kissing din nata ..su oganniya Maysam har wani lumshe idanu take burinta ya cika dan ita kam da zaya ciro bakin ma ya bata da ta yarda ..sun dan dau lokaci sanna ya saketa.. Maysam tayi Murmushi tace kokai fa ...yanzu jeka ina nan bazan fitaba .. Bece komi ba ya fita a ranshi kuma fadi yake wai taya akayi yarinyar nan ta fitsare haka.shi yasa fa bayason karatun turan nan..?(ni kuwa nace babu wani turai ai renon kace ...ko ka manta tun bata san sunan abunba ma kake mata shi ,,ka saba mata da dorata cinya a kowani time ..se yanzu dan tana ramawa kace baka san ya akayi ba ku jiye mun shi....🙄) Ice cream ,shawarma,snake ne ya sayo musu ..da kuma gassasun kaji😋..dan gashin su yana yi mishi dadi Suna dawo wa dan iya shege irin nata shawarma daya kawai taci se ice cream shima roba daya tace ya ishe ta .. Murad yace kai amma yarinyar nan kin raina duniya .. ..yunwar kenann... Oya sauko kice ya bude kajin.....kikam tayi tace bataci .. Murad yace walahi baki isaba dole se kin ci.. ki sani na fita da daren nan amma ki ki ci... 🤣🤣wai fans kusan miya hana ta cin kajin ne? Wai fa ita tsoro take ko na amarcinta ne shiyasa ma taki ci bayan ta hada miyanta.. Daga baya kokarin guduwa daki ma tayi ..aman Murad yayi saurin kamota ...ya dorata bisa cinyarshi(to baga shi nan ba🙄 )ya shiga bata tun tana dari2 har ta sake jiki taci abunta.. Bayan sun gama ta tattare komi takai kitchen ... Brosh sukayi sukabi lfyr gado... Maysam kam matsawa tayi ta shige mishi jiki kan kace mi bacci me dadi yayi awon gaba dasu.. Tun asuba bata koma bacci ba kamar kullum... Murad yana shigowa ya ganta bisa sallaya se karatun alqur'ani take..sata gaba yayi ya tankwashe kafafu ya wani rufe ido wai muryar tayi mishi dadi..a hankali yake bin ta suna yi tare.. Seda takai aya ta Rufe ta ajeshi tace yaya g. morning...da fatan ka tashi lfy... Murad yace ina fa na tashi bayan duk kinyi ta laftamun kafa ni duk jikina ma ciwo yake mu..kai dole ma ki koma dakin ki. Maysam ta turo baki gaba sede batace kalaba..amma a ranta fadi take babu inda zani ina nan .dan bazan iya kwana a dakin waccar abar ba ehe Sun danyi shiru .Maysam tace kai yaya babu ko dan Morning kiss din nan ma .. Kallonta yayi yayi yar dariya yace waike bakya gajiya ne.. Kara turo bakin tayi ta tashi ta shige tolet tana zuwa dede kofar ta murguda mishi baki tace e din ai duk renonka ne kai ka koya mun... Wanka tayi koda ta fito baya nan ya fice dayan dakin yin wanka tunda taki zuwa ita.haka tayi shirin ta na school dan gudun magana se tayi irin shigar dayake so wato hijab nikaf da safa.... Dukda kuyangin da suke nan sun yi musu abun break aman Maysam da rigima seda ta sake girka wani a ranta tana fadin kenan ma harda kuyangi ya samarwa matarshi ko ...humm..(kya de ji da kishinki🙄) Mafi saukin break tayi wainar kwai,da plainted se ruwan tea ..nan palo ta saka kuyangi suka jere mata su... Ta zauna kenan ya fito daga room da shirin shi shima ..zama yayi a kasa kusa da ita Maysam tace yaya ga naka can fa wannan nawane wanda na girka fa ... Murad yace to nakin zanci nima me rowa kawai. Shiru tayi mishi nan suka fara break din ...suna gamawa ya kaita har kofar school din su ..ya shiga wurin principal din yayi mishi bayanin komawar su can gidan shi... Abunku da jami'a kuma ma ta turai dan haka sugaban be wani nuna wani abuba ya bashi autorisation din zasu iya komawa ... Daga nan ma ya fice wajen aikin shi... Haka kuwa akayi bayan sallar isha'i suka tattara komi nasu suka zuba a motar Murad hann se gidan shi... Ganin barin mata su kad'e a bangare daban hatsarine duk da akwai dedekun dogarai a gidan amma it is a risk dan haka ya basu dakuna biyu na nan kasan bangaren dayake ikirarin na kishiyar Maysam ne ... Shikuma suna dakunan sama da Maysam .. Har Maysam na tambayar shi to in me bangaren ta dawo fa mi ze ce mata ne... Ya bata rai yace ke ina ruwanki ne.. Haka sukayita zama a nan gidan Murad cikin kwanciyar hankali suna kuma karatunsu sosai da sosai....shakuwar su ma kam se abunda ya karu Ana haka bayan two week ya shirya ze tafi ganin gida ..Maysam kamar tayi hauka ba dan ta kwallafa rai a karatun nan ..da babu abunda ze hanata zuwa gida ganin fulani..ranar daze tafiya sha kuka har yaji kamar ya tafi da ita da kyar ya samu ya lallabata ya tafi .. Ko su su fulani dirar bazata yayi musu dan ko jiya Mahmud daya kirashi kan cewa yana so in ze taho ya zo mishi da camera kamar goma haka hight class nacan ...koda ya tambayeshi yaushe zezo se ce mishi yayi kawai se sun ganshi .. Zo kaga murna wajen Fulani kamar mi tama rasa inda zata saka shi nan suka gaisa ya kara neman yafiyar ta... Tace dashi yanzu de ya shiga ya gaida dadyn shi se ya tafi yayi wanka yaci abinci ya huta daga baya sa yi magana .. Babu bata lokaci ya cika umarnin ta .. Fulani se kara godiya take ga Allah ..tana me kara addu'ar ya kare su daga sharri masu sharri.. Yana shiga wurin Sarki ya tarar da Madina acan da alama de wani muhimmin abu ya kawo ta dan basa shigowa fada a yini rana sede da dare.. Wata zabura da babu shiri Madina tayi cike da mamaki take kallon Murad a ranta fadi take yau ni naga jarababbe dawo kayi..in ba ma mas... Bata gama fadiba Sarki yace lfy de ko..? Wayence wa tayi da fadin farin cikin ganin d'ana ne nake yayi mana zuwan bazata ne tana wani dariyar yake amma da ka ganta kasan bata da gaskiya se wani fiki2 da ido take. Sarki ma shareta yayi dan murnar ganin Murad din ya rumgumeshi yana jin dadin ganin tilon dan shi.. Madina ta danne abunda ya taso mata tare da cewa bari na baku wuri zamu karasa maganar daga bayama ..sum2 ta fice tana saka da warwara... Sun jima suna hira da dadyn shi .....sanna yayi mishi sallama ya fice..Yana zuwa bangarenshi ya tarar da Mahmud yana jiran shi.. Rumgume juna sukayi suna me jin dadi ..nan ya sake bashi hakuri kan abunda yayi mishi .. Mahmud ya nuna mishi komi ya fice ...... Murad yace ga camerorin ka daka damen da zancen su .. Cikin sauri da hanzari Mahmud ya karbe yana fadin kai amman na gode Allah ya biyaka .. Murad yace wai ni mi zakayi dasu ne haka da ka wani azalzaleni ne akansu. .kaida ko budurwar taka ma na can England se ko yan gida zakana dauka halan .. Mahmud yayi dariya yace kaide yanzu ka yi me wuyar sauran zance zakaji shi wajen Momy ..yana fadar haka ya sa kai ya fice tare da fadin Allah ya hutas da gajiya.. Murmushi yayi shige bathroom.. A bangaren Maysam kam bata san ta shaku da yayan ta ba se yau ta saka waya gaba tana kallo.. jiran kiranshi kawai take ya shigo amma shiru...ta kirayi Fulani bayan sun gaisa take sheda mata mijinta ya iso lfy ..sun fan tattaba hira tukon suka kashe.wayar.. Shikam Murad dayayi wanka yaci abinci sanna yazo yabi lafiya matela amma kuma se bacci ma yaki zuwa se lokaci tunanin yar renon shi yazo yayi mishi katutu besan ya kara shakuwa da ita ba se yanzu ..duk se yaji gadon yayi mishi fadi..wayarshi ya jawo ya danna mata kira .. Maysam da rigima wayar na hannunta fa aman se akira na ukku ta daga ... Sallama yayi kafin ma ta amsa yace ina kika shiga ne kikabar wayar ina ta kiranki... Turo baki gaba tayi kamar yana gabanta tace ina na shiga ko ina ka shiga ..bayan ma kai ka manta da ni din.. Dafe kai yayi yace inji wa kekam bakya rabuwa da rigima. Fa.. Ai nan ta shiga zaba mishi shagaba kamar ba gobe da kyar ya lallabata ...... Suka taba hira sanna ya kashe wayar Se lokacin ya samu baccin ya dauke shi ....bashi ya tashiba se gabbanin azahar alwala yayi ya fice masalacin masarauta.... Daga nan kuma ya fice bangaren Fulani.. Tana lazimi ya shigo da alama itama yanzu tayi sallar seda ya bari ta gama sannan ya sake gaisheta ...nan suka cigaba da hirar su har tana tambayyar yar ta Maysam tace inji de baka matsa mata ko.. Murmushi kawai yayi aman a ranshi fadi yake ai yanzu kam ita take matsa min abu kadan se take kiss me ..gashi ko kallon banza bana iya mata ... Fulani ta katseshi da fadin nasande Mahmud ya sanar maka da komi ko.. Kalar tunani yayi yace akan mi fa ? Nan fulani ta sanar mishi da komi kan su Madina kafin ta gama hawaye na tazuba ..kamar karamin yaro ya rarafa ya dora kanshi bisa cinyar ta yana kuka .. Nan ta kara yi mishi nassiha tare da gaya mishi plan din su sosai yayi na'am da shawarar nan yakara shima tashi fasahar .......sosai yaji dadin irin yanda Mahmud ya nuna bajintar shi lallae ya cika aboki....... A washe garin ranar aka saka camerorin anan bangaren Fulani dana Murad ..kai harda na bangaren Murza ma ..na Madina ne kawai yayi musu saura... 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 A bangaren Madina kam tana fita ta dannawa Murza kira ...babu bata lokaci da shigo bangaren nan cike da zafin rai da bacin rai take sheda mata Murad ya dawo gida yanzu nan .. Murza tace kai ni wannan jaraba da mi tayi kama ..yaro nan dan bala'i ne ..yakama wanna karon muyi mishi me kan kat kawai.. Madina tace kawai kice ya haukata muna shi kiga kawai ma may be mota ta kadeshi ma ya mutu a yawon haukar tashi ...... Murza tace karai kuwa kawai hakan ma za'ayi.... Nan ta sake zube mata kudi .Murza ta faki idon mutane tayi satar hanya ta fice ...se gidan boka yankan adda... Tofa ya kuke gani ?shin zasu sake cin nasara ne akan Murad? Senaji comment dinku👆 Fasma 🖊yar mutan Zinder [07/08 à 00:13] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Ohh my Aisha tu me manque déja ...wish you all the best😍❤❤❤❤...* love you irin sosai din nan _My Mimsqueen Allah ya baki lfy ya sa zakkar jiki ne...🙏.._ Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 89__90 ```Manzon Allah (SAW)ya ce''idan wani daga cikinku ya tashi daga wajen zamansa sannan sai ya dawo to shiyafi dacewa da wajensa. Bukhari ne ya rawaito shi.``` [06/08/18 à 20:29]Ba ta dau lokaci ba se gata gaban boka yankan Adda ....nan ta kwashe dawowar Murad ta gaya mishi tare da sabon kudirun su.... Ya dan jima yana dan tsibacce2 shi har wata zufa take karyo mishi........can ya dago yace wannan aiki baze yiwu ba dan yaron a tsare yake ya fice inda kuke tammahani.. Murza tace to kawai ka haukatar mun da matar shi Maysam. . Sake yan tsubucce2 yayi yace ita kam wannan tama fishi sammun kariya dan ta rike addu'oi baza mu iya yi......ganin irin kallon da Murza ke mishi irin kallon nan ne na in bazaka iya ba kawai bari na nemi wani....a ranshi yace wannan fa batada mutunci yanzu seta tafi abunta batare da taban komi ba ...amma bari na mata irin ta mu ta yan iskan gari.. Wata dariya ya kwashe da ita lokacin har tana batun tafiyarta jin bukatar ta bazata biya ba gwara ta nemi wani gun.. Yace koma ki zauna aikin ze yiwu amma za'a kashe makkudan kudi dan wannan aiki ja ne.. Washe baki tayi tace yanzu naji zance me dadi.....to ina jinka.. Wani turare ya bata cikin kwalba yace gashi wanna asan yanda za'ayi ya shaki kamshi nan ..to ina tabbatar miki yana shaka kamshi ze gusar mishi hankali...sede wani ba shiba... Murza jitake kamar tayi fiffike ta ganta a wurin Madina ta sheda mata wannan daddan labari ....... Tana fita bokan ya kwashe da dariya yace zaku san dani kuke aiki ... Ba'ataba kawo min aikin danaga bazanyi nasara ba se wannan .kawai har kunsa na fara ji akwai abunda ze gagaren a duniyar nan..hhhh.. Yayi wani kirarin shi can kuma yace se kai dan hatsabibi ka bita kawai tana fito da turaren ka kwabeshi ya zube sanna ka bayyana siffarka ga wanda duk ya shaki turaren nan dan suyi hauka me degree kowama ya huta..dan in shi Murad din ne babu abunda zeyi mishi ..ni kuma bazanyi asarar turaren nan ba...fuuuu ya fice dan cika umarni.. Tana zuwa direct bangaren Madinar ta fice bakin nan se wageshi take ... Madina tace da alamade anyi nasara yau.. Murza tace kwarai kuwa dan kinga ma abunda ya bani ta fito da turaren zatayi wa Madina bayani ai kuwa Hatsabibi ya kwabeshi kwalba ta tarwatse a kasa turare ya zube anan.. Wani waro ido Murza tayi se kuma ta dauke numpashinta a million ta bar bangaren Madina dan ita tasan hukuncin wannan turaren... Ko iida fita daga palon batayi ba taji Madina ta kwalla wani uban ihu e kuwa se takara gudun ta har seda ta fita tukon ta dedeta nutsuwarta dan kar wani ya ganta.....gidanta ta shiga can kuryar daki har da saka sakata. . jikinta banda karkarwa babu abunda yake..kamar ace mata ke ta arce se wani waware ido take..... A bangaren Madina kuwa hauka turben takeyi kuyangi duk sunyi cirko2 a kofar dakin dan kana shiga inta damke babu me rabaka da ita dukan kawai zatayi ta lakada maka duk abunda ta rarima buga maka zatayi ..ga dariya ka-ka-ka tana fadin nice nan ajalinshi kamar yanda na zama ajalin dan uwanka da sweetbabyn ka..da waziri hhh Walahi yau sena kashe ka ..tun kana cikin zanin goyo nake bibiyar rayuwar amma kaki mutuwa to yau sede wani ba kai ba.. Lokacin labari har ya isa ga sarki dama suna zaune ne a fada harda Musa da Murad.dakula Mahmud .ai kuwa a tare suka shigo fulani ma isowarta kenan..sukaji tana tonawa kanta asiri ..kaf makircin datayi seda ta fadeshi yau .gaba daya aka dauki kabbara tare da da fadin inna lillahi wa inna ileyhi rajou'oun.......Malam Musa duk jikinshi yayi sanyi jin harda Diyar Maysam a harinta amma se ya shiga yiwa Allah godiya daya kubutar mishi da ita.... Fulani kam har ta fara hawaye jin itace ta kashe mata danta data haifa na Fari wato yayan Murad wanda ko sunanshi ba'ayi ba ya mutu ......kasa tsayawa tayi ta koma bangarenta cike da tausayin kanta da kuma tausayin Madina jin irin rayuwar data saka kanta saboda kishi kawai..... Murad nan ya zube ya shiga rera kuka jin da sa hannunta ya rasa rabin zuciyarshi ...,,,Mahmud ya rumgumeshu yana bashi baki tare da yi mishi yar nasiha..da kyar ya tsagaita ya rakashi har bangaren shi.... Ganin abun kara gaba yake Sarki yasa akayi mata allurar bacci shima iya tashin hankali ya shiga jin ita ta kashe mishi dan shi na fari ...ba dan yana kumyar mahaifanta ba da shi kade yansan irin hukunci da zeyi mata ..to mahaifinta sarkin garin Diffa ne duk da yanzu ya tsufa ya barwa danshi na fari to amman akwai alkunya a tsakanin su ...akwai mutunci ...dan haka ya daga waya ya sanar mishi komi .... Mahaifinta dantakon arziki kawai cewa yayi a mata hukunci dede da abunda ta aikata ... .. Sarki Mustapha ya roki alfarma kawai da za'akowa ta nan de.. Da kyar mahaifinta ya aminci ..aka kuwa kara mata wata allurar bacci aka sakata a jirgi han se Diffa.... Ayya munai miki bankwanan se wata rana 🤗wannan shine ake kira da kaykayi koma kan mashe kiya ..tana fatan haukata Murad gashi ta haukace ita din ...to hattara de Inna Murza abi duniyar nan a sannu .. saura ke.. 'Muje de zuwa.. 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Wunin ranar babu wanda yayi shi cikin jin da dadi kowa yana jimamin abunda Madina ta aikata ..bama kamar wanda tayi wa abunba....danshi Murad ciwon shi ma yake son tashi.. Har dare Murad be kirayi Maysam ba......karfe takwas na dare ya tuna da ita har ya danna kiranta se kuma ya tuna yanzu biyu na darene acan ..har ze kashe ya ji ta daga.kiran.. Da kuka tayi mishi sallama ..seda ya sauke ajiyar zuciya yace mi kuma akayi ne kiyi shiru ki fada mun ..jin murya shi wani iri yasa tayi shiru tace yaya mi ya sameka ne bakada lfy naji muryarka wani iri.. Ya ce mata banida lfy ciwona yake son farmini ... Wani waro ido tayi tace inna lillahi wa.....garin ya ? I mean mi ya tado maka da shi ne ..?.kamar zatayi kuka take mishi tambayar... Da kamar baze fada mata ba se kuma ya gaya mata duk abunda ya faru yau.... Banda inna lillahi wa ... Babu abunda take fadi Duk jikinta se yayi sanyi tama rasa abunda zatace mishi ..se kawai ta fashe mishi da kuka.. Shima cikin sanyi yace haba dami kike so naji ne da ciwon dake damuna koda kukan ki ne..dan har cikin ranshi yake jin kukan nata.. Shiru tayi tana ajiyar zuciya tayi matukar tausaya mishi ..nan ta dedeta nutsuwar ta shiga yi mishi nasiha tare da kallamai masu sanyaya zuciya ...... A ranshi yace kenan de yarinyar nan ta iya kwantar da hankali dan A kashi dari yaji kashi 40 na damuwar ya rage mishi ...yace yanzu fa biyu na dare ne ki kwanta kiyi bacci kinga gobe akwai school kada ki makara... Tace to naji amma pls kaci wani abu kafin ka kwanta dan nasan wunin ranar nan da kyar ne inka ci wani abun ..pls promise me zakaci sannan kasha maganin ka Promise kawai yace mata.... Nan ya kashe wayar ...babu laifin ya dan ji karfin jikin shi kadan.. Tana saukawa da zumar shan koda tea ne dan itama kusan wunin yunwar tayi da kawai be kirata ba ..ga mamakinta ta tarar da Mufeedah suna hirar itada Mahmud.a waya.zama tayi tare da fadin pls kice mishi dare yayi anan gobe akwai school sannan kuma ya tafi ya kular min da mijina baya jin dadi yanzu ... Duk abunda take fadi Mahmud na jinta sarai ..a hand free Mufeedah ta saka wayar yace to masu miji naji kada ki damu zan kula miki da shi ... Babu ko kunya tace kai aman fa na gode nima kam zan kula maka data ajiyar ta nan.. . . Se kuma ta jajanta mishi abunda ya faru ..daga baya sukayi sallama... Tea tasha ta haye sama dakin Murad abunta.dan har yau taki ta koma dakin wanda take ganin na kishiyarta ne.. 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 A bangaren Murza kam jin asirin ta be tonu ba yasa ta saki jikin ta kamar bata san komi ba ..sede kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa ..duk gani take itama haukacewar zatayi....fita ma kam yanzu ya gagareta kullum kunshe cikin daki ..abun har mamaki ya koma bawa M.Musa sede beyi mata magana ba. 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 Satin shi biyu ya fara shirye2 komawarshi ..sarki da fulani suka sakashi gaba suna yi mishi nasiha dan tunda abun ya faru mutawar sweetbaby ta dawo mishi sabuwa abu kadan se ya fara zazzaga fada ... Fulani tace kuma wly in kasan hantarar y'ata zakayi to tun wuri ka medasu hostel dinsu ..dan kada fadan nan naka ya hanata karatu.. To kawai yace aman a ranshi cewa yayi da kinsan abunda yake faruwa da bakiyi wannan maganar ba... Shi fa komin bacin ran da yake ciki komin fadan dayake yi inde kiran wayarta kade ma ya shigo to se yaji zuciyarshi ta sauko ..in har suna waya kusan mantawa ma yake dayana da damuwa bare inyana tsokanar ta ita kuma tana sauke mishi kwandon shagwaba..se yaji ya tafi ...ko tafiyar nan surprise ce ze mata kuma gashi ta matsa mishi da yaushe ze dawo ne.. Haka suka mishi fada da nasiha shide da to yake amsawa tare da ban hakuri...karfe goma jirginshi ya daga se England. ✈ ..safe a good journey To nima bari na daga haka nan .... Muje zuwa fans Love you all❤😍 Fasma ce🖊(Yar mutan Zinder) [10/08 à 09:45] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu* Dedicated to all my fans😍❤ 🅿91__92 ```Manzon Allah(SAW) yace '' wanda baya roko a wajen Allah to Allah yana fushi dashi. Bukhari ne ya rawaito shi. ``` [09/08/18 à 23:26] karfe Biyu saura na rana jirginsu ya sauka a England ..lokacin su Maysam suna school basu sauko ba. Amman ko ina tsaf2 da shi duk da kuyangi ke gyara dukuna aman banda nata da na oga Murad.. Yana shiga dakin wani sanyi kamshi ya buge hancinshi besan lokacin da da lumshe ido ba tare da yin ajiya zuciya. ..wanka ya shiga yayi ya fice masallaci ..dayake bashida yunwa dan haka can yayi zamanshi har akayi la'asr anan suka gamu da Mark suka gaisa yayi mishi sannu da zuwa har yana jaddada mishi aiki na nan jibge a office din shi. .suna ta hirar du har suka iso. kowa yayi gidanshi duk da har yau Mark beyi aure ba aman yana da gidanshi anan kuma kusa dana Murad yake . ... Yana zuwa kawai ya hau gado ga gajiya yana ji amma yasan baze iya yin bacci ba ..dan besa ba baccin bayan la'asr ba.. Gadon kawai ya hau ya shiga chat a whatsapp.... Katsam yayi karo da number Maysam kuma gata online..a ranshi yace karatun kenan? Salut(hello) ya aika mata Ai kuwa se gashi ta medo mishi da salut yayana comment vas tu?ita kam bata ma lura da wata numbershi ce suke chat din dan duk numbers shi MURADINA ta rubuta akai wasu da manya haruffa wasu kuma da kanana .shiyasa bata babanta su. .. Be amsa mata ba se cewa ma yayi karatun kenan. ..kuma ma ashe da gaske ne kina chat dinko? Wani yawu ta hade tama rasa irin amsar daza bashi .. ..dan ta kawar da zancen tace kai yaya wly nayi missing dinka dayawa kuma ma Momy tace tabaka sakona pls yaushe zaka dawo ne..brcause i need it dan wanda nazo da su sun k'are . Ya ganeta sarai amman seya biye mata dan yana jiranta yau seta gaya mishi tun yaushe ta fara ..... Sun dan taba hira inda take sanar mishi ai har sun tashi ne driver suke jira bezo ba...amman yanzu zasu koma gida ...sallama sukayi tana ta murna abunta jin yace mata cikin satin nan zezo... Su Mufeedah kam se tsokanarta suke tana ramawa.. Tun nan palon taji kamshin turaren sa amman seta basar..ai kuwa tana haurawa stair hancinta ya tambbatar mata da kamshi da karfi2 cikin hanzari ta tura kofar dakin ... Tana hangoshi da gudunta ta isa batayi wata2 ta fada kanshi dan murna tana yayana sannu da zuwa yaushe kazo ne... Rumgume juna sukayi ..sun dan jima a haka sannan ya saketa suna kallon juna tace ina Momy na ?.yanda ta wani langwabar da kai se yaga tayi mishi kyau . Yace tana nan she is fine ..tace tayi missing din ki .itama. Kwalla har ta ciko idonta tace nima nayi missing dinta a lot.. Goge mata hawayen yayi yana kallon dan karamin bakinta yace me rigima yau babu ko dan kiss din ma na welcom back.. Ya tsine fuska tayi tace ee..saboda na gaji da abun... A ranshi yace kenan de taji zafin maganar dana yi mata ranar nan.. Basarwa yayi shima ..ya dan daure fuska yace ban wayar ki ...tunda de ke bakya jin magana ....dan na san a chat din nan kika koyi wani salo2 .. Bashi wayar tayi ba tare da ta musa ba. Se kuma tayi haramar tashi ta bar mishi wurin .. Dawo ki zauna yace da ita.. Ya shiga duba wayar ..whatspp kawai ne take shima numbers fulani data shi seta su Mufeedah ....jikinshi yayi sanyi ganin da alama ma yaune ta bude shi kuma Momy ce tasakata dan tayi mata baya nin sakon maganin data bada akawo ma ..se tana turo mata photon duk magani tare da yanda zatayi anfani da shi. Kamar su Misk, bagaruwa,ganyen magariya dade sauran su se kuma advise din ta zanki shan fruit a kai2... Se kuma turarikana wuta dana shafawa kamar su humra,kullacca etc.. Ita kam se turo baki gaba take tunda har be yarda da ita bane harda yake tamata bincike a waya..koma yana gane mata sirrinta na ita da Momy Murmushi yayi ganin fa tayi fushi ...bakin ya dan buga kadan yana fadin ke bakinsan wata dununuwa kike komawa inkayi fushi ne... Kamar wasa kawai yaga hawaye shar2 a idonta ..... Hankali tashe yake tambayar mi akayi mata daga dan bugan nan se kuka... Maysam tace dama yaya baka yarda dani bane ... Waro ido yayi yace in jiwa ?kinjiki da wani zance . .ke kam bakya rabuwa da rigima.. Maysam tace ba gashi nan ba har da wani min bincike a waya.. Murad ya sauke ajiyar zuciya tare da matsowa ya rumgumeta tsam yace ba haka bane yar renota ki fahimce ni ... Yar reno kuma ta maimaita a zuciyarta .. Yacigaba da fadin social media yanzu abun tsoro ne ..na fiso kimeda hankalinki ga karatun ki......''ce n'est pas ce que tu crois parce que je te fais confiance a 100%.... Se lokacin ta sauke ajiyar zuciya itama tace ''merci yayana...''se kuma tace naji kace yar renonka ,..mi kake nufi da haka ido cikin ido take maganar .... Kauda fuskar shi yayi duk ya wani daburce .......dan ya kawar da zance yace idan zaki mun magana kada ki kara saka idonki cikin nawa... Cike da mamaki tace 'pourquoi?still ta kafeshi da ido.. Juyowa yayi da niyyar bata amsa hallau sukayi ido hudu.. Fasa maganar yyi sema tashi da yayi ya shiga tolet jin ana kiran sallar magarib ...amma a ranshi fadi yake anya yarinyar nan ba wani abu take sakawa idonta ba...tun tana ya karamarta inde har mukayi ido biyu da ita to bana iya mata muso akan abunda take so.....se in wani dirirce gaba daya ...mtsss ya ja tsaki shi kade .a bayin ... Yana fitowa fuuu ya fice ba tare da yakalli inda take ma.. Maysam alwalar ta shiga ta doro amma tunani ne fal ranta ..kawai mutum daga tambayya se ya hau fushi ..to Allah de ya kyauta . Niko nace ameen Sanin baya dawowa se bayan isha'i yasa tashiga kitchen ta hada mishi d'an specialité girki da jus.. Komi cikin sanyi jiki take yinshi ganin yayi fushi da ita .....bayan ta gama tayi sallah tazo dakin su Mufeedah ...exercice sukayi tayi har goma saura tukon sukayi sallama ..Mahmud ya kira Mufeedah suka fara zuba soyyayar su.. Itama Mariam babu laifi ta dan fara kula Mark dan ko kwawarshi ta isa a fara biye mishi. Ba laifi ta dan fara sonshi ..sede bataso ta zurfafa tunda tasan an riga da anyi mata miji a gida..... Murad kam har lokacin be dawo gida ba..iya tashin hankali Maysam ta shiga..wanka tayi tayi shirin bacci ta bade jikinta da humra..tana jiranshi anan palo har baccin yayi awon gaba da ita..... Se sha daya ya shigo .gidan.ganinta nan a takure bisa kujera se kuma ta bashi tausayi..dan yasan jiranshi ne take ...daukanta yayi da niyyar kaita cikin room kamshin humrar ya bigi hancin shi harda wani lumshe ido.... firgit ta farka ai kuwa tana sauke idonta akanshi ta saki mishi kuka ... Shima se zuciyar shi ta tsinke ..zama yayi tare dayi mata masauki a cinyarshi yana goge mata hawayen yace ya isa haka to mima nayi miki da kin ganni kawai ki saki mun kuka.... Cikin kuka tace to ba kai bane kayi fushi dani banyi maka komi ba...harda wani tafiya kayi dare Dan murmushin gefen baki yayi yace to ai ke ce se ki wani kafeni da ido ni kuma idon mu na sarkewa sena loosing control dina .ki dena bana so ''parfois j'ai l'impression que tes yeux me dominent même''..don suna sani yin abun da banyi niyya ba Se da yayi maganar ya farga ..amma seya mazge Itakam kankameshi tayi tace ba zan sake ba pls kada ka kara yin fushi dani .tana yi tana wani shafa mishi fuska ..ta kuma ji dadin kalam manshi Shima rumgumeta yayi nan ya shiga kissing dinta yau kam har da romance yayi mata sede bata hanashi ba kuma bata meda martani ba saboda tsaro😎...dan kada kuma yayi fushi da ita ma...da taga da gaske birkice mata zeyi ne sannan ta raba jikinta danashi lokacin idonshi har sunyi dan ja.. Tace nasan bakaci komi ba pls na kawo maka kaci ko,.? Yanda tayi maganar seya birgeshi gyada mata kai yayi dan babu bakin magana ...... Sosai yaji dadin abinci seda ya gama cika cikinshi ta hada mishi ruwan wanka yayi ..sukabi lafiyar gado..... Har bacci ya fara daukansu kamar wanda aka tsikara cuwat ta tashi ta zauna tace wai yaya har yanzu matarka bazata dawo ba ne... Cikin magagin bacci yace mizaki mata in tazo din ..wai ma mi yakawo zancen nan cikin dare ... Turo dan baki tayi tace kowa da abunda ya dameshi a rayuwa nikam itace damuwa na..kuma kawai ina son ganinta ne inga nida ita wayafi wani kyau.sanna da alama bawata katuwa bace tunda naga kayan dake wardrop kamar ma zamuzo kai daya...kaga kuwa wly tanayi mun in kareraya yarinya .....ehe Yace kai yama za'ayi ahadata dake ai kin kere mata akyau bazama ta kama kafarki. Yanzu de barni nayi bacci a gajiye nake.. Ai kam kamar ya zugata tace ba wani nan kawai dan na kyalleka kayi bacci ne kace haka..bayan ranar nan kace ta nada zallar kyau Harda shure2 tana ita bata yarda ba... Dayaga dagaske bazata barshiba tashi zaunan yayi yace to kiss me sena Gaya miki gaskiyan magana.. Yatsina fuska tayi tace a'a barshi kawai bana so ni na gaji da abunan .. Murmushi yayi a ranshi yace na jawa kaina da yanzu ina more abuna ..rumgumeta yayi yace to ''dort bien '' yayi kissing forhead dinta.. Meda kanta tayi bisa kirjinshi tace'' passe une excellente nuit yaya..''' Yace da ita shima '' pareil aussi et ne m'oublis pas dans tes rêves''.. Murmushi kawai tayi ta kara makalkale shi . har bacci me dadi yayi awon gaba da su.. .. Asuba ta gari 🌹🌹🌹. 🌹🌹 Wai fans ina labarin inna Murza ne?..yanzu kam tayi dan sanyi amma fa mumunan kudiri ta na nan makale a zuciyarta tana tunani sake taku ne tunda taga abun se kome musu yake. ..gashi kuma bata da kudin dazata na bawa bokayen .. Madina kam abun ba sauki kullum haukanta kara gaba yake . . kai daga karshe ma a daki aka kulleta tare da daureta da sasari dan inta b'alle ..masu kamota ma se sunji jiki... Mahaifinta ayanda ya fahimci abun kome mata ne yayi. Dan haka ya saka ana saukar qur'ani tare dayi muta Rukya....... Mahaifiyar tama kullum cikin yi mata addu'a take dan hannuka baya rubewa ka cireshi ka yar ..kuma ma in tayi mata baki ko ta tsinemata itade zatayi walaha dan uwa bata iya supporting din taga danta yana surffing..shiyasa ta dage da rokon Allah tare da nema mata gafara da kuma shiriya... .. Wannan kenan Kuyi hakuri fans na rashin jina kwana biyu bana jin dadi ne ... I need your addu'a.. Wanda suka kirani ta waya da wanda suka mun text na gode muku Allah ya bar kauna da zumunci..merci bien❤😘😍 Love yau all❤😘😘 Fasma ce 🖊yar mutan Zinder. [11/08 à 22:31] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Na gode da addu'ar ku gareni Allah ya bar kauna da zumunci ina alfahari daku fans ...love you all irin totaly din nan ❤❤❤😍..thanks all* Dedicated to all my fans😍❤ 🅿93__94 ```Manzon Allah (SAW) yace''wanda duk ze rantse ,to ya rantse da Allah ko yayi shiru'' Bukhari ya rawaito shi``` [11/08/18 à 22:30]A kwana a tashi ba wuya su Maysam har sunyi wata shida a England ..cikin watanin nan kuwa abubuwa da dama sun faru ciki harda saka ranar auren Mahmud da Mufeedah ,se kuma na Mariam da dan uwanta Ma'aruf ..wanda aka sa nanda wata shida masu zuwa dede da basu vacation kenan.. Soyyaya kam tsakani Mark da Mariam ta ginu sede babu yanda zasuyi tunda shima Mark din parent dinshi sun zaba mishi mata a can gida Niger ..duk da haka yaso ya hada duka biyun ya aura wato Mariam da kuma zabin iyayen shi to amma wuri ya kure mishi Ma'aruf ya rigaishi..kuka kam sun sha shi ranar bare ma Mariam kuma wani karin takaici da bakin ciki wata conscidence rana daya ne danashi da nata Mariam din.kuma abunda yake kara bawa Mariam haushi be huce ance mata mijin daza ta aura anan England yake aiki ba amma be taba zuwa ganinta ba da sunan dan uwanta ma bare ace da sunan mijin dazata aura....shiyasa ma ta yanke hukuncin tunda de bashida kirki itama baza nemeshi ba kuma da alama baya sonta kamar yanda itama bata sonshi.. Murad shi da su Maysam sune masu lallaba da rarrashi .... Mufeedah kam ba ama magana inde wajen zuba soyyarsu ne yi suke .kamar ba gobe... To bari mu leko oga Murad da yar gidan Momy.. Shi kam ana shi bangaren komi ya jagule mishi yanzu kam ya tabbata da Maysam'' occupe une partie de son corps .'.yanzu ya yarda da cewa ya fara fadawa tarkon son Maysam . sede har yau SWEETBABY na nan makale a zuciyar yansan de yanzu Maysam ta fara cinye rabin zuciyarshi ..(ina fatan de baku manta cewa rabin zuciya Murad gareshi .i mean rabin soyyayar Sweetbaby ta ciye shi da fari kam gaba daya sweet baby ta ciye zuciyar .. Mahmud ya bashi shawarar da ya rage dan shine miji ita mata wata rana idan har ya mallakar mata duka zuciya kenan baze taba ganin defaut dinta ba koda tayi badede ba..har fada seda sukayi a wancan lokacin tun kafin mutuwarta ..seda gabaya yayi nazari yaga kuma hakane ..namiji shike rike gida inya sake mata ita zatana bashi iko . koda rabin ne ma dayaya ya karata bare ya bata duka da kyar da siddi yayi kokari raba zuciyar ya ..to yanzu kuma Maysam take son ciye rabin....)tab zanga yanda zakayi 🤔.. Gashi yanzu d'an ta'ba tan man dayake yi bata barinshi setaga dama shikuma baya iya yi mata da karfi .ko kuma ta shiga kiran sunan sweetbaby.duk sha'awarta na dawai niya dashi ..ya rasa yanda ze yi da ita .kuma shi baze yi zina ba dan yayi migun tsanarta kai shifa ma mata basa gabanshi Maysam kawai yake kunde sanshi base nayi dogon bayani ba akan sweetbaby ..Maysam ma dan ya fara sonta ne .. .yau ma kamar kullum ta kama lahadi ba school shima kuma yana gida ....kunde san mutuniyar ku da iya tsokana ..dan yanzu batada aiki se saka english wear a cewarta ta gaji atampuna ..sede in zata school take sakawa amma inde a gida ne to fa abun ba sauki dama2 ma in zata sauko palon kasa wurin su Mufeedah takan dora after dress .... Zaune yake ya saka laptop gaba yana son yayi aikin shi aman oganiya ta kasa ta tsare taci uban kananan kaya se wani dan bala'in kamshi take zubawa na turare da humrori takuma zauna nan palon saman tana kallo tv abunta ga fruit kusa da ita tana sha .. .... Can tace pls yaya Computer muke so kasai muna akwai aikin da zamu fara dashi inaga gobe ma dana wajenka zani dan gobe ne zamu fara aikin. Tunda ta fara magana yake kallonta yajita sare kuma Sede yasan yana kallonta amma baze gaya maka taka meman abunda yake kallo ba a jikinta dan ya tafi duniyar tunani . abunshi .. Can ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin Ke zonan... Yi tayi kamar bata san da ita yake ba a ranta tace inde bazaka fasa kirana da ke ba to ni kuma zaka kwanan nan dan bazan amsa ba.. Se da yace yar renota zonan mana..haka ake gayawa mutum abu gatse2 ai seki zoki rarrasheni man tukon Se lokacin ta kalleshi tana turo baki tana gungunin cewa sekace wani baby za'a rarasheka tana isa babu kunya kawai ta d'ane cinyarshi tace gani to.. ... Damko wuyanta yayi yana wani shinshinata yace ci gaba da zaginan nawa tunda yanzu kin fara raina ni..idonshi kam harsun fara canza kala yizuwa ja. . Tace Ni kuma to yaushe kaji daga bakina .... Share zancan yayi da fadin yaude kad'e ki barni nayi wly na gaji hakurina ya fara karewa .....tun muna mu biyu muna sheda juna ki bari dan wata ran kika shiga hannu bazata miki kyauba...idonshi kyam a kan dan karamin bakinta Ganin inda ya nufa yasa ta fara zamewa tana fadin 'aa nide ka bari na kara girma tukon ina jin tsoro kam...kuma ma ina dayar matarka kaje mana wajenta wanda kake wani fadin tana da zallar kyau .. Yace ki bar maganar nan ba lokacin yinta bane kuma ma ni wasa nake miki babu wata aure dana yi... Cike da shagwaba da sangarta Maysam tace kawai wayo kake son yi mini ni fa gaskiya kawai na hakura da kai tunda de harta rigani kawai kace ta dawo ..ni baz... Bata gama fadi ba ya shiga kissing dinta dan ya gane kishine kawai ke dawiniya da ita ..da fari taso hanashi se kuma ta kyaleshi dan dama yau itama da san kasancewa a jikin shi ta tashi dan haka bata hanasa ba ..can naga abu yafara yin nisa har ina fadin ku kuma kuryar daki mana nan fa falo ne amma basa ma jina romance kawai suke abunsu ganin abun yana so ya fice tunani na ya sa na tattara yan komatsena zan bar musu palon har na juya naji Maysam na fadin nide bana so tsoranka nake pls ka bari na kara girma ..aman shi bayama jinta ..cikin kuka take fadin hakan... ganin fa da gaske yake yasa ta fara fadin yanzu amanar sweetbabynka zakaci ne ?.. Ganin baya jinta yasa takai bakinta dede kunnen shi da karfi tace Sweetbabyyyyyyy ..pls ina kike kizo zeci amanar ki .. Kamar giftawar walkiya naga Murad ya tashi cuwat ..ai Maysam a dubu ta arce dayan dakin wato na kishiyarta😜... Shi kam nan ya dunga bugun kujerar daya ke kai da hannushi ..yana fadin why3 ..am so sorry my sweetbaby bazan sake ba ..pls forgive me .na kasa controlling din kaina aman bazan kara ba ..a yanda yake maganar seka rantse tana gabanshi ..haka ya kari surutun shi ya shiga bayi yayi wanka tare da barin gidan ma gaba daya... Ita kuwa Maysam tana shiga dakin ta fashe da kuka dan se da tayi abun taga bata kyauta ba ..Ko babu komi mijinta ne Muradinta abunsonta kuma hakkishi ne ..gashi kuma tana da yakinin yayi fushi da ita yanzu..kai ita da mi ma zataji. Nan tace why3 yayana be cancanci haka daga gareni ba yanzu ko awani hali yake se kuma tace daga yau nayi alkawarin bazan kara hana sa ba dan gujewa fadawa ga halaka dan tsinuwar mala'iku ba wasa bane ..dan ta tuna da Hadisin ```Manzon Allah (SAW) dayake cewa ''idan mutum yayi kiran matarsa zuwa shimfidarsa setaki zuwa ya kwana yana fushi da ita to malaiku zasu yita tsine mata har safiya'(Bukhari da Muslim)``` Ta dora hannu aka cikin kuka tace na shiga tsinuwa goma(10) da gomiyatara(90) ..wata zuciyar tace kuma ki duba fa yayi miki uzuri da yawa ba yau yake bibiyarki da bin bayanki ba amman kina ja mishi rai. Wata zuciyar tace to ai ba laifinki bane tsoranshi ne kawai kike ji kada ya kareraya ki(ji fa🙄 to ya cemiki ana kareraya mitum ne.. )dan a yanda yake din nan kema kisan kukanki baze kwaceki ba sede sunan sweetbabyn shi. ..se kuma dayar zuciyar tasake tunatar da ita cewa ai hakkinshi ne dole kuma kibashi in baso kike ki kasance cikin tsinuwar malaiku kamar yanda kike ciki yanzu nan..tunawa da hakan a million ta fito ta fada dakinshi aman setayi rashin sa'a dan har ya fice a gida ....wani kukan ta sake fashewa da shi haka jikin babu kwari ta dauko waya ta danna mishi kira aman har ta katse be dagaba kai kira na biyu data sake sema akace mata wayar a kashe ....nan tashiga kuka tana fadin pls yaya pardonne moi kazo bazan kara hanaka ba .....can de ta lallashi kanta tare da alkawarin yau zata bashi hakkinshi koda be nema ba ita zata nema (tofa Maysam rigima🙆‍♀🙄) se kuma ta shiga duniyar tunani tace kai zanso sanin yaya sweetbabyn nan take koda ma photon ta tane ........itama de wanka tayi ta sauko duk jikinta yayi sanyi wurin su Mufeedah dan tasan itada ta ganshi se dare tunda yayi fushi da ita..haka suka wuni wanda Maysam ta dan sake kadan dasu suka sha firar su wanda yawancinta ta school ne ..... Tun bayan la'asr take shiga da ficen dora girki duk tabi ta gajiyar da kuyangin gidan dama su ukku kade .ne.abinci ma kala biyar tayi jus kala ukku ,banda qana nan specialites girki kamar su ''pain perdu salé, crêpe etc.. Su Mufeedah kam banda dariya babu abunda suke mata dukda sunsa daman ita takewa mijinta abinci kullum aman yau gilgilwar kan tata tayi yawa..itade bata kula su ba aikinta kawai take ....... Fans da gaske fa inaga Maysam zata bashi hakkinshi du da tana kunyar aman dan ta fita a tsinuwar malaiku zata daure dan kuwa duk wasu kayan da Fulani ta aiko mata yau seda tayi anfani dasu dan se jefi2 take aiki da su aman yau kam rankatakap ta dauko su. Kamar su kanunfari,bagaruwa,ganyan magariya..etc.. Ta jika wannan da zuma tasha in anjima tasha wani da madara...tofa abun nata yafara ruuko ido 👀kai fans ku tuna mata fa budurwatake zata sha wuya fa.. dan ni ba tama jina duk gani take kamar bana sonta da Muradinta ne🙄🙄..nide ba ruwana ehe.. Murad kam tunda ya fita ya fice office dukda babu aiki kiranta kam tun amota ya gani aman seya kashe wayar..yana nan har bayan sallar la'asr ga yunwa ta dameshi dan tunda ya fara cin abincinta ya dena cin na restaurant kona kuyangi dan baya jin dadin su kwata2 ....biscuit da madara yayi wunin sha se black tea.... .. Kunna wayar yayi ai kuwa sega kiran Mahmud ya shigo ..bayan sun gaisane Mahmud ke sanar mishi daman Momy ce tayi ta kiranshi tun dazu aman taji akashe kuma takira matarka tace ka fita to shine fa ta tada hankalinta.... Yace am fine aman bari na kirata to.. Mahmud yayi saurin cewa ''es tu sure que tu vas bien? ''(are you sure you are fine?) dan na ji muryarka wani iri fa.. Ajiyar zuciya yayi da kamar bazece komi ba se kuma ya sanar mishi halinda yake ciki ko ze sama mishi mafita.. Mahmud ya kwashe da dariya harta kullar da Murad yaja tsaki yace kaji matsalar ka ai..in baza ka sama min mafita ba to se anjima.. Tsagaitawa yayi yace to kawai tunda de ba santa kake ba ka murkusheta ko ta karfine ka anshi hakkinka mana.. Murad yace bazaka gane ba to ai yanzu na dan fara sonta bazan iya yi muta ta karfi ba ..kawai zanta hakuri.. Mahmud yaja tsaki yace duka ma nawa Maysam din take ne kada fa ka manta yar renonka ce.. Murad yace tab ai wly yarinyar nan ta fice tunanin ka ka barta nan da wly yanzu ita ke renona dan ta fini kwarewa ta kowani fanin..yanzu ita ke renona Mi Mahmud zeyi inba dariya ba ..can yace to kawai kasaka mata maganin bacci sekayi abunka..dan zaka cutu fa Murad yace a'a bazan iya yi mata haka ba gwara na cutun da nabi ta haka(🙆‍♀🙄ku taya Murad da addu'a fa dan soyyaya ta mishi mugun kamu aman shi yana ganin yanzu ne ya dan fara sonta)... Yaci gaba da fadin gashi kuma bana iya jimawa ina fushi da ita ..dan ko wanan abun datayi mun kasa fushin nayi kaga harda computer da suke so na sai musu su duka ukku.. Mahmud yayi mishi godiya tareda addu'ar Allah ya kara budi se kuma nasihar da yayi mishi kan ya lallabe ta tun wuri dan kada ya kasa jurewa ya fada ga halaka dan ita sha'awa c'est naturel ..ko wani dan adam yana da ita..dan haka kayi a hankali.. Godiya yayi mishi sukayi sallama tare da jaddada mishi ya kira Momy ko hankalita ya kwanta.. Suna gamawa kuwa ya kira ta nan suka nan tattaba hira ....fulani na tabayyarshi ya akayi ya kashe wayarshi .... Aman se ya kawar da zancen dan baze iya gaya mata ga abunda ya faru tsakanin shi da Maysam har ya kashe wayar kuma ma be taba yi mata karya ba kuma baze fara daga yau ba ..yace Momy ina maganar Ita Murza da fatan komi yana tafiya dede.. Fulani tace kwarae na saka a dunga binta duk inda zatayi ....aman de har yanzu bataje wani wurin ba..nan suka tattaba hira sukayi sallama.. Computer shi ya bude yana kallo se kuma naga yana sakin murmushi shi kade ..lekawa nayi naga miye ya saka shi dariya lokaci guda haka.. Hum 🙄photon Maysam ne da Sweetbabyn a screen din yana kallon yace tayaya zan ara miki computer na kiga photonki ne dana sweebabyna ne a screen ..ya kuma cewa kai amman fa suna tsanani kama fa. Kamar ya da kanwa.se kuma yace kai Sweetbabyna tafita kyau.se kuma yayi kalar tausayi yace miyasa ni kullum wanda nake so suke guje mun su barni ne..a lokacin danake bukatar su nan ya lalace da zancen shi shi kade...har kusan magrib ..sanan yayi alwala ya fice mosque.. Ina ganin haka nima na aje biro na dan na sauke farali... Muje zuwa ..🏃‍♀ Ina yinku irin sosai din nan😍😘❤.. Fasma ce 🖊yar mutan Zinder. [12/08 à 23:50] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Sumayya ,Iman,Maman Ss , Fatima to Maysam taji sakon ku kuma ta gode da shawarwarinku* ,😉 *tace zakuga sauyi...and tace tana yin ku irin sosai din nan😍.* *Fans bazan gajiya da mika sakon gaisuwata zuwa gareku ba ..ina sonku irin more totaly din nan* 😍❤😘 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿95__96 ```Manzon Allah (SAW) yace''wanda ya kawar da mugun abu daga hanyar da mutane ke wucewa ,to za'a rubuta masa kyakkyawan aiki ,wanda kuma aka karbi kyakkyawan aikinsa zai shiga Aljannah Bukhari ya rawaito shi.``` [13/08/18 à 00:00]Maysam kam tun bayan sallar isha'i ta gama kominta taci uban ado ta zauna nan palon sama tana jira amma ji kake shiru kamar an aikin bawa garin su ...yau ko exercises din bata ji zata iyayiba ...suma su Mufeedah basu neme taba ...nan ta kunna tv ta kura mata ido kai kace tasan mi ake yi alhali hankalinta na can duniyar tunani ...har karfe tara babushi babu labarin shi..hakanan jiki ba kwari ta danna mishi kiran kamar da wasa ta shiga sede be daga ba ....se ana biyar ya daga ko sallama babu yace wai miye ne kin dameni da kira.. Itama a memakon ta bashi amsa se ta fashe mishi da kuka ..... Yaso kashe wayarshi ya kyaleta se kuma yaji baze iya hakan ba dan har cikin ranshi yake jin kukan nan.. Dan haka ya tausasa murya yace kiyi shiru ki fada mun mike faruwa ...waya tabaki ne... Ji tayi wani abu yazo ya tsaya mata a makogaro a ranta tace be masan shine ya taba tan kenan wata zuciyar ta fara ingizata da cewa ai wannan ma reni ne ..bayan yasani sare bakya iya jure fushin aman yazo yana tambayar wane ya tabaki ,....hum ai duk laifin kine dakika bari har yaga damar ki haka ...duk son da kike mishi ai be kamata kiyi saukin bada kanki ba ..ko kin mata ranar da kuka fara haduwa da mari kuka gaisa ..bayan nan wace irin tsana ce be gwada miki ba ..seda ga baya kuma aman kiyi tsai ki gani yama tab'a baki hakuri kan duk irin abunda yayi ta miki ne.....sosai tayi na'am da hudubar zuciyar.. Dan haka a fili tace mishi babu komi.. Tana da share hawayenta . .... Sun jima can babu wanda yayi magana kowa da abunda yake sakawa cikin ranshi sun kusa minti 5 a shirun kuma babu wanda ya katse layin.. Murad ya katse shirun da fadin se anjima tun da de bakida abun fadi. .... Da sauri yace pls yaya ka dawo yanzu bana son kana cika dare a waje .. Ajiyar zuciya ya sauke yace shikenan ganinan zuwa .to. . Se lokacin ta sauke ajiyar zuciyar itama tace a shigo lfy.. Wani dadi taji jin gashi nan yanzu ze dawo .. Befi minti 30 ba ya shigo gidan...ai Maysam na ganin shi ta manta da wani huduban da zuciyanta ta mata ..da gudu taje ta rumgumi a bunta shima kara matseta yayi ajikinshi atare suka dinga sauke ajiyar zuciya ..sun jima a haka Maysam tayi karfin halin raba jikinta dana shi tace mutafi ka watsa ruwa se kazo kaci abinci dan na san bakaci komi ba .......beyi muso ba dan yunwa yakeji... tana gaba yana biye da ita a baya ..a ranshi yana raya anyi fa manya mata anan .....suna shiga bedroom yazo ta baya ya rumgumeta tare da sakalo hannushi ya kewaye kugunta ...se wani shinshina ta yake yace kinyi kyau kula kamshi nan yayi mun dadi ..... Itade batace komi ba dan tunda ya rumgumeta taji wata kasala ta rufeta.ga kuma kallamashi daya kara sanyaya ranta.ganin abun ya na gaba yasa tace pls ka bari kaci abinci tukon...... Da sauri ta zame tayi tolet dan hada mishi ruwan wanka ..ai kuwa tana ciki ya tarar da ita ...bayan ta gama zata fita yace na gaji da yawa ko zaki tayani ..dama daga shi se towel ne Wani waro ido tayi tana nuna kanta tace ni?tab ai kam ban kai wurin ba ....ni yar karamar nan dani zanyi wa babba wanka..tana wani yarfe hannu Yana matsota yace kin kai har kin fice ma ..yace tunda kin san kiss me ..har kin kwarai a fani to wannan ma nasan zaki iya Kalar tausayi tayi Tace pls yaya ka bari 'la prochaine fois zanyi ma aman yanzu wly kumyar ka nakeji..bazan iya ba... Dan murmushi yayi yace yanzu kuma ni ake kumyar ..iii lalle fa.. Da gangan ya fara kokarin wai ze zame towel din yana mata wani mayen kallon ai bata san lokacin data ce wayoo Allah Momyna zanga abuda yafi karfina tare da rumtse idon ta gammm.. ... Dariya ya shiga yi mata yace ashe kuwa zaki kwana kina kira bata jiki ba .ya lakice mata hanci yace jeki abunki zamu hade ai..... Tana jin haka ta arce ai daga tolet din ...dakin kishiyar ta tashi se gunguni take kan har yau bataga ya kishiyar take ba..wani tunani tayi tace to kode ya sauya lata gida ne? itama wanka ta sake yi ta bade jikin ta turaren ruka iri daban2......ta saka sleeping dress dinta me kyau tana fitowa shima ya fito a tare suka saki ma juna murmushi .. Dinning suka je tayi serving dinshi ita kuma ta saka shi a gaba tana kallo kamar wanda ta samu tv ........ Ganin haka yace ke kinci abinci ne.. A'a kaide kaci ka koshi tukon ni daga baya ma zanci.. Yace ai baki isa ba oya comon yar renota... Zumbure2 baki ta fara tace nide gaskiya ba yar reno bace na girma fa ..ko baka ganin bane ..ta tashi tana wani jujuyawa .. Hannunta ya kamo ya dorata a cinyarshi yace naji yanzu de lokacin cin abinci ne nan ya shiga feeding dinta ..inya ci so daya se ya bata ..a haka har suka cika cikin su ...dan ba kadan ba abinci yayi mishi dadi ......bayan sun gama ta kwashe komi ta gyara .. Anan palo ta isko shi ..zama tayi ta dora kanta a cinyar shi tana kallon shi tace pls yaya forgive me akan abunda nayi maka dazu ..wly bazan k... Da hannushi yasa ya rufe mata baki yace shikenan ya huce dama ban wani yi fushi dake ba.... Cike da murna ta tashi kai mishi kiss a kumatu tace merci yayana I love you ... Babu zato babu tsammani taji yace I LOVE YOU TOO.... ba Maysam ba ni kaina sandarewa nayi ..can na dan seset kai na ..ganin irin kallon da Maysam ke yiwa Murad yasani cikin tunani ban gama ba naji Maysam na fadin ..what did you say?you love me ?dama akwai ranar daza ka iya furtamun wannan kalamar?ko kuma dan ka yaudareni ne kake son fakewa da hakan.....?ni kam namafi zaton batan kai kayi kake fadin mun haka? Murad daya cika shima da mamaki yace iya gaskiyata nebabu wani zancen yaudara..abunda nasani kawai JE T'AIME a lot ... Tashi tayi daga kanshi a ranta dadi ne kamar ta mutu aman setace bari de tayi test din shi taga wani irin so yake mata shin da gaske ya fad'a sonta ko kuma a'a..kuma ma ai zata dan rama kadan daga wuyar daya bata dan bata manta ba ..dan haka afili tace dama rashin so yana iya rikidewa ya koma so ne ?..to idan ka manta bari na tuna maka ....kace baka sona ,kana zaune ne dani saboda farin cikin Momyka ..kace so daya ne tak shima kake yiwa sweetbabyn ka ....taya kake ganin zan yarda da kai rana tsaka bawai yaudarana kake ba... Na sani ko baka fada ba sha'awana kawai kake bawai sona ba ...dan bakin da ya furta baya sonka to ko daga baya yanuna yana so kawai dan ya yaudarekane .... Ka kwantar da hankalin inde gangan jikin na ce ka sameta ka kare base ka fake ba da cewa kana sona ba... Murad kam kalmomi sun kaurecema bakin shi ma yama rasa ta ina ze fara ... Be an kare ba se hucewarta bedroom ya gani ... Da sasarfa ya mara mata baya... Yana shiga yaga har ta shige tolet ..zama nan bakin gadon yayi ya zabga tagumi.yama rasa irinkalar tunanin dazayi....tana fitowa tace kashiga kayi alwalar ni nayi tawa...kayi kazo ka amshi hakkika tunda shine dama abunda kake so....ta kuwa hade fuska kamar ba ita ba...kuma kai kace bilhakki da gaskiya take maganar bayan tsoro ne fal ranta Jiki a sanyaye ya iso gaban ta batayi aune ba se jinshi tayi ya rungumeta yana fadin wai wata irin magana ce wannan kikeyi ki barta mana ni fa ke nike so ba jikin ki..... Ta fara kokawar kwace jikinta tana dadin dare fa yana yi lokaci nata tafiya kayi kazo ka amshi abunka.. Kara matseta yayi yace ni wly ba jikinki nake so ba kai ni hakki nawa ma na yafe amman kada ki mun horon wanan dan zuciyana bazata iya dauka ba kiyk kwanciyarki ma a gadon ..yana fadar haka ya saketa ..yau gadon ma baze hau ba dan haka doguwar kujerar dake dakin yaje ya kwanta...ya rufe idonshi kamar me bacci .. Umm Maysam kam tana fakar idonshi tayi wani tsalle tace kai amma Allah na gode maka ....... Aman kuma dan rigima irin tata seta dau filo da drap ta fice daga dakin abunta tana fadin mutum da dakinshi bazan ta kura mishi ba .ka hau gadonka ...yana kallonta harta fice a daki bece komi ba ...dafe setin zuciyar shi yayi ya ce why2 sweetbaby ta tafi ta barni ..kema kuma yanzu kin tafi ....inna lillahi wa inna ileyhi raji'oun..... Mayam kam tana fita ta kwanta a doguwa kujerar palon dan bazata iya kwana a dayan dakin ba ..wato na kishiyar ta..🤦‍♀.. Har fuskarta ta rufe da drap din tana zabga murmushi se kuma ta shiga duniyar tunani dan kada ayi katari ya fito ya ganta tana doka murmushi...ta kuma fa yarda da sonta ne yake dan da sha'awarta ce yake da ya amshi kayanshi ko ta karfin tsiyane.....aman kawai tana so ya dan garu kanan dan yasan mace ba abun wulankanta wa bace .ko yaya take... Nan baci me dadi ya awon gaba da ita ..... Bayan da kamar awa guda ya fito da nufin yaje ya lallbata dan zuciyarshi ta hana shi sukuni ....ganin tana bacci ta lafiyar Allah besan lokacin da murmushi ya subce mishi dan tayi mishi kyau da bacci seyaga kamar sweetbabyn shi dan ko position din iri daya ne... Nan ya zauna tare da dora kanshi a bisa kujerar yana mata kallon mansur 😜har bacci shima ya saceshi...(sorry Murad) Da asuba ta rigashi tashi.da addu'an tashi daga bacci.. bude idon da zatayi ta sauke shi a kanshi ba karamin tausaya mishi tayi ba gani kwanan zaune yayi kamar ba YARIMA Murad me jiran gado ba.....a hankali tace am sorry My King ..ita kade tace kai 'tu es tres mignon fa''ji tayi kamar ta rumgumeshi...ganin yana nan motsawa yasa ta rufe idonta ruf.. Tashi yayi da addu'a tashi daga bacci shima...nan ya kare mata kallo daga bisani ya mata kiss a goshi yace i love you my wife..sanan ya fice dan doro alwala.. Ba karamin namijin kokari tayi ba dan wani murmushi farin ciki ya kusa kubce mata ba ..ya na shigewa tace love you more my prince... Tana duniyar tunani taji motsin futowarshi da sauri ta sake rufe idon... Dukowa yayi ya dan shafi fuskarta da dan ruwan alwalar a hannushi ... Yi tayi kamar yanzu ne ta tashi..... Yace kitashi kiyi sallah ...sannan kizanki yin addu'ar yayida kika tashi Ya mutsa fuska tayi ta basar da maganar tashi tace yanzu tsakani ka da Allah rashin son daka ke mun har takai ka tadani daga bacci da ruwa .... Marerecewa yayi yace ruwan alwala ne fa ...to Allah ya huci zuciyar ki ..yana fadar haka ya mata kissi a kumatu ya fice... Yana huta tace Allah sarki Mon amour c'est pour ton bien que je fais tout ca.....sekuma ta tashi ....da shoki ta shige daki dan sauke farali .. To nima de bari naje nayi tawa ko ba haka ba fans😉 Love you all😍😍 Fasma ce🖊yar mutan zinder [14/08 à 02:07] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ *My Aisha Abani i miss you so very much and you too my Zarbaby😍❤😘* 🅿97__98 ```Manzon Allah (SAW) yace''kada dayan ku yasha wani abu a tsaye. Muslim ya rawaito shi. ``` [14/08 à 00:02] Be dawo gidan ba se wajejen 7 na safe ...lokacin tana kiciniyar hada mishi break.. Yana son ya iske kitchen din kuma baya son bayin shi su ganshi shi da kanshi ya shiga wai kitchen ..yarima guda ai se su rena shi .. Dan haka wanka ya shiga yayi abun mamaki kafin ya fito ta fito mishi da kayan da ze saka amma kuma bata room ....jiki a sanyaye .dan da ta saba mishi da ita ke shiryashi aman yau ko dan goge jikin ma be samu ba bare aje ga zancen shafa mai da saka kaya..duk se yaji ya damu ..haka ya shirya yayi komi ya fito da jakar computer shi a hannu lokacin bakwai da rabi tayi ...tana break a dinning dan haka shima zuwa yayi yana zaunawa ita kuwa tayi cuwat zata bar mishi wajen..hannunta ya rike yayi kalar tausayi yace to yanzu baza ma ki gaisheni ba kuma wa kike so ya serving dina .... Tana kallon gefenshi tace g.morning da fatan ka tashi lfy?tana fadar haka ta fara zuba mishi abinci...har ta gama ko kallonshi batayi ba ..zata fice yasake rukota yace yau kodan morning kiss bazan samu ba bare aje ga zancen feeding dina...taya kike son na tashi lfy bayan kin juya kin baya Ba karamar jarumta tayi ba, dan kad'an ya rage ta sheke da dariya amman seta mazge ga kula tausayin shi daya dirar mata..tana wani ya mutsa fuska tace dama na sani jikina ya dame ka bani ba ..tana fadar haka ta fara kokarin kissing dinshi da sauri yace a'a ki barshi kawai ..shima yana fadar haka ya fara cin abincin shi ... d'aga kada tayi irin na i don't care din nan ....room ta shiga ta fito cikin shirinta na school babu laifi irn shigar daya ke so take hi....itakuwa tayi hakane dan kada ya samu abunda ze fake dashi yayi mata magana. .tace dashi mun tafi se anjima. Tana saukowa ta gamu dasu Mufeedah suma cikin shirin su dan haka suka fita driver ya kaisu ... Murad kam tana ficewa yaji abincin ma ya fice mishi a rai dan haka office ya fice abunshi duk jikinshi yayi sanyi...... Haka ya wuni ba tare da yaci komi ba ..kuma da dare ma komi na bukatarshi ta aje mishi tayi ficewarta kasa wajen du Mufeedah sukayi exercice din su dan ita kam hankalinta a kwance yake ..abunda take so yana sonta shima.wajejan karfe goma suka gama ...tana hawa tayi wankanta tare da shirinta kamar jiya .....dakinshi ta shiga ta tarar da shi ya zabga wani uban tagumi yana can yana tunani da alama be san ta shigoba dan yayi nisa cikin tunanin ..daga nan take jifanshi da kallon kauna wanda shi bema san tanayi ba...seda tazo gaf dashi kamshin turarenta ya fargar dashi daga kai yayi ya kalleta tare da sake mata wani tsadaden murmushi ..ita kanta seda gabanta yaba ras..har jikinta ya fara sanyi ..aman kuma setayi ta maza tana wani ya mutsa fuska tace dama zowa nayi naji ko kana da bukatar amsar hakkin naka yau ne dan bana son fadawa cikin tsinuwar malaiku.. Yayi yar dariya ya girgiza mata kashi yace wai so nawa kike so na gaya miki ne ..kije kiyi kwanciyar ki kawai ki barni da abunda ke damuna ....kamar jiya yauma a palon ta kwana shima kuma da wahala bata kare mishi ba kamar jiyan haka ya kwana .a zaunen..seda sukayi kwana ukku a haka duk ya fara ficewa hayyacin shi ..har wata rama yayi abunka da dama ragowar damuwar sweetbaby ne..ga kuma Maysam na gasa mishi aya a hannu .gashi batada aiki yanzu ta dawo kissing din ta kamar da ..kuma daya meda mata setace ai dama abunda yake sone ...dole tasa yanzu inta kissing dinshi yaki medawa har ta gama abunta abunka ga wanda be saba jin wani abuba a jikin mace se akan Maysam ..shi se yanzune ma yasan yana da lfy dan da har su Mahmud suna kokonton ko bashida lfy na shiyasa mata basa gabanshi..to gashi yanzu abun yazo kuma wacce yake da bukatar ta nuna bata san zancen ba..wani lokacin in tayi wani style din da shafa wani turarenta me sunan Feminism har mararshi take kullewa yashiga ciwon cikin da babu shiri .. Yauma kamar kullum Maysam data dawo daga school din safe ta tarar dashi a palo yana kallon wani film da alama shima be jima da dawowa ba..wanka tayi kamar ko yaushe ta cakare da kayanta ta shafa kuma turaren dan da gayya take komi...kiciniyar dora mishi mafi saukin lunch take, dan tanada lecture yamma..shiga da fita goma dazatayi daga kitchen inta zo ficewa se ta biyo ta bayan kujerar dayake kai ..ta kamo kanshi ta sama ta duko ta bashi light kiss .daya meda martani se tace to ko kewa yowa zanyi ne ka anshi hakkin nakane.. Sede ya girgiza kai yayi murmushi..a haka harta gama ta jere a dinning din sannan tace'' ton dejeûne est prêt''.. suna tsaka da lunch din yace wai dan Allah mikike sone nayi miki ki dawo mun kamar da ...bazan iya jurar wannan hukuncin naki ba... Spoon din ta aje tace inaso ka nuna min irin kalar son dakake mun i mean ka nuna mun irin taka kalar soyyayar ka koma mrs romantico..😉 Dan murmushi yayi yace aman de kin sani ban iya soyyaya ba ko?hasalima banta ba soyyaba bayan wacce nayiwa sweetbaby na kuma kinga ita tun ina secondry da rasu ..ita kuma tana nursing..kinga kuwa wasu kallaman ma na soyyaya bamu sansu ba......tunshi ban taba soyyaya ba se yanzu dana fada tarkon sonki ..... Dan murmushi ta jinjina kai se kuma tace to ai se kaje ka koyo tunda de yanzu wai kace kana sona kamar yanda kake fadi .. Yayi saurin cewa son da nake miki ya fice wai .. Tace kuwa inde har hakane zaka iya kenan.. Jinjina kai yayi .suka ci gaba da cin abincin su ..kowa da abunda yake sakawa ..ita tana jin dadi har cikin ranta cewa ta samu wani gurbi a zuciyar shi..shi kuma yana tunanin ta ina ze fara... Suna gamawa ya fice a gidan ...sedaya fita a unguwar ma se yasamu wani guri yayi parking sannan ya dannawa Mahmud kira.. Bayan sun gaisa yace wata magana nake so muyi aman banda dariya fa.. Mahmud yace to ina jinka..se kuma ya ra sa ta ina ma ze fara gayawa Mahmud maganar .. Cande yace soyyaya nakeson ka koya mun.. Haba ai Mahmud ya shiga kwasar dariyarshi...harda rike ciki yake... Tsaki Murad yaje yace matsalata da kai kenan ... Mahmud kam da kyar ya tsagaita yace to ai ita soyyaya ba koyawa mutum ita ake ba kowa da irin nashi salon soyyayar ..bankiba de kace kallaman ta to suma zaka iya kirkirar naka kalaman specifique a toi seul .....nan de ya dan bashi yan shawarwari tare da yan kallamai ... Mahmud yace welcom to the lovers word ..ina tayaka murna.... Tsaki yayi ya kashe wayarshi... Se kula shi kade yake yiwa kanshi dariya Be koma gidan se bayan isha 'i lokacin har sun fara exercice aman dataji motsinshi seta sullube ma su Mufeedah tayi tafiyar ta .....ya fito wanka kenan ta shigo bata damu da towel ne kade jikinshi ba dan tama saba da hakan ..kaya ta fitar mishi zata tafiyar ta ya komo hannunta yana fadin ina zukekiyar babyna data dara zinaria haske da kyalli zata tafi haka tabar dan bawa Allah da zuciyar shi ta tsunduma cikin kogin so da kaunar ta ne.harta na falar tarwatse mishi a duk lokacin dayai gamdakatar da ita.yana wani lumshe sexy eyes dinshi...yake fadar hakan. Lumshe ido tayi dan kalaman direct cikin zuciyarta suka caka ..ba karamin namijin kokari tayi ba wurin kin nuna mishi taji dadi kallaman shi har dadi na kusan tarwatsa zuciyanta ba ..ta wani yamutsa fuska tace au yau kuma ni na amsa sunan BABYn kenan?na aza sunan nan sweetbabyn kane .kade.ni kam ai bankai wannan matsayin ba ..tana fadar haka tayi waje dan inta tsaya zata iya bada kai yanzu nan.. Murmushi yayi yace mujede zuwa ... Itakam tana fita ta shiga yi wa Allah godiya ai da shoki ta shige dayan dakin dadi kamar mi...... Haka daza su kwanta ya bad'eta da kallamai na soyyaya har taji kamar ta rungumi abunta amman se ta mazge ...seda sukayi kwana ukku kullum da iri salon soyyayar dayake bullowa da ita ..kusan wuni yake yana kawo mata flower,gift iri daban2 ,,a ko ina na gidan yabi ya rubuce shi da I love you Maysam ,kai har mirrow na gidan basu tsiraba ..kota goge kafin ta dawo ya sake rubutawa .....kaf draf din su ya sake sabbi kuma duka an rubuta I love You Maysam ,wasu an rubuta ''je ne vis que pour toi.my Princess'' wasu kuma je t'aime et je t'aimerai pour l'eternité aka rubuta ajikinsu..kai takai ta komo ko tolet din su yabi ya rubuce su da kallaman shi.....se kuma uwa uba riritata dayake da mayatatun kalamai na safe daban.,na rana ma haka ,na marece ma haka,shi kanshi mamakin kanshi yake bare akaje ga uwar gayyar.... Amman fa dan rigima har yanzu taki saukowa yanda yake so ba leifi ta dan rage shareshin datake .. sede kuma daga jiya zowa yau kamar ciwon shi ke san tashi dan yau kam asibitin ya wani amatsayi majinyaci ba docto ba.abunda kuwa ya tashi ciwon be fice wata waka da Maysam din ta tsira wato setaga yana aiki seta zo tana wakarta tun abun baya damunshi har yazo ya fara ..wakar itace 🎼 _Abun son zuciya shine kasamu me kishinka ,_ _Gobe inta samu hakika. Babu zancen rabewa_ 🎼.shi duk gani yake rabuwa zatayi dashi ....Mark yayi ya gaya mishi damuwarshi aman yaki fadi har ya gaji dan haka ya kira Mariam bayan sun gaisa yanemi yayi magana da Maysam ..bata musa ba..itakuwa lokacin tana ta tunanin shi dan kwana biyun nan ta lura da akwai abunda ke damunshi..ta kuma yanke shawarar yau zata zubadda kayan yakin ..ta rungumi Muradinta ..haba yayi ma kokari ai ... Mariam Ta bata wayar bayan sun gaisa ne yake sanar mata da mijinta bashida lafiya ...cike da tashin hankali take tambaya shi miya sameshi .. Nan de yace damuwa ce tayi mishi yawa sekuma ciwonshi dake son tashi ..ba karamar razana tayi ba.dan tasan itace sanadi....bata yi wata2 ba ta shigo taxi ya kawota likitar.. Yana baccishi ana mishi karin ruwa ....zama tayi kusa dashi tana kallon kyakyawar fuskarshi...ta kama hannushi daya ta damke shi gam kamar wanda za'a kwace matashi Har drip din yakare aka fidda mishi amman be farka ba ..nan Maysam ta shiga kukan zuci...bata yi aune ba tashiga yin na zahirin..... Kukanta ya tadashi ..ganinta kusa dashi ba karamin dadi yaji ba ..nan ya matsa hannun data rikeshi. Dayan kuma yana gige mata hawayen datake Ai tana ganin farkawar shi se dariyar farin ciki ta subuce mata ... Tashi yayi ya zauna dan yaji karfin jikinshi sosai . ... Sadda kanta tayi tace pls yaya ka yafe mun duk abunda nayi m.. Da sauri ya rufe mata baki da hannushi ya ce ni ya dace dana baki hakuri kan abubuwan danyi miki a baya.. Yace ina me baki hakuri sannan ina neman yafiyarki... Waro ido tayi cike da mamaki wai itace Murad ke bawa hakuri..yau Yayi dan murmushi yace kina mamaki ko?nima haka kin ringaya da kin dasa sonki a zuciyana ,,kece mace ta ukku a rayuna dana taba bawa hakuri .,daga Momy se sweetbabyna ..duk karancin shekarunta bana jin kunyar bata hakuri dan bana son bacin ranta ..to kema yanzu kin kin ciri wanan tutare a zuciya ta ...pls ki aje mukamanki yakin nan ya isa haka .. Rungume juna sukayi sekuma Maysam ta fashe da kukan da ita kanta bata san dalilin yinshi .ba. Yace kidena kukan nan har cikin zuciyata yake taba.wa...kuma na gode miki dakika yi mum wannan horon dan yanzu na tattance irin son da nake miki.kin nuna mun karfin matsayin ki ......sun jima suna musayar kalamai soyyaya wa juna su..nide ina share ina rubuta kalaman a wata paper dan kada in manta harafi daya ma in zanyi wa oga😎😎😜😜 Bayan sallar la'asr suka dawo gida. . tofa abun nema ya samu dan akwana biyun nan soyayyar suka zubawa babu kama hannun yaro...kuma har yau Murad be sake kokarin nemanta ba..ita kuma abun ya fara damunta dan tasani yana bukatar ta kawai de yana tsoran kada ta sake mishi abunda tayi ne..har wani kananan ciwon cikin shi tana sane dasu.. Dan haka yar tsokanar ku ta yanke decision final yau....... Kamar wacan lokacin ta sake wani sabon shirin ta nide idone nawa tunda konace kada tasha ma ba jina take ba ...dan haka nace jikinta ma ai ze gaya mata. .. Duk wani shiga da ficen ta yana nan zaune ya kallonta ....har lokacin salar magrib yayi ya fice.. abun na yau fa da gaske ne dan kuwa kajin amarcinta ma ita ta soya abunta ...ta jere komi a dinning. Aman fa zuciyanta banda bugun lugude babu abunda take tsorene fal ranta . tana de daurewa ne .',..a ranta tace gwara ita ta taimaka mishi tunda ita dayar matar tashi taki dawowa..(kai ranar nan fa yace miki babu wata kishiya🙄halan baki yarda bane🤦‍♀)... Be shigo gidan ba se wajejan tara da rabi dan ya biya likita sun samu wani emergency... Lokacin daya dawo tana wurin su Mufeedah ....sullube wa tayi ta tafi sama abunta.. Lokacin yayi wanka yana kallo a laptop dinshi . ... Daga bayanshi tazo ta leka computer taga miye yake kallo yana murmushi ne shi kade haka ....ai kuwa photon ta dana sweetbaby ne a screen din ..ai nan gabanta yai wani irin mummunan faduwa ta kurawa photon sweetbabyn ido kamar tasan yarinyar take gani.......namijin kokari tayi ta kewayo direct rufe computen tayi tace mi kake kallon photo baya gani a zahiri kuma a gabanka .... Jayota yayi ta fada jikinshi yace hakane to ai naga kin manta dani de shiyasa.... Murmushi kawai tayi ...ta tashi Nan ta kawo kajin tare da fresh milk da jus se kuma fruit tace zo muyi dinner.. Ya mutsa fuska yayi yace kici kawai a koshe nake.. Tab ai wly wannan bama magana bace oya com'on .. Girgiza kai yayi yace yar rigimace ke wly .... Zama yayi ..ta bude kajin kai ba Murad ba ni kaina na hada miyau dan wata irin suyace tayi musu se tashin kamshin dadi suke😋😋... Yace yau kuma soyyayun kaji akayi muna a dinner.. Umm na amarci ne ai dan haka kaci abunka.. Kwashewa yayi da dariya dan shi ya dauka duk wasa ne abun.. Itade kasa ci ma tayi duk ta wani tsure. ...ni kuwa nace kefa kika sa kanki dama kin ci kajinki dan zasu yi dadi a baki😋.... Ganin takasa ci yasa ya shiga bata a baki ...da kyar ya samu tayi baki biyu..tace ya isheta ..fresh milk kawai tasha... Shikam suyar ta mishi dadi dan haka yaci da dan yawa.. bayan sun gama ta tattare komi takai kitchen .... Wanka ta shiga tayi tare da alwala ...duk cikin sanyi jiki takeyin komi....umm turare sun sha kashi anan ta saka wata sleepingdress dinta me kyau ..dogon hijab ta saka ..lokacin data shiga dakin nashi ...har yayi shirin baccin shi yana kokarin hawa gadon... Da sauri tace ya haka kuma .... Da mamaki yake kallonta yace kamar ya fa.. Ba karamin karfin hali tayi ba tace kayi alwala zamuyi nafila ......kamar yanda sunna ta tanada Be kawo komi a ranshi ba dan haka beyi muso ba yayi ya jasu..rka'a biyu sukayi.bayan sun gama tace banji kayi muna addu'a ba ..shifa yanzu abun ma tsoro yake bashi .beyi nauyin baki ba.yace wai mikike nufi ne haka.. Murmushi karfin hali tayi tace hakkika zan baka ne yau.. Waro ido yayi ya saki baki da hanci yana kallonta .. Hannu tasa ta rufe mishi bakin tace miye kuma abun mamaki anan .. Ajiyar zuciya yayi yace kada ki damu ni na yafe .. Seda ta cire kumya ta sadda kanta kasa tace to ni kaban nawa hakki tunda kai baza ka amshi naka ba ... Zura mata ido yayi yama rasa abunyi ..da kyar ya tattara nutsuwarshi yace are you fine?kin san kuwa mi kike fada? Still kanta a kasa tace dama se mutum bashida lfy yake neman hakkishi ne?...kuma ma ai sabida bana so kashiga wani hali ne... Besake cewa komi ba nan ya shiga kwararo musu addu'a ...sannan yayi mata tambayoyi .. Cike da nutsuwa take amsa mishi .... Gado suka nufa bayan sun kwanta Murad ya mirgino yayi mata runfa yana shafa gashinta kanta yace ''es tu sûr que c'est ce que tu veux.....? Gyada kai kawai tayi dan se yanzu cikkeken tsoro ya shigeta (ayya ai kin makaro kuma ..ai seda nace kada kiyi kika yi 😜) Naso kwaso muku rahoto to aman sena ga abun ya fice karfin bironan dan haka sum2 na fito tare da rufo musu kofar .. Nan falon na zauna Um kuma kunsa ai mizanyi ...ragowar kajin nan na tasa agaba na fara ci😜😋 ..abuna......daga nan na dinga jin kuka da kananan ihun Maysam.. Ai kuwa mi zanyi inba dariyar ketaba...🤣🤣🤣🤣dama na gaya miki ai kika ki jina .....aman fa daga baya na nan tausaya mata fa😜😉.... Asuba tagari 😎😎😎 Muje zuwa 🏃‍♀ Ina yinku 😍😍😍 Fasma ce ✍yar mutan zinder [15/08 à 00:44] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 🎂🎂🎂 *oohh today is a special day for me because it's my birtday ....* 🍭🍩 *happy birtday to me ..am so Happy🎉🎉..joyeux anniversaire à moi* 😍😍❤😘😘 🎂🎂 *happy birtday to you JIDDA Kema* .🎉🍭 Dedicated to ME FASMA &YOU JIDDA😍❤ 🅿99__100 ```Manzon Allah (SAW) yace ''kada dayanku yayi tafiya da takalmi daya. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi..``` [15/08/18 à 00:00]Nan nima bacci ya kwashe ni ...asubar fari a kunne na akayi ta ..cikin hanzari ta tura kofar na shige ...Maysam na tsinkaya ta kududun ne a cikin bargo tana bacci ta aman da kagani kasan bawani dadin bacci takeji ba..inan tsaye ina kare ma komi kallon da alamade har sunyi wanka dan ko drap din an canzata ..fuskarta tayi fayau da ita ...se lokacin naga Murad ya fito daga tolet da alama wanka da alwala yayi ..fuskarshi har wani kyalli agonci take ga wani tsadaden murmushi da yake saki akai2 .....jallabiyar shi ya saka ya shiga jera nafilfili tare da addu'oi ga Maysam har akayi kiran sallar farko sa anan ya isa ya zauna bakin gadon dede setin Maysam ..... Shafa kanta ya dinga yi daga bisani kuma ya kai bakin shi dede kunnenta ya na yi mata rada..duk kwallafata banji miyake fada mata ba.. A hankali2 ta fara bude idonta da duk suka kumbura alamun tasha kuka kenan ta sauke su fes kan kyakyawar fuskarshi ....kawai seta saki mishi kuka wanda daga ji na shagwabane ..shi kuma gogan ya hau ya zauna se rarrashi yake ..da kyar ya lallabata ta tashi da kyar har wani dingishi take ya kaita tolet ya sake gasata a ruwan zafi sanna ta doro alwala ...... Shi yajasu sallar ...yau kam da kyar ta samu tayi azkar din ma dan wani mayan bacci takeji ....bayan sun gama ya jata suka koma gadon bacci duk ya wani mamatse ta ya rumgume ..tayi kokarin kwace kanta aman ba karfin ga kuma bacci da yaci karfin ta dan haka ta kyaleshi ...... Shikam kasa komawa bacci yayi kawai tusata gaba yayi yana kallonta wani sonta da kaunarta na kara shiga cikin jikin shi ...shi kade se sakin murmushi yake..yana zngura mata albarka Wajejan bakwai ya fita ya sanar da su Mufeedah kada su jirata bata jin dadi ....suka hayo suka tarar se kwasar bacci abunta take .....haka suka fice cike da jimami tare da tunanin ko mi ya sameta ...duk tausayinta ya cikasu ..suma duk jikin su yayi sanyi ganin Maysam batada lfy.haka sukaje driver ya saukesu ..dan da farko sunso ma kin zuwa aman se Murad ya nuna musu mahimmacin zuwan su dan insun dawo se su koya mata abunda aka koya musu.. .se lokacin suka sami dan kwarin guiwa .. Murad kam Kuyangi ya saka sukayi mata break masu dan romo2😋.. ..nan ya zauna palon yana kallo aman rabin hakalinshi na kanta biri2 se ya lekata ..yau kam baya jin ze tafi office dan haka yakira Mark ya sanar mishi wife dinshi bata jin dadi dan haka baze samu damar zowa ba.... Ita kuwa baccin gajiya take ..ba ita ta farka ba se goma ...ta lallaba tayi wani wanka tare da gasa jikinta se kuma taji dadi ajikinta ...dugawar riga na atampa ta zumbula tare da wani zabgege hijab a cewar bazata kara saka english wear ba tunda suna temakawa wajen tadawa Murad. Sha'awar ..aman intayi shigarna babu ta inda ze ga jikinta ma bare ya takurata Tan fitowa dariya ta subcewa Murad ganin irin tafiyar da take ... Haba ai kuwa nan ta duke ta shiga rera mishi kuka .....da kyar ya lallabata ...se harara take aika mishi Farfesun ma kadan ci shima dan ya matsa mata ne ..dan bata da appeti ko kadan.... Yau kam Maysam kin zama ma tayi kusa da Murad bare har ta dane cinya yayi2 takiye mishi kai daga karshe ma kuka ta saka mishi ..dole ya kyaleta ..taje can kujera dake nesa data shi ta zauna...ga kuma kumyarshi dake dawai niya da ita yau din Shi abunma birgeshi da dariya ya bashi.. Zaman kurame sukayi ..ita tana kallon tv shikuma ya na kallon ta ..can de yace waini yau baza ayi mun magana bane ..ni miye lefina bayan keki ka nema kuma na baki .. ..nan ma shiru tayi mishi... Daga haka seya tashi ze dawo kusa da ita ai kuwa ta saki kuka tana fadin wayoo Momyna se kasheni wly kada ka matso kusa dani mun bata tunda kayi mun mugunta .. ...guiyoyin shi biyu ya kai kasa yace inace abunda kikeso ne nayi miki ko.. Tana share hawayen tace to daga baya ba nace maka bana so ba amman kayi kunnen shegu dani .. Yana yar dariya yace sorry my honey ai banjiki bane kuma ma ni abunda kade naji shine kawo in sa maka ..dakike ta fada..se sunan yen dakika dinga jerawa na su zo su temakeki ... ..... Ya mutsa fuska tayi tace nide yanzu ba ruwana dakai dama na sani ba wani sona kake ba dan na tabbata lahira direct kaso aikani jiyan nan, kawai de kwanane a gaba .. Gumtse dariyar yayi yace shikenan bazan karaba ... Se lokacin ta saki ranta ..tace shikenan to kawo yatsarka mu shirya... Ya beko mata yatsar ....a memakon tayi abunda tace se kawai ta shiga waro ido tana kallon yatsar ..kamar wacce taga wani abun tsoro Ganin haka shima ya kai kallonshi wurin dan ganin mitake warawa ido hakane ...ganin ZOBEN dake yatsar ne take kallo yasa yace yana da kyau ko ? Gyada mishi kai tayi .. Yace ko kina sone na bakishi.. A'a abun ne ya bani mamaki dan ina da irin shi ...Abbana ya banishi lokacin dana za'ayi auren mu Kai har ma wannan rubutun M² dake cikinta ina dashi ..sede tawa tafi taka kyau da kyalli dan zinariya ne nawa..kai kuma azurfa ne ..tana yi mishi gwalo.. Mamaki da al'ajabi ya kamashi danshi yana iya cewa shida sweetbabynshi kade ne ke dasu a fadin duniyar nan ma dan kuwa shi ya saka aka kera musu su ...kuma abunda yasa yace haka can cikin zoben ba M² bane kade sunan su ne a jiki aman in baka luraba M² kade zaka gani ..yana kallonta yace ina naki zoben ne ..cike da zakuwa .. Kai na baroshi can gida cikin kayana dan banason ya bata... Murad yace to shi zoben naki yana rubutu ne acan cikin shi... Girgiza mishi kai tayi tace a'a bashida kawai M² kade ajikin.... Ajiyar zuciya yayi dan dama da kamar wahala asamu me irin shi sede me kama dashi ....nan suka ci gaba da hirar su da su Mariam suka dawo sukayi mata ya jiki ..bayan Murad ya fitane suke tsokanarta kode ta sama musu Baby ne... A ranta tace um bakusan jiyane ma aka bude hanyarba ku har ta wani baby kuke ..a fili kuma seta ce tab baby fa ni yar yarinya dani haka ..ai konayi ciki sena kara girma ..ku bakuga wuyar da akesha bane wurin haihuwa.. Suka kwashe da dariya Mufeedah tace to dai kada akwana biyu mu ganki da cikin kina wani cika bakin kin.. Kai bakinki ya sari danyan kashi wly ......nan sukayita barkon cin su hardaga baya suka koya mata darasin na yau..... Cikin satin kam soyyayrsu suke ci da cinke kullum suna makale da juna ..Maysam ta saki jikinta kamar da har da saka kananan kayanta ..sede shima be sake gwada nemanta ba .. .. Yau kam ta kama lahadi su duka biyun suna gida... Maysam ta cakare ta fito da biro da kuma wata notebook lokacin yana aiki a laptop dinshi ..koda ta zo batayi wata2 ba ta jaye laptop din ta dane cinya abunta ... Yana kallonta har wani lumshe ido yake dan turaren ta suna kashe mishi jiki .....kallonta kawai yake..yana admired dinta Daga bisani kuma yana wani shashafa yace kullum kara kyau kike wife .. Yar dariya tayi sekuma tayi kissing dinshi a kumatu tace nagode MURADINA ...yanzu de bawan nan ba lissafi nazo muyi... Da mamaki yake kallonta yace lissafi kuma... Umm tace ..se kuma ta fara yi mishi tambaya kamar haka ..shin kana da gidaje biyu A Maradi ko..,biyar a Niamey ko? Ya gyada kai ..yace e Ta ci gaba motar goma gareka ko? Yace ee Tace se kuma mall kana ukku a garin nan .da kuma hudu a zinder Cike da mamaki yace ee Tace da kuma jirgin ka na nan dana Niamey ko? Yace wai tsaya a ina kika samu duka wannan bayan Mall dina nan da jirgin dana saya ko kwana goma basuyi ba kuma kosu Momy ban fada ma ba ..tayaya kika san duk wannan... Dariya tayi tace to ai ba ina nasan su bane ..zaka tambaya mi zanyi dasu nan gaba zaka tambaya ...dan kai da kanka kayi mun alkawarin su.. Cike da mamaki yace ni kuma.. Shikenan bara na tuna maka ranar nan ne lokacin dakake amsar hakkika kace duka wannan abun ka banisu halak malak .. Se yanzu tabbase ya tuna..yayi dariya yace to ke yanzu mi zakiyi da duk wanna abubawa... Momy zan bawa su ..dan bansan ita waccar matar taka kyautar mi kayi mata ne ehe ...dan haka zan bawa Momysu ita tasan mizatayi da su.. Dariya yayi mata ganin kishine ya motsa yau din... Kwantar da ita yayi a kirjinshi yana shafa kanta yace wai miyasa kike kishi da matar da bakima santa ba... Da sweetbaby ya kamata kiyi kishinki dan ita keda rabin zuciyana kema kina da rabi...dan kishiyar da kike ta batu wasa nake miki tun wancan lokacin ..babu wani aure danayi ....ki saka a ranki daga ke na rufe kofa in Allah ya yarda dan ko nayi Allah yana gani bazan iya yin adalci tsakani ba...kai na baze iya daukan rigimar mata biyu ba ni ke din ma da za'a rabaki abani rabinki dan ke kade ma.caza mun kai kike bare mata biyu.. Wani sanyi dadine ya ziyarce ta tace har ta kara kankameshi gam a jikinta tana dariya farin ciki tace to ai ita sweetbaby bata nan taya ma zanyi kishi da ita bayan na san sonta a jinin jikinka ne yake yawo ....bazan iya yin kishi da itaba soboda kana sonta ..nima kuma duk abunda kake so nakanyi kokarkin na koyawa zuciyata sonshi ...dan na faranta maka rai...kaga ita tare na ganku bazanso rabaku da ita ba ..kara rugumeta yayi yana mata godiya ....yace to yanzu se mu fara procedure din transfert kenan... Dariya tayi tace wani tranfer ai kuma na yafe maka su dan dama saboda kishine ...dariya yai.shikenan to .. Can se yace kinga gift dinki ne... Kalar tunani tayi tace a'a.. Ok to kije ki sake duba karkashin pilonki zaki gani... Da sauri ta tashi ta shige...koda ta duba se kuwa taga wani envelop .....doko shi tayi ta kawo mishi.. Girgiza mata kai yayi yace a'a ai nakine ki bude abunki.. Ai kuwa tana budewa taga takardun gidane se key .... Zatayi magana yace gift dinki ne ...takardun gidan wannane da kuma key din sabuwar motar da na sai miki ..kamar yanda al'adar can gida ta tanada ba ..cewa washe garin daren farko za 'abawa amariya gift na fita kumya ..naso baki taki kema washe garin to aman ai ranar tazo mun a bazata shiyasa se yau nasamu ...na baki da fatan banyi lefi ba Cike da murna ta fada jikinshi tana me jin dadi .tace na yafe ..ai daka barshi ma dan wannan al'adane ba addini ba.. Murmushi yayi.ya rada mata a kunne cewa ina alfahari da ke babyna...ina tayaki murna kin kawo mi budurcinki na gode miki Allah ya albarkaci rayuwarki duniya da lahira...ya biyaki da mafificin alherin sa ...ina sonki wifey ta... Tana dariya farin ciki tace na gode Allah ya saka da alheri ya kara budi ...je t'aime plus.... Sosai yaji dadin adddu'ar ....se kuma yace to muje daga ciki ki kara nuna mun godiyar ki.. Master room ya fice da ita ..na kuwa mara musu baya dan ganin wacce irin godiya ce da har se anje kuryar naki za'a yita.. Tunda suka shiga suke aikin kissing din su kamar zasu cinye junan su ..nide ina tsaye ina jira ..dan inde wanna ne naga na saba gani ..ai kuwa abu ya fara kankama suka shiga romance ..ina ganin haka na jayo kafafuna na fito ..dan kusan ita soyyayar theori suna fada ne ina sauye muku amma ita pratical ta inda zan fara ma nake rasawa shiyasa nake bar musu dakin😜.. ...tun shi Maysam ta zama yar hannu a bunka ga renonshi yasa wani lokaci babu ko kunya itake nema ..soyyaya kam da tattali junan su duk wanda yagan se sun bashi sha'awa..sun kuma birgeshi ..karfi dayaji ta medasho mrs romantico ..Mark da Mahmud kam banda tsokana babu abunda suke mishi.. Babu ruwanshi da inda suke ako ina soyyaya yake gwada mata ..rayuwa tayi musu dadi ..su duka sunyi bulbul kwanciyar hankali ta zauna musu .. 🌹. 🌹. 🌹 A gurguje pls Bayan wata ukku Maysam tayi wani kyau da fari na ban mamaki ..ta kara cikowa musaman kirjinta..har wani fresh tayi ...Murad kam abun nema ya samu se kwasar garabasa yake ..... Yayinda ita kuma kwana biyun nan da zazzabi take kwana ... Se kuma wani dan banzan kwadayi abu inde me yaji2 ne to zataci shi ..kwade harda na banzan..yau ma suna zaune lafiya2 suna hirarsu irin ta masoya ..can Maysam tace my king zanci hadin boss.. Gyara zama yayi yace miye kuma wani hadin boss..? Dayake abun na rigima ne se kawai ta rushe da kuka har da shure2 ita kawai hadin boss zataci. Da kyar ya shawo kanta yace wai dan Allah miye ne sena fita na nemomiki shi ... Tace garin kwaki da madara da suga kuma ba'a saka ruwa hakanan ake shanshi.. Dafe goshi yayi yace to ni yanzu a garin ina zan samu garin kwaki ..ai tana jin haka ta sake fashewa da kuka tace kenan ma baza ka samo min ba. ..wayoo Momyna ina kike ne.. Babu shiri ya zari key ya fice ..be jima ba se gashi ya shigo ..nan ya hada mata ..tana ci taji yayi mata dadi .har wani lumshe ido take.dan haka rigima ta kwanta ......bayan ta gama yace taje ta dauko hijab dinta sutafi asibiti yayi mata wani test dan tabbatar da abunda yake zargi.... Ai kuwa bayan yayi mata test din ya gano karamin cikin dake makale a mararta na wata 2 da yan kwana ki... Tana nan zaune yashigo da test daya karbo daga lab..batayi aune ba taji ya dauketa yana juyi da ita ... Can ya sauketa yace am so very happy today.. Tana kallonshi tace what's happen ne...kake murna haka.. Yace toutes mes felicitations na kusa zama papa ke kuma mama a takaici'' tu es enceinte de deux mois'' Wani waro ido tayi tace what ?ciki? Yana yin yanda tayi maganar ne ya tsorata Murad ..a ranshi yace kadade fa bata son cikin .... . Love you all😘😍❤ Fasma ce🖊 yar mutan Zinder [16/08 à 22:26] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿101__102 ```Manzon Allah(SAW) ya ce''baya halatta ga musulmi ya leka gida ko dakin wani ba tare da izini ba. Bukhari ya rawaito shi``` [16/08/18 à 22:00]. Cike da karkarwar baki yace ee kina dauke da cikina na wata 2 da yan kwanaki ... Cike da dakewa tace aman de zubar dashi za ayi ko?dan ni ba isa haihuwa ba ..kuma ma karatun nawa fa yakake so nayi dashi What ?cikin nawa za'a zubar .? Wannan bama magana bace tun wuri ki rufe ta anan ..kuma inde akan karatune sede ki fasa makarantar wly bayan kin haifeshi kya gama inde har baza ki iya ba ehe Se kawai yaji ta fashe mishi da kuka harda dire2 ita bata san cikin nan dole se an zubar dashi..kuma makarantar ta bazata fasaba.taya ma za'ace ita yar karamar nan tanada ciki tab ..ai kuwa da sake wai anbawa me kaza kai... Tsawa ya daka mata yace shut up ...walahi cikin nan kamar kin haifeshi kin gama ko kina so ko bakya so... Itama cike da daga murya tace to mu zuba ni da kai ... Fuuu ta fice a office din tare da bugo mishi kofar... Ya mutsa gashin kanshi ya fara tare da fadin inna lillahi wa inna ileyhi raji'un.....mi yake shirin faruwa dani ne ?ya salam.... Da sauri ya bi bayanta amman kafin ya fito har ta shige taxi sunyi tafiyar su ..bin bayansu yayi shima .. A kofar gidan ya sauketa ta biyashi ta shige ...yana shigowa yaga zata shige daki da sauri ya shiga gabanta ....yace pls wify kada kin mun haka wly ina son cikin nan na kwallafa rai na a kanshi.... Maysam kam shafa wa idonta toka tayi tace bata san da zancen ba ... Murad ya kankance ido shima yace ...dama irin son da kike tinkaho kina mun kenan? Maysam tace babu ruwan so da kuma cikin dake jikina...ciki ne de nace bana sonshi yanzu ..ka bari sena kara girma zan haifama ko nawa kake so amma ba yanzu ba ..am so young da haihuwa.... Murad yace sukuwa suke da alaka yanzu na tambatar da dama ba sona kike ba tunda har bakya son gudan jini na .... To ai ba cewa nayi bana so ba . a yanzu nede bana so ... Kai.yau kam dan karamin yaki sukayi tsakanin su ..har takai Murad ya samata hannu wato ya wanka mata marin da shin kanshi seda yayi nadamar yin shi ... Ai kuwa Maysam ta hau ta kai kololuwa ..se kawai ta dau fushi da shi .. To da fari ya damu da fushin nata yana ta rarrashi shima kuma daga baya se yayi forget da ita... Sede matsalarshi da ita dabata cin abinci ...yana tsoron kada yunwa ta shigeta Seda suka cinye sati guda cur basa ko magana kai ganin junan su ma wuya yake musu dan tun safe yake tafiyarshi kuma baya dawowa se lokacin daya san tayi bacci ..su duka har wata yar rama da baki sukayi ..dan duk sun damu da junan su tsabar rigimar ta ne kawai ya jefa su cikin wannan hali..... Yauma kamar kullum dayake abun na rigima ne ..kin bacci tayi ta zauna nan tana jiran shigowarshi ..shima beshigoba se sha daya saura..tunda ya ganta a palo yasa za ayita yau.. Yi yayi kmar be ganta ba ze shige dakin shi da sauri ta shiga gabanshi tace yau seka gayan daga ina kake ..a ina kake cika dare .... Tsuka yayi yace da kin damu dani da bakiyi mun tambayar nan ba ...to in son sani kike to abunda bikya sone wato ina wajen wacce zan aura ne kuma nan bada dadewa ba tunda ke bakya son gudan jini na ..zan auri wacce zatayi ta haifa mun y'ay'a..ko kinada abun cewa.. Kamar saukar guduma taji zancen ...bata ce dashi komi ba ta shige dakinta ..ranar kam taci kuka... Tun su Mufeeda basu lura ba har suka san da basa magana ..basu de tambayeta mi ya gamasu ba dan tsakanin miji da mata se Allah...su de kullum cikin tausarta suke tare da bata hakuri ...tabi komi a sannu zata ga sakamako me kyau.. Shima a bangaren shi duk yabi ya fara susucewa kamar bashiba ..ko aikin ma baya meda hankalin shi akai ..Mark shike bashi baki da yayi hakuri .... Kai abun har ya fara taba ciwonshi ..dan haka Mark ya daga waya ya sanar da Mahmud kan ya lallabashi ko ya gaya mishi mike damunshi .. Mahmud ya daga waya ya kirashi ..tun suna gaisawa ya tabbatar da bashida lafiya ..cike da rarrashi da dubara yace pls Murad miyasa kake son tada ciwon kane ..?mi yasa baka tausayin kan kane.. ..duba dan yanda kake shan wahala kan ciwon nan?why bazaka bi komi a sannu ba. ..ka rungumi kaddarar Allah ba.... Ajiyar zuciya Murad yayi yace dan baka san mi yarin yar nan tamun bane ...dan taga ina sonta ne na damu da ita shiyasa take mun abunda taga dama ... Mahmud yace calme down yanzu fada mun mi tayi ma .. Yanzu in ba ta renani ba yarinyar ta kalli tsabar idona tace wai zata zubar da cikina?.ciki nane fa Mahmud gudan jini na...?kamar zeyi kuka.. Mahamud ya dan bashi baki duk da yasan bata kyauta ba amma se ya nuna mishi da yarinta ne kawai ke damunta har take son zubar dashi ..kuma ma da tana zubarwa da tayi kawai ka lallabata da akwai abunda yasa ta fadin hakan ..nan yayi ta lallabashi har yaji ya sauko ..yayi mishi godiya kamar kullum ..suka kashe wayar.. Itama kuma anata bangaren yaude Su Mufeeda sun tusata gaba kan abunda take fa be dace ba ..ya kamata ta gyara yau har tsawon wata guda kenan fa ..itama kuma ta damu da rashin mijinta kusa da ita .... Ajiyar zuciya tayi sannan ta sanar musu ai akan tace se ta zubar da ciki ne suke rigimar nan ... Mariam tace bakida hankali da kike son zubar da cikin ne ..... Mufeeda taso yi mata tsiya amma ganin halin da ake ne ya sata kyaleta ...tace ke miye dalilinki na on zubar da cikin ne .. Cike da yarinta tace to bakunga yanda ake shan wuya ne wurin haihuwa wasu fa har mutuwa suke..kuma kinga ai bankai haihuwa ba salon kawai naje nayi yoyon fitsari gani yarinya karama dani duka ma am 17 old fa.. .. Mariam tace gaskiya da kinyi wauwauta fa ..ke yanzu bakya son ki haihu a dinga ce miki mama ne.. Se kuma naga Maysam tayi dan murmushi tace ina so mana .. Mufeeda tace kuma bakya so ace wacce er kice ..kinayi mata wanka ,wasa ..in macece kina mata kitso ne..Manzon Allah ma yana cewa ''kuyi aure ku haiyayafa dan nayi alfahari daku ranar gobe alkiyama.....shin baza kiso ki haifu ki tarbiyatar da yayanki har Manzon cira yayi alfahari dakene . Maysam tashafa cikin tace tab ai ni kuwa nake so ..kawai de ina tsoro ne...aman kuma fa yanzu na fara sonshi kadan2..dan in naji yana motsi se ina jin dadi kuma... .dariya sukayi sukace muma kinga zamu zama mama .tunda mu triple.zaki haifa mana baby ... Mariam tace kuma ai ko wani me rai mamaci ne ..ba dole se wajen haifuwa ba ko yanzu in kwanan mutum ya kare ze mutu dan haka ki fidda wannan abun ma...kuma ma kin sani ko wajen zubarwar ki mutu...bama wanan ba to infa shi kade kwanki a duniyar nan..kada ki butulce wa kyautar da Allah yayi miki mana ..muatane nawa suke so amman basu samu ba .. Maysam tace hakane kuma fa . abunda yasa ban zubar ba naga Murad yana son shi ne shiyasa ma na barshi koda zan rasa rainane dan duk abunda yake so nima ina sonshi .kawai de banji dadin rashin fahimtar da yayi mun ne... .suna haka se ga kiran Fulani ya shigo wayarta..bayan sun gaisa fulani tace am so happy for you dauther na ashe tu es enceinte shine kuma baki taba fada mun ba duk wayar da muke yi...daga ke har mijin. Naki Rufe fuska tayi kamar tana gabanta tana dan murmushi kasa2 ... Fulani tace dazu Mahmud yake bani labari ..Allah ya raba lafiya ya kawo masu albarka .. Ameen tace kasa cike da kunya..kuma taji dadi da basu gayawa fulani abunda ke faruwa ba.. Nan.suka dan tattaba hira har take tambayar ta yaushene hutun nasu... Tace nan da wata guda ne..ta saka mata albarka sukayi sallama.. Ta juyo ta kalli su Mufeeda tace na gode muku hakika kun cika kawaye na gari ..Allah ya qara muna dankon kauna da zumunci ..a tare sukece ameen yar rigima ai yanzu seki tashi ki fara shirin tarbar yayan mu .. Dariya tayi ta kai musu duka tana fadin kujiye mun yara da iyayi... A tare suka kama haba suna dariya sukace seku matan aure ....muma de nan da wata biyu ne .. Haka suna ta tsokanar junansu ta haye sama .. Dama duk da basa shiri aman kullum seta gyara mishi dakin shi .....kafin sallar magarib ta gama kominta tayi wanka aman kuma tana da yakinin baze shigo yanzu ba dan tunda abun ya faru baya dawowa da wuri.. Ta dauko wayarta ..da kamar ta kira se kuma ta fasa ..can de tura mishi da text nin inze shigo ya taho mata da garin kwaki irin nan ranan dan yau shi babyn ka keson ci... Lokacin daya karanta har yaso yayi forget da ita to amma se yaji baze iya ba musaman dayaji tace babyn shi..dan haka ya biyo mata dashi .. Bashi ya shigo gidan ba se goma ..lokacin har ta fara baccin anan palon .. Ya so kyaleta se kuma ya tada ita ya bata garin ... Kin karba tayi se ma zuba mishi ido datayi kamar yaune ta fara ganin shi duk yayi yar rama ...shima kallonta yake ta dan rame da ga wuya aman kuma kirjinta da bayan ta bulbul da su .. Ya sauke ajiyar zuciya yace sakonki ne amsa.. Kin karba tayi cike da shagwaba tace to wa kakeso ya hada mun ne .. Girgiza kai yayi dan ya lura yau rigima takeji ..bece komi ba ya tashi yayi kitchen dan kamshin turarenta fizgarshi yake..... Hada mata yayi ya bata .... Tana kalloshi tace to waze feeding dina .. Abun nan fa baby ka ne kesan sha fa.. Zama yayi kusa da ita ..ai kuwa ta dane cinyarshi ta bude baki ya samata ...haya yayi ta bata a bakin Kallonta yayi yana shafa kanta yace baby nane kade . ke ba naki bane Kanta ta kwantar a kafadarshi tace nawane mane... Ajiyar zuciya yayi yace pls Wife ki aje rigimar nan muyi renon cikin nan cikin so da kaunar junan mu ..wly ina son yara dayawa kuma kinga ke kade nake dashi ..na rigaya dana rufe pls ki bar cikin nan ki haifa mun shi..ina matukar kaunarshi Wani kallo tayi mishi tace hum kace haka mana. .ko ka manta waccan lokacin kace daga wajen yarinyar daza aura kake ..shine kuma zakazo kana mun dadin baki .. Ajiyar zuciya yayi yace keman kinsan na fada ne dan naga ko zaki sauko aman bazan iya kara aure ba ..... Tana hawaye tace to ai kuwa ka cutar dani ranar dan tun lokacin bacci bana iyayi senaga shigowar ka .. Share mata hawaye yayi yace am sorry wify ni ma se bayan na fada na san ban kyauta miki ba ..kuma nima ai ba wani bacci nake ba ..kullum cikin dare sena bari kinyi bacci nake shigowa na ganki ba karamar azabtuwa nayi ba .. Maysam tace baka kaini ..dan nayi missing dinka alot ..pls kayi mun alkawari komin rintsi baza mu sake yin nisa da juna ba. ..dan bazan iya rayuwa ba kai ba ... Suka rumgume juna yace i promise you.. To ya zancen cikin ne ya shafa shi.. Hannunta ta dora bisa nashi tace ina sonshi nima dan duk abunda kake so ina son shi dama tsoron haihuwa ne nake ..kaga gani karama kada naje na mutu ko kuma nayi yoyon fitsari na tsufa da wuri kace bakayi dani.. Dariyar farin ciki da murna yayi yace ..to ai mutuwa tana bisa wuyan kowa kuma da kike zancen tsufa ..so nawa kike son na gaya miki badan jikin ki nake sonki ba....ki kwantar da hankalin ki kin rigaya da kisamu Murad .. Dariya tayi tace am sorry too da duk irin maganganu danayi maka ...bazan kara ba in sha Allah .. Rumgumeta yayi yace dama ni ba rikeki a rai ba ..to wai tsaya ma shekarunki nawane.. Tana turo baki tace saura wata ukku nayi 17.. Cike da tsokana yace yawwa shiyasa naga yarintar tayi yawa.. Bubbuga kafa ta fara ..tace kajika ko Da sauri yace desole wify yanzude a bani abinci naci yunwa nake ji se mu shiga ki nuna mun irin missing din nawa da kikayi ... Dining suka nufa tana fadin ni bawani nuna makan da zanyi tunda kai ma bakai missing dina ba nima to banyi ba.. Dariya yayi yace to yar rigimata to ai ni missing din ne danyi baya misultuwa ne.. Maysam tace daga yar reno na dawo yar rigima kuma...tana fadar haka tana serving dinshi Bayan ta gama ta shiga feeding dinshi cike da soyaya kamar yanda suke da .....yace to ai ke din ce kullum da kalar rigimar da kike bullowa...sosai yaci abuncin dan rabonshi dayaci kamar haka har yamanta duk da tana yi mishi kullum ta aje ..to ai ba abinci kade yake da bukata ba har da kullawar ta fimishi komi ma Koda suka gama tare sukayi wanka...wasan ruwa kam sun shashi kamar kananan yara ga cikinta ya taso masha Allah dan ya kusa wata biyar .... Suka fito kowa shi ya shirya dan uwanshi ..sannan suka bi lafiyar gado .yau kam abun ban sauki dan Maysam ce manager ...,director,kuma actor principal ..😝...Murad kam dan kallon ya zama ....ina gani haka na rufe musu kofar dan gudun gardama....😜dan fa inaga kwana sukayi suna abu daya kowa yna nunawa dan uwanshi irin missing din da yayi .... Tun lokaci suka sake shimfida sabuwar soyyaya wacce tafi ta dama ....ko tari tayi zakaga Murar ya. Wani lalace wurin tambayar mi take so .ina kema ciwo....tun tana jin kumya da mamakin abun dan ko gaban su Mariam ne babu ruwanshi ..har ta dena .... Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin kwanciyar hanki da kaunar juna.. Yau kuma suka zana exam din su wanda har sun fara shirye2n koma warsu ..Murad ma permission ya nema a wajen aikin shi suka bashi.. yayinda mall din shi ya damka su a hannun wani manager dake mishi aiki dan ya yarda dashi kuma komi ze ringa turo mishi ta internet dan yaga yanda komi ke tafiya....danharda Mark za suzo ..dan aurenshi nan da wata ne shima ..suma su Mufeeda haka.. Niger Yau kama duk inda ka wulga a masarautar zakaga anata shirye2 bangaren Murad kam komi seda sarki yasa aka sauya musu da daki aka gyara tsarin gidan.. Fulani kam ta saka ana shirya musu abinci iri daban2 .. Malam Musa kam baki har kunne yar lelenshi zata dawo ..banda Murza da bakin ciki kamar ya kasheta dan ta rasa hanyar da zatabi ta cutar da Maysam din ..ga shi yanzu Musa baya barinta fita ..bare taje ta aiwatar da kudirinta.. 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 Ana gobe zasuzo sukaje ya nuna mata mall din duk sunan Murad ne ajikin su ..yace su zabi duk abunda suke so ..nan sukayi wa yan gida tsaraba dan harda su Mufeeda... Washe gari jigin su ya daga A jirgin da ya saya na can za suzo dan su Momy su ganshi ... Suna cikin jirgin Maysam ta rike hannushi me zoben tace yaya ka tuna mun da munje na nuna maka nawa zoben dan kaga da gaske nawa yafi naka kyau.. Dariya yayi yace inSha Allah ..Allah de ya kaimu lafiya nima ai na matsu dana ganshi dan saboda na tattance wani abu.. Seda suka sauke Mariam a Maradi tukon jirgin ya sake dagawa su iso Zinder... To nima bari na daga nawa jirgin haka ko😉. Love you all❤❤❤😍 Fasma ce 🖊(FASSOUMA) [18/08 à 00:27] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿103__104 ```Manzon Allah (SAW) yace''idan na umarce ku da wani abu ,to ko zo dashi gwargwadon ikonku'' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` [17/08/18 a 23:01] Wajejan sha biyu na rana jirgin su ya sauka a zinder ...zo kaga murna a masarautar musaman wajen fulani da m.Musa dazega tilon y'arshi bayan kusan shekara guda ...bakin nan har kunne sab'anin Murza dake ta yake ..bata gama shiga bakin cikin ba seda taga Maysam tare da Murad ga cikinta daya dan taso ..har mumurza ido take wai ko mafarki take (ni kuwa nace mutum da matarshi to miye na wani mamaki tunda de badan ya kalleta a ka aura mishi itaba)...take ta ayyana wani mummunan kudiri a ranta...har da wani murmushi mugunta tayi ....fada suka fara sauka ..suka gaisheda Sarki ..cike da murna da d'auki yake amsawa bare dayaga Maysam da dan cikinta ..dadi ya gama mamayeshi ..ze samu jika To hakan ne ma a bangaren M.Musa dan yayi murna ba kadan da ganin yar shi ta kara girma tayi bul2 alamar hankalinta a kwance yake ga kuma albarkar aure .... Addu'a sukayi ta musu tare da saka musu albarka ....dagan nan bangaren fulani suka zarce ..itama tayi farin cikin ganin su ..ai kuwa Maysam na ganin Momy ta makalkale mata ta shiga zuba mata shagwaba...ita kuwa se lallabta take bare da taga cikin ya fara tasowa sosai taji dadi ...tace babyna mi kike son ci ne..? Tana dariya tace hadin boss zansha Momy.... Momy batayi nauyin baki ba tace miye kuma wani hadin boss... Maysam tace Momy ai shi yaya ya sanshi kawai ki sashi ya hadamun ..dan dama cewa yayi ai da zarar mun dawo ze dena mun wasu kana nan hidimar saboda bayi da dogarai ..har da yar kwallarta .. Murad dake kallon su tun dazu bece komi ba se yanzu da yace pls Momy ki rabu da ita rigima ne kawai take ji... Can de fulani dataga abun bana karewa bane tace su tafi su watsa ruwa se suci abinci ..in su huta daga baya sa yi hirar... Maysam dakinta na nan bagaren fulani tayi niyyar shiga ..dan yanzu tana bala'in kunyar fulani bazata iya binshi ba a gabanta .. Shima da sauri ya sha gabanta yace miye kuma haka my wife .kin fa sani na saba da jikin kusa dani ..ina shakar daddanan kamshin nan naki..ya kama hannunta yace mutafi can inda zamufi sakewa kinga nan Momy nanan ....kuma zan hada miki hadin boss kasa2 yake mata maganar aman ba karamar kunya ya bata ba dan se gani take kamar fulami na jinsu ..dan haka seta saci kalon fulani se taga hankalin ta baya ma kansu dan haka cikin sauri sum2 ta fice ..shima Murad ya mara mata. Baya..harda yar rawarshi Duk abunda suke fulani na lure dasu kuma taji dadin hadin kan da suka samu tare da kaunar junan su ..nan ta kara yi musu addu'ar Allah ya qara basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba... Suna kuwa zuwa ta aza mishi rigima dole ya hada mata dama ya taho mata da garin tun can...tare suka yi wanka ..sede tun kafin su kwanta aka fara kiran sallar dole yayi alwala ya fito masallaci itama tayi tata nan gida tukon suka bi lafiyar gadon.... Haka suke kullum a tare makale da juna ko a gaban fulani be hana wa ya nuna mata soyyaya itade ji take kamar kasa ta tsage ta shige dan kumya shi kuwa ko a kwalar rigarshi .. Fulani ma kam se de ta kau da kanta daga wata rashin kumyar tashi ..... Bayan sati da dawowar su suna palon bangaren su ..Mysam dake zaune a cinyarshi tana zuba mishi kukan shagwaban da bashi da dalili ...can ya kalleta yace to ki nutsu muyi wata magana.. Tsayar da kukan tayi ta tattaro hankalinta gaba daya wajenshi.. Gyaran murya yayi yace ya zancen zoben ki ne naji ki shiru ne... Dafe goshi tayi tace laaa Muradina ai na manta da shi aman bari naje na dubo shi dan yana dakina dake bangaren Momy... Murad yace mutafi to na raka..ki A tare suka shiga dakin ..aman sukayi ma zoben neman duniya basu samu ba...ita kam har ta gaji dan neme2 da tayi.. Kamota yayi ya zaunar yace ta bari shi ya ci gaba danema ..aman de kin tambbata anan dakin yake .. Tana meda numpashi tace ee to ina de kyautata zaton anan din yake sede bana tune inda na saka shi ne Ci gaba yayi da ne ma aman shiru... Can sega fulani ta fado dakin jin sukurniya a dakin ..turus tayi ganin Murad da kanshi ke neme2.. Tace son lafya kuwa... Jiki a sanyaye yace Momy zoben wife muke nema ne.. To amemakon ka saka kuyangi suyi se kai da kanka .. Momy baza ki gane ba ..zoben ne ai bana so wani ya ganshi kafin ni.. Girdiza kay tayi da abun nashi se shi......tafiyar ta tayi ta barsu nan.. Jikinshi duk yayi sanyi dan yaso yaga zoben nan yau..aman dole ya hakura .. Maysam tace am sorry hubby na baka wahala..ina ga fa na barshi a Maradi da mukayi patyn mu na karshe ina ga yana can .. Ajiyar zuciya yayi yace shikenan ki shirya se mu tafi sati me kamawa ...cike da murna tace to dama kuwa har nayi kewar su Mufeeda.. Aman kuma ganin damuwa a fuskarshi yasa taja shi zuwa bayin dakin dan duk ya hada zufa abunka ga wanda be saba wahala ba.. Wanka suka yo ..tanata janshi da hira ko ze saki ...ta koyi nasara har da dariya ya shigayi yama manta da wani zobe ....nan tashiga yi mishi cakulkuli suna ta dariya abunsu...daga nan kuma wasa ya fara canzawa a zafafefe Maysam ke aikawa Murad da sakon ni..(kai yarinyar bakida ta ido fa😅.).na so yau na doko muku aman se rasa ta ina zan fara dan yarinyar nan ta fice tunani na ..ina ganin haka na canza takuna na ja musu kofa .dan pratical se manya .. ... Sede Kash basu samu zuwa a satin ba dan asibityn na nan masarauta suka dinga samun emercency kuma duk na fanin shine ....ga doctor din me kula da wurin baya nan ..dole tasa ya kama aiki har zuwa lokacin dawowar doctor din..dan clinik din tasu tafi sauran kayan aiki .shiyasama duk wani emercency daya gagari sauran se aturo su nan...haka ya hakura kullum cikin buzy yake ..ga kuma rigimar Maysam a gida... ..itace goyo ,kokuwa ta aza mishi kukan se yayi mata doki ,kai shirme da rigima iri2 take mishi .. Seda yayi sati biyu doctor din ya dawo ai kuwa a washe gari suka daga se Maradi .fulani kam tayi fada a cewarta zasu wahalar da cikin ...kuma ga bikin Mahmud aman jin acan Maradin za'ayi komi.....kuma taga Maysam ta nuna tana son zuwa dan aure su Mariam saura one week .na Mufeeda kuma ..kwana goma ..seta kyalesu... Ba karamar Murna sukayi ba da ganin junan su ba... Wani abun mamaki be huce zoben dabaya nan ba ..shima duk sun burcike dakuna sun bar kuyangi da aiki amam babu zobe ...Maysam har da kwallarta ganin ta batar da zoben.....kai daga karshe ma Murad hakura da zoben yayi ..tunda daman da kamar wuya ace na sweetbabyn shi ne..shiyasa ya rarrasheta aka bar zancen shi Maysam tun zuwan su ta shiga hidimar bikin Mariam da dan cikin ta se shiga da fice suke itada Mufeeda ..in sun mata magana tace to suwa zasuyi in bata kama ba.. Se kuma dare in yayi ta addabi Murad da jikinta ciwo yake mata dole se yayi mata massage..shi kanshi wani lokacin mamakin kanshi yake yanda yake biye mata ..(hum macen kenan Murad😝) Har lokacin kuma Mark be taba zuwa ganin *zab'in iyaye*(littafin my my Fatima yar kasarmu😍) n shi ba ..yaude Dadyn shi ya ritsa shi ..tunda yake ta mishi fada be dago ba se yanzu .dayashiga bawa dadi hakuri.hum wai kunsan waye Mark kuwa? Ku biyo ni de ..dole yaja Mahmud ya rakashi ..da yake ya dawo shima ...dan Murad yana can yana fama da Maysam dake dan zazzabi gajiya Mark ke jan motar dan shi ya san gidan......koda sukazo sukayi horn me gadi ya bude musu kofa ... Shi de Mahmud ya cika da mamaki dan yasan san nan gidan su Mariam ne tripleM...aman se beyi magana ba Mahmud yace to ka kirata ta fito mana.. Ya tsine fuska yayi yace nifa banida numberta hasalima rabona da ita tun tana yar mitsitsiya da ita ... Ya kuwa kwashe mishi da dariya...yace kana da aiki kam Suna fito wa daga motar akayi sa'a sega wani kaninta yazo ze fita..dan haka suka aikashi ciki ... Iso akayi musu anan palon ..ummanta da yayunta ne a palon dan haka har kasa suka gaishe su..sanan wata kanwarta tayi musu rakiya bangaren baki... Mariam kam tun lokacin da taji wai Ma'aruf yazo ..se ta tsinci kanta cikin bakin ciki dan aganin ta ai reni ne wanan ace se ana sati sauran aure sannan ze zo ..badan ummata bace ta gaya mata da bame sata fitowa.. Wani katon hijab ta saka babu ko kwalli a idon ta ..yayunta na mata magana aman ta kyallesu ga babu su Mudeeda sun tafi bare su rakata..dole ta fito ta shiga palon da sallama ..kanta a kasa tunda ta shigo dan bata ma son ganin shi..ta gaishe su Mark kam tunda tayi sallama ya zuba mata ido ..miyan bakinshi sun kafe.. kuma daga shi har Mahmud babu wanda mamaki be kusan kashe shi ba..yama kasa magana dan duk gani yake gizo ne take mishi ...shi kuwa Mahmud mamakinshi dan yana labari soyayyar su ta can england Mahmud daya lura da haka se shi ya amsa ta tare da fadin tripleM ykk ya shirye2. Da.sauri ta dago idonta dan ta gane muryar Mahumd ..aman abunda ta gani ya kara bata tsoro ...sororo take kallonshi shima haka .. Mahmud yayi dan murmushi tare da tafa hannushi. Firgit suka dawo da tunanin hucin gadin da sukayi. ..kowa yana jiran bayani daga bakin dan uwan shi.. Shikam daya ga abun bana karewa bane se yace to Mariam ga abokina Ma'aruf Elh Ma'azu kuma dan abokin abbanki kamar yanda kika sani kuma shine wanda ze aureki ... A tare suka sauke ajiyar zuciya ..aman kuma sun kasa magana ..se sakin murmushi suke akai2 .. Mahmud yace to ni ina mota idan kun gama kurmaci se ka zo muta fi.. Yana fita Mark ya matsa kusa da ita ..yace lovely ta kinga wani okon Allah ko?Alhamdulillah ashe addu'ar mi bata fadin ba ..shiru tayi ..yace baza ki mun magana ba ..se lokacin ta dan saki..nan fa hira ta barke har sun manta da wani Mahmud bare su tuna da ba a daura auren su ba ..hirar masoya kawai suke sharba.. Har goma da wani abu shima seda Mahmud yayi mishi magana ne kamar kar su rabu haka suke ji .. Ai tana shiga ta dannawa su Maysam kira dan murna tama manta da Maysam matar aurece.... Ai kuwa hada musu call su ukku tayi ta shiga basu labarin abunda ya faru...sun tayata murna badan dare yayi ba sun zo gidan kam.. Ai tunda ga nan kullum a gidan yake kusan wuni a cewar shi yana zuwa gaida su Umma ne .... Biki ya kan kama ..duk wani event da akeyi Murad be hana Maysam dan yasan irin shakuwar dake tsakanin su ..sede yana cewa ta rage aiki dayawa ... To Alhamdullilah ranar daurin auren dunbun nan jama'a ne suka sheda aure Ma'arud elh Ma'azu. Da Mariam elh Moctar ...murna wajen ma'auranta ba'a ma magana ..da dare akayi paty na gani na fada wanda Murad shi ya dau nauyin komi ..an ci ansha ....tun a daren aka sada amariya da gidan mijinta.. Abun mamaki ita irin kukan nan batayi ba ..su Maysam se shakiyanci suke mata .. Mahmud ,Murad da wasu couz dinshi biyu ne suka tako shi ..ya yinda su ukku kade a dakin wato tripleM se wasu yan uwanta biyu ... Barkwanci sukayi tare da yi musu addu'oi samun zaman lfy ..sanan shi Murad yaja matarshi ..shima Mahmud ze sauke Mufeeda agida...se sauran kuwa couz dinshi zasu sauke su.. Bayan tafyar su ne su ka nan tattaba hira har take tambayar shi taya sunan shi ya koma Mark ne ..yar dariya yayi yace yaude ba ranar wanna tambayar bace ...yanzu ki tashi ki doro alwala wata rana insha Allah zan baki labari... Raka'a biyu sukayi kamar yanda sunna tazo dashi .tare dayi musu addu'oi.ya ciyar da ita kaji da fresh milk din da ya shigo da su.... Daga nan kuma suka fara kokarin fara pratical ...sum2 na fice a dakin tare da ragowar kajin😋😋... Washe gari kam Maysam da rigima ta tashi dan dama a al'adar garin amariya bata girki wani daga dangin mijita koma daga dagin amariyar ko kuma kawar ka zatyi maka girki har na tsayon sati dan haka Maysam tace ita tayi alkawarin yi musu su duka in aurensu ya tashi... Shide lallabata yake ita da ko tuwon gidanta wuya take sha bare tayi na wani ..dan bata cin abinci kuyangi in ba doleba acewarta ta fiso ta girkawa mijinta da kanta.. Suna haka ya daga waya ya kira Mark yace ya bawa Mariam zeyi magana da ita ..nan ya sanar mata rigimar Maysam ..kawai setace bata wayar .. Tana tura baki ta amsa ...sama2 suka gaisa dan bata son tace mata a'a.. Cike da lallashi da lallaba tace haba triple M so kike ki wahalar da babyn mune ..ke bakiga kin yi nauyi bane ..pls and pls kiyi hakuri ni na yafe kada kidamu..da kyar ta shawo kanta...nan suka dan tattaba hira suka kayi sallama Ba jimawa sega kiran Mufeeda ma ya shigo bayan sun gaisa itama tayi mata rigakafin ta yafe in nata yazo base tayi mataba.. Hka de rayuwa tayi ta juya musu inda har yau akayi auren su Mufeeda da Mahmud suma ..gajiya de Maysam ta tara ta .. Dan yar bidi'ar nan ta event seda akayi dan kala kusan hudu akayi wanda duka Murad ya dau nauyin su.... A ranar da aka kaita shima kuwa Mahumd be dagawa Mufeeda kafa ba ..masha duk sun kai budurcin su gidan mijin su sede mu musu fatan kazantar daki.... Bayan sati Murad suka fara shirye2 sun na dawowa...ana gobe zasu tafi suka shirya wa kansu nan karamin paty su ukku kowa da matarshi .. Anan ne ma su Maysam suka nemi sanin taya wai daga sunan Ma'aruf ya dawo Mark.. Ai kuwa su Murad suka shiga kwasar dariya tun kafin su basu labari yayin da Mark ya cika yayi fam ..yana fadin wly kada su sake su sanar musu ..aman sukayi kunnen shegu da shi..Mahmud yace *SANADIN ACCIDENT* ne ya samu sanan nan.. Murad ya fara basu labarin cewa lokacin suna england ne ..ranar da aka rantsar dasu cewa sun zama cikakkun doctorori ..bayan munyi patyn murnar mune .dare yayi sosai ..kowa ya kama haramar zuwa gida to daman shi lokacin be wani kware da motaba kawai ya yanka kan titi se ga wani guy yayi shaye2n shi ya bugu se langi yake a titi ..abunka ga dan koyo ..yayi ta mishi horn aman ko motsi ..ai kuwa Ma'aruf ya kade saurayi..dayake gaba da baya ne muke tafiyar kasancewar unguwa guda muke ...da sauri muka fito muka shigar da yaron motarmu lokacin bayama numpashi..muna zuwa aka shiga dashi emergency room ..aka bashi temakon gaggawa aman har lokacin be farka ba kuma gashi komi is normal ..lokacin da muka diba card din saurayi se mukaga sunan shi MARK tofa seda muka shafe two days aman be farka ba. .nan Muka shiga damuwa matuka ..bare ma shi Ma'aruf duk gani yake baze farka ba..se ya zamanto bashida aiki se kiran sunan Mark ko kuma ya tisa shi gaba yana fadin pls Mark kada ka mutu ka farfardo ..kai abun har cikin baccishi zakaji yana sambatun pls Mark kada ka mutu ,..wayoo Allah na kaji k'aina ka tashi kafadar Mark .. Ina zan saka rayuwa na in ka mutu Mark ..ace ni na kashe mutum.... Tun abun yana damun mu har ya dawo bamu dariya dan yanda yake yi ne se wanda ya gani... Ranar da ya farfado kuwa har da rawa yayi wai Mark be mutu ba ... Kamar da wasa se Mahmud yace wanna ai kaine ma Mark din ... To fa tunshi ne muke kiransa da sunan Mark din.. Gaba daya suka sa dariya har shi Ma'aruf din ..nan suka shiga tonawa kansu asiri bama kamar Murad ba daya kusan Mutuwa akan sweetbaby ba...da sabbatun da yayi tayi... Haka suka wuni ranar cike da farin ciki...da raha Washe gari su Maysam suka dawo Zinder cike da kewar junan su... Naso yafi haka aman am buzy ne ..littafin yama zo karshe ..ku kara hakuri akan na da.. Ina yinku irin totaly din nan🤝😍 Fassouma ce🖊(yar mutan zinder) [20/08 à 00:39] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Don't forget azumin Arfa na gobe Monday. In sha Allah...yanada falala me yawa dan* ```Manzon Allah (SAW) yana cewa; Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta) @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335. ``` *Allah .. ya sa muyi a dede ya kuma karbi ibadun mu Ameen(yar karmar tunatarwa ce)* *Allah ne masani.* Dedicated to all my fans😍❤ 🅿105__106 ```Manzon Allah (SAW) yace ''d'abi'u biyu basu taruwa ga mumuni:rowa da mummunar d'abi'a. Bukhari ya rawaito shi.``` [20/08/18 à 00:00] Tunda suka dawo suke sharba soyyayar su ..kuma har yau neman zoben take aman tama kasa tunano inda ta ajeshi .....cikinta kuwa har ya shiga wata na shida ..yayi girma sosai kowa yana mugun tausaya mata musamma ma Murad.... Bayan sati da dawowar su suna palon ta wani yi lamo a cinyarshi tace ''My only one ..nayi maka wata tambaya mana... Yana wani lumshe ido yace umm..dan hannayenta ba wuri daya suke ba A ranta tace mulki ya motsa kenan ...a fili kuma se tace miyasa baka son ayi celebreted din birtday dinka ne. Da kamar bazece komi ba se kuma yace saboda a ranar wani birtday dina dana sweetbabyna dan ranar birtday din mu daya ne kuma a ranar ne na rasa sweetbabyna ..SANADIN ACCIDENT din da mukayi.yana fadin haka yayi shiru dan tuni ya tuno da abubuwan da suka faru ranar . Maysam tace am so sorry aman pls wannan karon ka bari muyi celebreted..ka gafa saura two month ..se mufara shirye2 tun yanzo ko... Yace um baza ayi ba . fa. Tace why .. Saboda sweetbabyna .. Zata sake wata maganar Ya kuwa dankara mata wata zunkudediyar tsawa yace to baza ayi ba ....yana yi kamar ze doke ta ne.. Ai kuwa Maysam ta saki wani kuka me cin rai ...dan ta tsorata dashi Rumtse idon shi yayi dan har cikin zuciyarshi yake jin zafin kukan ..yana kokarin lallashin ta dan baze iya jurewa ba .. Ai kuwa kan ya ankare har bar mishi wurin ....room ta shige ta fada gado tare da sakin wani sabon kukan. ... Yana ganin ta harta shige .ya SALAM ya furta se kuma ya .rufe ido tare da dafe setin zuciyar shi yana fadin na fasayi saboda rabin zuciya na ..ga kuma dayan rabin yana so nayi ..nikam ya zanyi da rayuwata ne..se kuma yace am sorry my sweetbaby badan nayi fifiko ba sedan cikin dake jikinta ne kawai zan amince.....shikade yake ta hirar shi se kace tana gabanshi Can de ya tashi ya shiga daki ganin har lokacin bata yi shiru ba yasa da sauri ya isa ya dagota ..se yaji wani tausayinta ya kamashi. .ga cikinta . a memakon ya kwantar mata da hankali aman ace shi da kanshi ne yake tada mata shi kuma amatsayi sa na docto.. Rumgumeta yayi tsam a jikin shi yana fadin am sorry wify i don't mean to hurt you....... Maysam tace dama ni nasan ba wani sona kakeyi ba k.... Da sauri ya hade bakinsu yana girgiza mata kai yace kidena zancen nan pls ..ke kanki shedace akan irin sanda nake miki ..ko ban fada miki ba gangar jikina kadai ya isa ki gane da haka ...ke ta musaman ce a rayuwata .....shikenan yace bade birtday bane..yana share mata hawaye ? Ta daga kai.. To ki kwantar da hankalinki za'ayi shi .....kuma yanda kike son haka za'ayi shi ..... Ai bata san lokacin data rugumeshi ba tana zuba mishi godiya ..harda tamishi kiss a kumatu tace ''tu es le meilleur mari dans ce monde (you are the best husband in this world)...je t'aime à la folie... Lakuce mata hanci yayi yace rigima ta kare kenan.....in sonki my beauty ,so na hakika ..kin kasance lantarki farin wata dake haskaka rawuya wata ...dan soyayyarki a hankali take shiga cikin zuciyata ..kin dasa gadargar kujerar mulkin ki a zuciya ta .....ki tausaya mun kada ki gujeni ..kamar yanda sweetbaby ta g..... Da sauri ta rufe mishi baki tace kada kayi sabo .ba ita ta guje ka ba.Allah da ya halliceta yafimu santa.......kayi hakuri da kaddara Nan de sukayi ta kwantarwa da juna hankali ..... 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Bari mu leko Inna Murza.. Ita kam tun lokacin da taga Maysam da cikin nan hankalin ta ya dada tashi ..tana ganin Maysam zata kara samun wurin zama fa..dan haka ta kwallafa ran son ta zubar mata da cikin ko ta halin qaqa...shiyasa ma ta tare abangaren Fulani dan ta samu tasan irin shige da ficen Maysam din kuma .kusan kullum tana harin cikin sede bata samun nasara ..har yau Da Allah yayi Maysam ta fito daga bangaren M.Musa zata na fulani ..har ta fito hararabar gidan sega Murza da dan kofinta a hannu na jike2nta. ..ta bawa Maysam wai tasha tunda taga cikin ya tsufa ai ya kamata ace yanzu ta fara shan maganin itatawa dan haiwa tazo mata da sauki.kamar su sabulun salo ,etc.to itama haka in ka gani zaka zata shine ashe ta zuba wani maganin na zubar daciki a ciki ya narke .. Da farko har taki amsa aman Murza se ta fara fadin dama nasan baki yarda dani ba ki amince mun babu komi ciki.. Kuyangita de suna dan gefe da su basu san mima suke cewa ba.. Amsa tayi ta kurbi kadan sau biyu sanan tace ya isheta. Tace ngd Inna Murza ganin inta nuna damuwanta zata iya ganota yasa ta barta ..tace ba komi ai yiwa kaine a ranta kuwa fadi take zaki mun godiya me degree ....shegiya me kama da aljanu ai ayanda naga sun kwallafa rai acikin nan nasan daya zube zasu koro ki ...kizo na ci gaba daga inda na tsaya(Hum adeyi a sannu) Maysam tayi mata sallama ta fice ....Murza se wani washe baki take.. A bangaren fulani ma fira suka sha sosai har na kusan awa guda..... Har ta tashi da niyya tafiya cikinta ya fara murda mata ... Fulani tace ta zauna har ya fice ai hakane daman babyn ne ke juyawa.... Aman mi ciwon kamar karashi ake tace wayoo Momy cikina zan mutu ..ai kafin ta bata wani temako tuni jini ya balle ..Allah ya temaka sega Murad ya shigo beyi wata2 ba ya ciccibeta se likitar masarauta ... Emercency aka sata ..idanun shi sunyi wani ja ..yaso dhiga aman suka hanashi dan ayanda ya firgitar nan baze iya bata wani temako ba dan irin jinin da ke zuba da kyar ne in abun cikin ze rayu .... .. ... Fulani ma duk tausayi danta dan dauther ta ya kamata ganin irin kinin data zubda ga kuma yanda Murad ya rikice lokaci guda ..ta ce ya Allah ya tashi kafadun ita da abunda ke cikinta.. Ameen Seda suka shafe awa guda..sannan doctorin suka fiyo fuskarsu ba annuri... Da sauri ya isa yana fadin how is she ...,da fatan babu abunda ya samu cikin.... Shi yama manta da shi wani yarima dan sarkine bare.. ya tuna da bayi da dogarai a wurin....shide ta yaji lfy su yake Doctor yace follow me in my office ....da sauri suka bi bayanshi .lokacin Mahmud ma ya iso shima . Bayan sun zauna cike da girmamawa yace am sorry t.. Buga table din Murad hayi da karfi yace you are sorry for what?se wani huci yake kamar ze daki doctor din.. Mahmud ya dafashi yace calm down mana controle your self .kaji meze fada.. Ajiya zuciya doctor din yayi yace dama ta zubar da jini da yawa ne dan haka muna bukatar jini dan babu a blood lab .. .. Murad yayi sauri katseshi da fadin bayan karin jinin da akwai wata matsala ne ..i mean cikin be tabu ba.. Ee Alhamdullillah cikin yana nan be zube ba Se lokacin ya sauke ajiyar zuciya yace a dibi nawa ai group din mu daya ne .... Seda suka gwada dan tabbatar da hakan sanan aka diba aka samata ..result din wani test da doctor din yayi yace su murad suzo office.. Yana kallon Murad yace taya ka bari hakan ta kasance agidanka a matsayinka na doctor.. Ya mutsa fuska yayi yace ka fadi abunda zaka fada mana .. A hankali yace to matarka tasha magani zubar da ciki ne shi ya jawo kusan zubewar cikin sede Allah ya temaka bashida yawa wanda tasha shiyasama cikin be sami nasaran zubewa ba...aman akiyayi gaba .. Wani gumi ya keto mishi ba shiri .yace what ?how dare you?.amsar result din yayi ya karanta yage haka ne.. Wani huci ya shigayi kamar wata kububuwa ya fito daga office din yanda kasan ana hankanashi haka yake tafiya direct dakin da aka kwantar da Maysam ya shiga... _Kuyi manage da wannan ..wly dande nayi alkawari ne nayi wanan .dan kyan alkawari cikawa...am buzy kwana biyu nan ....aman zanyi kokari ganin na gamashi da wuri.a kwanakin nan...tkx for all support da kuke bani dakuma hakurinku tare da uzurin da kuke mun..Allah ya bar kauna da zumunci_ ❤ameen Love you all irin sosai din nan😎😍😘 Fasma ce🖊(Fassouma yar mutan Zinder) [23/08 à 00:18] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 ~Goron barka da sallah~ *Happy Sallah to all Muslim Allah ya memeta mana..yasa munyi a dede ..barkan mu da* *sallah . ina yinku iri more totaly din nan* ❤😍😍..... *ina jiran barka da sallah na da kuma soyena na fa* 😉😉🤝 Dedicated to all my fans😍❤ 🅿 107__108 ```Manzon Allah (SAW) yace''dukkanin ayyukan alheri sadaka ne . Bukhari ya rawaito shi.``` [22/08/18 à 23:30] Yana zuwa ya banka kofar se huci yake ....lokacin ta tashi tana zaune kadan2 tke meda numpashi ..duk ta wani jeme abun lokaci guda.. Ya na shigiwa direct wurinta yayi Beyi wata2 ba ya falleta da marin da seda taga star .....ze kara mata Fulani ta rike hannunshi cike da bacin rai tace koda wasa kada ka sake ... what happen to you?ka barta taji da abunda ke damunta se kawai ka shiga dukanta ..alhali kuma da tsohon cikin nan Momy baki san yarin yar nan mi tayi bane shiyasa kike fadin haka.. Fulani tace koma de miye ai se kabi a sannu ..ina gaya maka kullum ka dinga sawa zuciyar nan taka ruwan sanhi ..fa Haba Momy yarinyar nan fa cikin fa taso zubarwa dan tsabar reni tasha maganin zubar da ciki dan ta barar dashi Allah ne kawai be bata sa'ar yin hakan ba..yana fadi yna maka ma Maysam harara .. Itakam kanta a sadde yake tana zubar da hawayen...ba ta dago ba har lokacin dataji irin kazafin da yayi mata.. Da sauri ta dago kanta zatayi magana ya daga mata hannu yace kada ki ma fara bana son jin muryarki ma ....nine ma dana yarda dake bayan tun farko daman kin nuna rashin son cikin .. Pls yaya .ka . wata tsawa ya daka mata har seda ta firgita ..yayi kanta ze daketa.. Shima se jin Momy yayi ta daka mishi tsawar for the first time ....tace kada ka sake ka daketa ..marar tausayi da tsohon cikin nan zaka daketa dan bakada tausayi Da mamaki yake kallonta idon nan yayi jajur ya sadda kallonshi yace Momy ni kikewa tsawa saboda wata can... Momy ma cike da takaici tace Maysam ba wata can bace ...y'a ce kamar kowa ..tamana hallaci kuma matarka ce dan haka fita a dakin nan kafin nayi loosing din control dina.. Tsananin mamaki ya kara lullube shi yace Momy ni kike cewa na fita... Momy tace to da wani ne bayan kai .. Nuna Maysam yayi yace zaki gani ne..ya fice har ya kai kofar fita Fulani tace babu abunda zata gani se alheri..sannan ina baka shawarar kada ka zartar da hukunci cikin fushi .. Fuu ya fita ..se lokacin Mahmud ya shigo ..har kasa ya duka ya gaisar da Fulani tare da tambayar yame jiki ..se kuma ya shiga bata hakuri kan abunda Murad din yayi yanzu dan yana kofa yaji komi ..yace ayi mishi afuwa ran shine ya bace.. Itade Momy tana saurarenshi har ya gama ...tana kuma yaba hankali irin na Mahmud tare da jin dadin kasance warshi aboki ga danta.. Fulani tace yayi mata bayani .abunda ke faruwa.. .nan ya gayamata yanda sukayi da doctor ...itama bata ji dadi ba aman ba ta tsammani Maysam zata iya aikata haka ..kai ko in hakan ne ma to dawani abu akasa.. Maysam kam kara volume din kukanta tayi tana fadin walahi Momy ki yarda dani ban sha maganin komi ba.... Ajiyar zuciya Fulanin tayi tace ya isa haka to ..na yarda dake my dauther sannan kiyi hakuri kan abunda yayi miki.kinji ranshi ne ya bace . aman komi ze zama nml ..kada ki tada hankali ki mijinki yana da saurin yin fushi kuma saukarshi ma ta kankanin lokaci ne ..ki kyaleshi yanzu har ya sauko..shida kanshi zakiga ya dawo Rumgume Momy tayi tana sauke ajiyar zuciya ..tace walahi Momy ina son cikin nan. ..taya uwa zata iya kashe danta .. Nan de Momy tayi ta lallaba ta .. Momy a ranta kuwa tausayin Maysam take ..gata so young aman da kaifi tunani ..shiyasa take jinta sosai a jikinta dan tana sonta .. To inbama rashin hakuri na Murad ba ai komi tayi se kamata hakuri da izuri ka kumsawa yarinya ciki kuma harda duka ..to dami zataji ..ne.. Allah de ya kyauta... A ranar ma akayi decharge din su direct dakinta na bangaren Fulani ta koma dan acewarta mutumin da bayason jin muryarka ma to ai in ya ganga abun se yafi haka ..dan haka ta kudurta zata bashi space kamar yanda ya bukata ..kuma bazata kara nemanshi ba inde har bashine yazo da kanshi ba......ta sani ya kwallafa rai akan cikin nan to aman ai ya dace yayi bincike kafin ya yanke hukunci . ita aganin ta koshi ai be kaita san cikin nan ba ..dan babu wanda ya kai uwa son danta se mahalici mu ..to wai ma tayaya ze ce wai ita tasha magani zubar da ciki ..wata zuciyar tace ai dan kin nuna tun farko bakyaso ..badan haka ba ai da baze zarge ki ba..haka de tayi ta tunanin ta.. A bangarenshi kuwa se bayan yayi abun yayi nadama ..ai ko ba komi wifyn shi ce ..ya kamata yayi mata uzuri sannan ya lallabe ta ko zata gaya mishi miyasa ta aikata hakan ..se kuma wata zuciyar tace batada wani hujja .kawai dan ta bata maka rai ne..... Se kuma dayar zuciyar tace to ai rabin zuciyarka ce kaga yanzu kasakata kuka may be ma tana can tana yinshi . ..ai da sauri ya juya ze koma se kuma ya tuna maganar Momy cike da sanyi jiki ya koma cikin masarautar.. 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 A bangaren Murza kam ba karamar murna tayi ba da taga anyi likita da Maysam dan tana labe daman .Allah2 take taji labarin barewar cikin aman setaji akasin hakan..ranta yayi mugun baci aman kuma data ga yanda Murad din ranshi ya bace se ta danji dadi2 acewarta kafin su shirya zata hada wani target din ta zubar dashi gaba daya ..inya so se ya koro ta....tun nan ta shiga tsara yanda zatayi. . Dan munafinci so biyu tana zuwa duba Maysam da tana likitar kuma tunda aka sako su kullum.setaje . 🌹🌹🌹. 🌹🌹 Malam Musa kam da me martaba basu san wainar da ake toyawa ba ande cemusu bata ji dadi bane..kjma sun mata ya jiki ... Bayan sati da faruwar hakan Murad yaji baze iya jure rashin Maysam kusa da shi ba....duk ya fara dan ramewa dan bawani abinci kirki yake ciba dan ya saba da nata se yake jin wannan din bashida tast...dukda kuyangi na gyara mishi bangaren aman ba kamar yanda wifyn shi keyi ba .. dan kuwa ko tsohon cikin ta baya hanata gyara bangaren tsaf ..shi kanshi ya san yayi dace da sa'ar mata ...dan haka yau tun safe wurin Fulani yaje .yayi ta bata hakuri kan sharin shedan ne hakan bazata sake faruwa ba ..sannan ya bukaci data bashi matarshi.. Fulani tayi murmushi ..tace har ka gama fushin damu kenan ....to nide bakayi mun komi ba kaje ka bawa matarka hakuri sanan intace zata koma dakinta to ni mi nawa a ciki ..kajede ka lallasheta kawai..nan tayi mishi yar nasihohi Cike da kwarin guiwa ya nufi part din ..lokacin tana tolet ..zama a bakin gadon yayi yana jiranta .. Tana fitowa taganshi ai kafin yayi wani yunkuri ta koma ta datse kofar ....nan ya shiga kiranta ta bude mishi aman yanda kasan bada ita yake ba..haka ya gaji ya fita.. Murad be san abun nayi ne ba seda yaga ya shafe wata guda harda kwana ishirin Maysam taki kulashi kai rabon daya ganta ma har ya manta dan bata fitowa. Se yabar bangaren ..har karar ta yakai wajen sarki ..wata rana da dare suna hirar su shida fulani kamar kullum ya shigo bayan ya kwashi gaisuwa ne ...yake gayawa sarki shi fa ya a meda mishi matarshi .. Sarki ya kalli fulani da alamar tambaya ..wayen cewatayi da fadin mistake ne suka samu a tsakanin su ita kuma tayi fushi ta dawo bangarena ..ta kalleshi tace ko ni na rike maka mata ne.. Ya sadda kai tare da girgizawa.. Murmushi sarki yayi irin nasu na manya yace to kai son kawai kaje ka lallabeta mana..kasan su mata seda da lallaba Yace Dady nayi fa taki hakura kawai kasa baki ta koma.. Sarki yace bazan tirsasata ba itama ya ce kuma bansan mi ya hadaku ba ..kuma ma ai ba'a gajiya da lallaba mace ..kaci gaba da rarrashin ta zata sauko bare ma su mata akwai su da tausayi da raunin zuciua....yayi kasa da murya yanda Fulani bazata jiyo ba yace bari na gaya maka wani secret irin na mu na maza yanda zaka shawo kanta cikin sauki .. Kasa2 sosai yake mishi maganar wanda ni kaina banjiyo ba . nade ga Murad na wani sunne kai irin na inkaji kunyar nan ..yana kuma murmushi kasa2.. Fulani kam kallosu kawaitake cike da birgewa .. Yana gama fada mishi ya mike ya fice har ya kai kofar futa Sarki yace kada kaji komi zanji da tanan din ..wuf ya fita a palon dan yau dadyn nashi ba karamar mamaki ya bashi ba ..daman tsofi ma sun iya soyyaya haka..(ni kuwa nace zauna de nan ai fulani da sarki se a hankali dan ko kallon juna suke zaka iya hango tsantsar kaunar da sukewa juna..😝..).. Direct bangaren fulani ya fice ...lokacin Maysam zat shiga dakinta .. Be bari ta ganshi ba ..tana shiga direct tolet tayi ..shima kuma wuf ya shigo dakin ..ya saka key ya kulle....dede kofar tolet din ya labe bayan labule dan kada ta ganshi ta koma..... Tana fitowa ya shaki kamshin turarenshi ....har wani lumshe ido tayi dan tayi bala'i missing din turaren ...batayi zato ba taji an rumgumeta ta baya ...ta kuwa bate baki zata yi ihu da sauri ya rufe mata baki tare da fadin nine mijinki .. Ai kuwa ta shiga kiciniuar kwace kanta. ... Ganin haka yasa ya sake ta dan kada taji ciwo...tana kallon shi kallonirin na mi kake yi mun a daki ... Kalar tausayi yayi yace. To nima de nace Happy sallah my fans.. Love you all❤❤😍 Barka da sallah .. Bonne fete de tabaski a tous❤❤😍 Fassouma ce🖊(yar mutan zinder) [06/09 à 05:21] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Ina me bawa masoyan wannan littafin hakuri na rashin jina da kukayi hakan da farune sakamakon exam da aayi satin daya huce ..am so sorry na rashin jina kwana biyun nan shiyasa ma zan cire labarin na rage shi dan nayi na gama dan koni kaina bana jin dadin yanda bana typing kullum.....* *Wanda suka yi kirana da wanda suka mun text na gode Allah ya qara dankon zumunci .. Wanda kuma bansamu damar dauka ba ina me baku hakuri kun sani ina yin ku irin more totaly din* *nan* 😍😍😘❤❤ *Yan kungiyar mu ina alfahari da ku ina godiya da irin karfin guiwar da kuke bani Allah ya qara hada kanmu .ina yinku gaba da baya* ❤😍😘 _I miss you a lot my in law Xaynap queen keda my Arfat da kuma Momun Mufeedah Allah yasa kuna cikin koshin lafiya.._ Dedicated to all my fans😍❤ _special my zee'' Xaynab Idris ''ba shaharariya marubuciya ..kada ku bari abaku labarin littafinta dan akwai fadakarwa tare da annashuwa da ilimantarwa (kuneme shi me sunan RAYUWAR FADILA)Allah ya barmin ke_ 😘😍❤ 🅿109__110 ```Manzon Allah (SAW) ya ce''za a tayar da mutum akan abinda ya mutu a kai(gobe kiyama)'' Muslim ne ya rawaito shi``` [06/09/18 à 00:10] Kalar tausayi yayi yace haba my lovely wife ..am.so sorry nasan banyi dedeba aman hakan bazata kara faruwa ba..ni kaina bansa don mi nayi miki haka ..aman ga fuska ta ki rama marinki ko zaki huce dan na gaji da fushin nan .. ..yi tayi da daya duniya bada ita yake ba ..dan ko kallonshi bata kumayi ba ..se ma ya yan wake2n ta ma take ... Kara matsowa yayi kusan ta ya rike mata hannu kamar zeyi mata kuka yace kiji tausayi na ciwona na gab da tashi . .ya aza hannunta bisa zuciyarshi yace ji kiji yanda take bugawa ..pls ki mun ko magana ne ko naji sassauci akan abunda nakeji ..kin sani zuciyata bazata juri rashinki ba...nayi nadama kuma lokacin idona ya rufe ne ... Se lokacin ta dan kallo shi ..aman batayi magana ba ..setaga har ya rame kamar yanda ta rame itama ..gaba daya tausayinshi ya mamaye ta .,.jitake kamar ta rungumeshi aman se taga kamar tayi saukin saukowa ..baride ta nan kara garashi dan ko gobe kada ya kuma yi mata haka Dan haka bata ce komi ba ta bi lafiyar gado ma.... Yajima nan yana bata hakuri sanan ya tashi ze fice ganin ko kalloshi ta dena yi.... Dafe zuciyar yayi dan wani irin zut4 take mishi😝 ....har wani layi yakeyi kamar wanda yasa wani abu dan dishi2 ma yake gani..... Yana gab ta fita yaji Maysam ta rumgumeshi ta baya A tare suka sauke ajiyar zuciya ...Rikeshi tayi tsaf kamar wanda akace za'a kwace mata shi .... Da kyar ya jiyo da ita face dinshi ..sun kusan minti biyar suna kallon juna kowa yana kokarin aikawa da dan uwanshi sako ta kwayar ido.. Can Murad ya bude baki zeyi magana da sauri ta sa hannunta ta rufe mishi bakin tace ya isa haka ..nima am sorry da yanda na shareka ..ta kai hannuta wuyanshi tace duba min wanan rama da kayi kamar wanda baka cin abinci .... Dan murmushi yayi yace to ai kece abincin nawa..ganin ki kade ma kosar dani yake ... Idan ina tare dake bana bukatar wani abinci dan na rayu..na saka ki kade ma a gaba ina kallon ya isheni ........kamota yayi suka zauna bakin bed ya dorata cinyarshi ko nauyinta ma bejiba.....yace '' je t'aime a la folie ma princesse d'amour...ma bouche ne peut pas dire a quel point je t'aime ni mon corps ne peut pas l'exprimer .ni mon cerveau et mon coeur ne peuvent pas compter a quel point tu compte pour moi...tout ce que je sais est que je ne peux pas vivre sans toi ..sans toi ma vie n'est rien ...'' My repiration ''je ne vis que pour toi ..si tu me quitte un jour ca sera le jour de mort j'en suis sure ma douce dulcinée '' Ya kamo hannuta ya dora a setin zuciyar shi yace dama rabi ce to ina me tabbatar miki duk ranar da kika barni to nima a ranar za'a dauki gawata. .....''sache bien que ma vie ne depend que de toi.....je place ma vie entre tes mains..je compte sur toi pour ne pas la perdre... Maysam kam tunda ya fara magana taji kanta ya kara girma ..gaba daya se taji kamar tafi kowa yin sa'ar miji a rayuwa ....idanunta banda hawaye dadi babu abunda suke ..duk setaji babu ya ita a duniarnan ....zuciyarta wasai takeji Tace Mon bb cheri.ina kataba jin mutumin da yayi wasa da rayuwar shi ne ..idande har zan rasaka to kamar na rasa rayuwa tane .. ..ko mutuwa ina addu'ar idan tazo ta fara daukana dan nasan inde har kai ta fara dauka to kuwa ina me tabbatar maka da nima a ranar zan bika dan rayuwata batada wani anfani inde har baka cikin ta..son dan kemaka ya fice amisalta shi ''tu es ma raison de vivre''i love you more mijina Da sauri ya rufe mata baki yace haba kibar zancan mutuwa in har muna tare dake..ya zaki kirawo mana ita Dan murmushi tayi tace haba ''Autan maza '' ai ita mutuwa tana wuyan. ..kamata yayi duk wani musulmi munmuni ya dinga tunawa da ita akai2 akoda yaushe dan ita dole ce komin dadewa .. nan fa suka shiga zuba wa juna kalaman soyyaya wanda ya karasa Murad jin shima fa wani ne ...bama da inta kirashi da 'Autan maza ba ..(😝ko ba haka ba my kawali rams😜. )Se yaji kanshi yayi wani kara girma ..nan suka lalace da kalanmansu...daga nan kuma ogan niya ta shiga mishi kalon nata pratical din da ta kara koyo ko tulelen cikinta be hanata yiba ..nace tab yarinyar nan tayi nisa bata jin kira . daman an jima ba'a jiba .kun sani ai nan naja musu kofar .kawai nayi gaba abuna. Washe gari cike da farin ciki da annashuwa suka tashi .. Har tara na safe sunan nan dakin sun kasa fitowa gaba daya ya dabaibaye ta kuma gashi ya kulle kofar...seda ta fara mishi kukan shagwaba kan ita yunwa take ji sannan ya sarara mata yace to mikike son ci yanzu na saka akawo miki shi. .. Turo baki tayi cike da sangarta tace ni farfesun kayan cike nake son ci kuma kai nake so ka girka min .. Wani waro ido yayi yace ni kuma. Yana nuna kanshi. .. Noding din kanta tayi ta kuwa shagwabe fuska kiris take jira ta saki kuka.. Zama yayi ya dorata cinyarshi yace wify kin gane ni ko kunna gaz ma ban iya ba bare aje ga zancen farfesu ... Ai kuwa bata bari ma ya gama ba ta bare baki ta shiga rera bishi kuka wanda daga ji kasan na jin dadin rayuwane..kawai Shi kuwa ya lalace wurin lallashi . da kyar ya shawo kanta tare da cewa to sutafi can bangaren su se ya shiga kitchen din ya dafa mata yanzu nan yana shiga ze zama abun fadin cewa ga yarima me jiran gado can yana dafa abinci da kanshi . kinga kuma da bayi birjik zasu renani ne.. Hawayen ta goge tace shikenan to mutafi dan yau girkinka nakeson ci .... Suna fitowa suka tarar da fulani a nan falon tana kallon tv...da dan sauri Maysam ta nufeta ..Murad kuwa se fadi yake kibi a hankali fa... Har kasa ta duka dan gaishe da fulani da kyar ma ta dukan. Fulani bayan ta amsa tace mata way ni Maysam bakya tausayin kanki ne kina cikin watan ki fa na takwas inake ina dukawa mafarin ki kasa tashi kisa mijinki ya daureni dan naga akan cikin nan komi ze iya yi cike da zolaya take maganar.. Gaba dayan su suka kwashe da dariya Maysam tace tab ai sede ya dauremu gaba daya dan kafarki kafata ...... Murad yana turo baki yace lovely wife mutafi mana kinga bakici komi ba kada ulcer yakamin ke da little babyna .... Tab ai kam ba karamar kunya Maysam taji ba har jitake dama kasa ta tsage ta shige ...kanta a kasa ta kyaleshi .. Ganin haka yasa yaje ya tallabota ta mike ai kan kace mi harta fice a palon tayi sid din su .. Murad kam dariya ya shiga yi mata .. Fulani tace bason haka fa kaga kasa dauther na taji kunyata ko .. .. Murad yace to ni Momy minayi kuma kawai de ... Kafin ya karasa tace jeka kada yunwar ta shige maka ita .. Da dan saurinshi kuwa ya fice yana fadin haka ne.. fa Fulani ta girgiza kai cike da farin ciki a ranta tace inde Murad ne zeyi rashin ta idon nan fiye da haka ma ..dan kuwa tun be girma haka ba bayajin kunyar kowa inde akan nuna soyyayar sweetbabyn shi ce sede kai da ake abun agabanka kaji kunyar..... Sekuma tace Allah yaji kanki '' *MUNIRA''* ya rahamceki...(🤔🤔daman sunnan Sweetbaby *MUNIRA* kenan mujede zuwa...) A kitchen ya tarar da ita se hada zufa take rumgumeta yayi ta baya yana shafa cikinta yace pls zoki zauna banason kina ba kanki wahala haka bayan Allah ya yaye miki ita ...duk abunda kike so kisaka bayi su miki .... Kashe gaz din tayi dan ta gama abunda zatayi tana kallonshi tace nasan da haka aman jifa ta shafa dede wuyan shi tace yanda ka rame gaba daya ..nasan kuma harda rashin cin abinci dan kasha fada yanzu baka iya cin abinci inde har ba na Momy bane ko nawa .. ...ka barni na maka ''hangandi''(cin abinci dan yin kiba)kafin birtday dinka dan kada aga ban iya kiyo ba cike da zolaya ta karasa maganar... Lakice mata hanci yayi yace tab ai ni kade nason iya kware warki wajen kiyo ai ko se yayi mata rada akunne wanda banjiyo mi yace mata ba yace shi kade ma ya isheni na kiyu .har na ginu.. Kirjinshi ta kaima bugun wasa tace kai ko ..ka jika da wata magana kuma ... Ze kara wata magana tace pls yaya ni yunwa nakeji sosai da sosai fa.. Sorry yace tare da daukan kullar abinci data dafa suka fito gaba da baya ta rike kugu shi kuma rike da kullar dan gaba daya ya kore kuyangin bangaren dan acewar shi babu wanda zega shigar shi kitchen yana dafa abinci. . kuma yanzu baza ma su kara shigowa in ba aikin goge na share na safe se kuma in an kira su Kallonta yake cike da tausayi yanda take tafiya yace aman wife cikin nan yayi miki kyau ba kadan ba .. Murmushi kawai tayi ..a kasa suka zauna yanaci yana kuma bata a baki .. Murad yace yauwa yama zancen birtday din nan ne ko kin fasa.. Tana kallonshi tace tana nan ya akayi ne... Yar dariya yayi yace daman parent din Sweetbaby ne zasu zo kin san tunda akayi auren mu basu zo ba kuma dady ma yaso zowarsu lokacin bikin aman yanayi ciwonta be basu damar zowa ba ...kuma wani rashin sa'a lokacin sukazo kina england shi yasa yanzu sukacece zasu zo kodan su ganki... Tunda ya fara magana taji gabanta na faduwa ..bayan ya gama tace Allah ya kawosu lfy yaushene zasu zo.. Inaga de ana gobe birtday din ....sukaci gaba dacin abincin su.. Can yace gaskiya wife Allah yayi miki ni'imomi iri daban2 ciki harda ta iya lafiyayen girki.. Tunda ya fara magana ta bata rai har ya gama... Cike da kulawa yayi kalar tausayi yace mi kuma nayi my honey.. Kicin2 tayi da fuska harda yar kwallarta ta kissa tace to ni ni .se kuma tayi shiru... Gaba daya yaji shima kwallar na famar cike mishi ido yace only one kada ki bari hawayen nan su zuba dan dede suke da sukar mashi a zuciyana...yace fadi mun miye matsalar ki .. Bata bari suka zuboba tace to bakai bane.. Cike da rudu yace ni kuma minayi .. Cike da shirme tace to ai naji baka taba kirana da sunana ba ...kullum sede ka kirkiro wani suna bayan ni kuma ina son jin sunana ya fito daga bakinka dan na banbantashi dana sauran mutane..kuma na lura dakai duk lokacin dana kiraka da babyna seka lumshe ido tana wani turo baki.. Seda ya sauke ajiyar zuciya dan da hankalinshi ya tashi yace sorry baby ..inada dalilina nakin fadin sunanki ..hakane kina da gaskiya aman ki mun hakuri dan sunan yana mun nauyi a bakina ne.. Cike da mamaki da al ajabi jin abunda ya fada tace why ?kozan iya sani ..yana kallonta da kamar baze ce komi ba se kuma ya daure ya cize yace Sunan BABYna shine lakanin da My Sweetbaby ta mun aduk lokacin da kika kirani da sunan ina jine kamar itace ta kira..kuma abunda yasa ban taba kiranki da sunanki ba because ''tu as le meme nom que my ,SWEETBABY''(you have the same nam of my sweetbaby) itama MAYSAM ake kiranta dashi ....to bani ba ko wani naji ya kira sunan se gabana ya fadi dan duk gani nake kamar ita zan gani dana ji sunan ....lokacin da Momy ta fara gaya mun sunanki seda nayi three days ina jinya da.zuciyata...ina son Sweetbaby ta kasance itace rabin zuciyana...aman am sorry idan kinji haushi..... Maysam tace am sorry nima basan haka abun yake ba da ban yi korafi akai ba...ko kadan banji haushiba se ma dadi dana ji cewa inada suna iri daya da Sweetbaby ..ina sonta nima duk da bantaba ganin taba aman ta shiga raina nima ..Allah yaji kanta...Allah kuma ya kara ma hakurin rashinta babyna.... Ko yanzu seda ya lumshe ido dayaji ta kira sunan. Ai kafin ya bude Maysam tayi kissing din idon tace ''so handsome''..ina sonka dayawa mijina... Bayan ya bude idon yana murmushin jin dadi yace i love you more MAYSAM.. tab ai jitayi gaba daya duk duniya yafi kowa iya fadin sunan har wani ruwa2 taji a sunan lokaci da ya fadi..wata irin ajiyar zuciya tayi tare da lumshe ido dan sunan ya shigeta ba kadan ba...jitayi kamar ma shi ya kirkiro sunan(ni kuwa nace kika sani ko shi din ne ma) Lakice mata hanci yayi yace to waima ke miye sunanki na gaskene dan Maysam ba suna bane fa..ke kuwa naga har cikin takardunki haka a kasa... Zatyi magana wayarshi tayi kara ganin sarki ne yasa ya daga...yana ajewa ya zame daga jikinta yace dady ne ke kirana kiran gaggawa kissing dinta yayi ya fice da dan sauri2... Ita kam tagumi tayi tana tuna magagan nun su na yanzu .... 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹a gurguje pls Abude yazo dan gobe ne birtday dinMaysam da tsohon ciki se shiga da fice ake dan ma fulani na tilasta mata hutu ..su Mufeedah da Maryam ma sun zo suna ta murnar ganin juna. ..kowacen su kuwa da dan karamin cikinta.... Awani hall na cikin masarautar za'ayi ... Bayan sallar isha'i Maysam na bangagarenta se dube2 take da alama de wani abun take nema ..can kasan wasu kaya ta hango kayanta da Malam Musa yace da su ya tsince ta.... Tana kallon kayan ta ce ko yanzu ina mahaifana suke ?mi nayi musu suka rabu dani?to ko da gaske ni shegiyar ce kamar yanda inna Murza ke fadi ?..tana daga kayan Zoben nan ya fado ...cike da murna ta dauko ta saka a hannunta tace ashe nan na boyeka muka sha wuyar dubaka..cuwat ta mike tana fadin bari na kira babyna na sanar mishi... Wayarta a palo ta fito ta dauka ..kira na daya na biyu ya daga cikime da jin dadi suka shiga hirar su ta masoya Maysam tace wai kana ina ne kaga wani abu ? Yace gamu dawo wa daga tarben su Mom. ...to miye za'a gwada min .. Maysam tace devine quoi? Seda yayi yar dariya yace to waya cemiki ana fadin gift din dazakayi bawa mutum ai seki bari har zuwa gobe tukon ko.. Dariyar tayi tace to waya fada maka gift dinka ne zan fadama .. To in bashi bane minene? Tace yanzun nan ina duba wani abu na ga Zoben nan dana taba baka labari gashi nan ma a hannuna in fadama maka .... Wata irin faduwar gaba yaji yace gani nan zuwa yanzu in gani kada ki fidashi daga yatsarki ... Zatayi magana taga shigiwar Murza palon fuskar nan ba annuri kamar kullum .. Murza tace shigen ciki me taurin kan tsiya irin na ubanka da uwarka ..ashe kananan baka zube duk irin maganin dana baka ...to ai yau gani nan da kai na yau me rabani da kai se Allah.. Itade Maysam cike da tsoro take kallonta kuma tana jin irin maganganun da Murza keyi suka dada tada mata hankali ..Murad de yana jin magana kasa2 aman bayajin abunda ake cewa ...yana ta kira Maysam3 aman ba amsa .. Ita kuwa Maysam ganin Murza ta tunkarota ta wata wuka tana fadin yau sena kaiki lahira dake da shegen cikin nan yasa ta kwalla wani uban ihu kan kace mi tuni ta zube nan kasa sumamiya (nasande baku matan da yanda Maysam ke tsoron Murza ba)gashi kuma babu bayi duk Murad ya koresu Jin irin ihun da tayi yasa hankalinshi ya dada tashi gashi kuma da dan tazara kafin su iso ...ya sake kira yaji sweet off Dan haka ya kira Mahmud ya sanar mishi daya je bangarenshi ya duba mishi Maysam yayi sauri ... Dayake yana cikin masarautar dan haka da sasarfa ya fice part din.. Yana shigowa lokaci Murza ta kaiwa cinkin Maysam Halbi da kafa ta daga zata kara Mahmud yayi kukan kura ya damki kafar ya cillar da ita can....kafar me lafiya ta bugu da wani karfe kuma kanta ma ya bugu da da wani da center table a take ta sume... Tana sumewa nima nace bari nayi nan ..... Se mun hanu a next page wanda nake sa ran last page ne.......ina sonku irin dayawan nan kuma ina kara baku hakuri ...❤❤❤❤❤❤😍😍😍😍😘😘😘😘 Nice de taku har kullum Fassouma ce🖊(yar mutan Zinder) [10/09 à 00:06] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *Sakon gaisuwa dubun godiya da kuma ban girma zuwa ga yan groups din* ZURI'ARMU FANS2 MEERAH FANS GROUP UWAR RIKO FANS KALAR TAWA UWAR FANS SALMA FANS NOVEL CAT BY YA-YUSUF SURBAJO FANS HAUSA NOVELS RAYUWATA FANS NOVEL PLM TRUE LOVLY FANS GENTLE LADIES HAUSA NOVEL FATIMA (AS)HAUSA NOVEL NISA'UL KHAIR DON AMARIYAR SATIN NAN BRILLANT NOVEL FANS NOVELS LIBRARY ANSHOLLY NOVEL M.HAUSA NOVEL AYSH NOVEL HAUSA NOVEL AYAU 004HAUSA NOVEL BOOK FANS NOVELS .. 🤣🤣 *kai walahi kuna da yawa fa kuyi hakuri wanda ban ambata ba kusan kuna raina kuma ina yin ku irin more completly totaly din dan ❤😍😘😘* 😘😘 Dedicated to all my fans😍❤😍😍❤❤ 🅿111__112 ( _First of last page_ ) ```Manzon Allah (SAW) yace''marowaci ba zai shiga Aljannah ba ,haka ma mai mako.'' Al-Khatib ya rawaito shi``` . '' _Dayawa suna korafin sunan Sweetbaby to sunanta MUNIRA ....kuma Maysam yana nufin SWEET,Murad ma yanada nashi ma'anar ..zaku gane komi a last page'''..and kuma ai in kun lura kaf tunda littafi ya fara sunan mutanen_ _cikin yana farawa da 'M'' ne yake kamar su Ma'u,Murtala ,Murza,Musa etc..so ku bini zaku gane don mi na zabi sunan MUNIRA .. Thankx da tambayoyin ku_ .. _dan wanan yana mun nuni da kuna bibiyar book din_ 😍❤❤😘😘 [09/09/18 à 23:31] Mahmud kam gashi likita aman ya rasa irin temakon da ze bata ..kira yayi aka turo nurse din cikin asibitin masarautar..haka de da kyar kafin su iso ya dedeta nutsuwarshi ya shiga neman ceto ta ..ya jima kafin numfashinta ya dawo ..cikin ikon Allah kuwa tana farfadowa nurse din suna shigowa sede mi jini ya ballewa Maysam kamar mi..da sauri akayi emergency da ita kusan kaf doctororin masu fanin haihuwa wato gyneco da kuma sage femme dake asibitin suka shiga dan ceto rayuwarta... Abunka da gidan sarauta kafin ma Mahmud ya sanar da su fulani tuni labari ya isar musu Kan kace mi tuni fulani ta iso asibitin ganin Mahmud na kai komo yasa hankalinta kara tashi ..ta iso tana tambayarshi abunda ya faru..nan ya sanar mata tundaga kiran Murad har bugon da Murza tayiwa cikin. Nan ta shiga fadin inna lillahi wa inna ileyhi raji'un tare dayin salati ....se kuma ta bada oder da atafi a kama Murza a kai a kulleta kafin ta kudu ... A bangaren Murad kam hankalin shi ba karamin tashi yayi ba jin faduwar wayar Mom da suke tare itake tausarshi tana bashi baki kan babu abunda ze sameta ...gudu yasa aka kara dan duk iya hakurinshi ya kasa gashi in ya kira Mahmud din ma baya daga wa ...... Lokacin daya iso direct bangarenshi ya nufa dan yana da yakinin nan ze tarar da ita huyangi nayi mishi bayanin aman be masan abunda suke fada ba shide fatanshi ya saka wifyn shi a ido .. Ai kuwa abunda ya gani ne ya qara daga mishi hankali dan jini ne kamar wanda aka yanka kaza a tsakar falon ...ga kuma wasu kuyangi suna aikin gyaran gurin .. Nan suka zube suna gaishe shi aman ko takan gaisuwar bebi ba ya shiga tambayar su ina Maysam ...kasa magana sukayi dan suna tsoron hukuncin daze musu inyaji wanan abun ta bakin su.. Wata tsawa ya daka musu ai ba shiri daya daga cikin su ta shiga yi mishi bayani kan sude sunga an fice da ita asibitin nan kuma tana zubar da jini .. Be ma bari sun karasa ba ya fice se asibitin su Mom dake bayan shi suma suka mara mishi baya duk da ita ba wani dadin jikinta take ji ..... Tun daga nesa ya tsinkayi su Mahmud harda gudu2 ya hada dan shi yama manta da shi yarima ne bare ya tuna da wata sarauta har ya kai ga tuna da bayi a gurin .... Ganin yanayin su fulani yasa jikinshi yin sanyi ko ba 'a fada ba yasan wifyn shi ce ba lafiya..da kyar ya hada miyan bakin shi yace Momy ina Wify ta ?miya sameta ? Fulani kam ta rasa ta inda zata fara mishi bayani..se Mahmud ne yayi karfin halin rumgumeshi yana mishi nasiha kasa2 kan yayi hakuri da komi na rayuwa sanan ya sanar mishi yanda abun ya kasance ..beyi aune ba yaji lema a kumatunshi koda ya shafa yaga ashe hawayene yake Mahmud ya kalleshi yace pls kayi hakuri ai ba ancemaka ta mutu bane addu'ar ka take bukata kuka baze anfane da komi ba... Kara rumgume Mahmud yayi yace baka ji yanda zuciyana ke mun bane jinake kamar zata faso kirjini idan na rasata nima na tabbatar da binta zanyi ... Mahmud yana dan bunbuga bayanshi alamun lallashi yace ka rumgumi kaddara kamar ba musulmi ba ...haka kayi lokacin sweetbaby har ka kusa halaka kanka ..pls ka meka lamuran ka wurin Allah komi se ya zo maka cikin sauki. . ...fulani da Mom ma suka matso suna bashi baki tare da nasiha har yaji zuciyarshi ta fara dan saki bisa kulewar da tayi ... Nan kuma ya tada rigimar seya shiga ..babu muso suka barshi ya shiga ..ai kam seda yayi dana sani dan ganin irin bakar wahalar da Maysam ke sha .... Duk wuyar data ke sha tana ganinshi ta mika mishi hannu alamun yazo ..ai da gudu ya isa yasa guiyoyin shi kasa tare da rike mata hannu ...idon nan nashi yayi jajur alamun yasha kuka kenan ....ita ma ido duk su firfito se zufa take...tana jujuya kai kukan ma yaki zoma ta .... Likitoci kam kallon ikon Allah suke ..shi yazo ya hanasu aiki kuma shima bayi yake ba da kyar suka lallabashi ya fita a cewarshi ze doko rigarshi ta likitoci dan baze iya barin wify shi itakade ba... Yana fitowa ya shige office ya doko rigar..ze koma Mahmud da fulani na bashi hakuri kan yabari sauran docto suyi aikin su aman fafur yaki suna haka se kuwa ga Sarki ,M.Musa da kuma Dad suna shigowa asibitin suma .. Nan yaje ya rumgume sarki har da yar kallarshi kan wai su fulani sun hanashi shiga.... kallo daya sarkin yayi mishi ya ga baya cikin nutsuwarshi ..ko ya shiga ma ba wani abun ze iya ba dan duk ya wani gigice ..... sarki ya shiga bashi baki se suma su dad suka shiga zancen da kyar ya hakura de ya zauna zaman jira ..aman bini2 se ya lekata ... Kaf dinsu babu wanda ya samu ya rumtsa kusan dukansu bisa sallaya suka raya daren suna me rokon Allah ya Tashi kafadarta .bama kamar Murad da M.Musa .ba Kai abu kamar wasa har gabbanin asuba Maysam nacin bakar wuya ..kuma likitocin sun tabatar da nakuda take dukda EDD inta saura two week....... Wajejen hudu na asuba Murad ya saka farar rigarshi ya shiga dayake duk mata ne gyneco din yasa ya fara rena aikin su acewar shi basu san kan aikin su ba ... ....duk ta gala baita idon wanan shine. Shi kam ba karamar firgita yayi ba duk wata nutsuwarshi ya tattaro da sauri ya shiga dubata ..yaga da dan sauranta kafin ta haihun ..yanzuma..kawai yanke shawara yayi da 'a amata cs dan kada a rasasu su duka biyun dan daga ita har babyn su galabaita .......nan ya bada umarnin a kawo mishi form ya saka hannu kuma shida kanshi zeyi mata dan bayason a samu matsala..(ni kuwa nace dama kai da faninka ne ka tsaya sanya seda ta wahala haka🙄) Maysam ta dan ji ysoro aman jin shine zeyi mata yasa taji sanyi a ranta..... Su fulani ma sun tsorata bare da sukaji za'a iya rasa su duka biyun dan bata kai haihuwa ba tsokanota ne akayi kuma gashi Murad ne zeyi ba dan suna shanku be iya ba a'a sede ganin yanda ya bi ya damu ya susuce lokaci guda... Ba' a dau lokaci ba aka shiryata aka shiga dakin operation din ..shi kadene namiji a ciki duk sauran mata ne ..ko Mahmud hanashi shigowa yayi dan tsabar kishin tsiya(kai Murad a rashin lfyr ma seka nuna kishin🙄)....... Ai kam cikin ikon Allah kamar wanda take jira a shiga har an doko alurar kashe zafi ..nakudar ta taso mata kadan2 ..nan Murad ya dakatar dasu . yana dubawa yaga contractions ne Dama shine kusa da ita ai kuwa wata damka tayi mishi tare da yin nishi akai2 cikin yarda Allah sega kan baby nan har yayi rabi aman mi ita kuma a lokaci ta fara lumshe ido karfinta ya qare......... Cikin ikon Allah Cike da kwarewa Murad ya zaro shi ya doramata bisa cikin ya durkusa yayi sujudu shukur ..dede kuma lokacin aka fara asalatu dan asuba tayi..zagayo wa yayi yabata light kiss...ai kam yana dubawa yaga da namiji ne . ya so ace mace ce da yayi wa sweetbaby takwara to Amman wa ya isa yaja da ikon Allah haka namijin yayi niyyar bashi ..dan haka yashiga yin tasbihi da godiya ga Allah da sauke Maysam lafiya..lokaci guda wata mahaukaciyar kaunar yaron ta shige shi barema daya ga kamarshi daya da sweetbaby lokacin da'aka haifeta ..kaishi walahi seyace ma itace dan in ya leka ma kara lekawa yake wai kode mace ne dan shi gani yake bama kama ba ce ..a'a sweetbabyn ce ma gaba daya..nan ya shiga sakin murmushi tare da dariya kya3..bini2 se ya bata kiss itada baby ..ita abun ma kunya yake bata.. lokitocin ma sakin baki sukayi suna kallonshi .. Duk wani gyara shiyayi kayanshi daga nurse za suyi se yace ya gode su bari..doctororin kam ikon Allah suke kallon dan su kansu ba wani barin suba yayi ba sukayi aikin su ...abin mamaki baby bashida komi ma'ana yana cikin koshin lafiya duk wani test yayi mishi aman she is very fine dan ..haka ya saka aka kai Maysam dakin hutu tare dayi mata Allurai ciki harda ta bacci shi kuma ya fito da jaririn a hannunshi direct wurin su fulani ya zo yana doka murmushi suma suna ganin shi suka taryoshi ...hum irin rashin ta idon Murad ko fulani yaki ya baiwashi ...wai acewarshi sweetbabyn shi ta dawo kuma babu me amsarta bare ya rabashi da ita .... Mom tayi murmushi tace hala macece... Yana kallon yaron yace a'a namiji ne aman walahi kamar shi daya sak da sweetbaby na ..duba ki gani ..se lokacin ya bude misu shi . .ai kam a tare suka dau kabbara da tasbihi ga ubangiji dan gaskiya kamar har ta bace Murad yace walahi da macece da sweetbaby zanyiwa takwara kuma ma wani ikon Allah kinga rana guda lokaci guda aka haifosu ..dan shima wanan a kiran asalatu ya fado duniya kamar sweetbabyta itama .....gaban .Mom ne ya fadi nan zuciyarta ta kara tsanan ta bugawa har ta kasa hakura tace ka tabbata na mijine kuwa.. Yana murmushi ya bude musu suka gani ..kowa na wurin se barka suke mishi ..fulani ta tambaye ya Maysam din nan ya sanar musu tana dakin hutu..Mufeeda da Mariam baki har kunne se dadi suke ji suma sun zama uwaye wau...ai nan kowa ya fara rigay2 san amsarshi .. Hum oga kam shafawa idonshi toka yayi keme2 ya ki bawa kowa . Fulani cikin fada tace kasan baza mu shirya da kai ba inde har haka zakayi ko . haka lokacin da'aka haifi MUNIRA ka hana kowa ganinta bare daukanta ...to wannan karon kam bazan samaka ido ba.. Turo baki yake kamar karamin yaro shi adole anyi mishi fada aman still yaki basu shi... Mahmud ya lallabashi da kyar dan har an fara kiran sallah asuba ...badan yaso ba ya bawa Fulani shi se waywayen yake .... Suna dawowa direct ya nufi amsar danshi su fulani kam se kallon ikon Allah suke shi irin kunyar nan ma ta yan fari baya nuna wa....har sha biyu na safe ba'a fito da Maysam ba tana dakin hutu ya hana kowace nose shiga inba shiba ...fulani ganin har sha biyu yasa tace ni Murad ina dauther nane ko zamu iya ganin ta .. Babu kunya yace Momy ta gaji dayawa fa shiyasa na mata allurar bacci ...kawai inta tashi zan muku magana se ku ganta . Ai kuwa fulani ta shiga fada ai so ba hauka bane dazaka hanumu shiga ganinta ... A memakon ya barsu sema yayi kasa da murya yana fadin Momy kiyi a hankali kada ta farka da yake kusa da dakin suke........ Su fulani kam koma gida sukayi dan kimtsa tunda de yaki bari su ganta.. Mahmud ya ce wai ni ya zancen birtday ne ko an fasa ne.. Wata dariya Murad yayi yace wani birtday ai ni yau wife ta cike mun birtday dina tunda ta haifo mun sankacecen yaro ai kuwa kaga birtday ya qare...sede ko na dagashi har ranar sunan yaron ..tunda shima kaga ranar haihuwar mu daya dashi.. Se a hada Mahmud yace to ya kake ganin za'ayi da waccar azulumar ne... Dan danan fuskarshi ta sauya ya dena dan murmushi ma dayake yace walahi badan Dady yace na bari ze dau mataki ba da ni kade basan irin hukunci dazanyi mata. .ai ita so tayi ta kashemun mata da babyna to kuwa walahi ina me tabbatar maka dana rasa daya daga cikin su ita ma da ta bisu ...dan hukuci sak na addinin misulinci za'ayi mata. ..yanda ta kashe da gangan to itama jininta ya halasta.. Nan suka ci gaba da hirar su wanda kusan duk akan Maysam ne da babyn Dad da Mom kuwa tunda suka koma gidan hankalinsu ya kasa kwanciya gaba daya son yaron ya shige su bare da suka ga tsananin kamar shi da sweetbabyn su...dan ita Mom taso ma taga matar Murad din nan data haifi me kama da diyarta ... Bayan sallar azahar Murad ya shiga dakin da Maysam take da babyn a hannu...aka koyi sa'a ta tashi sede da gani bacin be ishe ta ba...ganin shi yasa ta sakar mishi da murmushi ... Matsowa yayi ya kwatar mata da babyn kusa da ita .ta kurawa yaron ido .. doko mata brush yayi bayan ta gama ya hado mata tea me kauri tasha dan dama ya tanadi kayanshi a dakin jiran farkawarta kawai yake .wani irin farin ciki su ji su duka sunma kasa furta komi kawai sun zurawa babyn ido ..... Can Murad ya rankafo ya sumbaceta a goshi yace na gode my lovely Maysam kin gama min komi kin haifamin yaro me kama da sweetbaby ..sede ince Allah ya saka miki da mafifici alheri. Allah ya biyaki da aljannarsa ma daukakiya .... Ita kanta maysam din wani sanyi dadi take ji yana shigarta bare inta ga baby wai fa itama yanzu uwa ce...se kuma hawaye shar2 ya fara zarya a kumatun ta . . Hankalin Murad ya tashi ya shiga tambayar menene ?ina yake miki ciwo.?duk yabi ya rude . Shafa fuskarshi tayi da hannuta tace ina kukan rashin mahaifa nane ,?ina tunanin wani irin laifi nayi masu da ta barni ne?a yanda naji wahar haihuwa yanda take bana tsammani ko shege ka haifa zaka iya jefar dashi........ To fa gaba daya kan Murad ya kulle ya shiga duniyar tunani tomi Maysam tke nufi ne..... Ganin hka yasa Maysam fadin am sorry babyna yau birtday dinka kaga ko happy birtday banyi maka ba... Kara rankofowa yayi yace wani happy birtday bayan baban happy da kika mun har da gift din dakika bani.. Cike da mamaki take kallonshi tace ni yaushe na baka,.. Dariya yayi yace to ina nufin kukan babyn mu lokacin daya zo duniya shi ya fanshi happy birtday dinki ..gift kuma haifo min shi da kikayi ya fanshe ki dan ''ce le plus meilleur cadeau que tu m'as donné'' Murmushi tayi tace kai kam Wani lokacin baka rabuwa da kayan dariya fa.. Se kuma tace ina su Momy ne ... Lakice mata hanci yayi yace se yanzu kika tuna da su ..to na sun tafi gida .dan kada su tadake tun dazu suke son su shigo aman na ki bari har suka gaji suka tafi.. Waro ido tayi kamar zatayi kuka tace haba baby Momy din nide gaskiya baka mun dede ba .....nide kace su shigk na ganta itada su Mariam Nan ya shiga lallabata harde ta koma bacci dan dama ba wani isarta yayi ba... fulani da Mom kam basu sake koma wa ba se bayan sallar la'asr ..lokacin Murad bayanan ya tafi masallaci dan haka suka shige dakin da Maysam take tana baccinta bil hakki da gaskiya .... Ai kam Mom tunda ta dora idonta akan Maysam ta kasa daukewa kai ko motsi ta kasa yi se nuna ta da takeyi ... Fulani na ganin haka hankalinta ya tashi dan tsoron ko ciwonta ne ze tashi... Mom ta fashe da kuka tare da fadin walahi wanan MUNIRATA ce .. Dam gaban fulani ya bada aman tunawa da kusan kullum haka Mom din take da taga me dan kama da Maysam din kawai seta rikice tace itace yasa ta sauke ajiyar zuciya ..tare da kamo hannu ta suka zauna aman idon Mom kyar akan Maysam ko kiftawa batayi ... Fulani tace kiyi hakuri wanan yarinya tare fa da Mahaifinta suke shine wazirin masarautar nan ma.. Se kuwa ta fashe da kuka wanda yayi sanadin tashin Maysam .... Ganin fulani yasa ta saki murmushi tare da fadin Momyna.. A tare suka dago kai suna kallonta .. Itama Maysam din gabanta ne ya fadi ta kurawa Mom ido ...se kawai hawaye shar3 da babu dalili suka fara zarya a fuskarta ..wanda ya dada tada hankalin su Momy .. Mom tace dan Allah ki barni na duba jikin ta a bayan Munira tanada wani tabo da aka haifeta dashi har su biyu se kuma bayan guiwatar nan ma akwai tabon konewa da tayi wanda kina tune da shi lokacin da aka zubawa Murad abinci ta fard'o miyar ta zube mata a kafar... Itade Maysam kallonsu take tama kasa cewa komi .aman gabanta se fat2 da karfi yake dan duk abunda Mom ta fadi tana da shi... Nan Mom ta miki ta isa kusa da Maysam din na kafar ta fara duba se gashi nan.Mom ta saki wani kuka ta ma kasa duba na bayan.. Fulani ta taso ta buda bayan Maysam din sega tabon nan a bayan ai kuwa atare suka rugumeta suna kuka Mom na fadi walahi itace diyata ce Munira Alhamdulillah yau Allah ya bayyana mun ita ..😱😱🤧😳 A bangaren Murad kuwa bayan sallahr asr ya nufi gidan dan yin wanka yana shiga yaci karo da kayan da Maysam ta zubar ..sede a bisa kujera suke ..da sauri ya dauke su yana kallon su ..tabbas wanan sune ajikin sweetbabyn shi lokacin data bata shekarun da suka fice.. Yace to mi yakawo su nan gidan ?waya kawosu?Kanshi ya dau caji yama rasa irin tunanin da ze yi ... Can maganganun Maysam na dazu suka fado mishi . be gama tuno su ba ya tuna da zancen ZOBEN ...ai beyi wata2 ba ya koma asibitin .tun yana sauri har ya gama da dan gudu2 likitocin se kallon ikon Allah suke .. Direct dakin ya shige lokacin Mom na fadin itace diyata MUNIRA .😨... ras2 ,dam2, fat2 zuciyarshi ta bada ya sankare anan ya kasa motsi ..😅😆😂 Ina ganin haka nima na sankaren da birona ...ku bari har na dawo dede zan karasa muku😝😝....... Se mun hadu a 2nd last page.in sha Allah Ina sonku irin sosai din nan❤❤😍😘😍 Fasma ce🖊(yar mutan zinder) [16/09 à 00:07] FASMA😍: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊 ( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ ) 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹 S.W.A✍ 🇳🇪Story&Written by *FASMA* 🇳🇪 *STAR WRITER'S ASS* Kungiya daya tamkar dubu ~Home of special&extraordinary writer~ hakika ina alfahari da ku Ubangiji ya qara hada kanmu ina sonku irin more totaly nan.. .. Godiya me tarin yawa zuwa ga tare da gaisuwa ga ya grup din: HYPE HAUSA NOVEL BOOK SKIPPER H.NOVEL NUCEE LUV N HOUSE A shafin Facebook kuma ban girmar gaysuwa zuwa ga yan: HAUSA YOUNG NOVEL JUST HAUSA NOVELS KHALISSAT KHAIDAR HAUSA NOVEL ZAYNABBAWA NOVELS HAFSAT HAUSA NOVELS(H²) KINGBOY ISAH HAUSA NOVELS LINAH NOVELS TAURARON(HAUSA NOVELS)BY HASSAN A2 TG..ETC WRITERS dimu kuma ban manta da kuba Alherin Allah ya kaimu a duk inda kuke Allah ya kara daukaka hazaka da baseera JINJINAR ban girma gareku musaman ma: ZEEQUEEN👸 MIMSQUEEN ARFAT ZEINAB IDRIS MOMYN MUFEEDAH UMMU USMAN FATIMA USMAN HAFSAT MAMAN SHAHID ARPHEETAH NAINA AISHA( NANAS) ZEEBELLS UMMU USWAN ASMALUV LISSA MIRA(MAMAN WALEED) ANSHOLLY MEELAT MUSA ZEE MAKAWA SAJIDA DR GITAL ASMA BAFFA SADNAF YUSUF KING BOY ISAH ETC... Dedicated to all my fans😍❤ina yinku fans irin more totaly &unconditionaly din nan❤❣💕💞💓💗💖 🅿 113__114 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 ```Manzon Allah (SAW)yace''ku kyautata wa iyayenku sai ya'yenku su kyautata muku. Hakimu ne ya rawaito shi``` [15/09/18 à 23:00] Ras2,dam2 ,fat2 zuciyarshi ta bada ya sankare anan ya kasa motsi.......... Ita kam Maysam ganin shi ya sa ta fara kokarin kwace kanta ..dan ita bata san wacece Mom ba kuma gashi tana fadin wai itace diyarta MUNIRA .ga kuma irin rikon data yi mata irin na babu me rabani dake din nan ne....gaba dayan su kuka suke ..sude su Fulani kukan farin cikin ganin ta ne suke yayinda ita Maysam ta ma rasa na miye takeyi .... Can kamar wanda aka cikara ya dawo da hankalinshi ai da gudu ya isa jikin gadon ..ko takan su Mom bebi ba ya kama hannunta yana duba ZOBEN ai kuwa abunda ya gani ya dada daga mishi hankali nan ma seda ya sake sandarewa din ..dadi, farin ciki suka sike shi har yayi suman tsaye na hucin gadi . Tuni hawayen farin ciki suka wanke mishi fuska a hankali ya ce Alhamdullilah Ala kulli halin ....Alhamdullilah yau SWEETBABY NA ta dawo garene tsawon lokaci .lallai dan Adam baya fidda rai daga rahamar Allah ..yaude gani ga babyna...Mom da Momy suka saki Maysam suka jiyo suna kallon shi fuskarsu ta kasa boye irin farin cikin da suke .. Ai kam kamar me jira ya rumgume Maysam data ke binsu da kallon mamaki dan bata gane komi ba..bata gama mamaki ba seda taga Murad ya saki kukan kuma gashi yana mata dariya tare da tatabata dan ya tabbatar da ita ce ..ga sabbatun dayake na sweetbabyna ..yana fadin walahi Momy itace Babyna ce wayoo ni Allah ...ji yake kamar ya meda ita cikin jikinshi ya huta yama rasa mi zeyi mata .. Maysam tace ban fahimce ku ba ..pls ku min explain what happen ..ku fahimtar dani .. Aman cikin su babu wanda yayi kokarin bata amsa ... Ganin abun bana karewa bane ya sa Maysam rike fuskarshi da hannuta biyu ta zuba mishi idonta masu saka cikin nutsuwa ..ai kuwa kamar asiri Murad yaji wata nutsuwa tana shigarshi a hankali2 ..Maysam tace pls mike faruwa ne ? Ajiyar zuciya yayi tare da lumshe idonshi yace zan gaya miki komi aman ba yanzu ba ina so se agaban kowa.... Itakam sun barta cikin duhu .....Murad kam ya manta da wasu su Momy na dakin yace wannan nakine sweetbabyna kafin Maysam ta ankare ya shiga kissing dinta kamar wani maye .. Wuf Mom ta fice adakin dan kunyar da Murad ya bata dukda bata gaji da ganin tilon diyarta ba.. Fulani kam sakin baki tayi tana kallon salon irin rashin kunyar Murad wanda yake shirin kwantar da Maysam din datake kokarin kwace kanta ganin fulani na dakin.... Fulani ganin fa da gaske yake yasa tace Murad2 aman yanda kasan da kurma take dan bayama jinta.. Ta sake cewa MUJAHEED2(😱Mujaheed kuma ?waye Mujaheed din?..to ku biyoni de😅 )..se asan nan ya dawo hankalinshi jin sunan da har ya manta danashima ya dan sakin Maysam yana sosa kai aman be bari ba suka hada ido da fulanin ba.. Fulani tace to zo ka huce ta bawa mutune wuri ka barta ta huta .. Gam ya kara rike Maysam yana kallonta wacce ta sunnekai saboda kumyar fulani tana kuma kokarin kwace jikinta da nashi.. Humm a memakon ya saketa sema ya kara matseta a jikinshi hawaye shar3 yace pls Momy kada ki rabani da ita walahi duk wani distance din daze sake shiga tsakanimu yana tafiya ne numpashin na......pls Momy ki tausaya mun ke kanki shedace kan irin son dana ke ma babyna ...da irin wahalar dana sha lokacin dana rasata ..tayaya kike ganin zan iya fita na barta yanzu bayan yanzu na ganota yanzu kam duk wani motsinta yana tafiyane da bugun zuciyata ..tayaya zan iya fita bayan shekaru dana dauka ina jinyar sonta a zuciyata wanda har yau be ragu ba dede ga kwayar zarra.. Fulani kam bata yi mamakin kallanmanshi ba . dan inde akan babyn shine zeyi fiye da haka ma ..sema tausayinshi daya kara lullubeta ..ta hada su duka ta rumgume tace Alhmadullilah Allah ya albarkaci rayuwar aurenku ya baku zaman lafiya ...yau akwai bidiri a gidan nan Babu kumya yace Ameen Momyna .... Momy ta sake su tace bari na bada sanarwa familly's meeting yau ..kaga se a warware komi.. Baki har kunne ya dagawa Momy kai ..ta fice se waywayen Maysam din take.. Itada Mom dake bakin kofa suka fice fada. Yayinda mamakin Maysam ya kasa boyuwa ganin irin farin cikin da Murad yake ...ga wani manne mata daya ke karayi .. Zata yi magana Suka ji kukan jaririn dake kan kadon su na jarinrai..da sauri ya daukoshi yana kalloshi ...cinyarta ya dora matashi ya bata dabino dan kasar MADINA ta tauna ta tsarta mishi ruwan abakin... Bayan tayi ne yace to ki bashi abinci shi yunwa yake ji ... Seda ya kawo mata ta wankeshi tas sanan ya dedeta mata yanda zata shayar dashi din 😂Maysam ta aza shayarwar da dadi ..da hanzarinta ta fiddo ta sa mishi ai kuwa babu shiri ta zare tana yarfa hannu tace wayyo ashe da zafi ... Murad ya kunshe dariya dan kada ta ki ba babyshi nonan yasa ya shiga lallabarta ....da kyar ta yarda ta bashi ..to sabuwar haihuwa ina wani ruwa ai kuwa da zafi ya isheta zareshi tayi ...ai kuwa shima ya bare baki yana kuka ...babu yanda Murad ya iya se ruwa ya bawa yaron ya koma bacci.. Bayan sallar isha'i aka shirya family meeting din gaba daya kowa ya hallara kama daga sarki fulani .Mom da Dad,Murad Mahmud M.Musa da kuma triple M wato su maysam ..da kuma babynta Etc.. Su fulani kawai suka san da zancen dan haka bayan an bude taro da addu'oi sarki ya bukaci Fulani datayi bayanin meeting din gaggawar data saka ayi ..nan fulani ta shiga yi musu bayani komi daki2 wanda tunda aka fara zancen kowa ya zurawa Maysam wacce take makale a jikin Murad yaki sakinta tayi dan nesa dashi ma ido ciki da al'ajabi wanan lamari ..dad kam tunda ya dora idonshi akanta ya tabbatar da jinin shice dan ga kamaninta nan dana matarshi karara . farin cikin shi ya kasa boyuwa wanda har seda ya taso ya rumgume Maysam din yana me jin dadi dawowar tilon yarshi Mom ma ta kara rumgume Maysam suna masu yiwa Allah godiya .. Sarki ma farin cikin dayake ciki baya misultuwa ..gyaran murya yayi tukon su Dad suka dan sassauta rikon da suka yi mata ..itade idon wannan shine ta rasa gane mike faruwa ... Da sauri ta koma kusa da Murad kasa2 tace pls yaya wai mike faruwa ne ban fahimci su Mom ba kan cewa ni yar su ce .. Kuma kaima se wani kirana da sweetbaby kake pls ka fahimtar dani sega kwalla ta cika mata ido ....zeyi magana sarki yace yaki nan yata zo nan... Jiki ba kwari ta isa wajenshi shima rumgumeta yayi yana me jin dadi dawowarta ..sanan ya zaunar da ita kusa da shi yace bari na baki labarin komi yanzu. Kowa ya nutsu dan jin abunda sarki ze fada wanda manya ciki sunsan komi.. 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 Asalin su Elh MUJAHEED shine Sarkin na takwas a wannan masarautar sarki ne me adalci da gaskiya yanada mata ukku biyu daga ciki Allah ya musu rasuwa kuma su Allah be basu haihuwa ba se matarsa ta biyu me sunan sarauniya Haj MUNIRA ita Allah ya arzuta da y'aya har biyu dan ba'a jima da yin aurensu ba Allah ya bata ciki wanda bayan ta haihu aka saka mishi sunan MOUSTAPHA wato ni. Se kuma bayan yan shekaru da dama ta kuma sake haihuwar mace wacce aka sawa sunan MAYMUNA wato Mom ...muntashi cikin jin dadi kasan cewar mu yayan sarki garin .. Nayi karatuna a kasar waje wanda bayan na gama ne na dawo sarki Mujaheed yayi murabus wanda a ranar nadi aka hada da aurena nida MARIAMA wato fulani wacce take diya ga sarkin AGADEZ ..... Shekara biyu Allah be bamu haihuwa ba haka muke zaune tunda munsan Allah ne me badawa..wata rana naje Diffa kaiwa sarkin garin ziyara anan ne na hadu da MADINA wanda mahaifinta ya nuna yana son hada *zuri'amu* (littafin nida Aisha ) .. Banyi kasa a guiwa ba dan ina ganin girmanshi da kimarshi yasa na amince da auren. Ban baro garin ba seda aka daura auren muka tafo tare. Bayan wata ukku Allah ya Arzutar da Fulani da samun ciki murna ba'ama maganar bayan wata tara ta haifeshi wanda ko sunan shi ba'ayi ba Allah ya amshi kayanshi wanda kunsan Madina ce tayi sanadin hakan .. Haka muka zauna cikin su babu wacce ta sake samun ciki har mukayi shekara hudu Fulani ta kuma samun wani cikin wanda bayan ta haifeshi aka samishi sunan kakanshi MUJAHEED wato Murad .. ..tun haihuwarshi be kuma samun wata ishashiyar lafiya ba kullum muna hanyar asibiti ...duk da irin gata dayake samu bare ma wurin Mom dinshi wacce tafi shakuwa da kai dan kusan ita ta renaka hakan yasa ka shaku da ita matuka . inyayi wata rashin lafy . har sa ran bazama ya ta shi ba muke aman daya ke da sauran kwanakina Allah ya tashi kafadashi ....kanada shekara tara akayi auren Mom itada dan sarkin Niamey me sunan Elh MOCTAR wato Dad dan haka bayan auren can aka tafi da ita . da kyar aka rabaku kai daga bayama dole tasa aka meda kai can wurinta saboda irin shakuwarku ...anan ka gamu da Mahmud wanda yake daya daga cikin familyn masarautar...... .bayan wasu watani ta samu ciki duk da kanancin shekaruka aman kana tausayawa mom dinka duk abunda take bukata kafin bayi su mata kai ka yi matashi kamr su yanka fruit etc.. A takaicede tare kukayi renon cikin ...bazan manta ba ranar wata lahadi wanda yayi dede da gobe birtday dinka wanda har paty mom ta tsara maka aman ranar ta tashi da dakuda .. Da asuba dede kiran assalatu ta haifi yarta mace kyakyawa da ita wanda tunda ka ganta kake murna da jin dadi anyi maka kanwa . daukanta ma kam seka ga dama kake bawa wanda kaso ko dad din seya lallabeka kake bashi ita yayinda Mom ta zama yar kallo dan se kaji tana kuka kake badata abata nono....gashi se fadi kake ranar birtday dinku daya dan haka tare zukuna patynshi....dama su yan barka basa ma tarkar amsarta....ko sunan ta kai ka zaba mata na farko wato Mufeeda wai dan kuyi kusan suna iri day shima dad din ya biye maka yasa yayi na'am da sunan aman se mummunan abu ya gifta ana gobe bikin wato rasuwar mahaifiyar mu ~Munira~ wanda ACCIDENT ne SANADI suna kan hanyar zuwa sunan ne ..dan haka akayi suna cikin lami tare da Sawa jaririya sunan MUNIRA wanda kwarai munji dadin irin karar da Dad yayi mana wanda za'ana kiranta Ummi....aman kai kam banda zumburen2n baki babu abunda kake yi wai anki sa mata sunan da kake so ko Ummi baka kiranta dashi ..kai daga baya seka shiga kiranta da SWEETBABYNA.. To fa SWEETABABY de ta tashi cikin gata daka shagwabantata sosai school kawai ke rabaku shima seda lallaba duk wani abunka yakan karene akan Munira tana da shekara daya kuka zo ganin gida nan ka bawa kowa mamaki dan kuwa cewa kayi wai aure kake so kuma Munira za'a aura maka harda su birgima dan ance maka a'a ..... ..ELH MUJAHEED ne ya lallaba ka tare da tambayarka miyasa kakeson aure ..budar bakinka se cewa kayi ai school na hana ka zama tare da ita aman idan anyi muku aure shikenan zaka dena school din kayi renonta. Kowa na wurin seda ya dara ..nan Elh Mujaheed ya bada wasiyar ko bayan ranshi ..ko ba dade ko bajima Murad bashida Matar data huce Munira..babu me ja da hakan dan hakan aka rubuta aka aje..shima dad lokacin be musa ba kuma be nuna kin amincewarshi ba . . .nan aka lallaba ka kan cewa in kana son auren to fa sekayi karatu daganan aka rufe maka rigimar ka.... To fa ko agaban waye da sweetbabyna kake kiran ta baka kumyar kowa .itama bata yarda da kowa se kai .tana kiranka da BABYNA. Bayan shekara biyu Allah yayiwa Elh Mujaheed rasuwa . munyi rashi matuka ... Bayan wasu shekarun biyu lokacin kana ss2 kuma ka dada canza mata suna zuwa MAYSAM koda Mom ta tambayeka ..se cewa kayi ai wani zubin kumyar dad kake Ji shiyasa ...data nemi sanin ma'anar sunan kuma sekace mata Ai Maysam yana nufin SWEET ne ..se kuma itama sunan ya birgeta to tunda ga lokacin sunan Ummi ya goge kowa yake kiranta da MAYSAM din ..se kuma aka shiga shirye2 birtday dinku kai na cikewar shekaru 14 ita kuma 4 kamar ko wace shekara aman wannan karon ka aza rigima kan a nan kakeson ayi muku patyn anyi rarrashi aman a banza dayake abun kaddararene yasa ka kwallafa rai itama kuma yar renontaka ta biye maka kuka hargitsawa Mom da Dad kwanya babu shiri suka tattataro suka zo nan garin koda mukaji dalilin zuwansu munyi musu fada sosai kan biye muku da sukayi .. Anan kuma aka shirya muku wani birtday din banzan kuma mantawa da wanan ranar ba rana birday din da safe wajejan goma na safe Fulani da Mom zasu rabon temako ga kauyikan dake kusa damu kamar ko wani bayan wata ukku2 tasoma bari har gobe saboda birtday aman kuma da ta tuna cewa duk bawan dake karkashin su ya kwana da yunwa sun shiga hkkinshi bayan su suna cikin wadata dan haka saboda birtday bazatayi cancel din bada temakon ta ba ..to itama Mom ta kuke seta bita batayi mata musu ba ...itama Maysam na ganin Mom dinta ta shiga kukan seta bisu ..kai kuma kafarta kafarka dan haka kaima ka bisu .lokacin dazaku tafine ka fiddo wani zobe wanda shine gift din da zakayi wa Maysam sosai ya burge mutane dan iri dayane zoben babbaci kawai nata na zinariya ne nashi kuma na azurfa ne wanda tafiyar su wannan haji ya saka Dad ya sa aka kera musu shi ....ku duka a mota daya kuke ..lafiya kukai temakon..se a hanyarku ta dawowa ne tsautsayi ya afka muku wandan kukayi wani Accident a take dreben motar ya rasu a wurin kukam gaba dayanku an wurwurga ku wanda kuka sume a wurin ku duka ... Nan bayin da kuke tare su suka nemi baku temako ..aman abun mamaki shine batan Maysam ko sama ko kasa ..anyi neman duniya aman babu ita babu alamunta .. Abu kamar wasa aman akayi neman nesa da kusa babu ita ..har kwararu police aka saka nemanta aman jikake shiru ..abu de kamar asiri ..seda aka jera sati anan nemanta aman shiru .....daga baya ma aka tabbatar musu da cewa inde har tana cikin jejin nan to sede wata ba itaba dan akwai namomin daji a wurin da kyar ne idan zata rayu ..shiyasama muka dangana da ita muka dauka da ta mutun.. .to fa nan kuma Murad ya bujiro da nashi sallon rashin Maysam dan bashida aiki se kuka ko kuma ya tisa photonta gaba yana kallo yana magana shi kade .. Kadan2 ya dawo shiru2 yayi bankwana da dariya fara'a da kuma sakin fuska ga mutane se kuma wata tsabagen fada da masifa ..abu kadan bayi sukayi ze saka ayi musu horo me tsanani . school ma ya dena zuwa kullum kumshe cikin kuryar daki ..abun ba karamin daga hankalimu yayi ba ..ga kuma abangaren Mom itama tun da abun ya faro tayi AVC take zuciyarta ta kamu wanda yayi sanadiyar kullum suna hanyar kasashen waje don neman magani...shima Murad da kyar aka lallabshi yayi candy da weak da izinin Allah ya samu ..ai kuwa muka yanke shawarara turashi turashi England ko ze samu damar sakewa yayi karatun shida Mahmud aka turasu dan ya samu ya kula da shi sosai tare da bayi da dogarai ..acan dinma ansha fama kafin ya dan sauko ya fara karatu aman fa bakar zuciyar nan na nan makalle dashi ..abu kadan ze sakashi fushi ......... Se anan sarki ya ja numpashi yace to kin ji labarin ki Maysam *SANADIN ACCIDENT* ne hakan ta faru... kaf palon in ka dauke parent din kowa se sharbar kuka ya ke bama ya Maysam ba da take ganin abun kamar almara ba..wai itace Sweetbabyn Murad daya ke matukar so ... Ashema shi ya reneta tun tana ciki ..se kawai ta sake fashewa da wani kukan wanda Murad babu ko kumya ya zo ya rumgumeta yana lallashi .. Sarki ya bukaci M.Musa dake cike da mamakin wannan lamari da yayi mishi bayanin gameda da Maysam din.. Be boye musu komi ba yayi musu bayani yanda ya sameta ..sunyi matukar mamaki jin inda ya sameta dan da wurin da accident din ya faru da kuma inda ya sameta da tazara sosai Sanan ya basu hakuri kan irin abunda Murza tayi mata ... .. Kowa na daki murna yake bama ya Maysam da ta samu iyayenta yanzu taji kuma irin so da gatan da suke mata ..ba ..an jima nan ana hira sannan ya aka rufe taro da addu'a .kowa yayi bangarenshi cike da jin dadi da farin ciki.... To fa oga Murad ya aza rigimar sede Maysam ta koma bangarenshi da zama dan yaga Mom na son kaita bangaren da suka sauka ..nan fulani ta shiga yi mishi fada ..to wai ma mi zatayi maka acan bangaren ne dan danyan goyon nan ..aman a memakon ya sauko se cewa yayi Momy ai waccar wifyna ce wanna kuma ai sweetbabyna ce kinga it's two person different ..kuma walahi ni banma gaji da ganin ta ba yana yi yana wani matsawa kusa da Maysam din ..ita kanta Maysam din kunya yake bata bare kuma su fulani ...daga bayama girgiza kai tayi tayi ficewarta ... Haka yace shikenan Mom kawai muje can naku bangaren dan nima na kwaura kawai ..Mom kam murmushi tayi dan tasan za'a rina dan zeyi fiye ma da haka din.. A bangarenma seda ya danne zuciyar shi ya basu wuri su kara sanin junan su aman bini2 seya leko su ya koma .. Sha biyu nayi yazo yace to Mom ki ban aron sweetbaby na nima kinga ma dare ya tsala seda safe ko... Mom harda yar kwallarta don ya tuna mata lokacin da suna yara ma haka yake mata da lokacin baccinta yayi zezo ya dauketa koda kuwa mi take mata ..seda safe su karasa ...dan haka bata musa ba ta sallami Maysam din .wacce take ta zumbura baki kan ita bata gaji da Mom din ta ba..haka ya lallabta aman mi ai kuwa jaririn yace besan dare ba nan ya shiga musu kuka abunka da sabuwar shiga itama kawai ta saka shi gaba tana kukan dan bata son ya zatayi da shi ba .. Murad kam banda dariya babu abunda yake mata ..can de dayaga da gaske take kukan yasa ya dau baby yana jinjigashi shima dan ayi se yayi shiru .... Ta kalleshi tace laa only one ya akayi mi kayi mishine ya dena kuka..dariya yayi yaceai ke ya biyo a kukan nan dan kwana kike kina kuka kuma ko ambaki nonon ba wani shiru kike ba ...kuma yanda kika ga yana kuka bakinshi na karkarwa to kema haka kikayi . Rufe fuskarta tayi tana fadin kai babyna banda sharri fa.. Wani lumshe ido yayi yace 'repete le encore' Tace mi din?Baby? Lumshe idon yayi yana murmushi yace Sweetbabyna ina sonki fiye da raina ...ya hada su ya rugume su duka.... Daga nan nima nace bari nayi musu sallama ..ko ba haka bata fans?😆😆😆😜😜.... Baride na dan kara samunku labarin.. Maysam tace baby to miyasa lokacin da aka daura muna aure ka nuna mun tsana da hantara inde har lalle ina kama da sweetbabynka a lokacin .. Yana mirmushi nan nashi me kashen yan mata yace to ai ko lokacin tsananin kamar ku ce ta saka nayi tayi miki haka dan duk wani kallon da zan miki ina kara tuno da itane wanda yke barazanar tada mun da ciwo na ne..bare kuma fatar jikin mu ta hade senaji zuciya na ta fara Kidan Zut3 shi yasa kika ga bana iya miki muso kan abubuwa da dama na kanyi loosing din controle dina da zarar idon mu sun sarke da juna ..ina sonki da yawa sweetbabyna pls idan kinga zan kauce kiyi kokarin nunamunu hanya dan da rabin zuciya na ne kika bayae gurbin aman yanzu kam gaba dayanta ''elle t'appartienne '' aman am sorry da duk abun da na miki a ba.. Bata bari ya qarasa ba ta hade bakinsu tare da girgiza mishi kai kusan raba daren sukayi suna hira daga karshe ya rumgumeta sukayi baccin su Ranar suna yaro yaci sunan MUHAMAMAD anyi shagali iri2 ..da walima kai abun ba'a cewa komi se san barka ku ma de kunsani base natsaya baku labarin bikin ba .. . 🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹 Wai ina labarin Inna Murza ne? Allah ba azalumin bawa ba Murza de ta sake rasa kafarta gudar data rage mata ..yayinda bugan kan da tayi ya haddasa mata tabuwar hankali .hauka turben takeyi (hum jama'a mubi duniya a sannu kana abun kirkin ma ya ka kare bare kana shuka sharri adoran kasa. ..kungade Murza duk abunda tayi nufin su Maysam dashi shine ya kome mata ..dan tayi niyar meda Maysam gurguwa idan baku manta ba aman Allah ya qareta ..taso haukata su nan nan ma batayi nasara ba ....komi zakayi ka yi tawwakalli da Allah ....duk abunda kakeyi ya kamta kasani Allah yana jinka kuma yana ganin ka ..sanan kaji tsoron Allah a duk inda kake ..Allah ya qara karemu mu da zuri'armu baki daya ameen ya kula shiryar da masu hali irin nata) .an kulleta anan cikin masarautar bisa umarnin Maysam dan ita tace ta yafe mata kuma ta nemi alfarmar da abarta nan dan kada ta shiga duniya..Murad ba haka yaso ba to aman Maysam ta zartar da hukunci babu yanda ya iya . sede muce Allah ya shirya masu shiryiwa ya sa sa su gane ga duk masu hali irin na Murza da makarabanta wato waziri da Madina.. 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 To fa abun na oga Murad ba sauki dan fa ya zama mijin tace ko kuma ma mijin kan tace dama kusan zuciyarshi a rabe biyu take to kuma yanzu Maysam ta mamaye ta duka tunda yasan itace sweetbabyn shi.. Yauma kamar kulum suna zaune a palon fulani ..ya wani tankwashe kafafu yana gyara madarar da za'abawa littlebabyn shi dan baya bari bayi su taba wai acewarshi yafiso suyi renon kayansu da kansu yayinda da Maysam ta saka babyn tana mishi wasa kamar wani babba ...Mom ta fara yi mishi fada akan ya dena sake ma Maysam da yawa haka ..tayaya tana zaune ace shi ze kada madara da kanshi.. Ya wani marece yace kai dan Allah Mom bana son ta wahala da yawa ne walahi a barta da shayarwarshi kade ma jiki take ji ..ita kam Maysam kanta akasa dan ita kanta tana mamakin wannan kaunar da Murad yake nuna mata ..Fulani de batace komi ba. Harkokin gabanta ma take Mom ta taba hannu tace wai anyya kana cikin hankalin ka kuwa miye na wahala anan wai ayya ma zaka iya mulkar kasar nan kuwa nan gaba ? Yana dariya yace kai Mom wani mulki kuma ai bazan iya barin Maysam dinta ba dede da yan mintuna bare aje ga zancen awwanin da zanyi a fada ..tab ai da kamar wuya .. Su duka sakin baki sukayi suna kallonshi ..shikam ko aka ya qara da cewa kunga ma nan da week zamuyi tafiyar mu England abun mu.... Se a sanan fulani tace ka tafide . itada ko arba'in bata yiba ina ita ina zuwa England.. Wata faduwar gaba ta ziyarce shi babu shiri har seda ya dafe baki na karkarwa yace Momy karatun fa? Walahi satin sama suke komawa kuma kinga can da nan ba daya bane... Jim Fulani da Mom sukayi suna nazarin maganarshi .. Fulani tace wai kana nufin da danyan goyon nan zata koma ..to kuwa sede in tare zamu .. Daga Murad har Mom seda suka dara .. Mom tace kina da aiki kam ..Momy de shiru tayi tana tunani dan ba karamin tausayawa Maysam take ba duba ga yanda Murad din ke kainenaye ta taso ace se tayi arba'in zata koma to aman ya ta iya ..a ranta tace kada fa yaje ya kuma dibgamata wani cikin da danyan goyon nan (😂😂😂ni kuwa nace to mi naki a ciki ai matarshi ce ki barsu abunsu kawai)ita knta Mom din bataso tafiyar yanzu b badan komi ba sedan basu jima da sanin juna ba taso ta dan jima ko sa shaku. Sosai ...dan haka suka kara himma wajen gyaran yarta su Haka kuwa akayi sati na zagayowa gaba dayan su suka daga se England wannan karon har da Mahmud dan yace kafar mtarshi kafarshi... Tunda sukaje suka meda hankalin su ga karatun su kun de sansu ai sede wannan karon kowa yana gidan shi ne dayake Gidan da Murad yake bare biyu ne se Mahmud da matarshi suka shiga dayan.. ..haihuwar Maysam da kwana 23 ta samu tsarki ai kam abunda Momy ke gudu shike shirin afkuwa dan Murad kam yanzu ya koyi jaraba babu safe bare ran da kowani loakaci ya medashi lokacin pratical ko a kitchen ya iskota to fa se yayi paratical a kitchen din..don ma ina kokarin tsayawa na kashe gaz din dayayi musu gobara ai😆😉da Maysam tayi magana se yace ai na safen na wify nane yanzu kuma na sweetbaby ne tun abun yana damunta har ta sakin ranta de ..yauma bayan komi ya lafa suna makale da juna Maysam tace baby wai ya akayi sunan ka ya koma Murad ne bayan Mujaheed ne... Seda yayi murmushi yana shafa kanta yace sunan ya samo asaline bayan batarki wato lokaci da aka medo ni england saboda son da kaunar dana ke miki yasa na cire harufa biyu na fakon sunana ''MU ''sena dauko harrufa na karshen sunanki''RA'' sannan na saka 'D'din karshen sunana se ya bada MURAD kisan don mi na zabi yin haka. Tana wani kara makalle shi dan wani sonshi take ji yana kara shigarta ta girgiza mishi kai .. Yace na farko abunda yasa don ina son kullum na kasance inada abun da ze tuna munke ne ..a duk lokacin dana ji MURAD ina tuna harufan sunanki dake ciki ..na biyu zakiga na sa RA din atsakiya to don kin kasance kece zuciyata shiyasa na sakaki a tsakiyar sunana kamar yanda zuciyata ke tsakiyar jiki....se kuma na ukku ma'anar sunan dan MURAD yana nufin MURADINA (mon choix)to kinji yanda akayi sunana ya koma Murad..kuma wani lokacin zakiji su Mahmud na kirana da M² to shima yana nufin MUJAHEED & MUNIRA kar yanda yake a cikin Zoben mu Wayyo dadi kashe Maysam kai ita bata masan dami zata saka mishi kan irin son da kaunarta ta da yake dan ta tabbata ko makawa babu yafita sonta ..... Bayan wata shida naga su Mufeedah se jan kafa ake don cikin su ya shiga watan haihuwa ....ai kuwa cikin satin su duka biyu suka sambalo yaran su duka maza zo kaga Murna wajen su Mark baki har kunne ..dole anan akayi sunan dan ana tsaka da school babu damar komawa gida....a tsakanin su sukayi yar walimau se yan Uwa da suka zo daga Niger dan sunan ...anci ansha kowa yana cikin murna da jin dadi yara sunci sunnan kakkaninsu na wurin uba dan Mahmud sunanshi MUBARAK yayinda dan Mark sunan shi MANSUR ..inka dauke Maysam dake kwance ba lafiya ...har su Maryam na tsokanarta wai kode wani ciki ne .... Batade ce musu komi ba dan ita kanta abunda take zargi kenan aman dan ta kwantarwa da kanta hankali se ta ce ai tana shayarwa kuma ma ai malaria ce.... Kai abu de kamar wasa jiki yaki yin sauki shide Murad ya gane komi sede yana son tabbatarwa dan haka yau tun safe suka jeya gwadata..ai kuwa abunda fulani ke gudune wato de Maysam na dauke da cikin wata daya da yan kwanaki ....Maysam suman tsaye tayi ..bazatce bata son cikin ba aman duka duka ma danta watanshi shida ace kuma yanzu tana da wani cikin ... Murad kam Murna kamar mi ..ya kalleta yace ya naga bakya murna ne da cikin ko bakya sone.. Da sauri ta girgiza kai sega hawaye shar3 tace yanzu duka ma fa Muhammad watanshi shida ace nayi mishi kane ni walahi ina tausayin shi.. Ajiyar zuciya yayi yace inde wanan ne kada ki damu ki ci gaba da bashi nono akwai maganin da zanki baku komi bazeyi ba yana cika shekara daya semu kaywa Mom Ko Momy yaye ko tunda yana cin abincishi? Dafe kirji tayi tace baby na shiga ukku bade Momy ba dan walahi fada zatayi dan seda ta gwasileni gashi yanzu kayi mun wani cikin dama Momy ta fada.. Haba mi zeyi inba dariya ba seda yaga tana kuka da gaskenta tukon yayi shiru tare da lallabata ya kuma sheda mata se akaishi wurin Mom.. Haka kuwa akayi yana cika shekara guda lokacin sun zo gida vacation sun yanke ranar birtday zata yaye shi ..su duka ukkun ranar birtday din dayane dan haka sosai aka shirya wa wannan birtday din har su Mom seda sukazo ..anci ansha sosai .da daren ranar suna zaune a daki su hudu da cikon Muhammad din na biyar Murad ya dauko jakar kayan Muhammad ya dau keshi da ga cinyar Maysam din ya bawa Mom yace Mom ga da nan mun baki renonshi dan yau aka yayeshi ... Ba Momy ba har Mom kallon mamaki take binsu dashi..tayide karfin halin cewa da wasa kake yaro duka ma shekara daya yau kace kun yayeshi a ina kuka taba jin haka ... Maysam kam tuni tayi hanyar waje dan tana jin kunya dan tasan Murad se ya tona asirin... Ai kuwa bata kai ga huta ba Mom tace dawo ki zauna ... Sum2 kamar munahuka ta dawo ta sadda kai .. Momy tace Murad3 walahi ka fita a ido in rufe bana son shashancin banza daga kai har ita kuruciya na damunku walahi.. Sassauta murya yayi yana bawa fulani hakuri tukon ya sanar da ita cikin Maysam din.. Gaba dayansu sakin baki sukayi suna kallon su ..Momy tace haba ni kam daman nasan za a rina koda kuka zo nayi zargin cikin to senaga ita me jariri se kuma tayi shiru da ga haka basu iya cewa komi ba se addu'ar Allah ya raba lafiya sukayi musu.... 🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹 Five years later(5ans apres) Yau ake walimar rantsar da sabbin doctarorin anan jami'ar England inda triple3 aka basu lambar yabo ita Maysam Cardiologist tayi ,Mufeeda gynecologist yayida Mariyam tayi pediatrist...aman fa abun mamaki su duka da nan cikin su kui2 kamar hadin bakin ....duk sun kara girma sun zama wasu mayan mata bulbul dasu a raina nace kai mazajenku sun iya kiwo fa😉😜 Murad ke rike da yaransu su ukku babba de na gane Muhammad se kuma twinx mace da namiji da kadan ya fisu tsayi wanda naji yana kiran su MUHSIN DA MUHSANA yaran bade kyauba sun kuwa sha alkyaba . Mark ma yana rike da yara biyu Mansur da kuma wata beauty baby me sunan MANSURA ..Shima Mahmud din yana rike da Mubarak da kuma wata baby MUSULMA..... kai yaran de kamar na sace su na gudu dasu😆 Gaba dayan su suka tattaro suka dawo kasar su dan sunce suna kishin kasar yayinda zasu fara aikinsu anan cikin asibitin masarautar bisa alfarmar da Maysam ta roka wajen su.....walima ga garuma aka shirya musu wanda kuma a ranar ne za'ayi wa Murad nadi dan sarki yayi murabus acewarshi ya tsufa ya barmishi.. Tode MURAD YANZU shike mulkar garin yana iya kokarin shi ganin yayi adalci da temakon talakawonshi ...sede abu dayane yake damunshi rashin zaman gida kullum yana fada ..shikam ya fiso kullum yaji shi kusa da sweetbabynshi ..korafi kam kullum tana shanshi dan se dare yake samun sararr kasancewa da ita se kuma inya saci jiki daga fadar ya lekata.. Yauma kamar kullum da dare suna zaune suna hirar wanda duk yawonci korafin ne ita kuma tana lallabarshi ..yana famar rumgumeta ta matsa tare da nuna mishi yaron su da suke kallon tv..dan muskutawa yayi yayi kasa da murya cewa yaron nan fa suna san shiga hakki shi..dariya tayi tace kadeyi a hankali dan yaron nan wayo ne dasu ..ba jima ba ma suka yi bacci anan dan haka ta kira bayin suka kaisu dakunan su ..komi suka kashe suka shiga dakunan yaran suna tofe su da addu'a sannan sukayi nasu dakin seda suka kimtsa komi suka bi lafiyar gado ...kamar wani abun arziki Maysam tayi firgit ta tashi zaune . .shi kanshi Murad din seda ya tsorata yace wife lafiya kode haihuwarce? Girgiza kai tayi tace a'a. Daman wata tambaya nakeson yi maka ne ... Umm yace dan yana wani shahsafata .. Maysam tace wai dan Allah dole ne seka kara aure ?dan naji cewa wai sarki dole ne ace akkala yana da mata biyu kwalla harta cika mata ido .. Murad dake kokarin kwantar da ita yace pls ki bar maganar nan waya fada miki ne. .. Maysam tace a'a nide ka amsa min tambayana .. Shi abunma dariya ya bashi yace a'a ni kam banida ra'ayin mata biyu ke kade ma kin ishen kaina baze iya daukar hayaniyar mata biyu ba ke ke kade ma a matsayin biyu kike da Swetbaby da Maysam dita sede ko kwarkwar zanyi😎😎😅. Zumbur Maysam ta mike tace what ? Yanda tayine seda gaban Murad ya yanke da sauri yace share zancen nan wasa fa nake miki ke kade ma kin isheni rayuwa so pls baby mu bar maganar nan haka ..kinga wani ikon Allah babyna SANADIN ACCIDENT na rasaki kuma SANADIN ACCIDENT na kuma samunki dag haka ma kina ba kanki amsa cewa dan ni akayi kuma nima haka kai Allah abun godiya daganan kuma Murad ya shiga koyar da ita sabon pratical ina ganin haka nace to nima baru na barku haka ya isa ko .. Se min hadu a sabon littafina me zuwa SO SOON insha Allah.. TAMMAT ALHAMDULILLAH . anan na kawo karshen wannan littafin kurakuren dake cikin shi Allah ya yafe min.. For correction or comment:+22799951593 Godiyar DA gaisuwar ban girma zuwa ga : Yayana MUJAHEED YAYA HAYAT(admins of admins) Ya AHMED GUMEL YA YUSUF IBRAHIM ABDOURAHAMAN AA DBOY ZAHRA HADIZA TUNAU MAMAN SHUREIM MAMAN AFNAN BAN manta da kuba *RAMATOU,LITTLE BALKISSA,SAMIRA,ZARA.DIZO,SARGA,N.FATCHIMA,SARAH,SUMMAYYA,MAMAMAN SS,MAMAN IMAN,UMMI,DALA,HAFSAH NASSIR,RAMATOU &FATIMA MUNICIPAL,SAFARA,KADI,NAFISSA,SALAMATU,HALIMA,FATIMA HASSAN,HAJO,MEENA,SUMAISU,DR FATEE,GARKUWA,UMAIMA,ZAKIYYA ABDULKARIM,SALIHA,ZEINAB SULEMAN,HASSAN,SAKINATOU,MAMAN ISLAM DA DJAMILA,MARYMA,AYSHA,HAIRAT,MAMAN JANNAT,UMMU AIMAN,PRETTY.IRSHAM,MAMAN JIDDA,AISHER DZ,DADY'S GIRL,ETC...*. kai masha Allah kunada yawa fa wanda basu ji sunan su ba kumun afuwa kuna rai ina yin ku irin more totaly din nan❤😍😍😍😍😍😍😍 Subahanakallahuma wa bi hamdika Ashhadu an lailaha illaha iila anta astagafiruka wa atubu ileyka... Ni FASMA NACE INA YINKU ❤❤❤.. TAKU HAR KULLUM FASSOUMA YAR MUTAN ZINDER.